MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 9 Na Samira Harouna

 MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 9

Na Samira Harouna


👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

        *MATAR MUTUM*

            _(K’abarinsa)_

👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

                   *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

       *SADAUKARWA*

                   

               _GA DUKA_

     *’YAN AMANA TA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_🤝

  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ 

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

                    *33*

Da girmamawa Asma’u ta sunkuyar da kanta ta rusuna sosai tace “Ina kwana.”

Da sauri Ashraf ya rik’e hannunta wanda yin hakan ya haifar mata da wani fad’uwar gaba da kuma tashin tsigar jiki, kallonta yayi cike da gargad’i cikin rad’a yace “Baya amsa gaisuwar ina kwana ko ina wuni, sallama kawai.”

Wasu yawu ta had’e sannan ta kalleshi, sai taga kamar ma bai san da zamansu ba kan shi a k’asa kamar yana wani tunani, zaman Hajia akan kujera ne yasa shi saurin d’aga kanshi ya kalli inda suke zaune, shiru yayi bai ce komai ba har saida ya tabbatar sun gaisa.

D’aga kan shi ya sake yi ya kalli Asas cikin wata tsumamiyar murya yace “Ashraf, zan iya sanin dalilin da yasa tunda aka d’aura aurenka baka zo ka ga Hajia ba sannan baka d’aga kiranta?”

Rarraba ido Asas ya fara yi yana kallon Hajia da sigar “Ki rarrashe shi dan Allah, ba zan iya da masifarsa ba a halin da nake ciki.”

D’auke kai Hajia tayi kamar bata fahimci me kallonshi yake nufi ba, sunkuyar da kai yayi sosai yace “Kuyi hak’uri dan Allah, ina cikin damuwa ne shiyasa.”

A tsawace kuma a hassale yace “Damuwa? Asas wace irin banzar damuwa ce ta gidan duniya da zata sa ka manta da mahaifiyarka? Har ita ta nemeka a waya  amma ka k’i d’aga kiranta, kasan girman laifinka kuwa?”

Wani wawan tsaki ya ja ya juyar da kan shi gefe sannan ya ci gaba da fad’in “Shin k’addarar aurenka ce ka kasa d’auka a matsayinka na musulmi? Ko kuma dai *Ryam* dana aura ce har yanzu baka cire a zuciyarka ba? Idan hakane ka fad’a min, yanzun nan a gabanka zan saketa sai ka aura inhar hakan zai sakaka farin ciki.”

Da sauri duk suka kalleshi har da Asma’u dake ganin kwarjininshi, da sauri Asas hankali tashe ya girgiza kai yace “A’a sheikh, wallahi na hak’ura har abada, na rumgumi k’addarata da hannu biyu, kuma insha’Allah zan ci gaba da rik’ewa.”

Wani nauyayyan numfashi ya sauke a sanyaye yace “Daga mu mazan har matan ya kamata mu d’auki wannan auren a matsayin k’addararmu, dukanmu babu wanda yayi hasashen hakan zai faru, babu wani mahaluki daya zauna ya tsara hakan, yin ubangiji ne, haka ya so ya kasance, shin da wace ni’ima ce muke k’aryatawa? Ikonshi ya fi gaban wasan bawa, komai yahudancin mutum idan mu’ujizarshi ta faru dole ya kan karya zuciya, saidai kawai mutum ya k’i gaskiya amma fa ya tgidanmu akan k’arya yake. Mu musulmi ne Ashraf da muka yarda a jerin rukunan imani guda shida akwai yarda da k’addara mai kyau ko marar kyau, tunda muka amsa sunan musulmi mu yarda da duk jarabawar da zata samemu, ko kana so ko baka so dole ta zo, ta maka dad’i ko bata maka dad’i ba dole a jarabceka, saidai fa mu sani duk jarabawar da za’a wa mumini matuk’ar yayi imani kuma yayi hak’uri, to yana da sakamako mai tsoka. Yanzu wane gata ne ya fi wannan? Wane addini ne ya zo da irin wannan alkairan ga mabiyansa? Zazzab’i zakayi mai mugun zafi da zai saka ka fita hayyacinka, amma daga sanda ka kwanta har ka tashi lada ce mala’uku ke rubuta maka na sannan ana kankare zunubanka, da wannan zan rok’eka kayi hak’uri da jarabawarka sannan ka rik’e ‘yar mutane da amana, ban da cin zarafi da halayen mata wato gori, watak’ila yarinyar nan ita ce warakarka da kake yawan fad’a mana.”

Sosai jikinshi yayi sanyi har yana share k’wallar dake taruwar masa, dan gaskiya da ya so yayi sati kafin ya zo gidan nan, sannan Asma’u ya so ya zauna da ita dumkum d’in nan har sanda zata gaji tace sallameni, amma yanzu sai yaji wata sha’awar son zama da ita na shigarshi da kuma kyautata mata. 

A tausashe sheikh ya sake fad’in “Mahaifiyarka da shaid’an ya zigaka har kake ganin ta maka ba daidai ba har da tagomashin hukuntata ta hanyar nesanta kanka da ita, ka bata hak’uri yanzun nan ka kuma nemi yafiyarta, sannan karka sake maimaita min irin wannan kuskuren dan ba zan d’auka ba, uwa daraja ce da ita, kima ce da ita da babu wani abu mai daraja da zamu iya had’awa da ita, munyi sa’a Allah ya bar mana ita, ita muke zuwa mu fad’a ma kukanmu da farin cikinmu, Ashraf kayi sa’a kai ta ka mahaifiyar ma tana raye, ni ina tawa take a yanzu? Nayi imani da zata dawo yanzu a duniyar nan na minti d’aya kawai ta umarceni da na auro biyu akan biyun da nake da a yanzu, wallahi tallahi zanyi dan farin cikinta, ita ta tsaya min na taka matakin da nake kai yanzu, ita ce k’ashin bayana da har na iya zama da d’uwawuna, addu’arta ce har yau take tasiri a gareni, kullum fata da burinta shi ne na zama babban malami kuma babban mutum.”

Wata ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi ya sa bakin hiraminsa ya share k’wallar data tarar masa a gefe, ya d’an jila yana shashek’ar kuka kafin yace “Sanda na fara hawa matakin da take da burin ganin na hau, sai Allah ya karb’i rayuwarta gaba d’aya ta bar duniyar, na d’auki hakan a matsayin jarabawata mafi girma, har yanzu ina kukan rashin mahaifiyata, ina kewarta, ina neman sa war albarka daga bakinta.”

Sake duk’ar da kai yayi dan sosai kukan nan ya ci k’arfinsa, mik’ewa yayi da sauri ya nufi hanyar fita, da kallo suka bishi jikinsu duk a tsume Hajia har da kuka ita ma, da sauri Asas ya taso ya zo kusanta ya zauna k’asa ya rik’e k’afarta yana magiyar “Dan Allah Hajiata, dan girman Allah ki yafe min, Hajia kar na mutu a yau kina hushi da ni, Allah k’onani zaiyi Hajia ki yafe min.”

Rik’e hannunshi tayi tana share k’walla tace “Ba komai Ashraf na yafe maka, ai tun jiya ma sheikh yasa na yafe maka.”

D’ora kanshi yayi a cinyarta yana sauke numfashi yace “Nagode Hajiata, Allah k’ara miki lafiya da nisan kwana.”

“Ameen.” Ta fad’a tana kallon Asma’u da tayi shiru jikinta yayi sanyi ganin sheikh na kuka, da hannu Hajia ta mata alamar ta zo, mik’ewa tayi tana gyara hijabinta ta zauna k’asa ita ma, dafa kanta tayi tace “Allah ya miki albarka Asma’u, kuyi hak’urin zama da junanku kunji.”

A tare suka jinjina kai kafin ta rik’o hannayensu ta had’a wuri d’aya, a take suka kalli junansu sabida yanda ta had’a hannayen nasu, cikin fara’a tace “Zaman lafiyarku shi ne farin ciki na, ku girmama junanku ba tare da tuna ta yanda aurenku ya kasance ba, na tabbata akwai abinda Allah yake nufi da auren na ku, komai k’ank’antar alama a cikin tarayyarku zamu d’auketa mu rik’e a matsayin abinda Allah ya hukunta, dan haka kuyi hak’uri ku tallafi junanku wajen samar da kyakyawan sakamakon da zamuyi nuni da shi.”

Jinjina kai sukayi sosai kafin ta saki hannayensu,  kallon Asma’u tayi tace “Ki shiga ciki k’awarki na nan.”

Da murmushi ta mik’e ta nufi inda Hajiar ta nuna mata, da sallama ta shiga d’akin tana tura k’ofar. Mimi da har lokacin take zaune a k’ofar ban d’akin da sauri ta mik’e jin saallamar Asma’u, bud’ewa tayi ta fito suka hada ido, wani kukan ta fashe da shi tare da tahowa a guje ta rumgume Asma’u tana fad’in “Asma’u mugu ne, ki tafi dani dan Allah ki kaini gidanmu, cire min kayana yayi.”

Cikin tashin hankali da rashin sanin inda zancen ya nufa Asma’u ta d’ago tana fad’in “Ya cire miki kaya? Wanene?”

Cikin turo baki tace “Waccen malamin mana.”

Wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke, kama hannun Mimi tayi suka zauna kan gado, a tsanake ta kalleta tace “Mimi me ya faru? Nasan dai haka kawai sheikh ba zai miki rashin kirkin da har zaki kirasa da mugu ba idan ba ke kika tsokano shi ba.”

Share hawayenta tayi dan zuwan Asma’un yasa duk ta ji babu wannan tsoron da k’uncin, cikin rashin damuwa tace “Ke ni bansan me na masa ba, kawai dai ya hau ni da masifa da tijara.”

D’an guntun tsaki tayi tace “Kinji fa yana malami amma yake fad’in idan iskanci zaiyi a niger zan d’auka shi kad’ai ne ya iya iskanci, hmmm.”

Ta fad’a tana mik’ewa tsaye, da kallo Asma’u ta bita tace “Ai gaskiya ya fad’a miki, mahaddacin Alk’ur’ani masanin sirrin yahudu da nasara kina ganin akwai wani abun ne da zai shige masa duhu?”

Tab’e baki tayi ta d’auki dogon towel d’inta ta d’aura a k’irji sannan ta k’arasa cire rigar gaba d’aya, matsowa tayi kusan Asma’u cikin rad’a tace “Ke har da tab’a min d’uwawu yayi, wallahi ki fad’a masa yayi na k’arshe.”

Dariya Asma’u tayi tace “Ai sadakinsa ya biya, kad’an ma kika gani yarinya kafin ki tare.”

Sake tab’e baki tayi ta shige ban d’akin Asma’u na fad’in “Ke tare da shi fa muke zaki  wani shanya ni a nan?”

Tsayawa tayi ta juyo tare da kallonta tace “Tare kuke? Wani gurin zaku je?”

Girgiza kai tayi tace “Ke bakiyi mamakin gani na ba a yanzu? Jiya ne dama yace sheikh ya ce mu zo nan.”

D’aga mata gira tayi tace “Wani abu ya muku?”

Girgiza kai tayi tana fara’a tace “Nasiha ya mana mai shiga zuciya.”

Yatsina fuska tayi tace “Ki gaishe shi to.” Ta fad’a tana shigewa ban d’aki dan yin wanka, girgiza kai Asma’u tayi ta mik’e tana murmushi ta fita a falon, jiranta ta samu Asas na yi tana zuwa yace “Muje.”

Yanda ya mata magana d sakin fuska sai ya bata mamaki, sallama tayi da Hajia suka fice a gidan, tun a mota ya so kasheta da mamaki sakamakon hannunta daaya rik’o yana matsawa yana sakar mata murmushi, yanda take sunkuyar da kai yasa shi kallonta yace “Wai kunya kike ji? Lallai ma *Naanah* gwara ki daina, dan babu abinda zai hanani yau dai na sa ki amsa sunanki a matsayin *Asma’ul-Husna* matar Ashraf.”

Gabanta ya shiga wani irin lugude yana fad’uwa, sake duk’ar da kai tayi ba tace komai ba sai rawa maa da bakinta ya d’auka, da haka suka k’arasa gida saidai bai sake fita ko ina ba, tare suka wuni kuma sosai suka samu wata irin fahimta da shak’uwa, dan yanda ya fahimceta shi ne ita d’in bata d’auki duniya da zafi ba, duk abinda aka mata ko ta samu zata karb’a da hannu biyu tayi godiya ga sarkin daya nufeta da samun wannan d’in, hakan yasa shi fara jin ta daban a zuciyarshi tare da mata wani kallo na matar aurenshi wacce zai iya yak’i a yanzun dan kare martabarta.

         *Yammacin litinin*

Fitar Hajia yasa Mimi shigewa d’akinta ta kunna wak’a a wayarta, duk da ita d’in ba gwanar rawa bace amma sai gashi ta zage tana tik’ar abarta a d’akin tana kuma gyaran d’akin, dan in kid’a ya kai mata har tsayawa take a gaban madubi ta cashi abarta kafin ta ci gaba da aikin.

Sheikh ma na shigowa gidan da niyyar daya bata sak’onta ya wuce gida, dan litilin d’in yau ta zama mai sauk’i aiki a gareshi a ofishi, dan haka yayi saurin baro ofishin ya fara biyowa ta gidan, Salamatu na gad’a mishi Hajia ta fita sai kawai ya wuce d’akin kai tsaye, duk da kuwa zuciyarshi na kwab’arshi k’walwarshi kuma na tuna mishi had’uwarsu ta safe, d’aure fuska yayi ya bud’a k’ofar da tunanin sai fa ya gyara mata zama dole yarinyar nan.

Ai kam turus yaja ya tsaya sakamakon jin kid’a da kuma ganin k’anwar *shakira*🤣, da d’an k’arfi ya furta “Hak’ik’a daga Allah muke kuma gareshi zamu koma.”

Waro ido yayi da kyau dan shi ko cikin yaranshi a k’iriniya ta yara bai tab’a ganin haka ba. Jin sautinshi ya fargar da ita da sauri ta tsaya tana kallonshi, pik’i-pik’i ta tsaya yi da ido tana neman hanyar dakawa a guje, takowar daya fara yi ce ta sa ta ja baya tana fad’in “Dan Allah malam dan soyayyarka da Allah karka dakeni, kaga dai Hajia amanata ta bari ko?”

Yanda ta k’arashe maganar da nunashi da yatsa irin a dole tambayarshi ne take cikin yanayin yi mishi hannun ya mai sanda sai ta so bashi dariya. Tara mata hannun dama yayi yace “Bani wayar nan?”

Galala tayi tace “Iyee?”

Fito da idonshi yayi yace “Na ce ki bani wayarki?”

Da sauri ta d’auka ta mik’o mishi tana sake fad’in “Malam ai ku an ce ba kwa hushi saboda magada annabawa ne ku, dan Allah kar ka rabani da wayar zan daina daga yau.”

Sama da k’asa ya kalleta ya mik’a mata k’atuwar ledar hannunshi, hannu biyu tasa ta karb’a shi kuma ya d’ora da fad’in “Wannan ita ce zata zama suturarki idan zaki  fita.”

Juyawa yayi kawai ya fita yana sake hangota tana ta kiciniyar rawa a shigowarshi, girgiza kai kawai yayi ya fita a falon, saida ya shiga mota dreba na jan shi ya shiga duba wayar, irin tarikitan hauka daya gani saida yaji kanshi ya fara ciwo, vidéos na wak’ok’i da girki da kwalliya da shirme da shiririta na dariya, hotuna na d’inki da matan da bai ma san dan d’inki ne aka aje hoton ba ko kuma dan kwalliyarsu, tsaf ya tattara komai ya goge ban da girki da yake ganin zasu anfani mace, sai kuma hotunan ta daya samu barkatai wanda ya tabbatar zuwan k’awayen nan nata zata samesu, kallon hotunan ya shiga yi yana murmushi, idan ya ga wani style d’in sai kawau ya tintsire da dariya shi kad’ai, lallai kawai ya gama yarda yarinyar yar zamani ce, da wannan ya isa gida inda suka zauna a duka babban falon shi da ahalinsa suka shiga hira da raha ana tsokanar juna, a sauk’ak’e kuma iyayen ke fahimtar wani kuskure na kalma a tare sa yaran sai su d’orasu a hanya.

Bayan fitarshi kuma Mimi ta bud’e kayan nan, hijabbai ne zumbula zumbula har k’asa ko hannaye basu da, sai nikab da safar k’afa. Kecewa tayi da dariya tana fad’in “Wayyo Allah na akaramakallah, yo wannan ka d’auka ni d’in wata aljana ce? Tabb’ lallai ma!”

Tattaresu tayi ta zuba akan gado ta shiga harkar gabanta da tunanin ta yanda zai dawo mata da wayarta ma, dan ita tafi damunta kam.

                   *Asa-Ma’u*

A wajen amaren kula yau fa daren na musamman ne dan sosai Asas ya zage damtse wajen kwasar amarcin shi da matarshi, kamar yanda yake hari matarshi ce zata zama silar warakarshi hakane ta kasance.

Sosai Asas ya rik’e wuta akan baiwar Allah Asma’u, tun tana jin kunyar nuna gajiyawarta har ta fara mishi kukan tab’ara tana magiyar ta gaji haka, mamaki yake yanda ya kasa sararawa ‘yar mutane, jikinshi k’ara rik’ewa yake yana d’aurewa, hakan yasa suka galabaita daga shi har ita. Wata masifaffiyar zufa ce ta shiga tsatsafo masa sanda ya sauke wani curarren abun daya tarar mishi a mara, take kuma sai jikinshi ya kwashi b’ari sosai, cikin tashin hankali Asma’u ta yunk’ura ta shiga tureshi a jikinta saboda ganin yana wani shure shure kamar zai mutu, fashewa tayi da kuka tana jan zanin jikinta da k’yar tana fad’in “Assss…a…” Gaba d’aya sai ma ta manta sunan da zata kirashi da shi.

Tsaf ta ga ya daina numfashi bare motsi, a firgice baiwar Allah duk da azabar da take ji a jikinta sai ta manta, da gudu ta shiga ban d’aki da zanin rufa a jikinta ta rufe jiki ta d’ebo ruwa ta shafa mishi, shiru ba alamar Asas zai dawo, ai da sauri ta bud’a kayanta ta d’auko doguwar rigar atamfa ta saka ta fito wajen gidan, cikin tashin hankali take k’wala kiran “Mai gadi, mai gadi.”

Kamar daga sama yaji kiran sunan shi ma a kid’ime ya fito yayo kanta, da gudu ta juya ta koma tana fad’in “Muje ka taimaka min, bashi da lafiya.”

Da gudu ya bi bayanta suka shiga d’akin, ganinshi kwance babu kaya a jikinshi sai zanin gadon data ja ta rufa mishi, juyawa yayi yana fad’in “Hajia saka mishi ko duguwar riga, bari ni saina kira lambar Hajiarshi.”

Fita yayi a d’akin da sauri tana matsar k’walla da cije leb’enta dan sosai take jin ciwo a jikinta, kawai dai tashin hankali ne wani yafi wani, da k’yar ta saka mishi dogon wandonshi na bacci da doguwar farar rigar, zaune tayi ta sakashi gaba tana kallo tare da rik’e hannunshi, babban abinda ke ranta a lokacin bai wuce “Kar a zo *sanadin takaba* ne yasa aure na da Asas ya tabbata, Allah ka tashi kafad’unshi kasa kar ya mutu ya barni, duk da ba son shi ne a zuciyata ba amma zan so ya zama mutumin da zai ci gaba da abonda ya fara.”

Mintuna ashirin da biyar suka kawo Hajia gidan tare da drebanta, tana shigowa d’akin Asma’u ta mik’e tana sake fashewa da kuka, cike da dagiya Hajia ta dafata tace “Me ya sameshi Asma’u.”

Cikin kuka tace “Hajia ban sani ba nima, kawai…kawai fad’uwa yayi haka.”

Sake kallonshi tayi ta kalli gadon, da sauri ta d’auke idonshi daga birbid’in jinin data gani a kan zanin gadon dake jikinshi, saidai tana mayar da idonta k’asa sai kuma akan pant d’in Asma’u, cikin dattako da hangen nesa ta fahimci me ya faru, kallon k’ofar shigowa tayi tace “Kabiru.”

Daga falo drebanta ya amsa da “Na’am Hajia.”

“Ku shigo ku kama mana shi.” Da sauri suka shigo tare da mai gadin, wani ikon Allah yau Hajia sam bata jin wannan rud’ewar da furgicin da take shiga idan ciwonshi ya tashi, sauta samu kanta da fad’awa zuciyarta “Idan har wannan ita ce warakar Allah ya yafe kurakurenshi, idan yana da sauren shan ruwa a gaba, Allah ya tashi kafad’unshi.”

Kallon Asma’u tayi sanda zata fita tace “Yata ki nutsu kinji, ki zauna ki kula da kanki kafin jikinki yayi tsami, ina tare dashi insha’Allah zan kula dashi.”

Cikin kuka Asma’u tace “A’a Hajia zan biku nima, a tsorace nake gaskiya ina so nasan halin da yake ciki.”

Girgiza mata kai tayi tace “A’a Asma’u, ki zauna ki samu euwan zafi kiyi wanka kinji, ki kula da kanki nima zan kula dashi.”

Cikin marairaicewa tace “Hajia ina so na je na ga halin da… *mijina* yake ciki.”

Murmushi tayi ta shafa kumatunta cike da tausayinta tace “Yanzu ki fara gyara jikinki, idan gari ya waye zan turo k’awarki sai ku tafi tare.”

Da sauri ta kalleta tace “Mimi?” Da fara’a ta d’aga mata kai alamar eh, jinjina kai tayi ta bita da kallo harta fita, jiki a sanyaye ta fito falon ta shiga madafa dan d’ora ruwan zafin kamar yanda Hajia ta fad’a.

               *Washe gari*

Tunda asuba sheikh ya zo asibitin ganin halin da yake ciki, cikin nutsuwa Hajia ta shiga fad’a mishi abinda Dr. D’in ya fad’a “Ya ce dai wannan karan ciwon ba kaman waccen ba, dan haka ruwa suka k’ara mishi ba tare da alluran da suka saba yi mishi ba.”

Numfashi ya sauke yana sake gyara tsayuwarsa yace “Insha’Allah Hajiarmu komai ya kusa zuwa k’arshe, jiya da dare nima na sak’o a email d’ina daga wani abokin karatu na dake Tunisie, kuma ya fad’a min ya sama mana lokacin had’uwa da wani babban likita daya k’ware a wannan fannin, insha’Allah yau zan gama shirya mana tafiyata da shi, gobe ko jibi zamu bar k’asar nan da izinin Allah.”

Da farin cikin jin haka tace “Masha’Allah, Allah nuna mana, Allah yasa ayi a sa’a.”

“Ameen.” Ya fad’a a sanyaye yana kallon Asas, d’an sake kallon Hajia yayi yace “Ina iyalinsa?”

Kallonshi tayi tace “Tana gida, amma na tura Kabiru ya d’auki Mimi a gida saiya kai ta can wajenta, dan na lura hankalinta ya tashi sosai kuma kamar bata da lafiya, amma na ce Salamatu ta fad’awa Mimi idan ta ga jikinta da sauk’i su zo nan tare ta ga jikinshi.”

K’uri! Yake kallon Hajia duk sanda tace Mimi yana jin wani b’all! A zuciyarshi, kallon fuskar Hajia kawai yake yi yana tunanin “Anya kuwa Hajia tasan wacece yarinyar nan?”

D’an d’auke kan shi yayi a hankali yana sauke numfashi, jim kad’an ya sake kallon Hajia yace “Hajiarmu zan wuce gida, dama daga masallaci nake, amma idan na shirya kafin na wuce aiki zan sake biyowa na ganshi.”

Da sakin fuska tace “To sheikh ba damuwa, sai ka dawo.”

                *Mim-Ma’u*

*Assalama alaikum*

_Kwanakin da suka wuce zaku ga na zage ina ta baku page bibbiyu a wuni d’aya wata rana ma har uku, ba komai ya kawo haka ba sai ganin kuna comment masha’Allah. Watak’ila lura da kukayi ina yi akai akai ne yasa wasu tunanin ko zaman banza ya min yawa, dan haka zakuyi tunanin barin comment da tunanin ai zan ci gaba da sako muku, magana ta gaskiya abinda yasa a can ma kuke ganinshi a kai a kai comment d’inku ne ya ban k’arfin gwiwa, yanzu kuma da kuka rage sai gaba d’aya na mayar da hankalina kan harkokina da kuma rayuwata, *jiya* da k’yar da taimakon *Kwate ta* (Sajida) na samu na saki page d’in jiya, to da irin haka wata rana ma kasa rubutun zanyi._

_Dan *Allah* mu daure mu k’arasa yan tsirarun page d’in da suka rage mana, dan *MATAR MUTUM* ba labari ne ba da zan ja shi da tsayi ba, kuma ina fata matar mutum ya zama labarina na k’arshe a harkar rubutu, idan Allah bai nufeni da hakan ba kuma ina fatan nayi hutu mai dogon zangon da har za’a fara mantawa da sunana kafin na ci gaba, dan Allah ku karfafa min gwiwa ta hanyar sambad’a comment ko na samu na kai k’arshen labarin nan, a grp d’ina a k’alla sama da mutum 50 suna karanta labarin nan a sanda na turashi, amma mafi aksarinku saidai ku turo stekers da sunan kun yi naku comment d’in shikenan, ba zan sake ganin motsinku ba sai na jinkirta yin posting. To a gaskiya idan haka ta ci gaba da faruwa zan dakatar da posting zan kammala rubutu ne saina had’a document na ajiye kayana, dan ni bana tsayar da rubutu idan na fara, kunga kenan shi ma zai shiga sahun litattafaina dana mallaka._

                 *MOM LATEEF*

*Alhamdulillah*👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

        *MATAR MUTUM*

            _(K’abarinsa)_

👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

                   *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

       *SADAUKARWA*

                   

               _GA DUKA_

     *’YAN AMANA TA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_🤝

  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ 

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

                    *34*

Duk da duhun safiya ce amma haka Mimi ta shirya tsaf abinta a cikin atamfarta riga da siket d’amammu ta saka hijab d’inta mai hannaye iya gwiwa tsayinshi, gashi kuma hijab ne irin na zamani mai wuya biyu ga kwalliya, dreba na ajeta gidan Asma’u ta shiga kallon gidan daga waje har ciki, saida ta kai daf da shiga falon ta sauke wata ajiyar zuciya tana jinjina kan ta, sosai tsarin gidan ya birgeta dan kamar yanda Asas yake fad’a mata haka ta samu gidan.

Saida ta bud’a k’ofar ta shiga a tausashe ta furta “Salam.”

Asma’u da dama zaune take tana jiranta da sauri ta fito daga uwar d’akin tana amsawa da “Wa’alaiki salam.”

Murmushi Mimi ta sakar mata inda Asma’u ta mata murmushin yak’e, cikin ciccije lab’e ta k’araso gareta tana fad’in “Muje.”

Hararanta tayi tace “Wai ke duk kin damu ko? Ke ga mai miji.”

A raunane tace “Ba zaki  gane ba Mimi, halin da nake ciki Allah ne kad’ai ya sani kuma zai sama min mafita.”

Cikin gimtse fuska tace “Wani abu yana faruwa ne?”

Kama hannunta tayi tace “Muje, zamuyi magana.”

Yanda ta ga Asma’un na tafiya ita ma sai ta shiga bin ta a haka har ta rufe gidan suka fita, dukansu zaune suke a bayan motar sunyi shiru suna kallon titi. Numfashi Mimi ta sauke tace “Hajia tace min ba kya jin dad’i na zo na taimaka miki, ke kuma hankalinki yana gun mijinki.”

D’an murmushi tayi tace “Hummm! Na ji sauk’i ai.”

“Kin tabbata?” Ta fad’a taana binta da kallon tuhuma, dan duk da bata da sani akan wannan harkar amma dai a karance karance da kutse kutse tana iya gane kad’an daga ciki, shiru kawai tayi bata sake cewa komai ba har suka isa asibitin clinique de gazobi.

A wajen ajiyar motocin ya paka suka bud’e cikin nutsuwa suka fita. Tsaf daga shigowarsu har fitarsu daga motar duk a kan idon Sheikh da shi ma shigowarshi kenan zai shiga d’akin da Asas yake, tsayawa yayi yana k’are mata kallo kamar ya d’ora hannu a kai yace “Wayyo shi wayyo Allah ya shiga uku!”

Akan me zata fito babu hijab d’in daya bata? Babu nikab a fuska bare safar ta k’afa, kenan ba zata tayashi kare martabarta ba? Wani huci ya sauke mai d’auke da siracin bala’i da gudummuwar kishi ta haifar, a sauk’ak’e ya shiga takowa cikin shigarshi ta kamala da mutumci.

Zasu wuce kenan suka ji drebansu Hajia na gaisheshi cikin girmamawa da ladabi, dakatawa sukayi inda Mimi cikinta ya fara juyawa ga fad’uwa da gabanta ya fara yi, Asma’u ma juyawa tayi tabbatarwa da tayi shine yasa ta sunkuyawa tace “Assalama alaikum.”

Da sakin fuska ya amsa mata da “Wa’alaiki salam, ya jikin na ki?”

Tsili tsili tayi da ido da tunanin wai haka Hajia ta mata terere? Da murmushi ta amsa da “Na ji sauk’i ma.”

Da fara’a yace “Masha’Allah, a ci gaba da hak’uri kinji, insha’Allahu zai samu lafiya, dan muna shirin fitar da shi waje.”

Jinjina kai tayi cikin girmamawa tace “Allah ya aminta.”

“Ameen.” Ya fad’a yana d’an satar kallon mutuniyar da tayi tsaye k’erere tana ta sinne kai alamar rashin jin dad’in had’uwa da shi duk ta bayyana a tare da ita, d’auke idonshi yayi ya mayar kan Asma’u da ita ma kan ta ke k’asa yace “K’arasa ciki.”

Gyad’a kai tayi da ladabi zata wuce Mimi ma kamar wutsiya ta bi bayanta, cikin dakakkiyar murya yace “Inna Issa.”

Kyab’e fuska tayi ta juyo ta kalleshi, wani kallon gargad’i ya mata yace “Zo mana.”

Turo bakinta tayi ta kalli Asma’u data shiga tafiya, a hankali ta shiga takowa tana ta turo baki gaba, ba tare daya kula da mutanen dake kai kawo ba ya rik’o hannunta dake waje dan ta saka hannayen hijabin, shi kuma abinda ya b’ata masa rai kenan yanda jan lallenta ya fito sosai kowa na kallo, cikin nutsuwa ya shiga nufa da ita wurin da motocinshi ke pake, jami’an na ganin haka su ma suka bud’e mishi mazauninshi, da hannu ya mata alamar ta fara wucewa. Kallonshi tayi ta fashe da kuka ta girgiza kai alamar a’a, wurga mata ido ya sake yi alamar fa ta shiga, d’aga kanta tayi tare da d’add’age yanda zata hangi Kabiru dan yanda yake tsaye gabanta masha’Allah ya gaje wurin da girman jikinshi da kuma manyan kayan.

Tana hangen Kabiru sai kuwa ta d’aga murya iya k’arfinta cikin kuka tace “Kabiru, ka fad’a ma Hajia an d’aukeni….”

Hararar daya wurga mata yasa ta saurin shiga motar tana sake fashewa da kuka tana ja baya har ta dangane a d’aya murfin k’ofar tana fad’in “Ustaz kayi hak’uri, kaga dai ni wallahi ban yi komai ba, ai ka karb’e wayata tun jiya ko? Kuma na hak’ura ban ce komai ba, dan Allah yanzu kuma me na yi? Kuma kuka hana cin zalin na k’asa, ni dai yanzu kayi…”

Jin an tayar da motocin sanda ya shiga yana kallon zasu bar asibitin yasa ta jujjuyawa, duka motocin guda uku kuma suka bar asibitin, shiru tayi da bakinta ta sinne kan ta da k’ura mata ido ne yayi yana kallo kamar zai cinyeta d’anye.

Tunani ne kala kala ke ta bijiro masa na yanda zai tsawatar mata ta fara gane idan ya ce tayi to kawai tayi ko bata so, zuciyarshi na ta hasaso mishi abubuwa da dama saidai ba d’aya wanda yayi ammana da su. Amma fa k’wala kiran sunan Kabiru da tayi ya masa zafi, a bainin nasi zata fitar da muryarta haka, to wai ko bata da ilimin addini ne? Amma kuma ai tana zuwa islamiyya.

Numfashi ya sauke a ranshi yana fad’in “Watak’ila asarar lokaci ne bata fahimtar komai.”

Da sauri ta kalleshi dan abinda ya fad’a ya fito fili, yanda ta kalleshi yasa shi farga da abinda ya aikata, fuska kawai yayi yace “E, ko kina ganewa ne?”

Had’e fuska tayi ta kumburo baki alamar fa ranta ya b’ace, waro idonshi yayi yace “Idan da kina ganewa ai da kin zama mai suturta kanki a cikin gida ma bare idan zaki fita, kinsan kuwa me Allah ya fad’a akan ku mata yanda zaku saka jalbab d’inku?”

Girgiza kai yayi yana sake tausasa murya yace “Ba zaki sani ba, shiyasa nake so na mayar dake islamiyya.”

Kawar da kanta tayi tana gunguni tare da fatan ya kaita inda zata sauka ta fad’i abinda ke ranta. K’ofar gidansu Hajia taga motocin sun paka sun tsaya, a hankali cikin nutsuwa ya bud’e b’angarenshi ya fita, mamaki da rashin sanin me ya dawo da ita nan yasa tana kallo har y’a zagayo b’aren da take, bud’e mata k’ofar yayi ya mik’a mata tafin hannunshi yana sakar mata murmushi da fad’in “Yan matan tsohonta muje.”

Marairaicewa tayi ka rantse da Allah marainiya ce, k’in mik’a masa hannun tayi ta fita a motar ta rufe da kan ta, gaba ta shiga zata wuce cikin sanyin murya mai kama da rad’a yace “Jirani.”

Cak ta tsaya amma bata juyo ba, saida ya tsaya kusa da ita kafin suka k’arasa shiga ciki, bai bi ta kan kowa ba sai wucewa da yayi har d’akin daya zama na ta a yanzun, tana kallo ya d’auki makullin d’an wani fau da fleurs alamar dai yasan inda ake ajewa ko kuma aljanunshi ne suka fad’a mishi, bud’e d’akin yayi tare da mata alama ta shiga, jiki a mace ta shiga kafin shi ma ya shiga maida k’ofar ya rufe.

K’yak’yabta mishi ido ta fara yi wanda suka kawo ruwa dan gani take irin na jiya zai sake mata, jan majina ta faraa yi a dole ita kuka take, cike da rarrashi ta kalleshi sanda yake zama bakin gadon ta shiga fad’in “Bawan Allah, ai dai yau ban maka komai ba? Amma idan akwai laifin dana maka wanda ban sani ba dan Allah ka yafe min, kaga kai babba ne mai halin girma, biye ma yarinya mashiririciya iri na b’ata lokacin ka ne zakayi.”

Cike da izza da gadara ya d’ora gwiwar hannayenshi akan cinyoyinshi yana kallonta, a dak’ile cike da d’aure fuska yace “Ina kayan dana kawo miki jiya?”

Da sauri ta nuna wurin kayanta tace “Suna can.”

“D’auko.” Ya fad’a ba alamar wasa, jiki na rawa ta nufi kayan ta shiga kakkarwar d’aukowa, tana zuwa ta zube gabanshi tare da durk’usawa tace “Gasu.”

D’an d’aga hannayenshi yayi daga tangalewar daya musu ya kalleta da kyau yace “Ryam.”

Tarr! Ita ma ta sauke nata idon cikin nashi, a ladabce ta amsa da “Na’am.”

A sanyaye ya shiga fad’in “Mutum ne ni dake da tsari a rayuwa, ina so idan na ce wa mutum yayi to yayi abun nan ba tare da nayi maimaici ba, kamar yanda kika fad’a ni babba ne ke kuma yarinya mashiririciya, Ryam na fahimci kanki yana rawa sosai, hankalinki ba wuri d’aya yake ba, sannan nutsuwarki bata tare da ke. Abu d’aya nake so ki sani shi ne idan na baki uamrni kawai ki bi, kin fahimta?”

Samun kanta tayi da kallon cikin idonshi tare da furta “Ko da umarnin ya sab’awa ubangiji?”

Yanda ya kalleta yasa ta sunkuyar da kai, cikin muryar shan k’amshi yace “Bana fatan na umarci wanda ke k’asa dani da sab’awa mahaliccina.”

Numfashi ya sauke yace “Yanzu d’auki hijab d’in nan ki saka, dan wannan na jikinki ba hijabi bane shirme ne da hauka.”

Da sauri ta kalleshi ta bud’e baki irin mamakin nan, sai kuma ta jinjina kai ta mik’e, d’aukar d’aya daga cikin hijaban tayi ta cire wannan ta saka, yanda ya sauka k’asa ya rufe mata k’afafu ne yasa ta kallonshi tace “Abdul amma wannan hijabin na mamansu Aisha ne ka d’auko min ko? Dubeshi fa sharb’eb’e ya zanyi tafiy…”

Shiru tayi dan ashe kallonta yake tana maganar nan, mik’ewa yayi tsaye tare da figota da k’arfi ta fad’a kan shi, lab’e fuska tayi alamar zatayi kuka tayi k’asa da kanta, cikin tsatsareta da ido yace “Maimaita na ji.”

Rarraba ido tayi tana d’an jan majina a hancinta sakamakon yanda k’amshin turarenshi ke shiga hancin na ta, cikin rawar murya tace “Mmm..ee?”

Ba tare daya d’auke idonshi a kan ta ba ya saka yatsanshi manuniya ya shiga zagaya labb’enta yana fad’in “Abdul mana, maimaita na ji.”

Wasu yawu ta had’e masu nauyi tana kakkauce fuskarta tace “Kus…kure.. ne.”

Tallabo hab’arta yayi yana son tilastata ta kalleshi, duk da fuskarta suna kallon juna ne amma idonta k’irjinshi suke kallo sai kuma hawaye masu d’umin gaske da suka shiga kwaranyo mata, cikin tattausan murya yace “Ni kuma kuskuren na ki nake so, sake fad’a naji.”

Idonta rufe ta girgiza kai alamar a’a, ba tare da shi kan shi yasan yayi ba y’a marairaice yace “Dan Allah Ryam, sake fad’an Abdul na ji.”

Rintse idonta ta sake yi gaba d’aya take ji kamar an zare mata rai dan ta kasa motsi, labb’enta ne suka shiga hard’ewa tana fad’in “Aaaaabbbbdulll.”

Murmushin gefen labb’a yayi tare da jan dogon hancinta yace “Mai tsiwar tsiya.”

Sakinta yayi yana fad’in “D’aura nikab d’in.”

Sharb’ar majina tayi irin shmmmmm! D’in nan kafin ya d’auki nikab d’in, d’orawa tayi zata d’aura sai kuma wata zuciyar tace “Kenan ma yin abinda yace kiyi zakiyi ?”

Sai kawai ta d’aura ta ba daidai ba ta fito da ido da hanci duk waje, wani k’ayataccen murmushi ya saki yana girgiza kai, matsawa yayi daf da ita yana kallon k’wayar idonta yace “Wato dai ni za’a ma wayo ko? Kin manta sanda aka haifeki ina daf da haifo kamarki ni ma.”

Cike da sangarta da sub’utar baki tace “Ai mamanmu ma ka girmeta.”

Sake bud’e idonshi yayi fes a kan ta yace “Inji wa?”

K’asa tayi da idonta tana turo baki, hannu ya kai tare da kunce d’aurin da tayi, a tsanake kamar yanda yasha ganin Hafsat na yi ya d’aura mata, cas kuwa ya fito mata da idonta biyu tare da kallonta ya saki murmushi yace “Daga yau haka nale son ganinki, ya kamata kisan cewa ke yanzu matata ce, akwai buk’atar shigarki ta nuna kamala, nutsuwa, tarbiyya da kuma ilimi, kin fahimta?”

K’ala ba tace ba hakan yasa shi zaro mata ido yace “Ryam…”

“To.” Ta fad’a tana kawar da kan ta, hannu yasa ya d’aga nikab d’in yasa yatsu biyu ya cabki leb’enta na k’asa kamar yanda ya mata shekaran jiya, wata k’walla ta matso cike da azaba tana rintse idonta sosai, ba alamar wasa a tare da shi yace “Muryarki, fuskarki, surarki, mutuncinki, duk mallakina ne a yanzu, kuma ina matuk’ar kishin wani ya hangi inuwar gonata, kada ki sake min d’anyan kan da kika min d’azu wajen kiran sunan Kabir, idan kika sake kuma wallahi kinji na rantse saina taune bakinki.”

Cikin wahala taa jinjina kai alamar to, sakin leb’en nata yayi tare da shigewa gaba yace “Saki nikab d’inki ki biyo bayana.”

Hannu d’aya ta d’ora a kai ta fashe da kukan da babu sauti tace “Wayyo Allah na ni Maryam, wannan ita ce jarabar da nake gudu ta auren tsoho, sam bai san miye soyayya ba bare ya nuna min, sai wasu dokoki da sharud’ai kawai yake gindaya min, yanzu ni gidan uban wa zan kai wannan hijab?”

K’wank’wasa k’ofar da yayi yasa ta zabura ta juya, tsaye yake yana jiranta da sauri ta fita a d’akin ya rufe kafin suka fita, da kanshi ya bud’e mata mota ta shiga ya rufe kafin ya shiga shi ma suka sake d’aukar hanyar asibiti.

Shirun daya ratsa motar yasa Mimi sauke numfashi a hankali, d’an kallonshi tayi da idonta dake waje cikin sanyin murya tace “Ni fa ba jahila bace, kuma Abbana ba a banza yake biya min kud’in laraba ba, ina da ilimin addini daidai gwargwado, karambani ne kawai da bud’ewar ido na ‘ya’yan yau da aka haifemu ba’a haifi halinmu ba, iyayena a tsaye suke kan tarbiyata, ni ce kawai nake ja musu zagi da zund’e, amma na tabbata duk wanda ya zageni iyayensa ya zaga, dan ni ban yi wa iyayena rainin da har zanyi cacar bakin da zata kaini ga zaginsu ba.”

Duk da maganarshi ta so tsaya mishi sai yayi gaggawar kawar da ita a rai ya d’an tab’e baki yace “Kin tabbata ba asara ake yi ba?”

Kallonshi tayi rai b’ace tana sako hawaye tace “E, na tabbata.”

Wani shak’iyin murmushi yayi yace “A Alk’ur’ani mai girma Allah yana fad’awa manzonsa cewa ” Qumi-llaila illa k’alila, (suratul muzammil, aya ta 2) me ye fassarar hakan?”

Kallonshi tayi tana malalacin murmushi tace “Ka tsaya a kowane dare sai kad’an kawai.”

D’orawa yayi da “A wata ayar yana cewa, Yah ayyuha-llazina amanu qu anfusakum wa’ahalikum nara’waquduha-nasu walhijara,alaiha mala’ikatun gilazun, shidadun-laya-asunallaha ma’amarahum wayaf-aluna ma’yu’umarun (suratul tahrim, aya ta 5).”

Ba tare data daina kallonshi ba dan mamakinshi take a yanzu kam tace “Yah ku wad’anda sukayi imani, ku kare kawunanku da iyalenku daga shiga wuta-wacce mutane da duwatsu ce makamashinta’a cikinta kuma mala’iku ne masu tsananin k’arfi da basa sab’a umarnin Allah kuma suna yin abinda aka umarcesu.”

Ba tare daya kalli sashen da take ba yace “A wata ayar cewa ake, Wa’iza sa’alaka ibadi anni’fainni qarib-ujibu da’awati-da’i iza’da’an, falyastajibuli-walyu’uminubi-la’alahum yarshudun (suratul baqara aya ta 185).”

A kaikaice ita ma ta amsa da “Idan bayina suka tambayeka a game dani ka fad’a musu ina kusa da su, ina amsa rok’on mai rok’o a a sanda ya rok’eni, ku rok’eni kuyi imani dani i…”

Kallon daya mata da sauri yasa tayi shiru tana d’auke kallonta daga kanshi gaba d’aya, sake d’auke idonshi yayi yana jin zuciyarshi na wani daka da k’arfi k’arfi, cikin k’arfin hali da son rikitata ya fita a b’angaren Alqur’ani ya koma hadisi ta hanyar fad’in “Fawallahu lazi-la’ilaha gairuhu, ina ahadakum-laya’amaluahalin-janna hatta’mayakunu bainahu-wabainaha illa’zira’un, fayasbik’u’alaihul kitab faya’amalu ahalin’nar fayadakulaha…”

Kallonshi Mimi tayi a ranta tana fad’in “Wato ita zai wa wannan jirgen?”

Cije leb’en k’asa tayi kafin tace “Hadisi na 4 mai taken ahwalul insan, Abi Abdul-Rahaman Abdullahi bin Mas’ud ne Allah ya yarda dashi ne yake fad’a, fassarar kuma ita ce na rantse da Allahn da babu wani bayan shi, lallai d’ayanku yana aikata aiki irin na yan aljanna harsai ya kasance tsakaninshi da ita saura zira’i d’aya, sai a rufe littafinshi sai ya dinga aikata aiki irin na yan wuta, kuma sai ya shigeta…Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.”

Kallonta yayi cike da gatse yace “Wane hadisi ne a gaban wannan?”

Murmushi tayi tace “A wane littafin hadisin???”

Yanda ta gama harbo jirginshi yasa shi saurin kallonta da ido cirrr kamar zai had’eta, d’auke idonta tayi daga kanshi tace “Idan a matin-l’1arba’una nawwiya fi ahadisin-lsahiha nabbawiy, hadisi na 6 shi ne hani akan bidi’a,, wanda uwar muminai uwar Abdullah A’ishata Allah ya k’ara yarda a gareta tace: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a garesa yace “Duk wanda ya zo mana da wani abu cikin lamarinmu ba’a cikinmu ba to mun mayar mishi” Bukhari da Muslim ne suka ruwaitoshi, a cikin wata rawaya ta muslim kuma yace “Wanda ya aikata wani aiki ba’a cikin lamarinmu ba to mun mayar mishi.”

Wani nauyayyen numfashi ya sauke a sirrince yana jin abun wani iri kamar mafarki, to dama tana da sani haka take sanin ne tayi take tsula tsiyarta? Kafin ya samu gamsashiyar amsa dreban ya kutsa hancin motar cikin asibiti, a inda motocin suke da farko yanzu ma aka paka, yana shirin bud’ewa tayi saurin cewa “Abinda nake yi ai baiyi kama dana jahilai ba, kuma bai aikata abunda ya sab’awa shari’a ba bare har kayi tunanin rashin ilimi ne ya jawo hakan.”

Saida ta bud’e motar zata fita ta sake kallonshi tace “Yana daga cikin kyautata musuluncin mutum ya bar shiga abinda bai shafeshi ba, hadisi ne ingantaccen, idan ka manta ka tuna hakan.”

Ficewa tayi ta shiga takawa da sauri tare da d’age nikab d’in ta kwanceta gaba d’aya har ta shige duk da bata san d’akin da zata shiga ba, tana shiga ta corridor suka had’e da Alhaji Saleh ya fito zai tafi, gaisheshi tayi har k’asa ya amsa da fara’a ya nuna mata d’akin, wucewa tayi da sallama aka amsa da bata izinin shiga, a hankali ta bud’a k’ofar tana mai sauke idonta akan Hajia, k’arasa shiga tayi daga Asma’u sai Hajia sai kuma wata matashiya da bata san ta ba tare da Aisha da kayan makaranta a jikinta.

Da fara’a Hajia tace “Mimi sai yanzu? Nayi taa jiran shigowarki ai.”

Murmushi tayi tana sunne kan ta, Asma’u ma murmushi tayi tace “Da alama gida ta koma ta canza hijabi.”

D’aga kai Mimi tayi ta kalleta tare da satar kallon Asas dake kwance yana bacci, d’auke kallonta tayi daga kan shi ta kalli Aisha dake fad’in “Aunty Mimi ina kwana?”

Da sakin fuska cike da jin kunya tace “Aisha sannu.”

“Yawwa.” Ta fad’a da fara’a, d’ayar ce tace “Ina kwana aunty.”

A sanyaye tace “Muna lafiya?”

“Lafiya lau.” Ta fad’a da sakin fuska ita ma, Hajia ce tace “Mai aikin gidanku ce ai, Hafsat take kama ma aiki.”

Sunkuyar da kai tayi a ranta tana fad’in “Gidan mu dai, ni ba zan zauna da tsohon nan ba, d’an rainin wayo ne.”

Yanda tayi maganar a zuciyarta yasa har bakinta saida ya motsa, mik’ewa su Aisha sukayi tana fad’in “Hajia ni zan wuce makaranta dreba na jirana a waje.”

Tab’e baki Hajia tayi tace “To Umma ta gaida Aisha mana.”

Kallonta Aisha tayi tace “Kuma dan kin samu ma na miki magana?”

“Kar ki min mana.” Ta fad’a tana d’auke kai, murmushi tayi tace “Nasan me ye matsalarki, idan na dawo zamu zauna dake Hajia.”

Zasu fita shi kuma ya bud’o k’ofar da waya a hannunshi, juyawar da tayi yasa suka fara had’a idonsu, da sauri ta janye nata gabanta na fad’uwa da sauri sauri, takawa tayi ta koma bayan Hajia ta lab’e tare da yaye hijabin ta baya ta d’orashi akan kafad’unta, hakan yasa bayanta ya bayyana a waje.

A sanyaye ta ji yace wa Aisha “Har yanzu baki tafi ba?”

Da ladabi kanta a k’asa tace “Abie Amie ce ta aikoni tare da Assia muka kawowa su Hajia abinci.”

Lumshe ido yayi tare da kaucewa a k’ofar suka fita, k’arasa shigowa yayi yana kallon yanda ta yaye hijabin, wato har tayi halin? Girgiza kai yayi ya kalli Hajia dake fad’in “Hajiarmu, mun gama shirin tafiya komai da komai, insha’Allah yau da k’arfe 08:00 na dare jirginmu zai tashi.”

Kallonshi tayi da mamaki tace “Yau kuma? Da wuri haka?”

Lumshe ido kawai yayi alamar eh, jinjina kai tayi daan ta fahimci ya gama kenan, a sanyaye tace “To da wa zaku tafi?”

A dak’ile yace “Ni, da kuma shi.”

Nan ma jinjina kai tayi ba tace komai ba, juyawa yayi zai fita sai kuma ya tsaya, kallon Mimi yayi da ita ma ta kalleshi ganin ya tsaya, nunota yayi da yatsa yace “…

_Nasan kunsan da gani posting da wuri ya nuna komai ya tafi zan-zan, hak’ik’a comment k’arfin gwiwa ne da kuzari😁 dan gashi allurarku ta sokeni da kyau, a ci gaba da gashi._

*Alhamdulillah*👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

        *MATAR MUTUM*

            _(K’abarinsa)_

👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

                   *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

       *SADAUKARWA*

                   

               _GA DUKA_

     *’YAN AMANA TA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_🤝

  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ 

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

                    *35*

Nunota yayi da yatsa yace ” *Maamah* wallahi idan baki gyara hijabin nan ba saina ajeta hulata gefe na miki abinda baki tsammani.”

Wani bazawarin murmushi ta saki tare da yin durk’ushe bayan kujerar Hajia tana fad’in “Hajia ai kinsan tun ina yarinya bana son zafi, shiyasa Mamana ma a waje take min shinfid’a ina kwana, wannan hijabin zai iya kasheni saboda girmansa yayi yawa.”

Hajia daketa rik’e dariyarta rufe baki tayi da tafin hannu, Asma’u kam kallonta tayi tace “Yaushe haka ta fara faruwa?”

K’wafa sheikh yayi ya juya zai fita Mimi dake hararan Asma’u ta sake fad’in “Sheikh baka bani wayata da ka ce ba.”

Da sauri ya juyo jin ta kimkima wata k’aryar, kallonta ya shiga yi irin mai nuna “Ke Mimi dan Allah zo ki kasheni ki huta.” 

Jinjina kai yayi yasa hannu aljihu ya ciro wayar dan dama tana tare dashi, mik’a mata yayi yace “Gashi.”

Karb’a tayi tana washe baki har kunne, juyawa yayi ya fita da sauri ta zagaya kusan Asma’u ta zauna tana bud’e wayar, abubuwan data fi damuwa da su ta fara dubawa, saidai mummunan gani tayi dan komai ya shafe hotunanta da girki kawai ta gani, sannan an yi désinstaller WhastApp d’inta alamar ba’a son ta dashi, gumtse baki tayi ta kalli Asma’u kamar zata kifa mata mari tsabar takaici.

Zuwa k’arfe 10:20 aka sallamesu a asibitin, har gida suka rakasu saidai daga cikin mota Hajia ta musu sallama ban da Mimi dake kunyar had’a ido da Asas, dan shima kunyarta yake ji fiye da yanda ita take jin kunyar shi ma, suna shiga gidansu su kuma dreba ya wuce dasu gida.

              *07:00*

Cike da son danne kewarta ko na ce buk’atuwar mace ya sake matseta a jikinshi yana sauke ajiyar zuciya mai nauyin gaske, tun ranar da ifiritiyar yarinyar can ta tashi boma-bomanshi sun kasa kwantawa, dan ya fahimci Hafsat bata jin dad’i sosai, dan haka bai ma nuna mata buk’atar hakan ba, lumshe ido yayi yana sake jin komai na dad’a mik’e mishi tsaye cikin muryar dake nunawa duk mai hankali halin da mamallakin muryar yake ciki ya shiga rad’a mata “Zzzanyi…kewarki manga na, ki kula min da kanki.”

Sake d’an rumgumeshi tayi ita ma tana yatsina fuska saboda rik’ewar da bayanta keyi tace “Insha’Allah, ka kula min da kanka kai ma, Allah ya tsare mana ku ya kareku.”

Kasa amsa mata yayi sai wuyanta daya shiga shinshinawa yana goga mata gemunshi a kafad’a, cije leb’e tayi tana rintse ido dan sosai take da buk’atar zama, hannu tasa ta dafe cikinta da sauri ya d’ago ya kalleta yace “Lafiya?”

Murmushi ta sakar masa tace “Ba komai.” Da alamar tuhuma yace “Kin tabbata?”

Jinjina kai tayi, ajiyar zuciya ya sauke yana rik’e da hannayenta yace “Ki tayamu da addu’a muje a sa’a da fatan dacewa, idan kika ji jikin nan ya matsa miki dan Allah kiyi k’ok’ari ki kai min kanki asibiti, Hafsa ba’a son zaman nan naki a wannan halin.”

Jinjina kai tayi tace “Insha’Allahu zan je.”

Jinjina kai yayi shi ma yace “A d’aki na aje miki katin banki na gida, sannan akwai makulin mota guda biyu na bar miki wanda zaki iya buk’ata.”

Murmushi tayi tace “Allah ya saka da alkairi, zanyi kewarka.”

Sake rumgumeta yayi tare da manna mata sumba yace “Nima haka.”

Sakin juna sukayi a hankali yana rik’e da hannunta suka fito falon, yaran suka samu suna tilawar karatu, duk mik’ewa sukayi suna binshi da addu’a, shafa kawunansu yayi dukansu ya sumbaci goshinsu har Aisha kafin ya musu addu’a ya fita zuciyarshi cike da kewar iyalinshi musamman ma matarshi da yake matuk’ar tausaya mata.

                *Asa-Ma’u*

Fashewa tayi da kuka duk da bai fad’a mata kalmar so ba, amma dai yanda ya nuna mata jin dad’inshi da godiya akan martaba da kimarta data kawo masa, had’e da jinjina mata akan irin bajintar da tayi a darensu, madadin ace yana kula da ita sai ya zama ita ce ta kula dashi har ta kasa bacci a wannan daren saboda halin da yake ciki. Ganin yayi rarrashin amma ta k’i yin shiru yasa shi aje jakarshi k’asa yace “Shikenan to tunda ba kya son tafiyar, bari na kira sheikh saina fad’a masa kawai na fasa tafiyar saboda ba kya so, kinga sai na zauna a gidan tare dake, amma fa kiyi hak’uri dan kullum zan dinga suma miki a guda.”

Da sauri ta rik’e wayar da yake k’ok’arin cirowa aljihu tana fad’in “A’a baan ce ba.”

Kallonta yayi ya sauke numfashi yace “To me kika ce yanzu?”

Sunkuyar da kai tayi tana share hawaye tace “Ka tafi Allah ya bada sa’a, Allah ya baka lafiya kamar kowa.”

Tallabo hab’arta yayi tare da fad’in “Sannan na dawo miki gida mu d’ora shagalinmu daga inda muka tsaya.”

Duk’ar da kai tayi cike da kunya tana Murmushi da sauri ya tallabota ta fad’a jikinshi, rumgumeta yayi sosai yana furta “Na fad’a miki wata magana.”

A k’asan mak’oshi tace “Um.” Sake matseta yayi yace “Zaki yarda dani idan na fad’a miki?”

“Um.” Ta sake fad’a a sanyaye, cike da k’warin gwiwa yace “Ina sonki a zuciyata *Husna*.”

Da sauri ta d’ago kanta daga k’irjinshi tana kallon fuskarshi, kamar wanda aka ce mishi zata hango burbushin sauran son Mimi da har yaanzu ke zuciyarshi sai kawai ya sunkuyar da idonshi k’asa, sautin murmushinta ne yasa shi kuma kallonta, cikin raha tace “Kamar ba gaske ba.”

Da alamar tuhuma yace “Kenan baki yarda ba?”

Girgiza kai tayi tace “Na yarda mana, kawai dai ina ji ne kamar a mafarki.”

Murmushi yayi yace “To ba mafarki bane, zahiri ne wannan.”

Murmushi tayi mai k’ayatarwa tare da gyara zaman hijab d’inta, rik’e hannunta yayi yace “Muje dreba na jiranmu a waje.”

Jinjina kai tayi tare da bin shi a baya duk da yana rik’e da hannunta d’aya hannun kuma jakarshi yake ja, tare suka nufi airport dan suna so suga tafiyarsu kafin su juyo su dawo.

                    *Mimi*

Kwance take akan gado tana ta karatun muktasur-lakhdari da ta samu a wayar, ba kuma shi kad’ai bane ta samu ire-iren litattafan nan dayawa a wayar wanda ta tabbatar shi ya saka mata su.

Da sauri Hajia ta shigo d’akin hakan yasa ta tashi zaune tana kallonta, hijab ne hannunta tana ta k’ok’arin sakawa tana fad’in “Mimi tashi mu tafi ki rakani, na tabbata yanzu suna filin jirgin nan.”

Da mamaki tare da wani fad’uwar gaba da taji a sirrince tace “Hajia tare zamu tafi?”

Saida ta gyara hijab d’in a fuskarta tace “E mana, ina so ne na samu abokin tafiya, ko ba zaki je ba?”

Sauke numfashi tayi a fili ta furta “Shikenan zan je.”

Saukowa tayi a kan gadon tare da nufa wurin kayanta, har ta d’auki hijab sai kuma ta yatsina baki ta mayar dashi tace “Dare ne fa, wa zai kula dani ma.”

Wani arnen mayafi ta d’auko shara-shara kalar fari kamar yanda fari yafi yawa a atamfar jikinta, riga da siket ne dai kamar mafi yawan lokuta d’inkin zamani, gidan nonuwan nan ya fito cas da shi haka siket d’in ya bi jikinta ya fito da mazaunai da wajen gwiwa ma ya ciresu daban, takalmi ta d’auka masu tudu hakan yasa ta shiga bada sautin d’as-d’as-d’as.

Gaban madubi ta tsaya ta d’an gyara d’aurin kallabin irin kawai zahra Buhari tare da shafe jikinta da turarenta mukhallat, masha’Allah yanda wuyanta ya fito sai kuma ta d’ora mayafin a kafad’u ta rik’e wayarta ta fito.

A mota ta samu Hajia tana amsa waya da alama kuma da Hafsat suke waya, dan haka Hajia bata kula da shigarta ba ta dai ji k’amshin turarenta kawai, saida ta kammala ne ta juyo ta kalleta tana fad’in “Daga nan zamu wuce gidanku na ga jikin Hafsat, da alama bata jin dad’i…”

Dakatawa tayi sakamakon ganin Mimi kamar wacce zata je bikin walima, zaro ido tayi tace “Takwarata da mayafin naan kika fito?”

Tsareta tayi da ido tace “E.” Ajiyar zuciya ta sauke ta furta “Ya Hayyu ya Qayyum.”

Jinjina kai tayi ta kasa cewa komai ba, dan badan sauri da take ba da sai ta canza mayafin nan, kar sheikh ya d’auka ita ke d’aure mata gindi ma take wani abun.

Basu jima ba suka isa dan sun fi dukansu kusa da filin jirgin, ko da motarsu ta paka wajen ta hangi na shi motocin da kuma ta Asas saidai babu kowa a wurin, fita sukayi saidai a yau Mimi jin ta take a sake kamar sanda tana budurwa, dan ta kwana biyu rabonta da mayafi ma, gaba Hajia ta wuce Mimi na bayanta suna tunkarar shiga cikin filin da mutane dayawa ke ciki sun rako ahalinsu a iya inda kujerun zama na farko suke, wasu kuma kai tsaye suke wucewa wajen kejuru na biyo wanda aka tanada domin masu tafiya.

Hajia na shiga suka kallo wajen kamar wacce ta k’wala musu kira, saidai kuma a take kallo ya koma sama wau shaho ya d’au giwa, ” *Mimi*?”

Shi ne kawai abinda ya furta tare da damk’ar hannun Asas d’aya hannun kuma gam a k’irjinshi, lumshe ido yayi yana son ambatan sunan ubangiji amma yau sai ya samu kan shi da kasa furta komai. Kallonshi Asas yayi da son gano yanayinshi murya k’asan makoshi yace “Sheikh kana lafiya?”

Ba tare daya bud’a idonshi ba murya na rawa a rashin sanin yanda yayi magana yace “Banda lafiya Asas, jikina ya min nauyi, zuciyata bugawa take da sauri, ban da lafiya gaskiya.”

Da sauri Asma’u ta kalleshi cike da tausayi dan tasan yanda ya ga Mimi ne, tsaf suka k’araso sai Asas daya shiga binta da kallo yana jin kamar ya tsawatar mata, sheikh dai har ya kasa kawaici ya iyaa furta haka? Lallai abinda yake ji a game da ita babba ne. Da sauri Asma’u ta fizgi hannunta suka koma gefe Hajia kuma na kallonshi da mamaki ganin idonshi a rufe.

Cikin b’acin rai tace “Me ye haka Mimi? Ya zaki fito babu hijab kuma kinsan zaki had’u da sheikh?”

Yatsina fuska tayi tace “To sai me? Tsirara na fito.”

A hassale tace “Ba tsirara kika fito ba a wajen mutane, amma a wajenshi tsirara ne, haba Mimi wai me yake damunki ne? Ya kike abu kamar mahaukaciya wani lokacin?”

Da d’umbum mamaki Mimi ta kalleta tace “Mahaukaciya? Asma’u akan sheikh d’in ne kike kirana da mahaukaciya, saboda kina so ki nuna min kin fini zama d’aya daga cikinsu kenan?”

Juyawa tayi zata bar wurin Asma’u ta rik’o hannunta cikin jin haushi tace “Ni ba mahaukaciya na kiraki ba, amma Mimi ke ma kinsan baki kyauta ba, a ganina ko dangata ta jini ce ta had’aki da shi ya zama dole gareki suturta jikinki, yanzu ya kike so mutane su kaalleshi idan aka san ke ce matarsa?”

Fige hannunta tayi da k’arfi tace “To sai me? Ya sakeni mana idan ba zai iya ba, ni na ce dama ya aureni ne? Kinga ba zan iya rayuwar takuran nan ba, tunda yanzu ke ma ahalin Sharif ce ki fad’a ma masu fad’a masa yaji ya sawak’e min.”

Juyawa tayi a hassale ta nufi hanyar fita mayafin na sauka a kafad’unta, gyarashi tayi cikin hushi ta sab’a a kafad’a d’aya ta shiga takawa da sauri na b’acin rai wanda ya haddasa k’adawar mazaunanta da kyau tare da tsallen zuciyar sheikh kamar zai suma a wurin yana binta da ido.

Numfashi ya shiga saukewa da sauri sauri da kuma k’arfi k’arfi, Hajia na d’an gefe tare da Asas dan tunda suka kula baya hayyacinshi suka matsa suna tattaunawa na tsakanin d’a da uwa, matsowa Asama’u tayi ta rumgume hannaye cike da jimami, idonshi kawai ya iya wulk’itawa ya kalli Asma’u cikin k’arfin hali kuma har yanzu hannunshi na kan k’irjinshi yace ” *Wacece ita*? Wacece Mimi da take son na sakata a cikin jarabawar da Allah ya min, yanayin nan sabo ne a gareni da ba lallai na iya sabawa da shi ba, ina tsoron kar a fara fahimta har na fara zama mahaukaci a idon jama’a, me yasa k’awarki ba zata bini a baya ba yanda zamu jima muna tafiyarmu? Wanene dalili ne yasa dole take so sai na mutu a kan ta? Me yasa? Me yasa Asma’u.”

Gaba d’aya jikinta sanyi yayi kanta a k’asa tana sauke numfashi, tunaninta shine ta yanda zata fara bashi amsar tambayoyin nan bayan gaisuwa ma har yanzu a kunyace take mishi, amma tunda akan abinda ya shafi k’awarta ne sai ta aro jarumta tayi k’arfin halin gyara muryarta tace “…

*Alhamdulillah*👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

        *MATAR MUTUM*

            _(K’abarinsa)_

👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

                   *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

       *SADAUKARWA*

                   

               _GA DUKA_

     *’YAN AMANA TA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_🤝

  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ 

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

                    *36*

Aro jarumta tayi k’arfin halin gyara muryarta tace “Mimi da kake gani a zahiri haka bad’ininta yake, ba kowa bace ita amma tana da suffa mai ban tsoro, sani na halayya babu wanda ya santa sama dani, dan ko iyayenta suna zarginta, saidai Mimi tana da sauk’i sha’ani idan kuka fahimci junanku, tana da ladabi da biyayya idan har tana girmama abu, matsalarta d’aya taurin kai, wanda shi ma nake fatan ka zama wanda zai canza mata wannan d’abi’ar.”

Gyara tsayuwa tayi ba tare data kalleshi ba tace “Idan halinku ya zo d’aya da Mimi zaku jima kuna tafiyarku, ni k’awarta saidai akwai wasu halaye na ta da muke samun sab’ani akan su, saidai hushin Mimi kamar d’igon ruwa ne, taurin kan ta ma haka na tabbata zaka iya ji da haka.”

D’an takawa tayi ta matso kusanshi ta kalli fuskarshi da har yanzu yake kallon hanyar da Mimi ta bi tace “Tana da suffar kura ne a jikinta, ga *tsoro* ga ban *tsoro*, ga wanda bai santa ba har ya had’a da tagomashin *zarginta*, amma nasan gaba kad’an kai ne zaka bamu masaniya akan wacece Mimi.”

K’arasawa tayi kusa dasu Hajia, a lokacin lokaci ya cika har an fara kiran sunayen matafiya, kamar wanda aka tsikara da tsinin allura sai kawai ya d’an zabura yana fad’in “Hasbunallahu wani’imal wakil.”

Da wani irin sauri ya shiga takawa yana nufa hanyar fita, kallonshi suka shiga yi inda Asas yace “Ina kuma zai tafi?”

Cike da dagiya Hajua ta d’auke kanta tace “Barshi zai dawo.”

Yana fita bakin k’ofar ya hangeta tsaye jikin motar ta rumgume hannaye sai cika take tana batsewa, tana ganin ya nufi inda take ta had’e fuska ta gyara tsayuwarta, ai akan shi ne Asma’u ta kirata mahaukaciya ko? To ta daina yi masa wasa daga yanzu (Kaji k’arfin hali ga uwata).

Yana zuwa bud’e motar yayi tare da kama hannunta ya wurgata ciki da k’arfi, shiga yayi yana rufe motar Kabiru ya fita a mazauninshi na dreba ya koma gefe. Sam sai ta k’i ta nuna tsoron yanayinshi, had’e fuska tayi sosai ta k’ura masa ido tana kallo, yanda take kallonshi sai ta dubutburtashi ya rasa me zai mata.

Hannayenshi ya d’aga da niyyar sake cakumota ya mata irin jijjigar ranar, sai kawai ya sauke a hankali ya kamo hannayenta ya rik’e a cikin na shi, sunkuyar da kan shi yayi k’asa baki na rawa rawa yace “Ryam *ya kike so dani ne? Dan Allah ki taimaka ki killace min kan ki, kinga wallahi zan iya fasa tafiyar nan idan kika ci gaba da yi min irin haka, Ryam kuka na ke so nayi saidai bansan ko zaki  iya rarrashi na ba, Ryam hankalina tashi yake idan kina fad’in ba kya son tsoho, hankali na bari jikina yake idan kina fad’in na sakeki, gaba d’aya rasa nutsuwata nake idan kina min irin rigingimun nan, shin so kike na ajiye babbar rigata ne na dinga saka k’ananan kaya? Ryam so kike na ajiye sanina a gefe na dinga yawo dake a gari muna tafe muna shan ice cream?* Ryam ina ake rage shekaru? Zan je a rage min indai zaki zauna dani, Ryam ina jin ki a zuciyata sosai kuma ina kishinki, sannan ina jin haushin wanda suka fara kalle min surarki, da zan iya hukuntasu to hukuncinsu shi ne k’wak’ule idonshi ne kawai abinda zan iya yi mai sauk’i, dan Allah Ryam ki taiamaka ki daina saka zuciyata na bugawa sosai a kan ki, kinga fa zan iya haukacewa dan rigimarki yawa gareta.”

Sakin hannayenta yayi ya tallabo fuskarta, yanda gaba d’aya tayi wani sororo tana kallonshi zai nuna maka kalamanshi sun sakata a wani yanayi na mamaki da d’imuwa, bakinta ya kalla da babu komai a kan shi sai kalarshi ta asali wato pink da bak’i, a hankali ya shiga matsawa da fuskarshi kusa da ta ta har saida ya d’ora labb’anshi a na ta labb’an.

Wani irin salo ya shiga mata mai tsayawa a zuciya, yanda yake zura harshenshi a bakinta yana zagayawa da shi ko ina, yanda yake d’an tattauna leb’enta a hankali, ga hannunshi d’aya daya jima da shiga rigarta, cabkar nononta yayi hakan yasa ta waro ido sai kuma ta lumshe saboda idonshi a kan na ta suke, a hankali a nutse ya shiga mulmula kan k’irjinta yana lailayawa yana shafasu, Mimi da gaba d’aya jikinta ya mutu yayi wani irin sanyi lak’was, ji take kamar ana mata tafiyar tsutsa, yam-yam d’in da take ji da kuma k’yak’yayi a gabanta sai kawai ta shiga sako hawaye masu zafi, hannu tasa cike da k’arfin hali ta fara tureshi, da k’yar ya cire bakinshi a nata tare da sake damk’ar fuskarta ya d’aga yana kallo, hawayen dake zubo mata ne ya shiga saka harshenshi yana lashewa, saidai abun ya fi k’arfin d’aukar hankalin Mimi, sai labb’anta suka shiga rawa tana son yin magana hawaye kuma suka ci gaba da sintiri, cike da k’warewa ya tsayar da bakinshi kusa da kurmin idonta yana tsotse hawayen da zaran sun zubo.

Kasancewarsu a kusa yasa ana kiran sunanshi tayi gaggawar bud’a idonta wasu hawaye na fitowa, tar ta sauke cikin na shi idon tana son tace masa “Ana kiran sunanka.” Saidai ba wannan kuzarin.

Murmushi ya sakar mata cikin muryar da shi ma yasan ya sake tak’alowa kanshi fitina yace “Ryam…indai..baki daina zubo…da haway..nan ba…, to babu inda zan tafi.”

Rufe idonta tayi tana jin yanda yake ci gaba da murza nononta, sunanshi da aka sake kira yasa ta k’arfin halin ture hannunshi taja baya ta dangane a jikin motar, sake matsawa yayi daf da ita ya mata rumfa ya had’a goshinshi da nata, sumbatar bakinta ya sake yi yana murmushin mugunta, harshenshi yasa a kunne yana zagayawa dashi, tuni ta fara k’amewa tare da sarewa da lamarin old man d’in, dan wani irin abu take jin yana taso mata da shi da bata tab’a ji a rayuwarta ba, wani marayan kuka ta saki daya fallasa sirrin muryarta na halin data shiga ita kan ta na son a sosa mata wajen dake k’yaik’yayi, d’agowa yayi ya kalleta ba tare daya daina murmushin nan ba, k’wank’wasa glas d’in motar akayi, juyowa yayi ba tare daya d’aga daga rumfar daya mata ba, d’aya daga cikin jami’anshi ne sai kuma Hajia a can gefe, wani numfashi ya sauke wanda iskar bakin ya sauka a fuskar Mimi, sake rintse ido tayi inda shi kuma ya zauna daga rank’wafawar.

Hannunshi yasa aljihu ya ciro katinshi na banki na aikinshi na gwamnati, kamo hannunta yayi ya damk’a mata yana kallon fuskarta yace “Dan Allah Ryma ki kula da kanki, daga million d’aya har abinda yayi sama ki d’iba a asusun nan, amma ki sani *ba zan tab’a yafe miki ba idan kika nemi kud’i a hannun wani gara*.”

Sakin hannunta yayi tare da tallabo kumatunta ya manna mata sumba a goshi, fuskarta ya sake kallo yace “Ki shiryawa tarewarki kafin na dawo.”

Bud’e motar yayi ya fice tare da rufowa, wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke tare da sake jingina a kujerar, numfashi ta shiga saukewa d’ai d’ai hawaye sun kasa tsayawa a idonta, d’ora hannunta na dama tayi a k’irjinta ta dafe tare da katin daya bata, cak tunaninta ya tsaya ta rasa me zatayi inba hawaye ba da kallon titi.

Yana fita shima had’e fuska yayi sosai bai ko kalli jami’in ba ya nufi inda Hajia take tsaye, dake manyan kaya ne a jikinshi sai bai ji wani d’ar ba dan ya tabbatar asirinshi a rufe yake, sallama sukayi da Hajia a kunya ce kafin ya wuce ciki da hanzari ya samu Asas har yayi gaba ya barshi.

A tare Hajia da Kabiru suka shiga motar, tana jinsu amma sai ta kasa motsawa bare ta kalli b’angaren da suke, har suka fara tafiya Asma’u ma dreba ya d’auki hanyar mayar da ita gida, saidai Hajia ta ce ta dawo ta zauna tare da ita tunda bak’uwa a gidan har yanzu. Tunda Hajia ta fahimci yanayin Mimi tasan an d’an matseta ne sai batayi magana ba kawai har suka isa gidan sheikh, kallonta Hajia tayi tace “Mimi zan shiga na duba saina fito mu wuce.”

D’an k’yabta ido kawai tayi alamar to dan jikinta a mace yake sosai, shiga tayi ta sameta a falo ita kad’ai zaune yaran suna d’akin karatun mahaifinsu, yanda ta ganta ne yasa tana zama tace “Hafsat haka kike zaune gida ba zaki tafi asibiti ba?”

Murmushi tayi kawai tace “Hajia wallahi ni duk tsoron zuwa asibitin nake, bana so na je su fad’a min abinda zai d’aga min hankali ne.”

Cikin fad’a Hajia tace “Saboda haka kuma sai kiyi ta zama a gida har ciwo ya cimmiki? Ni sai naga kamar ma nak’uda kike.”

Zaro ido tayi tana dariya tace “Hajia nak’uda kuma? Wata shida ne fa da sati biyu.”

Tab’e baki tayi tace “To miye a ciki? Ba’a haihuwa a wata bakwai ne?”

Ajiyar zuciya ta sauke tace “Ana yi Hajia, amma bana fatan nayi.”

“To yanda Allah ya tsara ai shine daidai.” Cewar Hajia tana gyara zaman jakarta, jinjina kai tayi tace “Hakane.”

Kallonta tayi tace “Kinga tafiya zanyi, daga filin jirgin muke dama na ce bari na biyo naga jikin na ki.”

“Har sun tafi Hajia?” Ta fad’a tana k’ok’arin mik’ewa da k’yar sanda Hajia ta mik’e, tana gyara hijabinta tace “Sun tafi, sai fatan sauka lafiya da kuma dacewa.”

A sanyaye tace “Allah yasa a dace.”

“Ameen.” Hajia taa fad’a, saida suka kai daf da k’ofa Hajia tace “Tare da Mimi fa na ke.”

Wani fad’uwar gaba ta ji ya ziyarceta har saida ta furta “Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un.”

A tsanake Hajia ta kalleta tace “Lafiya?”

Girgiza kai tayi tace “Ba komai, bayana ne.”

Wani murmushi tayi tace “Kiyi hak’uri kinji Hafsat, insha’Allahu Allah yana tare dake, nasan kina mamakin wace irin uwace ni? Ni kaina Hafsat sai bayan na yanke hukunci na fahimci me na aikata, hakan ya tabbatar min da k’arfin dake a cikin *tafiyar k’addara*, na tabbata auren Mimi da sheikh shine rubuce a *laulil mahfuz*, Asas kawai sanadi ne na tabbatar da auren, ba kuma za’a rasa samun rabo ba.”

Jiki a sanyaye ta danne kukan dake son taho mata tace “Hajia baki mana komai ba, nima na gane aurenta da shi ne abu mai yiwuwa shiyasa ya yiwu.”

Jinjina kai tayi tace “Ni zan wuce, saida safe.”

“A gaida gida Hajia.” Ta fad’a tana kallonta, tana hangenta har ta shiga mota suka fita a gidan sai kawai ta sako wasu hawaye  zuciyarta tana fad’in “Allah ka bani juriyar cinye wannan jarabawa, hak’ik’a ba dan mahaifiyata bace da sai na nunata a matsayin wacce ta fi kowa tsanata a duniya, had’a min sheikh da wata mace ba k’aramin rud’u bane a tare da ni.”

Juyawa tayi tana share hawayen fuskarta ta koma ta zauna tana shafar cikinta tana tasbihi da hailala dan samun sassauci a zuciya.

Suna k’arasawa gida da k’yar ta kai kanta d’aki ta kwanta ruf da ciki tana rufe fuskarta da mayafinta, zumbur ta mik’e tana yakice mayafin a fuskarta, shinshinawa ta sake ta tabbatar dai k’amshin turaren shi ne, shinshina jikinta ta shiga yi sai ta ji kamar ita ta shafa shi, fad’awa ta sake yi rairan tana kallon sama a hankali ta furta “Ya Allah.”

Wasu hawaye ne suka taho mata masu zafi ta had’e wayu masu nauyi, yanayin da take ji wallahi kaamar ta k’wala masa kira ya dawo. (😳 Ya dawo yayi me uwata?)

                     *Sheikh*

Sararin samaniya suke jirgi na tafiya ba da gudu sosai ba, jingine yake a kujerar idonshi ruf kan shi na ta dawo mishi da abinda ya faru, wata masifaffiyar sha’awar yarinyar ke ciciyarshi, yanda yake lailaya kan mamanta saida ya ji sha’awar kai shi a bakinshi, lokaci ne kawai bai bashi damar haka ba, sosai yake ciki da bege da shauk’in kasancewa da ita.

Asas na gefe shi dai kallonshi yake yana murmushi, yasan abubuwa dayawa a ge da Mimi haka kuma baisan abubuwa dayawa a game da ita ba, babban abinda ya tabbatar yana birgeshi da ita kuma shi ma sheikh tunda namiji ne zai birgeshi shi ne k’amshi, akwai yawan anfani da tunani ga kuma iya d’aukar ado, riga t-shirt da zani zata d’aura sai kaga yarinyar ta bada kala sosai.

Sheikh kuma har maganganun Asma’u saida ya d’orasu a mizani, dan a wajenshi ta sake tabbatar mishi da Mimi fa tana bin maza a rayuwarta ta baya, lokacin data fad’i “Mimi da kake gani a zahiri haka bad’ininta yake…”

Haka kuma maganarta ta cewa “Ni k’awarta ce saidai akwai wasu halaye da na ta da muke samun sab’ani…” Tabbas ya yarda Mimi ce jarabawarshi a rayuwa, kuma a yau ya yarda d’ari bisa d’ari zai karb’i jarabawar da Allah ya mishi ya rumgume da hannaye bibbiyu, ba k’aramin abu bane musamman daya kasance babban mutum, yasan daga lokacin da za’a fahimta al’umma zasuyi mishi tofin Allah tsine, sannan za’a iya kafa mishi hujja da maganganunshi na wa’azi da yake fad’in “Mace ‘yar duniya ko a kyauta aka bâ wa namiji ita an cuceshi, an cuci zuri’arshi.”

Kusan kowa a wurin ya rintsa idonshi da sunan bacci amma ban da sheikh dake tunanin Ryam da abubuwan da suka faru daga d’aura aurensu zuwa yau.

Bayan awannin da suka kwashe sai gasu tsaye akan k’afafunsu Allah ya saukesu lafiya, su ma kamar sauran matafiyan abokin sheikh da kan shi ne ya zo ya d’aukesu zuwa gidanshi, duk da a wajensu ba dare bane a lokacin amma saida suka ci abinci sukayi wanka suka kwanta dan huta gajiya.

                      *Niger*

Sam a daren kasa bacci tayi, gaba d’aya tunanin sheikh da abubuwan daya mata ne ya tsaya mata a rai, ga masifaffen k’amshin turarenshi daya tsaya mata a jiki, har saida tayi wanka ta goge jikinta da kyau amma a banza, ga wani sabon yanayi daya bayyana a tare da ita, wani irin shauk’i ke d’ibarta kamar tayi kuka. Dap da asuba ta mik’e tayi alwala ta d’auro alwala ta shiga nafilfili duk ita d’in ba mai k’ok’arin yin nafilar bace, saida akayi sallah asuba ta gama duk azkar kafin ta kwanta rama baccin da bata yi ba.

                      *06:10*

Kiran wayarta ya tasheta, da k’yar ta bud’a idonta da sukayi mata nauyi sosai dan baccinta baiyi nisa sosai ba, ba tare data duba lamba ba kawai ta d’ora a kunne a magagin bacci da tunanin cikin k’awayenta ne tace “Hello, dallah miye haka zaki katse min bacci na? Wannan ai shiga hakk’i ne.”

Sautin k’ayataccen murmushi ta ji a cikin wata tausashiyar muryar data sakata bud’a ido sosai yace “Ki gafarce ni yan matana, na d’auka a daidai lokacin nan kina azkar ne, amma baccin na ki ma samun nutsuwata, a huta lafiya zan sake kira anjima.”

Cikin muryar rad’a yace ” *Ina k’aunarki*.”

K’it! Ya datse kiran ita kuma sororo ta bi wayar da kallo, wata ajiyar zuciya ta sauke tana tashi zaune ta gyara zama, murmushi tayi tana girgiza kai tace “Wai yana k’aunata, ko kunya baya ji ya haifeni yake fad’an wannan maganganun.”

Tab’e baki tayi ta yatsina fuska tace “Tsoho kawai.”

Kaikatawa tayi da niyyar komawa ta kwanta sai kuma aka k’wank’wasa k’ofar d’akin, mik’ewa tayi tana d’aukar kallabi ta d’ora a kan ta, tana bud’ewa taga Hajia da shiri da alama fita zatayi, da girmamawa tace “Inaa kwana Haji.”

Da kulawa ta amsa da “Lafiya lau Mimi, antashi lafiya?”

Ita ma da kulawa tace “Lafiya lau, Hajia fita zakiyi  ne yanzu?”

Cike da jimami tace “Fita zanyi Mimi, Hafsat ce jikin nan sai a hankali, zan je dai yanzu dole zan tisata gaba muje asibiti, dama dan na fad’a miki idan kin tashi ki d’ora abinda zaki ci ne dan tare da Salamatu zamu tafi.”

Da yanayin alhini tace “Ayya Allah bata lafiya, insha’Allah zan d’ora.”

Da fara’a tace “Yawwa to, kuma zan kiraki idan ma zamu iya jimawa a can dan kiji halin da ake ciki.”

Jinjina kai tayi tace “Zan ji dad’i idan ya zama babu wata matsala.”

“Allah ya tabbatar.” Ta fad’a tana d’orawa da fad’in “Anjima kkawarki zata zo Asma’u, dan naga ba zata ji dad’in zama a can ba shiyasa na ce ta dawo nan.”

Da fara’a tace “To shikenan, Allah kawota.” “Ameen.” Ta fad’a tana wucewa, bin bayanta tayi saida ta rakata har farfajiya, ido biyu kawai sukayi da Salamatu a k’asan mak’oshi tace “Na kwana.” A zuciyarta ta k’arasa da cewa “Lafiya.”

🤣 _Ku fahimta fa, ba gaisheta tayi ba fad’a mata tayi ta kwana lafiya._

Salamatu dai da kallo ta bita dan ita yarinyar tafi mata kama da masu shafar aljanu, saida ta ga fitarsu a gidan kafin ta koma ciki a falo ta zauna ta kunna tv.

*Alhamdulillah*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *