THE NEW EMIR (SARAUTA) CHAPTER 2 BY NIMCYLUV

 THE NEW EMIR (SARAUTA) CHAPTER 2 BY NIMCYLUV



Narkakkun idanunsa ya zubawa cikin Masarautar yana yaba ƙyanta da kuma tsarinta,komai na masarautar abin birgewa ne,sai ƙyalli da sheƙi take  faɗin kuɗin da aka kashe wajan tsara masarautar ɓata baki ne,taɓe baki yay tare da juya fararan ƙwayar

idanunsa,Wani Bafade ne ya ƙarasu wajan da sauri yana zuwa ya samu kansa da zubawa Captain kirari kamar wani sabon Sarki kana yace “Mai martaba yace akai ka masaukinka anjima yana nemanka fada”cewar ɗan aiken,shuru wajan ya ɗauka domin Saifudeen ko inda ɗan aiken yake bai kallah ba bare ya saka ran zai tankasa,jinjina kai Bafaden yay yana girmama girman izzar mutumin ko Lil prince baya wannan jan ajin,cikin gajiyawa da kallon da mutane suke masa ya ƙara gyara tsaiwarsa tare da lumshe lulu eyes ɗinsa masu firgitar da ƴar mace ta faɗa tafkin ƙaunarsa,ya ware laɓɓansa cikin muryar mai amo da sauti yace “I need to rest” ya faɗi hakan yana ware manyan idanunsa a kan ɗan aiken,sosai haiba da ƙwarjin Saifudeen suka zuciyar ɗan aiken cikin rawar jikin yace “mai martaba ya bada uwarnin kaika masauki saika biyoni”ya faɗa yana yin gaba,shima Saifudeen baya ya mara masa tare da yiwa drever’nsa wanda kuma ya kasance bodyguard  ɗinsa nuni daya biyosa,motar ya faɗa kana ya dinga binsu a baya a hankali har suka isa wani ƙaramin ɓangare a cikin gidan sarautar wanda ya kasance yana kusa ɗakunan barori da kuyangi,cikin rawar jiki ɗan aiken yasa kai ya buɗe ƙofar kana ya shiga ciki,sashin ya haɗu domin hadda bene a ɓangaren da aka kaisa,cikin hali na gajiya ya faɗa wani bedroom dake tsakiyar ɗakin yana shiga ya saka key ya kulle,direct bathroom ya shiga babu jimawa ya cire kayan jikinsa tare da tsayawa saitin shower ya sakarwa kansa ruwa,duka hannayensa ya saka ya dafe bango dasu kana ya sadda ƙasa ruwa’n yaci gaba da sauka a naked fresh skin ɗinsa mai ɗaukan idanu,lumshe dara daran idanunsa yay yana sauraran yadda ziciyansa ke bubu very past ba tare daya san dalili ba,tunda ya samu saƙon an turashi 9ja masarautar bilhas domin kula da lafiyar Mai martaba data ɗansa,ya samu kansa cikin tsoro da fargaba haka nan yake samun kansa cikin faɗuwar gaba,wani zazzafan numfashi ya sauke tare da ware manyan idanunsa ya ɗaga kansa sama ruwa’n shower ya soma sauka saman ƙyaƙƙyawar fuskarsa bai ɗauke fuskarsa ba saida yaji numfashinsa na shirin ɗaukewa,kana ya janye fuskarsa ya kashe shower’n tare da ɗaura alwala,wani ash ɗin towel ya ɗauka ya ɗaura saman waist ɗinsa kana ya ɗauki ƙarami ya shiga goge sumar kansa,saida ya tsane jikinsa sosai kana ya fito a toilet ɗin,cikin nutsuwa ya shiga shafawa chocolate skin ɗinsa versiline mai daɗi da kuma sauƙin zafi a jiki,yama gamawa ya ɗauki turare ya feshe jikinsa dashi,wani long blue ɗin jeans ya ɗauka ya saka tare da wata red ɗin riga mai hula wacce ta kama jikinsa sosai,hatta nipples ɗinsa saida suka bayyana,comp ya ɗauka ya taje sumar kansa tayi luff a kansa har zuwa wuyansa sai zabga ƙamshi da ƙyalli take,miƙewa yay ya shimfiɗa abun Sallah ya gabatar da sallar Asar kana ya faɗa saman bed ɗinsa cike da gajiya bacci yay gaba dashi.







Zarina’s pov

Tunda ta tashi da asuba tayi sallah bata ƙara ƙwanciya domin yin wani bacci ba,sosai tsoro da fargabar maganganun su  Zaitun ya cika mata zuciya duk yadda tayi ƙoƙarin fahimtar zancen nasu amma brain ɗinta yaƙi bata damar hakan,tana zaune rungome da teddyn ɗinta sai sauke ajjiyar zuciya take sbd kukan data sha,a hankali aka turo ƙofar ɗakin aka shigo,cikin murnar ganinsa ta miƙe da sauri ta isa garesa,idanunsa ta zuba masa tana son cewa wani abu amma ta gagara,Idanu Prince ya zuba mata yana mai jinjina baiwa da tsarin halittarta,sosai brest ɗinta suke dagula masa lissafi,amma yay alƙawarin bazai taɓa sex da ita ba,amma tabbas zai rage zafi,kuma yay alƙawarin kozai rasa komai nasa saiya mallaketa as his wife,kallo guda yay mata yaji ta ƙwanta masa kuma nada bada jimawa ba zai gabatar da ƙudurinsa wajan Mai martaba,Murmushi yay mata tare da ware hannayensa alamar tazu garesa,kasan cewar bata fahimtar komai sai abinda aka ɗurata a kai yasa batayi wani tunani ba ta shige jikinsa,saurin cire jikinsa tayi jin wani abu ya daki kanta,runtsa idanunta tayi da ƙarfi cikin rawar murya tace.

              “YA HALILU YA GAFARU”

Sai kuma hawaye ya wanke mata fuskar wani jira ya fara ƙwasarta,ganin zata faɗi yay sauri saka wani ya jawota jikinsa,ya salam Zarina ji tayi tamƙar ana watsa mata dalma a jiki hakan yasa ta soma fita a hayyacinta,numfashinta ya shiga ɗaukewa ta fara fisge² tamkar wata sabon kamu,wani shu’umin murmushi yay ganin yadda brest ɗinta suke tsalle cikin farar rigar jikinta,ɗaukanta yay cak ya nufi saman bed ɗin ɗakin da ita,kana ya shiga ƙoƙarin haɗe bakinsu waje ɗaya domin sosai wani maganaɗisun sha’awarta ke ƙwasarsa,dunda yake sex da mata bai taɓa jin sha’awarsu yana yine domin biyan buƙatar ƙansa,amma yau anwayi gari yay arba da macen da ko idanunta ya gani sai yaji mararsa ta murɗa,ganin da kaske so yake yay kissing lips ɗinta ya bata san lokacin data gantsara masa cizo da ƙwasa a guje kamar mahaukaciya tayi waje ba.





A ɗan firgice ya farka daga nauyayyen baccin daya ɗaukesa mai tarin mafalkai marasa daɗi,shuru yay ya shiga maida numfashi,zan ya nisa cikin zazzaƙar muryarsa mai amo da daɗi yace.


“ya ubangiji nayi tawassali da ƙyawawan sunayenka guda ɗari babu ɗaya ya Allah ka shigemin gaba cikin lamarina,bana damuwa da kowa da komai rayuwan talakawa dayi rantsuwa zan kare rayukansu shine gaba na,amma wannan baiwar Allah da nake tunani a kanta ta dameni,ta tsayamin a zuciya tana neman tarwatsamin brain da tunaninta ya rabbi idan Aljana ce ki rabu dani domin nayi imani da Allah nafi ƙarfinsa da yardar Ubangiji,idan kuma mutunce ina rokanki daki baiyana gareni ki gayamin abinda yasa nake mafalkinki”ya gare maganar yana langwaɓar dakai tamkar ƙaramin yaro,ganin lokaci naja ga kuma kiran da Mai martaba yake masa yasa ya miƙe a hankali tare da faɗawa toilet yay taken shower kana ya fito ya shirya cikin uniform ɗinsa na sojoji mai kalan amy colour,mai saka hula ba sai gyara gashin kansa daya kumayi kana ya fice daga cikin sashin gaba ɗaya ya nufi ɓangaren Fada wacce ya gani ɗazu.



A baki Fadar ya tsaya yana jiran ai masa iso,ɗan aikene ya dawo yace “Mai martaba ya baka dama”taɓe baki yay ganin yadda jikin ɗan aiken ke rawa sai kace wanda yay arba da zaki,cikin nutsuwa da kamala ya sanya kansa ciki Fadar bakinsa ɗauke da sallama,gaba ɗaya jama’ar Fadar suka zuba masa idanu hatta Mai martaba saida ya kallesa,Tiraki dake kusan mai martaba yace “he just look like Sufrak bilhas” kallon da Mai martaba yay masa yasa yay saurin sadda kansa ƙasa tare da faɗin “tuba nake”



Saifudeen bai tsaya wajan kowa ba ya tsaya gaban Mai martaba tare da sunkuyar da kansa ƙasa cikin girmamawa yace “Allah ya taimaki sarki na amsa kira”jinjina kai Mai martaba yay kafin ya gyara zama yace.



“Muna maka barka da zuwa masarautar bilhas fatan kasan dalilin zuwanka nan? Daka yau zakana kasancewa dani a Fada har a tashi daga zaman Fada,sannan dukkan wani taro da zani kana side ɗina sbd tsaro,muna son ka saka idanunka a kan kula da wannan masarautar,sannan aƙwai hukunci mai girma ga duk wanda ya shiga lambu ba tare da izini ba,haka nan kuma wajan dawakai,fatan zaka sanye idanunka a kan wannan guri biyun da muka faɗa?” lumshe idanunsa Saifudeen yay tare da shafa gefen fuskarsa mai cike da saje sosai ya kejin laɓɓansa sun masa nauyi harya kasa magana sai samun kansa da jinjina kai alamar gamsuwa da maganar Mai martaba,shikansa Mai martaba saida ya jinjina girman miskilancin Saifu yana tunanin irin halinsa yana kamar ya haɗa jini da sarauta,Mai martaba ne ya gyara zama sannan yace.



“zaka sami maid a cikin kuyangun gidanan wacce zata dinga kula da cinka da shanka da kuma kula da tsaftar muhalli,idan ka samu lkc saika duba ka ɗauki wacce tai maka,mun salleka zaka iya tafiya daka gobe aikinka zai fara”miƙewa Saifu yay ba tare daya ce komai ba,yabar Fadar.



Wayarsa ce ta fara ringing alamar kira,banza yay da ita yaci gaba da tafiya yana bada faɗi tare  lumshe idanunsa,wani kiranne ya sake shiguwa jin ringing ɗin yana da banbanci dana ɗazu yasa yay saurin picking tare da manna wayar a kunnansa,cikin shagwaɓa da zallar ƙauna yace.



“Abbuna nayi missed ɗinka kewanka ya dami zuciyana hope kana lafiya”ya ƙare ya turo bakinsa gaba kamar ƙaramin yaro,shuru yay yana sauraran abinda akece masa ta cikin wayan,wani ƙwataccen murmushi ya saki wanda ya baiyanar da lumawar beauty point ɗinsa haɗi da gap teeth  ɗinsa,cikin soyayya ce “you know i luv u so ban jure rashinka Abbuna and…”maganarsa ce ta tsaya ganin ta fito a guje kamar mahaukaciya gaba ɗaya gashin kanta ya hargitse har ba’a iya ganin fuskarsa,sosai ya zuba mata idanu musamman yadda waist ɗinsa ke juya ta cikon dugun farin wandon da aka bata,taɓe baki yay ba tare daya ɗauke idanunsa daga gareta ba,ganin ta nufi hanyar fita daga masarautar yashi faɗin “Abbuna i will call u lrt luv u”yana faɗin hakan ya tsinke kiran ya cillar wayar a aljihu,yadda take gudu iya ƙarfinta yasan cewa bata cikin nutsuwarta,tsaki yaka kana ya rufa mata baya da gudu.




*_😂wasa farin girki bana cewa komai aci gaba da karatu a kakkaɓe zani a gyara zama wannan shi ake kira da sabon salo😍_*

Gudu take iya ƙarfinta   ba tare data san inda take saka ƙafarta ba,sosai take cikin tashin hankali tsoro da kuma firgiji,babu abinda take gani cikin idanunta sai wani ƙaton baƙin dodo yana kawo mata cafka dason ƙwace daimond ring ɗin hannunta sai zalalo harshe waje yake,gane hakan yasa taci gaba da gudu tare ds jure dukkan wani zafi da raɗaɗin da ƙafarta keyi mata,burinta bai huce ta jita jikinta wanda zata samu nutsuwa ba,sosai take son tsira daga sharrin jibgegen dodo’n.
               Saifu ganin yadda take gudu kamar wata barewa ga kuma yadda ta kusa nawowa daf da ƙatutun ƙofar masarautar yasa shi ƙara ƙaimi tare da rufa mata yana mai jin haushin gudun da take,taku ɗaya zuwa biyu yay ya damƙo hannunta,ihu tasa ta shiga fisge² alamar ƙwatar kanta,hannu yasa ya ɗalle mata lips cikin ƙaushasshiyar muryar yace.
            “kee!  oya buɗe idanunki maza” ya faɗa yana zuwa mata fitinannun idanunsa,Zarina kam sam bafa fahimtar abinda yake cewa sabida wani irin tsoro daya kamata,cikin firgici ta buɗe manyan idanunta tare da kallon wani side ɗin nada ban,wata ƙaƙƙarfar ajjiya zuciya ta sauke ganin dodon ya juya da gudu fukafikinsa naci da huta,jikinta ne ya saki gaba ɗaya numfashinta ya tsaya ta faɗa jikinta babu numfashi,ɗan ware manyan idanunsa yay alamar mamaki,kasa aikata komai yay sai fuskarta daya zubawa idanu yana son ganin full face ɗinta amma gashin kanta daya zuba saman fuskarta yaƙi bashi damar gani,a kasalance ya miƙa hannu da niyar matsar da gashin fuskarta yay saurin tsayawa sabida muryar Lil prince daya daki kunnansa,tsayawa yay ba tare daya taɓa komai na jikinta ba.
     
“let her go”
Shine abinda prince ya faɗa lokacin da yake ƙarasuwa wajan cikin shigarsa ta ƴar ƴan sarauta,taɓe baki Saifu yay banda hali na taimako ita harta isa ya taɓa jikinta ba’a haifi wata ƴar macen da surar jikinta zata ruɗesa ba,tsaki yaɗan jaa a hankali kana ya sake ta faɗi ƙasa,yanayin yadda fuskarta ya sauya zaka san tabbas taji zafin faɗuwar,yana sakinta ya juya abinsa tare da soma tafiya cike izza da taƙama da kuma nutsuwar daya gama ratsa jinin jikinsa.
Tsayawa yay yana kallonta babu abinda ya zubawa idanu a jikinta irin ƙirjinta ganin yadda yake sama da ƙasa saiya bawa brest ɗinta dake cikin riga damar juyawa,wani wahalallan yawo ya haɗiye a ransa yana yaba ƙyawun halittar yarinyar,bai taɓa ganin yarinya mai ƙaramin shekaru da irin wannan girman halittar ba,sosai wutar sonta da ƙaunarta ke ratsa masa sassan jikinsa,tabbas yana jin zai aureta kuma ya zauna da ita matsayin yana sonta,zai zama mutum na farko daya karya tarihin masarautar bilhas,zai auri kuyanganrsa kuma zai zauna da ita,domin bazai iya jure kallonta haka ba,feelings ɗinta da ƙaunarta na neman wargatsa masa ƙwaƙwalwa,dole yaje ya faɗawa Mai martaba ƙudirinsa na auren *Kuyanga Zarina* da wannan tunanin ya saka dukkan hannunsa ya ɗauke,babu inda ya tsaya sai sashin da aka sauketa,yana zuwa ya ƙwantar da ita tare da zuba mata idanu cikin mayan sonta daya gama ɗibarsa yasa hannu ya shafi wuyanta tare da zura yatsansa tsakiyan brest ɗinta,lashe lips yay kana ya miƙe ya nufi wani ɗan ƙaramin fridge  gorar ruwa mai sanyi ya ɗauka tare da ɓalle murfin gorar ya sheƙa mata ruwan cike da mugunta,wata ƙyaƙƙyawar ajjiyar zuciya ta sauke.
Zabura tayi ta miƙe zaune tare da fasa komai,kanta ta juya ta fara ƙarewa ɗakin kallon,cikin muryar shagaɓa da kuka ta fara kiran “Mom! Abba! Yaya!”tsoro ne ya kama prince yana mamakin yadda maganin da suke mata harya wargatse,kallonsa tayi kana tace.
“who are you pls? Where is my Mom i want to see her dan Allah let go of me”ta faɗa tana sakin wani kukan,haɗe rai Lil prince yay cikin kakkausar murya yace “Mom!Abba!Yaya da kike babu abinda za suyi maki kingane,ki ɗauka dukkansu sun mutu kene kikai saura a wata duniya tada ban,duniyar ƙare kukanki babu mai jinki,sannan nayi alƙawarin da ƙarfin mulkina haɗi ikona da cikar izzata saina mallakeki matsayin mata ko kina so ko bakisu,tunda harni prince na amince da hakan tabbas saina aikata,kuma sonki da nake bazai hana naci maki uwa ba and ki cirewa zuciyanki tunanin wani idanma aƙwai,idan kuma babu fny kin tsira daga shiga ko mata” 
Tsoransa ne ya kamata gaba ɗaya jikinta ya shiga rawa kamar ana kaɗa mata gangi,cikin hukuncin Ubangiji ta shiga karanta addu’a lokacin da kaji tsoron zaluncin wani mai mulki,bakinta na rawa taci gaba da nanata addu’ar.
“اللهم رب السموات السبع ،ورب العرش العظيم ،كن الى جارا من (فلآن) واحزابه من خلا ئقك،ان يفرط علي احد منهم او يطفى،عز جارك،وجل تناوك،ولا إله إلا أنت .”
Ta ƙare addu’ar cikin kuka ganin kukan bashi da magani yasa ta miƙe tare da shigewa toilet tayi alwal dan bata jin zata iya wanka,abin sallah ta shimfiɗa kana ta zauna ta fara tilawar al’ƙurani cikin ranta ta daɗe a zaune kana akai kiran sallar magrib,miƙewa tayi ta gabatar da sallah kana ta mayar da sallar issha’i bayan taji anyi kira,tana zaune si Zaitun suka shigo hannunsu ɗauke da abinci da abisha kala² su dubilan,alƙaki, bakilawa,apple,inibi,da dai sauransu,bata kulasu ba haka Zaitun ta gama surunta ta fice a ɗakin cike da tausayin Zarina.
Ta daɗe zaune a wajan tana kaiwa Ubangijinta kukan cikin hawaye da kuma tausayin halinda take ciki a yanzu,sosai ta zurfafa tunani tana son tuna inda aka ɗaukota da kuma inda take a yanzu amma abun ya gagara,da wannan tunanin bacci ya ɗauketa ba tare data sanya komai cikinta ba.
Saifu zuciyarsa fal baƙinci ya shige side ɗinsa,shi kansa bai san ƙuncin daya samu kansa aciki ba,akan luntsumemiyar kujerar dake parlour ya zaune,wani zazzafan huci ya fesar daga cikin bakinsa,cikin ɓacin rai ya cusa hannayensa duka biyun cikin tulin sumar kansa ya hargitsa,cikin zazzaƙar muryarsa mai sauti da amo yace “who is she,why zan taɓa ta? Damn it”ya faɗa yana kaiwa ƙujerar dake zaune naushi,miƙewa yay da sauri ya shiga zagaya parlour can yay wani murmushi wanda ya tsaya iya laɓɓansa tare dajan gemunsa yace “ji banza wai let her go,bata tsarina bare kayi wani banza tunani da wata muryarsa ƙatuwa zai fasan kunne”ya ƙare maganar yana ƙwaɓe fuska,amma gudun me take haka? Kamar wata mahaukaciya ƙilama itama ƴar Mai martaba ce,ya ƙarasa maganar cikin ransa lokacin da yake samu waje ya zauna,ya mutsa fuska yay sosai cikinsa ki kiran yunwa,miƙewa yay ya nufi kichin  yana zuwa ya kunna gas tare da ɗura small put saman gas,ya ɗan jima kana ya ɗauki indomie ya zuba ya rasa tayaya zai dafa ta,ya nayi yana jaa baya,bayan indomie ta dafune yasa hannu zai buɗe murfin pot akai rashin sa’a tiriri ya daki hannunsa,da sauri ya saki pot ɗin tare da faɗin “auchiii”kashe gas ɗin yay yama hqr dayin girkin,bedroom ɗinsa ya shige tare da buɗe fridge  ya ɗauki hollandia da cake ya soma ci,bai wani ci da yawa ba ya ajjiye sauran,kana ya miƙe ya nufi bathroom wanka ya sakeyi kana ya sauya kaya ya nufi masallaci domin yin sallah magrib,bai dawo sashin nasa ba sai wajan 10pm yana dawowa ya kira abbunsa vedio call yayta zuba masa shagwaɓa kamar ba soja ba😂.
A 2weeks lrt
Haka Saifudeen ya kama aikinsa,koda yaushe suna tare da Mai martaba,haka zai ƙaraci tsaiwarsa gefen Mai martaba ba tare da yace ƙala ba,ko magana akai masa saidai ya jinjina kai alama yaji koya gamsu,a haka harya fara fahimtar Masarautar,a nan ya fahimci Masarautar ba irin Masarautar da yake tunani ba,Masarauta ce mai son kanta wacce bata damu da al’ummarta ba,burinta shine ta gina kanta,a nan ya fahimci zallar zalunci da akewa talakawa da ƙarfin mulki,tabbas idan yace ransa bai ɓaci ba yay ƙare bashi da ra’ayi shiga sabgar daba tasa ba,amma bazai iya ganin zalunci ya ƙyale ba dalilin hakan yay rantsuwa da alkur’ani akan zai kare rayukan talakawa da kuma dukiyoyinsu bisa gsky da amana,duk iya wannan tsayin lokacin Saifu bai taɓa ganin Zarina ba hasalima ya manta da ita.
Zarina an ƙara mata tsaro sosai inda take danko waje bata fitowa sabida tsaro,tayi kuka harta gaji kuma ta yarda da zancen Prince inda yake cewa ta ƙare kukanta babu mai jinta,waje ɗaya take jin daɗi idan taga Zaitun takan ɗebe mata kewa sosai harta mantar da ita abubuwa da yawa sosai take ƙaunar Zaitun ɗin kamar yadda itama take ƙaunarta,yanzu ma tana zaune tana karatun alkur’ani kamar yadda ta saba,turo ƙofar da akai itane yasa tayi saurin ɗaga jajayen idanunta ta saukesu akan ƙofar,ajjiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi ganin Zaitun,amma ganin halin da Zaitun ɗin ke ciki yasa ta zuba mata idanu,cikin kuka Zaitun tace.
“Zarina mun shiga uku,yau shine wa’adin da Mai martaba ya ɗiba a kanki a yau yake buƙatarki a tirakarsa,babu wanda yasan wannan zancen saini domin nice Kuyangarsa ta Amana,amma Zarina ban iya bari a cutar dake yaya zanyi domin na kare mutuncinki?”
Ware manyan idanunta tayi cike da tsoro kana kuma wani sabbin hawaye suka zuba cikin idanunta,alkur’ani hannunta ta rungome ta shiga rera kuka kamar ranta zai fita,wannan wacce irin rayuwace? Wannan wanne irin zamani muke ciki? Mai yasa shugabanni suke amfani da ƙarfin mulkinsu domin cimma nasaransu akan talakawansu? Shin shi kaɗai ne mai wannan halin ko duk sauran masarautu haka suke? Mai yasa akoda yaushe talaka shine a ƙasa? Mai yasa talaka bashi da wata power bashi da wani ra’ayi sai abinda shugabanninsa suka tsara masa.
Zaitun ma kukan ta saka ta rungome Zarina tana faɗin “Alfarmar Annabi da kur’ani ba zaki tuzarta ba,zanyi duk yadda zanyi na kare rayuwanki da dukkan ƙarfina da kuma ikona,dan Allah Zarina dukkan abinda nace maki kada kiyi musu kawai ki aiwatar kada ki sake ki buɗe wannan ƙofar inda bani bace nazu” tana faɗin hakan ta rugu da gudu tabar ɗakin.
Kukan Zarina ne ya tsaya tabi bayan Zaitun da kallo,hannu ta ɗaga sama tace “Ya Allah kaine gatanmu a wannan lokacin kaine zaka iya kiyaye rayuwarmu daga sharrin wannan mutanen,Ubangiji ka karemu da kariyarsa Ubangiji ka tsaremu da tsarewarka Ya gaffaru kayi mana gafara idan mutuwa ce hutu garemu Ubangiji ka ɗauki rayuwarmu mu hutu”ta ƙare addu’ar cikin wani kuka mai rikita zuciyar mai sauraranta.
Misalin 10 na dare,tana zaune tsakiyar gado tana rusar kuka,anyi mata shiga ta sarauta idan kaganta zaka ɗauka ta haɗa jini da sarauta sabida adon data sha,wasu kuyangu ne su biyu ne suka shigo cikin ɗakin,kana ganinsu kasan amintattun Mai martaba ne wanda suka san sirrinsa,suna zuwa suka kamata tare da miƙar da ita tsaye,sosai ta ƙara rushewa da kuka ganin da gske yau za’a rabata da mutuncinta,haka suka ɗauketa basu tsaya ko ina ba,sai Tirakar Mai martaba suna zuwa suka ajjiyeta saman luntsumemen gadonsa na alfarma,kana suka fice daga ɗakin,Cike da farin ciki Mai martaba ya fito daga cikin wani bedroom ɗin daga shi sai wani ƙaramin boxer  yana zuwa yasa hannu ya kashe hasken ɗakin,nan duhu ya bayyana a ɗakin,kukanta ne ya ƙaro cike da tsoro ta fara girgiza kanta alamar bata so,ƙara kusantuta yake yana zuwa ya fisgota ta faɗa jikinsa,cikin sauƙi ya zare kayan jikinta sabida nauyinsa daya sakar mata,cikin zumuɗi ya kaiwa brest ɗinta cafka sabida tsune masa idanu da sukai,sosai ya fara romantic ɗinta babu ji babu gani,banda kuka tana roƙansa magiya babu abinda take,hannu yasa ya zare pant ɗin jikinta kana ya ɗauki maganin da boka ya bashi ya tura mata a ƙasanta.
Da gudu ta fito daga ɗakin da aka kulleta ko ina na jikinta ɓari yake kamar mazari,tama rasa wacce hanya za tabi domin kuɓutar da ita,ƙara ƙwasa tayi da gudu ta nufi wata hanya inda rashin sani ya kawota ƙofar Tirakar Mai martaba,tsayawa tayi da kukanta sabida kukan data jiyo daga cikin ɗakin wanda ta tabbatar nata ne,shikenan abinda take gudu ya faru zuɓewa tayi a wajan tana rusar kuka kamar ranta zai fita,motsin da tajine yasa ta ƙwasa da gudu tayi wani ɓangaren,gaba ɗaya ta fice a hayyacinta kamar mahaukaciya banda kuka da kiran sunanta babu abinda take.
Yana tsaye yana amsa waya yaji anfaɗu jikinsa babu numfashi,cike da tsoro ya ƙatse wayar tare da tallafota zuwa jikinsa,ƙyaƙƙyawar fuskarta ya zubawa idanu saida numfashinsa ya kusa ɗaukewa sabida tsarin halittar ta,juyawa yayi domin yaga abinda ya bata tsoro koya biyota amma baiga komai ba,ganin wajan babu kowa kuma dare yayi,yasa ya ɗauketa cak tare da mannata da faɗɗan ƙirjinsa ya nufi sashinsa da ita,yana zuwa ya shimfiɗeta ya ɗauko ruwa mai sanyi ya shafawa fuskarta,a firgice ta farka tare da saka wani sabon kukan ta ƙanƙamesa tare da turo fuskarta tsakiyar ƙirjinsa,lumshe idanunsa yay yana sauraran yadda take cizonsa haɗi daya ƙoshinsa gaba ɗaya ta fice a hankalinta,dara daren idanunsa ya buɗe ya manna a kanta,ganin tana abu kamar mahaukaciya koda yay magana ba lallai tasan abinda yake faɗa ba,a hankali ya tallafo haɓarta ya zuba mata narkakkun idanunsa,cikin mutuwar jiki da kuma kasalan daya saukar masa ya ɗura jajayen laɓɓansa saman lips ɗinta tare tura halshensa cikin ƙaramin bakinta.
Cikin gushewar hankali da rikecewa haɗi da zaucewa Mai martaba yaci gaba da shigewa jikinta,a duk lokacin daya shiga jikinta yana jinsa a sama domin ya riga daya manta inda yake,bashi da wani buri daya huce samun gamsuwa da ita,sanadin shiga jikinta yasashi sanin cewa tabbas shiɗin lafiyayyen namijine mai jini a jika,a kanta kuma yasan cewa zai iya shafe a wanni saman mace ba tare daya samu gajiye ba ko kuma sinadarin jikinsa ya saki,san zuciyarsa da neman duniyarsa ya rufe masa idanu yayinda ya manta cewa ita ɗin budurwace bawai wacce ta nuna a harkarfa,yadda yake sakin jikin yana shige jikinta tare da sunbatu yana sakin magana kaɗai zaisa ka tabbatar ba ƙaramar shigarta yake ba,ya saki dukkan wani ƙarfinsa kuzarinsa lafiyarsa a kanta,zafi da raɗaɗin da ratsa jikinta haɗi da lungu da saƙo na sassan jikinta ya sata fice cikin hayyacinta,banda ƙiran sunan Allah babu abinda take,wata azaba ta musamman wacce bata taɓa jinta ba tunda tazu duniya ta keji tana ratsa ƙasanta,gaba ɗaya jikinta rawa yake yadda take fidda numfashi a galabaice zaisa kasan cewa ba ƙaramin nauyi ya sakar mata ba,gaba ɗaya jiniyoyin kanta sun tashi sunyi ruɗu² banda ambaliyar ruwan hawaye babu abinda ke fita a idanunta,a duk lokacin da zai shiga jikinta tana jine kamar ana suka mata wani mashi a ƙasance,ga wasu manyan dodanni da idanunta suke gane mata,sunyi masu ƙawanya sai zubawa Mai martaba wani jan abu suke saman kansa,wasu manyan tsutso na tashi sama suna reto kana su koma saman sumar kansa,dalilin hakan yasa ta ƙara rikicewa tsoro da fargaba suka ƙara saukar manta,iya rayuwarta bata taɓa ganin tashin hankali irin wannan ba,ko a film da story na books bata an taba aikata irin wannan ta asar da idanunta suke gane ba,tsananin ruɗewa da tayi da kuma yadda Mai martaba ya ƙara shige jikinta da ƙarfi yasa ta manta da wani salati lokaci guda kuma taji kamar an saka gudu an daki tsakiyar kanta,tsoro da fargabar da suka cikata ne yasa ta saki wata firgitacciyar ƙara.
         Mai martaba ƙara shagewa yay a kanta yana durzarta son ransa babu kunya cewa ita ɗin zata iya zama ƴar wajansa idan akai duba da irin manyan shekarunsa,wasu irin surututai yake shiba hausa ba shiba turanci ba kana shiba igala ba hakanan shiba indianci bare barbarci kana kuma azu feranch,yadda kalaman ke fita a bakinsa a harharɗe yay kama da wanda yake faɗin ɗalasiman tsafi,a kuma dai² wannan lokacinne yaji ta saki ƙara wanda ya tabbatar masa data je ƙarshe wajan azabtuwa a hannunsa,yadda ya kejin kansa a lokacin yasa bazai iya cire jikinsa daga nata ba,domin sai yanzu ya kejin wani ƙarfi da kuzari na zuwan masa.
    Ya zama aƙallah wajan 1hour da kusan rabi a jinkinta yana abu ɗaya,a wannan lokacinne kuma wata ƙyaƙƙyawar zufa ta soma saukar masa,jikinsa ya ɗauki rawa kamar mazari gaba ɗayan nauyin jikin nasa ya ƙara sakar mata kana ya shiga laluban wani ƙyalle cikin sa’a ya ɗauki ƙyallen ya shimfiɗa ƙasansa wata ƙara ya saki lkcn da yake zare jikinsa daga nata,take kowa wani farin abu mai haɗe da jini har wani hayaƙi yake yay tsartuwa saman ƙyallen,jikinsa yaja ya mirgina gefe wani ƙawataccen murmushi ya saki wanda yake nuni da zallan mugunta,a hankali ya miƙa hannunsa saman bed ɗin ya kunna hasken ɗakin,
Nan take wani haske ya gauraye ɗakin miƙewa yay zaune kana ya juya fuskarsa tare da ɗurata saman tata,wata zabura yay tare da faɗin “what! Zaitun fa?”.
Wani zazzafan numfashi ta sauke a hankali ta soma shige cikin jikinsa sbd jin tana samun relief daga ciwon data keji,wani sanyi da kuma nutsuwa ne ya soma ziyartar zuciyanta da gangar jikinsa,a ƙaro na biyu da ƙara shigewa jikinsa tare da tura duka kanta cikin faffaɗan ƙirjinsa mai yalwataccen gashi wanda yay ƙwance luff ganin sha’awa.
Lumshe idanunta tayi wanda ta kejin sunyi mata nauyin sbd yawan kukan da take,wani sihirtaccen ƙamshine ya fara kaiwa hancinta ziyara.
Wani ƙamshine na musamman wanda bata san kalansa ba,haka nan duk tunaninka da wahala ka fashimci wanne kalan parfume yayi using dashi a jikinsa.
Sosai ta samu nutsuwa da gamsuwa a jikinsa,ƙamshin parfume ɗinsa daya gama ratsa hancinta yasa ta soma fitar da wani numfashi mai zafin gske,a hankali kuma jikinta ya soma rawa alamar zazzaɓi nason kamata,hakan yasa ta ƙara shige jikinsa jin wani ɗumi na musamman na ratsa cikin jikinta daga jininsa zuwa nata, a hankali ta soma ware lower lips ɗinta a ƙoƙarinta nason furta wata kalman.
Lumshe sexcy eyes ɗinsa yay yana sauraran yadda take goga masa lips ɗinta a nipples ɗinta,wani irin baƙon nayanyi ya soma kawowa gangar jikinsa ziyara wanda hakan ya hadda miƙewar jijiyoyin kansa suka ruɗu² saman forehead ɗinsa,tabbas idan yace baiji wani abu game da ita ba ƙyarya amma yabar hakan matsayin rashin sabo,domin wannan shine karon farko da wata ƴar mace ta taɓa shiga jikinsa,hakan kuma ya hadda miƙewar gargasar jikinsa wani sanyi ya fara ratsashi,amma idan kaga fuskarsa ba zaka yaɓa cewa ya shiga wani hali ba,sosai yake da jure da kuma danne abinda yake ransa dan baison kowa yaga rauninsa yana ganin hakan shike sawa a raina.
Zafin zazzaɓin dake ratsa ɓangwan jikinta da kuma wani irin abu dake yawo saman fresh skin ɗinta,yasa ZARINA fashewa da kuka da soma kaiwa Saifu duka da ɗan ƙarfin daya rage mata.
Yadda take dukan nasa sai yaji tamkar ana masa  susa take basa,bazan iya jure wannan halin data sanya shi ba,hakan yasa ya zagaya hannayensa zuwa bayanta yay mata rumfa,a hankali ya soma jijjigata tare da ɗan bubbuga bayanta almar rarrashin dan aduniya baison yaga hawaye a idanun ƴar mace,sosai yake da zuciyar imani da kuma tausayin mata,shiyasa lkcn guda yaji tausayinta ya dirar masa a zuciya.
Numfashi mai zafi ta shiga saukewa jikinta gaba ɗaya ya saki hakan kuma ya tabbatar masa da bacci ya ɗauketa,wani murmushi ya saki ganin yadda gaba ɗaya ta shige jikinsa kana ganin yadda ta ƙwanta luff saman jikinsa zaka fahimci bata saba bacci ita ɗaya ba,cikin zazzaƙar muryarsa mai amo wacce take fitar da wani sauti na musamman yace.
     “you just look like cat”
Yana faɗin hakan ya taɓe baki kana ya miƙe da ita a jikinsa ya nufi duguwar sofa yana zuwa,zai ƙwantar da ita idanunsa ya sauka kan ƙaramin yatsanta ina a nan daimond ring ɗinta ya samu muhallin zama,runtsa idanunsa yay da ƙarafi ganin wani haske mai ƙarfi ya fito da cikin ring ɗin ya haske cikin idanunsa,kansa ne ya shiga sara masa take wani jira ya fara ɗibansa,sosai ganin ring ɗinta ya keson war gatsa mata littafi,ganin ring ba ƙaramin caza masa brain yay ba,cikin juriyarsa ta soldier  ya gyara tsaiwarsa ya auro dukkan wata jarumta ya sanya kansa,shimfiɗeta yay saman duguwar sofar kana ya cire babbar rigar sanyinsa ya rufeta da ita,remote ya ɗauka ya rage gudun a.c’n kana ya kashe hasken ɗakin,cikin nustuwa data gama ratsa jikinsa ya shige cikin bedroom ɗinsa.
Gaba ɗaya neman bacci yay ya rasa daga cikin idanunsa,daya rufe idanunsa ita keyi masa gizo tare da hasken ring ɗin dake hannunta,ƙwaɓe fuska yay tare da langwaɓar da kai tamkar zaiyi kuka yace.
           “Aljanata barni da tunaninki haka nan pls”ya ƙare maganar yana manne ƙirjinsa da pillow  ɗin bed ɗin,almost 1hour yana ƙwance yana zancen zuci kafin bacci ɓarawo yay nasarar ɗaukesa.
Tashin hankali Mai martaba ya shiga ganin Zaitun ƙwance tana sauke numfashin wahala yayinda blood yay faca² a ƙasanta,gumi sai yanku mata yake,wata zuface ta shiga yanko masa duk da irin sanyin a.c’n dake kaɗawa cikin ɗakin,yaya hakan ta kasan ce,mai yasa zaiga Zaitun mai makon Zarina?.
Wannan abun ba ƙaramin tayar masa da hankali yay ba,amma sauƙin da yaji ganin ya samu Zaitun cikakkiyar budurwa kuma age ɗinta zaiyi ɗaya dana Zarina,ya tabbatar maganin zaiyi aiki a jikinta.
Tsoransa guda ɗaya ne sabida kasancewar Zaitun kuganyarsa ce,amma ya yanke shawarar zai kira boka yay masa bayani,da wannan tunanin ya shige cikin wani ƙuryar ɗaki mai duhun gaske,wannan ɗakin ɗakine na musamman wanda babu wanda yasan mene cikinsa hatta ga Lil prince,yana shiga ya kulle ɗakin wajan 5minutes ya fara surutai haɗe da faɗin wani irin kalamai na musamman,ys daɗe ciki kafin ya fito ya faɗa toilet yay wanka ransa fes yaje ya nemi wasu amintattun  Barorinsa yasa suka ɗauki Zaitun suka maida sashinsu,kana shima ya ƙwanta bacci yay gaba dashi cike da sunbatu.
Washe gari
A hankali ya soma buɗe sexcy eyes ɗinsa wanda suke cike da bacci,domin har yanzu bai gama jinsa dai²,ƙara lumshe idanunsa yay jin still kansa bai bar sara masa,ga wani zazzafan zazzaɓi dake neman ɗaukansa,cikin yanayin kasalan daya samu kansa tun daren jiya ya ƙara buɗe idanunsa a karo na farko ya saukeso kan agogun ɗakin waro manyan dara daren idanunsa yay ganin har shida tayi baiyi sallah danshi tunanin irin tashin daren daya saba yay lafila yay,wannan wanne irin la’alallan bacci yay mara ma’ana,cikin zazzaƙar muryarsa wacce nutsuwa ya gama ratsa ya ware jajayen laɓɓansa yace “Damn sleepyn”kana ya zura da ƙyawawan ƙafafunsa,ya miƙe tsaye direct toilet ya nufa yana zuwa,ya sakarwa kansa shower kana yay brush ya ɗaura al’wala ya fito,bai damu da ruwan dake sauka daga tsakiyar kansa zuwa kan chocolate skin ɗinsa ba,haka ya nemi farar jallabiya ya zura a jikinsa,tare da ɗura hula irin ta makkah ɗinan wacce akewa laƙabi da tashi kafiya naci,masha yadda hulan ya zauna saman sumar ga yadda sumar yay luff saman wuyansa saika rantse cewa shiɗin baƙin balarebe wanda ya haɗa jinsi biyu,a sannaya ya shimfiɗa paryer mat kana ya tada kabbarar sallah ya soma rera karatunsa cikin zazzaƙar muryarsa mai amo da sautin,ya daɗe cikin karatun kafin yaje ga ruku’u haka shima ya jima ya miƙe ya nufi sujjada,haka ya gafatar da sallarsa cike da nutsuwa,sosai yake addu’ar neman tsari ga dukkan wanda yake nufinsa da sharri kana ya nemi yafiyar ubangiji bisa latti da yay,yana idarwa ya miƙe tare da,ɗaukan kayan traning ɗinsa ya sanya kana ya ɗauki ƴar ƙaramar bag ɗinsa ya zuba,gorar ruwa mai sanyi a ciki tare da fresh milk,ya nufi parlour.
Gaba ɗaya ya manta da batunta cikin sashin nasa,hakan yasa ya nemi hanyar ficewa daga cikin ɗakin,ba tare da tunanin komai ba,dan baya tunanin ganinta sbd ya manta da batunta.
Handle ɗin ƙofar ya kama zai buɗe ya jiyo shassheƙar kukanta,da mamaki a fuskarsa ya tsaya tare da tambayar kansa kukan wace ko waye?yaya akai wani yazu sashinsa bai sani ba?saman bag traning ɗinsa ya gyara a shouldersa kana ya juya a hankali tare da manne idanunsa a kanta,saurin lumshe idanunsa yay tare da dafe kansa sbd idanunsa da suka sauka gefen ƙirjinta,cikin ransa yace “Astagafirullah”ƙara ware idanunsa yay a kanta kana ya fesar da wani huci mai zafi ta hancinsa,yana mamakin abinda take masa a parlour har yau bata tafi ba,taimako ne yayi mata mene kuma take nema yanzu ya ƙare maganar cikin ransa yana taune laɓɓansa.
Ganin yadda jikinta ke rawa ga kuma yadda ta takure waje guda hawaye na ambaliya cikin idanunta ya tabbatar masa bata da lafiya,wani tausayin tane ya kamashi,cikin takunsa wanda yake nuna ainahin cikar zatinsa na kamalarsa haɗi da nutsuwarsa ya soma takawa gareta,durƙusawa yay a hankali ya zuba mata fitinannun idanunsa wanda suke ɗauke da wani saƙo na musamman,lumshe idanunsa yay a hankali kana shima ya taune nasa laɓɓansa,cikin wasu seconds ya ƙare ware idanunsa a kanta,ganin yadda take taune laɓɓanta har wani jaa sukai dan azaba ya sashin miƙa hannu a hankali ya saukesu a kan.
Yalwataccen gashin kanta wanda ya bazu saman fuskarta,runtsa idanunsa yay lkcn da ƙyaƙƙyawar fuskarta ta bayyana garesa,cikin nayanin mamaki da kuma al’ajabi yace.
“Aljanata”ya faɗa yana zuba mata idanunsu wanda suka soma juyawa zuwa jaa,ya kasa kasgatawa cewa ita ya gani hakan yana nufin ita ɗin mutunce ba aljana ba kamar yadda yay tunani a farko,a hankali ya ƙorawa ring ɗin hannunta idanu wanda ya haske masa idanu sbd sheƙin da yake,ƙara durƙushewa yay saman carpert ɗin tare da kamo hannunta ya haɗa da nasa wanda ring ɗin ke manne a jiki,wani ƙyaƙƙyawan haske ne ya haɗu waje guda sbd haɗuwar rings ɗin waje guda,cikin yanayin tsoro ya saki hannunta tare da miƙewa  ya shiga takawa zuwa cikin bedroom ɗinsa,saukar daddaɗan muryarta cikin kunnansa ya sashi tsaya,tabbas itace hakan ya tabbatar masa cewa ita ɗin mutunce,mai yasa ta tsaya masa a rai?,mai yasa take zuwar masa cikin baccinsa?,mai yasa suke ɗauke da zobe iri ɗaya kuma a yatsa ɗaya? Jin cool voice ɗinta ba ƙaramin sauya masa tunani yay ba,tayi amfani da muryar tausayi rauni muryar ɗauke take da neman taimako,a ƙaro na biyu yaji ta ƙara faɗin.
“Please help me”ta ƙare maganar muryata na rawa alamar kuka gaf yake da ƙwace mata.
Yadda kansa ke juya masa yasa shi fara ganin wani duhu jiri ya fara ɗibansa,cikin nuni da shiɗin cikakken soja ne maiji da isasshiyar lpa da ƙuzari,ya saka hannunsa ya dafe kansa dake barazanar tarwatse,tsananin sara masa da kansa keyi masa ne ya sashi taune laɓɓansa,jarumtar dake garesa ya sashi soma takawa zuwa bedroom ɗinsa idanunsa rufe,ba tare daya saurareta ba ko kuma ya duba halin da take ciki ya shige bedroom ɗin tare da banko ƙofar da ƙarfi ya murza key.
Zarina najin shigewarsa cikin ɗaki ta fashe da kuka zuciyarta na aiyana girman wulaƙancinsa,bashi da zuciyar imani da kuma tausayi,jikinta na rawa ta miƙewa tsaye a hankali ta soma takawa tare da niyar ficewa a sashin,zafin zazzaɓinta ne ya ƙaro lkcn da sassan jikinta suka fara amsar iskar da take kaɗawa a wajan masarutar,runtsa idanunta tayi tare da taune lips ɗinta,teeth ɗinta na haɗuwa waje guda suna bada wani sauti,a haka taci gaba da jan jikinta dan bata burin ci gaba da zama da mutum irin mara imani bare tausayi,tana fita sashin ta suka haɗu da Kuyanga Kulsum,cikin tashin hankali Kulsum ta kalli Zarina tace.
“Thank God you are fine,Zarina ina kika shige tun asuba muke nemanki shuru hankalinmu duk ya tashi?”zuba mata idanu kawai tayi ba tare data ce ƙala ba,sbd nauyin da zuciyarta tayi mata tamkar ansaka dutse an danne mata zuciya haka ta keji,wasu sabbin hawayene suka ƙara sauka daga cikin idanun Zarina su take tace wani abu amma ta gagara faɗa sbd nauyin da laɓɓanta sukai mata,gane hakan yasa Kulsum saurin kama hannunta wani tausayinta ya kamata,cikin muryar Kuka Kulsum tace.
“Mun shiga uku Zarina,wannan wacce irin rayuwa muke ciki ne haka?muna rayuwa kamar a bariki,muna rayuwa kamar prison wlh na gaji wannan abun yay yawa,ai mulki ba hauka bane,anci *ZARAFI* nmu ana nuna mana za’a iya komai damu da ƙarfin mulki,Zarina rayuwarki aƙwai matsala wlh damu dake duk muna cikin matsifa yanzu haka Mai martaba ne yaywa Zaitun faɗe gaba ɗaya bata gane komai banda sunanki babu abinda take faɗa,shine tun jiya nake bulayin nemanki amma babu ke sai yanzu da aka aikoni wajan Captain Saifu kawo masa breakfast na ganki,mene kike cikin ɗakinsa badai a can kika ƙwana ba?”Kulsum ta ƙarasa maganar cikin kuka da tsoro haɗi da firgici.
Kasa cewa komai Zarina tayi sai jikin Kulsum ta faɗa tana sakin kuka mai tsuma zuciyar dukkan mai saurare dama mai karatu,kukane wanda yake nuni da yankewar jin daɗin rayuwa,kukane wanda yake nuni da fidda rai dajin daɗi,kukane dake nuni inama Allah zai ɗauki raina na huta da wannan rayuwa,kuka ne dake nuni da zallar baƙin ciki damuwa ƙuncin zuciya,tabbas banda yazu a hadisi cewa idan mutum ya kashe kansa wuta ce masaukinsa babu shakka da ita da kanta zata kashe kanta,bata saba ba,bata san mene tashin hankali ba,tana jin kanta kamar wata sabuwar halitta sbd tension ɗin da take ciki,ganin kukan yayi yawa yasa Kulsum tsagaitawa da nata kukan ta shiga rarrashin Zarina,ƙara fashe Zarina tayi da kuka wanda hakan ya ƙara bawa zazzaɓin jikin damar ƙara ta’azzara,cikin Kuka tace.
“Nagaji i need to go back to my hause,ina tsoro ban iya wannan tashin hankali ina son tsira da raina da kuma mutuncina,wlh i’m tried”ta ƙare maganar tare da ƙanƙame Kulsum tana jinta kamar Mom ɗinta,kama hannunta Kulsum tayi suka ƙarasa sashinsu inda Zaitun ke ƙwance,suna shiga Zarina ta ƙwace hannunta tare da nufar inda Zaitun take a ƙwance tana zuwa ta faɗa jikinta ƙara rushewa da kuka,Murmushi Zaitun tayi wanda yafi kuka ciwo kan Zarina ta shafa tace.
“Masha Allah,Allah kaine abin godiya,tana daɗi da Ubangiji ya bani ikon kare mutuncinki naji daɗi da abin ya tsaya iya kaina bai shafi ƙimarki ba,Zarina ke haske ce a cikin wannan Masarautar,Da yardar Ubangiji saikin zama silar kuɓutar da rayukan jama’ar Bilhas,Ubangiji ya baki baiwa wacce ba lallai ke kisan da ita,ki cire tsoro a ranki ki fuskanci dukkan wani ƙalubale da zaki fuskanta,ki zama mai juriya kada ki taɓa bari prince ya fahimci rauninki?”ta ƙare maganar numfashinta na fusga da ƙarfi.
Ƙara ƙanƙameta Zarina tayi tana kuka tare da faɗin “No! Please kibar faɗin hakan mutun cina da naki duk ɗaya suke,mai yasa zaki bada kimarki ki adana ta wani,mai yasa zakimin hakan wlh kinsa zuciyata  ciwo bazan taɓa yafewa kaina ba,indan har wani abu ya sameki,bazan daina kuka ba indai har zakici gaba da kuka a cikin idanunki”ta ƙare maganar tana rushewa da wani sabon kuka,murmushi Zaitun tayi tare da guge hawayen idanunta kana ta riƙe hannun Zarina tace “Abu guda zakimin kisa zuciyata farin ciki ina son kiyi amfani da damarki ki ruguza ikon wannan masarautar ina son ya zamana kece kika kawo ƙarshen wannan zalunci,ina son ki ƙwatarwa jama’ar bilhas ƴan cinso da baiwar da ubangiji ya baki,wannan zuben na hannunki ba haka nan yake zaune a hannunki aƙwai ɓoyayyen abu tattare dashi,tabbas zaki nasara a kansu”da faɗa tana sakin wani murmushin kafin tana idanunta ta rufe,da sauri Zarina ta shiga girgizata tare da faɗin “Tashi dan Allah wlh bazan iya komai babu ke ba,na amince da dukkan abinda kikace kuma zan aiwatar amma ina buƙatarki cikin rayuwata”cikin sannan fitar hayyaci da kuma ɗaukewar numfashi Zaitun ta buɗe idanunta tare da kama hannun Zarina ta ruɗa bisa saitin zuciyarta tace “kinji yadda zuciyata ke aiki ko?to kada ki damu ina tare dake koda yaushe ban bari a cuceki,ina son ki ƙulla alaƙa mai ƙarfi tsakaninki dame Babban ɗaki zan rubuta maki wasu bayanan wanda zaki buƙacesu,Kulsum ɗauketa kuje waje domin tayi wanka ta sauya kayan jikinta ki bata abinci taci zanyi kewarku gaba ɗaya”ta ƙare maganar idanunta na fidda ƙwallah,kuka Zarina tasa tare turjewa haka Kulsum taci gaba da janta har suka fice a ɗakin.
Ajjiyar zuciya ta sauke lkcn da taga sunbar ɗakin,wasu hawaye ta fitar daga cikin idanunta,sbd yadda ta kejin ana zuba mata wani abu a jikinta kamar narkakkiyar dalma haka ta keji,rufe idanuta kana ta buɗe da sauri ganin wani jan abu ya gilma ta cikin idanunta,a hankali ɗakin ya shiga girgiza wani ihu ya soma karaɗe cikin ɗakin,wata guguwa ta shiga bayyana kamar ƙiftawar idanu haka wata jibgegiyar halitta ta bayyana a gabanta,tana zalalu halshe gaba tare da fiddo da banyan haƙwaranta masu tsayi da kuma tsini,sbd tsoron da yayi mata yawa kasa motsawa tayi bare tayi tunanin yin wata addu’ar kamar yadda ta saba,ihu da ƙara ta saki lkcn da halittar ta damƙi wuyanta ta shaƙe,cikin ɗaukewar numfashi Zaitun ta shiga faɗin “La’ilah ha’illahu Muhammadul rasulullah S.a.w”tana faɗin hakan numfashi ya tsaya idanunta suka ƙafe sukai fari jikinta ya saki a wannan lkcnne kuma halittar tayi wurgi da Zaitun kana ta fara wani ihu tare da jijjiga wata sabuwar guguwa ta bayyana kafin wani lkc halittar ta ɓace ɓat.
Su Zarina na fita suka nufi wani ƙaramin ɗaki a nan Kulsum ta haɗa mata ruwan wanka mai zai kana ta fice da ɗakin,zuciyarta cike da tsoran halin da suka bar Zaitun,dircet ɗakin da Zaitun take ciki ta nufa tana zuwa ƙofar ɗakin taji kamar an daki kanta,dan haka ta juya da sauri ta nufin inda tabar Zarina tana zuwa ta sameta harta kammala wankan ta fito,kaya da ɗauko mata farare tas kana ta bata aminci,ƙincin amincin tayi sai kuka da take tana kiran Heart dream and Mom,nan Kulsum ta fahimci zazaɓin dake jikinta da ƙyar ta rarrasheta taci abincin kaɗan ta bata magani tasha,ƙwantar da ita tayi bata bar ɗakin ba,sai da taga tayi bacci kana ta rufe ƙofar ɗakin tayi waje.
Bata ƙarabi dakan Zaitun ba,ta koma sashin Kilishi domin yi mata aiki daman acan take ba,tana ƙoƙarin shiga,taji an fisgota ta faɗi ƙasa kafin ta buɗe idanunta taji an wanketa da mari,cikin ƙaraji Lil prince yace.
“Ina Zarina ina kika ɓuyeta?”ya faɗa yana kai mata wani marin,kuka Kulsum ta shiga faɗin “nima rabona da ita tun jiya munyi nemanta mun rasa”ta ƙare maganar tana sakin wani kukan,wani marin Lil prince ya ƙara kai mata kana yace “ohh sannu ni zaki maida ɗan iska ɗazu zanje Fada naganki tare da ita yanzu kice ba haka ba,ok good”ya faɗa yana bawa Fadawa umarnin suka mata sukaita ɗakin duhun,koda wasa bai yarda a gata abinci ba bare ruwa”kuka ta saka tana neman yafiya amma yay burus ya shige sashin Kilishi,haka Fadawan suka janta zuwa ɗakin duhu wanda yake da nesa da cikin gidan sarautar.
Saifu’s pov
Tunda ya shige ɗakinsa ya zube kan bed ɗin ɗakinsa ya shiga juye a kansa,tunani ne fal cikin ransa babu abinda ya tsaya masa a rai sai ƙyaƙƙyawar fuskarta da kuma daimond ring ɗinta wanda ya kasance iri ɗaya da nasa babu banbanci,ya daɗe a wajan domin har akai a zahar yana wajan a ƙwance yana tunani,ganin tunanin bashi da wani amfani ya miƙe ya nufi toilet kayan traning ɗinsa ta cire ya saƙale kan hanger,shower ya sakarwa tare lumshe idanunsa ruwan na dukan ƙyaƙƙyawan naked chocolate skin ɗinsa,babu abin ɗaukan hankali jikin Saifu irin muɗaɗɗan faffaɗan jikinsa,saidai ba ko’ina yake a murɗe ba,amma kallo guda zakai masa kasan cewa shiɗin lafiyayyen mutum ne mai ta ƙama da cikakkiya da kuma kuzari,sosai yake da tsarin halitta mai jan hankali da kuma ɗaukan hankalin ƴan mata, six packs on his body  shine abu na biyu mai ɗaukan hankali,wani zazzafan huci ya fesar ta cikin bakinsa,kana yasa duka hannayensa ya dafe jikin bango ruwan ya shiga dukan bayansa,ɗan ya tsuna fuska yay sbd mararsa data ɗaure masa,when zai daina ciwon mara sai yanzu zai daina wahala da wannan banzan feelings ɗin,a hankali yasa hannu ya shafa sumar mararsa tare ɗan matsawa da ƙarfi,ƙara runtsa idanunsa yay sbd zafin da yaji ya rasa sassan jikinsa,wajan 30minutes ya ɗauka kana yay brush ya ɗaura alwala,a nan toilet ɗin ya busar da sumar kansa,kana ya fito yana zuwa ya nufi dressing mirrow inda aka shirya masa kayan shafarsa,wani lotion mai ƙamshi ya ɗauka ya shiga shafawa jikinsa,yana kammalawa ya fesa jikinsa da body spray,kana ya taje kanta ya shafa mai a sumar kan,wajan wadrope ya nufa ya ɗauki wani blue black ɗin long jeans ya sakawa jikinsa,sannan ya ɗauki rigarsa ta sojoji ya saka a jikinsa,sosai yay ƙyau cikin shigar da yayi,covet shoe ya ɗauka ya sakawa kansa,kana ya ƙwashe wayoyinsa,ya fice a ɗakin,bai ko kalli inda take ba,dan yasan zuwa yanzu ta gaji ta bar masa ɗakin,yana fitowa ya nufi masjid domin gabatar da sallah,bai daɗe ba ya fito ya nufi hanyar Fada domin amsa kiran Mai martaba,yana gaf da shigewa Fada ya hangi Fadawa na jan wata a ƙasa,ɗan waro idanunsa yay ganin Lil prince biye dasu,ransa ne ya ɓaci idanunsa suka rufe,cikin takunsa na isa sa izza ya fara takawa izuwa garesu,suna ƙoƙarin janta wani ɓangaren ya buɗe baki tare da dataka masu wata uwar tsawa hatta prince saida ya firgita,cikin taƙaicin abinda sukewa matar ya nufusu gadan-gadan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *