SIRADIN RAYUWA CHAPTER 6 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

 SIRADIN RAYUWA CHAPTER 6 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA


Cak qwaqwalwarta ta tsaya da aiki na wucin gadi,komai yayi mata dif tamkar qwaqwalwar tata bata taba wani aiki ba,ta daina fahimtar komai sai maganganun umma luba dake mata amsa kuwwa cikin kunnuwanta,sun dade suna maimaita kansu kafin tasoma fahimtar abinda takeson gaya mata
“Taje ta bada fansar kanta da budurcinta wa yariman qasar kaisa na tsahon shekara daya” a dunqule idan ta fahimta kamar hakan umma luba take nufi ko?,ta jefi kanta da tambayar,saita daga idanunta dasuke walainiya ta xubawa umma luba su,shin tasan ma’anar abinda take fada kuwa?,anya hankalinta daya?,a cikin hayyacinta ma take?,bataga alamun wasa saman fuskarta ba face tsantsar gaskiya dason isar da saqo bare tace wasa take mata,karon farko data motsa labbanta 
“Ban gane ba umma,ban gane abinda kike nufi ba” murmushi tasakar mata dukka bisa qoqarinta na kwantar mata da hankali
“Kin gane maigado saidai kicemin kin rude,kuma tabbas koma wacece da bata zaci samun irin wannan damar ba ta sameta sama taka dole rudani ya shigeta,kije kiyi tunani kawai nan da jibi,saboda kwanaki biyar yarage mana muje mukai duk wadda muka samu” wani abu ya tsaya mata iya wuya,ta fahimta takuma fuskanta,wato bazasu akayi suyi farautar yara marasa galihu irinta,musamman idan akayi katari da masoya abun duniya masu kwadayi shikenan kaya ya tsinke a gindin kaba?,duk haqurinta duk sanyinta ba zata lamunci a qasqanta mutunci da darajarta ba,lallai ya kamata idanma umma luba tana da wani tunani na daban a kanta ta warware matashi,don a gaba bata fata hakanan bata sha’awar ta sake soko wata magana makamanciyar wannan a tsakaninsu iya zamansu,koda tanason aure koda lokacin da zatayi aure yayi ita ya kamata ta zaba bawai a zabeta ba,bare a yanzu da qaramar qwaqwalwarta take cunkushe da matsaloli,gajeriyar rayuwarta take quntace take kuma takure,a gaba daya tunaninta da abinda idanunta suke gabe mata shine,aure gaba dayanshi matsala ne,babu komai cikinsa face jefa kai cikin damuwa da matsaloli,me yasa ma zata yarda anan kusa da qananun shekarunta ta fada matsala kwatankwacin matsalolin da taga umma katti da sauran matan da babanta yake aurowa suke fadawa?,shi yasa ko daya bata sha’awarsa,koda ya zame mata dole tana duban nisan zangon da zata qara diba kafiin ta fada komarsa
“Aure a nawa qaramin tunanin ana yinsa ne a sanda namiji da mace sukaga juna suna so,suka kuma amince da juna,shi namijin zai tattako koya tura wakilansa zuwa gidansu yarinya su nema masa aurenta,baya ga haka babu wani sharadi da ake gina aure a kansa na cewa bayan lokaci kaza akwai wani abu kaza dazai faru,yakan zama tarayya tahar mutuwa a yadda nake ganin yana faruwa a mafi yawancin gidaje,kiyi haquri umma luba,ni bazanyi aure ba,koda zanyi aure toba yanzu zanyi ba,ki nemo musu wata,nasan da yawa zasu amince,zan wuce gida sai Allah yakaimu gobe” da mamaki take duban bilkisu,ashe yarinyar ta iya magana har haka,ashe tana da zurfin tunani da hankali?,koda ba’a gaya mata ba iya zamanta da bilkisu ita zata bada shaidar ta iya talaucinta,hakanan ba makwadaiciya bace,amma bata taba zaton zata bijirewa wannan tayin ba.
      Ganin da gaske bilkisun tafiyar xatayi,kuma idan har tatafin wata qatotuwar dama ce mai gwabi da zata subuce mata,wadda samu ko maida kamarta saitaci wuya,wala’alla ma cikin abokan aikinta wata takawo tata kuma a karbeta ta rasa dukkan wata dama matsayi da daukaka da zata samu a masarautar kaisa,zumbur tamiqe tana qwalawa bikisu kira wadda batakai ga fita ba,gabanta tasha tana dubanta cikin kwantar da murya da karyar dakai
“Haba maigado,haba,qauna ce fa tasa na zabeki na tsallake dubbai,ya kamata ki dinga sara kina duban bakin gatari,a yadda kikeson ‘yan uwanki na zaci zaki iya sadaukar da farincikinki saboda tasu rayuwar ta inganta?,kin gwammace ku dawwama a haka bilkisu bayan ga dama da kika samu ta fidda kowa daga qangin da yake ciki?,shekara daya tak fa rayuwarki zata inganta,me za’a gutsira daga jikinki?” Idanunta masu maiqo tazubawa umma luban tana dubanta ganin yadda ta haqiqance,itadin ba tsararta bace hakanan basu saba ‘yar tankiya ba,inda sun saba din da taji amsa dai dai da ita,datace bata amsa yadda ya kamata,tana tsammanin a yadda idanun al’umma suka rufe kowa ya tasa kudi gaba fiye da mutuncinsa itama bikisun haka take?
“Kiyi haquri umma luba kamar yadda nace miki dafarko bazan iya ba,don Allah ki duba cikin dubban ki zaba wata,nasan za’a dace” daga haka tarabeta tafice daga gidan,tanajin iska na dibanta,hakanan maganar na ratsata fiye da yadda ta tsammata,sai taji tun daga kan hanya kamar zazzabinta daya sauka yana niyyar dawowa,maganganun sukaci gaba da juyin waina a tanda cikin qwaqwalwarta,ta rasa ma wanne zata kama.
      Tsaka da haka taji kamar ana ambatar sunanta a sanda take qoqarin shigewa gidansu,yanayin yadda sautin ke fita saitaji kamar tasan me kiran,don haka ta tsaya cak ba tare data waiwayo ba,hakan yabashi damar qarasowa gabanta,abubakar saddiq ne,sanye cikin shadda dinkin tazarce,kansa babu hula,kana masa kallon farko zakasan yana ji da gayu da samartaka,jifanta yayi da murmushi saita janye idanunta daga kanshi,hakanan yake mata kwarjini,tasamu da qyar ta tattara lafuzan gaisuwa saman lebunanta ta aika masa,ya amsa idanunshi kan labban nata dake masifar burgeshi,ya fuskanci bayan kyau yari yar tana da wani qasaita da izza wadda wala’alla itadin batasan tana dashi ba,miskilancinta yana burgeshi,hakanan yanayin dakiya da basarwarta.
       “Kwana biyu baki ganni ba,amma koki cigiyata ko?” Yafada yana dan fidda murmushi gami da shafar sumarshi,maganar tasa ta sake tarwatsa tunanin dake fareti a kwanyarta,saitayi kaman zata kalleshi bisa mamakin furucinsa saikuma ta basar,ta nemeshi akan me?,idanma tasan inda yake din ya cancanci ta nemeshi?,yasake sakin murmushi ganin yadda tasake basarwa
“Koda yake bakisan inda nake ba ko?,kuma baki sha’awar amsar numberta ba kosau daya,koda kin saninma nasan masu suna bilkisu da sarauta,da wuya anemi din,to gashi na sake kawo kaina a karo nabiyu,kuma sai naga kamar sauri kike,ko zaki aramin minti goma cikin mintunanki muyi magana?” Da sauri ta girgiza mishi kai alamun a’ah,duk da hakanan take ganin qimarsa,amma a yanzun bata sha’awar dogon magana,dan shuru yayi alamun baiji dadi ba,amma saiya dage kafadunsa
“Ohk,ba damuwa,asake samin wani lokacin saina dawo muga juna….,ko a bani phone num saina kira ko?”
        Kafin tabashi amsa babanta yafito daga cikin gidan,tunda taganshi tasan komai zai baci ne,don haka tabude bakinta dasauri tace
“Sai jibi in sha Allahu,babu damuwa” yasaki murmushi,don ba qaramin dadin amsar jibin data bashi yaji ba
“Allah yakaimu,na gode qwarai”. Kafin ta amsa ya iso garesu,don haka saita wuce zuwa cikin gida kawai tabarshi da sadiq,koma meye ita bata sha’awar yafaru a gabanta.
        Ko kadan a cikin ranta bata ji ta daina zuwa aiki gidan umman luban ba,a nata ganin komai yana da muhallinsa,yadda maganarsu keda muhalli na daban haka aikinta ma,babu abinda zai shafi wani,saidai yadda maganar ta tsaye mata yasanya washegari bata da qwarin jiki dana zuciyar tafiya gidan aikin.
       Rashin zuwan nata yasanya umma luba babu abinda bata saqa ba,abu na farko tsoron tawaye daga wajen bilkisun kamar yadda ta raya,don haka wata washegarin ta yanke gwara ta fuskanci fulani da maganar,wala’alla asamu wata mafitar.
      Kamar kowanne lokaci idan zatayi ganawar sirri da amintattun nata,waje ne kebantacce wanda yake cike da sirri da aminci,fulanin aysha ce daga tsaye cikin shigar alfarma dake nuna xallar mulki da sarauta,yayin da umma luba ke zube a gabanta,kanta a qasa bayan ta kammala dukkan bayananta.
      Tattaki fulani aysha tayi tana nazarin maganar da umma luban tazo mata da ita,tasan tunda lubabatun takasa sukuni kan lamarin babu ko tantama yarinyar ta cika mace,takuma cika dukkan sharuddan data gindaya musu kafin fararwarsu aikin,ba shakka ba umma luba kadai datasan yarinyar ba,har ita kanta tacika da mamakin yadda za’a samu wasu ko wata cikin qasarsu da zata iya bijirewa wannan tarin alkhairi dasu a nasu ganin suke ganin kamar alfarma ce sukayiwa koma wacce diya ce,eh mana alfarma,tunda banda wannan dalilin da ko cikin mafarkinta bata taba hasashe ko hango azeez din yana nema ko auren daya daga cikin yaran talakawansu ba,azeez din mai tsada ne,saboda haka dole komai dazai rabeshi yazama mai tsada mai daraja
“Kin tuntubi mahaifinta?,idan kin tuntubeshi shidin me yace?” Fulani ayshan ta jefa mata tambayar,ta girgixa kanta da sauri
“Tuba nake Allah ya taimakeki,sam sam na manta da wannan,ai Allah yabaki yawan rai ina da yaqinin cewa idan na tuntubeshi ma magana ta qare,yanzu kuwa zan tashi,bazanyi qasa a gwiwa ba zan sami mahaifinta” murmushi fulanin tayi cikin zuciyarta,don idan ka kalli saman fuskarta ba zakaga alamunsa ba,saita soma takawa zuwa saman daya daga cikin kujerun tana dauko wata jaka tana kuma magana da umma luban
“Ki jaddada masa matsayin wanda ake nemawa diyarsa koda shima zaice zaya musa,daga yanzu bana buqatar a sake magana da ita yarinyar,yardar mahaifinta tamkar yarda ce,abunda nake da buqata kawai shine,hoton yarinyar don inason in ganta dakyau,na tantance kuma na tabbatar da dacewarta da yarona” tana kaiwa nan taciro kudade rafar ‘yan dubu dubu tana miqawa umma luba,jikinta na rawa cikin sauri ta amshe tana zuba mata godiya kana tataso cikin farinciki tafito daga falon tana cusa kudin cikin zaninta,tana kuma jaddadawa kanta lallai zatayi dukkanin me yiwuwa taga komai yatafi yadda akeso,takuma cimma nasara.
       A lokacin da umman luban tazo tana daga daki kwance,taji murya kamar tata,amma sanin cewa babu wani abu da zai kawota gidan saitaci gaba da kwanciyarta tana jan istigfari cikin ranta kamar yadda tasaba yi a yawancin lokuta idan bata da abunda zatayi,ita daya ce cikin dakin tana sanya ran gobe tawuce wajen aikinta,dukka qannenta sun tafu islamiyya,Allah yasanya weekend ne gobe take saka ran zuwa har makarantar boko.
       A falon amarya ladidi tasauka,lokacin yana zaune saman daya daga cikin kujerun falon,gama sa’insarsu da ita kenan akan shinkafa,tace haram tabashi abincinta yaci,tunda rabonshi da kawo cefane yau kwanaki uku kenan,yayi barazanar da muzuran duka a banza ladidi ta dauke kanta,yunwa ce kawai ke sadakarshi,gashi babu ko sisi cikin aljihunsa,yasan ko giyar wake yasha bazai tunkari katti tabashi abinci ba,don tunda ya qara auren nan taja masa layi,irin layin da bata taba ja masa ba,ta tattarashi dukka ta barwa ladidi shi,ta yaranta kawai da sana’arta take.
        Ya sake shafa cikinsa yana tsinewa talauci karo na babu adadi,sam a rayuwarsa bai taba kawowa zai tsunduma cikin talauci irin na wannan qarnin dana yafa ba,dai dai lokacin da ladidi ta dage labule suka shigo tare da umma luba
“Baquwa ce takeson magana dakai” ladidi tafada tana wucewa uwar dakanta don adana miyarta data gama soyawa,yabi kwanon da ita kanta ladidin da kallo yana hadiyar yawu kamae tsohon maye,don tuni qamshin miyar yagama cika mishi ciki yasake tada mishi yunwarsa.
     Gaisuwar da umma luba keta faman rattabo masa tadawo da hankalinsa,saiya maida hankalinsa gareta yana amsawa cikin yanayin nuna rashin sanin mutum,saita taqaita masa wahalar dakai ta gayamishi wacece ita
“Uwar dakin maigado ce,gidan da take aiki” gyara zamanshi yayi gabanshi nadan faduwa,yayin da wani sashe na zuciyarsa yacika da fatan Allah yasa kudin aikinta takawo mata ganin kwana biyu bata je ba ya amsa ya kalmashesu ya rage radadi na kwana biyu
“Au…..to….to,madallah,ina fata lafiya daiko?” Murmushi tayi tana gyara zamanta
“Lafiya lumi,sai alkhairi dake tafe dani” jin haka yasa yasake tattara nutsuwarshi yana dubanta,tadan karkace ta zaro rafa daya ta dubu dubu cikin irin wadda fulani aisha ta mata kyautarta ta aje gefan malam bilya,bin kudin yayi da kallo a mamakance cikin ranshi yana qissima abubuwa da yawa
“Kadda ace kudin aikin nata takawo mata,to amma maigado na karbar maqudan kudi haka masu yawa amma bata taba jin qaina ba?,kodai yau Allah ne ya toni asirinta?”
“Wadan nan….dama wasu masu tarin yawa zasu zama mallakinka matuqar ka aminta da maganar da nake tafe da ita” mamakin jin zai mallaki kudin suka kamashi,saiya dafe kudin yana sake gyatta zamanshi 
“Wacce magana ce wannan baiwar Allah?”.
      Ba tare data boye mishi komai ba tayi masa bayani filla filla,ta shaida masa yadda sukayi da bilkisu a gidanta,sannan ta rufe bayanin nata da gaya masa irin tarin maqudan kudaden da zai samu da alkhairi iri daban daban.
      Ba malam bilya bs,hatta ladidi dake daki wadda dama fakare tayi batasan sadda tafito zuwa falon ba tana rarraba idanu tare da qissima yadda zata sake kame mijinta malam bilya matuqar hakan ta kasance
“Kan ubancan!,amma ban taba sanin baqincikin maigado ya ta’azzara har haka ba da tuni na jima da nema mata maganin samun salama,ashe yarinyar nan bata qaunata duk ban sani ba sai yau?” Yafada yana duban ladidi wadda tasamu waje daura dashi tazauna itama tana neman muhallin da zata tofa tata
“Ai malam kada kasake kada kabari wannan damar tawuceka,koda a mafarki kasameta aika more ballantana a gaske” ladidi ta tofa din kamar tadda bakinta yaketa motsi tunda tafito
“Niko ladidi idan nabar hakan ta kasance a cikin tababbu marasa rabo ai nine sahun gaba,maigado zataci ubanta,wanne amfani zatamin na tsahon shekara gudan dazai kawomin wannan alkhairin” da sauri umma luba ta dakatar dashi
“A’ah malam,bada zafi zaka mata ba,kayi mata cikin hikima da lallashi wataqila tafi fahimtarka a matsayinka na mahaifinta,kaga babu yadda ban kwatanta mata ba amma taqi,ni kuma qauna ce tasa na zabeta cikin dubbai,inasonta da wannan alkhairin” wuyar rigarsa daya zame yajawo yazauna sosai saman kafadarsa,cikin nuna isa da hura qofofin hanci yace
“Yo yarinyar dana haifa a cikina ma saina tsaya ina lallabata?,ai indai nine na haifi bilkisu to kije kawai ki shaidawa ranki ya dade…..koma ku rankaya tare mu sanar mata na bawa yarima ita,zan mata lallashi nafarko amma idan na fuskanci asara takeson jaza mana tofa bazan mata ta dadi ba….kekam babu abunda zamuce dake sai godiya,don ba qaramin masoyinka bane zaiga alkhairi haka ya rungumo ya nufoka dashi”.
        Kowannensu cike da farincikin zuwa gabar samun cikar burinsa sukayi sallama,don bata tsaya taga bilkisu ba bare tasan da zuwanta ko suyi magana.
       Miqewa malam bilya yayi yana jinsa yau da wani irin nauyi sanda yake cusa rafar kudinsa a aljihunsa,ganin yasoma haramar ficewa sai ladidin ta lanqwasa murya
“Malam,bakaci abinci ba zaka fice” harara ya watsa mata
“Ki riqe kayanki mana kici ko zaki qara kumari,an gaya miki ni matsiyaci ne?,ni nan da kike gani duk inda nayi arxiqi bibiyata yake a jinina ne”
“Kayi haquri malam….karka watsamin qasa a ido mana,ta yaya zaka iya shawo kan yarinyar nan bayan kasan cewa mace sai mace ‘yaruwarta,nina gama tsara yadda zamusha kanta amma naga kana da niyyar botsarewa” jin ta ambaci kalmar shawo kan bilkisu yasan kuma ladidin akwai hikima saiya sassauto,yana wani ciccin magani murya ciki ciki yace
“To yanzu ya za’ayi?” Tamiqe da hanzari tana cewa
“Kasan kwananta wajen nawa kamar bata da lafiya,kuma gidan nan kasan cewa ba wani cikakken abinci gareshi ba,yanzu haka qila tana kwance bataci komai ba,bari na zuba maka abincin saina tasota itama na zuba mata tazauna kunaci tare kana janta da hira harka sako mata zancan” dariya yasaki
“Yauwa ladita,ladi ga tsiya ga dadi” ya qarashe maganar yana komawa mazaunin daya tashi dazu,yayin da itama tasaki dariyar tana wucewa zuwa uwar dakanta,tasamu farantai biyu tayi zubin shinkafa da miya da salad harda nama tafito falon dasu,ta ajesu dukkaninsu a gabanshi kana tafice don kiran bilkisu.
     Cikin mamaki ta amsa sallamar jin muryar wadda yau tashigo dakinsu,matar da tunda tazo gidan ko ta qofar dakin nasu bata taba wucewa ba bare tayi batan kan shigowa koda me yake faruwa kuwa cikin gidan.
      Tilas tamiqe tazauna ganin murmushi saman fuskar mama amarya makar yadda yaran gidan suke gaya mata,saita qaraso tadan tsaya daga gefan bilkisun
“Sannu maigado,jikinne dai?” Wani mamakin yasake kamata,saita daure ta gyada kai harda qarin bayani
“Alhmdlh nasamu sauqi ma”
“Masha Allah,naji dadi,babankune sai haquri,baya kyautawa wallahi sam,koda baka da kudin hidima da iyalinka amma ai aqalla ka jasu a jikinka ko?,yanzu gashican duka yadamu,yanason miki sannu amma yana nauyin wai bai siya miki magani ba tunda kika kwanta”
“Baban namu!” Tayi subutar bakin fada cikin muryar dake nuna zallar mamaki idanunta kan ladidi,don iya abinda hankalinta zai iya tunawa bata taba ganin alhini saman fuskarsa don daya daga cikinsu bashi da lafiya ba,kai ta gyada tana murmushi
“Shi dinfa,shi matsalarsa idan baida kudi saiya watsar da kowa maimakon yayi bayanin bashi dashi ne,yanzuma shine ya aikoni yace kizo yana son ganin jikin naki” kusan daskarewa tayi,don bata ma gane ba saida ladidin tasake gaya mata,sannan tamiqe jiki ba qwari ta ciro mayafinta dake rataye jikin qofa cikin mutuwar jiki tabiyo bayan ladidi,don hakanan kawai jikinta ya bata dukka abinda yake faruwa ba gaske bane bogine,akwai wani abu aboye a qasa,don ruwa baya tsami banza,dabi’ar data zama jini da tsoka tsahon shekaru sama da ashirin ba qaramin abu bane zai sauyata cikin gaggawa haka ba,amma kome meye zataji zata gani,don kusan tafi kowa karantar halayyar baban nata cikin yaranshi,saboda dogon zama da sukayi tare dakuma baiwar fikira da Allah yayi mata na saurin fahimtar abu.
Sanda suka shiga dakin tuni ya soma nisa wajen kai lomar abincinsa,bakinsa cike da shinkafa yake nuna masa inda ya aje daya plate din yana cewa
“Qaraso nan maigado,sannu,Allah yayi miki halin juriya irin na maimunatu na” duk da tazauna a inda ya nuna matan amma bata dubi abincin dake wajen ba,don sam ko kusa ko alama ko amafarki bata taba kawowa a ranta nata bane
“Gani baba” ta fada kanta a duqe kamar yadda suka saba yawancin lokutta,saboda tsananin rashin sabo da rashin jansu a jiki
“Yaya jikin naki?” Sai data masa duban mamaki kana tasake maida kanta qasa ta amsa
“Da sauqi alhmdlh,na warware”
“To madalla,madalla” soma yunqurin miqewa tayi,ya dakatar da ita da sauri
“A’ah,zauna mana ga abinci nan kici,kya tashi bayan ke aka zubowa?” Duban abincin tayi tadubi baban nata,yasan cewa tambayoyine fal a bakinta,amma kasancewarta bamai yawan surutu ba sautari kana gane tana da abun fada ne da hanyar duban abu da idanu
“Zauna kici maza,keda ba isashshiyar lafiya gareki ba” mama ladi tasaka baki,saita koma tazauna cikin matuqar sanyin jiki tajanyo abincin gabanta.
 
       Tsananin rashin sabo da mamaki suka sanyata kasa kai koda loma daya bakinta,sai faman juya abincin kawai take da cokali tana sauraren hirarrakin da baban nata yaketa soko mata,wadda ta kasa bashi cikakkiyar amsar koda abu daya,saboda jinta take gaba daya banbarakwai,har zuwa lokacin daya kammala cin nashi abincin,saita aje cokalin itama tamiqe
“Zauna mana me gado,wai saurin me kikeyi?,magana zamuyi ai” yafadi dai dai sanda mama ladi ta jiye mata ruwan randarta mai sanyi a kofin silba a gabanta tadora da cewa
“Shine ai,kamar ana cizonki”.
        Shuru ne ya ratsa dakin na wasu mintuna yana kama zaren maganar farawarsa zuwa qarewarsa,sa’annan yaja wata gyaran murya mai kauri kafin yasoma magana
“Wato maigado haka Allah yake lamarinsa,saika haifi yara rututu amma a cikinsu sai Allah ya daukaka darajar wani,yayi masa nasibin da kaf cikin yaran naka babu maishi,wani al’amarine ya tunkaromu na alheri wanda dukkaninmu alherin xaibi ya shafi kowa da kowa haula da zuri’a,amincewarki kawai muke nema harni mahaifinki”.
      Yana fadin hakan taji gabanta ya yanke yafadi,tasoma ambatar sunan Allah tana addu’ar rabbi yasa ba abinda zuciyarta take raya mata bane,idan kuwa shine ta tabbatar da cewa ta kade daga ita har ganyenta
“Gidan sarautar garin nan suke neman izinin hada zuri’a dani ni malam bilya na shekara daya,wanda acikin shekarar zasu azurtani na zama daya daga cikin jerin alhazawan da ake zance,nasan ke yarinya ce mai biyayya,ba zaki taba cewa komai ba akai,saboda haka tunima na bayar da aiken cewa nabasu ke!” Kamar saukar ruwan sama da tsawa haka taji maganar tashi,ba tare data shirya ba wasu hawaye masu dumi suka soma layi tun daga cikin idanunta zuwa saman kuncinta. Lahaula wala quwwata illa billah!. Ta sani dama tasan xa’a rina wai an saci zanin mahaukaciya,tasan cewa matuqar wannan batun yashiga kunnuwan mahaifinta to magana ta riga data qare.
       Dukkaninsu sunga hawayen dake zirya a fuskarta,hakan yasanya mama ladi gyara zama gami da dora nata sharhin
“Duk ɗa nagari burinsa shine ya farantawa iyayensa yacika burinsu,kuma alhmdlh kedin kin samu shaida a wajen mahaifinki,don kaf ƴaƴansa babu wanda yake naci da damuwa dayimin zancanshi shida mahaifiyarsa irinki,shi yasa muke da kyakkyawan fata dakuma zaton ba zaki watsa mana qasa a idanunmu ba,don ke kanki basai an gaya miki ba cewa babbar masarauta ce take nemawa babban yaro kuma magaji a wajenta aure,kinga wannan bama lamari bane da za’a ce an tsaya ana jayayya akai ko tantama ba” duk da hawayen dake idanunta hakan bai hanata duban umma ladi ba,ba abun mamaki bane donta fadi hakan,saboda sama taka ta ganta,batasan cinta shanta ba bare sutturarta,ba’a maganar lafiya da ilimi harta kawo wannan minzalin,idan akwai wanda zata zarga shine mahaifinta,da har ya amshi wannan wasan yaran hannu bibbiyu yake da muradin wanzar dashi,ba tare daya tuna cewa diyarsa bace ita jininsa ce,dukiya ta rufe masa ido,koda baisan komai na dawainiyarta ba,baison ciwo da zafinta ba amma ai tsatsonsa ce
“Kayi haquri baba,karka bada aurena ta wannan sigar don Allah,hanyar da duk wani mutumin qwarai yaji zaiyi Allah wadai da ita,idan ka matsu ne na matsa daga gabanka,kana iya neman wanda zai aureni saboda Allah,ya riqeni saboda Allah,yaqaunaceni saboda Allah,yakuma zauna dani saboda Allah,wanda zaiga girma da mutuncinka martaba dakuma qimarka,ka duba maganata don Allah” ta qarashe fada cikin rauni,duk da cewa tafada ne koda wani abu zai iya taba ranshi ya waiwaya yadubi abinda yakamata,tasanshi sarai akwai kafiya da tsaiwa kan maganar da yakega tayi masa kuma itace dai dai,ba kasafai ake sauko dashi daga dokin naƙi ba idan yahau.
       Cikin hargagi da kaurara murya yace
“Ke bilkisu!,naji duk abinda kikace da uwardakinki,nasan kuma dama ra’ayinki kenan,to ba yardarki nake nema ba,hakanan ba shawartarki nake ba,na yanke hukunci ne a matsayina na mahaifinki wanda yake da iko dake,ki yarda kokar ki yarda wannan ya rage naki,tashi ki fita ki bani waje”.
       Wani irin duhu duhu da hajijiya take gani,haka ta dinga laluben hanya,a daddafe takai kanta dakinsu,tazube tana sakin wani marayan kuka,karo na barkatai tasake fadawa cikin halin bege da fatan inama ace anty zuhra tana nan,inama ace anty zuhra zata dawo kafin mai afkuwa ta afku,tasan idan da tana nan zatayi dukkan maiyiwuwa ta hana faruwar lamarin,duk da matsananciyar ƴar tsamar dake tsakaninta da mahaifin nata.
       Ranar za’a iya cewa ba ita kadai ba,hatta da ƴan ƙannenta babu wanda ya runtsa,ta kasa boye tashin hankalinta sam,kuka tayi mai yawa wanda ya qara yawan zazzabin da tayi tunanin yatafi kenan ashe yana labe,yasamu mafaka kuwa yasake rafketa.
************
      Washegari bayan duka qannenta sun wuce makarantar Allo,tana kwance a daki ita daya,tanaji tana gani makarantar data ci burin taje yau hakanan tabi ruwa,don bata da ƙwarin jikin da zata iya niƙar uwar tafiyar data saba.
       Mama ladi ce tayi sallama tashigo dakin dauke da kofin silba da faranti mai dauke da kunu da wainar gero
“Sannu maigado,tashi kisanyawa cikinki wani abun kinji,su iyaye haquri ake dasu ana musu biyayya don a wanye qalau” hakanan ta qaraci babatunta ta fice,batako daga kai ta dubeta ba bare ta tanka mata,kamar ta sanya qafa ta shure abincin haka gaji,abun sam babu Allah a ciki,yau da qyar tasamu ta hadawa qannenta abinda sukaci da safe suka wuce makaranta,babu wanda yadamu da basu koda danyar qwayar gero,amma ita din yanzu gashi ana bibiyarta da abincin har shimfidar kwananta.
      Umma katti ce ta bankada labulen dakin tashigo,fuskarnan a dinke tsaf kamar hadarin kaka,wanu kallo takewa bikisun sannan tace
“Wai me yake hadaki da waccar matar da naga daga jiya zuwa yau sai wani haba haba takeyi dake?,ko wani sabon munfurcin da tuggun xa’a hada baki dake a qullamin?,to idanma hakane ina mai gargadinki dajan kunneki ahir dinki,kuma shima munafukin uban naku wanda nasan da saninsa ake shirya komai zanje yanzu nasameshi,don ba’a siya sai dana gama dawainiya daku daci daku sannan azo za’amin wannan iyayin ba ehe” daga haka tajuya tafice tana mita.
     Batasan ya suka ƙarke ba,amma ga mamakinta da daddare itama saigata da nata abincin tana mata magana cikin lallama,inda ta dangwarar da wancan da wanda mama ladin tasake kawo mata a nan ta dangwarar da natan itama.
*********     ***********
      Kashingide take saman lallausan carfet din dake madaidaicin falon alfarmar tana amsa wayar sumaira,wadda ke karatu a qasar kano jami’ar bayero,tana hannun yayarta uswa dake aure a masarautar kanon.
       Yanayin yadda take amsa wayar kawai ya isa ya nuna maka zallar yadda qaunar ‘ya’yan nata,wanda dama hakan aqidartace,halayyarta ce son ƴaƴa
“ƙarshen watan nan muke sanya ran zuwa ma ammi,mu duka harda anty uswa,su irfan zasu samu hutu” cikin jin dadi tace
“Allah ya kawominku lafiya,dama inason ganinku gaba dayanku” daga nan sukayi sallama kana ta maida kanta ga umma luba dake duƙe gefe tana jiranta
“Uhmm,ina saurare” gyara zama tayi tana fidda murmushi
“Ai Allah yabaki yawan rai,Allah ya dafa miki tuni an wuce wajen,don mahaifinta ma yace yabaku,ai babu mai iya ja daku,ya amince yabaku ita” murmushi fulani tasaki,sannan tatashi tazauna sosai
“Dakyau,aikinki yana kyau lubabatu,tun zuwanki nafarko naji dukka hankalina ya karkata kan naki zaben da kikayi,saboda na tabbatar ayadda kika kasa zama kikazo kika shaidamin komai yarinyar ta hau mixanin da nakeso,hakan yayi”. Farinciki ya cika zuciyar umma luba,tana ganin kakarta gab take da yanke saqa cikin masarautar kaisa
“Allah yabaki yawan rai,godiya nake,na gode da yabon dana samu daga gareki,yanzun Allah ya taimakeki kina da buqatar ganin yarinyar ne a kawota?” Hannu ta daga mata kana tace
“Bani nake buqatar na ganta ba,inajin yarima shi yafi cancanta ya ganta,idan tayi masa shikenan sauran ayyukan sun gama kammaluwa,abinda kawai yarage sai daurin aure,dakuma biki daga can nasu bangaren,don a nan bangaren namu,bana fatan koda ƙadangaren gidan nan yasan da maganar balle jama’a” cikin girmamawa ta rusunar dakai
“Baki da wata matsala Allah ya taimakeki,yadda kika dama haka kowa zaisha,tauraruwar mai martaba,hasken masarautar kaisa….in shaidawa yarinyar su shirya tafiya can ƙasar da yarima yake kenan?” Kai ta girgiza
“Eh….su shirya cikin satin nan zan sama muku visa keda ita da mahaifinta da mahaifiyarta”
“Angama ranki yadade,Allah yasa ki gama lafiya,godiya nake,nizan koma don nasamu zarafin isar da saqonki” ta furta cikin zumudi da farinciki,don nata manta qasar ba,bata kuma manta irin dadi da kashe ƙwarƙwatar idanu da sukayi ba,duk da cewa dubiya sukaje amma sukam fes haka suka dinga jinsu,kamar wancan karon wannan karonma sai data wanke umma luba da kudi,ba tare data damu da cewa kwanaki kadan ta bata wasu masu yawa ba.
       Zuciyarta fes,ranta fari qal,babu tunanin komai a ranta,saima hasaso yadda komai zai tafi dai dai take,yanxu abinda yarage shine tasoma nema musu visa kamar yadda ta gayawa umma luba,wayarta dake aje gefanta tadauka tasoma neman wata number,saikuma ta tsaya saboda wani ɗan gajeran tunani da tayi,tasauya akalar kiran nata zuwa layin azeez,tana kiran tana mita can qasan ranta ita daya,tunda sukayi maganar da ita bai sake tada zancan ba,iyakaci idan yakira suka gaisa sukayi maganar data shafesu shikenan,kamar ma bai damu ba ko nashi da interest akan zancan,itakam babu abinda zai dakatar da ita,tasan gata ne zata masa,don ta yadda yake sharewa kuwa tasani da zarar taga matar a gefanshi zai ware ya manta komai.
      Yanzun kam dole tasoma samunshi da maganar,tasan halin miskilancinsa,sai suje yaqi ganinsu harsu dawo suyi zuwan banza,wannan kadanne daga aikinsa.
       Dai dai lokacin da azeez din suke zaune a wani wajen kebantaccen wajen shaqatawa,wajene da za’ace yana da tsarki akan sauran guraren shan iska dake mexico city.
      Komai nashi farine da ratsin baqi dan kadan,kamar yadda na lura kusan dabi’arsa ce son farin abu,farin wando ne a jikinsa mai azabar kyau wanda ya zarce gwiwarsa amma baikai idon sahu ba,sai shirt me gajeran hannu,v neck wadda tafidda qirar halittarsa,kallo daya zaka yiwa dantsensa kasan yana daga qarfe,qafafunsa rufaffun takalma ne hightop suma farare qal dasu kamar ba’a taba sanyasu ba,sai kanshi dake saye da p_cap fara mai adon baqi a jiki,wadda ya jawota ne sosai tarufe fiye da rabin fuskarsa dake duqe kacokam kan farar laptop dake saman cinyarsa,yana latsata a nutse da hannunsa dake dare da baqin agogo rolex na fata wanda yazauna sosai a hannun nashi.
       Saboda shi abokan nashi suka shirya wannan fitar bisa amincewarsa bayan ya tabbatar da tsarkin wajen,amma idan kaga yadda yayi shakulaton bangaro da hirar tasu saika zaci shidin bare ne a cikinsu ba tare suke ba,duk da irin shewa da suke bugawa irin ta zaratan samari da jini ke yawo a jikinsu,hakanan duniya ke gara musu yadda ya kamata.
      Suma basu wani damu ba,tunda idan da sabo sun saba da halayyar azeez,ba kasafai zaka sameshi yana hira ba,ba qaramar sa’a ka taka ba duk sanda kuwa ka sameshi yana hirar,ba kowacce irin hira ke burgeshi ba,hakanan ba’a kowanne yanayi yake zama ya bata lokacinsa wajen yin hirar ba,koda yazauna a cikinsu zaka sameshi da waya ko tab a hannu yana wani abun daya shafeshi.
        Iska da yanayin gurin daya mishi ma shine yazaunar dashi har tsahon wannan lokacin,baya ga haka da saidai kawai su taddashi gida yawuce abinsa.
        A sannan wata budurwa ta iso,duk da cewa shigar doguwar riga tayi amma kuma hakan bai hana wasu daga sassan jikinta fitowa ba,yalolon mayafin data yafa dinma iyakarsa wuya,qafarta sanye da hill shoes,kallo daya zaka mata ka bata sunan ‘YAR DUNIYA,saboda dukka yanayinta ya nuna hakan.
        Kai tsaye gaban kamal ta tsaya,cikin nuna tsantsar rashin kunya da rashin tarbiyya tadubeshi
“Ka gama guje gujen naka?” Saiya dubi sashen da azeez yake,saidai da alama baima kosan da zuwan nata ba,baya fatan yasan da zuwan nata,don har yau kusan idanun azeez na kanshi,kuma sharudan daya gindaya masa suna nan,duk da yayi niyyar bijirewa amma mommynsa tace yayi haquri ya karba haka,suci gaba da zama tare,saboda akwai wani target nasu kan azeez din,matuqar yabari misunderstanding yasake shiga tsakaninsu to target dinsu zai samu matsala
“Pls lisma,kije zan sameki a gida,ko wani wajen” zare glasses din idanunta tayi tana cuna baki
“Baka isa kasake yaudarata ba ai,kayi na farko kuma kayi na qarshe,bari na gaya maka kamal,ni gaba nake dakai na rantse da Allah akan bariki da iskanci” tafada tana dan daga murya da alama temper dinta tasoma hawa.
      Ganin haka cikin wadanda suka san tsakaninsu da lisma din suka soma bata baki,gamida lallabarta taje din kamar yadda yace,sun mata alqawari zai sameta kamar yadda yace.
        Kusan duk abinda ake a kunneshi amma saika rantse baya wajen,ko baisan da zuwan nata ba,yana sauraren komai,yana tunanin ba sabgarsa bace ko abinda yashafeshi,hasalima yana ganin zubewar qimarsa ce kamarshi ya tsaya wani maida magana ta hadashi da watsatstsun ‘ya’ya irin wadan nan,saidai kalaman data sake fada suka ja hankalinsa harta daga kai yana dubanta fushinsa yanason motsawa
“Ku rabu dani naci uwa da uban dan iska,maqaryaci macuci mayaudari kuma maha’inci,jinin asara haihuwar iska” idanunsa ya lumshe na wasu sakanni kana yabudesu,yamiqe cak yana aje laptop dinshi daga inda yatashin yana kuma qoqarin controlling anger dinsa kafin ya isa gareta,saidai hakan bata samu ba saboda maganganun data ci gaba da fadi.
       “Getout of there!” Yafada cikin wata kakkausar murya data ja hankalinsu dukka harda masu bata haqurin,waiwayowa tayi tana neman wanda ya bata wannan umarnin kai tsaye kamar ubanta ta yagashi shima,saidai suna hada ido saqon ya isa qwaqwalwarta,wannan ba kalar wanda ake iya yagawa bane,kwarjininsa kadai yana karya lagon koma waye kai,maimakon magana saita maida glasses dinta ta rabashi sum sum tawuce daga wajen bayan ta kalli kamal taja masa qwafa alamun zancan bai mutu ba.
       Idanunsa qur bisa kamal wanda kallon yariman ya rudashi,baison yadda yake zubawa mara gaskiya idanu haka,ran azeez ke tafasa sosai,saboda yanajin xagin datawa kamal din kamar da familynsu gaba daya take,kusan laifin kamal yafi nata yawa a wajensa,tunda yasan cewa idan babu qira meye zaici gawayi?,idan bai kulata ba ina taga fuska da qwarin gwiwar zuwa ta tsaya haka a gabanshi tana gaya masa wadan nan muggan kalaman.
       Akwai magana da yawa a bakinsa,amma saidai baison yace komai da zai tozartashi cikin bainar jama’a masu yawa,tunda dai jininsa ne,hakanan bugu da qari ammi ta masa magana kan yadinga controlling fushinsa akan kamal,tunda dan uwanshine,uwa uba kuma akwai ‘yar tsama sosai tsakaninta da momi mahaifiyarshi,so kada tadinga ganin kamar ita ke sanya azeez din yana yiwa kamal din wasu abubuwan.
       ƙoƙari yayi yasoma hadiyr fushinsa,harya isa inda ya aje system dinsa ya dauketa yakashe sannan yasoma takawa don ficewa a wajen,tunda sukaga hakan sunsan tafiya zaiyi,don haka babu wanda ya tsaidashi.
       Yana gab da ficewar wayarshi tadauki tsuwwa,daya duba yaga ammi ce saiya qi dagawa,harsai daya isa motarshi yabude yazauna asit dinsa kana yabi kiran nata.
      “Kana lafiya ko?,jiya banga kiranka ba”
“Lafiya qalau ammi,jiya duka wayar tawa a kashe take,muna da test ne,dana gama karatu sai kawai nabarta a kashe saida muka fito,sanda muka fito kuma dare yayi anan babu damar kira”
“To ma sha Allah….kan maganar nan ta aurenka…..yanzu haka nasa an samo maka yarinyar,ina tunanin cikin satin nan zan turo maka ita ka ganta,idan tayi maka shikenan,inaso ne ayi komai a gama within two to three weaks”.
      Dayaji ta bagarar da zancan tun wancan lokacin ya zaci tabar maganar ne,sam ya manta shaf da batun,don har yashiga sabgoginsa,bashi data cewa kuma bashi da damar musu,tunda yasakar mata ragamar komai kuma tayi din bai isa ya canza ba,cewarsa a’ah kamar ya taso da wani case ko wata matsalar ne tsakaninsa da ammin,gwara ya amsa koda baiso,koda babu abinda zata amfana masa,amma ko daya baya da buqatar zuwan yarinyar,koma ya take ba matsalarshi bace shi
“No ammi….basai tazo ba,kawai ku qyaleta” sai tadan bata fuska kamar yana gabanta kana tace
“Kamar yaya?,dama an taba aure ba tare da anga juna ba?” Shuru yadanyi na wasu daqiqu sannan yace
“Ba wani matsala bace,itadinma bata ganni ba tace ta amince” kai ta girgiza
“Akwao banbamci tsakaninka da ita,saidai kuma idan akwai wani abu daka shirya kake kuma boyemin….ko kuma kana da wadda kake da muradi daban da kakeso ayi hadin da ita” shima kai ya girgiza kamar tana wajen
“Ba haka bane ammi,indai ke tayi miki nima na tabbata zatayimin,sannan bawai abu bane na dindin ba bare ace ana buqatar dogon nazari ko zabe,it was just like a game…babu damuwa” sai datayi shuru sa’an nan tace
“Is ohk,amma zan amshi koda pic dinta ne na maka sending ta email dinka saika duba” bayason yafiya mata musu,saboda tana da wani girma da daraja a idanunsa,hakanan tafi qarfin komai kamar yadda tafi gaban komai,don haka yace
“Alright ammi,na gode” ƙaramin murmushi tasaki
“Anything for you” tafadi,daga haka suka kashe wayoyinsu.
      Sauke wayar yayi daga kunnenshi yana sauke ajiyar zuciya,kana ya waiwaya yana duban almustapha daya shigo motar sanda yake gab da gama wayarshi,mutum nabiyu rak a rayuwarsa da yasan abinda yake gudana,saidai shidin bai bayyana masa cewa shekara daya ne rak zaman nasu ba,tun kafin mustapha yayi magana azeez yarigashi
“She prepared anything” murmushi yayi yana dukan kafadarsa
“Dan gata” ganin yanason maida maganar wasa saiya saki qaramin tsaki yana fitowa daga sit dinsa ya zagaya zuwa inda mustaphan ke zaune yabude murfin motar yana cewa
“Kaimu gida da Allah” yana dariya mustaphan yafito saukayi exchanging seat,ya tada motar suka fice daga gurin,yayin da azeez yayi relax a kujerar motar kawai yanason yayi emptying qwaqwalwarsa daga kowanne irin tunani.
    Wani irin farinciki ne yake ratsashi tun sanda umma luba ta gama gabatar da saqon fulani aisha,bakinsa ya kasa rufuwa,lallai arxiqin daya dade yana mafarkin samu yanxu yasameshi,maganar hausawa gaskiya ce da sukance DARE ƊAYA ALLAH KANYI BATURE,yaushi malam bilya akewa albishiri din cewa za’a rushe gidanshi yazabi kalar irin ginin da yakeso ayi masa,yakuma zabi sana’ar da yake da sha’awar yi,hakanan yazabi irin motar da yakeso yadinga hawa,rawa ne kawai bai taka ba gaban umma luban,amma koda tatafi bai iya daurewa ba sai daya taka din,mama ladi tana tayashi,cikin ranta tana godewa Allah daya sanya batayi gaggawar barin gidan ba,ashe da ita za’aci arziqi,sai daya gama sa’an nan yasoma tambayar mama ladin
“Ina mai gadon take ne,kiramin ita na shaida mata tashirya,sati uku ya rage mata a gidan nan”
“Anya ko tana cikin gidan nan,tun sassafe naji karakainarta da yara tana shirin fita makaranta” idanu ya fidda waje
“Ai bataji ba kenan?,bata yarda da hanata zuwa makarantar da nayi ba?,zamu gamu,nida itane,har makarantar zanje yanzu kuwa” ya fada yana shura takalmansa yafice daga gidan cikin hanzari zuwa makarantar tasu,don yanajin kamar bilkisun nason jawo masa wata asara ce dashi kuma bazai iya jurarta ba.
      Kwanakin gaba daya tunda take zuwa makarantar kusan babu abinda take tsinanawa banda kwanciya,koda yaushe zaka sameta kife da fuskarta saman tebur,tashin hankalin da take ji yana fuskanto rayuwarta jikinta ya bata ba qarami bane,ta yaya ya akayi mahaifinta ya aminta da wannan bahagon tunanin?,me yasa ya amincewa wannan wasan yaran saboda dukiya kawai?.
     Hakanan tasamu kanta da yawan duban sashen da bilkisun ke zaune,duk da bamai yawan magana bace amma koda tana zaune ne shuru to zaka sameta da littafi a gabanta tana dubawa,koda ba zatayi hira da kowa ba,duk da basa shiri,babu wata magana mai dadi dake hadasu,amma saita tsinci kanta da rashin jin dadin sauyawar bilkisu,ko ba komai a baya sukanyi compatition a aji wajen bada amsa a subjects da dama idan malami yayi tambaya,sukanyi rige rigen miqa classwork tsakanin ita da ita,duk da talura badon ita bilkisun takeyi ba,amma rashin ganin hakan kwana biyu duka sai taji babu dadi.
      Kasa shuru tayi ganin kusan awa guda bata motsa daga yadda take ba,ta tabo hanan dake gefanta
“Wai meke damun bilkisu kwana biyu” cikin mamaki hanan tadubi afnan din,don tunda suke bata taba jin takirayi sunanta ba saboda takun saqarsu,kai ta girgiza
“Oho mata,waya sanmata ne” idanunta kan bilkisun dake duqe saman benci
“Kamar tana cikin damuwa” sake daga kai hanan tayi daga kwafar note din da take ta dubeta
“Meye damuwarki a ciki ke idan hakanne” kafada ta daga
“Nima ban sani ba” daga haka tabar zancan,saidai batasan me yasa idanunta suka kasa sauka daga nahiyar da take ba,har zuwa lokacin da aka aiko kiran bilkisun daga office din principal.
     Tayi mamakin kiran,don tunda take bata taba yin wani laifi ba cikin makarantar ballantana tace ko wani abun tayi akeson ganinta,hakanan tamiqe tana gyara hijabinta cikin kasala da mutuwar jiki taja qafafunta tafice.
       Ba jimawa afra tafita fitsari,sai gata tadawo tana qunshe dariya,hanan ta dubeta
“Lafiyarki ke kuma?”
“Wallahi wani abun tausayi nagani kuma abun dariya,mutuniyar billy ana can ana sharbar kuka a office din principal,babanta yazo yacireta daga makaranta,aure zai mata,aurenma na dole,ke kinga baban nata kuwa?,kamar wani mai tallan agwaluma,ke wallahi me yanke flowers din gidanmu yafishi kyan gani,kuma kina gani kinsan babanta ne wallahi” dariya duka wadanda ke role din suka fashe dashi,ga mamakinsu afnan kallonsu kawai tayi ba tare datace komai ba,tausayin bilkisun taji ya saukar mata,ashe da gaske ne ita din ba diyar kowa bace?,ashe abinda yake damunta kenan cikin kwanakin nan?,shiko me yasa zai cireta daga makaranta,duk qoqarinta da himmarta nazuwa makaranta,kaf ajinsu itace take daukan na daya kowanne tearm,afnan din ke mara mata baya ata biyu,ko ya gaji da biyan kudin makarantar tasune?,tunda a yadda afra ta siffantashi tabbas ba qaramin namiji bane mai irin wannan qaramin qarfin dazai iya biyan kudin makarantarsu
“Wai bakiji mutuniyarki bane?” Hanan ta tabo afnan tana fada dariya tana cinta,wani kallo tayi mata sannan tace
“Naji mana,amma banga abun dariyar bane,tunda dai macace ‘yaruwarmu,muma xamu iya fadawa irin qaddararta” shuru kowannensu yayi da mamaki suna duban afanan din
“Kuna mamakine?,bilkisu bata taba yi mana laifin komai ba,inda ace za’a titsiyemu da bulala ace mu fadi abinda ta taba yi mana duk cikinmu babu mai amsa,saimu da muke cusguna mata ma amma bata taba tsayawa ta biye mana ba….”
       Shigowar bilkisun ajin yakatse sauran maganar tata,kallo daya zaka mata kasan tasha kuka bana kadan ba,tawuce seat dinta tazauna gamida maida kanta yadda yake dazun.
       Har duka periods din suka qare aka tashi daga makarantar bata dago kanta ba,saida kusan kowa a ajin yafice yabarta kana ta hada jakarta da qyar tawuce itama.
      Duk da uwar ranar da ake qwalawa ko kadan zafinta bai dameta ba,qunci da baqincikin dake cikin zuciyarta yafi ranar zafi da quna a gangar jiki da zuciyarta,da mahaifinta za’a gama hannu a tarwatsa rayuwarta?,wadanne irin azzaluman masu sarautane su?,wadanda basu damu da buqatar kowa ba saita qashin kansu,dama duka qarya ce da shaci fadin mutane da suke cewa
“Masarautar kaisa badai adalci ba,dukka mai neman adalci to kansa tsaye yanufeta” gashi ita yau adalcin take nema xalla daga garesu amma sun gaza dubanta,indai da gaske ne daga masarautar kaisa akeson shirya mata wannan abun,indai da gaske ne afnan jinin masarautar kaisa ce iya dabi’u da halayenta kawai sun isa su gaya mata cewa lallai sudin mutane ne masu dagawa zalunci da takura,inama ace wanda yamutu yana dawowa yau ummanta tazo taga halin data tafi tabarta a ciki,inama ace wanda yayi nisa yanajin kira anty zuhriyya tazo taga yanayin datake shirin afkawa ta tsamota,tasamo mata adalci da nutsuwar ruhi.
     Tafiya kawai take ba tare da tasan inda take jefa qafarta ba,bata ankara ba tajita tsamo tsamo cikin wani ruwa,sai a sannan ta maida hankalinta,ta duba dakyau sai taga ashe kwatace,dai dai sanda motar dake dauke da afanan take dosowa wajen.
      Tun daga nesa taga kamar bilkisun,a hankali ta bada umarnin ya gangara gefan titin,tana tsaiwa motar tabude murfin da kanta kana tafito tana qarasowa inda bilkisun ke tsamo qafafunta tana son ci gaba da tafiya ba tare data damu da tsaiwa tayi ratse koda a fanfunan gefan hanya bane ta gyara jikinta.
      Riqotan da akayi ya sanyata tsaiwa
“Bilkisu bilyamin” taji an furta a hankali,yadda aka kira sunan yasanya tagene daya daga cikin ‘yan makaranta ko ajinsune,saita waiwaya don taga waye,mamaki ya cikaya ganin afnan abdallah mu’az kaisa tsaye tana dubanta cikin alhini da mamaki
“Ya akayi kika fada kwata bilkisu,me yasa bakihau mota kin koma gida ba bayan baki da lafiya” kai ta kada
“Ba komai,yanzu zan isa gida” tasan ta fadane kawai,amma ko ba’a gaya mata ba tasan akwai tazara tsakanin unguwarsu da unguwar da makarantar tasu take
“Ki tsaya ki wanke jikinki,karki dinga tafiya ana kallonki” bata tsaya jin amsar bilkisun ba tayi magana daga cikin motar,saiga drivern yafito cikin hanzari hannunsa dauke da ruwan roba manya guda biyu.
     Baki tasake yadda taga afnan din ta balle ruwan roban takama gefan unifoarm din nata cikin rashin damuwa tana tittilewa a jiki tana wanke ruwan kwatar,saita kai hannu da sauri ta riqeta
“Zubamin zan wanke dakaina” murmushi ta sakar mata,bata musa din ba taci gaba da xuba matan tana wankewa,lokaci lokaci tana satar kallon bilkisun,harga Allah tausayi take bata,ta tsani kalmar auren dole,koda a littafine take karantawa tota aje littafin kenan,saboda bata manta dauki ba dadin da aka dinga yi cikin gidansu ba lokacin da maimartaba yaso baiwa arifa yayarta tabiyu wani ba,yadda arifan tashiga tashin hankali qwarai harsu kansu saida suka tayata shiga damuwa,daga baya dai Allah ya warware da yake wani baya auren matar wani.
     Tas tawanke,ta kama inda zai matsu ta matse kana ta yarfe
“Na gode” tafada a sanyaye tana duban afnan,tare da mamakin meya sauyata haka?,don ko amafarkinta bata taba tsammanin afnan din nada tausayi da sauqin kai ba
“Ba komai,kishiga mota saimu saukeki a hanya” motar takalla kana ta kalli afnan,tana qoqarin hadiye wani abu dake taso mata,hala afnan tana cikin masarautar kaisa ne amma batasan dukkan abinda ke faruwa ba,da zata iya data gaya mata cewa a yanzun ta tsani dukkan wani abu daya shafi masarautarsu,saidai ko Allah ma yace kada laifin wasu mutane yasa ka kasa yi musu adalci,babu ruwan afnan cikin batun,don ga alamu sun suna batasan ma meke faruwa ba,wala’alla data sani ko kallon tsiya ba zata mata ba bare na arziqi,a yadda suke da ita abaya na rashin jituwa a tsakaninsu
“Ki barshi,zan iya qarasawa ai,kada na bata muku mota da danshi,kinga a jiqe nake,na gode sosai” saita soma takawa,tausayinta takeji sosai,ba zata iya barinta tawuce ba,saitasha gabanta
“Don girman Allah kishigo mu saukeki,bakyau maida alkhairi” ta kashe mata jiki,tilas tabita tabude mata murfin motar,sai data soma shiga sannan itama afnan din tashiga.
      Wani sassanyan sanyi ne yasoma ratsa kowanne loko da saqo na jikin bilkisu yana busar da gumin da ada ta hada saboda tafiya a zafin rana data soma,sanyin da rabonta data jisa tun lokaci anty zuhriyya na rayuwa a kusa da ita,duk da yanayin da take ciki sanyin ya mata dadi,saita lumshe idanunta kawai tana jin yadda motar ke tafiya wani suuuuu kamar ba saman kwalta suke tafiya ba,kai kace a iska ko a sama suke tafiya.
      “Kiyi haquri xan miki shishshigi bilkisu,duk da ina zaune aka gayamin,ban sani ba gaske ne koba gaske bane,amma indai da gaskene auren da bakiso za’a miki,kizo na kaiki wajen abbana,na tabbatar da cewa zai hana faruwar hakan,don tun daga cikin gidansa zuwa al’ummar qasarsa ya haramta auren dole tun daga kan yayata arifa” idanunta tabude akan afnan,ashe haifaffiyar sarkin kaisa din ce ita,hakan na nufin ita din ‘yaruwa ce ga yarima wanda akeson bata?,uwa daya ko uba daya ko uwa daya uba daya?,rashin sani yafi dare duhu,batasan daga can zancan yataso ba take da yunqurin kaita don samun adalci,akwai adalci da gaske irin wannan a masarautar amma ya kasa biyowa ta kanta?,waishin ins matsalar take ne?
“Karki damu,babu damuwa,na gode da kulawa” abinda tace mata kenan,don koda ace ba daga gidan tushen matsalarta take ba bazata iya kai mahaifinta qara kan zai aurar da ita ga wani ba komai lalacewar mahaifin nata.
        Basu sauketa a hanya ba kamar yadda da farko afnan ta fada ba sai da suka danganata da bakin layin
“Na gode” tasake maimaitawa tana duban afnan din,itama ita take kallo cikin murmushi tace mata
“Babu komai” koda sukayi gaba da kallo tadinga bin unguwar tasu,tana ganin tarin banbance babance qarara,wane sashe na zuciyarta yana sake cika da tausayin bilkisun,da kuma ganin kuskurenta qarara na sanya ‘yar tsama ga innocent mutum kamar bilkisun,wadda bata taba taka mata ba bare ta zubar mata.
**************
     Cikin irin kebantattun lokutta da take warewa ne domin iyalinta,tana zaune a falonta na musamman,sanye take da doguwar riga mai hade da hula na wani irin yadi mai sulbi da taushi,afnan ce kanta saman cinyarta,hannunta riqe da wayarta,saidai hankalinta bai kan wayar tata gaba daya,ta ta’allaqashi ne wajen bawa amminta labarin bilkisu,da abinda ta fuskanta daga rayuwarta duk da bata taba bude baki anyi magana makamanciyar haka da ita ba,har sai da fulani aysha ta soma gajiya dajin labarukan autar tata afnan tace da ita
“Baki da sauran abunyi mata ai afnan,tunda tace babu komai tagode” cikin shagwaba irin ta wadanda suke auta a wajen iyayensu tace
“Toni ammi tausayi take bani wallahi,da bama shiri amma yanxu tausayinta nake”
“Ai shikenan,saikiyitayi,daga min cinya hakanan na huta” tana dagawar jakadiya tayi sallama bakin qofar falon tana jiran abata izini tashigo,saita dubi afnan
“Idan kin fita ki mata ixini” amsawa tayi dato tana gyara yafen mayafinta,kana ta wuce jakadiya kuma tashigo.
      “Allah yabaki yawan rai….an shaidawa ubabatu kuna son ganinta,gata kuma ta iso”
“Anyi mata izini tashigo”
“An gama Allah ya taimakeki” daga haka tajuya tafice,cikin qiftawa da bismillah umma luba ta bayyana cikin falon.
      Babu jinkiri fulani aisha tasoma zayyana mata dalilin kiran
“Da farko munason ki shaida musu a sanda zasu tashi zuwa gidan zama nawucin gadi kafin a kammala musu ginin gidansu kafin lokacin da za’a daura auren….zamu dauketa zuwa gidan da za’a kebeta…inason ayi mata horo na musamman,ayi mata gyara na amare na musamman irin gyaran da aka jima ba’a yiwa wata diya ba,duk da cewa xabinmu ce zuwa wani lokaci amma ko babu komai zatayi tarayya da jininmu ne,sabida haka inason a sauyata amantar da ita wacece ita,a dabi’anceta da dabi’a ta gidan sarauta,halayyarsu yanayin maganarsu da sauransu saboda yarima yaji dadin zama da ita ba tare da yana tuna wani abu na daban ba,ko yaji damuwa cikin ranshi,bayan wannan inason ayi mata training na yadda zata kula kanta,babu buqatar takoyi yadda zata zauna dashi,don iya aikinta kawai zataje tayi,kula da komai nashi yana da masu yi masa shi,bana buqatarma takoya din saboda wasu dalilai nawa dana barwa kaina sani,abu na iko,inason ki shaida musu,su lissafa dukkan adadin dukiyar da sukeso a matsayin dukiyar auren ‘yarsu,ko nawa ne zamu biya,su fadi ko nawa suke da buqata daga nan har zuwa ranar rabuwarsu,bisa sharadin idan an rabun,zasu manta cewa ‘yarsu ta taba auren mai suna abdul’azeez,yariman masarautar kaisa,munason rabuwa tahar abada,ta rayu takuma ci gaba da rayuwa babu shi ko digo cikin tunaninta,wannan shine babban bangare kuma babban sharadi na tafiyar alaqarmu,samun akasin hakan kuma dai dai yake da faruwar kowanne abu….” Saita tsagaita tana maida numfashi
“Wannan sharadin kusan shine abu na farko dana fara shaidawa mahaifinta,yakuma yarda yayi na’am da hakan dari bisa dari” kaita gyada cikin nutsuwa sannan tadora
“Ko a mafarki bama buqatar su hado diyarsu da wani abu,itadin kawai zallarta muke da buqata….abu na qarshe shine,za’a daura aurensu cikin masarautar mali cikin ahalina ba’a qasar kaisa ba,daga nan zamu dauketa zuwa muhallin da zata zauna na tsahon shekara daya,ba zata bar wajen ba harsai sanda kwanakin suka cika”
“Allah yabaki yawan rai an gama,wannan saqo zai isa kunnensu da izinin Allah” kai tasake jinjinawa
“Da kyau,ina da buqatar hotonta wanda zai turawa yarima don yaga irin zabinmu….jibi zata bar gidansu zuwa gidan da muka tanadar mata tazauna,zamu aika da mai hoton can,inason a zaman ya kasance kina daya daga cikin masu kula da ita,har zuwa lokacin da zasu wuce mali,tukuicinki kuma kizauna ki zaba dukkan abinda kikeso a duniyar nan,matuqar mun mallakeshi xamu bakishi”
“Godiya nake Allah ya taimakeki,wannan karamcin naki da bashi da kwatankwanci bakina yayi kadan yayi miki godiya,kalmomin bakina sun qare fulani”. Umma luba ta fada cikin rudewa da zallar farinciki.
      Ƙarfe biyu da rabi na dare ne amma saika tsammaci tsakiyar rana ce tarwai saboda yadda idanunta suke a bushe kuma a soye raqayau,babu digon wani abu mai suna bacci tattare da ita,bata jin koda alamarsa duk kuwa da yadda ya qware wajen iya sata.
      Ji take kamar zata zauce a duk lokacin data tuna kalaman da mahaifinta ya gama rattaba mata daxu bayan sallar isha’i,YA SAIDA ITA,YAYI CINIKINTA wannan itace kalma mafi sauqi daya kamata mahafinta ya gaya mata akan hanyar dayabi ta dogon sharhi kan buqataun masarauta akanta
Jin zantukan nashi take tamkar a shirin film ko kuma a qagaggun labari na hikayoyi,wadan nan sharuddan da dokoki dukkansu sunfi kama dana matar da za’a siyeta a matsayin baiwa ba ‘ya ba,ta ina zata fara?. Ta ina lamarin zai yiwu?. Saita waiwaya tana duban qannenta dake kwance suna bacci ba tare da sunsan gagarumin tashin hankalin dake fuskantarsu ba. Ta ina zata soma barin wadan nan bayin Allahn da yafi kyau a kirasu da marayu?. Ta yaya zasu iya jurewa rashinta?. Wa zata barwa su?. Umma katti?,mama ladi?,koko mahaifinsu da yafi kowa rashin damuwa da rayuwarsu,wanda asanda take masa bayaninsu ma cewa yayi basu da wata damuwa tunda zasu samu sauyin muhalli,zasu kuma samu ci sha da suttura maikyau.
      Wani abu dake mata yawo saman kwanyarta kamar ana mata tafiyar tsutsa haka tadinga ji,ta dinga kaikawo tana tafiya tsakanin qannen nata daga bango zuwa bango na dakin. Ji take kamar ta zura da gudu tabar gidan…tabar qasarma gaba daya,da sauri ta juya tafice daga dakin,saita tsinci kanta tayi hanyar soro tana muradin ficewa.
      Sanda tabude qofar gidan babu abinda yasoma mata maraba sai zallar duhun dare,wanda ya cukudu da haushin karnuka daya cuka anguwar tasu
“Wa kika barwa su?” Daga qasan zuciyarta aka jefa mata tambayar data sanyata tsaiwa cak
“La haula wala quwwata illa billahil aliyyul azim”. Tasamu kanta da furtawa sau babu adadi,wanda wannan ya taka rawa wajen sanyayar jikinta,tamaida qofar ta kulleta kamar yadda take,kana ta janyo qafafunta zuwa cikin gidan.
 
        Maimakon tanufi dakinsu kai tsaye saita durfafi bakin famfonsu gadan gadan,ta kunnashi kana ta duqa gami da tara hannayenta,saita bige da alwala.
      Bata damu da neman abun salla ba,hakanan saman dandaryar sumuntin dakin ta tada sallar,sallar data jata har zuwa lokacin da akayi kiran assalatu,ta bada farali wanda daga wannan bata kuma sanin abinda ke faruwa ba,gwanin iya sata ya saceta duk da yadda take kokawa dashi da nuna mishi nata maraba da ziyararshi.
        A kallon farko zaka san cewa babu wani abu da yayi kama da sukuni tattare da ita,duk wata wulgawar da yaran zasuyi binsu take da kallon zallar tausayi,bata ankata ba tuni mahaifinta yagama gaya musu cewa zai aurar da yaayarsu,wanda hakan yayi masifar dugunzuma hankulansu gaba daya,tana zaune tana saqa da warwara sai ganin yara tayi sun sata a gaba gamida zagayeta,gabanta na faduwa tana fatan ba abinda take hasahe bane ta tambayesu lafiya
“Aure wai zakiyi yaaya inji baaba,kema aure zakiyi ki tafi kibarmu mudaina ganinki yaaya?” Hauwa ce tajefa mata tambayar cikin matuqar mutuwar jiki dakuma saddaqarwa.
      Da idanu ta dinga binsu da kallo dai dai da dai dai,tana jera kalaman da zata gaya musu,saidai yanayin dake saman fuskar kowannensu ya sagar mata da gwiwar kowanne yunquri nata,tausayinsu yasake ninkuwa cikin zuciyarta,qwarin gwiwarta da karsashin data tattaro suka baje,ta rasa abin cewa,sai kawai ta sanya musu kukan data jima tana boyewa,karo na farko a rayuwarta,karon farko data nuna gazawarta a gabansu,abinda komai girman nauyi da tsanani bata taba bari gazawarta ta bayyana koda saman fuskarta ba,saboda tasani itace kadai qwarin gwiwarsu,itace kadai hope dinsu,batason tayi abinda zata kashe musu fata da burinsu da dukka suka aza wuyanta.
Kuka take haiqan irin kukan dake nuna zallar tashin hankali da shiga taskun rayuwa,fuskarta kife a tafin hannun hannatu,yayin da dukka yaran suke kewaye da ita,kowannensu kuka yake kamar yadda yayar tasu take,kai…tama zarta yaya a wajensu,uwa ce kuma ubace gata sannan jigo cikin rayuwarsu.
      A yau din da ake niyyar tsigeta daga cikinsu akaita can wata uwa duniya ji take kamar ana shirye shiryen zare ranta ayi jana’izarta ne,tana hasashen rayuwa babu qannenta,bayan babu wani tartibin hannu da zata barsu,dukka bayanan da mahaifinta yayi mata akansu basu gamsar da ita ba,me jiya tayi ballantana yau,meya tsinanawa rayuwarsu a baya bare a yanzu,ya ilahi me tasa babu wanda yaduba kokenta?,babu wanda yaduba quncinta?,babu wanda ya waiwaya yaduba uzurinta?,kowa yasanya buqatarsa gaba fiye data kowa?,kowa nashi muradin shine a gabansa?.
       Dai dai lokacin data soma jiyo hargagin mahaifinta daga tsakar gidansu wanda yasoma zama filin Allah,saboda tuni akayi nisa wajen rugujeshi,yana zubawa umma katti masifa,wadda a yanzu take tsananin yi masa biyayya da takatsantsan,kan tashiga tafito da maigadon,ubanme takeyi mutane suna jiranta a waje?,kai kace irin amaren nan da ake shirin kaisu gidajen mazajensu a yammacin daurin aurensu.
       Kafadarta umma katti ta dafa cikin tausasa harshe tace
“Haba maigado,kamar zaki barsu hannun bare?,bayan ga mahaifinsu gani da nake kamar uwa a wajensu?,ki kwantar da hankalinki,kamar yaune zakije ki dawo ki samesu lafiya kinji?,don Allah karki tashi hankalinki”. Sai a sannan ta daga rinannun idanuwanta tana kallon umma katti,kallo take mata irin kallon da wanda aka cuta yakewa azzalumi,tsahon xamanta tare da ita zata iya cewa bata taba jin lafazi mai dadi daga bakin umma kattin ba sai a dan tsukinnan da aka fara wannan sabgar,bata daukan zamanta tare dasu a matsayin wami abu mai alfanu,tunda shekarun dukka da suka shude basu canza komai ba,sai yanzu?,amma yata iya,dole tayi magana da ita,cikin muryar dake nuna kuka ya suqeta tace
“Ga amanar Allah nan a hannunki,Allah shine shaida umma”
“Karki damu,qannenki ba zasu tagayyara ba,mu da zamu shiga rayuwar daula da hutu?,rashin abinci da suttura dukka fa zai zame mana tarihine a rayuwarmu” ta qarasa fada tana murmushi da alamu abun yana mata dadi,cikin qunci da takaicin umma kattin tadauke kai daga gareta,dole tayi farinciki tunda tasamu mafita ba tare da an taba martabar nata diyan ko guda daya ba,saita dubi hannatu,ta kama hannunta tariqe tsam hawaye naci gaba da kwaranya
“Hannatu,bayan babu ni kece makwafina….na baki dukka amanar qannenki….ina fata zaki zama jaruma,zaki sanya dukka qarfinki ki tallafesu a yayin da sukayi rauni” kuka tafashe dashi sosai,cikin sheshsheqa tace
“In sha Allahu yayaa,zamuyita miki addu’a Allah yadawo mana dake” saita dauke idanunya daga kan hannatun tamaida kan qannenta,kowanne da abinda ta gaya masa gwargwadon sanin halinsa da tayi,hauwa’u ce tashin hankalinta yafi nakowa,takuma sanyata kuka fiye da wanda tayi a baya,da lafuzzan bakin yarinyar tafice daga gidan ba tare data jira rakiyar da umma katti da mama ladi keta qoqarin yi mata ba,ba tare data jira ba tabude motar da kanta tashiga,kana ta cure waje daya saboda sanyin ac da bala’in da takeji yana gigita rayuwarta,tana sake fashewa da wani kuka mai azabar radadi dacin rai kamar ana yankar zuciyarta ta sake kame jikinta waje daya
“Shikenan yaaya idan kika tafi kema,kinga har yanzu ba’a ga mamata ba,bayan kince ko batazo ba ke zaki kaini gurinta,shikenan kema kin tafi ko yaaya?”.
      Batasan motar tatashi ba bare taji alamun tafiyarta,tunani ne kala kala fal cikin kwanyarta,zuwan abubukar saddiq tatuna,mutum na farko bayan afnan da taga yanuna damuwa qarara saman fuskarta kan yanayin datashiga,fuskarsa ta hango lokacin da babanta ke rattaba mata ya zaba mata miji,biki saura sati biyu,karya sake ganinsa qofar gidansa,data san da zuwan wannan ranar data tsaya ta saurari abubakar,wala’alla ya zame mata garkuwa,da tasan da afkuwar wannan mummunar qaddarar dako amanar qannenta tabari a hannunshi,duk da batasan wayeshi ba,batasan halayyarsa ba,amma hakanan jiki da zuciyarta suke bata gwara shi akan mutanen gidansu,jikinta yake bata zai iya,zai iya kula mata dasu,saidai dukka bakin alqalami ya riga daya bushe babu makawa.
       “Ranki ya dade mun iso” taji ana fada daga gefanta,abinda ya sanyata dago kai kenan cikin mamaki tana duban mai maganar,umma luba ce,saidai wannan karon tana maganar cikin qanqan da kai da wani irin respect,kai kace ubangidane da yaronshi.
      “Duk abinda akace kiyi bakiyi ba,ko kika musa tsahon wannan yarjejeniyar,Allah ya isa tsakanina dake ban yafe miki ba” taji zuciyarta na tuna mata kalaman mahaifinya na qarshe,wanda dasu ya sallameta,wata iriyar dakiya taji tazo mata,wai meye yaragewa saura a rayuwarta?,tabarsu kawai,tazuba musu idanu koma me zasuyi suyi,idan sunso su rabata da ranta.
        Cikin mutuwar jiki ta zuro qafafunta tasauko daga motar,sai kuma ta tsaya cak tana duban gidan,tsoro yana son shigarta.
     Wani irin qawataccen gida mai cike da ni’imar dake bayyana kanta tun daga farfajiyar gidan ba tare da kakai ga shiga cikin gidan ba,tasan cewa sanda suka baro gidansu rana ce tarwai mai zafi a sararin subhana,amma ga mamakinta gidan babu alamun rana tattare dashi,sai wata irin iska mai dadi dake kadawa,ko ina luf luf yake,kamar ka shiga wata qasaitacciyar gona,tafiyar da sukayi daga gidansu zuwa nan din a qiyasinta bazai wuce tafiyar awa daya ba bare tace kafin su isone yammaci lis tayi
“Ga hanyar da zamu shiga cikin gidan nan,ki kwantar da hankalinki,tun daga nan zaki gane kin soma samun sauyin rayuwa” umma luban ce dai tasake fada cikin taushi tana nuna mata hanya,ala wadai da sauyin rayuwa irin wannan,sauyin rayuwar da zai doraka bisa wani SIRADI da bakasan qarshensa ba,sauyin rayuwar da zai sanya asiyeta tataho bauta kwatankwacin yadda ake cinikin bayi ada,wanda banbancinsa da wancan kadanne,sauyin rayuwar daxai binne dukka wani buri nata,ya rabata da ‘yan uwanta,ya katse mata karatunta,ita kuwa me zatayi da wannan sauyin?,dukka wadan nan maganganun tana yinsu ne a lokacin da suke takawa zuwa hanyar da zata sadasu da falon gidan.
       Tun daga falon ta fahimci lallai akwai banbanci mai tarin yawa da sauyi da rayuwarta ke fuskanta,makeken falone wanda yake dauke da dukka abubuwan more rayuwa,saidai bata da nutsuwar xama ta kalli wani abu,a qalla ta tadda ma’aikata nata kawai kusan guda biyar,suna shiga suka soma zubewa cikin girmamawa suna gaidata,bata iya amsawa ba saboda abu uku,baqinciki haushi da takaici,abun sam bai burgeta ba ko kadan,umma luba bata barta anan ba sai data danganata da wani hamshaqin daki daya amsa sunansa,dakine da iya kallonshi ma wata ni’imace ta daban bare kasancewa a cikinsa,ko daya bai bata sha’awa ba duk da yadda aka tsarashi,aka kuma qawatashi,saita zabi zama qasan dakin tana ririta zuciyarta gamida wassafa yadda rayuwarta zataci gaba da gudana cikin wannan dakin.
       Azahar tanayi umma luba ta gabatar mata da abinci har cikin dakin ba tare data nemi ta fito muhallin da aka tanada ba saboda cin abinci dake falon.
       Wata iriyar lafiyayyar shinkafa ce da kaza da hadin salad,sai farfesun nama dana kifi kala daban daban,bayan nau’ikan lemuka,ko a idanu abincin yafi qarfin cikin mutum daya,amma dukka aka jere saboda ita daya,ko kadan abincin bai burgeta ba bare ya bata sha’awa,a sannan tunaninta shine,su hannatu sunci abinci?,idan sunci me sukaci?,waye yabasu?,waye yakula dasu?,sai wani kukan ya balle mata,a maimakon cin abinci saita sanya kanta tsakanin qafafuwanta taci gaba da rerashi.
        Sosai umma luba tazauna tana bata baki gamida lallashi dason shawo kanta,ko daya batason ganinta kojin kalaman bakinta,don kusan itadin itace ummul aba’isin fadawarta kowacce musiba a rayuwa,banda ta zabeta…banda tazo har gida ta shaidawa mahaifnta….takuma yi masa romon bakan abinda zai samu….da tuni iyanzu tana csn cikin qannenta,duk da rayuwarsu babu wadata sai fatara qunci talauci da yunwa,amma tanajin tafiye mata sau dubu fuye da wannan rayuwar da batama soma fuskantarta ba,rayuwar da akayi cinikin ‘yancinka na wasu watanni aka miqaka ga hannun wasu.
       Ganin cewa umma lubar ba zatayi shuru ba saita miqe kawai ta durfafi inda ta nuna mata dazu bayan sun shigo a matsayin bandaki,tatura tashige kana ta maida qofar tarufe,saita samu gefan bathtube tazauna ta dora daga inda ta tsaya,sai datayi mai isarta,taji ta rage wani nauyi sosai daga qirjinta sannan ta dubi agogon data lura dashi cikin bandakin tun shigowarta,lokacin sallar azahar yayi harma yadan gota,don haka tazarce da daura alwala kana tafito.
       Sanda tafito babu kowa cikin dakin,da alana tagaji da jira tafita,saita kintaci gabas kawai ta tayar da sallarta,ko bayan ta idar dinma bata kallo sashen da abincin yake ba,haka taci gaba da zamanta tunani kuma ya qulla qawance da ita.
     Ƙarfe biyar da ‘yan mintuna na yammaci taji an dan taba qofar,tsahon sakanni batace komai ba tana duban qofar,sai taji an turo an shigo,baquwar fuska ce da bata santa ba,hannunta riqe da wani abu,cikin girmamawa ta rusunar da kanta tana cewa
“Ranki ya dade,mai gyaran jiki ce ta iso,tace a shaida miki,daga wajen fulani take” jim tayi kamar ba zata amsa ba,saidai ko bata amsa din ba babu abinda zaya canza,don haka saita miqe kawai tana gyara hijabinta wanda tun daga gida ta taho dashi
“Ammm….afwa ranki ya dade,ga wadan nan kayan,su zaki canza kafin kifita” wani kallo ta watsa mata kana tawuceta tana shirin ficewa,saboda tsabar wulaqanci suturar da tazo da ita daga gidan uban nata ma sai an rabata da ita saboda tsabar raini,da sauri tace
“Ranki yadade kiyi haquri ki canxa,fitarki a haka zai janyomin matsala,ki taimakeni” tsaiwa tayi tana dubanta,yadda ta marairaice mata ya tabbatar mata da iya gaskiyarta ta fada mata,sai taji tausayinta ya tsarga mata,wala’alla itama bata da iko da kanta sai abinda aka bata umarni,saita dawo da baya ta amshi kayan daga hannunta,ganin haka yasanyata juyawa tafita daga waje don ta bata damar canzawar.
      Saman gado tazube kayan kana tasoma daddagasu da ɗai ɗai da ɗai ɗai tana qare musu kallo,ko ba’a gaya mata ba tasan cewa kayane masu daraja da tsadane,wani santsi da sulbi suke,doguwar riga ce mai wani irin wadataccen mayafi,haka ta ware kayan ta sanya ba tare data damu da kyansu ko tsadarsu ba,kawai zatayine saboda matar kada ta gamu da matsala kamar yadda ta nemi alfarma a wajenta.
      Wani kebantaccen dakine na musamman ta taras da matar zube ita da kayan aikinta,kana gani kasan ta kusamman ce,kuma takanas aka daukota saboda aikin,dukkan abinda ake bilkisu idanune nata,tsahon awanni biyu cas tuni an soma fidda ainihin kyan choculet colur skin dinta,an yashe duk wani datti ko gashi dabai dace da saman fata ba,hakanan gashinta tana kallo aka masa ɗai ɗai akayi masa wankan tsarki,duk da cewa shidin bawai datti ne dashi ba,saidai wani samfurin gyara da aka masa yasake masa tsaho santsi dakuma laushi.
***********
     Kwanaki uku kenan tana cikin wannan gidan,wanda dukkan wani nau’in abubuwa na morewa rayuwa babu abinda ba’a aje mata ba,saidai iyakarta dakin sai dakin da ake mata gyaran jikin da babu abinda tafi tsana a duniya sama da yammaci yayi azo wannan hidimar,bata taba yarda ta taka wami wajena gidan na daban ba baya ga wannan dakunan guda biyu,abinci kuwa iyakarta na safe sai kuwa na dare,kowanne tsakurarsa kawai take abisa dole badon son ranta ba,gadon dake dakin kuwa iyakarta dashi kallo,ko sau daya bata taba kwatanta kwana akanta ba,yan uwanta ne tsaye a ranya fiye da komai,hatta da makarantarta yadda ta qwallafa rai tariga daga sallama amma tunanin qannenta bai bar ranta ba,kwanakin ajere ana mata wannan hidimar ta gyaran jiki,cikin jikinta a karan kanta tasan cewa akwai gagarumin sauyi,amma taqi baiwa kanta cikakkiyar damar karantar haka bare har takai ga duba xuwa wannan.
        Ta dade da zubawa sarautar Alla idanu,takuma zama kamar mutum mutumi,saboda tasan cewa tawayenta babu abinda zai qareta dashi,kanayin tawaye ne a inda kasan kana da abin fada kana kuma da gata sa’annan za’a daga kai a dubi buqatarka.
***************
     Wasu irin kalolin fitilune ke kamawa da kashe kasu  a qaramar harabar da aka qawata kawai saboda daukan hotunam bilkisu da za’a turawa yarima azeez,daga gefe tana zaune saman wata qawatacciyar kujera,ba kujerar bace abar kallo,kwalliyar da aka mata mai kyau sanyi da kuma tsari shine abun kallon,ga dukkan wanda yasan bilkisun kace ya kalleta tayi sharhi guda daya tak zai gaya maka cewa
“Ban taba sanin haka bilkisu keda kyau irin nayau ba,ashe choculet fatarta ba qaramar baiwa bace dakuma qarin sirri cikin kyanta”.
(21)
      Wasu irin kayane dake nuna alfarmar masu alfarma a jikinta,suke kuma nuna mulki da qasaitar dukkan masarautar da suka fito daga cikinta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *