UMM ADIYYAH CHAPTER 87 BY AZIZA IDRIS GOMBE
Www.bankinhausanovels.com.ng
dawo ba ta kiransa hakan.
“Na’am Twinkle me ya faru?”
“Ina tsoro…”
“Wani abu ki ka gani?”
Wuyanta ta shiga shafawa kamar tana goge
wani abu. Ya san tsigar jikinta ne yake
tashi. “Fada min me ki ke so na yi miki?”
“Uhm! Za ka iya canza daki?”
Fuskarsa ce ta tattare cikin mamakin kala-
manta. “Me ya faru da nan din, bai miki
bane?”
Rarraba idanu ta yi ta ce, “Uhm… Ya yi min
kawai ina so ka canza daki ne, ka bar ni
a nan.”
Kallonta yake yi kamar ta sha omo ko giyar
wake. “Yaya ki ke tsammanin na raba
daki da ke? Sannan a garin da ba namu ba
cikin otel? Me ya faru?”
Idanunta ta sauke, “Ba na son… Ehm. Ba dai
kai bane, amma ba na son ganinka.”
Shiru Zaid ya yi, ya kura mata idanu wani iri.
Subhanal-