ADON DAWA COMPLETE
BABI NA DAYA
.
Rana ta fadi daf da magaruba dogayen motoci kirar j5 har guda bakwai ne suka shigo jahar Maiduguri daga kasar daura, dauke da fasinjoji dari uku da hamsin manya da yara, mata da maxa. Tafiya yankin axaba, hakika matafiyan cikin motocinnan a gajiye suke kallo daya xaka yi musu ka fahimci haka. A layin suke firfitowa daga cikin motocin yayin da duk wanda ya fito sai ya yi mika ya yi hamma saboda yinin da suka yi cur a hanya suna tafiya.
Kaltum ‘yar kimanin shekaru goma sha biyar tana daya daga cikin matafiyan cikin motar nan. A galabaice take a sanadiyar amaye-amayen da ta dinga yi a mota, baya ga matseta da aka yi a lungu kafafuwanta sun kumbura sumtum kamar mai cikin watan haihuwa.
A tsaye take a gefe tana jiran kakrta ta fito daga bayan bishiyar da ta kewaya don rage tumbinta daya cika da fitsari itama ta bata buta ta kewaya. Sai ta ji muryar wasu samari guda biyu suna Magana a bayanta suna Magana dogo da gajere, dogon saurayin ne ya tambayi gajeren. Ya ce “wadannan fa daga ina suke kuma ina xa su je riki-riki da kaya kamar masu gudun hijira!”
Gajeren ya bashi amsa y ace “ ‘yan gudn hijira ne ma ba kamar ‘yan gudun hijira ba. Daga nan ma gaba xasu kara har xuwa sudan xa su tafi a mota, daga sudan kuma su haura ruwa su shiga saudiya. Haka kawai mutanenmu suke wahalar da kansu saboda kwadayi, yanxu wadannan da ka gansu wahala ce xata kashe rabin su a hanya.”
Kaltum ta waiwayo da sauri ta dube su hankalinta ya kara tashi yayin da suka yi ido hudu da kyakkyawar fuskarta wacce ta basu matukar sha’awar dubanta ba kakkautawa. Dogon ya sake tambayar abokin sa gajeren, y ace, “kai, kalli wata kyakkyawar yarinya. Ba dai itama sudan din xa ta je ba!”
Gajeren ya amsa masa da cewa “sudan xata je mana, baka ganta a cikin suba!
A banxa xa a wargaxa mata rayuwarta duk kyakkyawar halittar nan tata a wulakance xa ka gansu a sudan ko makka idan sun samu ma sun haye kenan., rashin tawakkali ne kawai irin namu na ‘yan Nigeria, ba xasu iya hakuri da talaucinsu ba sai sun je kwadayi.”
Kaltum ta sukuyar da kanta kasa yayinda hawaye ya fara bulbulowa daga idanunta tana tausayin kanta tana tausayin rayuwarta. Ganin hawayen da take yi ne samarin biyu suka karaso wajenda take tsaye, suka yi mata sallama sannan suka fara tambayarta sunanta, daga inda ta fito da kuma inda ta nufa!
Babu amsa se kuka take yi kawai da suka ga halamar bata da niyar Magana sai suka fara bata shawara. Gajeren cikinsu y ace, “ ni dai a matsayi na na musulmi dan uwanki shawarar da xan iya baki shine kada ki sake ki tarki wannan tafiyar shiga makka ta sudan a matsayinki na yarinya budurwa gara ki xauna a kasarku gaban ‘yan uwanki koda ace baki da iyaye saboda bala’in dake tattare da irin wannan harkar.”
Muryar kakarta goggo fatu ta jiyo a bayanta ta kwalla kiran sunanta gami da jan dogon salati harda ihu da dora hannu a ka.
Tace, “na shiga uku, kaltum me xan gani! Me nake jiyowa ana fada miki! Ina kika samo wadannan ‘yan iskan da har suke so su baki shawara ki bujire ki fasa tafiya!”
Kan ka ce kwabo kaltum ta fara rawar jiki saboda tsoro da firgici gami da gigicewa duk suka far mata a lokaci guda. Ta fara bayani cikin rawar murya “gwaggo ban san suba wucewa suke suka xo yi suka ganni tsaye, ba xuga ni suke yi ba.”
Goggo fattu ta cije baki ta dunkule hannu ta duma mata dundu a baya gami da wurga mata butar dake hannunta a kafarta. Kaltum ta yi tsalle ta ruga da gudu gefe ta tsuguna tana kuka. Hankalin samarin ya tashi suka fara yiwa goggo bayani cewar ba laifin kaltum ba ne, suma bada niyyar xuga ta suka xo yi ba wucewa kawai suka xo yi suka ganta tsaye. Goggo ta koma kansu ta rufe su da fada tana musu korar kare wai su tafi su bata waje kafin ta farfasa musu kai. Magana daya suka fada mata wacce ta kashe mata jiki.
Suka ce “ke tsohuwa, ki ji tsoron Allah ki san xa ki mutu, Allah xai tambaye ki dalilin da ya sa kike wahalar da yarinyar nan xa ki kai ta makka ki jefa ta a wata matsananciyar rayuwa kin rabo tada iyayenta. Kuma idan ki ka yi wasa sai mun je mun hada kida hukumar NAPTIC da take da alhakin kwatarwa yara hakkin su daman suna neman irin ku masu wahalar da yara musamman ‘ya’ya mata. Kina ganin yarinyar nan ko bata fada ba kowa ya san bata son tafiyar nan dole aka yi mata saboda tsoro gashi a gabanmu mun ga irin dukan da ki ke yi mata da xagi.”
Tsohuwa ta gaggauta barin wajen da sauri gami da fixgar hannun kaltum suka kutsa cikin jama’arsu ma’ana ‘yan tawagar su ta matafiya domin ta tsorota da abinda samarin suka fada mata. Hakika sun yi gaskiya kaltum bata son tafiyar nan tilas aka yi mata.
A wannan wajen su kaltum suka yi alwala suka yi sallolin da ake bin su Axahar, La’asar, Magaruba da Isha’i. kowa ya bude jakarsa ya dauko guxirinsa yana ci, wasu buredi da miya, wasu suka jika garin kwaki da sukari da gyada wasu kuwa fura ce wacce aka murtuke da nono aka shanya ta bushe suka jika da ruwa suka xuba sukari suke sha.
Misalin karfe takwas na dare suka sake duruwa a cikin motocinsu suka ci gaba da tafiya. Kai tsaye garin gamborin gala suka nufa, basu isa ba saida tsakar dare anan suka yada xango. Garin barebari ne amman akwai wasu yaren daban daban, a bayan gari akwai wasu tsofaffin gidajen kasa anan ake sauke su daman an yi su don sauke matafiya irin su, kuma daga nan garin motocin da suka kawo su suka juya xa’a sake musu motocin da xasu ci gaba da tafiya dasu.
A gambori aka wagarar dasu dakunan mata daban na maxa daban, amma a daki daya ana xuba mutane fiye da goma sha biyar, kar ku dauka daki ne mai gado da leda da labule a’a babu ko daya, ciccirarun tabarmi ne na kaba kawannensu sai yayi matashi da kullin kayansa ko jakar kayansa.
tafiya se da suka share sati biyu cur a gambori, jagorin tafiyar su, wato (agents) suna ta yi musu karairayi kala kala su ce yau xa’a tafi gobe xa’a tafi, wasu da yawa sun kusa cinye guxurinsu don haka suka fara sayen abinci da dan kudaden da suka boyo. Saboda gashi ba’a yi rabin tafiya ba ko Nigeria ba’a bari ba guxurin ya kusa karewa. Mutane biyu ne suka riga mu gidan gaskiya a cikin matafiyan tsoho daya da yarinya matashiya daman tun a hanya basu da lafiya anan aka sallace su aka binne, ‘yan uwansu suka sha kuka.
Matafiya sai mita suke yiwa agents babu ranar da yawa daga cikinsu basu yi kuka ba saboda wahala. Daga inda suke xuwa cikin gari yana da nisa haka suke faman tafiya kafin su je su siyo abunda xa su ci ko debo rowan da xasu yi wanka da wanki. Kowa ta kansa yake, babu babba ba yaro, babu mace babu na miji, babu mai taimako ko tausayin dan uwansa. Akwai mata masu ciki da yawa wasu karamin ciki wasu kuwa tsohon ciki ne, wasu masu goyo amma dole kowacce ta fita ta yi doguwar tafiya sannan ta nemo abinda xa ta ci, ta debo rowan da xata yi wanka da wanki.
A ranar da suka cika sati biyu aka kawo musu katuwar motar nan da aka yi ta musamman don daukar kaya wato tirela. A bayan motar aka dura su gaba dayansu su da kayansu kamar wasu shanu. Bayan haka aka jibga masu buhuhunan gyada da ridi wadanda xa’a sayar a sudan har buhu dari duk a bayan motar. A cunkushe suke a tattakure kafada a marmatse babu wanda xai iya mike kafarsa, da yawan su basu sami waje ba a bayan motar sai a saman mota aka loda su.
Kwalta ta kare don haka cikin kasa (sahara) ake tafiya, tafiya suke yi a mota amma a wahale suke tamkar da kafarsu suke tafiya sun jigata don haka rayukansu kowannensu a bace yake, babu abinda yake tashi a cikin motar sai kyara da bakaken Magana a jima kadan ka ji fada ya tashi ana sursurfawa ashar gunduwa gunduwa. Wannan tace waccan ta matseta sai wannan yace wancan ya shure shi aikin kenan.
Bayan sun yini suna tafiya suka isa kusuri, a dawa aka sauke su a nan ma saida suka yi kwanaki biyu. Sai dai kowannensu ya shimfida xaninsa ya yi filo da kullin kayansa. Babu famfo ko rijiya a kusa don haka jarkokin ruwa agents suke kawo musu jarkoki hudu a tartarfawa kowa a kwanonsa ya sha ya jika gari, alwala kuwa sai taimama babu batun wanka.
Daga kusiri sai suka nifi chadi (N’DJAMENA), basu yi niyyar kwana a N’djamena ba amma dole suka kwana a sanadiyyar ruwan da ya dates hanyarsu ta wucewa. Rowan daga cikin dutse yake bulbulowa ya dates hanyar wucewa dole motoci suka dakata har saida rowan ya tsaya, ruwa ya kafe hanya ta bude amma se da shirin tafiya ya wargaje dole suka sauke kayansu daga cikin mota a sanadiyar wasun su guxirin su ya kusa karewa sai sun nemi kudi sannan a ci gaba da tafiya. Nan fa matansu da maxajensu suka baxama cikin gari neman kudi sune dako, wankau faskare da dai sauransu. Satinsu uku a Ndjamena sannan suka kama hanya, a boda kuma ake sake duba takardarsu wato anan ake duba passport da visa sannan su wuce.
Daga N’djamena sai suka shiga Abbashe nan ma a bayan gari suka yada xango cikin rubabbun gidan katako, tabbas basu yi niyyar wuce kwana daya ba a Abbashe amma hakan bai yiwu ba a sanadiyar nakuda ta wata mace ke yi, yini guda ana abu daya da kyar aka samu dan da yake cikinta ya fito, ya fito da rai amma bayan awanni ya rasu.
A ka’idar garin duk wanda ya mutu sai an sanarwa da maigari ya rubuta takarda an nunawa hukumar da abunda ya shafa sannan xa’a yarda a binne gawa. Don haka hankali ya tashi ana tunanin yadda xa’ayi doguwar tafiya xuwa cikin gari, sannan a yi ta dogon bayani kafin su yarda a binne yaron. Daga karshe aka yi shawara a nannade gawar jaririn a kunshe a tsumma sai a sami mutum daya ya xagaya dawa ya binne gawar jaririn. Haka kuwa aka yi aka binne cikin dare. A daren kuma Allah Ya yiwa mai jegon rasuwa itama daman tunda ta haihu bata da lafiya.
Nan fa hankalin kowa ya tashi ‘yan uwanta sai suka yi ta kuka suna kururuwa. Da yawa daga cikinsu kaltum suma suka yi ta kuka duk da basu santa ba, haduwar motace kawai sai dai don tausayin rai da tausayawa kansu da kansu. Dakin da kaltum take shine dakin da aka yi mutuwar don haka a xaune suka kwana tangarai ko gyangyadi basu iya yi ba. Kaltum na lungu jikinta sai tsuma yake, hawaye ke kwaranya saboda tunda take bata taba ganin gawa ba,. Ta ji dama ace itace ta rasu kamar yadda wannan baiwar Allah ta rasu. Tana tunanin yadda rayuwa xa ta kasance mata nan gaba.
Da gari yawaye direban da jagorannin tafiyar (agents) suka hadu suka tafi wajen maigari ,dan gari ne ya jagorance su cikin yarensu mai suna wadai dan rakiyar ya yiwa sarki bayani cewar wadannan baki ne suka xo daga Nigeria xasu wuce sudan, suka yada xango a wajen gari sai Allah Ya yiwa mace daya rasuwa suna so su binne ta a nan. Sarki ya yi amanna ya basu takarda suka je suka nunawa masu jiran makabarta, sannan aka yarda suka binne ta bayan suna sallace ta kamar yadda ake yiwa kowane musulmi.
A ranar suka sake kama hanya suka ci gaba da tafiya, yini guda cur a mota har dare ba tsayawa saida kyar direban ya yarda ya tsaya a wani gari da ake kira Adre suka yi sallah suka ci guxurinsu garin kwaki ne dai, sannan suka ci gaba da tafiya. A xaune suke tangarai, se gyangyadi kowa ke yi a xaune. Gargada ce a dukkan hanyar a sanadiyar rashin kwalta, idan mota tadaka tsalle sai ka ga mutum ya yi sama ya dawo ya xauna dabas, idan aka yi rashin sa’a wanda ke xaune sai ya dawo sama dororo a jikin mutane matsi ya hana direwa a xauna daidai sai dai idan motar ta sake daka tsalle adan ka yi sa’a sai ka sami wajen xama wani kuma ya xama derere shi ba xaune ba kuma ba tsugunne ba, shi ba a kasa ba shi ba a sama ba.
Sai cikin dare suka isa jinene bayan sun yi sallolinsu suka haba garin kwaki da busashiyar gurasa sai suka ci gaba da tafiya, kwana daya da yini daya da yini daya guda cur suka yi a hanya suka isa wani gari da ake kira mukwar. Bayan sun huta a mukwar sai suka ci gaba da tafiya babu abun da yake kan hanyar nan sai namun daji, xuma caba caba ga ‘yan fashi. Basu tsaya a ko ina ba sai da dajin majawara.
Dajin majawara daji ne wanda yake shiru, tsit ko kukan tsuntsu babu balle gidajen bil’adama. Daga nan kowa dakatawa babu mahalukin da xai iya tsallakewa a sanadiyar tsantsar hadarin da ke tattare da ci gaba da tafiya. Dole ne duk motar da ta xo dajin majara sai ta ja ta tsaya a doka har sai motoci saba’in sun cika sannan sojoji su xo su tsallakar dasu saboda mugaye, kasurguman ‘yan fashin da suke fashi a hanyar. Don haka said a ‘yan tawagar su kaltum suka yi kwanaki uku a nan suna jiran motoci saba’in su cika sannan a hayar dasu.
A ranar da suka cika motoci saba’in sannan aka shirya ci gaba da tafiya a lokacin da xa su tafi da yamma wani dankareren maciji ya sari daya daga cikin ‘yan twagar su kaltum, kan ka ce kwabo mutumin ya sassankare kumfa na xubowa daga bakinsa. Jama’a suka bi macijin da jifa amma tuni ya sulale ya shige dawa basu kashe shi ba, daga karshe mutumin ya mutu a wajen, a nan aka binne shi suka shiga motocinsu suka fara tafiya. Amma a kowace mota said a sojoji bibbiyu suka shiga suna harba bindiga sama har sai an wuce mugayen daxuka da barayin suke. Tun da yamman da suke tafe ba tsaya ba har se da gari yawaye, sannan sojojin suka sassauka daga motocin da suka rako suka shiga motocinsu suka juya. Sannan su kuma matafiya suka ci gaba da tafiyarsu.
Tafiyar kwana biyu suka yi ba kakkautawa sannan suka shiga kartum tutu babban birnin sudan. Sun kwana daya a kartum, a wajen garin akwai dakunan katako da aka yi musamman don kwanan matafiya. Da suka waye a nan sannan suka ci gaba da tafiyar, kwana guda cur suka yi a hanya sannan suka isa kartum bahari sai suka nufi bur sudan nan ne inda ruwan daya hada sudan da makka ,ruwanne ya hade da ruwan maliya. Daga bur sudan kuma tafiyar mota ta kare don haka masu mota suka sauke su su da jifgin kayansu suka juya.
Daki ne na guntayen katakwaye joni joni, rufin dakin ma duk hudaddun katakwaye ne baya da katakon nan babu ko kwayar dakunan sai wanda ya ci sa’a ne xai tarar da kwalaye a shimfide a dakin. Ga duhu a sanadiyar rashin fitila gashi tsakar dare suka iso don haka babu wata wata kwanciyar kowa yake so ya yi. Aka ware dakunan mata da na maxa daban, amma a kowane daki mutane ashirin ne xuwa ashirin da biyar duk da haka wasu a xube suke a tsakar gida wasu maxan kuma a xube a kofar gida. Su dai fatansu su kwantar da hakarkarinsu su mike a sanadiyar kagewar da bayansu ya yi saboda kwana da yinin da suke yi a xaune a mota a tattakure.
Misalin karfe daya na dare suka isa bur suban a gajiye suke don haka idanuwansu a rufe suke burin kowanensu ya sami inda xai yada hakarkarinsa. A guje suke rububin hayewa kan wasu tudu da suka iske a cikin dakunnan katakon cikin rashin sani basu san kabarurrukan suka kwanta yayin da wadanda basu sami hawa ba suka bi layi suka doddora kansu a kan kabarurrukan.
Kaltum da kakarta sun yi sa’a sun sami daki, a cikin dakin ma kaltum ta yi sa’ar samun hayewa kan tudun dake tsakiyar dakin. Dan tudun maidan tsawo ne da fadi daidai kwanciyar mutum daya don haka da ta shimfida xaninta aka ta yi filo da dan karamin bacco dake dauke da kayanta sai ta yada kai xata kwanta. Kakar tace ta daka mata tsawa tace “kaltum, kina da hankali kuwa! Ina kasa cikin kasa turmus ke ki sami mulmulallen tudu ki kwanta harda shimfida xani ki yi filo da jakar kayanki ni babu ko daya, to ki sauko kasa cikin kasar ki kwanta nixan haye tudun.”
Kaltum na karkarwar jiki don tsoro ta sauko da sauri, goggo fatu ta haye tudu harda juya baya ta yi kwanciyarta, kaltum ta mike a kasa cikin yashi ta kwanta, burinta ta kwanta da hakarkarinta ma kawai ta huta gajiya. Nan ma manyan mata suka dinga yi mata carin masifa wai sai ta matsa lungu ta babbake musu fili. Ba ta tankawa kowa ba ta takure a lungu ta yi shiru.
Bayan da kowa ya gama cuku-cukun kwanciya sai kowa ya yi shiru ya rufe ido kafin kiftawar ido barci mai dadi ya kwashe su, kan ka ce kwabo minshari ne iri iri ke tashi tun daga kofar gida xuwa tsakar gida har cikin dakuna kai ka ce busa sarewa ake ko kuma goga gurmi ake yi saboda tsabar gajiyar dake jikinsu.
Kaltum na runtsa idanunta barci mai dadi ya kwashe ta amma fa bata kai minti talatin ba ta ji ta yi wata mummunar firgita, ta xabura ta bude ido a xaune dabas ta tsinci kanta. Duhu kirin dakin ko tafin hannunka ba ka iya gani, ta duba gabas da yamma kudu da arewa sai taga kamar wani mutum dogo da fararen kaya a tsaye a bakin kofa yana tunkaro ta, nan da nan ta kwanta ta kudundune, jikinta na rawa tana makyarkyata ta fara addu’a kafin ta karasa wannan sai ta kama waccan addu’ar.
Irin wannan raxanar ceta afkawa goggo fattu wacce ta haye kan tudu. Gara ma kaltum akan goggo fattu saboda ita har girgixata aka dinga yi kai ka ce wani ne ya danketa yake wujijjigata. Ta galabaita sosai tun tana salati a cikin mayafi harta fara salati da karfi sai ta fara kwalla kiran sunan kaltum da duk wacce ta san sunanta a dakin. Can kaltum ta yi karfin hali tana cikin mayafinta tace “goggo, menene!”
Goggo tace “kaltum, xo ki sauke ni daga kan tudun nan shake ni ake yi ana girgixa ni kamar xa’a kifa da ni cikin kasa na kasa motsa jiki na.
To pa!!! ko me nene ya kawowa su goggo fattu gaisuwa, ban sani ba, se ku biyo mu dan jin yadda xata kaya.
.
To da patan littapin ya muku?
ADON DAWA 3
BABI NA UKU
A lokacin dasu kaltum suka cika sati uku a bur sudan dole tasa suka fito neman abunda xa su kai bakinsu, mata da maxa, yara da manya kowa ya ja xugarsu suka shiga gari.
Tawagar ‘yan mata su biyar kaltum, rakiya, huwaila, jidda’u da amina suka fankama garin ADON DAWA don yin bara. Suka kuwa ci sa’a suka samo kudi da yawa wanda xai ishesu su ci abincin yinin yau. Kalmar da suke ambata itace “karama fisabilillahi” sai kaga an miko musu kudi. Su kan basu wahid jine wato kamar naira daya kenan, wasu se su basu hamsin jine ficika kenan idan kuwa suka ci sa’a sai a rana daya saisu hada maitan jine daga nan saisu wuce cikin gari maka makan wajen sayar da abinci (restaurant)su sayo abunda suke so, kamar su kisra wato sinasir ko su sayi esha wato gurasa, wani lokaci saisu hada da ful. Ful wake ne manya manya sai a dafa shi ba gishiri ana ci da gurasa. Idan suka samo kudin bara da yawa saisu sayi baitil mandi shima dafaffiyar shinkafa ce fara sai a kwarara madara akai, a yanka tumatiri da albasa, a yanka karas da kabeji, sannan a dora gasashshiyar kaxa a barbada dan gishiri sannan a ci.
Daga dukkan alamu yunwar da ke addabar su ta fara sauki har sun sami karfin da suke iya debo bokitai da manyan darukan ruwa akansu, su niki tafiya mai nisa sannan su samo ruwan da xa suyi amfani dashi wajen wamka, wanki da wanke-wanke. Ta cikin makabarta suke bi sannan su isa gabar kogin da suke debo ruwan.
Ruwan baya shawuwa saboda jajawur ne mai dandanon gishiri.
Jikin kaltum yakan yi sanyi har takan fashe da kuka idan taga yadda ake binne mutane a makabarta. Saboda sahara ce don haka suke yin dogon rami mai xurfi sosai, wanda mai hakawar sai ya shige ciki sosai yayi xurfi.sai an daina hango shi sannan ya miko hannunsa a kamo shi waje dan ba xai iya fitowa ba. Sannan saisu taru su saka gawa, sannan su jera bululluka a maimakon itace saboda yashi ne itatuwa ba xa su tsaya ba. Allahu Akbar!
Allah Ya sa mu cika da imani, Y a jikan musulman da suka riga mu gidan gaskiya.
Ameen.
A yau kaltum bata bisu bara ba saboda tana son ta wanke kayan jikinta kwaya daya kacal, yayi dakun dakun har gefen xanin ya yage don haka ta yanke shawarar sai kowa ya tafi bara sannan ta rufe gida ta cire kayan ta wanke ta xauna ta jira ya bushe sai ta yi wanka ta saka. Da ta tabbatar mata da maxa sun fita daman tun da sassafe ta debo ruwan wankinta, sai ta tsinci guntayen sabulai ta harhade ta ajiye. Suna ficewa sai ta rufe kofar ta fara wanke riga da dankwali da mayafin ta shanya ta koma gefe ta takure tana jiran su bushe.
Ta duba gabas da yamma, kudu da arewa na gidan sai tace a ranta “yanxu fa a makabarta muke rayuwa alhalin muna raye.”
Ta sake duban katon tudun kabarin da yake gefenta ta mika hannu a hankali ta shafa tace, “ko mace ce ko na miji ne a cikin kabarinnan Allah Shi ya barwa KanSa sani. Allah Ya jkansu da gafara.”
Ta ji hawaye yana sirnanowa daga idanuwanta don tausayin kanta da irin matsananciyar rayuwar da take ciki. Ta tuno gwaggo fattu wacce ta kawo ta nan ta ajiye ta ita kuma ta haye ta yi tafiyarta makka tana can tana jin dadin rayuwarta.
Babban tashin hankalin shi ne iyayenta basu san halin da take ciki ba don su a tunanisu tana saudiya kuma tasan mugun halin gwaggo fattu ba xata yi waya ba ko ta aika wasika ta fada musu gaskiya ba sai dai ta bar su a haka, suma kuma iyayen nata ba waya gare su ba balle su san lambarta ta makka su buga mata su tambayi halin da take ciki. Kaltum ta fi jin haushin iyayenta su da suka yarda suka yarda suka bayar da ita aka taho da ita don basa tausayinta. Ta ji ta tsani kowa a duniya kamar yadda kowa baya sonta, sai ta fashe da kuka mai tsananin ta kifa kai a jikin katakon dakin su. Kuka take yi haikan amma tana fada cikin daga muryar ta “inna lillahi wa inna ilaihi raji’un”
Tsananin bugun da ake yiwa kofar gidan ne ya sata tsagaita da kukan da take yi, ta kasa kunne tana sauraro sannan ta gaskata wani ne yake buga kofa. Sai ta mike tsaye ta yi wuri wuri tana tunanin yadda xata yi. Shawara take yi shin ta je a haka da daurin kirji ta bude kofar, sai dai ai bata sani ba mace ce ko na miji! Idan namiji ne ba xata iya tsayawa da daurin kirji a gabansa ba musamman yadda maxan suke ‘yan iska ko wanka ka ke yi idan baka kula ba saisu yi ta liken ki. Haka idan ki ka yi sake a daki kina barci baki killace jikinki ba sai dai ki ga suna ta xirga xirga ta kofar dakinku suna kallonki a dole wucewa bandaki su ke yi, ko suyi ta leke ta hudar katakon musamman dakin su kaltum da yake kunshe da ‘yan mata.
Ta ji sautin bugun kofar ya kara tsamari don haka ta yayimi jikakkiyar rigarta ta saka ta jawo jikakken mayafinta ta sharba a kanta ta goge idonta saboda hawayen da yayi mata kawanya. Ta isa da sauri bakin kofar ba tare da ta tambaya ba ko waye ta ja sakata ta bude game da wangale kofar. Jikinta na rawa ta dubi wacce ke bakin kofar sai taga madina ce tayi sauri ta duka a tsorace.
Ta ce “sannu da xuwa, yi hakuri ban xo na bude miki kofa da wuri ba ina kokarin saka rigata ne.” madina tayi murmushi t ace”lah ai ba komai kaltum.”
Kaltum ta mika hannu xata kar bi himilin daurin kayan dake kanta sannan ga leda a hannunta. Madina tace “bar shi kaltum, ba komai ba sai kin taya ni ba ai na xo gida mu shiga ciki.”
Kaltum ta dawo tsakar gida inda ta cire jikakkiyar rigarta da mayafinta ta mayar kan igiya ta shanya. Madina kuwa ta wuce cikin dakinsu kai tsaye ta xarce kan kwalin shinfidar ta da jakar kayanta a gefe ta ajiye himilin tsummakaron da ta samo. Ta fito tsakar gida inda kaltum ta daga ido da sauri ta dubeta sai suka yiwa juna murmushi a lokacin guda. Kaltum ta mayar da kai kasa don kunya da girmamawa. Madina tace “kaltum me yasa yau baki fita bara ba!”
Kaltum ta dan yi murmushi tace “kayana ne suka yi datti nake so na wanke sai sun bushe sannan in fita.”
Madina tace “ me yasa sai sun bushe xaki tafi, ki wanke ki shanya sai ki saka wasu kayan ki tafi ki nemo abunda xaki ci, yaushe xa’a ce tun safe baki karya ba har rana tayi yanxu kina jira sai kaya sun bushe!”
Kaltum ta langwabar da kai gefe tace, “ai bani da wasu kayan, kayan jikina ne kadai nake da su, kakata ta tafi da kayana hade da nata ta haye tana cikin wadanda suka tafi makka.” Hawaye ya sarnano daga idanuwan kaltum.
Madina ta tambayeta cike da mamaki tace “au iya mairo ba kakarki bace daman!”
Kaltum tace “kawar kakata ce, garinsu daya tare muka taho dasu, rakiya ce jikarta.”
Tsawon mintina biyar madina tayi tana kallon kaltum saboda tsananin tausayin ta da ya lullube mata xuciya, ta rasa kalma guda daya da xata iya furta mata. Tana tausayin kanta da kanta, amma ta fi tausayin kaltum yarinya karama ba uwa ba uba, ba dangin iya balle na abba a kasar da bata taso ba.
Kaltum ma ta yi shiru kanta a sunkuye a kasa sai kwalla data cika mata ido ta rasa abunda yake damunta saboda kuncin rayuwa.
Madina ta yi ajiyar xuciya ta share hawayen daya cika mata ido, sai ta shiga cikin daki inda ta kwance daurin tsummakaron data shigo dasu ta fara daddagawa tana warewa. Kala biyu riga da siket ta debo ta fito ta mikawa kaltum, kamar an xare mata laka haka ta mika hannu ta karba. Ta kurawa madina ido tana sauraron abunda xata fada, madina ta juya xata shiga daki sai kaltum tace,” wanke miki xanyi!” sai dai babu sabulu, nima guntayen sabulai na tsintsinto a bandaki na yi nawa wankin.”
Madina ta waiwayo ta dubeta sai tayi murmushi t ace “a wanke suke, baki nayi kyauta ki saka nima yanxu nan aka bani su sadaka a garin ‘yan Adon dawa.”
Farin ciki ne bayyane hade da mamaki suka halacci fuskar kaltum ta yi murmushin da har saida wushiryarta ta bayyana yayin da gafen kumatunta ya loba wato (dimple) ta dago da fararen idanuwanta dara dara ta dubi madina ta fada cike da annashuwa.
“anty kin bani kyauta in saka!”
Madina ta yi dariya tace “na baki kyauta kaltum, me ye sa kike mamaki!”
Kaltum, ta sunkuyar da kai kasa ta yi godiya sannan ta fara warwarewa tana duddubawa farin ciki fal a xuciyar ta. Kafin madina ta fito daga daki kaltum ta saka riga da siket cas da ita kuwa kamar dan ita aka saya daidai jikinta sun yi matukar yi mata kyau. Madina ta fito daga daki dauke da wata bakar leda a hannunta tana duban kaltum sai suka yiwa juna murmushi a lokacin guda. Madina ta yaba da yadda kayan ya karbe ta, sannan ta samu inuwa ta xauna a kasa ba tare da ta nemi wani abu ta shinfida ba. Kaltum ta jefa xanin da ta kunce a cikin bokitin data adana sauran kunfar data wanke riga da mayafinta ta fara sabawa . madina ta kwance leda sai ga kisra da ful.
Madina ta dubi kaltum tace “xo mu ci abinci yarinya”
Wannan kalma ta bawa kaltum matukar mamaki wanda har yasa ta dago da sauri ta dubeta har na tsawon ‘yan dakiku masu yawa ta kasa Magana, can ta yi murmushi.
Ta ce “na koshi, nagode.| madina tace, “me kika ci da xaki ce kin koshi.! Ki saki jikinki da ni ki xo mu ci ai xai ishe mu daman dayawa na siyo in ci yanxu sauran inci daddare ba komai, Allah de bani wanda dan ci daddaren.” Tsananin yunwa ce daman ta addabi cikin kaltum banda kugi babu abinda cikinta yake yi saboda ya fafake babu komai tun a bincin jiya da rana bata sake samun abunda xata sakawa hanjinta ba. Ta ajiye wankin ta goge hannayenta ajikin siket din dake jikinta ta karaso a hankali inda madina ke xaune, cikin kunya da nutsuwa ta xauna yayinda hannunta ya dau rawa a lokacin da take kokarin gutsurar gurasar madina ta dubeta, sannan ta tambayeta cike da mamaki.
Ta ce “kaltum lafiya, meke damunki, ya naga kina karkarwa kuma duk kin tsangwami kanki! Haba kaltum ki saki jikinki ai ba wani abu bane duk wanda ya taimaki wani shima Allah xai taimake shi.” Kaltum ta sunkuyar da kai kasa ta fada cikin sanyin jiki.
Ta ce, “ina mamaki ne saboda tun a mota kowa ta kansa yake babu mai taimakon wani ko dai dai da mukurwar ruwa ne sai naga kin bani sutura kyauta sannan kin siyo abinci kince in xo in ci shine na keta mamaki.”
Madina ta yi murmushin karfin hali ta dafa kafadar kaltum tace “yarinya ba haka bane duk masu yin haka jahilai ne, babu yadda xa’ayi musulmai su hadu a waje daya su ce babu wanda xai taimaki dan uwansa musulmi. Babu mai imani ga duk musulmin daba xai so wadan uwansa abunda ya sowa kansa ba.
Ko a lahira aikinmu ba xai kaimu shiga aljanna ba sai dai alfarma albarkacin masu albarka. Kaltum, ki cire wannan mugun tunani a ranki, ki dauka a xuciyarki duk runtsi duk talaucin da kike ciki komai kankartar abu xaki taimakawa wanda ki ka fi ko da babu mai taimaka miki domin Annabi Muhammad (S.A.W) y ace “hannun da yake mikawa shine a sama, ya fi hannun da yake karba shine a kasa.”
Babu wanda kaltum take yi sai gyada kai hakika tana gamsuwa da abunda madina take fada mata. Suka ci, suka koshi suka kora da ruwa sannan kaltum ta yi godiya ta tashi ta je ta ci gaba da wankinta, ta dauraye ta shanya. Dai dai lokacin iya mairo da tawagarta suka shigo, a jigace suke saboda tsananin yawon bara da suka yini suna yi da alama kuwa kwalliya ta biya kudin sabulu saboda kowaccensu hannunta dumu dumu da ledoji. Cikin fara’a kaltum ta tare su gani da yi musu sannu da xuwa. A tunaninsu kwadayin abunda suka samo take don haka kowa ya tsuke fuska babu wanda ya amsa gaisuwarta sai ma dai kauce mata suke yi suna kewaye ta suka nufi daki.
Iya mairo ce ta tsaya tace mata “sannu isashshiya ‘yar gata wacce bata iya wahala ba, kowa ya fita nema ke kina kwance a gida wa xai nemo ya baki a wannan marrar da nafsi nafsi babu mai taimakon wani, keta wanki ma kike yi. Waye ya baki aron Kaya ko kin fara tsayawa sai kinga ba kowa ki bude jakunkunan mutane ki daukar musu kaya! To kada ki sace kayan wani a kama ki kice kin sanni ko kice ni kakarki ce.
Rakiya ma ta leko daga daki ta tsoma baki tace “tun shigowata nake kallonta daga gani kayan nan na wani ta sato saboda bai yi kama dana bola ba kuma bata fita bara yau ba. Tun da safe ta debo ruwan wanki bata kara fita ba.” Sai sauran ma suka tsoma baki babu wacce bata yi mata cari ba a cikinsu.
Kaltum tadago da sauri ta dubi madina yayin da madina ta yi mata nuni da hannu alamar ta yi shiru kada tace komai. Kaltum ta sunkuyar da kanta kasa sai wani kuka na takaici ya kece mata marar kakkautawa. Ta koma gefe ta tsugunna tamkar almajirarsu yayin da kowaccensu ta shiga daki ta baje ledar abincita suka ci. Wasu shinkafa ce da miya, wasu baital mandi, wasu taliya, wata macaroni. Abun mamaki sai suka dinga yiwa madina tayi wai ta xo su ci. ta ce ta gode a koshe take amma babu wacce ta tuntubi kaltum.
Wani kululun takaici ya tsayawa kaltum a wuya ta fara tuhumar kanta tana tambayar xuciyarta wane irin mugun hali nake yiwa mutane haka suka tsane ni! Me nake yi wanda kowa baya sona aka tsane ni!”
Sai tayi xunbur ta mike ta shiga daki wajen shinfidar kwalinta ta dauko robar cin abincinta, yayin da kowacce ta dinga kare abincinta wasu ma suka fara daure ledar abincinsu a tunaninsu rokarsu xata ta yi, ta dube su duba irin na takaici ta langwabar da kai ta matse hawaye sai ta fice, ta yayimi gyalenta ba tare da ta yiwa kowa Magana ba har madina da take xaune a tsakar gida a wajen da suka ci abinci har yanxu bata tashi ba.
Fitarta kofar gida keda wuya sai ta tsaya cak ta dubi gabas da yamma, kudu da arewa babu abinda take gani sai tulun bola da kabarurruka yayin da gabanta kuwa katon kogi take hangowa yana ambaliya. Ta ji a ranta tamkar ta fada kogin nan ruwa ya hadiyeta ta mutu ta huta da bakin cikin rayuwa sai kuma ta tuna da wa’axin da aka yi musu a makarantar islamiyya cewar duk wanda ya kashe kansa ya mutu a kafuri. Ta juya ta dubi kabarurrukan da ke gabanta sai tayi sha’awar dama ace ita ce a ciki a mace ta mutu an binne ta. Ta ji a ranta rayuwar wadannan bayin Allah da suka mutu ta fi mata irin rayuwar da take yi a duniya jin dadi da kwanciyar hankali.
Kamar daga sama ta ji Magana a bayanta, ta waiga da sauri saida suka hada ido da madina.
Ta ce “kaltum ina xaki je!”
Kaltum ta saki fuskarta ta yi murmushin karfin hali. Ta ce “xan je bara.”
Madina tace ki kula da kanki, shawarar da xan baki itace kada ki je garin jange saboda kin ga ke yarinya ce akasarinsu kuma ‘yan iska ne gara ki je garin Adon dawa tunda su na da musulmai xa su fi tausaya miki. Hadari ne ma ki dinga tafiya ke kadai ba’a tawaga ba saboda irinku suke so ‘yan mata ba kamar mu ba manya ba damuwa.
Kaltum ta gyada kai tace “to anty bari in je garin Adon dawan.” Ta juya ta tafi yayin da madina ta dade a tsaye tana kallonta har saida ta kure ta daina hango ta sannan ta girgixa kai don tsananin tausayin kaltum ta shiga gida.
Kaltum tafiya take amma fa har yanxu bata fasa kuka ba harta iske gidajen Adon dawa. Ta fara shiga gida daya bayan daya, Kalmar da take ambata itace “karama fi sabilillahi”
Da alama yau bata fito da sa’a ba daga inda ake kyaleta ta yi ta bara ta gaji ta tafi da kanta sai inda ake yi mata korar kare. Ta yanke shawarar tunda yamma tayi yanxu duk maxan suna kasuwa bari ta je can ko Allah xai sa ta dace. Kaltum ta kama hanyar jim arab, nan ta iske dandaxon maxa kungiya kungiya suna sha’aninsu wasu suna caca, wasu kuwa suna hira suna shan jabna, yayinda wasu suke saye da sayarwasu. Kaltum na fara bara sai ta ci sa’a duk rumfar da tayi bara sai a miko mata sadakar wahid jine wato kamar kandala, farin ciki ya lullube xuciyar kaltum don ada ta shiga wani mawuyancin hali tana tunanin yadda xata yi in har bata samu ko kwabo ba idan ta je gida xasu kusa cinyeta da baki bayan wulakancin kala kala.
Ta ci gaba da bara harta karkashin wata inuwa inda dandaxon samari ne xalla, sun shinfida katuwar tabarma suna ta shan jabna suna caca. Sun kaisu goma sha biyu dukkanninsu shekarunsu basu wuce ashirin da biyar xuwa ashirin da bakwai ba. Shewa da ihu kawai suke yi da alama basu da matsala a rayuwa. gasu a kauye, a cikin gidajen katako da katangar kaya yayin da suturar jikinsu bakin yadi ne mai layi layin fari wacce suke dinka ‘yar shara da wando iyaka guiwa amma koda yaushe sai kaga suna farin ciki ko me yasa. Kaltum take xayyanowa aranta sannan ta bawa kanta amsa “tabbas dole suyi farin ciki a rayuwarsu saboda suna tare da iyayen su, a garinsu, kuma ga dukiyoyinsu” ta katse tunanin da take yi da ta ji suna tambayarta “lafiya, me kike nema a wajenmu!”
Tayi firgigit t ace “karama fi sabilillahi.” Kalma daya ta ji wani daga cikinsu ya fada a cikin yarensu sai taga dukkaninsu sun waiwayo sun kalleta a lokaci guda. Ta yi sauri ta sunkuyar da kanta kasa, da tadago taga har yanxu suna kallonta, sai ta sa gefen gyalenta ta rufe da fuskarta. Daga karshe ta yanke shawarar gaggauta barin wajen tun kafin su iskance ta.
Cikin harshen larabci daya daga cikinsu yace ta xo, kasancewar tana jin larabci sosai tun tana karama sai ta juyo ta dawo wajensu a nutse cikin ladabi amma fa duba daya xaka yi mata ka tabbatar a tsorace take. Ya dubeta sama da kasa duba irin na kurulla yayi dariya ya shafa baki don haka kaltum ta fara fuskantar manufar kiranta da yayi, sai ta fara ja da baya.
To pa, ko ya data kasance tsakanin kaltum da en samarinnan!
Sai ku biyo mu dan jin yadda xata kaya
ADON DAWA 4
Ya fada cikin shagobe “ke me kyau, yaya sunanki!”
Ta na mkyarkyata tace “kaltum”
Su dukka suka maimaita sunan “kaltum” a lokaci guda suka ci gaba da dubanta suna kwada kyawunta, suna mamakin kyawunta don basu xata akwai masu kyau a cikin bakin almajiran nan ba saboda sun dauke su wulakanttatun bayi.
Daya daga cikin su ya dubi shugaban tawagar mai suna Mambela wanda har yanxu bai ce komi ba sai duban kaltum yake yi kasa kasa.
Cikin yarensu yake Magana yace “ranka ya dade shugabana mambela kai ka dace da kyakkawar halittar nan, du da de ba niman mata kake ba, lallai tana da kyau kuma ta hadu. Ya kamata a mika maka ita cikin shagon nan kawai in ka gama sai ka bata alif jine (dubu daya) ka ga sai tayi sati tana cin abinci, gobe xa ka ga ta dawo da kanta.”
Duk da cewar a cikin yarensu ya yi Magana bata ji duk abubuwanda yake fada ba amma ta fuskanci abunda yake fada, don haka sai ta juya da sauri ta fara tafiya. Mambela yace “tabbas yarinyar na ta dace da ni don haka ku dauko min ita, ku shigar min da ita cikin shagon nan.” Ba tare da bata lokaci ba kartai hudu suka bi ta da gudu suka damkota cak suka daga ta kamar kaxa suka nufo inda mambela ke xaune. Tuni robar bararta da yan kudaden data samu suka waste a kasa, ta kurma ihu kai kace rai ake xare mata.
Cikin kuka tace “inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un. Laa ilaha illa anta subhana inni kuntu minaxxawalimin.”
Mambela yace su ajiyeta kasa a gabansa yayin da ta xabura da gudu sai ya damki hannunta ya fada cike da damuwa cikin harshen larabci.
Ya ce”kaltum bkya son kudi ne! bakya son mambela dan sarki, mai kudi da dukiya!”
Ta fada cikin firgicewa da kuka mai tsanani .
“eh, bana so.”
Ya yi murmushi cikin mulki da kasaita y ace “amma ni na ji ina sonki, so mai dinbin yawa kuwa. Yaya xa’a yi ken an!”
Abokansa suka fada cikin fusata “ka bamu ixini mu shigar maka da ita ciki kawai, ka gama da ita mu ma idan ka gama ka bamu sauran, tunda bata da gata a kasar nan waye xai tsaya mata.”
Mambela ya mike tsaye cak yana duban kaltum dake tsugunne a gabansa har yanxu kuka take, gardawan kacokan sun xagayeta babu hudar da xata samu ta arce . mambela ya dade a tsaye yana dubanta daga shi sai mahaliccinsa ya san abunda yake aiyanawa a ransa. Can ya dago ya dubi yaransa daya bayan daya sai yayi murmushi da kyakkyawar fuskar nan tasa, sannan ya yi musu nuni da hannu ko bai furta ba su sun fahimci abunda yake nufi nan da nan suka fara aiwatar da abunda ya umurcesu dasu yi domin ba’a yiwa mambela musu a garin.
Kartai uku ne suka damko ta suna kokarin shiga da ita shago. Ta kurma ihu ta ci gaba da kiran “inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un.”
Muryar wani tsoho ne suka ji a bayansu ya fada cikin yarensu, daga dukkan alamu ransa a bace yake, y ace “haba mambela ko sauran ba musulmai ba ne ai kai musulmi ne, ko kunyi niyyar cutar da yarinyar nan albarkacin sunan Allah da take ambata ya kamata ku kyaleta.”
Suka ajiye ta yayin da ta balla da gudu ta je bayan tsohon ta labe, karkarwa kawai take yi. Gyalenta ya dawo wiyanta, kanta babu dankawali sai burtintin kitson da ya tuttuje wanda ya cika da yashi a sanadiyar rashin siminti balle katifa a dakinsu. Tsohon ya juya ya dubi kaltum yayi mata yarensa, sai ta girgixa kai ta yi masa larabci. Ta ce, “bana jin yarenka, larabci nake ji kadai” ya fada cikin harshen larabci “yi hakuri yarinya, daura dankwalinki, goge hawayenki ki tafi gidanku. Ki daina shigowa kasuwa bara wajen maxa ki dinga bararki a cikin gidajen mata ya fi miki alkhairi a matsayinki na yarinya mace budurwa kuma kyakkyawa.”
Ta gyada kai t ace “ nagode, ba xan sake xuwa ba. Baba karaka ni gidanmu tsoro nake ji kada su bini su sake tare ni a hanya.”
Ya ce to muje in raka ki.
Jikinta na karkarwa, hawaye yana kwaranya ta shige gaba tsohon na biye da ita a baya har suka yi nisa.
Mambela ya cije baki ya gyada kai ya dubi abokinsa.
Ya ce “xan jinyata tsohonna idan be daina shiga shirgata ba. Yanxu haka shima idan suka raba daji yaga ba kowa xai iya yi mata lalata, shine mu ya hana mu. Xamu hadu da kaltum wata rana wallahi ba xan hakura da ita ba duk ihunta.”
Abokansa suka ci gaba da xuga shi suna bashi kwarin guiwar gami da daukar masa alkawarin idonsu idon kaltum xa su kamo masa ita.
Har kofar gidansu kaltum tshon nan ya raka ta da gudu ta fada cikin gida ba tare da tayi msa godiya ba saboda a firgice take don tsananin tsoron da ta ke ciki.
Kaltum ta dawo gida da magaruba, kallo daya xaka yi mata ka tabbatar hankalinta a tshe yake ko Magana aka yi mata sai ka ga ta xabura. Babu irin tambayar da ba’a yi mata ba amma amsa daya ta gagara sai hawaye da take xubarwa. Daga ita sai Ubangijinta suka san abunda ya faru amma bata fadawa kowa ba.
Madina ceta ja hannunta tsakargida, suka shafe tsawon sa’a guda tana lallashinta tana bata baki da dubaru iri iri akan ta fadi abunda yake damunta amma kaltum ta ki cewa uffan, sai girgixa kai kawai take yi alamar babu komai. Karshen maganar madina t ace “babu yadda xa’ayi kice babu komi amma kuma kina kuka.”
Ta bata ruwa a buta tace ta yi alwala, ta yi sallah, ta yi addu’a ko me nene ma Allah Ya sawake mata.
Karkarwa hannu kaltum yake yi data dauki buta ta xagaya ban daki, ta fito tana alwala jkinta na rawa, kukan dai bata fasa ba har yanxu. Tana sallah tana sheshekar kuka a bayyane, hankalin madina ya tashi amma sai ta ji haushin kaltum ya kama ta saboda ta ki fada mata matsalarta. Su kuwa su huwaila banda xagi da dungure mata kai babu abunda suke yi suna cewa watakila satar kayan jikinta tayi masu kayan suka doke ta.
Rakiya tace “watakila gidan wasu ta shiga ta satar musu abinci tunda da yunwa ta fita tun jiya bata ci abinci ba.”
Amina t ace, “ko kuma xagin wasu ta yi suka kikkifa mata mari don bata da kunya.”
Iya mairo t ace, “ku kyale ta mana karta fadi abunda yake faruwa tunda bakin hali ne da ita babu mai jin cikinta.”
Kaltum na kudundune a kan kwalinta cikin mayafinta sai kuka take yayin da jikinta yak eta karkarwa. Har kowa y agama cuku cukun kwanciya, aka hure acibal bal wato fitilar da ake cika kwalba da kanaxir ayi lagwani da tsumma.
Duhu ya bayyana a cikin dakin, yayin da gari yayi shiru alamar dare ya tsala, kowane bawa ya kwanta hakarkarinsa kamar yadda masu iya Magana suke cewa dare mahutar bawa. Wannan dare kuwa ya xamarwa kaltum daren jan aiki babba maimakon ta huta sai ma ta tashi tsaye.
Misalign karfe daya na dare kaltum tayi firgigit ta mike tsaye a firgice gami da kwalla ihu mai tsanani tana fadin “wayyo Allah na, ku taimakeni gasu mambela nan xasu kamani.”
Ta tattaka sauran matan dake kwance a tsakiyar dakin burinta kawai ta fice waje da gudu. Gaba daya ‘yan dakin suka tashi a gigice suna riketa, tana bankarewa tana xubar das u sai da ta fita tsakar gida da gudu tana ihu tana fadin.
“su mambela ne xasu kamani, gasu nan xasu kashe ni.”
Madina da jidda’u ne suka bita da gudu suka damko ta suka shigo da ita daki sannan ta dan lafa ko minti biyar ba’ayi bat a sake kwalla ihu ta fice ta gudu. Wannan karon harda iya mairo a masu bin ta da gudu suka cafko ta. Ba ‘yan dakin su kadai ba gaba daya ‘yan sauran dakunan gidan babu wanda ihun kaltum da dawainiyar masu rike ta bai tasa daga barci ba. Kowa ya fito ido luhu luhu saboda barci suna tambayar “me ke damunta!”
“ba mu sani ba.” Amsar da su madina ke bayarwa ken an. Su duka suka kewaye kaltum suna tambaya,
“waye mambela, mutum ko aljan!”
Babu amsa, makyarkyata kawai take yi tana kuka, madina ce mai ilimn kur’ani ita ke tofa mata addu’o’I sannan kaltum tadan lafa harta fara gyangyadi, sannan ta sake firgita ta mike tsaye tana kokarin rugawa da gudu suka damko ta, suka xaunar da ita har yanxu fada take.
“ga mambela nan da abokansa xasu kamani.”
Su dukka sun tausaya mata, kowannensu mata da maxa sai addu’o’I suke tofa mata har saida ta lafa sannan suka koma dakunansu. Wsau suka kwanta amma wasu suna tsaye akanta har saida gari yawaye tangarai sannan kaltum ta sami barci. Sai kowa ya shiga neman ruwan alwala da sauransu.
Kaltum barci take yi haikan mai nauyi wanda bata iya jin duk wani motsi da surutan da ake yi akanta, bata bude ido ba sai karfe biyu na rana. Ta tashi xaune firgigit ta dubi sama da kasa, gefen hagu da damanta sai taga babu kowa sai ita. Ta dinga kokarin tuno komai. Kanta ne yake tsananin ciwo dan haka ta shafe awa guda a xaune ta rasa abunda yake mata dadi. Can ta daure ta yunkura xata tashi sai ta koma jabar ta xauna, ta sake cije baki ta rike katakon ginin dakin ta yunkura da karfi sannan ta mike tsaye. Ta fara tafiya a hankali yayin da kafarta ke xugi a sanadiyar bubbugewar da ta dinga yi jiya. Hakika duk ilahirin jikinta ciwo yake yi musamman kafadar ta saboda ciccibar da abokan mambela da ‘yan dakinsu suka dinga yi wajen jawo ta.
Ta fito tsakar gida ta tsaya ta dubi kowacce kusurwa babu kowa sai ita kadai, ta sake ci gaba da tafiya har saida ta fito kofar gida sannan ta sulale ta xauna a gefen wani kabari ta xura masa ido tana kallo. Sai hawaye ya fara sirnanowa daga idanuwanta, ta fashe da kuka mai tsanani ta fara Magana ita kadai tamkar tababbiya.
Ta ce “a ina nake! Ni wacece! Wa nake da shi a duniya! Me na ke yi a duniya!”
Sai kwakwalwarta ta tuno mata mambela da abokansa a lokacin da suke kokarin ciccibarta xasu shiga da ita wannan shagon, sai ta rushe da kuka. Ta ce “inna lillahi wa’inna ilahi raji’un. Yaya xan yi da rayuwata! Kowa ya tsane ni, kowa baya sona, kowa yana hantara ta, ga kishirwa ga yunwa. Allah Ka dau raina a saka ni a cikin kabari in kwanta in huta in daina ganin kowa, kowa ya daina ganina balle wani ya ji haushina.”
Ta sa hannu ta shafa kabarin ta fada cikin kuka ta tambaya tace “waye a cikin kabarin nan, mace ko namiji! Ina so in xama kamar ku, in mutu kamar yadda kuka mutu. In daina motsi kamar yadda kuka daina, in daina tafiya kamar yadda ku ka daina, in daina bara balle su mambela su kamani.” Yayin da kuka ya ci karfinta ta kasa ci gaba da Magana.
Muryar mai sayar da ruwa ne ya katse ta, ta dago idanuwanta da sauri ta dube shi, sai a lokacin ta tuno tsananin kishirwar da take matukar addabarta. Ta fada cikin wata marainiyar murya “saga dagiga moya hilwa wala murra!” ma’ana mai ruwa tsaya ruwan dadi ne ko na xartsine!
Mai sayar da ruwa ya tsayar da jakunansa ya dubeta yayi murmushi y ace “muya hilwa” ma’ana ruwan dadi ne.”
Ta ci gaba da Magana cikin harshen larabci tace “ka sauke min jarka daya.”
Ya sauko daga kan keken jakinsa da farin ciki yana godiya ya na fadin”Allah Ya yi miki albarka yarinya, kin taimakeni da xaki sayi ruwana yau ko digon ruwa ban siyar ba ban samu ko kwabon da xan yi cefane ba.
Maganar da yayi ya ambaci kudi shi yasa ta tuno dan silillikan data samu jiya da yamma. Sai ta yi sauri ta laluba jikin siket dinta, ta ji ba komai, sai ta tuno ashe sun xube a lokacin da ake ciccibar ta a kasuwa daga kudin har robar bara sun xube. Sai ta ji hankalinta ya tashi ta shiga tunanin abunda xata fada masa. Ya katse tunanin da ta ke yi ya tambaya, “a ina xan juye miki ruwan!”
Sai ta yi firgigit ta dube shi sannan ta sunkuyar da kai kasa, ta sosa keya, ta fada cikin gargadar murya “baba ka yi hakuri ba ni da kudi, ashe kudin ya xube jiya a jim arab. Ko xaka bani kofi daya in sha sadaka saboda Allah kishirwa nake ji.”
Tsoho ya tsuke fuska ya ciccibi jakar ruwansa ya mayar kan jakunansa yah aye, ya kada su suka tafi. Kaltum ta bishi da kallo har yayi nisa ta daina hango shi sai ta sulale ta kwanta a kasa domin a halin yanxu ta kasa kukan ma karfinta yakare. Can ta ji wata mryar kamar daga sama ana Magana cikin harshen larabci yace.
“yarinya, tashi ki karbi ruwa ki sha Allah Ya taimake ni yadda na taimake ki jikata.”
Ta daga ido da sauri sai taga mai sayar da ruwa ne ya dawo . ta tashi xaune da sauri yayin da farin ciki ya lulube mata xuciya, ya sauko daga kan keken jakunansa y ace.
“a ina xan juye miki jarka daya!”
Ta tashi da sauri ta shiga gida ta dauko bokiti ta kawo masa, ya tuttule mata jarka guda har saida bokitin ya cika taf da ruwan dadi. Ruwan da mutu daya baya iya siya a cikinsu sai daisu hada kudi su saya su uku ko su hudu su yini suna sha, ko alwala basa iya yi dashi sai dai su je kogi su dauko ruwan xartsi su yi alwala, wanka da wanki.
Kaltum ta dube shi ta fada cikin lallausar murya “baba, Allah Y dube ka kamar yadda ka dube ni, Allah Ya kawo maka ciniki ka samu na cefane kamar yadda ka taimake ni.”
“amen jikata” Kalmar da yake fada mata ke nan har ya hau keken jakunansa ya tafi yana daga mata hannu itama tana daga masa.
Ta tsugunna ta kafa kai a cikin bokitin ta sha ruwan nan tamkar rakumar da ta bude tankin cikinta. Ta dago ta yiwa Allah hamdala, ta sake kafa kai ta sha, ta sha, harta gaji sannan ta mike ta samu karfin ciccibar bokitin ta shiga dashi cikin gida, bayan ta kama ruwa sai ta shiga yin alwala ta shiga daki tayi sallolin axahar da la’asar domin har la’asar tayi. Tana idarwa amai ya kece mata a wajen da take xaune saida ta amayar da gaba daya ruwan da ta sha. Idonta ya yi jawur ya dinga xubar da hawaye saboda wahala sai a nan ta tabbatar yunwa ceke damunta ta fara tunanin ta inda xata samu abinci ta ci. Motsin shigowar mutanen gidan ne ta xaburar da ita ta yi sauri ta tula kasa akan aman ta rufe sannan ta fito tsakar gida da sauri sai taga ba ‘yan dakinsu ba ne.
Su na ganinta suka fara tambayarta yaya jikinta ta amsa da sauki. Duk da ta shiga rudani bata fahimci sannun da suke yi mata ba . tana tambayar kanta da kanta.’daman ba ni da lafiya! To ciwon me nayi da har ‘yan wasu dakin suke yi min sannu!”
Ta tambayi xaibu ko taga su iya mairo! Xaibu t ace ta bar su a gari ‘yan jange suna wankau, wasu daga cikin ‘yan matan kuma suna wajen sayen abinci suna saya. Kaltum ta yi shiru tana tunanin a ranta tana tababtarwa kanta kanta cewar ko yunwa xai kashe ta ba xasu bata loma daya ba, gara ma madina xata iya bata abinci ta ci amma da kunya jiya ta bata yau ma ta jira sai ta bata.
Xaibu ta katse tunaninta t ace “baki fita bara ba ne yau!”
Kaltum ta gyada kai tace “ban je bara ba saidaI yanxu xan tafi. Ko xaki bani aron robarki in tafi bara tawa ta bata jiya.”
Xaibu ta shiga ta dauko mata roba, a cikin robar da gutsurin gursa. Farin cikin ya lullube xuciyar kaltum, ta karba ta duka ta yi godiya ta yagi gayan gurasa ba tare da tagama taunawa bata hadiye tamkar mayunwancin xakin da yasa mu danyen nama. Fitowar ta keda wuya sai ta sake cin karo da tsohon nan mai sayar da ruwa akan jakunnan sa, ya dubeta yayi murmushi.
Ya ce “jikata, ki godewa Allah, ki yiwa Allah gadiya domin ke ‘yar baiwa ce, ki yi min addu’a ko Allah xai amsa min bukatuna.”
Kaltum ta yi kasake tana dubansa duba irin na rashin fahimta, ya lura da hakan sai ya ci gaba da cewa “na taimake ki daxu, ki kayi min addu’a kuma Allah Ya amsa miki. Ina barin wajenki na samu mai siyan ruwana ya saye dukka ya bani kudina, a yanxu haka jira na yake in je in debo masa wani ruwan in kawo musu xasu juye suba ni kudina. Na manta rabon da in sayar da jarkokin ruwa na duka har sau biyu lokaci guda. Yaya sunan ki!”
Ta yi murmushi ta amsa masa da “kaltum” ya dau waka yana cewa “kaltum ‘yar baiwa, kaltum ‘yar albarka.”
Ya wuce yana rera waka yayin da ta bishi da kallo fuskarta cike da murmushi. Ta fara xaiyano mutanen da suka fara sonta a rayuwa. madina, mai ruwa sai kuma xaibu wacce ta bata gurasa yanxu.
Muryar ‘yan dakinsu ta jiyo haya haya suna tafe suna tayar da kura tamkar dokunan da suke sukuwa. Kallo daya ta yi musu ta sunkuyar da kai kasa don tasan xaginta xasu yi, ta yi mamakin da ta ji su dukka suna yi mata sannu, yaya jiki! Ta amsa musu “da sauki.”
Iya mairo t ace “xaki iya xuwa bara, Amma ki yi sauri ki dawo kar ki kai magaruba don kar kiyi gamo irin na jiya.”
To pa, anya kaltum tana sane da halin da ta shiga jiya kuwa!
Meye dalilinta na shiga wannan halin!
ADON DAWA 5
.
Kaltum ta tambaya a bayyane “gamo, wane irin gamo!”
Rakiya t ace “kin fi kowa sani ki ke tambayar mutane.”
Suka wuce suka shige cikin gida suka bar ta a nan tsaye tana tambayar kanta abunda suke nufi.
“shin me ya faru da ni jiya har ake ta min sannu!”
Ta nufi garin jange sai ta juya ta kama hanya garin Adon dawa, can ta ja burki ta tsaya cak data tuno abunda su mambela suka yi mata a kasuwa jiya ta yarda robar barar a kasa ta toshe kunne ta tsugunna ta kudundune jikinta kamar wacce xata nutse a cikin kasa. Wani hannu ta ji ya dafa bayanta, sannan ta ji wata murya mai laushi ta ambaci sunanta, kaltum ta dago a firgice sai taga madina ce.
Ta tashe ta tsaye, ta tambaye ta lafiya! Me take yi a tsugunne a nan! Amsa ta gagari bakin kaltum, madina ta yi shiru ta fara tunanin “anya kuwa kaltum bata yi gamo da aljannu ba a garin nan!”
Kaltum tace “bara xanje.” Ta tsugunna ta dauki robarta ta juya tana tafiya madina ta kwalla mata kira, kaltum ta waiwayo ta kalleta. Madina t ace “kin tabbata xaki iya xuwa bara yau! Domin baki da lafiya.”
Kaltum ta gyada kai t ace “xan iya xuwa” madina ta bita da kallo har said a ta yi nisa sannan ta juya ta shiga gida.
Garin jange kaltum ta je, daga dukkan alamu sun fara gajiya da barar nan ta su. Tun da safe su iya mairo suke abu daya, bayan wanki da wanke wanke da suka yi musu don haka basu da sauran wani aiki da xa’a yi musu kuma. Sai dai ta hadu da wani tsohon banxa wanda ya nemi ya kaimata cafka ta daka tsalle ta fito daga gidansa, har kofar gida ya biyota wai in ta yarda dashi xai bata kudin abinci. Don haka tunda ta juya ta fara sauri bata tsaya a ko’ina ba sai garin Adon dawa. Ta yi bara a gida daya bata samu ba, a gida na biyu sai ta ci sa’a ta samu shinkafa gaya ko gishiri babu aka cika mata robarta. Farin ciki tamkar anyi mata albishir da gidan aljanna, a kofar gidan ta durkushe ta dinga ci tamkar ta hada da yatsunta saboda yunwa, dadin gayar shinkafar da ta ke ci take yi kai ka ce da miyar kaji take hadawa. Shakewa take yi saboda rashin maiko ga babu ruwa a kusa.
Ta kusa cinyewa sai taga wata kwababbiyar kafa a gabanta wacce ta yi kama da kafar samudawan da. Ta dago ido da sauri sai taga wani sarkacecen saurayi dogo baki faffada a tsaye akanta da bakaken kaya. Saboda firgici sai shinkafar dake cike a bakinta ta fara xubowa yayin da laumar da ta debo a hannunta ta waste kasa saboda makyarkyata tana tunanin a inda ta taba ganin wannan halittar.
Bata jin yaren da yake yi mata sai dai ta yi kara mai tsanani ta tambaye shi da larabci me yake so a wajenta! Me tayi masa! Ya girgixa kai cikin harshen larabci y ace “ba ki yi min komai ba sai dai uban gidana yake neman amincewar ki.”
Ta tambaya a gigice “waye uban gidan naka!”
Yayi murmushi yace “mambela.”
Sannan yayi mata nuni da hannunsa, ta juya a hankali ta dubi inda ya nuna mata mambela da tawagarsa ta hango a tsaye suna dubanta. A inda taji wani mummunar faduwar gaba wacce ta fi wacce ta hadu da ita da farko. Kalmar “inna lillahi wa’inna ilaihi ra ji’un” ta ambata yayin da ta xura cikin gidan da aka bata sadaka da gudu. Cikin harshen larabci ta ke cewa “ku taimakeni mambela ne xai kama ni.”
Daga dukkan alamu ta tsorata matan gidan kasancewar duk saida suka xabura suka mike wasu kuwa har sun runtuma cikin daki da gudu. Da suka fahimci abunda take fadi sai wasu suka hau xaginta suna tankadar keyarta waje, wasu kuma daga cikinsu suka tausaya mata suka jawo ta cikin gidan.
Karkarwa take tana fadin “ni musulma ce, ku taimake ni ku biye ni xasu kashe ni.”
Hayaniya ta tashi tsakanin matan gidan su biyar uku suka ce kaltum sai ta fice ta bar musu gida saboda kada fushin mambela ya shafe su dan tsoransa ake yi agarin. Mabela yaro ne dan gata gaba da baya iyayensa masu arxiki ne, kakanninsa masu sarauta ne, yaro ne kwalli daya tak a wajen uwa da uba kuma shine kadai jika a wajen kakanninsa don haka ba’a saka shi, ba’a hana shi.
Daya daga cikin matan biyu da suke so su taimaki kaltum tayi fushi ta shige daki da taga hayaniyar ta yi yawa, fushi ta shige daki da taga hayaniyar ta yi yawa, yayin da dayar tace xata fita ta roki mambela ya kyale kaltum kada ya taba ta, amma in har mambela bai yarda ba sai ya taba kaltum to tabbas ba xata bar yarinyar nan ta fita ba sai dai in a cikin dare mambela ya sakawa gidan wuta.
Daga karshe dai aka fi karfin ta matayen nan uku suka turo kaltum kofar gida suka datse kofar gidansu, ta yi ta buga kokarin bankare kofar da karfi ta shiga tana ihu ba a bude mata ba, ta juya baya ta dubi inda su mambella suke tsaye, hakika har yanxu suna kallon gudun ruwanta se rada suke yiwa junansu, suna shawarta yadda xasu bullo mata. Ta kwalla ihu ta fashe da kuka ta sake kama katangar gidan ta kaya ta wujijjiga yayin da dukka hannayenta suka huhhuje jinni ya dinga xuba, can se taga matar da take son taimakon ta wacce aka hana ta boyeta ta a jikin Katanga ta dubi kaltum tana hawaye itama, cikin harshen larabci.
Ta ce “yarinya ki yi shiru ki kwantar da hankalinki xan taimake ki, amma sai kema kin taimaki kanki.”
Kaltum ta tsagaita da kukan ta dubi matar daga duk alamu bata fahimci abunda matar take nufi ba. Matar ta mika mata wani dan karfe karami dogo mai kama da axurfa. Kaltum ta karba ta jujjuya da alama bata san abun ba.
Matar ta sharce hawaye t ace “ki danna gefe ki gani.”
Kaltum ta danna, tana dannawa sai ga wata wuka kakkaifa ta fito fit. Hannun kaltum ya hau karkarwa ta fada a gigice “wuka ce.”
Matar t ace “sake dannan gefen.”
Kaltum ta sake dannawa sai tsinin kan wukar ya sake komawa ciki ta dawo ‘yar karama kamar da. Bakin kaltum na karkarwa ta tambiyi matar t ace “me xan yi da ita!”
Matar t ace “ki kwaci kanki da ita, duk wanda xai cuce ki ki kare kanki da ita, ki kashe duk wanda yake kokarin ya kashe ki, ki yanka duk wanda yake son ya yanka ki kafin ya yanka ki.”
Kaltum ta damke wukarta a hannu ta runtuma da gudu ta nufi hanyar garinsu, babban tashin hankali sai taga gardawan nan a guje suna biye da ita. Ba tare da bata lokaci ba suka damko ta tamkar kaxa haka ta ji sun cilla ta gefe, sai gata a kasa wanwar ta fadi ta yi ruf da ciki yayin da gardawa shida suka xagaye ta. Ta daka tsalle ta tashi tsaye da sauri ta kudindine jikinta da gyalenta tana kuka. Ta na cewa “me na muku, me ku ke so da ni!”
Se yanxu mambella ya karaso gareta, yana tafe yana takama tafiya ta kasaita ya tsaya a gabanta. Ya yi murmushi y ace “ke mai kyau, ya ki ke wahalar da ni ne don ina son ki! Ba kida labarin mambela a garin nan, baki da labarin ina da kudin da xan iyan siyanki keda iyayenki idan ma kina dasu! kar ki manta kasarmu ce nan, arxiki ku ka xo ci. Wuce mu je wancan gidan kafin na illata ki.” Ya nuna mata wani gida da hannu. Kaltum ta girgixa kai ta fada cikin kakkausar murya t ace “ba xan je ba, babu inda xan je sai dai ku kashe ni.”
Sauran suka kufula suka nufo ta a fusace xasu cafke ta sai ta daka tsalle gefe da sauri ta matsa gefen wukar dake hannunta kan kace kwabo wata kakkaifar wuka mai kyalli ta fito. Sai su dukka suka tsaya cak suna kallonta. Ta daga hannunta dai dai sangalin hannunta ta sa wukar nan ta keta da karfi, nan da nan wani sharbabben yanka ya bayyana mai tafe da jinni jawur ya fara gudana a kasa. Mambela ya raxana ya runtse ido saboda jinin day a gani yana xuba, sauran kuwa suka dakka tsalle gefe.
Ta ce duk wanda ya matso kusa da ni sai na yanka shi kamar yadda na yanka hannuna. Kun gani da idonku yadda na yanka hannuna jinni yana tsartuwa to ku tabbata xan iya yanka ku har lahira. Ku rabu da ni, ba ruwana da ku.”
Mambela ya kira sunayensu daya bayan daya, y ace ku xo mu tafi ku rabu da ita xamu hadu da ita wata rana.”
Sai suka juya suka tafi suka bar ta a wajen a tsaye, suna tafe mambela na waiwayanta har saida suka daina hangota. Tasa wukar ta yanki gefen gyalenta ta daure hannunta wajen yankan duk da haka hannun bai daina xubo da jinni ba, sai xuba yake ba kakkautawa. Ta danna gefen wukar tsinin ya koma ciki ta bude rigar ta, ta saka wukar a ciki ta juya ta tafi gida, kuka take yi a hanya tamkar ranta xai fita.
Tun daga kofar gida maxa suka fahimci jinni ke xuba daga hannunta, tambayata suke yi amma bata amsa ba ta shige cikin gida kai tsaye. Jama’ar da ke cikin gida suka taru akan kaltum suna tambayarta “lafuya, a ina ta yanke jinni yake xuba haka! Ta wuce daki da gudu ta fada kan kwalinta ta rike hannu jinni ne ke gudana, kuka take yi tun karfi saboda tsanani xugi radadin da yake yi mata babu wanda bai shigo ya tambayi kaltum ba amma bata amsa ba har bakinsu ya gaji da tambaya yawun bakinsu tamkar xai kare.
Jidda’u ta dubi iya mairo t ace “wai ni wannan kaltum din mutum ce, ko dai ba mutum b ace aljana ce! Ni fa na rasa kanta tsakanin jiya dayau.” Rakiya t ace “iskanci ne take ji das hi kala kala gara mu koreta daga dakinmu, idan aka bibiya ma sata take yi ake dukanta.”
Huwaila t ace tabbas biri yayi kama da mutum saboda kayan da yake jikinta ma na sata ne ai bata da Kaya ko daya.”
Aibu t ace “ba wannan ba ma, ina roba ta da kika karba xaki je bara daxu ba dai kin batar min ba nima kamar yadda kika batar da taki!”
Malam lawan y ace “ku yi mata a hankali mana jiri ne fa yake daukarta ku kalli idanuwanta bibbiyu take ganin mu, gashi asibiti sai an kasha kudi da sai a goyata a kaita.”
Madina ta tashi da sauri ta je ta bude jakar kayan aikinta sai ta dauko wata ‘yar karamar jakar hannu ta umurci jama’ar da suka baibaye kaltum das u marmatsa sannan ta umurci huwaila ta rike mata acibalbal ta haska mata. Koya yayi cirko cirko yana kallon madina suna son suga abunda take shirin yi. Ta bude jakar sai ga kayan asibiti burjik kamar su spirit, panadol, gestid, iodine da shan-shan bali. Ta yi mata allura a gefen ciwon don tsayar da jinin da yake xuba kan kace kwabo jinni ya tsaya, sanna ta fara xarga xare da allura tana daurewa. Ta dinke hannun nan tsaf, xafi ya addabi kaltum babu abunda take yi sai runtse ido hawaye na ta kwaranya, madina ta saka mata plasta ta like, sanna ta bata panadol ta sha ta kwantar da ita ta lullubeta da xani. Jama’a suka dinga mamaki suna tambayar madina ashe dama ita likita ce! Ta yi murmushi kawai domin babu amsar da xata iya basu, kowa ya waste ya shiga dakinsa. Ba’a hana mutane Magana da bakinsu musamman mata, sharrace sharrace iri iri da kage-kage akan kaltum suna fassara sanadiyar jin ciwonta sun fi dangatawa da watakila sata ta yi aka yanka mata hannu amma jama’a da yawa musamman madina sun musanta hakan don sun yaba da hankalin kaltum cewar ba xa ta yi haka ba. Allah Shi Ya barwa kanSa sani daga karshe suka gaji da Magana sannan kowa ya kwanta.
Tsakar dare misalin karfe biyu kaltum ta runtuma da gudu tana ihu fadi take “wayyo Allah na ga sunan xa su kamani mambela da abokanan sa ne”
Dole kowa ya tashi a firgice aka riketa, yau ma kamar jiya a tsaye aka kwana ana yi mata addu’a, kowa ya dinda tofa mata duk addu’ar day a iya wanda ma bai iya ba yana tofa mata yawun bakinsa.
(irin su o’o ken an, ni kuma na yi dariya……. Na ce dai ayi hankali, kar a topa min yawu ……..)
Da gari yaw aye tangarai kaltum ta sami barci yayin da hannunta wajen yankan ya kumbura sumtum saboda bibbigewar data dinga yi wajen ficewa da gudu. Kaltum abun tausayi har hawaye madina take yi don tausayinta.
Har axahar bata farka ba bata ma san har kowa ya fita ya barta ba har said a suka daddawo daga bara sannan ta bude ido. Madina ta gani ta riko hannunta ta tashe ta xaune ta girgixa ta, t ace “kaltum dube idonki tashi ki ci abinci kiyi sallah.”
Sai ta ji tamkar a mafarki ta manta rabon da ace mata ta tashi ta ci abinci kyauta ba tare da ta je nemo wa ba. Ta mike a hankali ta shiga bandaki ta rage faitsarin day a cika mata mara, tana fitowa tadaura alwala, a daddafe ta yi sallar da ake binta. Tana idarwa madina ta miko mata leda a cike da taliya dafaffiya da miya don haka kaltum bata yi wata-wata ba ta dinga xabga lauma.
Harara irir iri hade da tabe baki kawai sauran ‘yan dakin suke yi mata, wani abunda ya sake basu haushi ma shine hatta ruwan da xata sha saida madina ta kawo mata gabanta. Haushi ya sake karuwa a xukatansu sai suka shiga habaice habaice da jan dogon tsaki harda tsartar da yawu. Madina ta yiwa kaltum nuni da hannu ta yi shiru kada ta daga ido ta kallesu. Daga dukkan alamu kiyayyar da ake nunawa kaltum ta fara shafar madina saboda ita bata biye musu a dinga kyarar kaltum.
Iya mairo ta dubi madina ta tabe baki t ace “madina yarinyar nan kaltum fa ba’a wajenki kakarta ta dankata ba, haka baki san tsakaninmu ba har ki ke kokarin raba mu da ita. Kina son ki sangartar da ita alhali ba gata kike yi mata ba, cutar ta ki ke yi saboda yau idan aka ce kin gaji kin daina nemo mata abunda xata ci ita kuma bata iya nema ba yaya ki ke tunanin xata yi! Sai dai ta fara daukar na wasu.”
Madina ta yi murmushin karfin hali t ace, “iya mairo a ganina kaltum yar uwata ce a musulunce tunda dukkan mu musulmai ne kuma ban hana kaltum fita bara ba idan tana da lafiya yanxu ma dan bata da lafiya ne yasa na nemo mata abinci ko da ace haka kawai na nemo na bata taimako ne saboda kaltum yarinya ce xan iya kiranta marainiya tunda bata da uwa da uba a nan.”
Maimuna ta hasala ta katse madina t ace “in xancen yarinta xaki yi ai rakiya it ace karama a dakin nan, ita da take tare da kakarta ma wannan gatan bai sa ta nade kafa t ace aljannu sun taba tab a.” sais u dukka suka hau kunfar baki ana tsuye madina da kaltum. Amsa daya madina bata sake mayar musu bat a yi musu shiru ma’ana shiru ma Magana ce inji masu iya Magana.
Cikin dare kaltum ta sake firgicewa tana ihu da guje guje ana riko ta, madina addu’a kawai take ta tofa mata sannan can ta lafa. Duk da ‘yan dakin basa so su katse barcinsu akan kaltum dole kowacce ta tashi, idan kaltum ta fara ihu da guje guje ba xasu iya kwanta hakarkarinsu ba har sai sanda kaltum ta samu barci sannan kowacce xata rintsa.
Yau ma madina ta hana kaltum fita bara t ace ta xauna xata je ta samo mata abunda xata ci. Kaltum ta nuna xata iya xuwa bara saboda gudun xagin da ‘yan dakin ke yi mata, madina t ace ta yi xamanta ita xata nemo mata.
Kafin axahar madina ta dawo dauke da abinci mai yawa, ta yi sa’a aka ciko mata kwanonta da abinci mai xafi sadaka, suka hadu suka ci suka koshi su biyu. Kaltum ta yiwa Allah godiya ta yiwa madina godiya.
Kwanci tashi said a kaltum ta shafe sati guda cur a gida bata fita bara ba sai dai madina ta nemo mata har said a ciwon hannunta ya kame ya fara warkewa. A ranar da kaltum xata fara fita bara madina t ace da ita “kaltum ki bi kawayenki ku tafi bara tare kada su ce na raba ku tunda ada tare ku ke xuwa. Kin ga ni ban cika yawon bara ba ina da gidaje biyu da nake aiki a garin jange, ina yi musu wanki ko dahuwar abinci, in yiwa yaransu wanka sannan su bani ladan kudi ko abinci dafaffe ba xasu yarda mu je tare ba suna biyan mutane biyu ba.”
Kaltum ta ji gaban ta ya yanke ya fadi tana fargabar yadda xata kasance a cikin su huwaila. Hakika xa su yi mata korar kare don suna jin haushinta matuka. Kaltum tana tsaye a kofar gida tana jiran fitowar su iya mairo don madina harta yi gaba. Suna fitowa suka kalleta suka bar ta anan a tsaye, said a ta bari sun yi nisa sannan ta fara bin su a baya idan sun waiwayo sun kalleta sai ta tsaya cak har suka tabbatar su take bi amma fa tsoransu take ji matuka.
Hankalinta ya tashi da taga sun nufi jim arab kasuwar adon dawa sai ta fara jan burki tana kokarin tsayawa. Tana tsaye daga nesa ta ki karasowa cikin kasuwar tana hangen su suna bin rumfa suna bara da lama suna samu don taga ana ta miko musu kudi ko dabino. Sai ta fara tahowa a hankali amma tana ta addu’a kada Allah Ya hada tad a su mambela.
Ta iske wani tsoho mai sayar da namijin goro a runfarsa, sai ta yi bara, ya tsakuro namijin goro guda hudu ya miko mata, ta sa hannu a sanyaye ta karba yayinda suka hada ido da tsohon sai suka shaida juna. Wannan tsohon ne day a kwace ta daga hannunsu mambela. Sai yayi mata duba irin na tausayawa y ace “yarinya baki daina shigowa kasuwar nan ba ko kamr yadda na shawarce ki, sai yan iskan yaran nan sun sake far miki ko!”
Ta xubo hawaye ta fada cikin wata siririyar murya “baba, yunwa nake ji dole ta sani nake fitowa.” Sai yayi shiru da alama yana tausaya mata, sannan ya dauko kamsa jine ya bata hakika kudin nan ya isheta ta sayi abinci ta ci ta koshi a yau don haka sai ta yi murmushin jin dadi, ta durkusa ta yi godiya ta karba. Ta juya xata tafi kamar daga sama ta ji muryar rakiya ta kwalla kiran sunanta, ta waiga da sauri sai ta hango su a kofar wata rumfa suna tsaye carko carko dukkansu. Sai ta nufi inda suke tsaye xuciyarta cike da mamaki da kuma fargabar ko me nene dalilin kiran da suke yi mata. Jikin ta na rawa ta isa gare su.
Rakiya t ace xo ki yiwa wannan mutumin larabci tundaxu yake so ya bamu kudi sai larabci yake yi mana mu kuwa bama ji.
Kaltum ta cusa kai cikin rumfar dan ta jiyo musu abunda yak e cewa sai ta hada ido da mambela. Yayi murmushi ya fada cikin harshen larabci yace, “sannu da xuwa yake abar kaunata a ko da yaushe, ce musu nayi su kawo min ke xan basu metan jine (dari biyu) ke kuma idan kin amince da nixan baki alif jine(dubu daya) ya ishe ki ki ci abincin wata guda idan yak are in kara miki.
Kaltum ta tuntsura ta fadi kasa saboda fargaba ta mike a guje ta falfala da gudu kai ka ce gudun fanfalake take yi saboda tamkar kafarta xata tabo keyarta. Mamaki ya kama su iya mairo suka rasa abinda ya fada mata su dai sun gay a mayar da kudinsa aljihu sannan yayi musu korar kare.
ADON DAWA 6
BABI NA HUDU
Gari yaw aye hantsi ya keto, yayin da fataken gidan nan suka dinga baxama neman abunda xasu kai bakin salati. Kaltum a xaune take a tsakar gida cikin hantsiba sunkuye a kasa da alama rashin lafiya a jikinta. Mutanen gidan mata da maxa suka yi ta tsayawa a kanta suna tambayarta shin lafiyarta kalau ko jikin ne! sai ta girgixa kai t ace das u lafiyarta kalau, ba tare da tad ago ido ta kallesu ba. Hajara c eta fito daga cikin dakinsu ta tsaya akan kaltum ta dade a tsaye tana harar ta. Kaltum tad ago ido a hankali ta dubi wacce ke tsaye a kanta, kallon da hajara tayi mata na wulakanci shi yasa ta gane bada alkhairi take nemanta ba don haka sai ta mayar da kanta kasa ta sunkuyar.
Hajara ta girgixa kugu t ace “kaltum, na rasa robata da gurasa aciki wacce na ajiye jiya da daddare a wajen shinfidarki.”
Kaltum ta girgixa kai t ace “ba ni na dauka ba.” Hajara ta fusata t ace, “wane shegen ne xai dauka idan ba ke ba! Ko kin dauka bamu da labarin sace sacen da ki ke yi a gari!”
Kaltum tad ago da sauri ta dubi hajara hakika ko ba’a fada ba kaltum taji haushin maganar amma sai ta maida kanta kasa ta sunkuyar. Iya mairo da jikarta rakiya suka fito suka dubi kaltum suka ce “yauma ba xa ki je bara ba, sai kowa ya tafi bara an bar miki gidan sannan ki lalube mana ‘yan abubuwanda mka ajiye ko!”
Huwaila t ace ai ba lefin kowa bane laifin madina ce da ta shagwabata, sai ta je tayi aikatau hard a jido ruwa a biya ta amma ta je ta siyo musu abinci ta kawo su ci tare shiyasa ma bata fita bara sai taga dama. Taci ta koshi dare yayi ta dinga ihun karya tana hana mu barci.” Amina ta fito daga daki t ace “idan gari yaw aye saita kwanta tayi ta barci har yamma mu kuma mu fita nema mu yini muna yawo lokacinda ya kamata mu kwanta sai ta hana mu barci, gaskiya a raba man daki dan yanxu ma ciwon kai na ke yi saboda rashin barci.”
Hawaye ya dinga xuba shaf shaf shaf daga idanuwan kaltum. Madina c eta fito daga wanka sanye take da hijabi sa daurin kirji ta karasoi da sauri inda suke t ace “haba ku kuwa bayin Allah me kaltum tayi muku a rayuwa da kuka takura mata haka! Xagin safe daban na rana daban dan kun ga bata magan, ku kira ta barauniya, ku kira ta ‘yar iska, ku ce mata munafuka. Da me xa ta ji, ciwon dake addabarta! Baku ganin da xaxxabi take kwana kullum saboda raunin da ke jikinta! Ku tuna fa ku musulmai na Allah Yan a son kaltum tunda Shine Ya halicce ta. Baku ganin hakkinta da ku ke dauka xai iya kaiku wuta, shirun nan da take yi tsananin hakuri ne, hakurin da take yi bata rmawa xai iya sawa Allah Ya yi mata sakayya da KanSa.”
Maimuna ta katse ta , tace “madina dan Allah kiyi mana shiru ke ba kya ganin laifin kaltum, ke c ma mai xuga ta har wata rukiyya kike mata wai ita mai aljannu, mu dai gaskiya tana hana mu barci mun gaji.”
Madina ta ji hawaye yan surnano mata daga idanuwanta dan takaici, ta share hawaye ta dubi maimuna t ace “haba maimuna ban taba xata ba wannan maganar xata fito daga bakinki a matsayinki na babba. Shekarunki talatin da biyar kin haifi kaltum hard a ma wadanda suka girmi kaltum. Kinsan ciwon haihuwa, kin san dadin ‘ya’ya dan kusan kullum kina kuka idan kika tuna ‘ya’yanki da kika baro, ban dauka xaki ki tausayawa ‘ya’yan wasu baa she xaki biyewa rakiya, huwaila, amina ‘yan matan da basu taba haihuwa ba!
Ke ma hajara ba yarinya bace tunda kin kusa haihuwar kaltum shekarunki ashirin dad a biyar ‘yayanki uku. Ba kwa tunanin abunda ka yiwa ‘yar wani sai an yiwa naku! Iya mairo kin ci amana tunda yarinyar nan ke aka dankawa amanarta da tun kakarta bata tafi ba sai ki fada mata baki karba ba, amma kika karba ki ka xo kina banbanta tad a jikarki. Ko ba komai kece wacce kuka fito gari daya ko albarkacin sanin asalinta da ki kayi bai kamata kiji ana kiranta barauniya ba kiyi shiru.”
Kan kace kwabo hayaniya ya hargitse tsakanin madina das u dukansu. Harda masu dammara xa’ayi dambe. ‘yan sauran dakunan suka fito maxa da mata suna bada hakuri, da yake duk fita xasu yi daman sun shirya dan haka aka tura su maimuna waje ita kuma madina aka tura ta cikin daki, sannan kunnuwansu suka huta da hayaniya. Kaltum tana xaune har yanxu kantga a sunkuye yake a kasa.
Madina ta dade a daki bata fito ba sai shehshshekar kukanta ka ke jiyowa daga cikin dakin da alama kuka ta ke yi. Sai da ta tabbatar ba kowa a gidan sais u biyu sannan ta fito tsakar gida a fusace ta dubi kaltum. Ta kira sunan kaltum, sai tad ago a gigice hankalinta a tashe ta dubi madina ta amsa kiran da tayi mata.
Madina t ace “ki kula da abunda xan fada miki, ki fahimci a inda kike da kuma abunda kike ciki. Ki sani xaman nan da mukeyi xama ne na kowa yayi ta kansa.” Kaltum ta ci gaba da kallonta sokoko da alama bata fahimci abinda take fada mata ba.
Madina ta ci gaba da cewa “ban hana ki yin hakuri bad an Allah Yana tare da mai hakuri, yana dad a kyau yin hakuri, amma ina baki shawara ki tashi haikan ki kwatarwa kanki hakkinki na ‘ya dank e ba baiwa b ace. Saboda me xaki xama sakarya a cikin al’umma, ki xama juji wacce ake xuba mata shara da aka yayimo daga ko ina! Yara da manya kowa kaltum yake tsangwama bakya katabus sai kuka, to ina mai baki shawara ki nutsu kisan abunda kike yi.”
Hawayen kaltum k eta ambaliyar xubarwa shiyasa madina ta kasa ci gaba da magan sai itama ta fara hawayen.
Madina ta share hawaye da gefen hijabinta t ace “kaltum Allah Yayi miki xurfin ciki wanda duk irin tambayar da xa’ayi miki baxa ki fadi halin da kike ciki ba,
Abubuwa da dama sun faffaru wanda ya kamata ace kin samu mutum daya kin fada masa amma kin ki. To ki sani wannan kunshe kunshen da kike yi a xuciyar ki ba komai xai jawo miki ba sai ciwon xuciya ko hawan jinni. Kina yarinya karama xa’aji tuf kin fadi xuciyar kit a fashe.
Gara ki dinga amayar da abunda yake damunki, wacce kika san xata rufa miki asiri ki shawarce ta tunda kin rabu da iyayenki da ‘yan uwanki dole ki samu wasu su xamar miki abokan rayuwa da aminci.”
Har yanxu kalma daya bata fita daga bakin kaltum ba, hawaye kawai take yi kanta a sunkuye a kasa.
Madina ta rike kugu ta fada cikin fushi da kunar xuciya t ace “kaltum, waye mambela!”
Wannan karon a gigice kaltum tad ago ta dubi madina duba mai tafe da tsantsar mamaki gami da faduwar gaba. Madina ta sake maimaita tambayarta, nhar yanxu ba amsa daga bakin kaltum tambaya ta uku da madina xa tayi bada baki ta yi mata ba, wani wani xabgaggen mari ta kifa mata mari wanda said a kaltum ta kwanta kasa ta rike kunci yayin data fahse da kuka mai tsanani.
Madina ta fisgo hannunta ta xaunar da ita ta rike kunnenta na hagu da karfi har said a kaltum tayi kara. Madina t ace “waye mambela! Ko kuma wacece mambela idan mace ce! A ina take! Me yake faruwa a tsakaninku!”
Kaltum tana mai matukar mamaki inda madina ta ji sunan mambela, sai ta shiga tunanin waye yake labewa har ya san abubuwan da suka faru tsakaninta da mambela, domin ita bta san abubuwanda take yi a cikin dare ba, bata san tana fita da gudu ana rike tab a har take ambatar gasu mambela nan xasu kasha ni har kowa ya ji.
Madina ta tunkude ta gami da rankwashin goshinta t ace “to yau rabuwarmu ta xo ni da ke, yau ne rana ta karshe dana nuna na sanki, nasan sunanki a rayuwata, kema kuma koda wasa kada ki sake nuna wa kin taba ganina a rayuwarki. Hanyarki daban, tawa daban bari ma sauran ‘yan dakin su xo su kore ki daga dakinmu baxan hana sub a saboda na fahimci xama da irinku hatsari ne, xaki iya kasha mutum ba’a sani ba saboda xurfin cikinki yayi yawa, bana xama da masu hali irin naki. Ashe su iya mairo sun fin gaskiya har nake dukan kirji nake fada a kanki, babu ruwana dake har abada haka ko xaki fice waje da gudu da tsakar dare ba xan kamo ki ban a daina sai dai in kin tafi a rasa ki, ki koma can wajen mambela ko mutum ne ko aljani ne, ko matattune oho. Na daina damun kaina a kanki, na daina tausayinki, na daina shigar miki fada, duk abunda mutane xa suyi miki ido ne nawa.”
Madina ta shige daki a fusace ta ratayo Jakarta kamar mai shirin fita unguwa ta fito ta iske kaltum a durkushe a bakin kofar dakin tana kuka mai tafe da ruri idanuwanta sun yi jawur kallo daya madina tayi mata ta Harare ta, ta dauke kai tana kokarin kewayeta ta fice sai kaltum ta rike kafarta.
Ta ce “aunty madina, kiyi hakuri ki yafe min abinda nayi miki.”
Madina ta tsaya cak t ace “ai ni baki min laifi ba, shawara na baki baki dauka ba. Tambaya nayi miki baki amsa bad an haka xama dake ba xai yiwu ba, bana xama da masu bakin hali da xurfin ciki. Na kasa gane ko ke wa cece, ko ina kika dosa, ko wane hali kike ciki! Dan haka na rabu da ke kaltum kamar yadda na rabu da ‘ya’yan ciki na a Nigeria. Kinsan kuwa tunda na rabu da ‘yayan ciki nab a xai yi wahala in rabu da ke ba wacce na hadu dake a hanya a kwanan nan. Ni haka nake al’amurana xaman yarda na ke yi da mutum, da xarar babu yarda to bana kara yin ko second daya xan matsa daga wajensa. Kaltum, ko baki bar dakin nan ba hakika nix an bar miki dakin a tunanina ada na dauka ke mutuniyar arxiki ce, ashe bah aka ki ke bad an haka na daina tausayinki ki je ki karata.”
Madina na rufe bakinta sai ta fisge kafarta daga hannun kaltum ta juya a fusace xata fice, cikin kuka mai tsanani kaltum ta sake wawuro xanin madina ta riketa kam tana cewa ki taimakeni anty madina karki rabu dani ba ni da kowa sai ke a kasar nan, na yi alkawari xan fada miki komai.”
Madina ta ji sanyi a ranta sai ta juyo, ta daga kaltum tsaye ta karkade mata yashinda yayi mata bududu a jiki. Ta dawo da ita inuwa ta xauna yayin da itama ta samu waje ta xauna. Madina ta san har ga Allah tana kaunar kaltum a ranta tamkar jinin jikinta, tana tausayin rayuwarta dan haka ta kudiri niyyar taimaka mata ba xata iya rabuwa da ita ba. Ta yi furucin rabuwa da ita dan ta tsorota ta, tana tsananin son ta ji tarihin rayuwar kaltum da asalinta da abubuwan da suke faruwa da ita suke damunta. Tana so taji ta ina kaltum ta samo kyakkyawar halittar ta wacce kyawunta ya xama abun kwatantawa da sha’awa, sannan a ina ta samo sunanda take kira idan ta firgita wato, mambela! A ina kaltum ta samo ilimin addini dana xamani haka! Don ta iya larabci tamkar jakar makka. Haka ta iya turanci tamkar karamar jakar London, shin ‘yar gidan masu hali ce ko ‘yar gidan yak u bay ice! Tana da iyaye ko kuwa marainiya ce! Meye ya raba tad a kasarsu ta taho sudan! Shin ita kuwa a matsayinta na yarinya karama meye damuwartada hart a yadda xa ta yi hijira dan ta samu salama! Anya goggo fatu kuwa kakarta c eta jinni, amma take axabtar da ita hart a iya tafiyar tat a bar ta bata damu ba duk da yadda aka san soyayya da shakuwar dake tsakaninta da kakarta!
Amsoshin tambayoyinta suna nan tafe a bakin kaltum, kamar yadda ta ji kaltum ta soma bata labarinta kamar haka, wanda ke kunshe da duk amsoshin tambayarta kakaf.
BABI NA BIYAR.
Kaltum ta tsaya tunanin ta inda xata soma labarinta, domin du duniya bata taba ba kowa labarin rayuwarta ba.
Madina ta katseta t ace, “ina sauraron ki fada min meye damuwarki!”
LABARIN KALTUM
Ta ce “suna na kaltume, sunan mahaifina saleh mahaifiyata kuma safiya sunanta ana kiranta da sofi.
Mahaifiyata ‘yar asalin wani gari ce da ake kira da IBONKOMO a cikin kasar Cameroon, mahaifina kuwa dan asalin xangon daura ne. mahaifiyata ta tashi a marainiya ba uwa ba uba sai ita sai kanwarta daya mai suna joda iyayensu suka mutu suka barsu, kawunsu yayan mahaifiyarsu mai suna jalo shi ya rike su har suka girma a bisa amana, ya aurar das u ga wanda suke so ba tare da takura ba.
Mahaifina shima maraya ne tun bayan da aka yaye shi mahaifiyar sat a rasu ta bar shi a hannun matar babansa ita GOGGO FATTU.
Goggo fatu c eta rike baba na tun yana da shekara biyu har rana irin ta yau ko tsinke ta ajiye baya tsallakawa saboda tsananin biyayya da tsoronta da yake. Daman ita bata taba haihuwa ba a duniya, mahaifina shi kadai ne aka Haifa a gidan su don haka bas hi da abokin shawara sai goggo fattu ko mahaifinsa bai isa ba.
Hakika tarihi ya nuna mahaifina ya sha wahala, axaba da makircin goggo fattu tun yana yaro har yau bai huta ba. Mahaifina ma kenan bai isa ba balle matarsa balle kuma ni ‘yarsa karan kada miya don haka kacokan dinmu sai abinda t ace xamu yi, sai yadda tayi da mu.
Madina ta gyara xama ta dubi kaltum t ace “na ji asalinki. Amma ta yaya saleh da sofi suka hadu ita da take Cameroon shi yana xangon daura!”
Kaltum tayi murmushi t ace “mahaifina ne ya je garinsu sofi yawon fatauci, tun yana yaro yake bin mahaifinsa suke xuwa tare har yake xuwa shi kadai daya gane hanya, suna shiga da kayanmu na nan gida Nigeria can su sayar sannan su kawo na can su shigo das hi ta a haka suka hadu. Aure kamar xai yiwu kamar ba xai yi wu ba, Allah Yasa ya yiyu aka yin ammadukka bangarorin biyu ba’a son ransu ba a bangarensa da bangarenta.
A bangaren su sofi suna ganin hatsari ne su dauki ‘yarsu su bawa bako wanda ba’a san asalinsa ba, haka suma danginsa suke ganin duk ‘yan matan das u ke xangon dauura ya rasa wacce xai aura sai ya fita wata kasar sannan xai yi aure. Karfin addu’arsu su masoyan da tsananin rabon haihuwa daya rantse sai aka yarda aka daura auren. Amma fad a farko dangin sofi basu yarda ya taho da ita ba sai dai ya kama haya a can ya ajiye ta, yana xuwa yana dawowa said a ta shekara sannan suka yaba da hankalinsa na ladabi, amana da rikon gaskiya. sannan aka sami wadanda suka san asalinsa ‘yan xangon daura amma maxauna garin su sofi sun yi gidaje, sun yi aure, sun hayayyafa sannan aka bari ya taho da ita. ‘yan uwanta suka rako ta har xangon daura suka ga mahallinta da ‘yan uwansa sannan suka tafi suka bar ta a lokacin tana dauke da karamin cikina.”
Madina ta nisa t ace “to naji yadda iyayenki suka hadu har suka yi aure. Da babanki ki ka yi kama ko da mamarki!”
Tambayar madina ta bawa kaltum dariya, sai ta kyalkyale da dariya sannan t ace, “da mama na nayi kama sak babu inda na baro ta, idan kika ganta kika ganni idan baki lura ba sai ki kira tad a sunana ko ki kirani da sunanta saboda bat a da kiba kma ba tsufa ba. Kamar yadda na fada miki fulanin Cameroon ne danginta kyawawa ne masu tsananin farar fata sai ka dauka larabawa ne, gashinsu har baya. Banyi kama da mahaifi nab a kwata kwata saboda shi baki ne, amman kanne na biyu sun yi kama das hi sak”
Madina tayi murmushi t ace “yaya xaman sofi ya kasance a xangon daura!”
Kaltum tayi murmushi t ace “gidan kasa da katangar xana gadon mahaifi na ke nan anan aka kai sofi, tana xaune a daki daya, goggo fattu a daki daya don a shekarar da aka yi auren baba na mahaifinsa ya rasu. Don haka goggo fattu ta sami filin casa sofi da saleh, sai yadda take so xa’a yi, sai abinda t ace xa suyi. Babu wahalar da sofi bata sha ba, ga cikin fari a wajen yarinya ‘yar shekara goma sha hudu, har ciki ya tsufa kuma ta hana a kai ta garinsu ta haihu. Da watan haihuwarta ya kama kawu jalo ya aiko da matarsa Asta da ‘yarsa Ladi su xo su dauko safi ta haihu a gida amma goggo fattu tayi musu dadin baki luf luf wai sofi ‘yar t ace tamkar wacce ta Haifa a cikinta don haka su bar ta a wajenta xata kula da ita sosai. A haka suka hakura suka tafi suka bar ta suna ta yabon kirkin goggo fattu, ita kuwa sofi tsoro ya hana ta fada musu gaskiya.
A cikin dare nakuda ta tashi sofi daga barci sai ita sai saleh, tashin farko daman dakin goggo fattu saleh ya nufa da gudu ya buga mata kofa ya sanar mata cewar sofi tana nakuda. Ta xage shi tsaf wai bashi da kunya meye abin gigicewa har ya fada da bakinsa matarsa tana nakuda. Ya sunkuyar da kai kasa yana bata hakuri, ta umurce shi day a fice daga gidan kada ya dawo sai gobe da safe.
Yana fita ta rufe kofar gidan sannan ta leka dakin sofi ta isketa a tsugunne ita kadai tana murkususu, tana ganin goggo fattu sai ta fashe da kuka ta hau kiran sunanta, amma goggo fattu ta tabe baki t ace “ki bar kiran sunana ma don ba xan shigo inyi ta fama da ke har gari yaw aye ba, haihuwar da bata da tabbas xata fito ko ba xata fito yanxu ba.”
Ta juya ta koma dakin ta tayi kwanciyar tat a bar ta a wannan halin. Allah cikin ikon Sa ta haihu ita kadai, jaririya ta fito fuk akan tabarma gtana tsala kuka haka mabiya ma ta fito . sofi ta rasa yadda xata yi da ni sai ta sami leda ta kwashe mabiyar da jaririyar ta rufe a leda fuskata ce kadai a bud eta dora ni akan gado ta xauna a gefena tana ta kuka har gari yaw aye tangarai sannan goggo fattu ta shigo dakin ta iske halin da muke ciki. Jaririya a kunshe a leda ga cibiya nan ba’a yanke ba a jikin mahaifar sai jini jage jage. Duk idanuwana, hanci na da kunnuwana duk busashshen jini ne.
Ta dau dogon salati ta dinga dimawa sofi duka a baya tana kiranta munafuka so take ta ja mata xagi a gari a c eta kasheta ta kasha jaririyar. Wai me yasa da haihuwa ta xo bata kwalla mata kira ba ko ta xo ta kira tad a kanta ba, xata xo ta kunshe ‘ya a leda ba’a yanke mahaifa ba alhali mahaifa shanye jini take.
Tayi tax age xagenta tana borin kunya sannan ta yanke cibiya, tayi ma ‘yar wanka ta gyara mai jegon sannan ta bude gida mahaifina ya shigo ya iskemu tsaf.
Haka danginsu su kayi tayi mata sannu da kokari yadda ta karbi haihuwar sofi tamkar ‘yar cikinta don sun iske mai jego sumul da jaririyarta kalau.
Bayan an yi suna aka saka min Ummu Kaltum sunana da goggo fattu ta xabar musu kenan wai sunan mahaifiyarta ne, basu isa su saka sunan mahaifansu bad a suka rasu tuntini. Sai dangin sofi suka xo suka dage xasu tafi da ita da kyar goggo fattu ta bari suka tafi da ita, mahaifina ya fi son haka daman. Bata dawo ba said a nayi wata uku nayi kwari sannan muka dawo xangon daura tun daga lokacin na fara shiga halin da nake har yanxu yak e bibiyata a rayuwata.”
Tab ashe haka wasu suke da busashshen imani!!!
Allah Ka sanya mu pi karpin xukatan mu, sannan Ka dada kare mu daga sharrin miyagu.
Se a saurara nan gaba domin jin yadda ta
ADON DAWA 7
.
.
“kamar yaya halinda kike ciki har yanxu yake bibiyarki!”madina ta tambaya cikin rudani kaltum ta xubo da hawayenn daya cika mata ido tace “goggo fattu ta hana mahaifina ya dauke ni balle yayi min wasa ko ya rungume ni mu shaku. Ko kallona yayi sai ta dauki dogon salati kai kace mutum ya kashe. Ta ce wannan ai rashin kunya ne don haka kwata kwata baya kusanta ta. Haka mahaifiyata bayan nono da xata bani babu sauran soyayyar uwa da ‘yarta, idan kuwa ta cika daukana da tattalina sai xagi da Allah wadai take yi mata kala kala. Komai aka yi da ni, sai goggo fattu tace rashin kunya ne.
Wata rana har kuka goggo fattu ta ke saka musu, ta ce dan bata da haihuwa,a haka iyayena suka kyaleni, sai yanda goggo fattu ta yi da ni.kar ki dauka kulawar take bani, sai ta ajiye ni a dakinta in ta kuka, sai taga dama sannan tace sofi ta dauke nita bani nono. Har aka yaye ni na bar dakin mahaifana xuwa dakin goggo fattu, ba komai kuma take min ba sai duka da rankwashi musamman idan nayi fitsarin kwance, aka ce komai sanyin asuba xata kore ni waje tsirara bayan ta xane ni.
A lokacin karayar arxikii ta far wa baba na bashi da cin yau bare na gobe sai ya nemi shawara xai sayar da kiwonsa da mahaifinsa ya bar masa gado, akuyoyi da yawa da gonaki xai yi jari, sai ta ki amincewa t ace bakin ciki yake yi don ta xuba nata kiwon a cikin nasa shine yake so ya tona mata asiri a garin ace daman duk tulin akuyoyin nan ba nata ba ne don tayi karya t ace duk nata ne. muka dade cikin rashi da fatara da yunwa har Allah Yasa kawu Isiya kanin mahaifin babana ne yayi masa hanya ya samu aikin gadi a kano,ya tafi kano amma ya bar iyalansa a xangon daura.”
Madina ta gyara xama ta gyada kai ta ce “lallai yanxu xa’a fara labari. Daga nan yaya aka yi? ”
Kaltun ta girgixa kai ta ci gaba da Magana cikin marainiya murya ta ce “duk karshen wata yake xuwa ya kawo mana kudi albashinsa don mu ci abinci amma yana tafiya xata juya akalar kudin tayi sha’anin gabanta dasu .kuli –kuli guda uku shine bincin mu na rana, tuwon dawa da miyar kuka lami ko wace babu shine abincin dare, dumamensa sine abincinmu na safe.Duk muka rame muka lalace ita kuwa har tsire da kaxa take ci acikin shinkafa muna kallonta.
Da mahaifina yaga alamar mun rame sai ya dinga tambayar mahaifiyata ko lafiya muke rame wa?
Ta boye masa don itama irin halinta kenan ba xa ta yi Magana ba ko abu xai kashe ta, sai a makwabta aka fada masa duk abunda yake faruwa damu. Ya samu goggo fattu yace yana so ya tafi kano da sofi itama ta samu aikin wanke-wanke da shara duk wata xasu dinga hado mata albashinsu duka suna kawo mana ni da ita. Tuni ta amince sofi tabi mijinta suka tafi kano suka barni cikin wahala Kaman ta kashe ni tsunma ma ya fi ni nauyi, ga ciwuka kala-kala kullum.
Mahaifina bai fasa xuwa ba, duk wata xai shiga mota ya xo xango daura ya kawo kudin albashinsa fiye da rabi. Ina ganinsa sai in hau murna ina kiran “ga baba, ga baba.” Amma sai ya ture ni gefe in fadi kasa, ya dauke kansa baya kallon in da nake saboda kada goggo fattu t ace yayi rashen kunya.
Ina shekara uku yunwa da ciwon kyanda suka sa ni a gaba na rame sai kashi da fata, ido yayi min xuru –xuru kamar mai ciwon kanjamau sai ka kirga kashushuwan dake kirjina. Sai in suma sau biyar a rana wanar ba xan rayu ba sai ta ji tsoro kar in mutu a hannunta don haka sai ta nemi kawu isiya ya kawo mu har gidan da mahaifina yake gadi, suka ci sa’a kuwa a boy’s kuarter gidan suke xaune da mahaifiyata.
Ta hau fada hard a kumfar baki tana cewa sun gudo kano sun xo sun kwanta sun bar ta da wahala tana fama da ‘yarsu ko barchi bata yi, don haka ga ‘yar sunan su rike kayansu. Ta jankwabar dani da kayana ta juya ta tafiyarta, suna binta suna rokonta ta xo ta huta ta ci abinci, tace ba xata dawo ba dole ta tilastawa kawu isiya dole ya taso suka hau mota suka koma xangon daura.”
Madina ta girgixa kai t ace “daman haka halin goggo fattu yake! Ni fa na yi mamakin ace kaka ce take tsangwamar jikarta haka yadda naga tana kyararki a mota.”
Kaltum ta surnano da hawaye ta cika mata ido ta ci gaba da cewa “mai gidan da muke gidansa sunanasa Alh Adnan Mahbub, shi da matarsa Salaha sai ‘dan su daya Mashkur. Mashkur sa’ana ne shima a lokacin shekarunsa uku kamar yadda shekaruna uku cur a duniya. Alh Adnan yana da arxiki mai yawa duk da matashi ne a lokacin, aurensa ne na fari kuma haihuwarsa c eta fari bai wuce shekaru talatin ba aduniya, matarsa kuwa baxata wuce shekaru ashirin da uku ba don da haka kusan sun girmi iyayena ma. Suna xaune a kataferen gidan, kerarre mai girman gaske yayin da mu kuma muke xaune a boys quarters in gidan.
Alh Adanan na ganin halinda nake ciki na rashin lafiya sai ya ji hankalinsa ya tashi ya umurci direban saya dauke mu ya kai mu asibiti ni da mahaifana. Ya ce ayi duk abinda ya kamata ayi xai biya ko nawa ne. asibitin nasarawa aka kai ni a lokacin shine asibitin da yake tashe sai dan wane da wane. Likita na ganin yanayin jikina sai ya bamu gado muka kwanta aka dinga kara min ruwa da allurai. Allah cikin ikon Sa kafin sati guda na murmure, shi yasa aka ce kowace cuta da maganinta. Na samu sauki har na fara tashi xaune ina surutu kuma komai aka bani ina ci. Kusan kullum Alh Adnan da matarsa salaha suna xuwa su gaishe ni a asibitin bayan kayan dadi na marmari da abinci iri-iri da suke yini suna aiko direba yana kawo mana asibiti.”
Madina tace “gaskiya wadannan iyayen gidan naku suna da kiriki.”
Kaltum tayi murmushi tace “suna da matukar kirki shi da matarsa dukka. Bayan an sallamo mu mun dawo gida sai muka ci gaba da rayuwarmu a gidan, ina matukar jin dadin gidan saboda na samu walwala ba’a dukana, babu yunwa, ba babu hantara.
Makaranta mai tsadar gaske aka sani.
Madina tace “Allah kenan, haka yake ikonSa.”
Kaltum tayi murmushi tace “na tsinci kaina mai farin ciki matuka sai dai matsala daya data addabe ni itace bana samun kulawar iyayena. Ba kulawar rashin wanka da wanki ba ne, kuma ba matsalar abinci ba ne, basa hira da ni, haka basa saurarona, ko na matso kusa dasu saisu matsa saboda wancen ra’ayin da goggo fattu ta cusa musu.”
Madina tace “ban fahimci basa sauraronki ba, kamar yaya? ”
Kaltum t ace “kunyata su ke ji saboda ni ‘yar farice don haka na xama tamkar mujiya a tsakiyarsu sai kallo da ido. Ina matsowa kusa dasu saisu ture ni ko su tashi daga wajen, idan na taho musu da hira saisu gwale ni ba xasu saurareni ba. Idan xan yini ina kuka babu wanda xai lallashe ni a cikin su. Har ‘yan gidan suka fara fuskantar hakan, Alh Adnan ya dinga yiwa mahaifana nasiha yana nuna masa wannan kunyar da yake yiwa ‘yar fari ba’abun burgewa ba ne illa jahilci da cutar kai.
Akwai wata ranar asabar ba xan taba mantawa ba da sassafe misalin karfe takwas, a lokacin ana tsananin sanyi. Ni da mushkur muka fito bakin get wajen da babana yake xaune yana jin dumi da itace, yayin daya rufa da burgujejen bargo. Yana ganinmu ya tabbatar sulalowa mukayi muka fito ba tare da sanin iyayenmu mata ba, saboda ko rigar sanyi babu a jikinmu, ba hula, ba takalmi daga ni sai yar yaloluwar singileti da pant, haka mushkur daga shi sai karamar jallabiya ba dogon wando. Ana tsananin hunturu, mai tafe da haxo, da iska mai kura don haka hanci da ido sai xuba suke yi, yayin da duk ilahirin tsikar jikinmu ta tattashi.
Babana na ganinmu sai ya kira mushkur ya dauke shi akan cinyar sa ya rungume, ya lullube shi da bargo, yayin daya juyar dashi saitin garwashi suka yi ta jin dumi, suka juya min baya. Ina xaune akan benci a bayansu ina ta makerketa ban isa in kutsa cikin bargon ba saboda nasan hantara ta xai yi ya kore ni.
A cikin wannan hali Alh Adanan ya fito ya iske mu, sai ya ji ransa ya baci yayi ta yiwa mahaifina fada yana cewa shi fa ba burge shi yake yi ba in har xai bar ‘yar sa ta cikin sa a wulakance ya tallafi dan wani. In har iyayena basu shaku da ni ba to ina xansa raina, ya kwatanta wannan abunda suke yi da suna ADON DAWA wato gida bai wadata ba an wadata waje ma’ana ya wulakanta ‘yarsa ya tallafi bare.
Alh Adnan ya dauke ni ya rungume ni ya shiga da ni cikin falonsa ya dauki bargonsa ya lullube ni yayin daya kunna min room heater jin dumi ta lantarki. Yana lallashi na, ya bani biskit da alewa, har said a ya tabbatar hantsi yayi, sanyin safiya ya lafa sannan y ace in je gida ayi min wanka a saka min kayan sanyi. Haka shima mushkur yake samun wannan gata daga wajen mahaifana har goyon sa mama na keyi amma ni ban isa matsowa kusa da ita ba.
Dan haka na kasance ako da yaushe ina hanyar bangaren daddyn mushkur. Ina tashi daga barci wani lokacin ko karyawa bana yi sai in yi wuf nagudu wajensa, sai dai idan ban ci sa’a ba nayi karo da maman mushkur sai ta kora ni gida, idan kuwa tana kicin ko ban daki tuni na isa gare shi a falonsa ko akan gadonsa, yana gani na sai ya rungume ni ko daga ni sama cimak, ya wujijjiga ni in yi ta dariya.
Musamman saboda ni yake ajiye katan katan din alewa da biskit da kananan kwalayen lemuna. Ko da yaushe ka ganni ina ciye ciye, baya ga karatun boko dana arabiya da yake koya min. ya na sona saboda ina son karatu, kuma ina son in koya.
Ko da yaushe ina tambayarsa abun da ban gane ba haka duk abun daya koya min duk daren dadewa ya tambaye ni sai na fada masa bana mantawa, in da ya kara sona kenan.
Sabanin dansa wanda ya tsani karatu don haka ma basa shiri da uban. Gashi ina da tsananin wayo kamar ba ‘yar fari ba, ga ladabi da biyayya, na iya hira tatsuniya kala-kala da labarum nake bashi yayi ta dariya ya na tuntsurewa da dariya tamkar yana hira a cikin abokansa.
Amma fa bana labarin da kowa saishi kadai, idan baya nan sai ka rantse ni doluwa ce don bana Magana, sai kallo da ido a gidanmu saboda bana hira da iyayena. Don haka duk sanda daddy yayi tafiya kwana biyu sai kowa ya gane bana jin dadin rayuwata. Jikina sai yayi sanyi, in kaura bakin get ina duban hanya musamman idan na ji karar mota sai in xankada da gudu in leka, idan naga bashi ba ne sai raina ya baci ko kuma in fashe da kuka. Idan kuwa na ci sa’a shi din ne sai in yi ta tsalle da ihu don murna yayin da nake fara xaxxago masa labaru iri-iri dana tattara ina jira ya xo in fada masa.”
Kaltum tayi shiru tana matse hawaye, yayin da madina ta tsura mata ido tana yi mata kallon tausayi.
Madina ta nisa tace “ikon Allah idan da ranka babu abunda baxa ka jiba. yaya kuka kasance? ”
Kaltum ta gigixa kai tayi dan murmushi ta ci gaba da cewa “daddy shine tamkar uwata, ubana, kuma abokina. Shi kadai yake goge min hawaye a idona saboda a kasance koda yaushe ina cikin kuka a sanadiyar kyarar da mahaifana da kuma mamar mushkur ke yi min, tatsane ni saboda taga mijinta yana tarairayarta fiye da dansu na cikinsu.”
Madina ta girgixa kanta t ace “Allah sarki duniya, abun al’ajabi baya karewa ban tabajin irin wannan kauyenci ba. Daga kanki ba’a kara haihuwa ba a gidan ku? Mushkur ma ba’a hqifa masa kanne ba? ”
Kaltum tace “an haifawa mushkur kanne biyu amma dukkansu ba’a haifesu da rai ba, saura kiris mamarsa ta rasa ranta a garin haihuwarsu. Saboda duk a juye ake fitar mata dasu ta hanyar tiyata ma’ana kan jaririn ne suke komawa kirjinta, kafafuwan a kasa sai anyi tiyata ake fitar mata kuma a mace don haka nema aka juyar da mahaifarta baxata sake haihuwa ba. Ni kuwa mahaifiyata ta haifi namiji mai bina ya rasu bayan an yi suna, sai ta dade bata haihu ba sai daga baya ne haihuwar ta bude, kusan duk shekara sai ta haihu, a yanxu haka kannena bakwai na baro mata da maxa.”
Madina t ace “suma kannen naki suna jin kunyarsu basa kula su kamar yadda suke yi miki!” kaltum ta girgixa kai tace “iyayena suna son su, suna wasa dasu, suna hira dasu ba kamar yadda suke yi min ba har tsayawa nake ina kallonsu ina mamakin ashe mama da baba sun iya yiwa da wasa da lallashi.
Duk wani abu da ake bukata na makaranta sai na jira daddy ya xo sannan in fada masa, ya bani in kai makaranta idan kuwa baya gari ko baya kasar sai dai idan kashe ni xa’a yi a makaranta don duka amma babu wanda nake iya tara in fadawa sai daddy.
Ina shekara takwas nagama nursery har na shiga primary, ina primary 3 a lokacin ne karshen karatuna ya xo.”
“kamar yaya karshen karatunki ya xo? ”
madina ta tambaya cike da damuwa.
Kaltum t ace “eh, a lokacin ne goggo fattu ta aiko tana son ganin mahaifina, yana rawar jiki ya tafi kiranta a can garin mu xangon daura. Ta sanar masa abun da take bukata daga gare shi, gashi baya iya yi mata musu. Nan danan ya amsa mata ba tare da yayi kokonto ba saboda tsoro.”
Madina ta gyara xama t ace “me take bukata a gare shi!”
Kaltum ta cije baki tayi murmushin karfin hali t ace “ce masa tayi ya amince ta sayar da gadonsa da mahaifinsa ya bar masa sannan da tabkekiyar gonarsa dake garin sandamu, wacce mahaifiyarsa ta mutu ta bar masa, sannan da dinbin awakinsa xata biya kudin jirgi ni da ita mu tafi makka neman kudi. Idan muka je xa mu samo dukiya mai yawa , sai ta biya shi linkin ba linkin in kudin gonarsa.”
Madina tace “ya yarda a cire ki daga makaranta ku tafi maka? ”
kaltum t ace “a take ya yarda, haka mahaifiyata ma bata hana ba a sanda ya sanar mata. Ko da wasa babu wanda ya fada min shirye-shiryensu, ni dai nasan ankai ni gidan daukar hoto an yi min kananan hotuna, goggo fattu ta xo ta kwana biyu a gidan mu, sai kuma ranar da naga mahaifiyata ta xuba min kayana a dan buhu, goggo fattu tace in taho mu tafi.”
Madina tace “daddy ya sani bai hana a tafi da ke ba? ”
Kaltum ta girgixa kai tace ‘sai da suka ga daddy baya na sannan suka tarki tafiyar, koda wasu basu shawarce shi ba, matarsa ma bata sani ba.
Na tsinci kai na a cikin jirgi, sannan na tsinci kai na a cikin birnin makka.
Madina t ace ‘ki ce kin taba xuwa makka ba wannan ne xuwanki na farko ba? ”
Kaltum t ace”na dade a makka a can na koyi larabci, yanxu haka lungu-lungu da sako-sako na sani a cikin garin makka, haka da ace na samu xuwa xaki yi mamakin irin mutanen da xa ki ga sun sanni duk da na girma nasan xasu shaida ni saboda kammanina basu canxa ba.”
Madina tace”yaya xamanku da goggo fattu ya kasance a maka?
Amma dai bata wahalar dake ba tunda kin girma ba kamar sanda ta yeye ki ba, ga ku kuma a kasa mai tsarki, gashi komai a wadace ba’a wahalar abinci”
Kaltum tayi jugum can ta nisa t ace “uhum wahala ma daya kenan, ai ba xai yiwu in iya xayyana ta gaba daya ba saboda axabar tayi yawa.
Wahalar da na saha ina ‘yar jaririya ai karama ce saboda tsana bansan komai ba, a wannan lokacin kuwa nasan “eh” nasan a’a, na san ace in yi abu in yi, ace in bari in bari.
Da farko dai mun ci sa’a mun sami gidan haya a unguwar ‘yan kasa wato a unguwar masfala, a gidan wata balarabiya mai suna hajiya isra, hajja isra ruwa biyu ce mahaifiyarta baka, mahaifinta balaraben makka ne dan haka gadimiya ce. Hajja isra tana da ‘ya daya mai suna ahlan. Ahlan sa’ata ce, mahaifin ahlan ya rasu ya bar musu gida sama da kasa. Suna xaune a sama, mu kuma muna haya a kasa mu kadai ne.
Hajja isra tana da kirki matuka,tana sona sosai musamman yadda taga mun shaku da ‘yarta Ahlan, har ana cewa muna kama kasancewar Ahlan tayi kama da mahaifiyarta ba suyi kama da larabawa ba sak nima kuma gani fara sol mai gashi sai nake kama dasu. Ta kan yiwa goggo fattu wasa t ace “yadda fuskar nan taki take baka kirin idan askarawa (yan sanda) suka ganki da kaltum ki ka ce jikarki ce sai sun kama ki, suce karya ki ke ‘yar larabawa kika sato. Saboda baku yi kama ba kwata-kwata, gara ki dinga saka nikaf da safar hannu da ta kafa idan xaku fita tare.
In da xaki tabbatar hajja isra na sona sai ta siyawa ‘yarta ruguna ko sarka da ‘yankunne na gwal, biyu take saya iri daya ni da Ahlan musamman a lokacin sallah. Haka abinci, komai ta dafa sai ta aiko min sai dai kash aiken baya xuwa gare ni saboda goggo fattu karbewa take yi bata bani. Da takardar Ahlan ta ‘yan kasa hajja isra ta saka ni a makarantarsu Ahlan, muke xuwa tare duk da ba’a koyar da boko larabci xalla ake yi sai karatun qur’ani ta tahfix ce. Na koyi larabci, na koyi karatun qur’ani sosai, nasan baki, hadisai da daman na haddace su kuma xan iya fassarawa, haka fikihu, tafsir, sira da sauransu. Muna xuwa makaranta da sassafe misalign karfe takwas xuwa karfe goma sha daya muke tasowa. Muna tashi daga makaranta idan na shiga gida na ajiye jakar makaranta sai in karbi kudi a wajen goggo fattu in tafi sarar kaya sannan in je in sayar.”
Madina tace “ban fahimce ki ba. Ke kadai din ne xaki iya xuwa ki sari kaya da kanki? ”
Kaltum tace “ni nake xuwa in saro kaya, kar k ice tafiyar ba nisa, ko a mota tafiya ce mai nisa daga masfala xuwa shara Mansur masallacin mai cixo. Sai na niki tafiya kamar raina xai fita in saro kaya masu yawa sannan in doro kayan a kaina in nufi harami in da xan baxa a bakin hanya ina sayarwa. Idan na sayar sai in koma shara Mansur masallacin mai cixo in sake saro kaya in koma harami in sayar, har sai dare yayi bayan sallar isha’I sannan nake komawa gida sai na tabbatar kudin ya lunku sau biyu. Ma’ana idan riyad dari biyar ta bani sai ya xama riyad dubu biyu, ranar da ban yi ciniki ba ne xan kai mata ruyad dubu daya da ‘yan kai.”….
.
Gida fa ya fara shiru, mai yasa aka rage
ADON DAWA 8
.
Madina tace “amma tana farin ciki da cinikin da kika yi mata bata kyarar ki ko? ”
Kaltum ta tabe baki ta ce “ko a lokacin xahma ma’ana lokacin da baki suke nan an fi yin ciniki wato lokacin Umara da Hajji idan ta bani riyad dubu daya in yi sari, daga safe xuwa dare sai nayi mata riyad dubu biyar xuwa dubu shida amma bata godewa kuma se ta dake ni kullum.”
Madina tace “to cnikin nawa take so kiyi mata? ”
Kaltum t ace “duka na take yi kullum ba sai nayi laifi ba, ba kuma dan ban yi ciniki ba. Yadda na lura doka ce wacce ta wajaba a kaina kullum sai ta xane ni ko da laifi ko ba laifi. Daman ina dawowa take ce min in cire kayana a bakin kofar shigowa daga ni sai dan wando, sannan in karaso gaban ta in durkusa, in mika mata cinikin dana yi. Sai ta kirga ta soka a aljihunta sannan ta xaro wayar rediyo ta fara sharara min a duk ilahirin jikina, laifin da take cewa nayi shine ban dawo da wuri ba ko kuma sharar da nayi da wanke-wanken da nayi da asuba kafin in tafi makaranta bai fita ba. In yi ta kuka da ihu ina mata magiya tayi hakuri ba xan sake ba. Har sai hajja isra ta jiyo ta xo ta kwace ni sannan take kyaleni, amma tun sanda ta yiwa hajja isra targade a yatsa garin kwata ta hajja isra ta daina saukowa ta kwace ni ki san larabawa da tsoro. Sai dai ki ji tana cewa “fattu kiji tsoron Allah, ki kiyaye ranar da hakkin yarinyar nan xai tabaye ki.” Amma goggo fattu bata ji, gobe ma xatayi min wanda yafi na yau.”
Kaltum ta fashe da kuka, yayin da madina ma taji hawaye ba kakkautawa yana xubo mata suka dauki lokaci mai tsawo babu wanda yake Magana don takaici. Can kaltum ta ci gaba da Magana cikin kuka take cewa “bulalar roba irin ta jona rediyo nan sai ta farfashe a bayana, yayin da karfen cikin wayar ke shiga cikin naman jikina ya nutse, jinni yayi ta fita. Idan wayar ta fatattake ta kare sai ta bani kudi in je in siyo wata a kanti da kaina, in kawo mata. Idan itama ta kare sai ta sake aikena in siyo wata.”
Kaltum ta juyowa da madina bayanta, yayin data daga rigarta sai ga shatin bulala xabga-xabga reras a jere a bayanta da wuyanta.
Madina ta shashshafa bayan yayin data gyada kai tace “kwarai kuwa wannan tabon duka ne. Allah sai Ya kama matar nan da hakkin yarinyar karama wacce bata jiba bata gani ba. Ta rabo ki da iyayenki ta xo ta axabtar da ke.”
Kaltum t ace “idan bayana ya farfashe yana jinni sai ta kaini bandaki ta daure hannuna da wuyana da kafata a jikin famfo kamar yadda na gaya miki sani take in cire kayana daga ni sai dan wando, sai ta dauko farin omo ta gurxa min a baya na a wajen ciwon sai kaji ya dau xugi yana tafasa, yana kumfa sai ciwo ya kakkame, sai jinin ya tsaya.”
Madina tace “ta daure ki a bandaki fa kika ce, kamar wata dabba?
Ko dabbace xatayi mata haka? ”
Kaltum t ace “na sha kwana a bandaki ina rawar sanyi har gari ya waye sannan ta jibgo min abinci t ace sai na cinye. Shinkafa himilin guda da kaxa dankwaleliya tace sai na cinye tas, inyi ta turawa badon ina jin dadin abincin ba saboda bana cin abinci sosai na saba in yini ina talla baci basha don haka nama daina son cin abincin kwata kwata.
Idan nace mata ya isheni sai ta kwada min mari tace sai na cinye duka, in yi ta ci har wani lokacin in amayar da duk abunda na ci, sai ta sani in kwashe aman in gauraya da abincin tace in cinye abincin da aman dole nake cakudawa in ci gaba da ci.”
Madina ta tsartar da yawu gefe,
(NI KUMA DAN ANTY, HAR SE DA NA KOMA YIN AMAI , YANXU MA AKAN AMAN NAKE OOOOOOOOO…….)
Ta dau dogon salati. Ta ce “kaltum kin sha wuya, kai wannan abu da me yayi kama?
Ke kuwa me kika yiwa wannan tsohuwar take wahalar da ke haka da alama don bata taba haihuwa bane take miki haka, da ta san xafin haihuwa da ta rage wani abu duk muguntarta.”
(NI KUMA NA CE, “BA WANI DAMAN MUGUNTAR A JININTA YAKE, WASU BABU HAIHUWA KUMA SUNA DA TAUSAYAWA DAN UWA. ALLAH MA YA TSARE MU DA IRIN WANNAN RASHIN IMANI. AMEEN)
Kaltum ta matse hawayenta tace “duk unguwar sun san ina shan wahala duk da basu san wata axabar da nake sha a cikin gida ba, amma suna ganin irin wahalar da nake wajen daguwar tafiya in saro kaya sannan in je in sayar, in koma in sake sarowa duk da kafa, saboda tsabar daukar kaya a kaina sai da kaina yayi tolo gashin wajen ya kade ya gurguje saboda wahala.
Akwai wani yaro saurayi a makwabtanmu mai suna Anwar. Bakar fata ne amma haifaffan Saudi ne yana tausaya min matuka y ace duk sanda xan je sari in je in karbi kudin motar xuwa da na dawowa in daina tafiya da kafa. Haka kuwa aka yi duk sanda na fito daga gida xan je in kwankwasa kofar gidansu ya fito ya bani riyal biyu, riyal daya na xuwa daya na dawowa. Sai in je in shiga doguwar bus a kai ni har kofar kantin sari, in saro kaya himili guda in sake hawa mota in tafi harami in sayar. Abunka da yarinta idan na sayar xan sake komawa in saro wasu bana shiga mota sai in tafi a kafata tunda Anwar bai bqni wanda xan sake komawa ba tsoro kuma ya hana in dauka a kudinta, gani nake kamar xata gane.
Wata rana da axumi na fito daga gida karfe shida da rabi na safe, gari ma bai karasa wayewa ba saboda akwai baki a garin don haka ana cin xahma. Anwar ya bani kudin mota na tafi na hau doguwar mota mai beni hawa biyu, sama da kasa don haka sai na samu lungu na shige a can sama.kan ka ce kwabo barci ya dauke ni kasancewar axaune a bandaki na kwana, tsirara ga tsananin sanyi dan haka ban samu nayi barci ba har asuba sannan ta kwance ni ta turoni sari ko karyawa banyi ba, anyi mana hutu saboda axumi a lokacin.
Ina wannan barci har aka wuce dani inda xan sauka ban sani ba. Da barci yayi barci saina sulale na mike a karkashin kujera na kwanta sosai na lulluba da gyalena. Ban tashi farkawa ba said a wata mata ta tashe ni ta ce in tashi masu mota dasu kai motar wajen parkin, sun gama aikin ranar. Sannan nayi firgigit na biyo bayanta muka sakko tare da ita. Ina tafe ina laluba kudina a cikin jaka dana daure a tsantsata, hakika kudina yana nan riyad dubu daya.
Ina fitowa sai na ganni a wata unguwa da ake kira shara sittin, sai ban damu ba saboda tafiyar da xan yi xuwa sharu Mansur babu nisa sosai don haka na tabbatar barci kadan nayi don ba’a wuce dani da yawa ba. Na duba sararin samaniya hakika har yanxu rana bata futo ba yayin da na duba agogon dake daure a hannuna karfe bakwai daidai. Sai farin ciki ya kama ni tunda na san karfe shida da rabi na fito daga gida mintuna talatin kadai nayi a hanya. Na dinga tafiya ina sauri kamar xan ci daka sai dai wani abu daya daure min kai sai naga du kana rufe kantina kuma kowa na haramar tafiya masallaci ko’ina sai kiraye-kirayen sallah ake yi. Sai nake ganin jama’a da dama suna cin dabino, wasu na shan shayi a cikin kantina ko a cikin motocin su, gashi axumi ne kuma asuba ta wuce an gama sawur. Na tambayi xuciyata me yasa suke karya axumin su?
Tambayoyi kala-kala na dinga yiwa kaina har na isa kantin sari. Mutum daya na iske yana alwala a bakin kantin. Cikin harshen larabci ya amsa min y ace “ba’adis salat”ma’ana, sai an idar da sallah xasu bude kantin. Na dube shi duba na rashin fahimta n ace “ba kuyi sallar asuba da wuri ba ne? ”
ya yi dariya yace sallar magariba xa mu yi ba dai asuba ba. Ko dan bakya axumi shi yasa baki damu a sha ruwa da wuri ba ko?
Sai gabana ya yanke ya fadi, nan da nan na rikice. Na ga wata mata ta xo wucewa jikina yana karkarwa n ace mata “karfe nawa yanxu? ” ta duba agogon dake daure a hannunta t ace “karfe bakwai.” Na tambaye ta “bakwai na safe ko bakwai na dare? ” itama sai tayi dariya sannan t ace “bakwai na dare ne. ba ki ga ana shan ruwa ba? ”
Sai na sulale na tsuguna ina ta salati, ina kuka hakika yau na shiga uku ban san abunda xan je in gayawa goggo fattu ba, ga dare yayi gashi ban juya mata kudinta ba. Ta yaya xan iya mayar da riyad dubu daya ya xam riyad dubu biyar ko dubu shida, daga magaruba xuwa dayan dare? Sai da su kayi sallar isha’I aka yi asham sannan suka bude kantina nan da nan na shiga na saro safar kala kala, da doxin doxin din carbina. Na fito na shiga mota na nufi harami kuka kawai nake yi jikina yana rawa, duk Alhajin da na gani sai in bishi, bakake da farar fata hawaye na xuba ina cewa ku siya kaya na don Allah idan ban sayar ba duka na xa’ayi a gida. Da yawa saisu tausaya min su saya ko basu yi niyya ba, wasu kuma saisu bani kudi sadaka, wasu kuma su fisge rigarsu su wuce subar ni. Kan ka ce kwabo na siyar na ruga da gudu na je na kara saro waqsu, na sake dawowa harami na sayar.
Akwai wasu kawayena ‘yan indiya da muka saba dasu a wajen talla, suma dasu ka ga ina kuka sai suka tausaya min suka sarar min da kayansu dukka a yadda suka saro na dora riba na sayar. A lokacin dasha dayan dare yayi jama’a sun fara tafiya masaukinsu suna barin harami sai mu ma masu talla suka fara neman hanyar gida. Ina tafe ina kirga kudin cinikin da na yi, saura kadan ya cika riyal dubu uku, sai na dinga kuka ina addu’a yayin da hankalina ya kada yayi gida ina tunanin abunda xan tarar don cinikin yau ba yawa. A titi na tunkaro wata mota wacce ta karkato xa ta tsaya (parking) gwuiwata ce ta daki gaban mota. Kan kace kwabo kwabrina ya fahse jinni yakece, na fasa ihu na daka tsalle gefe na tsuguna.
Hankalin direban ya tashi ya fito da gudu a gigice saboda yasan hukuncin kade mutum a kasar, ko ba’a ji ciwo ba balle a ce har an ji ciwo har jinni yana xuba. Larabci yake yi min, tambaya yake yana cewa wai me yasa nake tafiya kaina a kasa, bana lura da motocin kan hanya duk da horn dinda yake yi amma ban jiba? gashi nan na ja ya buge ni xan janyo masa wahala. Sai yaga ina ta bashi hakuri burina in tafi in bar wajen ban damu da ciwon da na ji ba. ya kira ni na xo, sai ya dunkulo kudi masu yawa ya bani yace in tafi chemist in sayi magani.
Na karba kudin ina murna, na wuce ina godiya sai na hada da kudin cinikina ya xama riyad dubu biyar harda doriya. Nan fa na ji hankalina ya kwanta na tsaya a fanfo na wanke jinin sannan na shiga gida. Na isketa a kufule tana jirana da bulalarta a hannu, kallo daya tayi min na gane manufarta. Sai na fara cire abayata na xama tik daga ni sai wando. Ina karkarwa na xo na durkusa na mika mata ciniki, ta karba ta kirga. Sai ta Harare ni ta ce “ina kika je aka ganki a mota daxu da magariba bayan ni ban baki kudin mota ba? ”
Sai na ji xuciyata ta harba tabbas wani ko wata sun ganni har an fada mata. Sai na shiga dogon tunani ina neman hanyar da xan kare kaina. Ta daka min tsawa t ace “Halima kawata ta ganki kina saukowa daga mota ina ki ka je? ”
Sai wata fasaha ta fado min nace askarawa ne suka kamani, suka tafi dani da kyar suka sake ni suka sake ni. Ta fixgi kunnena ta murda da karfi t ace duk sanda na sake na bari askari ya kara kamani to Nigeria xa’a mayar dani, ina xuwa Nigeria kuma daga filin jirgi xa’a yanka ni saboda yankan kai ake yi a Nigeria. Sannan ta kunnawa risho wuta yayi ja sosai sannan t ace in dauki risho din yana ci da wuta in xo in wuce ta gabanta yayin da take shauda min bulala idan na bari risho din ya fadi ko yayi karkacewa to dukan ya xube. “sai kaltum ta fashe da kuka mai tsanani.
Madina ma kukan take, ta dafa kafadar kaltum tana lallashinta tana bata baki. Tsawon lokaci kaltum bata daina kuka ba, saida kyar ta ci gaba da Magana. Ta ci gaba da cewa “tun ina kukan idan tana dukana har na daina kuka, tun ina ihu har na daina ihu, wannan abu kuwa yana bata haushi matuka ta fi so ta dake ni in yi kuka da hawaye sannan ta ji dadi don haka take dukana kamar xata fitar min da rai ni kuwa bana iya kukan.
Da wahala ta yi wahala sai nake fita in da Askarawa suke kame don su kamani amma basa kamani, sai daga baya na gane ashe basa kama masu talla sai masu bara don haka ina ganinsu sai in wurgar da kayan tallar nayi wuf na fada cikin masu bara. Naci sa’a kuwa rannan aka kamani aka kaimu sijin wato kurkukun da ake ajiye wa’anda aka kama ma’ana wa’anda basu da takardar ixinin xama.”
Madina tace “yaya rayuwar kita kasance a sin?
Kuma yaya goggo fattu ta yi data ji an kama ki? ”
Kaltum t ace “ai babu wanda ya san an kamani sai dai idan ta ji shiru ban dawo ba ta shiga tunani, musamman idan ta ji labarin an yi kame a harami. Bata cika damuwa ba saboda tasan riga kafin da ta yi min, ta riga ta tsorata ni da xuwa Nigeria . tace idan na yarda aka kawo ni Nigeria yanka ni xa’a yi a filin girgi, ni kuwa na yarda na dauka da gaske take yankan ake yi din. Su kuma askarawa baxa su yarda su kai yaro kasarsu ba shi kadai sai an hada da iyayensa. Don haka saisu tambayemu muna da iyaye a nan Saudi ya? Sai mu ce a’a saboda idan muka ce eh, to xa’a aka mu gaba a kaimu wajen iyayen namu.
To a haka da suka gaji da tambayar iyayen mu muka ce babu suka fitar da mu suka kaimu harami, amman ranar jikina se da ya gaya min, domin irin abunda ta saba min na cin xali, shi ta min. sauran da muke siya da siyrwa da su ba’a dukansu ko basu sayar da kayan su duka ba, basa damuwa saisu mayar gida gobe su xo su sayar amma banda ni, yi nake kamar raina xe fita sai na siyar ninkin baninki du da haka kuma ban tsira ba. Kaltum ta rushe da kuka.
Madina ta girgixa kai yayin data kurawa kaltum ido tana duban ta xuciyarta cike da tausayi akan tausayin da take ke ji a da. Can kaltum ta dago da luhu luhun idanuwanta ta kalli madina idanuwansu yayi musu jajawur ta ci gaba da cewa “da wuya tayi wuya shekara ta xagayo na fara wayo ina tunanin mafita sai naga babu wata mafita wacce ta wuce in koma sijin in xauna shine kadai salamata. Saboda a sijin akwai bangaren yara xalla a inda ake bamu duk wani abun dadi da ko a gidanmu ba ma ci. Shinkafa da dakwaleliyar kaji ga taliya, macaroni, lemo iri iri, nono (laban), madara, xuma da gurasa, kankana, da sauransu.
Watarana na ji labarin ana kame a wata unguwa tuni na xubar da kayan talla na nufi wajen, na sami fili na xauna ina bara. Da nayi sa’a sai suka gano ni suka kuwa xo cafke ni suka yi, suka tafi da ni sijin. Na shafe wata biyu cif a sijin, ina walwalata tare da sauran yara har akayi karamar sallah muna can, suka bamu kayan sallah kala bibbiyu.”
Madina tace “atamfa ko leshi? ”
Kaltum ta yi dariya t ace “larabawa ai basa saka atamfa ko leshi, dogayen riguna ne da dankwalayen su sai riga da siket ko wandaduna jeans wanda xamu saka daga ciki sannan mu dora da abaya daga sama, muci, mu sha, mu yi wasa, babu duka, babu xagi, sai dai muna leka wata ‘yar huda muna ganin bangaren karuwai da aka kamo su ake duka.”
Madina t ace “kullum sai ayi ta xane su? ”
Kaltum t ace “a’a, duk sanda aka kama karuwa sai a sakata a wani daki wanda aka sakale bulala sako sako, bulalen an jona su da na’urar lantarki. Ana saka karuwa sai a fito a barta a ciki sannan a kunna na’urar, makunnar na waje. Kan ka ce kobo bulalen nan sun hau aikinsu na duka ciki da waje, duk tsallanta haka ko kwanciya tayi sai dukan ya sameta, abunka da na’ura mai kwakwalwa daga sanda bulala tamanin ta cika sai injin ya mutu da kansa ma’ana bulala tamanin hukuncin xina, ana kiran dakin XANXANA.”
(YA ALLAH KA TSARE MU DAGA AIKATA TA, DA MU DA EN UWAN MU MUSULMAI BAKI DAYA AMEEN.)
Madina ta yi tagumi t ace “ikon Allah, kaji kasar da ake shari’a ake hukunta masu xina ba kamar kasarmu ba Nigeria wanda a wani bangaren ma xina ta xama fassion. Yaya ake yi da karuwa, idan an gama dukan ta? Nasan mafi yawancin su ‘yan Nigeria ne ko? ”
Kaltum ta girgixa kai t ace “cikin ikon Allah kuwa ban taba ganin an kamo bakake ba, sai irin kananan mutanen nan wato ‘yan Asia kamar Indonesian, malesian ko indiyawa. Idan an gama dukan daya sai a fito da ita a shiga da wata kuma, suyi ta kuka suna ta ihu daga nan suma sai akwashe su kowacce a kai ta kasarta bayan an bata mata passport dinta.”
Madina t ace “to yaya aka yi dake a sijin, tun daba xaki taba yarda ki nuna gidanku ba? ”
Kaltum t ace “tsoro kala kala ya hana in nuna, na daya ina storon in kaisu wajen goggo fattu a kamo ta nasan na lahira sai ya fini jin dadi, haka ina tsoron dira a filin jirgin Nigeria t ace xa’a yanka ni don haka na ki fada ina da iyaye. Suka gaji da ajiyarmu suka kai mu bakin harami suka ajiye mu, saura yara suna ta murna sun xo gida ni ina bakin ciki an raba ni da sijin, in da ba’a dukana, ba’a daure ni, bana talla.
Hakika ta gana min axaba irir iri, bata xuba min kalanxir ta kona niba, amma ta kyarta min ashana ta daddana min hannayena da kafafuwa na bayan duka. Ta shaida min cewar ai ta ji labarin har wajen kame nake xuwa da kaina don tsan ba’a kama masu talla sai masu bara.
Haka ake tayi kullum sai wahala da axabtarwa har na cika shekara sha biyu a duniya wato shekarrunmu hudu da rabi a makka. Na gaji da duka sai na sake xuwa wajen masu kame suka kama ni karo na uku kenan. Wannan karon kuwa na hadu da wasu yara sa’annina wanda suma irin matsalata ke gare su. Muka yanke shawara mu nuna iyayenmu a kamo su akai mu kasarmu ko xamu huta da wahalar duka. Na sanar musu cewar kakata goggo fattu tace yanka mutane ake a filin jirgin Nigeria, suka ce karya ne tsorata ni kawai goggo fattu keyi. Don haka ana tambayarmu muna da iyaye mu uku muka ce “eh muna da iyaye.” Sauran da suka ce basu da iyaye aka dawo dasu bakin harami aka xube su. Mu kuwa da muka ce muna da iyaye kowacce aka hada ta da Askarawa bibbiyu da mota don ta nuna gidansu. Tiryan tiryan na kaisu gidanmu, ashe labari ya kai kunnen goggo fattu tun kafin mu karaso kofar gidan cewar an ganni da Askari. Tabbas waya aka doka mata, don haka ta shige cikin tankin ruwa anan suka xaliko ta aka kwaso mu da kayanmu kwacokam. Hajja isra da ‘yarta Ahlan na kuka muma muna kukan rabuwa dasu, aka tafi damu sijin ammam ba na da bane, wannan sijin din na masu tafiya ne don haka yara da manya a hade suke.
Tun a sijin goggo fattu ta fara dukana, xagi ba adadi ko abinci na karbo sai ta kwace tace ba xan ci ba. Kwananmu uku ban ci abincin kirki ba, lauma daya ko biyu sai ta faki idon ma’aikatan ta fusge abincin ko ta ci ko ta xubar. A rana ta hudu aka kwashe mu, aka kai mu jidda airport daga nan sai aka saka mu a jirgin da xai kawo mu Nigeria yayin da farin ciki ya lullube min xuciyata su goggo fattu kuwa suka dau kuka da kururuwa kai ka ce lahira xa’a kaisu da ransu. Bana farin ciki don xan je in ga iyayena ko kadan ban tuno su, farin cikina daya ne xanga daddy, xanga mashkur dansa abokin wasa na to daga nan sai kannena guda biyu a lokacin na baro Amani da Yasmin, saida na dawo naga mamana ta sake haihuwar ‘ya’ya biyu Mohammad da Ishak.”
Madina ta tambaya “ya kuka kasance da goggo fattu a Nigeria? ”
Kaltum ta sharce hawaye tayi murmushin karfin hali tace “goggo fattu ta shaidawa iyayena abunda na jawo mata, cewa da gangan nake xuwa wajen masu kame har suka kama ni, na nuna ta. Duk da irin himilin kudin dana nemo mata har tsawon shekara hudu da rabi amma sai ta boyeta ce bamu samo komai ba don haka kudin gonakin babana da dabbobinsa da ta siyar sun mula ba xata biya ba. Ta ce wai bana tsinana mata komai a can sai kwanciya, yara kanan suna neman kudi wadanda ma basu kai ni girma ba.
Babana yayi shiru yasan halinta amma sai ya biye mata yayi ta xagina kuma ya bata hakuri, sai dai duk wanda ya kalli jikina yasan shatin duka ne a ko ina. Wuyana, dantsen hannayena, tsintsiyar hannayena duk sun dashe, sun yi jawur saboda dauri abunka da fara don a lokacin na fi haka fari sosai.
Haka daddy yana ganina ya tambaya yace “kaltum meye ya faru da wuyanki da ma duk jikin ki?
amman wannan shacin duka ne. wa yaketa dukanki haka? ”
wannan amsa ta gagare ni, balle iyayena sai ita goggo fattu take bayani tace “ai bata jin Magana a garin tsalle tsallenta take karkarcewa.” Ai idan mafadin Magana wawa ne, majiyanta ba wawa ba ne. sai dai su kyaleta a haka amma basu yarda da bayananta ba kowa yasan shatin duka ne. duk ilahirin kayan da kika sani wadanda hajja isra take saya min da gwalagwale sarka da ‘yan kunne da xobuna du ta kwashe babu wanda ta bani. Hatta da wando (fant) idan na saka sai ta kira ni daki tasa na cire ta ce wai ba nawa ba ne nata ne. kaya kadan ta bar min ta hada da himilin dilolinta tasa a mota aka kaita xangon daura, bayan ta shafe wata guda cur a gidanmu. Banda ‘yan tsummakaron data hada iyayena da kannena wato gumama babu abunda ta basu shine tsarabar su.”
Madina t ace “amma wannan matar makira ce bata tsoron Allah. Yanxu ina xata kai hakkin dukiyar mahaifin ki data danne ta gado? Yaya rayuwarki ta kasance kuma a kano tare da iyayen ki? ”
Kaltum t ace “kamar yadda muka saba sai kunyar da iyaye na suke ji ta karu, rashin kulawar ta dadu, dakina daban na kannena daban.
Aikina kuma wanke wanke da shara da yiwa kanne na wanka, aikina yi na ke, ba se an saka niba saboda na saba da aiki har bana son xama. Mama kuma ita ke dafa abinci safe rana da dare.”
Madina t ace “ba a cikin gidan su mashkur take dafa abinci ba har kuma ku samu, ko an raba girki saboda kun yi yawa yanxu? ”
Kaltum t ace “ai a lokacin su mashkur sun tashi daga kano sun koma Abuja daddy yayi arxiki ya ninka na da, sun wuce xama a irin wannan gidan yanxu. Gidansu na Abuja tamkar aljannar duniya, ga motoci kala kala.”
Madina t ace sai suka bar muku babban gidan kuka bar boys quarters? ”
(Wash , hannuna, se na ji kawar da su karye sabida typing gaskiya na gaji, masu so ga littapi nan suma suyi.)
.
ADON DAWA 9
.
TRUE LIFE STORY
.
Kaltum t ace “idan ta daddy ne ba damuwa xai iya barmu mu shiga mu xauna amma matarsa anty salaha bata da kirki baxa ta yarda ba. Sai wata ‘yar uwarta tsohuwa mai suna Iya Altine itace take xaune a cikin gidan, tana sharewa tana goge goge don kada a bar gidan ya lalace saboda suna dadewa basu xo hutu ba. Daddy dai yafi xuwa akai akai ba kamar mashkur da mamansa ba, sai sallah ko bikin ‘yan uwa da yake su dukkansu ‘yan kano ne. mu dai muna xaune a boys quarters sai ma rashin dadi daya karu, saboda a yanxu basa gidan bare mamana ta dafa musu abinci su ci har mu ma mu samu mu ci, mu ke cefanen mu, mu auno abinci, sannan mu dafa don haka daga masara sai gero, shinkafa jifa jifa muke iya saye. Ga uwa uba duk gonakin da ake nomawa mahaifina kakaf goggo fattu ta sayar, bama samun ko kwayar masara daya daga gona sai dai mu auna daga albashinsa, sai ‘yar kyautar da daddy yake yi masa akai akai idan yaxo. Tunda ta abunda xa’a ci ake, babu wanda yayi tunanin a saka ni a makaranta. Da kanwar mahaifiyata ta xo wato goggo joda daga garinsu Cameron sai na bi ta muka tafi can na xauna. Hakika na ji dadin xama a kasar kuma na sake, ina walwala acikin dangin mahaifiyata suna sona sosai. Duk da kauye ne, talakawa, Fulani ne amma komai ya wadata. Ga abinci iri iri, ga ruwan fanfo, ga wutar lantarki.
Duk wasu labaru da tarihin rayuwata, da ta iyaye na, da yadda suka hadu aka yi auran, da yadda xamana ya kasance a hannun goggo fattu ina yarinya duk goggo joda ta fada min, badan ita ba da ba xan san komai ba saboda da mahaifana basa hira da ni. Amma mahaifiyata tana hira da kanwarta tana fada mata komai. Naja baki na gum na rufe ban fada musu irin axabar da goggo fattu ta gana min a saudiya ba. Sai dai duk sanda na cire rigata xanyi wanka kowa ya kalli bayana sai ya tambaya ni “wannan shatin meye.” Kuma har rana irin ta yau ina kwaikwalo robar wayar da ta shige min jikin nama na.
Wata na uku cur a Cameron sai kwatsam naga babana da direban daddy a mota sun xo daukana wai daddy ne ya turo su, su xo su tafi da ni kano an samarmin makarantar sakandire, rabi boko rabi Arabic ce. Bada sona ba na baro Cameron na dawo kano don bana jin dadin gidan mu musamman dasu daddy suka kaura Abuja ga tsananin rashin abinci.
Na iske daddy a kano, ya kira ni, sannan ya kira babana, mama ta muka xauna a gabansa a kasa kan kafet.
Ya fara bayani yace “nayi matukar bakin ciki dana dawo daga tafiya aka ce an cire kaltum daga makaranta an tafi da ita saudiya neman kudi. Naji tamkar in fasa ihu saboda takaicin yadda kuka tauyewa yarinyar nan hakki, ku ka tauye mata rayuwa gashi dai yanxu ta dawo ba dammar a mayar da ita aji uku na primary saboda ta girma, in da Allah Ya rufa asiri ta shiga makaranta a can, tasan qur’ani, tasan baki xataa iya karanta larabci aduk inda ta gani haka duk abunda aka fada mata da larabci xata ji shine naga ya dace asamar mata sakandire wacce ta hada Arabic da boko sai kwakwalwarta ta tafi daidai saboda har yanxu ta iya karatu da rubutun boko don haka ta je ta gurgura ta tsinci abunda xata tsinta.”
Daga karshe ya roke su Allah da Annabi su barni inyi karatu kada su sake cire ni su ce xa’a kaini Makka ko xancen aure. Ni kuma yayi min fada da na mayar da hankali nayi karatu musamman a bangaren boko shine wanda ban iya ba sosai. Muka yi masa alkawarin xamu bi duk abunda ya fada mana.
Makarantu uku na shiga, makarantar boko da safe, ta Islamiyya da yamma sai kuma ta dare karatun hadisi ake da tauhidi. Nayi bakin jini a waje ‘yan makaranta saboda na fisu kokari, nice karama a ajin manya cikin xabga xabgan ‘yan mata, suma na fi su kokarin domin kullum ni nake karatu da larabci malami yana fassara musu. Duk in da aka bude daga cikin kowanne littafi sai kiga na iya saboda an dade da koya min a Makka. Hakan ya jawo min farin jinni a wajen malamai kacokan suna so na, wasu ma daga cikinsu so irin na soyayya suke nuna min. yayin da hakan ya jawo min tsananin bakin jinni a wajen dalibai kacokam sun tsane ni, ba ni da ta kamammiyar kawa guda daya saboda ana tsoran kada bakin jinina ya shafe su.
Kullum idan aka tashi daga makarantun nan da nake xuwa guda uku, sai dalibai sun tare ni sun ja min kunne akan kada in sake dagewa wajen yin karatu tiryen tiryen bayan su basu iya ba, malamai su dinga yi musu kallon dakikai. Wasu kuwa saisu tare ni su dake ni akan samarinsu da suke ji kishin-kishin yanxu ni suke so alhali ni ban san hawa ba ban san sauka ba. Ba na saurayi, ban taba yi ba saboda da wadannan dalilai duk sanda garin Allah yawaye sai na ji gabana yana faduwa ina fargabar tafiya makaranta saboda a makarantar boko ma nice monita a ajinmu saboda kokarina suma sai suyi ta xagina idan na rubuta sunan ‘yan surutu, a islamiyyar yamma har abun yafi haka ta dare ma haka. Abu ya hadu ya yi min yawa na rasa yadda xanyi da rayuwata gashi babu wanda xan iya tara in fadawa har iyayena tunda ba hira muke yi dasu ba.
Wata rana daddy ya gani da idonsa an tashi daga makarantar islamiyya da yake makarantar bata da nisa daga gidanmu da kafa nake xuwa. Shi kuma ya xo gari, ya xo wucewa xai tafi gida sai ya hango manyan ‘yan mata su hudu sun tarar min suna ta dukana suna yi min kwallo da jaka da dan kwali. Ya tsaya da mota yayin da ya fito a gigice ya xo ya raba yana daga ido sai yaga ashe nice. Ya fatattake su, yahau lallashina yayin daya dauko tissue ya bani na goge hawayena, ya karkade min hijabi na da dan kwali na ya bani na sa ke haka jaka ta da kan sa ya dauko ya saka min a mota yace in shiga gidan gaba in xauna. Bayan ya bani baki kuka ya tsaya sai ya shiga yi min tambayoyi a kan abunda ya hada ni da manyan ‘yan mata har guda hudu fada. Ya ce a iya sanin da ya min bani da jan fada amma yaya akayi na tsokane su.?
Da farko na boye masa nace ba komai saida naga ransa ya fara baci, ya fara Magana cikin tsawa da fushi sannan na xayyano masa duk abun da yake wakana a duk makarantun da nake xuwa cewar haka ake tare ni kullum ana dukana da xagi saboda na fi su kokari. Ya tausaya min matuka amma ransa yabaci saboda ban fada masa tuntuni ba ya dau mataki. Yasan ba xan fadawa iyayena ba don bana hira dasu meyasa shi ban fada masa ba da wuri ba tunda ya xo garin a ‘yan kwanakn?
Nayi shiru ban bashi amsa ba.
Sannan yayi min wata tambaya cikin wata tattausar murya y ace “kaltum ada bakya boye min damuwarki, ada bakya shakkar ki tare ni ki fada min abunda yake damunki ko abunda ki ke so amma a yanxu bakya yi. Kina so in yi fushi dake? ”
Na girgixa kai yayin dana sunkuyar da kaina nace “a’a”. y ace “to daga yau ki tare ni ki fada min duk wata damuwarki, xan yi miki maganinta in shaa Allahu. Gobe da safe xan je makarantarku ta boko in sanarwa malamanku da shugabannin makarantar duk abun da dalibansu ke yi, haka da yamma xan je islamiyya, ta dare ma xan je xan fada cikin babbar murya duk dalibar da ta sake dukanki sai nayi shari’a da iyayenta. A haka muka isa gida, bai bar niba saida y ace in rubuto masa duk abunda nake da bukata na makaranta da na gida na ci da na sakawa a jiki, sutura da man shafawa da sabulai. Haka kuwa aka yi na je gida na rubuto masa ba tare da na nemi shawarar kowa ba, na shiga har falonsa washe gari da sassafe na durkusa na gaishe shi sannan na bashi na wuce xuwa makarnta.
Kafin a fito breakfast sai ga daddy da shugaban makaranta (principal) a ajinmu. Principal ya tashe ni tsaye yace un nuna masu dukana, daya bayan daya na dinga xakulo su, sannan ya sa su wankin bandaki da sharar sati guda. Haka da yamma daddy ya xo ajinmu shi da shugaban makaranta, irin na safe aka yi musu, suma na nuna su . amakarantar dare ma haka aka yi, shike nan daga nan na sami salama da kwanciyar hankali, ganin daddy da aka yi yayi shiga ta alfarma, ga lumtsetsiyar mota shi ya kara min daraja a wajen malamai da dalibai suka dinga gulma suna cewa ashe ni ‘yar gidan masu kudi ce har ake cewa babana mai gadi ne. duk xancen ya dawo kunnena sai nayi dariya kawai. A gaskiya kuma na fi kama da daddy fiye da mahaifina saboda daddy fari ne dogo mai hanci sam dansa mashkur bai yi kamada shi ba, ya fi kama da anty salaha mamarsa, baka ce gajera amma dai fuskarta mai kyau ce tana da dogon hanci siriri.”
Madina ta nisa tace “cafdijam ana irin wannan kara da xumunci ashe? Amma daddy nan yana da kiriki, a xamanin nan waye xai tsaya ya damu da rayuwar ‘yar mai gadinsa? Irinsu basu da yawa a xamanin nan.”
Kaltum t ace, “sai lokacinda wani dan unguwar mu mai suna Hussain ya takura yana sona, ya hana ni sakat a unguwarmu. Gidansu ajikin katangar gidan mu yake. Har gidansu ya fi gidan mu girma da kyau . Ya ce shi fa a duniya babu macen da ta yi masa sai ni, ni kuma bana son sa dan ban isa xance ba dan haka duk sanda ya xo sai in gudu gida in ki fitowa. Haka idan xanje makaranta sai ya dauko lumtsetsiyar mota wacce babansa ne kadai yake hawa a gidan yace sai na shigo ya kai ni makaranta ni kuma in ki shiga. Ya yi ta bina a mota har bakin get din makarantar. Idan an tshi ma shi xan gani dam ma ma haka.
Da daddy ya xo gari na fada masa, ya dauki mataki kuwa ya jawa yaron kunne kuma ya shaidawa mahaifinsa aka yi masa fada cewar ya kyale ni in yi karatu, sannan na sami sa’ida ya rabu da ni. Duk wannan abunda ake yi iyaye na basu sani ba, ko da sun sani ma basu nuna min ba, nima kuma daman ba fada musu xan yi ba.
Ina aji hudu na sakandire wato S.S 1, domin an yi min tsallaken aji guda daga aji daya aka kai ni aji uku saboda kokarina a dukka bangarori biyu boko da na addini. Shekaruna goma sha biyar a duniya, tsautsayi ya rufto min har na tsinci kaina a cikin wannan hali.” Sai ta rushe da kuka.
Madina ta daga kan kaltum ta goge mata hawaye ta tambaya cike da mamaki “ban fahimce ki ba? ”
Kaltum ta goge hawaye da gefen siket inta, t ace, “wata rana da maraice muna xaune ni da iyayena a tsakar gida. Ina wanke wanke a gefe, babana da kannena suna xaune a kan tabarma suna cin gyada, mamana tana xaune a bakin murhu tana tuka tuwo, yayin da iya Altine tsohuwar da nace miki a baya ‘yar uwar mummy salaha ce wacce take xaune a gidan tana kular musu dashi.”
Madina t ace, “eh na gane ta, me ya faru? ”
Kaltum ta nisa t ace “itace ummul aba’isin da ta hada min tuggun daya kawo ni nan.”
Madina ta gyara xama ta yi tagumi tace “ina sauraronki kaltum.”
Kaltum ta yi shiru yayin da hawaye ya fara diga da alamar maganar da take shirin fitowa daga bakin xaxxafa ce, tana yi mata kuna a rai.
Ta ce “iya Altine ta dube ni ta yi murmushin munafurci t ace “oh kaltuma gidanku shiru-shiru da ke tun daxu ana ta hira da kannenki ko uffan baki ce ba kamar bakuwa. Wannan da rikon ki ake yi a gidan nan ba iyayen ki ba ne ai sai ace wahalar dake ake yi, kowa yana cin gyadar nan amma ke kin ce bakya ci yanxu idan wani ya shigo ai sai yace hana ki aka yi. Idan ana so a ji hirarki sai idan daddy ya xo, sai in jiyo muryarki ras tana bashi labari shi kuma yana ta dariya.!
Mamana ta yi murmushi t ace “haka suke yi tun tana yarinya daga ya ji kukanta xai shigo har nan gidan ya dauke ta. Ya ce min “Safi, me kika yiwa gimbiya ta? ”
Babana y ace “ai abu da dama sai dai in ji a bakin direba, ko in gani tace daddy ne ya saya mata na makaranta ko sayayyar amfanin gida. Sai addu’a tsakanina da mutumin nan yana da matukar kirki.”
Sai ni kuma na yi Magana saboda babu yadda xa’ayi xancen daddy ban ji xuciyata ta yi fari ba. Na ce daddy abokin hirata ne, daddy ne mai share min hawaye idan ina kuka, shine mai sona a duniya wanda baya sona in shiga damuwa.”
Sai altine ta tabe baki tace “ko er gida xa’a yi a ci amanar mommy salaha? ”
Wannan Magana ta iya altine tasa gaba daya mun girgixa, muka dago kai muka kale ta. Babana y ace “haba iya altine me yasa kike irin wannan maganar?
Ai hanyar jirgi daban ta mota daban, yadda uba ba xai iya auren yarsa ba haka daddy yake da wannan yarinya.” Haushi ya sa baba ya tashi ya saka takalmin sa ya tafi bakin get. Mamana ta girgixa kai tace “ai ko da wasa ma bai kamata a furta wannan maganar ba.” Iya altine sai ta wayance ta share maganar data ga dukkanmu ranmu yabaci. Bayan ta yi sallar magaruba ta cika tunbinta da tuwo sai ta yi mana sallama ta shiga bangarenta ni da kannena muka ta fi makarantar dare.
Washe gari da safe lahadi ce ina gida ban je makarantar boko ba sai ga mummy salaha ta diro a kofar dakina, ta biyo jirgin safe daga Abuja xuwa kano.
Sai muka ji tana fada da xage-xage wai ni da iyayena munafukai ne daga yau xamanmu yakare a gidanta. A gigice muka firfito ba tare da mun fahimci abunda take fadi ba. Duk da haka ni da iyayena da kanena muka durkusa a gabanta muna bata hakuri. Ta kwalawa iya altine kira ta xo, t ace ta fada mana laifin da muka yi mata don mun raina mata hankali muna nunawa ba mu san abunda muka yi ba. Iya altine ba kunya, ba tsoron Allah ta maimaita sharrin da ta shirya mana a waya. Ta ce da bakinta da nata na fada a gaban iyaye na nace daddy yace yana sona nima ina son sa kuma yana saya min duk abunda nake so, wai har iyayena suma sun amince ayi aure. Mu dukka muka dau salati muka hau rantse rantse ba ‘ayi haka ba. Mummy salaha t ace ko ba haka ba ne ita daman xuciyarta bata kwanta mata da ci gaba da xamana a gidanta ba saboda na xama budurwa, kyau ya taso, tana fargaba ko ni ban ce ina son sa ba, shi xai iya cewa yana sona. Ga tsananin shakuwar da ya yi da ni tun ina yarinya, don haka mu kwashe kayanmu mu fice mata daga gida ta bamu kwana uku kafin daddy ya dawo daga London, kada ya dawo ya hana mu tafiya. Ta shiga gidanta ta xauna tace ba xata koma Abuja ba har sai ta tabbatar mun bar gidan.
Hankalinmu ya tashi muka rasa in da xamu saka ranmu. Ta ina xamu fara, kuma ina xamu nuna?
Gidan kasarmu na xangon daura ya rushe babu ko daki daya a ciki. Tun dawowar goggo fattu daga Makka ta yi aure a daura, mijinta ya kwashe dukiyar ya sake ta yanxu haka a daura take xaune a gidan ‘yar uwarta babu cin yau ballena gobe kasancewar gidan ba kowa duk ya rurrushe.
Babana ya dora hannu a ka yana rusa kuka, mamana har ta fishi tawakkali ita take bashi baki ita ke cewa mu je mu sayi kara ayi bukka mu xauna gidan haka. Bayan an yi haka da kwana biyu, saura kwana daya wa’adin kwanakin data bamu ya cika mahaifana suka yi shawararsu, bansan me suke nufi ba suka ce in hado kayana kocokan in shirya in fito. Jikina na rawa na hada kayana a jaka. Babana ya saka ni a gaba muka fito daga gidan, bansan inda xamu je ba. Muka tsayar da acaba biyu muka hau har kofar ruwa tashar kuka sai naga mun hau motar daura. Ni dai ina ta lissafi a hanya ina tunanin wajen wa xa’a kai ni?
Sai gamu a gaban goggo fattu itama da alama tayi mamakin ganinmu. Koda suka kebe da babana, ya fada mata cewar ya kawo ni, ni da ita xa mu koma Makka sai ta fara washe baki tana farin ciki amma fa da yasa hannunsa a aljihunsa bai fito da kudin kirki ba sai dai ya bata ixini ta sayar da gidansa na xangon daura mu yi kudin jirgi. Da aka yi lissafi kudin gidan ba xai isa kudin jirgin ko mutum daya ba, sai tace masa ya kwantar da hankalinsa xamu tafi ta mota mu shiga sudan sannan mu haura Makka ta ruwa kudin xai isa. To a haka mahaifina ya tafi ya bar ni ko sallama bai yi min ba, yana kallon hawaye da yake xuba daga idanuwana saboda na tuno axabar da na sha a wajenta a wancen karon.
Na shafe wata guda a daura sannan gida ya sayu muka biya kudin tafiya da sauran shirye-shiryenm
u muka taho. To shine wannan ganin namu da kika yi a cikin mota. Da idonki kinga yadda take kyarata, take duka a cikin jama’a, kin ga horon yunwar da take yi min , kin ga horar da take min, duk da haka se da ta hada da jakar kayana kacokam ta tafi dasu da gangan ta bar ni da kayan jikina kadai. Domin kawarta iya mairo ta fada min cewar tun a can daura agent ya sanar mata cewar tunda bata cika kudin bisa ba idan aka samu matsala ban wuce ba babu ruwansa tace eh ta yarda.” Sai kaltum ta rushe da kuka.
Madina ta surnano da hawaye ta girgixa kai t ace “kaltum ki bar kuka ki sa axuciyar ki duk abubuwan nan da suke faruwa mukaddari ne daga Allah , haka madina tayi ta bata Magana a karshe ta ce “xamu haye mu shiga makka idan shiga makkan kike so da ixinin Ubangiji.”
Kaltum ta girgixa kai yayin data dago da jajyen idanuwanta ta dubi madina ta fada cikin takaici t ace “bana so in shiga makka don a kowanne lokaci xan iya haduwa da goggo fattu ni kuma bana so in kara sakata a ido na har abada
. bana so in sake komawa Nigeria.
Alhaji adnan ne kadai nake tunawa nayi kuka, naji ciwon rabuwa dashi saboda na san shi kadai ne xai yi kunar xuci idan ya xo ya tara bana nan.na fada xan maimaita ko a gaban matarsa shine kadai yake sona nima nake sonsa a rayuwata. Ba xan banbance wane irin so na ke yi masa ba, shi ne kadai a duniya wanda yake mayar min da hawayena da yake shirin digowa kasa dariya. A ko ina ina ji dashi sosai a gida ko a makarnta tsakanina da jama’a sai kyara amma shi yana lallashina, Allah Ya dasa min sonsa a raina tun ina karama da son da ya kamata nayiwa uwata da ubana shi nake yiwa haka ban taba tunanin wani ba a cikin dinbun samarina da sunan wanda xan aura, sannan ban taba tunanin xan auri daddy ba sai dai ban san me yasa na damu dashi ba, idan ban gan shi ba bana jin dadi. Ina girma ina sake ganewa cewar shine mutum kwara daya me yi min wahala.
Kyarar dasu rukayya suke min da kakarta da saura ma, du na saba domin haka kakata goggo fattu ta ke min. a makaranta, kyara, da muka je hutu Abuja wajen mommy salaha hutu ma be kare ba ta koro ni.. se ta fashe da kuka..