ƁATACCEN YANAYI CHAPTER 10

ƁATACCEN YANAYI






CHAPTER 10




Suna gama waya da Yasmeenah ta wuce closet dinta ta ciro wani shirt da black trousers to saka. Sai da ta gama shiri tsaf kan ta dau box dinta ta fara arranging kayanta. She has decided she’s not spending a night again a gidan Hamma Suraj, gida zata koma. She’ll stay for like 2 days a gida kan ta wuce gun Yasmeenah, zata mata surprise visit just to clear her mind off things and dodge her brother too. Sai da ta tabbatar cewa both Hamma and Zubaidah sun wuce various places of work dinsu kan ta fito ta wuce. Tana zuwa gida bata zauna ba, parking kayan da zata buqata tayi ta wuce tayi lodging a hotel. +

Murmushi tayi as she tried recalling last 6 months of her life, from the first day da ta hadu da Khalifa Al-Haydar har zuwa yanzu. In ta tuno wani abun tayi dariya, wani kuma in ta tuna sai dai tayi frowning. A haka har barci ya kwashe ta. A haka tayi 3 days a hotel kan ta wuce Abuja. Tun dai da ta turawa ýan gida text cewa she’s doing good, zata yi dan tafia for a week or so ta cire sim card dinta. Ta cigaba da using dayan contact dinta wanda in ba Yasmeenah ba da Ameer PA ba me number din.

Yasmeenah ba kadan ba taji dadin ganin Laylah. Murna a gun ta har da hawaye and to crown it all, a ranar da Laylah ta iso ita ma Leek ta iso. Ranar kam dadi kamar zai kashe Yasmeenah. Dama plan suka yi both Laylah and leek to surprise her. At night, after dinner Yasmeenah na zaune kan gadon ta with both Laylah and leek lying their heads on her laps suna ta hira. Can kowa yayi shuru, lokacin leek tayi seizing opportunity to finally speak.

“Maamah…..”. Ta kira Yasmeenah a hankula. Kuka Yasmeenah ta fashe da dun for the first time kenan in 20 years da leek ta kira ta da sunan mama. Tunowa kawai ta fara da lokacin da ta hana leek kiranta da sunan.

“My baby”. Yasmeenah ta fadi a hankula. A lokacin Laylah ta miqe da niyyar basu waje, she figured they needed privacy amma much to her surprise sai Yasmeenah ta ce tayi zaman ta. “We’re family afterall”. Ta fadi tana murmushi. A lokacin Laylah ta lura da yadda tsufa ya dan fara nunawa a fuskar Yasmeenah, all thanks to the stress she’s been through the past few months.

“I’m so sorry, for how i reacted the other day. I was just angry. Amma wallahi duk duniya bani da irin ki,, and I love you so much. I won’t let a father that cares less about my existence ruin our bond”. Ta fadi tana kallon Yasmeenah “kiyi haquri kinji Maamah na, ina son ki kuma bazan taba barin ki ba”. Ta fadi mata.

“Shhhhhh”. Yasmeenah ta sa hannu a bakin ta, a sign for leek to keep shut “just shut up and hug me, would you”. Yasmeenah ta fadi tana goge hawaye. “And you too”. Ta jawo Laylah tayi hugging dinsu duka. Sun dade a haka kan Yasmeenah tayi breaking embrace din.

“I think you girls should see this”. Ta fadi tana jawo tablet dinta “A little investigation from my private detective”. Ta fadi tana nuna musu wasu hotuna.

“Leek here’s your aunt Gumsu, your uncle, your cousins and then there’s your grandma”. Ta nuna musu pictures.
No way! My grandma is still alive”. Leek ta fadi tana tsalle kan gado “I have a family, like a family Forreal!”. Ta fadi tana ta jin dadi. +

Sai da ta bari suka gama tsalle tsallen su na murna kan ta cigaba da musu bayani “My name is Adama, my real name”. A lokacin bakin Laylah ya kai qasa dun tsananin mamaki. A duniya bata taba ganin mutum me shegen zurfin ciki ba irin Yasmeenah.


“Ya aka yi kika fara ansa Yasmeenah”.

“He gave the name to me”. Ta fadi tana share wani dan hawaye, fuskar ta riqe da wani murmushi.

“He? You mean my dad?”. Yasmeenah tayi nodding kanta. “Ba zaki fadi mun komi a kansa ba? Bana so naji sunansa, just something about him”.

“He has the most beautiful smile. Idanun ki sak nasa. You know that thing you do with your toes when you’re tensed? Shima haka yike”. Ta fadi tana dariya. Yasmeenah ta buda baki zata yi magana ringing din wayarta ya katse su.

