WATA SHARI’A






CHAPTER 18



Tunda suka bar kotun su Brr. Sa’eed ke cuku cukun yanda zasuyi su buga takardar da zata tabbatarwa kotu cewa asibnin Dr. Khalid ce shi kad’ai, 
Da sa‘a kuwa suka samu aka bugata yanda babu wanda zaiga takardar yace ta k‘arya ce, ni kaima  nayi,matuk’ar mamakin wannan takardar, saboda tamafi ta kirkin tsaruwa, babu wanda zai ganta yace ta k’arya ce sai ni da nasan kan zancen. Ana sauran kwana uku su koma kotu ne Sultana suka fita ita da Ummimah da Umar zasu koma police station maganar batar Safiyya, 
Sun ‘tsaya a daidai roundabout suna jiran traffic light ya basu hanya, wani irin hold up ne sosai wanda basuyi mamakinshi ba
saboda duk ranar Friday ana samun irin hold up aduk fad’in garin Katsina. 
Wasu matasa ne su biyu akan mashin sunabtukinsu cike da natsuwa har suka kutso ta daidai inda su Sultana suke, 
Kallon mamaki ta bisu dashi kam tace “Wai nikam honey ka gane wancan masu mashin d’in?”, 
D’aga kanshi yayi tare da sauke gilashi ya kashe AC, ya kallesu sosai yace 
“Ya bazan ganesu ba, basu bane mashayan nan wanda muka tab’a haduwa dasu har wancan na gaban ya bani complimentry card dinsa ba?”, Murmushi ta masa tare da fad’in 
“Ehh lallai ka ganesu, tunda suka k’ariso nake kallonsu sai daga baya na tuna ashe sune”, 
“Aikuwa dai kinga sune, haka fa rayuwar d’an shaye shaye take, baya da wani galihu a rayuwarsa, kullum a tozarce yake saboda baisan me zai aikata ba a Cikin halin mayen da yake”, 
“Wallahi kuwa, batada wata amfani rayuwar, hatta da matar aure ba lallai ya samu ta kirki ba, to ina dalilin wannan rayuwar kuwa”. 
Suna cikin surutunsu basu san an basu hanya su wuce ba, matasan dake kan mashin d’in kuma basu da hanyar da zasu wuce saboda daga d’ayan gefensu daf ce babba. 
Hakan yasa suka k’ara kutsowa daidai gilashin da Umar ya sauke na gaban mashin d’in yace 
“Haba malam ya zaku ringa fira kuma ku kasa bamu hanya mu wuce?”. 
Caraf Ummimah taji muryar da ba zata tab’a mantata ba a rayuwarta, 
Shiru tayi tare da fad’awa a kogin tunani, 
Har suka bar wurin bata san lokacin da suka rabu da masu mashin d’in ba 
A bakin police station d’in suka isa duk suka fita a mota amma Ummimah tunani take, 
Hankalin Sultana ya tashi harta bud’e motar saitin Ummimah amma duk bata san anyi ba, Zama tayi daga gefenta tace 
“Ummimah” amma bata san tayi ba, D‘an bubbugata tayi firgigit ta dawo hayyacinta tana fad’in 
“Ina yake’! Wallahi yana cikinsu, amma shi bayyi ba, nasan muryarsa bazan tab’a mantawa da ita ba, shine wallahi” ta fashe da kuka sosai tare da duk’ar da kanta bisa cinyoyinta. 
“Me kike fada ne Ummimah? Lafiyanki kuwa? Waye kike magana?” Duka a had‘e Sultana ta jefo mata da wannan tambayoyin, 
Umar na tsaye abunku da Barr. Har ya fara fahimtarwani abu, 
“Muje kawai mu fito, idan mun koma gida kafin nan ta dawo hayyacinta sai mu mata ko wace irin tambaya”, 
Tashi Sultana tayi tana k’ok’arin tayar da Ummimah, 
“Ki barta anan kawai ai ba dad’ewa zamuyi ba” ya fad’a bayan ya kama hanyar shiga station din, itama Sultana bin bayanshi tayi amma fa kanta d’aure yake, ta mastu taji inda 
maganar Ummimah ta dosa. 
Koda suka shiga basu wani dad’e ba, inspector ya shaida masu cewa tsaye suke ana bincike sosai kuma suna sa ran insha Allahu zasu samu nasarah, ya tabbatar masu da cewa yanzu haka akwai ‘yan sandansu hud’u da kwanansu biyar basu nan, suna cikin gari banda 
aikin bincike babu abunda sukeyi. 
Cikin farin cikin wannan maganar Umar da Sultana suka koma mota, a yanda suka bar Ummimah haka suka sameta, sabodaji take tamkar wani tsohon tabo ne aka fama mata, “Ki daure ki daina kukan nan dukda bansan dalilinki na yinshi ba, kar ki tadowa kanki 
ciwo kinsan kinada hawanjoni”. 
D’ago rinannun idanuwanta tayi ta share hawayenta, amma kuma idan ta share sai wani ya ringa fitowa, A haka har suka isa gida bata gama kukan ba, A parlor suka samu su Mama zaune suna firar kotu ita dasu Zarah, Sallamah Sultana tayi ita dake gaba sannan suka shiga, Koda Mama ta kalli fuskar Ummimah ta tabbatar da ba lafiya ba, sabada idonta yayi jajur sannan har ya fara kumbura, Da gudu ta iso inda take tare da d‘ora kanta bisa cinyar mama taci gaba da rizgar kukanta sosai kamaryanzu ne komai ya faru, Itama mama kukan take tana tambayarta abunda ya faru amma ta kasa fadi. “Haba Ummimah? Ya zaki tayarwa mama da hankali bayan kuma kinsan ku duka biyun ba isasshiyar lafiya ne daku ba? Dan Allah ki daina mana, ki mana bayani tunda dai harmu da muka Fita tare din bamu san dalilinki na yin kukan nan ba, ki mana bayani idan akwai abunda zamu iya yi miki sai muyi” Sultana ta fad’a Cike da tausayi, Umar ma zama yayi daga can gefe yana sauraren abunda Ummimah zata fad’a. Da k’yartayi shiru ta sauka k’asa, cikin rawar murya tace 
“Wallahi ko tantama babu muryar sarki Manu ce naji, wanda a Cikin mutum tara shine kawai baimin fyad’e ba” ta sake fashewa da kuka. Su duka kallon mamaki suka bita dashi, kowansu ya kasa furta komai sai kallo, Zarah ce tayi k’arfin halin cewa 
“Ummimah kodai muryarsu tayi kama ne kawai? Naga Sarki Manu a Jalingo suke me zai kawosu Katsina?”, “Kamarya me zai kawosu Katsina Zarah? Kinsani kodama d’an katsina ne? Wallahi ba zanyi kaffara ba muryarsa ce naji, shine kawai yake da imani a Cikinsu, shi kad’ai ne yasan ko su waye sukamin fyad’e, ku taimaka ku tayani nemanshi domin ya tabbatarda Gentle ce ta sakasu suyi min fyad’e” ta k’ara fashewa da kuka tana k’ara jin tsanarGentle a rayuwarta. 
Umar ya kalli Sultana itama ta kalleshi, bayan ta kawarda kallonta daga gareshi tace “Idan zan iya gano katinshi to tabbas wannan abu ne mai sauki akwai complimentry card d’inshi wanda ya tab’a bamu farkon ganinmu dashi yana Cikin maye yace wai Abban Hafsa ya d’aukeshi aiki, ban yar dashi ba yana aJiye, saidai kuma ganoshi ne zayyi wahala dan ba zan iya tuna ko wacejaka bace nama fitada ita a lokacin ba”. Saurin tashi tsaye Ummimah tayi ta matsa inda Sultana take, “Muje zan tayaki dubawa, wallahi kin kara tabbatarmin da shi d’in ne dan saboda ko a lokacin da sukamin fyad’e duk a cikin maye suke saishi ne kawai kuma naji suna ambatar yau baisha komai ba, alamar ya saba sha kenan”. 
Tashi Sultana tayi tace “Muje to” bin bayanta Ummimah tayi suka shiga d’akinta. 
Baki daya jakunkunan dake rataye a bag hanger d’in saida ta saukosu, kamar 
mahaukata suke zazzagejikkunan amma basu samu ko wace takarda ba, K0 natsuwa basuyi waje dubawar har suka kai k’arshe, sake duddubawa sukayi a karo na biyu amma babu su, 
Hankali tashe Sultana tace 
“Wallahi ni nasan ban yarda ita ba na sakata a jakata, amma da yake Hafsa bataji ta yiwu ita ta fitar tayi wasa da ita, amma kuma abun mamaki Hafsa bata tab’a minjaka idanna ajiye, akwai dai inda take”. 
Jiki ba k’wari suka bar d‘akin, da fitarsu kuwa ya tabbatar da basu samu takardar ba, Umaryace “Ku d’auko duka jakunkunan ku kawo nan a duba a nitse, nasan ba lallai bane idan kun ajiye hankalinku wurin dubawa”.ba Juyawa sukayi suka kwaso duka jakunkunan suka kawo, Cike da natsuwa Umar da Zarah ke dubawa, Rabiatu kam dama uwar kuka ce, tuni itama ta b’arke da kukan tana k’ara tausayin k‘awarta. ’ 
Wata peach hand bag Umarya d’aga, a cikinta keda purse ‘yar k’arama, bud’eta yayi yaci karo da complimentry card d’in matashin daya bashi. 
“AIhamdulillah, gashi na gani” Umarya furta fuskarshi d’auke da murmushi. “Alhamdulillahi” duka ‘yan dakin suka had’a baki wurin fad’i. Karb‘a Ummimah tayi ta karanta sunan, “Suleiman Usman Saraki, Sarki Manu” Ummimah ta fada a ranta, “Yanzu sunan baizo d’aya ba?” Ta tambayesu, 
Saima yanzu sunan ya fad’o masu a rai, Umar cike da farin ciki yace 
“K‘warai kuwa suna yazo d’aya, ko tantama babu, sarki manu shine mai katin nan”. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *