MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 8
Na Samira Harouna
👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨
*MATAR MUTUM*
_(K’abarinsa)_
👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*’YAN AMANA TA*
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*29*
Wani k’ayataccen murmushi ya sakar mata tare da jawota gaba d’aya ta kusa fad’awa jikinshi, d’an kashe mata ido d’aya yayi yace “Kin fad’a min ‘yan matana, amma ai lafiyarki tafi komai a wajena.”
Kallon ka tausaya min ta bishi da shi sharrr hawaye na dararowa a idonta, Rakiya dake kallonsu ce tace “Malam ko dai a bata magani ne? Dan naga kamar ba zata bari mu d’auki jininta ba bare muga zazzab’i me take.”
A hankali ya kalli Rakiyar saidai bai ce komai ba dan abinda ya fahimta shi ma kenan, kuma shi dai ba zai iya dagewa ya matseta a jikinshi ba, ganin haka ya tabbatarwa Rakiya me yake so, dan haka ta koma ta zauna mazauninta ta shiga duba magunguna da dama ake ajewa wasu na zazzab’i ne na rigakafi, Mimi dai na kallonta a ranta fad’i take “Shi ma ba sha zanyi ba, dan kin bar abinki ma kin bawa wani.”
Sheikh ta mik’a tare da fad’a mishi yanda zata sha, godiya ya mata ya mik’e hakan yasa Mimi mik’ewa ita ma, shigewa yayi gaban yayi da Mimi ke fad’in “Sai anjima.”
Da fara’a Rakiya tace “Sai anjima madame, daure a sha magani fa.”
Murmushi kawai tayi ba tace komai ba har suka fice, yanzu ma dai nesa da shi ta tsaya har saida ya shiga mota kafin ta k’arasa da sauri ta shiga ita ma, a d’an hassale ya kalleta yace “Wai kunyar me kike ji na jerawa tare da ni? Ryam abun k’yama ne a jikina?”
Da sauri ta zaro ido baki bud’e tace “Ni? Wallahi ba ha…”
Hannu ya kai kamar zai bugi bakinta yana fad’in “Komai zaki fad’a sai kinyi rantsuwa, me yasa babu gaskiya a lamarinki ne wai?”
Mar-mar-mar! Tayi da idonta tare da nok’e kanta kamar wata mage tace “Kayi hak’uri to na daina.”
K’wafa yayi ya aje mata ledar maganin a cinyarta yana yi wa motar key, kallonta ya sake yi sanda yake k’ok’arin hawa kan titi yana fad’in “Ni ne kika kalli idona a gaban kowa kika kira tsoho ko?”
K’wafa yayi yana jinjina kai, cikin turo baki ta d’anyi gunguni hakan yasa shi hararanta yace “Me kika fad’a?”
Girgiza kai tayi alamar a’a, wani mugun kallon ya mata yace “Na fad’a miki ki koyi fad’an gaskiya, bana son k’arya Ryam ina tsanar mai yin ta, dan alamomi a cikin alamar munafiki.”
A hankali ta jinjina kai alamar gamsuwa, saida ya d’auki hanya kamar an bar zancen sai kuma ya kalleta yace “To yanzu fad’a min me kika fad’a?”
A d’an gigice ta kalleshi a ranta tana fad’in “Matsalar tsofafin nan fa kenan jinini.”
A zahiri kuma cewa tayi “Ina tsoron na fad’a kayi hushi.”
K’uri ya mata da ido yana kallo sai kuma ya d’auke kanshi yace “Ba zanyi ba, zan kwatanta halin annabi Muhammad (S.A.W), har ma na had’a miki da halin dattijon arzik’i sahibin fiyayyen halita Abubacar Siddiq, bayan banyi hushi ba har sai na yafe miki ma sannan na miki kyauta.”
Baki sake tace “Dukana zakayi?”
Kallonta yayi yace “Bana duka, saidai akwai hanyoyin da nake ladabtar da marasa jin magana irinki.”
Kallon titi tayi tana d’an kumburo baki, kamar daga sama ya sake fad’in “Ina jinki fa.”
Kallonshi tayi tasa hannu da hijabinta ta rufe bakinta, cikin muryar rad’a tace “Dama kawai…cewa nayi..ai sa’an Abbana ne.”
Da sauri ya kalleta ita ma da saurin ta fashe da kukan shagwab’a tace “Ai ka ce min ba zaka dakeni ba, kuma kai ka ce na daina yin k’arya.”
K’ank’ance idonshi yayi tare da d’auke kai yana girgizawa, kawai ya tabbatarwa kan shi wannan bata cika shekara sha takwas ba, shi kam ya zaiyi da ita yanzu? Shiru sukayi suka ci gaba da tafiya har ta gaji da kukan sakarcin ta daina, saida yaji tayi d’ip ya d’an saci kallonta, yanda ta rakub’e tare da dunk’ule jikinta tana kallon titi zai tabbatar maka har yanzu bata jin dad’in jikinta, murya a d’an dak’ile yace “Zan baki kyautarki zuwa gobe insha’Allah.”
Jinjina kai tayi alamar to, da haka suka isa gidan, a farfajiyar ya sauketa ta tunkari shiga ciki, da kallo ya bita har ya hangi Hajia ta tarbeta tana ta tab’a jikinta, lumshe ido yayi ya bud’e ya feso iska yana fad’in “Ina ma baki lalata k’uruciyarki ba.”
Jingina yayi a kujerar motar ya sake lik’e idonshi, a hankali abinda ya faru a asibitin ya fara dawo mishi, a gaskiya ya tabbatar mace ce har da k’ari, dan kuwa a yanda yaji indai ba gizo ko rud’un zuciya bane, to yaji komai ya nuna kuma a tumbatse yake. Wani dogon tsaki yaja sakamakon tuna waccen ranar da aka mata tereren nan, hakan na matuk’ar tayar masa da hankali, yana jin zafi da kuma d’aci a zuciyarshi idan ya tuna k’aramar yarinya kamar waccen tasan ta bayar da kanta a bata kud’i tayi sutura mai kyau da tsada sannan ta rik’e k’atuwar wayar da mahaifinta zai iya jan jari har da d’aukar nauyin gkdan shi ma. Saida ya ga b’acewarsu ita da Hajia sun shige falon kafin ya ja motar ya bar gidan shi ma.
A falo Hajia ta zaunar da ita duk da har a lokacin akwai sauran mutane, abinci tasa aka kawo mata dan ta ci tasha magani, saidai rashin k’warin jiki da d’and’ano a baki ga kuma kunya yasa ta kasa cin komai, sai madara ta d’an sha ita ma saida yan uwan Hajia suka sa baki.
Magani Hajia ta b’alla ta mik’a mata, girgiza kai tayi kamar zatayi kuka tace “Um um.”
Harara ta cilla mata tace “Ban gane um um ba, takwara karb’i nan kisha kafin kiji a jikinki.”
Karb’a tayi amma ta rik’e a hannu ta kasa sha, cike da rarrashi Hajia tace “Yawwa yar albarka shanye kinji, saboda lafiyarki ne ai, ko kina so ciwo ya kwantar dake ayi ta d’irka miki allurai?”
Girgiza kai tayi alamar a’a, wata tsohuwa dake zaune sun gama shirin tafiyarsu ce tace “Ki barta ai kar ta sha, idan zazzab’i ya kayar da ita ni ba abinda zai hanani yi mata siraci da ganyen darbejiya.”
Murmushi Hajia tayi tace “Haba Hajia ai ba za ayi haka ba, amarya guda ta kwanta rashin lafiya kuma bata arzik’i ba.”
Kallon Mimi tayi tace “Kinga yar albarka shanye kinji, dubi fa guda uku ne kawai.”
Cikin marairaicewa tace “Idan nasha amai zai sakani ne.”
Girgiza mata kai tayi tace “Ba zakiyi ba kinji, idan kika saka a ranki zakiyi ne shiyasa kike yi.”
Sake marairaicewa tayi ta d’an d’aga hannunta tana so tasha, sai kuma ta sauke tana rintse idonta, ganin haka yasa Hajia kallon wata yarinya a cikin yaran bak’in tace “Ke Khadija tashi madafa d’auko min muciyar nan ki gani, na ga ita ma kamar d’an gidana ne wajen rashin son magani.”
Dariya mutanen d’akin sukayi inda Mimi ta shiga rarraba ido tana kallon hanyar madafar da yarinyar ta nufa da kuma Hajia, tsohuwar nan ce tace “Shi ma fa haka yake bai son magani, kuma kai gashi Allah ya jarabeka da ciwo.”
Cike da jimami Hajia tace “Ki bari kawai Hajia, Ashraf idan zai sha magani saina titseyeshi da mabugi kafin yasha.”
Da mamaki wata ta kalleta tace “Mabugi fa? Da girman na shi?”
Cike da tabbaci Hajia tace “Wallahi kuwa, har yau har gobe idan zai sha magani sai raina ya gama b’aci na rik’e abun duka.”
Kallon Mimi tayi tace “Da fari da yake fad’a min aurenshi zai zama silar warakarshi na d’auka ke d’in zaki jajirce ne wajen kula da maganinshi, ashe kema kamar shi d’in ne a rashin son magani.”
Dariya tsohuwar tayi tace “Ashe da an taru an lalace.”
Sunkuyar da kai Mimi tayi dan k’awarta ce kawai ta zo mata a rai, “Ko ya ta kwana a gidan?” Shi ne abinda ta tambaya, cike da k’arfin hali ta d’aga kan ta ta jefa k’wayar magani d’aya a baki ta kora da ruwa da sauri, tana had’ewa ta sake jefa sauran idonta duk a rufe kamar zatayi amai, tana had’ewa aje kofin tayi tare da mik’ewa dan nufa masaukinta, kallonta Hajia tayi cikin tausayi da tunanin maganar Asas da akayi ne ta jawo mata sabon yanayin, rik’e hannunta tayi tace “Kinyi waya da mamanki kuwa?”
Girgiza kai tayi a hankali tana jin amai na taso mata, da d’an mamaki tace “Me yasa to? Ya kamata ki kirata ki gaisheta, kinsan uwa mace tana kwana cikin zulumi da fargaba a ranar da aka d’auki ‘yarta zuwa gidan wani da sunan aure.”
A hankali ba tare da ta fahimci zancen Hajia ba tace “Bana da waya ne.”
Zaro ido tayi tace “Ba kya da waya? A’a ai wannan kafin kiyi aure kenan, yanzu wuce ki kwanta zan kira *mijinki* na fad’a masa.”
Da wani irin kallo Mimi ta bita kafin ta d’auke kanta tana jin kamar ta d’ora hannu a kai tace “Wayyo ni wayyo kaina.” Wai mijinta, mutumin daya haifeta shi ne ake kira mijinta? Ohh wannan wace irin rayuwa ce? Da k’yar ta kai kanta d’aki ga aman dake taso mata ga kuma rashin k’warin jiki. Tana shiga da gudu ta shige ban d’aki ta sako aman nan, kaf maganin da tasha ta amaye kafin ta kuskure baki ta fito ta kwanta a galabaice.
*Asa-Ma’u*
Da safe daga gidan Hajia aka aika musu da abun kari, bayan sun karya kuma Asas ya fita ya bar gidan ba wata hira a tsakaninsu, da fitarshi ba jimawa yayarta Rayya ta zo gidan bisa umarnin mamansu, kayanta data zo mata dasu ta shiga gyara mata har da wasu kayan aiki na mata da mamanta ta tara mata da kwanukan cin abinci, saida ta gama gyara mata komai a lokacin k’anwar Mamansu ma da kuma yayarta suka zo.
Sosai Asma’u ta ji dad’in zuwansu dan sun mata nasiha da nuna mata tayi hak’uri sannan ta shiga jikin mijinta amma fa ba da fitsara da bud’ewar ido ba, anan har suka d’an dafa mata tamtabaru ta ci aka bata zuma tasha, da taimakon Rayya sukayi girkin rana mai rai da lafiya dan kauan abinci babu abinda babu, haka suka ci suka k’oshi suna raharsu har saida sukayi sallah la’asar suka tafi, lokacin ita kuma ta shiga d’ora girkin dare a nutse ta fara da gyara namanta, duk da ba wani girki ta iya na zamani mai kyau ba, amma dake Mimi uwar jaye-jaye ce da shige shige, wannan ma data d’ora yanzu Mimin ta ga sun tab’a yi ita da Maimuna shiyasa ta fara, hakan yasa ma sai taji kewar k’awarta da tunanin ko me take yanzu? Ya take a sabon gidan data samu kanta?
Daf da magriba ta kammala ta gyara komai ta tsaftace gidan kamar ba tayi ba, ganin magriba ta gabato sai tayi alwala ta fara yin sallah, tana idawa ta shiga wanka tana jin kamar kar ta fito a ban d’akin, har yanzu zuciyarta ta kasa yarda ita ce a wannan daular, ta kasa yarda ita ce ta auri mijin da k’awarta tayi muradin samu, ta kasa yarda ita ce dai Asma’u ta auri Asas namijin da har k’awayensu gulmarsa suke wajen had’uwarsu akan komai.
Tana fitowa a sauk’ak’e ta shirya cikin shaddar da sukayi ita da Mimi da niyyar suyi shigar bikin Mimi da ita a musu hotuna kafin su canza na d’aukar amarya, saida ta gama shirinta a tsanake lokacin har an gama sallah isha’i ta fito falon tana baza k’amshinta. Cak ta tsaya gabanta ya buga da k’arfi sakamakon ganin Asas zaune yana kallo fuskarshi a had’e sosai, rarraba ido ta shiga yi da tunanin me za tayi?
K’amshin turarenta ne ya kai mishi a hanci da sauri ya juyo inda yake jin k’amshin, yana ganinta yayi saurin lumshe ido tare da hango surar Mimi a idonshi, farar fuskarta mai d’auke da dogon hanci da kakkauran labb’a da matsakaitan ido, ajiyar zuciya ya sauke tare da bud’e idonshi a hankali ya sake kallonta, k’ak’aro mata murmushi yayi tare da mata alama da hannu “Zo.”
A hankali cikin ruwan sanyi ta k’arasa tana daddafe cikinta dake motsawa, tana zuwa gefenta ta tsaya kusa da k’afafunshi ta zauna k’asa, da sauri ya nuna mata kan kujera yace “Zauna a nan.”
Girgiza kai tayi alamar a’a, shiru yayi ya na d’an kallon fuskarta da tayi kwalliya mai sauk’i ko gira bata zana ba, shi kuma a yanda yake son matarshi ta kasance mai cab’a kwalliya da ado ne kamar ba gobe. Jin bai ce mata komai ba yasa ta bud’a bakinta daya mata nauyi tace “Ina wuni?”
A dak’ile ya amsa da “Lafiya lau, ya gida.”
Kasa amsawa tayi dan duk a duburburce take, sam bata tab’a ganin irin wannan had’ewar a tare dashi ba, kullum tsakaninsu wasa ce da raha irin ta mijin da k’awata zata aura da kuma aminiyar amaryar da zan aura, mik’ewa tayi kamar an cijeta ta kalleshi tace “Na kawo maka abinci ne?”
D’aga manyan idonshi yayi ya kalleta, sai kuma ya mayar da kallonshi kan tv yace “Um.”
Da sauri ta juya hakan yasa shi bin bayanta da kallo, wani murmushi ya saki mai kama da kuka saboda tuna yanda *lokaci* yayi k’uli-k’ulin Rakiya da shi ya canza masa komai, duk da bai tab’a mata kallon daya wuce k’a’ida ba kula bata tab’a tsayawa gabanshi cikin shigar rashin kamun kai ba, amma dai a yanda yake ganin sittin saba’in a cikin hijabin Mimi yasan ba k’aramin kaya ta mallaka ba, duk da kuwa ita ma Asma’u tana da su saidai kawai a *barwa rai abinda ya ke so.*
Kan k’aramin table ta aje kwanukan ta shiga zuba mishi hannayenta sai rawa suke, tana idawa ta aje mishi gabanshi ta koma gefe a k’asa ta zauna, cikin jin haushi ya kalleta yace “Ya zaki dinga zama a k’asa? Koma sama.”
Da sauri ta mik’e ta zauna kan kujerar tana mayar da kanta k’asa, jawo plate d’in yayi ya fara cin abinci a wani yatsine kuma a yangance, ita dai da ta ji ta k’osa da zaman sai ta mik’e tace “Da wani abu da kake buk’ata na yi maka ne?”
Wani irin kallo ya jefa mata yace “Kamar me?”
Yanda ya mata tambayar yasa Asma’u saurin durk’usawa tace “Kayi hak’uri.” Mik’ewa tayi har tana had’a hanya ta bar falon ta shige d’akinta, da kallo ya bita sai kuma ya d’an ja tsaki ya ci gaba da cin abincin dan ba laifi ya masa dad’i a baki.
Yana idawa yasha ruwan data zuba mishi ya mik’e da kanshi ya d’auko lemu a fridge ya dawo ya zauna, kallo ya shiga yi tare da giccirawa yana kuma tunanin abinda ya faru ranar *juma’ar jiya* wacce ta gigita mishi komai na shi, bai gushe a nan ba saida 11:00 ta buga kafin ya mik’e ya kashe komai ya nufi d’akinshi, shiryawa yayi cikin kayan bacci kafin ya dawo d’akin Asma’u dan kawai ya zauna d’akin kar ya bar yarinyar mutane ita d’aya.
Yana shiga tuni ta jima da baccinta a cikin doguwar rigar bacci, kitsonta ya fito ras dan d’an kwalin ya fad’i, kashe fitilar yayi ya kwanta gefenta ba tare daya rufa da zanin data rufa ba.
*Mim-Sheikh*
Bayan sallah azahar Shapi’a ta zo gidan ganin Mimi, yanda ta sameta babu lafiya sai taji kamar ta mata kuka, Hajia ma cikin zulumi da jimami take fad’in “Kin ganta wallahi da zazzab’in nan ta kwana, tasha magani na d’auka yayi sauk’i ashe a banza, kuma sun je asibiti ta ce ba’a mata allura ba, ta sake shan magani da k’yar amma har yanzu jikin.”
Kallon Mimi Shapi’a tayi tace “Mimi da bata son magani, anya kuwa tasha?”
Cikin rashin sani Hajia tace “Na fari dai bata nayi na fita, amma bayan dawowarsu daga asibiti a gabana tasha.”
Cike da kallon tuhuma ta kalli Mimi tace “Kin tabbata baki amaye shi ba Mimi? Na fa sanki a kan magani.”
K’asa tayi da kanta tana layi tana so ta koma ta kwanta, Hajia ma dake kallonta cewa tayi “Kenan da gaske maidoshi kikayi?”
Shapi’a ce tace “Tabbas indai Mimi, da wuya ai ta had’e magani ya zauna mata.”
Hab’a Hajia ta rik’e tace “Oh Allah! To kinga ko mijinta zan kira ya maidata asibiti a k’ara mata ruwa ko allura?”
Jinjina kai Shapi’a tayi tace “Gaskiya kam, dan a hankali yanzu nan tsaf zata rasa jini a jikinta.”
Waya Hajia ta ciro zata kirashi Mimi tasa kuka tana fad’in “Dan Allah karku fad’a masa, aunty ai kinsan Mamana jibda take shafa min ko? Dan Allah ki ce karta kirashi a shafa min jibda zan daina.”
Dakatawa Hajia tayi ta kalleta tace “Kin tabbata?”
Cike da tabbaci tace “Wallahi jibda Mamana ke shafa min duka jikina saina daina.”
Juyawa Hajia tayi zata fita tana fad’in “Abu mai sauk’i, dana sani ma tun tuni da ba an wuce wajen ba.”
Fita tayi sai Shapi’a data kalleta tace “Yanzu Mimi me ke anfanin haka? Kina bak’unta ma amma sai an gane halinki na taurin kai?”
Turo baki tayi tace “Amma aunty ai kuma kunsan bana son magani ko.”
“Mun sani Mimi.” Ta fad’a tana tsareta da ido tare da d’orawa da fad’in “Amma ko dan bak’uwar fuska ai sai ki sha.”
Sake turo baki tayi tace “Ai nasha maidoshi ne nayi.”
Jinjina kai tayi tace “Dama zuwa nayi naga ya kika kwana, mamanki da tace ma ba sai na zo ba tunda dai bâ gidanki bane aka kawoki, ni dai nace sai na zo dan bai kamata ace babu wanda ya zo dubaki ba kamar wata marar dangi.”
Kyab’e fuska tayi tace “Aunty ita Mama sai yaushe zata zo?”
Zaro ido tayi saidai kafin ta bata amsa Hajia ta shigo rik’e da kwalbar jibda babbar a hannunta, tana zuwa mik’awa Shapi’a tayi tace “Gashi to shafe mata jikinta.”
Karb’a tayi tana dariya da fad’in “Kina ji da ita ko? Wai yaushe mamanta zata zo?”
Dariya Hajia tayi tace “Mamanki zata zo amma bayan tarewarki gidan mijinki.”
Hira sosai suka sha har kusan la’asar Shapi’a bata tafi ba kuma sosai jikin Mimi yayi sauk’i dan har wanka tayi ta canza kaya, Hajia na mamaki sosai yanda ita jibda ce maganin zazzab’inta duk da tasan dama tana magani da dama.
10:30 daidai ya kawo k’ofar gidan, mai gadi na bud’e mishi zai shiga kawai ya tuna da akwai fa wani nauyi a kan shi, tunda suka dawo daga asibiti bai sake sanin abinda ke faruwa ba, dan ko Hajia basuyi waya ba saboda hidimar dake gabansa, juya akalar motar yayi dan ba zai yarda hakk’in k’aramar yarinyar nan ya zamar masa babban nauyin da zai kasa saukewa ba.
“Bawan Allah…” Wannan sunan data ambata ne ya dawo a kunnuwansa, wani k’asaitaccen murmushi ya saki tare da sake murz sitiyarin dan yau kam shi kad’ai ya wuni yawo a gari yana fad’in “Marar kunyar yarinya kawai, gata yar firit amma firita ce a jininta.”
Da wannan ya isa gidan su Hajia tare da tunkarar falon kan shi tsaye…
*Alhamdulillah*👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨
*MATAR MUTUM*
_(K’abarinsa)_
👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*’YAN AMANA TA*
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*30*
A tausashe ya rabka sallamar da tasa Salammatu amsawa tana kimtsa zamanta daga kallon tv, kamar zata nutse k’asa dan girmamawa ta shiga, gaisheshi, da girmamawa shi ma ya shiga amsa mata dan ba yarinya bace, cike da kulawa yace “Hajia tana ciki ne?”
Nuna mishi d’akin Mimi tayi tace “Ta shiga ciki zata dubata.”
Da ido ya amsa alamar to tare da nufa d’akin, da kallo ta bishi da mamakin yanzu nan fa aka barshi da yarinyar can fitsararriya sai ka ganta da ciki wata rana, tab’e baki tayi tana mayar da kallonta kan tv da fad’in “Maza ho.”
K’wank’wasa k’ofar ya fara yi daga ciki Hajia tace “Waye?”
A sanyaye yace “Ana.”
Da fara’a tace “Shigo sheikh.”
A hankali ya bud’a k’ofar tare da d’ora idonshi akan Hajiar dake tsaye, bai yarda ya kalli inda ya tabbatar tana nan ba saida ya gama gaisawa da Hajia, cikin sakin fuska take fad’in “Da na ga dare yayi ai na d’auka ba zaka zo ba, kuma dana tuna kai ne fa sai na sa a raina zaka zo komai dare.”
Wani lallausan murmushi yayi tare da d’an shafa sajenshi yace “Hajiarmu kenan, sabgogi ne dayawa, har zan shiga gida kuma na taho.”
Da fara’a tace “Allah sarki, Allah ya bada ladar d’awainiya.”
“Ameen.” Ya fad’a tare da d’an kaikata idonshi ya kalleta, da sauri ya ji zuciyarshi ta fara bugawa, doguwar riga ce a jikinta ta bacci mai laushi, kan ta kuma babu d’an kwali sai gashinta data d’aure, jibda ce take k’ara shafawa a jikinta gaba d’aya.
Tunda ya shigo bata kalleshi ba, kuma sam bata da niyyar zata kalleshi sai murzawa hannayenta jibda take, d’an cije leb’enshi yayi na k’asa kafin yace “Ya jiki?”
Sai lokacin ta d’aga kai ta kalleshi, a cikin ranta tayi k’wafa tuna abinda ya mata a asibiti da tunanin “Zan rama, sai na mayar da kai kamar *kakana*.”
Sakin fuskarta tayi tace “Da sauk’i *malam*.”
K’uri ya sake mata da ido da nanatawa a ranshi “Malam?”
Hajia dake ta murmushi tana kallonsu ne ta d’an gyara murya tace “Bari na baku wuri ko.”
Da wani matsiyacin sauri Mimi ta kalleta tace “A’a Hajia, ba abinda zai min.”
A lokacin shi ma yayi saurin juyawa cike da kunya yana fad’in “A’a Hajia, saida safenku.”
Amma jin abinda Mimi ta fad’a sai yasa ya tsaya ya sake juyowa, sai kuma ya jinjina kai ya juya zai fita, bayanshi Hajia ta bi tana fad’in “Dama ina son magana da kai.”
Da kallo Mimi ta bisu da addu’ar “Allah yasa ta masa maganar wayata, ina so na samu waya.”
Suna fita a falon ta zauna a kan kujera, tunda ta ga ya zauna a k’asa ya tabbatar mata yau uwa ake da ita kenan, dan akwai ranar da zasu zauna kan kujera ita dashi, to ranar ana matsayin malami kenan, cikin dattako ta k’ara gyara zamanta tace “Sheikh, nasan nayi maka hawan k’awara a lamarinka a game da auren nan, saidai ka sani ba nayi bane dan na nuna na isa da kai, na tabbata auren nan zai zame maka alkairi insha’Allah, ina fatan baka k’ullaceni ba ko?”
Da sauri ya girgiza kai yace “Subhanallah Hajia! K’ullata kuma? Ko d’aya wallahi, na d’auki hakan a matsayin abu ne da dama Allah ya rubuta zai sameni, tabbas da ita d’in ba *matata* bace da ban sameta ba ko da kuwa ina son haka.”
Jinjina kai tayi tace “Naji dad’in haka, yanzu maganar tariyarta nake so naji, yaushe ka tsara?”
Sunkuyar da kai yayi yana mai jin kunyarta sosai, to shi ya zai ce? Ya fad’i ranar da za’a kawo masa tsarar Aisha? Shiru kawai yayi ya kasa magana har saida Hajia tace “To idan ya maka mu barshi a sati d’aya, lokacin na tabbata ka gama gyara mata na ta b’angaren.”
Numfashi ya sauke a sanyaye yace “Allah ya sa haka shi yafi zama alkairi.”
“Ameen.” Ta fad’a ita ma, d’orawa tayi da “Sannan sheikh dan Allah kayi hak’uri da yarinyar nan, kaga fa shekarunta k’alilan ne, dole sai kana kawar da kai da hak’uri, inba haka ba zatayi abu a cikin k’uruciya kai ka ga kamar wauta ce ko kuma da gangan.”
Jinjina kai yayi yace “Insha’Allah za’a kiyaye Hajia.”
Murmushi ta masa tace “Naji dad’i, Allah ya maka albarka, sai kuma magana ta gaba.”
Jinjina kai yayi alamar saurare, d’orawa tayi da “Waya na ce me zai hana ka siya mata? Kaga zata dinga kiran iyayenta ai.”
Da wani irin k’arfi ya d’aga kai ya kalli Hajia yana kiran “Waya kuma?”
Ita ma da mamakin yanda taga firgici a tare dashi ta amsa da “E, waya.”
Iska ya feso tare da duk’ar da kanshi yana ambatar “Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un.” Shi ya siya mata waya? Yarinyar da baisan irin girma da mahimmancin data bawa waya a rayuwarta ba, idan fa ya bata ta ci gaba da rayuwarta data saba, har shi fa sai Allah ya hukuntashi dan yana da kamasho. Cikin nutsuwa da salon bayar da umarni Hajia tace “Zan jira zuwa gobe da safe sai ka kawo mata.”
Lumshe ido yayi tare da d’an sinne kai ya jinjina shi alamar to, shiru babu wanda ya sake magana har saida ya d’an tank’ware k’afafunshi yace “Hajia.”
Da kulawa ta amsa da “Na’am.” D’orawa yayi da “Ki fara shirin aurar da jikarki Eesha, insha’Allah na mata miji kuma bana tunanin za’a d’auki lokaci mai tsayi.”
Da fara’a sosai tace “A’a masha’Allah, wannan ai abun farin ciki ne, Allah ya sa alkairi ya nuna mana ranar.”
A sauk’ak’e ya amsa da “Ameen.” Jim ya d’anyi kafin yace “Hajia ni zan wuce gida.”
Mik’ewa dan ta fahimci so yake ta mik’e kafin yayi tsaye a kan ta shi ma, a hankali ya mik’e sukayi sallama a mutumce tana fad’in “A gaishe min da mazajen kwabon nan.”
Murmushi yayi yana amsawa da zasu ji ya fice kamar yace “Wayyo Allah.” Hajia ta umarceshi ya siyawa Ryam waya, me zatayi da ita? Su wa zatayi mu’amula dasu? Ko dai ma ita ta ziga Hajia kan a siya mata wayar? Da tunane tunanen nan ya isa gida.
*Saminu*
“Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un!” Abinda ta fad’a kenan sakamakon ganin Saminu zigidir babu kaya a jikinshi da wayarta a hannunshi yana kallon hoton Mimi wanda sukayi ta d’auka ranar kamu, yana kallonta yana ta lailaya dokinshi a dole yake son biyan buk’atarshi daga kallonta, juyawa tayi hankali a watse zata fita, da gudu ya biyota ba tare da jin nauyin jikinshi ba yana d’aura towel d’in shi yana kiran “Maimuna, Maimuna tsaya kiji.”
Juyowa tayi a hassale ta kalleshi tace “Me zan ji? Wannan wace irin rayuwa ce? Me kake aikatawa haka dan Allah?”
Fashewa tayi da kuka hankali tashe cikin son rarrashi ya rik’o hannunta, da k’arfi ta fizge tana fad’in “Karka k’ara tab’ani.”
Da alamar rarrashi yace “Naji to shikenan, amma dan Allah ki saurareni, Maimuna ba abinda kike tunani bane, wallahi…”
Sai kuma ya rasa me zai fad’a, sake juyawa tayi ya yi saurin shan gabanta yace “Ina zakije Maimuna? Dan Allah ki rufa min asiri, na yarda nayi laifi ki yafe min kinji.”
Cikin sako hawaye tana kallon fuskarshi tace “Dama kana sonta ne? Ko kuma dai gaske ne abinda nake ji a gari a game da kai na neman mata?”
Da sauri ya girgiza kai yace “Ko d’aya Maimuna, wannan jita-jita ne na mutane karki yarda, Mimi kuma kamar ‘ya ko k’anwa take a garemu ai, ban tab’a jin haka a kan ta ba.”
Cikin d’aga murya tace “To me yasa kake kallonta kana son dole sai kaji dad’i ta haka? Fuskarta ce ke birgeka ko kuma albarkatun jikin da Allah ya hore mata?”
Sassauta murya yayi yace “Ba haka bane, Maimuna ina da buk’ata ne kuma ke naga kina saurin gajiya dani, bana so na zama mai takura miki shiyasa ban nemeki ba.”
Tsareshi tayi da ido tana kallon fuskarshi, ta jima haka kafin ta sauke numfashi tace “Alhaji zan daina maka k’orafin gajiya idan ka min alk’awarin ba zaka sake kula mata a waje ba.”
Da sauri jiki na rawa yace “Na daina, dama kuma bana yi wallahi, yanzu muje to.”
A sanyaye ta bi bayanshi suka koma d’akin, d’auke wayar yayi ya aje gefe tare da kwantar da ita akan gadon, saidai tsaf abinda bata sani ba yana saduwa da ita ne amma kuma a idonshi Mimi yake gani, zuciyarshi ta gama haska mishi ita tare da k’awata mishi ita, musamman idan ya tuna kwancin nan nata a asibiti, yanda nonuwanta sukayi carrr daga sama kuma yake iya hangen matashiyarsu jajir dashi, ga s’uwawunta da suka kwanta akan gadon su ma sosai. Da haka har ya samu biyan buk’atarshi saidai babu gamsuwa dan hankalinshi a wani irin yake.
*Ahalin Mimi*
Aje abincin tayi gabanshi tare da zama gefenshi tace “Malam gashi.”
D’an zabura yayi ya kalleta da alamar nisa yayi a tunani, Yaseen da Amir da suke gefensu ne suka kalleshi Amir na fad’in “Abba kaga yau ma mama shinkafa ta dafa mana har da nama.”
Kallonshi yayi yana dariya yace “Da gaske? To ka k’oshi dai ko?”
Da dariya shi ma yace “E, Abba.”
Murmushi yayi tare da jawo kwanon gabanshi zai fara cin abincin, da sauri Mama ta mik’e ta koma gefe kusa da k’ofar shiga ban d’aki, durk’usawa tayi ta shiga kwaranya amai, mik’ewa yayi hankali ya tashe ya k’arasa gareta yana fad’in “Subhanallah, uwar uwata lafiya? Baki da lafiya ne dama?”
Kakarin aman ta take yi bata kulashi ba, saida ta gama ya bata ruwa ta kurkure baki, mik’ewa tayi ta zauna kan tabarbar tana dafe kanta dake ciwo, gabanta ya zauna yana fad’in “Rabi’atu, baki lafiya dama? Me yake damunki?”
A hankali cikin muryar galabaita tace “Ba komai, ba wani abu bane.”
Da kulawa yace “To ko gajiyar bikin nan ce?”
Da sauri tace “E ita ce.”
Yanda ta bashi amsar ya sa mishi shakku, kallon tuhuma ya mata yace “Uwar uwata, ko dai Amir zaki wa k’ane?”
Da sauri ta kalleshi tana rufe baki tace “Kai.” Sai kuma ta kalli su Yaseen, su ma su suke kallo, cike da kunya ta mik’e ta shige d’aki, dariya yayi tare da bin bayanta ya sameta zaune, kusanta ya zauna yana fad’in “Masha’Allah Rabi’a, nagode miki kinji, hak’ik’a wannan abun alkairi ne da farin ciki, Allah ya rabaki da abinda ke cikinki lafiya.”
Sunkuyar da kai tayi tace “Malam kunya nake ji wallahi, mun aurar da ‘ya kamata yayi ace mun aje wannan gefe yanzu.”
Da mamaki ya kalleta yace “Iyeeeh! Kaji min matar nan, me zamu aje gefe d’in? Haramun muka aikata?”
Turo baki tayi ta sake yin k’asa da kanta, mik’ewa yayi yace “Uwar uwata fito ki ci abinci kinji, bayan wannan ma idan da wani rabon ni zan antayo dashi zuwa duniya.”
Baki wangale ta kalleshi tace “Inna lillahi! Rashin kunya.”
Juyowa yayi ya nunota da yatsa yace “Ke Rabi fita idona in rufe, na lura take-taken iya shegenki ne duk uwata ta d’auka, har take kallona ni da sheikh take fad’a mana tsofaffi.”
Dariya Mama tayi ta sunkuyar da kanta, fita yayi ya zauna ya fara ci abincin cike da farin ciki a zuciyarshi, Mama kuma bata sake fita ba a k’arshe ma Yaseen da kansu sukayi shinfid’a suka taka kujera suka d’aura gidan sauro.
*Mim-Sheikh*
Da yake ba mai son zama da hijabi bace yanzu ma haka ta fito daga ita sai riga da siket d’inta na leshe, simple d’inki ne mai rap-rap amma dake tana da jiki sai ya mata wani irin kyau ya zauna a jikinta, gashinta data d’aure tayi irin d’aurin daya fi birgeta wanda tsakiyar gashin ke fitowa ta zauna a gadon bayanka. Duk da ta hangeshi amma bai dameta ba, k’arasowa tayi a sanyaye tana furta “Assalama alaikum.”
Da fara’a Hajia ta amsa da “Wa’alaiki salam, takwarata kin tashi?”
Da ladabi ta zauna k’asa kusan k’afarta tace “Na tashi, ina kwana?”
“Lafiya lau, ya jikin naki? Da sauk’i ko?”
Da fara’a ta amsa “Da sauk’i sosai.” A hankali ta d’aga idonta ta kalleshi, karaf idonsu suka had’e dan kallonta yake a lokacin ganin wani wata arniyar shiga da tayi, da sauri ya janye na shi idon yana fad’in “Astagfirullah wa’atubu ilaikh.”
Sunkuyar da kan shi yayi har sanda siririyar muryarta ta dakeshi tana fad’in “Ina kwana malam?”
Da sauri Hajia ta kalleta tana murmushi, saidai bata ga laifinta ba dan bata san abinda yake so ba da wanda baya so, kallon sheikh tayi da a lokacin ya d’ago matsakaitan idonshi ya zuba mata harara yace “Ban ganshi ba nima, kun had’u dashi ne?”
Kallonshi tayi sai kawai tayi mar-mar-mar da ido tace “Allah huci zuciyar gafarta.”
Da sauri Hajia ta gumtse dariyaarta dan ta fahimci wata yar tsama ce ke numen kunno kai tsakanin d’a kuma sirikinta da sabuwar amaryar ta shi, kwalin wayar dake gefenshi ya d’auka ya jefo mata sai a cinyarta, da sauri ta kalleshi sai kuma ta d’auki kwalin tana dubawa, a zuciyarta ta furta “Samsung galaxy.”
Muryarshi ta ji a d’aure yana fad’in “Hajia tasa na siya miki waya, ki kula ki kuma san abinda zakiyi da ita, wallahi na kamaki da wayar nan kina abinda bai dace ba jikinki zai fad’a miki.”
Kallonshi tayi a raunane tace “Amma malam ai ka ce baka dukan mutum, ni fa banaa son duka wallahi.”
Bud’e baki yayi da jinjina rashin kunyar Ryam, gyara zama yayi ya nunata da yatsa yace “Ki jaraba yin abinda zan dokeki ki gani, ke sai na d’aureki kafin zan sa a zane min jikinki da tsumagiya.”
Galala tayi sai kuma ta kalli Hajia ta sunkuyar da kanta, cikin muryar son yin kuka tace “Ai Hajia ta ce ni amanarta ce, babu wanda zai dakeni ta k’yale mutum.”
A d’an hassale yace “Ke…” Sai kuma yayi saurin kallon Hajia, jinjina kai yayi irin zamu had’u d’in nan, Hajia dake ta son kecewa da dariya rufe baki tayi, yau kam tana ganin ikon Allah, ko abokan wasa fa yanzu sun ajiye wasar gefe guda basa yin ta da sheikh, amma kaga yarinya yana fad’a tana fad’a, shi kuma har da wani biye mata wai kamar ba wannan mai taka tsantsan d’in ba?
A hankali Mimi ta yunk’ara zata tashi tace “Hajia ki masa godiya.”
Rintse ido yayi yana addu’ar Hajia ta matsa daga gurin nan ya cabki wuyan yarinyar can, kai kutmelesi inji yan duniya, shi wai ake wa wannan iskancin? Da kallo Hajia ta bita tana jin wata irin k’aunar yarinyar na sake ratsa zuciyarta, dan abunda tayi yanzu sai ya nuna ba yarinta bace tayi ba kuma k’uruciya bace ko raini, aji ne, ajinta ta ja da kyau, dan har yanzu ita dashi basu keb’e ba bare su zama d’aya ta yanda zata zama mai arha a gareshi. Maido kallonta tayi ga sheikh da niyyar mishi magana sai taga ya bi Mimi da harara, saidai wani abu data k’ara fahimta a cikin hararar akwai kallon birgewa duk da shi baisan yayi ba, amma dai tabbas yanayin fuskarshi yanayi ne na shagala da kuma kallon birgewa da d’aukar hankali, idonshi ne kawai ke hararen suma gaba kad’an akalar hararan zata canza ba tare da sanin mai su ba.
Juyawa tayi ta sake kallon Mimi dake daf da shiga d’akinta tace “Mimi.”
Juyowa tayi tace “Na’am Hajia.” Dawowa tayi a nutse a sanda sheikh ya d’auke idonshi daga kallonta yana fad’in “A’uzu billahi mina shaid’ani rajim.”
Tana zuwa kan tebur ta nuna mata tace “Je ki fara cin abinci ina zuwa yanzu.”
Jinjina kai tayi tare da nufa kan teburin, sosai ya sunkuyar da kanshi yana son dole yafi k’arfin zuciyarshi ba sai ya kalleta ba, kallonshi Hajia tayi tace “Da wani abu da kake buk’ata sheikh?”
Girgiza kai yayi a hankali yana jin wani irin mutuwar jiki da kasala a lokaci d’aya, jinjina kai tayi ta mik’e tace “To muje ka ci abinci?”
Girgiza kai ya sake yi da k’yar ya iya cewa “Na k’oshi.”
Jinjina kai tayi ta nufi teburin tana fad’in “Bari na ci abinci ni, kasan uclerta bata jurar yunwa.”
Jinjina kai yayi alamar gamsuwa, so yake ya mik’e amma kallon fitinanniyar yarinyar can ya canza mishi yanayinshi, bayan kasalar da yake ji na sauko mishi har da wani shauk’i yake ji, a hankali ya d’an gyara zamanshi cikin dubara ya saki ‘yar mik’a a zuciyarshi yana fad’in “La’ilaha ilallah Muhammadu Rasulullahi sallalahu alaihi wa sallam.”
Mik’ewa yayi ya d’an k’arasa kusa da su, yanda take tsaye tana zubawa Hajia abinci sai yaji yana sha’awar k’are mata kallo, yanda ya ganta yar dagwai dagwai d’in nan ga kayan nan da suka mata kyau, a hankali ya kalli kwabar madubin dake geffen shi saidai Hajia ta bawa kwabar baya ne, tsaf ya hangota a ciki tana zuba abinci, take ya jefawa kanshi tambayar “Wai me yasa ta fitsare ne tun a waje?”
Haushin wannan tambayar da jin wani mahaukacin kishi yasa shi kallon Hajia yace “Sai anjima.” Da sauri ya shiga takawa ya bar falon, Hajia da kallo da mamaki ta bishi har ya fita a gidan ma.
*Alhamdulillah*👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨
*MATAR MUTUM*
_(K’abarinsa)_
👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*’YAN AMANA TA*
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*31*
Zumud’i ne ya hanata zama ta ci ta k’oshi da kyau, mik’ewa tayi tana d’aukar kwalin wayar tace “Zan shiga ciki.”
Da murmushi ta kalleta tace “Har kin k’oshi?”
D’aga kai tayi alamar eh, wucewa tayi dakinta tana shiga ta zauna kan gado, jiki na rawa ta ciro wayar tare da k’ok’arin kunnawa, samunta tayi a kunne da kuma sim a ciki lokacin da komai nata daidai alamar dai an saita mata ita, gidan sim d’in ta gani da lambar a rubuce, murmushi ta saki dan irin lambar nan ce manya gata kuma duk suna kamanceceniya da lambar sheikh da yake kiranta a da da kuma lambar Ashraf.
Tunani ta shiga wanda zata fara kira, Abba dai yanzu tasan an fita buga-buga neman na kai, Mama dama ba waya ne da ita ba, lmabar Asma’u kawai take da a kan ta, dan haka ta saka lambar tare da danna mata kira, ta d’an jima tana k’ara kafin Asma’u dake zaune suna kari tare da Asas jiki na mata rawa ta d’auki kiran tana satar kallonshi, dan tsoronta d’aya kar a zo namiji ne ya kirata tunda ba kowa yasan tayi aure ba, a sanyaye sosai Asma’u tace “Hello.”
Daga b’angaren Mimi ma a tausashe tace “Hello, Asma’u ta Mimi.”
Wani basaraken murmushi ne ya sub’uce mata tare da aje cokalin hannunta tace “Mimi ta Asma’u, kina lafiya? Ya kike? Kin daina kuka?”
Da sauri ya aje cokalin hannunshi shi ma sai kumaa ya basar tare da d’auke idonshi daga kan Asma’u, cikin murmushi da jin dad’in k’aunar da Asma’u ke mata tace “Na daina, amma idan kika ga Abbana ki fad’a masa na daina masa magana, dan shi ne ya aurar dani ga sa’anshi.”
Dariya Asma’u tayi ta mik’e tsaye tana jan kujerar baya dan bata so su siyar da halin a gaban Asas, cikin fara’a ta nufi d’akinta tana fad’in “Ba wani nan, ai ke da Abba bata b’acewa, shi kuma wanda kike kira tsoho zakiyi bayani ne da bakinki a gaba.”
Da sauri Mimi tace “Me kike nufi? Wai ni zan zauna wannan tsohon ya lalata min k’uruciya?”
Da mamaki Asma’u tace “Kayya Mimi! Da alama dai har yanzu baki fahimci karatun da nake so ki fahimta ba, kina fariya da cika baki akan rayuwar da baki da ikon tsarawa kanki ko da yanda zakiyi atshawa, bare kuma rayuwarki ta ‘yanci, abokin rayuwarki.”
Sauke numfashi tayi cikin shagwab’a tace “Asma’u ke ma fad’a zaki min? Me yasa ba zaku dubi abin ta wata fuska ba, ‘yarshi fa Aisha na tabbata ko na girmeta shekara d’aya na bata, ni yanzu ne nake fara tawa rayuwar, shi kuma ya gama cinye tashi contract d’in, so kuke na zo nayi masa takaba ne? Shikenan ni ba k’uruciyata k’arshe na shiga layin zawarawa yanda farashi na zai zube k’asa warwas.”
Dafe gaban goshi Asma’u tayi tace “Mimiiiii!”
Yanda ta kira sunanta yasa Mimi fad’in “Me ya faru? Ko mijinki naa gida ne?”
Sai kuma taji kamar zatayi hawaye, tana jin Asas sosai a cikin zuciyarta, irin yanda ta tsara rayuwarta dashi da yanda ya dinga tayata k’awata burinta abin hamdala, amma gashi *tafiyar k’addara* ta sauya musu komai, cikin son danne abinda ke zuciyarta tace “Zan kashe waya, sai anjima, ki kula da kanki.”
Da sauri Asma’u tace “Mimi.”
Dakatawa tayi daga shirin kashe wayar, a hankali tace “Dan Allah ki nutsu kinji Mimi, na sanki farin sani fiye da kowa, kar ki sake yin abinda zai sa wani ko wata ya zargeki.”
Marairaicewa tayi alamar rarrashi tace “Dan Allah kinji.”
A sanyaye Mimi tace “Insha’Allah Asma’u, nagode.”
Murmushi tayi kamar tan agabanta tace “Sai mun had’u kinji, wata rana zan zo na ganki.”
Jinjina kai tayi tace “Shikenan, Allah ya yarda.”
Kashe kiran sukayi inda Asma’u ta aje wayar, fita tayi ta koma falon ta sameshi yana tsakurar abincin, saidai kallo d’aya ta masa ta fahimci hankalinshi a tashe yake kamar akwai abinda ya shiga tunani har ya b’ata masa rai, sai kuma ta tuna wayar data fara gabanshi, hakan yasa ta tunnin ita ce silar b’acin ran nashi, a sanyaye ta zauna tana satar kallonshi, ganin yanda yake cin abinci kuma fuskarshi kamar zata tab’ashi ya fashe da kuka yasa ta cewa “Lafiya ko?”
Kallonta yayi lokaci d’aya kuma ya d’auke kanshi yace “Ba komai.”
Ture plat d’in yayi ya mik’e yace “Ni zan fita, saina dawo.”
Da sauri ta mik’e tsaye tana fad’in “Amma yau k’awaye na sun zo zasu zo min wuni.”
Dakatawa yayi yana kallonta yace “To, da wani abun da kike buk’ata ne?”
Girgiza kai tayi tana sunkuyar da kai tace “A’a ba komai, dama na fad’a maka ne dan ka sani.”
Lumshe ido yayi alamar shikenan, juyawa ya saké yi zai fita tace “A dawo lafiya, Allah ya tsare.”
“Ameen.” Ya amsa yana ficewa a falon, saida ta ga fitarsa a gidan sanda mai gadi ke mayar da k’ofar yana rufewa kafin ta zauna ta k’arasa abincinta, tana idawa ta tattare kwanukan ta kai madafa ta dawo falon ta zauna dan ba shara bare goge goge da zatayi, kallo ta shiga yi a tsanake tana canja tashar da take so ga sanyin ac na ratsata ga kuma sanyayyan lemun data aje, lallai Allah kai ne Allah, wacce ta tashi a gidan mutane dayawa, dan a kad’an mutanen gidansu zasu kai ashirin da biyar idan lissafasu za’ayi, a haka fa dan akwai mata masu aure ga maza da ba zaman gidan suke ba. Yau gata a k’aton gida ita d’aya tana yanda take so, lallai tarayarta da Mimi alkairice a gareta dama danginta.
12:02 su Salma suka diro gidan, da murna ta fito daga madafa tana fad’in “Marasa mutumci, shi ne sai yau aka ga damar zuwa?”
Dariya suka saka sai Jamila data k’are mata kallo tace “Kinji wata tsifa kuma, ba shekaran jiya ne muka kawoki gidan ba.”
Salma ce ta cire mayafinta tace “Rabu da ita, me take so muzo muyi a jiya? Mu zo cin kaza ko kuma gasa mata jiki?”
Dariya suka sake shek’ewa da ita Asma’u kula tab’e baki tayi tace “Ku zauna dan Allah ni bana son iskanci.”
Juyawa tayi zata d’auko musu ruwa Ruky tace “Asma’u wai me mijin nan naki ya baki ne har kin fara sauyawa haka?”
Dungureta Salma tayi tace “Dan uwarki duk wanda aka kawo a wannan aljannar zai k’i canzawa ne? Ai sai marar rabo duniya da lahira.”
Wata dariyar sukayi har da Asma’u data kawo musu lemu da ruwa, d’auka duk sukayi suka fara jik’a mak’oshinsu, zaune tayi tana kallonsu tace “Amma daga nan zaku je ku gano min k’awata ko?”
Da sauri Salma tace “Wa? Wai Mimi kike nufi?” Cikin d’aga murya ta tapa hannaye ta shiga fad’in “Ai Mimi zuwa na musaamman zan mata, ba dai ni ta dinga wa dariya zan auri tsoho ba mai k’aton ciki, wallahi idan na je gidan sai nayi dariya kamar cikina zai k’ulle, ke k’arshe ma saina kwaso mata shoki wallahi.”
Tsaki Asma’u tayi tace “Ramawa zakiyi kenan? Amma dai kinsan mijinki yafi nata tsufa.”
Da k’arfi Salma tace “K’arya ce wallahi, shekarun sheikh sun fi na mijina.”
Ruky ce ta kai mata duka tace “Shegiya wai mijinta, yaushe aka d’aura muku auren?”
Hararanta tayi tace “Ke kauce dallah.”
Jamila ce tace “Maganar gaskiya fa Salma karki fara, dan in gaskiya za a bi ko sheikh ya girmi Alhajinki amma sheikh ya fi shi kyawun jiki.”
Ruky ce ta tintsere da dariya tace “Ai ko a majigi kika ga sheikh kinsan tsohon duniya ne wallahi, ke karfa kiyi mamakin idan yana d’aga k’arfe, dan a kujerar nan idan ya zaune haka zaki ga kafad’unshi a bud’e.”
Jamila ma dake dariya cewa tayi “Ai shiyasa ni nace wallahi da ya so ni da gudu zan aureshi.”
“Sai kuma ya zamaa rabon Mimi ba.” Cewar Asma’u tana hararenta, Salma ce tace “Ko ma dai menene mijinta ya fi nawa tsufa, kuma sai na rama duk tsiyar data min wallahi.”
Tab’e baki Asma’u tayi tace “Allah ya shiryaku to, ni na matsu ku shiga hannun wad’anan dattijan arzik’i ko sun bambamce muku zare da abawa.”
Cike da salon shak’iyanci na yan mata suka saka mata dariya Salma na fad’in “Su Asma’u manya, wato har an shiga daga ciki ko? Da alama dai jarumi Asas ya gama aiki.”
Girgiza kai tayi tace “Har yanzu babu wannan tunanin a tare damu, ba anan kusa ba bâ kuma lokaci.”
Kallonta sukayi kafin Ruky tace “Uhum! Ke dai bari muga kun shanye wannan satin tukuna, namiji da kinibibi ke kuma mace san kowa k’in wanda ya rasa.”
Jamila ce tace “Ai tsaf zai manta da wata Mimi ya kwashi garar Asma’u.”
Dariya sukayi sai Asma’u data girgiza kai tace “Ku wallahi baku da kunya.”
Mik’ewa tayi tana fad’in “Bari na kawo muku abinci.”
Da kallo suka bita har ta shige, da sauri Jamila ta kallesu tace “Ke ki dubi daula ki gani, wa ya san Asma’u zata auri mai kud’i? Ita da ko saurayin kirki bata da.”
Ruky ce tace “Allah ya kareta daga sharrin tarikitan samarin ne saboda mijinta bai bayyana ba.”
Salma kam cewa tayi “Ni ba wannan ba, wai yanzu ya zasu rayu ne suna auren yan uwan juna ita da Mimi bayan kuma abinda ya faru ranar auren nan?”
Cikin rad’a Jamila tace “Bari kedai, nima abinda na fi tunaani kenan, kuma fa har yanzu da alama k’awancensu na nan, kuna ganin hakan ba zai shafi alak’arsu ba?”
Ruky ce tace “Da zai shafi alak’arsu daya tab’a tun ranar, mazan dai na fi jiye ma, kinsan maza sun fimu rik’o fa, kar a zo tafiya tayi tafiya Asas ya kasa cireta a zuciyarshi.”
Salma ce tace “Ai shi d’in ne, baiwar Allah kuma fa zata fuskanci matsi idan haka ta faru.”
“Gaskiya kam.” Cewar Ruky, jin fitowar Asma’u yasa Jamila saurin fad’in “Daga nan dai muyi k’ok’ari muje wajen Mimi, ina so naga tab’ara da iya hege.”
Dariya sukayi har da Asma’u data fito tana fad’in “Ta daina ma na sani, babu abinda zaki gani Jamila.”
Salma ce tace “Wacece? Mimin? Ai kuwa dana tsine mata, yo a zaman da zatayi gidan nan idan bata kafawa sheikh tarihi ba ai bata cika Mimin dana sani ba.”
Ruky ce tace “Gaskiya kam, ko wajen iya d’aukar wanka ai Mimi zata rikita gafarta malam.”
Tintserewa sukayi da dariya sai Salma da tace “Sai ma ta gifta ta gabanshi tana sittin saba’in.”
Cikin dariyar mugunta Asma’u ma dake rik’e ciki tace “Wata rana kam zamu ga yayanmu babu hula a kai.”
Da ire-iren hirar nan suka shiga cin abinci ana tapawa ana shewa, sosai suke nishad’i inda Asma’u ma ta ji dad’in zuwan nasu sosai duk da tana bak’i lokaci lokaci daga danginta zuwa mak’wabta, sai daf da magriba suka bar gidan dan girki ma su suka tayata yin shi ta gyara gidanta tsaf kafin suka tafi bayan sun karb’i lambar Mimi wacce ta kirata d’azu da cewa zasu kira su saka ranar da zasu tafi gidanta duk da bata tare ba.
*Mimi*
Tunda ta samu wayar nan ta shige d’aki ta shiga latse-latse, a k’arshe dai da taga wayar an loda mata kud’i sai kawai ta shiga yanar gizo, a take ta bud’e WhastApp duk da bata da lambar kowa, haka ta shiga man-hajar videmate ta dinga d’auko wak’ok’i na hausa na kallo dana saurare, kiran sallah azahar kawai ya tasheta a wurin tayi sallah kafin ta fito falo, ta samu Hajia na d’aki sallah sai kawai tayi zaune ta k’urawa tvn ido wacce ita dai ta fahimci kamar tasha d’aya suke kallo kullum wato *sunna tv*.
Da yamma da kanta ta shiga madafar duk da har yanzu bakinta bai sake had’uwa dana Salamatu ba, haka ta shiga had’a abinda ranta ke so kamar yanda Hajia ta bata wannan damar, Salamatu dai na kallon ikon Allah, gata k’aramar yarinya mai jikin yan hutu, amma yanda take takawa tana wani motsa k’ugunta kamar da gayya, sai taji kamar yarinyar zata shiga ranta sai kuma tayi saurin tunawa kanta abokiyar gaba ce fa. 🥴 a banza indai uwata ce.
Daf da magriba suka kammala ta kai komai kan tebur ta shiga d’akinta dan yin sallah, saida ta idar da sallah kafin ta shiga wanka, tana fitowa ta zauna a gaban madubi, wani karsashi take ji tare da jin bari fa ta cire komai a ranta kar ta zama wata ‘yar k’auye. A sauk’ak’e ta shiga linde fuskarta da hoda ta ruwa mai haske sosai kalar fatarta, kafin ta zana gira da kalar maroon data fito da fasalin fuskarta, saida ta fara shafa eyeshdow a saman idonta ta shafa mascara kafin ta shafa jan baki kalar maroon mai duhu sosai a sama sai k’asa data shafa lips sannan ta shiga fitar da tsarin labb’enta da wata hodar mai haske amma mai d’an k’yalli.
Mik’ewa tayi ta kalli kanta a madubi ta kanne ido d’aya dan ta birge kanta sosai, k’arasawa tayi gaban drower kayanta, wata fitinanniyar rigar shadda ta d’auka wacce tana d’aya daga cikin kayan da Asas ya fara aikata mata, d’inkin ya bala’in haukata ta yayi kyau sosai, yanda kalar fatarta take sai kalar kore mai duhu, tsaye tayi gaban madubi kamar wasan yara ta laulaya d’an kwallin, a yanda tayi d’aurin zaka rantse kawai tayi ne dan babu yanda zatayi, amma ko da ta ja shi baya ya fito mata da goshinta tare da fito da gashinta a gaba, a baya ma ta fito da jelar gashinta sai yayi wani irin kyau kamar zama akayi na musamman aka d’aura.
Wayarta ta d’auka ta fita ko wuk’a aka d’ora maka zaka iya rantsewa matar wani shugaban k’asa ce dan wani d’aukar ido tayi wal wal wal, Hajia ta samu a falo tana kallon tv da kuma wayarta a hannu saidai da alamar damuwa a tare da ita, ganin Mimi ne yasa ta sakin baki tana kallonta, ajiyar zuciya ta sauke tare da tuna yanda Asas ke fad’a mata yana son mace yar gayu da iya ado, murmushi ta mata tana fad’in “Takwarata kin fito?”
Murmushi tayi ita ma tace “Barka da hutawa.”
“Barka.” Ta fad’a tana sake kallon komai na jikinta, a gaskiya ba dan taga gidansu ba sai tace ba daga nan ta fito ba, cikin fara’a tace “Yau fa kinsha aiki, dan na ga abinci jere akan table.”
Murmushi kawai tayi tana sunkuyar da kan ta, cikin zolaya Hajia tace “Sai nayi tunanin ko cheif ce ke a wajen iya girki.”
Da sauri tace “A’a Hajia, karambani ne kawai da sa kai, a wayar k’awaye na nake gani dama ko kuma a YouTube.”
Da fara’a tace “Masha’Allah, ai karambanin mai kyau ne.”
Cikin ladabi Mimi tace “Zan d’an zagaya farfajiya ne.”
Da murmushi tace “Ba komai, ki kula.” Jinjina kai tayi tare da fita a hankali, tana fita kai tsaye wajen ajiye motoci ta nufa, mota biyu ce a pake a wurin, tsayawa tayi ta fara d’aukar hotuna masu kyau.
Bud’e k’ofar gidan da taji anyi yasa ta juyawa dan ganin mai shigowa, tana ganin motar sheikh da sauri ta lab’e bayan motocin tana fad’in “Old man an taho, wai me yake kawoshi gidan nan ne kullum?”
Kusa da motocin aka paka motar, tana hange taga wani mai bak’ak’en kaya ya bud’e mazaunin baya, a sanyaye ya fito cikin k’asaita da nutsuwa, tab’e baki tayi tana kallo ya rufe motar, zai fara takawa sai kuma ya tsaya tare da juyawa bayanshi kamar zai kalli inda take, da sauri ta sake lafewa tana dafe k’irjinta, sake juyowa yayi ya kalli jami’in yace “Ku jirani a nan.”
Gyara tsayuwa yayi yana hard’ewa wuri d’aya da bak’in glas d’in shi, takawa ya shiga ta b’angaren da take hakan yasa Mimi hanjinta motsawa kamar zasu fito waje, rintse ido tayi sosai data tabbatar wajenta ya nufo, saidai tana mamakin yanda yasan tana nan, ai kam gabanta ya tsaya yana k’are mata kallo daga k’asa har sama.
Cikin dakakkiyar muryar shan k’amshi da b’acin rai yace “Me kike yi a nan?”
Bud’a ido tayi tar a kan fuskarshi sai kuma tayi k’asa da su, cikin rawar baki tace “Um..dama..na zo shan iska ne.”
A gajarce yace “Shan iska?”
D’aga kai tayi alamar eh, takawa yayi d’aya biyu na uku ya kai daf da ita, ja baya tayi dan sai taji ta kamar gaban wani basamude, tsaf ya rufe da girman jikinshi da kuma manyan kayanshi, d’ora hannayenshi duka biyu yayi jikin motar data jingina, hakan ya haifar da k’wak’waran kusanci a tsakaninsu kamar zai rumgumeta, d’auke numfashi tayi tana kallon fuskarshi da yanayin tsoro da kuma sakarci, fuskarshi a had’e sosai yace ” *Ke yanzu matata ce, ba kamar matar kowane gaja bace, suturtata jikinki da kama min kanki ya zama wajibi a gareki, wannan kwalliyar ni kawai ya dace ki wa, gashinki kuma kar na sake ganinshi a waje.*”
D’auke hannayenshi yayi tare da k’urawa fuskarta ido yace “K’amshin nan haramun ne ki sa ki fito waje, ke Ryam ba zan yarda hakk’inki ya kaini wuta ba, wallahi ki kiyayeni kinji na fad’a miki.”
K’wafa yayi tare da ja baya yace “Kuma ki zauna a nan karki fito har sai na bar gidan nan.”
Zaro ido tayi dan sai lokacin kawai ta farfad’o daga halin daya jefata, maganganunshi sun shigeta ta sama musu muhalli tare da tunanin abinda yake nufi. Yanda ta zaro ido yasa shi fad’in “Kin ji me na fad’a?”
Da sauri ta jinjina kai cikin tsoro tsoro da firgici tace “Na ji, amma kuma…”
“Amma me?” Ya fad’a yana binta da harara, girgiza kai tayi alamar ba komai, jinjina kai yayi yace “Magana ta dake mai yawa ce, zan tarasu ne har ki sameni gidana.”
Kyab’e fuska tayi tana neman fashewa da kuka tace “Ni wallahi ba zan je ba, haka kawai a wani kai ni gidan…”
Da sauri ya kalleta yace “Gidan me?”
Girgiza kai tayi alamar ba komai, zaro lata ido yayi yace “Me na fad’a miki akan k’arya?”
Da sauri ta fashe da kuka tare da fad’in “Ai dama cewa ne zanyi gidan old man.”
K’ank’ance idonshi yayi yana kallonta da mamaki, bakinta data turo tana zuba shagwab’arta yasa yatsu biyu ya cabkoshi, gam ya rik’e hakan ya haddasa mata sakin k’arar data shiga dodon kunnen wanda ke gidan a lokacin, hankali tashe ba tare da tunanin zata iya yin haka ba ya had’ata da motar tare da yin wuf da bakinta ya had’a da…
*Alhamdulillah*👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨
*MATAR MUTUM*
_(K’abarinsa)_
👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*’YAN AMANA TA*
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*32*
Hankali tashe ba tare da tunanin zata iya yin haka ba ya had’ata da motar tare da yin yuf da bakinta ya had’a da tafin hannunshi ya taushe, zazzaro ido tayi haka shi ma dake kallonta da mamaki, da gudu jami’an suka tunkaro wurin dan su lafiyar sheikh ce nauyinsu, kuma basu san shi da waye a wurin ba, daga d’aki ma Hajia fitowa tayi tana kallon Salamatu data rigata tace “Kamar ihun Mimi ko?”
Jiki na mata rawa tace “Ni ma haka na ji Hajia.”
“Me ya sameta to?” Ta fad’a tana nufa farfajiyar gidan, yanda jami’an suka fad’o bayan motar d’aya har ya ciro bindigar da gwamnati ta basu tare da izinin harbi idan suka ga had’ari, juyowa yayi ya kallesu tare da sakin bakinta, babbaketa yayi yana kareta wai shi a dole kar su ganta, fuska a had’e sosai yace “Me ye?”
Cikin girmamawa d’ayan yace “Yallab’ai mun d’auka da had’ari ne.”
“Ba komai, ku tafi.” Ya fad’a yana sake wani ciccijewa, juyawa sukayi zasu tafi sai kuma ga Hajia da Salamatu apujajen, sake matsawa yayi nesa da ita yana k’wala mata harara, cikin tashin hankali Hajia ta shiga kallonshi tana fad’in “Sheikh lafiya? Naji ihun Mimi.”
Matse bakinshi kawai yayi da sauri Mimi ta tafi da sauri ta isa kusa da Hajia, da kallo ya bi bayanta yanda take tafiyar da sauri, zuciyarshi ce ta tambayi “Anya yarinyar nan ke da k’ugun nan?”
Numfashi ya sauke a hankali yana kallon Hajia na share mata hawaye tana fad’in “Me ya sameki? Wani abu kika gani?”
Girgiza kai tayi cikin kuka tace “Shi ne ya tsoratani.”
Kasa d’auke idonshi yayi a kan ta duk da kallon da Hajia ke masa tana fad’in “Sheikh wani abu ka mata?”
Sai kuma ta kalli Mimi tace “Ko dai wasa ne yake miki?”
Cikin shagwab’a ta kalleta ta turo baki tace “Hajia kina nufin wasar kaka da jika?”
Da sauri Hajia tayi saurin rufe bakinta a bayyane tace “Kai.”
Salamatu ma ta zazzaro idonta waje tayi, shi kuma sheikh daga tsayen da yake duk irin yanda ya kai da b’acin ran masu tsaron nan nasa sun wani zo masa a wajen da bai dace su zo ba sai ya tsinci kansa da sakin k’ayataccen murmushi, lallai ma Ryam abun na ta yanzun ya fara d’agowa kamar so take ta hassala shi, so take kawai ta ringa juyi da shi kamar biri da abokin wasansa.
Murmushi ya kuma yi ya juya ya nufi ciki ta d’ayan b’angaren ba tare daya ce komai ba, daga Hajia har Salamatu sun jinjina lamarin Mimi, Hajia na janye da hannunta har suka koma cikin d’akin sannan ta saketa ta nufi d’aki abin ta.
Tana shiga ta kwanta tana lumshe idonta, k’amshin turaran Dadyn nan na mata dad’i a hancinta bata san dalili ba, ga wani tattausan hannunshi daya rufe mata baki dashi, yanda ya matsa a jikinta sosai sai abun ya nemi tsaya mata a kai da zuciya.
Idonta ta sake lumshewa ta kuma bud’ewa tana tab’e bakinta ta shiga kiran lamber Abbanta.
Tana fara ringin ya d’aga, amma daga nesa nesa take jin maganarsa yana fad’in “Kina gani kuwa wata lamba ce ban santa ba, kin san masu shan jinin nan fa an ce da gaske ne?”
Yar dariyar mamanta ta ji tana fad’in “To kayi sallama mana malam ka ga fa kud’in mutumen na tafiya.”
Dariya tayi a bayyane ta furta “Abba ni ce fa.”
Dai-dai ya matso wayar ya ji muryarta a sanyaye tana kuma dariya tana kiran sunansa hakan ya saka shi fad’in “Uwata ce?”
Wata yar dariyar tayi tace “Ni ce nan Abba.”
Shi ma dariyar yayi sai kuma da sauri ya gimtse yana fad’in “Ke wa ya baki waya?”
Bakinta ta turo a sanyaye tace “Shi mana.”
Mamanta dake sauraro tace “shi wa?”
Bakin ta kuma turowa tace “Shi akaramakalahun mana.”
Mama bata san lokacin da murmushi ya k’wace mata ba tana girgiza kai tana jin Abban na amsa gaisuwarta ta mik’e ta shiga kakkauda kayayyakin dake ajiye hankali kwance.
Cikin sangarta tace “Abba yaushe zaku zo? Dan Allah idan ma ba zaku zo ba ku turo min su Yaseen mana.”
Abba yayi murmushi yana girmama rashin hankalin mamansa, su su zo? Ko a turo mata Yaseen? Sanin da yayi ita d’in ba ‘yar a kwatantawa a laluma bace sai kawai ya datse kiran yana d’an murmushi, ko ba komai muryarta ta saka shi farin ciki, a bayyane yake yi mata addu’ar samun nutsuwa.
Hajia na zaune saman kujera, sheikh na zaune saman kafet ya tank’washe k’afafunsa bayan sun k’ara gaisawa da kyau har an kawo masa ruwa ya d’an sha, da yanayin da take ciki ta dube shi a sanyaye tace “Sheikh, na rasa ina autana ya shiga, ka ga tunda aka yi abun nan ban ganshi ba ba shi ba labarin iyalinsa, idan na kira baya d’agawa, tun abun baya damuna har ya fara damuna, ka ga magungunansa duka a nan bayan nan ka sanshi da wasa da cikinsa, shin laifi nayi mai girman da ya saka yayi fushi har haka dani?”
Sheikh da yake saurarenta ya kawar da kansa gefe guda yana d’an nazari kafin ya sauke ajiyar zuciya a sanyaye yace “Ki yafe masa, sannan gobe insha’Allah zai zo ya gaishe ki, kar ki saka damuwa a ranki na tabbata da yana cikin matsala daya nemi uwa, kiyi masa addu’a sannan ki masa nasiha, idan ya zo ki saurareshi ki rarasheshi.”
Hajia na gyad’a kanta tana jin girma da soyayyar Sheikh kamar na wanda ta haifa a cikinta, a gaskiya shekarunsa basu kai irin girman da duniya ke bashi ba, amma da yake tun bai kai haka ba yake da halayya na dattako, girma da darajar Alk’ur’ani dake kansa ya k’ara masa kima da darajar da ko mutum ya tsofe shi sai ka ga yana neman zubewa ya gaishe shi sai idan shi yayi gaggawar tarewa domin kuwa arzikinsa da baiwar da Allah ya bashi bai saka shi barin kansa ganin manya na gaishe shi a tsugune ba.
Da haka yayi masu sallama ya fita domin yana da wajen zuwa har uku, ga kuma na hud’u ya k’aru dan kuwa zai je ya same shi a wajen daya tabbata baya wuce nan.
Saida ya je yayi yawace yawacensa, duka wajen da yake da na zuwa ya je ya gabatar da ayyukansa a tsanake kafin ya nufi wajen da ya tabbata Asharf na cen.
Kusa da masallacin kadafi ne wajen da yake zama tare da abokansa, motocin sheikh na tsayawa samarin uku dake zaune suka mik’e duk suka yo wajen motar ciki har da Ashraf da sai da gabansa ya fad’i amma haka ya dake yana murmushi a lokacin da d’aya daga cikin mai kare lafiyar sheikh ya bud’e samarin duk suka duk’a suna mik’a hannayensu suna mik’a gaisuwarsu.
Cike da kamala da daraja d’an adam yake amsa masu d’aya bayan d’aya har suka gama gaisawa kafin ya juya cikin halin kyauta irin nasa ya d’auko enveloppe ya mik’a masu kamar yanda ya saba indai zai tsaya sai ya basu duk da duk cikinsu ba zauna gari banza, amma a matsayinsa na yayansu kuma uba a wajensu sannan mai kyauta yakan yi hakan wanda hakan ke saka su nishad’i da farin ciki, su kansu suna koyan halayya irin nasa domin suma suna yiwa gajiyayyu da k’annensu bare kuma iyayensu.
Ashraf na masu sallama ya shiga motar ya zauna aka rufe suka d’auki hanya, shiru ba wanda yayi magana har suka iso k’ofar gidan Ashraf, kuma ba waya suke daddanawa ba hasalima cikin motar ba hayaniyar komai sai shirun da yayi yawa.
Muryarsa na rawa rawa yace “Dan Allah kayi hak’uri.” Dan yau sheikh d’in tsoro ya bashi tare da jin shakkarshi da kwarjininshi ta yanda yake jin ba zai iya masa wasa ba yau.
Sheikh kam d’an juyar da kansa gefe yayi ya kuma juyowa a hankali ya dube shi har ya d’an fad’a kad’an, a hankali ya cire dubansa yana jin zuciyarsa na tsintsinkewa, abinda yake son fad’a shi ne “Kai Ashraf shin dan na auri Ryam ne kake irin haka? Shin matata na zuciyarka ne ko me? Shin baka cire min iyali a ranka ba ko me? Kai marar kunya halan baka d’auki k’addarar aurenka ba? Shin ka isa ka auri matar wani ne?” Sannan ya d’an wanwanka masa marin da zai farkar da shi, sai dai kasantuwarsa da wanda yake a wajensa ya saka shi kawar da kansa a sanyaye yace “Gobe da safe wajen 11:00 ka zo gidan Hajia da iyalinka, insha’Allah zanyi jiranka a cen.”
Daga haka ya d’auke kansa a duban Ashraf wanda ya gyad’a kansa yana k’ara sadda kan nasa ya bud’e ya fita yana mai yi masa saida safe.
Daga nan gidansa ya k’arasa, sai dai bai shiga ba sai da ya gabatar da wasu karatuttuna a masallaci sannan ya nufi cikin gidansa.
K’arfe 10:30 ce, hakan ya sa ya samu yaransa duk sun yi bacci, Hafsat kuwa na saman kujera ta mik’e k’afafunta a sama tana jan carbi idaonta lumshe. Sanyi yaji a zuciyarsa a lokacin da yayi arba da fuskarta, sanyin idaniyarsa ce ita, sanyin zuciyarsa ita d’in, kwanciyar hankalinsa ce ita wacce ta amsa sunan *mar’atus-saliha*.
Duk’awar da yayi a gabanta ya sakata bud’a idonta masu cike da bcaci tana kallonsa, murmushi ta sakar masa hakan ya saka shi lumshe idonsa a hankali ya d’ora hannunsa saman cikinta yana kallon fuskarta yace “Shin ajiyar *Abdallah* na ci gaba da wahalar da Nurul ayni ne?”
Murmushi tayi masa a hankali tana d’an girgiza kanta, domin yanzun da sauki bata jin curewar nan saidai mugun baccin da take yawan yi ta kamo hannunsa tana dubansa tace “Ai komai nauyin kayan jagorana zan iya rik’ewa da hannu bibbiyu abu na.”
Murmushi yayi yana mik’ewa a hankali ya kamata ya mik’ar da ita ya nufi d’akinsa da ita domin ya san cewa ta gama da yaren ta gama da b’angarensu shi kuwa tuni ya rufe daya shigo.
Saman lallausan gadon ya shinfid’eta ya d’an rank’wafa a hankali ya kama leb’enta na k’asa ya bata kyakyawan sumba mai sanyi, a hankali ya shiga tofa mata addu’a yana shafa gashinta kafin yace “Allah yayi maki albarka, Allah ya tashe ki lafiya cikin hayyacinki, Allah ya yafe maki kurarenki wad’anda kika sani da wad’anda baki sani ba, Ina son ki Manga na.”
A gaskiya ba zata iya kwatanta irin farin cikin da mijinta ke sakata ba, gata dai aure ne na had’i amma tunda ya fuskanceta suke zama irin na fuskantar juna, kowa na yin kaffa-kaffa da lamarin d’an uwansa, har zuwa yanzu da auren wata ya kuma hawa kansa bai saka rud’u da rawar kai irin na yawancin mazan da zasu d’auko yarinya ke shiga ya ringa nuna mata wasu abubuwan ba, yana bata lokacinta da kuma isashen darajarta, tana jin kanta tamkar ita d’aya ce tak a duniyarsa kuma tana jin dad’in hakan, ita kam ta yaba kuma tana k’ara yaba auren YA SHEIKH.
Tun yana nan bacci ya kwasheta, a hankali ya nufi bayi dan yin wanka da alwala domin yana son kwantawa da wurin shi ma yau dan tashin tsakiyar dare yin nafilfili cikin nutsuwa.
*Washe gari*
A yau shigar sheikh ta gama tafiya da nutsuwarta, tsaye take gabansa ta d’an taka pillow d’in daya ajiye mata tana rik’e da hiraminsa ta k’ara d’an yin d’add’age ta d’ora masa a saman kansa shi kuwa yana tallabe da bayanta sanan ta tsaya tana kallon fuskarsa, zata iya rantsewa wannan dan tsili tsilin farin gashin dake gemunsa k’ara masa kyau yayi ko na mutum da masoyi ne? A hankali ta d’ora hannunta saman faffad’en k’irjinsa da kuma shafafen cikinsa , idonnta ta lumshe muryarta cen ciki tace “Kishin mijina nake, shin idan ya fita a haka ya ya yan mata zasu yi da begensa? Kayi kyau har ka gaji ya habibi.”
Murmushi yayi cikin nutsuwa yana k’ara tareta a jikinsa yace “Ke kike ganin haka ya Mar’atusaliha, kyau kuma ai an barshi tun k’ananun shekaru, ki kular min da kanki kafin na dawo, ban yarda ki yi aikin da zai wahalar min dake ba.”
Murmushi ta masa tana manna masa sumba a kumatunsa shi kuwa bai saketa ba sai da ya sauketa daga saman pillown sannan ya d’aga mata hannu ya juya ya nufi waje cikin sasaukar shiga irin ta larabawa domin doguwar riga ce ta jalabiya da dogon wandonta sai hiramin da ya d’ora, kayan sababi ne sannan manyan kaya ne masu tsadar gaske da daraja gashi sun amshi jikinsa sosai.
A lokacin daya zo dan shiga falon Hajia ya samu takalma a k’ofa na mata hakan ya saka shi juyawa cikin nutsuwa ya koma cen wajen motocin gidan ya ajiye kujera ya zauna yana rik’e da wayarsa Android da d’an tissu ya shiga danna wayar dan yana son kiran Hajiar ya ji idan bak’in na gida ne ya shiga domin yanzun goma ce har da rabi duk inda Ashraf yake ya tabbata yana hanya.
Yar hayaniyar da ya jiyo ce ta saka shi d’an duba gefen da yake zaune.
Su Salma ne su uku sai Mimi ta hud’unsu sun fito sun nufo hanyar tsakiyar gidan wace take d’an kusa da motocin gidan suka ja suka tsaya.
Idonsa ya so cirewa yana dan tab’e bakinsa saidai me? Da sauri ya maida kanta sakamakon ganin ba ko hula a saman kanta bare d’an kwali ko hijabi.
Dariyar da Mimi tayi ne ya saka shi zuba mata ido ta dafa gefen kafad’ar k’awarta tace ” Na dai ji, kina ta maganar na isheku tsoho tsoho gani daram a matsayin matar tsohon na ji, aman ai ko ya ya dai Old man ya fi mijinki wallahi tunda shi ban ga tumbi a tare da shi ba!”
Salma ce ta zaro ido tace “Shegiya! kar dai ki ce min har kin gano girman oga? Wayo duniya wayo aure mai daraja yanzun Mimi ke din na da nake gani a b’agas har kin je cen da Haj man ya sheik?”
Mimi ta yatsina bakinta tace “Kunga ni fa irin wannan zancen naku ke had’ani daku, shikenan ba damar a had’u da ku sai ana kauce layi? To bama wannan ba ke yanzu wannan kayan nawa ai kin san mai iya jansu sai d’anye sabon jini ….” Ta fad’a tana mai d’an juyawa a gabansu ta d’an juya mazaunanta
A hankali ya lumshe idonsa yana furta ” A’uzubillahi mina-shaid’anin rajim! subhanallah, subhanallah, subhanallah, hasbunallahu wa’imal wakil, Innalilahi wa’inna ilaihi raju’ne!”
A hankali ya ringa jin ransa na biya tayin neman rigimar yarinyar cen, wai yanzun shine old man kuma bata jin kunyar fad’a a gaban kowa? Uwa uba yanzun su yaren nan ina iyayensu da suka fito da sassafe suke son fitar da matar mutane har suke maganganu na rashin d’a’a haka? Shin wai yaya aka yi tarbiyar ‘ya’yanmu ta lalace? Wai Ryam ita ce da cewa shi ba zai iya juya wannan abin dake jikinta ba?
Wani d’an murmushi mai ciwo yayi yana datse leb’ensa na k’asa, idonsa da suka yi ja suka kad’a ya kuma d’orawa a kan k’ugunta, lallai sai ya nunawa yarinyar cen meye namiji, meye mai sunan namiji, sai ya banbance mata k’arfin namiji ba a shekarunsa yake ba, sai ya danna mata abinda zata ji har mak’ogwaronta, sai ya jijiga rayuwarta da hajijiya ya timata a k’asa ta yanda ko an ce ga namiji gabanta zai fad’i! Da haushi haushi ya kalli yanayinsa yana mai jan tsaki a bayyane yayi gagawar d’ora k’afa d’aya kan d’aya ya matse k’afafunsa sannan ya dafe gaban goshinsa da hannunsa mai d’auke da agogon azurfa.
Ruky ce tace “Kun ga ku wuce mu tafi dan Allah, shiyasa ban so muka biyo ba yau wallahi, zama na musamman nake so muyi dake ai.”
Salma ce tace “To wai yaya ke ma zaki koma makarantar?”
Cike da tabbaci tace “Me zai hanani kuwa, ku zuba ido ku gani.”
A haka suka ringa yar hirarsu ta k’awaye suna shan dariyarsu kafin suyi gaba tana nan tsaye da rigar dake jikinta doguwa kalar bleu, rigar sosai take rawa a jikinta koda bata da abin kad’awa bare tana da su.
Mik’ewar mai gadi ya nuna alamun zai bud’e k’ofa ya saka sheikh saurin mik’ewa tsaye daga zaunen da yake.
Da sauri ya kuma kallonta ganin tsaye take ta zubawa motar dake danno hancinta cikin gidan ya saka shi d’aga k’afarsa da saurin da bai tab’a tunanin yana da shi ba sakamakon irin yadda zuciyarsa ke bugawa ya ware yan yatsunsa da kyau ta yadda zata shiga juwa idan ya isar mata da sak’on da yake son isar mata wanda ya tabbata duk dukan da Abanta zai mata da muciya bai tab’a shigarta haka ba ya nufeta gadan gadan idonsa har rufewa suke da tsabar kishi da tsoron kar Ashraf ya tarda ita da wannan shigar.
Bata ankara ba, bata lura ba kamar yanda bata san dashi ba, hannunta kawai taji an figa da wani irinu k’arfi dake nuna wanda ya mata rik’on a hassale yake, da sauri ya shiga janta zuwa falon ita kam kamar zata kifa a k’asa, Hajia da fitowarta kenan tun da Mimi tayi bak’i ta shiga d’aki ta gansu tare, saidai yanda fuskar sheikh ke d’auke da mafificin b’acin rai sai kawai ta shiga furta “Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un!”
Fatanta d’aya kar sheikh yayi abinda za’a bugashi a jarida, mutum ne da ba zaka ce ga abokin fad’ansa ba, amma dai bai iya hushi ba ko kad’an.
D’akinta ya wuce da ita tare da wurgata ta fad’i k’asa, k’ara ta saki da k’arfinta ta furta “Ahhhhhh….”
Tsaf ta had’iyeta sakamkon fizgo damtsenta da yayi ya mik’ar da ita da k’arfi, bata gama gane ko da fuskarsa ba kawai ya damk’i damatsanta ya shiga jijjigata kamar b’era a cikin kwano cikin wata irin muryar ban tsoro yake fad’in “Ke wai har yaushe kikayi girman da maganganu irin wannan zasu riga fita a bakinki? Ni ne kike wa duk abinda kika ga dama Ryam? To ki sani na karb’i wannan tayin rashin mutumcin na ki, wallahi ba dan tsoron Allah ba da inna kirta miki wata buru’ubar ke sai kin d’auka ko ni kad’ai ne d’an iska a duk fad’in niger, amma a haka ma zan miki daidai da kalar naki rashin mutumcin, ni zaki dinga kallo kina kirana da sunayen da kika ga dama har a gaban k’awayenki, ke duk duniya babu wanda ya tab’a kwatanta yi min abinda kike min a yanzu, wallahi idan kika ci gaba ba zakiyi sati a gidan nan ba gabana zan mayar dake dan na kula k’arancin sani ke damunki.”
Tureta yayi hakan yasa tayi tangal tangal zata fad’i dan sosai ya wujijjigata, hanayyenshi ya zagaya ta k’ugunta ya jawota da k’arfi, take ta fad’a kanshi tana zaro idonta tana kallonshi a matuk’ar tsorace dashi, bai tsaya jiran komai ba y’a damk’i d’uwawunta da hannayenshi yana matsawa yana fad’in “Wai har wannan kike juyawa kina fad’in ni ba zan iya jansu ba, na tabbata dan Allah ya tsara kowace halitta da mazaunai shiyasa ke ma kika mallakesu, amma ba dan haka ba ke ina abinda zai isheni a nan bare har ya d’aga min hankali na.”
Ba tare da tunanin komai ba ya kama hannayen rigarta yayi k’asa da su hakan hakan yasa nonowanta dake hulu-hulu farare tas dasu suka bayyana dan ita fa zuwan su Salma ne suka tasheta daga bacci, ba tayi wanka ba barre ta saka bras. Sheikh da yana zage rigar yace “Har wannan b’erayen…”
Cak ya dakata dan ganin abinda ke neman fin k’arfinshi, bai tab’a hasashen zata kai haka ba sabida yanayin shekarunta da fuskarta, tabbas ko hannu zaisa ya damk’a zasu cika girman tafin hannunshi, hakaan ya haddasa mishi wani mugun jiri ya nemi kayar da shi, da sauri ya tureta a jikinshi ya juya baya yana rufe ido tare da furta “Ya Hayyu ya Qayyum.”
Mimi kam a gigice ta juya da gudu ta shige ban d’aki ta rufe k’ofar ta jingina, sulalewa tayi ta sako da wasu hawaye masu zafin gaske, a rayuwarta bayan mamanta ba wanda ya tab’a kwatanta tab’a inda mutumin nan yau ya tab’a, a hankali ta saki wani kuka mai tsuma zuciya tare da gyara rigarta, wani irin bugu zuciyarta ke yi kamar zata fito daga k’irjinta.
K’wank’wasa k’ofar da Hajia tayi ya dawo dashi hayyacinshi, a hankali kuma a nauyaye ya shiga taka k’afafunshi da k’yar ya k’arasa fita, tsaye take bakin k’ofar duk a tsure take da tunanin abinda zai faru, cikin girmamawa tace “Ashraf ne suka k’araso.”
A hankali ya lumshe ido alamar to, takawa ya fara yi zuwa falon saidai kash wani babban tashin hankali da abun kunya ne ya bayyano a jikinshi, sai yaji kamar ya cire hiraminsa yayi walki da shi ko zai rufe mishi sirrinshi, da k’yar yayi dubarar dan jan rigar har ya k’arasa ya zauna akan kujera.
*Alhamdulillah*