DA WATA A KASA COMPLETE
Gaje* Ke Gaje kina ina ne waiko baki san na shigo gidan bane.” ? Matar da aka kira da wannan suna ta fito daga garken awakai da wani ‘katon buhu a hannunta, tana fad’in “Maigida wannan kiran fa Allah yasa dai lafiya naji ko sallama ba kayi ba kana ta ‘kwala min kira.”
Ya shiga karkad’e guntuwar tabamar dake gurin ya shimfid’a ya zauna had’e da cire wata hula me kunnuwa daga kansa, yasa hannu ya sharce gumin dake saman goshinsa yace.”Ke dai zo zauna kiji labari mai dad’i.” Gaje ta aje buhun hannunta tana washe ha’kora tace”Da alama dai yau kasuwa tayi kyau ko kuma ka samu gara’basa wani ya kawo tallan shanu a arha .”
Yace”Duk babu ko d’aya Ina Asiya take.”? Tace”Yanzu yanzu ta tafi rafi jidon ruwa.”
Ya washe bakinsa yana kallonta yace.” Ashe yarinyar nan Asiya ‘kashin arzi’ki ne da ita, yanzu nan maigari ya kirani fada ina zuwa yake shaida min cewar yana nemawa babban yaronsa Isma’il auran Asiya saboda yaga kaf garin nan babu mai nutsuwarta da hankalinta ai a take na amince nace na bashi.”
Ya’karasa maganar yana dariya hade da gyara zamansa.
Wani irin shan kunu tayi ta ‘bata fuska sosai tace” Shi yanzu Isma’il din ne yake cewa Asiya duk tafi matan garin nan nutsuwa da kamun kai? me ya gani a jikinta da har zaiyi sha’awar auranta, duk matan dake garin nan ya rasa wacce zaice yana so sai wannan shashashar mahaukaciya, kai kuma ka shigo kana wani murna da dariya.”
Mai Shaniya jikinsa yayi sanyi da jin abinda matar tashi take fad’a yace.”Yanzu Gaje kina so kice mun Asiya bata kai matsayin da Isma’il d’an maigari zai aureta ba, meye aibun yarinyar ? kodan bake ce kika haifeta bane yasa kike wannan maganar.”?
Gaje ta fashe da kuka tana fyace hanci tace”Da kyau! a gwara kayi min gorin rashin haihuwa wato kai har kana da bakin magana ka manta irin hidimar da nayi da Asiya ko? Uwarta tana shaifarta ta mutu ta barni da wahala nice kashinta da fitsarinta har ta girma amma saboda tsabar butulci irin naka zaka goranta min.” Mai Shaniya jikinsa yay sanyi yace.”Gaje duk abin nan fa bana tashin hankali bane! ni a ganina wannan abun na farin ciki ne da murna, yanzu idan Asiya ta auri Isma’il dan gidan maigari ai mun zama abun kwatance a gari wallahi nasan maigari sai ya bani rawani, sannan ko ke za’a dinga girmamaki idan kika shiga cikin ‘yan uwanki mata.”
Gaje ta gyara d’aurin d’ankwalinta a cukune tace”Wannan al’amarin fa ba zai yuwu ba Malam domin ni nasan Asiya ba cikakkiyar mace bace ko manta lalurar da tayi a lokacin da take yarinya ‘karama tare da kai muka dinga sintiri zuwa gurin me magani daga karshe aka samu maganin da ya magance mata ‘kurajan gabanta, to tun daga sannan gabanta ya bud’e sanyi ne da ita sosai dan yanzu haka idan ya tashi haka za kaga tana ta susa kamar zata yage gabanta.”
Mai shaniya yace.”Gaje yanzu ya za’ayi? na d’okanta da al’amarin nan wallahi ina so Asiya ta auri Ismail dan gidan maigari.” Gaje tace”Aikuwa aure ba zaiyi ba dan kasan ranar da Isma’il ya tabbatar da cewar Asiya ba budurwa bace to a ranar zai saketa, Ismail bai cancaci ya auri mace irin Asiya ba, hakanan Asiya bata cancanci ta auri namiji saurayi kuma santalele kamar Isma’il ba.”
Mai shaniya ya goge hancinsa yace.”Gaje kaina duk ya d’aure wallahi ban san me zancewa da maigari ba gashi nayi masa al’kawarin bawa d’ansa Asiya.”
Gaje ta gyara zamanta tana kallonsa tace”Kaga Mai shaniya babu maganar rufa rufa a harkar aure! kawai ka fito fili ka sanar masa abinda ke faruwa, Idan Isma’il yaga xai iya auran Asiya a haka babu budurci to sai ya bada sadaki, Idan yaga bai zai iya ba to anan fadar kafin ka fito ka bada kyautarta wanda yaga zai iya auranta da sunan bazawara sai ya bada sadaki ko dubu biyar ko dubu uku ka daura mata aure ka huta.”
Mai Shaniya jikinsa duk yayi sanyi yace.”Wallahi Gaje duk na dauka yarinyar nan ta samu lafiya ashe da shauran ciwo.”
Gaje ta ta’be bakinta tace”Malam kenan nice nake ganin ikon Allah! Asiya fa kullum hannunta na cikin wandonta tana susa babu dare babu rana mussaman idan ta kwanta bacci da daddare, gani nakeyi ma anya kuwa cutar sanyi ce kad’ai da ita kodai aure take so ne take sa hannunta a gabanta, ita dai ta sani! ni dai shawara nake baka ka bada ita sadaka kuma dik wanda zaka bawa to ka shaida masa cewar bata da lafiya kuma bata da budurci.”
Mai shaniya yace.” Gaje maganarki abar a duba ce kadafa yarinyar nan ta janyo min abun kunya a gari ace kulluma yarinya hannunta a cikin wando.”? Gaje na ‘kokarin yin magana ta shigo gidan kanta d’auke da tulu madaidaici, taci uwar d’amara!! Zaninta ya d’angale sama ‘kwarinta duk a waje! Can inda randunan su na ruwa suke ta nufa ta juye a hankali ta ajiye tulun ta d’an sassauta d’amararta ta cusa hannunta cikin zaninta ta samu nasarar zura hannunta cikin wandonta ta hau susa tana lumshe idonta. Gaje ta zunguri Mai shaniya tana nuna masa ita…..Mai shaniya yayi zumbur! ya mi’ke! hankali a tashe ya nufeta hannunaa rike da zabgegiyar bulalar da yake ‘kora shannunsa ya lafta mata ita a gadon bayanta……”Shegiya me kike sosawa a cikin wando.”? Abinda ya fad’a kenan yana sake lafta mata bulalar a jikinta, kuka takeyi tana bashi hakuri ta zube gwiwanta a ‘kasa.
Yace.”Dan Ubanki ba zaki fad’a min abinda kike sosawa a wandonki ba”? Tana kuka tace”Wallahi babu komai Baffa kayi hakuri bana sosa komai.”? Gaje ta taso daga inda take ta kwad’a mata mari tace”Ma’karyaciya gashi nan har yanzu hannunki guda na cikin wandonki zakice babu komai.” Da sauri Asiya ta zaro hannunta daga cikin zaninta tana kuka tana fad’in bana sosa komai Baffa kayi hakuri.” Mai shaniya ya jefar da bulalar hannunsa yana kallon Gaje yace.” Yanzu naga zahiri Gaje naga Zahiri! to wannan yarinyar ba zan bari ta wulakantani ba, yanzu yanzu zan nufi Fada domin na shaidawa maigari abinda ke faruwa aure zanyi mata na huta.”
Gaje tace”Yanzu kayi magana Malam maza tashi kaje fada ka sanar da maigari abinda ke da akwai.
Mai shaniya ya dauki hularsa ya kwafa, ya zura wani takalmi sauciki irin na roba kwataf-kwataf sai kace kuturu ya futa daga gidan rasa a ‘bace!