MY BESTIE’S HUSBAND CHAPTER 2 BY REALFAUZAHTASIU

MY BESTIE’S HUSBAND CHAPTER 2 BY REALFAUZAHTASIU

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

_____________________________

_____________________________

Girgiza Kai Rafi’ah tayi tace “Aa Ni’imah mijinki azzalumine bashida adalci baison me sonsa ba meyesa laifin wani zai shafi wani….” Katseta tayi tace “naji Rafi’ah nidai ki taimakeni kije don darajar qauna da aminta kinji” ajiyar zuciya tayi jikinta ya qara sanyi tace “shikenan zanyi qoqari bari zance da Ammi zanzo gurinki asibiti duk yanda mukayi zakiji” ajiye wayar tayi ta fara kaiwa da komowa a dakin zuciyarta cunkushe da tsoro yanzu ita ya zaayi ta taka taje gidan Ja’afar Wakil da wanne irin yanayi zai karbeta?

Tambayar da takeyiwa kanta ta kasa samun amsa kenan daqyar ta iya sawa kanta juriya ta dauki doguwar rigarta ta zura tayi rolling mayafin ta dauki takalmi da wayarta da key din motar Ammi ta fice daga dakin ta nufi dakin ammi tana bisa sallaya ta zauna bayan ta idar da sallar ta dubi yar tata tace “ina zaki?” Sunkuyar dakai tayi qarya ba dabi’arta bace shiyasa takejin nauyin yinta to yanzun dai dole ta kamata tace “zanje wajen Bestie ta kirani tanason ganina urgent don Allah kada kice aa Ammi” murmushi  ammi tayi tace “toni na Isa na hanaki kidai kula da kanki don Allah Kuma ki Kama bakinki tsakanin Mata da miji sai Allah akansa sai taji haushinki”

+

Jinjina Kai tayi cikin jin dadin sa’ar da Allah ya bata ta fito ta dauki motar ta fice Kai tsaye unguwar da martaba estate take ta nufa Saida taje daidai get din tayi parking ta dauki wayarta ta kirashi bai dagaba saboda yaga tsayawar matar koma yaji a jikinsa itane hakan yasashi turo mata da number gidan tayi horn security din ya bude Mata ta shiga tabi titi na biyu tayi parking daidai block 29 ta sake kiransa ya bai dagaba sai megadi da taga ya bude Mata ta shiga tayi Parking ta sake kiransa sai taga wani mutum ya fito sanye da rigar kitchen da alamun kuku ne yazo ya qwanqwasa Mata glass din ta zuge ya gaisheta tare da cewa “yallabai yace a shigar dake” Saida gabanta ya fadi tayi kamar tace aa saidai tasawa kanta juriya ta fito ta kulle motar tabi bayansa suka shiga ya mayar da qofar ya kulle taja ta tsaya a parlourn qasan tana qarewa gdan kallo manyan hotunansu ita da Ni’imah da sukayi kafin bikin sun qarawa parlourn kyau kowanne an rubuta  world Bestie’s tayi murmushi tana me maida hankalinta ga kallon hotunan.

Ji tayi an zagaye weast dinta da hannu anyi kissing dogon wuyanta tare da shaqar qamshinta tayi saurin janyewa lkcn da yake sauke ajiyar zuciya tace “kace inzo zaka bani lkc ka saurareni na roqeka da girman Allah kada ka qara tabani J Wakil ko bance maka komai ba Allah zai sakamin domin Kaine namiji na farko da kataba hada jiki dani”

Lumshe idonsa yayi ya bude yace “gdannan ya dace dake My Bestie dama ace kin shigo kenan” kalmarsa taso bata dariya ta dai dake ta maze tace “meye dalilinka na tozartamin Bestie na bayan ka cire Mata darajarta Kuma kake burin mayar da ita qaramar bazawara?” Takowa ya farayi gabanta tanaja da baya yana sake binta saura qirin takai qofar yayi maza ya shammaceta ya danna Mata key taja numfashi tare da zuba masa ido jikinta na rawa sai hawaye sharr tayi saurin zamewa ta zube aqasa shima ya zauna yakai hannu zai riqo nata ta janye yace.

“Kina tsoronane? Meye kike tsoro game da mijinki mijinki ba fasiqi bane Kuma ko Ina fasiqanci bazanyi dake ba kinada matsayin da sunnah ce ta dace dake ba zina ba Rafi’ah ki amince da buqatata wlh cikin wata daya zaayi komai a gama ke ni idanma wata dayan tayi Miki nisa zan iya ko gobe a daura mana aure saina daukeki mu tafi Indonesia bazamu dawoba Saida bebynmu Kinga lkcn kowa yayi surutunsa ya gama saimu fara sabuwar rayuwa ko?”

1

Gabadaya kallon mahaukaci takeyiwa Ja’afar Wakil bata bashi amsa ba taja fasali tace “bestie ce tasani zuwa gunka ba zuwan kaina bane tace nabaka hqr Kuma ka fadamin laifinta munyi maka alqawarin gyarawa da qarfin buwayar zatin ubangiji….”  Hannunsa ya aza ya dago habarta ya zuba idanunsa cikin nata tayi saurin lumshe nata yayi murmushi yasan duk taurin kan mace indai zata kalli qwayar idonsa saita rusuna yace.

“Naqasunta baya damuna domin nasan dama wacece ita ba wata bace sai yar gidan Hajiya Sahura qawar Hajiya Fatsum Iko mahaifiyata iyayen da basa kwabar yayansu musamman Mata sannan basa basu horon zama da miji sukw dauka cewa izza da iko zasu siyi zuciyar miji nop duk ba wannan ne damuwata ba damuwata shine ki amince dani ki karbi soyayyata idan kin amince wlh na amince zan dawo da qawarki gdannan a daren nan zata zauna albarkacinki Kuma zan wanzar da adalci tsakaninku sannan zanyi hqr da duk wani lapse nata nayita mernege har zuwa lkcn da zan shigo dake matsayin Mata ranar da zanyi asalin angwanci zan huta iyakar hutawa ranar da Prince Ja’afar zai kwana yana wanzar da qauna me yado a zuciya a gurin daya dace”

Harara ta maka Masa tare da miqewa tace “idan Kuma ban amince bafa?” Murmushinsa na Isa yayi ya miqe ya zare doguwar rigarsa idanunta ya sauka a faffadan qirjinsa me yalwataccen gashj tayi saurin dauke idonta shikam bai damu ba ya dauki wandonsa na yadi yasa ya dauki rigar ya sanya yasa hula ya matso gabanta yanata zuba qamshi yace “kofa baki amince ba kin amince Rafi’ah dolene ki aureni domin nasani kowama yasani ni dake mun dace sosai”

STORY CONTINUES BELOW

Dagowa tayi tace “ban amince ba Amma zaka dawo da  Bestie na Ja’afar inada Wanda nakeso wlh harma munyi alqawarin aure nifa bantaba sonka ba hasalima wlh natsani namiji irinka mara sanin darajar alaqa Ja’afar Wakil please kada kaja alaqar nan har kayi yanda duniya zata fahimta Allah yasani bazan taba iya wannan cin amanar qaunarba bestie ta aminta dani ta dauki amanar kanta da duk wani sirrinta tabani munyiwa kanmu alqawarin rayuwa tare mutuwa tare Amma kana neman kawo mana tasgaro cikin tafiyarmu munyiwa junanmu alqawarin hada yayanmu aure idan Allah yaja rayuwarmu Ja’afar kada ka zama makamin yanke kyakkyawar alaqarnan kaji?”

Ta qarashe mgnr tana durqushewa a gabansa inda idanunsa yake kanta yace “kinason farin cikinta?” Saurin daga masa Kai tayi ya sake cewa “meyesa kika yarda kizo gdana saboda ita?” Sunkuyar dakai tayi yace “talk mana” dagowa tayi idonta cike da qwallah tace “saboda inason ta dawwama cikin farin ciki tare da abinda takeso” murmushi yayi yace “to ita meyesa bazatayi Miki wannan sallamawar ba?”  Dagowa tayi suka hada ido ya qanqance qananun idanunsa ya nunata da yatsa yace “duk da cewar zuciyarki taqi gasqata Miki cewar kinasona Amma ni inaji a jikina jikinki da ruhinki sun karbeni Ni’imah itace qaddarar da take wahalar  damu babu wani abu naki da yake boyayye a gurina kinason namiji me irin siffata to kin samu nine Rafi’ah nine Ja’afar Wakil ki karbeni kawai a wucce gurin babu wanda ya usa canza qaddarar Allah fah dagani harke babu abinda muka isa mu canza dole mu karbi duk hukuncin da ubangiji yayi akanmu”

Numfashi ya sauke yace “kada ki damu muje a daren nan zanyi Miki abinda kikeso bazaki kwana da ciwon mutuwar auren Bestienki ba Amma kisani a gobe zan sanar da manyana halin da ake ciki dama rashin samun dama daga gareki ya hanani furta musu koma….” Wata tsawa ta daka mishi data sanya gabanss faduwa tace “karka kuskura  kada ka fara wlh bazan taba yarda da wannan haukan ba kuma ma Ina katabajin anyi wannan sakarcin to nidai bada yawuna ba idan kuwa ka sanar Kaine da kunya na rantse da Allah saina kashe kaina na huta kowama ya hut….”

Wata fizga yayi Mata ya hadata da jikinsa ya matse yana lalubar bakinta ta fara tureshi ya sake daidaita qirjinta a nasa yanajin yanda dukiyar qirjinta take gugar nasa qirjin, jin yanda electric din jikinsa suke wani touching yasashi saurin sakinta ya zauna a hannun kujera yana cakuda numfashi inda itama tayi baya da sauri tanajin wani shorck a cikinta da bata tabajiba  daqyar ta daidaita nutsuwarta yana kallonta yanajin wani sabon baqon yanayi miqewa yayi da sauri yana korar shaidan da a’uziyyah ya dauki key din motarsa yace “muje ko?” Babu musu tabishi tana fita ta fada tata motar baiso hakan ba amma Babu yanda ya iya da ita haka ya shiga taja suka fice jikinta har yanzu wani yammmm yakeyi Mata tanajin wani yanayi da bata tabajiba,  gidansu  Ni’imah suka nufa Kai tsaye suka shiga tayi parking ta fita ta shiga gdan shikam baima fito a motar ba tana shiga Hajiya Sahura ta washe mata baki tace “da daren nan Rafi’ah lfy” numfashi taja tayi qasa ta gaisar da Mama tace “bestie fah Mama” sama ta nuna Mata tace tanacan tanata aikin kuka kamar kanta ka fara yo bandama abinta mijin da ya sakeki har yana fads Miki Wai sabodakene burinsa bazai cikaba meye na damuwa basai ta qyaleshi ya cika burin ba mugani”

Itadai miqewa tayi tace “tare muke dashi yana waje yace ta fito su tafi  ya wucce” miqewa Mama tayi tace “tabdi Amma yakai riqaqqen dan iska bama zai shigo ba….” Kafin ta rufe bakinta sai gashinan ya shigo sai Kuma tayi shiru harda washe masa baki suka gaisa Dad taje ta Kira a sama yazo suka zauna Rafi’ah ta Kira Ni’imah tana ganinta ta rungumeta tana dariya me hade da kuka tace “da gaske ya mayar dani Bestie wayyoh dadi kema Allah yakaimu ranar da zan saka Miki yana Ina?” Janyo hannunta tayi cike da tausayin qawar tata suka fito ya dubeta ya kawar dakai ita kuwa sai wata kwarkwasa takeyi Masa shi Kuma rabin hankalinsa nakan Rafi’ah Dad ne ya lura da satar kallon Rafi’ah da Ja’afar yakeyi inda yayi gyaran murya zai fara mgn tayi saurin daga wayar qarya tana cewa “ok Ammi ganinan zuwa ki basa hqr” miqewa tayi ta dubi Ni’imah tace “zan wucce Bestie ki kula da kanki don Allah Allah ya kiyaye gaba” zuruf Ja’afar ya miqe yace “bari na rakata ki shirya ki jirani Ina zuwa” kafin ma wani yayi mgn ya fice suka kalli juna ita da Ni’imah Ni’imah tayi Mata murmushi tace “na gde Allah yabar qauna kema ki kulamin da kanki”

Har bakin motar ta rakota ta shiga yaja suka fice suna fita ya dubeta yace “amaryata me kikeso” ko kallon tsiya bai samu ba balle na arziqi mgnr duniya taqi tankasa sai latsa wayarta da takeyi taji yayi parking batare da ya sake mgn ba ya fice taja dogon tsaki tare da cewa “shashasha kawai” Bai wani jima ba ya dawo ya zuba kayan daya siyo a kujerar baya ya sake zama yaja ya nufi hanyar unguwar tasu yana parking ko sallama bata tsaya sunyi ba ta fice ta nufi cikin gda yabi bayanta dake jujjuyawa da kallo ya sauke numfashi ya bude ya dauko kayan yabawa megadi ya shiga dashi shikuma ya fice ya samu sahu ya hau ya nufi gidansa ya bawa driver mota yace yaje ya dauko Ni’imah a gda.

Lkcn da ta shiga ta tarar da Abba suka gaisa yace “ya jikin bestie din” amsawa tayi a gajarce ta haye sama ta cire rigarta da taketa zuba qamshin turaren Mr Ja’afar Wakil ta daura towel ta fada wanka taji an shigo dakin koda ta fito sai taga anti Murja ds kaya ta dubeta tace “anya wannan mutumin ba maye bane Rafi’ah?” Tabe baki tayi tace “dan wahala ba wlh na tsaneshi” murmushi anti Murja tayi tace “ni bawai shi na tsana ba tashin hankalin da zaayi idan ya fadi qudirinsa nake tsoro” batace komai ba ta shafamai a lallausar fatarta ta zura rigar bacci ta kwanta bacci me dadi ya dauketa  yauma mafarkinta irin dai wanda tasabane sai ta yanzu take fahimtar inda ya dosa watoar wannan mutumin da take yawan gani ba kowace bane  Ja’afar Wakil ne.

1

Da safe da wurwuri ta tafi makaranta saboda batason damuwa wayarta ma kasheta tayi ta jefata a jaka ranar bata samu zama sai dare ta kunna wayar ta sake sata a silent ta shiga karatu tana ganin kiraye kiraye taqi dagawa sai saqonni sukayita tururuwar shigowa  Suma bata budeba tayi kwanciyarta Saida safe ta duba wasu duk shirmen Ja’afar ne taja tsaki ta qara kashe wayar.

Suna garden suna dan tattaunawa wani abokin karatunsu yazo yace “kinada baqi fah Rafi’ah” dafe qirji tayi tace “waye?” Batare da yabata wani attention ba yace “naga motarsa ansa JMW”  iska ta furzar tace “kacr bakaganni ba kawai” zaro ido yayi yace “tabdi wlh bazan iyaba wannan guy din yana mgn kamar anyi masa dole” harararsa tayi ta tashi ta koma wani bangaren can nesa ta zauna wata flower ta rufeta taci gaba da karatunta ya akayi ya akayi saiji tayi an qwace littafin ta dago a tsorace.

Numfashi taja tare da miqewa ya zuba Mata ido yace “kina wahalar dani Rafi’ah da wanne zanji ne abubuwa sunyimin yawa fah inason samun sauqi ta bangarenki Amma kinqi tausayamin ya zakiyi da haqqina ne meye laifina don nace inasonki ni bada wani abun banza nasoki ba da aure fah Rafi’atuh meye laifin masoyinki?”

Miqewa tayi tana tattare takardunta tace “meye laifina Nima don nace banasonka bakuma zan taba sonka ba nikam bantaba ganin mayen mutum irinka ba ka rabu dani ka fita a rayuwata kaqi bafa ayinso dole to me kake nema danine maci amanar qauna?” Sosai yaji dacin kalamanta Amma bashida meyi shine ya kawo kansa dole ya jure iyakar wuya watarana sai labari.

Murmushi yayi yace “albishir nazo nayi Miki yau naje na samu Dad mahaifin Ni’imah na sanar dashi inasonki da aure yaje ya sami Mai Martaba ya sanar dashi Kuma inason komai ayishi a game cikin one month kamar yanda akayi na aminiyarki saboda haka daga yanzu ma zaki iya fara shirye shiryenki Nima zan fara daga yau bansan ra’ayinki ba zaki zauna a gidan sarauta ko Kuma Zaki zauna da bestie dinki”……..

_Ina mamakin mutane da basawa rayuwa uzuri, shin Ina tunaninmu yake tafiya da muke manta komai yana gudana ne bisa iko da sahalewar Ubangiji bawai ra’ayinmu da_ _iyawarmu ba? Am sorry to say sisters and brothers mgnr addini babu ra’ayi a cikinta, idan har kunya zata saki kibar halal to shakka babu aure shine Abu na farko daya kamata ki bari saboda babu abinda yafishi rashin_ _kunya a duniya Amma Kuma shi Ubangiji da kansa yake cewa_ _(WALLAHU LA YASTAHAYI MINAL HAQ) tabbas Allah bayajin kunyar gaskiya saboda haka mu cire son rai mu tunkari gaskiya komi dacinta da ciwonta, Oum hairan ba son rai take rubutawa ba gaskiya take rubutawa wannan karon🤗_
1
___________________________
___________________________
Miqewa tayi tsaye ta zuba masa manyan idanunta masu saukar masa da kasala a mamakance take kallonsa yayi murmushi ya juya yana tafiya yana cewa wani abune zaikaini Indonesia Amma dole zan bari sai angama komai na bikinmu saboda bazan ballo ruwa nabarki da tarewa ke kadai ba, tabbas bakida laifi a cikin wannan lamarin amma duniya bazatayi Miki adalci ba hakanne yasa na shirya sanya qafar wando daduk Wanda ya nemi uzzurawa rayuwarki”
Baijira cewarta ba ya fice daga garden din Nina dake zaune tanajinsu ta taso tace “tabdi nidai bantaba ganin nataccen mutum irin JMW ba shi ko tsoro bayaji baya ko tunanin me zaije yazo?”
Jinjina Kai tayi tace “so yake ya yankemin duk wata walwalar rayuwata Nina yacika son kansa da yawa duk wani Abu da zan nusar dashi ya kasa ganewa wai har takai ga yaje ya fadawa Dad mahaifin Ni’ima wannan haukan nasa….” Zaro ido Nina tayi tace “wht? Da gaske tabdi kina ruwa Dan kuwa duk juyin da duniya zatayi indai manya suka shiga mgnr nan to kuwa saikin aureshi Kinga aminta zata qara qarfi gaku aminai gaku kishiyoyin juna….”
Batason shirmen Nina don sosai zuciyarta take tuquqi har wani daci takeji a saman harshenta  itakam ta gamu da alaqàqai ya zatayi ne Ja’afar ya gane Kuma ya yarda batasonsa zama tayi dabar bisa gado tana jin kanta na wani juyawa yau duk arhar hawayenta ya qafe qaf yaqi zubowa namiji hankaka tabbas namiji buhun qayane namiji ciwon yatsa, tama rasa da wacce kalma zata fassarashi tayi daidai dashi Ja’afar ko iya haka yabarta ya gama da ita ya rusa alaqarta da Bestie dinta, wayarta ce ta dauki ruri tayi firgigit ta duba saitaga number Bestie gabanta yabada wani rass tunaninta lbr yaje Mata aikuwa ta kasa daga wayar sai lkcn kuka ya qwace Mata ta rinqa kuka me shiga rai itakam tana ganin masifa a rayuwarta yanzu badan mutuwa data dauke Mata Yassar ba da tuni ba wannan zancen akeyi ba.
Ji tayi an dafata ta dago ganin Nina yasata sake rushewa da kuka tace “bansan me zance da Ni’imah ta yarda dani ba a lkcn da wannan qazamin lbrn yaje Mata Nina kaina ya kulle wlh narasa gane mafitar rayuwata sai nakejin kamar na kashe kaina na hut….” Rufe Mata baki tayi tace “subhanallahi wannan ba kalmace ta Muslumci ba Rafi’ah ki daina idan fah Allah ya qadarta aurenki dashi bakida tsimi bakida dabara idan Kuma bai qaddara ba ko kinaso bazai yuwuba to ki fawwala masa komai duk wani motsinki yana yuwuwane da amincewar lillahi”
Shiru tayi kafin daga baya ta dago tace “amma mijin aminiyata Nina haba abin ya wucce tunani yakasa saurarona ya fahimci nufina wlh Koda baya auren Ni’imah ni baimin ba bawai don baikai ba aa halinsa ne baiminba banasonsa Nina ya zanyi ya gane banasonsa” murmushi Nina tayi tace “aa fah qaryane wannan wlh duk inda namiji ke kaiwa asoshi JMW yakai kawai dai kice saboda Ni’imah ne bakiji kinasonsa ba kuma ma badan dai mu Mata bamuda lissafi wlh mijinta tunda yaji a ransa batakai masa ba har ya darsa aure aransa to kuwa sai yayi ni sainaga da a auro maka bare da bakasan halinta ba ai gara wacce kasani tasanka in zata iya cutar dakai kasani idanma bazata iyaba kasani namiji fah idan yasa kansa Abu idonsa rufewa yake kunnensa toshewa yakeyi,
Sannan nifa sai nake ganin kamar itama bazata tashi hankalinta ba tunda tasan ba haramun bane” dago idonta tayi tana share hawayenta tace “bakisan Ni’imah ba bantaba baki lbrnta ba Nina Ni’imah qawatace aminiyata tun bamusan kanmu ba tun muna qanana nasani tanada zafin kishi ni da ita Tasha fadamin tsaf zata iya kashe mijinta ta kashe kanta indai yace zai qara Mata kishiya saboda bazata iya sharing din miji ba da wata to balle ni da ni kaina nasan indai na yarda na auri mijinta to naci amanar qauna kuma qauna bazata yafemin ba Ina tayata kishin mijinta saboda nasan tanasonsa fiye da yanda kike zato, nifa dana auri mijinta gara na mutu babu aure yafimin sauqi wlh ko bansan Ni’imah ba lbrn kishinta aka bani zan guji mijinta domin dawwamar lfyta da kwanciyar hankali na balle ni nice me bada lbrn”
STORY CONTINUES BELOW
Numfashi Nina ta sauke tace “to ilahi ya kyauta Amma ki daina kukannan kiyi addu’a ki tashi muje muyi C.A dinnan mu fito sai ki tafi gida nima gda zan tafi tunda anbamu hutun qwaqwalwa hakan zaibaki damar samo bakin zaren domin wannan mutumin da gaske yake wlh” miqewa tayi suka fita sai yamma suka gama C.A din ko hostel bata koma ba ta nufi gida hakanan tunda ta sauka a mota ta tari adaidaita taji gabanta yana faduwa jikinta a mace ta shiga gidan tana  jin faduwar gabanta na tsananta,
Ajiyar zuciya tayi ganin parlour babu kowa tayi hayewarta sama tayi wanka ta canza kaya sannan ta fito,
********
*_Waiwaye adon tafiya_*
Mahaifin Rafi’ah Alh Nuhu mutum me jan iyali a jiki da kyautata musu kwata² su ukune Allah yabashi Yaya Rashid Aunty Raziqa sai ita auta Rafi’atuh inda suka taso cikin gata saboda mahaifinsu dan bokone Kuma dan siyasa sannan dan kasuwa da arziqi a gdansu bakin gwargwado gashi dason taimakon talakawa.
Don asalin alaqarta ma da Ni’imah cikin taimakon mahaifinta ne shekaru 18 baya lkcn sunada 3 years a duniya mahaifin Ni’ima maqocin shagon Abba ne a kasuwa sai karayar arziqi ta sameshi dake harkar gold sukeyi barayi suka shigo kasuwar sukayi barna Abba ma an taba dukiyarsa sosai amma dake yafisu qarfi Kuma shi kayansa ne na kansa yasa bai tozarta ba inda Alh Sabo mahaifin Ni’ima ya kasance kayansa hadin gwiwa ne don kaso 70% ba nasa bane gashi yana cikin wadanda akafi yiwa barna.
To dake akwai fahimtar juna tsakanin Alh Sabo da Alh Nuhu yasa Alh Sabo yana kuka yake zayyanewa Nuhu halin da yake ciki yana fada masa yasai da gidansa ya rage bashin kudin mutane duk wata kadara tasa ya siyar Amma bai gama biyaba har yanzu da saura 14 million da ake binsa gashi ko abinda zasuci babu a gidansa gidanma sai gdan gado ya koma kuma mahaifiyarsa ta mutu tun yana qarami matar babansa Kuma basa shiri da matarsa don kullum ciki gori takeyi musu.
Sosai Alh Nuhu ya tausaya masa take yayi masa alqawarin bashi gurin zama a gdansa sannan zai biya Masa bashin Kuma zai zuba masa sabon kaya yake juyawa har Allah ya sake dagashi ranar Alh Sabo yayi kukan farin ciki hakance ta faru a ranar Sahura ta dawo gdansu Rafi’ah da zama duk wani alqawari da Abba yayiwa Dad ya cikashi ashe kudin na Sarki Muhammad Wakil ne mahaifin Ja’afar da aka Kai masa sai yace yabarshi kawai ya yafe masa wadanda ya karba na baya ma don banasa bane na abokinsa ne murna ta cika Dad suka taho abin mamaki Abba saiya miqa masa kudin yace yasai gda dasu Amma yaqi karba qarshe suka tsaya a tsakiya kan cewa saidai a sake zubasu a shago ya zamana shima da hannun jarinsa hakance ta faru iyayensu na juya kudinsu gidansu na zaune lfy Sahura irin matannan ne masu homa dajin su wasune sai fankama ta qaru sun samu ci gaba a aro domin ko a lkcn gdan Abba ba qarami bane sosai ta rinqa shigewa Ammi har suka zama qawaye inda aka samu akasi ita Sahura macece me yawo ita Kuma Ammi batada yawo hakance tasa Sahura tafita mutane gata tun a lkcn da bin malaman masifa itakuma Ammi komai akayi sai tace Allah zai iya mata.
Anan gdansu Rafi’ah aka haifi qanwar Ni’imah Yusrah sai sabon balli ya tashi musamman da Sarkin Wakil ya turo matarsa ta tsakiya wato Hajiya Fatsum barka habawa sai firita ita tazama babbar mace har matan sarakai ke zuwa Mata barka to dake hali yazo daya sai Sahura da Fatsum suka dinke duk da Fatsum ta girmi sahura don a lkcn ma yaronta autan ma yana Cairo yana karatu shikuma babban yana Uganda yana karatun Parmarcy matan Kuma biyu tayi musu aure Salma da Dija wanda sune manya.
Haduwarta da Hajiya Fatsum yasata qara kanainaye Dad duk abinda tace shi yakeyi gashi tun a wancan lkcn ba wata biyayya ta cikaba kwanciyar aure idan zaiyi da ita saiya biyata, Ni’imah kuwa da Rafi’ah  Allah ya hada jininsu ko bacci baya rabasu dole duk inda sukayi bacci nan suke kwana tsakanin dakunan iyayen nasu sunada shekara biyar aka sasu makaranta tun a lkcn Rafi’ah tafi Ni’imah mayar da hankali a karatu ita wasane akanta sai fada da tsokanar masifa ga surutu ita Kuma Rafi’ah irin silent dinnan ce batada hayaniya duk da tsokanar Ni’imah batada qarfi idan tayo tsokana saita gudo gurin Rafi’ah to itamma ba qarfine da itaba Amma sai ta hana a daki Ni’imah tace a rama akanta.
Haka sukayita tafiya har secondary a jarabawa ne suka raba layi saboda Ni’imah bata samu abinda akesoba sai ta tafi Art ita Kuma Rafi’ah Science Ni’imah taso jan Rafi’ah ta koma art Amma taqi tace na marasa qoqarine a lkcn ne Kuma wata qauna ta qullu tsakanin Rafi’ah da dan wan babanta Yassar Amma fah soyayyar bada Rafi’an akeyi ba duk wani Abu saidai ya fadawa Ni’imah ita Kuma ta fada mata.
STORY CONTINUES BELOW
Daidai lkcn ne Dad yagama tamfatsa gdansa suka tashi suka koma ranar ansha daru dan Ni’imah qin tafiya tayi inda ita Kuma Hajiya Sahura ta nace saita tafi da yarta har wani cewa takeyi ga sabon gida mi zaayi da tsoho ta manta taohon yayi mata Rana na kusan shekara goma, dukkansu Saida sukayi rashin lfy aikuwa Basu rabuwa sai kwanciyar bacci musamman da Abba shima ya Gina wani gidan kusa da unguwar su Ni’imah duk da dadan nisa Amma yafi dayar unguwar kusa don Nan idan bakasa gandaba da qafama zakaje lkcn ne Abba ya qara aure aunty Murja itama me sanyin hali babu ruwanta, zamansu lfy Lau da Hajiya Amina wato ammi Kuma daidai lkcn ne akayi auren aunty Raziqa shima Yaya Rashid yayi aure gidan ya rage saura Rafi’ah kadai aikuwa itama guduwa tayi sai tayi sati bata gidan tana gdansu Ni’imah wannan aminta tana burge kowa don ko Yassar yasani idan zaisaiwa Rafi’ah Abu to dole saidai yasai biyu ita da Ni’imah inkuwa ba hakaba bama zata karba ba yasha tsokanar Rafi’ah yace “to waini ko ku biyu zan aurane?”
Dariya takanyi tace “nikam da nafi kowa murna gani ga Bestie na gidanmu daya mijinmu daya kaga shikenan aminta tayi Rana” duk lkcn da ta fadi haka sai Ni’imah ta harareta tace “Allah ya kiyaye nayi sharing miji ke nifa wlh Bestie yanda ban taso naga kishiya a gdanmu ba haka zan rayu babu kishiya don wlh yanda nakejin kishin mijina tun kafin nasanshi zan iya kasheshi ns kashe kaina akan batun qara aure” Rafi’ah takanyi murmushi tace “nikam banida matsala akan abinda ubangiji ya halalta Ni’imah kishi kafirci ne shiyasa nake roqon Allah kada ya jarabceni da zazzafan kishin da zai hanani yiwa mijina biyayya kishin da zaisani yin shirka kishin da zai hanani haduwa da Allah salin alin Ina roqon Allah indai yayoni a wannan sahun to ya qaddaramin mutuwa kafin nayi aure don bana fatan na zamewa mijina fitina masifa Kuma bala’in rayuwarsa”
Tsaki Ni’imah takanyi tace “ai saikiyi banza mara sanin ciwon Kai yo akanme zanyi addu’a Allah ya ragemin kishi bayan kishin adone ga ya mace nifa ko akan kishi da Yusrah ma bugawa zamuyi me qarfi ya kwaci kansa Kuma wlh don na kashe kishiya bazan taba nadama don nasan itama ba Sona takeyi ba da zata samu dama zata iya kasheni to da ka bari a kasheka gara Kai ka fara kashewa”
Yanayin Rafi’ah bata musu balle jayayya hakan yakansa da taja taga Ni’imah ta kafe akan ra’ayinta saita qyaleta abinda ta dauka wani abin halitta ce baka Isa canxa mutum ba haka watanni sukayita turawa tafi na tafiya har shekaru saura wata bakwai candynsu akasa auren Rafi’ah da Yassar murna gurinsu baa cewa komai Yassar kusan yanayinsu daya da Rafi’ah shima sanyine dashi yana nuna Mata madarar qauna me mantar da zuciya damuwa kullum suna tare babu abinda yake rabasu su uku sai bacci wani lkcn suna zaune sai kawai Ni’imah ta Kama kuka idan suka tambayeta sai tace tana tunanin ranar da Bestienta zata tafi ta barta ta kwana ta yini bata ganta ba, itama Rafi’ah saita Kama kuka abinka da quruciya tasha samun Yassar ita dashi ta roqeshi ya auresu su biyu yakanyi dariya yace.
“Bakida hankali yarinya ni ba mijin mace biyu bane Kuma ko zan qara aure Ni’imah batayimin ba banason farar mace sannan ta cika son jiki da rakin masifa ke nifah har tausayin mijinta nakeyi” akan haka Wai yana kushe Bestienta akwai lkcn da Saida sukayi sati uku basa mgn har saida manya suka shiga abin saboda ita Rafi’ah tata matsalar kafiyar masifa indai aka sake ta furta abu to komai wuyarsa sai tayi shiyasa iyayenta suke takatsantsan da furucinta dama Hausawa sunce muskilin mutum wuyar sha’ani gareshi shiyasa yawa yawan mutane suke cewa ta fiye jin izza kamar wata yar sarki wasu suce don tana dakyaune take wulaqanta mutane.
Wanda a zahirin rayuwa ma ta gaske tafi Ni’imah sanyi da sauqi hali kowa takaka da me kudi natane saidai in taku batazo daya ba Amma dake bata da magana sai aka fassarata baibai, lkcn da suka gama exams sukayi candy ansha shagali iyayensu suka shirya musu party sannan Yassar ya shirya musu wani lkcn bikinsu saura wata biyar.
Ita Rafi’ah ba ma’abociyar son zama babu bawa brain aiki bace hakanne yasata zaqula wata makarantar amare ana koyar da girke² da kwalliya da tarairayar miji, da murnarta tazo ta fadawa aminiyar tata aikuwa Ni’imah ta sheqe da dariya tace “cabb kina da aiki kice innayi auren ma wahala zanyi da har zantafi wani koyan kula da miji da girki wlh bazan iyaba kema ki zauna ki huta abinki girki ko kuku yayi ai tarairaya kuwa yanda ya koyan haka zanyi masa” Rafi’ah tosa jan hankalinta Amma taqi jikinta a sanyaye taje gida take fadawa Aunty Murja ta rinqa rarrashinta tace “ance sai hali yazo daya ake abota amma ku taku halin ya bambamta nisan yayi yawa kamar misalin sama da qasa Kuma kun kasa rabuwa bazaku rabuba abin daga Allah ne kawai ki bari zan fadawa Abbanki ya biya muku idan ya biya ai dole zataje”
Haka kuwa akayi Abba ya biya musu Amma fir Ni’imah taqi zuwa saima ta kwanta tace batada lfy itakuwa Rafi’ah ta rinqa zuwa makarantarta tana dauko darasinta, sosai take kwashewa abin gwanin ban sha’awa idan tazo gida tayita practice Ni’imah tana Mata dariya tana cewa “wallahi anma Raina muku hankali yo wannan abin zaa koya mini tab kina ruwa itadai bata kulata Saida tayi wata uku tana training din sannan aka yayesu aka basu certificate ita harda gift saboda tana cikin dalubai masu hazaqa na shekarar.
Shirye shiryen biki ya kankama sunata tsare²nsu ya rage saura sati shidda tafiya ta Kama Yassar zasuje daurin auren abokinsu Jos da zai tafi yazo sukayi sallama daqyar suka rabu hakanan duk jikinsu a sanyaye, dake yammace lkcn da suka tafi wajen bakwai na dare mahaifin Yassar ya Kira Abba a waya take Abba ya miqe yana salati inda kowa dake parlourn ya miqe suna tambayarsa “menene?”
Cikin kidimewa Abba yace “Yassar ne sukayi hatsari ya karye a wuya yanzu ma haka suna asibitin garin nan” ai Bai rufe bakiba Ni’imah da Rafi’ah suka saki wata qara itadai Rafi’ah zubewa tayi a gurin matsayin gawa aka kinkimeta suka fita asibitin da Yassar din yake sukaje aka kaita wani daki suka fice suka nufi Emergency cikin motar su hudune shi kadai Allah ya karbi rayuwarsa wayyoh zokuga kuka gurin Ni’imah na tausayin aminiyar tata da ta dauki so da qaunar duniya ta dorawa saurayin nata tana kuka tana cewa.
“Mutuwa! Wayyoh mutuwa meyesa kikayi mana haka meyesa kika daukewa Bestie na mijinta innanillahi wa innah ilaihirraji’un Allahummah ajirnih fih musibati wa’akalifni khairin minha” kuka take me tsayawa arai daidai lkcn Rafi’ah ta fito a guje ta nufo gurin ganin yanda kowa yake kuka yasata runtumawa dakin a guje ta nufi inda su Abba suke lkcn an janyo zani zaa rufe masa fuska ta fuzge zanin ta saki wata qara tare da fadawa jikinsa hawayenta yana malala tana jijjigashi tana cewa “Yassar ka tashi banason wasannan dama ka saba idan muna Hira ka kwanta kacemin ka mutu na fada maka banaso ni banaso wayyoh Yassar dina kada ka tafi kabarni wlh yau zan fada maka kalmar da ka dade kanacewa na fada maka naqi fadanta inasonka don Allah ka tashi…..”
Likitan ne ya share hawaye yace “baby saidai hqr Allan daya baki ya karbi abins…..” Daga gadon ta sulale bata sake sanin inda takeba sai bayan kwanaki uku ta farka taga Ni’imah a kusa da ita sai kuka takeyi ta tashi a firgice tace “mafarki nayi ko Ni’imah Yassar dina yananan ko?”
Kukan Ni’imah ne ya qara tsananta tace “ya zamuyi da wannan qaddarar haka Allah yaso Rafi’ah kinada tawakkali da dangana don Allah kada ki bani kunya ki dauki wannan qaddarar da hannu biyu Allah yafimu sanin abinda yake nufi daya dauke Yassar na tabbata zaiyi Miki zabi mafi kyawun kyau mafi alkhairin alkhairai” rungume juna sukayi sukaci kukansu me isarsu baki Rafi’ah ta kasa budewa saboda zuciyarta azalzalarta takeyi abubuwa da yawa suke tunkudowa daga zuciyarta sunnason bakinta ya furta idan ta furta Kuma zata iya ficewa ma daga muslumci a hankali ta fara furta astagfurullah! Astagfurullah!! Astagfurullah!!!”
Kawai sai tayi dif sai shassheqar kukanta da yake tashi Abba ne ya shigo ya matso da sauri yace “subhanallahi kukan kukeyi uwar manya to ya zaayi sai hqr Allah yana tare dake shikam Yassar ai yadace yasamu shaida Kuma yayi mutuwar shahada tasa tayi kyau saura mu Allah yasa muyi kyakkyawan qarshe irin nasa” janyota yayi yana share Mata hawayen yana bubbuga bayanta daqyar da taimakon Ni’imah suka samu tayi shiru Ni’imah ta hada Mata shayi tasha kadan tabata magungunan tasha Dad da Abba sukazo suka tafi dasu sunata yimata nasiha hakance ta dan sanya zuciyarta sanyi amma tuquqin mutuwar yana qasan ruhinta wannan dalilin yasa taci alwashin bazata qara son wani namiji ba a rayuwarta balle ya tafi ya barta…….
_______________________
_____________________________
An dade sosai kafin Rafi’ah ta saki jikinta taci gaba da rayuwa kamar kowa kyawunta da nutsuwarta yasa take samun masoya ta ko Ina ita Kuma tayi kicin² ta sanya shuni da tabo ta liqe idonta taqi kallon kowa taqi sauraron kowa  dake autace babu wanda ya matsa Mata duk da abin yana damun Abba sosai ga aminiyarta da samarinta tana sauraro Amma ita ko samarin  Ni’imah bata kulawa duk wanda yazo saidai tace ta gaisheshi qarshe ta dage aka sama Mata admission a ATBU  ta fara karatun medicine itakuwa Ni’imah daqyar saboda Rafi’ah ta yarda ta fara diploma a mass communication shima don ta rasa tsayayyen saurayine ne yawancinsu yan Shan minti ne sai suzo su lallabeta su matseta su tafi Saida sukayi kaca² da Rafi’ah akan hakan sannan ta hqr ta daina kulasu suka duqufa karatunsu.
Dayake taga bacin ran Bestie dinta abinda bata taba ganiba tsahon rayuwarsu yasa ta shiga taitayinta ta mayar da hankali a karatunta ashe dama tanada qwaqwalwar iskanci ke hanata karatun da gatan taga idan bata iyaba Rafi’ah zata koya mata yanzu Rafi’ah bata zama Kullum saitaje cikin garin Bauchi daga Azare ta dawo sai kadaici ya fara damunta ta zauna tayi zugum tana tunanin wataran fah rabuwa zasuyi kowacce ta tafi gidan mijjnta, haka sukaci shekara daya sukaci biyu Ni’imah ta gama diploma dinta tayi saa kuwa ta samu point me kyau.
+
A lkcn ne karatun Rafi’ah ya fara zafi hakance tasata yanke shawarar komawa cikin makaranta da zama saboda tana cinye lkcnta a go and come sannan ga surutun Ni’imah ya fara isarta Kullum mgnrta aure aure shiyasa tasa Abba ya Kama Mata hayar hostel ya zuba Mata komai da komai ta koma can da zama amma duk weekend tana dawowa gida idan har ba lkcn exams bane babban abinda yake damunta shine yawan mugun mafarkin da takeyi da Bestienta da wani mutum da bata ganin fuskarsa kullum mafarkin baya zuwa Mata da siffar alkhairi da farko takan dauka shirmene na mafarki amma da abin ya ta’azzara saitake fadawa Abba.
Shine yake cewa da ita mafarkin shirme baa riqeshi gabadaya dole ya kasance an manta wani bangare nasa ko an mantashi gabadaya yakance Mata ta dage da addu’a Allah ya rangwanta qaddararsu tabbas mafarkin da abinda yake nuna Mata zuwanshi dama akan samu haka indai mutum ya kasance me taqawa da miqa lamura ga Ubangiji to allah a yanayiwa wasu ludufi na nuna musu abubuwan da zasu faru gaba a mafarki domin su roqeshi sauqi da rangwame”
Wannan dalilin yasa ta qara matsa qaimi wajen roqon Allah sauqi rahma da taimako cikin kowacce qaddara me kyau ko akasinta, suna tsaka da kakar exams ne lkcn tana level 300 Ni’imah ta kirata da murna suka gaisa tace.
“Albishirinki Bestie”  amsawa tayi da zaquwa  tayi dariya sosai tace “nakusa zama amarya shekaran jiya Sarki Muhammad Wakil ya kawowa Dad ziyara shine yaganni bayan ya tafi ya Kira Dad yake cemasa, idan baiyimin mijiba yanaso ya bawa danshi Prince Ja’afar Wakil aurena wai shekarunsa sunyi nauyi 36 amma bayada niyyar fitar da Mata duk angama nuna nasa yammatan dangi yace basuyi masa ba ance ya kawo sama da shekara yaqi cewa komai har yayan abokai sarakai duk ya kaishi ya gani duk yace basuyi daidai da text dinsa ba”
Numfashi Rafi’ah ta sauke cikin murna tace “Alhmdllh ranar da muka dade muna jira tazo amma kedin kinyi masa?” Murmushi tayi tace “to ganinan dai yazo jiya dake yana gari yazo weekend Amma ko 5 minutes baiyi ba ya tafi Kuma bayan gaisuwa ko kalma daya Bata shiga tsakaninmu ba Saida zai tafi yabani hundred k wai nasa Kati ke kinganshi kuwa hadadden guy dan gayu ga DATA a hannunsa motar da yazo da itama jiya naga ansa tallanta a JAA LIFESTYLES 60 millions Kinga kuwa ai zan fantama ko?”
Rafi’ah bata fiye dariya ba saidai murmushi amma kalaman qawar tata Saida suka bata dariya tace “kullum burinki a kudi ya qare kamar wacce kika tashi da haushin talauci meyesa ne Ni’imah ki bari don Allah kudi basuda wani muhimmanci a aure soyayya tafi komai indai da rufin asirin ci dasha da sutura da gurin zama majority’s na Mata tunanin kudi sune jin dadi shine ke wahalar damu bance kudi ba abinso bane aa nima inasonsu Amma banaso su zama abin duba a mizanin auratayya ki auri mutum domin Allah da Kuma cancanta Bestie Kuma kada ki auri namijin da baya sonki ki auri wanda yakesonki idan kinji kinason dole saikin aureshi to kiyi qoqarin koya masa sonki tanyar kwadaita masa kyawawan halayenki qwaqwalwar namiji tanada fadi Amma zuciyarsa jaririya ce an halicceta dason me rarrashinsa da faranta masa yanason tarairaya da tattali uwa uba hqr domin soyayya da rayuwar aure tafi komai buqatar hqr Bestie Ina tayaki murna da samun irin mijin da kikeso Allah ya daidaita yasa kizama tauraruwa a zuciyarsa Kuma ya baki ikon kula dashi”
Numfashi ta sauke tace “amin sarki wa’azi idan sweet yazo zan bashi lbrnki da nasiharki gareni ke har record nayi fah zan kunna masa” murmushi Rafi’ah tayi tace “bakya girma bakya rabo da shirme ki gaisarmin da angonmu bazan dawo ba saina gama exams” sallama sukayi suka aje waya Rafi’ah tanajin farin ciki Bestienta zatayi aure Amma idan ta tuna rabuwa zasuyi sai taji hawaye ya wanke Mata fuska washegari Ni’imah ta kirata ta fada Mata mgn fah ta girma har ansa lkcn biki wata daya Amma angon yabar qasar bazai dawo ba sai ana saura sati daya biki.
STORY CONTINUES BELOW
Tayi Allah sanya alkhairi tare da cewa saura practicing uku su gama exams suna gamawa zata taho su fara shirye²n biki Ni’imah taci gaba da cusa soyayyar Ja’afar a zuciyarta shikuma bai wani qoqarin koyawa kansa sonta kawai ya karbetane bisa tursasawar mahaifansa musamman Hajiya fatsum da tayi tsalle ta dire tace bazai watsa Mata qasa a idoba da wanne ido zata kalli Hajiya Sahura tace danta bayason yarta.
Wannan yasashi hqr dadin dadawa da roqon da Mai martaba yayi masa na cewa kada ya bashi kunya tunda yarinyar ta amsa shima ya hqr zai sota a hankali tunda batada matsala, dole ya yarda da zabin na iyayensa amma tunda ya tafi Cairo gurin qaninsa bai sake tunawa da itaba Saida yaga saqonta a WhatsApp voice ne a qasa ta rubuta Masa _“Mijina bude kaji abinda aminiyata tacemin game dakai tanada hankali gata da hangen nesa inasonta fiye da yanda nakeson komai”_
Budewa yayi ya fara saurara jin sautin muryar Saida yasa gabansa faduwa hakanan baisan dalili ba yaji ya kwadaitu dason ganin mamallakiyar wannan zazzaqar murya kuma ma’abociyar hankali”
Batare da tunanin komai ba ya rubuta Mata _“to yayi muryarta tayi dadi Allah yasa haka fuskarta take”_ bata kawo komai ba tace _“fuskarta tafi muryarta dadi komanta mekyau ne kyau ya qare tunda aka halicci Bestie dina”_ dariya yayi yace _“anya kuwa sai nakega kamar batafiki ba”_ da wannan ya yaudareta ta turo Masa hoton da sukayi ita da Rafi’ah  a kwance yake Amma Saida ya miqe zaune ya zuba Mata ido tanata zuba murmushi yar siririyar wushiryarta sama da qasa ta qarawa kyakkyawar fuskarta kyau gata yar duma duma ma’ana chubby ko inanta a cike kamar babu jijiya da qashi a jikinta dukda batada jiki amma ta wucce kace Mata siririya sumarta har goshinta dauke kansa yayi ya maida hankalinsa ga Ni’imah sai kawai ya rinqa ganin muninta musamman da yake ita siririya ce shikuma Allah yayisa dason chubby star din hoton yayi daidai lkcn da Ni’imah tace _“kayi Shiru Sweet?”_ Ajiyar zuciya ya sauke yace _“ban tantance ba turomin Wanda take ida kadai kema kike ke kadai”_
Sakaryar tura masa tayi bai jira me zatace ba ya daukesu to Gmail dinsa ya kashe Wi-Fi dinsa yaje yayi wanka ya dawo ya bude abincinsa yanaci yana kallon hoton kyawun qawar budurwar tasa yana birgeshi yanajin wani yanayi me wuyar ganewa a qasan zuciyarsa tun daga wannan ranar Ni’imah ta samu kansa daya fahimci itanma batada wani abin cewa idan ba lbrn qawar tata ba sai yake biye Mata sosai suyita Hira tana bashi lbrn Rafi’ah don karta gane yanajin dadin lbrn wani lkcn yake gwasaleta  amma bata iya dainawa hakanan suka rinqa tafiyar da soyayyar ita a haukanta sone yasa yake biye Mata shikuma sonjin lbrn qawarta yasa yake janta jikinsa, 
Ana saura sati biyu bikin Rafi’ah ta dawo suka shiga shirye shiye da invite din qawaye wata rashin saa tunda ta dawo  Ni’imah keson hadasu ko a wayane amma taqi karba sai tace “ai batason yasan muryarta yanda zaiyi saurin ganeta so take tabashi mamaki duk ranar da suka hadu, to shima dake dan duniyar qasa da qasa ne bai takura ba duk da yasojin zazzaqar muryar a kunnensa Amma ya hqr yana saita sa’arsa batare daya bari kowa ya fahimta ba Amma bai zurfafa sosai ba saboda shima shima yana tunanin tanda zaayi ana saura sati daya bikin ya dawo saboda ya kasa jurewa yaje takanas ya sami Mai martaba ya fada masa idan da hali a hqr da aurensa da Ni’imah zai kawo wacce yakeso very soon
Kai tsaye mai martaba yace masa Babu hali dole ya dauki yan qafafunsa ya tafi bangarensa inda Muhseen yazo ya sameshi ya dubeshi yace “yadai ango meye ne naga kamar bakafa da walwala” kawai dakai yayi sanin da Muhseen yayi ba mgn zaiyi ba yasashi cewa “wlh wata baby ta rudani Prince Ja’afar na rasa Kuma ta inda zan fara” kallonsa yayi yace “nima halin da nake ciki kenan gashi nace da Mai martaba a hqr da aurennan yace babu hali wlh indai haka so yake to andade ana wahala a duniya ji nakeyi kamar idan ban sameta ba bazan iya rayuwa ba kay nifa nasan akwai qura a gaba don wlh ba aminta ba ko twins ne saina rabasu saina auri kowacce”
Dagowa Muhseen yayi da mamaki yace “suwa?” Batare da tunanin komai ba yace “Rafi’ah da Ni’imah Ni’imah ta kawomin tallan Rafi’ah zuciyata ta karbeta bantabajin son Ni’imah ba Amma son aminiyarta Rafi’ah yana neman zautani gashi a yanzu ban isa motsawa ba ko zan motsa sai na bari ita na sata daga ciki” gumine ya karyowa Muhseen yace “garin yaya hakan ta faru kanaso inaso ya zaayi kena….” Daukeshi yayi da mari yace “ka cire matata ce idan ka matsa wlh kasanni tsaf zan batar dakai” numfashi Muhseen yaja zafin zuciyar Ja’afar da kafiyarsa abar rubutawa ne a world news idan bai tursasawa zuciyarsa mantawa da Rafi’ah ba to tsaf zai iya aikata abinda yayi niyya nacine dashi kamar kuturu.
1
STORY CONTINUES BELOW
Miqewa yayi yace “Allah yabada saa Amma Kai kanka kasan abinda bazai yuwu ba ka dauko Ja’afar kasan halin Mata da kishi kuwa da zakaji shawarata sai nace ka cire ka hqr mace tanada sauqin samu alaqa kuwa wuyar qullawa gareta” Bai ko saurareshi ba ya miqe ya shige toilet ya biya buqatarsa ya fito yana goge jikinsa.
Muhseen baiyi fushi ba yace “Dazu Rafi’atuh ta kirani take tambayata meye shirinmu game da events sudai guda biyu zasuyi zasuyi BESTIE’S day sannan zasuyi NIKAH day so mukuma meye namu shirin?” Murmushi yayi yace kace nace duk abinda ta tsara shi zaa wanzar” haka Muhseen ya kirata yanajinsu ya sanar da ita ta amsa da cewa “kace masa muna gdy” daga haka ta kashe wayarta suka kalli juna sukayi ajiyar zuciya a tare.
Kusan komai na bikin tsarinta ne an kashe kudi sosai duk wani saqo ta gurin Muhseen yake zuwa Allah ya sardanta sabani tsakanin Rafi’ah da Ja’afar duk zuwan da zaiyi batanan wannan dalilin yasa basusan juna ba sai ranar dinner ranar ne ganinsu da juna na farko amma shi ya dade yanajinta a ransa da mafarkin cikar burinsa akanta wannan dalilin yasa baisa wasaba a lamarinsa yakebin duk wata hanya da yasan burin nasa zaiyi sauqin samuwa.
Kamar dai yau tunda ya tashi da safe ya shirya ya fice daga gdan Kai tsaye gdansu Rafi’ah ya nufa saboda yaji lbrn dawowarta a gurin Ni’imah da suna waya jiya da dare gaisawa sukayi da megadi yace ya shiga yayi masa sallama da Rafi’ah fitowarta daga wanka kenan tana shafa mai Anti Murja ta shigo tace “ki gama kizo kinada baqo a waje?” Kallonta tayi tace “waye anti?” Iska ta shaqa tace “bsnsani ba Mado ne yazo yacemin kinada baqo kiyi sauri kije don yadan jima”
Jitayi kamar tace bazata ba saidai ta daure ta tashi ta sanya kayanta ta fesa turare da dauki mayafinta kasancewar dama Shirin fita takeyi ta fito gabadaya tun daga nesa taji gabanta na faduwa babu wata alama da take nuna Mata wayene numbers na motocinsa JMW ne so wannan number Bauchi ce BZ124 AZR shiyasa bata kawoshi ba ta matsi motar sosai tana duba fuskarta a wayarta tsayawa tayi a jikin motar ta bude Jakarta ta jefa wayar daidai lkcn ya zuge glasses din motar ya leqo ta dago suka hada ido gabanta yabada wani rass taja baya da sauri tare da cewa “A’uzubillahi”
Zuba Mata ido yayi yana mamakin halinta wato shedan ta mayar dashi neman tsari takeyi dashi wani Abu ya hadiye me daci ya fito a motar ya tsaya a gabanta qanshinsu ya cakudu ya qara matsarta sosai yanda Motsin kirki bazata iyaba yace “Ammatana Rana gurin nsn kinsan farin mutum baya jure Rana a taimakeni ki shiga mota mu tattauna sauri nakeyi Mai martaba yake nemana naji bazan iya zuwa ba sai nazo naganki mun sake tattaunawa” hannunsa yakai zai riqo nata ta janye yayi murmushi yace “mutum da abinsa ake hana masa any way muje ina zuwa da sassafennan?”
Tabe baki tayi ta juya zatabar gurin yayi saurin riqeta ya fincikota ta fada jikinsa yaja numfashi me qarfi yanabin wuyanta da hancinsa yana sunsuna ya dora lips dinsa saman wuyan nata ya sumbata tare da sauke Mata hucin numfashinsa me dumi da dumama yanayi nandanan taji yanayinta na sauyawa a hankali tayi qasa da kanta ya janye tare da bude motar yaja hannunta yasata ya kulle ya zagaya ya shiga yayi Mata key yayi ribbers  ya fice daga gdan tunda suka fito kanta yake qasa ta kasa ko daga ido ta kalleshi yayi murmushi yanason mace me kunya wai wannan dan abin take sunkuyarwa da kai to ranar da bis ta dauri sin Kuma baisan ya zasuyi ba.
Rage tafiyar yayi ya juyo ya dubeta yace “ina zamune My brid?” Dagowa tayi ta kalleshi kawai sai yaga ashe kuka takeyi yayi saurin tsayawa yace “kuma me nayi nidin?” Sake qasa tayi da kanta ya kashe motar ya matso jikinta ta janye ya zauna a inda yake yace “menene laifina yanzu Rafi’ah?” Kukanta ta sakarwa sauti tace “kanason hanani farin ciki a rayuwata Ja’afar badon niba ka kyaleni wallahi cikin tekun masifa kakeson jefani banason kana shiga lamarina idanma ganin banyi aure bane yasa kake shigemin ka qyaleni wlh cikin satinnan zan fitar da miji Koda banasonsa indai zaka barni don Allah Ja’afar zuciyata qarama ce shiyasa bana cunkusa Mata damuwa zan iya canyo Mata ciwon da zai zama ajalina….”
Hannunsa ya dora a bakinta  yace “yanzun ma wayace kisa damuwa bakifa da wata damuwa ni naji Kuma ni nagani ni zanyi maganin kowacce matsala Rafi’ah kalmar qarshe na rantse da Sarkin da yake nufina da bude bakina ina furuci idan kika qara roqona akan na qyaleki zanyi Miki abinda baki taba tunani ba aurene naji na gani Kuma saina aureki duk Wanda zai mgn ya shekara baiyi ba yanzu haka jirana akeyi naje na bada kudin aurenki a yau zaazo gdanku a kawo ke idan kika takura ma wata gudan saina fasa baki nace a yau zaa dauramin aure dake muga qarshen tsiya haba don Allah ya kikeso nayine da wanne zanji kowa na gdanmu ya daina saurarona ya daina kulani saboda ke badan Mai martaba me fahimta bane Allah ya dorani akan Hajiya Innah ta shigemin gababa da yanzu bansan halin da nake ciki ba Hajiyata kuwa ko gaisuwata bata amsawa ita da yan’uwana saboda ke duk naji na dauka saikece zaki kasa jurewa wanda inada tabbacin bazaki samu matsala da iyayenki ba domin nasan sudin dattijai ne zasu karbi qaddara a yanda tazo musu, please na roqeki ki daina dagamin hankali wlh tallahi kinasona tsorone ya hanaki ganewa qaryane hadisin mutane da suke cewa ana barin halal don kunya babu wata halal da  kunya ta Isa danneta saidai idan kaso wahalar da kanka”
Numfashi yaja ya sake dubanta da idanunsa da suka canza kala yace “Rafi’ah ni ba yaro bane nasan kaina bazan taba yarda na cutar da zuciyata saboda wata ba watanma wacce zuciyata ta kasa karbarta sannan ta kasa bani kulawar da nake buqata, kema inaso ki bude tunaninki ki yarda da zabin Ubangiji gareki Wai Ina raba dare kikeyi kina roqon Allah yayi miki zabi na alkhairi to meyesa alkhairin yazo kike qoqarin sanya hanu kiyi fatali dashi haba meye haka don Allah wacce irin yarinta ke damunki ne?”
Ya qarashe mgnr da qaraji abinda yasanya jikinta daukar rawa ta toshe kunnenta idanunta naci gaba da tsiyaya tta bude dan qaramin bakinta tace “kai ba alkhairi bane a gareni wlh bazaka taba zama alkhairi ba banasonka Ja’afar banasonka bazan taba sonka….” Fincikota yayi da qarfi ya sanya hannunsa yayi baya da kujerar ya turata ta kifa rigingine tana kokawar tashi yabita ya danne idanunsa a rintse itama ta rintse nata jikinta yana rawa ta sake sakin Kuka me sauti yayi saurin hade bakinsu guri daya suka rinqa kokawa tanason qwatar kanta ta kasa sake kwanciya yayi a jikinta ya riqe hannunta yaci gaba da shan bakinta wasu hawaye masu zafi suka sulalo daga idonsa suka zuba akan nata ya bude idonsa a hankali yana kallon yanda hawaye ke ambaliya a idanunta.
Cigaba yayi dashan bakinta da wani salo Mai fitar da hayyaci daqyar ta tattara qarfinta ta tureshi shima saboda mutuwar da jikinsa yayine yasa ta samu wannan damar ta tashi da sauri yana sauke numfashi yana qoqarin saita kansa yace “kada ki qara cemin bakya sona Rafi’ah Ina ganin mutuncinki kada ki zubar dashi da kalamanki ni qaunarki nakeyi Kuma aurenki zanyi ba iskanci zanyi dakeba ki koyi tauna kalamanki akaina idan kika horar da zuciyata da rashin adalci da tausayi zakifi kowa wahala domin kece a cikinta saboda haka duk haukan data debo sai kinfi kowa hadiya so ki rinqa tauna lafazinki akaina”
Bai bari tayi mgn ba yaja motar da sauri har yanzu jikinsa a mace yake ya sake juyowa yace “bana tambaya sau biyu Kuma bana bada umarni sau biyu ki fadamin inda zaki idan ba hakaba zan tafi dake gidanmu duk sanda kika shirya mgn kyayi” a gajarce cikin gunji kuka ta fada masa inda zata yayi murmushi ya juya akalar motar ya tsaya a wani Mall yayi Mata shopping ya dawo yaja suka tafi daqyar take bashi directions na inda zata har sukaje qofar gidan yayi horn aka bude suka shiga yace “inane nan din?” Qin bashi amsa tayi ya daka Mata tsawa yace “mgn nake Miki inane nan?” Cikin kidimewa tace “gig…gidan Aunty Raziqa” ajiyar zuciya yayi ya bude Mata yace jeki Kuma ki jirani zan dawo komai dare na daukeki wlh kikayi gangancin tafiya zakisha mamakina”……..
_Hmmm! tab Rafi’ah kina ruwa🤣_
___________________________
Ficewa tayi da sauri har tana neman kifawa yabita da ido yana fitar da wata iska me zafi shima ya fito megadin ya Kira ya tambayeshi ko me gidan yananan ya amsa masa da “Eh yau yana hutu” ajiyar zuciya yayi yace “kayimin sallama dashi” da sauri megadin ya nufi cikin gidsn domin yasan waye Ja’afar Wakil a parlourn ya tarar dasu aunty Raziqa tanata rarrashinta tana tambayarta abinda ya faru.
Dubansa sukayi yace “Abuh Aulad ake Kira a waje” fitowarsa kenan suka fita tare da mamaki suka rungume juna Dr Naseer yace “Prince JM yau a gidana Amma dai ba zuwana bane wannan don nasan bakamasan gidana ba rabona dakai tun a Victoria I-land 3 years kenan” hularsa ya cire yace “wlh amaryata na kawo gdanka shine nace a kiraka nasan gdanka mana bandaisan matarka ba Ashe yayarmu ce?” Mamakine ya cika Dr Naseer yace “wa kenan?” Harararsa yayi yace “wace baquwarku yau?” Saita nutsuwarsa yayi yace “pretty nagani a parlour tana kuka dama tare kuke?” Murmushi yayi yace “itace amaryata wlh yarinyar tana wahalar dani sosai narasa ta Ina zan bullo Mata ta fahimceni” sake dubansa yayi yace “amaryarka ko budurwarka?” Dagowa yayi yace “duk daya itan budurwa tace Kuma amaryata saura kwanaki 29 idan ka cire yau saura 28 idan banda gobe saura 27 so ba laifi bane donna kirata matata fatane da Allah zai cikashi”
+
Wani numfashi Dr Naseer yaja yace “amma yaushe kayi aure inace baafi 3 mouths ba?” Daga Masa Kai yayi yace “eh ai kasan hudu Allah yace muyi ni ba zuwa nayi kayi jaridarka akaina ba ka kula kuma kayiwa matarka kashedi kada ta kuskura tabar Rafi’ah ta tafi ko nakai goman dare banzo ba zanzo ta jirani nazo na mayar da ita gida” yana fadin haka ya miqa Masa hannu yace “ka Bata kulawa sosai itadin rayuwata ce” mota ya shiga yabar Naseer tsaye shanye da baki Saida ya fita daga gdan megadi ya kulle qofar sannan ya juya ya shiga har yanzu kuka takeyi ya zauna ya zuba Mata ido ya dade yana nazarinta kafin ya furzar da iska yace.
“Ina kika samo wannan dan Izzar Rafi’ah Ja’afar Wakil fah?” Miqewa aunty Raziqa tayi tace “wai dama shine ai mijin aminiyarta ne meye hadinta dashi?” Kallon Raziqa yake yace “soyayya Mana harma da ranar aure yacemin saura 29 days a daura aurensu ni abokinane tun muna secondary bashi da sauqin mu’amala Izzar masifa ke gareshi indai ya nuna abu yace yanaso to ko zasusha wahala dagashi har abin saiya sameshi baya kula mace duk kyaunta nayi mamaki da akace zaiyi aure yasha fadamin shifa mace bata gabansa zai iya rayuwarsa shi kadai saboda baison damuwa to sai gashi baifi 3 mouths da aureba ya dauko wani aure ya akayi Rafi’ah?”
Matsawa tayi gsbansa ta Kama hannunsa tana kuka na fitar rai tace “wlh bansani ba bansan tsautsayin da yasa yasanni ba Uncle kayi wani abu akai mijin Bestie dinane ya yakeso nayi idan taji wannan baqin qudurin nasa?”
Miqewa Naseer yayi yace “hmmm ai kawai hqr zakiyi don wlh tunda kika kuskure kika fada komarsa to sai ya samu ko ta tsiya kota tsiya-tsiya” sake zubewa tayi a gurin ta riqe qafar Aunty Raziqa tace “nashiga ukuna meyesa kowa abinda yake fadamin kenan wlh banasonsa” kamota Raziqa tayi tajata dakinta tunda taga qanwar tata tasan tana cikin tashin hankali amma batayi tunanin yakai hakaba, zaunar da ita tayi tace “ya akayi haka Rafi’ah garin yaya har kika bashi dama ya tura gda Abba ya amsa har suka karbi kudinsa bayan kinsan mijin aminiyarkine”
Tsayar da kukanta tayi tace “kina zarginane aunty Raziqa yaushe na zama maci Amana da zan yarda da wannan hargitsin hatsin barar wlh bantaba bawa Ja’afar dama ba komai nasa iko yake gwadamin banasonsa Amma yace dole ne ma nasoshi Ni Kuma tsanarsa nakeji”
Shiru sukayi na dogon lkc kafin aunty Raziqa tace “Hmmm! To Allah ya kyauta Amma akwai qura Wakil family basuda sauqi akan qudurinsu tare mukayi karatu da Karimah qanwarsace babansu daya itama haka take indai tace tanason abu ta saita sameshi kiyi addu’a kawai Allah yasa hakan shine yafi alkhairi sannan kisa a ranki miji yafi qawa duk kuwa girman shaquwarku to wacce shaquwa ma ta rage ai babu ita tunda namiji ya shiga tsakiyarku kishine zaku fafatashi na mutuwa wannan shi ake Kira ranar biyan buqata rai ba abakin komai yakeba qanwata bazan zugaki kici amanar aminiyarki ba Amma idan ya dage ki hqr ki karbeshi dama wani lkcn ana samun haka garashi ma aurenki zaiyi wasu lalacewa sukeyi a titi yaqine yake tunkaroki qarfinki bazai qwaceki ba sai taimakon Ubangiji da samun yardar mijinki….”
STORY CONTINUES BELOW
Kuka takeyi sosai itakuma Aunty Raziqa ta dage nasiha take Mata da nuna Mata ba kanta aka faraba a fakaice take kwadaita Mata son auren Ja’afar Wakil hardai ta samu tayi shiru da kukan  Amma qasan zuciyarta ciwo yakeyi Mata lamarin Ja’afar tsoro yake bata tayaya ma zata iya kallon idon Ni’imah tace Mata mijinta zata aura? wannan tunanin bai barta ba bacci ya dauketa bata tashi ba sai bayan azahar tana tashi ta shiga tayi wanka tayi sallah ta dade cikin sujjadarta tana roqon Allah kada ya tabbatar da wannan kwadon tuwon alkamar bama zai cuwu ba.
Tana idarwa aunty Raziqa ta shigo tace “kizo to kinsha bacci ko?” Miqewa tayi ta gyara fuskarta kasancewar kwalliya ta zauna a jikinta ko batayi ba kamar tayine takowa tayi tanajin gabanta na faduwa kawar da idonta tayi daga kansa a fili tace “maye kawai” abin mamaki batasan yaji ba sai taji yace “tukunna ma sai ranar da komai ya kammala zaki tabbatar da ni asalin mayene akanki don wlh nayi Miki alqawarin tun daga yatsanki har qofa ta qarshe ta gashinki saina lashe”
Juyawa tayi ta kalli inda su anti Raziqa suke lunch taga hankalinsu ba akansu yakeba kafin ta dawo da nutsuwarta taji ya rungumeta ta baya ya sanya hannunsa ya dago habarta qamshin turarensa ya sakar Mata da wata kasala me qarfi ya dago habarta ya dora bakinsa saman nata suka lumshe idonsu a tare tare da sauke ajiyar zuciya ya dora hannunsa saman qirjinta batare da ya kamaba daya na kan mararta daya na qirjinta ga bakinsa cikin nasa”
Wai Ashe bashi kadai bane kawai sai haske tagani a cikin idanunta dake lumshe suka bude da sauri kawai sai taji gurin ya dauki tafi Muhseen ne da wani camera man, janyewa tayi da sauri ya sake janyota ta fada a hannunsa nanma Saida suka qara haskasu sannan camera man din ya fice Muhseen ya kalli JM yace “maye kawai”  dariya ya kwashe da ita Yana sakinta abinda bata taba gani a fuskarsa ba ta kalleshi taji qirjinta yabada wani dam ta dauke Kai ta zauna cikin tsananin jin kunya.
Jitayi yace “eh ka fada dama ka samu ko matata mijinki mayene ko?” Harara ta galla masa ya sake kwashewa da dariya yace “zanga ranar da zaa daina hararata nikam yanzu ya zakiyi dani fadamin abinda kike shiryawa game da aurenmu?” Daukan cup din lemo tayi takai bakinta ya matso ya zauna kusa da ita ya dauko abincin ya diba yakai bakinsa ya sake diba yakai Mata ta janye yace “kada ki wahalar da shari’a kotu batason gardama ki karba kawai idan kinqi kuwa kinsanni yanzu zan baki charge”
Ga mamakinsa sai yaga tana neman bare Masa baki yayi saurin saita kansa duk wani annurin farin ciki dake fuskarsa ya dauke yace “Ansha fama Ashe ba banzaba kafiyar ma gado kikayi Abba koro mutane yayi da kudin aurena naje har kasuwa na sameshi yayimin kaca² baa taba cimin mutunci kamar Wanda akayimin a sanadin aurenki ba Dad ma babu abinda Bai nuna masa ba yaqi amsawa qarshe dai sai Dad ne yayiwa Mai martaba jagora sukakai kudin Darazau gidan Baba Hudu kayy yau Baba Hudu ya gamamin komai a duniyar nan wlh dattijon arziqi cewa yayi tunda abin yazo da haka kawai a daura inyaso nanda 1 mouth din ayi biki zancen da nakeyi Miki Mai martaba da waziri da sauran wakilaina Basu baro Darazau ba Saida suka tabbatar da igiyar aurena ta hau kanki….”
Miqewa tayi a gigice yayi saurin riqeta yace “meye hakan?” Kawai sai yaga ta sulale qasa jikinta ya dauki tsuma haqoranta suna haduwa ya matsa kusa da ita kafin yakai ta dauki cups din dake gabanta ta jefeshi dashi a goshi ji kakeyi qwal take jini ya balle masa ya dafe gurin da sauri ya dago ya kalleta kawai sai gani yayi ta fizgi wuqar dake jikin kankana ya kuwa kwaso gudu ya riqeta suka rinqa kokawa tans kuka me gunji tana Kiran sunansa tana cewa “ka qyaleni Ja’afar ka qyaleni na kashe kaina na huta wlh banasonka na tsaneka na tsani kaina Ja’afar meyesa rayuwa tayimin haka meye nayiwa duniya da batamin adalci wlh saina kashe kaina bazan taba karbarka a miji ba”
Duk qarfinsa sai gashi ta watsar dashi a qasa ya sake tashi daidai lkcn da Abba ya shigo gdan ganin yanda aka taru akan autar tasa rai biyar sun kasa riqeta sai kuka takeyi tana ihu tana rantsuwar saita kashe kanta yayi mugun tashin hankalinsa dama abinda yake tsoro kenan yasanta yasan batada control indai akakai hqrnta qarshe kafin ya ida qarasawa ta zubar da Ja’afar Muhseen Naseer Raziqa da Musa camera man daqyar Ja’afar ya qwace wuqar duk ta yankeshi da ita a hannu,
Kwasa tayi da gudu ta nufi kitchen Abba ya daga murya ya qwala Mata Kira sai ta zube a gurin tanabin kowa da kallo ta sake sakin kuka me ciwo ta fada jikin Abba daya tsugunna a gabanta yara Rashid ya riqota ta lafe a jikinsu tana sake shigewa jikinsu tana kuka me tafasa zuciya tace.
“Allah ya isana wlh Abba bazan taba yafewa Baba Hudu ba me nayi masa me na tsare masa da zai dauramin aure da wannan tsinannen maci Amanar Abba kace ya sakeni wlh zan kashe kaina Kona kasheshi banasonsa na tsaneshi tsana ta gaske wayyoh Abba zuciyata qirjina Abba wayyoh rayuwata wayyoh Bestie na meyesa kika dauko mana jarfa ya yanke mana igiyar zumunci saboda cikar burinsa…..
Bata gama rufe bakinta ba sukaji an banko qofar da qarfi dagowar da zasuyi sukaga Ni’imah ce da gudun bala’i ta nufi Rafi’ah da wuqa a hannunta tsirara tana kuka itama gabadaya parlourn sukayi kanta suka tareta batakai ga qarasawa ga Rafi’ah tayi tayi ta qwace ta kasa sai ta sake sakin kuka tana cewa.
“Ashe munafukace ke maci amana mijina kikeso bansani ba Rafi’ah me nayi Miki a rayuwarmu ta 21 year’s kika zabi yimin wannan sakayyar mijina Rafi’ah Allah ya Isa tsakanina dake kin cutar dani kin yaudareni kullum alkhairinki nake fada bantaba ganin sharrinki ba Ashe ke naki sharrin
yafi na kowacce mace a duniya na rantse da Allah indai Ina raye kamar yanda kika yankemin farin ciki saina yanke Miki naki keda farin ciki har abad…..”
Tsawa Ja’afar ya daka Mata ta juya kansa yayo kanta yana huci ya shaqota yace “da nace kada ki fito shine Saida kika fito to daganan ki wucce gdanku….” Saurin katseshi Abba yayi da cewa “haba kaikuma mema ka fara gani da har zaka fara yanke hukunci Ja’afar aj bakaga komai ba tunda haka ka zaba gasunan duka matanka ne kalmata ta qare tunda abinda Allah ya hukunta ya riga ya faru Abu daya da zan fada maka shine, yata Rafi’ah batada hayaniya zuciyarta a tsarkake take idan ta gyaru Kaine idan ta lalace Kaine bazan taba baka itaba tunda baka Isa da gidanka ba ka gama danan sannan saika dawo nan…”
Yana fadin haka ya figi hannun Rafi’ah suka fice sakin Ni’imah Ja’afar yayi yabisu yana Kiran Abba shiko ko sauraronsa baiyi ba ya cilla yarsa a mota yaja suka fice shima motar ya dauka a guje yabisu sun rigashi zuwa suna zuwa Abba yace da megadi kar yabarshi ya shigo, aikuwa yin duniya magiyar duniya mado megadi ya hanashi shiga gdan komawa yayi cikin mota ya buga kansa da sitiyari zuciyarsa na tafasa baiyi aune ba saiji yayi glass din motarsa ya tarwatse ya dago da sauri tare da budewa ya fita daidai lkcn da glass din ya tarwatse ya zubawa Ni’imah ido kawai sai yaji ta bashi dariya ma ya tsare Napep ya shiga ya fada masa inda zaa kaishi da gudu ta biyo sahun tana cewa “ka saukeshi wlh cikin biyu saidai ya zabi daya azzalumi macuci mayaudari maci Amana…”
_Kaina ya kulle da wannan chakwakiya 
____________________________
Tunda suka dawo gidan mutanen gdan suka hadu a kanta suna aikin rarrashinta yin duniya taqiyin Shiru Koda tayi niyyar yin shirun idan ta tuna da furucin aminiyar tata ta Kuma tuna da cewa yanzu fah da ita da aminiyarta duka sunan matan mutum daya suke amsawa sai taji sabon kuka ya qwace Mata qarshen qarshema zazzabi ne ya rufeta ba qaramin artabu sukayi da Abba ba sannan ta daina furta zata kashe kanta yajata yakaita daki kamar wata qaramar beby ya kwantar da ita ya rinqa bubbuga bayanta har bacci ya dauketa sannan ya tashi ya fita.
Dakinsa ya shiga ya Kira wayar Dad ya daga suka gaisa yace “Haba Sabo meyesa kayimin haka don Allah banji dadiba wlh duk da na matsu naga Rafi’ah ta fitar da miji Amma ai ba irin wannan matsuwar da zaa kasa duba alaqa ba yanzu ga abinda wannan auren ya janyo daga ita har Ni’imah babu me hayyaci ita tanata kukan bataso saita kashe kanta kota kashe Ja’afar ita Kuma Ni’imah tana zargin da sahalewarta akayi wannan auren Sabo wannan bayyananniyar cin amanace fa da kowa zai shaida….”
+
Katseshi yayi da cewa “meyesa zaka tsuke tunaninka ka rinqa tunani irin na Mata Alh Nuhu Ni dama na dade da fahimtar hakan zata faru Ja’afar yanason Rafi’ah tunkan ya auri Ni’imah da an qara jinkiri baayi gaggawar hada aurensa da Ni’imah ba qila da Rafi’ah zaigani ya zaba to Amma Allah ya hukunta dukkansu matansa ne saboda haka muyi Shiru kawai mu karbi abinda Allah ya zartar Ni’imah ai ba ita tayi kantaba naji duk haukan da taje tayi muku wlh akan lamarin nan zan iya cin mutuncinta indai bata nutsu ta fahimci abinda ke gabanta ba bandama shirme irin nasu na Mata da yaje ya dauko Mata bare ta girgijeta ai gara ya auri aminiyartata babu wani cin amana a auren sunnah dukkansu matansa ne haka Allahu ya tsara to mubi kawai muyi Shiru”
Sosai Alh Sabo ya rinqa tausar Abba da kafa masa hujjoji hardai ya rusuna ya karbi abin tare dayi musu fatan alkhairi Amma yana Jinjina yanda zaman zai kasance shi tausayin ma Ja’afar din yakeyi har gara Ni’imah qila ta tausu ta dadi Amma Rafi’ah tanada wuyar sha’ani akan abinda ta yarda aranta ba daidai bane”
Bangaren angon Ja’afar kuwa da Ni’imah tunda yaje gida ya haye samansa yanada dan qaramin clinic a cikin bangarensa ya fara dressing din hannunsa ya yanku sosai amma baiji haushi ba saima murmushi da yayi yace “zan saitaki ne Rafi’ah wahalar dama zamowarki tawa tunda kin zama ai asiri ya rufu” yana wanke ciwon yana cije lebe har ya gama ya koma ya kwanta yanajin zugin hydrogen din ya jima a kwance sannan yaji alamun shigowarta saman ta hau ta kalli qofar a rufe ganin hakan yasata fara dukan qofar da dukkannin qarfinta tana cewa.
“Tunaninku zakuci amanata ku hutane qarya kake Ja’afar Wakil tabbas baka fara shiga damuwa ba wlh ka zubar da farin cikinka tunda kaci amanata macuci mayaudari maci Amana azzalumi, Ashe dama abinda yasa kullum bakada Hira saita Rafi’ah kenan Ashe da gaskene saqon da aka taba turomin cewa kullum sai anganka a makarantarsu ka dauketa ni Ina tunanin saboda nine macuci Ashe kanka kake ginawa to wlh dole ayi dayan biyu dole ka saki daya cikinmu domin baa fada daya sarki biyu Ja’afar ka budemin ka fadamin laifin da nayi maka da zakayimin wannan sakayyar….”
Yanajinta yayi Mata banza tayi bugun duniya yaqi budewa zagin duniya tayi masa ya shareta saboda dama ya shiryawa zuwan wannan lkcn baizaci ma haukan nata zai tsaya iyanan ba a yanda ko a Hira take nuna masa ita zata iyayin komai akan kishiya, yanajinta ta gaji ta zube a gurin taci gaba da kukanta tana cewa “Allah dama mafarki nakeyi na bude idona naga ba gaske bane Allah ka mayarmin dashi tunani na shaidan Allah bazan daukaba wlh kasan bazan daukaba bazan iya zama da Bestie na matsayin kishiya ba Allah ka kashe wannan azzalumin Ja’afar na huta Allah ka hada hardani  nikam na shiga ukuna Allah….”
Maganganu takeyi kamar zararriya yanajinta yaqi budewa saboda shi kansa zuciyarsa a cunkushe take bada damuwar Ni’imah ba aa damuwar halin da Rafi’ah take ciki shine yake addabarsa gashi Kiran duniya yayi taqi dagawa ya tura Mata saqo taqi replying dabara ce ta fado masa ya Kira number Ammi don dama tun ranar data kirashi tayi masa warning yayi saving ring biyu ta daga da sallamarta ya amsa tare da cewa “Ammi barka da Rana” jin muryarsa yasata hadiyar wani takaici Amma dake dattijuwa ce saita dake tace “lfy Ja’afar ya gdan”
Shiru tadan ratsa kafin ya ja numfashi yace “inata Kiran wayarta taqi dagawa Ammi Allah yasadai lfy?” Iska ta furzar tace “yo wanne lfy Ja’afar dama kanasonta da lfy ne ai da sauqi ma da bata hadiyi zuciya ba tanacan tana fama da zazzabi” miqewa yayi zaune yace “ya Salam bari nazo na dubata” yana fadin haka ya kashe wayar ya tashi shi kansa idan zaa dubashi din so yake bai Saba da tashin hankali ba shi tashin hankali fitar dashi a hayyaci yakeyi.
STORY CONTINUES BELOW
Doguwar riga yasa ya dauki key ya fice a hanya ya kira Muhseen yake sanar dashi ya daukeshu suka tafi daqyar megadi yabarsu shima Saida Ammi tayi masa mgn suka shiga sukayi parking Rashid dake fitowa yazo suka gaisa yayi masa ya hannu saboda yaga aika²r da qanwar tasa tayi, shine yayi musu jagora har parlourn baqi suka qara gaisawa ya dauki wayarsa ya kirayi Rafi’ah ta daga lkcn ta tashi tasha magani tayi salla yace “kizo ki sameni maza a parlourn baqi” bai jira cewarta ba ya kashe wayar ta kalli Ammi Ammi ta kawar dakai tace “
“Kidaibi a sannu kada ki zafafa kiyi biyu Babu ba mijin babu aminiyar ita rayuwa baduk abinda kakeso kake samu ba iyakar saninmu munayi Miki addu’ar samun miji na qwarai Kuma kema munsan kinayi tunda Allah shi ya zaba ya zaayi dama shi muka miqawa zabin Kuma yayi abinda ya dace”
Ficewa tayi tabarta da sassanyar gwiwa wasu hawaye suka zubo Mata wayar Yaya Rashid ce ta sake shigowa cikin kuka ta daga tace ”gag ganinan Yaya” miqewa tayi ta zari hijjab saboda sanyin da takeji ta fice ta sauka ta nufi parlourn baqin ta tura qofar ta shiga da sallamarta idanunsa na kanta suka amsa Yaya Rashid ya miqe shida Muhseen suka fice tare dajan qofar ya rage daga ita saishi ganin taja ta tsaya yasashi shareta yaci gaba da danna wayarsa kawai takaici yana cika masa ciki Wai kawai laifinsa don ya sota ya aureta ne take basa wannan ciwon kan jibi yanda ta wani tsaya masa aka kamar sa’anta.
Dagowa yayi ya dubeta tama kawar da kanta gefe daga facing dinsa idanunta ya balle da ruwan hawaye miqewa yayi a ransa yana dannan zuciyarsa dole ya koyi rarrashi don alamu sun nuna masa Kuma yaji a bakin Ni’imah amaryar tasa yar shagwaba ce a sangarce take kuka bayayi Mata wahala idan Kuma akaqi bata hqr sai tayini tanayi kamar wata qaramar yarinya shikuma gashi ba gwanin iya rarrashin mace ba to ta inama zai iya shida ko rakiyar zance baitabayi ba Saida yazo kansa Kuma itadin daya kamata su daidaita su fahimci juna taqi bashi hadinkai da tuni sun wucce babin kansu saidai suji da Ni’imah yar tujara, Hannunsa yakai ya kamo hannunta ta fincike kamar wacce akayiwa allura ta balle da bala’i tana nunashi tace “zan zagi babanka idan ka qara tabani mara zuciya kawai Wanda aka dafa zuciyar kare aka bashi ya ciny…..”
Wata tsawa ya daka Mata me hade da ihu data sanyata ja da baya yayi saurin dukan qofar da qafarsa ya fara matsarta tana janyewa Saida sukaje qarshen dakin ya damqi wuyanta idanunsa sun kada sunyi jawur jikinsa sai rawa yakeyi ya bude bakinsa dake tsuma yace “bana umarni sau biyu wannan shine na uku ki rinqa sanin kalmar da zaki fadamin duk so bazan dauki raini da wulaqanci ba ni ba qasqantaccen bawa bane da zaki rinqa jana a qasa kamar karenki dole ne Rafi’ah dole kisoni kiyimin biyayya domin Ni nan mijinki ne ba yaronki ba kuma ba dan iska baneni nida kike ganina bana daukar raini raini ma a gurin macen da nakeso kawai don nace inasonta wlh idan kika bari kikakai zuciyata qarshe zan wahalar da ruhinki Rafi’ah zaki kasa samun jin dadi ta ko Ina ni a gurina zaki samu farin ciki to nima nema kike ki qureni”
Sakinta yayi ya koma ya zauna yana huci taja ajiyar zuciya me qarfi iya tsorata ta tsorata dashi ta shiga taitayinta guri ya nuna Mata  a hassale yace “ki zauna naceee!” Da sauri ta zauna yaja numfashi ya sauke muryarsa ya sauko gabanta ya Kama hannunta yana murza cikin a hankali ya dago kanta idonta a lumshe yace “karki qara fadamin irin wannan mgnr kinji?” Da sauri ta daga masakai bakinta na rawa ta fada jikinsa ta rushe da kuka tace “me kakeso yanzu dani ni kadaina zuwa gidanmu ka daina zuwa gurina ka daina Sona nima bana sonk…..”
Bata idaba ya wawuri bakinta yasa a nasa ya fara aika Mata da wani zazzafan kiss me gigita yanayi qoqarin qwacewa takeyi shikuma yana qara shigar da ita jikinsa yana danna kanta tare da hura Mata iskar hancinsa da ta hadu ta sakar Mata wata kasala, a hankali ya dagata cak ta fara tureshi tanason qwacewa shikuma ya riqeta a qirjinsa suka zube a kujera bakinsa na cikin nata ya tura hannunsa cikin hijjab dinsa tsoro ya lullubeta don ko riga babu a jikinta saga ita sai bra.
Taushin fatarta ya kidama masa lissafi ya qara tura hannunsa tayi nasarar zame bakinta ta fashe da kuka tace “please ka bari don Allah banas….” Mgnr ce ta maqale lkcn da ya sauke hannunsa kan bra dinta ta rintse idonta jikinta ya dauki tsuma ta saki gunji a cikin kukanta tayi saurin girgiza masa Kai tace.
“ Innanillahi don Allah Ja’afar ka bari banaso nashiga uku Ammi na wayyoh Abbana wayyoh Yaya Rashid…..” Rufe Mata baki yayi jikinsa yana rawa yace “Calm down bazanyi Miki komai ba” tureshi ta farayi tace “Zaz….zafi kabari nipples dina zafi” hakan dama yakeson yaji yayi murmushin mugunta yace “kinason na bari?” Saurin dagansa Kai tayi tana zubar hawaye yasa bakinsa ya fara lashe hawayen bai daina motsata ba yace “kicemin kayi hqr My Bestie kabari akai makani gdanka tukunna sai kayi komai”
Rintse idonta tayi kunya hade da tsoro suka qara shigarta yasa hannunsa ya janye hijjab din ya zubawa qirjinta ido wani kyaune dasu na musamman yaja numfashi yana Shirin Kai bakinsa ta riqe kansa tanayi masa magiya ya dago qananun lumsassun idanunsa yace “Kinqi kice waike kunya ki fada ki tsira banajin kunya akan halal kema shaidane bazanji kunyar taranki gajiya anan ba wlh ke kinsani” ganin abinnasa na canza salo yasata saurin maimaita masa abinda yace,
Sakinta yayi yana murmushi sosai yakeji a jikinsa don da gaske yau feeling dinta yakeji, hijjab dinta yaja Mata ya rufe Mata jikinta ya kwantar da kansa yace “daga yau na soke sunan Bestie akan kowa ni kadaine na cancanci sunan nan karna qarajin Ja’afar a bakinki Bestie shine sunan da nakeso ki fara kirana dashi a gaban kowa harda Mai martaba”
Matse qwallarta tayi ta miqe zaune har yanzu qirjinta dukan tara² yakeyi ya dubeta yace “ammi tacemin bakida lfy Kinga nima ciwon da kikajimin ya jikin naki” Shiru tayi masa wani haushinsa takeji da ninkin tsanarsa ta tsani mutum mayaudari kalaman Ammi ne kawai suke danne zuciyarta da tuni ta qara illatashi, miqewa tayi tabi ta gefensa yana kallonta tunaninsa wani abin zata dauko sai yaga ta bude qofa ya miqe da sauri Amma kafin yayi wani yunquri harta fice ya daki bango yanajin abin aransa dukkan wasu alamu na bayyane sun nuna hikimarsa bazata jawo masa hankalin Rafi’ah ba saiya hada Mata da addu’a.
Dole miqewa yayi ya fito suka fita da Muhseen tunda suka taho ya kife kansa a cinyarsa har sukaje gdan bai dagoba Saida sukayi parking Muhseen ya taboshi ya dawo daga duniyar tunanin daya tafi ya kalleshi murmushi yayi yace “abinda kowa yake jiye maka kenan kaqi yarda gashinan tun baaje ko inaba ka fara ciwon Kai”  bude motar yayi ya fice ya nufi cikin gdan yanajin wani qauri yana dukan hancinsa da sauri ya qarasa shiga yaga wani baqin hayaqi yana tashi ta sama ya kwasa da gudu a step na qarshe yaja yayi turus ganin Ni’imah tsaye gaban wutar da takeci da sauri yakai dubansa ga wutar abin mamaki suturunsa ne da takalmansa tasawa wuta Kuma take tsaye a gabansu tana jiran su cinye…
Sosai abin ya girgizashi Amma dake qwallon dan duniya ne sai kawai yayi murmushi ya shiga cikin dakin wata suit dinsa da sauran wasu kayan da bata dibaba ya debo ya miqa Mata yace “kin manta da wadannan”……

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *