BABBAN GORO BOOK 2 CHAPTER 10 by sumayyah Abdulkadir
Da ta ga za ta yi kuka sai ta yi maza ta shige bukkar Badijo, sai kau da kai yake wai shi ya yi fushi. Ita kuma tana binshi da kallon ka yafe ni. Ita kanta Inna sha’awa suke bata, da ta ga Marwah ta manta da suyar ta sun shige bukka da dansu a hannunsu, sai ta fito tana karasa mata.
Yau da dare Rugar Ardo ta yi tsit, duk al’ummar rugar sun ya da hakarkarinsu kasa, shakuwa ta damu Badijo.
Har ta tashi Inna ta bude randa ta debo ruwa ta kawo mata shimfidarta, ta tallafo ta tana ba ta ruwan, sakamakon aci bal-bal din an rage ta, ba ta ankara da cewa ruwan dawowa yake yi ba. Tuni Mai kowa da komai Ya amshi abinSa. Da ta ji shiru tsammani ta yi ta koma barci, sai ta kwantar da ita ta koma shimfidarta.
Anisa ma ta tashi tana zaune dungurgur ta rasa me ke damun ta? Ta rasa inda za ta sa kanta da soyayyar dan’uwanta.
Ita ma Inna kasa komawa baccin ta yi, ta dauro alwala ta zo ta soma nafilfili tana rokawa ‘yar’uwarta sauki wajen rabbil izzati.
Asuba ta yi sannan ne Anisa ta yo alwala ita ma ta fara bada farali. Ita kuma Inna Binta sai kawai ta dora sallar asubahi.
Gari ya soma haske ya yi dan shaaaa! Haka, basu ji maganar Badijo ba ko gyaran muryarta.
A ka’ida kuma duk asubah sai ta tashi kowa ya yi sallah, har karfe shida na safe. Inna Binta ta yanke shawarar tashin ta.
Kallo daya ta yiwa ‘yar’uwarta ta tabbatar mai
kowa da komai ya amshi abinsa.
Ta ce, “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un!”
Sai ta janyo mayafinta jikin kofar bukkar ta yafa tana hawaye ta nufi gidan Liman ta sanar da shi. Sannan ta dawo kofar bukkar su Marwa, “Dini kun tashi ne?”
Zahraddeen dake sanye da short – nicker din (Adidas) da farar singileti fara sol saboda zafi, ya yayibi zanin matarsa ya rufa sannan ya ce, “Ni ne dai na tashi”.
Ta ce, “To ita ma tashe ta ku fito jana’izar Badijo wa’adi ya cika”.
“Daga Allah muke kuma gare shi zamu koma”.
In ji Zahraddeen. Ya yi hanzarin zura kaftanin shadda a jikinshi da dogon wando, sannan ya soma jan yatsun matarsa.
Cikin barci ta ce, “Na fa yi sallah, don Allah ka barni in dan runtsa”.
Ya ce, “Watarana dukkanmu haka zamu tsinci kanmu a kabari daga barcin safe”.
Ta girgije ta ce, “Me kuma ya kawo zancen kabari saboda Allah?”
Ya ce, “Badijo ta rasu….’
Kafin ya rufe bakinsa ta kai kanta bukkar Badijo daga ita sai rigar barci ko kallabi babu a kanta.
Ta tarar Inna Binta da Abuwa matar Liman suna yi mata wanka, sai ta sulale a gefe za ta fara kuka.
Inna ta ce, “Kul! Tashi maza ki je ki kintsa ki zo mu yi mata karatu kafin maza su taru”.
Anisa tana ta suma ana yayyafa mata ruwa tana farfadowa, amma in ta ga gawar Badijo sai ta
sake sumewa. Don haka aka fita bukkar da ita.
Ta taso ba ta san iyayenta ba sai Badijo, wajen haihuwarta uwarta ta rasu, babanta shine da daya kwal da Allah ya baiwa Badijo. Ita ta raine ta da madarar shanu har Allah ya kawo ta yau inda ta ke.
Ba ta san dangin mahaifiyarta ba saboda Fulanin tashi ne ba zaunannu ba. lokacin da suka aurar da mahaifiyarta gaba suka yi basu tsaya ba tunda ta tubure tana son Haruna, alhalin ba dan rugarsu bane.
Sai da ta yi wayo babanta shima ya rasu, sakamakon wata saniya da ta soka masa kaho a ciki wajen kiwo.
A haka Anisa da kakarta suka rayu, basu da kowa sai Inna Binta, ita ta sata a makaranta tare da Rabi’a, akwai shakuwa ta ‘yan’uwantaka tsakanin Rabi’a da Anisa.
Tun bayan auren Rabi’a Anisa ta dauke kafarta daga Zaria, tana nan tana jinyar Badijo.
To yau hukuncin Allah ya cika a kan Badijo. Jama’a sosai suka halarci jana’idar ta, bayan an kaita makwancinta suka ci gaba da _ karbar gaisuwa har kwana uku.
A ranar sadakar bakwai Inna Binta ta yi umarni ga dattijan rugar Ardo suka daura auren Zahraddeen da Anisa.
A kuma ranar ne suka hada kayansu domin barin rugar. Motar Zahraddeen dake rufe cikin tamfol ta yi kura futuk, yashi ya rufe rabin tayoyinta. Haka ya zage yake wanke motar da kansa ciki da
bai dinta, yasa karfi ya banbarota daga cikin yashi da kwanjinsa, ya yi mata ful tank da fetir din da tuni yayo guzurinsa a but din motar ya soma diban kayan amfaninsu marasa nauyi yana zubawa a boot, irin su mujallu da computer (Ipad), da makullan gidansu, amma ko kayan sakawar da suka yi amfani dasu a bukkokin basu dauka ba.
Zannuwan gado, filallika, barguna da takalmansu duk basu dauka ba sadaka suka barwa iyalan Liman.
Sai da ya gama zuba dukkan kayansu ya dubi Anisa dake gefe kan kunkuru tana mike da kafafu wadda ke nuna babu abin da ya dameta yanzu.
Ya harareta ya ce, “Ke ba za ki dauki komai ba?”
Ta ce, “Komai kai”.
Ta mike ta je ta kinkimo katuwar akwatin karfenta da take amfani da ita tun a makaranta da Ghana Must Go shake da sutturunta ta dire a gabansa.
Sannan ta kinkimo katon kunkurunta shima ta dora a kan akwatin, ta ce, “Suke nan basu da yawa”. Zahraddeen don haushi bai san sanda ya ce,
“Kin ci ubanki bakauyar banza!”
Ta ce, “A’a-a’a! Ubana yana kabarinsa ban san halin da yake ciki ba ka daina zagar min shi”.
Ya kama baki, “To ki rama mana”.
Ta zumbura baki ta turo dankwalinta goshi dogon gashi ya zubo kamar na Larabawa, amma wallahi bai burge shi ba, ganinta ma ya yi ta koma kamar tunkiya.
Daidai sanda Inna da Marwah suka fito yafe da mayafansu, Inna rike da hannun Daddy, suka tadda diramar da ake tsakanin Zahraddeen da amaryarsa.
Ya ce, “Wallahi Inna ba zan saka wannan akwatin karfen mai kama da akwatin ajiyar gawa a boot din motata ba, balle wannan jakar buhun cike da tsummokara, bare kuma kunkuru da ransa”.
Ai kuwa Anisa ta balle da kuka, “Ni wallahi ko ba za a dauki komai ba, ba zan bar kunkuruna ba. Ni na raine shi tun yana karami, na ci da shi na sha da shi har ya zamo abin da nake zama a kai in ji dadi, in dube shi in ga kamar na ga wani dan’uwana a raye”.
Gaba dayansu sai jikkunansu suka yi sanyi, Marwah ta ce, “Don Allah ka barta da abinta”.
Ya ce, “Na ji, amma wadannan shirgin ba zan dauka ba, za su sa motata makalewa cikin yashi da kwazazzabo”.
Inna ta dube ta (Anisar) “Kwashe su ki mayar dasu”.
Ta kwasa ta mayar.
Ya ce, “Dauke shi da kanki ki sa shi a boot din ni ba zan iya ba”.
Ta ce, “Tab! Wallahi ba zan sa shi a boot ya kasa numfashi ya mutu ba”.
Ya ce a ransa, “Wannan ba karamar ‘yar iska ba ce”.
A fili kuma ya ce, “To ya zaa yi kenan? Look ina da abin yi, I’m not tolarating nonesense, sai ki san yadda za ki yi da shi kuma”.
Inna ta ce, “Sai ki dora a kan cinyarki”.
Ta ce, “A’a, kafafuna zan dora a kanshi har muje”.
Zahraddeen sai ya bude mota ya fada bai kara bi ta kanta ba, ya dauki dansa ya aza a tsakanin cinyoyinsa ya tada mota.
Marwah ta shiga gaba, Anisa da (tortoise) dinta da Inna suka shiga baya, yaja motar a hankali ya kure A.C din day a dade bai sha ba. Suka bar Rugar Ardo, jama’arta na daga musu hannu.
Kowa jikinsa na sanyaye, ‘yar takaitacciyar rayuwar da suka yi a wannan waje will foreber remain fresh in their memory.
Sun dandana rayuwa mai dadi, mai sauki da ada basu san da ita ba. Wannan ya kara musu imani da wadatar zuci, hadi da godiya ga Allah a bisa baiwar da ya yi musu wadda bai yiwa sauran ‘yan Adam ba.
“Wannan shine hierarchy of social class….”. In ji Marwah.
“Yan Adam ba daya muke ba, kamar jerin ‘yan yatsu ne wani ya fi wani, kowa da yadda Ubangiji yake son ganinsa.
Ga shi zaman ya kara musu shauki da kaunar juna, ya kuma kawo sauyi cikin rayuwarsu wato karuwar Anisa cikinsu.
Marwah ta dauki hakan a matsayin daya daga cikin kaddarorin da Allah ya rubutawa Zahraddeen, ba don baya sonta ba ko ya gaji da ita ba, ko Inna ba ta sonta ba. Babu daya.
Ita ma mai taya su ce su kula da rayuwar ‘yar’uwarsu da ta zamo dolensu, in dai Zahrad
deen zai cika alkawarin da ya dauka na cewa ko farcenta ba zai kama ba.
(Dariya) ku taya ni ji makarantan Takori, anya? (Murmushi).
Marwah Dan Kasa ta cira kai tana kallon kwazazzabai da shanu na kiwo, wasu na cin ciyawa, wasu na shan ruwa a korama. “Fondest thought!” In ji Marwah. Tana mai kara dayanta Allah a zu
clyarta. 28 KK
A ZARIA Ss un iso yamma likis, kafafun Marwah sun kara kumbura, jikinta ya yi tsami matuka, ta gaji iyaka. Don haka suna isowa Nura ya tarbesu, ya bude musu gate. Amma da ya hango budurwarsa Anisa
sai ya hangame baki yana dariya yana tafa hannuwa.
Ya ce, “Yayi-yayi sarauniyar”’.
Ta balla mai harara, “Ji ka don Allah kullum cikin kananan kaya, kai baka yadda ba Bature, ai duk iya sa kaya abi bayan Yaya Deeni….”. Zahraddeen ya dago a birkice jin abin da ta fada, ya yi saurin taka totur da ya kusa yin gaba dasu yasa giya baya, saura kadan su daki bango saboda firgitar da tasa shi suka yunkuro kamar zasu ci da baka. Itama Marwah ta yi dummmmm….., ba su ce komai ba.
Nura ya bude mata mota ta fito ta kinkimo kunkurunta, tsalle ya yi yai baya, ita ko ta ce me za ta yi ba dariya ba.
Ta ce, ‘““Matsoracin banza, a haka zan aureka kana jin tsoron kunkuru kamar wani mace?”
Ta fada tana mere baki tana kallon shi sama da kasa a raine.
Ya ce, “Oho dai! In ma Yaya Dinin kike hari da matarsa har da dansa, kuma ya fi karfinki wallahi, ni din dai da kika raina nine zan aure ki, don nine daidai ke”.
Ta kada masa cinya, “Sai abi wani sarkin ba Ado ba, ni nan amaryar Yaya Deeni ce, ko Inna?”
Ta juya ga Inna don ta tabbatarwa Yaya Nura ita amaryar Yaya Dini ce.
Ita dai Inna ko kallon su ba ta tsaya yi ba ta shige cikin gida rungume da Daddy a kafadunta wanda ke ta sharar barci.
Zahraddeen ya fito daga mota ya zagaya ya fito da mai dakinsa, Nura ya karaso yana gaishe shi,
sai ya hangame baki yana dariya yana tafa hannuwa.
Ya ce, “Yayi-yayi sarauniyar”’.
Ta balla mai harara, “Ji ka don Allah kullum cikin kananan kaya, kai baka yadda ba Bature, ai duk iya sa kaya abi bayan Yaya Deeni….”. Zahraddeen ya dago a birkice jin abin da ta fada, ya yi saurin taka totur da ya kusa yin gaba dasu yasa giya baya, saura kadan su daki bango saboda firgitar da tasa shi suka yunkuro kamar zasu ci da baka. Itama Marwah ta yi dummmmm….., ba su ce komai ba.
Nura ya bude mata mota ta fito ta kinkimo kunkurunta, tsalle ya yi yai baya, ita ko ta ce me za ta yi ba dariya ba.
Ta ce, ‘““Matsoracin banza, a haka zan aureka kana jin tsoron kunkuru kamar wani mace?”
Ta fada tana mere baki tana kallon shi sama da kasa a raine.
Ya ce, “Oho dai! In ma Yaya Dinin kike hari da matarsa har da dansa, kuma ya fi karfinki wallahi, ni din dai da kika raina nine zan aure ki, don nine daidai ke”.
Ta kada masa cinya, “Sai abi wani sarkin ba Ado ba, ni nan amaryar Yaya Deeni ce, ko Inna?”
Ta juya ga Inna don ta tabbatarwa Yaya Nura ita amaryar Yaya Dini ce.
Ita dai Inna ko kallon su ba ta tsaya yi ba ta shige cikin gida rungume da Daddy a kafadunta wanda ke ta sharar barci.
Zahraddeen ya fito daga mota ya zagaya ya fito da mai dakinsa, Nura ya karaso yana gaishe shi,
sai ya hangame baki yana dariya yana tafa hannuwa.
Ya ce, “Yayi-yayi sarauniyar”’.
Ta balla mai harara, “Ji ka don Allah kullum cikin kananan kaya, kai baka yadda ba Bature, ai duk iya sa kaya abi bayan Yaya Deeni….”. Zahraddeen ya dago a birkice jin abin da ta fada, ya yi saurin taka totur da ya kusa yin gaba dasu yasa giya baya, saura kadan su daki bango saboda firgitar da tasa shi suka yunkuro kamar zasu ci da baka. Itama Marwah ta yi dummmmm….., ba su ce komai ba.
Nura ya bude mata mota ta fito ta kinkimo kunkurunta, tsalle ya yi yai baya, ita ko ta ce me za ta yi ba dariya ba.
Ta ce, ‘““Matsoracin banza, a haka zan aureka kana jin tsoron kunkuru kamar wani mace?”
Ta fada tana mere baki tana kallon shi sama da kasa a raine.
Ya ce, “Oho dai! In ma Yaya Dinin kike hari da matarsa har da dansa, kuma ya fi karfinki wallahi, ni din dai da kika raina nine zan aure ki, don nine daidai ke”.
Ta kada masa cinya, “Sai abi wani sarkin ba Ado ba, ni nan amaryar Yaya Deeni ce, ko Inna?”
Ta juya ga Inna don ta tabbatarwa Yaya Nura ita amaryar Yaya Dini ce.
Ita dai Inna ko kallon su ba ta tsaya yi ba ta shige cikin gida rungume da Daddy a kafadunta wanda ke ta sharar barci.
Zahraddeen ya fito daga mota ya zagaya ya fito da mai dakinsa, Nura ya karaso yana gaishe shi,
ya jarbi jakar Marwah da wayoyin Dinin dake hannun shi ya bi bayansu, hannayensa rungume da kugun matarsa wadda ke cira kafa da kyar saboda kumburi.
A haka suka karasa har kofar falonsu. Nura ya yi azamar bude musu kofar gilashin suka shiga, bai bi ta kan mahaukaciya Anisa ba.
Yadda yake kiranta a ransa. Ta bisu da kallo ta kyabe baki ta wuce wajen Inna rungume da kunkurunta, ta ajiye shi a tsakar gida, ta samo masa ruwa ta ajiye masa, ta bude jakarta ta fiddo cake din da suka ci a mota ta rago masa ta gutsittsira masa, sannan ta shige bandaki ta yi wanka, ta yi alwala ta samu Inna a falo ita da Daddy tana fifita masa shayi, shi kuma yana ta mutsittsika ido alamun barci ya tashi.
Ko kallon yaron ba ta yi ba cike da takaici ta dubi Inna ta ce,
“Saboda Allah Inna kin gani ko? Ya sani na baro kayana yanzu ga shi na yi wanka bani da wanda zan canza dasu”’.
Inna ta ce, “Bari Nura ya karbo miki wurin Maman Daddy kafin a hada miki lefenki’”.
Ta fiddo ido, “Me kika ce Inna? Kayan kishiya zan saka? Tab! Wuce nan wallahi”.
Inna ta dunkule hannu ta sakar mata, “Ungo naki, shashashar banza, ba zan dauki wannan haukan da kike shirin kawo min cikin gida ba.
Tun dazu ina jinki kina ta hauka na yi miki shiru. To wallahi ki kama kanki, ki yiwa bakin ki linzami.
Wadannan masu ilimi ne, in kika ishesu za su yi
barin mahaukaciya dake su kalle ki a dabba, don haka ki nutsu ki san me kike ciki.
Wannan surutun ki daina shi, ki yi biyayya ga wadanda kika taras, don ba sa’o’in wasanki bane ba”.
Ai kuwa sai Anisa ta balle da kuka har da ihu.
“Ni dama na san rayuwata sai Allah yanzu, babu uwa babu uba, babu Badijo waye zai so ni? Na san ni ba kowa ba ce Inna, tunda ubana bai bar min gadon arziki ba.
Dadin abin dai bani na ce ina son Yaya Dini ba Badijo ce, Allah ya ji kanta”.
Ta zube a nan tana ta shirga kuka. Inna ta bude baki ta kasa magana, ta kwasowa kanta abin da zai dagula mata lissafi, ya kawo rashin kwanciyar hankali cikin iyalinta, ya lalata zumuncinta da ‘yar’uwarta dake kabari da babu abin da ba ta yi mata a rayuwarta ba.
Nura ne ya jiyo kukan ya ki karewa ya shigo yana cewa, “Wa ya taba min matata ne?”
Ya zube a gabanta ya dafa kafadunta, da gudu Inna ta rarumo ludayi ta rafka masa a hannu. “Matar auren kake dafawa?”
Har ga Allah shi Nura firgita ya yi, sannan ya soma ja da baya.
Da zuciya daya yake son Anisa, tun tana karama, amma ya yi nauyin baki bai fadi ba sai dai cikin tsokana.
Ya ce, “Inna wa ta aura?”
Ta ce, “Abban Daddy”.
Tunda ya sulale a kan kafafunsa ya dukar da kai bai dago ba, haka zalika ita ma Anisan ba ta
daina kukan Inna ba ta sonta ba.
Wani tunani Inna ta yi, wannan yarinya fa taki ce, amana ce a hannunki, duk wani matsayi da za ki ba matar Dini a zuciyarki bai kai nata ba.
Sai ta matso gabanta ta dagota tana lallashinta. Nura ya ce, “Idan auren ne ba ta so Inna to ni a kwance ayi dani mana? Inna na dade ina son Anisa, wallahi Yaya Dini ba zai taba sonta ba, don ba class dinsa ba ce. Ai BABBAN GORO sai magogin karfe”’.
Inna ta yi mishi dakuwa, “Don kabarin ubanka ka fitar min daga daki, kada ku hadu ku sa min hawan jini.
Yi hakuri Anisa daina kukan, yanzu me kike so ai miki?”
Ta ce, “A dinka min kaya, nima in yi masa kwalliya, ba kayan matarsa ba”.
Duk halin da Nura yake ciki bai san sanda ya fashe da dariya ba.
Ya ce, “Au! Ke kina son sa kenan?”
Ta galla masa harara ta ce, “Wallahi in baka rabu dani ba zan danna maka ashariya. Ni matar yayanka ce, don haka duk shekarun ka na zama yayarka”’.
Inna ta ce, “Kin fadi gaskiya Anisa, tashi ka bar mana dakin mu”.
Anisa da ba a iya mata ta ce, “Ina! Ai ni ba a dakin ki zan zauna ba Inna, gidan mijina za ni, wanda nake zamansa ba ruwana da wata matarsa, yadda take fankama ita matar shi ce, haka nima. Ba ta fini matsayin komai ba, in ta fini arziki, ni kuma na fita kusanci da Yaya Dini, kin san an ce
kuma wata kusan ta fi wata.
In ta fini ilimi, ba ta fini zuciya mai So da Kaunar Yaya Dini ba.!!!
Ke dai Inna dinka min kaya in koma gidan ki yi gefe ki zuba ido ki sha kallo”.
Ta tafa cinya. Nura na ta dariya har da tuntsurawa. Inna ta sassauta murya ta zauna sosai a gabanta.
Ta ce, “Anisa don Allah ki daina irin wadannan maganganun da kike yi, ki daina wannan zakewar, namiji ba a yi mishi haka, wanda yake sonka ma, balle wanda a kan dole ya aure ka.
Mene ne damuwarki da matarsa da kike son lallai sai kin yi kunnen doki da ita? Ki tsaya a matsayinki, ki nutsu in fa har kina son in ci gaba da shiri dake.
Komai dan a hankali ne, kaifin bakinki da wautarki ba su za su baki soyayyar Dini ba, face ya yi miki kallon mahaukaciya, don Allah ki nutsu. Yadda kike marainiya haka itama take, yadda kike amana a hannuna, haka ita ma take. Ubanta ya fi karfin komai a wajena tunda shi ya maida Dinin mutum din da har ya baki sha’awa kika so shi.
Ya yi masa kaunar da ko mahaifinshi na raye iyakar kaunar da zai nuna masa kenan. Ki barni in ji da yadda za ku zauna lafiya ya so ki a hankali kada kisa jinina ya hau.
Ga daki nan na baki kusa da nawa shiga ciki ki kwanta ki huta, akwai sabbin atamfofina da ban daura ba bari in dauko miki’.
Ta mike ta yi daki. Anisa ta ce, “Tab! Ba zan sa
dinkin tsofaffi ba ya kara raina min wayo”.
Inna ta yi salati ta ce, “Wato duk abin da na gaya miki ta bayan kunnenki ya wuce ko? To shi kenan kada ki saka, debo naki masu daudar ki saka yadda za ki fi burge shi.
In dai Dini ne wallahi gaki nan ga shi, na daina magana Allah Ya baki sa’a”.
Nura ya ce, “Wallahi kuwa, Inna kin ga da anyi sakin sai a daura da ni”.
Anisa ta kai mai duka da ludayin Inna ya fice da gudu.
Haka Inna ta kwana da Anisa tana lallashi da ban baki, idan ta bullo ta nan, ita kuma sai ta bullo ta can.
Da Inna ta gaji ta rabu da ita ta hau kulla gidan sauro (net), don ita da jikanta su kwanta lafiya, don ko ya ya sauro ya ciji Daddy sai ya yi zazzabin cizon sauro kamar wanda ya tashi a Turai.
A nasu bangaren, kwana suka yi Zahraddeen yana messeging kafafun ta da suka kumbura.
Da asubah bayan sun idar da sallah ta yanar gizo ya yi booking jirgi da yake da bizarsu a hannu zuwa Paris, inda yake so Marwah ta haihu domin EDD dinta ya nuna saura sati biyu.
Shi kuma hutunsa na wata uku ne sun ci wata biyu a Rugar Ardo. Sunyi sa’a akwai jirgi mai zuwa direct (kai tsaye) Suisra wanda zai tashi karfe goma sha biyun dare na yau, amma ta Abuja Zai tashi.
Don haka ya soma shirin ba tare da ya yiwa Marwah bayanin komai ba, ta dai ga yana ta shirya Trolly, ya kwashi na Daddy ya kai dakin Inna,
lokacin ita Innar tana sallar asubahi. Sai da ya gama komai ya wuce wajen Inna ya tadda tana wuridin da ta saba duk safiya, sai ya samu kujera ya kwanta ya dan mike yana jiran ta karasa.
Anisa ta fito cikin atamfar Inna, ba ta san yana falon ba da brush da makilin din Nura a hannunta ta wuce toilet.
Ta dade tana wanke bakin yana jinta sannan ta fito da alwalarta.
Nan ta ganshi a kwance, dadi kamar ta yi ya ya. Ta ce, “Ya Dini yaushe ka shigo?”
Ya dan dago ido yana kallon ta cikin kayan Inna tana ta yawo a ciki, kafadar rigar na sabulewa yana dariya ya amsa.
“Tun dazu”.
Ta ce, “Ka kwana lafiya?”
Ya ce, “Lafiya lau”.
Ta ce, “To bari in yi sallah sai in yi wanka in yi maka kwalliya”.
Yace, “To”.
Inna ta aje carbinta ta shafa fatiha, haushi da takaicin Anisa yasa ta kasa tuna me _ take karantawa a wuridin.
Da sauri Anisa ta wuce daki ganin kallon gargadin da Inna ke mata. Ta juya ga Dinin wanda ya taso ya ciro Daddy daga cikin net ya rungume shi a jikinsa yana cewa da Daddy,
“It is morming my darling Daddy, Gud morning…open your sparkling eyes and say bye to Dad, he is gonna trabel without you…..kiss me my durling Dad, I’ll miss you…..so much…..
Daga can dakin Anisa ta kasa shiru don haushi ta ce cikin kunkuni.
“Allah dai Ya sa mun je makaranta balle ayi zaton bamu san me ake cewa ba”.
Inna ta daga murya tana cewa, “Magana kike yi ne Anisa?”
Ta kyabe baki kamar Innar na kallon ta, ta ce, “A’a, tadin zuci ne”’.
Zahraddeen ya jita sarai ya dauki Daddy ya shiga bandakin Inna don ya yi mishi brush ya ci karo da audugar always a cikin masai, da alama an So ayi floshing dinta ne ta ki tafiya.
Ai da sauri ya fito, ya leka dakin da take sai ya ga wai kuma tana sallah. To ko Inna ce? Ya ce a ransa.
Kai! Inna ta wuce yin jinin al’ada. Ya kasa shiru ya ce, “Inna a daina sa miki auduga cikin masa, a dinga samun bakar leda ana kullewa ana sawa a shara, in ba haka ba masanki za ta toshe yadda ko anyi floshing ba zai tafi ba.
Sannan a raba toilet, kazami ya dinga shiga na tsakar gida kar a watsa miki kwayoyin cutar bandaki. Sannan jahili shine wanda bai san in ana jinin al’ada ba a sallah ba”.
Kunya duk ta kama Inna kamar ba danta ne na cikinta ba. Anisa kuwa baki bai mutu ba, ta ce, “Oho dai! In ma mun yi kazantar babu yadda za a yi damu mun zama dolen mutum, mun zama duwawunsa dole ya zauna damu.
Ilimin addini kuma ba a fimu ba, domin shi ya gaya mana cewa idan jinin al’ada ya wuce kwana goma sha biyar ayi kunzugu a ci gaba da sallah,
ya zama jinin cuta…… Inna ta daga murya da karfi, “Anisa! Anisa!! Ki shiga hankalinki, waye abokin wasanki a nan da mutane suna magana za ki sako musu carkwadeden bakin ki”.
Shi kam Zahraddeen sai ya fice ya yi dariyarsa mai isarsa, sannan ya dawo dakin ya zauna ya yiwa Inna sallama.
Ya ce, yanzun nan za su wuce Abuja, a daren yau za su tashi zuwa Paris, za suyi wata guda sai Maman Daddy ta haihu za su dawo da Babyn.
Inna ta yi fatan alheri da fatan zawa da dawowa lafiya.
Allah ya so wannan karon Anisa ba ta ce komai ba. Da Marwah ta kintsa a nan ta same su, ita ma a nan ne ta ji zancen tafiyar.
Daddy ya makale babanshi shi sai an tafi da shi. Daga uwar daka suka ji Anisa ta fashe da kuka, gaba dayansu suka yi dakin ban da Zahraddeen, domin sunyi zaton wani abune ya same ta.
Amma me? Da suka dame ta da lallashin me ya same ta, sai ta bude ido jawur ta dubi Marwah, “Ki gayawa mijinki, ban taba yin ZINA ba, ban taba yin MADIGO ba, ina rokon Allah Ya kare ni, da duk zuri’a tad a masu kaunata, ina rokonSa kada Ya sa na yi idan ya tafi ya barni ban san ranar dawowarsa ba……….. ”
“La ilaha illallahu!” In ji Inna.
“Muhammadur rasulillahi…..” In ji Zahraddeen dake falo. (Sallallahu Alayhi Wasallama) inji Marwah.
Sim-sim-sim ya ja dogayen kafafunshi ya gudu,