One week din da Laylah tayi a Abuja tare da leek and Yasmeenah was so far the best thing that has happened to her in the past 4 months, tun incident din abunda ya faru tsakanin ta da Al-Haydar, that was the first time she was genuinely laughing. And she was thankful to both Yasmeenah and leek, ba wanda ya dago mata sunan sa. Sannan tayi making up mind dinta to turn down offer inda aka mata na organising what the press loved to acknowledge as the “wedding of the century”, wato auran khalifa Al-Haydar to Saima Mohammed.

Koh da plane dinsu yayi landing yola, after spending 10 days with Yasmeenah and leek, tayi mamakin ganin Hamma Suraj a arrivals lounge yana jiran ta. She remember making it clear to Ummati cewa ta aiko chauffer ne ya dauko ta, and she didn’t expect Hamma ta come pick her up dun ta san yana gun aiki by time inda zata iso. Waving mata hannu yayi kan ta qarasa inda yike, ya anshi da trolley dinta ya fara ja.ja. +

“How have you been?”. Ya tambaya ita kuma ta basa ansa kan ta tambaya ya matar sa da baby Ammah. Har suka shiga mota ya fara tuqi ba wanda ke cewa dan uwansa komi. Hasalima Laylah qosawa tayi su isa gida, dun dense ambience din motar yayi yawa. Karshe kuma tayi making up mind dinta to just apologise for what happened. Ta buda baki zata yi magana kenan a daidai lokacin shima ya juyo ya Kalle ta zai yi magana.

“I’m sorry”.

“I’m sorry”. Duka suka fadi a lokaci daya. Dariya dukan su suka kwashe dashi a lokacin da Laylah tace ‘jinx’.

“Har yau baki girma ba”. Ya fadi yana dariya.

“Says the one who still cries on his wife’s shoulder like a baby”. Ta fadi tana rolling idanunta. Shuru suka kuma yi dukan su kan Hamma Suraj yayi breaking silence din.

“I’m sorry…. I know I don’t have the right words to show how very sorry I am amma dan Allah accept my apology. Na dau alwashin, from this day onward i’ll try to always be there for you, I promise to make up for all the times I weren’t there when you needed me. Duk wanda ya kuma daga miki yatsa na rantse sai na karya yatsar”.

“Koh da amininka ne”. Ta fadi tana dariya “It’s okay Hamma, shits happen”.

“Mahmoud bazai kuma shiga harkar ki ba. I’ve warned him to stay out of your way”.

“Thank you”. Ta fadi a hankula. Daga nan ba wanda ya kuma cewa komi. Har suka isa gida ba wanda ya kuma cewa kowa komi. Sai da suka isa zata fita daga car din ta mai magana.

“Ermm…. Hamma”.

“Na’am”.

“Let this remain between us. Ummati, Abba, I hope….”.

“Karki damu, i’m not a fool to let them know”. Ya fadi yana mata murmushi. Dan ijiyar zuci ta sauke, cause bazata iya imagining abunda zai faru in iyayenta suka ji wannan mummunar labarin ba. Allah dai ya yafe mana gaba daya.

Tana shiga kam Ummati ta hau ta da fadan tafia a sace bata fadi wa kowa ba, duk ta sa hankulan su ya tashi. Da kyar ta rarrashi Ummati ta daina jaraba kan ta wuce sama dakin ta. Fadawa tayi kan gadon ta ta kwanta ba tare da ta cire boots dinta ba, dogon ijiyar zuci ta ije kan ta hau tunanin Auta wadda ta koma school. Sai lokacin ta gane how lonely she is, duk duniya bata da kawar da ta wuce Auta, sai kuma Yasmeenah and leek. Bayan su bata da kowa sai iyayenta da Hamma Suraj.

‘Zubaidah!’. Tunanin ya fado mata a rai. She’s the only person da take kusa da amma kuma bata ganin zata iya koma gidan Hamma Suraj after all that happened. Tabe fuska ta yi kan ta miqe da niyyar shiga wanka. Dun haka kawai tayi deciding ta koma school, dun yi masters dinta. Sai da tayi sati guda tana shawara da kan ta tukun ta fadiwa iyayenta qudirinta. Abba yayi murna da haka ita kam Ummati fada ta rin qa yi wai shikenan ita bazata ta fiddo miji ayi aure ba, duk mates dinta na dakin mazan su da ýaýansu sai ita zata wani ce makaranta zata cigaba. Da kyar Hamma Suraj ya sa baki tukun ta yarda. Without much hesitation aka yi working komi, Laylah ta sama admission. Abun ka da masu kudi.
kudi.

“Good day class, I am doctor Mahmoud Gidado. The lecturer to tak…..”. Be gama magana ba qarar footsteps dinta suka tsayar dashi. Mahmoud ya kasance irin lecturers dinnan da basu tolerating late coming. Koh da ya buda baki zai yi fada a kan baya son late coming kasawa yayi ganin wadda ta shigo ajin. Tunda ta shigo gaba daya class idanun kowa kanta yike, shi kansa Mahmoud kasa dauke idanunsa yayi kanta. Ita kam koh a jikinta ta qarasa ta sama seat kusa da wani mutum ta zauna, murmushi ta mai bayan ta zauna ta dan fadi hello a hankula. Shima murmushin ya mata ya mayar mata da gaisuwar ta. +

“So as i.i.i wa…aa..s saying….”. Duk ya rude ya kasa magana, sai in’ina kawai yike ta yi. Da kyar dai yayi composing kansa yayi one hour a class madadin 2 hours inda ya kamata yayi in su.

A kwana a tashi ba wuya gun Allah, kamar wasa har Laylah tayi 7 months da dawowa yola, ba khalifa ba labarin sa. Bata ganinsa sai newspaper koh news dun yanzu ya fito duk duniya an san koh waye asalin Al-Haydar. A fadin sa cewa farautar da yike yi ya kusa zuwa karshe, labarin auran sa ya gama cika ko ina sai shirye shirye ake ta yi. Ita kam Laylah abota ne sosai ta qullu tsakanin ta da Mu’azu, seat mate dinta a class wanda ma’aikaci ne da road safety dan kuma babban gida. Sauran ýan class din kam dama ba wani shiga harkar su take ba, iyakar ta da su gaisuwa. Shikam Mahmoud har baya so ace yana da lecture dasu saboda gaba daya hankalinsa baya kwanciya in yaga Laylah. Ya rasa yadda yike ji a ransa game da ita. Ya tsani ya ga wani namiji a tare da ita.


Wata ran Saturday bata da abun yi ta shirya da nufi zuwa inda ya zame mata tamkar second home yanzu, wani dan orphanage home ne nan a cikin gari. Lokaci zuwa lokaci tana zuwa tayi spending time da marayu, yin haka na debe mata kewa sosai. Har ta shirya zata wuce sai tayi deciding ta shiga wani eatery ta siya snacks wa yaran.

“Hey”. Ta ji wani very familiar voice ya mata magana. A hankula ta dago kai ta juya dun ganin koh da gaske shi din ne.
Beep, beep”. Ta ji qarar shigar text wayarta. Miqewa tayi daga kwanciya ta jawo wayar from bedside drawer dinta ta buda message din. +

“Let’s have dinner, don’t say no please”. Murmushi kawai ta saki bayan ta gama karanta text din kan tayi typing din reply. It’s been 3 months since their reconciliation and things have been quite peachy between them.

Koh da ta shiga mota ta fara tuqi ba abunda ke yawo ranta in ba haduwar su a eatery ba 3 months ago. Ranar ne Mahmoud ya bata haquri akan maganganun da ya fadi mata da rashin mutuncin da zainaba ta mata. Tun daga ranar kuma shikenan suka yi rekindling friendship dinsu. Duk da to Laylah, they’re nothing more than friends, ta san a gun Mahmoud ba haka bane dun ta dade tana noticing dinsa, she’s been watching his movements. It seemed an old flame was beginning to sparkle again. Iyayen Laylah on their own side kam sunyi murna kwarai da new improvement inda aka sama a relationship din Laylah da Mahmoud. Ita kam zainaba tana can kishi kamar ya kashe ta dun Mahmoud har barazanar qara aure ya fara mata. Gaba daya ta rasa kwanciyar hankali, shiga da fita ba irin wanda bata yi dun taga Laylah ta fita daga rayuwar su. 2

Koh da Laylah ta isa, samun Mahmoud tayi zaune da ýan matan sa koh hirar me suka masa oho sai dariya suke ta yi. Takwarar ta ce ta fara hango ta ta rugo da gudu tayi hugging dinta kan Mahmoud ya miqo holding his other daughter in his arms suka gaisa.

“Where’s baby Isma’il”. Laylah ta tambayi yaran baby brother dinsu, sabon baby in da zainaba ta haifa.

“He’s home with mommy!”. Kauthar ta ansa.

“Okay girls, let’s order”. Mahmoud ya katse su. Sun ci abinci su cike da nishadi ana ta hira da dariya just like a happy family, something which hardly happens with his real wife. Koh kadan basu zaman 30 minutes da zainaba wani argument be hada su ba, and most atimes ita ke initiating arguments din and aka duba sai aga over something very trivial ne amma sai gashi nan da Laylah, his Laylah, his first love, the woman he has always envisioned as the mother of his kids suna zaune suna cin abinci cikin kwanciyar hankali. Mahmoud na matukar jin dadin yadda Laylah ke kula masa da yaransa, wani yace ita ta haife su. Har weekend take insisting a kawo mata su, warm nature dinta yasa yaran suka yi warming up to her very easily. Kullum basu da hirar da ya wuce na auntie Laylah, auntie Laylah this auntie Laylah that, much to the dismay of their mother wadda take ta faman haushi cewa an kwace mata miji ana nema a kwace mata yara ma. Sai kace ba ita tayi sake ba.😕
Suna zaune shuru a mota, yara duk sunyi barci har ita kanta Laylah barci ya dan fara tafia da ita kawai kamar cikin mafarki taji Mahmoud na kiran sunanta. +

“We’ve arrived”. Ya fadi mata. A hankula ta dan murza idanu kan ta juya ta dubi yaran da ke barci a backseat ta dan yi murmushi.

“When they’re awake, tell them auntie Laylah wuvvvs them”. Ta fadi masa tana shirin sauka. “And take care of yourself too, thanks for today”. Ta fadi tana buda qofar motar amma sai Mahmoud ya tsayar da ita.

“Laylah. Wait”. Ya fadi da sauri. A hankula ta dawo ta zauna ta rufo qofar. Juyowa tayi directly facing him.

“Yes?”.

Sai da ya ja dogon numfashi kan ya buda baki dun magana “I still love you Laylah”. Ji tayi kalamansa sun daki kunnuwanta kamar saukar aradu. Dan runtse idanu tayi kan ta basa answer.

“Play time’s over Mahmoud”. Ta fadi tana buda qofa. Cikin hanzari ya kama hannunta.

“No, wait. Please”.

“Ka daina irin wannan wasan Mahmoud. Koh dun ka kirani da sunan karuwa ne yasa kake neman mun irin wannan wasan da hankali, you have your wif…..”.

“Ba inda aka ce bazan iya qari ba”. Ya fadi yana kallon ta. “Wallahi I love you, I always have. Koh na rana daya that feeling has never left my heart, no matter how hard I try. I can’t hold it in any more, I hate the way you smile at other guys, that Mu’azu dude, wallahi I always loose focus in ina class dinku. Laylah plea…..”. 1

“Mahmoud be kamata muna maganar nan ba, go home please. Your wife is waiting”. Ta fita daga motar ba tare da ta saurare sa ta shige cikin gida. Mahmoud kam kai ya dora kan steering wheel ya shiga dogon nazari, ya dade a haka kan yayi starting motar sa ya dau hanyar gida. Koh da yana tuqi, bai daina tunanin scene inda yayi unfolding minutes ago ba. Shi dai ya san bazai iya haquri da Laylah kuma koh da ya fadiwa mahaifiyar sa kudirin sa na qara aure murna tayi sosai da decision din barin ma da taji ya ce Badejo tsohuwar budurwarsa is the lady he has in mind.

A daren ranar dai ba wanda ya iya barci, ba Laylah ba ba Mahmoud. Dukan su yadda suka ga dare haka suka ga wayewar gari. Aikam immediately after lecture the next day, Mahmoud ya ayi instructing din Laylah da ta same sa a office dinsa. Jiki ba wani karfi ta nufi office dinsa, ta dan jima bakin qofar tana nazarin zancen da zasu yi kan ta tura qofar ta shiga ta same sa ya zauna shuru, from all indications he was lost in thoughts. Yayi Snapping out of trance dinsa ya buda baki zai yi magana sai Laylah ta riga sa. +

“Mahmoud I’ve told you, this can’t work”.

“Why can’t it? Just tell me why Laylah. I have money now”. Zancen sa ya daki wani chord a zuciyar ta. Ta rasa meyasa kowa ke tunanin rashin kudi ne ya hanata auran Mahmoud the first time he proposed. “I know I’m not as wealthy as you are, neither i’m I as wealthy as mazan da ke zuwa gun ki but please Laylah, we’re meant to be together don’t you see. Shekara nawa Laylah, but fate still keep bringing us back together”.

“Mahmoud wealth has nothing to do with this. Matters of the heart….”. Bata gama ba ya katse ta.

“Toh menene Laylah. What’s my flaw da baki sona?”.

“I’m scared it’s not you that’s flawed, it is i”. Ta fadi kai a qasa “Mahmoud I doubt zaka yi accepting dina if I tell you about all that happened in the span of those 8 years I was away”.

“Try me Laylah, kina wasa da irin son da nike miki. I’m ready to accept you and all your flaws. I don’t even want to hear them, I believe they’re in the past now. What awaits us is nothing but a beautiful future. Ban zo da wasa ba, i’m dead serious Laylah”.

“But you’re married Mahmoud. To zainaba for that matter, it’ll be awkward. Gaskia bazan iya ba”.

“Look, Laylah we’re Muslims and polygamy abu ne da subhanahu wata’alah ya halarta mana. Maganar wani zainaba duk be taso ba. Amincewar ki kawai nike nema Laylah, that’s all that matters. Duk wani abu da zai biyo baya me sauki ne”. Dogon numfashi ta ja kan ta fadi masa cewa ya bata lokaci tayi nazari tukun. A haka suka rabu ta wuce ta shiga motar ta tayi hanyar gida shikuma ya cigaba da aikin sa duk da hankalinsa ba kan scripts inda ke gabansa suke ba, his mind was elsewhere soaring.

Koh da ta isa gida, Laylah bata bi ta kan zancen Mahmoud ba. Watsa ruwa tayi kan ta sauka qasa ta ci abinci suka zauna hira da Ummati. Sai bayan da ta idda sallan isha tukun ta kira Auta a waya domin suyi shawara. Karshen ta conference call ta hada between her, Auta da Zubaidah dun su shawarta akan issue din. Sun dade on phone, suna ta ba Laylah effective advices, mostly showing her the pros of saying yes to Mahmoud’s proposal.
Sai da ta miqe tayi salatul nawafil tukun da niyyar yin salatul istikhara much later kan ta kwanta ta jawo waya ta shiga duba tweets. The next day bata da abun yi a school dun haka barcin ta mai lafia ta sha bata tashi da wuri ba. Sanda ta tashi kuma bayan ta gama going about morning businesses dinta ta tura wa Mahmoud text akan they should meet later during the day. Ana maghreb ta fara shirin tarban Mahmoud. Kwalliya ta zauna ta dau lokaci tayi, ta sa boubou gown na wani tulle lace me shegen kyau, ta fesa turarukan ta iri iri kan ta sauka to ensure refreshment inda tace a shirya masa anyi. +

Mahmoud sai da yayi sallan isha kan ya qarasa gidansu Laylah. Kasancewar sa dan gida yasa kawai ya shiga ciki without any hesitation. Sai da ya fara shiga cikin gida ya gaida su Abba tukun ya wuce Majlis inda male visitors ke sauka ya jira isowar Laylah. Tana shiga suka gaisa ta tambaya family dinsa kan aka kawo masa refreshment. Hirar karatu suka dan fara can kuma aka dan fara tabo na business Laylah tana dan basa insight on her business and how she wish to expand it. Finally, Laylah ta gyara murya domin ba wa Mahmoud answer, the moment he had been awaiting ever since his arrival.

“Soooo….” ta fadi tana wasa da dan azurfan da ke ring finger dinta “I gave your proposal careful thought. I think it’ll be a nice idea becoming a mother figure to your girls”. Ta fadi tana ýar murmushi wanda ya tsaya iya bakin ta.

“Is that yes?”. Ya tambaya his smiling widening. Ita kam nodding kanta kawai tayi in affirmation. “Forreal! Yes yes! Finally, i’ll have my Laylah all to myself”. Ya fadi cike da murna sai fadin Alhamdulillah yike ta yi.

“Urmm zainaba… ban san yadda zata dauki news din ba”. Ta fadi a hankula.

“Karki damu, dole she won’t take the news likely considering all that has happened between you two lately amma insha Allah i’ll talk to her, i’ll make her see reasons and insha Allah nayi alkawari I’ll try my possible best to be equal and just tsakanin ku. Baza ki yi facing wani problem ba da izinin Allah kin ji”. Yayi ta bata baki in an attempt to calm her.

“Soooo yanzu when do I come for formalities”. Ya fadi.

“Haba malam! Da sauri haka, me yayi zafi”.

“Lallaima, ai nifa ba da wasa ba. A bari ya huce shi ke kawo rabon wani kuma wani dating zamu tsaya yi Ehh? We grew up together fa”.Toh da wannan kuma. I’ll talk to Hamma insha Allah sai yayi wa su Ummati magana”. Ta fadi. +

“Shikenan, nima gobe sai na wuce Girei in the morning dan nayi magana da su Daada and my uncles”. A haka suka rabu kowa cike murna.

Aikam the following morning Laylah tayi sammako dun ta sama yayanta a gida kan ya wuce office tayi masa bayanin komi. Kwarai da gaske yaji dadi, saboda ya san Mahmoud mutum ne na arziki kuma zai kula masa da sister dinsa dun haka yayi assuring dinta cewa he’ll notify their parents bayan ya hadu personally da Mahmoud sun yi magana. Jawo hannunta Zubaidah tayi zuwa bedroom din ta suka hau gado kamar yara suna ta squealing. Suraj na ji yo hayaniyar su, kai kawai ya gyada.

“In kin gama tsalle tsallen kya zo ki ban breakfast na wuce aiki”. Ya fadi in a tone da zasu ji shi. Dariya suka fashe da kan Zubaidah ta miqe ta nufi hanyar waje dun ta sallamesa. Ita a ranar night shift take. Ta na gamawa ta kira Laylah suka yi having breakfast duka tare suna gamawa suka zauna dun yin face time da Auta su breaking mata good news. Aikam Auta ta fi kowa murna ana fadi mata ta fara picking colours in kayan da zasu siya da number of events inda zasu yi. In fact har guest list tace zata fara compiling ranar. Sarkin zumudi.

Aikam Hamma Suraj na fadiwa su Ummati suka dinga murna dun suma sun yaba da Mahmoud. Sannan suka bar wa Suraj wuqa da nama, cewar kanwar sa ce dun haka yana iya yin duk abunda yaga ya dace so without much hesitation Suraj ya fadiwa Mahmoud ya aiko magabatansa dun ayi formal introduction a kuma yi fixing date. A haka aka zauna aka yi deciding to have the wedding in December which was 3 months away. Zainaba kam tunda maganar auran Mahmoud da Laylah ya iso ta ta rasa sukuni. Duk ta bi ta rasa kwanciyar hankali, ba kadan hankalinta ya tashi ba dun ta san Laylah is a strong competition. Duk abunda take tunanin tana dashi Laylah ta fi ta dashi. Dun haka ita da mahaifiyar ta da kawaye aka ta shige da fice gidan bokaye da malamai, neman asiri har Maiduguri, duk dun a fasa biki amma ina Kullum sai Matsowa kusa time yike, ga shirye shirye ana ta yi ba dare ba rana. Tsohon gidan da suka zauna Mahmoud yayi renovating ya dawo kamar sabo, daidai standard din wanda suke ciki a yanzu, a nan Laylah zata zauna. Unguwar ba nisa da unguwar da zainaba take. Da ka gansa yanzu kaga hutu da kwanciyar hankali, dun kusan Kullum in ya tashi aiki sai ya bi gun Laylah kan ya shiga gida kuma tafi basa kulawa fiye da matar sa da ke gida wanda ba abunda da ta iya daga gulma da kawaye sai kallon zeeworld and telemundo, going from one wedding to another, aikin kenan Kullum. Batawa cikin ta ta ci ba, bata yi wa yaran ta sun ci ba bare wani miji. Koh su yaran suna jin dadi in Baban su yace zai kai su weekend gun auntie dinsu because tana basu full attention dinta, tana bata su sosai. Kan a maida su gida sai ta tabbata an sake musu sabon hair do, an gyara su tas. Hakan nayi wa Mahmoud dadi matuka. +

Ita kam zainaba sabon mota ya sake mata ya mata alkawarin kujerar hajj duk wai cikin compensation da ake ba mata in zaa yi fadin kishiya banda kaya da siya mata amma duk wannan didn’t calm her down, ita kawai a fasa bikin shine burin ta.

Wata ranar Monday very early, after tayi dropping yara a school kawai tayi zooming off to GRA inda gidansu Laylah yike. Bakin gate ta dinga manna wani mahaukacin honk har sai da security man din ya buda mata gate ta shiga. Bata ma tsaya ta gyara parking ba ta fito daga cikin mota sai ihu take tana approaching main entrance din gida. A makeken living room inda ke downstairs ta tsaya tana ta fuming sai Ummati ta shigo cike da damuwa a fuskar ta tana lafia?.

“Ina take, ina wancan Shegiyar Karuwar take!”.

“Subhanallah! Me zan ji haka ni Rabi’atu”. Ummati ta fadi tana mamakin wai zainaba ce ke fadin haka.

“Dallah rufe mun baki tsohuwar banza, har da ke ai. Shegiya baqar munafuka! Ni din da kike fadin kin dauke ni tamkar diya shine zaa hada baki dake a cutar da ni dun iya shege. Ban barin gidan nan yau wallahi sai na ci wa wancan Karuwar diyar take mutunci. An je an gama yawon karuwanci an kwaso cuta zaa zo a liqa mun….. inaaa bazan yarda ba”. Zainaba ta dinga, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba.

Shima Abba hayaniyar da ya ji yayi yawa ne yasa yace wa yaron da ke kula dashi in Ummati bata kusa ya tura wheelchair sa zuwa main living room din gidan yaji dalilin wannan hayaniya da sanyin safiya. “Ke Baiwar Allah Meya faru”. Ya tambaya a hankula.

“Dallah rufe mun baki, tsohon banza. Shiyasa a haka zaka dawwama akan kujerar guragu. Mutane ne ba abunda kuka sa gaba sai kwadayi da cin amana toh wallahi sama tayi wa yaro nisa. Duk na sha karfin ku, sai ma na hadu da wancan annamimin, baqin munafiki mai halin ýan wuta, sai kace ba da shi aka zo neman aure na ba amma yanzu dun gulma ya dau gwalgwajin kanwar sa ya jonawa mijina, kun rasa yadda zaku yi da ita kawai zaku liqa masa. Waya ce muku shi bola ne da kowa zai iya watsar da sharan sa?”. Ta dinga, Ummati dai tana tsaye tana ta kallon ikon Allah. Laylah kam hayaniyar da ta ji yayi yawa ne ya tashe ta, miqewa tayi ta zauna kan gadon ta ta rasa reason for the noise so early. Da taji shuru noise din sai qaruwa yike kawai ta dau dan karamin hijaab dinta ta sanya ta fito. Koh da ta sauko taga masu aikin gidan sun taru ga iyayenta nan, ga kuma zainaba sai maganganu take fadiwa mahaifiyar ta. Cikin hanzari ta qaraso. +

“Toh bari in fadi miki…..”. Zainaba ta fadi tana nuna Ummati da dan yatsa. Bata gama fadin abunda take ba Laylah ta kamo dan yatsar ta dinga murdawa tana kallon yadda zainaba ke flinching in pain. 1

“Me zaki fadi mata? Fadi mu ji”. Laylah ta fadi still tana murda mata hannu. “Uwar ki bata koya miki girmama na gaba da ke ba koh?”. Ta kuma fadi in a very calm tone, koh kadan bata bari bacin ran ta ya nuna ba “Now I see why mijin ki ke buqatar wani auran. Empty vessels sure make the loudest noise”. Ta fadi tana mata flinging da hannu.

“Banza, ballagaza, shara, bola dake har zaki buda baki ki wa mahaifiya ta rashin kunya? Toh wallahi kiyi hattara da ni. Ki ji tsoron randa zan shigo gidan Mahmoud, dun daga ranar ya tashi daga sunan naki, like as I said before in me wuri ya zo sai me tabarma ya nade ya tattara ya san Inda dare ya masa”.

“Ke!…”. Bata gama magana ba Laylah ta watsa mata mari, koh gama farfadowa daga zafin marin bata yi ba Laylah ta qara mata wani a dayan kumatun. Gaba daya ta sa hannayenta kan kumatu tana sosawa dun tsananin zugi da both cheeks ke yi, ga hannunta da ke mata dan karan zafi, from all indications Laylah ta mata targade. 1

“Tsohuwar banzan can da kika bari Girei ita ce ke ba ni ba. Ni Badejo nike, yarinya ýar halal. So next time call my name with respect dun wallahi very soon zaki fara zuwa guna neman permission din yin abubuwa ke da gidanki. Yes that’s how much control I’ll have over the household. Mara hankali da tunani kawai. Go home and start counting your days”. Laylah ta fadi mata. Without warning kawai ta riqo mata hannunta daya ta jawo ta har bakin qofa ta tura ta waje kan ta jawo qofar ta rufe tana fadin a gayas.
Zainaba kam jiki ba sauran karfi ta wuce ta shiga motar ta, sai lokacin ta tuna cewa ta bar baby dinta cikin mota, yaro har yayi kuka ya gaji ya kama yatsa yana ta tsotsa har yayi barci. Tana fita daga harabar gidan tayi parking mota gefen titi ta duqar da kai, kawai sai kuka ta fara tana sosa kumatun ta. Laylah ta girgiza ta ba kadan ba. Tsoro ne ya da da cika ta duk ta rasa abun yi. Da kyar ta samu ta tuqa kanta zuwa gida. Tana isa ta kira kawar ta da ta bata advice din zuwa gidansu Laylah yin cin mutunci tana fadi mata yadda tables din suka yi turning. +

Laylah kam on her own side haquri ta shiga ba iyayenta akan cin mutuncin da aka musu saboda ita tana gama haka ta hau sama zuwa dakin ta ta dau waya ta kira Mahmoud da niyyar yi masa tatas. Da ace insult din kan ta ya tsaya da Laylah bata damu da kiransa ba amma dun cin fuska har iyayenta baa bari ba. Aikam yana daukar waya ta fadi masa cewar ya ja wa matar sa kunne koh tsayawa sauraron sa bata yi ba ta katse wayarta. Yana ta kira shuru, kawai yaji hankalinsa be kwanta ba dun be san irin damage inda matar sa tayi ba dun haka kawai excuse ya dauka, yayi cancelling class inda yike dashi ya wuce gidansu Laylah. Koh yadda yaga iyayenta sun gaida shi jiki a sanyayyaye told him everything, yasan all is not well. Koh da ya zauna jiran Laylah ta fito, Addu’ar sa daya; kar ta zo masa da bad news. Kada yarintar zainaba yasa suce sun fasa.

Sai da Laylah tayi wanka ta shirya kan ta fito zuwa Majlis din. Kan ta wuce ta shiga kitchen ta bada orders wa masu aiki da su kawo mata breakfast dinta Majlis din, and su kawo da extra plate. Tana shiga ta dan yi masa murmushi, bata bari emotion dinta yayi getting best of her ba. Ta shiga bata dade ba aka kawo breakfast din, kayan tea aka kawo da toast. A hankula tayi spreading butter on some toasts kan ta hada black tea ta ije masa gabansa. Kamar ta san koh breakfast be yi ba. Sai da ya gama cin abinci kan ta fara mayar masa da duk abunda ya faru from A to Z bata boye masa komi ba, har marin da ta wa zainaba. Shikuma kunya ya ji yayi ta bata haquri yana fadin he’ll look into the matter. Be tafi ba sai da ya shiga cikin gida ya ba su haquri suka ce masa ba komi, Allah dai ya kiyaye.

Daga gidansu Laylah, Mahmoud gidansa ya wuce direct be koma office ba. Yana shiga kam ya sama zainaba zaune da kawayenta sai hira suke ana shewa, tun daga bakin qofa yike jin muryoyin su sai habaici suke ta yi. Koh da yayi sallama ya shiga ba wacca ta ansa masa a cikinsu. Shima rai bace ya shiga ciki ya kira zainaba kan ya wuce bedroom. Ita kam kamar ba da ita yike ba ta zauna suka cigaba da shewarsu, sai da ya jira ya gaji tukun ya kuma kiranta a waya.

“Koh kin manta ina jiranki ne”. Ya fadi tana daga wayar.

“Na sani ai amma abu nike”.

“Abu kike? Abu kike?”. Ya maimaita kalamanta.

“Koh ba kaji ne sosai”.

“Toh shikenan”. Ya katse wayar sa kan ya koma kan reading desk dinsa. Sai da ya gama abunda yike tukun ya fita sitting room din ya izza ta da kawayenta ga abinci sun baje suna ci. Hannu ya sa ya jawo ta zuwa hanyar bedroom dinsu, basu kai ga shiga room dinba ta fisge hannunta daga grip dinsa ta juya zata koma Aikam Mahmoud ya kwasa mata mari wanda ya kusa kai ta qasa, bata gama warke zugin marin ba ya qara kai mata wani a dayan kumatun. Kawayenta kam tsit suka yi suna kallonsa, rai a bace. bace. +

“Mara mutunci, mara hali kawai. Tir da halin ki wallahi. Mara hankali. Yanzu ribar me kika ci da kika tafi kika je kika wa people old enough to be your parents rashin kunya”.

“Allah kyauta wancan matsiyatan su zama iyaye na”. Ta fadi ai kam ya kuma kwashe ta da mari.

“Sakarya kawai, jahila”. Ya fadi kan ya ciro takardar da ya rubuta mata saki biyu ya wurga mata “Sai ki koma can gidan uban ki kiji da shi, kan na dawo dama koh wace tsinanna ta bar mun gida”. Ya fada kan ya nufi inda infant baby dinsa ke kwance yana barci a pram dinsa ya dauke sa ya fita da shi. Zainaba sai kuka take tana kwala ihun sunansa, tana tambayar sa inda zai kai mata jaririn ta shi kam koh ansa ta be yi ba ya wuce. Har ya shiga mota sai ya kuma ya fito ya koma bedroom ya dauko key din motar da ya siya mata daga kan dressing table inda ta bari ya sa pocket yayi waje. Straight school din sauran yaran yayi ya dauko su, time din closing be ma yi ba ya dauko kayan sa dun gudun kar zainaba ta riga sa. Yana dauko su ya wuce gidan sister dinsa dasu ya ije mata.

Zainaba kam juyawa tayi taga kawayenta hanyar qofa zasu wuce koh sallama basu mata ba. Abun ya mata zafi amma duk zafin sa be kai na sakin da aka mata ba. Yanzu tayi biyu babu, dama bata biye wa shawarar kawarta ba. Yanzu komawa Girei ya ganta, gashi Mahmoud ya kwace mata yaro, gashi koh key din mota be bar mata ba. Zube wa tayi a qasa, hannayenta bisa kai tana ta zuba uban kuka. Wannan shi hausawa ke ce wa kaikayi ya koma kan mashekiya😂😂😂😂.
2

▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪

😂😂😂😂Who enjoyed this chapter? Cause I definitely enjoyed writing it. I love witnessing dramas as they unfold.



Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *