WANNAN RAYUWAR CHAPTER 13
Da dare Anty Zainab ta dawo da kayan sannan sukai sallama. Sallah sukai sannan abinci suka ci sannan ta mike ta shiga daki. Wanka tayi ta shirya cikin wasu kayan baccin ta masu kyau. Gajeren wando ne da riga marar hannu sun mata kyau kayan sun kara haska tarure take fesawa ya shigo. Tsayawa kallon ta yayi can kuma ya karasa gaban mudubi ya tsaya ta bayan ta tare da daura kan ta a kafadar ta. Hannun sa kuma ya na kan cikin ta yace
‘Kinyi kyau Zuma ta!”
“Nagode!”
Dagata yayi ya zura hannun sa a aljihu ya dauko wani box mai kyau budewa yayi taga sarka ce da dan kunne har da zobe na gold.
“Ummu kin shayar dani abin da ban taba zato ba kin ban komai a duniya ki bani martabar ki shin ni dame zan saka miki?”
“Kai taso na Kawai ya ishe ni.”
“Sonki dole ne a waje na Ummu amman ki fadan me kike so bayan shi.”
“Ba abinda nake so miji na sai kai kadai.”
“Ni naki ne Ummu.”
“Godiya nake.”
“Ga kyauta Ummu nan bata kai darajar abinda kika ba. amman dan Allah kiyi manage da ita.”
Ido ta zaro ta amsa tana fadin
“Wow tawa ce.”
Sai ta ajiye ta rumgume shi tana tsalle tare da fadin
“Ya salam!”
Ta dauki sarkar tana fadin
“Nagode Miji Allah ya kara budi da arziki wannan ya fi min komai Yaa Muhammad!”
Amsa yayi ya dauki sarkar ya saka mata ya dauki dan kunne shima ya saka mata ya sa mata zobe take ta kara kyau ta fara walwalai. Daukar ta yayi yai kan gado da ita. A kan gado ya dire ta yana fadin
“Komai zuma ta ta saka kyau yake mata.”
Murmushi kawai tayi ya janyo ta ta shige jikin ta ya fara lallubar ta. Duk da yadda take a tsorace bata nuna masa ba haka ya gama cakudata sannan ya rumgume ta yana fadin
“Zuma ta jaruma ce ina sonki.”
Ajiyar zuciya ta sauke. Ya rumgume ta yace
“Muyi baccin mu ba abinda zan miki Zuma ta ki huta kema yau ko?”
Ta kara shigewa jikin sa. a haka bacci ya dauke su basu suka farka ba sai asuba.
*
Bayan sati daya.
A sati dayan da ya wuce ya nunawa Ummu kulawa sosai ga soyayyar sa duk da ba abinda ya kara shiga tsakanin su amman yana bata kulawa da soyayya kullum fadi yake ki kara hutawa Ummu na ranan kin yi kokari.
Tin da ya tafi masallaci bai dawo ba dan yana zuwa training. Sanye take da three quarter da karamar riga tana suya a kitchen kan ta sanye da hula bata ji sallamar sa ba sai kawai jin hannun sa tayi akan kirjin ta. Ajiyar zuciya ta sauke tana fadin
“Yaya na ka dawo?”
Kai ya gyada yace
“Na barki da aiki ko yau na jima!”
“A’ah ai ba wani aiki sosai.”
Ta kashe gas din ta juyo ta daura hannun ta a kafadar sa tana fadin
“Muje kayi wanka ko?”
Wani kallo ya kure ta dashi har ta tsargo zata juya yabjuyo da ita yana kashe mata ido daya. Juyawa tayi da sauri tana fadin
“Gaskiya yau ka kaini na gaishe da Umma sannan na debo ya’yana!”
STORY CONTINUES BELOW
“Tab Umma tace yara sun zama nata kema ki haife naki!”
“Kai Yaya nasan kai zaka fada.”
Ta fada tana gyara wajen. Yai murmushi yace
“To shikenan muje kiji.”
Juyowa tayi tace
“Yauwah ni kam Yaya me zai hana Umma ta dawo nan muyi rayuwar mu gaba daya!”
“In munje duk kya fada mata.”
“To shikenan!”
Ta gama gyara wajen ta jere musu komai a dining sannan ta shiga ta fara cire kayan jkin ta. Shigowa yayi ta wuce bandaki. Kaya ya cire yabi bayan ta.
*
Bayan ta fito ta shirya cikin wani blue kalar less wanda akaiwa ado da bakin zare tayi kyau kamar ka sace ta ka gudu. Muhammad ya shirya cikin bakar shadda wacce ta amshe ya kara kya. Dining suka wuce hannun su tsakale da na juna suka zauna tai serving nasu ita ta bashi yana bata a haka har suka koshi suka koma falo.
Karfe biyu ta hada musu wata jallop taliya da taji hanta ta hada musu lemon kwakwa. Muhammad sai santi yake mata sai da suka gama sannan ta shiga daki ta dibar wa Umma turaruka masu kamshi sannan suka fice. Gari suka zagaya dan sai da ana la’asar suka karasa gidan Hajiyar sa.
Suna zuwa ya tafi masallaci ita kuma sai da tayi alwala ta shiga daki ta samu Umma na sallah. Sallah ta tayar itama sai da suka idar sannan suka hau gaisawa. Yaa Muhammad ne ya shigo suka gaisa.
Ummu tace
“Ina yarana Umma?”
“Suna Isilamiyya!”
“Masha Allah. Umma daman nazo ne akan wata magana.”
“To ina jin ki!”
“Umma nace tinda muna da waje isashen me zai hana ki dawo mu zauna gaba daya.”
“Au Wato ya fada miki kin zo kema ki sani a gaba ko?”
Kallon Muhammad tayi tace
“Umma wallahi bai fada komai ba.”
“To Ummu ni ba zan dawo gidan ku ba nan ya fiye min mu zauna a haka kuyi zaman ku nima menene aibun nan din.”
“Babu Umma amman wai kina tare damu zamu na rage miki aiki.”
“Aiki nan din har nawa yake. Ki bar zancen dawowa ta nan kawai Ummu.”
” Shikenan Umma yaushe yaran zasu dawo to!”
“Wane yara Ummu ai yara sai dai su zo muku hutu amman sun zama nawa Allah kema ya baki masu albarka duk ina so in zaku kawo min su.”
Shiru tayi dan kunya ta bata ma. Muhammad yace
“Sai da na fada mata wai zatai miki magana.”
“Kiyi hakuri yanzu na riga na saba da yaran nan rabani dasu ba zanji dadi ba kuyi hakuri dan Allah.”
“Ba komai Umma Allah yasa mu dace!”
“Amin!”
Suna zaune suna ta dan taba hira har biyar da rabi sai ga yaran nan suna zuwa suka rasa gun wanda zasu fara zuwa. Gun Ummu sukai dan sun jima basu ganta ba suna fadi
“Mami ina yini?”
Kansu ta shafa tana fadin
“Lafiya lou ya makaranta?”
Jannah tace
“Lafiya lou!”
Junaid yace
“Anty ina kika tafi kika dade!”
Ta shafa kan su tace
“Ai yanzu na dawo ko yara na.”
Kai suka gyada tace
“To kuje ku gaida Abbi dinku.”
Suka tafi gun Abbin nasu. Nan suka gaishe sa ya dauke su yana tambayar su makaranta. Fita Umma tayi ta barsu suna ta hira da yaran nasu. Sallah magariba ya sa ya wuce da Junaid. Ummu kuma sukai ita da Jannah. Anan suka ci abincin dare sai karfe tara sannan suka tafi kamar kar su tafi bama Ummu da taji dadin gidan ga yaranta.
*
**
***
****
*****
******
*******
********
*********
Hajiyar su ce ta shigo asibitin tai parking ta fito kamar ance ta kalli gefe taga Fauziyya tsaye jikin mota tana danna waya. Da sauri ta karasa tana fadin
“Fauziyya!”
Fauziyya ta dago da sauri tana kallon ta. Hajiyar ta saki murmushi tace
“Ashe dai kece?”
“Nice ina yini?”
“Lafiya lou yanzu da gaske Fauziyya kinyi aure kin bar mu.”
“Eh Hajiya kema Allah kawo miji kiyi.”
“Wa ni me zanyi da aure? Kema da kikai ina nan ina zaman jiran ki dan zaki dawo ki samen ne.”
“Allah rufa min asiri kuma Farisa ma dake tare dake muna nan muna mata addu’a insha Allah zata nutsu.”
“Hmm haka kika ce ko? Daman nasan duk ke kika rabani dasu to wallahi ki sani Fauziyya ba zan taba barin ki ba.”
Wani murmushi mai ciwo Fauziyya tayi tace
“Allah yafiki. Kuma ba abinda zai faru dani sai alheri ni ban cuci kowa ba dan haka Allah ba zai baki ikon cuta ba tinda na tuba na koma gareshi a baya ma abinda ya faru dani kaddara ce kuma ina rokar Allah ya yafe min. Kuma kema ina rokar Allah ya shirya ki.”
“Ba yanzu ba sai na karasa cin duniya ta da tsinke. Kuma la lashi zumar ki.”
“Duniya bata da tabas domin in yau kece gobe bake bace. Kuma ni mafi karfin ki ko da banyi aure ba bana lesbian bare a yanzu dan haka ki sani Allah yana tsare dani kuma shi zai tsare ni.”
Muhammad ne ya karaso ya kalle ta yace
“Lafiya dai ko?”
“Lafiya lou Baby mije ko?”
“Ba lafiya ba domin nasan baka san wa ka aura ba shiyada kake zaune da ita to wannan da kake gani….”
“Wa ya fada miki bansan wacece ita ba?”
Ya katse mata maganar tata.
“To na fiki sanin.wace Fauziyya kuma abinda ya faru da ita kaddara ce wanda baya wice kan kowa ba. Ki kiyayi bakin ki in ba haka ba zaki tsinci hakoran ki a kasa dan bana laminta a taba min Fauziyya da ki taba ta gwara kin tabani.”
Ya kamo hannun Fauziyya ya saka ta a mota ya rife ya koma gefen sa. Duk Hajiya na tsaye tana kallon su. Reversed yayi Sakina dake ciki ta dagawa Hajiya hannu tana mata gwalo.
Kwafa Hajiya taui ta shiga kotar ta ta bar asibitin. Tana kan titi ta fara kiran layin Yaron ta. Yana dauka tace
“Ya ake ciki akan aikin nan.”
“Hajiya na kira kuma ina tura sakon sai dai ranan an min kashe di abinda ya bani tsoro kenan.”
“Dallah ba biyan ka nayi ba kacigaba ba abinda zai faru kaji ko.”
“Shikenan.”
Ta kashe ta fara kiran wayar Boss. Yana dauka tace
“Boss har yanzu baka samo address din yarinya ba bare ka kawon ita.”
“Hajiya bata garin ne fa.”
“Inji wane dan iskan yanzu in ganta zaka ce min bata garin.”
“To ai mu haka aka ce mana.”
“To na baku nan da kwana uku ku kawon yarinyar nan kuna ji na ko?”
“An gama Hajiya.”
Ta kashe wayar ta fara neman layin Malamin ta yana dauka tace
“Malam ya ka duba min?”
“Na duba amman shiru dai. Kuma in har baki cika abunda na fada miki na neman yaran nan su hudu ba komau naki ya gama lalacewa.”
“Na shiga uku yanzu yaya zanyi?”
“Ya rage naki.”
Ya kashe wayar. Gefen titi ya paka ya kifa kanta a kan sitiyarin motar tana mai sakin kuka. Yanzu yaya zatayi kada duniya ya juya mata baya.
*
Suna zuwa guda su Sakina suka fice Muhammad ya kalle ta tayi kasa da kai tace
“Ka yafe min dan Allah!”
Hannu ya daura akan bakin ta yace
“Shitt. Baki min komai ba Baby. Ki sani ina sonki Allah ya kare min ke ya kiyaye min ke.”
Jikin sa ta fada tana fadin nagode Sosai Baby wane irin mutum ne kai?”
“Kamar yadda kike sai dai ni an hallice ni dan na sokine kawai.”
“Nagode Baby Allah saka maka da alheru.”
“Amin Baby.”
“Yaushe zamu tafi.”
“Sai magariba.”
“Allah kaimu.”
“Amin!”
Yai kissing nata sannan sukai sallama ta bude mota ta fita.Tana shiga gida suka wuce dakin su. Kwance ta samu Halima. Tace
“Tashi kici abinci ki sha magani!”+
Ta kalli Sakina tace
“Kawo mata abinci!”
Ta mike ta fita. Tace
“Halima ki rufawa kanki asiri ki cire damuwar wani da namiji akan tunanin yaron nan nasan shi kika saka a ranki duk ya janyo miki haka. Haba Halima shi yana can kila ya manta da ke, amman ke kun sa damuwa a ranki.”
“Anty nima ba shi naket tunani ba.”
“Me kike tunani to?”
“Anty nayi babban laifi ga Allah dan gaka dile nji tsoron haduwa ra dashi wannan ke.kara saka min fargaba da tsoro a raina.”
Tai murmushi tace
“To naji sai me?”
“Anty a *wannan rayuwar* wa zan aura? Wa zai soni?”
Kai ta gyada tace
“Dole kiji tsoron haduwar ki da Allah domin kowa ma.yana jin tsoran haduwar sa dashi ta yadda zaki ji saukin haduwar ki dashi shine ta tuba da yawaita istigifari abinda kikai ki roki Allah ya yafe miki sannan ki tsarkake zuciyar ki ki mike da bautar Allah. Allah gafuru haramin sai kiga ya yafe miki.
Abu na biyu in har kika mika komai ga Allah a sannu komai zai zo miki da sauki, kina zaune Allah zai kawo miki miji na gari wanda zai rufa miki asiri. Ba a cire rai da rahamar ubangiji.”
Hawaye ne ya zubowa Halima. Fauziyya tace
“Dan haka ki daina saka damuwa in damuwa tai miki yawa kika mutu baki gama rokar Allah yafiyar ki ba. Kina rokan Allah ya baki tsawon ran dazaki na masa ibada ba ki mutu ba.”
Ta dafa Halima tace
” Dan Allah ki daina saka damuwa ina tare dake kuma zan shige miki gaba a komai. Da so nayi a hada dake da Hafsa da Sakina har ma da Hajara ai muku aure amman zamu jira muga me Allah zai yi kila ka lokacin dukka kiga kema Allah ya kawo miji miji na nunawa sa’a. Kiyi ta addu’a da tuba Allah ya yafe miki.”
“Nagode Yaya Fauwaziyya hakika samun ki a matsayin Yaya ya fi min komai. Kin zama mana uba da uwa da katanga Allah ya jara girma yasa ki gama da duniya lafiya Allah rufa miki asiri ya baku zaman lafiya ya kawo ya’ya masu albarka nagode Yaya.”
“Kada ki damu kanwata. Ba godiya a tsakanin mu in ban muku ba wa zanyi wa?”
“Haka ne amman dole nayi”
Sakiata shigo ta ajiye mata abincin tana fadin
“Ai kuwa dai mungode gashi ta dalilin ki zamuyi aure dan in ta Baba ne ai mu mutu ba aure.”
“A’ah ba haka bane gani yake kawai ba mu girma shima rashin zama tare ne yasa hakan.”
“Ke bakya ganin laifin babane kawai.”
“Mahaifin mune fa.”
“Amman shine ya jefa mu ga fadawar ga halaka ko?”
“A’ah fa shine sila dai. Amman wannan jarabawar muce. Kuma a yanzu neman yafiyar Allah muke shi da mukaiwa laifi to dan me bazamu yafewa Baba ba. Dan Allah ku yafe masa”
“Uhmm!”
Suka fada gaba dayan su. Haka ta dinga tausar su har ta bawa Halima abinci taci ta sha magani ta kwanta.
Karfe tara yazo ya dauke ta suka tafi. A hanya ya tsaya ya siya musu Yahuza suya sannan suka wuce gidan su. Suna shiga tayi dakin ta ta cire kaya ta shiga tai wanka. Wasu kayan bacci ta saka masu kyau sosai. Tayi lighy make up ta fito a Fauziyya :eauty din ta. Falo takoma ta zauna tana kallom TV. Wanda azahiri TV take kalla amman a badili ba shi take kalla ba tunanin rayuwa kawai ta.
STORY CONTINUES BELOW
Yadda rayuwar su ta baya ta kasance sai gashi yai ita ce ta auri babban mutum kamar Muhammad. Namiji daya tamkar ya dubu wanda yake da dabi’u masu kyau mai son ra kyakywa mai asali da ilimi. Ji gidan ta shin me zatayi in ba godiya ga Allah ba.
Bayan duk laifukan ta Allah ya amshi ta ya bata wannan mijin me son ta shin me zatai inba godiya ga Allah ba.
“Alhamdulillah. Allah kara mana zaman lafiya da kaunar junan mu.”
Ido taji an rufe mata ta baya. Murmushi ta saki tana fadin
“Baby.”
Ya karaso ya tsaya yana kallon.ta. murmushi ta saki tai kasa da kan ta. Shima murmushin yayi yace
“Baby kinyi kyau.”
Ya kama hannun ta ya mikar yana binta da kallo.
“Nagode amman ka fini kyau.”
Ta kama hannun sa ta zaunar akan kujera ta nufi kitchen yacr
“Me kuma zakiyi?”
Ledar gaban sa ta nuna masa ya mike da sauri yana fadin
“Dawo ki zauna bari na dauko.”
Ta saki murmushi tana fadin
“Haba Baby dauko plate din kawai.”
“Bana son matata ta wahala.”
“But ina son aljanna.”
“Indai Aljanna ce kuma ta waje na zaki samu na baki Baby Allah baki ita madaukakiya.”
Ta rumgume shi tana fadin
“Allah ya hada mu acan.”
“Amin Baby!”
Haka suka shiga suka dauko ya zuba musu suka ciyar da juna bayan sun gama suka baje a falon suna kallo. Yana kallo yana tsokano ta har sha daya saura suka kashe kayan kallon suka wuce daki dan yin bacci. Sai da suka sha soyayyar su wacce kullum tamkar sabuwa suke jin ta. Dan yadda Muhammad ke jin ta kullum kamar sabuwa gashi ya iya soyayya da kula da tarairaya. Wanda in kana tare yake mantar da kai komai. Daga shi har ita yan baiwa ne da kullum cikin kuka suke da goduya ga Allah da ya mallaka musu junan su.
Dan sam.Fauziyya bata san wani dadin sex ba in ba akam Muhammad ba duk wanda tayi a baya tayi shi ne dan ba yadda zatai ba a son rai ba wanda bata jin dadin sa bata samun nutsuwa sai a yanzu da ta hadu da jarumin namiji. Kamar yadda shima yake godiya da Allah ya bashi yar baiwa mai ni’ima wacce yake kwasar garar sa. Shi kadai yasan me yake samu a wajen ta. Da kyar suka bar junan su dan sai bayan biyu sannan sukai baccin.
*
**
***
****
*****
******
*******
********
*********
**********
Yana fita ya fara mamakin me ya kai Isma’il gidan su Sadiya. A haka ya karasa gida ya kwanta yana tunanin yadda zai tsara rayuwar sa na auren mata biyu a lokaci daya.
Anya baiyi wauta ba baiyi kankanta ba. To in har yayi hakan ya zaiyi da alkawarin da yayi da zuciyar sa na zai auri Halima da wanda yai wa Sadiya. Tabbas ba kyau karya alkawari dan haka dole ya aure su duk biyun.
Hakika zai yi jahadi kuma dole ya tusawa Isma’il bakim cikin auren Sadiya kuma ya auri Halima kamar yadda yace in ya cika mai tausayi. Kuma tabbas zai girbi abinda ya shuga Allah zai kama shi akan yaudarar yan matan da yayi haba daya.
Yana kwance yaji ana kiran magariba alwala yayi ya tafi masallaci. Bai dawo ba sai da akai isha’i. Falon Mamin sa ya wuce ya zauna yana kallo. Da ta fito ta ganshi ta zauna tama fadin
“Lafiya dai ko?”
Kai ya sosa. Tace
“Me yake damun ka.”
“Ba komai.”
“Ba komai dai ba komai dai kullum Allah ya nunan lokacin da zaka fada min damuwar ka dai.”
Yao murmushi yace
“Mami ai babu ne shiyasa.”
“Hmm Allah yasa.”
Yai murmushi. Tace
“Kaje kaci abinci to.”
Ya mike ya karasa ya zuba abincun. Tana kallon sa da kyar yake cin abincin shima dan kar tace baya ci ne. Haka ya gama cakula ya dawo falon ya zauna. Mami ta kalle shi tace
“Wai ina sirika ta ne ya jilkin?”
“Da sauki.”
“Yaushe za ai abun ne Kabir?”
“Mami an kusa insha Allahu.”
“Allah tabbatar da alheri.”
“Amim.”
Agogo ya kalla yaga tara tayi mikewa yayi yace
“Mami zanje na kwanta sai da safe.”
“To Allah bamu alheri.”
Har ya kai kofa tace
“Ni kuwa ina Isma’il kwana biyu!”
“Yana nan Mami aiki ne yai masa yawa.”
“Ka gaishe min dashi.”
“Zaiji!”
Ya fita ya nufi dakin sa. Kan.kujera ya zaua ya zaro wayar sa.
Ba abinda yake so.yaji in ba muryar Halima ba amman tayaya to. In ya kira me zai ce. Sai ya fara dailing sai ya kashe yayi haka fin sau biyar sannan ya daure ya bara ta ta tafi.
Tana kwance bayan tafiya Fauziyya tasha magami ta kwanta taji wayar ta na kara hannu ta sa ta dauka bata damu da duba waye ba kawai ta kai kunnen ta. Sallama yayi ta amsa sai yaji muryar ta wani iri yace
“Kina lafiya dai ko Halima?”
“Uhmm wallahi Kabir bana jin dadi!”
“Me yake damun ki inzo na kai ki asibiti?”
“A’ah dazu Anty Fauziyya ta kaini.”
“To me yake damun ki?”
“Wai jini nane ya hau.”
“Ya salam Halima ban hanaki saka damuwar nan ba.”
“Kabir nifa ba wata damuwa dake raina a yanzu komai ya wuce.”
“Amman ya akai haka.”
“Nima ban sani ba.”
“Jiya kin min alkawarin ba zaki kara kuka ba yau kimin alkawarin ba zaki kara damuwa ba.”
Shiru tayi yace
“Bazaki iya ba ko?”
“Xan iya!”
“To ina jin ki.”
“Nayi alkawari ba zan sake damuwa akan abokin ka ba.”
“Yauwah yan mata yanzu ya jikin?”
“Da sauki.”
“Kinsha magani?”
“Nasha.”
“Yanzu ya kike ji?”
“Naji sauki.”
“To Allah kara sauki.”
“Amin!”
“Kijr ki kwanta kinji sai da safe.”
“Nagode Kabir.”
“Never mind!”
Ya kashe wayar yana jin nutuswa yaji muryar ta.
Sadiya ce ya fado masa ko ya itama jikin nata. Neman layin ta ya fara. Har ta kwanta itama taga kiran sa cikin farin ciki ta dauka tana sallama. Ya amsa yana fadin
“Ah lallai jiki yai sauki!”
“Alhamdulillah!”
“Masha Allah ya na baro ki.”
“Lafiya lou sai kewar ka.”
“Da gaske?”
“Eh.”
“To kinci abinci?”
“Naci.”
“Magani fa?”
“Shima haka.”
“Yanzu sai bacci kenan.”
Kai ta gyada sai kuma ta fara jan sa da hira. Tin tara da rabi sune har sha daya saura sannan sukai sallama kowa ya kwanta. Daki ya mike ya shiga ya watsa ruwa shima ya kwanta.
*
Washe gari da yamma ya shirya xai je gidan su Halima ganin yayo ta hanyar gidan su Sadiya ya karasa yai parking kiran ta yayi yace
“Gani a cikin gidan ku fa.”
“Kai da gaske?”
“Fito ki gani.”
Ya kashe wayar. Yana tsaye ta leko ta barander dan ba su jima da waya ba bai ce zai zo ba kuma ba abinda take so in ba yazo din ba.
Dan haka da gudu ta koma ta yafo mayafi ta fito ta same shi tace
“Wai sai kana tsayawa anan!”
“Ai tafiya zanyi nazo na ganki ne kawai.”
“Ina zaka? Amman ka shigo ko ruwa ne kasha ko?”
Yai murmushi. Tace
“Please!”
“Shikenan muje!”
Anan.ya shiga ta kawo masa ruwa da lemo. Bai sha komai ba bayana awa daya yai mata sallama dan yau yana son yaga Hafsa sosai.
Sai dare Muhammad yazo ya dauki Fauziyya suka tafi. Bayan ya tafi Hafsa ta kwanta wayar ta taji tana kara tana dubawa taga Ahmad ne. Dauka tayi cikin sanyin murya yace
“Baby na lafiya?”
“Lafiya alhamdulillah.”
“Anya naji muryar ki haka.”
“Ba komai fa!”
“Kinyiwa Yaya Fauziyya maganar.”
“Na mata amman in kazo mayi maganar.”
“Da akwai matsala ne?”
“Babu.”
“Shikenan ai gobe muna tare.”
“Allah kaimu.”
“Amin. Wai bacci kika fara ne?”
“A’ah but your voice show akwai wani abu.”
“Eh Deedat tsoro nake ji!”
“Wanne irin tsoro?”
“Kada wata rana ka juyan baya.”
“Baby ba abinda zai sa na juya miki baya.”
“Ka tabbata?”
“Na tabbata to me zai sa na juya miki baya ina sonki!”
“Kasan halin mazan.”
“Ki cire haka akai na.”
“To Allah yasa.”
“Baby na miki alkawarin har abada ba zan juya miki baya ba.”
“Allah ya yadda.”
“Zan kula dake zan faran ta miki nai miki duk abinda kike so.”
“Nima zan maka biyayya insha Allahu.”
“Allah ya yadda ba zaki soni ba.”
“So kuma na nawa!”
Yai murmushi yace
“Kina so na?”
Kai ta gyada tace
“Eh ina son ka.”
“Godiya nake.”
Tai murmushi. Yace
“Me kika tanadar min gobe?”
“Me kake so?”
“A’ah ai ni na fara tambaya.”
“Shikenan zan tanadar maka kaina gobe zaka ganni zan maka kwalliya sannan da wani albishir.”
“Dan Allah da gaske?”
Kai ya gyada yace
“Godiya nake amman da ki fadan albishir din na kagu naji.”
“A’ah sai goben?”
“To ni me kike so na kawo miki?”
“Kai kadai nake so Deedat!”
“Ai daman ni naki ne.”
“Wannan haka yake to ganin ka kawai nake so.”
“Kada kisa na taho yanzu.”
“Ah haba Madam din fa da kace tare zaku zo.”
“Gobe ta taho.”
Tai murmushi tace
“Ka kwantar da hankalin ka Allah dai ya kaimu goben.”
“Amin amman kinsan kuwa mun fi wata ukun da na diba.”
“Kai Deedat!”
“Wallahi kinga lokaci ya kusa ko?”
Tai murmushi tace
‘Kabi komai a sannu.”
“Haba Baby duk wannan bin da nake a sannu.”
Tai murmushi tace
“Shikenan dare yayi ka tafi wajen Anty na.”
“Ai tayi bacci ni kuma na kasa shuyasa na kira ki mu sha wayar mu”
“Da gaske?”
“Eh!”
“Toh ya labari?”
STORY CONTINUES BELOW
“Labari sai na yadda son ki ya hanani sakat komai nake hankali na.na.wajen ki ke kawau nake so na gani mafarki na kullum naki ne buri na ga kin zama tawa.”
“An kusa insha Allahu.”
“Allah ya yadda ban san wane farin ciki zan shiga ba. A lokacin da zan kwana a jikin ki!”
Gaban ta ne ya fadi a ranta tace
“Ko ya wannan ranar zata kasance?”
Da wanne ido zata kalli Ahmad. Tsoro ya kamata yace
“Kina ji na Baby!”
Da sauri ta dawo daga tunani tace
“Eh!”
Yace
“Me kika tanadar wa wannan ranar?”
“Tsoron zuwan ta nake.”
“Haba dai cool down ba wani abu za ai ba fa. Just soyayya zamu sha mu kwana zubawa furen mu ruwa.”
“Hmm Deedat kenan. Allah nuna mana ranar amman ina fatan zaka amshe ni a duk yadda nake.”
“Haba Baby xan zo ki a duk yadda kike zan so ki ko ba ido da hanci da kafa da hannu ni ke kadai nake so.”
“Nagode da soyayyar ka Deedat Allah tabbatar mana da alheri.”
“Amin Amin!”
Haka suka raba dare tare yana ta narka mata zuciya da kalaman sa masu sanyi. Wanda suka saka masa nutsuwa da farin ciki. Duk kwanan farin ciki suka yi dan sun sha hirar soyayyar su.
*
**
***
****
*****
******
*******
********
*********
Ummu da Muhammad zaman lafiya suke basu da matsalar komai. Da safe yaje aiki karfe hudu ya dawo a lokacin zai samu kulawa da tarba ta musamman. Dan an hada masa abinci kala kala da lemuka sosai yake samun kula da soyayya. Daga shi har Ummu sun kara kyau sunyi kubul kubul dasu.
*
Da safe da ya tashi ita ta hada masa ruwan wanka hatta wankan ita ta taimaka masa yayi ta fito ta goge masa jiki ta shafa masa mai ta dauko kayan sa da.under wears din sa duk ta saka masa ita ta shirya sa ta shafa masa turare bayan ta gama ta tsaya tana kallon sa tana fadin
“Yaya kayi kyau!”
“Kin fini kya Ummu na.”
“Kai haba dai.”
Gaban mudubi ya kai ta yace
“Kalli fa.”
Ta juyo tace
“Nafison na ganka da na ganka ta mirrow.”
Yai kissing goshin sa. Tace
“Muje kaci abinci kada ka makara fa.”
“Wallahi Ummu ji nake kamar na ajiye aikin nan. A cigaba da mana business din mu.”
“Saboda me?”
“Saboda na kasance dake.”
“Haba Yaya ai kullum muna tare bayan anjima zaka dawo.”
“Hmm baki ji yadda nake ji ba wallahi dan fitar da nake.”
Ya janyo ta jikin sa. Tace
“Kayi hakuru wata rana sai labari.”
“Hake ne. Ummu na.”
Ya kama hannun ta suka fita falon. Ita ta ciyar dashi yaci ya koshi sannan ya fito har bakin mota ta kai shi tana masa addu’ar Allah kiyaye hanya sannan ta dawo.
Hada hadar abincin rana ta fara. Tayi masa Chinese fried rice wacce ta koya a group din Amrah Auwal Mashi wato kitchen pride. Dan group din sosai take karuwa da shi ta hanyar koyan abinci kala kala na zamani da gargajiya. Kayan amfanin ta ta sama kamar haka
4 cups cooked rice
2 onions
1 tablespoon grinded scotch bonnets (optional)
Seasoning to taste
1 cup carrots and green beans
1 teaspoon curry powder
1 teaspoon ginger and garlic paste
1/2 teaspoon turmeric (I used fresh one)
1/4 cup stock
4 tablespoons vegetable oil
1 teaspoon mixed spices
Pinch of parsley flakes
1/4 teaspoon nutmeg
Fried meat/sausage or whatever😹
3 eggs (ki yi scrambling inshi without anything only egg din)
Ta zuba oil a pan ta zuba sliced onion, ginger and garlic paste. Ta zuba grated turmeric. Ta jujjuya a hankali. Ta zuba carrots and green beans, da yake tana son attaruhu sai ki zuba, ta zuba seasonings and spices ta jujjuya sosai har taji ya fara kamshi sosai, ta rage wutar har veggies din sun yi taushi sosai. Sai ta zuba parsley ta motsa. Ta zuba shinkafa wadda ta san ta gama tsanewa sosa. Ta jujjuya a hankali sai ta juye scrambled egg din ta motsa sosai. Ta zuba ruwan stock ta rufe da wuta kadan ya yi steaming. Sai ta kashe ta zuba soyayyen nama kina juyawa a hankali.
Tana gamawa ta yanka cabbage ta gurza carrot ta yanka cucumber sannan ta yanka dafafen kan ta ta hada caslow ta saka a cikin firij. Kwakwa ta dauko fa kankare bayan ta sannan ta wanke ta dauki blender ta markada sannan ta tace ta zuba madara da sugar da flavour ta saka a firij.
Kitchen din ta gyara ta wanke komai. Sallah aka kira tanshiga tayi alwala tayi sallah. Bayan ta idar tana kan sallaya sai ga kiran Muhammad nan. Dauka tayi tai sallama. Ya amsa tace
“Yaya ya aiki?”
“Alhamdulillah nayi missing matata ya gidan?”
“Lafiya lou.”
“Kinci abinci?”
“A’ah”
“Saboda me?”
“Sai ka dawo.”
“A’ah ban yadda ba yanzu ki tashi kici kinji.”
“To Yaya kai fa?”
“Ni bayan kin cika min ciki na.”
Tai murmushi tace
“To kasha ko nutrimilk ne please.”
“Shikenan nagode sai anjima!”
Sukai sallama. Kitchen ta shiga ta dauki kaza ta yayyanka sannan ta tafa sa bayan ta gama ta hada jajjagen attaruhun ta tayi pepper chicken. Ta saka a plate tayi raping nasa sannan ta ajiye akan dining ta kai flask din ta da ta hada masa abinci. Duk ta ajiye. Falo ta dawo ta zauna ta kallo tana cin naman da tayi da lemo. Ta gama ta kwanta. Bacci ne ya dauke ta bata farka ba sai hudu saura da sauri ta mike taba mika ta shiga daki wanka tayi ta shirya cikin wata purple din atamfa mai star anyi star din da peach tayi kyau dinkin riga da siket ne off sholder farar fatar ta ta fito. Ta gyara kan ta tayi daurin ta mai kyau ta shafe jikin ta da turare kala kala masu dadin kamshi. sosai tayi kyau ta dawo kamar amarya.
Falo ta fito ta dawo tana zaune taji horn dinsa agogo ta kalla taga biyar saura kwata. Mikewa tayi a corridor ta hadu dashi ta rumgume shi tana fadin
“Barka da zuwa Yaya na.”
“Barka kadau Baby na ya gidan?”
“Gashi nan ba dadi dukka.”
“Ah haba dai saboda me?”
“Baka nan kai ke haskakan gidan in ka fita duk gidan duhu.”
Daukar ta yayi gaba daya suka wuce akan kujera ya ajiya ta ta mike ta dauko masa lemo da ruwa ta zuba masa ya amsa ya sha sannan ta kama sa sukai daki ta taimaka masa ya cire kayan sannan ta hada masa ruwan wanka ya shiga. Ita kuma ta koma tana gyara kan dining. Yana fitowa ya shirya cikin kananun kaya. Yana cikin shafa turare ta shigo. Tace
“Yaya na yayi kyau.”
Ya kamo hannu ta yana fadin
“Kema haka Baby!”
“Muje kaci abinci ka dade yau.”
Suka karasa dining ta zuba masa abinci nan ta fara santi. Bayan sun gama suka koma falo suka xauna suna hira har aka kira magariba.
Ya tafi masallaci ita kuma tayi sallah a guda tana idar wa ta shiga kitchen ta hada faten dankali wanda yaji hanta da vegetable tayi shi yai ruwa ruwa sannan tafita ta barshi ya karasa dahuwa dan an kira isha’i. Tana idarwa ta koma ta sauje ta canja kaya zuwa egliish wears masu kyau. Ta fito falo ta zauna tana can carbi.
Muhammad na shigowa yayi tazali da ita yaji wani abu na taso masa. Da sauri ya mike ya karasa wajen ta yana fadin
“Baby na kinyi kyau.”
“Thanks”
Nan suka zauna suna hira abinsu. Wajen takwas ta kawo masa faten tare suka ci yana ta sanyi abinsa.
Haka rayuwar su ta cigaba da tafiya cikin kwanciyyar hankali da fahimtar juna da soyayya.
Kabir yaiwa Yaa Hafsat waya ya fada mata ranar zuwan su. Bayan sun gama waya ya kira Halima ta dauka nan suka gaisa suka taba hirar su sannan sukai sallama. Sadiya ya kira yana dauka suka gaisa sannan yace
“In nace xan turo gobe nayi wuri.”+
“Tayaya xance kayi wuri Kabir Allah kaimu da safe sai na fadawa Abbi.”
“To shikrnan ina fatan kina sane da ku biyu ne.”
“Ba matsala zan fadawa Abbi.”
“Nagide Sadiya.”
“Nice da godya Kabir”
“Aah nine ni da ake so na.”
“Aah ni dai ni da aka amshe ni”
Haka sukai tayi kowa yaki ya yadda har Abbi nata ya dawo ya leko ta wannan yasa tace
“Ina zuwa Kabir.”
Ta kashe wayar ta mike tana fadin
“Sannu da zuwa.”
“Yauwah ya gidan?”
“Alhamdulillah!”
“Ba dai matsala ko?”
“Babu Abbi amman ina son muyi magana.”
“To!”
Ya zauna yace
“Ina jin ki.”
Tace
“Abbi daman wanda yake so nane yake son ya turo gobe.”
Sai ta rufe fuskar ta da hannun ta. Abbi yace
“To toh dan waye?”
“Nan taiwa Abbi bayani.”
“Abbi yace
“to Allah ya kaimu.”
“Amin amman Abbi mu biyu zai hada a lokaci daya.”
“Ku biyu kuma Sadiya?”
“Eh Abbi!”
“Ke ba matsala a wajen ki ko?”
“Babu Abbi na aminta.”
“To Allah yasa haka ne mafi alheri. Allah ya hade kawunanku.”
“Amin Abbi nagode.”
Ya mike yace
“Sai da safe.”
“Allah bamu alheri.”
Ya tafi ta dauki waya ta kira Kabir suka cigaba da hirar su.
*
Ranar da zasu zo kuwa Yaa Muhammad da Baba suka tarbe su. Suka zauna cikin gurma da arziki. Bayan gaishe gaishe. Uncle din Kabir yace
“To mu dai dan mu Kabir yaga yar ku kuma yana so munzo gaba daya zamu ba kayan komai da aure da saka rana sai kuyi bincike kan cikar lokacin in kunga ba wata matsala shikenan lokaci nayi sai a kawo laifi da biki in da matsala kuma sai muce shikenan Allah haka nemafi alheri.”
Baba yace
“To shikenan”
Nan suka dire komai sukace suna auren nan da wata daya. Yaa Muhammad yace
“ba matsala in mun bincika munga ba matsala zamu aiko da mun baku ita.”
“Muna godiya amman ina fatan kunsan su biyu zai aura a lokaci daya ko?”
Yaa Muhammad da yasan da komai yace
“Eh ya sanar damu.”
“To madalah!”
Nan sukai bankwana. Sai da suka tafi Baba yace
“Wanne bincike za ayi ai da an basun kawai”
“A’ah Baba abi komai a tsari itama Haliman tafi daraja a idon dagin mijin ta.”
“To ai shikenan!”
Yaa Muhammad ya mjka masa kudin yace
“To Baba gasu”
“Ai da ka ajiye kan zuwan sauran ko?”
“Haka ne!”
Nan sukai sallama shima ya tafi. Gida ya koma yaiwa Fauziyya bayanin komai. Ya bata kudin ta ajiye. Tace
“Mungode Baby Allah saka da alheri.”
STORY CONTINUES BELOW
“Amin. Amman bana son godiyar nan.”
“Kayi hakuri!”
“Ai bakya laifi!”
“Nagode!”
Sai ta zaro ido ta daura hannu akan bakin ta.
A lokacin yasa ayo masa bincike kan kace mai an kawo masa rahoto daga gida har abokan kasuwancin sa da abokan sa. Bashi da aibu sam.yaro ne.mai hankali da biyayya bai taba fada da kowa ba kuma baya shashanci duk da Allah ya rufa masa asirin dukiya.
*
Mahaifan Kabir daga na gidan su Sadiya sukaje nan ma ankarbe su hannu bibbiyu sannan sukai muusu bayani kamar yadda sukai a gidan su Halima. Suma.feedback din thesame da na gidan su Halima akan za a aiko in an basu. Wato in sunhi bincike haka suka koma sukaiwa Mamin sa bayanin komai.
*
Da yamma bayan ya dawo ya wuce bangaren Mami. Ya zauna suka gaisa. So yake ya tambaye ta amman sai yaji kunya ganewa da ita tace
“Uncle din ka sun dawo.”
“To Mami.”
“Duk sun amshi abinda aka kai sai dai sunce zasi aiko in sun baka dan sai sunyi bincike.”
“Masha Allah. Allah tabbatar da alheri.”
“Amin!”
Nan ya mike yaci abinci yai dakin sa. Cike da murna.
*
**
***
****
*****
******
*******
********
*********
**********
Sosai Allah ya budawa Muhammad. Wanda ya zama ga aikin gwamnati ga kasuwan ci dan haka ya zama babban alhaji ya kara kiba yai kyau saboda da kula da yake samu daga Ummu Itama tayi kyau bama da take da karamin ciki.
Yau weekend duk weekend ba inda yake fita yana falo shida Su Jannat da Junaid wanda suka zo musu weekend jiya jumma’a. Muhammad sanye da three quarter da riga suma yaran Ummu ta shirya su cikin kannanun kaya masu kyau sunyi kyau Ummu ce ta fito daga kitchen sanye da doguwar riga yar kanti mai kyau ta gyara gashin ta ya zubo a vayan ta. Plate ta ajiye musu wanda daya yake dauke da cake da donot da meatpue dayan kuma cookies ne da peanut a ciki ta koma ta dauko musu lemo ta ajiye.
Zama tayi tace
“Yaa Muhammad yaushe zamu gidan Yaya Zainab!”
“Wallahi suna raina ko gobe muje?’
“Yaya in munje gobe mu dawo yaushe?”
“Gobe mana.”
“Kaga tinda su Jannah sunyi hutu da mu muje muyi sati kai sai ka dawo.”
“Ba xan iya ba.”
“Please!”
“In kika barni zan shiga wani hali.”
“To next friday sai mu tafi mu dawo monday gaba dayan mu.”
“Allah kaimu.”
Knocking aka yi. Ummu ta mike ta karasa kofar. Rukayya ce ta shigo tana ganin ta ta ce
“Lah Yaya Rukkaiyya. Sannu da zuwa.”
“Yauwah!”
Ta bata amsa ta shiga. Junaid dake kan kafar Abban saya dago yana kallon su. Agefen sa ta zauna tace
“Ina yini Yaya Rukayya?”
“Lafiya lou ya gidan?”
“Alhamdulillah.”
Ummu ta kalli Jannah da Junaid tace
“Ku gaisar da Ummun ku.”
Kallon ta sukai sukace
“Ummie mu kece Ummin mu ba ita ba.”
Ido ta zare musu tace
“Ba xaku gaishe ta ba kenan.”
“Ina yini?”
Jannah ta fada. Junaid ya kalli Baban sa yace
“Abbu mu bar nan.”
Daukar yaron yai ya kalli Jannah yace
“Dauko min wayoyi na.”
“Ta dauka suka gaba har ya wuce ta tace
” ina yini?”
Bai kalle ta ba ya amsa. Ya wuce. Ummu ta mike ta kawo mata snack tace
“Ba a sauke abincin rana ba ki dan taba.”
Nan suka zauna suna dan hira. Can wayar tatayi kara tana dubawa taga Muhammad.tana dauka yace
“Me kike ne kin bar mu mu kadai?”
“Yaya kasan Yaya Rukkayya ce tazo.”
“To kizo.”
“Toh!”
Ta kalle ta tace
“Bari naje ina zuwa.”
Ta shiga zaune taga yaran suna game shi kuma yana zaune ta karasa ta zauna tace
“Gani.”
“Family ya hadu babu ke.”
“Kai Yaya! Yaya Rukky ce fa tazo.”
“Shine me bakuwa ce?”
Jannah tace
“Ummie zo ki shigar min.”
Junaid ya dago yace
“Abbi nima shigar min”
Suka miko musu wayar amsa sukai suna bugawa. Jannah da Junaid na ta ihu duk wanda yaci a haka Ummu ta cinye Muhammad Jannah ta mike tana ta tsalle.
Wayar ta mike masa tace
“Ana kiran sallah fa.”
Alwala sukai ya fita masallaci shi da Junaid ita kuma sukai alwala ita da Jannah suka fita falo. daki ta kai Rukayya tai alwala tai sallah.
Muhammad da Junaid na dawowa a dining sukai tsaya na Ummu tai serving nasu. Lokacin da Rukkay ta fito. Tace
“Bismillah Yaya Rukayya.”
Ta karasa ta zauna akan kujera. Muhammad ne ya mike yace
“Ki kawo mana daki na kawai.”
Ya kama hannun ya’yansa sukai ciki. Daukar musu tayi takai musu sannan suka zauna suka ci tare.
Sai yamma ta tafi. Baya ta bata abubuwa da yawa ta tafi. Tana daki tana waya Yaa Muhammad ya aiko Jamnah tazo tace tazo su fita.
Ummu tace
“Kice ni na gaji kuje kawai.”
Tana komawa ta fada masa ya ce
“Ku zauna ina zuwa.”
Ya nufi dakin ta. Ya ganta rike da waya ya shiga ya zauna yace
“Nace ki shirya zamu fita kika ce me,?”
“Ni ba zani bane!”
“Akan me?”
“Kawai.”
“A’ah Ummu nah fada min me akai miki.”
Kallonsa tayi tace
“Bama kasan me kai min ba!”
“Tayaya zan sani.”
Idon ta ne ya kawo ruwa tace
“Yaya yanzu ya dace abinda kayiwa Yaya Rukayya!”
“Me nai mata?”
“Amman ka sakar mata kuyi hira ko?”
“Akan me Ummu!”
“Ko dan ita yata ce kuma ya’yan tane ka debe su bata samu damar ganin su ba.”
“Wayace miki tana son ganin su.”
“Yaya ya’ya da uwa fa.”
“Ummu kada wanna ya kawo mana sabani a tsakanin mu. Ni ba mu’amalar da zan iya da Rukayya gaisawa ta ita amman daga haka shikrnan. Ya’ya kuma tayi wasa da damar ta kina jin abinda Jannah ta fada dazu dan haka kece uwar su har abada.”
Kukan karya ta saka masa nan ya hau lallashin ta da kalamai masu sanyi da daga nan suka wuce duniyar masoya sai da suka sha soyayya sukai wanka suka shirya suka fice zaga gari.Karfe hudu da rabi Muhammad ya dawo. Yai parking Fauziyya ta fito ta kama hannun sa suka shiga ciki. Dining ta kai shi sai da ta ciyar dashi yaci ya koshi sannan suka koma falo tana jikin sa suna hira.
“Wai su Ahmad da Khaleel sunzo.”+
“Eh mana bakaga motar su ba.”
“Tayaya zan gani ina tare dake.”
Tai murmushi tace
“Sunzo suna can.”
“Masha Allah”
*
Hirar soyayya suka sha abinsu wanda karfe biyar suka fito dan zuwa su gaida Yaa Muhammad. A kofar falon da Sakina take ta karasa tayi knocking.
“Busmillah.”
Khaleel ya fada. Ta leka tace
“Xamu gaida Yaa Muhammad nace bari na fada muku.”
Ya mike yana fadin
“Yanzu muke maganar.”
Ya fito. Sakina da Hafsa sukai gaba suka biyo bayan su. Sallama sukai a kofar dakin. Fauziyya dake jikin sa tagyara zaman ta sannan suka amsa.
Shiga sukai su Ahmad na binsu a baya. Zama Hafsat da sakina sukai a two sitter. Ahmad da Khaleel suka shiga Muhammad ya mike ya mika musu hannu. Suka gaisa sannan yace
“Bismillah!”
Zama sukai sannan suka gaisa da Fauziyya cikin girmamawa. Anan suka zauna suna hira gaba dayan su. Har akai magariba suka tafi masallaci su kuma sukai sallah a ciki.
Bayan sun dawo Yaa Muhammad ne kadai ya shiga ciki su kuma suka tsaya a waje anan suka karasa hirar kamar kar su tafi. Daga baya dai suka rabu duk ba dadi.
Suna komawa suka kwaso kwanukan anan falo suka ci abinci sannan suka shiga da suka wanke kwanukan.
*
Washe gari da safe tana kwance kiran wayar Kabir ya shigo mata mikewa tayi ta kai kunnen ta tayi sallama. Ya amsa yana fadin
“Yaya Hafsa barka da safiyya!”
“Yauwah Kabir ka tashi lafiya?”
“Alhamdulilah! Dama kira nayi mu gaisa.”
“Amman ka kyauta daman nima ina son na kira ka.”
“To ina fatan lafiya dai ko?”
“Lafiya Alhamdulillah! Akan zancen turowarka ne in ka shirya kaanar dani zuwan magabantan naka sai na fadawa Baba.”
“Alhamdulillah Baba kenan ya yadda?”
“Eh ya yadda dan haka daga ko yaushe zaka iya turowa.”
“Insha Allah Yaya Hafsa a cikin satin nan zan fada musu in sun saka ranar zan fada miki.”
“Insha Allahu!”
“To sai anjima.”
Yana kashe wayar yai sujudul sukhur yana fadin
“Allah nagode maka. Allah kasa haka shine mafi alheri.”
Ya mike ya shiga yai wanka ya fito ya shirya cikin kananun kaya yai kyau sosai. Bangaren Mamin sa ya shiga. A falo ya same ta a zaune ya durkusa ya gaishe ta cikin fara’a ta amsa taba fadin
“Me muka samu yau?”
Ya gyara zama yace
“Mami zancen aure nane!”
“To Alhamdulillah ya ake ciki?”
“Mami mata biyu nake son na aura a lokaci daya.”
“Kabir mata biyu zaka iya kuwa?”
STORY CONTINUES BELOW
“Mami zan iya!”
“To su ba matsala a tsakanin su.”
“Mami babu insha Allahu.”
“Yanzu Kabir har yaushe kayi yan mata biyu a lokaci daya?”
“Mami Daya mun jima dayar ce bamu jima ba.”
“Kaga kenan kaci amanar daya a ciki ko wacce wacce kuka jima wacce mukaje dubo ta?”
“Eh ita Mami.”
“Allah sarki yarinya mai hankali kenan ga nustuwa. Allah ya tabbatar da alheri ni naji dadi Autah zai aure kwanan nan insha Allahu zanga jika na daga kai.”
“Allah ya kawo masu albarka.”
“Amin Amin! Zan kira Kawun ka daKaninasai nai musu bayani sai suje ko?”
“Mami dan Allah suje cikin satin nan sannan su nema min alfarma kar ya wuce wata daya.”
“Kabir!”
Mami ta kira suna sa ya shafa kan sa yana murmushi tace
“Shikenan tashi kaje ka karya!”
Ya mike ya karasa dining ya ci abinci sosai sannan ya dawo wajen Mami ya zauna. Mami tace
“Ya’yan wane?”
“Ita Halima wacce kika je dubawa yar Alhaji Khamis ce dan kasuwa ne mahaifin ta. Ita kuma Sadiya mahaifin ta Alhaji Muhammad ne shi dan siyasa ne sosai.”
“Naji kace Halima da Sadiya?”
Kai ya gyada yace
“Eh Mami duk sunan su daya daya Halima daya Sadiya.”
“Ah masha Allah ka zama Kabir mijin Halima da Sadiya kenan. Allah ya tabbatar da alheri ya bada zaman lafiya ya hade maka kansu”
“Amin Mami.”
Ya mike yace
“Ni zan fita kila daga nan na biya ta wajen Kawu Sagir da Kawu Salisu.”
“Kabir kenan shikenan in kaje din ma ai ba matsala amman kan ka karasa zan kira nai musu bayani dan kar suce ba zaka aure su ba.”
“Nagod Mami Allah kara girma da nisan kwana Allah yasa ki gama da dhuniya lafiya.”
“Amin Kabir Allah maka.albarka.”
“Sai na dawo.”
“Allah kiyaye hanya Allah bada sa’a.”
“Amin!”
Wajen aiki ya fara zuwa sannan ya tagi wajen kawun nasa. Kamar yadda sukai da Mami kan yaje tai musu waya tai musu bayanin komai dan haka yana zuwa ya kara fada masa a take suka fada masa zasu je ranar laraba dukka gidanjen ina yake a fara zuwa nan ya fada musu ya basu address sannan ya taho da murna bakin sa yaki rufuwa.
*
**
***
****
*****
******
*******
********
Duk da haka ba a daina turawa Muhammad text ba wanda yaje ya kaiwa abokin sa dan sanda aka dauki number akai traicing. Jami’an tsoro ne suka gano wajen da mai number yake wato a nan bakin badala inda suka gane mutane biyu ke aikin da Hajiya wato Momyn su da kuma shi wanda ta bawa aiki dan shine ma ya samo.mata number Muhammad har ta fada masa yadda zai na yi.
Yau da magariba suka hada maji’an tsaron su suna zaune sunyi tatil da abubuwan maye suka rufar musu wanda ba wanda yai kokarin guduwa a cikin su. Haka aka debesu dukka aka wuce dasu cell. Tin daren ake basu kashi har washe gari da mayen ya sake su.
Wanda anan akai akai su fadi wanda yasa suke hakan amman sukaki. Ogan su wanda Momy ta bawa aikin aka dauke aka kai shi daki na daban ana baki kashi wanda jin da yai zai mutu a banza ya tona mata asiri ya fadi ko wacece.
*
Hajiya Momy ce kwance bata jin dadi duk abin duniya ya ishe ta domin duk kungiyar tata na neman tarwatsewa wanda take ji dadi nasu duk sun guje ta sun canja uwar daki wasu sun tuba ko Farisa yanzu ta daina ganin ta abun duniya duk ya ishe ta.
Waya ta dauka ta fara turowa duk member na association din nata sako kan cewa akwai meeting nan da karfe bakwan dare kowa ya daure ya hallata kan lokacin dan samuwa ce. Abinda yasa su kwadayin zuwa kenan. Banda Farisa da bata kasar gabaki daya.
Karfe shida na dare kofar gidan ya cuka da manya manyan motoci kowa yai parking ya shiga a ciki harda Anty matar Baban su Fauziyya wacce ta za cikakkiyar karuwa dan karuwancin ta take ci da auren ta. In ka ganta kace budurwa ce dan shigar da rayi tasha mai ta zama fara.
STORY CONTINUES BELOW
Karfe bakwai Hajiya Mony ta fito cikin shigar girma sai dai ta rame dan yadda take jin jiki. Zama tayi aka fara kawo gaisuwa. Ta kalli Antyn su Fauziyya tace
” Ya’yanki matsiya tane amman!”
“Me sukai?”
“Wallahi duk abinda ke faruwa sune sila.”
Nan ta fada musu komai da komai. Kowa shiru yayi yana jimami.
Antyn su tace
“Ni wallahi da yake bana zama a gidan ban san me yake faruwa ba. Amman tabbas naga canji a gidan mu.”
“Kinga ko? Duk auren Fauziyya ne ya janyo.”
“To yanzu menene abunyi?”
“Kamar yadda na fada muku malam yace ba zan taba samun abinda nake so ba in har yaran nan basu dawo ba. Bama wannan ba ya tabbatar mu da in suka dawo kungiyar mu zata shara tayi suna a fadin duniya gaba daya dan haka nake son dole mu hada karfi da karfe dan musan abunyi ko a kashe auren Fauziyya ko a kawon ita nayi abinda zanyi da ita.”
Wayar tace ta hau kara ta dauka tace
“Ga mugu nan na bashi aiki akan Fauziyyar bansani ba ko an dace.”
Ta dannan received takai kunne. Ya ce
“Hajiya ya kina ina ne?”
“Me ya faru mugu ko an dace ne?”
“Eh ga yarinyar nan na dauko.”
“Shikenan ina gida ka kawon ita.”
“An gama Hajiya.”
*
Ya kashe wayar ya kalli su Muhammad yace
“Tana gidan!”
Mota aka fitar guda buyu daya cike da yan sanda daya sune a ciki suka tafi gidan Hajiya.
*
Tana kashe wayar tace
“Alhamdulillah gata nan za a kawo ta.”
“Yauwah bari mugan ta yarinyar da ta daga miki hankali.”
Nan aka cigaba da hira ana yi ana dan taba shaye shaye.
*
Tin daga bayan layi suka ajiye mota sai driver aka bari kawai suka fita a hankali suka karasa suka zagaye gidan gaba daya sannan babbansu ya shiga ciki da wasu yan sandan.
Suna tsaka da harkokin su aka Mugu ya shigo. Hajiya ta kalle shi tace
“Tana ina?”
Kai ya hau girgiza mata sai ga sauran yan sandan sun shigo dagowa sukai suna ganin yan sanda suka saki dariya dan sun raina su. Abokin Muhammad da yake babban dan sanda ya tsuke fuska dan daman an basu damar yanzu su kama bata gari da yan iska dan haka yace
“Arrest them “
Ya kalli daya daga cikin yan sandan yace
“Kira motar su karaso”
Ba ai minti biyu ba sai ga motocin gava daya aka kwashe su aka tafi dasu. Har na dakuna wanda wasu daga su sai daurin kirji aka fice dasu a ciki har da Antyn su Fauziyya daga nan direct police station ka kai su.
Washe gari aka wuce dasu court ba a basu wata dama ba aka kulle su kawai. Sai da aka gama komai sannan Muhammad ya koma gida.
A falo ya samu Fauziyya tana zaune ya shiga ta mike da sauri ta fada jikin sa tana masa oyoyo. Akan kujera suka zauna tace
“Wai me yasa baka zama kwana biyu ne?”
“Munyi wani aiki ne?”
“Wane aiki fa?”
“Kinsan Babbar Hajiya Hajiya Momy!”
Ido ta zaro yace
“Ki kwantar da hankalin ki Baby.”
“A ina kasamo labarin ta?”
“Bana fada miki ana kira na ba da kawon zamcen ki na kai kara ne akai tracing aka gano waye ta nan aka je har gida aka kwashe su sunkai su hamsin yanzu duk an yanke musu hunci shekaru biyar biyar a gidan yari.”
“Har da Farisa ko?”
“Wacce Farisa?”
“Kanwata ce.”
“Toh ban dai sani ba tinda suna fa yawa.”
“Please ka tambayo.”
“Ki kwantar da hankalin ki”
Kai ta hau girgizawa. Ganin ta tada hankalin ta yasa ya kira abokinsa a handsfree ya saka wayar Abokin sa Auwal yace
“Ya akai Muhammad?”
“Eh dan Allah a cikin list din wadan nan da aka kamo nake so a duba min Farisa Khamis!”
“Ok bari aduba.”
Ya kashe waya bayan minti talatin ya kira yace
“Ranka ya dade ba sunan.”
Amman duk da haka Fauzuyya hankalin ta bai kwanta har sai da aka turo list din da kanta ta duba taga ba suna ta nan ta sauke ajiyar zuciya.
Tace
“Nagode My love!”
“Kada ki damu komai zan iya miki.”
Tai murmushi yace
“Me kika girka mun?”
“My love kasan me wallahi na shiga zan maka girki daga jin kamshi kayab miya na fara amai na kasayi.”
“Subnahllah na fada miki baki da lafiya kinki yadda kinga yadda kika koma so weak kuwa!”
Tai murmushi tace
“Kayi hakuri Hafsa tazo ta dafa maka.”
“Kai dan me kika kura ta ai da kin bari in na dawo sai muje mu siyo ko?”
“A’ah muje kai wanka sai muzo kaci ko?”
“Allah miki albarka.”
Nan suka shiga ta tayashi yai wanka ya fito ya shirya cikin kananun kaya dining suka wuce ta zuba masa yafara ci yace
“Ke kin ci?”
Kai ta girgiza tace
“Banason naci”
“Ah haba dai taho kici kinji Babyna”
Ya debo ya kai bakin ta tana jin kamshin tayi bandaki a guje taba zuwa ta fara kwara amai bayan ta yabi ya dafe ta ta gama ya taimaka mata ta wanke baki ta dawo falo tana mai da numfashi. Key ya dauka ya dauko mata hijab ya dauke ta sai mota.
Ahmad yana komawa ya samu Dady a falo. Shiga yayi ya zauna yace
“Dady daga gidan su Hafsa nake”+
“Yarinyar da kake neman aure ko?”
“Eh ita!”
“To me ya faru?”
“Dady iyayen ta ne suka nemi da in aiko.”
“To ba damuwa zuwa jibi sai aje sai ka sanar.”
“Insha Allah nagode Dady.”
“Ba komai Allah bada zaman lafiya amman ina son ka bani address nay bincike kan naje ko?”
“Eh Dady hakan ma yana da kyau.”
Nan ya bashi address da sunan yarinyar yai masa sallama. Cikn gida ya shiga sauri sauri ya wa Momy sallama ya tafi dan dare yayi.
*
A falo ya same ta tana aikin nata. Ya shiga da sallama ya zauna akan kujera ta juyo tace
“Shine ka tafi ka barni ko?”
“To kina bacci tashin ki zanyi?”
“Eh mana.”
“Gobe kya je.”
Ya mike yayi ciki. Tabishi da kallo tana son mijin ta. Zaman ta dashi ta gane yana da saukin kai da kyautatawa iyali. Amman dan me ita ta kasa bashi dama su zauna lafiya. Saboda zugar kawaye sunce in tana masa biyayya sosai sai na wulakanta bama da baya son ta. Kuma ta yadda dan wanda sukai auren soyayya suma ya zaman ke kayawa bare ita da auren hadi ne ita ke son sa.
Zata bashi lokaci taga gani in yaso sai ta sakar masa. Amman itama tana son mijin ta tana son tana kyautata masa.
Tashi tayi ta kashe kayan kallon tai daki ta kwanta kawai. Waya ta dauko ta shiga whatsapp kawar ta Kausar ta sama a online tai mata sallama ta amsa yana fadin
“Ai ma zata kina wajen mijin naki.”
“Ina fa yanzu ya dawo wallahi Kausar Yaa Ahmad tausayi yake bani.”
“Tausayi akan me?”
“Abinda nake masa.”
“Zauna tausayin ki ya samu dama ya gasa ki. Malama ki cire wani tausayin sa ki gama kame shi sannan.”
“Har yaushe kenan watan mu nawa da aure mun fi wata shida fa haka rayuwar aure na zata kasance.”
“Ki bari sai kinyi shekara lokacin nima haka nayi yanzu baki ga zaman mu muke lafiya.”
“Shikenan yaushe zaki zo?
“Eh to zan duba yaushe zaku tafi?”
“Kinsan kwana biyu zamuyi dai mu juya.”
“Zan kokari na samu na shigo.”
“Shikenan”
Haka suka cigaba da hirar su har goma sha daya sannan sukai sallama.
Ahmad na shiga yai wanka ya fito ya shirya cikin kayan bacci sannan ya hau gado. Waya ya dauka ya fara neman layin Hafsa.
“Ya kaje gida?”
“Alhamdulillah nayi kewar ki.”
“Kai Deedat!”
“Da gaske nake. Ina fatan kasancewa dake har abada. Mutuwa kadai nake son taraba mu soyayya ni dake zan kasance.”
“Fatana da kai kenan! Na baka riko kai ka ajiyen zuciya ta dake gun ka dan har abada kana raina. Kada ka guje min.”
“Hmmm Mai niyyar alheri kada ka canja Allah baya son mai nuna izza zan tarairaya baza na gaza zan kula dake zan tarairaye ki tamkar kaza kece ni, nine ke soyayya da taraiyya.”
STORY CONTINUES BELOW
“Ka ciren damuwa da lallurar dake kunshe a cikin zuciya ta. Ka kawo gyara a cikin rayuwa ta. Da kai nake bacci in tashi kana raina kalbi na kai na ajiye.”
“Aljanna ta kece silar haka ne na nace bani da wata sai ke zanyi fada da duk wanda yace zai kwace min ke. Kece tawa yar budurwa soyayya ce ta sani nake yabon ki.”
“Ina kaunar ka Deedat kada ka juyan baya!”
“Akan me zan juya miki baya. Bayan ina son ki soyayyar ki ta kamani ni nasan me nake ji akan ki. Bana taba fushi dake ko ina fushi na ji muryar ki zuciya ta na sanyi tayaya zan barki a shirye nake dana dauke ki. Kar ki manta dani da alkawari na ba zan taba juya miki baya ba.”
“Soyayyar ka ni sai na fada banga irin ta ba. Ina fatan ta daure a haka. A sirince zuciya ta ka kwace nai sa’a da me so na mai hali mai kyau. Alhamdulillah!”
“Son ki ba da karamin zafi ya shige ni ba. Zan iya komai dan ke, kece a zuciya ta. Madarar da kika ban ta soyayya taki daban ce.”
“Naji dadi ina fatan kada ka manta da wadan nan kalaman naka.”
“Insha Allahu ba zan manta ba insha Allahu ba zamu taba samun sabani ba.”
“Allah yasa.”
“Tushen alkwari amana ce.”
“Wannan haka ne!”
“To zan rike amanarki na rike ki da amana.
” Nagode my Deedat! Kaje ka kwanta kar mu shiga hakkin matar ka.”
“Ba wani hakkin ta da zamu shiga sai dai in korata kike.”
Hamma tayi tace
“Ni na isa na kore ka in ta nine mu kwana tare.”
“Uhmm ko?”
“Eh mana. To yanzu kije ki kwanta sai da safe kinji.”
“Allah bamu alheri.”
“Amin ki kular min da kanki.”
“Insha Allah!”
Sukai sallama ya kashe wayar yana juyi akan gadon sa. Shin yaushe zau mallaki Hafsa ne ya zaiyi ranar da ya mallaki Hafsa wanda zata kasance kwane a jikin sa.
Ya salam shin wane dadi zai ji
“Allah ka mallaka min Hafsa in ita alheri ce ka sanya alheri a tsakanin mu ka kade fitina da duk wani sharri ka sadamu da alheri.”
Ya lumshe ido.
Hafsa ma suna gama waya kuka ta saka dan zuciyar ta ta karye ba kadan ba. Shin ya zata kasance a gidan Ahmad ji yadda yake daukin ta kada taje yaki amsar ta fa. Kuka ta fashe dashi. Sakina dake bacci ta farka ta. Ta mike da sauri yana fadin
“Lafiya Hafsa me ya faru?”
“Yaya Sakina ya zanyi da rayuwa ta yaya zanyi?”
“Kinga ki nutsu ki fada min.”
“Yaya Sakina tsoro nake ji!”
“Tsoron me?”
“Ta yadda Deedat zai same ni.”
“Bangane ba baki fada masa komai bane!”
Shiru tayi tana na zari in tace bata fada ba tasan zasu fada masa ne kada kuma su fada ya fasa auren ta bayan ta gama kamuwa da soyayyar sa. Dan haka tai sauri ta girgiza kai tace
“A’ah ya sani kawai dai ina tsoro ne. Ko wacce mace na fatan mijin ta ya amshi budurcin ta amman…..”
Sai ta fashe da kuka. Yaya Sakina tace
“Ki daina kuka ba abinda zai faru kinji?”
Kai ta gyada tace
“Allah yasa kada ya tsane ni daga ranar.”
“Haka ba zata faru ba insha Allahu.”
“Allah ya yadda.”
“Amin. Ki kwanta.”
“A’ah sallah zanyi.”
Ta mike ta dauro alwala sannan ta wuce ta tada sallah. Kwana tayi akan sallaya tana kai kukan ta ga Allah sai da tayi sallah asuba sannan ga koma bacci.
*
**
***
****
*****
******
*******
********
*********
**********
Washe gari Khaleel kasa zama yayi ya juya dan ya sanar da Dadyn sa. Ai kuwa yana komawa yai masa waya yace
“Dady yaushe zaka dawo?”
“Son menene?”
“Dady gidan su Sakina ne suka ce na tura fa.”
“Masha Allah ka kwantar da hankalin ka ina hanya zuwa gobe zan sauka sai muyi maganar.”
“Thank you Dady!”
Sukai sallama. Yai wanka ya fito cikin kananun kaya fuskar sa dauke da annushuwa da farin ciki. Hajiyar dake zaune a falo ta kalle shi tace
“Wai Son me ka samo mana kake ta fara’a haka?”
Zama yayi yace
“Suruka na samo muku.”
“Wacece”
“Wacece in banda Sakina.”
Ido ta zaro tace
“Wai Son baka rabu da yarinyar nan ba.”
“Momy munyi dake zan rabu da ita ne. Ina son ta dan me zan rabu da ita. Yarinyar nan jarabta ce Allah ya daura mata amman ba a son ranta ba kuma yarinyar da zata taren ta fadan ko ita wacece dan me ba zan rufa mata asiri ba so kike na guje ta in na guje ta wani yaje ta kara fada masa kila ya tona muku asiri ko kuma ta kara komawa gidan jiya. Momy Jihadi fa zanyi.”
“Hmmm Khaleel bana son auren ka da Sakina sam dole kai ne zakai jihadi akan ta.”
“Akwai laifi dan nayi Momy bayan kina daya daga cikin wanda ya lalata mata rayuwar ta”
Mikewa tayi ta kwada masa mari. Hannu ya dafe kuncin sa. Tace
“Ka shiga hankalin ka. Ni ba sa’ar ka bace ka sani ni mahaifiyar ka ce.”
Tayi sama. Zama yayi yana binta da kallo. Lallai Momy yau shi ta mara akan Sakina. Shi kuwa yana son sakina kuma sai ya aure ta wannan ma ai cin zali ne su lalata yarinya sannan tace ba zai aure ta ba. Wannan kadai jarabawa ce gasu masu hali irin nata zai zama iznah sai ma ya aure tan ta haifa masa ya’ya.
Mikewa yayi ya bar gidan gaba daya sam bai dawo ba sai washe gari da rana yana shigowa ya gane Dadyn sa ya dawo da kwarin gwiwa ya shiga dakin ai kuwa ya same shi afalo.
Karasawa yayi ya zauna yace
“Dady ina kwana”
“Lafiya lou ina ka shiga Mu’azam?”
“Dady naje gidan su Salim ne.”
“Ban hana kwanan waje ba.”
“Dady kayi ba zan sake ba kuma wallahi gidan su Salim na kwana ka tambayi Abban sa.”
“Shikenan ana kiyayewa dai da jin tsoron Allah.”
“Insha Allahu! Dady zancen gidan su Sakinan ko?”
“Mu’azam ai ka bari na huta ko?”
“Dady gobe nake so naje.”
“Uhmm saime?”
“Dady a saka sati biyu dan Allah.”
“In basu shirya bafa?”
“Dady sai ka tambayi dalili in na taimako ne sai a taimaka musu.”
“Mu’azam kenan!”
“Please Dady!”
“An gama”
“Yauwah Dady sai a fara hada lefe ko?”
Momy ce ta sauko cikin shiga ta alfarma tana ganin Khaleel taji hankalin ta ya kwanta karasowa tayi.
Dady ya kalle ta ya kalli Khaleel yace
“Wannan kuma ai Momyn ka zakaiwa magana.”
“Menene?”
“Wai lefe!”
Fuska ta bata tace
“Wai ba zaku janye zancen yarinyar nan ba ko?”
“Akan me za a janye!”
“Saboda ba na so!”
“Ke zaki zauna masa da ita.”
“Ni dai nace bana so.”
“Hajiya ina kara fada miki kibi komai a hankali kina addu’a in alheri ne Allah tabbatar in ba alheri bane Allah ya bashi wata.”
Mikewa tayi tai sama suka bita da kallo.
Khaleel ya kalli Dady yace
“Please Dady kada ka biyewa Momy.”
“Ba zan biyemata ba sai da kwakwaran dalili dan haka ka kwantar da hankalin ka. Allah ya sa alheri ce yarinyar.”
“Amin Dady nagode.”
“Ba komai Mu’azam.”
“Gobe da yaushe zamu?”
“Da yamma ko?”
“Dady da safe kuma ni a kanon za a barni.”
“Khaleel rawar kan yai yawa fa.”
Kai ya sosa yace
“Ince kyakyawa ce.”
“Hmm eh mana Dady Amman ba wannan ya gama dauken hankali ga ita ba.”
“Tana da hankali kuma ina tausayin ta ina son na taimaka mata.”
“Allah baka ikon yi to”
“Amin!”
Ranar yini sukai hirar Sakina shi da Dady har Allah Allah yake gobe tayi.