YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 14 BY HARUNA USMAN

 YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA

CHAPTER 14 BY HARUNA USMAN

Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA

Sarki ya ce, “Ku dai samarin wannan zamani al’amarinku sai ku, yanzu kowannenku ya bar yankinsu, ya shiga cikin hadarin neman yarinya? Kun san halin mata kuwa? Ko da yake yanzu dai duk a Kyale wannan zance. Shin ka yi nasara game da abin da ka fita nema?”

Yarima Amir ya ce, “A’a, Allah Ya taimaki Sarki, amma na sami labarin inda za mu iya samun labarinta. Shi ne na dawo in shirya in sake fita, an ce can kasar Arewa akwai wani Sarki wanda shi ma hakan ta faru ga ‘yarsa kuma an tabbatar cewa yana da cikakken labari. Daga wurinsa kuma sai in tsunduma duniya neman ta.” Da Sarki ya ji zancen dansa sai ya ce, “Ya kai dana, ina ji maka tsoron yawo cikin duniya, ka dai ga dan Karamin misalin abin da ya faru ga abokinka, mafi yawancin jama’‘arsa sun rasa rayukansu, kuma ga shi kai ne mutane suka sa wa ido a matsayin magajina.

ZAMU TASHI 

Sai dai kuma soyayya ta rufe maka idanu ko mulkin ma naga kamar ba ka damu da shi ba. Kuma shi mulkin nan in ka bari ya Kwace maka, to ba za ka sami wani ba, amma ita mace kana zaune sai a kawo maka ko guda nawa kake buKata.

Yanzu ma maganar da ake yi akwai wata yarinya da da na ajiye musamman don kai. Kuma na tabbata kyan ta da cikar halittarta in bai wuce na yarinyar da kake wahala a kanta ba, to ba ko zai gaza ba. Ka je yanzu bayan mun gama cin abinci ka gan ta.”

Da dan Sarki ya ji zancen mahaifinsa, sai ya yi godiya sannan ya ce, “Ya kai babana mai girma, ina fata ka yi mini gafara a game da abin da zan fada.”

Sai Sarki ya ce, “Aminci gare ka ya dana. Fadi

jawabinka.”

Dan Sarki ya ci gaba, “Godiya nake. To a cikin jawabin mai martaba ya ce akwai mata da yawa, sai dai kuma abin da Sarki ya sani ne cewa ko a cikin rigunan Sarki akwai guda daya wadda ya fiso. Haka ma dawakin Sarki da ‘ya’yansa. Haka nan ma a duk cikin abin da Sarki ya mallaka ballantana kuma cikin matansa. Saboda haka ya babana, ni yanzu hankalina yana wurin wata kuma ina ji a cikin raina cewa ban

yanke tsammani ba. Ni yanzu in ba ita na aura ba, to gaskiya ina jin hankalina ma ba zai dawo kan sarauta
ba.

Ranka ya dade ita kuma waccan yarinya da ka tanadar mini, to na gode Allah Ya Kara girma, amma Baba ka yafe ni. Ni ko ganin ta ma bazan yi ba don na san ba zan so ta ba alhali masoyiyata na raye…”
Bashari ya yi sauri ya dubi abokinsa ya kifta masa ido, yana mai masa nunin cewa ya bi a hankali, har ma a daidai nan Basharin ya katse masa magana ya ce, “A‘a, kai dai kada ka yi saurin yanke hukunci, ka bari ka gan ta mana.”

Sarki ya ce, “Yauwa, ka ji magana ke nan.” Sarki na zaton lallai in ya ga yarinyar, to dole ya ji yana son ta ko da ba kamar waccan ba, ta yadda zaa iya lallaba shi ya aure ta. Daga nan ko ba komai zuciyarsa za ta fara rage tunanin waccan da baa san inda take ba.

Aka gabato da abinci da kayan marmari iri-iri, a

kan cewa in sun kammala Bashari zai raka abokinsa su shiga su ga yarinya. AMMa al’amarin yarinya ‘yar Fulani kuwa, lokacin da Ja’e mai yi wa mahaifinta kiwo shi da abokansa suka sassari mahaifinta a gabanta suna tunanin sun kashe shi kamar yadda suka kashe kaninta, to ita sai suka daure ta suka kada tare da shanu. A kan hanyarsu suka sayar da ita ga wasu fatake a  kan dinare dubu uku.
Da fataken da suka saye ta suka lura da kyanta, sai suka yi ta tattalin ta suna kulawa da ita yadda ya kamata har suka isa birnin Jagirgiri inda Sarki Mus’ab yake sarauta. Suka Ki kai ta kasuwa don wayo da kuma lura irin ta kasuwanci. Maimakon haka sai suka tsayar da shawarar tallatawa Sarki.

Suka sa Bingyel ta yi wanka sannan suka kawo sutura da kayan kwalliya irin na alfarma suka ba ta ta fece ado. Babu shakka in ka gan ta za ka ce ko watakila tana cikin kyawawan aljanun nan ne da akan yi labari. Wadannan fatake ba su zame ko ina ba sai fada, aka yi musu iso suka shiga har wurin Sarki. Ita kuma yarinya ta rufe jikinta kaf har da fuska.

Aka yi sa’a kuwa a ranar Sarki Mus’ab na matukar jin nishadi. Ya tambaye su dalilin zuwansu.

Fataken nan suka rusuna, sannan sai babbansu ya ce, “Ran Sarki ya dade, haja ce irin taku ta manyan sarakunan duniya muka kawo maka, yarinya ce balagaggiya wadda har yanzu yarinya ce ba ta zama mace ba tukuna. Kyakkyawa ce wadda za ta iya bugawa da kowace mace a bangaren kyau.”

Sarki ya umurci yarinya ta bude fuskarta, ai yana ganin ta sai ya zuba mata idanu kurui yana mamakin irin wannan kyau nata. Zuciyarsa ta fara sarke
Www.bankinhausanovels.com.ng sarken cewa, “ tsarki ya tabbatar wa wanda Ya halicci wannan kyau.”
Yace, “Nawa kuka sayi wannan yarinya?”
Suka ce, “Dinare dubu uku ne Allah Ya ba ka yawan rai.” Sarki ya ba Ma’aji umurni cewa a ba su dinare dubu goma, sannan a ba kowannensu manyan riguna goma-goma, suka fadi suka yi godiya don tsananin murna da irin wannan sallama. Ita kuma yarinya Sarki ya sa aka shiga da ita cikin gida tare da umurnin cewa kada a kuskura a sa ta aikin komai, kuma a rika ba ta abinci na alfarma da isasshen kayan marmari don jikinta ya Kara kyau da ni’ima, tare kuma da sutura irin wadda ta dace da kyakkyawa irinta. Jakadiya ta ce, “An gama, ran Sarki ya dade.”
Tun daga wannan rana da aka shiga da ‘yar Fulani cikin gidan Sarki, babu abin da ya sauya na irin halin Bacin ran da take ciki tun daga lokacin da dan Fulani ya yi musu wancan mugun alkaba’i. In ta tuna dan’uwanta da mahaifinta da a iyakar saninta ta tabbatar da cewa an kashe su a gabanta, da kuma saurayinta Bashari, duk sai abubuwa su dugunzuma su cakude mata a zuciya, sai ta fashe da kuka. A mafi yawan lokuta kuma da zarar hakan ta faru, to sai ta dauko sarewarta tana busawa, wata irin busa mai sa tausayi a wurin mai sauraren da ke da masaniyar yadda busa ke tafiya. Amma a wurin sauran gamagarin mutane, sai mutum ya ji busar kamar don sa nishadi ake yi, wanda hakan ya sa in ta fara sai mutanen cikin gidan Sarki duk su natsu suna ta saurare.

Duk abin nan da ake yi da duk lokacin nan da aka dauka, Sarki bai taba shiga inda take ba. Sai dai duk lokacin da ya ji busa, to ya tabbatar da cewa ita ce. Kuma shi kansa yana matuKar jin dadin busar.

Wannan shine al’amarin ‘yar Fulani.

Amma shi Bashari mun bar shi a fadar Sarki yana cin abinci da abokinsa dan Sarki tare da Sarkin suna ta hira irin tasu ta saraki. Sarki na ta nuna musu irin kyan wannan yarinya da kuma KoKarin tausa dansa a kan cewa ya bar wa Allah, in waccan yarinya da ya ke nema an gan ta, sai ya yi ta biyu ko ta uku da ita. Shi kuma yaro yana ta kewaye-kewaye cikin kunya. Can sai suka ji busar sarewa na fitowa daga cikin gida, sai Sarki ya ce musu, “To, yarinyar da na tanadar maka ce ke wannan busa.”

Suka yi tsit suna sauraro, shi kuwa Bashari sai tsigar jikinsa ta shiga tashi, ya tabbatar da yanayin busar kuma ya fahimci wadda ke yin ta. Ai nan take ya sa hannu cikin aljihunsa ya zaro tasa sarewar ya fara
Www.bankinhausanovels.com.ng mayar da busa.
Mamaki ya rufe Sarki da dansa, amma tun kafin su sami damar yin tambaya sai ga yarinya ta fito daga cikin dakinta a guje ta nufe inda su Sarki ke cin abinci, don ita ma ta riga ta tabbatar da wanda ke busar. Matan gida suka biyo ta a guje suna zaton ko ta zautu ne. Tana shigowa Bashari ya gan ta, ai bai san lokacin da ya tsallake Sarki da gudu ba ya nufi inda take ya tsura mata idanu. Kafin ka ce mene ne wannan, dukkan su sun yanke jiki sun fadi a sume saboda tsananin mamaki da kuma rashin zaton yadda hakan ta kasance a gare su.

Aka zuba musu ruwan randa mai sanyi suka farfado, shi kuma dan Sarki sai ya fara labarta wa mahaifinsa cewa wannan yarinya da aka tanadar masa ita ce abokinsa ya fito nema, kuma Allah Ya sa abokin nasa ya dace. A nan Sarki ya sake hakikance cewa lallai soyayya ba Karamar aba ba ce.

Bashari ya gabatar da abokinsa Amir dan Sarki ga ‘yar Fulani da irin taimakon da ya yi masa lokacin da suka fito neman ta. Ya kuma shaida mata cewa mahaifinta bai rasu ba yana nan yana samun sauki.

Amir dan Sarki ya ce, “To ai faduwa ta zo daidai da zama ke nan, yanzu sai in kammala shirina na tafiya Kasar Arewa kawai. In na je na kai Bashari da ‘yar
Www.bankinhausanovels.com.ng Fulaninsa gida, sai in wuce.” Bashari ya ce, “Haka daidai ne, amma maganar ka wuce ba ta taso ba, don kuwa in mun mika ta gida hankalin iyayenmu ya kwanta, to Kafata-Kafarka za mu je neman taka budurwar. A cikin hankalina ba zan taba samun natsuwa ba irin alherin da ka yi mini da kuma yanayin yadda Allah Ya Kaddara yanke wahalata sanadinka sannan kuma a ce in kyale ka ka tafi kai kadai alhali kuwa na san matsayin soyayya.”

A haka rundunar dan Sarki ta mutum dubu ta motsa zuwa garin su Bashari. Aka fito taryar su har da Sarki da Sarkin Fulani don yanzu ya sami sauKi. Bingyel ta ga mahaifinta, ta ruga ta rungume shi suna kukan barka da arziki.

Bayan sun sauka sai aka kawo Ja’e dan Fulani da sauran abokansa aka yi musu shari’ar fashi da makami da kuma kisan kai. Laifi ya tabbata a kansu, aka sa hauni ya dauke musu kawuna.

Bashari ya ba Sarki labarin abokinsa yarima Amir da irin taimakon da ya yi masa tare kuma da labarin cewa shi ma yarinyar da zai aura ce ta Bata. Kuma yanzu zai wuce Kasar Arewa neman labari, yana son zai bi shi in ya so in sun gano yarinyar, sai su dawo gaba dayaa fara hidimar biki.

Sarki ya ce, “Ni ban Ki ka raka abokinka ba, amma

Www.bankinhausanovels.com.ng da sharadi, muna iya gaggauta daurin aurenku da Bingyel tukuna, bayan biki da kamar mako daya sai ku yi tafiyar ku.” Dole suka amince.

Aka daura auren Bashari da ‘yar Sarkin Fulani, aka yi gagarumin bikin da a iyaka tarihin Kasar wanda aka sani, ba a taba irinsa ba. Sai dai kuma wani babban abin bakin ciki, ana gobe amarya za ta tare sai kawai aka ga wani abu ya zo ya sungume ta ya yi sama da ita, masu ihu na yi, masu jifa na yi, amma kafin ka ce haka, yarinya ta bace a cikin sararin samaniya aka daina ganin ta.

Labarin bakin ciki da Bacin rai kuma dai ba sai an tona ba. Surutai suka cika gari iri-iri, wasu na cewa ai yarinyar Kashin tsiya gare ta ba ta da sa’a ne, wasu kuma cewa suke yi ai kyanta ya yi yawa ne, shi ya sa aljanu za su aure ta. Maganganu dai ba kai ba gindi.

A karshe dai Sarki ne ya yi ta rarrashin Bashari da Sarkin Fulani a kan cewan Allah Ya so yadda aka ga yarinyar da farko haka ma za a sake ganin ta. Aka yi ta addu’ar Allah Ya bayyana ta tare da tona asirin

wancan aljani mai sace ya ‘yan mutane. Yanzu kam tafiya zuwa Kasar Arewa ta tashi daga matsayin rakiya a wurin Bashari ta zama ta dole. Aka Kara musu runduna ta mutum dubu suka  nausa,

A kwanaa tashi cikin wata uku da kwana goma sha bakwai suka isa kusa da gari, suka aike wa Sarkin Kasar cewa su bakinsa ne, kuma ga su nan Karasowa.

Kasancewar Wazirinsa ba ya nan ya tafi rangadi, sai aka turo wasu manyan hakimai suka tarbe su aka sauke su a gidan saukar manyan baki na Sarki. Su kuma tawagarsu suka yi tantuna a wajen gari, aka aike musu da shanu da awaki da sauran kayan abinci da na sha don su huta sosai.

Bayan dan Sarki Bashari da abokinsa sun kintsa, sai suka tafi fada don yin gaisuwa, Sarki ya tarbe su cikin mutunci da girmamawa.

Kowannen su ya labarta wa Sarki labarinsa tare da cewa abin da ke tafe da su shi ne don su sami labarin wancan aljani wanda aka ce a wurinsa ne kawai za su
samu don shi ma hakan ta faru ga tasa ‘yar.

Hawaye suka shiga gangarowa daga idanun Sarki shar-shar har sai da suka rude suna mamakin abin da zai sa dattijo kamar wannan kuka. Sai ya ce musu, ) “Ya ku ‘ya’yana, kun fama mini ciwon da ke cikin zuciyata ne, amma fa ba na ce kun yi laifi ba ne, don kuwa matambayi ba ya bata. Kuma gaskiya ne kamar yadda kuka sami labari cewa ni ma ‘yata tana can wurin wannan aljani ya sace ta. Allah dai Ya karya
Www.bankinhausanovels.com.ng Sarkin aljanu Sham’una!” Nan Sarki ya kasa mallakar kansa, ya sake barkewa da kuka su kuma suka rika ba shi hakuri har sai da hankalinsa ya dawo tukuna. Daga nan sai yace musu, “Ku koma masaukinku, in Allah Ya so yau Wazirina zai dawo, shi ne zai ba ku cikakken labarin wannan maridi.”

Suka yi sallama suka fita suna tausaya masa. Suka je bayan gari wurin jama’arsu, kowanne ya warware ‘yan matsalolin da suka taso, sannan da yammaci suka koma masaukinsu. Shigowar su gari sai suka ji gari ya rude da sowa da murna, da suka tambaya sai aka shaida musu cewa Wazirin gari ne ya dawo lafiya daga rangadi.

Waziri ya shiga wurin Sarki ya yi gaisuwa. Bayan sun gama ganawa sai Sarki ya ce, “Waziri muna fa da bakin wasu ‘yan Sarki su biyu, sun zo ne don neman bayanin mugun aljanin nan da ya sace mana ‘ya. Su ma hakan ce ta faru gare su, saboda haka gobe in Allah Ya kai mu sai a shirya liyafa, ka yi hira da su don na ga samari ne tsarorin ka.”

Waziri ya ce, , Allah Ya taimaki Sarki.”

Da gari ya waye, dan Sarki Bashari da abokinsa yarima Amir suka nufi fada suka yi gaisuwa, suka koma gefe suna ta ‘yar tattaunawa. Can sai ga Waziri
Www.bankinhausanovels.com.ng
ya zo don yin gaisuwa. Sarki ya gabatar da Wazirinsa ga ‘yan Sarki, ai Waziri na waigawa don gaisawa da su sai kawai suka yi ido hudu da Bashari sai ya ce, “Bashari.”

Bashari ya ce, “Na’am, Habu.”

Sai suka rungume juna cike da farin ciki. Waziri ya labarta wa Sarki cewa wannan dan’uwansa ne wanda suka fito neman ilmi tare da shi. Ana cikin haka sai ga wani sakon ya shigo fada cewa ga wasu bakin nan sun zo, Waziri ya sa Madaki ya je ya tarbo su, suka shigo suka yi gaisuwa, kuma ga alama su ma neman labarin ne ke tafe da su. Sai jagoran bakin ya ce, “Don Allah Bashari ne da Habu ko kuwa idanuna ne ke yi mini gizo?”

Waziri Habu ya ce, “Ba gizo ba ne, gaskiya ne idonka ya nuna maka Yahaya.”

Bayan duk an kammala gabatar da juna, sai Sarkiya ce, “Lallai yau babbar rana ce a gare mu, saboda haka a buga tambari akwai Kasaitacciyar walima.”

Sarki ya gode musu sannan ya alKawarta musu cewa matukar dai Allah Ya fitar da wadancan ‘yan mata daga hannun Sham’una, to zai halarci garin kowannensu don a yi biki da shi.”

Ran nan ba su yi barci ba, haka suka zauna suna ta hira. Waziri Habu yana labarta musu abin da ya sani

Www.bankinhausanovels.com.ng game da aljani Sham’‘una da irin Karfinsa da kuma cewa tunkarar wannan aljani ba nasu ba ne, sai dai su yi ta addu’ar Allah Ya bai wa dan’uwansu Idrisu nasara a kan haka.

Kowannen su ya gamsu. Sarki ya umurci Waziri Habu da ya yi musu rakiya don komawa garuruwansu.

Yanzu kam kallo ya koma sama, kowa nasarar jarumi Idrisu ya ke saurare. Don dole sai dai a ce saurare din, ko kuma zato, don qalubalen ba gama garibane…

LOKACIN da Sarki Zulkiflu da Wazirinsa Habu suka sauke jarumi Idrisu dan Hamidu a gabar teku sai ya shige cikin dajin da ke gabansa ya ci gaba da ketawa, kuma kasancewar irin wannan tafiya ba bakuwarsa ba ce, sai abin ya zo masa da dan sauki.

In ya gaji sai ya saki Jagora shi kuma ya nemi wuri ya huta, bai tsayawa ko ina sai dai in akwai matukar bukatuwa zuwa ga hakan. Yi ya ke ta yi ba dare ba rana har ya iso bakin wani Katon kogi.

Babu hanyar hayewa, kuma ba wasu manyan itatuwa ballantana ya dan sassaka jirgin da zai iya daukarsa shi da dokinsa, saboda haka sai ya karkata dama ya yi ta tafiya ta gefen rafin har na misalin yini sannan ya yi sa’a ya iso wata gaba wadda a kusa da ita akwai wani dan Kauye, kuma abin kamar an shirya aka dace jirgin ruwan da kan zo sau daya a kowane mako don ketarewa da jama’‘a zuwa daya gabar ya iso. A cikin wannan dare masu jirgi suka ce za su juya,

Www.bankinhausanovels.com.ng Idrisu ya yi cinikin Ketarewa da shi da dokinsa, aka daidaita suka shiga aka mika, a haka suka yi ta yi har sai da suka yi tafiyar kwana uku sannan suka iso wani tsibirl mai matukar ban sha’awa. Ko ina a tsibirin ciyawa ce kake gani koriya shar ko kuma ka ga wani irin yashi fari sal, ga itatuwan dabino da inabi ko ina barjak, kan hanya ko ina ka duba sai inuwa linkim, don itatuwa ne ta kowane gefe suke sa kowace hanya a tsakiya. Tsuntsaye launi daban-daban kowanne da irin kukan gidansu.

Wata irin iska mai sanyin dadi da ke kewayawa a tsibirin dole ne a ambace ta musamman irin yadda kowane lokaci take hadewa da Kanshin da kan fito daga furannin da ke kofar kowane gida suna ba da gudummawar wani irin tabbaci na natsuwa da cikakkiyar lafiya ga duk wanda ya tsinci kansa a yankin.

Yawancin abincin mutanen wurin ‘ya’yan itatuwa ne wadanda suke da su, sai kuma zuma, nono da cukui da ake kawo musu. Allah Ya yi musu arzikin ma‘adinaina KarKashin Kasa da kuma na gefen ruwa.

Wani babban abin ban sha’awa game da tsibirin shi ne mutanensa, masu kyawawan halaye, girmama juna, kula da addini da kuma son baki, kowanne ka gani babba da yaro, mace da namiji ta bangaren ilmin
Www.bankinhausanovels.com.ng addini sai abin ya ba ka mamaki.
Sai dai kash, akwai wani abu da ke matukar damun su a tsibirin. Wato wani irin dodo ne, shi ba mutum ba shi kuma ba dabba ba. Kansa kawai ya kai girman akawalin doki, kuma yana da idanu hudu, daya a goshi, daya a keya, daya a kasan kunnensa na dama dayan kuma a saman kunnensa na hagu. Kowane kunne ya fi matsakaiciyar tabarma fadi kuma yana da bakuna guda biyu, daya a baya dayan kuma a gaba, kuma kowane baki zai iya hadiye Kato komai girmansa.

Wannan dodo dai yana da hannaye guda hudu wanda kowanne yana iya daukar babban dutse da shi, kafafuwansa kuwa kamar wasu manyan itatuwan rimi, cikin sa Kato wanda ko da wasa ba za a iya misaltawa da na toron giwa ba. Jikinsa kuma rabi da gashi daya rabin kuma babu, sannan yana wani irin doyi mai tsananin tayar da hankali. Ba kananan dabbobi irinsu kaji, talo-talo da awaki ba, kai hatta dawaki da rakuma in suka ji doyinsa ba duka ne suke rayuwa ba.
A dabi’a, a duk shekara wannan dodo kan fito daga cikin ruwan rataye da wani irin akurki mai girman katon gida, ya yi ta farautar mutane yana jefawa a ciki sai ya cika shi taf da mutane sannan zai juya ya nufi

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *