ƁATACCEN YANAYI CHAPTER 8

ƁATACCEN YANAYI








CHAPTER 8






A haka suka fara kokawa, uncle Mukhtar na kokarin cin ma burinsa a kan ta ita kuma tana kokarin kwato kanta. Gashi ba abun ta saki ihu ba, ya toshe bakin ta. Cikin wannan halin ba wanda a cikin su ya ankara da shigowar motar auntie Sarah gidan ba sai da suka ji motsi, alamar ana kokarin buda lock din dakin. Nan uban gumi ya fara keto wa uncle Mukhtar, Tabbas yau dubun sa ta cika. In Sarah ta kama sa kashin sa ya bushe, wa zai dinga nemo mai projects kuma dun dama duk projects in da ake kawo masa dan uwan ta ne ke masa hanya. +

Nan da nan basira tazo mai, ya buda button nasa biyu ya fada kan gado kan ya jayo ta ta fado saman sa.

“Dan Allah kiyi haquri ki rabu dani. Bazan iya yaudarar mata na ba, in ba ke ba Badejo wani irin kyautatawa ne Sarah bata miki…….”. Ya dinga fadi a lokacin da auntie Sarah ta shigo dakin.

“Me zan gani haka”. Ta fadi tana sakin wayoyin da ke hannunta da key din motar ta a qasa. Cikin hanzari Badejo ta sauko jikinsa ta dau kallabinta wanda tuni ya fadi qasa. Qasa kawai tayi ta fara rokon auntie Sarah.

“Wallahi auntie ba haka bane….. Un…..unc….uncle ne…..”. Bata gama magana ba auntie Sarah ta matso kusa ta cakumo ta ta fara jan ta waje, suna isa gun da daya daga cikin masu aikin gidan ke gugan uniforms din yara auntie ta tsaya.

“Sai kin ci uban ki yau wallahi”. Ta fadi kan ta kwata iron din me zafi daga hannun me gugan zata na na wa Badejo a fuska.

“Auntie dan Allah kiyi haquri, wallahi uncle shi yace naje na gyara mai daki”. Ta fadi cikin hawaye.

“Shine kika ce bari kiyi using opportunity ki mun seducing miji koh, wallahi sai kin ci na jaki yau”. Auntie Sarah ta fadi tana kai wa fuskar Badejo hari da iron din ita kuma ta kauce da sauri ta hanyar duqawa sai saukar iron din ta ji a bayan ta ta saki wata ihu me karfi. 1

“Ai Allah yau sai nayi disfiguring wannan fuskar da kike alfahari da ita, har kike ganin zaki iya kwace mun miji. Kai Musa qara zafin iron din”. Ta fadi cikin zafin rai. Ta daga hannu zata kuma sakin wa Badejo iron din a jiki wani namiji ya zo ya riqe ta gam.

“Sarah! What’s this? Me ya faru”. Ya tambaya.

“Nawfal ka rabu dani, yau sai na kassara yarinyar nan. Ta rasa wanda zata bi sai mijina”. Ta fadi tana fisge kan ta amma ina dan uwan ta ya mata riqo sosai ta kasa kwance kanta daga riqon. Da kyar ya shawo kanta ta ije iron din suka fara tafia, Badejo kam na gun tana ta faman shara kuka, ga zafin qazafin da aka mata ga zafin qunar da tayi. Koh bakin door din barin dakin basu isa ba auntie Sarah ta saki wata ýar ihu, water dinta yayi breaking. Nan da nan Nawfal ya dago ta yana kwala kiran uncle Mukhtar ya fito. Cikin hanzari aka wuce da ita asibiti.

Ita kam Badejo na isa quaters dinsu ta fada Jikin zainaba tana kuka tana fadi mata duk abunda ya faru. Zainaba ta rungumo kawarta suka ta kuka tare, sai da suka yi kukan ta ishe su kan zainaba ta miqe da niyyar dressing ma Badejo burn dinta. Auntie Sarah kam tunda aka wuce da ita hospital sai bayan 2 days suka dawo gida ta haifi danta santalele, Aikam a ranar da ta dawo Badejo bata qara koh da 30 minutes ba a gidan.

Tana shiga ta izza ta kitchen ta jawo ta waje a wulakance tace wa wata mai aikin gida ta je ta kwaso mata kayanta ta bar gidan. Masu aiki ne sun kai su biyar suka taru ana ta ba auntie Sarah haquri, at least ta bari kashe gari da safe, yanzu ina zata cikin dare haka, an riga da anyi sallah isha’i. Sam auntie Sarah tayi kememe kan cewa Badejo baza ta kuma kwana mata a gida ba dan haka tayi mata watsi da kaya a waje tare da kudi naira dari biyu wai tayi kudin mota dashi zuwa yola dun mugunta da rashin imani. A ina dari biyu zata ishi mutum kudin mota daga Abuja har zuwa yola.
Haka Badejo ta mike ta kakkabe jiki ta tsinto kayanta tana hawaye. Yanzu ita ya zata yi? Ina zata je, ina zata sama kudin motar komawa gida kuma in ma ta koma tace wasu Ummati menene? Takaicin Hamma Suraj ma kadai ya ishe su bare kuma su zo su ji dalilin barin ta gidan aikin ta. +

“Ya Allah gani gareka, ka zaba mun abunda ya fi alkhairi a gareni”. Ta fadi ta cigaba da tafia ba tare da tasan inda take zuwa ba. Haka ta sha tafia har kusan goman dare kan ta isa tashan da suka sauka farkon zuwan su Abuja. Zama tayi shuru a wani dan dakali tana ta kallon jama’a kowa na aiwatar da abunda ya kawo sa. Ga karuwai nan suna tsayuwan neman customers, ýan tasha ana ta hayaniya, masu fada nayi, masu busar cigari nayi, masu caca nayi. Ga masu abinci nan ma iri iri. Kowa dai na harkansa. Tana cikin zaman ta shuru tana sharar kuka taji an tabo ta, juyowar da zata yi ya buso mata hayakin cigari a fuska.

“Toh ýan mata yaya ne?”. Ya tambaya tayi shuru bata ansa shi ba. “Magana nike”. Ya kuma fadi still tayi shuru. Sai kawai ya ja tsaki ya fara zagin ta.

“Shegiya, karuwa ýar iska. Daga gani gudowa kika yi daga gida. Ai bani na aike ki kwaso cikin shege ba ko ma wani laifi kika aika ta da ya sa ki barin gida. Dama na so na kaiki dakina ne ki huta nima na huta”. Ya fadi kan ya wuce. Jin haka yasa kukan Badejo ya qaru, wai ita ce yau ake kira da karuwa, ýar iska, me cikin shege.

Gani tayi zama a tashan bazai amfane ta da komi ba, dama ta so ne tazo ta roqi drivers koh akwai wanda zai ji tausayin ta ya kaita yola. Daukar ýar jakarta tayi ta fara tafia, bulayi ta ringa yi ba tare da ta san Inda zata ba, a haka har ta iso wani dan tebur kamar na me shayi haka, ya tashi sai tayi addua ta kutsa qasan tebur din inda ta tabbata ba wanda zai lura da ita ta shimfida zanin ta guda daya ta kwanta. Gaba daya daren ranar kasa barci tayi tana ta tunani iri iri. A karshe dai tayi concluding cewar zata cigaba da neman aiki kawai madadin ta koma gida haka, ta san komi yaya dai zata samu aiki. Ba ita ta sama barci ba sai kusan subh dun haka har me shayi yazo bata tashi ba. Shima sai da tin din milk daya ya fadi qasa ya sa hannu zai dauka yaji mutum, duqawar da zai yi yaga Badejo nata sharar barci, nan da nan ya nemo sanda ya kwala mata.

“Shegiya tashi! Ance miki nan muhallin mahaukata ne”. Ya fadi a tunanin sa mahaukaciya ce, ita kam Badejo taji bugun da ya kai mata sosai da sosai. A hankula ta buda ido taga ya daga sandar sama zai kuma kai mata wani bugu.


“Aah aah dun Allah, zan tashi”.
Oya maza tashi! Mahaukaciya kawai”. Ya fadi. Ita kam tana tashi ta ruga a guje, har ta mance zanin ta da ta shimfida a qasa garin sauri. Haka ta cigaba da tafia, gashi jikinta duk ya butu butu, duk inda ta gota sai an Kalle ta, har da ta tsaya wani shago dun ta sayi bread da dari biyun da auntie Sarah ta bata masu shagon suka koreta, a tunanin su zauttaciya ce ita. Tafia take ta yi ba dun ta san Inda ta nufa ba ga yunwa da ke addabar ta. Tana cikin tafiyar ta iso gun wata me koko da qosai. Nan ta tsaya matar ta saurare ta, ta siya kokon ashirin da qosan talatin. Ba dun zai ishe ta ba sai dan tsumulmulan kudi. Dari biyun nan was the only cash she had. For 4 days haka Badejo take ta bulayi a streets din Abuja har ta gama kashe kudaden hannunta tas, ta fara yawo on an empty stomach. A rana na biyar ne tana tafia ta iso wani qaton building wanda offices ne. A bakin entrance din building din taga banner which read; *Secretary, receptionist and cleaners needed* cike da farin ciki ta dosa hanyar building din, da niyyar shiga ta gwada luck dinta koh Allah zai sa a dace tunda duk gidajen da ta kwankwasa tun a gate ake sa me gadi ya zuba mata mai. +

“Ke dallah ina zaki shiga”. Me gadin building din ya kwalla mata tsawa.

“Aiki nazo nema”. Ta basa ansa.

“A hakan?”. Ya nuna ta da hannu yana ýar dariya “Daga gani wannan sabon hauka ke damunta”. Ya fadi yana dariya. Kuka ta fashe mai da tana mai bayani cewa ita ba mahaukaciya bace, situation ne ya maida ta haka sai yaji ta bashi tausayi.

“Kinga yanzu yamma tayi, boss karfe 4 yike barin office kuma yanzu hudu saura minti 9, ki dawo gobe da karfe takwas haka sai ki gansa koh Allah zai sa a dace”. Ya bata shawara. Godia ta mai, har ta juya zata wuce ya tsayar da ita.

“Baiwar Allah, kiyi wanka kuma, ba zaki iya shiga da wannan warin da kike yi ba”. Ya fadi.

“Toh a ina zan samu bayin yin wankar? Kusan kwanana goma kenan bani da gun sa kai”. Ta fadi ta cigaba da tafiyar ta sai kuma taji ya kirata.

“Baiwar Allah dawo”. A hankula ta koma. Murmushi ya mata yace ta shigo, sannan ya mata nuni da ta zauna kan dakalin dakinsa. Tana zama yace mata ta shiga dakinsa tayi shirin wanka, tana ta shakka koh dai wayo shima yike son mata amma sai ya tabbatar mata da bazai cuce ta ba, yana da diya sa’ar ta. Dun haka Badejo tayi addua a zucin ta kan ta shiga dakin. Kayan jikinta ta tube kan ta daura zani jikinta ta sa dan hijaab tazo ta shiga wanka. Ta dade tana cuda jikinta, sai sai da tayi ensuring tas dirt inda ke jikinta ya fita kan ta watsa ruwa, ta tsane jikinta ta fito. Tana fitowa ya fadi mata inda zata ga man shafawa. Sai da ta gama shirin ta tas, ta sa kaya masu tsafta kan ta fito da zauna kan dakali ta fara mai godia. Kwanon abinci ya turo mata da ledar pure water shima ya ije daya gabansa. Yadda yaga tana rushing din abincin ya basa tausayi, kan kace me ta share kwanon tas, cikin tausaya wa ya miqa mata nasa kwanon. Tana kallonsa ta gefen ido ya share hawaye sannan ya miqe wai yana zuwa.Yana tashi shago ya wuce ya siya soap da detergent yazo yace ta kwaso kayan dattin ta ya wanke mata su tas, sannan ya goge mata wasu masu kyau wanda auntie Sarah ce ta bata kwance, yace ta sasu gobe in zata gun boss. Ya bar mata dakinsa ya shimfida tabarma waje ya kwanta. Early the next morning ya tashe ta tayi sallah sannan yace ya ce ta shiga wanka ta shirya. Tsaf ta shirya ta fito, lafiyeyyen tea da bread har da egg na jiran ta. Cikin hawaye ta dinga mai godia da zata wuce. +

“Na gode sosai Baba Haruna, ba zan taba mance wannan taimako da ka mun ba. Allah ya saka maka da alkhairi”.

“Ahhh haba Badejo, ai yi wa kai ne. Allah bada saa, Allah ya taimaka. Kinga zuwa anjima kadan zan wuce can zamfara ganin gida ba lallai ki dawo ki izza ni ba, sai dai abokin aikina. Amma ga wannan ki riqe, ba yawa”. Ya sa mata naira dari biyar a hannu. Kuka take sosai tana mai godia, ya mata fatan alkhairi. “Ina fatan in na dawo mu kuma haduwa, Allah sa ki sama aikin”. Tace Ameen kan ta wuce.

A hankula ta taka har zuwa main entrance din building din, sai da tayi ýar addua kan ta tura kofar ta shiga, receptionist din cikin fara’a ta tambayi abunda ya kawo ta, ta fadi sai tayi directing dinta to 5th floor din building, wai a nan office din boss yike. Har 12 suna zaman jira kan boss din ya iso ya fara attending to mutane masu son ganinsa. Sannu a hankali har aka iso kan Badejo.
A hankula ta buda kofar ta shiga. Wani mutum ne zaune a kujera, a wulakance bazai wuce yana late 30’s dinsa ba koh early 40’s. Da ka gansa ka ga naira da hutu, ba zaa kirasa mummuna ba at the same time kuma ba wai irin wannan tsinannen kyau garesa ba, he’s just okay. Cike da murmushi ya tarbeta.

“Ýan mata sannu koh”. Ya fadi yana mata wani kallo wanda yayi shige da irin kallon da uncle Mukhtar ke mata.

“Yallabai ina yini”. Ta rusuna tana gaida shi cike da girmamawa.

“Yawwa malama sannu, Bismillah zauna mana”. Ya fadi. Jiki na rawa ya buda fridge ya dauko juice ya ije mata. Ita kam Badejo sai mamakin fara’ar mutumin take dun tun jiya Baba Haruna ke fadi mata ba wani mutunci ne da boss ba. “Toh me ya kawo ki?”. Ya tambaye ta.

“Aiki nazo nema”. Ta fadi kawai taga ya fashe da dariya.

“Aiki? Toh kina da takardun ki?”. Ya tambaya tace mai aah ita shara ma take so dun ba takardu gare ta ba, koh school cert bata da.

“Amma kinga shara be kamaci yarinya tsaleliya irin ki ba. Kinga ki a mudubi kuwa. Ba wanda ya taba fadi miki kina da kyau?”. Ya tambaya tayi shuru. “Kamata yayi ace kin zama secretary na, post din zai an she ki sosai”.

“Da gaske”. Ta dago kai tana kallonsa da ýar murmushi. Gani tayi ya lashi labbansa yana mata murmushi.

“Ehh mana, kuma albashin ya fi tsoka”. Ya fadi mata. “Amma kuma gashi baki da takardu”.

“Toh ai matsalar kenan”. Ta fadi tana dan tabe baki. “Ni dai kawai in zan sama sharan falillahil hamd”.
Kinsan ya zaa yi, naga kina da hankali, kuma kin kwanta mun a rai. Goro kawai zaki ban na baki aikin, a matsayin secretary na”. +

“Kai haba! Goro wannan, toh bara nai maza na je na siyo”. Ta miqe tana fadi. Har tayi hanyar qofa ya tsayar da ita.

“Ke dawo, ba wannan goron nike nufi ba”.

“Toh wanne?”.

“Zauna man tukun”. Ya fadi mata “wato kinga koh, ke yarinya ce me matukar kyau, ga ki da elevations; front and back. Kin hadu wallahi, kamar hadari. I just want a glimpse through your veil. Kina jin turanci ai koh”.

“Ehh ina dan ji amma fa ban gane zancen ka ba”.

“Kin gane koh, guesthouse dina ya kamata muje, ki huta mu dan shakata. Gobe sai ki fara aiki. Albashin ki dubu sittin”. Salati kawai Badejo ta saki, wai ita meyasa duk mazan da take haduwa dasu ke neman ta da alfasha ne, ba me so ya taimaka mata fisabilillah. Duk jikinta suke bi. Hakika kyau ma wani lokacin in yayi yawa ya kan zamo jaraba.

“Aah nikam, bazan iya ba”.

“Haba ýar gari, so daya fa kawai. Ai ke ba kalar talaka bace ba wallahi”.

“Amma ni ýar talakawa ce, a cikin ta na tashi, a kauye kuma Kullum cikin godiyar Allah nike”.

“Baki so ki bar rayuwar kauye? Baki so ki zama big girl. In biya miki hajji da umrah, in kaiki India mu huta. Da mun dawo na turo gidanku”. Ya fadi, all in an attempt to convince her “kinji ýar budurwa, so daya kawai, bazan bata lokaci ba. Kan ki sani munyi mun gama”.

“Auzubillahi min nas-shaydanir rajim”. Ta fadi “Ka cinye aikin ka baa so, Allah shine gata na, bazan saba mai ba dun biyan buqata ta”. Ta miqe ta wuce shikam ya ja tsaki yana zagi.

“Shegiya, da kafafun ki zaki dawo. A ina zaki sama aiki a sama in Abuja. Koh ba nan ba sai kin sayar da Jikin ki can wani gun”. Ya fadi kan ya cigaba da aikin sa.

STORY CONTINUES BELOW

Ita kam Badejo na fitowa daga building din bata kai ga gate ba sai dan wayar da ke hannunta ya hau ruri. Tana dubawa taga Ummati ce. Sai da ta saki ýar ijiyar zuci kan ta ansa wayar. Tana danna answer button ta kafa wayar a kunne sai taji Ummati koh sallama bata mata ba kuma bata ansa gaisuwar ta ba. Cikin murya me nuni da kuka take ta dinga magana.

“Ummati lafia?”.

“Ba lafia ba Badejo, ba lafia ba. Abban ki….. Suraj….. Auta”. Duk Badejo ta rude.

“Ummati ki Kwantar da hankalin ki muyi magana mana”. Da kyar ta samu mahaifiyar nata ta sauko ta fara mata bayani. Tunda ta fara magana Badejo taji kanta yayi wani mugun nauyi, taji ta kamar baa duniya take ba kuma, yadda ka san ana buga mata bell da karfi a saitin kunnenta haka take ji.

“Dan Allah ki roqi hajiyar ki, in zata iya biyan ki kudin aikin ki ma wata biyu koh uku, ki rufa mun asiri Badejo. Ban san yadda zanyi ba”. Ummati ta fadi kukan ta na qaruwa. Karfin hali Badejo kawai tayi tana rarrashinta..
Karki damu Ummati, zanyi magana da ita, Insha Allahu zaa san yadda zaa yi kinji. Kiyi ta mun addua Ummati na, Allah ya yaye mana wannan qangin rayuwar da muka samu kan mu a ciki”. Ta kashe wayar kan ta zube a qasa tana ta sharar hawaye. Ita yanzu ya zata yi, daga ina zata fara, ta ya zata fara fadiwa Ummati an koreta gun aiki, daga ina zata sama dubu sittin ta tura gida. Kai! Allah gata bawan, gashi the only person da ta sani baya nan, Baba Haruna ya riga ya kama hanyar zuwa ganin gida. +

Zaman ta a qasa zancen Ummati kawai ke ta mata yawo a kai, wai Abban su jiki ya tashi rai hannun Allah, oxygen ma aka sa masa ana buqatar kudi in ba haka ba zaa cire, gashi Suraj ya siyar masu da only asset in su da ya rage, gidan da suke ciki, abun takaici ma a wulakance ya siyar da gidan ya kashe kudin a banza gashi yanzu an basu notice din satin biyu, gashi ya je ya yi fada an sari ďan councillor an rufe su a prison, ana neman bail din dubu ashirin in ba haka ba zaa wuce da magana sama. Kai Allah! Gashi Auta zata zana entrance exams dubu goma sha biyar, shima deadline din biya nan da sati biyu. Badejo ta dade a gun tana kuka kan ta miqe ta wuce bakin gate din building din ta zauna, duk ta rasa abun yi, ina zata je, daga ina zata fara, gun wa zata nemi taimako.

Har yamma tana gun a zaune shuru kowa da yazo Wucewa sai da a Kalle ta a wuce, har karfe hudu yayi. Tana zaune lokacin da aka buda wa boss mota, tana hango shine ta miqe ta dosa motar, yana ganin ta shima yayi slow down ya budo mata door din gaba. Tana ganin haka ta shiga ta zauna shuru, for like 10 minutes ba wanda yayi magana a cikin su.

“Ya aka yi? Kin sama aikin ne”. Ya tambaye cikin tsokana.

“Zaka biyani albashina gobe? Da na fara aiki”. Ta tambaye sa.

“Eh eh! Zan qara miki dubu ashirin akai ma”.

“Toh muje”. Ta fadi, wasu hawaye masu sanyi na gangarowa daga idanunta. 4

Suna isa ba tare da wani bata lokaci ba boss ya fara aiwatar da niyyar sa a kanta. Shikenan! Ta aikata abunda ta dade tana gudu, abunda Ummati ke gargadin ta Kullum Kullum da ta gujewa, yanzu da wani ido zata kalli iyayenta, Abban ta most especially. Da wani ido zata hadu da creator dinta. Me zata ce, shikenan zancen aure tsakanin ta da Mahmoud ya qare?, ita da ta mai alkwari zata tsare mutuncin ta. Shikenan ta zama victim of circumstances. Yadda Badejo taga rana haka taga dare ranar, ta kasa barci taji duk kyama take ba kanta, ina ma ana iya juya hannun agogo.
‘It’s the first and last time, you did it for a good cause. You need the money, be strong, be very strong’. Abubuwa ne iri iri suka dinga mata yawo a kai daren ranar har zuwa wayewan garin Allah. Miqewa tayi taje tayi wanka kan tazo ta sanja kaya tayi sallah, har zuwa lokacin barci yike be tashi ba. Yana tashi ya Kalle ta yana murmushi yana neman ya sake abunda da yayi daren jiya da ita amma ta qi basa hadin kai. Sai da yayi wanka ya fito ya shirya kan ya kirawo masu aiki aka kawo breakfast. Badejo kwata kwata bata da appetite dun haka fridge kawai ta buda ta dau robar ruwan sanyi ta sha kan ta miqe ta ce mai zata wuce. +

“Yaushe zan fara aikin?”. Ta tambaya.

“Aiki?”.

“Ehhh, aiki”.

“Dama akwai zancen aiki between us, kawo shedar ki”. Ya fadi yana wata ýar muguwar dariya. “Ke dabbar ina ce? Ke har kin kai matsayin na baki aiki a babban firm kamar nawa. In ba sakaren mutum ba wa zai ba village champion irin ki aiki”. Ya ja ýar tsaki. 1

“Dandanon ki kawai na so naji”. Ya fadi yana lasar labbansa “and wallahi you’re tasty, koh Zuma bazata fadi fadi miki zaqi ba”. Ya saki wata ýar dariya. Ita kam lokacin Badejo tuni ta zube a qasa tana sharar kuka.

“In kin yarda zan baki aiki, ki dinga debe mun kewa a duk sanda nike buqatar haka”, ya fadi yana daga mata gira.

“Allah kiyaye na zama karuwa”.

“Dallah rufe mun baki, jahila kawai. Yanzu da ke da karuwan me bambamci”. Ya fashe da ýar dariya kan ya sa hannu hannu a cikin aljihun wandon sa ya ciro kudi naira dari biyar ya wurga mata. 2

“Ga wannan kya sha pure water ki huce zafi. Aiki kuma Allah ya sa a dace”. Dirshen Badejo ta baje a qasa tana rusa kuka shikam koh a jikinsa. Me tayi ne? Wannan wana irin hali ta sa kanta a ciki? Gashi yanzu ta tashi da biyu babu, ba kudi ba budurci, ta bayar dashi on a gold platter to someone not deserving of it at all. Wai Allah! Yanzu ya zata yi ne, gashi ta ba Ummati assurance zata turo kudi. Tana cikin wannan halin ne wata mata ta shigo, sanye take da kaya matsatsu, ýar budurwa ce da bazata wuci 25 years ba. Tana isowa ta zauna cinyar sa suka fara romancing juna gaban ta ba kunya ba tsoran Allah.

“Wannan kuma wacece?”. Yarinyar me sunan Rosie ta tambaya.

“Bara wai ta shigo mun, na ce mata tayi haquri, ga dari biyar na bata ta qi wuce wa”. Ya fadi, hannun sa nata yawo Jikin Rosie. Wani harara ta ballowa Badejo tare da daka mata tsawar ta tashi ta basu gu. Tsananin takaici Badejo ta miqe ta dau dan ghana must go dinta ta bar dari biyar din a qasa, inda ya wurgo mata. A zuci tana ta mai Allah ya isa da fatar baza ya taba qarewa da duniya lafia ba.

Fita tayi tana ta tafia ba tare da sanin inda ta dosa ba, ita dai gata hannun Allah. Kwana uku ta yi tana tafia ba tare da sanin inda take nufa ba, duk inda dare ya riske ta zata kwanta tayi addua ta yi barci, yunwa kam har yana neman illata ta. Duk ta lalace, tayi wani iri. A rana na hudu ne, da yamma haka, gari ya fara duhu, tana zauna kusa da kofar wani gida taga yaran gidan guda biyu mace da namiji sun fito zubar da shara ta hango ledar wani bread da ya fara hunhuna a cikin bolar da zasu zubar. Sai da ta bari suka zubar suka wuce kan ta isa gun da gudun ta ta ciro bread din ta hau kan ci, ci take ta yi kamar yaqi, tana ci hawaye na sauka daga idanunta.
Wata motace haddaddiya ta zo tayi parking daidai inda Badejo ke zaune tana cin bread dinta. Whining tinted glass din motar aka yi, wata matar zaune a bayan motar wadda duk a kan idanunta Badejo ta bi bola ta dau bread din ce tayi magana cikin sanyayyyar murya. +

“Ke yarinya”. Ta kira amma shuru Badejo bata dago ba saboda bata ji ba.

“Madam gani nike fa kamar mahaukaciya ce”. 1

“Aah Sule, wannan bata yi kama da mahaukaciya ba. Mun kai 10 minutes fa muna kallon ta. Ba alamar hauka a tare da ita”. Tana gama fadin haka ta sauko daga motar ta dosa inda Badejo ke zauna tana ta famar tura bread dinta koh ruwa babu.
A hankula matar ta taka har ta isa inda Badejo ke zaune tana ta gabzar bread dinta, koh lura da matar bata yi ba. Koh da matar ta zuquna, ta dade tana kallon Badejo idanunta cike da kwalla kamar tana tunanin wani abu. Ta dade a zuqune kan ta sa hannayenta biyu a kan cinyoyin Badejo. +

“Ýan mata”. Ta kirata a hankula. Ido kawai Badejo ta zuba wa matar bata ce mata komi ba. Can kuma dai sai ta buda baki tai magana.

“Lafia?”. Ta tambaya matar.

“Ina gidan ku yike?”. Tambayar da matar ta fara mata kenan. Sai da Badejo ta dau lokaci kamar tana nazarin wani abu kan ta nata ansa.

“Can yola”. Ta fadi kan ta kuma gutsurar bread dinta.

“Yola!”. Matar ta fadi cikin mamaki “Me kike yi nan Abuja toh”. Ta tambaya amma Badejo koh kallon ta bata yi ba bare ta bata ansa, gaba daya hankalinta na kan abunda take ci.

‘Tabbas wannan yarinyar na buqatar taimako’. Matar ta fadi a zuci kan ta miqe ta kakkabe rigar ta. “Taso muje”. Ta fadi gami da miqo wa Badejo hannu amma sai Badejo ta qi, tsoran ta kada a kuma maimaita abunda ya faru a gidan auntie Sarah. Matar tayi tayi amma Badejo ta qi bin ta a haka dai ta haqura ta tashi ta wuce, zuciyar ta fal da tunani iri iri. Gashi Badejo ta mugun kwanta mata a rai, duk da cikin tsumma da datti take, haka be hana matar hango tsananin kyaun da Allah ya mata ba.

Har ta isa gida zuciyar ta cike yike da tunanin Badejo, tana ta tunanin mene zai dauko yarinya ýar budurwa kamar Badejo tun daga can gida yola, har zuwa Abuja.

“Allah sa ba abunda nike suspecting bane”. Ta fadi a hankula. Ranar dai da tunanin Badejo ta kwana, hakan ya sa ta tashi da sassafe next morning din. Masu aiki nata mamaki da suka ga ta shiga kitchen da kanta ta hada breakfast kuma tayi packing komi a cikin warmers kan tayi arranging warmers din a wani dan picnic basket ta wuce mota da shi. Da sauri take ta tuqi tana addua Allah sa ta izza Badejo cikin saa kam ta izza ta zaune inda ta ganta jiya ta zuba uban tagumi. Cike da fara’a ta sauko mota riqe da basket din ta iso inda Badejo take.

Ita ma a qasa ta zauna, ba tare da damuwa akan kayan jikinta ba. Ita ta fara buda baki tayi wa Badejo magana.
Kin tashi lafia?”. Ta tambaya. +

“Alhamdulillah…. ina kwana”. Ta gaida ta in a polite way. Silence ne ya rufe afterwards kan can matar ta turo mata basket din gami da mata Bismillah. Ganin Badejo bata da niyyar buda basket din ya sa matar budawa ta ciro warmers din da wani dan plate tayi serving dinta abinci. Cikin hanzari Badejo ta ja kwanon ta hau cin abinci, ba tare da wanke hannu ba koh wani abu. Shuru matar tayi tana kallon kwalla sun cika mata idanu, ga bisa dukkan alamu ta fada duniyar tunani. Tarin da taji Badejo nayi ne ya dawo da ita reality, cikin hanzari ta buda bottle water inda ta riqo ta miqa mata. Haka ta cigaba da shafa mata baya har tarin ya tsaya.

“Ki ci a hankula”. Ta fadi mata amma Badejo kamar ba da ita ake ba “Ya sunanki?”. Ta kuma tambaya. Sai da Badejo ta gama taunar abincin da ke bakin ta kan ta dago kai ta bata ansa.

“Badejo”.

“Ina son ki Badejo, zaki biyo ni gidana?”. Ta tambaya. Tana fadin haka Badejo ta turo plate din abincin da take ci ta matsa da baya. Kawai tuno da abunda uncle Mukhtar ya mata da kuma irin cin mutunci da auntie Sarah ta mata ta yi sai ta fara hawaye. Nan hankalin matar ya tashi ta hau bata haquri.

“Laaa dan Allah kiyi haquri, ba da wani nufi na fadi haka ba. Naga be kamaci diya mace ace tana kwana a titi ba, akwai mutane mugaye, in biki fada hannun masu fyade ba kya iya faduwa hannun cultists, shiyasa. Kiyi haquri kinji Badejo, ni fisabilillah nike son ki”. Ta gama fadi ta miqe zata wuce motar ta sai ji tayi Badejo ta tsayar da ita. Har ta fara jin dadi maybe tayi having change of heart ne amma koh da ta juyo sai Badejo tayi mata nuni da basket inda tazo dashi. Murmushi tayi kawai ta juya ta kwashi kayanta ta shiga mota ta wuce.

Attitude din Badejo towards her be sa tayi sanyin gwiwa ba dun ta tabbatar da akwai incidence inda yayi traumatising dinta har ya sa ta jin tsoron mutane da kuma rashin yarda dasu. Dun haka ta umurci cook dinta da ayi dinner da wuri. Haka kuwa aka yi, ranar by 6 pm an gama dinner, ta kuma shirya abinci a basket ta wuce wa Badejo dashi. Still dai nan gun da ta maida kamar muhalli matar ta same ta. Murmushi ta mata, ita ma Badejo sai ta mayar mata da murmushi. Abun ya matukar ba matar mamaki. Murmushi ya qara fiddo da kyaun Badejo, saboda inta yi murmushi sai kumatun ta ya lotsa, dimples inta su fito. Matar taso yaba kyaun da Allah ya mata amma sai ta hi tsoron kada ta kuma razanata dun haka ta ja bakin ta tayi shuru. Mamaki ne ya dibe matar da taga Badejo na jan ta da hira.
Na fadi miki sunana amma baki fadi mun naki ba”. Ta fadi a hankula. Murmushi matar tayi a zucin ta tana fadin it’s a progress.

“Yasmeenah….. that’s my name”. Ta fadi mata. 1

“Yasmeenah koh Yasmeen”. ta tambaya

“Toh ai duk suna daya ne, amma na fi son Yasmeenah”. Ta mata bayani tana shafa mata kai. Koh kadan Yasmeenah bata kyamaci Badejo ba.

“Baki da yara? Kullum ke da ke zuwa”. Ta kuma tambaya.

“Ďiyata daya, tayi aure tana can Port Harcourt da family dinta”. Kai kawai ta gyada cigaba da cin abincin ta ba tare da ta kuma magana ba. Sai da ta gama ci ta wanke hannu kan ta dago ta kalli Yasmeenah ta kuma magana.

“Na gode……. Allah baki abunda kike so”.

“Ameen”. Yasmeenah ta fadi tana tuno babban abunda take quduri a rayuwa. Tsam Yasmeenah ta miqe bayan ta gama hada kayanta ta nufi motar ta. Har ta buda zata shiga sai muryar Badejo ta tsayar da ita.

“Hajia….”. Ta fadi a hankula “Kin fasa tafia gida dani ne?”. Ta tambaya. Da sauri saurin ta Yasmeenah ta dawo ta riqo hannun Badejo.

“Sosaima, zaki iya bina gida”. Ta riqo ta har inda tayi parking, ta buda mata qofa kan ita ma ta wuce ta shiga ta ja mota. Suna tafe tana da jan Badejo da dan hira.

Wani gida qato suka isa, Yasmeenah tayi honking nan da nan aka buda mata gate ta shiga. Motoci ne sun kai goma parked a harabar gidan, kuma duk cikin motocin ba karami.
‘Da gani matar babba ce’. Badejo ta ayyana a ran ta.

Shiga gidan suka yi, nan Badejo ta kuma sakin baki gun kallo. Ta ma rasa a cikin gidan auntie Sarah da wannan gidan wanda ya fi kyau da tsaruwa, ga uban dukiya da aka zuba a gidan. Riqe hannunta Yasmeenah tayi har zuwa wani daki wanda ya hadu matuka. Zama tayi shuru akan gado kamar yadda Yasmeenah ta umurce ta da tayi. Ji tayi gadon na da wani shegen laushi ga uban kanshi da ke tashi a dakin. Ta bi ko ina da idanu. Can ta wani angle a dakin dakin ta hango wani dan trestle table wanda akai pictures frames ne. Miqewa tayi ta isa gun ta qurewa hotunan kallo, Yasmeenah ce da wata yarinya, ýar budurwa me matukar kyau. Hotunan da ke gun sun fi karfin ashirin amma duk na Yasmeenah ne da yarinyar, wasu a ciki tun tana yarinya har ta kai ga girma. Sai wasu guda biyu kuma wanda Yasmeenah ce da yarinyar da wani namiji, wani kuma Yasmeenah ce da yarinyar riqe da baby a hannunta.
That’s my daughter”. Ta ji muryar Yasmeenah a bayan ta “Duk duniya ban da kamar ta”. Ta fadi tana murmushi kan ta cigaba da ba Badejo labarin diyar ta. There was this kind of joy and pride a fuskar Yasmeenah a yayin da take bawa Badejo hirar diyar ta, Hakika bond dinsu is very very tight.

“Toh enough of Leek, shirya ki shiga wanka, na hada miki ruwa”. Yasmeenah ta jawo hannunta zuwa hanyar Bathroom din. Dan zaman da tayi gidan auntie Sarah ya sa ta saba da using some modern gadgets and equipment. Dun haka koh da ta shiga bathroom din, with ease tayi wankar ta ta fito although ta dade tana cudan jikinta. Tunda ta shiga hawaye ke zuba daga idanunta in ta tuna wautar da tayi.

Koh da fito, shafa mai tayi kan ta buda closet inda Yasmeenah ta fadi mata ta duba, zata sama kayan sawa. A cikin few kayan diyar ta da suka rage. Gama sa kayanta ke da wuya Yasmeenah ta budo kofar ta shigo, murmushi tayi ta kalli Badejo kan ta zaunar da ita gaban vanity table, tayi plugging din hair dryer ta fara busar mata da kai. Shuru ba me ce wa kowa komi a cikin su, har dai finally Yasmeenah tayi breaking silence din.

“Meya fiddo ki daga gida, me ya kawo ki Abuja?”. Ta tambaya.

“Aiki”.

“Aiki?”. Ta tambaya.

“Ehhh aiki, abunda ya kawo ni Abuja kenan”. Ta fadi kan ta fara ba Yasmeenah labarin ta A-Z. Tun daga rasa aikin Abban ta har ya zuwa rashin lafiyar ta, zuwa abunda ya sameta gidan auntie sarah, da yadda tayi wautar rasa budurcinta, duk ta kwashe ta fadi wa Yasmeenah. Koh da ta gama narrating story dinta, Jikin Yasmeenah ya riga da ya gama mutuwa. Ta dade ba abunda da take yi sai jan dogon numfashi. Labarin Badejo ya fama mata wani tsohon miki da ke zuciyanta, wanda a tunanin ta ya dade da warkewa or so she thought. Safaa da Marwah kawai ta dinga yi a cikin dakin kan daga baya ta matso zuwa inda Badejo take ta shafa mata baya tana rarrashinta dun kuka sosai take.

“My dear that’s life for you. You have to be strong”.

“Nima na taba fadawa cikin wani situation similar to yours. Maybe, just maybe someday nayi sharing story na da ke”. Ta fadi kan ta fita daga dakin.
……And?”. Khalifa ya tambaya da yaji tayi shuru in banda jan majina da hawaye ba abunda take yi. +

“Kashe gari da safe, Yasmeenah ta bani kudi eighty thousand na tura gida dun Ummati ta samu ta rage crisis inda family dinmu ke ciki a lokacin. Koh da na tura mata kudin, rashin lafiyar Abba kadai ya cinye dubu hamsin a cikin kudin kan aka zo aka yi bailing din ya Suraj out of prison, da kyar suka anshi dubu ashirin. Sauran dubu goman kuma bazai isa registration din Auta ba, bazai isa Ummati ta kama hayan gida ba tunda ya Suraj ya sayar da gidanmu, ga rashin kudin kula da buqatun su,……”. Ta kuma tsayawa kan after some time ta cigaba.

“Dun haka, a few days after I sent the money to them, Yasmeenah tayi wani baqo wanda a lokacin babban ma’aikacin government ne. Zuwan baqon nan ne ya wayar mun da kai, har na san asalin sana’ar Yasmeenah. She’s a pimp, connecting ýan mata take yi da manyan mutane a biya ta kudi. Dun haka ranar baqon yazo a sama me budurwa kyakyawa that’ll entertain him for the weekend sai ya ganni…..”. Ta fadi murya na rawa.

“He offered me a hundred and fifty thousand naira, I was desperate, I needed the money and afterall there was nothing left of me, tunda I’ve already lost the one thing I’ve always been urged to safeguard, na zama baqar ashana. Out of desperation nayi taking offer din, ya biyani kudina na tura gida na biya wa iyayena buqatun su. And since from that day, sunana ya tashi daga Badejo to Laylah Jaan…… The heartthrob of the whole city, the heart desire of every man. Slowly nayi ta kashe wa ýan mata kasuwa dun duk wanda yazo sai yace shima sai ya dandani zumar Laylah Jaan. It became like a competition to the men, kowa na so ace shi ya fi biyana kudi masu yawa da yayi amfani da ni”.

Dogon numfashi khalifa ya ja, koh kallon ta ya kasa ya buda baki ya tambaye ta “And your parents? Kika ce musu kina samun kudi a ina?”.

“Karya nayi musu, nasan baza su taba jin dadi sanin diyar su ta zama karuwa, me siyar da jikinta dun samun biyan buqatun ta ba dun haka nace musu na sama aiki da wata hajia me kirki kuma ta sani a makaranta sannan zata dinga tura musu kudin da zai ishe su kula da kansu har na gama karatu na fara aiki. A haka na koma makaranta, da kudin karuwanci, nayi sponsoring Auta, da kudin karuwanci, na kai ya Suraj rehabilitation har ya gyaru ya koma karatu, da kudin karuwanci, na kai Abba na kashen waje da dama, da kudin karuwanci, Ummati tayi hajji da umrah, da kudin karuwanci. Da kudin karuwanci na ginawa iyayena gidan da duk Girei ba irin sa. Da kudin karuwanci na ba the people that mean the world to me all the happiness they deserve in the world”. Ta zube qasa tana kuka kamar ran ta zai fita.
I sacrificed my love, my body, my conscience just to make them happy. Na sabawa mahallici na just to keep them happy. Na rufe jikina da zuciya ta da Jirwaye just to place food on their table and happy smiles on their faces”. Ya so ya tambaye ta ya rabuwar su da Mahmoud ya kasance amma ganin irin kukan da take yi ya sa shi karaya. 2

“You need some rest”. Abunda kawai ya iya fadi mata kenan kan ya bar dakin ya koma living room din suite din ya zauna shuru cikin utter darkness. He was just trying to digest all she told him, yana ta nazarin rayuwa, circumstances and how cruel some people can be and most of all, ba abunda ya mai zafi kamar yadda har da hannun ýar Uwar sa a cikin bacewar rayuwar Laylah. 6

Khalifa ya dade a gun zaune shuru yana nazari iri iri, kwata kwata be yi tunanin haka meeting dinsu zai yi turning out ba. Yanzu her story has thrown his heart in confusion, be ma san me yike so ba kuma, ya kasa tunanin da kyau. Can towards subh ya leqa ya sama Laylah a kwance ta ci kuka har barci ya kwashe ta a qasa. Da har kamar zai daga ta ya maida kan gado sai kuma ya sanja mind dinsa kawai ya dau tuxedo dinsa da ya jefar kan gado the previous night ya nufi exit din Suite din. Without second thoughts ya fita daga Suite din. Yana isa lobby din ya anshi car key dinsa ya fi ce. Kwata kwata be damu da koh karfe nawa bane yayi ta driving recklessly a empty streets din Abuja.
Badejo kam on the other hand ba ita ta tashi ba sai minutes past 9 the next morning. Koh da ta dudduba bata ga alamar sa ba there and then she got the message. Without being told, ta riga ta san response dinsa. +

‘No responsible guy would want to associate with a whore afterall’. Ta fadi a zuci kan ta daga wayarta tayi dialling number din Yasmeenah.

“Send the chauffer”. Ta fadiwa Yasmeenah. Koh gaisuwa bata tsaya sunyi ba ta katse wayar kan ta shiga bathroom to tend to her early morning business. Fitowar yayi daidai da lokacin da driver ya kirata cewar ya isa gaban Al-Haydar empire. Jacket dinta tazo dauka ta ga bundle na kudi, American dollars da ya ije mata. Hawaye masu dumi ne suka sauka daga fuskar ta kan ta dau jacket din ta wuce, leaving the money lying there. Wato shikenan Abdulmalik koh ta ce khalifa shima karuwa ya dauke ta, da har zai ije mata kudi. Toh bata son kudinsa, a da tayi kwadayin cin kudin khalifa Al-Haydar amma yanzu, sanin the real face behind the name has turned down her vibe. A hankula, cike da takama, with her head held up high ta fito daga suit din tana taku dai dai har ta isa parking lot din hotel din inda driver ke jiran ta.

Suna isa gida, bata tsaya ko ina ba sai dakin ta, ta tube kayan jikinta ta fada ban daki. Ta dade sosai a ciki ba abunda take yi in ba rusa kuka ba har sai da Yasmeenah ta yi knocking door din ta ji koh lafia taji ta shuru.

“I’ll be out in a sec”. Ta fadi kan ta miqe daga qasa inda ta zauna comfortably tana ta sharar kuka. For the second time, she has lost her key to happiness….. For the second time in life, she has lost true love all kudos to the path fate and circumstances lead her to. 3

Wanka tayi kan ta fito ta izza Yasmeenah zaune bakin gado tana jiran fitowar ta.

“Wannan da kika dade a wanka haka, it seems khalifa Al-Haydar had a wonderful night”. Yasmeenah ta fadi with a hint of mischief in her tone.

“He sure did”. Laylah ta ansa ta fuska ba walwala. Daga nan ba wanda ya kuma cewa komi. Yasmeenah tayi busying kanta da phone dinta while Laylah took her time to doll up. Mai kawai ta shafa, ta fesa body spray kan ta nufi closet ta nemi wani free gown ta sanya. Kusancin da ke tsakanin Yasmeenah da Laylah ya sa ta sensing something wrong amma kuma bata yi pressing issue dinba dun haka kawai ta fita ta nufi downstairs. Kitchen ta wuce direct ta fara mixing batter zata hadawa Laylah breakfast of one of her fave meals. Tana gama frying pancakes din tayi arranging dinsu neatly a plate kan ta dora a kan tray wanda ke dauke da mug na tea already, ta buda fridge ta dauko dressings for pancake din kan ta wuce dakin Laylah da abincin.
Come eat”. Laylah ta so objecting amma Yasmeenah bata bata room for that ba “Come on, I made it with so much love”. Tayi convincing dinta. Koh da ta fara cin abinci, Yasmeenah na lura da yadda ta ke ta wasa da pancakes din kawai her mind far off in a trance. +

“Something went wrong?”. Ta tambaya amma shuru “It’s okay if you don’t wanna talk about it, I’d just go to my room”. Ta miqe heading for the door.

“Abdulmalik is khalifa Al-Haydar……. Khalifa Al-Haydar is Abdulmalik”. Maganar ta ya sa Yasmeenah Mutuwar tsaye. Ta dade in shock kan ta juyo ta kuma tambayar Laylah, just for confirmation.

“Who is who?”.

“Abdulmalik, the guy I’m crazily in love with. Turns out the poor driver, the single father of one is none but the mysterious khalifa Al-Haydar. khalifa Al-Haydar inda nayi shekaru ina targeting”. Ta fadi kan ta kuma fashewa da wani kuka me ratsa zuci. Da gudu Yasmeenah ta qarasa kan gado ta riqo ta, ta sa kanta a shoulder dinta tana ta shafa mata gashi a hankula, in a soothing way. Sai da kukan ya ragu kan ta kwashe duk yadda suka yi tas ta fadiwa Yasmeenah.

“You think I did the right thing?”. Ta tambaya.

“Right now I’m so proud of you baby”. Yasmeenah ta fadi tana kissing hair dinta “And I’m very certain zai dawo, he loves you. Just give him some space, he needs time to digest all you told him, to clear off his mind. Kin ji, just cheer up. Mu zubawa sarautar subhanahu wata’alah ido”. Ranar dai haka Laylah ta wuni kuka Yasmeenah kuma nata faman bata haquri daga karshe dai tayi making up mind dinta to call the only person that can cheer Laylah up dun haka daukar wayar Laylah kawai ta yi ta fara dialling number din, ana dagawa ta sawa Laylah wayar a kunne ta fita ta basu waje.

Ýar uwa kenan, rabin jiki. Cikin few minutes Auta tayi abunda Yasmeenah ta wuni tana yi ta kasa. Kan kace mai Laylah nata dariya da fara’a, koh da suka gama wayar mood dinta yayi improving sosai. A haka dai kwanaki suka fara gushewa ba khalifa Al-Haydar ba labarin sa. shi be kira ba, be kuma neme ta ba.

Cikin ýan few days dinnan, life lost meaning to Laylah. Kullum bata da aikin da ya wuci zama cikin daki tayi ta tunani. Daga baya da ta gaji da zaman daki sai ta fara fita in the evenings zuwa park for long walks. Koh events planning business dinta bata wani kula da, komi ta bar wa Ameer PA dinta ya dinga kula da business din, sai dai ya kawo mata feedback.
Kamar wasa, aka yi two months Laylah bata ji daga khalifa Al-Haydar ba dun haka ta yi making up mind dinta to take the right step. Ranar da dare ta shiga dakin Yasmeenah dun suyi magana. A hankula ta tura kofar ta sama Yasmeenah zaune a armchair inda ke dakin tana karatu. Murmushi tayi mata kan ta qarasa ta zauna kusa da ita a dayan armchair din. Shuru shuru bata ce komi ba dun haka Yasmeenah ta cigaba da karatun ta. +

“I’m leaving”. Maganar ta ya sa Yasmeenah sakin novel inda take karantawa ta dago tana kallon ta. “Hey! Not forever”. Ta fadi tana wata ýar dariya “For sometime, I want the world to forget about Laylah Jaan, just to clear off my mind and stay off the social circle for a while”.

“How long are are we talking about here?”.

“I don’t know; months, one year, 2 years, 5 years. I just don’t know. All I know is zan dawo”.

“Kema barina zakiyi Laylah, leek left and you’re leaving too. Duk duniya ban da irinku”. Kawai ta fashe da kuka.

“Hey, wallahi zan dawo. Kullum zan dinga kiranki, i’m not leaving the world, yola zan koma for a while. You can stop by anytime you miss me”. Ta fadi. Yasmeenah kawai jawo ta tayi jikinta tayi embracing dinta affectionately.

“I am proud of you Laylah”. Ta fadi mata. Koh da Laylah ta miqe zata koma dakin ta sai ta isa bakin kofa ta tsaya.

“Yasmeenah”.

“Na’am”.

“It’ll be good if you go home too you know, atleast su san kina raye”. Ta fadi kawai ta juya ta wuce. Kashe gari da sassafe suka tashi Yasmeenah ta mata rakiya zuwa airport. Sai da taga tashin jirgin su kan ta koma gida zuciyarta fal da tunani. Maganar da Laylah ta fadi mata the previous night ne kawai ke ta mata yawo a kai. Hakika ya kamata ta nemi gida. Tana isa gida dakin ta ta wuce directly ta buda wani drawer ta ciro wani dan envelop wanda yike dauke da details din family dinta da suka rage. About 3 years ago ta sa aka mata investigation amma tunda aka kawo rashin courage ya hanata buda envelop din. Koh da ta ciro envelop din, ta dade tana nazari on whether or not to open it kan tayi making up mind dinta to just open it. Tana budawa contact din farko ta fara dialling, contact din ýar Uwar ta Gumsu.
Hello…”. Shuru Yasmeenah ta kasa magana. +

“Hellooo….”. Aka qara fadi a background tana jin haniya kaman na yara suna argument.

“Yasmeen! Dan Allah kuyi shuru in ji magana”. Ta ji ta fadi kan ta kuma cewa hello amma shuru Yasmeenah ta kasa magana sai wasu hawaye masu sanyi da ke sauka kan kumatunta.

“Yasmeenah….. is that you? Ke ce?”. Ta tambaya amma kuma sai Yasmeenah ta yi saurin katse wayar. Gaba daya ma ta kashe wayar ta kwanta tana kuka. She has never felt so lonely and vulnerable in her life.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *