WA NAKE SO CHAPTER 17

 WA NAKE SO CHAPTER 17

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Shiru Aisha tayi. Abbah yace

“Aisha tashi ku shiga.”

Mikewa tayi gaban ta na faduwa tana tunanin tayaya zata shiga bandaki tare da mutumin da ba muharammin ta ba. Akan keken suka daura shi ya kara kama hannun ta yana kallon ta sannan nurse ta fara turawa a haka suka karasa bandakin.+

Katon bandaki ne wanda yake da sink da bath sai labule da ya raba wajen daya bangaren wajen shit. Ciki suka shiga dashi suka fara cire masa riga ido ta runtse. Daya ya fara hada masa ruwan wankan daya ya dauki tooth brush din sa ya saka masa toothpaste.

“Gashi!”

Nurse din ya fadawa Aisha. Ido ta bude taga yana miko mata brush din sa amsa tayi ta dago ta ganshi zaune da gajeren wando da singlet iso ta runtse da sauri ta mika masa amsa yayi yana kallon ta wani nurse ya matsa dashi ya wanke bakin sa sannan ya saka shi a cikin bath din juyawa tayi zata fita yace

“Aysherrrr!

wani irin yar taji a jikin ta wanda yasa ta saurin tsayawa bata juyo ba yace

“Dan Allah kada ki tafi ki barni!”

Shiru tayi yace

“Dan Allah!”

Juyawa Nurse din yai dan dauka soso ya girgiza masa kai yace

“jeka zan iya!”

Juyawa yayi ya fita. Aisha na tsaye ta juya masa baya ya fara wankan bai jima ba ya gama ya dauki towel ya goge jikin sa sabida yadda bai jin gwarin jikin sa yasa bayan ya gama ya koma kan kujerar ya zauna yana sauke numfashi.

“My cloth!”

Ya fada nan nurses din suka karaso suka shigo suka fito dashi suna zuwa inda Aisha take ya kamo hannun ta tare suka fito suka shiga dressing room din dakin. Kaya ya kasa idon ta a runtse sannan suka fito dashi hannun sa rike da na Aisha.

Akan gadon suka zaunar dashi sannan nurse din ya dauki abinci dan ya bashi amman ya make kafada kamar karamin yaro. Kallon Aisha kawai yake yi. Nurse din ta karaso tace

“Ko zaki bashi naga yana ta kallon ki.”

Dagowa tayi ai kuwa suka hada ido da sauri ta dauke kan ta ta amshi kwanon ta karasa gaban sa. Kamar mai counting words tace

“Bismillah kaji Yaya na!”

Baki ya bude ta fara bashi tea din sannan ta bashi fate dankalin da hanta da akayi shi yai ruwa ruwa. Sosai yaci ya gama ta goge masa baki sannan ta bashi magani ya sha. Abba ne ya shigo ya kalli Aishan yace

” kinyi sallah ne?”

Kai ta girgiza yace

“To kije kiyi kiji!”

Zata tafi Aliyu ya kamo hannun ta. Abbah yace

“Ka bari tayi sallah mana.”

“Abbah guduwa zatayi wallahi ta saba tazo ta gudu in na sake ta gubuwa zatayi, in ta tafi guduwa zatayi ta sabai min haka.”

“Ba zata gudu ba.”

“Abbah jiya ma fa haka muka da tazo sai ta gudu dan Allah Abbah ka bari ni ba zata tafi ba.”

“Haba Aliyu Sallah fa zatayi ba zata gudu ba jiya da ka ganta a mafarki ne yau kuma a zahiri ne in ta gudu ni nai maka alkawarin dawo maka da ita ka kyale ta taje tayi alwala tazo tai sallah kaji.”

Dagowa yayi yana kallon ta sai yace

“Aysher!”

Dagowa tayi ta kalle shi idon ta cike da hawaye yace

“Please promise me u will not run away!”

“I promise you!”

Sakin ta yayi yana sakin wani murmushi na musamman. Janye hannun tayi ta nufi bandaki ya bita da kallo. Abbah ya zauna a kujerar dake gefen sa yace

“Aliyu!”

STORY CONTINUES BELOW

Dagowa yayi yace

”Jiya naje garin su Aisha daga can na taho da ita da Yayan ta. Ajiyan muka nema maka auren ta kuma aka baka ita.”

A zabure ya dago yana kallon Abbah.

*

*

Yaa Muhammad da Faisal ne suka shigo dakin Mamah tace

“Ku shiga ya farka ma.”

Sukai dakin.

*

Abbah yace

“Ajiyan aka daura auren ku yanzu Aisha matar kace.”

Kai ya hau girgizawa yace

“Abbah da sanin ta akai hakan ko kuwa?”

“Bata sani ba Yayan ta da Iyayen ta ne suka yadda aka daura muku aure.”

“Abbah kuna nufin auren Dole kukawa Aysher!”

Su Faisal ne suka shigo. Yaa Muhammad ce

“Ko kadan ba auren dole mukaiwa Aisha ba domin kuwa Aisha na son ka ko su Umma da Baba sun sani ni shaida ne akan son da Aisha take maka tana maka son da batawa kowa a duniyar nan taki ka ne danni kuma dan alkawarin da mukai amman Aisha na son ka kuma na tabbata in ta san an daura muku aure zata yadda ta amshe ka dan gaka ka daina fadin auren dole akai maka.”

Hannu ya mika masa Yaa Muhammad ya karaso ya zauna a gefen gadon yace

“Ya jikin?”

“Da sauki! amman Muhammad wallahi ban san su Abbah zasu zo ba da sam ba zan yadda ba,  ina son Aysher amman ina maka kwadayin ta dan me ka yadda aka bani Aysher?”

“Saboda tana son ka,  kuma kaima kana son ta har ka yadda ka sadaukar da farin cikin ka dan ita wannan wacce irin soyayya ce,  ni dan uwan tane na jini wanda duk abinda Aisha take so dole naso shi dan me ba zan so ka ba dan me ba zan baka Aisha ba dan samuwar lafiyar ka da cikar burin ka. Kai mutum ne wanda in akai rashin sa anyi babban rashi ko dan amanar ka da gaskiyar ka. Ka fini bulatar Aisha ka fini cancanca ga Aisha ga Aisha nan na baka ita amana ka rike min ‘kwanwa da amana.”

“Wane irin mutane na hadu dasu haka a rayuwa,  mutanen da basu da son kansu sun fi son su sa wani farin ciki da annushuwa sun fi son kyautatawa wani akan su. Shin wane irin mutane wadan nan hakika ban taba haduwa da zuri’a masu karamcin ku da dakkatako da son wasu akan kan su ba sai ku. Muhammad da gaske ka bar min Aysher! Yanzu Aysher tawa ce?”

Kai ya daga masa. Yace

“Da gaske Aisha taka ce Aliyu. Aisha ta zama ta Aliyu dan haka ka kwantar da hankalin ka Aisha ta zama taka yanzu ba mai iko da ita sama da kai.”

Gabas ya kalla yayi sujudul shukur yana idar wa ya rungume Muhammad yana fadin

“Dame zan saka ma dame zan saka maka Muhammad ka min abinda ba a tabai min ba ka min abinda bantaba zata ba ka min kyauta da abinda ban san dame zan maka tukuwici ba ka min kyauta da abu mafi daraja a gun ka dani ka ban farin ciki na Muhammad you deserve more than anything i mean anything Muhammad.”

Aisha da ta fito daga bandaki ta kalle su sai kawai ta fuce adakin. Acan falo ta tada sallah tana idar wa ta hade kai da gwiwa dan yadda kan ta ke ciwo ta rasa wane irin ciwon kai ne wannan da yaki barin ta. Ko dan tafiyar da sukayi ne da abincin da bata ci bane.

Dagowa Aliyu yayi ya kalli Faisal yace

“Friend zo ka tayani godiya.”

Ya kamo hannun sa. Ya kalli Abbah yace

“Abbah kaima ka tayani godiya.”

Sai kuma ya fara hawaye Muhammad ya kalla yace

“Da wane kalmomi zan maka godiya? Shin da wanne kalmomi zan maka godiya ban dasu ban san sa wane kalmomi da baki zan maka godiya ba sai dai zan kasance cikin maka a ddu’a a duniya har karshen rayuwa ta Allah ya saka maka da mafificin alheri Allah kaima ya baka mai son ka wacce tafi Aysher Allah ya sa ka gama da duniya lafiya ya biya maka bukatun ka na alheri ya shige maka gaba ya raba ka da iyayen ka lafiya ya sada ka duk alheran duniya yadda ka faranta min Allah faranta maka.”

Sai ya fashe da kuka yana fadin

“Wallahi na rasa tayaya zan saka maka na rasa tayaya zan maka godiya addu’ar da nake maka tayi kadan Muhammad!”

“Ka bar kuka dan Allah ka sani nafi bukatar addu’ar akan komai kuma naji dadin Addu’ar ka ina godiya Allah ya baku zaman lafiya ya sanya alheri fatan alheri gareku. Ba na baka Aisha dan kai min godiya ko wani abu ba na baka Aisha ne dan Allah dan kuma rabon ka ce dan Allah kabar kukan ba kaga a halin da kake ba.”

Ya fada yana share masa hawaye.

STORY CONTINUES BELOW

“Kukan farin cikine Muhammad.”

“Change it with a special smile please!”

Hawaye na zuba a idon sa ya fara murmushin sa mai kyau da narkar da zuciyar duk wanda ya kalle hhi.

Muhamma a zuciyar sa fadi yake

“Lallai Aisha tayi dacen abokin rayuwa da iyayen miji mutane ne masu karamci duk arziki su da mulkin su suna da dattako dan haka yana mata murna sosai yanzu yasan burukan ta da yawa zasu ciki a rayuwar ta yaji dadi sosai da ya kasance ya sada ta da cikar burin ta.

Kokarin sauka ya farayi Muhammad ya kama sa yace

“Ina zaka?”

“Zanje naga Aysher!”

Zaunar dashi yayi yace

“Bari a kira maka ita.”

Abbah mikewa yayi ya fita. Yaa Muhammad yabi bayan sa.

*

**

***

****

*****

******

*******

Since daga nan Aslam da Fateema suka kule domin yadda yake kula da ita kiran safe daban na rana daban haka nan yaje office ya tayata zama ko su dan fita kan tai bacci sai yai mata gud nyt wannan ya kara musu shakuwa sosai a tsakanin su dan wani bai zama bai kira wani ba duk da in sun zauna majority tana bashi labarin Fu’ad ne sometimes kuma in yana abu tace

“You act like My Fu’ad!”

Wannan yake sakawa yake burgeta dan sanyin halin su iri daya ne da Fu’ad a wasu dabi’un kuma kamar Fauwaz shima in yana yaba ta in ta saka Hijab sai ta tsaya kallon sa kawai. Sometimes ma sai ya mata tafi a fuska take dawowa hankalin ta in ya tambaya tace ba komai in ya dame ta ne sai tace

“Ka tina min da Yaa Fauwaz ne.”

Dan haka zaman ta dashi ba laramin tino mata da wadan nan mutane biyu masu mahimmanci a rayuwa yake ba. Shima kuma duk ta yadda zai tusa kai a gunta yana yin sa.

A haka suka kwashi sati uku tare wannan weekend din suna Falo ita da Momy wayar ta tai kara tana dubawa ta saki murmushi tace

“Momy ga Uncle fa.”

Hararar ta Momy tayi. Dagawa tayi ta kai kunne tace

“Ka yini lafiya Uncle?”

“Alhamdulillah!”

“How was d weekend!”

“So lonellly!”

“Why?”

“Saboda ban ganki ba if am not with you am feeling like….”

Mikewa tayi ta nufi kofar fita a falon Momy ta bita da kallo.

Murmushi tayi tace

“U are just joking Uncle kai da kake da mata agefe go to her and enjoy your life!”

“Seriously my mood is just so confused,  i don’t know if am sad, happy, lonely,  bored or what ever. Fateema i just want to see you ko na samu naji dadi dan na gane missing naki ke dawainiyya dani. Kinga yau sai na gaishe da Momy ko?”

Shiru tayi yace

“Please my sister!”

“Alright!”.

“Nazo din?”

“Eh!”

“Ok thanks!”

Ya kashe wayar. Mikewa yayi ya shiga daki yai wanka ya fito ya hau shiryawa yana cikin shiryawa Jidda ta shigo ta bishi da kallo.

Sai da ya saka kaya ya tsaka hula ya fesa turare ya juyo yana kallo ta yace

“Kallon fa?”

“Kayi kyau My love!”

“Thank you!”

“But My love  ka canja da yawa why? Yanzu ina zaka je?”

“Wane canjin nayi wife?”

“Da da yamma kake dawowa amman yanzu sai after magrib fa”

“But i told you aiki ke tsayar dani ko?”

“But mostly weekend is my day amman yanzu ina zaka ka yi wanna kwalliyar!”

Hancin ta yaja yace

“My wife kenan uwar kiga a gidan Aslam,  zani gun kanwar ki!”

“What?”

“Please Jidda kar ki sa damuwa i told you since ni mijin ace hudu ne so ki dauki kaddarar ki a yadda tazo miki.”

“Amman dai tsokana ta kake ko?”

“Duk yadda kuka dauka.”

STORY CONTINUES BELOW

“Haba Aslam ka tsaya muyi maganar fahimta mana.”

“Am all ears!”

“Please ina zaka inzo in rakaka?”

Ido ya zaro yace

“Zancen zaki rakani.”

Tai murmushi tace

“kamar ya zance!”

“Nace zani gun kanwar ki my new wife to be insha Allah.”

A zabure ta mike tace

“Wai da gaske kake?”

Kamo hannun ta yayi yace

“Yes dear dan haka ki soma shiri.”

Ya mike yace

“Sai na dawo i love you!”

Tana zaune bata san ma me yake fadi ba sai jin karar tashin motar sa tayi a guje ta fito amman kan ta fito parlour ya bar gidan gaba daya.

Daki ta koma ta fashe da kuka tana fadin

“Na shiga uku yau Aslam aure zai yi ina bazan iya ba kishiya wallahi bazata sabu ba.”

Waya ta dauka ta kira Sadiya tana kuka tana dauka tace

“Lafiya Jidda?”

“Ina fa lafiya Sady Aslam aure zai kara!”

“Kamar ya aure zai kara?”

“Yanzu fa yaci kwalliya ya fita wai ya tafi zance!”

Tsaki Sadiya ta saki tace

“Daga yaje zance shine sai aure.”

“Kinsan Halin sa fa ko mata bai kalla tinda ya fadai hakan da gaske yake ni yanzu yaya zanyi?”

“Haba Jidda wai ke kamar ba mace ba menene dan an miki kishiya kina gani ni gidan mai mata zan shiga ni hanani shiga tayi kuma for godsake menene a ciki dan an miki kishiya mijin ki na son ki kema mace ce everything she has kina dashi sai ku hau fafatawa wajen faranta masa shine kadai kishin da zakiyi ki nuna masa kulawa fiye datata shawara fa kenan ki kwantar da hankalin ke ko banza kece uwar gida kuma sai yadda kikai amman fa in kin kwantar da hankalin ki.”

“Wai meyasa Sady ke kullum bakya bani shawara masu kyau sai na gargajiya haba wane in zauna ai min kishiya ai macen da ta isa ba ai mata kishiya kina so ace ni ban isa ba kenan please ki samon mafita.

“Mafita daya ce ki dauki kaddara ki dage da Addu’a Allah sanya alheri ke kuma Allah baki hakuri ya kara sonki a zuciyar mijin ki. In anyi auren Allah baku zaman lafiya ya kade fitina sannan ki……”

Katse wayar tayi tana sakin tsaki ta fara kiran layin Khady. Tana dauka tace

“Besty am confused ina cike da damuwa yaya zanyi.”

“Cool down my dear what wrong?”

“Wai Aslam aure zai yi?”

“Yaushe kuma?”

“Ni ban sani ba yanzu dai ya tafi zance.”

Dariya tayi tace

“Yanzu me kike so?”

“Ni bana son yayi auren”

“An gama ki jirani zuwa gobe amman fa ki kwantar da hankalin ki dan banson damuwar ki”

“To amma ki samon mafita mai kyau.”

“Baki da matsala;”

“Thanks;”

Ta fada tana kashe wayar sake sake take a ranta ina ma taga yarinyar nan wallahi da ta lakada mata na jaki. Haka ta dinga safa da marwa. Ta rasa nutsuwar tagaba daya

*

Yana fita ya tsaya yai shopping a wani mall sannan ya wuce gidan su Fateema horn yayi mai gadi ya bude masa yai parking sannan ya fara dailing numberta. Ringing daya,  biyu ta dauka

“Am outside Dr!”

“Ok gani nan”

Ta fada ta kashe wayar. Hijab ta dauka ta saka akan dogon bakin siket din dake jikin ta da riga bodyhuge mai sogon hannu. Blue black ne sai yai mata kyau ya kara mata haske ba kwalliya a face din ta daga hoda sai man lebe sai kamshi take mai sanyi.

Tinda ta fito yake binta da kallo tin daga kafar ta dake sanye da wani black flat shoe wanda yai mata kyau tafiyar ta ma abar kalla ce mai kyau da burgewa. Har ta karaso bai sani ba sai da ta tafa hannayen ta sanna  ya dawo daga duniyar da ya tafi.

“Ya dai?”

Ta fada tana dage masa gira. Murnushi kawai yayi ya dan shafo kyewar sa yace

“Barka da fitowa.”

“Yauwah ka zo lafiya?”

“Alhamdulillah. Ya Momy na? Ko da yake kaini na gaishe ta first!”

STORY CONTINUES BELOW

Murmushi tayi tace

“To muje.”

Tayi gaba yana bin bayan ta bayan ya dauko ledar da yazo a da ita a mota.

A falo ta nuna masa kujera tace

“Bismillah let me call her!”

Tana fadar haka tayi sama dakin Mony ta shiga ta tsaya daga bakin kofa tana jin wani iri na yadda zata fada mata Aslam yazo zasu gaisa.

“Lafiya ya zo ne?”

Kai ta gyada tayi kasa da kai tace

“Wai so yake ku gaisa yana falo”

Murmushi Momy tayi ta saka Hijab tace

“Muje to “

Suka sauko a tare kitchen fateema tayi shi kuma yana ganin Momy ya sauka akan kujera ya zube a kasa kan sa a kasa ya fara gaishe ta cikin girmamawa. Momy tace ya koma amman yaki a haka suka gaisa tana tambayar ya gida da Hajiyar sa da Iyalai.

Fateema ce ta fito rike da Tray da lemo da ruwa sai cup a kai. Ajiyewa tayi Momy ta mike tace

“Madallah!”

Sannan ta nufi falon sama. Fateema ta kalle shi yace

“To ai ta tafi ka koma ka zauna.”

Dagowa yayi ya kalle ta yana mata kallon zaki sanine dan yadda take masa dariya. Ya koma ya zauna yace

“Wannan weekend din sai naga kin kara kyau.”

“Kai kenan maganar ka Uncle ni ina Anty na ai nazata tare zaku zo.”

“Tace in gaishe watarana zata zo ai.”

“Ya weekend?”

“Before so lonely but now greatful!”

“Hmmm ka fiya abinda dariya Uncle. Ina su Jannah da Nur?”

“Suna gun Mami na. Suna cinye min kayan dadi.”

“Kai kana gidan ka kana ci menene dan sunci naka.”

“To ba auta bane ni.”

Ya fada a shagwabe. Sai ya bata dariya tace

“Kai Uncle!”

“Eh mana.”

“Jidda na fama da shawagabar ka fa”

“Kemaki saba tin yanzu.”

“A’ah ni ai nayi a baya ta My Fu’ad amman yanzu ba zan iya ba.”

Take mood din ta ya sauya. Dan haka yace

“No please continue wit your smile dear shi Yaa Fauwaz fa Fisrt,  middle or last born?”

“First born ne like me.”

“Ayyah ai kam zakina shan shagawabar auta a gun Fu’ad ba.”

“Hmmm gaskiya amman abin sa yana burge bi. I love him i will always an forever love him.”

Shiru Aslam yayi yana kallon ta da tausayin kan sa da ita.

Murmushi tayi tace

“Fu’ad yayi a rayuwa he is simple and special in all his attittude and behavour.”

“Allah sarki!”

Kofar falo aka budo tare akai sallama da sauri ta mike tana fadin

“Baba!”

Sai ta nufi kofa aguje ta fada jikin Baba tana fadin

“Oyoyo Baba Uwani na.”

“Zaki yardani Fateema.”

Sai kuma ta sake ta suka rumgume juna ita da Yasmeen. Mai aikin su ne ya shigo da kayan su nan Falo sannan ya juya. Baba tai ciki tana fadin

“Aikin kenan kamar wanda suka shekara basu ga juna ba.”

Fateema ta juyo tana fadin

“Baba bakiyi missing nawa ba.”

“Menene mitsin kuma?”

Aslam yai murmushi ya sauka akan kujera yana gaishe ta. Ta kalle shi tana amsa da sakin fuska tana fadin

“Wajen wa kazo?”

Fateema tace

“Gunki!”

“Oh zance kazo guna ko an fada maka zan dawo kazo kwasar gaisuwa wato bazata akai min Alhamdulillah yau Fateema ta kawon Miji gida nagode Allah. Allah yasa alheri yasa ayi damu.”

Fateema da Yasmeen sunyi sama bata san me Baba take fadi ba.

Aslam kuwa kan sa a kasa yake amsawa da Amin. Baba tace

“Ni ba son a ja abu da dadewa dan yanzu an daina wannan mu ba yara bane muna da rufin asiri ko yau ka shirya kazo kaje gun kawun ta ayi abunda za ayi kawai ai ta zaunu da ta zauna zaman jiran wani Fu’ad bayan shi Fu’ad din fa ba aure a tsakanin su sai uku yai mata ba gwara ta kama miji ba itama ta sani ko yana can yai auren sa shima.”

“Haka ne Baba.”

“To Allah ya sanya alheri ya sa ayi damu.”

“Amin Baba!”

“Bari na shiga ciki na watsa ruwa na dan huta”

“A fito lafiya Baba!”

Ya fada ya koma ya zauna Baba ta shige daki.

Tare suka sakko Momy da Fateema da Yasmeen sukai dakin Baba. suna shiga Fateema ta fito. Ya mike yana fadin

“Ban taba ganin ki kina farin ciki kamar yau ba am so happy.”

Tai murmushi tace

“Ya naga ka tashi.”

“Zan tafi na arawa Baba ke ki kula min da amarya ta ga wannan ba yawa a bawa Momy ita kuma Baba zan zo na musaman dan na samu amarya.”

“Tab zama ka sake ta ne inda baba ce. Amman gaskiya kada ka kuma ai wahala ne wannan.”

“Menene wahalar dan nayiwa Momyn mu abu.”

“Kada ka kuma!”

“Banyi alkawari ba.”

“In dai haka ne bana son ka kara zuwa to.”

“Ai kuwa naga waje ni.”

Suka fita tana murmushi yana isa motar tace

“To angode ka gaida gida da Madam.”

“Zataji Doctor nagode.”

Ya shiga ya tayar ya fita tana daga masa hanni.Washe gari kamar yadda Khady tace zataje gidan Jidda da rana ta isa. Ta same ta duk a hargitse. Zama tayi tace

“Jidda amma nace ki nutsu kar kisa damuwa ko?”

“Na kasa Khady hankalina ya tashi jiya fa da ya dawo har da cewa tana gaishe ni da gaske fa yake ya zanyi Khady kina ganin ban haihu ba ai bora zan zama bama da ta shigo ta haihu.”

Tsaki Khady ta daki tace

“In ta shigo din kenan. Ki barmin komai a hannu na zanje gidan su yarinyar kawai ki samo mana address din ta in hakan baiyi ba shima zamu samo wata hanyar ko ta malamai ne sai an raba su ba zai aure ta ba.”

Rumgume Khady tayi tace

“In kikai min haka kuwa kin min komai Besty!”

“Kada ki damu damuwar ki tawa ce.”

“Thank you shiyasa nake som amman Sady ko?”

“Bana ce ki daina fada mata abubuwan ki ba. Ba son ki take ba wallahi.”

Dariya tayi tace

“Nagane Besty ita kullum tace kai hakuri ta ina bazan iya ba.”

“Yauwah yanzu ki shige masa ki gano inda yarinyar take kinji?”

“Ok!”

Ta mike tace

“Zani unguwa zamu hadu da Najah ma xan mata maganar naji me zata ce ita ma nasan tana da hanyar .”

“Nagode Khady har naji dadi da nutsuwa ta,”

“Kar ki damu!”

Ta mike ta rako ta kofa sukai sallama sannan ta koma ta hau gyaran gidan da komai. Ta gama ta daura girkin da tasan Aslam Yafiso.

*

Sai dare ya dawo yana dawowa ta amshe shi cikin kulawa shi kansa yayi mamaki yadda ta kula dashi dan da safe ko magana batai masa ba haka ta dinga bashi kulawa sam bata nuna masa tana son jin zancen wata wacce yake so ba sai rayuwar su da suka cigaba da yi cikin kwanciyar hankali.

Haka lokaci ya dinga tafiya dan sosai Aslam da Fateema suka shaku yana zuwa gida su gaisa amman yawanci iya karasa waje sai yace zai gaida Momy ko Baba take kai shi.

Saturday

Yau ta fita wani meeting da aka gayyace su duk ma’aikaya private hospital wanda suke mamalakin su sam ta manta bata fadawa Aslam ba dan haka shi kuma da yamma kawai ya nufi gidan.

A compound yasamu Baba tana zaune parking yayi ya fito ya durkusa ya gaishe ta. Ta amsa tace ya zauna da kyar ya zauna akan kujerar sannan yace

“Fateema tana ciki ne?”

“Au bata fada maka ba ai yau tin safe ta fita tana can gun aiki. Ni kam Aslam ba zaka fito kuyi auren nan kowa ya huta ba ka tsaya sai biyewa shirmen Fateema kake yi.”

Kai ya sosa yace

“Baba ni a shirye nake Fateema ce dai.”

“Ita ta hanaka ko?”

“A’ah!”

“To ka kyale ni da ita zanyiwa Kawun ta magana duk yadda mukai zan fada maka.”

“Nagode Baba Allah kara girma.”

“Amin Amin.”

Ya mike ya ajiye mata kudi masu yawa yace

“Ni za tafi Baba nagode.

“To nagode ka gaida gida da iyali.”

“Zasu ji.”

Ya shiga mota yana jin wani sanyi domin yasan ya kusan samun Fateema ko a yadda ta sake dashi yasan a yanzu ba zata ki sa ba.

Yana komawa Gida Jidda ta tare shi tana fadin

“Honey ba dai daga wajen kanwata kake ba har ka dawo.”

STORY CONTINUES BELOW

“Wallahi bata nan ne!”

“Ina taje?”

“Aiki ta tafi.”

“Ayyah wai a wacce unguwar take ne?”

Kallon ta yayi ya saki murmushi tace

“Wai dan mu sada zumunci”

“In ta shigo kwayi.”

Ya mike ya shige dakin sa. Da kallo ta bisa tana mamaki dan Aslam akwai basira baka fiya jin cikin sa ba ko samun information da bai shafe ka ba.

Mikewa tayi ta shiga daki. Waya ta dauka ta fara kiran Khady. Tana dauka tace

“Khady anya kuwa Aslam zai fada min wacece yarinyar nan.”

Ki kara trying in bai fada ba masan abinyi ma.”

“Shikenan!”

Ta mike ta koma dakin sa akan gado ta same shi kare da waya a kunnan sa tana shigowa ya katse wayar yana kallon ta. Tace

“Honey abinci fa.”

“No ki kawon lemo kawai.”

“Amman baka ci abinci fa gashi kace kaje bata nan da sai nace acan kaci.”

Yai murmushi kawai yana kallon Jidda tace

“Please love.”

“Zanci zuwa anjima yanzu dai kawon lemon.”

“Ok;”

Ta fada ta mike ta fita. Ya bita da kallo kawai.

*

Baba Uwani ce zaune a gun Uncle Aminu, bayan sun gaisa tace

“Daman batun wannan yaron da yake neman Fateema ne.”

“To masha Allah Fateema ta tsayar da miji yanzu kenan?”

“Eh amman ta tsaya tana ta ja masa rai.”

“Ah to yazo kawai in dai sun dai dai ta ayi komai a gama ko kuwa?”

“Yauwah Aminu abinda nake so kenan da yazo ya turo magabata a tsayar da komai dan Allah ni bana son a sa lokaci da yawa.”

“Insha Allah Baba.”

“Yauwah Allah yayi albarka.”

“Amin Baba nagode!”

“Allah ya jikan dan uwanka Umar!”

“Amin Baba!”

Ta mike tace

“Bari na tafi sai anjima zan fada masa.”

Mikewa yayi ya tako mata har bakin gate sannan ta wuce ta koma can gidan.

*

8:00pm Fateema tafito daga dakin ta sanye da doguwar riga marar nauyi kan ta sanye da hula. Baba ta kalla tace

“Sannu da gida Baba!”

“Yauwah Fateema ya aiki?”

“Alhamduliah!”

Ta fada tana isa dining ta zuba abinci ta faraci. Bayan ta gama ta dawo Falo Baba tace

“Ina wannan yaron dake zuwa wajen ki?”

“Oh Aslam?”

“Eh shi in kunyi waya ki fada masa ina neman sa.”

“Lafiya dai ko Baba?”

“Lafiya kalou.”

Sallama akayi suka dago gaba dayan su suna kallon Suraiyya da Yaa Kamal da suka shigo. Fateema ta mike tana fadin

“Maman Biyu barka da karasowa.”

“Yauwah Momyn twins!”

Tai murmushi. Baba ta rike baki tace

“Hala cikin nan ya girma anya ba yan biyu bane kai bai wuce wata tara bama kuwa?”

“Haba dai Baba bai wuce ba.”

“To Allah raba lafiya. Amin kake fita da ita sai taje ta haihu maka a mota.”

“Baba mun fito ta dan motsa jikin tane.”

“To Allah dai ya raba lafiya.”

Fateema ta kalli Suraiyya taga tana yatsina tace

“Ya dai?”

“Wallahi baya nane ya rike.”

“Ai fa haka zaki ta fama har Allah ya raba lafiya.”

Baba ta fada. Sannan tace

“Fateema ki dauko mata tofin da na amso mata.”

Mikewa Fateema tayi dakin Baba. Sannan suka gaisa da su Suraiyya da Yaa Kamal. Momy ce ta sauko tare da Yasmeen da ta gama homework dinta. Tana ganin Suraiyya ta rumgume ta tana fadin

“Anty Suraiyya oyogo;”

“Ni sake ni bayan kinki zuwa.”

“Ina nan tafe.”

Fateema ce ya fito ta bata tofin ta amsa ta sha sannan ta bawa Kamal ragowa. Basu jima ba suka tafi.

STORY CONTINUES BELOW

Daki Fateema ta shiga dan kwanciyya wayar ta tai kara dauka tayi ta kai kunne tana fadin

“Bakai bacci ba.”

“Tayaya zanyi bacci banji ya kike ba ina ta kira ba a dauka ba lafiya?”

“Ina falo gun Sister Suraiyya ya kake ya daren?”

“Alhamdulillah!”

Wai me kake kullawa da Baba ne?”

“Me kika gani?”

“Tace nace kazo ne tana son ganin ka.”

“Ikon Allah to insha Allahu gobe zan shigo.”

“Allah ya yadda baka fadan me kuke kulawa ba.”

“Zumunci.”

Ya fada a takaice.

“Shikenan ni zan kwanta sai da safe!”

“Allah tashe mu lafiya.”

“Amin ngd agaida Madam!”

“Zataji.”

*

3am Kamal ya kira Fateema ta mike cikin bacci ta dauki wayar ta. Ganin shine tai saurin dauka tana fadin

“Lafiya Yaa Kamal?”

“Suraiyya ce ba lafiya zan biyo mu tafi asibiti yanzu.”

“Ok sai ka karaso.”

Ta mike ta shiga toilet ta wanke baki da fuska ta fito ta saka katon hijab akan kayan baccin ta. Falo ta fita ta bude a hankali sannan ta tsaya a compound bata jima da tsayawa ba Kamal ya kira ta yana bakin gate Baba mai gadi ta bugawa kofa ya fito a tsorace yana ganin ita ce yace

“Lafiya Hajiya?”

“Lafiya lou buden kofa zan je asibiti ne Suraiyya ce ba lafiya.”

“A kira driver ya kaiki mana.”

“A’ah Yaa Kamal yana waje.”

“Ok!”

Ya bude ta fita ta isa motar ta shiga inda Suraiyya ke baya sannu ta hau mata tana dubata, haihuwa ce dan haka suna isa aka shiga labour room da ita su Fateema suka rufa akan ta batai awa ba ta haifi yan biyun ta lafiyayyu nan aka gyara su aka gyara mamansu aka kai su dakin hutawa.

Sai da suka duba sukaga komai lafiya sannan ta kira Momy. Da mamaki Momy ta dauki waya tace

“Lafiya?”

“Momy Suraiyya ta sauka lafiya an samu Twins mace da namiji!”

“Alhamdulillah suna lafiya dai ko?”

“Eh suna lafiya.”

“Masha Allah.”

Nan ta kashe wayar.

Da safe kuwa tin bakwai Mony ta karaso da break din su. Suraiyya da har tai wanka anyiwa Babies wanka sai kamshi suke ta ci abinci. Momy da ta tahowa da Fateema kaya bandaki ta shiga tai wanka ta shirya. Ita ta cigaba da kula da Suraiyya. Sai karfe biyu aka sallame su suka koma gida har da Fateema.

*

5:00pm ya iso bakin gate din gidan. Parking yayi ya fito. Yasmeen ce ta fito dan dawowar ta daga makaranta kenan aka fada mata Suraiyya ta haihu shine ta kira Yaa Kamal dan yazo su ya tafi da ita. Wannan yasa ta zata shine. Tana ganin sa ta saki murmushi tace

“Ina yini?”

“Lafiya lou. Ina Baba?”

“Tana ciki!”

“Kice mata nine nazo.”

“Ok!”

Ta juya ta shiga ciki bata jima ba ta fito tace

“Wai ka shigo.”

Tare suka shiga ya same ta a falo ya durkusa yace

“Ina yini Baba?”

” lafiya lou ya aiki?”

“Alhamdulillah!”

Yasmeen ce ta kawo masa ruwa da lemo yai godiya tayi sama. Baba Tace

“Jiya nayi magana da kawun nata yace na tura ka shiyasa nace ta turo min kai”

“To shikenan Baba a wacce unguwa yake.”

“Ai ba nisa nan bayan layi ne gida na uku mai Abuja brown paint! Yana da bakin gate.”

“To Baba yaushe zan iya zuwa?”

“Ko yanzu in yana nan zaka iya zuwa.”

“To Baba nagode Allah kara girma.”

“Amin Amin nagode Baba.”

Ya ajiye mata kudi ya mike tace

“Haba Aslam ka kwashe ai abun yai yawa.”

“Baba dan Allah ki barshi.”

“To nagode a gaida gida da iyalai.”

STORY CONTINUES BELOW

Yasmeen ce ta sauko tace

“Baba ni dai zanje driver ya kaini tinda Yaa Kamal bai karaso ba.”

Baba tace

“Shikenan.”

Aslam yace

“Ina zakije?”

Tace

“Gidan Anty Suraiyya!”

“Oh me jego muje na ajiye ki.”

“Toh.”

Baba tace

“A’ah ka da ka bari yanzu Kamalin zai zo gajen hakuru ne kawai irin nata.”

“Baba bari na kai ta ba matsala.”

“To angode.”

Suka fita ya kai ta har kofar gidan sannan ta shiga. A falo ta same su Momy tayi daki wajen me jego dasu Fateema.

Fateema tace

“Yauwah Yaa Kamal din ya dawo bari naje”

Yasmeen tace

“Uncle ne ya kawo ni ba Yaa Kamal ba.”

“Uncle kuma yana ina?”

“Yana waje.”

Fita tayi ta same shi a cikin mota. Karasawa tayi tace

“Ko ka kirani kuma?”

“Ina naga kina cikin mutane ya me jego da twins?”

“Suna lafiya ai tinda kazo sai ka shigo ka gansu ko?”

“Hmmm zan dawo nagan su.”

“A’ah kawai ka shigo kaga babies dina.”

“Shikenan muje.”

Ya bude mota ya fito sannan suka shiga anan sittingroom ta bude masa ya shiga ta dauko masa yaran ta kawo masa. Ya amsa yai musu addu’a sannan a ajiye musu 10k yace

“Ga shi nan kan nazo ganin su da Maman su.”

“Kai Uncle….”

Mika mata yaron yayi yace

“Ki gaishe da Mai jego.”

Sannan ya fita ta maida yaran ta fito tace

“To angode Allah saka da alheri.”

Yai murmushi ya shiga mota ya tayar. Tana tsaye har ya bar wajen sannan ta koma ciki.

*

Bayan kwana biyu da yamma ya shirya ya nufi gidan Uncle Aminu. Yana zuwa yai parking a kofar gida ya nufi gate din yai knockinh mai gadi ya leko suka gaisa, sannan yace

“Alhaji Aminu yana nan?”

“Eh bismillah!”

Ya shigo yace

“Wa za a ce masa?”

“Ahamd ne!”

“Ok!”

Ya aika wani yaro ya fada ba a jima ba yaron ya dawo yace ai masa iso sitring room cam aka kai shi ya zauna.

Bai yi minti biyu ba Uncle Aminu ya fito yana ganin sa ya mike yana yin kasa da kansa. Ya karaso ya mika masa hannu suka gaisa sannan ya ce

“Bismillah!”

Zama yayi sannan ya kara gaishe shi. Uncle Aminu yace

“Ko kaine wanda Ke neman Fateema.”

“Eh Alhaji.”

“Masha Allah! Ni kawun ta ne kanin mahaifin ta, mahaifin ta ya rasu shekaru uku da suka shige. Fateema tayi aure shekara biyu da suka wuce auren ta ya rasu kuma yanzu haka tana aiki nasan ka sani ko?”

Kai ya gyada yace

“Eh nasani Alhaji!”

“To yanzu ina son nasan waye kai?”

“Sunana Ahmad Yahya Ahmad dan gidan Alhaji Yahya Ahmad, ina aiki a ma’aiaktun mahaifina ina da mata daya. Ban taba haihuwa ba.”

“Masha Allah da gaske kana son Fateema?”

“Eh Alhaji!”

“Shikenan ka ban address naka na gida da gun aiki zamuyi bincike in mun gama zan nemeka .”

Nan ya bashi sukai sallama cikin girma juna ya tafi.

Duk abin nan da ake Fateema bata sani ba har Uncle yai bincike ya gama ya gane ba ruwan Ahmad yana da hankali da tarbiyya uban sa babba mutum ne.

Dan haka ya kira Ahmad kan zai iya turo manyan sa in ya shirya.

Ai kuwa a satin ya aika mahaifin sa suka je. Nan suka saka lokaci wata biyu. Nan sukai sallama cikin aminci.

Sai bayan an kawo kudi ne sannan Uncle Aminu ya isa gidan su Fateema da kansa. Bayan magariba yaje tana daki tana zikirin ta ya shigo bayan sun gaisa da Momy ya shiga wajen Baba nan ya fada mata duk abinda akayi. Dan haka aka kira Fateema da Momy.

Suna zuwa ta gaisar da Uncle ta xauna. Momy ma zama tayi yace

“To Fateema jiya an kawo kudin auren ki da Ahmad wanda yanzu an saka wata biyu masu zuwa nayi bincike a kan yaron na gane yaron yana da hankali da tarbiyya wannan yasa nazo na fada miki Allah ya kaimu lokacin ya tabbatar da alheri.”

Tin da Uncle ya fara magana ta kasa gane me ma yake fadi dan ita ji tayi kamar ba a duniyar take ba ita za ayiwa aure da wa to meyasa ba a bata dama ba. Haka Momy tayi godiya Uncle ya mike ya fita.

Tabota Momy tayi ta dago hawaye ta gani yana bin kuncin ta.

“Haba Fateema menene na kukan to?”

“Momy ni bana son sa bansa wanene shi ba!”

“Ki kwantar da hankalin ki ai Uncle ya fada min shi da kansa yaje ya nemi auren ki dan haka kiyi hakuri kiyi biyayya ga Uncle din ki.”

“Momy Fu’ad fa…?”

Ta fada tana girgiza kai tace

“Momy ni Fu’ad kadai nake so dan Alllah ki bawa Uncle hakuri”

Tana fada ta mike ta fice a dakin. Baba ce ta fito tana fadin

“Kinsan waye yaron kuwa?”

“A’ah!”

“Wannan yaro Aslam ne ni naga yana sonta kuma ya damu da ita ganin yana da hankalin sa yasa na bashi dama yaje gun Aminu.”

“Allah sarki. Allah sanya alheri to.”

“Amin!”

Na n ayi sama.

Ranar kwana Fateema tayi kuka da sake sake tana tunanin ina Fu’ad yake.

*

Washe gari har karfe goma bata fito ba wannan yasa Momy ta zata ko ta tafi aiki duk da tasan bata saba haka ba amman da ta leka sai taga motar ta wannan yasa ta nufi dakin ta.

Kwance ta same ta akan gado. Zagayawa tayi ta ga idon ta a lumshe amman fuskar ta tayi ja ta kumbura dan yadda ta sha kuka.

Zama tayi ta dafata sai taji jikin ta ya zafi. Kai ta girgiza. a hankali Fateema ta bude ido tana kallon Momy.

“Fateema baki da lafiya?”

“Kai ta dafe ta lumshe ido.

“Kuka kikai shiyasa meyasa kikai kwana kina kuka kinsan ciwon ki ko? Ko kina son ya dawo ne?”

Kai ta girgiza tace

“Momy yaya zanyi ni bana son koma waye Fu’ad nake so…”

“Fateema ki nutsu ki gane rayuwa mana. Yanzu ina fu’ad din?”

Kai ta girgiza.

“Ace Fu’ad zai dawo yau kina da ragowar igiyar da zata hadaku ne kada ki manta saki uku fa yayi miki ki dawo hankalin ki.”

Ido ta runtse. Mony tace

“Kila ma yana can yai auren sa har da ‘da ko ‘ya!”

Da sauri ta bude ido tana kallon Momy.

“Dan Allah momy kada kema kice Fu’ad yai aure ni kadai Fu’ad yake so.”

Kallon Mamaki Momy ta tsaya yi mata can kuma tace

“To ya isa daina kukan ke kadai yake so amman yanzu dai zan baki shawara kibi umarnin Uncle din ki kinji insha Allahu zaki ga da kyau.”

“Momy bin Umarnin Umcle tamkar rabuwa ta da Fu’ad ne fa.”

“To inbaki bi umarnin nasa ba shi kuma shine zai sa ki kasamce da Fu’ad yau shekara nawa babu Fu’ad more than two years fa Haba Fateema ya kamata kisan abinda kike yi.”

Kai ta hade da gwiwa tana kuka. Momy ta dago kanta tace

“Stop dis crying please Fateema. Bana son wannan kukan naki wallahi kar ya kawo wata matsala ki cire damuwa a ranki ki mikawa Allah komai insha Allahu zakiga sauyi mafi alheri. In kika kai kukan ki ga Allah zai zaba miki abinda yake mafi alheri. Yanzu kije kiyi wanka kizo kici abinci muje asibiti a baki magani kinji?”

Ta fada tana goge mata idon fuskar ta ta shiga ta hada mata ruwa. Shiga tayi tai wanka ta fito ta saka kaya tea kadai tasha ta sha paracetamol suka tafi asibiti ba dan taso ba.

Dr Auwal ne ya duba ta yace dole ta rage damuwa dan damuwar ita ta jawo mata ciwon kai da zazzabin. Ya bata magani sannan yai mata fatan samun sauki.

Sai da suka dago gida ta dauki wayar ta dake charge missed call din Aslam ta gani tsaki ta saki dan ita ji tayi ta tsani duk wani namiji in ba Fu’ad ba.

*

A gida kuwa da Hajiya Fateema ta tambaya wacce zai aura bai boye mata komai ba. Nur da Jannah kuwa murna kamar me Fateema zata auri Uncle din su.

*

Momy ta kira Hajiyar Fu’ad ta fada mata kawo kudin auren Fateema da saka rana Hajiya tayi Allah sanya alheri tace tana nan zuwa nan Momy ta fada mata duk halin da take ciki. Hajiya tace

“Fateema kenan ai auren shine rufin asiri tasan ina Fu’ad din ya shiga tayi auren Allah yasa shine mafi alherin a rayuwar ta Amin.”

“Amin nagode!”Zaune yake falo yana aiki a system din sa. Jidda ce ta shigo cikin kwalliya mai kyau ta zauna a gefen sa tace

“Honey wata fa yayi banji alert a.”+

“Haka ne wai so nake kiyi lissafi da kayan fadar kishiya ai.”

“What?”

“Eh ko irin nata kike so?”

“Me fa?”

“Laifen!”

” honey auren ya taho ne?”

Kai ya dafe yace

“Am sorry dear an saka lokaci remains two month insha Allahu.”

Wani abu ta hadiye da kyar tace

“To amman ni dai ka turon nawa kawai ina bukatar kudin ne nan kusa akwai abinda zanyi.”

“An gama uwar gida ran gida.”

Ya mika mata wayar sa yace

“Kiyi transper duk yada kike so.”

Amsa tayi ta saki murmushin da yafi kuka ciwo tace

“Nagode!”

Turawa tayi ta bashi. Ya ajiye yace

“To me kike ganin za ayi a bikim?”

“Zanyi tinani kan time dim.”

“Yauwaj.”

“Baka fada min wacece amaryar ba!”

murmushi yayi yace

“Ki kwantar da hankalin ki zaki ganta as suprise!”

“Ni dai bana so kawai ka fadamin.”

“To in baki santa bafa.”

“Ina son na santa tinkan bikin ne?”

“Zan fada miki but not now!”

“Promise!”

“I promise you!”

“Thanks!”

Ta fa tana mikewa tayi cikim daki.

Tana shiga ta daura hannu a ka kamar zaya kurma ihu sai ta zauna ta dauki wayar ta. Tana kuran Najah ta dauka tace

“Najah wai me kuke yine? Bikin saura wata biyu fa.”

Tsaki tayi tace

“Ki kwantar da hankalin ki zan shigo zuwa jibi bana gari.”

“Yanzu Najah har jibi nifa shiyasa Khady tafi min abinda nake so da ita ce zuwa zatayi a gobe goben nan duk inda take.”

Dariya Najah tayi tace

“Shikenan in nazo kyaji dalilin cewa sai jibin sai anjima.”

Khady ta kira tana dauka tace

“Ya dai?”

“Kema kin sani ai.”

“Meya faru?”

“Auren Aslam ya kusa fa.”

“Haba dai?”

“Wallahi saura waya biyu.”

“Ikon Allah akwai wani malami zanje wajen sa amman ki kara samo mana information akan yarinyar nan.”

“Yaki fa ko yanzu yaki fadan amman dai munyi magana yanzu yace zai fadan kan time din.”

“Gud! Ki kwantar da hankalin ki dan Allah.”

“Insha Allah.”

*

Kwana biyu gaba daya ta daina fita duk ta shiga damuwa ta rame ta fita a haiyacin ta. ko wayar bata san ina ta shiga ba. Momy tayi fadan, tayi nasiha, tayi lallashin amman duk a banza dan haka itama ta share ta kawai.

Ta auri zaman daki sai kallon picture din Fu’ad ko karatun alkur’ani. Duk dai ta fitar da rai da rayuwa da jin dadi.

shi kan sa Aslam da yaje asibiti akace bata nan yai mamaki ya kira wayar ta yafi sau nawa amman bata dauka. Yau ma yana dawowa daga aiki ya wuce wajen Fateema amman bata nan wannan yaza ya nufi gidan nasu kawai. Yana zuwa yai parking.

STORY CONTINUES BELOW

Yasmeen da ta Dawo kenan ta karasa tana fadin

“Uncle welcome.”

“Welvome too Yasmeen ya ckul din?”

“Alhamdulillah!”

“Where is Doctor?”

“She is iniside!”

“How she is?”

Shiru tayi tace

“Two days ko falo bata shigowa tana daki always reciting kur’an but gaskiya she is sick ina zaton na tambaye ta tace ba komai.”

“Ok je kice mata nazo ina waje ina ta kiran number bata dauka.”

“Ok Uncle.”

Tayi ciki. A falo ta samu Momy tace

“Barka da gida Momy.”

“Yauwah Yasmeen ya makaranta?”

“Alhamdulillah! Where is Anty?”

“Tana daki!”

“Uncle ne yazo yace na kira ta.”

“Ok je ki fada mata.”

Tayo dakin Fateema. A zaune ta same ta a kan kujera ta jingina kan ta da kujera idon ta a lumshe tana sanye da hijab hannun ta rike da counter tana yin tasbihi a haka sai kace bacci take in ba hannun ta ka kalla da yake dannan counter din ba.

“Anty!”

Yasmeen ta fada. Ido ta bude tana kallon ta yace

“Sannu da gida Anty!”

“Yauwah!”

“Anty Uncle ne yazo.”

“Kije kice masa bana jin dadi yaje ya dawo wani lokacin.”

“But Anty…”

“Please Yasmeen my head is paining me. leave me.”

“Did you take your medicine?”

“Yes!”

“Get well soon Anty!”

“Thank you!”

Ta maida kanta ta kwanta. Tana fita ta samu Momy. Momy tace

“Tana ina?”

“Momy kanta ne yake ciwo wai.”

“Je ki kai shi sittingroom ga ta nan”

Ta fada tana yin ciki da kalloYasmeen ta biya sannan ta fita dan sanar masa.

“Uncle muje gata nan!”

“Ok thank you!”

Suka isa ya zauna yace

“Ya makarantar ana dai karatu ko?”

“Yes!”

“Good!”

Tace

“Bari naje na cire uniform.”

“Ok!”

Ta wice.

Momy na shiga tace

“Maza tashi kije ke haka ake daga an miki maganar aure sai ki fitar da rai da rayuwa kin daina zuwa aiki kin daina cin abinci kin daina walwala haba Fateema haka zaki cigaba da rayuwa haka zakije gidan mijin kina masa?”

Ido ta bude tana kallon Momy idon ta cike da kwalla.

“Ni ba kuja nace kimin ba. Amman yana da kyau ki amshi kaddararki yau da Fu’ad din ne ya mutu da ya kenan shikenan shima ba zakiyi aure ba wato ke ba zaki amshi kaddarar ki ba ko kin nunawa Allah abinda ya daura miki baki gode masaba Haba Fateema kina da sani da dan haka kiyi amfani da ilimin ki, ki amshi jaddarar ki kika sani ko shine mafi alheri a rayuwar ki. Allah na jarabta bawan sa inyaga yaci yai masa tukwici da alheri dan haka kema ki daure kici wannan jarabawar abu shekara biyu har da wani abu yaki ci yaki cinyewa Yanzu wannan abin da kike shi zai hana auren da za ai miki ko me?”

“Momy kiyi hakuri na kasa cire ab a raina ne ina in son Fu’ad ban son na rasa shi.”

“Na sani amman ki daure ki danne ki cire ki samu ki samu wata nutsuwa kinji ki daure ki kara dagewa da addu’a sannan ki rungumi kaddarar ki da hannu bibbiyu insha Allah zakiji dadi nan gaba.”

“Insha Allahu Momy.”

“Yauwah yanzu kije ki wanke fuskar ki sai ki dan shafa hoda kije Aslam na sitting room.”

To ta fada ta mike ta nufi bandaki. Fuska ta wanke sannan ta fito tana goge ta da karamin towel. Man lebe ta shafa ta dan saka hoda sannan ta fito falo.

Momy dake zaune ta kalle ta tace

“Yauwah koke fa.”

Tai murmushi ta fita.

*

Sirttng room ta nufa kirjin ta na bugawa ta rasa ko saboda menene tana isa tayi sallama a kofar dakin yana daga ciki ya amsa. Labulen ta daga ta shiga kan ta a kasa.

STORY CONTINUES BELOW

*

**

***

****

*****

******

Kokarin sauka ya farayi Muhammad ya kama sa yace

“Ina zaka?”

“Zanje naga Aysher!”

Zaunar dashi yayi yace

“Bari a kira maka ita.”

Abbah mikewa yayi ya fita. Yaa Muhammad yabi bayan sa. A zaune ya same ta ya kalli Maryama yace

“Me take yi ne?”

Wajen ta ta karasa ta daga ta ta dago ta kai ta da ido ta nuna mata Yaa Muhammad ta kalle shi ya ce

“Kije!”

Kai ta gyada ta mike a hankali taba ganin dishi dishi tayi dakin. Faisal na ganin ta shigo ya mike yana murmushi yace

“Ango!”

Duka ya kai masa yana murmushi ya fice. A hankali ta taka ta karasa gefen gadon kallon ta ya tsaya yace

“Zagayo tanan Aysher na!”

Dagowa tayi ta kalle shi sai tai saurin dauke kai dan wani kallo da yake mata a hankali tana dafa gadon ta zagaya ta side din da yake tana zuwa yaja hannu ta sai jin ta tayi a kirjin ta yai mata wata wawuyar rumguma wacce sai da taji numfashita kamar zai dauke. Kasa hanasa tayi dan sam ba karfi a jiki ta sai lamo da tayi ajikinsa

Shi kuwa ido ya lumshe kawai yana fadin

“I love Aysher! Dan Allah ki soni ki kasance dani har karshen rayuwa ta kece kadai farin ciki na Ina kaunar ki Aysher!”

Ido kawai ta lumshe tana mai jin kalaman sa har tsakar kanta. Jikin ta kuwa ya dada yin sanyi. Ya jima yana fada mata kalamai masu ratsa zuwa sannan da kyar ya sake ta. Dafa gadon tayi ta sa hannu ta janyo kujera ta zauna tana kallon kasa. Hannun ta ya kama ya matso kusa da ita yana kallon ta. Kanta na kasa wannan yasa ya sa hannun sa ya dago habar ta, suna hada ido tai saurin lumshe ido.

“Aysher i didn’t hear ur voice since u came please say something!”

Kai ta dauka tace

“Ya jikin Yaa AK?”

“Jiki ya ganki yaji sauki Aysher! Wannan ya karasawa na yadda da son da nake miki zuwan ki ya warkar dani ga duk abinda nake ji, ina jina tamkar wanda bai yi ciwo ba, na fada miki son ki shine rayuwa ta in bashi mutuwa zanyi samuwar ki a gareni shine cikar buri na da farin cikin raina. Ina son ki Aysher dan Allah ki soni ko kwatan yadda nake son kine!”

“Nifa bance bana son ka!”

“Na sani Aysher shiyasa nake rokar son naki ya kara daduwa akan wanda kike min, ina son, son da kike min ya kai ko da rabin na Yaa Muhammad din kine.”.

Kai tati kasa dashu. Yai murmushi yace

” i love you Aysher!”

Ido ra lumshe tana jin wata nutsuwa da sanyi na shigar ta, daga lumshe ido bacci ya dauke ta dan yadda taci bashin shi ga gajiya ga ciwon kai. Sun jima a haka yaji jikin ta ya saki dago ta yayi yaga idon ta a lumshe kansa ya kai goshin ta hancin su ya hadu ya tura bakin sa yai kissing lips din ta sai a sannan ya gane bacci take gyara mata kwanciyya yayi a jikin sa. Yana shafa mata baya a hankali shima ya lumshe idanun sa.

Magarib aka kira wannan yasa Faisal ya taho dan ya taimaka masa yayi alwala kan su tafi masjid suma yana shigowa yaja birki. Har zai juya sai kuma yace

“Yanzu in na koma wa zai shigo ya same su a haka?”

Wannan yasa kawai ya shiga a gefen gadon ya tsaya yana kallon wani wajen ya tabo Aliyu yace

“AK it is time for prayer fa!”

Ido ya bude ya kalle shi sai kuma yace

“Ok!”

Juyawa yayi zai fita yace

“Ka tsaya ka taimakan mana.”

“Ai naga kaji sauki kalli fa!”

Ya nuna masa Aisha dake kan sa. Murmushi ya saki ya fara shafa fuskar ta a hankali ta bude ido suna hada ido tai saurin runtse idon ta sai kuma taji ta akan abu da sauri ta bude ido tabi inda take kwance da kallo. A zabure ta mike wanda tana mikewa tayi baya luuu zata fadi cikin zafin nama ya mike ya taro ta ta fada jikinsa rumgumeta yayi yana fadin

“Kiyi a hankali!”

Hannu tasa ta dafe kan ta dake ciwo kamar zai rabe duk da tai bacci bai sake ta ba ciwon kan. Kallon ta yayi yace

“Yana miki ciwo ne?”

Kai ta girgiza ta fara kokarin zare jikin ta daga nashi zaunar da ita yayi akan kujera sannan yace

“Relax!”

STORY CONTINUES BELOW

Ya juya dan ganin ina Faisal yake sai yaga wayam murmushi yayi ya nufi bandakin a hankali yana shiga ya dauro alwala ya fita. Tana zaune a inda ya barta ya kalle ta yace

“Are you Alright kuwa?”

Kai ra gyada ya karaso inda take yana kallon ta kamar yana son ya gano me yake damun ta. Can yace

“U are not Aysher!”

Dagowa tayi da sauri sujlka hada ido kasa dauke idon su sukai daga kallon junan su ita ce ma tayi karfi halin janye nata, yace

“Kije kiyi alwala its time for magrib!”

“Alright!”

Ta fada tana mikewa a hankali amnan sai jiri ya debe ta da sauri ta dafe kujerar da take kai ya kalle ta yace

“Aysher you are not fine!”

Kai ta girgiza ya kama hannun ta yace

“Let me help you!”

A bakin tap din toilet ya barta ya juya ya fita. Alwala tayi sannan ta juyo ta taho tana dafe bango tana zuwa ta zauna akan kuherar dake dakin. Sai da ya idar ya nuna mata gefen sa da yake babban carpet ne yace

“taho kiyi sallah mana.”

Mikewa tayi a hankali ta isa ta hau ta tada sallah tana idar wa ta jingina kan ta da gadon sa tare da lumshe ido. Kallon ta ya tsaya yi. Suna a haka aka bude dakin. Hajara ce ta shigo ta zauna akan kujera tana fadin

“ya jikin?”

Mikewa yayi a hankali ya koma kan gadon yana kallon ta tare da sakin murmushi yace

“Alhamdulillah ya kike?”

“Lafiya!”

Aisha da bacci ya fara debe ta kalla sai kuma ta dauke kai ta mike ta fita kawai. Yaa Muhammad da Faisal da Umr da Farouk ne suka shigo. Umar ne yace

“Ya jikin Yaa AK?”

“Da sauki Umar!”

Ya kalli Farouk shima yace

“Ya jiki?”

“Da sauki.”

Yaa Muhammad ya karaso yace

“Ai ya samu abinda yake so jiki yai sauki!”

Murmushi dukka sukai. Ga mamakin su sai sukaji Yaa AKyana fadin

“Wannan haka yake Aysher ita ce rayuwa ta numfashi na farin ciki na.”

Dukkan su mamaki suke masa banda Yaa Muhammad domin shi ba sanin halayar sa yayi ba. Umar ya kai wa duka wanda har da rike baki dan mamaki yace

“See you ku kadai to kuka san soyayya!”

Farouk yace

“Alhamdulillah Inlow Aisha ta canja mana Bro Thank you so much!”

Faisal yace

“Daman xcan haka yake.”

“Kaji dai tsoron Allah!”

Sukai dariya. Umar yace

“Abbah ne yace muzo mu dauki Inlow Aisha dan taje gida ta huta tasha hanya tana bukatar hutu dan ta huce gajiya.”

“Haba dai ai anan zata kwana!”

Ido Unar da Faroyk suka zaro. Farouk yace

“Ni dai ba zan iya jin wannan ba.”

Ukar yace

“Tsaya ni dan uwa!”

Suka fice. Yaa Muhammad da Faisal ma sukai dariya. Aliyu yace

“Kaji shakiyan yara lokacinvda sukai tasu soyayyar na saka musu ido.”

Yaa Muhammad yace

“Kwantar da hankalin ka matar ka ce kayi yadda kakeso. Ni dai zanje na huta sai da safe Allah kara sauki.”

Sannan ya juya Faisal yace

“Sarkin soyayya!”

“Naji nayi!”

Ya harare shi yace

“Sai da safe.”

Ya fita. Mikewa yayi ya leka Aisha da ta rufe fuska da hijab ta jin gina kan ta da gado tana bacci. Hannun ta ya dauke yana leken fuskar sai yaga tana bacci daukar ta yayi ya kwantar akan gadon ya zauna akan kujera yana kallon fuskar ta. Murmushi ya saki yace

“Sleeping beauty my wife.”

Kofar aka budo ya dago kai yaga Abbah da Mamah ne. Mai martaba yace

“Nace azo su tafi kace me?”

Kai ya dan sosa yace

“Please Abbah!”

“Kasan basa barin me jinya ai!”

“Ok nima naji sauki su sallamen kawai mu tafi tinda haka ne.”

Doctorn dake duba sa ne ya shigo ya tsaya kallon sa da mamaki yace

“Badai patient dina bane haka a zaune.”

Abbah yai murmushi yace

“Shine!”

Gadon ya kalla yace

“Wannan fa?”

“She is the medicine that cure his aid.”

Murnushi Doctor ya saki yace

“Alhamdulillah how are you feeling now?”

“Alhamdulilah nothing more sai rashin kwarin jiki bakina ba dadi.”

Dafa shi yayi yace

“Shima soon zai tafi insha Allah. Allah kara sauki. Kana shan maganin ka. Kaji?”

Kai gyada har ya juya Abbah yace

“Yace a sallame sa fa.”

“Why?”

“Dan nace ba a barin mai jinya!”

“Wa za a bar masa.”

Gadon Abbah ta nuna. Doctor ya saki dariya yace

“Ai ita magani ce abarta.”

“Thank you Doctor!”

Aliyu ya fada. Mamah da Abbah kallon sa kawai suka tsaya yi. Basu taba ganon Aliyu cikin farin ciki irin wannan ba.

Sosai suka ji dadi amman sai ya basu kunya. Mamah ta leka ta tace

“Bacci take?”

Fuska ya bata yace

“Mamah lafiyar ta kalau kuwa?”

Abbah Mamah ta kalla yace

“Ayyab itama tayi ciwo dan tana kan shan magani ba.”.

” haba no wonder!”

Abbah yace

“Mu zamu tafi Naryam zata kawo muku abinci ka kula da kan ka da ita sai da safe Allah kara sauki.”

“Amin Abbah nagode sosai.”

“Sai da Safe Aliyu. Allah kara sauki “

Mamah ta fada.

“Amin Allah tashe mu tafiya.”

“amin!”

Suka fada suka fice. Hajara na falo Mamahn tace zamu wuce ko zaku taho tare da Maryama?”

“No muje kawai.”

Ta mike tabi bayan su Mamah tace

“Ai bakuyi sallama ba.”

Juyawa tayi ta shiga dakin. A bakin kofa ta tsaya ganin Aisha a kwance yasa ta kalli gadon takalli Aliyu dake kallon ta.wani kishi ne yakamata a ranta take fadi wai wacece yarinyar nan ne?

Dagowa yayi ya ganta sai ya mika mata hannu. Bata shigo ba tace

“Daman tafiya zamuyi sai da safe!”

Tana fada bata jira amsar sa ba ta fice da kallo ya bita yana girgiza kai sai kuma ya maida kallon sa ga Aisha.

*

Su Mama na komawa gida suka samu Maryama ta gama hada misu abincin har ta fito suka hadu da Su Yaa Muhammad da Su Mamah sun dawo. Tsaya tayi tace

“Kai kun dawo.”

“Eh ki maza ki kai musu kada suji yunwa.”

“Yaa Umar please kazo ka rakani.”

“Tab wanka zanyi naje nayo waya da my love wallahi.”

Yaa Farouk ta kalla kan tai magana yace

“Mee too!”

Fuska ta bata kamar zatai kuka Yaa Muhammad ya kalle ta sai yaga tai masa kamar Aisha in tana shagwaba dan haka yace

“Haba Autar don’t cry mana muje ni na raka ki.”

“Da gaske?”

Kai ya gyada tace

“Thanks you!”

Sannan tai wa Umar da Faroyk gwalo ta bi bayan sa. Tare suka tafi.

Sallah isha’i aka yi ya mike yayi sannan ya dawo ya zauna yana shafa face din ta. Sallamar su Maryama yaji ya dago ya kalle su yana amsa sallanar.

Naryama tayi murmushi tace

“Yaya kenan ya jikin?”

“Da sauki ya kike?”

“Lafiya!”

Wajen gadon tayi ta leka Maryama tace

“Inlow bacci take?”

“Yes!”

“Ga abincin ka nan zamu tafi da ita ko?”

Hararar ta yayi yace

“Sai ki tafi da itan na gani.”

“Oh anan zata kwana?”

Yaa Muhammad yace

“Kinga shige muje ango sai da safe!”

“Allah bamu alheri.”

*Antty*Suna fita ta kalle shi tace

“But Kayi namijin kokari da ka bawa Yaya na Anty Aisha nasan ka samu babban matsayi agun Abbah da Mamah da shi kansa Yayana. Yayana bai taba soyayya ba ko matar sa ta farko zabin Abbah ce but sam shi ba son ta yake ba ko da yake laifin tane sam ita bata iya kula ba bare har ta janyo ra’ayin sa. Kasan time din da muka je taho dashi bata san bai da lafiya ba ita tana can gidan gwamnati shi yana gidan sa.

Ba yabon kai ba wallahi zakuji dadin auren Yaya na da Anty Aisha saboda Yaya na mutum ne mai ilimi da aiki dashi ga hakuri ladabi biyayya ga tarbiyya duk gidan mu ya fi kowa kuma Mamah da Abbah ma sun fi son sa kai kowa na son Yaya na sai dai barshi da miskilanci amman tin fara aikin sa a garin ku ya canja Yanzu zamu zauna muyi hira mu gaisa. Kai Alhamdulillah ni tinda naga Anty Aisha naji ina son ta kuma ina fatan suyi aure sai gashi ashe wai son ta yake kai so wonderful. Naji dadi da naji ka barwa Yaya na Anty. Allah saka da alheri ya baka kaima mai sonka.”

Tinda ta fara magana yake kallon ta yana kallon wani abu in tayi kamar Aisha dan haka sai yai murmushi kawai.+

Ta cigaba da magana tace

“Mu shida Abba ya haifa Yaa Abubakar,  Yaa Usman,  Yaa Aliyu,  Yaa Umar da farouk sai ni Autah. Muna zaune lafiya duk sunyi aure da ya’ya ni kadai ce banyi ba sam Yaya ya hanani kula samari kullum sai yace shi zai zaba min mijin aure da yake nima ina son Yaya na kuma nasan ba zai min zaben tumun dare ba yasa na ki kula su. Na gama univesury dis year na karanta biochemistry. Ina so duk abinda Yaya na take so sosai.”

Murmusshi yayi tace

“kai fa?”

“Hmmm ni me?”

“Komai akan ka!”

“Ai kin sani!”

“No!”

“Ni dan kanin Baban Aisha ne. Since kafin a haifi Aisha ni dan mamanta ne dan ita ta yaye ni daga yaye ba koma wajen ta. Sai da Mama na ta haifi ya’ya biyar sannan Maman Aisha ta samu cikin Aisha. Tare mukai raino har ta haifi Aisha komai ni kewa Aisha. Mahifin Aisha ya rasu since tana baby da mamanta zata tafi da yake yar Niger ce shine Baba yace ta bar mana Aisha. To haka na cigaba da dawainiyya da Aisha ina son Aisha ina tausayin ta. A haka muka rayu makaranta ita ta rabani da Aisha dan nayi nisa a lokacin Yayan ki ya shigo rayuwar ta. Na karanci Agricultural inda yanzu na fara bautar kasa. Kinji komai akai na.”

“Ashe Aisha yar garin su Mamah ce. Haba no wonder shiyasa take kyakyawa masha Allah. amman banfa san suna ka fa.”

“Nima ai ban san naki ba.”

“Am Maryam Kabir MK!”

“Muhammad Abubakar!”

“Mai babban suna.”

“Kema haka!”

Tai murmushi. Suka shiga falo suna murmushi. Mamah suka sama da Abbah zaune. Abbah yace

“Kun dawo?”

“Eh Abbah ashe acan Anty zata kwana.”

“Ya matsa doctor ya daure masa gindi.”

“Hmm Yaya kenan!”

“Ki xubawa Mubammad Abinci su Umar duk sunci.”

Mama ta fada.

“To ta amsa.”

Mamah tace

“Muhammad kaje kaci abinci kaima ka samu ka huta ko?”.

“To nagode!”

Ya bi bayan Maryama a dining ta zuba masa ta zauna itama ta zuba tana ci tana bashi labari sai dariya suke da suka gama ma hira suka zauna yi basu suka tashi ba sai wajen sha daya shima dan su Mamah sun tafi daki ne yasa yace shima sai da safe.

STORY CONTINUES BELOW

Umar ya sama yana waya da matar sa Faisal kuma na chatting. Farouk kuma yai bacci. Wanka ya shiga yayi ya fito shima ya kwanta sai bacci.

*

Suna fita ya shafa face din ta yace

“Aysherrr!”

Ido ta, ta dan bude ya sakar mata murmushi yace

“Sallah ko?”

Mikewa tayi zaune ta jingina da gado dan har time din jiri take ji ido ta lumshe tana son taji ya tafi. Sai da taji ta daidaita sannan ta bude idon ta,  ta ga ya kura mata ido. Murmushi kawai tayi ta mike ta sauka ta fara tafiya taku daya, biyu kawai ta zube a wajen da sauri ya mike ya dauko tana fadin

“Lafiya? Me yake damun ki?”

Kai ta girgiza tace

“Jiri nake ji.”

Bandaki ya shiga da ita kawai tai alwala ya dauko ta akan gado tai sallah tana idar wa ya fita da sauri. Yana fita suka kusan cin karo da wani Doctor yazo duba shi.

“Ah Aliyu kaine?”

“Yes please zo ka duban matata!”

Ya janyo hannun sa suka shiga dakin. Kwance suka same ta akan gado ta lumshe idon ta.

Doctor ya tsaya Aliyu ya karasa ya kira sunan ta a hankali. Ido ta bude ta kalle shi yace

“Sannu!”

Kai ta gyada karasowa Doctor yayi yace

“Sannu!”

Ta gyada masa kai. Ya ce

“Me yake damun ki?”

“Jiri da ciwon kai.”

“Ayyah sorry!”

Ya fada ya dauki abin auna jini dake dakin ya auna jinin ta sannan yace

“Kina cin abinci?”

“Na kasa ci.”

“Ok!”

Ya kalli yace

“Zan saka mata ruwa sannan zan je zan kawo mata magani kan nan ta samu ta sha ko tea ne.”

“Ok!”.

Tea ya hada mata sannan ya dibar mata peppersoup din da aka kawo musu. Dago ta yayi ya fara bata tea din. tea tasha amman nama biyu taci ta kautar da kan ta.

Yace

“Sannu!”

Ta gyada kai ta koma ta kwanta. Ba ajima ba doctor ya dawo ya bata magani ta sha sannan ya saka mata ruwa. Nan da nan bacci ya dauke ta. Sai da ya kara duba Aliyu sannan ya tafi.

Abinci yaci kadan sannan ya zauna gadi da kallon Aisha. Can kuma ya mike yayo alwala ya tada sallah yana mai godiya da Allah da ya bashi Aisha take yaji komai ya daina masa ciwo a jikin.

Karfe dayan dare aka zo aka cire mata ruwan ta na karshe lokacin Aliyu na kanta a tsaye ta bude ido tace

“Yaushe zamu tafi?”

“Ina?”

“Gida!”

“Ai anan zaki kwana.”

Da sauri ta mike tace

“Anan din ni dai a’ah ina su Maryama su zo mu tafi ba zan kwana ba.”

Tahowa yayi ya zauna a gefen ta yace

“Dare fa yayi karfe daya yanzu ina zaki? Su Mamah ma duk sun tafi.”

Baki ta tabe kamar zatai kuka. Ya kama hannun ta yace

“Yanzu ki kwanta kiyi bacci kinga kan ki yana miki ciwo,  kinji.”

Ya komar da ita ya kwantar ya mata addu’a ya tofa mata, sai da ya tabbatar ta samu tayi bacci sannan ya koma kan sallaya. Sai karfe uku saura yaji bacci na son dibar sa sannan ya koma ya hau gadon ya lullube su sannan ya jata jiki sa. Ai sai ta kara shigewa jikin sa.

*

6:00am sai lokacin ya farka yau mamakin irin baccin da yayi da bai tashi yai sallah ba da sauri ya mike ya shiga bandaki yayi wanka ya dauro alwala ya fito ya saka kaya sannan ya tada sallah. Yana kan sallaya nurses din dake kula dashi suka shigo nan suka gaisa suna masa ya jiki sannan suka tambaye shi meke damun sa kan Doctor yazo suka tafi. Mikewa yayi ya hada mata ruwan wanka sannan ya zauna a gefen gadon. Fuskar ta yake kalla me kyau da ita hannu ya saka a saman kanta yaji ba zafi sannan ya saka a wuyan ta nan ma haka hannun ta ya kama yana matsawa a hankali ido ta bude tana kallon sa.

“Karfe shida fa bakiyi sallah ba.”

Da sauri ta mike tana kallon dakin bai da bambanci da rana da dare saboda irin fitilun dake dakin. Sai kuma ta dire kafar ta ta nufi vandaki. Alwala ta dauro tazo ta tada sallah. Tana idar wa ta juyo ta kalle shi ya kura mata ido. Kai ta dauke tace

“Ina kwana?”

STORY CONTINUES BELOW

Mikewa yayi ya koma kan sallayar ya zauna a gaban ta yace

“Ya jikin?”

“Alhamdulillah! Ya naka jikin?”

“Alhamdulillah!”

“Allah kara sauki.”

“Amin! Taso ki kwanta kinji!”

Ya dago ta ya maida kan gado. Ta kwanta tare darufa ta lumshe ido. Bata jima ba bacci ya dauke ta.

Karfe takwas Maryama da Yaa Muhammad suka shigo asibitin hannun Yaa Muhammad rike da kayan Aisha Maryama kuma abincin su ne. Falon suka shiga suka buda sannan suka isa bed room din sukai knocking izinin shiga ya basu suka shiga. Maryama ta ajiye kayan hannun ta sannan tace

“Ina kwana?”

“Lafiya lou. kin tashi lafiya.”

“Ya jikin”

“Da sauki!”

Yaa Muhammad ne ya shigo sukai musabaha da juna ya tambaye shi ya jiki. Sannan Maryama tace

“Bata tashi ba.”

“Yes itama bata jin dadi! Dan jiya ma sai da akai mata karin ruwa.”

“Ayyah Allah bata lafiya.”

“Amin!”

Yaa Muhammad ma yace

“Allah bata lafiya.”

Ya mike ya kalli Maryama yace

“Muje ko?”

Ta mike tace

“To Yaya Allah kara sauki sai anjima.”

“Ina su Mama?”

“Suna gida. Sai anjima zasu zo.”

“Su agaishe su.”

Suka fita. Karfe tara ta farka ya karasa yace

“Sannu!”

Kai ta gyada. Ya dago ta yace

“Kizo kiyi wanka ko?”

Shiru tayi sannan ta mike ya shiga ya hada a ta ruwan sannan ta dawo ya kama hannun ta, ta shiga. Wanka tayi ta fito sanye da rigar ta da hijab. Dressing room ya nuna mata ya mika mata ledar kayan ta. amsa tayi ta nufi dakin. Tana budewa taga doguwar riga ce golding kala mai adon stone farare. Daga su sai dan mayafin ta. Sakawa tayi ta rolling mayafin nata.

Tana fitowa  ya zuba mata ido dan bai taba ganin Aisha ba Hijab ba kullum sanye take da Hijab yau ne kadai babu Hijab itama tana ganin kallon da yake mata tai sauri ta juya ta koma ta dauki Hajib din ta, ta saka tafito. Murmushi yayi kawai ya girgiza kai. Kan ta a kasa ta isa kan doguwar kujerar dakin ta kwanta. Tea ya hada mata ya zuba mata dankalin da su Maryama suka kawo sannan ta mike ya dawo inda take ya ce

“Tashi ki karya.”

Mikewa tayi amman tea kadai tasha tace ta koshi. Yayi yayi taci taki ci da ya matsa sai ta saka mata kuka lallashib ta yayi tai shiru sannan ya bata magani tasha sannan ta koma ta kwanta.

Yana zaune a gaban ta yace

“Me yake miki ciwo yanzu”

“Kaina ne baki na ba dadi!”

“Sannu!”

Likitan da ya duba ta jiya da dare me ya shigo da sauri Aliyu ya mike yana fadin

“Doctor kan ta bai daina ciwo bafa.”

Karasowa yayi yai mata tambayoyi sannan yace

“Ki daure kici abinci.”

“Baki na ba dadi bana so ci.”

“Ohk!”

Ya fita ya dawo yace ta hau gado. Ruwa ya kara saka mata sannan ya kalli Aliyu yace

“A samar mata soft abu like fruit ta dan sha.”

“Ok!”

Nan ya duba Aliyu yace

“Aboki na jinin ka ya sauka komai normal fa.”

Aliyu yai murmushi kawai.

Karfe sha biyu su Mama suka zo, suna shigowa suka samu Aisha akan gado tana bacci hannun ta ana mata karin ruwa. Aliyu da ya fito daga toilet ya durkusa ya gaisheshi suka amsa suna mata ya jiki ya amsa sannan Mamah tace

“Ya jikkn nata ashe bata ji dadi ba.”

“Walahi Mamah matsalar ma bata son cin abinci yanzu ma fruit Doctor yace a samar mata ko soft abu da an kawo mata youghurt ma.”

“Ok bari na fadawa Usman”

Ta fada tana daukar waya nan ta fada masa ba ayi awa daya ba ya shigo da manyan ledoji. Nan ya ajiye Mamah ta bude taga fresh milk ne da yoghurt sai fruit din. Gyara mata tayi sannan ta ajiye.

STORY CONTINUES BELOW

Karfe daya ta farka bayan Aliyu ya zare mata ruwan da ya kare tana ganin su Mamah ta mike tayi kasa da kanta ta fara gaishe su. Suka amsa suna mata sannu sannan suka fita. mamah ce ta taimaka mata ta shiga ta kuskure bakin ta ta dawo da ita ta ajiye ta ta dauki kankanar da ta gyara ta fara bata. Aliyu ne ya karaso ya amshi bowl din yace

“Bari na bata Mamah.”

Yana amsa ta mike suka fita ita da Abbah suna fitowa Su Yaa Muhammad suka shigo da Faisal  dakin suka shiga Aisha na ganin Yaa Muhammad ta kura masa ido hawaye ya cika idon sa.

Karasowa yayi yace

“Menene?”

“Yaya kaina!”

Ta fada tana kamo hannun sa.

Hawayen idon ta ya goge yace

“Zai daina kinci abinci”

Kai ta girgiza. Ya bata fuska yace

“Kinga matsalata dake ko?”

Ya nufi kayan  abinci da suka kawo ya zubo mata ya mikawa Aliyu da suke gaisawa da Faisal. Bayan sun gama Faisal ya kalli Aisha yace

“Madam ya jiki?”

“Da sauki.”

“Allah kara sauki.”

Aliyu amsar bowl din hannu Yaa Muhammad yayi yace

“Bata maza kici haka zakina zama ba zakici abinci ba”

Baki ta tabe zatai kuka yace

“sai fa kinci.”

Aliyu yace

“Ai mata a hankali.”

“Bafa ta son cin abinci kana ganin ra gata nan.”

Yai murmushi yace

“Zaki ci?”

Yaa Muhammad ta kalla taga ya balla mata harara dan haka ta gyada masa kai duk dan ta wanke laifin ta a wajen sa.  Cokali uku tayi tace ta koshi. Fruit din ya bata ta dan sha.

A ranar su Yaa Abubakar da Yaa Usman da Umar da Farouk suka koma,  sai ya rage daga Faisal sai Yaa Muhammad.

Jinya sai ta juye kan Aisha dan sai da ta kwana uku tana amsar karin ruwa da maganguna sannan ta danji dama dama. Tana mamakin yadda aka barsu daki daya Da Yaa AK. Duk da ba sanin yadda suka bacci tayi ba dan sai ya raba dare sallah yake kwanciyya da asubar fari kuma ya tashi. Sai dai ta ganshi akan sallaya ko kan kujera.

Kulawa take samu sosai daga Abbah da Mamah har da Yaa AK ma sosai take mamaki. Hajara dai da ta shigo ta duba sa take fita ta zauna a falo ita da ta kara shiga sai in zasu tafi.

Ranar da su Aisha sukai kwana hudu da zuwa su Momy suka zo tare da Sha’awa da su Yaa Abubakar da iyalan. Su sunyi farar dubiya domin ba wanda zaiga Aliyu yace yai jinya dan har yayi kumari abun sa to ya samu burin zuciyar sa. Matan su Yaa Abubakar ne suka samu labarin Aisha sai sannu suke mata suna nan nan da ita.

Momy da sha’awa kuwa da suka ganta sai suka ga kamar yar uwar Mamah dan yadda suke kama. Tinda suka zo Sha’awa da Hajara suka dinke suna makale da juna.

Washe gari ma ko asibitin basu leko ba. Kwanan su biyu suka juya. Lokacin Aisha taji sauki ragal dan kuwa ta gudu gida ta bar kwanan asibiti ranar data tafi bai sani ba sai da su Mamah zasu tafi yace tana ina aka ce sun tafi da Maryama daru ya saka musu kamar karamin yaro shima sai ya bisu da kyar suka lallashe au. Ranar kuwa kasa bacci yayi sam. Ai kuwa washe gari ya tada balli shi ya warke a sallame au. Ba yadda suka iya haka suka bashi sallama suka daura shi akan medication na sati daya kan suga ko zaiviya tafya gida gaba daya.

*

Suna gida Maryama da Aisha suna hada abinci zasu taho dashi asibiti suka ji dawowar su. Da gudu Maryama ta fito tana ganin Yaa AK ta fada jikin sa tana murna shi kuwa sai baza ido yake yaga ta ina zai gano Aisha.

Aisha kuwa tana kitchen ta kasa fitowa dan riga da siket ne yan kanti Maryama ta bata ta saka sababbi a jikin ta gashi ba hijab yana daki. Maryama ganin yana ta leke leke yasa yace

“Ya dai Yaya?”

“Ina Matata?”

Baki ta rufe da hannu ya dan harare ta. Tayi kasa da murya tace

“Tana kitchen.”

Ai zumbur ya mike ya shiga kitche din tsaye ya same ta juyawa kofa baya a hankali ya karaso ya karasa bayan ta ya rungume ta tsorata tayi jin jikin ta a jikin mutum. Tana kokarin ta jiyuyo taji kamshin turaren sa. Ajiyar zuciya ta sauke yace

“Shine kika gudu kika barni to na biyo ki.”

Sakin ta yayi ta juyo tace

“Ina kwana?”

Jin bai amsa ba yasa ta dago ai sai taga kura mata ido yana kallon ta da sauri ta juya masa baya tana jin wata matsanaciyar kunya. Sai da ta juya sannan ya dawo cikin haiyacin sa. Kan sa ya shafa ya matso ta bayan ta yace

“Yavjikin ki Aysherrr!”

Yadda taji maganar har tafin kafar ta tace

“Uhm Alhamdulillah. Ina kwana ya jikin?”

“Naji sauki Aysher nagode da kulawar ki zuwan ki ya zama magani gareni.”

Bata juyo ba ganin haka yasa ya leka fuskar ta. Idon ta a runtse yake. Yai murmushi ya girgiza kai yace

“Zan shiga daki ki kawon wani abu kinji?”

Kai kawai ta gyada ya juya ya fita. Yana fita ta sauke ajiyar zuciya ta juya ta nufi dakin su da sauri ta dauki hijab ta sakata ta nufi falowa taiwa su Abbah sannu da zuwa.Kitchen ta koma ta samu Maryama na karasa hada abinda suke yi. Tsayawa tayi Maryama ta juyo tana kallon ta tace

“Menene?”+

“Uhmm daman daman Yaa AK ne yace na kai masa wai wani abu!”

“Wani abu kamar me?”

Hannu ta daga tayi alamar bata sani ba. Murmushi Maryama tayi tace

“Oh toh!”

Sannan ta hada mata abu a jug da cup ta bata. Har ta amsa ta juya sai ta juyo tace

“Yana wane dakin to?”

“In kin shiga corridor dakin dake karshe ne nasa.”

“Toh!”

Ta juya ta nufi dakin da yake. Yana shiga ya wuce bandaki ya watsa ruwa sannan ya fito dauke da towel yana shafa mai. Gajeren wando ya saka da singlet yana shafa turare yaji knocking din ta. Karasawa bakin kofa yayi ya bude hannun ta dauke da plate da jug da cup akai. Hanya ya bata ita kuma ta zata amsa zai yi gani tayi ya juya wannan yasa ta bi bayan sa ta ajiye a kasa sannan ta mike zata fita.

“Aysher!”

Tsaya tayi tace

“Na’am!”

“Zo!”

Juyowa tayi ta karaso ta tsaya daga nesa dashi. Hannu ya sa ya kamo hannun ta sannan ya zaunar da ita agefen sa.

Hannun ta yake murzawa a hannun sa yana kallon yadda tayi kasa da kanta.

“Ya jikin naki”

“Uhm uhmm naji sauki.”

“Kin tabbata?”

Kai ta gyada. Yace

“Yanzu ba abinda kike ji?”

Kai ta gyada hannu yasa ya dago kanta ta suna hada ido ta runtse idon ta. Fuskar sa ya kai saitin fuskar ta, kofar dakin aka budo wannan yasa ya dago yana kallon waye.

Hajara ce tsaye tana kallon su. Aisha ma ido ta bude ya juyawa taga Hajara da sauri ta mike ta nufi kofa,  hanya ta matsa mata ta wuce tana mata wani kallo sannan ta shigo tana kallon Aliyu da yake shafa kai. Shigowa tayi tace

“Wacece wannan ne? Me yasa ta shigo dakin ka?”

Fuska ya hade yace

“Ni dai ba fasiki bane kinsani ko?”

“To wa ya sani tinda ba gidan mu daya ba.”

Mikewa yayi a zafafe ya kaiwa bakin ta bugu take ta dafe bakin ta saki kuka dan yadda taji zafin bugun.

“Iyaye na ba fasikai bane kuma nima haka kada ki kara halakan tani da fasikanci in ba haka ba zaki gane kuranki. Nonsense get out from my room.”

A duke ta fita ta shiga dakin ta. Tana karasawa gaban mirrow taga jini a bakin ta.

“Allah ya isa!”

Ta fada ta shiga bandaki ta wanke bakin ta.

Kan gado ta dawo ta kwanta tace

“To wace wannan yarinyar ko yar uwar sa ce amman dan me vansani ba su Momy ma basu santa ba.”

Tsaki ta saki dan ita kanta ji tayi ta tsani yarinyar.

*

Aisha na fita ta shige dakin su. Kwanciyya tayi a kan gado gaban ta na dukan uku uku tana kwance bacci ya dauke ta. Karfe biyu saura Maryama ta shigo tayi mamakin ganin ta a dakin dan ta zata tana wajen Yaa Aliyu. Zama tayi ta fara tashin ta dan lokacin sallah yayi. Ido ta bude a hankali. Maryama tace

“Yaushe kika dawo?”

.

“Tin dazu!”

“Au ai na zata kin tsaya taya shi hira.”

Baki ta tabe tace

“Matar sa dai ta taya shi.”

“Ke kenan!”

Mikewa tayi ta shiga vadaki. Aisha ta bita da kallo tana cewa me kenan. Baki ta tabe bata jima ba ta fito daure da alwala. Mikewa tayi itama tayi alwalar. Sai da sukai sallah sannan suka fita dan yin lunch.

STORY CONTINUES BELOW

Kowa yana dining din Mamah da Abbah sai Yaa Muhammad da Yaa Faisal,  gefen sa Yaa AK ne Maryama zaune a gefen Mamah sai kujera empty guda biyu daya kusa da Yaa AK daya kusa da Faisal. Karasowa tayi ta zauna. Mamah tace

“Ita Hajarar fa?”

“Tace ta koshi.”

Maryama ta fada. Serving nasu Maryama ta fara Momy ta mike ta shiga dakin Hajara. Kwance ta same ta a kan gado tace

“Hajara me kika ci kika ce kin koshi.”

“Mamah na koshi ne kawa.”

“To ko wani abu kike so?”

“A’ah!”

“Shikenan!”

Mamah ta fita ta zauna ta fara cin abinci. Kasa ci Aisha tayi. Yaa AK da ke kusa da ita ya dan tabo kafar ta dagowa tayi tana kallon sa ya dan kanne mata ido ya dage mata gira. Kai ta dauke.

Matsowa yayi wajen kunnen tavyace

“Ko na baki a baki?”

Da sauri ta dago tana zare ido. Ya dannen dariyar sa yace

“Eh kici ko nai miki dura Allah!”

Spoon ta dauka ta fara ci a hankali a hankali. Mamah da Abbah ne suka mike suka bar wajen. Suna tashi Yaa Muhammad da Faisal ma suka mike. Maryama kwanukan ta kwashe ta kai kitchen.

Mikewa tayi yai saurin kamo hannun ta kallon sa tayi yace

“Sit!”

Zama tayi yace

“Maza kici abincin ki!”

“Na koshi fa.”

“Ki dada me kika ci?”

“Ai daman ba yunwa nake ji ba.”

Spoon ya dauka ya debo mata, ya kai bakin ta hannu tasa zata amsa ya girgiza mata kai yace

“Bude bakin ki.”

Ido ta rufe ta bude ya zuba mata. A hankai take taunawa,  sai da ta cinye ya kara debowa ya bata. Sai da ya bata spoon biyar sannan tace

“Allah na koshi Yaa AK!”

Ta fada kamar zatai kuka. Lemo ya zuba mata ya mika mata. Amsa tayi ta sha sannan ta kwashe plate din tayi kitchen.

*

Karfe bakwan dare ta fito daga wanka. Doguwar riga ta saka ta dauki hijab ta saka. Maryama ta gani tace

“Ina Yaa Muhammad?”

” Suna compound!”

Fita tayi ta samu Mamah a falo. Tsayawa tayi tace

“Sannu Mamah!”

“Yauwah Aisha! Ina zaki?”

“Wajen Yaa Muhammad zani.”

“Ok!”

Fita tayi ta samu Yaa Muhamnad zaune yana danna wayar sa. Zama tayi a kujerar kusa dashi ta turo baki tace

“Yaya na!”

Juyowa yayi yana kallon ta sai ya dauke kai yace

“ya akayi Kanwata?”

Baki ta turo ya juyo yana kallon ta.

“Me kuma ya faru?”

Idon tane ya fara kawo ruwa take hankalin sa ya tashi. Hawaye take yai tambayar duniyar taki tayi magana yai lallashin ma shiru. Suna cikin haka Yaa AK ya fito shi da Faisal. Yana fito idon sa ya fada kan Aisha dake goge idon ta. A hankali ya karasa wajen ya durkusa a gaban ta yana fadin

“Menene?”

Kai ta girgiza Ya kalli Yaa Muhammad yace

“Me ya same ta?”

“Taki tai magana sai kuka kawai.”

Dagowa yai yana kallon ta da idanun sa, sai ya mike ya kama hannun ta kawai sukai cikin gida. Mamah suka sama a falo ta bisu da kallo. Bedroom dinsa ya shige da ita.

Zaunar da ita yayi a gefen gadon sannan ya durkusa a gaban ta yana fadin

“Aysher ki fada min me yake damun ki?”

Kai ta hau girgizawa yace

“To menene kike kuka?”

“Ni kawai bana jin dadi.”

“To me kike so?”

Kai ta hau girgizawa. Murmushi yayi ya daga ta tsaye ya hugging nata yana fadin

“Bana son inganki kina kuka Aysher na ki fada min me kike so?”

Kai ta kwantar a kafadar sa ta na sauke ajiyar zuciya. Hannu yasa yana shafa bayan ta a hankali yace

“Ki daina kuka kinji ko kina son ki ga Ummah ne?”

Kai ta gyada masa yace

“In kuma na dauke ki daga wajen su fa”

Kafada ta make tace

“A’ah!”

Dariya yayi ya bude baki zai magana kenan aka budo dakin. Shine ya juyo yaga Hajara tsaye a bakin kofa. Kai ya dauke yace

“In na dauke ki sai kin shekara bakije wajen su ba.”

STORY CONTINUES BELOW

Kafada ta make.

“Ina son magana da kai yallabai.”

Hajara ta fada tana daga bakin kofa.

Bai kalle ta ba yace

“In kin koyo sallama sai kizo muyi maganar.”

Juyawa tayi a fusace ta rufe kofar sannan tayi knocking ta bude tana sallama. Amsawa yayi ya ajiye Aisha a gefen gadon ya kalle ta yace

“Ina jinki?”

“Uhmm ta bamu waje mana.”

“Akan me?”

“Zanyi magana da miji na.”

“Itama mijin tane ai!”

” kamar ya?”

Hannu ta ya kama suka fita a dakin. Aisha kuwa kai ta jingina da gadon tana sauke ajiyar zuciya. Zuciyar ta ce ta cika da rudani na abubuwa da yawa. Tana son Yaa AK amman kuma ba zata iya cewa bata son Yaa Muhammad ba.

Tana cikin tunanin nan ya shigo dakin. Mikewa tayi a hankali tace.

“Sai da safe!”

“Zo nan!”

Ya fada yana kamo hannun ta. A gaban sa ta tsaya kan ta a kasa yace

“Ki daina kuka da sa damuwa a ranki Aysher na Allah na tare dake kinji.”

Kai ta gyada yace

“Za a kai ki gun Mamah kinji.”

Nan ma kai ta gyada yace

“Ko da abinda kike bukata?”

Kai ta girgiza yace

“To muje ki kwanta ko zaki tayani kwana.”

Kafada ta make masa. Murnushi yayi yace

“Shikenan muje.”

Yabi bayan ta har dakin su. Tana shiga yace

“Kwanta to.”

Kwanciyya tayi yaja mata bargo yace

“Sai da safe!”

Kai ta gyada ya mike zai fita Maryama ta shigo tana fadin

“Ai na zata acan zaki kwana!”

Ganin Yaa Aliyu yasa tayi shiru. Ta danne bakin ta da hannu. Matsawa tayi ya wuce tace

“Sai da safe.”

Kan gadon tayi tace

“Kai Sister wallahi Yaa AK yana son ki sosai.”

“Saboda me kika ce haka?”

“Hmm bai da magana tinda muka zo garin nan sai na Yaushe zaki zo. Kullum fa. Kan ki zo kwanan sa nawa a kwance bai ko bude ido ba zuwan ki yasa ya mike gashi daga zuwan ki ya warke. Kinsan waye kuwa Yaa Aliyu. Tab miskili ne amman jibi yadda yake miki akan ki yanzu bai kunyar yayi abu ko kadan wallahi Yaa Aliyu yana son ki,  ki taimaka ki so shi ko rabin son da yake miki ne.”

Murmushi kawai Aisha tayi ta gyara kwanciyya kamar ba zatai magana ba sai tace

“Ina son sa amman kuma Yaa Muhammad fa?”

“Wane Yaa Muhammad din? Yanzu fa ke matar wani ce ki daina kiran Yaa Muhammad ki cire shi a zuciyar ki.”

A zabure ta mike zaune tana fadin

“Kamar Ya?”

*

**

***

****

*****

******

*******

*

Sirttng room ta nufa kirjin ta na bugawa ta rasa ko saboda menene tana isa tayi sallama a kofar dakin yana daga ciki ya amsa. Labulen ta daga ta shiga kan ta a kasa.

Tin da ta shigo yake binta da kallo har ta samu waje ta zauna.

“Ina yini?”

“Lafiya lou Fateemabya kike ya gida?”

“Alhamdulillah!”

“Meyake faruwa Fateema?”

Tai shiru. Mikewa yayi ya dawo gaban ta ya zauna a kasa gabanta. Da sauri ta dago dan ba abinda ta tino sai Fu’ad lokacin da Dady ya rasu yana lalashin ta.

Kai ta kife akan cinyar ta ta saki wani kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Zama yayi a kasa ya dafe kansa. Sun jima a haka tana kuka shi kuma yana sauraron ta amman yadda yake jin kukan nata tamkar ana zuba masa ruwan dalma a jikin sa. Sai da yaga ba zata daina ba sannan yace

“Dan Allan Fateema ya isa haka me akai miki kike kuka shikenan ke kenan kuka haba Fateema wa yace miki rayuwar ki dan mutum daya take rayuwar ki tana da mahimanci ga mutane da yawa ba daya ke likita ce ko alumma suna da hakki kula akan ki tinda kina da ilimi akan haka sannan iyayen ki kannen ki yan uwanki da masoyan ki wa yace miki a duniya mutum yana da masoyi daya ne babu Fateena kina da masoya masu san ki dan Allah ki daina wannan ki saki ranki ki samu kema wanda zai baki farin ciki. Gushewar mutum daya a rayuwarki ba shine zai rusa miki farin ciki ba baki san a lokacin da ka rasa wani abun Allah sai ya sauya maka da wani ba. Haba Fateema wannan fa jarabawa ce Allah yake miki yana daga cikin kaddarar ki ki daure ki cinye jarabawar nan zaki samu sakamako mai kyau. Kuma Allah ba dan baya son ki bane ya jarabce ki dan ya gwada imanin kine. In kana abu Allah bai jarabce ka ma sai ka tsaya ka duba anya kana yin komai dai dai kuwa dole akwai ta idan Allah ke jarabar mu. Ina mahaifin ki ne ya rasu da ya rasu kin daina rayuwa ko kin tagayyara to ki dauka tafiyar Fu’ad ma ba zai rusa miki farin ciki da rayuwa ba. Kila Fu’ad ba alheri bane a rayuwar ki,  kila wani alherin ke tinkarar ki Allah ya dauke sa. Dan Allah Fateema kiyi amfani da ilimin ki, ki mika komai ga Allah insha Allahu Allah yana tare dake kuma ba zai taba barin ki,ki tozarta ba da izinin Allah. Bama wannan ba yanzu in yau Fu’ad ya dawo shin me zaki masa Fateema ba aure fa a tsaknain ku kinga kenan yaya dan haka mafita a rayuwa shine ki mika komai ga Allah kina addu’a Allah zaba miki mafi alheri da sannu Allah zai amsa addu’ar ki ya baki abunda yake alheri wanda baki taba zata ba. Kiyi hakuri ki daina kukan nan.”

STORY CONTINUES BELOW

Jikin ta ne yai matukar sanyi dan haka ta dago tana goge idon ta. Kallon ta yayi yace

“Ki daina kukan kinji.”

Kai ta gyada tana mai cigaba da goge idon nata sai da ta gama sannan tace

“Nagode Uncle Allah saka da alheri.”

“Ba komai Fateema. Me yake damunki?”

“Uncle na shiga tashin hankali dis two days gaba daya na rasa komai komai ya tsaya min na kasa tunanin komai na rasa ya zanyi komai na mika komai ga Allah kuma a sannu na fara samun sauki da sanyi a zuciya ta.”

“Masha Allah. Allah ya dauwamar miki da wannan sanyin da saukin har karshen rayuwar ki.”

“Amin.”

Sukai shiru sannan tace

“Uncle ana so a rabani da Fu’ad ta karfi da yaji.”

“Tayaya?”

“Wai Uncle Aminu ne zai min aure.”

“Wa ya fada miki aure da zaki zai rabaki da Fu’ad Fateema. Indai son da kikewa Fu’ad na gaskiya ne ko da kin auri wani ba zaki taba rabuwa da Fu’ad ba,  ba ina nufin zaki ta tunanin sa da jin soyayyar sa ba a’ah zakina tunashi lokuta da dama wanda wannan tunawar zata sa kina masa addu’a soyayyar gaskiya kenan wacce ko mutuwa mutum yai ko bai bar baya ba in ka tuna shi zaka na masa adsu’a toke ma haka zata kasance  amman rabaki da Fu’ad sai Allah  ko mutuwa.”

Kallon sa take yace

“Dan haka kiyi hakuri ki amshi abinda Uncle ya kawo miki nima zan je wajen sa kika sani ko dani za ai?”

Hararar sa tayi ta rufe fuska hawaye na kawo mata.

“Ki daina wannan kuka Fateema wallahi har cikin bargo na nake jin sa. Bana so kukan ki Fateema please ki daina.”

Share hawayen ta tayi yace

“Yanzu wannan yasa kika daina zuwa aiki da daukar wayata?”

“So kake naje aiki nayi kisa na dinke wani abu a cikin mara lafiya. Kwata kwata bana hayyacina.”

Murmushi yayi yace

“Hmmm wayar ki fa meyasa bakya daukar call dina duk kinsa na shiga damuwa.”

Dagowa tayi ta kalle shi suna hada ido ta dauke kai kawai. Yace

“Uhmm?”

“Bansan inda wayar take bama ni tana silent shiyasa!”

“Amman kinsan zan kira ai.”

“Naman ta komai da kowa Uncle.”

“Har ni?”

Murmushi kawai tayi. Yace

“Ni dai ina son a bani wani special place in ur heart!”

“Haba ai u have it wa nake kulawa sai kai fa ban taba mu’amala da wanda ban sani ba daga Fu’ad sai kai!”

“Gud a sannu zan samu matsayin sa kenan.”

“Da wuya Uncle abin bana wasa bane ai.”

“Saboda me kika ce haka.”

“Mun dauki shekaru fa dayawa since ina yarinya tin shekaru goma sha fa!”

“Ni kika san iya rayuwar da zamuyi tare.”

“Haka ne but shi aikasan tun yarinta fa.”

“Ni kuma tin yanzu har tsufa insha Allah.”

“Allah yasa to.”

“Amin. Amma ji yadda kikaa rame kina cin abinci kuwa?”

His statement is similar with Fu’ad’s Statement always why so? Abinda take yawan tambayar kan ta. Abubuwa da dama suna mai maita kansu in Aslam yai mata abu sai taga kamar Fu’ad. Shiru tayi yace

“Fateema!”

Amman shiru ya kara kiran ta shiru. sai da ya kira ta sau uku sannan ta dago a firgice. Yace

“Tunani kuma tunanin me kike?”

“Nothing me kace?”

“Kina cin abinci kuwa kalli yadda duk kika rame fa.”

“Hmm ina ci mana.”

“Ni ban yadda ba tashi mu fita ko zaki samu some fun!”

“Uncle am not interested!”

“Saboda kin fiso ki ta zama da damuwa ko?”

“No…”

“In ba haka bane ki tashi muje kije ki fadawa Momy ina waje ina jiranki.”

Yana fada ya fita. Mikewa tayi tabi bayan sa yai parking space tayi cikin gida. Momy da Baba na zaune a falo ta shiga da sallama. Suka amsa. Tsayawa tayi ta kasa magana Momy tace

“Lafiya?”

“Uhmm daman Uncle ne wai zan rakashi!”

“To Fateema ki dai kula da kanki.”

“Insha Allah!”

Ta fada tana juyawa. Sai kuma ta juyo tace

“Ina Yasmeen?”

“Tana ciki tana homework.”

Juyawa tayi ta fita kawai a bakin mota ta same shi tana karasowa ya zaga ya bude mata tsayawa tayi yace

“Menene?”

Kai ta gurgiza yace

“Bismillah to.”

Shiga tayi ya rufe ya zagaya. Motar ya tayar sannan suka fita wani park ya kaita suka dinga zagaye wajen har da hawa su lilo sosai ya sa ta sake ta samu farin ciki wanda ita kanta taji sauki sosai a ranta bayan sun gama suka koma aka kawo musu ice cream nan suka sha anan suka taho yaiwa Yasmeen tsarabar sa da Alwala kala kala. Gida ya kai ta sannan sukai sallama suka tafi.

*

Aslam ne zaune a gaban Dad din sa. Bayan Alhaji Yahya ya gama shan furar sa ta gado ta dare ya kalle shi yace

“Ya akai yi ne Baba na.”

Kai ya dan sosa yace

“Dad ni wallahi gani nake kamar time din bikin nan yai yawa lokacin yaki yazo.”

Murmushi Alhaji Yahya yayi yace

“Kai Babana wata biyun ne yai yawa ai kamar yau ne ka kwantar da hankalin ka a sannu zakaga lokacin yayi ba kyau gaggawa fa.”

“Allah Dad ina tsoron rasa tane.”

“Bata son ka ne?”

“A’ah kada dai wani yazo ya dauken ita.”

“Ka kwantar da hankain ka in hakan ya faru kasa a ranka wannan ba rabon ka bace. Amman ina maka fatan ta zama rabon ka in Alheri ce in ba alheri bace kuma Allah ya sauya maka da wata. Ya baka ya’ya masu albarka.”

“Amin Dad nagode Allah kara lafiya da nisan kwana.”

“Amin amin!”

Yayi kasa da kai alamar girmamawa yace

“To Dad ni za tafi sai da safe.”

“To Babana Alah tashe mu lafiya.”

Ya mike ya fito. A falo ya samu Jidda ita da Nur suna hira. Jannah kuwa na danne danne a wayq. Dakin Momy ya shiga zai mata sallama ta kalle shi tace

“Ya dai Aslam?”

“Momy auren nan nake so a dawo dashi kusa amnan Dad yace da wacan lokacin da wanda za a saka duk daya ne kada nayi gaggawa.”

“Haka ne. Kai meyasa kake son a matso dashi.”

“Kawau Ni Momy na matsu naga na aure ta ne yarinyar tana bukatar kulawar miji dan ta samu ta rage damuwar ta ta samu nutsuwa da farin ciki.”

“Kayi hakutin kamar yau ne gashibmunci dayi biyu. “

“Shikenan ya batun lefen?”

“Jibi zasu dawo ma sun gama komai.”

“Masha Allah sai me kuma?”

“Ba komai ka barshi in akwai ma zan bayar.”

“No momy ai kinyi a na Jidda wannan kuma nima abarni nayi.”

“Kada ka damu ai da akwai ne kuma kasan Fateema ‘yata ce.”

“Hakane Mom Allah kara arziki ni zamu tafi. Sai da safe.”

“To Allah bamu alheri.”

Suka fito tare. Ya kalli jidda yace

“Muje ko?”

Yayi waje sallama tayiwa Momy  sannan ta shiga tayiwa Dad sannan sallama ta fito su Nur suka rakota wajen mota suka shiga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *