ƁATACCEN YANAYI CHAPTER 5

ƁATACCEN YANAYI







CHAPTER 5










Jirgin su na isa Nigeria ta tadda Yasmeenah na jiran ta. Cikin murna ta qarasa ta yi hugging
din Yasmeenah.
“Ya Allah! l’ve missed you Yasmeenah”. Ta fadi kawai ta fashe da kuka.
“Nifa dadina da ke kenan, shegen son kuka. Oya yi shuru, 3 weeks kawai fa kika yi biki
ganni ba”. Yasmeenah ta anshi jakarta ta riqe mata suka karaso inda tayi parking mota.
Laylah na maida sim dinta na Nigeria gida ta fara kira, ta yi dialling number din umman t
“Ummati”. Ta kira sunan mahaifiyar ta kamar yadda suke kiranta.
“Na’am ýar albarka, kin dawo kenan”.
“Shigowa na Nigeria kenan'”
“Masha Allah, ya aikin? Komi lafia koh?”. Ummati ta tambaya ita kuma Laylah ta ansa ta da
komi lafia lau. Ta tambayi Abban ta da kuma ýan uwan ta.
“Duk lafia lau suke, Abban ki nema be ji dadi ba, jiki ya dan tasan me”
Salati tayi kan ta ansa mahaifiyar ta “me ya same sa ne haka? Kuna da kudi isasshe? Zan
turo kudi da na shiga gida kuma ina samun hutu daga gun aiki zan zo”. A haka suka ta
zance har suka wa juna sallama ta ije wayar. Duk hankalinta a tashe da taji an ce Babanta
ba lafia.
Bayan sun isa gida, sai da Laylah tayi sallah sannan ta ci abinci ta huta tukun ta kwashe tas
duk abunda ya faru a Australia ta fadi wa Yasmeenah. Guda Yasmeenah ta saki.
“Ahhh Lallai! Diyata akwai ki akwai goshi. Tunda nike hada Junaidu da ýan mata ba wadda
ya tabawa kyauta irin naki. Amma kuma Laylah baki ji, na sha fadi miki a wannan sana’ar
there’s nothing like love, baa soyayya. Ke a ganin ki wa zai auri karuwa?”. Ji tayi kalaman
Yasmeenah sun sosa mata zuciya amma kuma ta san gaskiyar zancen kenan, ba wanda zai
taba accepting dinta.
“Yanzu mance wa zakiyi da wani Abdulmalik ki fara shirin tarban next customer dinki. Na
fadi miki Ali Na sidi har nan gidan ya tako kafarsa yazo yace shima yazo Laylah Jaan ta lasa
mai irin nata zumar”. Ta fadi mata “kuma kema kinsan kudi zasu fito jikinsa. Yanzu duk
wani zancen Al-Haydar a watsar, wannan ya ma na nisa. Tunda ga wanda ke hannu sai mu
kama su gam ai koh”. Yasmeenah ta fadi tana taunar chewing gum. Ita kam Laylah dukji
tayi wannan rayuwar ta fita mataa kai amma kuma bata san daga ina zata fara ba.
Tunda ta dawo rayuwar ta ta sanja, ta rage fita in ba dai aiki ne ya fita da ita waje ba.
Kullum bata da aikin yi sai kallon hotunan ta da Abdulmalik tana zubar da kwalla. Duk
yadda take son barin wannan sana’ar ta riga tawa kanta alkawarin bazata bari ba har sai
randa ta ci kudin Al-Haydar. Amma kuma yanzu da babu Abdulmalik ta wace hanya zata
samu ta hadu dashi.
Shikam Abdulmalik yana dawowa sai da ya fara biya wa ya duba lafiyar dan sa kan ya wuce
gida. Nawfal ya lura da dan uwan nasa, tun ranar da ya hadu da Laylah, ana gobe zasu
dawo be dawo normal ba, duk ya sanja. Kwata kwata ya ma daina zancen ta, baya so kuma
a dago hirar ta.
“Khalifatullah”. Ya ji muryar mamansa. Matsowa tayi kusa dashi ta dora kanta a shoulder
dinsa. Wani dan kiss ya dora mata a kai kan ya tambaye ta abun da ya faru.
“What’s wrong Begum?”
“Duk ka sanja, wani abu ne ya faru a Australia?”. Ta fadi “Ni bani son ina ganin ka haka, duk
sai naji ba dadi”.
Shafar lallausar suman kanta ya fara kan ya gyara murya. “Ke fa kin cika damuwa, nothing
happened, everything’s going well. Na kusa kama barawo insha Allah”. Ya gama mata
bayani kan ya tashi zai fice. Harya kai bakin qofa sai ya juya ya kuma mata magana.
“Fadeel is moving back here next week'”.
“Da gaske. Jikana zai dawo hannuna”. Ta miqe tana murna “Na dade ina jiran zuwan
wannan ranar. Have youfinally made up your mind? Akwai diyar qawata dama, yarinyar
akwai hankali, nasan zata riqe mana marayan Allah tsakanin ta da Allah”
“Begum ya isa please. Ban shirya aure ba har yanzu. Kawai dai zai dawo nan ne, na fi so
yana kusa dani. Yola yayi nisa”
“Kayya, for how long?, next month zaka yi 35 for heavens sake khalifa”.
“Begum let’s not start please. I’m stressed”. Ya fadi ya wuce dakinsa wanda ke ground floor
din gidan. Tun faruwar incident din Fatima khalifa ya rabu da hawa bene, koh elevator sai
ya dage ya rufe ido yike shiga.
Wuni yayi ranar a cikin bedroom dinsa dun koh da aka kirasa out for dinner sai cewa yayia
kawo mai nasa dakinsa baya ji da fita. Begum ta gane cewa akwai abun da ke damun dan
nata kuma baya son sharing shiyasa yike dodging haduwa da ita dan haka ita ma sai ta fita
harkar sa ta basa space. Ranar isowar Muhammad Fadeel ya zo, ranar babu sukuni Al-
Haydar mansion. Masu aiki ne ke ta kai komo, ana shirin isowar karamin uban gidansu.
Dama already tunda Abdulmalik ya fadi wa Begum cewa Fadeel zai dawo gun su ta sa aka
sake interior in dakin da yike zama in yazo hutu, aka sanja komi na dakin an siyo sabo an
saka. Kayan wasa ma duk an cika dakin dashi. Har game room aka hada mai. Garden din
gidan shima haka an zuba kayan wasa.
Girki kam ana ta yi iri iri, a dora wannan a sauke wancan. Duk abincin da Begum ta san
yana so ta sa a dafa mai. Sai da ta tabbatar an gama komi tsaf tukun ta wuce gefen ta dun
ta shirya. Tana cikin shiri taji alaman shigowan motoci.
Shima dama Abdulmalik ba inda yaje ranar, yana gida jiran isowar dan sa, tun safe ya aika
one of their private jets zuwa yola ya dauko dan nasa. Yana jin qarar mota ya fito waje.
Motoci ne guda 3 masu na alfarma suka yi parking a harabar gidan. Fadeel be ma jira an
buda mai qofa ba ya buda da kansa ya rugo da gudu zuwa inda Babansa ke tsaye. Gudu
yike yana murmushi irin na mamansa, duk sanda Fadeel yayi dariya Abdulmalik gani yike
kamar Fatima ce ke dariya. Dukawa yayi qasa sanda yaron nasa ya qaraso ya rungume sa
kamar zai shige cikin sa. Be san sanda kuka ya kufce mai ba. Fatima kawai yike tunawa,
yana jin wani so da kaunar dan sa na dada ratsa jikinsa.
“A..Ab..ba”. Yaron ya fadi yana numfashin sama sama sabida gudun da yayi. “Abba
hayatee”
“Chuchu na… my little tiger”. Ya fadi still hugging the boy. “It’s good to have you back
son
“Then stop crying, the occasion is a happy one”. Ya fadi yana gogewa mahaifin sa hawaye.
Yana hango Begum ya ruga da gudu ya fada mata a jiki shikuma Abdulmalik ya qarasa inda
Hajjo take, tana takowa a hankula ya anshi jakar da ta riqe da ya riqe mata har suka iso ciki.
Kan ka ce me Fadeel ya fara displaying halin sa na barna da rashin ji a gidan. Yana ta faman
ba masu aiki ciwon kai gashi ba daman suyi bugu a bakin aikinsu. Sai da Hajjo tayi 2
days a Abuja kan ta koma yola. A ranar da zata koma kam ta sha kuka dan ba karamin
kewar jikan nata zata yi ba, abun farin cikin ta amma ya ta iya. Week na zagowa aka hiring
teachers inda zasu dinga zuwa gida suna koya wa Fadeel karatu. A duk lokacin da
Abdulmalik ya sama kansa da shiga cikin damuwa in dai ya ga fuskar dan sa duk sai yaji
damuwar ya gushe, a haka dai life ya cigaba gradually duk da akai akai ya kan yi tunanin
Laylah amma koh so daya be taba yunkurin neman ta ba. A cewar sa, if they’re destined to
meet again to komin dadewa fate will bring them back to each other.
Wata ranar sati, Abdulmalik na cikin study dinsa yana aiki daga nan ya fara lulawa duniyar
tunanin sai ji yayi ana kwala mai kira ana jan hannun rigarsa.
“ABBA! ABBA!”, Fadeel ya dinga ihu dama ga muryan nasa very sharp.
“Wai me? Dawo da kai gidan nan laifi ne Fadeel?”. Ya tambaye dan nasa dun tun randa
Fadeel ya dawo gidan Abdulmalik ya rasa sukuni, daga Fadeel yayi fitinar yana son kaza sai
Laylah amma koh so daya be taba yunkurin neman ta ba. A cewar sa, if they’re destined to
meet again to komin dadewa fate will bring them back to each other.
Wata ranar sati, Abdulmalik na cikin study dinsa yana aiki daga nan ya fara lulawa duniyar
tunanin sai ji yayi ana kwala mai kira ana jan hannun rigarsa.
“ABBA! ABBA!”, Fadeel ya dinga ihu dama ga muryan nasa very sharp.
“Wai me? Dawo da kai gidan nan laifi ne Fadeel?”. Ya tambaye dan nasa dun turn randa
Fadeel ya dawo gidan Abdulmalik ya rasa sukuni, daga Fadeel yayi fitinar yana son kaza sai
yayi na yana son wani abun. Gashi da shegen tsiwa da tonan fada. Da ace ba a gida ake
Zuwa koya me karatu ba da an sha fama dun da sai ya dinga neman fada a makaranta.
“You promised to take me out today rememberrrr”. Ya fadi da wani irin grin da ke nuna
wawulon bakin sa. Sanin halin yaron nasa ya sa ya miqe ba gardama.
“Go tell your nanny to dress you up, i’ll be downstairs waiting”. Sai da Fadeel ya tsaya yana
imitating wai irin rawar Michael Jackson kan ya wuce dakinsa shiri. Abdulmalik kam dariya
kawai ta tsaya yana ta yi.
Koh da suka isa national park and zoo be san meyasa zuciyar sa ta dinga wani irin bugu ba,
kaman wani abu na shirin faruwa, something great, something amazing.
“A dangerous plan, just this time
A stranger’s hand clutched in mine
‘l take this chance, so call me blind
I’ve been waiting all my life…A hankula take ta bin wakar zaune a garden in da ke
harabar gidan da suke zama ita da Yasmeenah. Qaton gida ne me ginin zamani wanda wani
senator ya bawa Yasmeenah as tukwuicin hada sa da tayi da Laylah Jaan. Ita kuma
Yasmeenah tace bazata koma gidan ba sai tare da Laylah. Gida ne qato mai compartments
da yawa. Daga Laylah sai ita sai kuma masu aiki da ke zuwa suyi su tafi, sai mai gadi, driver
da kuma yarinyar Yasmeenah wadda ta riga ta yi aure tana zama a portharcourt da ýayanta
biyu sai dai tazo hutu ta koma.
Zaman ta a garden din ba abunda take yi in ba tunani ba, tana kallon pictures din ta da
Abdulmalik tana ta tunani. Gashi tunda ta dawo Nigeria about 3 months kenan amma koh
a hanya basu taba koh da cin karo bane. Toh ina ma take wani fita bare har ta sa ran zata
hadu dashi.
“Maybe you made the wrong decision by turning him down’ Zuciyar ta ta fadi mata.
“No! The decision was a right one. Wata zuciyar ta fadi.
Cigaba da jin waqar ta tayi trying as much as possible ta kawar da tunanin sa daga
zuciyarta amma kuma inaa. Muryar Yasmeenah kawai taji ta katse mata nazarinta.
“Earth to Laylah, tunanin me? Wannan matsiyacin kike tunani har yanzu koh?”. Ta fadi tana
tabe baki. “Laylah I’ve told you, love ba namu bane, it’s too much luxury for us. It only ends
up with you getting hurt. Love sucks sweedie. Cheer up, just consider your moments with
him as a rebound shikenan”. Ta fadi tana shafa wa Laylah baya. Daga nan tace su tashi su
shiga cikin gida ta shirya su fita shan iska.
Ba gardama Laylah ta tashi ta wuce daki ta fada wanka. Tana fitowa ta shirya cikin wani
maroon colour Pakistani top da blackjeggings ta rufe kanta da maroon turban cap. Tana
gama shiri taji tana son tayi make up, haka ta zauna gaban vanity table ta dau kayan
kwalliya ta dinga yi har ta gama. A hankula Yasmeenah ta tura kofar dakin ta ta shigo.
“Are you set?”. Ta tambaya.
“Yeah, i’ll be out in a jiffy”. Ta fadi da murmushi. Turare ta fesa kan ta dau car key dinta da
other necessities ta fito. Lokacin guda kawai taji mood dinta ya sanja. She felt happy and
alot more at ease with herself. Har wani murmushi ta dinga yi a hanyar ta na fita.
Yasmeenah ta izza ta jingina Jikin mota tana jiran ta.
“Tll drive”. Ta fadi tun kan Yasmeenah ta miqo hannu karban car key. Dariya kawai
Yasmeenah tayi ta shiga mota ta zauna. Da suka zo fita Laylah har kyauta tayi wa mai gadi
kan suka wuce. Waqa ta sa tana tuqi tana bin waqar tana rawa. Kasa shuru Yasmeenah tayi
sai da ta mata tambaya.
“Jaan, what’s with the sudden mood change?”.
“No idea! just have a feeling something good’s awaiting me. Scratch that something
good’s awaiting us Yasmeenah”
“Hmmmm”. Yasmeenah ta sa hannu a chin dinta kamar me nazari. “Something good”
“Yeah. Something life changing, in a positive way”. Ta fadi suka dan cigaba da hira har suka
isa national park and zoo. Sun gama siye siyen da zasu yi kenan zasu wuce su sama wuri su
zauna sai ga Yasmeenah ta hadu da wata qawarta. A nan suka dan tsaya ana gaisuwa aka
kuma fara dan taba hira. Can Laylah ta matsa dan gefe dun ta ansa waya, tana cikin
magana a wayar ne wani dan yaro ya rugo bayan ta da gudu ya qanqame kafafunta.
Tll get back to you Ameer”: Ta fadi ma PA dinta wanda suke discussing wani sabon
assignment da aka basu na organising din wani fundraiser event for orphans, harndicaps
and less privileged sannan ta kashe waya. Zata juyo taji an qanqame kafar ta da karfi. Sai
da tayi da gaske ta iya Juyowa. Ido ta hada da wani dan yaro me matukar kyau wandaa
shekaru bazai wuce 7 years ba. Tsananin kyau da sha’awa da yaron ya bata ya sa ta dan
zuqunna. Ta buda baki zata yi magana kawai taji yaron ya kamata yayi hugging dinta
“Hey wh..” Bata gama maganar ba ya rufe mata baki da dan karamin palm dinsa.
“We’re playing hide and seek. He’ll get me a new play station if I win”. Ya fadi mata yana
murmushi “You’ll help me hide, won’t you”. Komi na yaron kamar mace, harta dan karamin
voice dinsa, smile dinsa ga dimple inda yike da. Ga kuma gashi baqi wuluk me tarin yawa a
kansa.
“But I have to go”. Ta fadi.
“Don’t say no, Pleaseeeeeeee mommy”. Ya fadi a shagwabe yana maraice mata kamar zai yi
kuka. Ita kam duk ya gama sa zuciyar ta karaya tunda ya kirata mommy. Murmushi tayi ta
riqe mai hannu suka wuce can wani lungu inda ba zaa yi noticing dinsu sosai ba. Farko
zama suka yi shuru for about 5 minutes kan yaron ya fara mata magana.
“Can I see your phone please”. Ya tambaya ita kuma ta miqa mai. Password ya fara tambaya
ita kuma ta sa finger print dinta kan ya ansa ya fara game. Can kuma ya miqa mata wayar
ya tabe baki.
“It’s boring'”. Miqa mai popcorn inda suka siya tayi ya karba yana dariya har qaton wawulon
sa ya fito. “Let’s be friends”. Ya fadi yana miqo mata hannu. Karbar hannun tayi, tayi
shaking dinsa.
“‘m Laylah and you young lad?”.
“T’m muhammad Fadeel but it’s safe to call me Chuchu”:. Dariya tayi tana mamakin shegen
wayon yaron.
“How old are you?”. Be yi magana ba sabida popcorn inda ya cika baki da, yatsu Bakwai
kawai ya nuna mata ita kuma ta gyada kai alamar ta gane.
“How about you?” Ya tambaya da ya gama taunar. Ruwa ta miqa mai kan ta basa ansa.
“l’m 26”
“You’re biiiig”. Dariya tayi kawai. Yaron ya shiga ran ta sosai. Shuru suka kuma yi kan
yace mata wai tayi musu hoto a wayan ta. Ciro wayar tayi ta fara daukar su selfies yana ta
yin funny posts. Kwata kwata ta mance da zancen wata Yasmeenah sai da wayar ta ta fara
ringing taga ita ke kira.
“Ina kuma kika shige kika barni”. Yasmeenah ta tambaya. Laylah ta kwatanta mata inda
suka zauna. Kan ka ce mai sai ga Yasmeenah a gun. Buda baki tayi cike da mamaki da ta isa
taga Laylah tare da dan yaro sai kashe hotuna suke ta yi abunsu basu ma lura da isowar ta
ba.
“Yaron wa kika samo?”. Yasmeenah ta tambaya.
“Is she your mom?”. Fadeel ya tambaya yana kallon Yasmeenah “Can I call you grannie?”.
“Kai! Kiji yaro zai mai da ni tsohuwa. Call me Yasmeenah”. Ta fadi tana wasa da gashin
kansa wanda ya taru sosai. Sake tambayar Laylah inda ta sama yaro tayi ita kuma ta
kwashe komi ta fadi mata. Ita kam Yasmeenah lokaci guda tajo yaron ita ma ya shiga ran ta.
Zama tayi ta sa shi a cinya tana ta mai wasa tace Laylah ta musu hoto tare.
Shikam Abdulmalik yana can daga zuwa ya ansa waya ya barwa Tariq amanar Fadeel
amma kuma da ya gama wayar ya dawo sai ya izza babu Tariq bare Fadeel a inda ya bar su.
Wayar Tariq din ya dinga kira amma kuma baa dagawa duk hankalinsa ya tashi. Tunani ya
fara koh anyi kidnapping dan sa ne. Nawfal wanda suka bari a gida ya kira kai tsaye yana
tambayar sa koh Tariq da Fadeel sun dawo gidan ne amma yace mai aah. Hankalinsa ya da
da tashi ya ce wa Nawfal ya same sa da sauri a park din, yana tunanin kidnapping dinsu aka
yi. Be zauna ba ya cigaba da Juyawa cikin park din yana neman su amma shuru har Nawfal
ya is
Shima kam Tariq tsurewa yayi, daga an bar masa yaro, Fadeel ya matsa mai ya sa tsiwa wai
sai sunyi playing hide and seek kuma in ya ci sai ya siya mai play station. Ba yadda ya iya,
haka nan ya yarda saboda tsananin nacin Fadeel. 30 minutes kenan tunda Fadeel ya ruga
wai dun ya buya amma shuru be gansa ba. Gashi ya mance wayar sa a mota bare ya ce zai
dauko ya kira Abdulmalik yaji koh Fadeel na tare dashi. Kwata kwata tunanin ya je ya dauko
wayar a mota be zo masa ba kawai yawo yike ta yi cikin park neman yaro. Ya san kashin sa
ya bushe indai ya koma gun Abdulmalik ba tare da Fadeel ba. Sanin kowa ne yadda
Abdulmalik ke matukar ji da dan nasa. Gudun kada wani abu ya same sa ne ya sa ya hana a
sa shi a makaranta instead ake zuwa gida koya mai karatu. Tariq dai yayi ta yawo yana
gumi.
Shikam Fadeel na can yana ta wasa da su Laylah, duk ya bi ya cika su da surutu. Suna ta cin
dariya, duk dan yaron ya saci zuciyar su har lokacin ya wuce basu ankara ba kuma tunanin
ce masa ya tafi gun iyayen sa be zo musu ba. Suna cikin hirar su da Fadeel, yana basu
labarin elephant inda ya gani na fada da monkey lokacin da yaje India holiday, wai har
elephant din ya nemi ya zaune cikin monkey din amma ya shiga ya raba su kawai suka ji an
kwala ihun sunansa.
“Muhammad Fadeel!”.
Koh da zasu wuce gida, Yasmeenah ta miqawa key din mota ta ce mata ta tuqa. Jikinta duk
yayi sanyi. Lumshe idanu tayi ta settling sosai a seat din motar. Koh da ta rufe ido, vivid
picture din abunda ta gani earlier ne ke ta yawo a kanta.
Suna cikin hira ne wani wai assistant din mahaifin Fadeel ya hango su ya zo daukar yaron.
Da gudu Fadeel ya miqe, ya manna wa Yasmeenah kiss a kumatu, ita ma Laylah ya juyo ya
yi hugging dinta sannan ya manna mata kiss a both cheeks dinta.
“l owe you”. Ya fadi kan ya ruga. Juyawar da yayi ya ruga da gudu ne Laylah ta lura da
rubutun da aka yi a bayan Tshirt dinsa.Fadeel Al-Haydar. Koh da ya qarasa gun
wanda yazo daukar sa, ta ga ya rada wa mutumin abu a kunne sai mutumin ya ciro pen da
wani dan kamar complimentary card da aka basa ya bawa yaron. Juyowa Fadeel yayi ya
dawo da gudu yana magana numfashin sa sama sama saboda gudun da yayi.
“Yo..your nu..mber”. Ya miqa mata dan card din da pen. Bata iya cewa komi ba kawai ta
rubuta mai number dinta ta basa. Da gudu ya ruga akai akai yana Juyawa yana daga musu
hannu har ya bace musu da gani. Qarar horn inda Yasmeenah ta saki wa wani me keke
napep ne ya dawo da ita reality.
“Hmmm Yasmeenah”. Ta kira sunan a hankula.
“Yes bae”
“Yanzu wancan yaron dan khalifa Al-Haydar ne?”.
“Do you need to question me again? Tun yaushe Google yayi confirming mana dan sa ne.
Muhammad Fadeel Al-Haydar”
“Fadeel yace da Babansa yazo park din. Kenan we were close to meeting khalifa Al
Haydar”
“Ke fa wannan obsession din ya fara yawa. Dan Allah ki mance wannan Al-Haydar din. Ya
sha karfinmu”. Shuru ta yi ta cigaba da nazari har ta ciro waya ta fara kallon hotunan ta da
Fadeel. Yaron ya tsaya mata a rai sosai. Sannan kuma wannan mutumin da yazo ya dau
yaron ta san ta taba ganin sa a wani gu amma kwata kwata ta rasa inda ta taba ganin sa
gashi ta fadi wa Yasmeenah ta karyata ta, wai maybe deja vu ne kawai. A haka suka isa gida
ba me cewa kowa komi. Laylah na Wucewa dakin ta ta fara shirin kwanciya kasancewar the
next day a very busy day for her.
Haka rayuwa ya cigaba, Laylah nata aikin ta. Aside from sayar da jikinta, Laylah tana da
cover business wanda take wa iyayenta karya dashi. Tana events planning and
management wa mutane in suna da sha’ani especially kuma mutane na alfarma, masu
naira. Daga nan kuma atimes take haduwa da manya mutane, kusoshin qasa.
Ranar da aka sa na fundraiser event din ya iso. Kowa ya so aikin da Laylah da team dinta
suka yi. Yadda tayi planning event din ya burge kowa and Alhamdulillah masu kudi da yawa
da politicians sun halacci tarun dun haka aka sama donations da yawa. Zuciyar ta fara
bugu tayi sosai da sosai da taji an ambaci sunan Khalifa Al-Haydar, cewa be sama damar
zuwa taron ba amma ya aika aminin sa Nawfal Muhammad Fadoul yayi representing dinsa.
Daga kai da Laylah zata yi ta hadu da abun mamaki.
Rufe idanunta tayi ta kuma budawa dun confirming koh what she was seeing was really a
reality. Abdulmalik ne tsaye a gefen Nawfal suna ta gaisawa da mutane. Koh da ya dago
idanunsa basu fada koh ina ba sai a kan Laylah. Nan suka tsaya suna ta kallon jurna.
Miqewa tayi jiki babu sauran karfi ta fara tafia. Kawai tuno last day dinsu tayi a Australia
and all that ensued between them taji kunyar sa ta kamata. Gani take kamar bata kyauta
mai and in ta tsaya a gun sanin yana kusa, da wuya ta iya controlling emotions dinta dan
koh a lokacin da ta gansa, ji tayi kamar ta ruga da gudu tayi hugging dinsa, ta fadi mai how
much she missed him. Ji kawai tayi an riqo mata hannu.
“Bamu gaisa ba zaki wuce. Haka kika tsane ni? Koh hello ba zaki iya tsayawa ki mun ba?
Koh kina kunyar aga kina magana da driver ne”: Ta ji muryar that she had been longing to
hear for weeks. Dogon ijyar zuciya ta sauke kan ta juya tayi facing dinsa. Ta kai minti biyu
duk ta rasa me zata ce mai kawai sai tayi following instincts dinta. Jawosa tayi jikinta tayi
hugging dinsa lightly. A hankali ta sauke ijiyar zuciya, taji lokacin daya hankalinta ya
kwanta. Kanshin cologne dinsa me dadi tayi ta shaqa taji kamar kar ta sake sa amma kuma
da ta tuno islamically it’s not right tho wasu suna yi, ita ma tana cikin masu yi tunda ita har
jiki take sayarwa bare kuma wani hug. Sai dai kuma bata san wani kalar mutum ne shi ba
tho lifestyle dinsa clearly shows how social and western he is kuma gashi cikin mutane
suke.
“T’ve missed you”. Tayi saurin zame jikinta daga nasa “Sorry if I was too forward, I was just
overwhelmed by your presence”
“Shhhhhh” ya sa mata yatsar sa a baki. “I’ve missed you more”. Ya fadi yana mata irin
murmushin nan da ke hanata barcin dare. Wani sonsa ke da da shiga zuciyar ta. A da, she
was living in oblivion, Kullum tana yaudarar kanta cewa ba sonsa take ba amma tun dan
months inda suka yi basu ga juna ba ta tabbatar da lallai sonsa take, Sosaima kuwa ba
kadan.
“Shine baka neme ni ba?”. Ta fadi tana dan bata rai.
“Ke fa kika nuna baki son na neme ki. Ba ajinki bane yawo da driver”
“Ni nace maka haka?”. Ta fadi tana rolling idanu. Dariya yayi kan ya bata haquri a zuciyar sa
kuma yana ta murna ne. What she just did ya tabbatar masa da cewa abunda yike feeling
for her isn’t one sided, ita ma from all indications she feels something similar.
Sannu a hankali suka taka zuwa parking lot, inda Laylah tayi parking hadaddiyar motar ta
me qirar BMw. Buda motar tayi suka shiga suka bar kofofin a bude sabo da tsananin zafi da
motar yayi. Sun jima a zaune ba wanda ke cewa kowa komi sai dai su dan saci kallon juna.
Ita ta fara buda baki ta yi breaking silence din.
“How has life been?”.
“Alhamdulillah”. Murmushi tayi kawai bata ce komi ba kuma. “Soooooo are we still
buddies?”. Ta tambaya.
“Depends on you, in baki damu da zama friends da mere driver ba”
“What ifI don’t want friendship?”. Ya tambaya. Shuru tayi ta dade tana nazari kan ta buda
baki tayi magana.
“T’m cool with it. Just say the word and l promise to disappear without a trace”.
“Oh really” Ya juya ya Kalle ta da kyau yana daga mata gira. Lura yayi da expression din da
ke fuskar ta, kamar ya sanja. “So as I was saying”, ya tsaya ya san gyara murya “What if l
want something beyond friendship?”.
“Something like?”. Dariya yayi kawai be ce mata komi ba. Pen inda ke breast pocket dinsa
ya ciro ya jawo hannunta ya rubuta number dinsa a kan tafin hannun. “Call me when you
have the answer, and remember i’ll be cool with whatever your response is. Fi waqt akhar”
Ya fita ya rufe mata door din motar. Tana kallo ya wuce cikin hall inda ake fundraiser event
din koh Juyowa ya sake kallon ta be yi ba. Kai kawai ta ije kan steering wheel din motar
zuciyar ta na mata saqe saqe iri iri ga wani irin sonsa da ke da da shiga ran ta.
One thing she has noticed about Abdulmalik is that gashi dai talaka amma sai shegen
attitude. Gashi da charisma and wani aura na power da yike da. Duk sanda zai yi magana,
babu tsoro bare fargaban wani abu ya faru yike yi. Maganar ma in zai yi sai ya dau lokaci
yana nazarin words inda zai furta, Yanga dai da jan aji akwai shi sosai a gun sa. In ba
Abdulmalik ba, wana driver ne har ya kai yawa Laylah magana the way he just did.
Murmushi kawai tayi, arrogance is a quality she had always adored in men. Rufo door din
gefen ta tayi ta ja motar ta zuwa gida mind dinta too preoccupied with thoughts. Sai da ta
kai gida tukun ta kira P.A dinta wanda ta bari a can gun event din.
Abdulmalik kuma tunda Tariq ya dawo dauke da Fadeel a kafadar sa suna wasa ya hau mai
fada akan irin tsoron da suka basu. Shi dai Tariq be ce komi ba yayi ta bada haquri. Fadeel
ne ya fara bawa mahaifin nasa labarin new friends inda ya hadu da. Tariq be ce komi ba sai
da ya bari suka shiga cikin gida tukun ya nufi hanyar study din Abdulmalik inda ya same sa
har ya shiga ya kama aiki a computer dinsa.
“Sir..”
“Yes Tariq… what’s the problem?”. Ya tambaya.
“Ummm ba wani serious abu bane”. Ya fadi yana sosa kai “dama..”
“Look Tariql don’t have all day, dama me?”
“The lady little master was talking about, it was her sir. Laylah, the lady from Australia”
Dago kai Abdulmalik yayi yana kallonsa.
“Laylah? You’re sure of that?”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *