BABBAN GORO BOOK 2 CHAPTER 1 by sumayyah Abdulkadir

BABBAN GORO BOOK 2 CHAPTER 1 by sumayyah Abdulkadir 


BABBAN GORO…..

sibitin da ‘file’ din gidansu yake can suka nufa, basu sha wahalar ganin likita ba, likitan Bayerabe ne. 

Ya duba ta sosai, sannan ya yi mata B.P ya girgiza kai ya dubi Imam wanda ke rike da hannun daman ta duk da halin da take ciki bata fasa zabga mishi harara ba, harara mai zafin gaske, a lokaci guda kuma tana kokawar kwace hannun nata daga cikin nasa, amma bai damu ba, ko kuma bai ma kula ba da abinda take yi din ba, domin lafiyar ta ce ta dame shi a wannan lokacin. 

Dr. Mathew ya dubi Imam ya yi mur

mushi ya ce, “Tunda bata so ka sakar mata hannun, baka ganin yadda kake shan harara ne?” 

Kansa ya rausayar. Ya ce, 

“Kyale ta Doctor, ni ai har na saba, da harara tana tabo na tabbatar da yanzu babu masaka-tsinke a jikina”’. 

Dariya Dr. Mathew ya yi, ya ce, “Mrs. Safah mene ne damuwar ki? Me kike so baki samu ba? Ga irin wannan caring-husband tareda ke?? Mene ne matsalar ki a rayuwa da kika bari har zuzzurfan tunani da damuwa ya janyo miki high blood pressure da kuruciyarki?” 

Shima likitan hararar aka zabga masa, tana so ta ce, “Wannan ba abin da ya shafe ka bane”. Amma ba ta so ma su ji sautin ta. Da ya ishe ta da nacin tambaya sai ta kwantar da kai bisa tebirin shi ta saka musu kuka. 

Imam ya tsugunna a gabanta idanunshi sun yi jajir don yadda _ sautin kukanta ke ratsa zuciyarsa yana dagula masa kwakwalwa, ya dago kanta 

daga tebirin ya rungume ta, abinda bai taba faruwa tsakaninsu ba, wani irin shock jikkunansu suka karba a lokaci daya, jikinshi yana rawa muryarshi tana karkarwa_ yake _lallashinta. Abinda bai sani bane ko kuma ya sanin yasa kafa ya take sanin da gangan, duk da baya so ya yarda cewa hakan dinne, zuciyarshi da gangar jikinshi aiki suke according to (abisa ga) maganganun Shahidah. Abinda shi kansa bai taba tsammanin ya iya bane wato (lallashin mace). 

Muryarshi ta yi rauni ya ce, “Safah nine dai baki so ko? Wannan ne damuwarki? To ki kwantar da hankalin ki zan yi miki duk abin da kike so ko da zai hada da rabuwa ne, in dai hakan shine samun lafiyarki, farin cikin ki da kwanciyar hankalin ki….. Amma ba yanzu ba ki bani lokaci in yi nazari sosai, ta inda hakan ba zai batawa iyayenmu rai ba, ko su yi fushi da dayan mu akan kin yi musu biyayyah.”. 

Ga mamakin shi sai ya ga ta dago. Ya kai hankicinshi yana dauke hawayen dake zuba daga idonta, ya akayiya — aka — yi ya kai ga runguma sosai yana ta faman lallashin ta, abinda ya kaishi ga soma sumbatar dogon wuyanta, ba tareda zuciyarshi da gangar jikinshi dake ingiza shi ga yin hakan sunyi shawara dashi ba. 

Shaf! Ya manta da cewa basu kadai bane, ba a gidansu bane, Mathew yana zaune, ji ta yi kamar ya katse gudan jinin da ke gudana a cikin ilahirin jikinta, ta nemi numfashinta ta rasa na wucin gadi, don wani abu ne da babu wanda ya taba yi mata a rayuwarta tunda iyayenta (Zainabu da Aliko) suka haife ta. 

Wani ‘situation’ ne tamkar ‘electrical shocking’ wanda ya tsirga har cikin kwakwalwarta. 

Dr. Mathew sai ya yi sanda ya wuce ya fice ya bar musu ofishin. Rufe kofar shi ne ya dawo dasu hayyacinsu, dukkansu suka zube ragwaf, cikin ku

jera, don jikin kowannensu ya gama mutuwa suna kokarin daidaita numfashinsu. Kamar wadanda suka yi gudun 1000mile. 

Amma har zuwa lokacin bai saki hannunta ba, ta yi ta yi ta kwace ta kasa, sai ta kai masa cizo a damtsen sa har sai da ta ji hakoranta na shirin karo da juna amma ko gezau bai yi ba, kamar ba jikinsa ta huda ba. 

Jini ya soma zuba amma bai kula ba, karewa ma, sai ya kara fizgota da azama ya rungume yana lallashi, ban baki, ban hakuri da kalamai na soyayya, masu tausasa zuciya. Wadanda a tsammanin sa, ba daga bakin shi Imam suke fitowa ba. Don bai san dasu cikin kwakwalwarsa ba. Gaskiyar Mami ne da tace “ …. ranar lallashin bata zo ba ne, Imamu Almustapha…….. Sai ta rage sautin kukan ta tana shessheka a hankali, tana shakar lallausar kamshin akba-amara dake tashi a hankali daga jikinsa. A haka Dr. Mathew ya dawo ya same su. 

Yana murmushi ya rubata mata magungunan da suka dace da ita, musamman wanda zai kawar da febern, tare da gargadin ta cewa ta cire ko ma meye ke damun ta ko ta nemawa kanta solution tunda bazata gaya mishi ba ya bata shawarar da yake ganin zata amfane ta, idan har tana son ingancin lafiyarta. 

Imam ya yi mishi godiya, bayan ya karbi takardar maganin. Mathew sai ya kirashi ya nuna mishi hannunsa da biro. Da sauri ya kalla, hannun na tsiyayar jinni, a lokacinne radadi na azaba ya ziyarceshi. Amma bai tsaya ba balle ya karbi taimakon da ya lura Dactan nason yi mishi, haka ya juya ya fita. 

Yana rungume da ita a barin daman sa suka fito zuwa wajen mota, ba ta da karfin da za ta taka kafafunta guda biyu, don haka ne ta yarda har suka fito a hakan. 

Dr. Mathew shikadai a ofis takaici kamar ya kasha shi, buga teburinsa yayi 

da kafarshi ta dama, cewa yayi “shiiiit!’ Ya antayo zagi cikin yarensa ya dannawa hausawa, a wurinshi wawaye ne da suke nuna suna son mace, ita din banza! Kamar Imam??? Shi ina zai tolerating wannan iskanci??? Suna so su maida kansu Indians wadanda basu da abin yi sai kashewa kansu rayuwa don soyayyah. 

Shi ya bude kofar motar ya zaunar da ita ya rufe, sannan ya zagaya ya shiga mazauninsa. Tafiya yake sannu-sannu, kamar bai son ya daina tukin. Amma kansa zagayawa yake jiri na dibarshi. Sanyin na’urar sanyaya mota na ratsa jikkunansu, wanda ya _ hade da kamshin jikin kowannensu, tare da kamshin air fresh din motar na turaren ‘oud-abyad’. Ya saukar da nutsuwa da aminci a zuciyar Imam har ya soma jin zai zai karbi Safah da duk abinda ta zo da shi albarkacin kaunarsa gareta, a nata bangaren itama tata zuCiyar sanyi take yi sabida yanayin,ya wanke zuciyar SAFAH daga daci da 

kuncin dake cikin ta. Ta fara tunanin solution kamar yadda Mathew ya ce. Ba ta hanyar nuna kiyayya ba. 

Har ta soma jin kiyayyar ta ga auren da aka yi mata da dan’uwanta rabin jikin ta Almustapha ba da son ranta ba na decreasing gradually da 50%. (raguwa a hankali da kaso hamsin cikin dari). Ta riga ta yi amanna da cewa ZAHRADDEEN MAITAMA….. ya haramta gare ta. Babu soyayyar shi ko daya a halin yanzu cikin zuciyarta, tun daga ranar da aka daura auren sa da ‘yar’uwarta rabin jikinta. Ba kuma wani daban take hangowa ba take son neman maslaha da Imam sabida shi ba. Zahraddeen is her past, and her husband (Imam) is her present…… then why the hatred? (Kiyayyar ta mecece?) 

Ta soma kalubalantar kanta da cewa, ‘Me ya hanata son dan’uwanta? Me ya hanata karbar soyayyar mijinta dake sonta da dukkan zuciya, ruhi da 

gangar jikinsa? Amsar mai wuya ce idan aka tirketa aka ce sai ta fadi. Domin ita kanta, ba za ta ce ga dalili ba. 

Abinda ta sani kawai shine, ba ta son Imam da soyayyar aure, saboda ya nuna mata soyayyar ne a lokacin da bai isa a ce ta san menene bambancin so da kauna ta ‘yan uwantaka ba. Gashi ta dandana SO akan wanin sa, ta san dadin sa da dacin barin sa. In bacin hakan ita kanta tasan Imam banda soyayyah ta Allah babu abinda zai ci da ita. Tunda ba fin sauran mata gashi aka ta yi ba. 

Shekarunsa goma yana karatu a Birtaniya, wadanne irin mata ne bai gani a duniya ba? Amma ya tsallako su ya dawo, sabida ita, ita kadai ranta. Alhalin ba wani abu ta fi sauran mata ba ba kuma kyau ta fi kowa a duniya ba, sai soyayyah ta lillahi da haduwar jini. Wadda yake kimsa ta a zuciyar bayinSa ba tareda yayi shawara dasu 

ba. Menene laifin mai son ka? 

Ji ta yi ya tsayar da motar a gefen titi, ta yi saurin dagowa ta dube shi da idanun bidar dalili cikin kokarin boye sabon tunaninta da rauninta. Kallonta yake, da idanuwa masu – sanyi, wadanda ke cike taf, da so da kauna, kallon ta yake da idanuwa masu cike da soyayyar da biro ba zai iya rubutawa ba. 

Amma hakan bai sa ko kadan zuciyarta ta russuna ba, daga matsayin da zuciyartata ta bashi; bloody brother (not a sweeeceetieece……). Russunawar da zuciyarta tayi tausayi ne da kaunar jini kawai kawai. Ta hakura da Zahraddeen, ta kuma tabbatar ta rasa shi har abada, amma ba za ta iya rayuwar aure da wanda zuciyarta bata yi amanna da hakan ba. 

Abinda take ji akan Imam a yau, ba iri daya ne da wanda ta ji a Zahraddeeen ba; sympathy and pity (na Imam) in

fatuation (na Zahraddeen). 

Kanshi ya kwantar a kan sitiyari, idanunshi a runtse, ya rasa inda zai sa kansa, ya rasa inda zai tsoma zuciyarshi ya ji sanyi. Bai san me zai yi ya sayowa kanshi soyayya a zuciyar Safah ba. Da gaske ne ba ta son sa, kuma har abada wanda ya ce baya son ka ba zai dawo ya ce yana son ka ba. Yau ya yarda ba’a sayen soyayya, duk tsadarta yau da ya sayo! Wanda ya furta a fili da boye, zahiri da badini baya yi da kai LET HIM GO! Da sannu zai gane amfanin ka, da sannu zai gane muhimmancin ka a gaba, da sannu zai gane wanene mai son sa, wanene mai kaunarsa, ka barshi ka yi da mai yi da kai. Ardhullahi Waasi’a (Duniyar Ubangiji fadi gareta). Idan wani ya ki ka da wuni, wani da kwana zai so ka. Kuma babu mai sanyata sai sarki ALLAH, not eben physical or material attachement. 

A yau ya ga alamomi da yawa, 

wadanda a da can idonshi ya rufe da soyayya har baya gani, tunda ga shi har ta hada kanta da hawan jini kawai saboda ba ta son shi, an aura mata shi akan dole. 

Karamin misali dubi yanzu jini ne ke zuba daga jikinsa, yana karar da hayyacinsa, yana hajijiya da kuzarinsa tana gani ko a jikinta, kwayar idonshi bacewa take neman yi dauriya kawai ya ke yi, idan da tana son sa ko kadan, kamar yadda Shahidah tace lallashi zai sayo, ayau da ya gani ko kadan, ko a kwayar idonta, sanda zata nuna damuwarta ko kulawa akai ma bazata sani ba. 

Shi nata ciwon gigita shi yayi, ya fitar dashi daga hayyacinsa, ya janyo masa asarar tafiyarsa neman abincin sa, aalah kadai ya san iya matsalar da zai fuskanta da shugabansu akan hakan, domin bature babu abinda ba zai jura ba, amma banda _ saba_alkawari. Wanda ma ba fitar jini ba kenan abu mai daga hankali. 

Wanda ita tayi sanadinsa, baya jin ko ciwon hauka yake zai tya mintsinin Safah duk irin laifin da ta yi masa, balle ya huda jikinta ta hanyar day a san zata cutu, kawai don ya rike hannunta a matsayinsa na mijin aurenta na sunnah bama da wata manufa ba. 

A take wata irin zuciya ta shige shi, mai bada ‘courage’ wato karfin zuciya, ga son yiwa Safah duk abinda take so, don hankalinta ya kwanta. IDAN SO CUTA NE, TO HAKURI MA MAGANI NE. Har zuwa lokacin kuka take, kanta cikin cinyoyinta. Ya ce (cikin wata irin murya da ta kasa amincewa cewa tashi ce). 

“Safah!” 

Bata dago ba haka nan ba ta fasa kukan ba, in banda tafarfasa ba abinda zuciyar shi ke yi. Hannu yasa ya fincikota, ya ce, “Fadi duk yadda kike SO….. Na rantse da wanda raina yake hannunSa….. a yanzun nan zan yi miki. Ko da hakan na nufin cewa 

rushewar farin cikin rayuwata ya zo, …. ko da hakan na nufin cewa, ni zan cutu, zan yi farin ciki idan har hakan shine kwanciyar hankalin ki. 

Fada min yanzun nan, me kike so in yi miki ki maida kyakkyawar rayuwarki ta baya? Abin nufi, what may be solution to your problem right now?” 

Ido ta sunkuyar, sabida ta kasa hada ido das hi a yanayin da yake ciki, wanda bata taba ganinsa a cikin kwatankwacin sa ba, amma hakan bai hanata fadin zahirin damuwar tata ba don samun maslaha ga zaman lafiyar zuciyarta. Allah Shi ke sanya so a zukatan bayin Sa, to bai sanya mata soysayyar Imam ba, baya ga ta ‘yan uwantaka. Sosai ta ce, 

“Bana son ka da aure Ya Imam, na furta amma kowa ya ki saurarena, SO daban KAUNA daban, me_ yasa bazaku gane hakan~ ba? _son ‘yan’uwantaka nake yi maka. Na fada na kara ….. bazan iya zaman aure da kai ba, bana son ka as a husband…. (a 

matsayin miji) muharramina nake kallonka, majibincin § al’amurana bayan Daddy, kuma dan uwan da banda kamarsa. Idan kai dan halak ne cikin tyayen da suka haifemu, to na rokeka ka rabu dani in zauna lafiya da iyayena,…… ka yi rayuwarka in yi tawa, ko ana so dole?” 

Ya girgiza kai, idanunshi sun rikide, sun juye sun shagide, ya cigaba da girgiza kan kamar kadangare yana cewa, “Gaskiyar ki kam. Ba’a SO dole…..to Safah ki je na sake ki…..! Na sake ki!!…….Na sake ki!!!” 

Ya maimaita har sau uku. 

Ba karamin razana ta yi ba, don ta dauka zai iya yin komai amma banda wannan. Itan kuma ba wai ta fada har zuci bane, har ma da tabara ta wadda miji ya mace a kanta, domin abinda taga yayi akanta yau, tasha mamaki sosai, bayan zuwa lokacin zuciyar ta ta fara saduda, tun daga lokacin da gangar jikin su ta hadu a ofishin 

Mathew, wasu allurai suka huda kirjin ta suka shige cikin zuciyarta, taji wasu irin sauyuka a zuciya da gangar jikin ta, da bata taba jin irinsu ba a rayuwarta, ta san ba zai taba iya yin hakan ba, shiyasa ta fadi, har da iya shege. Don ta bashi haushi ya fita hanyarta. 

Ga Imam din, ya aikata, don ya cika dan halas din cikin Uwa da Ubanshi. Wadanda ke kwance cikin kushewarsu, aka ambato su yau aka yi masa kandagarki dasu sabida ya nuna soyayya shekaru ashirin cif. Wallahi ko zal mutu babu aure, yau ya hakura da Safah, hakura ta har abada muddin ya cika dan halas din. 

A lokaci daya tsoro mai tsanani ya shige ta. (Hattara mata, masu amfani da soyayyar da miji ke musu su azabtar da shi). Takarda ya dauko a aljihun motar ya rubuta ya dora mata a kan cinyarta. Ta kasa daukan takardar ta kasa magana, sai ta saki baki tana kallonshi tana kallon takardar a tso

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *