BABBAN GORO BOOK 1 CHAPTER 6 by sumayyah Abdulkadir

 BABBAN GORO BOOK 1 CHAPTER 6  

by sumayyah Abdulkadir


Ko fada su kai a junansu baya wuce kwana daya sun shirya sun manta komai. Don haka ta ga gara ta tunkari Safan kai tsaye ta yi mata bayanin abinda take zargi. 


Karfe tara na daren ranar ta yiwa Zahraddeen rakiya ya tafi. Tana dawowa ta cimma Mami a gefen gadonta ta yi tagumi. 


Ta zauna a gefenta ta sauke mata tagumin ta ce, “Maminmu, lafiya kika zuba wannan uban tagumi? Har na shigo baki san na shigo ba’. 


Ta dube ta sosai da idanunta da ba sauki a cikinsu, ta ce, 


‘“Safah”’. 


Ba ta amsa ba illa ta dube ta, sabida yadda ta kirayi sunan nata_ cikin kakkausan harshe. 


Ta ce, “Me _ ke tsakaninki da Zahraddeen?” 


Ta sunkuyar da kanta kasa. Ba ta yi magana ba, sai da Mami ta yi mata tsawa ta ce, “Ba magana nake yi dake ba?” 

Cikin sarkewar murya ta ce, “Ki yi hakuri Mami….dama…..dama gobe ne Deen yake son ya sanar da Daddy, ni kuma dama yau zan sanar dake muna son junanmu……..mun yanke shawarar yin au….” 

Ji kake kauu! Mami ta dauke ta da mari har sai da ta ga wuta, ta nemi ji da ganinta na wucin gadi ta rasa. Mami ta ce, “Abinda za ki yi mana kenan? Tozarcin da zaki yi min kenan? Sabida kin je jami’a idon ki ya bude da maza. Kina nufin ba za ki auri dan’uwanki mai kaunar ki ba? Me Zahraddeen din yake da shi wanda Almustapha ba shi da shi? 

Ke ko kunya ba ki ji a ce za ki auri yaron Baban ki? Boyi-boyin Babanki? Dube ki don Allah, kina kallon kanki a madubi kuwa? Amma ki rasa a inda za ki kare da zaman aure sai a cikin garin Zaria? 

Me yake da shi? Me zai baki? Duk abin da zai baki daga aljihun ubanki zai fito. Wannan shine abin da kike 

ganin kin yiwa rayuwarki daidai?” Tana share hawaye ga mamakin Hajiya Zainab sai ta bude baki muryarta na rawa ta ce, “Mami ni ba ruwana da kudi, matsayi ko mukami, face abin da zuciyata ta aminta da shi. Ni ba kin Ya Imam nake yi ba, kawai dai ba zan iya auren shi ba, don ganin shi nake tamkar dan’uwana da muka fito ciki daya. 

Ki yi hakuri Mami ki sanya min albarka, domin Deen nake so, shine zabina…..”. 

Mami sai ta saka salati, kafin ta fashe da kuka. Yau tana fada Safah na mayar mata a kan da namiji da baya da tabbas. 

Ta ce, “Da gaske Safah ba za ki auri Imam ba?” 

Ta ce, “Ku yi hakuri Mami, wallahi bana son sa da aure!”’. 

Ta ce, “Ashe kuwa za ki sake wasu iyayen ba mu ba, muddin kika kafe a kan bakan ki. Yaron na dawainiya da son ki tun ranar da aka haife ki, amma 

da abin da za ki saka masa kenan? 

To wallahi ba da ni ba, wannan cin fuska da cin amanar…..”. 

Safah ta ja shessheka ta ce, 

‘““Wallahi Mami ban taba yaudarar Ya Imam ba, balle in ci amanar shi. Ko mail da yake mini Marwa ce take amsa mishi bani ba, duk wani hannunka mai sanda da zai nuna bana ra’ayin auren shi na yi mishi tun ma kafin in hadu da Zahraddeen. 

Me zai hana ya auri ‘yar’uwata tunda na lura ita tana son shi?” 

Haushi ya kashe Mami. Ta ce, “Kin fi shi ido ne, ko kin fi shi sanin da wanzuwar Marwan ya ce ke yake so? Tashi ki bani wuri tun ban yi mugun kalami a kanki ba’’. 

Ta mike sum-sum-sum ta fice, a ranta tana cewa, “Ko duniya za ta taru a kanta ba za ta auri wanda zuciyarta ba 

ta so ba’. aK ok 2K of 

Karfe goma na dare Mami ta cimma 

Daddy a dakin barcinsa yana sauraron rediyon BBC. Mami ta samu waje ta zauna ta yi jigum, ranta a jagule, zuciyarta a hargitse. 

Kallo daya Daddy ya yi mata ya san yau wani abu ya sukurkuta mishi Zainabu-Abu. Ya rage rediyon ya taso daga mazauninsa ya zauna a gabanta. Ya mika hannunshi ya kama nata ya ce, 

“Wa ya tabo min Zaynabu-Abu, uwarbiyu, mai tagwayen suna, mai tagwayen ‘ya’ya?” 

Duk da bacin ran data ke ciki, saida ya sata dariya. Ta yi murmushi, wanda iyakacinsa fatar bakinta, ta ce, 

‘Daddy kenan, kada ka ce min baka san abin da ke faruwa cikin gidannan ba? Ka taba zama ka yi tunanin dalilin sintirin Zahraddeen a gidannan a ‘yan kwanakin nan?” 

Cikin faduwar gaba Ya ce, “Me ya faru? Na ganshi dai yana zuwa, amma ba zan ce ga dalili ba”. 

Ta yi kwafa ta yi huci mai zafi ta ce, 

“Wai Zahraddeen da Safah son juna suke!”’ 

Ya ce, “Gyara min kalaman ki Zainabu, ko dai Zahraddeen da Marwah?” 

Ta girgiza kai ta ce, “Oh-oh! Yadda na fadi haka al’amarin yake. Baki da baki Safah ta gaya min nan duniya Zahraddeen take so”. 

Daddy ya yi shiru, can kuma ya ce, “Wannan ai shirme ne, ki kwantar da hankalinki, zan gansu dukkansu”’. 

Ran Mami ya baci ganin bai dauki abin da muhimmanci ba. Ta ce, “Ni dai ka ja mishi kunne, kada in kara ganin kafar shi cikin gidan nan da sunan wai ya zo wurin Safah yana hure mata kunne da_ wannan munafukar muryar tasa kamar ta basarake, Safah da miuinta, kuma ko babu ban ga me za ta ci da Zahraddeen ba. 

Bakin rijiya….ba wajen wasan yara bane. Ban da rashin hankali ya dubi Uwargijiyarshi ya ce yana so da aure? 

Saboda kankanba da neman wuce gona da iri ko saboda mene? Ai BABBAN GORO SAI MAGOGIN KARFE,…… kuma Tuwon Girma…. Miyarsa nama” 

Daddy ya yi murmushi yana kada kai ya ce, 

‘“‘Wannan ba hujja ba ce, ku mata ban san irin ku ba wallahi. Ni a wajena Zahraddeen mutum ne har mutum, mai nagarta, daraja da sana’ar da za a bawa aure. 

Ba don maganar Imam ba, babu abin da zai hanani wanke Safah in ba shi ba tare da na yi la’akari da hujjojinki ba. Mutum da karatunshi da usuli da lafiya da addini da aikin yinsa, me ake nema a nagartaccen miji da ya wuce wannan? 

Jarumi haziki irin Zahraddeen, mai zuciyar neman na_ kansa, mai kwakwalwa, kyakkyawar zuciya da halaye na kwarai, gaskia da amana, wadanda suka yi karanci ga matasan zamanin nan, wallahi ba don Imam ba, 

zan baiwa Zahraddeen Safah ba tare da na ji ko da dar ba”. 

Mami ta kama baki cikin mamaki. Cikin takaici ta ce, 

‘Kenan kana nufin babu matakin da za ka dauka? Idan aka yiwa Imam haka anyi adalci kenan?” 

Ya ce, “Ni ban ce miki na amince ba, hujjarki kawai na soka (criticizing). Na ce dake zan gansu, ki bi komai a hankali, ki cire bacin rai, fushin fari ba naki bane, tunda ba ke za ki yi mata zaman auren ba”’. 

A wannan daren Mami ba ta yi barci ba, yadda ta ga rana haka ta ga dare. Ita kam duk haushin Daddy ya rufe ta, me Safah take nufi? Da wacce fuska za ta dubi danta Almustapha idan Safah ta watsa musu kasa a ido? A washegari Safah ba ta ga walwalar Mami ba, ta daure mata sosai. Da Marwa take sabgoginta, itama sai ta kama kanta, ta killace kanta a daki tana rubuce-rubucen ta. 

Sai dai zuciyarta cike take da tsoron Mamin, idan ta tuna marin da ta sha jiya. Ba ta taba ganin bacin ran Mamin irin jiya ba. 

Har kullum ita cikin kauna take nuna musu komai, ba ta taba _ tunanin Mamin na da zafi har haka ba. Ta yarda ta amince akan Imam, Mami zata iya batawa da kowa hada dasu ‘ya’yan cikinta kuwa. Don har fadi musu take 

“kafin in sameku shi na samu, a lokacinma dana riga na fidda rai da samun ‘ya’ya. Sai ya zamo wani irin nagartaccen Da, mai debe min kewar ‘ya’yan da bani da su. Don haka zuwanku bai rage komi daga kaunar dana ke yi masa ba. Sabida ya maye min gurbin ‘ya’ya goma, a lokacinda banida ko daya!!! 

Balle ke kuma na haife ki ne kawai, amma bansan kashinki ba _ bansan fitsarinki ba, sai shayarwa ta dan lokaci, wadda ciyarwar dashi yayi miki da madara ta fita tsaho”’. 

Karfe takwas na dare Zahraddeen ya zo, Mami na falo cikin seater tana sauya tashar MBC zuwa Aljazeera. Tun daga jin sallamar shi ta bi ta daure fuska irin yadda ba ta taba yi masa ba. Ya zube gwiwoyinsa a kasa yana gaishe ta, ta kafa mishi ido ba ta amsa ba. Karshe sai ta mike ta shige kafar benen da za ta sada ta da dakin barcinta, ba tare da ta ce da shi komai ba. 

Daga shi har Safah gwiwoyinsu suka yi sanyi, ita Safah ma kunya ce ta kama ta. Aka rasa mai fara yin magana a cikinsu. 

Daga baya Zahraddeen yai ta maza, ya yi murmushi cikin basarwa ya ce, “Mun yiwa Mami laifi halan?” 

Ta yarfar da hannu, ta lumshe ido “Tun jiya haka take, na kasa gane mata’. 

Ya yi shiru cikin tunani, can kuma ya ce, “Mai yiwuwa ne ba ta yi na’am da al’amarin mu ba”. 

Ta ce, “Babu komi, za ta huce a 

hankalv’. 

Daddy na saukowa daga matattakalar bene Mamin biye da shi rike da brief case dinsa ya yi tozali dasu a falon. 

Ya yi murmushi yayin da Mami ta kara hade rai. Ya ce, “Dama ina son ganin ka”. 

Ya mike cikin girmamawa ya bi bayansa suka nufi falon ganawa da bakinsa dake daga harabar gidan. 

Daddy na bisa kujera, Zahraddeen na gefensa bisa kilishi. Daddy ya ce, “Ya sakon da na baka na 

Wilcod din Abidjan?” Ya ce, “Ya zo ya amsa tun shekaran jiya”’. 

Ya ce, “To madallah’’. 

Sai kuma ya yi shiru, shi ma Zahraddeen kanshi na kasa. Ko motsin kirki ya kasa. 

Can Daddy ya ce, 

*““Zahraddeen”’. 

Ya dago da fararen idanunshi ya dube shi amma bai amsa ba. 

Ya ce, “Meke tsakaninka da Safah ne?” 

Zahraddeen ya rude, ya soma indainda, saboda kwarjinin da Daddy ya kara yi masa, har ya soma ganin wautar kansa, da wuce gona da irin sa. Daddy ya yi murmushi ya ce, 

“ Zahradden feel free with me. Ka amsa min mana, ni Babanka ne ba bakon ka bane’’. 

Ya yi ta maza ya ce, “Am Daddy, dama…..dama ina son mu samu lokaci ne, sannan in gabatar maka da kaina a matsayin mai neman auren Safah, mun daidaita kanmu”’. 

Daddy ya yi murmushi ya lumshe ido na “yan mintunsa sannan ya budesu a hankali akan Zahraddeen din ya ce, “Zahraddeen zaka iya hakura da son da kake wa Safah, ka juyar dashi ga ‘yar uwar ta? Ina nufin, ka _ auri abokiyar tagwaitakarta MARWAH?” A firgice ya dago ya dubi Daddy, 

kamin ya yi magana Daddy ya ce, “Safah da mijinta, tun ranar da aka haife ta, amma idan kana ganin za ka lya auren ‘yar’uwarta sati mai zuwa ka kawo min sadakin naira dubu goma in daura muku aure rana ita yau. Lahadi kenan, zan daura auren Safah da Almustapha tare da naku. Tashi je ka ka yi shawara, ina sauraron ka”. 

Ya bude baki zai yi magana Daddy ya ce, “Ka je ka yi shawara tukunna, ba zan yi hakan ba sai da amincewar ka. Ina sonka ne Zahraddeen, ina son hada jini da kai, saboda kai mutum ne na gar. 

Banda shi wancan alkawari, ba abin da zai hanani baka wacce kake so cikin ‘ya’yana. Amma Safah da Marwah duk daya ne, abin da ya yi Safah shi ya yi Marwah, sai dai bambanci na akida da halayya wanda za ka iya lankwasawa cikin dan lokaci kalilan. Tunda har yanzu yara ne. Tashi jeka ka yi tunani sosai, ka kuma shawarci Innar ka, na baka kwanaki 

uku ka zo min da abin da ka yanke”. 

Zahraddeen ya mike ya fita, kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, ya nufi motarsa ya bude ya shiga ya zauna ya kwantar da kai a jikin sitiyari. Bai yi aune ba sai jin danshi ya yi a kan fuskarsa, ya mika hannu ya shafo su, hawaye ne, shi kansa bai san dalilin zubarsu ba. 

Ya fi minti talatin a hakan, kamin ya ja motar masu gadi suka bude mishi get ya fita. Ya yarda ba zai samu Safah ba, amma ba ya jin da ranta zai iya auren ‘yar’ uwarta-shakikiyarta. Karewama wadda suka fito duniya tare a lokaci daya. 

Ba aure ya damu ya yi da wuri ba. Kasancewarsa saurayi da bai taba aure ba, ba kuma shashanci yake yi ba, balle ya tantance yanada bukatar mace soon ko a’ah. Safahn kawai yake so, soyayyarta ce ta sanya mishi son yin auren. To amma ya zai yi ya budi baki ya ce da Daddy baya son ‘yar cikinshi, 

wanda shi a ganinsa karamci ne ya yi mishi? 

Me yasa Safah ta boye mishi cewa akwai alkawarin dan’uwanta a kanta? Tayi masa wasa da hankali da zuciya…..Har ya iso gida bai san inda hankalinsa yake ba. Kuma tambayar da yake so yayi mata kenan, hakika tayi mai wasa da zuciya, don bazai iya cewa ta yaudare shi ba, don ya yarda son da take masa na gaske ne, na tsakani da Allah ne. 

Alh. Aliko na zaune a falon shi, ya kira Mami ya ce ta turo mishi Safah. Tana zaune a bakin gadonta ta yl tagumi, Marwah na jera kayansu da aka kawo daga wanki cikin wardrobe. Mami ta yi sallama ta shigo dakin. A hanzarce Safah ta dago kyawawan idanunta ta dube ta. Kallo daya za ka yl mata ka san cewa cikin damuwa take, damuwa mai tsanani. 

Mami ta balla mata harara ta ce, ““Taso muje”’. 

Ta mike babu kuzari ta bi bayan Mamin har falon Daddy. Jikinta a matukar sanyaye, don ta tabbata Mami ta fasa kwan. 

Daddy yana ta aiki cikin takardu da farin gilashi a idanun shi lokacin da suka shigo. 

Ya janye takardun gefe ya kuma cire gilashin ya bi Safah da kallo a lokacin da take zama a carpet. Kallo daya ya yi mata ya karanto matsananciyar damuwar da take ciki. Don duk ta zabge cikin kwana daya kacal. 

In banda alkawarin da ya yi, da matsayin Imam a wurinsa, da ba abinda zai hana shi baiwa wannan soyayyar goyon baya, ba ya son Zahraddeen ya kubucewa gidansa, don haka ne ya yanke shawarar wanke Marwah ya ba shi in har ya amince. Ya tabbata ahankali zai sota, sabida tanada nata kualities din itama. Duk da ya san ita din mai dagawa ce (ba kamar Safah ba), amma abu kKadan yana tankwara ta. 

Sannan ba zai taba dauke alkawarin Imam ba, sai in har shi da kansa ne ya ce baya yi, wanda ya san har abada hakan ba za ta faru ba. 

Ya kai duban shi ga Hajiya Zainab ya ga yadda ta hade fuska ta yi murtuk, Sai ya yi murmushi ya ce. 

‘A lokuta da dama ku mata kuna bani mamaki, kina kin Zahraddeen ne saboda kawai yana karkashi na. Ba kya duba asali, halayya, addini da dabi’a. 

Manzo (S.A.W) yaron Nana Khadija ne, kuma ya aure ta, ta kuma so shi saboda nagartattun halayensa da amanarsa. 

Ba za ki yi la’akari da wannan ba ki kuma duba cewa soyayya hadin Allah ce, ba yin mutum ba?” 

Ya maida duban shi ga Safah, wadda kalaman mahaifinta ke sanyaya mata zuciya, har ta soma hango alamun nasara cikin al’amarin ta. 

Idanunta suka cicciko ta ce, 

“Don Allah Daddy ka bawa Mami 

hakuri, ina son Zahraddeen shima yana so na. Mami Zahraddeen ma mutumin kirki ne wallahi. 

Ni ban ce bana son Ya Imam ba, amma bana yi mishi soyayya ta aure, Zahraddeen nake so Mami ba zan iya auren Ya Imam ba…..” 

Ai kuwa ta kara harzika Mamin, daga dan sanyin data yi da nasihar Daddy, ta buge bakinta ta ce, 

“Ashe baki da kunya Safah? Ni kike gayawa kina son wani bayan Da na da na raina na yi mishi tarbiyyar da nake so? A gabana kike cewa ba za ki iya auren Almustapha…….. ” 

Sai ta soma kuka, 

“….Tunda ka daure mata gindi ku tozarta alkawari, shi kenan zan bar muku gidanku, don bani da idanun da zan dubi Imam, alhalin tana auren wani can. Ka aura mata duk wanda kuke so…” 

Daddy shiru ya yi yana kallon su, ya dubi Mami da har ta kai bakin kofa ya ce, “Zainabu”’. 

Sai ta dakata, amma ba ta juyo ba. 

Ya ce, “Kin ji hukuncina ne kamin ki yanke naki hukuncin? Dawo_ ki zauna’’. 

Ta koma ta zauna. 

Ya ce, “Ba tsoron ki nake ji ba, ba kuma so nake in yi miki abin da kike so ba, illa nima na san muhimmancin alkawari, kuma ni da bakina na yi wannan alkawarin ba ke ba. 

Don haka na yanke cewa zan baiwa 

Zahraddeen Marwah….” 

A razane Safah ta dago ta dubi Daddy. Ya girgiza mata kai ya ce, “Ki yi hakuri Safah, gara ka auri wanda ke sonka, a kan ka auri wanda kake so!. Bana kin al’amarin ki da Zahraddeen, ko kadan bana ki, sai dai ba zan iya daga alkawarin Imam a kanki ba. Na yi kokarin neman mafita mafi maslaha na kasa sai wannan din. Wato bana so Zahraddeen ya kubuce mana. 

Ki sowa ‘yar’uwarki abin da kike sowa kanki. Ki yi min alfarma Safah 

in cika wannan alkawarin nawa, ni kuma in yi miki duk abinda kike so a duniya. Alfarmarki nake nema, Safah, zan samu?” 

Kuka ya _ci_ karfinta, tausayin mahaifinta ya lullubeta, ganin yadda ya karyar da murya ya kwantar da kai yana rokonta kamar ba shi ya haifeta yayi ta wahala da ita har ta girma, ya kawo Zahraddeen din cikin rayuwarsu har ta ganshi ta ji tana so. Ta ce cikin rishin kuka, 

“Ka yi duk yadda kake so da mu Daddy….har abada mu masu biyayya a gareka ne. Na yarda da hujjar ka. Na yi maka wannan alfarmar Daddy….” Ta ci gaba da kuka a hankali. 

Zuciyar Daddy ta karye, ya ce, 

“To amma Safah, kukan na mene ne haka? Kukan ki, na nuna min cewa….. na zalunce ky’. 

Ta yi saurin toshe bakinta da mayafinta, ta hadiye kukan da karfi ta ce, 

“Babu zalunci tsakaninmu daku 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *