MASIFAFFAN KAUNA COMPLETE
Tsaye take cikin shagon kafen komputa, tana tsaye agaban kantan shagon tana sanye dawani dogon maroon hijab daya kode sosai yana jamata kasa tana kallon mutumin shagon wani dogon matashi dake zaune kan kujera gaban system yana danne danne a system din, daga gani kasan aiki yake aikin ma hala na yarinyar dake tsaye ne sabida yanda take kallonshi kaman tana hango abinda yakeyi akan system din. Zare manyan oily idanunta kawai take tana kallonshi gabanta nafaduwa tana fargaban karta fadi waec dinan bayan tasan da kyar Baba yabiya mata kudin tazana, batason abinda zaisa bazata shiga koda dan FCE bane, tana cikin dogon tunaninne taga Matashin mutumin yatashi dagakan kujeran dayake kai yay wajen printer dan daukan paper data bullo daga printer, cigaba da faduwa gabanta yayi tana kara zare idanun kaman kwan lantarki, daukan paper yayi yakoma table din yadau katin waec dinta yazo gaban kanta yamika mata takardan yana murmushi yace “congratulations Fatima Zarah an tsallake Waec kinada credit guda shida, 6 credit gareki natayaki murna, Allah ya sanyama takardan albarka” yay maganan yana mika mata takardan, karban takardan tayi da sauri tana kallon takardan tanada C a maths English da sauran important topic din dayakamata science student nadashi, wani wani irin cool charming murmushi daya lobar da dimples dinta duka biyun tasake fararen hakoranta suka bayyana, batai wata wataba tawani irin zube akasa tai sujjada, dariya mai shagon yayi yajuya abunshi yakoma kujeran zaman shi yana dariya yace “wayaga su ustaziya Faty” tashi tayi tana murmushi tasauke yar jakanta da fatar jikin jakan dukta daye tsabagen wahala ta bude zip tasaka takardan da katin ciki sanan ta maida zip din ta zage sanan takalli mai shagon tace “nagode Yaya Habu” juyowa yayi ya kalleta ya kureta da ido ita bamata lurada kallon dayake mataba tajuya tafita daga shagon da saurinta tana tafiya takasa daina murmushi tsabagen yanda take murna kaman ba gobe, ahaka taketa tafiya ita kadai har zuwa anguwan su da yara suka cika layin suna wasa ana ihu ana wasa, wucewa tayi ta shiga cikin wani dan babban gida dakeda dogon zaure, gidan na hayane dake dauke da dakuna biyar, kowani daki falo ne sai uwar daka guda biyu, bayin gidan guda hudu biyu na wanka biyu na kashi General bayi, ga makwarara wajen wanke wanke ga dankararen kitchen dinsu inda kowa ke zuwa yay girkinshi, gidan yaci uban siminti kal kal kaman zaka taka ka zame.