KO WANNE BAKIN WUTA COMPLETE

KO WANNE BAKIN WUTA COMPLETE

🔥 🔥🔥🔥🔥🔥

*KOWANNE BAKIN WUTA*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥

    ( da nashi hayakin)

💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by

    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*

    Wattpad @fadeelalamido

*Bismillahi Rahamanir Rahim*

      

                1-2

🔥”Wata kyakyawan mota ce ta faka Awani dankareren gida, medan  karan kyau”

     “Motar ce tafi daukan hankalina dan haka ita na zubawa ido”

     “Zuwa can wani Zafgegen saurayi ya sakko daga ciki, Mai da hankalina nayi gurin kallon shi”

   ” Dogone fari tas, shekarun shi zasu kai irin talatin da wani abu din nan, ga wani irin kyau da Allah ya zuba mai, kai kace balarabe ne”

      “Abu daya ya bani mamaki, fuskanshi babu fara’a ko kadan”

    “Zuwa can ya nufa cikin gidan, cikin zafin nama, tafiyan shima abin kallo ne, domin kuwa daka ganshi dole ka kauce ka bashi hanya”

    

       ” Yana isa kofar da zata sadashi da falon ya ya tura kofar tare da sallama cikin wata siririyar murya”

     “Wata hamshikiyar mata nagani, cikin fara’a take amsawa tare da zuba mishi ido”+

        ” Kujeran dake kallon tata ya zuna, sannan ya bude baki daker yace”

    “Sannu da gida Umma”

   

    “Cikin fara’a matar tace”

     “Yauwa sannu *Majeed*, ya wajen aikin naka?1

    “Murya ciki ciki, yace”

    ” Lafiya Alhamdulillahi”

     “Yayi kyau, matar ta fada sannan ta dauki wayarta dake gefe ta fara dannawa”

    “Shima wadda aka kira da suna *Majeed* komawa yayi ya kwanta ajikin kujeran  tare da rufe idon shi”

     “Suna cikin haka wasu ‘yan mata su biyu suka shigo, tare da cakakin surutun su, tare da shewa”

      “Wannan shewa tasu ita tayi sanadin bude idon *Majeed* tare da kara shan kunu”

    ” Wata kyakyawan yariya nagani wacce tai tsananin Kama da wannan saurayin da aka kira da *Majeed*”

     “Sai dai tana ganin *Majeed* ta shanye dariyarta, dayar yariyar da take bayanta kuwa kallo tabi *Majeed* dashi sosai har ta fara mance a inda take”

      “Sai da ta gaban ta jawo hannunta sannan ta farga, dan haka suka karasa tsakiyan falon”

    ” Umma ce tace ku kuma fah? kamar anjeho ku”

    “Fadawa jikin Umma tayi, ta kwanta, tare da fadin wlh Hajiya mun gaji ne, dayar ko zama tayi akasa cikin girmamawa ta gaida Umma “

    “Ahankali Umma ta fara shafa kan yariyar tare da fadin”

  ”  *Ummi* wai bakiga *Majeed* bane???

“Batare da ta kalli *Majeed* tace”

  “Ina wuni?

    “Lafiya, ya fada ahankali, tun daga haka *Ummi* bata sake cewa komai ba” dan haka itama dayar tace”

    Ina wuni?

   ” Lafiya, yace kamar yadda yacewa *Ummi* dan haka itama taja tai shiru, sai dai taso gaisuwan ya wuce haka”

     “Umma ce ta sake cewa, Ummi tashi ki haduwa *Majeed* abinci”

STORY CONTINUES BELOW

   ” Cikin sauri ta mike daga jikin Umma ta nufa kitchen, bayan minti 5 ta fito hannunta dauke da katon tire, agaban *Majeed* ta ajiye, sannan ta tsuguna tana zuba masa”

      Harta gama, ta tashi agurin, be dago ya kalleta ba”

    Jikin Hajiya ta koma ta kwanta, sannan ta rufe ido kamar me bacci”

    “Mikewa *Majed* yayi tare da fadin”

   “Umma na wuce, idan Abba ya dawo ace ina gaida shi”

    Kallon abincin da aka ajiye mishi Umma tayi sannan tayi murmushi tace”

   ” Toh *Majeed* ka gaida mutanan gidan”

    “Cikin Zafin nama ya fice afalon, *Ummi* najin fitan shi ta bude ido, tare da kwashewa da dariya”

    “Umma  ma dariya tayi sannan ta d’akawa *Ummi* duka abaya tare da fadin”

    ” Fitsararriya, kin dai maida *Majeed* abin dariyar, dayazo ya tafi kin dinga mai dariya kenan”

    “Faduwa kasa tayi tare da dafe wajen da Umma ta daka, tana sosawa tana cigaba da dariya”

     Itama kawar tata dariya ta fara, tare da fadin”

    ” Towai me kikema dariya?

     “Kara tintserewa *Ummi* tayi da dariya tare da fadin”

    “Kinga, bafa cin abincin zaiyi ba, amman yanaji Umma tace akawo masa, bece a’a ba, kuma yana kallo na zuba mishi amman ya mike yai tafiyar sa, kara kwaashewa tayi da dariya tare da cigaba da cewa kulum fah haka yakeyi, sai anzuba masa sai ya tashi yabarshi sai kace wani zautattace🤣”

    “Mikewa Umma tayi tana kokarin shiga daki take fadin”

   ” Ai kece babban mahaukaciya, tunda gashinan kinata dariya harda hawaye, kuma ki kiyayi ranan dazai kamaki kina masa dariya, dan kisan halinsa baya daukan raini”

     “Har Umma ta shige daki, Ummi ba tabar dariya ba, sai da ta gaji dan kanta tai shiru, abincin ta dauko suka fara ci”

     ” Suna tsaka dacin abincin kawar Ummi ta kalleta tace”

   ” *Ummi* wai wannan *Majeed* din ya kuke dashi?

    “Murmushi tayi sannan tace”

   ” *Yaya Majeed* yaron wan Abban mu ne, baki taba ganin shi agidan nan ba ko?

   ” Eh gaskiya ban taba ganin shiba, amman kisan menene?

   A’a sai kin fada”

   “Wlh ya burge ni, yana da kyau sosai, sai dai naga kaman ranshi abace yake, ko gaisuwar mu ma daker ya amsa”

    “Dariya *Ummi* tayi sannan tace ai indai *Majeed* ne bakiga komai ba, ba abin da aka masa, tsabar fadin raine da masifa data cika mishi ciki, jinshi yake kamar wani sarki”

     “Kai Ummi kodai Umma ce tamai fada kafin mu shigo?

     “Sadiya kenan, wlh ba’ayi mishi komai ba, haka dabi’arshi take”

     “Hmmm lallai, amma fah kyayunshi ya tafi dani, kuma da ace nice nabashi abinci yaki ci haushi zanji, amman naga ke dariya ma kike”

   “Ai ni Sadiya, ban dauki *Majeed* da mahimmanci ba, bare lamarinshi ya dinga bata min rai, gaisuwa ce kawai take hadani dashi, kuma ko ya amsa, ko kada ya amsa babu abin da ya dame ni, abinci kuma ko saunawa Umma zatace nazubo masa zan zuba masa tunda bani na dafa ba”

     “Kuma da kike ta cewa wani wai yana da kyau, ni ina ruwana da kyan shi? wlh banga abin birgewa awajen *Majeed* ba, dan wlh ni ina tausawa matar da *Majeed* zai aura, Magana mafah wuya take bashi, dan Allah wannan wani Soyayya zai iya?

STORY CONTINUES BELOW

   “Hmmm ai ba’anan takeba, *Ummi*, ni dai wlh dazai soni da babu abin da zai hana ni auren shi, nifah ko yanzun banso ya tashi ba, naso ya zauna naita kallon shi”

    “Dariya *Ummi* ta kwashe dashi sannan tace”

   Wlh kinyi asara Sadiya kawai daga ganin sarkin fawa sa miya tai zaki, ki raba kanki da wahala dan duk wadda ta aure *Majeed* hawan jini ne zai kasheta, bafah ya fara’a bare aje maganar dariya, ai idan kika auri Majeed tamkar kinkashe rayuwarki ne”

     “Dan bana tunanin *Majeed* yasan wani abu waishi So, bakiga yaki aure kwata kwata ba, ko rannan naji su Abba suna cewa ya kusa shekara 40, amman betaba cewa ga wata yariya da yake so ba”

   “Haka, Ummi sukai ta tattaunawa akan halayen *Majeed*”

    Washagari *Majeed* na kwance adakin sa, da misalin 5:30pm, mahaifin shine ya tura kofar ya shigo dan haka cikin sauri *Majeed* ya sakko daga gadon ya dauki jallabiyan shi yana kokarin sakawa yake fadin”

     “Sannun da zuwa Daddy”

    “Zama yayi abakin gadon, tare da amsawa sannan yace”

   ” *Abdulmajid* nazo muyi magana ne ta fahimta tsakanina dakai, domin narasa gane inda ka nufa”

  ” Cikin sanyin jiki, *Majid* ya taho kusa da mahaifinshi ya zauna tare dasa idon shi akasa”

    ” *Abdulmajeed* nasan koda ban fadaba, kasan akulum maganata bata wuce na Auren da kake ki, atunanina yanzun acikin abokan ka babu wadda beda iyali sai kai, kuma abin da na lura dashi hakan be damunka, dan haka muka yanke shawara cewa Zamu hadaka Aure da *Ummi*1

     “Cikin sauri ya dago kai ya kalli mahaifin shi, sannan ya maida kansa kasa, memakon yaji tashin hankalin, za’amai auren zumunci saima yaji wani nishadi na shigan shi”

     “Muryan Alhaji yaji yana cewa”

    “Ko kanada abin cewa ne?

   “Girgiza kai *Majeed* yayi tare da fadin a’a”

   “MikewaDaddy yayi tare da fadin”

   “Yauwa ko kaifah?, naji dadi sosai, duk da nasan cewa ka amince ne kawai badan kana son *Ummi* ba, sai dan bin Umarnin mu, Allah ya maka albarka”

     ” Ameen *Majeed* ya fada ahankali, juyawa Daddy yayi ya fita fuskarshi dauke da murmushin jin dadi”

     “Fadawa kan gadon Majeed yayi ya kwanta, wani irin farin ciki yaji yana shigarshi dan haka ya fara tunanin, toh wai ni daman son *Ummi* nake ne??

    “Fuskan *Ummi* yaita aunowa yana murmushi, tabbas *Ummi* tana da kyau, bata da makusa, sai dai ko yaya zaman su zai kasance bayan sunyi Aure?, dan tunda yake da wayonshi gaisuwa kadai ke hadashi da *Ummi*”

     “Washegari ma haka *Majeed* ya tashi da. Wani irin nishadi wadda yafi na jiya, bayan ya gama shiryawa ya nufa babban falon gidan”

     “Kafin ya karasa ya tsaya ya kara daure fuskanshi cikin tsare gida, yayi sallama”

     “Nan danan yaran dake falon duk suka shiga tai tayin su, gaida mahaifiyarshi yayi sannan yace zan wuce saina dawo”

    “Dan murmushi tayi sannan tace”

   “Yau kana fushi kenan dan haka bazakai breakfast ba ko?, wai mesa kake haka?, badaman amaka zancen Aure saika kama fushi”

   Ahankali yace”

    Momy nifa ba fushi nake ba, ina sauri ne kawai”

     Gyada kai tayi tare da fadin adawo lfy”

    Juyawa yayi ya fita, yana fita kannensa suka saka murna tare da mafadin”

    “Shikenan muma yaya Majeed dinmu ya yadda zaiyi aure”

    ” ‘Daya budurwan ce tace aini Wlh babu abin dayafin min dadi sai danaji  ance Ummi zai aure, kuma shima ya amsa”

    ” ‘Dayar ce tace kedai bari kawai Hussaina aiko yaya Majeed besu, dole mu sharalle abokin nan”

    “Wani irin dariya mahaifiyar su tayi tare da fadin”

    “Lallai kuwa jikin ku zaiyi tsami indai Majid ne ko cikin tarone zane ku zaiyi, garama ku kama kan ku”

    “Hassana ce ta mike tare da fadin”

    Aini daman babu ruwana, inadai jin dadin zaiyi aure, amman wlh ni Ummi ma tausayi take bani,   yaya Majeed fa awuni daya mgnr shi basa wuce kalma 10, kuma ga Ummi da shegen surutu”

    “Haka suka cigaba da tattaunawa akan halayen Majeed dana Ummi”

     Karfe 3: 30 ya tashi Aiki, yaso ya biya gidansu *Ummi kamar yadda ya saba kullum, amman haka kurum yau yaji kunyan Mahaifiyar Ummi yake, sannan kuma besan wani irin yanayi Ummi zatashiga idantaji lbrn ba,  Tsaki yaja tare da fadin” yanzun fama wata kila rainani zatayi, dole inkare mutuncina bazan taba barinta tagane meye azuciyata ba”

   Kwana yayi ya nufa gida, bayan yagaida Mahaifiyar shi ya shige dakinsa”

     Da misalin karfe 4:55pm majeed yaji Kanwar shi Hassana tana buga mishi ko fah tare da fadin”

    ” Yaya! Yaya! Abba nakiran ka”

     ” Naji, kawai yace sannan ya ajiye wayoyin sa dake hannun sa yafi ce”

    Tun kafin ya shiga falon yaji muryan Ummi da su Hussaina sun cika dakin da surutu”

     Wani Uban tsawa ya buga wadda tai sadin faduwan wayar dake hannun Ummi, ‘yan biyu kuwa aguje suka nufi falon mahaifin su, kowacce idonta awaje”

                

          Maman Yazeed🔥 🔥🔥🔥🔥🔥

*KOWANNE BAKIN WUTA*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥

    ( da nashi hayakin)

💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by

    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*

    Wattpad @fadeelalamido

             3-4

🔥”Dan haka lokaci da *Majeed* ya shigo falon Ummi kadai ya gani ta kankame jikinta, tare da runtse ido”

    Kallonta kawai yayi ya girgixa kai, ya wuce tare da fadin”

     ” ‘Yan rainin hankali kawai”

      “Kamshin turaren da taji babu, shi ya tabbatar bata daya wuce, dan haka ta fara bude idonta ahankali, tunda take aduniya bata taba tsorata irin na yau ba, ta dade tanajin anacewa Majeed mafadaci ne Amman bata taba yadda ba sai yau, dan ita gani take magana ma ba iyata yayi ba”+

      “Wayarta ta dago nantaga tayi kwatsa kwatsa, dan haka nan take ta fara hawaye, tana cikin wannan halin ‘yan biyu suka fito tare da fadin, kije ana kiran ki”

   “Mikewa tayi, rike da fasheshshiyar wayanta ta nufa falon”

     “Tana shiga ta wuce can kusa da kafafuwan mahaifiyar *Majeed* ta zauna, sai dai yana yin zaman ya fara bata tsoro, domin ta kula maganace me mahimmanci za’ayi?

    “Ahankali Daddy ya kira sunanta tare da fadin”

   ” Inason kibani hankali ki, sannan kuma ina fatan zakiyi mana biyayya kamar yadda dan uwanki yayi”

     “Dagowa tayi ta kalli Daddy tare da faduwan gaba”

    “Cigaba yayi da cewa Ummi, ajiya muka yanke shawaran zamu hadaku Aure keda *Abdulmajeed*”

    “Cikin sauri ta runtse ido, sannan ta bude su tare da fadin”

   ” Allah ka gaggauta farkaddani daga wannan mummunan mafarkin, mikewa tayi tsaye cikin daburcewa”

    Cikin sauri mahaifiyar Majeed ta riketa tare da maidata gurin zamatan, kuka Ummi ta saka tare da fadin”

  Momy da gaske ne ba mafarke nake ba???

    ” Ba mafarki bane Ummi, gaske ne”

    “Jikinta babu kwari ta koma da zauna, kowa ita ya zubawa ido, har Majid da mafiya yawan lokaci kansa aduke yake, amman yau ya zubawa *Ummi* ido yana kallonta”

     Abba ne ya kalleta yace”

  ”  Ke, ki nutsu bana son shashanci”

     “Cikin sauri Daddy ya daga masa hannu tare da fadin”

      “Babu ruwanka Sani, dole mu saurare ta, dan baza amata auren dole ba”

   ” A’a, wanne irin magana ce wannan yaya, kana gani fah, *Majeed* da yake Namiji ma ya mana biyyaya bare ita mace??

    “Bahaka abin yakeba sani, *Abdulmajeed* namiji ne, yana da daman dazai kara auren wadda yake so kowanne lokaci, ita kuwa macece idan muka tursasata ta aureshi dole, bamu mata adalciba, yanxun ba da bane, halayen yaran yanzun yasha babban da yaran da, dan haka bazamu tursasa Ummi ta aure Majeed ba”

    “Juyawa yayi ya kalle Ummi daketa share hawaye yace”

  ”  Daina kuka *Ummi* maza ki share hawayen ki, kuma ki bude baki kiyimin magana karkiji kunya, kina son *Abdulmajeed* ko a’a???

    ” Dagowa Majeed yayi ya daura jajayen idonshi akan Ummi, dan tuni yaji hankalin shi yafara tashi”

  ”  Itako *Ummi* cikin sauri ta kalli alhaji tace”

STORY CONTINUES BELOW

     Wlh Daddy bana son shi, dan Allah karku hadani dashi, *Mukutar* nake so”

    “Murmushi Alhaji yayi yayin da Abba ya hada fuska, hakama Umma mahaifiyar Ummi bataji dadin maganar Ummi ba, Momy ko mahafiyar Majeed jitayi duk gwuwarta tayi sanyi”

     “Shiko Majeed har yanzun idonshi nakan Ummi wani irin kallo yake mata idon shiko yayi jawur”

    “Muryan Daddy sukaci yace”

     Wanene mukutar?

   “Abba ne yace wani yaro ne dake zuwa wajenta dan gidan Alhaji Yaro”

   ”  Toh yanzun daman kai kasan akwai wadda yake zuwa wajenta kabarni inata shirme?

     ‘Ton Alhaji gani nayi gida be kushiba ai ba’akaiwa dawa ba”

    “Dan murmushi Alhaji yayi, sannan yajuya ya kalli Majeed yace”

    “Toh Majeed kadai ji, Ummi tana da wadda take so, dan haka Maganar Ummi babu ita Sai kaje ka nemi mata”

      “Tunda Alhaji ya fara magana Majeed ya sauke kan shi kasa, yana idawa kuma ya mike cikin sauri ya fita a falon”

  ” Gaba dayansu shi sukabi  da ido, kowa da abin da yake tunani acikin zuciyar shi”

    Basu tashi taron ba har saida akacewa Ummi ta fadawa mukutar ya turo iyayen sa, dan haka koda suka koma gida zuciyar Ummi kar”

     Majeed ko yana komawa dakinsa kashe wutan dakin yayi dan haka duhu ya baiyana, daker ya lalube gado ya kudun dune, hakan nan yaji hawaye yana zubo masa”

   ” Yana cikin haka yaji anbude dakin, cikin sauri ya fara share hawayen fuskan shi”

   ” Majeed, yaji muryan mahaifiyar shi ta mafada”

    “Na’am Momy”

    “Meyasa ka shigo cikin duhu ka zauna bayan injin akunne yake?

    “Zafi nakeji Momy”

   ” A’a Majeed kanajin zafi ai saika kunna AC, matsawa tayi inda makunnin wutan yake ta kunna, hango majeed tayi atakure dan haka ta matsa bakin gadon ta zauna”

    Shima tashi yayi ya zauna”

”  Kura mishi ido Momy tayi, sannan tace Majeed daman kana son Ummi ne???

 

   “Murmushi yayi tare da fadin”

   Ni ba sonta nake ba Momy, kawai dai nayi mamaki ne, nina kasa cewa bansonta amman ita ta fadi bata sona kiri kiri”

Hmmm kawai tace zuwa can ta kalli Majeed tace”

    “Wannan ba abin damuwa bane Majid idan kaga dama ma saika riga Ummi aure”

  ” Sunkuyar dakai yayi sannan yace”

   Momy dan Allah karku kara ma wata tallah ta, bare ma wata ta sake cewa bata sona, nida kaina zankawo mata”

    “Murmushi mama tayi tare da buga bayan majeed sannan tace”

   “Majeed kai din ne zaka iya ka iya kawo mata”

  “Kallonta yayi cikin ido sannan yace”

  “Momy wai me kuka maidani ne?, nifa ba yaro bane, kuma ai aure lokaci ne, idan lokacina yayi ai zanyi”

    “Murmushi Momy ta sake yi sannan tace toh Allah ya nuna mana lokacin Majeed, zanso naga yariyar da zaka kawo”

    “Murmushi yayiwa Momu sannan ta mike ta fita”

    “Ko bayan fitan mama tunanin Ummi yaita yi ya rasa yadda akayi ta shiga zuciyar shi lokaci daya, duk yadda yaso ya kawar da tunaninta abin ya faskara”

    Dan haka washegari bayan ya tashi aiki ya nufa gidan su Ummi”

    “Yana saka hancin motan shi ya hango wani saurayi zaune bayan motar shi, ji yayi gaban shi ya fadi, dan saurayi ya hadu iya haduwa, acikin zuciyar shi yace kar dai ace wancen shine Mukutar”

    “Daker ya iya karasawa gurin adana motoci ya faka motar shi, sannan ya sakko ya nufi shiga cikin gidan”

    “Sai dai shima Mukutar ganin Majeed sai da gaban shi ya fadi, domin ganin shi yayi kamar wani balarabe, shigarshi zuwa takunsa sunyi matukar birgeshi, sosai yaji kishi ya kamashi dan ko namiji yaga Majeed zai yi wuya ya iyamai kallo daya, bare kuma mace”

     “Acikin zuciyan shi yace wannan wanene?, me zaiyi acikin gidan su Ummi?, gani yayi babu me bashi amsa dan haka yace”

    “Lallai ya zama dole in gaggauta neman auren Ummi”

               🔥Mmn Yazeed🔥 🔥🔥🔥🔥🔥

*KOWANNE BAKIN WUTA*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥

( da nashi hayakin)

💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by

*Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*

Wattpad @fadeelalamido

5-6

🔥” Shiko Abdulmajeed yana daf da isa kofar falon Ummi ta fito tana zuba kamshi, daganin ta tana cikin farin ciki, kallo yabita dashi harta karaso daf dashi dan haka ta kyauce dan gudun karta gogi jikinsa”

“Harta gotashi yajuya yasa hannunshi ya jawota, tare da hadata da bango ya matseta, take Ummi taji tashiga wani yanayi wannda bata saba jinsa ba, domin hannun Abdulmajeed na sauka ajikinta taji kamar wuta ya jata”+

“Banda zaro ido babu abinda Ummi take, tuni jikinta ya dauki yarawa dan inda wani ne yace mata Abdulmajeed zai yi haka zatace karya ne”

“Runannun idanunsa ya zuba mata, cikin daure fuska yace”

“Ina wasa dake ne??

“Cikin sauri ta girgiza kai”

“Wato dan kina murna saurayin ki yazo shine zaki angajeni ki wuce gurin wancen dan ciranin, kin wani sako turaren ‘yan kuli, kenan adole zaki birge saurayi, ban da wari da karni babu abin da kike yi”

“Hawaye ne suka fara zubo mata, domin ita tasan bata gogi jikin shi ba, neman fitina kawai yake, ganin inda ya tsureta da ido yasa tace to kayi hakuri dan Allah”

“Dallah rufe min baki, banza mummuna kawai, me kama da mayu”

“Ran Ummi ne ya fara baci, dan haka ta sukuyar da kanta kasa, tare da zunburo baki”

“Wa kike murgudawa baki??, Abdulmajeed ya fada tare da kara matseta jikin bango”

“Sosai takejin wasu kasusuwa na jikinta na mata zafi, saboda matsan da yayi mata”

“Yan yatsunsa ya hada guda biyu ya d’ane mata baki, tare da fadin Mara kunya kawai, ‘yar rainin hankali”

“Sosai taji zafi dan haka ta fashe da kuka tare da rike bakinta, jitayi har gurin ya kunbura”

“Cikin Zare ido yace kuma daga yau karna kuma ganin wani yazo gurinki da rana, me zai sashi zuwa da rana idan ba iskanci ba” wlh idan nakuma ganin sa daga ke harshi d’an ciranin sai kunci uban ku, sakinta yayi sannan yayi gaba ya shige cikin falon”

“Itako Ummi ganin inda ta koma firgai firgai yasata ta kasa fita, kuka take sosai dan haka takira mukutar awaya ta fadin mai abin da Abdulmajeed yayi mata, adabur ce yace, ya kuke dashi???

“Yayana ne, yaron wan Abba ne, shine wadda nabaka lbr”

“Cikin daburcewa ya sake yace”

Ummi bana son na rasa ki, idan na rasaki Ummi tamkar na rasa rayuwata ne, bazan iya rayuwa babu keba, dan Allah karki bari narasaki”

“Haba Mukhtar ai nagaya maka, anjenye zancen shi, ka kwatar da hankalin ka”

“Ummi ina tunanin idan iyayen ku suka fuskaci yana sonki zasu iya dawo da zance”

” Ai ba sona yake ba, shi dai kawai dan neman balaki ne, idan beyi ba bejin dadi”

“Waye ya gaya miki?, wlh Ummi Son ki yake yi”

Yanzun kina ina?

“Share hawaye tayi sannan tace, gani nan tsaye ina hango ka, bazan iya karaso wa bane, ya kunbura min baki, sannan yace ma wai wari nake”

“Dan murmishi yayi kadan, sannan yace, toh ki karaso mana Ummi, ni ke nake so, ba kwalliyar ki ba, kun buren bakin ki bazai sa inga munin ki ba, dan bashi bane agabana”

STORY CONTINUES BELOW

“Cikin muryan kuka ta sake cewa, ni bazan iya zuwa ba, turaren dana sakama yace na ‘yan kuli ne, kuma ni kaina yace karni nake”

“Yanzun kina nufin bazan gankiba, yaufa kwana 3 bamu haduba, wai bakijin tausayi nane?, dan Allah ki daure ki karaso”

“Kashe wayar Ummi tayi, sannan ta nufo gurin mukutar”

“Tun kafin ta karaso ya sakar mata murmushi har ta iso gabanshi idonsa na ganta”

Bayan sun gaisa yace”

“Ummi ayau din nan zan matsawa Alhaji yazo ya neman min auren ki, wannan yayan naki da gangan yaci Zalin ki, dan dai ya bata min rai, tare da bata kwalliyar da kikayita domin ni”

“Daidai lokacin ta hango Abdulmajeed yafito yana tafiya cikin azama kaman yadda ya saba”

“Nan danan ta kara rikicewa, yana zuwa daidai gurun su yajuyo ya galla masu harara”

“Dukar dakanta tayi yayin da Mukutar ya mikawa Abdulmajeed hannu tare da fadin barka da fitowa”

“Banza Abdulmajeed yayi dashi, tare da kara wurga mai harara, sannan ya juya ya shige motar shi yabar gidan”

“Ajiyan zuciya mukutar yayi sannan yace”

“Ummi ina gudun ranan da iyayen ku zasu ganu halin da wannan yayan nake yake ciki, domin naganu mahaukacin sonki acikin idon shi”

” Mukutar kadaina wannan tunanin, Abdulmajeed ba sona yake ba, haka halinsa yake, bahagon mutum ne, kuma ni duk abin da yayi min zan jure bazan gayawa kowa ba, balle har suma suyi zargi kamar yadda kayi”

“Dahaka sukayi sallama da Ummi ta nufa gida, koda Hajiya ta tambayesa meyasa meta abaki cewa tayi faduwa tayi”

” Fada Hajiya tai mata akan ta rage saka takalma masu tseni”

“Daren ranan Mukutar ya turo magabatan shi domin a neman masa auren Ummi”

Bayan sun gaisa cikin girmama juna, Alhaji yaro ya gayawa Abba abin da yake tafi dashi”

“Dan murmushi Abba yayi sannan yace”

” Ai tsakanin zuri’armu da taku babu zancen tsayawa bincike, domin munyi kuruciya tare, wasa tare, kowa yasan kuwa, ada ban da yanzun da zumunce yayi wuya, dan ni danaga mukutar din ma ban shaidashi ba, ita take gaya min yace mata shi dan gidan Alhaji yaro ne”

” Jikin Alhaji yaro asanyaye yace”

” Alhaji ban katsekaba, azahirin gaskiya bani na haifi Mukhtar ba, Mukutar yaron kamfani nane, yaro ne menatsuwa sosai, dan haka muke tare dashi har yanzun, yana da gaskiya da rukon amana”

“Cikin Tsananin Mamaki abba yace”

” Ban fahimceka ba alhaji?, kana nufin d’an dan uwanka ne?

“A’a, Alhaji ya fada sannan yaci gaba da cewa, aikine ya hadani dashi, har nake jinshi tamkar dan da nahaifa, biyayyar da mukutar yake min, kodan dana haifa sai haka, sanadin haka ya kawo mun iyayen shi mun san juna, iyayen mukutar mutanan Niger ne”

” Shiru Abba yayi zuwa can yace”

“Toh babu damuwa amman inason kabani lokaci zanyi shawara, kafin mu yake wannan mgnr”

“Toh ba damu amman dai zan kara jaddada maka, mukutar yaron kirkine, kuma ya matsa sosai yana son agama komai da wuri, d’azun ma ya hadani da Mahaifin sa mukai waya, yabani wuka da nama, kuma zasu halarci daurin Auren”

“Jikin Abba asanyaye yace toh insha Allahu babu damuwa, kadai bani likaci ko zuwa jibine zanyi shawara”

“Daga haka sukayi sallama da Alhaji yaro, bayan tafiyan su Abba ya nufa gidan su Abdulmajeed domin sanar da dan uwan shi halin da ake ciki”

STORY CONTINUES BELOW

“Shima shiru yayi yana nazari, zuwa can yace”

“Alhaji yaro, mutumin kirki ne, kuma da be yadda da yaron ba bazai zo neman masa aure ba, ina ganin babu wani abu”

“Cije lebe Abba yayi tare da fadin”

“Kai! amman ni dai gaskiya ina wani tunani, haka kawai bamusan iyayen shiba saimu dauki yariya mu bashi?

“Toh ya za’ayi, tunda suna son junan su, kuma yaran yazun idan kace zaka musu ta karfin tsiya sai kaga anje babu kwanciyar hankali, idan ko su suka kawo wadda su ke so, duk wuya sai kaga sun jure”

“Girgiza kai Abba yayi sannan yace”

“Shikenan, yanzun zan gayawa mahaifiyarta suje suyi shawara, idan tace taji tagani, zan turo maka Alhaji Yaro saiku gama Magana amman ni dai ko wani abu ya biyo baya ta kuka da kanta”

“Murmushi Alhaji yayi tare da fadin”

“Kana nufin kace zakayi fushi da ita kenan, a’a wannan be dace ba, kamata yayi mutaru mumata batan alheri, so da yawa fushin iyaye shike kawowa ‘ya’yan mu matsalolin, mudai muyi addu’a Allah ya tabbatar mana da alheri”

“Cikin rashin kwarin jiki abba yayi sallama ya koma gida, cikin matsanan cin damuwa yake fadin ma Umma halin da ake ciki, itama ji tayi babu dadi, dan haka Washegari ta samu Ummi akan maganar”

“Umma toni ai bada ‘yan uwanshi zan zauna ba, ‘yan uwanshi suna Niger fah, muda zamuyi zaman mu nan, ina ruwana dasu”

“Hmmm bazaki ganeba Ummi, ni inaga ki hakura da mukutar kawai shine yafi miki Alheri”

“Dan danan hawaye yacika idonun Ummi cikin kuka tace Umma sai dai idan sabo da yaya Abdulmajeed kuke son ku hanani auren Mukutar, amman wlh Mukutar beda matsala kuma ni Wlh bazan auri Majeed ba”

“Kuka take sosai, dan haka Umma tace a’a kwantar da hankalin ki, shima Abdulmajeed din aiba son ki yake ba, me zaici dake, sanin kankine babu abin da zaki nuna masa, ai idan ma ya aureki shi aka cuta, sanin kanki ne Nigeria tana alfahari dashi, wlh duk wadda ta samu Abdulmajeed a matsayin mijinta ta more miji”

“Cikin kunkunai tace Majeed din da yakejinsa kamar wani tababbe, wanne soyayya zai iya”

“Mamaki ne ya kama Umma, sosai, duk da tayi maganar ne ciki2 amman sarai taji abin da ta fada, dan haka ta miki tare da fadin”

“Ai kece tababbiyar, daman Abban kine yace agaya miki, kuma nagaya miki”

“Toh ni dai Umma dan Allah Mukutar din nake so”

“Cikin tsanin mamakin Ummi, Umma tabar dakin sannan ta sanarwa Abbanta yadda suka yi”

“Girgiza kai yayi tare da fadin shikenan, amman badan banason na mata auren doleba bazan bari ta aureshiba”

Washegari Alhaji yaro ya sake dawowa, tunda yayiwa Abba waya cewa gashi yazo, Abba yasa aka bude masa dakin baki, shiko dakin Ummi ya nufa, tana kwace tana latsawa wayarta taga shigowan Abba, cikin sauri ta tashi ta zauna tare da fadin”

Sannu da zuwa Abba”

“Kallonta Abba yayi yace yauwa Ummi ya gida?, yau kwata kwata ban gankiba”

” Abba yau natashi da ciwon kaine saboda daren jiya nakasa bacci”

“Meya hanaki bacci?, kina tunani ko?

“Cikin sauri ta dukar dakanta kasa, kamar wadda ta tuna wani abu”

” Dan murmushi Abba yayi sannan yace ko kina tunanin Mukutar din ne?

“Kara sunkuyar dakai tayi tare da girgiza kai”

“Ummi ?, kindai dage mukutar din kike so ko?

” Abba ya fada tare da tsareta da ido”

“Kasa magana tayi kantako kaman zai fadin kasa, saboda yadda ta dukar dashi”

Dan haka Abba ya girgiza kai ya juya ya fita, daukan Alhaji Yaro yayi zuwa gidan su Abdulmajeed, acen aka gama mgn alhaji Yaro yaba da komai da ake bukata har aka tsaida rana wata 2 masu zuwa”

“Nan danan lbr ya karade dangi, sai dai dayawa sunji haushin Ummi dataki Abdulmajeed, bama kamar Hassana da Hussaina dan Hassana har da hawayenta”

“Shiko Majeed ranan dayaji antsaida ranar auren Ummi komawa yayi tamkar wani gunki, idan ya zauna ya kalli guri daya saiya dade be mutsaba”

“Cikin dare kasa bacci yayi, haka yaita juyi akan gadonsa, yadda yaga rana haka yaga dare, dan haka Washegari ya tashi da zazzabi, haka ya daure ya tashi yayi wanka yasha magani ya nufa gurin aiki, batare da yabari kowa yaga fitan shiba”

“Ko agurin aiki ma kasa komai yayi sai faman rawan sanyi yake yi, dan haka abokin aikinsa Sadiq ya daukoshi domin maidashi gida, bayan ya saya mishi duk magungunan dazai bukata”

“Ahanya su ta zuwa gida Sadiq ya kalli Majeed yace”

“Majeed wai meke damun ka kwana biyu?, sai nake ga kamar akwai abin da kake boye min?

“Cikin rawan sanyi Abdulmajeed yace”

“Hmmm Sadiq wai kirikiri Ummi ta ta kalli tsabar idona tace bata sona”

“Da sauri Sadiq ya kalli Abdulmajeed, domin ji yayi kaman anfizzo zacen daga cikin cikin Abdulmajeed, dan abune ne wahala kaji Abdulmajeed yayi zancen mace, dan haka cikin tsananin mamaki Sadiq yace wacece Ummi?

“Tsaki Majeed yaja sannan ya juyar da kanshi can gafe yace”

“Ummmi kanwata ce, yariyar ganin Daddymu ne, nan ya kwashe yadda akayi ya gawa Sadiq”

“Mamaki kwance akan fuskan Sadiq yace, tokai daman sonta kake ne???

“Ni basonta nake ba, amman naji haushi da tace bata sona, kuma jiya danaji ansa mata rana nakasa bacci, Sadiq zuciyata tanamin zafi sosai”

“Kwashewa Sadiq yayi da dariya, dan haka Abdulmajeed ya harareshi tare da fadin”

“Menene haka, kai matsalata dakai kenan, ina gaya maka damuwata kai kuma kana min dariya, Wlh bakaramin zafi najiba da Ummi tace bata sona, koda yake ba laifinta bane, laifin wadda suka kai mata tallata ne, kuma datace batasona memakon su tursasata sai sukace wani wani na neme wata, har yakai nan beji Sadiq yace komai ba dan haka ya juya ya kalle sa”

Ganin sa yayi rike da ciki yanata faman kyalkyalta……

Maman Yazeed🔥 🔥🔥🔥🔥🔥

*KOWANNE BAKIN WUTA*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥

    ( da nashi hayakin)

💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by

    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*

    Wattpad @fadeelalamido

                7-8

🔥”Sararawa Sadiq yayi da dariyar sannan yace”

   “Kai! amman wannan abu yamin dadi wallahi, kai da hadadun babys kebi kana musu yanga, yau sai kagaka kana makerketa, inda nasan hakane ma ai bazan baka magani ba wallahi, barinka zanyi kai tayi ina kwasan dariya”

     “Hmmm Majeed ya fada sannan ya kalli Sadiq yace”

    “Narasa yadda a kayi nafara son yariyar nan, hakanan na tsinci kaina ahaka”

” Murmushi Sadiq yayi sannan yace”

    Kasan Allah, mucire zancen wasa, tunda har kaji kanason yariyar nan kawai ka sameta  ka gaya mata kana sonta”

    Allah ya kiyaye wlh, bata isaba,, tayi kadan, inagaya maka gaban iyayen mu ta fashe da kuka tanacewa ita bata sona, dan me ni zan nace ina sonta?

   ” Toh kar kace, ka xauna a daura mata aure da Mukutar din”

      “Wani irin kallo Abdulmajeed ya wurga mai, sannan yace karka sake kiramin wannan sunan, danji nake tamkar kana watsamin wuta wlh”

    “Bazan bariba, ai sunan kanina ne mukutar, ka isa ka hanani kira ne?

     “Tsaki Abdulmajeed yaja tare da fadin”

    “Tsaya na sauka, Abdulmajeed ya fada cikin fushi”

   ” Banza dashi Sadiq yayi yacigaba da tukinsa dan haka Abdulmajeed ya kama sitiyarin motar”

   ” Tangal2 suka fara atiti dan haka cikin rudewa Sadiq yace Abdulmajeed meye haka ?, wai kashemu zakayi?, ganin baya sauraranshi yasa ya matsa gefen hanya ya tsaya”

    “Budewa Abdulmajeed yayi ya fice, cikin tsanani fushi tare da yanayin dake nuna ya fusata sosai”

“Gaba yayi abinshi, ganin inda jikinshi ke rawa yasa Sadiq yaji bazai iya barinshi agurin ba, dan haka ya kara binshi da mota, sannan ya sakko tare da fadin”

        “Yi hakuri kazo mu karasa, kaga baka da Lafiya”

     “Bazan hauba, dan tsabar wulakanci ina gaya maka abin da nakeji  ajikina ka maida abin wasa”

    “Murmushi Sadiq yayi tare da fadin”

  ” Shine nace ai kayi hakuri nabari ko?, hannun shi ya jawo sannan ya bude mishi motar ya zauna”

    “Har suka isa gida basu kara Magana ba, har cikin dakinsa yakaisa sannan ya koma Office”

    ”  Hassana ce kema Momy gulman taga Sadiq ya dawo da yaya Abdulmajeed gida, kuma taga kamar bashi da Lafiya dan haka Momy ta nufi dakin”

     ” Acikin bargo ta sameshi har yanzun jikin shi rawa yake yi”

     “Zama tayi abakin gadon tare da kiran sunan shi”

   ” Amsawa yayi batare da ya fito da kansa ba, dan haka Momy ta jaye bargon daga fuskan shi tare da fadin”

   ” Meke damun ka?

    ” Zazzabi ne Momy”

    ” Zazzabi kuma Majeed?, wani abu na damunka ne?

   ” Girgiza kai yayi tare da fadin a’a”

STORY CONTINUES BELOW

    “Abdulmajeed meke damun ka ? nasan akwai abin da yake damun ka, tun kana karamin nakaranci halayen ka”

    “Momy nace miki ba komai, yanzun bazan yi Zazzabi ba sai ina cikin damuwa?

   “Hmmm Abdulmajeed daren jiya bakayi bacci ba ko???

     ,”Nayi bacci mana, mezai dameni dazan kasa bacci”

    “Hmmm Abdulmajeed ka daina cutar da zuciyar ka,   wajen shegen girman kai da miskilancin tsiya, ace magana ta fatar baki ta dinga gagaran mutum”

    “Momy nafa ce miki babu abin da yake damuna”

   ” Mikewa Momy tayi cikin haushi ta nufi fita dakin tana fadin”

   ” Kai ka sani, jiki magayi”

   “Har kashegari Momy bata sake zuwa dakin Abdulmajeed ba, sai dai taitasa ido taga fitowan shi har kusa 10:00am taji shiru dan haka lokacin da Alhaji ya mata sallama zaitafi Office ta dakatar dashi”

    “Tsayawa yayi tare da fadin yaya akayi?

    “Abdulmajeed fah tun jiya yana kwance beda lafiya”

    “Meke damun shi??

   “Alhaji nifa ina tunin Majeed son Ummi yake, dan tun ranan datace bata sonshi nakula yana cikin damuwa”

    “Shiru Alhaji yayi zuwa can yace”

    “Shine ya gaya miki haka??

    ” A’a nice dai na fuskanci haka”

    “Toh ki barshi azuciyan ki, domin anriga da anbada Ummi ga wanninsa, kuma shiba yaro bane dazai kasa gaya mana abin da yake so, yanzun ace Kamar Abdulmajeed, bazai iya bude baki yayi Magana damuba?”

     “Ya mutsa fuska Momy tayi tare da fadin”

   ” Haba Alhaji saikace baka tausayin sa?, tunda yana sonta ai sai ahakura da wancan din”

   ” Dan murmushi daddy yayi sannan yace”

    “Inace agaban ki yariyar nan tace bata son Sa, koko so kike atursasata ta aureshi dole, dan Allah karki kara tasar da wannan zancen ayanzun Ummi matar wani ce fah”

    “Har Alhaji ya juya ya fita Hajiya nabinshi da kallo, mamaki take acikin zuciyarta wannan wanni irin ubane dabe damu da matsalar dansa ba”

     “Dakin Abdulmajeed ta shiga tasameshi zaune abakin gado ya hada kanshi da guiwa”

     “Yanajin mutsi ya miki tare da kwaso wayoyin sa dake gefen gado yana fadin”

   “Ina kwana Momy kinjini shiru ko?

    “Cikin tsura mai ido tace eh na dauka ma jikin ne”

    “A’a Momy nasamu sauki ai, yanzun ma gurin aiki zani”

    “Toh yayi kyau, Allah ya kara Lafiya”

    “Ameen ya fada ahankali, tare da Momy suka fito falo sannan ya mata sallama ya tafi”

    “Bayan ya tashi aiki gidan su Ummi ya nufa cike da zumudin son ganin Ummi”

    “Yanayin Sallam akofar falon, Ummi dake kwance akan kujera gabanta ya yanke ya fadi, cikin sauri ta dafe kirjinta, sannan ta amsa sallaman”

     “Shigowa yayi ya zauna akan kujera kamar inda ya saba, kara hade fuska yayi sannan ya fara dannan wayarsa”

    “Atsorace Ummi tace”

     Ina wuni?

   “Lafiya, shiru palon ya dauka na wani lokaci sannan yace”

   Ba kowa ne agidan??

STORY CONTINUES BELOW

   “Eh….. am daman… Umma batanan nikadai ce agidan”

    “Wani irin yamutsa fuska yayi sannan yace”

    “Ai waike kina saka kanki amatsayin mutun ne?, tsaki yaja tare da fadin”

    ” Aini banga mutum nan ba, banza wawiya kawai matar dan cirani”

    “Wani irin kallo ta masa  sannan ta miki ta nufa kitchen, zuwa can sai gata ta hado masa abinci kamar yadda take hadu masa idan Umma nanan”

    “Agaban shi ta aje sannan ta dago ta kalleshi, Yaya Mukutar ga abincin nan”

    “Kallonta yayi azabure tare da zaro ido afusace ya dauki daya daga cikin kulolin data aje masa ya jefeta dashi”

    “Azubure ta miki saboda zafin miyar daya watsu ajikinta, tare da binshi da kallon mamaki”

   “Nunata yayi da yatsa, duk ranan da kika kara kirana da Mukutar wlh saina barki kwance ni zakima rashin kunya?

    “Sai alokaci Ummi ta ganu laifinta harga Allah bada gangan tayi ba, asalima ban da yanzun daya fada batasan tayiba, saidai yadda ya fata mata jiki da miya abin ya bata haushi, dan haka ta zunbura baki tare da kunkunai”

    “Gadan gadan ya nufota da niyar kai mata duka”

   “Rugawa tayi da gudu tare da fadin Allah ya isa”

    “Sosai ran Abdulmajeed ya kara bacci, juyawa yayi ya fice agidan yana huci”

    “Tun daga ranan Ummi bata kara yadda sun hadu da Majeed ba, tanaganin lokacin zuwan shi yazo saita tsiri baccin karya, ko tad’i ma ba sosai takeyi ba, dan gudun karsu hadu da Abdulmajeed”

    ” Shirye shiryen biki aketayi gashi yau sauran kwana 3 rak  adaura wa Ummi aure, dan haka Abdulmajeed ya kara rikecewa hatta ‘yan uwa duk sun fara fahimtan halin dayake ciki”

    “Ummi da Mukutar kuwa babu wadda ya kaisu farin ciki, sosai suke cikin annashuwa”

    “Komai daya dace asaiya ‘yar gata ansaiwa ummi, yau kwana 3 kenan da akaje gidan mukutar aka mata jere”

   “Duk halin da ake ciki Abdulmajeed yana sane dan haka hankalinsa ya kara tashi, sosai yakejin son Ummi azuciyar shi, babu wadda yasan halin dayake ciki sai Sadiq sai kuma Momy data fahimci haka”

  ” Ana gobe dauren aure Momy ta nufi dakin Alhaji”

    “Ganinta cikin damuwa yasa  Alhaji ya kalleta yace”

     Lafiya?

   “Babu fah Lafiya Alhaji, yau kwana 3 kenan yadda aka ajewa Abdulmajeed abinci haka ake dauka, ko dubawa bayayi bare yaga kalarsa”

   “Shiru Alhaji yayi sannan yace”

    Kiramin shi”

   “Lokacin da Momy ta shiga dakin yana zaune yayi tagumi tare da kurawa wayarsa ido, gawani guntun hawaye asakon idon sa”

   “Har Momy ta gama kare mai kallo be sani ba ahankali ta karasa gaban shi tare da zare wayar ahannun shi”

    “Dagowa yayi da sauri yana kallonta adaidai lokacin data kurawa wayarsa ido”

   “Durkusar dakai yayi tare da fadin kash😬”

   “Dagowa Momy tayi tana kallon shi sannan tace”

   “Hmmm Majeed kenan kai da kace baka son Ummi kuma inna ka samu pic dinta?

    “Hawayen dake makale afuskan sa ya share sannan ya shafa keyar shi yace”

STORY CONTINUES BELOW

    “Momy sai inason Ummi zan sami pic dinta, wani abokina ne ya turo min dayake tambayata wai kan wata ce?

    “Murmushi Mama tayi sannan tace Abdulmajeed zanso daka daina yaudaran kanka kafito ka nuna abin da kake so”

   “Momy dan Allah kibar wannan maganar ni bana son ta, kamar yadda kike tunani, bayan so irin na ‘yan uwantaka bansan  kuma wani so danake mataba”

     “Cikin ido Momy ta kalleshi sannan tace”

   “Toh ai shikenan Abdulmajeed karka manta gobe daurin auren Ummi”

     “Ai ina sani Momy”

  ” Gyada kai Momy tayi sannan tace kaje Baban ka na neman ka”

    “Juyawa tayi bata jira yace komai ba”

    “Ajiyan zuciya yayi sannan ya mike ya fice”

   Abdulmajeed zaune agaban Mahaifin shi bayan ya gaidashi yace”

     “Abdulmajeed, meke damun ka kwana biyu?

     “Bawani abu dayake damuna Daddy

    “Kallon shi Alhaji yayi sosai sannan yasake cewa”

  ” Abdulmajeed kai ba yaro bane karami dazan zauna ina rarrashin ka dan ka fadamin abin dake damun ka, ni mahaifinka ne inason sanin abin da kake so dahar yake hanaka cin abinci”

    “Cikin sukuyar dakai Majeed yace, Zazzabi ne  Daddy”

    “Hmmm Zazzabi kuma Abdulmajeed?, toh shikenan Allah ya sauwake maka, ina fatan kana sane da daurin auren Ummi gobe, inason ingan ka agurin da wuri, idan ba hakaba ranka zaiyi mummunan baci, mgnr abinci kuma Inga dama kaci idan kaga dama karkaci babu abinda ya dameni”

    “Cikin sanyin jiki Abdulmajeed yabar dakin yarasa yadda a kayi ya kasa sarrafa kanshi har ake fahimtan halin da yake ciki, sai dai abinda yayiwa kansa alkawarin ko son Ummi zai kasheshi baxai taba furta kalman so agareta ba”

Daurewa yayi yai wanka ya nufi Office, duk wadda ya kallesa yasan yana cikin damuwa, duk da yana basarwa, bayan ya tashi aiki gidan su Ummi ya nufa sai dai yau yakasa shiga gidan domin tun aharabar gidan yaji gabansa ya fadi, saka makon motoci daya gani cike da gidan ya tabbatar mishi lailai har yanzun maganar auren Ummi da Mukutar nanan”

     Yafi minti 17 zaune amota idan ya saka wancen saiya kwance, zuwa can ya dauki waya ya kira Sadiq”

    “Daga can Sadiq ya dauki waya tare da fadin”

     ” Ranka ya dade, yaya jikin naka?

    “Nace maka banda Lafiya ne?

     “Dariya Sadiq yayi tare da fadin”

     “Ai ka dade da zama majinyaci, sai dai idan kai din baka sani ba”

     “Hmmm Sadiq kai munafuki ne, yazun dai kasan menene?

    Saika fada”

   “Gobe daurin auren Ummi”

  ” Eh ai nasamu Labari gurin Momy, yazun kana gaiyata tane?

”  Hmmm eh, idan kaga dama zaka iya zuwa, amman indan dan nine karkazo, dan nima ba zuwa zanyi ba”

   ” Ok toshi shikenan Allah ya kara ma Lafiya”

   “Katse kiran yayi domin yakira shine ya fadan mai yadda yakeji yau, amman yaga Sadiq nema yake ya mai dashi abin tsokana”

     “Yana sauke wayar ya juya yabar gidan, wani iri yakeji acikin zuciyar shi tamkar ya hadiye zuciya ya mutu saboda tsananin kishin Sadiq dayake ji”

    “Bayan ya isa gida yana kokarin shiga falon yaji muryan Sadiya da Humaira kannan sa ne dake gidan mazajen su suna tsaka da fada akan yadda sukaji Labarin wai Ummi taki Abdulmajeed”

    “Tsayawa yayi ya gama sauraran abinda suke cewa, sannan ya tura kofar tare da Sallama”

   “Tsit sukayi bayan ya shiga palon suka faramai sannu da zuwa,”

    ” Amsawa yayi adakile kamar yadda ya saba, fuskan nan murtuk babu alamar fara’a sannan yace meya kawo ku?

   ” Inda inda suka shiga sai Momy ce tace”

   “Wanne irin meya kawo su ?, bayan gobe daurin auren kawar su”

     “Lumshe ido yayi sannan ya bude tare da Fadin”

    “Ok haka ne na manta ne, cikin sauri ya nufi dakinsa, yauma Abdulmajeed be iya runtsawa ba, koda asubama kasa zuwa masallaci yayi saboda wani irin matanancin sanyi dayake ji”

     “Adakinsa yai dallah bayan ya idar ya sake komawa gado, har kusan 12 na rana yana kwance yanajin yada  aketa hayaniya agidan, zuciyar shi kamar ta fito haka yakejinta, gashi yayi yayi ya runtsa hankan ya gagare shi dan haka idonshi yayi jawur tare da matsanan cin ciwon kai”

    “Yanajin wayar shi na Ringing amman ya kasa dauka, damisalin Karfe 1:00 Momy ta shigo dakin, kamshi turaren Momy yasashi bude ido”

    “Abdulmajeed har yanzun kana kwance?, yau fa ko masallaci bakaje ba”

   ” Eh Momy wallahi banada Lafiya ne sanyi nakeji amman ai nayi adaki”

    ” Allah ya sauwake yanzun ka daure katashi kayi wanka Alhaji na jiranka yace kafarka kafarshi, dan zuwan Sadiq uku gidan nan amman kaki daukan wayar shi”

    “Momy wlh bakin dauka nayiba, bammasan waye ba, kuma dan Allah kiba Alhaji hakuri wani irin sanyi nakeji bazan iya zuwa ba”

    “Kare mashi kallo mama tayi sannan ta juya ta fita”

   ” Batafi minti 5 da fita ba Alhaji ya shigo dakin daidai lokacin da Majeed ya fito daga toilet”

   “Hannu Alhaji ya nuna mishi tare da fadin”

  ” Yaushe nazama abokin wasan ka? Dahar zan gindaya maka duka kaki bi?

    “Durkar dakai yayi cikin yanayin dake nuna yana cikin damuwa yace”

    “Kayi hakuri Daddy wlh banda Lafiya n……

  ” Daga mishi hannu Alhaji yayi tare da fadin”

   “Baka isaba Abdulmajeed, nabaka minti 10 ka sameni amota, koda ace zaka mutu acen ne saika ji dauren auren nan wallahi, ni zaka kawowa iskanci da rashin kunya, koko ni nasata tace bata Sonka, duk kabi ka dami mutane da fadin ran jaraba”

    “Alhaji na fita Majeed ya koma toilet tsintan kanshi yayi da zubar da hawaye sosai wani na korar wani, babu abin dayafi kona mishi rai kamar yaji ance wai Ummi tace bata sonsa, cikin sauri yayi wankan ya fito, shiryawan ma agaugauce yayita dan gudun kar minti 10 da aka diban masa su cika”

     “Cikin gudu gudu ya fita agidan amota ya samu Alhaji kamar yadda yace”

   ” Koda suka dauki hanya babu abin da Abdulmajeed ke saukewa sai ajiyan zuciya me karfin tsiya”

    “Duk sadda ya sauki sai Alhaji ya juyo ya kalleshi, acikin zuciyan shi yake tambayan kanshi wannan wanne irin taurin kaine?, yarasa a inda Abdulmajeed ya debo wannan ahalin na mugun zufin ciki, ko Hajiya tsohowa da take fadin, *Bawan Allah* halina ya kwaso bata taurin kai irin nasa

    “Ahaka suka isa kofar gidan daya cika ya tumbatsa da dan mutum domin alartan daurin auren Ummi da Mukutar”

Mmn Yazeed🔥 🔥🔥🔥🔥🔥

*KOWANNE BAKIN WUTA*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥

    ( da nashi hayakin)

💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by

    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*

    Wattpad @fadeelalamido

                *9 -10*

*WAIWAYE*

Alhaji Sulaiman Habib da Alhaji Sani Habib wa da kani ne, ‘yan asalin jahar Kano Su Uku iyayen su suka haifa, mahaifin su ya dade da rasuwa, mahaifiyar su Zainab ita taita fadi tashi akansu har suka kawo matakin da suke ayanzun”+

  Mahaifin su Alhaji Habib attajiri ne da jahar kano tasan da zaman shi, dan haka ko bayan mutuwar shi basu san wani abu waishi talauci ba, domin yabar musu kaddarori tare da kanfanuni da dama”

    Hajiya zainab bafulata ce, dan haka ‘ya’yanta sulaiman da Sani ita suke yowa,, dan idan ka kalli Alhaji Habib zaka dauka bashine mahaifin su ba, domin shi baki ne gajere, yayin da su suke dogaye kuma farare”

  “Alhaji Sulaiman shine mahaifin Majeed, tare da Matarsa Hajiya Hadiza, ‘ya’ya Shidda  suka haifa, Salma ita ce Babba wadda ayanzun tana  zaune a Madina tare da Mijinta, Abdulmajeed ne yake binta, Sai kannan sa Sadiya da Humaira, suma suna dakin mazajen su a yanzun haka, sai ‘yan biyu Hassana da Hussaina waddda ayanzun suna cikin shekara ta 20”

    Tun tasowan Abdulmajeed mutum neshi wadda Magana bata dameshi ba, idan ya kula wuri yacika hayaniya tashi yake ya kebe kanshi”

    Baya wasa da kannan shi, bare yayi musu dariya, hakan yasa suke matukar shakkan shi, acikin su babu wadda yake hira da ita, inkaji sunyi magana tofa sai dai in aiko su akayi, su fadi sakon ya kuma basu amsa amurtuke”

     Sai dai Allah yayi shi mutum ne mematukar son karatu, baya wasa da karatu kwata kwata, saboda nacin karatu sai ya kwana zaune acewar shi karatu yafi shiga da daddare, sai dai duk randa ya kwana babu bacci yakan tashi da matsanan cin zazzabi, kuma bashi zai hana gobe ya sake ba, daker Momy ta samu ta yakece mai kwana zaune tahanyar nuna mai baccinrai sosai, yana dainawa ko ya samu lfy”

     ” Atunanin iyayen sa babu wani abu da Abdulmajeed yafiso fiye da karatu, sun fahimci hakanne ta hanyar nacin karatu dayake dashi ta fannin boko da islamiyya”

     ” Ta ko ina ba’a barshi abaya ba, wadda hakan yakaishi ga babban nasara, dan bayan ya kammala karatun sa ya fito da sakamako mekyau, inda yasamu nasaran zama babban likita, ya fara aiki da wani babban asibitin gwamnati dake Adamawa, sosai ya karbo, mutane na matukar son shi, soboda yaddda yake da kwarewa akan aikin sa, nan danan Nigeria tasan da Matashin likita, Abdulmajeed Sulaiman Habib”

     Yanayin aiki yasa Majeed sai yayi watanni bezo gida ba, dan haka daddyn shi ya bude masa babban Asibiti anan Kano domin yafison ganin shi akusa kasancewar shika dai ne namiji acikin ‘ya’yan shi”

    Asibitin yasamu karbowa sosai, dan mutane da dama nason Dr Abdulmajeed ya dubasu, duk da haka be fasa ziyarta asubotocin gwamnati dake fadin Nigeria ba, asati yakan zabi Asibiti guda daya domin kai musu ziyara, duk ko Asitin da ‘yan jahar suka samu lbrn zuwan shi, zaka sameshi ne ciki makil da jama’a, dan haka Abdulmajeed ke da farin jinin ‘yan mata, sai dai shi baya kula su, acewar shi, basu bane agaban shi”

   “Itako Ummi wadda taci sunan kakarta Zainab, ita kadai Alhaji Sani da Umma suka Haifa, tun daga kanta basu sake samun haihuwa ba, dan haka Abdulmajeed ne kadai namiji acikin jikokin Alhaji Habib, dan haka Hajiya Zainab ta dauki duk wata kulawa tabawa Abdulmajeed shi kadai, sosai take nuna tafi sonshi acikin jikokinta ko wani abu taci saita rage masa, dan haka suke fada sosai da Ummi dan duk abin da ta taba agidan sai Hajiya tace ajeyeshi na *bawan Allah* ne,

STORY CONTINUES BELOW

    Sosai Ummi take kulewa dan haka kullum cikin mata korafi take, ke komai aka taba agidan ki sai kice na *bawan Allah* ne, toh waye ba bawan Allah ba, mutumin ma da baci zaiyi ba illa yaita yatsuna fuska, yakuma tafi yabar shi”

    “Hajiya Zainab takan ce eh kijira yazo idan yace beci sai kici, amman yanzun kan bazan baki ba”

    “Cikin fushi Ummi ke bari gidan, tare da fadin bazan sake zuwa ba bare ma kimin wulakanci”

     Sosai Ummi kejin haushin yadda kakarsu take ma Abdulmajeed duk da cewa har kannan sa ma sunajin haushi amman na Ummi yafi nasu, musamman sunan da take kiran shi dashi, wai wani *bawan Allah*

    

      *CIGABAN LABARI*

“Tunkafin Abdulmajeed ya sakko daga motar, ya hango gungun abokan Mukhtar, Mukhtar din ya gallawa harara acikin zuciyar shi yace shege muna muki ji inda yake yake hakura wawan banza kawai, tsakin dayaja afili, yasa Alhaji yai saurin juyawa ya kalleshi, Abdulmajeed dabesan me yakeyi ba yanacan yana zubawa Mukutar harara”

    “Bayan Alhaji ya sauka, Abdulmajeed amotan yaci gaba da zama, domin jin shi yake kamar anzare mai laka”

    “Har Sadiq ya shigo motar ya zauna be sani ba, dan haka Sadiq ya dafa shi sannan yace”

    ” *Dr Abdulmajeed* ya kamata ka dinga sarrafa zuciyar ka, menene haka?, kana son yariya ka kasa fitowa ka gaya mata, kana ikirarin kafi karfin kace mata kana son ta, amman gashi cikin dubban mutane ka kasa boye son da kake mata, wlh Abduajeed duk wadda ya kalleka dole ya fahimci kana cikin damuwa, kuma banga dalilin dazaka tada hankalin ka ba, dan bakin alkalami ya riga da ya bushe”

    “Mekake nufi da wannan kalaman naka?, cewan Abdulmajeed adaidai lokacin da jijiyoyin kansa sukayi rudu rudu”

  

     ‘Cigaba yayi da cewa”

    “Angaya maka koda ayau Ummi zata bude baki tace tana sona, wlh baxan aureta ba, yariyar da ta kalli idona tace bata sona, har abada bazan taba furta mata kalmar so ba”

   ” Wani irin munafukar dariya Sadiq yayi sannan yace, indai hakane Abdulmajeed banga dalilin dazaka dame zuciyar ka da tunani ba”

  ” Nifa ba Ummi bace damuwata, hakanan naji inajin haushin Ummi da mukutar fiye da yadda baka tunani, bana son Mukutar natsaneshi arayuwata, wai kamar Ummi ce zata gwammace dan cirani akaina”

 

    “Kafin Sadiq ya bude baki sukaji ana tsaka da daurin auren Ummi da Mukhtar, Abdulmajeed ji yayi kamar anbuga masa katako akai tundaga lokacin besake sanin inda kansa yake ba, lokacin da hankalinsa ya dawo jikin shi gani yayi Sadiq namai fifita, Daddy da Abba suna tsaye akan shi, binsu yayi da kallo daya bayan daya, nan ya tabbatar wa kanshi a asibiti yake”

    ” Yunkurawa yayi ya zauna tare da fadin me muke yi anan?

    ” Hannun shi ya kallah ganin karin ruwa ya tabbatar mishi dacewa bashi da lfy”

     “Mikewa Sadiq yayi ya fita, dan haka Abba ya dawo bakin gadon ya zauna, ahankali yace”

   “Abdulmajeed meyake damun ka?, abin ciken da abokin ka yayi ya tabbatar mana da cewa ciwon Zuciya yana daf da kama ka, kuma ba komai bane ya jawo hakan illah yawan tunani da kake yi, Abdulmajeed mu iyayen ka ne karka boye mana komai”

    “Sunkuyar dakai Majeed yayi sannan yace”

    “Abba babu abin daya yake damuna, ni bana wani tunani”

    “Shiru Abba yayi nawani dan lokaci sannan yace Abdulmajeed kodai kana son Ummi ne”?

     “A’a Abba, ni babu wata damuwa axuciyata”

    “Shiru Abba ya sake yi zuwa can yace”

    “Toh Allah ya baka Lfy Abdulmajeed”

  “Ameen ya fada ahankali”

STORY CONTINUES BELOW

    “Alhaji ko uffan bece ba, saima wani irin kallo dayake. Bin Abdulmajeed dashi”

    “Washegari aka sallame shi ya koma gida, zuciyar shi cike fal da tunanin Ummi, yana son yaji wani labari akan Ummi amman ya rasa wadda zai tambaya”

    “Kasa sukuni yayi, dan haka ya dafe kansa zuwa can tunanin kiran Umma ya fadomai, dan haka ya dauki wayarsa ya kirata”

    “Bugu biyu Umma ta dauka tare da fadin Abdulmajeed ya jikin naka, wlh baki ne suka min yawa naso nazo na dubaka yau”

    “Dan murmushi yayi tare da fadin”

    ” Bakomai Umma aina samu sauki”

   Toh Allah ya kara lfy”

     “Ameen ya fada sannan ya danyi shiru zuwa can ya tsinci kansa da fadin ina Ummi fah?

      “Gaban Hajiya ne yai mummunan faduwa cikin rashin kwarin jiki tace”

     “Majeed Ummi kuma? ai Ummi tana dakin Mijinta ko ka manta ne”

    “Rasa abin cewa yayi dan haka ya katse kiran hawaye yaji yana sakko masa, ya dinga sa hannun sa yana sharewa, ahanli zuciyar sa ta shiga rayamai ga Mukhtar can yana taba jikin Ummi”

     “Wani irin kara ya saki sannan ya miki ya fara fatali da kanyan dakin gaba daya kansa kullewa yayi dan haka ji yake kamar ya miki yaita gudu yana zunduma ihu”

    ” Mikewa yayi ya zari takalmin sa, rabon shi da wanka tun ranan dazai tafi daura auren Ummi yau kwana biyu kanan”

    ” Juyawa yayi ya fita afusace ko sallama bema mutanan dake falon ba, bare ya gaida su”

    “Gaba daya binsa sukayi da kallo har ya kule, Mama ce ta juyo ta kalle kannan sa tace”

     “Kuna ganin Ikon Allah? Anya kuwa kan Abdulmajeed kalau yake?

    “Sadiya ce tace ni madai Mama abin ya fara bani tsoro”

   “Cikin tsanani damuwa Mama tace dan Allah ku dinga mishi addu’a Allah ya yaye masa abinda ke damun sa, shima zan gaya masa ya ringa addu’a, dan da nayi alkawarin bazan sake bin takansaba tunda na fadi abin dake damunsa yace ba haka ba”

    “Gaba dayan su suka taru sukaita bawa Mama hakuri”

    “Shiko Abdulmajeed  wurin aikinsa ya nufa’ yana kokarin shiga ne ya hango wani Mutumi zaune yana shan sigari tunawa yayi ya taba jin wani mutumi yana cewa, idan yana cikin damuwa yasha Sigari sai yaji damuwar sa ta yaye, juyawa yayi ya kwala ma megadi kira, aguje ya taho dan besabajin Ogan su ya bude murya haka ba, 5k ya Ciro ya mika masa sannan yace Sigari zaka sawo min”

     “Iyyee😳 me kace Ranka ya dade?

    “Tafiya Abdulmajeed ya fara tare da fadin aikajini sarai, karka batamin lokaci”

     “Kudin Baba ya kallah sannan ya daga kai ya kalli majeed, cikin rashin kwarin jiki ya juya ya fita, iya sanin shi Oga Abdulmajeed beson warin sigari, ko kadan, kwali 2 ya siyo ya nufi Office din Abdulmajeed Sallama yayi tare da tura kofar”

    “Abdulmajeed ya gani ya kwantar da kansa akan teburen dake gaban sa”

   “Ahankali Baba yace gashi ranka ya dade”

    “Cikin sauri Abdulmajeed ya daga kansa ya karba sannan ya kalli Baba me gadin yace, toh dame zan kunna”

    “Cikin dariricewa baba yasaka hannu aljihu yaciro ashana ya mikawa Abdulmajeed”

    “Yana fita Abdulmajeed ya zaro sigari guda daya ya kunnan, tun yana sha yana tari har yabari, dai dai lokacin daya kunna kara ta 4 Sadiq ya shigo Office din, innalillahi wa inna ilaihir raju’un Abdulmajeed menene haka kuma???, kan ka daya kuwa??

    “Dago jajayen idon shi yayi ya daura akan Sadiq sannan yace”

    “Sadiq nakasa daina tunanin ne, ji nake kamar naita ihu”

    “Subuhanallahi Abdulmajeed me zai hana ka gawa Allah halin da kake ciki, amemakon akajefa kanka cikin hadari, nasan kana da illimi kasan illar da sigari take yi ajikin mutum”

    “Nasani Sadiq nima zansha na wani dan lokaci ne, domin inkawar da tunanin dake yawan damuna, tun kafin auren Ummi nake addu’an Allah ya ciremin tunaninta amman gashi har tana dakin mijinta tunani ya hanani sukuni”

    “Shiyasa ka zabi wannan hanyan ? Abdulmajeed kaifa ba yaro mane”

   “Sadiq kayi hakuri da zaran nabar tunani zan daina sha”

    “Afusace Sadiq ya juya ya fita, ta wani bangaren Abdulmajeed ya bashi tausayi amman beji dadin gannin sa da sigari ba”

   “Majeed ko har yasha kara goma beji ya koma inda yake so ba, dan haka yaita kunna wa babu kyaukyautawa, be fargaba saida ya shanye kwali daya, kan tabur ya ajiye kwali sannan ya dauko dayan ya zari daya ya kunna”

     “Dai dai lokacin Sadiq ya sake shigowa, sosai Office din ya tuki da wari dan haka Sadiq ya to she hancin sa, tare da fadin”

    “Wai menene hakane Abdulmajeed, kana son ka zama mashayi ne??, waye ya gaya maka haka ake shan sigari? guntayen sigarin ya kallah sannan ya kalli kwalin daya kare yace”

    “Majeed Acikin awan dabifi daya ba kashanye kwalin sigari, wai kai wanne irin zuciya ne dakai? gaskiya kayiwa kanka fada, So hauka ne?

    “Kaga Sadiq ka rabu dani, ni kadai nasan abin dake damuna, ka fita ka bani guri”

     “Bazan fitaba, wawa kawai mara tunani Sadiq ke fadin haka lokacin dayake kokarin zuwa gurin window, bubudewa yayi tare da daga labule yana cigaba da fadin duk ka hada Office da wari, ko kunyan mutane bakaji, akan macen da batasan kanayi ba kana nema ka zama zararre”

     “Tattara kuntun sigarin yayi ya watsa abula sannan ya dauki kwalayen ya zuba aljihu”

    “Hade fuska Abdulmajeed yayi tare da fadin”

    “Wlh Sadiq ka kiyayeni ina ruwanka dani, dallah malam ka bani abuna kudin ka ko nawa?

    Wlh bazan bayar ba, kuma duk abin da zaka fada bazanji haushi ba”

    Girgiza kai Abdulmajeed sannan yace, dakasan abin da nakeji da bakazo kusa dani ba, inacin damuwa Sadiq narasa inda zan saka kaina naji dadi, Sadiq bazan jura ganin Ummi tare da waniba, inajin zafi idan na tuna tana gidan waccen dan ciranin, mikewa yayi ya kamo hannun Sadiq yasa akirjin shi tare da fadin”

     Sadiq taba kaji abin da zuciyata take min, wlh idan har zan cigaba da ganin Ummi tare da wannan gantalallen zuciyata zata BUGU…..

   *Mmn Yazeed*🔥 🔥🔥🔥🔥🔥

*KOWANNE BAKIN WUTA*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥

    ( da nashi hayakin)

💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by

    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*

    Wattpad @fadeelalamido

                *9 -10*

*WAIWAYE*

Alhaji Sulaiman Habib da Alhaji Sani Habib wa da kani ne, ‘yan asalin jahar Kano Su Uku iyayen su suka haifa, mahaifin su ya dade da rasuwa, mahaifiyar su Zainab ita taita fadi tashi akansu har suka kawo matakin da suke ayanzun”+

  Mahaifin su Alhaji Habib attajiri ne da jahar kano tasan da zaman shi, dan haka ko bayan mutuwar shi basu san wani abu waishi talauci ba, domin yabar musu kaddarori tare da kanfanuni da dama”

    Hajiya zainab bafulata ce, dan haka ‘ya’yanta sulaiman da Sani ita suke yowa,, dan idan ka kalli Alhaji Habib zaka dauka bashine mahaifin su ba, domin shi baki ne gajere, yayin da su suke dogaye kuma farare”

  “Alhaji Sulaiman shine mahaifin Majeed, tare da Matarsa Hajiya Hadiza, ‘ya’ya Shidda  suka haifa, Salma ita ce Babba wadda ayanzun tana  zaune a Madina tare da Mijinta, Abdulmajeed ne yake binta, Sai kannan sa Sadiya da Humaira, suma suna dakin mazajen su a yanzun haka, sai ‘yan biyu Hassana da Hussaina waddda ayanzun suna cikin shekara ta 20”

    Tun tasowan Abdulmajeed mutum neshi wadda Magana bata dameshi ba, idan ya kula wuri yacika hayaniya tashi yake ya kebe kanshi”

    Baya wasa da kannan shi, bare yayi musu dariya, hakan yasa suke matukar shakkan shi, acikin su babu wadda yake hira da ita, inkaji sunyi magana tofa sai dai in aiko su akayi, su fadi sakon ya kuma basu amsa amurtuke”

     Sai dai Allah yayi shi mutum ne mematukar son karatu, baya wasa da karatu kwata kwata, saboda nacin karatu sai ya kwana zaune acewar shi karatu yafi shiga da daddare, sai dai duk randa ya kwana babu bacci yakan tashi da matsanan cin zazzabi, kuma bashi zai hana gobe ya sake ba, daker Momy ta samu ta yakece mai kwana zaune tahanyar nuna mai baccinrai sosai, yana dainawa ko ya samu lfy”

     ” Atunanin iyayen sa babu wani abu da Abdulmajeed yafiso fiye da karatu, sun fahimci hakanne ta hanyar nacin karatu dayake dashi ta fannin boko da islamiyya”

     ” Ta ko ina ba’a barshi abaya ba, wadda hakan yakaishi ga babban nasara, dan bayan ya kammala karatun sa ya fito da sakamako mekyau, inda yasamu nasaran zama babban likita, ya fara aiki da wani babban asibitin gwamnati dake Adamawa, sosai ya karbo, mutane na matukar son shi, soboda yaddda yake da kwarewa akan aikin sa, nan danan Nigeria tasan da Matashin likita, Abdulmajeed Sulaiman Habib”

     Yanayin aiki yasa Majeed sai yayi watanni bezo gida ba, dan haka daddyn shi ya bude masa babban Asibiti anan Kano domin yafison ganin shi akusa kasancewar shika dai ne namiji acikin ‘ya’yan shi”

    Asibitin yasamu karbowa sosai, dan mutane da dama nason Dr Abdulmajeed ya dubasu, duk da haka be fasa ziyarta asubotocin gwamnati dake fadin Nigeria ba, asati yakan zabi Asibiti guda daya domin kai musu ziyara, duk ko Asitin da ‘yan jahar suka samu lbrn zuwan shi, zaka sameshi ne ciki makil da jama’a, dan haka Abdulmajeed ke da farin jinin ‘yan mata, sai dai shi baya kula su, acewar shi, basu bane agaban shi”

   “Itako Ummi wadda taci sunan kakarta Zainab, ita kadai Alhaji Sani da Umma suka Haifa, tun daga kanta basu sake samun haihuwa ba, dan haka Abdulmajeed ne kadai namiji acikin jikokin Alhaji Habib, dan haka Hajiya Zainab ta dauki duk wata kulawa tabawa Abdulmajeed shi kadai, sosai take nuna tafi sonshi acikin jikokinta ko wani abu taci saita rage masa, dan haka suke fada sosai da Ummi dan duk abin da ta taba agidan sai Hajiya tace ajeyeshi na *bawan Allah* ne,

STORY CONTINUES BELOW

    Sosai Ummi take kulewa dan haka kullum cikin mata korafi take, ke komai aka taba agidan ki sai kice na *bawan Allah* ne, toh waye ba bawan Allah ba, mutumin ma da baci zaiyi ba illa yaita yatsuna fuska, yakuma tafi yabar shi”

    “Hajiya Zainab takan ce eh kijira yazo idan yace beci sai kici, amman yanzun kan bazan baki ba”

    “Cikin fushi Ummi ke bari gidan, tare da fadin bazan sake zuwa ba bare ma kimin wulakanci”

     Sosai Ummi kejin haushin yadda kakarsu take ma Abdulmajeed duk da cewa har kannan sa ma sunajin haushi amman na Ummi yafi nasu, musamman sunan da take kiran shi dashi, wai wani *bawan Allah*

    

      *CIGABAN LABARI*

“Tunkafin Abdulmajeed ya sakko daga motar, ya hango gungun abokan Mukhtar, Mukhtar din ya gallawa harara acikin zuciyar shi yace shege muna muki ji inda yake yake hakura wawan banza kawai, tsakin dayaja afili, yasa Alhaji yai saurin juyawa ya kalleshi, Abdulmajeed dabesan me yakeyi ba yanacan yana zubawa Mukutar harara”

    “Bayan Alhaji ya sauka, Abdulmajeed amotan yaci gaba da zama, domin jin shi yake kamar anzare mai laka”

    “Har Sadiq ya shigo motar ya zauna be sani ba, dan haka Sadiq ya dafa shi sannan yace”

    ” *Dr Abdulmajeed* ya kamata ka dinga sarrafa zuciyar ka, menene haka?, kana son yariya ka kasa fitowa ka gaya mata, kana ikirarin kafi karfin kace mata kana son ta, amman gashi cikin dubban mutane ka kasa boye son da kake mata, wlh Abduajeed duk wadda ya kalleka dole ya fahimci kana cikin damuwa, kuma banga dalilin dazaka tada hankalin ka ba, dan bakin alkalami ya riga da ya bushe”

    “Mekake nufi da wannan kalaman naka?, cewan Abdulmajeed adaidai lokacin da jijiyoyin kansa sukayi rudu rudu”

  

     ‘Cigaba yayi da cewa”

    “Angaya maka koda ayau Ummi zata bude baki tace tana sona, wlh baxan aureta ba, yariyar da ta kalli idona tace bata sona, har abada bazan taba furta mata kalmar so ba”

   ” Wani irin munafukar dariya Sadiq yayi sannan yace, indai hakane Abdulmajeed banga dalilin dazaka dame zuciyar ka da tunani ba”

  ” Nifa ba Ummi bace damuwata, hakanan naji inajin haushin Ummi da mukutar fiye da yadda baka tunani, bana son Mukutar natsaneshi arayuwata, wai kamar Ummi ce zata gwammace dan cirani akaina”

 

    “Kafin Sadiq ya bude baki sukaji ana tsaka da daurin auren Ummi da Mukhtar, Abdulmajeed ji yayi kamar anbuga masa katako akai tundaga lokacin besake sanin inda kansa yake ba, lokacin da hankalinsa ya dawo jikin shi gani yayi Sadiq namai fifita, Daddy da Abba suna tsaye akan shi, binsu yayi da kallo daya bayan daya, nan ya tabbatar wa kanshi a asibiti yake”

    ” Yunkurawa yayi ya zauna tare da fadin me muke yi anan?

    ” Hannun shi ya kallah ganin karin ruwa ya tabbatar mishi dacewa bashi da lfy”

     “Mikewa Sadiq yayi ya fita, dan haka Abba ya dawo bakin gadon ya zauna, ahankali yace”

   “Abdulmajeed meyake damun ka?, abin ciken da abokin ka yayi ya tabbatar mana da cewa ciwon Zuciya yana daf da kama ka, kuma ba komai bane ya jawo hakan illah yawan tunani da kake yi, Abdulmajeed mu iyayen ka ne karka boye mana komai”

    “Sunkuyar dakai Majeed yayi sannan yace”

    “Abba babu abin daya yake damuna, ni bana wani tunani”

    “Shiru Abba yayi nawani dan lokaci sannan yace Abdulmajeed kodai kana son Ummi ne”?

     “A’a Abba, ni babu wata damuwa axuciyata”

    “Shiru Abba ya sake yi zuwa can yace”

    “Toh Allah ya baka Lfy Abdulmajeed”

  “Ameen ya fada ahankali”

STORY CONTINUES BELOW

    “Alhaji ko uffan bece ba, saima wani irin kallo dayake. Bin Abdulmajeed dashi”

    “Washegari aka sallame shi ya koma gida, zuciyar shi cike fal da tunanin Ummi, yana son yaji wani labari akan Ummi amman ya rasa wadda zai tambaya”

    “Kasa sukuni yayi, dan haka ya dafe kansa zuwa can tunanin kiran Umma ya fadomai, dan haka ya dauki wayarsa ya kirata”

    “Bugu biyu Umma ta dauka tare da fadin Abdulmajeed ya jikin naka, wlh baki ne suka min yawa naso nazo na dubaka yau”

    “Dan murmushi yayi tare da fadin”

    ” Bakomai Umma aina samu sauki”

   Toh Allah ya kara lfy”

     “Ameen ya fada sannan ya danyi shiru zuwa can ya tsinci kansa da fadin ina Ummi fah?

      “Gaban Hajiya ne yai mummunan faduwa cikin rashin kwarin jiki tace”

     “Majeed Ummi kuma? ai Ummi tana dakin Mijinta ko ka manta ne”

    “Rasa abin cewa yayi dan haka ya katse kiran hawaye yaji yana sakko masa, ya dinga sa hannun sa yana sharewa, ahanli zuciyar sa ta shiga rayamai ga Mukhtar can yana taba jikin Ummi”

     “Wani irin kara ya saki sannan ya miki ya fara fatali da kanyan dakin gaba daya kansa kullewa yayi dan haka ji yake kamar ya miki yaita gudu yana zunduma ihu”

    ” Mikewa yayi ya zari takalmin sa, rabon shi da wanka tun ranan dazai tafi daura auren Ummi yau kwana biyu kanan”

    ” Juyawa yayi ya fita afusace ko sallama bema mutanan dake falon ba, bare ya gaida su”

    “Gaba daya binsa sukayi da kallo har ya kule, Mama ce ta juyo ta kalle kannan sa tace”

     “Kuna ganin Ikon Allah? Anya kuwa kan Abdulmajeed kalau yake?

    “Sadiya ce tace ni madai Mama abin ya fara bani tsoro”

   “Cikin tsanani damuwa Mama tace dan Allah ku dinga mishi addu’a Allah ya yaye masa abinda ke damun sa, shima zan gaya masa ya ringa addu’a, dan da nayi alkawarin bazan sake bin takansaba tunda na fadi abin dake damunsa yace ba haka ba”

    “Gaba dayan su suka taru sukaita bawa Mama hakuri”

    “Shiko Abdulmajeed  wurin aikinsa ya nufa’ yana kokarin shiga ne ya hango wani Mutumi zaune yana shan sigari tunawa yayi ya taba jin wani mutumi yana cewa, idan yana cikin damuwa yasha Sigari sai yaji damuwar sa ta yaye, juyawa yayi ya kwala ma megadi kira, aguje ya taho dan besabajin Ogan su ya bude murya haka ba, 5k ya Ciro ya mika masa sannan yace Sigari zaka sawo min”

     “Iyyee😳 me kace Ranka ya dade?

    “Tafiya Abdulmajeed ya fara tare da fadin aikajini sarai, karka batamin lokaci”

     “Kudin Baba ya kallah sannan ya daga kai ya kalli majeed, cikin rashin kwarin jiki ya juya ya fita, iya sanin shi Oga Abdulmajeed beson warin sigari, ko kadan, kwali 2 ya siyo ya nufi Office din Abdulmajeed Sallama yayi tare da tura kofar”

    “Abdulmajeed ya gani ya kwantar da kansa akan teburen dake gaban sa”

   “Ahankali Baba yace gashi ranka ya dade”

    “Cikin sauri Abdulmajeed ya daga kansa ya karba sannan ya kalli Baba me gadin yace, toh dame zan kunna”

    “Cikin dariricewa baba yasaka hannu aljihu yaciro ashana ya mikawa Abdulmajeed”

    “Yana fita Abdulmajeed ya zaro sigari guda daya ya kunnan, tun yana sha yana tari har yabari, dai dai lokacin daya kunna kara ta 4 Sadiq ya shigo Office din, innalillahi wa inna ilaihir raju’un Abdulmajeed menene haka kuma???, kan ka daya kuwa??

    “Dago jajayen idon shi yayi ya daura akan Sadiq sannan yace”

    “Sadiq nakasa daina tunanin ne, ji nake kamar naita ihu”

    “Subuhanallahi Abdulmajeed me zai hana ka gawa Allah halin da kake ciki, amemakon akajefa kanka cikin hadari, nasan kana da illimi kasan illar da sigari take yi ajikin mutum”

    “Nasani Sadiq nima zansha na wani dan lokaci ne, domin inkawar da tunanin dake yawan damuna, tun kafin auren Ummi nake addu’an Allah ya ciremin tunaninta amman gashi har tana dakin mijinta tunani ya hanani sukuni”

    “Shiyasa ka zabi wannan hanyan ? Abdulmajeed kaifa ba yaro mane”

   “Sadiq kayi hakuri da zaran nabar tunani zan daina sha”

    “Afusace Sadiq ya juya ya fita, ta wani bangaren Abdulmajeed ya bashi tausayi amman beji dadin gannin sa da sigari ba”

   “Majeed ko har yasha kara goma beji ya koma inda yake so ba, dan haka yaita kunna wa babu kyaukyautawa, be fargaba saida ya shanye kwali daya, kan tabur ya ajiye kwali sannan ya dauko dayan ya zari daya ya kunna”

     “Dai dai lokacin Sadiq ya sake shigowa, sosai Office din ya tuki da wari dan haka Sadiq ya to she hancin sa, tare da fadin”

    “Wai menene hakane Abdulmajeed, kana son ka zama mashayi ne??, waye ya gaya maka haka ake shan sigari? guntayen sigarin ya kallah sannan ya kalli kwalin daya kare yace”

    “Majeed Acikin awan dabifi daya ba kashanye kwalin sigari, wai kai wanne irin zuciya ne dakai? gaskiya kayiwa kanka fada, So hauka ne?

    “Kaga Sadiq ka rabu dani, ni kadai nasan abin dake damuna, ka fita ka bani guri”

     “Bazan fitaba, wawa kawai mara tunani Sadiq ke fadin haka lokacin dayake kokarin zuwa gurin window, bubudewa yayi tare da daga labule yana cigaba da fadin duk ka hada Office da wari, ko kunyan mutane bakaji, akan macen da batasan kanayi ba kana nema ka zama zararre”

     “Tattara kuntun sigarin yayi ya watsa abula sannan ya dauki kwalayen ya zuba aljihu”

    “Hade fuska Abdulmajeed yayi tare da fadin”

    “Wlh Sadiq ka kiyayeni ina ruwanka dani, dallah malam ka bani abuna kudin ka ko nawa?

    Wlh bazan bayar ba, kuma duk abin da zaka fada bazanji haushi ba”

    Girgiza kai Abdulmajeed sannan yace, dakasan abin da nakeji da bakazo kusa dani ba, inacin damuwa Sadiq narasa inda zan saka kaina naji dadi, Sadiq bazan jura ganin Ummi tare da waniba, inajin zafi idan na tuna tana gidan waccen dan ciranin, mikewa yayi ya kamo hannun Sadiq yasa akirjin shi tare da fadin”

     Sadiq taba kaji abin da zuciyata take min, wlh idan har zan cigaba da ganin Ummi tare da wannan gantalallen zuciyata zata BUGU…..

   *Mmn Yazeed*🔥 🔥🔥🔥🔥🔥

*KOWANNE BAKIN WUTA*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥

    ( da nashi hayakin)

💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by

    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*

+

    Wattpad @fadeelalamido

         11 – 12

Itako Ummi tunda ta tare agidan Mukutar yake tarairayanta, cikin kwana biyun nan Ummi taga soyayya agurin Mukhtar wadda batai tunanin samun sa ba”

      “Yaso ya kusanceta tun adaren farko da aka kawota gidan sa amman tunda ya kula tanajin tsoro yabarta”

     “Manne da juna suke kwaciya bayan sunci wasan su sungaji”

    “Tunda mukhtar ya fahimci Ummi mutunce ita mason wasa ya biye mata suke lalacewa gurin wasanni da guje guje kamar wasu kananan yara”

    “Yauma kamar kullum bayan sun gama breakfast Mukutar ya kalli Ummi yace”

     “Kin koshi kuwa?

      “Nakoshi mana, kai baka koshi bane?

   ” Shagwabe fuska yayi sannan yace”

    ” Nakushi amman bakina be koshiba”

     “Mikewa tayi tsam ta zagaya ta bayanshi, ta sagalo hannunta wuyan shi, sannan tasa bakinta saitin kunnen shi ta make murya kamar me rada tace”

     “Yanzun yaya za’ayi??

    “Kunneta ya jawo shima ya make tasa muryan yace”

   ” Muje gado muyi wasa sai mu mufito na kara”

    “Matsawa tayi da sauri tare da make kafada, wai kai baka gajiya na wasan agado?

    “Yafi dadi Ummi”

   “Kara make kafada tayi ni dai banso”

   “Mikewa yayi ya jawota jikinshi yace toke fada wadda kike so?

   ” ‘Yar tsere zamu yi”

   ” Hancinta yaja tare da fadin me wayo”

     “Yana rike da hannuta suka isa filin da aka tanadar domin motsa jiki”

  “Yar tsere  suka shiga yi, sai dai  duk Mukhtar ne keyin na farko, dan haka Ummi ta hade fuska kamar zatai kuka”

   “Shiko Mukhtar yanata kwasan dariya tare dayi mata gwalo”

    “Tun tana dagewa ita adole saita wuceshi har tagaji tace, Bana yi”

    “Dariya sosai Mukutar yayi, ganin inda ta bata rai sai kunbura take”

   ” Bayan ya tsagaita da dariyar yace”

    “Sweetheart yi hakuri ki sake gwadawa,  wannan karon kila ki dace, danna fara jin yinwa”

   “Jin yace haka, yasa ta yadda aka kara, aguje suka kwasa, wannan karon Mukutar ahankali yayi dan haka Ummi ta wuce shi, shiko kafin ya kasara ya fadi, yana fadin”

    “Wash, nagaji Ummi, wash kafana, wayyo cikina sweetheart  yiwa nakeji”

   ” Dariya Ummi tai tamai zuwa can tafara mai gwalo tare da fadin”

    Nafishi jarunta”

  “Shima Mukutar dariya ne fal cikin shi, cikin nuna jarunta Ummi ta tallabo shi, suka nufi palon su, yana cigaba da fadin wayyo Ummi cikina kafafuwana sun rike”

STORY CONTINUES BELOW

   “Har suka isa falon dariya Ummi keyi, bayan ta zuba mishi abincin yaci kadan yasake cewa”

    “Nidai har yanzun bakina be koshiba”

“Lankwasa kai tayi, gaskiya ka barshi haka, da dare zan tafama wadda yafishi dadi”

    ” Ok toh muje mu kwanta muyi bacci”

   ” Suna makale da juna suka shiga daki, sai da sukaci wasansu sannan wani nannauyan bacci ya dauke su”

    “Haka suka cigaba da rayuwa cikin tsananin farin ciki da kwanciyar hankali, har suka kwashe sati 2 Mukutar be kusanci Ummi ba, acewarsa sai ranan da ta saki jiki ta daina jin tsoro”

     ” Ranan data cika sati Uku ne hakurinsa ya gaza , domin Ummi takaishi kololuwa da wassannin ta dan haka adaren ranan ya maida ummi cikakkiyar mace”

    ” Duka, daya kushi babu wadda mukhtar beshashi ba, dan haka yau Ummi ta tashi tana fushi dashi”

   “Da kanshi ya hada musu breakfast Har Mukhtar ya gama danasa Ummi na kunbure kunbure, shiko daya kalleta sai dai yai murmushi domin jinsa yake babu wadda yakaisa sa’ar mace aduniya”

     “Mikewa yayi ya daukota cak ya daura acinyan shi, cikin son ganin kwayan idonta yace”

     “Kina fushi da mijinki Ummi dan ya karbi hakkin sa??, kuma ahaka kike ikkirarin kina sona?, auren soyayya mukayi fah ba auren kiyayyaba?

     “Cikin shagwa tare da rufe fuskanta tace”

    “Bakai bane kamin da zafi”

    ” Tallabo fuskanta yayi tare da fadin bazan kara miki da zafiba Sweetheart, amman kema ki daina gaddama kinji?

    “Kaita daga ahankali, cikin murmushi ya shiga ciyar da ita abaki harta koshi, sannan yace toh tashi muje ki kwata sai nayi miki tausa”

    “Kwaciya Ummi tayi agado Mukutar yaita matsa mata duk wani gaba ta jikinta”

     “Ummi ko fakan idon Mukutar take tana kare mishi kallo, tare da godewa Allah daya tabbatar da Mukutar ya zama miji agareta, Abdulmajeed ne ya fado mata arai, Allah na gode maka dakasa Abdulmajeed bezama miji agareni ba, Abdulmajeed wanne soyayya zai iya inban da zaman kunci da takaici”

     “Da wannan tunanin bacci ya dauketa, sai da Mukhtar ya tabbatar tai bacci sannan ya dawo gabanta ya zauna”

    ” Sunbatan goshinta yayi sannan yace acikin zuciyar shi”

   ” Allah ka dawwamar da rayuwar mu cikin farin ciki da kwanciyar hankali,   ka kumasa Ummi tasoni bayan ta fahimci wanene ni”

    Shiko Abdulmajeed bayan fitan Sadiq mikewa yayi yabar Office din gaba daya”

    Gidan kakarsa ya nufa yana mesa ran idan yaje yaganta wata kila yaji dadi”

   “Jikin shi sanyi kalau ya nufa gidan, bayan ya isa ya sakko ya shiga gidan tare da kara takura fuskan shi, sannan yayi sallama ahankali”

   Tsohowar kakar tashi ta amsa fuskanta dauke da fara take fadin”

    A’a idon ka kenan?, yau rabonka da gidan nan kwana nawa?, idan ban manta ba tun kan asa ranar auren Ummi”

    “Jin Hajiya ta ambaci Ummi Abdulmajeed yaji kamar ansoka masa kibiya azuciya dan haka ya kara bata fuska”

    “Gefenta ya zauna yana huce, cikin rashin fahimta Hajiya tace”

    “Bayan Allah yadai?, naganka wani sukuku, wani ne ya bata maka raine?

    “Kanshi ya Sosa, sannan ya dan shafa gemunsa tare da fadin”

STORY CONTINUES BELOW

   “Hajiya nagaji da duniyar nan wai gani nake tamkar rayuta bata da amfani”

    “Kul, Bawan Allah karka sake furta irin wannan kalma, gayamin menene matsalan ka”

     “Kauda fuskan shi yayi sannan yace”

    “Hajiya nima basan meke damuna ba, zuciyanta kullum cikin tunani take, bana iyayin minti 2 batare da nayi zurfi cikin tunani ba, Hajiya ki taimake ni, wlh ina cikin tashin hankali”

      “Binshi da ido Hajiya tayi, kwala tagani kwance acikin idon shi, dan haka ta jawoshi jikinta cikin nuna tsananin tausayi tace”

     “Kai natsu ka gayamin meye yake damun ka, karka yadda ka jefa zuciyan ka cikin wasiwasi dole akwai abin da yake damun ka, karka boyemin komai”

    “Rufe idanun shi yayi sannan yace”

    “Hajiya haushin Ummi nake ji”

    “Cikin mamaki ta zuba mishi ido zuwa can tace”

  Abdulmajeed tamaka wani abune?

    “Tashi yayi ya zauna ya zubawa Hajiya runannun idanun shi dasuka cika da kwallah sannan yace”

    “Hajiya agabana fah tace bata sona, bazata aureni ba, ko kunyar idona batajiba”

   “Mamaki ne ya kara kama Hajiya, saidai har yanzun tarasa inda maganarsa ta dusa dan haka tace”

     Abdulmajeed ai inace Ummi taimakon ka tayi, tunda kaima ai basonta kakeba, kuma ka kasa fada, dan Ummi ta fada ni banga laifinta ba, itafa bawai kinka take ba, tasan kai dan uwanta ne najini dole tasoka tana nufin batama so irin na aure, dan haka ka daina zarginta”

    Cikin fada yace ai koma wanne irin sone bekamata ba, ta gwammace ta aura dan cirani akaina, soboda ta tsaneni, agaban idona tacewa daddy bata sona”

    Kallon shi kawai Hajiya take cikin tausayawa zuwa yanzun ta fara dagoshi, dan haka taji hankalinta ya tashi cikin hikima tace”

    Bawan Allah kayi kuskure babba, meyasa baka gayamin ba, da bazan taba yadda ta auri waniba, gida be kushi ba ai baza’abaiwa dawa ba, amman Bakomai Allah ya baka wadda ta fita”

   Tsaki yaja tare da fadin”

   “Hajiya ki gayamata bani bata har abada, nima bana sonta kamar yadda take bata sona”

    “Bazai yiwuba Abdulmajeed, kaida Ummi ‘yan uwane yazama dole kuyi zumunci”

    Mikewa yayi yana fadin wlh hajiya ba zanyi zumunci da Ummi ba, kuma harna koma ga mahalilcina bazan daina tuna kalmar da ta furta  agareni ba”

    Kaga, bawan Allah kayi hakuri mana, ban sanka da wannan halin ba”

   “Cikin sauri ya juya ya fita duk da kiran da hajiya take zunduma mai be waiwayeta ba”

    “Figan motarshi yayi yabar gidan, itako Hajiya tagumi tayi tare da mamakin yaya akayi bata taba lura bawan Allah son Ummi yake ba?

   ” Neman mafita ta fara, daga can tace yazama dole aneman masa mata yayi aure, wata kila radadin dayakeji zaiyi sauki”

    “Har yamma babu tunanin da Hajiya take saina Abdulmajeed bata son taganshi cikin damuwa”

      Shima Abdulmajeed haka ya koma gida zuciyar shi na tafarfasa, ji yayi tamkar sigarin daya sha bata masa amfani ba, juyi yaitayi agado har aka kira sallan mangariba, daker ya iya tashi ya nufi masallaci, bayan an ida sallah ya nufo gida”

       Ko tsakiyar dare bebar tunanin Ummi ba, gani yake kamar a idon shi Mukutar ke yamutsa Ummi, tunanin daya aure shi kenan tun bayan auren Ummi, daya tunata toh zai gantane tare da Mukhtar suna tsaka da faranta ran junan su dan haka hankalin sa ke matukar tashi”

STORY CONTINUES BELOW

    Yauma kamar kullum Abdulmajeed ya tashi da cewan kai, sai dai yaki yadda ya kwanta, dauriwa yayi ya shirya yabar gidan”

    Duk halin daya ke ciki Momy da Abba suna sane dashi, sai dai sun dauki alkawarin bazasu sake tambayar shiba, tunda bakin alkalami ya riga ya bushe, acewar su idan yagama fushin ya dawo hanya”

    “Ummi dai tana gidan mijinta batamasan yanayi ba, idan zurfin ciki yayi masa rana gobe ma ya kara”

    Itama Umma mahaifiyar Ummi ayanzun ta fara fahimtan Abdulmajeed son Ummi yake, dan tunda ya suma ranan daurin aurenta aka wuce tashi Asibiti besake zuwa gidan ba, sabanin da kullum ya tashi aiki gidan yake fara zuwa”

   ” Abba ma ya gama fahimtan Abdulmajeed dan haka yake tsananin jin tausayin sa, inda anbi shawaran shi da bazai tabawa Mukutar auren Ummi ba”

      *******

“Ranan da Ummi ta cike sati 6 agidan Mukutar ta matsamai ya kaita gida taga Umman ta”

    Cikin lallashi yace kibari bayau ba, duka2 yau kwanan ki nawa?

    “Hawaye ta matso sannan tace kwana na 52, wlh na dade, nidai ka taimakeni inje inga Umma kona minti 5 ne”

    “Yadda take shagwaba ta narnarke masa ajiki yasashi ya kasa hanawa, cikin lumshe ido yace toh jiki ki shirya amman fah kafar ki kafata”

    “Cikin murna ta nufi dakinta tana fadin, eh na yadda”

   ” Ajiyan zuciya Mukutar yayi bayan yaga kulewar Ummi, tare da wani irin mugun sonta da yakeji acikin jinin shi, waddda yake jin tamkar idan babu Ummi bazai iya rayuwa ba”

      “Cikin kankanin lokaci Ummi ta fito cikin shirin tafiya, Mukutar nasauke ido akan Ummi shi yaji hankalin sa ya tashi”

     ” Dan haka ya mike ya isa gareta dare da fadin Baby mukoma daki”

    Cikin shagwaba tace a’a kabari muje mudawo mana”

     “Shima make kafada yayi tare da cewa wannan kwaliyar taki bata fita bace”

     “Ganin Ummi tayi raurau da ido alamar kuka, yasa Mukutar ya hadiye kwadayin shi tare da cewa shikenan muje”

    “Mukutar kejan motar Ummi zaune agefen sa, saidai hannun su na sarke dana juna har suka isa gidan Abba”

      “Mukutar ne ya fara sauka sannan ya zagaya ya bude mata, tare da gyara mata dan karamin mayafin dayake sagale ajikinta, yadda ya shige mata tamkar zai dauketa”

    “Acikin wannan halin sukayi sallama abakin falon, zame jikinta tayi daga na Mukutar ta shigo yana biye da bayanta”

    “Palon wayam babu kowa, juyawa Ummi tayi ta kalli Mukutar sannan tace”

     Zauna barin kira Ummi, cikin dakin Umma ta nufa tana kwalawa Umma kira”

   “Umma dake toilet tana wanka taji muryan Ummi, wani irin farin cikine ya ziyarci zuciyarta”

   “Nan dan ta karasa wankan ta fito, tana fadin Oyoyo ‘yar gudaliyata”

    Da gudu Ummi ta fada jikin Umma suka rungume juna, zuwa can Ummi ta dagota ta gurita da ido, tabbas Mukutar ya iya kiyo ganin yadda Ummi tayi wani bulbul kamar ka latsa jini ya fito abin ya faranta ran Umma”

   “Cikin fara suka gaisa sannan Umma tace ya Mukutar din?

   “Umma ai muna tare yana Palo”

    “Shine kika barsa shi kadai maza kije gurin shi barin insa kaya”

   “Juyawa Ummi tayi, Umma tabi bayan ta da kallon fuskanta dauke da murmushi”

    “Ummi na komawa ta zauna dafda Mukutar tare da fadin gatanan zuwa”

STORY CONTINUES BELOW

    Kara shigewa jikinta yayi sannan yasa bakinshi acikin kunneta bansan me yake gaya mataba saidai gani nayi Ummi na kara shigewa jikinshi tare da lumshe idanunta”

     Daidai wannan lokaci Umma ta shigo ganin su haka yasa tai saurin juyawa ta koma daki”

  Sosai ran Umma ya baci bakin gado ta zauna jikinta asanyaye”

    “Dai dai lukacin Ummi ta shigo sumi sumi domin sunga juyawan Umma, zama tayi kusa da Umma tana me wasa da ya tsunta”

    Cike da haushi Umma ta kalleta itama dagowa tayi suka hada ido da cikin sauri ta maida kanta kasa sannan tace”

      “Umma kizo muje ku gaisa”

    Kun gama rashin kunyan ne??

    “Kara sunkuyar da kanta kasa tayi domin bata da bakin bama Umma amsa”

  Wannan shi kike kira soyayya?, Umma ta sake wurga mata wannan tambayan sannan tacigaba da cewa”

    Toh ki shiga hankalin ki, kisan me kikeyi, kunya adoce agun mace, yanzun idan gidan iyayen shi kukaje abin da zakuyi kenan?, wannan ita kike kira wayewa?, ashe shiyasa ki kaki Abdulmajeed sabo dashi yana da kunya, be iya fitsaraba”

     “Kan Ummi akasa tace Umma toh kiyi hakuri, bazan sake ba”

    “Ni ba laifi ki kamin ba, ai mijinki ne, amman ina tunatar take wannan ba al,adanmu bace, koma menene ku dinga bari sai kuna cikin gidan ku”

    “Sosai kunya ta kama Ummi dan haka ta kasa cewa komai illa wasa da take da hannunta, zuwa can Umma tace”

    “Baki tambayi Abdulmajeed ba?, kuma ranan bikin ki kinsa beda Lafiya amman bakiyo waye kice ya jikinshi ba”

    Gyara murya tayi sannan tace”

    “Aini Umma ban sake tunawa dashi ba ma”

   Cikin ido Umma ta kalleta tare da fadin”

   Iyeee lallai, dan uwan naki ya shiga wani hali amman kice kin manta?

   Toh ni Umma ina ruwana dashi?, amman toh zan kira daddy mugaisa”

   Yatsun baki Umma tayi sannan tace”

   Har yanzun dai Ummi baki da hankali, Abdulmajeed fah har yanzun bashi da Lafiya, duk abin da yake karfin hali yake yi, kamata yayi daga nan ku wuce ku dubashi”

    Zaro ido Ummi tayi domin bata so haduwa da Abdulmajeed nan kusaba, dan haka tace”

   Umma wallahi ni tsoron sa nakeji”

    Wanne irin tsoro sai kace wani dodo, be kamata ace kinkai har yanzun ma bakije kin doboshi ba, shiru Umma tayi sannan tace”

   Ummi ni sai nake ga kamar Abdulmajeed sonke yake”

  Gabanta taji ya fadi, da sauri ta dago ta kalli Umma sannan tace”

   Meyasa kikace haka?

   Ummi Abdulmajeed tun ranan daurin auren ki bashi da cikakiyar Lafiya, duk da yana boyewa amman mutane da dama sun fuskanci haka, ranan da kikai kwana biyu agidan mijinki ma yakirani, abinda ya bani mamaki bayan mun gaisa sai yake tambayata wai ina Ummi, ranan wuni nayi cikin tunani, kuma tun daga ranan daurin auren ki Abdulmajeed be sake lekowa gidan nan ba”

     

     Jikin Ummi asanyaye tace”

    Hakama Mukhtar yake cewa tuntuni, dayaga ya Abdulmajeed yazo sai yace wai wlh sona yake, Umma ina ranan dana shigo bakina akunbure?, har nace miki faduwa nayi?

    Eh, Umma tace tare da alamar tunawa, sannan Ummi tacigaba da cewa toh ya Abdulmajeed ne ya d’anemin baki, kuma yaita kushe kwaliyyata, har yana cewa wai idan yasake ganina ina tadi da rana dagani har saurayin sai yaci Uban mu, karashe zancen tayi cikin dariya”

   Itako Ummi cikin tausayawa tace”

   Waiyawo Allah, Wallahi da ace na fahimci Abdulmajeed sonki yake ko zaki mutu bazaki auri Mukhtar”

    “Dariya Ummi tayi tare da fadin nikam ban sonshi saidai yajira ‘yata

    Tabe baki Ummi tayi tare da fadin”

    Toh fitsararriya, tashi muje mugaisa saiki rokeshi kuje ku duba Abdulmajeed din”

    Tare suka fito da Umma, bayan sun gaisa, Ummi take gaya mishi rashin lafiyan Abdulmajeed”

   Sosai ya nuna tausayawan shi akanshi har ya juya ya kalli Ummi yace”

  

    Baby daganan sai mu wuce mudubashi ko”

    Eh tace ta hanyan daga kafada”

    Bayan sunyi sallama da Umma suka fita, adaidai bakin kofar Mukutar ya tsuguna Ummi ko ta dare bayan sa, har sun isa bakin motar Ummi tace itafa sai yazagaye gidan da ita”

    “Cikin nuna baxai iyaba yace haba Baby kingafa kinada nauyi idan nai kudu dake jikina tsami zaiyi”

   “Eh naji idan mukaje gida ni kuma sai nama tausa, harsai kace ya isheka”

    Kinyi alkawarin?

     Gyada masa kai tayi dan haka ya kwasa akuje”

     Sunacin wannan halin Abba ya sako hancin motarsa cikin gidan tare da baza idonshi domin tabbatar da abun da yake hangowa”

    “Suma da alokacin suka kula da shigowan Abba tuni Mukutar ya fara kokarin zamar da Ummi tare da fadin kingani ko”

    ” Bayan Abba ya tsaida motar shi, cikin sauri Mukutar ya isa ya budemai tare da fadin Sannu da dawowa Abba”

    “Cikin fara’a Abba ya amsa tare da fadin”

    “Yau ga Mukutar ga Ummi”

    Dariya Ummi tayi, tare da sunkuyar da kanta kasa”

    Bayan sun gama gaisawa suke fadawa Abba gaida Abdulmajeed zasuje”

   Sosai Abba yaita samusu albarka, har suka shige muta yana binsu da kallo”

    Bayan sun fice ya girgiza kai, tare da fadin yaro yaro ne, saboda wannan shiriritan taki dan uwanta, amman bakomai tunda duk halinsu daya, sai suyita haukan su, har zuwa ranan da hankali zai shige su, shikuma Abdulmajeed Allah ya zaba masa mafi Alheri”

     Itako Ummi gabata ne yaita faduwa bayan ta ganta afarfajiyan gidan su Abdulmajeed, kuma ga dukkan alama yana gida dan duk motocin dayake hawa ta hangosu agurin da aka tanada domin adana motoci”

    Hakanan takejin kamar haduwanta da Abdulmajeed ba alheri bane, kuma tasan haduwanta dashi yau indai yana gida ya zama dele

Mmn Yazeed🔥 🔥🔥🔥🔥🔥

*KOWANNE BAKIN WUTA*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥

( da nashi hayakin)

💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by

*Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*

Wattpad @fadeelalamido

13 – 14

Ita kadai ta fara shiga gidan da fara’a Momy ta tareta tare da fadin har kin fara fita?

Murmushi Ummi tayi sannan ta shiga gaidata, sosai Momy taji dadin zuwan Ummi har cikin zuciyanta”

Zuwa can Momy ta taso ta zauna kusa da Ummi tare da jawota jikinta tare da fadin”

Ummi kinga yadda kikai kyau kuwa, ashe dai Mukhtar din ya iya kiyo”

Sunne kai Ummi tayi ajikin Momy tare da fadin ai tare muke dashi”+

Shine zaki barshi awaje sai kace wasu baki?, ai yanzun Mukhtar ya zama dan gida, tashi maza ki shigo dashi”

Bayan fitan Ummi ba jimawa tashigo da Mukhtar har kasa ya tsuguna yagaida Momy, sosai Mukhtar din ya burge Momy, dan bata taba ganin saba sai yau, zuwa can falon yai shiru”

Ummi ce ta katse shirun ta hanyar cewa Momy su hassana basa nan ne?

Eh sun shiga kasuwa amman nasan yanzun suna hanya”

Shiru Ummi tayi zuwa can ta sake cewa”

Yaya Abdulmajeed fah?

Dan jimm Momy tayi cikin rashin kwarin jiki tace yana dakin sa”

Shiru Ummi ta sake yi akaro na biyu, domin tunanin hanyar dazata bollo”

Zuwa can taji muryan Momy na fadin”

Ummi jeki kira Shi mana su gaisa da Mukhtar din”

Toh kawai Ummi tace sannan ta mike ta nufi hanyar da take ganin Abdulmajeet din yana fitowa dan ita bata taba zuwa dakin saba”

Mukhtar din kuwa ji yayi kamar yace a’a amman babu dama dan haka yaita raba idanu”

“Itako Ummi bayan ta isa kofar da take tunanin ta Abdulmajeed ce ta fara bugawa”

Abdulmajeed dake zaune yana zukan sigari yai saurin kashe wa tare da boye guntun agefen gado sannan yace waye?

Nice ta fada ahankali, jin Muryan Ummi yasa Abdulmajeed daburcewa tare da fadin shigo”

Turo kofar Ummi tayi bakinta dauke da sallama, saidai warin sigarin daya isa hancinta yasata cikin dan karamin tunani daman Abdulmajeed nashan sigari ne, tabbas dakin nan warin sigari yake yi, kuma sosai akasha ba kadan ba”

So take ta toshe hancinta amman tana tsoron Abdulmajeed dan haka ta daure tace ina wuni?

Wani irin kallo ya mata me kama da harara tare da fading da ban wuniba zaki ganni”

Shiru Ummi tayi tana wasa da hannunta tare da rasa abin cewa”

Zuwa can Abdulmajeed yace wai lfy kikazo kika tasani agaban?, daga ina kike”

Daman Muje gida ne nida Mukhtar shine Umma tace mubiyu mugaida ka”

Cikin sauri ya dauke kai kansa gefe, ji yake tamkar ya tashi ya rufe ta da duka, ban da rashin kunya tasani acikin wani hali sannan tace tazo ne ta gaidani?

Juyawa yayi ya kalleta fuskan shi amurtuke yace”

Dake da Mukhtar din kunci kutumar uban ku”

STORY CONTINUES BELOW

😳zaro ido Ummi tayi domin bata taba tunin haka ba, abun kuma harda zagi”

Cikin karaji yace ko bakije abin danace bane?

Adaburce tace naji, Allah ya baka hakuri”

Mikewa yayi azafafe, ni zaki gawa mgn sabo da wuyanki yayi kauri ko?

Komawa da baya Ummi ta fara domin yadda ya taso ya tsoratata”

“Sai dai har ya iso inda take bata samu ta isa kofar ba”

Cikin sauri ta manna bayanta ajikin kofar,tare da zare ido tana kallon yadda Abdulmajeed yayo kanta”

Runfa yayi mata tare da fadin”

Ni sa’an wasan kine dahar zan gaya miki mgn ki bani amsa?, ki kalli cikin idona ki gani namiki kama da wannan banzan mijin naki”

Girgiza kai tayi arude”

Toh ki shiga hankali ki, atsarina kinyi kadan infadi magana ki bani amsa, sannnan daga yau karki kara cemin Yaya, niba yayan ki bane, ki kirani da Abdulmajeed kawai, ki dauka kamar atiti kika sanni, ban son ki kuma har abada bazanyi zumunci dake ba, ko mutuwa nayi karki nuna kinsan gawata bare wani abu dana bari”

Sosai hankali Ummi ya tashi, dan haka hawaye ya fara zubo mata, lallai akwai wani babban abo da na masa, idan ba haka ba, me yayi zafi shiba wutaba”

Har yanzun yananan ayadda yake becire hannunsa ba bare ta samu da wuce, hawaye ne kawai ke shatata a idanunta, zuwa can tai karfin hali tace”1

Na maka wani abu ne?

Au tambayata kikeyi?, mena gama gaya miki yanzun?

Shiru tayi sannan ta dukar da kanta kasa tare da fadin kayi hakuri”

Hannun shi yacire tare da fadin munafuka kawai kina abu kamar mutuniyar kirki, banza wadda batasan me take ba”

Hawayenta ta share ganin ya juya yana kokarin komawa gado yasa ta bude kofar tare da fadin, Momy na kiran ka”

Bata jira abin da zaice ba ta fice da sauri”

Kafin ta isa palon saida ta tsaya ta share hawaye sannan ta koma kusa da Ummi ta zauna tare da fadin gashi nan zuwa”

Idon Ummi Momy ke kallo tanason taganu wani abu, shima Mukhtar ita yake kallo zuciyar shi cike da tuhuma”

Zuwa can Abdulmajeed ya fito hannun shi duk biyun acikin aljihun fuskan shi murtuk kai kace be taba dariya ba, bayan kujeran da Momy ke zaune ya tsaya ahankali yace gani”

Juyawa Momy tayi ta kalli shi cikin hade rai tace to ka karaso mana ai Ummi tare da mijinta Mukhtar take”

Kara matsowa yayi kadan”

Cikin rashin jin dadi Momy ta kauda kanta gefe”

Cikin fara Mukhtar yace yayan mu anwuni Lafiya?

Can gefe Abdulmajeed ya kalla tare da fadin Lafiya”

Mukutar ya sake cewa ya karfin jiki?, ashe bakaji dadi ba?

Injiwa ya yace maka banji dadiba?, ni kalau nake, nama fiku lafiya, yana gama fadin haka ya juya ya koma daki, adaidai lokacin da Mukhtar ke fadin”

Haka muke so babban yaya”

Momy ko Abdulmajeed tabi da kallo, tare da mamakin hali irin na Shi”

Dahaka sukayi sallama suka fita”

Suna barin gidan Ummi ta fara kuka”

Waigowa mukutar yayi ya kalleta yayi murmushi, sannan yace”

STORY CONTINUES BELOW

Nasan zuwa yanzun kinfara fahimtan halin da yayan ki yake ciki akanki”

Share hawayen tayi sannan tace”

Ai ba abin da kake tunani bane, kaifa cewa kake wai sona yake yi, wlh Yaya Abdulmajeed baya sona, asalima ya tsaneni harta kai beson ya kirani ‘yar uwanshi”

Dariya Mukhtar yayi tare da fadin”

Saboda kin kishi ba”

Waigowa tayi ta kalle Mukhtar sannan tace kana nufin saboda nakishi sai ya dinga fadin min duk abin dayazo bakin shi?, har zagina fa yayi”

Hmmm Ummi ai dole yaji zafi tunda yariga yayi zurfi asonki, kuma ya kasa cireki acikin zuciyan shi”

Shiru sukayi har sukayi tafiya me tsayi, zuwa can Mukhtar yace”

Ummi nima daga yau ban yadda ku kara kebewa da Abdulmajeed ba”

Wani irin kallo tamai, tare da fadin sabo dame?

Kamar bazaiyi mgn ba, zuwa can yace”

Saboda ba muharramin ki bane”

Ajiyan zuciya ta sauke sannan ta kauda kanta gefe”

Bazai yuwuba saboda saboda dan uwanna ne”

Me kikace? Mukhtar ya fada tare da juyowa ya kalleta”

Kauda kanta tayi tana zunboro baki tare da fadin duk tsiya ai dai dan uwan nane, dan me zaka ce karna sake mgn dashi?

Toh me dan uwa, ba nufina kenan ba, kebewa nace ina nufin karki kara shiga dakinsa dan gsky ina kishin matata, idan kika kara kebewa dashi ban yafe ba”

Sosai Ummi taji haushin zancen shi, gashi maganganun da Abdulmajeed ya gaya mata sun tsaya mata arai, sannan warin sigarin daji adakin sa ya tsaya mata arai, ji take tamkar warin giya taji soda rashin jin dadin da taji”

Har suka isa gida Mukhtar be jiyo ya kalleta ba, Ummi ta kula Mukhtar fushi yake, wannan yana cikin halayen dayasa akullun sonshi yake kara shigan sa, komai ka masa baya babatun fada, koda abin ya masa zafi, sai dai kaga yana kokarin sharewa”

Suna shiga cikin palon su dakin sa ya nufa batare da ya waiwayo ba, dan haka jikin Ummi ya kara sanyi”

Itama dakinta ta nufa tai wanka tare da dauro alwala, zuwa can taji fitan Mukhtar acikin zuciyanta tace lallai maza sunyi fushi”

Bashi ya dawo ba sai wajen karfe 9:00pm sosai hankalin Ummi ya tashi, sai dai tayi alkawarin ko karfe nawa zaikai be dawo ba saita jirashi kuma tavashi hakuri, koda ya shigo kallonta yayi sannan yayi murmushi kadan tare da fadin baki bacci ba?

Mikewa tayi ta isa kusa dashi tare da rike hannun shi tana fadin tayaya zan iya bacci bayan kana fushi dani”

Kofar dakin sa ya bude ya shiga ya zauna abakin gado sannan yace”

Bana fushi dake, jeki kwanta abinki”

Hayewa cinyar shi tayi tare da fadin”

A’a wlh fushi kake, ni dai kayi hakuri, idan baka dawo kaman daba nikam bazan iya bacci ba”

Hmmm to naji kibar ni zuwa safe zan huce dakaina”

Tabe baki tayi kamar zatai kuka, sannan tace”

Ai bazan iya bacci ba alhalin nasan fushi kake dani”

Ni badake nake fushi ba, rainane ya dan bacci kuma nasan zuwa safe zan huce”

Tsura masa ido tayi tare jin wani irin sonshi me tsanani yana kara shigarta, sosai takejin dadin salon nuna fushin sa, domi ta tabbatar inda Abdulmajeed ne yaji haushi haka matsiyacin duka zai mata”

STORY CONTINUES BELOW

Dan murmushi tayi domin tunawa da Abdulmajeed yasa ta fahimci da ace shi ne mijinta da tana cikin kuncin”

Cikin dariya tace Sweetheart saboda Abdulmajeed kake fushi?

Dagowa yayi ya kalli Ummi sannan yace”

Gaskiya kebewan da kukayi yaban haushi kuma nayi mgn kince min dan uwanki ne, haka na nufin kin fara tausaya mishi kenan, kuma ni bazan so haka ba, tunda da aurena akanki, kuma ina soki sosai”

Cikin dariya tace toh kayi hakuri, nima ban fahimceka bane na dauka kana nufin indaina mgn dashi ne, kuma dana dade adakinsa tareni yayi yanata gayamin maganganu har dasu zagi, Sweetheart ko bakace ba ni kaina bazan kuma shiga ba, kuma dan Allah ka daina saka Abdulmajeed ajerin masu hankali, wlh Abdulmajeed bashi da hankali, tun tuni yake abubuwan marasu hankali amman su Umma basa ganewa, har wani kirari kakarmu take mai, wai *miskili kafi mahaukaci ban haushi,* yanzun kuma abin nasa naga kara gaba yakeyi, ni kiran daddy ma zanyi ince akaishi Asibiti aduba shi”

Juyowa Mukhtar yayi ya kalli ummi fuskan shi dauke da murmushi, sannan yace”

Lallai Ummi yarinta na damun ki, Abdulmajeed din za’akai asibiti?, lfyn sa kalau fah, shi yasan abin da yakeyi, kuma nan gaba kadan zaki fahimci haka”

Kallon shi tayi sannan tace”

Toh mubar zancen shi hakanan dare yayi fah”

Shirin kwanciya sukayi sannan suka hau gado, saidai har yanzun Mukhtar be saki jikinsa ba dan haka Ummi ta fara mai cakulkuli tun yana nonnukewa harya sake ya fara kyalkyata dariya”

Washegari da asubar fari wayar Mukhtar ta hau tsowa, cikin sauri Ummi ta bude idonta, ta dauki wayar”

Tundaga taga number ta fahinci kiran daga Niger ne, tana niyar dagawa Mukhtar ya bude idonsa cikin sauri ya warce wayar tare da dannwa ya kara akunnen sa”

Binshi tayi da ido domin inda ya kwace wayar harsai da ya bige mata hannu”

Ahankali taji Yayi sallama tare da fadin, Ummayo ankwana lafiya?

“Batasan amsan da aka bashiba ita dai taga ya kara ya mutse fuska tare da fadin”

Nace miki zamu taho ki kwatar da hankalin ki mana, aikine yamin yawa amman dazaran yayi sauki zamu taho”

Shiru yayi alamar yana saurara zuwa can yace”

Toh ai zaku ganta amman sati guda zamuyi”

Shiru yasake yi, Ummi ko ban da zuba mai idanu babu abun da take, gashi mukhtar din yana amsa wayar fuskanshi kicin kicin kamar dai wadda aka takurawa”

Bakin shi ta sake bi da kallo lokacin da yake fadin”

A’a Ummayo ni gaskiya bana so, itama Zainab din bazata so ba, kawai abarshi”

Kara tamke fuska yayi alama fada ake mai yai shiru, zuwa can ya tashi ya zauna duk wayar na manne akunnen shi”

Zuwa can yace zanzo ai, kiyi hakuri”

Shiru, dagacen ya sake cewa bata tashiba ai, Ok sai anjima”

Ajeye wayar yayi tare dajan ajiyan zuciya, sannan ya juya ya kalli Ummi tare da sakar mata murmushi”

Itama murmushi tayi tare da fadin”

Dawa kake waya?

Kauda ido yayi Mamana ce”

Wani irin Ummi tayi sannan tace shine baka bani mun gaisaba?

Karki damu wata rana zaku gaisa”

STORY CONTINUES BELOW

Kallo shi tayi sosai sannan tace toh yaushe zaka kai ni?

Hmmm zakije Ummi suma sun matsu su ganki, ina sone ki kara kwari tukuna dan kada ki galabaita, kisan Niger banan bace”

Kana nufin yanzun bani da kwari ne?

Ba irin wannan nake nufi ba, kidai bari tukuna zamuje”

Shiru tayi zuwa can ta sake cewa”

Naji kanacewa Baka so, kuma Zainab ma bazata soba, menene wannan ne?

Murmushi yayi tare da jan karan hancinta yace”

Kai yariyar nan kin cika tambaya, daman kasa min kunne kika yi?

Ba zancen kasa kunne ai agabana kayi”

Hmmm ai duk abin da nake so nasan shi kike so”

“Bawani nan, ka fada min, ka sani koni naso?

“Mikewa yayi tare da fadin, tashi muje kar lokacin salla ya kure”

“Mekewa Ummi tayi tare da son sanin abin da akace mishi acikin wayar”

Koda Mukhtar ya tafi Office tunanin da taitayi kenan, atunanin ta kamar akwai abin da yake boye mata”

Washegari ma daidai wannan lokacin da aka kira shi jiya aka sake kira dubawa tayi taga dai wannan number ce ta jiya dan haka tai saurin dauka tare da sallama”

Daga can cikin wayar taji muryan mace tana mgn, bata fahimtan me take fada ba saboda hausarta bata fita yadda ya kamata, saiji take ma kamar tana hadawa da yare”

“Gyaran murya tayi tare da fadin ina kwana?

Magana matar tayi sai dai bata fahimci abin da tace ba, dan haka ta rasa abincewa”

Daidai lokacin Mukhtar ya fito daga toilet ganin wayar sa akunnen Ummi yasa shi saurin karasowa ya amshe tare da karawa akunnen sa”

Sallama yayi tare da fadin ankwana Lafiya”

“Zuwa can taji ya sake cewa eh itace”

Shiru yayi sannan daga can taji yayi kasa da murya tare da fadin”

Haba Ummayo kimata uzuri bata sani bane, kuma dan Allah karki gayawa Baba zan mata fada”

Shiru ya sake yi daga cen ya kuma cewa”

“Nan da wata biyu insha Allahu”

“Wa za’awa fada? Ni? Me nayi? Ummi ke fadin haka acikin zuciyarta”

Kallon shi ta karayi sannan ta kara cewa me za’ayi nan da wata biyun?

“Ganin ya ajiye wayar ta tsaya tana kallon shi tare da jiran tsammani”

“Kan shi ya daga sama, zuwa can ya sauke tare da ajiyan zuciya, kallon Ummi yayi tare da fadin”

“Idan ankirani karki sake daukan wayar”

Sabo dame Ummi ta tambaya zuciyarta cike da zullumi”

“Na dai gaya miki, idan ba haka ba zakijawa kanki matsala”

“Matsala kuma? Wacce irin matsala?

“Juyawa yayi ya fice adakin, matsanancin tunani Ummi ta shiga acikin zuciyan ta tace menene haka kuma, nifa arayuwata bana son matsala”

Ranan Ummi wuni tayi cikin zullumi tare dasan sanin menene yake faruwa?

*******

Shiko Abdulmajeed bayan tafiyan su Ummi tsaki yaitaja tare da rasa abin yi”

“Washegari da yamma yana shirin tashi aiki Sadiq ya shigo office dinsa”

Zama yayi suna fuskanta juna, bayan Sadiq ya gama karewa Abdulmajeed kallo yace”

“Har yanzun dai tunanin Ummi ne?

Kyau da ido yayi sannan yace”

Wacece haka kuma, akuyar gidan kuce?

Dariya Sadiq yayi sausai har hakoran shi suka baiyana sannan yace ance da makaho ga ido yace wari gareshi saboda yasan ba zai samuba, kara shekewa yayi da dariya tare da kara cewa”

Wai ina labarin sigari?, gaskiya Abdulmajeed karamin kwakwalwa gare kare ka, wai kaine ka dauki kara”

Hmmm kaga Sadiq banaso iskanci nakula neman magana kake”

Shigowan wata buduwa sanye da kayan jinya yasa duk suka maida hankali gurin kallonta”

Gaida su tayi sannan ta ajiye wasu takardu agaban Abdulmajeed tare da fadin Dr Mubarak ne yace na kawo ma”

Dagowa yayi ya kalli yariyar itama kureshi tayi da ido, zuwa can ya maida kallon sa kan kirjinta, gaba daya halittan jikinta abayyane yake, sabo da yadda kayan suka matseta, hakanan Abdulmajeed ya kasa dauke idosa akanta”

Itako yariya yadda ta kula Dr Abdulmajeed nabinta da kallo ta fara dan kirgiza kirjinta, domin ta dade ta neman wannan daman”

Yadda Sadiq ya kula da abin da Abdulmajeed keyi da yadda yariyar ke masa yasa yace da yariyar inace kin bada sakon ko?

Kai ta daga alamar eh”

Sadiq yasake cewa toh sai anjima ko?

“Har yariyar ta juya Abdulmajeed yace ke zonan”

Saida gabanta ya fadin domin Muryan Abdulmajeed wani irin kwarjini gareta”

Juyowa tayi ta kalli shi”

Dauke kansa yayi sannan yace, daina kallo na”

” Cikin sauri ta dukar da kanta kasa”

“Sadiq ko kallon Abdulmajeed yayi sannan ya kalli yariyar tare da shafa gemun sa”

Yaya sunan ki?

Abdulmajeed ya tambaya tare da jawo takardun da ta ajiye mai”

Cikin siririyar muryanta tace *Nafisa*

“Yi yayi kamar beji taba yaciga da rubutu akan takardan”

Zuwa can ya dago ya mika mata daya daga cikin takardan yace ki kaimasa, zai baki wani ki kawo min shi yanzun nan”

Tana juya baya Abdulmajeed yabita da kallo”

Sadiq ne ya zungureshi tare da fadin meye haka?,

Kauda ido Abdulmajeed yayi sannan yace”

Meye kuwa?

Naga ka kureta da ido ne, Sadiq ya fada cike da tuhuma”

Eh nakureta da idon ko zaka dod’emin ido ne?

A’a wane ni, nidai gani nayi mata basa gaban ka, kuma naga kasa ma yariyar mutane na mujiya”

Mikewa Abdulmajeed yayi tare da fadin”

Zan fita idan ka gama zaman ka rufemin Office”

Abakin kofa suka kusan cin karo da nafisa zata shigo, cikin sauri ta kyauce ta bashi hanya”

Wucewa yayi tare da kara tamke fuska saida ya shiga gabanta yai nisa sannan ya waigo yace biyo ni”

Dan zaro ido tayi sannan tabishi kamar yadda yace…….

Mmn Yazeed🔥 🔥🔥🔥🔥🔥

*KOWANNE BAKIN WUTA*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥

    ( da nashi hayakin)

💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by

    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*

    Wattpad @fadeelalamido

            *15 – 16*

Motar shi ya nufa, Nafisa nabinsa abaya, bayan ya bude ya shiga ya zauna yace shigo”

   Cikin rarraba ido Nafisa ta shiga gaban motar ta zauna”

    Harya tada motar yaji wayarsa na neman agaji dan haka ya tsaya ya dauka”

     Sadiq ya gani dan yahaka yayi tsaki tare da maida wayar majiyarta sannan ya figi motar aguje yabar asibitin”+

    Sadiq dake can nesa yana hango su ya ja tsaki tare da fadin”

     Me yake shirin faruwa da Abdulmajeed ne?, yana yin abu saika ce karamin yaro, ko ina zai kaita oho”

    Tsaki ya kuma ja akaro na biyu, wucewa Office din shi yayi yaci gaba da aikin sa”

   

    Shiko Abdulmajeed tafiya yayi me nisa sannan ya sauka gefen hanya ya tsaya”

    Ahankali ya juya ya kalli Nafisa, hakanan yaji shiganta ya burgeshi cikin  fararan kaya take riga da wando wadda suka matseta matuka, wandon ya kalla yadda ya matseta acikin zuciyan shi yace koya suke suna saka irin wannan wandon oho”

     Maida idon shi yayi kan kirjinta, sosai ya shala wajen kallonta”

    Itako Nafisa daman haka take so dan haka dan haka ta fara kissa da kisisina tare da nuna batama san yanayi ba”

    Sosai hankalin Abdulmajeed ya tashi, sai dai wannan karon yasha babban dana lokacin daya rasa Ummi”

    Koda yakejin yana son Ummi betaba jin irin wannan yanayin ajikinsa ba, wannan karon ji yake tamkar ya taba jikin Nafisa, sai dai bazai iya hakan ba”

     Tsaki yaja sanna ya karkace ya ciro sigari a aljihun sa ya kunna ya fara sha tare da fesa hayakin ta window motar”

    Ganin ya dauke idon sa akanta yasa ta waigo tana kallon shi,  gaskiya tana son Abdulmajeed sosai, ta dade tana neman hanyar da zata rabe shi, sai dai baya kallon kowa bare ya saurare shi, yau gata acikin motar Abdulmajeed tasamu daman da ‘yan mata da yawa ke neman samu, sai dai ta kula Abdulmajeed zaiyi wuyan sha ani, dole ta neman wa kanta mafita, dan haka ta gyara zama tare da kashe murya, tace”

     Doctor yagana mun tsaya ahanya mu karasa mana”

     Juyawo yayi ya wurga mata wani kallo tare da fadin ina zamu karasa?

       Dauke kanta tayi tare da cigaba dayi masa kwarkwasa”

    Ido Abdulmajeed ya zuba mata sosai, tana daga zaune amman jikinta sai wani girgiza yake rudewa Abdulmajeed yayi yama rasa a ina yake”

    Cikin sauri ya mika hannun shi ya juyo da ita suna fuskanta juna, ido suka kurawa juna, ahaliki Abdulmajeed yakai hannun shi wuyan rigar Nafisa”

    Tsintan kanshi yayi da jan zif din rigar ya sauke shi kasa”

     Ajiyan zuciya Nafisa tayi ganin abin da Abdulmajeed yake shirin yi”

     Ido ya sake kurawa wajen acikin zuciyan shi yace lalai yariyar nan tantiriya ce, domin babu komai ajikinta bayan rigar aikinta ajikinta”

     Batare da yayi wani tunani ba ya fara ya mutsa Nafisa, Nafisa ko kara sake jikinta tayi zuwa can ta shiga maida martani, kafin wani lokaci duk sun shiga cikin wani yanayi dan haka sai da suka kwashe kusan awa daya suna abu daya, zuwa wannan lokacin rigar nafisa bata jikinta gaba daya”

STORY CONTINUES BELOW

     Saida Abdulmajeed ya gaji dan kansa sannan ya bari ya koma gefe tare da sauke ajiyan zuciya”

     Itako Nafisa rigarta ta dauko tana kokarin mayarwa jikinta dukda bataso abin ya tsaya anan ba, amman hakan ma babu laifi domin yau ta sheda Mazama kala kala ne, duk acikin wad’an da suke neman ta babu wadda yasan hannun sa kamar Abdulmajeed, badan tasan halin saba, da tace ya kware a harkan, ko ahaka yasata nishadin, da bata taba tunanin samu ba”

     Tana cikin wannan tunanin taji ankwasheta da mari”

    Gaba daya tunaninta daukewa yayi, zuwa can taji Abdulmajeed yana cewa”

    Meyasa zaki dinga saka tufafin dasuke matse jikin ki?, kina nuna halittan da Allah ya miki ga kowanne jaki, ni banason iskanci yariyar yar karama kin iya kwartanci”

   Ido kawai Nafisa tasa tana kallon shi, acikin zuciyanta tace kagamin mutu dan rainin wayo, ka gama zaucewan ka ajikina, kuma kazo kana zagina, shafa kumatunta tayi sannan ta gyara rigarta, batare da tace mishi komaiba ta bude motar ta sauka”

   Tsaki Abdulmajeed yaja sannan ya ja motar ya isa gurinta”

    Kudi ya dauko masu yawa ya watsa mata tare da fadin karuwar banza kawai”

  Figan motar yayi yabar wajen”

 

    Murmushi Nafisa tayi sannan ta tattara kudin ta zuba ajaka tare da fadin ai babu laifi”

    Gida ta nufa, sai dai har dare ta kasa mance Abdulmajeed acikin zuciyanta, sosai take tuna farin cikin daya sata”

    Bayan tagama jin zugin marin da yayi mata ta fara dariya, afili tace”

    Kagamin rigimammen mutumi, ban da rigima ka gama sambatun ka ajikina sannan kazo kana kirana karuwa?

    Kwashewa tayi da dariya tare da tuno yadda Abdulmajeed yaita sarrafata”

     Shiko Abdulmajeed daya koma gida sai da yayi wanka tsarki domin ta wajaba akansa”

     Sosai yake tuna Nafisa suran jikinta ya burgeshi matuka, yau tunanin Ummi ya rago sosai acikin zuciyan shi, dan haka Abdulmajid ya maida wannan dabi’a ta zamar mai jiki da zaran ya tuna Ummi kobaya Office zai tura adauko mishi Nafisa, sai dai duk abin da zasuyi iyakacin su mota, sannan iya wasa kawai yakeyi da ita ya sallameta bayan ya bata kudi tare da tarin wulakanci, bashi zai hana gobe ya sake kiranta ta biyoshi ba”

    Ahaka sukaja watanni masu dama suna aikata zunubi, ayanzun abin ya zamar musu jiki akullum idan basu haduba basa jin dadi, dayaji yana son tabata zai kirata awaya duk inda take zataje ta same shi”

    Kullum Sadiq cikin yiwa Abdulmajeed fada yake, duk da basa fita tare amman Sadiq yana fahimtan cewa suna tare, dan haka yau Sadiq ya tareshi da mgnr”

    Abdulmajeed tunda ka rasa Ummi, halayen ka duk sun canza, kuma wannan yariyar Nafisa da kake tare da ita kwata kwata bata da tarbiya, amman wai sai gashi jiya Sani yazo ya dauketa a motar ka, natambaye shi yace kaine kace ya daukkota, idan ma sonta kakeyi ai gara ka aureta amman yawo da ita Sam be dace ba”

    Ok kana nufin zargina kake kenan?, ni dan iska ne?, kuma da kake cewa na aureta mezanci da ita?, kai ka aureta mana”

   Hmmm Abdulmajeed sai ana gayama gaskiya ka kama fada, kaine naga kamar kana sota, kuma inba sonta kakeba me zaisa ka dinga kulata?

     Takardun dayake gavashi ya fara dubawa tare da fadin baka da aikin yine”

       *******

Ummi na hango zaune da tsohon ciki, ta mike kakafunta, Mukhtar na zaune agefe ya matsa mata kafa”

     Ummi ko banda ya mutsa fukka babu abin da take”

STORY CONTINUES BELOW

    Muryan Hajiya Maryam suka jiyo tana sallama, wato matar Alhaji Yaro me gidan Mukhtar, Mukhtar d’in ne ya amsa mata”

    Tana shigowa Mukhtar ya mike tare da mata sannu da zuwa”

    Ummi ma kokarin mekewa take dan haka Hajiya tace a’a yi zaman ki, kina fama da kanki Allah dai ya rabaku Lafiya”

    Mukhtar ne kadai yace ameen Ummi ko acikin zuciyanta ta amsa”

   Bayan Hajiya ta huta tace Mukhtar, mahaifiyar ka ta matsu tanason ganin ka, tare da iyalin ka, kuma kaima baka kyautawa meyasa baka gaya mata matar ka nada ciki ba?

   Cikin Sosa kai yace daman na barine saita haihu”

   A’a Mukhtar gaskiya be dace ba, mahaifiyarka tana sonka, yakamata ace kakai Ummi asun ganta tun tana Amarya, takirani tana fada akan cewa, kaki ka kawo musu matar ka, shine tace tayi hakuri wata kila dan kaga tana da cikine ka bari saita haihu, sainaga ranta ya kara bacci daga karshe na fahimci baka gayamta bane, da tasa rigima sai dai kakai musu zainab ta haihu acan, amman nashayo muku kanta daker, ta amince idan ta haihu Lafiya tayi arba’in zaku tafi, kuma ni na dauki alkawarin zan taso musu keyar ku”

   Murmushi Ummi tayi tare da fadin wallahi Hajiya ni tuntuni nake son zuwa shine yake hanawa, kuma ko kirasa tayi awaya baya bani mugai sa”

     Toh aidai duk tsiyar shi dole kuyi zumunci tunda anriga anzama daya”

    Kusan yamma Hajiya takai agidan su Mukhtar sannan ta tafi”

    Adaren ranan Ummi ta haifi danta na miji me kama da baban sa, sosai kamar yayi kaki ya tufar”

Murna gurin Ummi da Mukutar ko ba’a magana, adaran ya bugawa Abba waya”

    Alhamdulillahi Abba yaita maimaitawa, sai washegari da safe labari ya wade dangi, cikin harda Abdulmajeed daya tsinci zancen lokacin daya fito domin yin breakfast”

     Sosai ya hade fuska tare da fasa cin abin cin komai ya mike ya koma dakin sa”

    Wanka yayi yabar gidan, yana isa Office ya kunna sigari damuwa ya shiga da tashin hankali yakira Nafisa yafi akirga amman bata daga wayaba dan haka yaita shan sigarin”

     Zuwa can kiran Nafisa ya shigo wayar shi, cikin sauri ya daga tare da fadin ina kuma kika shige ita kira baki daga ba”

    Wlh ina hanya ne banji ba, amman na shigo Asibitin yanzun”

    Ok toh fita waje gani nan zuwa”

    Cikin dauki tace toh”

   Ahanya suka hadu da Sadiq yana kokarin zuwa gurinsa tare da fadin”

     Ashe mun samu karuwa”

    Tsaki Abdulmajeed yaja sannan yace gaba da tafi”

      Ganin idon Abdulmajid yasa Sadiq fadin”

   Gaskiya Abdulmajeed yana da wuyar sha’ani, ace shi kullum tunanin shi shine daidai, idan ya likewa abu daya ya like kenan saikace tsohon maye”

    “Ji inda yake mazurai saika bayuwaciyar kyanwa”

     Shiko Abdulmajeed yana fita ya dauki Nafisa suka wuce”

   

     *****

   Ummi ko tana samun kulawa sosai agurin Hajiya Maryam da Momy, har ranan suna ya zagayo yaro yaci sunan Ahmed

    Sosai akai shagalin suna inda sunan ya kasan ce dangin Ummi ne kawai, sai wasu daga cikin kawayen hajiya Maryam da ‘ya’yanta”

   Tunkafin Ummi tai arba’in Hajiya ta fara tuna musu da maganar tafiyan su Washegari ranan da tayi arba’in”

STORY CONTINUES BELOW

    Sosai Ummi ta fara shirye2, tare da siyan kaya tsaraba wadda zata bawa yan uwan Mukhtar”

     “Wani irin kallo takewa Mukhtar dan ganin shi baya zumudin tafiyan, bataga yasai komai ba”

    Ranan da Ummi tayi arba’in Mukhtar ya kaita gidan Abba da niyar da yamma zata wuce gidan hajiya Maryam shikuma ya dauketa acan”

    Abba da Umma sunyi murna da ganin Ummi da d’anta sunyi bulbul gwanin ban sha’wa”

     Nan Ummi take sanar musu tafiyan su Niger gobe”

    Umma jitayi ta shiga damuwa domin Ummi kadai Allah ya basu bata son tai nisa dasu”

    Yaushe zaku dawo?, Umma ta tambaya cikin rashin kwarin jiki”

    Shi dai yace sati zamuyi, amman nasan yadda mamansa ta kosa muje sai munfi sati”

   Jinjina kai Umma tayi domin sai taga rawan kan Ummi, dan haka tace toh kidai natsu ki kama kanki banda rawan kai, dan bakisan halinsu ba kamar yadda basu san nakiba, kuma kuna zuwa hankalin su kanki zai dawo, banda mannewa miji, domin wasu iyayen suna ganin haka zasuce kin mallake musu d’a, dan haka ku aje halin ku agefe har ku dawo”

    Tunda ake magarnar tafiyan bata tabajin guiwanta yai sanyi ba sai yau, sosai taji damuwa, Abba daxai dafi aiki kudi yabata yace tayi tsaraba”

       Gurin karfe 3:00 Umma tasa drive yakai Ummi gidan su Abdulmajeed ta musu sallama”

     Itama Momy tayi farin cikin ganin Ummi, Ahmeed ko tinda suka shigo yana hannun ‘yan biyu”

    Itama Momy sai da ta mata dan nasiha kwatan kwacin wadda Umma tai mata, dan haka ta farajin tsoron tafiyan”

    ‘Yan buyu na tsaka da wasa da Ahmeed Abdulmajeed ya shigo, ganin kyakyawan yaro besan lokacin daya isa gurin su Hassan ba, tare da mika hannun sa yana fadin kai! yaron waye ne?

   Harya dauki dan yana kokarin kaishi kirjin sa Hussaina tai karaf dace yaron Ummi ne”

    Cikin sauri ya mika mata tare da share hannun sa kamar ya taba kashi”

   Duk abin da suke Momy da Ummi na kallo sadda ta hango Abdulmajeed zai dauki Ahmeed wani irin dadin taji, ganin yadda yayi kuwa da akace d’an tane yasata damuwa”

     Sallama tayi musu ta dauki Ahmeed suka wuce  gidan hajiya Maryam, can ma dai gargadin taita mata, sai dare Mukhtar ya yadauketa suka koma gida”

     Dukda jikin Ummi asanyaye yake be hata hada kayan tsarabarta ba, goya Ahmeed tayi ta sauke akwatinnan ta gaba daya ta loda kaya aciki”

    Tana cikin wannan halin Mukhtar ya shigo cikin sauri ya kara mata yawa akunne tare da fadin”

     Daddy ne ya kira kuyi sallama”

   Sallama tayi cikin wayar sannan ta shiga gai dashi”

    Cikin fara’a yake amsawa sannan yace ai dazun ake fadamin buzun abokina yazo, naso nagan shi, amman ba komai watarana zamu hadu”

   Dariya kawai Ummi keyi”

   Daddy ya sake cewa ance gobe zaku tafi ko?

   Eh Daddy gobe zamu tafi ai ba dadewa zamuyi ba”

    Toh Allah ya sauke ku Lafiya, dan Allah kina sauka kiyo waya kinji ko?

    Toh daddy insha Allahu”

    Kunyi sallama da Abdulmajeed kuwa?

   Eh daddy nadai ganshi amman ni fushi yake dani, rannan ma cewa yayi karna sake mai mgn, kuma ni bansan me namai ba”

STORY CONTINUES BELOW

   Rabu dashi mashiriricin mutum ne”

     Daddy kodai za’a kaishi Asibiti ne aduba kwakwalwar sa, har fa cemin yayi wai ko mutuwa yayi karna nuna nasan gawar shi, kuma ni wlh daddy ban mishi komai ba”

    Dariya Daddy yayi sosai sannan yace, Mamana ki kwantar da hankalin ki, lfyn shi lau, iskance ne irin nashi, duk abin da yake yi da gangan yake dan haka na zuba mashi ido, amman nakusa yin maganin shi, dahaka sukayi sallama da daddy, ta juya tana kallon Mukhatar daya kurawa kayan dake gabanta ido”

    Wayar ta mika mashi, ahankali  yace wannan kayan fa na menene?

   Kayan dazanyi tsaraba ne nake hadawa?

   Dariya yayi tare da fadin lallai Ummi, da kinyi shawara dani da baki kashe kudin ki ba, akwati daya zamu dauka shima dan karmu rasa kayan sakawa ne, idan ma sun yadda mu saka kenan”

    Wani irin kallo tamai tare da fadin”

   Kana nufin garin ku ba’a saka kaya ne?

    Murmushi yayi sannan yace ana sakawa mana, amman gaskiya bazan boye miki ba, akwai irin kayan su na al’dar kauyen mu, kowa ka gani a garin irin shi ne jikin sa”

     😳Zaro ido tayi tare da fadin wanne iri ne kayan?

     Idan muje zaki gani ai”

    Cikin sanyi jiki ta sukuyar da kanta, ko wanne irin kayane wannan oho? zuwa can ta dago tace nidai tunda na riga na saya zan tafi dashi ko siyarwa sayi”

    Girgiza kai yayi tare da fadin”

    Wannan kayan ko muntafi dashi wahala zatasa ki zubar dasu ahanya, dan haka kibarshi kawai shi zaifi”

   Wanne irin wahala muda zamu tafi amota, kanayin mgn kamar zamu tafi amotar haya?

   Murmushi yayi, sannan yace, Ummi bazan je da mota ba, domin ko naje da mota bazata min wani amfani ba, dan hakama da dauki drive dazai kaimu, kinga idan ya kaimu dole zamu karasa”

    Wani irin kallo tamai sannan tace, kana nufin da kafa zamu tafi?

     Idon Ummi ya kallah tare da fadin”

     Eh akwai tafiyan da zamuyi da kafa”

    Shiru tayi tare da sunkuyar dakai, Muryan Mukhtar taji yana fadin”

   Tunanin me kikeyi?, kodan kinji nace akwai tafiyan kafa?, karki damu idan kingaji daga ke har Ahmeed zan goya ku”

    Murmushi tayi sannan tace wai da nisa ne sosai?

    Ummi karki damu idan munje zaki gani”

     Tunda taji haka bata sake cewa komai ba, sai dai tarin tunani daya addabeta”

    Washegari tunda kafin Mukhart ya tafi masallaci yayi wanka, sannan ya tashi Ummi tare da fadin”

    Maza ki shirya mun yi dame motar ana fitowa masallaci zaixo”

   Jikin Ummi babu kwari ta shirya Ahmeed itama cikin sauri sauri ta shirya”

     Bayan Mukhtar ya dawo masallaci Ganin inda Ummi taci kwalliya tare da saka takalmi me shegen tsini Mukhtar yayi dariya sosai”

    Zunburo baki tayi kamar zatai kuka domin zuwa yanzun kwata kwata taji tafiyan ta fita kanta”

    Yadda Mukhtar ke kallonta yana dariya ta tabbatar wa kanta dariyar mugunta ce”

     Ahmeed ya dauka sannan ya zauna afakin gado shiru taga yayi tare da zubawa yaron ido”

    Ya dade ahaka zuwa can taga yana tufamai addu’oi”

    Sosai hankali Ummi yakara tashi, kamar tace mai ta fasa tafiyan, zuwa can tace”

   Hmmm me d’a, nima gaskiya sai mun biya gida Abbana yamin addu’a

   Dariya yayi sannan yace ban da wadda yayi miki jiya?

     Suna cikin haka wayar Mukhtar tai kara dan haka ya mike tare da mika mata Ahmeed shikuma ya dauki akwatin yana fadin taho mu tafi”

    Mamaki taji ganin Mukhtar dagashi sai jallabiya, acikin zuciyanta tace nufinshi ahaka zai tafi?

    Abaya suka zauna Ummi ta kwantar da Ahmeed agefenta tare da rufe shi sosai da zanin goyon shi, ajikin Mukhtar ta kwanta har sukayi tafiya me nesa Ummi tana bacci”

   Tun Ummi tana ganin tafiyan mai sauki ne harta fara gajiya, kwalkwal tayi da idonta lokacin da taga karfe 4:56pm sosai Mukhtar yake mata dariya tare da fadin”

    Haba Ummi tun bamu isa Niger ba kika sare”

    Kuka tasa tare da fadin ni gaskiya nagaji, ga Ahmeed ya dameni da tsotso”

   Hmmm kiyi hakuri kibashi ai kinci abinci”

   Daker ta yadda ta bashi nono sannan ta kudundune domin wani irin sanyi takeji”

    Damisalin 11:34pm suka isa garin, lokacin Ummi tayi bacci kashi kashi, Ahmeed ko banda kuka babu abin da yake”

    Mukhtar fadi yake ai mun iso Ummi yanzun zamu sauka”

    Abin da yabata tsoro shine tunda suka shigo gurin da Mukhtar yace nan ne hanyar dazata sada su da garin su suka daina ganin haske daga hasken fitilan motar su, saita aci balbal da suke hangowa, mamaki ma taji da taji Mukhatar yace ya isa haka, koya ya keyi yake gane garin oho”

    Mukharta ne ya fara sakkowa sannan ya dauki Ahmeed yace da Ummi sakko muje”

    Tana sako kafarta taji ya lumi acikin kasa dan haka ta kwallara kara”

    Afirgice Mukhtar yace menene?

   Wayyo wani abune ya janye min kafa”

    Wayar shi yasa ya haska, sannan yasa hannun ya jawo kafar tare da fadin”

    Daman Haka kike da tsoro, Sahara ce fah”

     Takalmin shi yacire ya mika mata sannan yace juyo bayan ki, ki goya shi saboda sanyin dare”

    Wahaye ne yazubu mata, tasa hannunta ta share sannan ta goya Ahmeed, muryan Mukhtar taji yace muje ko?

     Duk da bata ganin fuskan shi juyawa tayi ta kalle shi cikin muryan kuka tace”

    Ina zani?, al halin bana ganin gabana, wai ina ne gidan nifa nagaji”

    Ummi karki tadamin hankali, inace nagaya miki akwai tafiyar kafa dazamuyi”

    Cikin kuka tace Haba Mukhtar, banda tafiyan da mukayi amota kuma ace sai nayi ta kafa, ni gaskiya munemi guri mu kwana inyaso inna huta sai mu wuce”

   Wayar shi yasa ya haska fuskanta ganin hawaye face face yasa hankalin shi ya tashi”

   Kuka kikeyi Ummi?, toh naji barin shinfida miki zanin ki kwanta inyaso dasafe saimu karasa”

     A ina din zan kwanta?

   Anan mana, kinaganin komawa mu cikin gari abu me sauki ne?, kina ganin tafiyan da mukayi tsakanin nan da cikin gari”

      Cikin kika tace nidai wlh bazan iya kwanciya anan ba”

    To ki daure muje idan muka karasa saiki huta gaba daya”

    Haka Ummi ta daure taita tafiya hannunta cikin na Mukhatar bakajin komai sai kukan tsuntsaye , burinta kawai taji yace munzo, amman shiru, illah tambayanta da yakeyi Ummi ingoyaki ne?

    Cikin kuka take cewa a’a”

    Ahakali garin ya fara haske, sai alokacin ta kula adajin Allah suke bagida gaba, ba gida baya, baka ganin komai sai tarin bishiyoyi maso dogon zango, siririyar hanyace atsakiya daga ita sai mukhtar suka cika hanyar bataga alamar ankusa kawowa ba dan dogowan hanya take hangowa zukuku atsakiyar bishiyoyin…..

   *YANZUN AKAFARA😰*

   

     Maman Yazeed✨: 🔥 🔥🔥🔥🔥🔥

*KOWANNE BAKIN WUTA*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥

    ( da nashi hayakin)

💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by

    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*

    Wattpad @fadeelalamido

            *17 -18*

Juyawa tayi ta kalli Mukhtar tace”

    Yanzun acikin nan akwai mutanan da suke rayuwa?

     Kai ya daga mata almar eh”

     Shiru tayi zuwa can tace, wlh nagaji da wannan tafiyan”

     “Gyara goyon kizo na goya ku”

    Haba Mukhtar sai kace bani da imani, jifa inda kake tafiya kafanka babu takalmi, ni wlh banta tunanin kafan ka na taka kasaba ma”+

   Hmmm aike kikajamin da kika sako wancen takalmin, koda yake daman na saba idan na gaji da tafiya nakan cire takalmin”

    Kallo ta sake wurga mishi sannan tace toh wai neyasa babu mashin ne ahanyar nan”

     Gaskiya basa amfani da dashi, domin mutanan wannan gari basu cika zirga zirga ba, idan ma zasuyi kowanne gida suna da jaki, zuwan da nayi na karshe naga sun fara amfani da amalanke saboda daukan kaya”

   Jinjina kai Ummi tayi acikin zuciyanta tace”

    Da ace inada labarin garin nan gaskiya da bazan zoba”

   Juyawa tayi ta kalli Mukhtar tace”

    Amman dai yanzun mun kusa ko?

    Da sauran tafiya, ai idan mun kusa keda kanki zaki hango gari”

    Innalillahi wa inna ilaihir raju’un wlh da nasan haka garin nan yake da nisa da bazan zoba gaskiya”

    Hmmm Ummi kenan agabana?

    Turo baki tayi, sannan tace, haba dan Allah garin ya cika nisa, kuma gani da karamin goyo, jin inda kayana suka koma, dubi ma akwatin mu kamar anciro shi daga cikin kasa, ni yanzun ma tunanin yadda zamuyi mukoma gida nake yi, ji nake kamar munzo bayan duniya”

    Daure fuska Mukhtar yayi sannan yace”

    Idan zamu dawo ai da akwai jaki gidan mu dole zasu fito damu bakin garin, yanzun ma da ace sunsan da tahowan mu zasu turo mana jaki”

     Toh meyasa baka gaya musuba, tunkafin mu taho, ko daman ka shirya kaban wala ne shiyasa tun agida kake min dariyar da nasara dalilinta, ashe ta mugunta ce”

    Cikin fada yace gaskiya Ummi kina da korafi, tun dazun kike cimin fuska”

     Dif Ummi tayi bata sake magana ba, sosai taji haushin kalmar wai tana da korafi, duk wannan bakar wahalan da tasha begani ba?

    Tundaga lokacin bata sake magana ba tafiya kawai take”

    Abin da ta lura dashi har yamma ta fara gashi basujin kiran sallah babu azahar babu la’asar, kuma gashi tayi alkarin bazata sakewa Mukhatar magana ba da tace mai su tsaya suyi sallah”

      Zuwa can Mukhatar yace”

     Ummi wai fushi kike ne?, dan na gaya miki gaskiya?, Toh Allah ya huci ran ginbiya”

     Daker ya shawo kanta sannan yace ta sauke Ahmeed abashi nono”

    Ruwa ta fara bashi sannan ta bashi Nono, mai dashi baya tayi, sukai sallah sannan suka kama hanya”

STORY CONTINUES BELOW

    Sunyi kusan tafiyan awa daya, Mukhatar ya lura kamar Ummi rawan sanyi take, dan haka hankalin shi ya kara tashi”

    Tsunawa yayi agabanta yace hau, batai musuba ta haye bayan sa domin inda hali ma jikin shi zata shige saboda sanyin da takeji”

    Shima yayi tafiya me nisa da ita abayan sa, sosai ya gaji, sai dai baya son Ummi ta fahimci haka”

    Zuwa wannan lokacin ya fara hango garin nasu dan haka ya daure yana kokarin karasa wa, Ummi ku tacire tsammani dan haka bata kallon hanya lomo tayi abayan sa”

     Daga can ya fara hango amalanke yana tahowa dan haka yaja ya tsaya tare da fadin Ummi sauko”

     Zamewa tayi ta zauna akasa, tare da fadin dauki Ahmeed zan kwanta ne”

     Kwace shi tayi Mukhatar ya daukeshi tare da fadin inaganin yanzun zamu samu abun hawa”

    Ko kallon shi Ummi batayi ba”

    Tun kafin me tura amalanken yazo gaban su yafara fadin”

    A’a Muntari sai yau agarin??

   Dan Murmushi Mukhtar yayi tare da fadin”

   Wlh kuwa, aike ne ya rikeni”

   Juya amalan ken yayi tare da fadin kuzo muje”

    Mutumin ya mikawa Ahmeed, sannan ya dauki Ummi ya sakata aciki shima ya shiga ya zauna sannan suka fara tafiya”

    Sai alokacin idon Ummi ya fara washewa ta dobi mutumin dake saman jakin”

    Bakaken kayane ajikin sa, na saki, tare da makin takalmin roba”

    Wandonsa daidai guiwa rigar ko bazata wuce kwan kwaso ba”

   Duk da ta baya take hangosa ta shaida mutumin baki ne sosai mai tarin gashi”

    Wasu irin gini take hangowa wadda aka rufeshi da bakin tabo, dan beyi kama da fenti ba”

    Suna isa unguwar mutumin ya daga murya yana fadin muntari ya iso tare da iyalin sa”

   Mata da mazane sukaita lekowa tare da dagawa Mukhtar hannun”

   Shima hannu yaita daga musu, yadda Ummi ta lura duk mutanan garin bakin kayane ajikin su, basu hadawa da komai”

   Akofar wani gida suka tsaya, ahankali mutanan gidan suikata fitowa, tare da runguman Mukhtar”

   Daya daga cikin matan ne tace”

   Muntari kayi sauri  Ummayo tayi fushi dakai sosai kaje ka bata hakuri”

    Hannun Ummi ya jawo ya nufi cikin gidan da ita, dakin dake kallon su ya nufa sannan ya juya yacewa Ummi idan zaki gaida kowa agarin nan karkice inakwana, domin sun dauki hakan tamkar raini ne, sai dai kice Ankwana Lafiya?

    Gyada masa kai kawai tayi”

   Suna shiga dakin Mukhtar ya zauna akasa, itama Ummi zaman tayi kamar yadda taga yayi”

    Wata dattijuwa ce zaune itama da bakaken kaya, idonta sosai ya bawa Ummi tsoro dan haka ta dukar da kanta sannan ta gaidata”

    Lafiya kawai tace, nan danan Abdulmajeed ya fado mata azuciyanta dan shima amsa gaisuwan sa bata wuce Lafiya”

    Tashi Mukhtar yayi bayan ya gaidata ya mika mata Ahmed”

     Kura masa ido tayi sannan ta dago ta kalli Mukhtar ta fara yare”

   Sun dade suna yarawa yadda ta lura kamar fada ta masa, zuwa can Mukhtar ya waigo yace”

    Ummi tashi kije wancen dakin gani nan zuwa”

STORY CONTINUES BELOW

   Mikewa tayi ta kalle shi sannan ta kalli Ummayon  data rungume Ahmeed smirking a”

     Ahankali ta fice adakin  cikin matukar son ta kebe da mijinta tare da danta dan sai take ganin kamar ta shigo cikin wata hallita ce daban”

    Dakin daya nuna mata tashiga, babu laifi wannan dakin da haske bakamar na Ummayo ba dasai kayi da gaske kake gani, kuma akwai dan madaidaicin gado”

    Zama tayi abakin gadon tana son kwanciya amman ita tafison taga Mukhtar akusa da ita, tare da danta”

    Zuwa can Ummayon tashigo da Ahmeed ahnnunta sai tsala kuka yake”

   Ummi na mika hannunta daga ancire masa kayan dake jikin sa ansa masa bakaken kaya, harda wasu irin sarkoki”

     Hadiye miyo tayi sannan ta karbeshi, Ummayo na juya baya Ummi ta fashe da kuka, anya kuwa zata iya kwana agarin nan, ji take kamar tazo kenan, wayarta ta lalubo acikin jakarta ta lalubo number Ummanta domin neman mafita”

    Zaro ido tayi lokacin taga wayar na nuna babu Network”

    Kuka taci sosai cikin tausawa kanta, kwata kwata bata taba tunanin akwai irin wannan garin aduniya ba, ta tabbata inda iyayenta sunsan ina cikin irin wannan garin bazasu taba yadda ta kwana ba, zasuzo su dauketa”

   Kasa daina kukan tayi data kalli shigar dake jikin Ahmeed hankalinta ke tashi, wannan aisai mura ta kamashi”

    Zuwa can mutane sukaita shigowa ganinta, babu laifi suna sakar mata fuska sosai”

     Zuwa can taji ankira sallan mangariba, cikin sauri ta tashi ta goya Ahmeed ta fita”

    Buta ta dauka, wata yariya ta gani atsakar gida ita tambaya makewayi, bayan ta fito tayi alwala ta koma dakin”

     Bayan ta idar da sallah aka kawo mata wani irin bakin tuwo, inza’a kasheta bazata iya shaida na meye ba”

     Duk da tanajin yunwa amman bazata iya cin shiba”

    Bakin gadon ta koma tayi tagumi, ta kosa taga Mukhtar domin tace mishi inda hali su koma gobe”

     Saican dare ya shigo, ahankali Ummi ta sauke ajiyan zuciya”

   Murmushi ya mata tare da fadin”

    Yaya?, nasan bazaki iya cin abincin garin mu ba ko?

     Kai ta daga masa tare da fadin”

    Gaskiya karka kara tafiya ka barni irin haka”

   Dariya yayi sannan ya mika mata ledan hannun shi tare da fadin nama ne kici, kafin gobe na nemo miki wanne abun”

    Budewa tayi tana yatsuna baki ta fara ci”

   

    Mukhtar na ganin haka yai murmushi sannan ya sauka ya jawo tuwon da aka kawowa Ummi ya faraci”

    Bayan ummi ta gama gyatsa tayi sannan tace”

    Amman dai gobe zamu tafi ko?

    ‘Dagowa yayi ya kalleta,  har kin gaji ne?, kina nufin kwana daya zamuyi?, ai Ummayo bazata yadda ba, kina ganin ma sati dayan dana ce mata zamuyi tace a’a”

     Hawaye ta share sannan tace toh yanxun sai yaushe zamu tafi?

     Kiyi hakuri muyi sati 2 sai mu koma”

    Kuka Ummi tasa mai, tare da fadin wlh bazan iyaba, yanzun ma ji nake kamar abayan duniya nake, gaskiya ni  zan koma gida, inyaso kai ka taho daga baya”

    Ummi banson rigima fah, inace ke kikaita matsawa nakawoki2?

   Ai dana ce ka kawoni saika gaya min yadda garin yake, wlh da bazan zo ba”

STORY CONTINUES BELOW

    Shiru yayi badan yaji dadin kalamantaba sai gudun karya bata mata rai, zuwa can yace”

  Ki kara hakuri, kuma ki sake jikin ki, idan muka kwana biyu zaku saba”

    Kukanta ta cigaba dayi zuwa can ta dauko Ahmeed tace”

   Dan Allah dubi shigan da akamai saikace wani jinjirin aljanu😢”

    Jiba, Ummi cin fuskan ya isa haka fah, Ummayo tasaka mishi wannan kayan da hannuta, ki dinga sanin mgnr dazata dinga fitowa bakin ki “

    Share haye tayi sannan tace”

   Nidai cire mishi zanyi dan sanyi ake”

   Karki kuskure ki cire mishi, idan kuwa har kika cire mishi zaki samu matsala da Ummayo, ko ni ban isa inhana tasa mai ba bare ke, bavu abin da zai sameshi da yardan Allah, kuma bazan boye miki ba garin nan akwai bayu dan haka ki dinga addu’a kuma banda fitan dare”

  Mikewa Ummi tayi tare da fadin innalillahi wa inna ilaihir raju’un, Mukhtar meyasa kamin haka, meyasa zaka kawo ni garin nan?

    Cikin sanyin jiki yace kiyi hakuri Ummi, babu yadda zanyi ne, insha Allahu watarana sai labari, domin ina fatan idan Allah ya kara buda min zan maidasu can”

     Washegari tun da sassafe Mukhtar ya dauki Ahmeed akan zai shiga gurin Ummayo”

    Tun tanasa ran dawowan shi harta hakura domin ganin rana ta fara fitowa, nonowan ta taji sun ciciko, dan haka hankalinta ya koma kan Ahmeed ya kamata akawoshi abashi nono”

Tana cikin zaman jiran tsammani wani sauriyi ya shigo, kama suke da Mukhatar sosai, cikin fara yace ankwana lfy?

    Bayan ta amsa ya zauna akasa sannan yace”

    Ni kanin Muntari ne”

   Daker ta kakaro fara’a tace”

    Sannun ya sunan ka?

   Sunana Saminu”

   Murmushi tayi sannan ta sake cewa kuma be taba cewa min yana da kani ba”

   Allah sarki, ai duk gidan nan shine babba, mu 7 ne duk maza, amman yanzun mu 3 muka rage agida”

    Ganin inda ya sake jiki yana hira da ita sata fadin”

    Toh sauran mutuwa suka yi?

    Eh to yanzun dai babu tabbas dan neman su kawai akayi daya bayan daya aka rasa, shima Muntari lokacin da ya tafi, ancire rai dashi kamar yadda aka cire rai ga sauran, kwatsam sai gashi ya dawo, amman sai yace ba zama zaiyi ba, domin ya samu aikin yi a Nigeria”

    Shiru Ummi tayi tana nazari zuwa can tace”

   Toh daman yayi karatu ne”

   Sanda yabar gida beyi karatu ba,  saboda akauyen nan babu makaranta, amman tun zuwan shi na farko ya shaidawa Ummayo yayi karatu acan”

    Tabe baki Ummi tayi sannan tace”

   Amman sauran ‘yan uwan naku da suka tafi kun neme su kuwa?

   A ina zamu nemesu?, ai mutannan kyauyen nan basu cika fita daga cikinta ba, idan ko mutum ya iya fita abu ne me wahala ne ya dawo”

    Girgiza kai tayi tare da fadin”

   Suna da gaskiya Saminu ko nine wlh bazan dawo ba”

    Zaro ido yayi tare da fadin”

    Kiyi shiru kada Ummayo ta jiyoki, domin ita so take Muntari ya dawo gida, domin duk acikin mu tafi sonshi, sabo da sonda Ummayo takewa Muntare kullum take tafiya bakin yanki domin tajiyo Muryan shi ta dawo”

STORY CONTINUES BELOW

    Inane bakin yanki”

   Madakatar Mota”

Kana nufin inda mota ta sauke mu muka fara takowa akasa?

   Eh yace tare da tsareta da ido”

    Cabdi, toh mezaisa sai daje can sannan tai waya?

       Ai mu garin mu waya bata amfani, ko Muntari inyazo da tasa saidai yayi fitila da ita, amman da anje bakin yanki shi kenan”

    Sosai cikin Ummi ya kara duran ruwa, batasan lokacin da tace, gaskiya da nasan haka garin ku yake da banzo ba, hawaye ta share tare da fadin gashi yace min akwai mayu”

  Eh akwai su, amman ai mun sansu, kanta sankar ne, basa ma ‘yangari komai sai bako, bakon ma indai ansanar masu da zuwan shi basa tabashi”

     Amman dai gaskiya garin  nan bashi da dadi gani nake kamar nazo bayan duniya”

   Ai nima Muntari yace zai roki Ummayo nabiku dan nayi karatu acan”

   Hmmm Allah yasa ta amince”

    Shigowan Ummayo ya katse masu hiran , abinci ta ajiye tare da kallon Saminu tace”

     Sarkin surutu kana nan daman?

    Eh ina taya maman Ahmeed hira”

   Juyawa tayi sannan tace maza taso ka dauki Amadu ka kaishi gidan b’agelu domin tasan da zuwan su”

   Mikewa yayi yana fadin Ummayo ai basai ankaishi ba, barin infada mata kawai”

    Bataji abin da Ummayo tace ba, dan haka hankalinta ya tashi gashi babu waya bare ta kira Mukhtar ta sanar mai, tunda taji ance Amadu wata kila Ahmeed dinta ake nufi”

   Kuka taci sosai rabota da Ahmeed tunda duku duku da Mukhtar ya fita dashi, gashi har mangariba nashirin zuwa, kuka taci sosai idonta yayi jajur”

    Sai bayan isha’i Mukhtar ya shigo, ganin Ummi cikin kuka hankalin sa ya tashi”

    Cikin sheshshekan kuka take gaya mishi anhanata danta tun safe”

   Ahankali Mukhtar ya shiga lallashinta tare da kwatar mata da hankali”

    Amman ina dukkansu kwana zaune sukayi domin Ummi kin bacci tayi ita sai ankarbo mata danta”

     Mukhtar hakuri yaita bata domin karboshi yana iya zama musu babban matsala gara su jira harta kawo shi da kanta”

    Kiran sallah farko Ummayo tai sallama abakin kofar sannan tace ga Amadu”

   Mikwa Mukhtar yayi ya amsoshi, rungumeshi Ummi tayi, tare da saka kuka, sai dai abin da ya bata mamaki koda tasa mai nono abaki kin sha yayi, saima gyatsa da yake, kuma babu alamar wahala ajikin shi, sai tsiltsilah kafa yake tare da zillo kamar yaddda lafiyayyun yara ke yi”

   Cikin mamaki tace kaga yaki shan nonon”

   Damuwa tagani karara afuskan shi, sannan ya mike yana kokarin fita yace, ai nasan Ummayo bazata barshi da yunwa ba”

    Tsurawa yaron ido tayi tana hawaye take fadin kazo sabowar duniya yaro, inbanda haka yaya za’ayi ko wata uku yaro biyiba adura mai jagwalgwalo”

   Adaddafe Ummi suka caka kwana goma sha Uku da zuwa garin, shirye shirye Ummayo ketayi zasu tafi gobe, Ummi jinta take kamar wadda akawa bishara da gidan aljannah”

    Daren ranan ne kuma tajiyo fadan Ummayo, gaskiya Ummayo masifaffiya ce, tunda yazo garin bata taba ganin fara’arta ba, da alama babba laifi aka mata dan taji muryan mutane sunata bata hakuri”

    Zuwa can Mukhtar ya shigo dakin yana huci, kafin ta ankara wata tsowa ta shigo tana fadin haba muntari hayi hakuri ka barmata shi”

   Cikin sauri ya mike ya fita, abin da ummi ta lura dashi baya son ta fahimci abin da ake mgn akai

     Zuwa can ya dawo ya zauna yana kokarin kawar da damuwa, acikin zuciyarta tace, wata kila Ummayo ta hana shi tafiya da saminu ne, dan haka ko ajikinta taita hada kayan su”

   Shiko Mukhatar sai dai ya kalleta ya kuma kalli Ahmeed tare da fadin”

    Gobe sai gida ko?

Cikin murmishi take gyada kai acikin zuciyanta take fadin, har abadah bazan sake zuwa garin nan ba”

    Ranan bata iya runtsawa ba, da asuba Ummayo ta buga musu kofa, cikin mamaki Mukhatar ya bude, inda tayi fushi dashi jiya be zaci zata huce nan kusaba”

   Yana budewa tace kutashi ku shirya karkui dare”

    Sosai Mukhtar yai murmushi sannan yace”

   Ummayo kiyi hakuri, ba’ason raina na miki haka ba, yayi kankanta ne”

    Ba komai Muntari nafahimce ka, kuyi sauri jakin saminu zaija amalanken ku”

    Cikin sauri ya juya yacewa Ummi jekiyi wanka, barin kai Ahmeed Ummayo tamai dan mufi sauri shiryawa”

    Ummi na dawowa tasamu Mukhatar agado, yadai tafada tana kare mai kallo”

    Dan danan ya yake hakuri, tare da fadin, ke nake jira, amman inajin kamar ma kada nayi wankan”

    Nidai kaje kayi kawai mutafi”

   Murmushi yayi ya fice, fitan shi ba dadewa Ummayo ta leko tana fadin”

    Ke Zainab fito da kayan ku ga jakin Saminu ya iso”

    Wani irin murna Ummi taji tare da farin ciki yau zatabar wannan gari da batai tunanin bari ba, akwatin ta dauko ta daura a Amalen kenan sannan ta Saminu ya dauko buhun kayan da Ummayo ta ahada musu yasa aciki”

   Ummayo ce ta mikawa Saminu Ahmeed cikin shiga irinta al’dar garin su, ba bakin kaya idon nan anrangada mishi kwalli”

    Saminu ne yace ma Ummi kishiga ki zauna kafin yazo”

   Cikin Amalenken ta zauna sannan ya mika mata Ahmeed tare da fadin barin yiwa Muntari magana yai sauri dan inason na dawo ayau, naga ya jima sosai”

   Ummi ko mutanen garin ne suka kewayeta sunata mata sallama itako sai murmushi take”

    Ta gefen ido take hango yadda Ummayo take banka mata harara dan haka taki yadda su hada ido”

    Ihun da Saminu ya kurma yas gaba daya suka maida hankalin su hanya da suke jiyo ihun”

    Ummayo ce ta farabin hanyan sannan sauran suka rufa mata baya”

   Cikin mummunan faduwan gaba Ummi ta fito daga cikin Amalanken tare da kara rukunkume danta ta nufi hanyar makewan domin sanin dalilin Uhun Saminu……..

     

     *Zan dakanta anan sai bayan Sallah idan mekowa me komai ya kaimu, inama kowa fatan alheri, Allah yasa ayi Sallah lafiya👏🏻*: 🔥 🔥🔥🔥🔥🔥

*KOWANNE BAKIN WUTA*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥

    ( da nashi hayakin)

💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by

    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*

    Wattpad @fadeelalamido

  

             19 – 20

Tunkafin ta karasa ta hango Saminu rike da Mukhtar, daker yake tafiya yayin da zufa ke ke karyo mai”

    Arikece take fadin”

   “Menene ya sameshi?

     Maciji ne ya sareshi cewan saminu cikin kokarin tallabe Mukhtar yake fadin haka”

   Innalillahi wa inna ilaihir raju’un na shiga uku na lalace, Kuka tasa sosai tare da kara rungume Ahmeed”

   Ummayo dake rikice fifita kawai takewa Mukhtar, tana fadin”

    Muntari saikace bako?, amatsayin ka na haifaffan kyauyen nan ka tsaya maciji ya sareka?

     Mukhtar dake cikin azaban radadi nishi kawai yake”

    Bayan sun kaishi dakin su, Ummayo ce takoma dakinta ta hadu duk abin da sukewa mutum da zaran hakan ya faru, bayan ta shafawa Mukhtar magani agurin ta bashi wani ya sha”

    Ya dade yana cikin azaban radadi, ko idonsa baya iya budewa”

   Sosai Ummi ke kuka kaman ranta zai fita, goya Ahmeed tayi sannan ta zauna akusada Mukhtar tacigaba da zubar da hawaye”

   Ganin inda yake hada zufa, yasa Saminu ya dauki mafice yana masa fifita, Ummayo ma na tsaye akansa tana fadin”

    Kai muntari har yanzun be lafaba?, zaga iya gane launin majicin?

     Cikin mawucin hali ya girgiza kai”

    Tashin hankali Ummayo ta fada, sannan ta juya tace da Saminu, jeka fadawa sabowa”

    Cikin kuka Ummi ta kalli Ummayo tace”

   Mama akaishi Asibiti mana”

    Waigowa kawai tayi ta kalli Ummi cikin fada tace”

    Mu tunda muke bamu taba zuwa asibiti ba, dan hakama bamu dashi agarin nan”

  Sunkuyar dakai Ummi tayi sannan ta sake cewa”

    Mama toh afiddashi cikin gari mana”

   Ke karki kawo min rashin kunya, kina nufin kin raina mana ne?, kakan kakan shima anan aka haifishi, annan sukai rayuwa har suka haifemu, kuma basan wani avu waishi asibiti ba sai dai muji labari, sai yanzun kice zaki tsara min yadda zanyi da d’ana”

   Sadda kai Ummi tayi kasa tana share hawaye, zuwa can sabowa ta shigo”

    Wani garin magani ta zuba agurin sannan sannan ta dago tana mai sannu”

    Tun yana daga kai alamar yana amsawa harya fara bude idon sa”

    Dagowa Ummi tayi suka hada ido da Mukhtar, murmushi ya mata sannan ya dago hannun shi ya mika mata”

   Kukane ya kara kwace mata, ahankali ta mike ta karasa kusa dashi”

    Hannu yasa ya kwantar da ita ajikin shi tare da shafa kanta, yana fadin yi hakuri, ki daina kuka”

   Ido matan dake gurin suka zuba musu, ganin inda Ummi ke shashshakan kuka yasa Mukhtar ya daga kanshi ya kalli Saminu yace”

     Saminu muje ka kaimu bakin yanki mu wuce na samu sauki”

STORY CONTINUES BELOW

    Kul Ummayo ta fada tana mai nunawa Mukhtar yatsa, kana cikin wannan halin zaka tafi?, kafi kowa sanin saran Macijin garin nan kana sane sarai, zaka saida ranka ne akanta?

    Bakomai Ummayo zan tafi, can akwai manyan Asibitoci dazasu bani magani karki damu”

   Hannu Ummayo ta daga ta nuna sama tare da fadin”

    Kwarankwatsa dubu bazakabar garin nan ba har sai kawarke sarai”

    Kan Ummi ya shafa, sannan yace”

   Toh naji, Ummayo zan zauna, amman inason kibani dama na raka Ummi bakin yake ta tafi, inyaso ni idan na samu sauki sai intafi”

    Wani irin damka Ummi tamai tare da fadin idan na barka anan hankalina bazai kwantaba, juyawa tayi ta kalli Ummayo tace”

   Mama dan Allah kiyi hakuri ki bari mutafi”

   Eyyee lallai, wato kin fini son d’ana, to bari kiji idan har kina matsayin matar shi dole ki tsaya kiyi jinyar shi, ban yadda ki tafiba, afusace Ummayo ta juya ta fita”

     Suma sauran matan juyawa sukayi sukai waje dan haka Ummi ta kara shigewa jikin Mukhtar cikin matsanancin kuka tace”

    Yanzun meye abin yi?

   Shafa kanta kawai yakeyi ya kasa cewa komai”

    Haka Ummi ta zauna cikin tsananin damuwa da fargaban rashin sani yaya rayuwar su tayi yu wannan garin”

    Sosai mutanan garin ke zuwa duba Mukhatar yadda ta kula ya saba da mutanan garin sosai, kowa yazo da irin shawaran dayake bayarwa akan maganin dazai sha”

    Washegari Mukhatar kasa tashi yayi, sosai kafar shi ta rike, ahalin ya kira Ummi”

   Zumbur ta shi ta zauna”

   Nakasa mutsa kafata Ummi”

    Acibalbal din dake dakin ta dauka ta haska kafar, innalillahi wa’inna ilaihir raju’un ta fada, sannan ta matsa ta dagashi”

   Wani ruwa ne yake fitowa daga cikin kafar tayi wani kwaba kwaba kamar wadda tai watanni tana ciwon”

     Tunda ya daura idon shi akan kafar ya fara hawaye, sannan ya juya ya kalli Ummi tare da fadin”

   Ummi yazama lallai zaki tafi ki barni agarin nan, idan ko ba hakaba akwai matsala babba”

    Kuka Ummi takeyi har fuskanta zafi yake mata sabo da kukan da taci, ayanzun bata da wani buri Illah ta ganta a Nigeria, amman tana bakin cikin tafiya tabar Mukutar a nan”

     Kiramin Ummayo, Mukhtar ya fada yana kara yamutsa fuskan shi”

    Cikin rashin kwarin jiki ta fita”

   Ummayo ce ta fara shigowa sannan Ummi ta biyo bayanta”

    Muryan Mukhtar taji yana fadin”

  Ummayo, kinga kuma yaddda kafata ta koma”

    Abin dayabawa Ummi mamaki gani tayi Ummayo ta fara kuka sosai, zuwa can ta zauna ta riki hannun Mukhtar”

   Ahankali yace Ummayo dan Allah inason Ummi ta koma Nigeria

    Bata iya magana jinjina kai kawai take, kuma har yanzun hawaye bebar zubo mataba”

   Ummi dake manne abango hawaye ke zubo mata tare da majina alokaci guda, wani irin daci takeji acikin zuciyanta mara misaltuwa”

   Ummi na kula da Ummayo wunin ranan tayita ne cikin kuka, dan haka ko abinci ba’a daura ba”

    Shima Saminu tunda yaga halin da Mukhtar ke cikin ya kifa gai ajikin sa har aka kwashi tsayon lokaci be dagoba, sadda ya mike kuwa idon shi jawur, ya fice”

STORY CONTINUES BELOW

   Washegari da safe ma kafar Mukhtar tafi ta jiya, Saboda kuka fuskan Ummi kunbura yayi”

   Ranan daya cika sati daya da wannan ciwo jikin shi yai zafi sosai dan haka ya rike hannun Ummi hawaye na zuba afuskan sa yake fadin”

   Kiyi hakuri Ummi, ban san cewa haka zata faruba, naso ace muyi rayuwa me tsayi nida ke, amman hakan ba zai yiyuba, dole zan tafi nabarku badan raina yasoba, kuma abin bakin cikin, shine zantafi da barki acikin wannan gari da babu komai acikin sa illah tarin takaici, dan Allah Ummi kar kibar Ahmeed agarin nan, nayiwa Saminu mgn zai taimakeki zuwa bakin yanki, acikin akwatin mu akwai kudi, nabaki duka, kiyi amfani dashi, idan Ahmeed ya girma ki sanar mai ina tsananin son shi, Allah ya albarkaci rayuwar ku”

    Cikin kuka Ummi tace”

   Bangane ba Mukhtar kai ina zaka?

   Ba inda zani Ummi, inanan, ina gaya mikine dan wata rana ki tuna nagaya miki, kuma ina neman afuwanki kiyafe min👏🏻”

    Na nayafema Mukhtar, nima ka yafemin😭👏🏻

    Bakimin komaiba, idan ma kin min nayafemi ki, nine na miki laifi Ummi, ki sani, zantafine da bakincinkin barin ki danayi anan”

    Nifa bana gane wannan mgnr taka mekama da ta tsuniya, sun isheni haka ka bari”

   Toh nabari Amman kiramin Ummayo”

   Lokacin da Ummi suka shigo da Ummayo daker Mukhtar ke numfashi kuma yana mgn amman ba’ajin abin dayake cewa”

   Zama Ummayo tayi kusa dashi tasa kunnenta asaitin bakin shi, Ahankali tafara jiyo abinda yake fadin”

    Ummayo Ummi ta tafi da Ahmeed, karki ansheshi”

    Shiru taji dan haka ta dawo da kallonta gurin shi”

    Salati tasa, tare da kururuwa, Ummi naganin haka ta karasa jikin shi, girgizashi take iya karfinta”

   Ganin babu alamar zai mutsa ta zame akasa, bata kara sanin me ake ciki ba, sai ganinta tayi sheme akasa”

  Mutane tagani cike da gidan, kowa ita ya zubawa ido”

   Ummayo ce ta fito tana fadin ta farko?

    Wata tsuhuwace tabata amsa da eh”

   Kamata tsohowar tayi suka shiga dakin Ummayo, riga ta dauko abakin gado baka ta mika mata tare da fadin ungu saka kinji yariya, Allah yaji kanki, mutuwan miji akwai daci”

    Da taimakon matar Ummi tasa rigar sannata taimaka mata ta daura zanin, wanni zanin aka dauko mata ta aka rufa mata”

    Tsowar ce tace wannan shine cikar takaba, karki sake kibari mayafin ya sauka akanki”

  Ummi dai ba baka sai kunne, saidai jefi jefi hawaye na zubo mata”

    Tanaji tana gani aka shirya Mukhtar anan dakin Ummayo aka tafishi, daidai lokacin Ummayo da Ummi sunyi kuka kaman ransu zai fita”

   Bayan akai Mukhtar makwancin sa andawo, Saminu ya shigo dakin Ummayo, yana share hawaye yace”

   Maman Amadu dauko Ahmeed kizo muje”

    Ina zamuje?, cewar Ummayo data tsare Saminu da ido”

   Ummayo munyi da Muntari tunjiya, yace min idan ya mutu karna kara awa biyu ban fita da Su bakin yanki ba”

   Mikewa Ummayo tayi cikin tsananin tace”

   Kuna nufin zaku hadamin zafi biyu, yau yau da rasuwan shi zabar garin ko takaba zata tsaya tamai ba, toh idan zata tafi ga hanya nan amman ban da Amadu, dan ba zanyi biyu babu ba, dole tabar min shi don indinga ganin shi amakwafin Muntari na, idan ko har ka kuskura kuka yaudareni Allah ya isa”

STORY CONTINUES BELOW

    Sunkuyar dakai Saminu yayi cikin rashin kwarin jiki, zuwa can ya dago ya share hawaye sannan ya juya ya fice”

    Atakure Ummi ta zauna ko motsi ta cika sai kawayen Ummyo su bita da ido tare da fadin”

    Wannan ko tana son Muntari ?, jifa inda ta kasa natsuwa bare ta tsaya tamai ingantacciyar takaba”

   Dasun fadi haka Ummayo ke dagowa ta gallah mata harara”

   Dole take sawa ta dukar dakai, tare da zubar da hawaye cikin zafin zuciya, tare da nadama me tsanani, maganar mahaifitace ta fado mata, ranan da ya shigo har dakinta yake kara tabbatar da ra’ayinta yake cewa”

   *Ummi kin dai dage Mukhtar din kike so ko?*

Shirun da tayi yasa Abba ya kada kai ya fita, sosai hawaye yake zubo mata acikin zuciyarta take cewa”

  Nasan ina tsananin son  Mukhtar, kamar yadda shima yake sona, iya zaman mu na shekara daya, da wasu watanni da mukayi bamu taba samun matsala ba, kuma ban sameshi da wani mummunan hali ba, illah na boye min aslinsa, ashe ya boyemin ne dan yasan basu da d’abi’a, meyasa nabi son zuciyata bayan iyayena sunso suyimin gata, sunso su nunar dani illah dake cikin auren wadda bakasan cikkakiyar asalin ba, amman nacewa Ummana nishi nake so, ai bada ‘yan uwanshi zan zauna ba”

    Ahankali tasa hannu ta share hawaye sannan taci gaba da cewa”

    Gashi yau Mukhtar ya tafi yabarni acin bakin garinsu, Tsakiyar dajin Allah, kuma acikin ‘yan uwanshi masu bakar akida, yaya zanyi inbar garin nan?, gashi Ummayo nason ta hanani d’ana, bazan iya tafiya nabar shiba wlh”

   Batasan sannan da ta kurma uhu ba tare da fadin”

     Wayyo Allah na nashiga uku, yaya zanyi? Me zanyi naji dadi?, Allah ka kawo min agaji”

    Wata daga cikin kawayen Ummayo ce tace”

    Zaman yariyar nan bazai yiyuba anan ya kamata abude dakin takama asata, inba hakaba kuwa, zata mai gurbatacciyar Takaba”

              **  **

        Yau haka nan Abdulmajeed ya tashi da bacin rai, dan haka ya kunna abin daya saba dayaji baccin ran nashirin taso masa, duk da ayanzun ya rage tunanin Ummi, dan yana da abubuwa biyu maso rage masa damuwa, wato Sigari da Nafisa, dan ayanzun ji yake tamkar bazai iya rabuwa da Nafisa ba, hakama sigari”

    Be ankaraba yaji anturo kofar, cikin sauri ya daga kansa ya kalli kofar”

    Momy yagani tsayi cikin tsananin baccin rai, ahankali sigarin ya zame kasa, azabure ya mike tare da fadin Momy?

    Hannu ta daga masa tare da fadin”

    Daman abin da kakeyi kenan?, Abdulmajeed haka ka koma kuma?, yau she ka fara wannan d’abi’ar, Abdulmajeed abin da ka zabawa kanka kenan?, toh yayi kyau, duk abin da akace kayi bazanyi mamaki ba, nagode, Allah ya saka maka da alheri, Allah kuma ya shirye ka, matse hawaye tayi sannan ta juya ta fita”

    Sosai jikin Abdulmajeed yai sanyi beji tahowan Momy ba, dabe bari ta ganshi ba”

     Tsaki yaja, sannan ya nufa dakin Momy, tunda ya tunkari dakin ya fara jiyo muryan Umma, tana mgn cikin kuka”

     Tsayawa yayi abakin kofar ya kasa kunne sa, kasa kasa yaji Umma na cewa”

    Sati guda fah tace zasuyi, gashi yau har sati 3 basu babu labari, kuma abin dayafi bani tsoro tunda suka tafi basuyo waya ba”

    Babu komai insha Allahu ai Lafiya ke buya, kuma ai kinji tace mamar sa ce ta matsa, wata kila ita ta dage sukara mata kwanaki, cewar Momy dake kokarin kwantar wa Umma da hankali”

STORY CONTINUES BELOW

    Hmmm, wlh naji ajikina akwai abin daya faru, tunda Ummi ta tafi bana cikkaken bacci, gashi inayin munanan mafarkai akanta, ko jiya tashi nayi na zauna dan dana rufe ido, Ummi nake gani tana matsanancin kuka tare da kiran sunana”

      Jikin Abdulmajeed sanyi yayi gaba daya, take tunanin Ummi ya bijiro masa, ahankali ya juya ya koma dakin sa, nan ya shiga tunanin yana son yasan wanni hali take ciki”

     Zuwa can yaji tsayuwar mota, dan haka ya tashi ya fito, a daidai lokacin daya isa Palo, Abba da Daddy suka shigo palon, yadda ya kula dukka zuciyoyin su babu dadi”

   Bayan sun zauna Su Momy ma suka fito, gaida su yayi gaba dayan su sannan shima ya zauna akasa”

    Umma ko har yanzun share hawaye take, Daddy ne yai gyran murya, tare da cewa”

     Hajiya ki daina kukan nan, insha Allahu Lafiya lau zata dawo, amman dai kuskure munriga munyishi, sai dai kuma akori gaba”

    Momy ce ta kalli Daddy tace kun samu Alhaji yaron kuwa?

    Eh, mun same shi, sai dai shima abin takaici besan takamaimai dan wanne jaha mane a Niger din, sannan yace shima tuntuni yake gwada numbar dasu iyayen sa suke ki ranshi ta ida amman bata zuwa, agaban muma ya sake kira, amman bataje ba”

   Innalillahi wa’inna ilaihir raju’un Umma ta fada tare da rushewa da kuka”

     Momy ce tace, gaskiya Alhaji kuma kunyi kuskure ai tun kafin ku amsa zancen Mukhtar ya kamata kusan suwaye iyayen sa”

    Abba ne yayi karaf yace, ai ni tunani na tunda Alhaji Yaro yasan iyayen sa zancen bincike ya kare”

    Shiru palon yayi bakajin komai sai tashin kukan Umma”

Daddy ne ya katse shirun da fadin”

    Yanzun dai kowa ya kwantar da hankalin shi karma kubari Hajiya taji wannan mgnr, ya zama dole mu binciko inda Mukhtar yakai Ummi, dan d’an mutum ba abin wasa bane”

    Har sukayi, suka gama Abdulmajeed bece komai ba, agurin suka watse suka barshi”

   Bayan Momy ta raka su Umma sun wuce ta dawo ta wuce Abdulmajeed a Palo ta shige dakinta”

    Shima Abdulmajeed mikewa yayi yabi bayanta, domin akwai karin bayanin da yake nema gurin Momy, sai dai, abin mamaki yana yin sallama tace”

   Abdulmajeed karka kuskura ka shigo min daki, kafi kowa sanin cewa duk wani me busa hayaki, bana zama kusa dashi”

    Dakatawa yayi, tare da dafa kofar, shiru yayi na wani lokaci, zuwa can yace”

    Am….. Momy dan Allah kiyi hakuri, nima ba ason raina bane lalura ce, kuma insha Allah zan bari”

    Ni kake gayawa lalura dan ubanka?, toh kabari inzo gurin zakaga lalura”

    Shiru yayi zuwa can yasake cewa”

    Momy kiyi haku dan Allah karki fushi dani, shiru yayi yana jiran jin me zata ce, shirun dayaji na kusan minti 5 yasa ya kara cewa”

    Momy, na shigo?

  Nan ma shiru dan haka ya kada kai cikin tsananin baccin rai yai waje”

    Gidan Sadiq ya nufa, sosai Sadiq yaji mamakin Ganin sa, bayan sun gaisa Sadiq yace”

   Daga ina haka?

Nisawa Abdulmajeed yayi sannan yaja tsaki yace”

    Sadiq waini yaushe zanji dadin ne, narasa inda zamsa kaina, kuma abin takaici yau Momy ta kamani da Sigari, sannan Ummi sunyi ta fiya ita da wannan wawan yaron, yau sati 3 kenan babu labari”

    Shima Sadiq nisawa yayi sannan ya kalli Abdulmajeed yace”

    Yayi kyau Abdulmajeed gara da Momy ta kamaka, saura Nafisa ahankali wata rana inbaka bari ba asirinka zai tonu, kuma inace nan ka gama cika baki cewa baka son Ummi, amman gashi ka kasa cereta azuciyarka, duk ka zama wani iri, ta dalilintaSai anyi mgn kace bason ta kake ba”

   Nifa matsala ta dakai kenan, ina tare dakai amman bakamin fatan alheri, idan ba mugun nufiba, yaya za’ayi ka dinga min fatan tsiya, nifa ayanzun bazan iya rabuwa da  Nafisa ba, dan haka na yanke shawaran  aurenta zanyi, Ummi kuma nace maka ban sonta, koka yarda ko kada Allah yasa ka yarda bazan taba son Ummi ba,  nakula bakasan koni waye ba, amman inaji ajikina, nan gaba kandan zaka sanni sosai, Abdulmajeed ke fadin haka idonshi jawur, sannan yaci gaba da cewa”

   Bazan taba son Ummi ba, kamar yadda kake tunani, barin gaya maka, Natsanin Ummi da Mukhtar kai hatta dan da suka haifa bana kyaunar ganin shi, kaga kuwa babu wata soyayya atsakanin mu, kamar yadda ta bude baki acikin bainar jama’a tace bata sona! kuma damuwan da kaga nayi, nashigeshi ne saboda halin danaga iyayen mu aciki, dan haka na dauki alkawarin zan bincikota aduk inda take dumin farin cikin iyayen mu, wlh☝🏻 ko duk matan Duniya zasu kare bazan so Ummi”

: 🔥 🔥🔥🔥🔥🔥
*KOWANNE BAKIN WUTA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    ( da nashi hayakin)
💨💨💨💨💨💨💨
Story & Written by
    *Fadeela Lamido*
*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*
    Wattpad @fadeelalamido
    *SADAUKARWA*
Hannatu Adam
Faiza Musa Bunu
Maman Zaran
Hussaina Faji
Mmn kayra
Mmn Fahad
preety Zeee
Mariya
Deejahr
Nanacy
Beauty
Hadiza Tinau
      &
Hafsat Yusuf
👍🏻👍🏻👍🏻👍🏻
+
          *21 – 22*
Dariya sosai Sadiq yayi zuwa can ya dakata da dariyar yace”
   Abdulmajeed kenan wani lokacin kana bani dariya, kamar yadda wani lokacin kake bani haushi, amman koma dai menene nan gaba zan tabbatar dashi, yanzun dai meye abin yi?, ko zamuje na rakaka kabawa Momy hakuri ne?, amman saika min alkawarin bazaka kara shan sigari ba”
    Cikin sauri yace nayi insha Allahu zanyi kokarin ganin nabarta”
     Dahaka suka kama hanyan zuwa gurin Momy, tana zaune apalo ganin Abdulmajeed tare da Sadiq yasa ta daure fuska”
    Nesa da ita Abdulmajeed ya zauna sannan Sadiq ma ya zauna tare da mika gaisuwa”
    Cikin daure fuska Momy ta amsa, sannan shiru ya ziyarci palon”
     Ganin inda Momy ke daure fuska, shi kanshi Sadiq ya tsorata, dan haka daker ya iya bude baki yace”
   Momy munzo ne domin mubaki hakuri, dan Allah kiyi hakuri Abdulmajeed yayi alkarin bazai kara ba”
  Hmmm, Sadiq, kaima haka kake?, karka yadda ka biyewa Abdulmajeed ku zama makaryata kuma munafukai, ko bakaga shi ko aure ya kasaba?, kasan me yake aikatawa? tunda har ya iya busa hayaki Allah kadai yasan abin da yake aikatawa, wlh Abdulmajeed yabani tsoro”
    Baya aikata komai Momy, auren ma ai ya kusa yi, ya samu yariya, dazanran sun gama daidaitawa zai kawo zancenta gida”
    Kauda kai Momy tayi sannan tace shi dai ya sani, kuma nariga nagaya masa indai yana son yagani kamar dah sai ya gyara halin sa”
     Ai yama bari Momy insha Allahu”
    Dahaka Momy tabar su afalo, Abdulmajeed ko be iya cewa komai ba”
   Washegari Abdulmajeed ya tashi ta tunanin hanyar dazaibi ya gano garin su Mukhtar, besan meye dalili ba, hakanan yakejin yana son yasan inda Mukhtar yakai Ummi har tsayon wannan lokaci basu dawo ba”
       ** **
Itako Ummi rayuwa ta mata tsanani, tunda kawayen Ummayo suka sa aka sakata wani daki wai da sunan dakin takaba, saita wuni bataga gilmawan mutum agurin ba, ko Ahmeed ba sosai ake batashi ba, yana gurin Ummayo so daya ake batashi arana kuma baya wuce awa daya take dawowa ta dauke shi, su biyu ake kawo mata abinci arana tun bata iya ci  harta saba”
    Kullum cikin hawaye take tare da data sani me tsanani, sai dai kuma mafiya yawan lokuta tanajin kewan Mukhtar na tsananin damunta, tare da tausaya mai, akowane lokaci tana mai addu’a domin kafin zuwanta wannan kyauye taji dadin zama dashi, bazatace ga wani abu mummuna wadda Mukhtar ya taba aikata mata ba, kuma ta tabbatar wa zuciyarta ba’a son ransa yabarta acikin wannan garin ba, asalima beso zuwa ba, dan babu yadda zaiyi ne, dan haka batajin zafinsa’ tasan kaddara ita ta kawota garin nan tare dabin son zuciya”
   Irin wannan tunanin Ummi ke wuni tana yi tare da zubar hawaye”
   Tunawa tayi da lokacin da zasu shigo wannan kyauyen yadda Mukhtar yaita tarairayanta, har takalmin kafarsa ya cere yabata shiya tafi haka, sannan yaki nuna gajiyar sa duk da cewa yagaji din, amman be nuna ba haka ya dauketa daga ita har Ahmeed ya goya, yai tafiya me tsayi bace ya gaji ba”
STORY CONTINUES BELOW
   Cikin matsanancin kuka tace yaya zanyi na koma gida?😭 idan nakasa tafiya da takalmin kafata, waye zai cire nashi yabani?, 😭haka idan nagaji har na kasa tafiya waye zai goyani?😭, waye zai bani cikkayar kulawan sa har na koma gida kamar yadda Mukhtar yabani?😭😭😭, kuka take sosai xuwa can ta sake cewa”
    Bansan ranan komawata gidaba, tunda Ummayo tace bazata bani Ahmeed ba, ni kuma bazan iya tafiya nabarta ba, dan da inbar Ahmeed agarin nan gara ya mutu nasan mutuwa yayi”
    Washegari da safe Ummayo tashigo da Ahmeed ahannunta mikawa Ummi tayi, cikin rawan jiki ta karbeshi tare da samai nono abaki, abin da Ummi ta lura dashi yaron be wani damu da nono ba atunanin ta kamar akwai abin da Ummayo ke bashi”
    Dan kadan yasha yacire bakin shi, tare dabinta da ido, itama idon tazuba mai tare da zirarowan hawaye”
    Ummayo ce ta miko hannu ta amsheshi tayi waje”
    Hawayen Ummi ta share sannan ta shiga tunanin da ta saba”
    Muryan Saminu ta fara jiyowa yana tahowa, wani wawan ajiyan zuciya ta sauke, domin shika dai yake sakar mata fuska”
    Shigowa yayi tare da sallama, bayan Ummi ta amsa mai ya nemi guri ya zauna, gasuwa ya kara mata, sannan duk sukai shiru na wani lokaci”
    Zuwa can yace”
   Mmn Amadu, nazo ne nabaki shawara, kinga zaman ki agarin nan bazai yiwuba, dan banga amfanin zaman ki ba, kamata yayi kije gida kamar yadda Muntari ya fada, naso na fitar dake tun ranan da Muntari ya rasu, furucin Ummayo nacewa lallai sai anbar mata Ahmeed yasa nabar mgn, dan haka yanzun ina baki shawaran ki tafi kawai kibarshi, Ummayo tana son Ahmeed sosai babu abin da zai sameshi, kuma kinga yanzun ya saba da Ummayo”
    Mikewa Ummi tayi, cikin tsiyayan hawaye tace”
    Saminu bazan iya tafiya nabar shiba, domin tafiya nabar shi yana nufin mun rabu har’abada kenan, saminu d’ana nefa nina haifeshi, kamar yadda takejin Mukhtar azuciyanta, nimafa haka nakejin Ahmeed anawa azuciyan, idan tana tunanin zata ringa ganin Ahmeed kamar Mukhtar ni wazan kallah amatsayin Ahmeed??? koko ana nufin nibani da yanci ne??,  ban san zafin d’aba?
    Hawaye Saminu ya share sannan yace”
    Haka ne Maman Amadu duk abin da kika fada haka ne, amman duk da haka nizan fison kitafi din, dan nasan Ummayo ko sama da kasa zata hade, bazata badashi ba, dan itama nayi nayi da ita tayi hakuri tabakishiamman tace da anan kauyen kuke, zatabar miki shi, dan tasan duk lokacin daso ganin shi zata ganshi, yanzun ko tace idan kika tafi dashi ta tabatar ta rabu dashi kenan har abada”
    A’a Saminu ka lallashi Ummayo ta bani Ahmeed, kuma ta hadani da wani yaga inda muke duk lokacin taji nason ganin Ahmeed, zata iya zuwa”
   Hmmm ai duk wata dubara da kika sani nayi, amman tace ita Sam”
    Ajiyan zuciya Ummi tayi sannan ta koma ta zauna tare da fadin”
   Saminu zamana be kareba agarin nan, zanci gaba da zama har ranan da Ummayo zataji tausayina tabani d’ana”
Mikewa Saminu yayi zai fita, har yakai kofa Ummi ta kira sunan sa”
     Ja yayi ya tsaya tare da juyowa”
    Hawaye na tsiyaya idonta tace”
     Dan Allah zan baka wayata kataimakeni kaje bakin yanki, acikin wayata   akwai numbar Ummata ka kirata ka gaya mata Mukhtar ya rasu, idan baka sametaba ka kira ta Abba kona Daddy, kai ko wacce numbar cema ta shiga ka sanar musu Mukhtar ya rasu, ina cikin wani hali”
  Kuka Saminu ya fara domin Ummi tayi matukar bashi tausayi, share hawayen yayi sannan yace, insha Allahu yau zanje, karki damu”
         **        **
STORY CONTINUES BELOW
    Abangaren iyayen Ummi kuwa, har yanzun hankali ya kasa kwanciya  tun suna boyewa har takai kowa ya sani, yan uwa sai jajantawa juna sukeyi, haka mukota nata zuwa jaja tare da addu’an Allah ya baina su, domin yanzun sun cike wata guda da tafiya”
    Gidan Alhaji yaro ma hankali be kwanta ba domin su abba kullum cikin sitiri suke da tambayan ko anji wani lbr?
    Dan haka hankula duk ya tashi, inda alhaji yaro ya yanke shawaran dazaran Mukhtar ya dawo sai dai ya saki Ummi, danshi ya cire hannun shi aciki, danasani matuka yayi tare da alkawarin bazai kara tsawa wani gurin aure ba illah ‘ya’yan da ya haifa, domin Mukhtar ya watsamai kasa a ido”
    Hajiya ko tunda ta samu wannan labari ta shiga tashin hankali, idan ta fara kuka babu me iya lallashinta sai Abdulmajeed, yauma shine zaune agabata yana bata hakuri”
    Hajiya kiyi hakuri ni nayi alkawarin zan bincike garin, ba dai ance d’an Niger bane?,  sunan kauyen kawai nake bukata, zanje gidan Alhaji Yaro ya gayamin sunan kauyen zan tafi”
    Share hawaye Hajiya tayi *Bawan Allah* Allah ya maka albarka, dan Allah ka binciko min takwarata, idan ko har ta shigo garin nan aure ya kare tsakanin ta Wannan yaron, ta dawo gida kawai   idan komai ya lafa tai aurenta”
   Wani irin kallo yaiwa Hajiya sannan yace”
   Toh ita tace miki bata son shi ne?, tanafa son mijinta, kuma ma ban da abinki, *wanne wawan ne zai aure sauran d’an cirani*, wata kila ma ta samu tsaraban cututtukan zamani”
    Kallon shi Hajiya tayi asheke tace”
   Bakinka ya sari danyen kashi, Bawan Allah yaushe ka zama haka?
  Mikewa yayi kawai sai da yayi dan nisa sannan yace”
  Karki sake kuka hajiya indai Ummi ce zata dawo”
     Daga nan gidan Alhaji yaro ya nufa bayan sun gaisa ya gaya mai daga inda yake, sannan ya sanar dashi dalilin zuwan shi”
   Cikin nuna damuwa Alhaji Yaro yace”
   Ai iyayen ka sunzo, akan wannan maganar kuma nima ba azaune nake ba, ku kara hakuri yana dawowa zansa ya saketa domin gudun sake faruwan wani abu maka mancin haka”
    Cikin daure Fuska Abdulmajeed yace”
   Niba burina aureta ya mutuba, nikawai burina insan garin daya fito, tunda tanason mijinta”
    Aini babban matsalan basan sunan kyauyen ba, amman insha Allahu zan bincika, ku ramin hakuri”
    Cikin baccin rai Abdulmajeed ya baro gidan tare da tarin damuwa dan haka ya kira Nafisa awaya”
   Cikin kankanin lokaci ta iso, sai dai ta kula yana cikin damuwa dan haka cikin kissa ta fara tambayen shi abin dake damun shi”
    Duk da cewa beso ya fada mataba amman ganin inda taita narnarkewa ajiki yasa, ya tsinta kansa da sanar da ita damuwan shi”
    Sosai tanuna tausayawanta sannan tace idan zaka tafi Niger din zan raka ka, domin inbaka kulawa ta mussamman, tare da taimaka maka idan bukatan hakan ta taso, kuma akwai yan Niger a unguwar mu zan bincika ko Allah zaisa asamu wadda yasan shi”
    Yau kasa komai yayi da ita, haka suka rabu batare daya kalli komai ajikinta ba bare yayi abinda ya saba”
    Cikin dare Abdulmajeed zaune ya kunna sigari yanata faman bulbulan hayaki, zuciyar shi kuwa cike dason ganu hanyar da zai billowa al’amarin Ummi”
   Ahankali yaji karan phone din Abba, mikewa yayi arude ya nufi window domin ta gurin yaji karan”
    Yana kokarin daga labulan yaji muryan Daddy na fadin”
   Innalillahi wa inna ilaihir raju’un, yanzun ina Ummin take?
    Bejira yaji me zai sake fadi ba yayi waje aguje, mika hannu yayi ya amshe yawar”
   Muryan namiji yaji yana fadin”
   Dan haka tace na taimaketa na sanar muku”
   Waye kai? shine tambayan da Abdulmajeed yayi acikin wayar”
   Sunana Saminu, kuma ni kanin Mukhtar ne”
   Shi mukutar din fah yana ina?
    Mukhtar Allah yamai rasuwa tun satin su Uku da zuwa
     😳😬 zaro ido Abdulmajeed yayi cikin tashin hankali yace”
   Ya rasu???, yanzun ina Ummi?
    Tana nan cikin kyauyen mu, ita ta aikoni na sanar muku”
    Bata wayar Abdulmajeed ya fada cike da bada umarni”
   Ai, cikin kyauyen mu babu network, nima saida nayi tafiya me nisa sannan nake kiran ku”
     Toh toh kanaji na yaya sunan kyauyen???
     *Bakin yanki*”
   Bakin yanki? Abdulmajeed ya sake maimaitawa sannan yace toh  munan zuwa”
    Dahaka suka rabu sai da suka kashe waya Abdulmajeed ya tuna be tambaya sunan gidan wadda zai tambaya ba idan ya isa Bakin yankin”
     Nan ya warwarewa Daddy komai, tun kafin gari ya gama haske Daddy ya nufa gidan Abba”
    Bayan ya gama mai bayani kamar yadda Saminu ya sanar, sosai hankali Abba ya kara tashi, Mukhtar ya mutu?, ummi kuma wanne hali take ciki”
    Shiko Abdulmajeed tun daren ya fara shirin tafiya dan haka yakira Nafisa yace tamai binciken wani kauye wai shi Bakin yanki”
       Sallama yaje yiwa Abba da Daddy, sosai sukaji dadin yadda ya nuna kulawan shi sai dai Umma dagewa tayi ita lallai da ita zai tafi”
     Yana zune agaban su Abba ana tsaka da rarrashin Umma, Nafisa takira wayar Abdulmajeed, dauka yayi ya kara akunnen sa yai shiru, dan beson afahimci da mace yake wayar”
    Daga can cikin wayar Nafisa tace”
    Ranka ya dade, nayi bincike akan kyauyen Bakin yanki”
    Sai dai sunce kauyen nada matukar had’ari, kuma akwai tafiya wacce za’ayita da kafa wadda take daukan akallah tsayon awa 10 ko fiye da haka  kafin ashiga cikin kyauyen, ataikaice dai shiga kyauyen zaiyi matukar wahala, gashi ance garin cike yake da mayo”
    Ya mutsa fuska Abdulmajeed yayi sannan yace”
    Bar maganan maye ko menene kuke kiran su?, basu dameni ba, amma Ita tafiyan awa goman dole akafa akeyinta ???🤔🇺 🇼 🇦✨: 🔥 🔥🔥🔥🔥🔥
*KOWANNE BAKIN WUTA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    ( da nashi hayakin)
💨💨💨💨💨💨💨
Story & Written by
    *Fadeela Lamido*
*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*
    Wattpad @fadeelalamido
            *22 – 23*
Eh akafa akeyinta dole, domin sun shaida min babu abin hawa ahanyar, kuma daji ne, babu gida gaba, babu gida baya”
    Nisawa Abdulmajeed yayi sannan ya sauke wayar ya kalli su Abba da suka tsare shi da idanu”
   Mikewa yayi yana shirin fita, Dadyy ya takatar dashi, tare da tambayan shi menene ke faruwa”+
   Fuskanshi na dauke da damuwa yake sanar masu komai, game da garin, da Ummi take ciki, sosai hankalin kuwa ya kara tashi”
     Cikin kuka Umma tace”
   Anya kuwa Abdulmajeed za’abita garin nan, kaji fah ance akwai mayu aciki karkazo ka tafi ayi bawan ba kannin”
    Sunkuyar dakai Abdulmajeed yayi zuwa can yace”
    Zanje Umma ai bekamata abarta cikin wani haliba, duk inda take yanzun hankalinta ba akwance yake ba, ya kamata afiddata daga cikin damuwa”
     Daddy ne yace ai dole aje nemanta idan ta kama ma harmu sai mu tafi, kuma tunda yace zai iya inaga sai dai mumai addu’a, sannan asamo masa manin miyagu gurin Hajiya, saidai dole ya dage tafiyan zuwa gobe, domin mukarajin wani karin bayanin game da garin”
    Dahaka su daddy suka wuce gida, Abdulmajeed ko babu abin da yake Jinjina wa sai wannan tafiyan kafan domin shi be saba tafiya akafaba”
    Da yamma Sadiq ya ziyar ce shi, nan yake gayamai halin da Ummi ke ciki, ya nuna tausayawan shi agareta harma yace dashi za’ayi tafiyan”
    Mussaman Nafisa ta zubawa iyayenta karyan cewa, anzabesu amatsayin wad’an da zasu karaka doctor Abdulmajeed Habib wani babban Asibiti dake Niger domi kai ziyara ga marasa Lafiya kamar yadda ya saba”
    Dan haka batasha wahalan shawo kansuba suka amince mata”
     Shiko Sadiq sai da ya sanar da iyayensa gaskiya halin da ake ciki, hakama matarsa Fatima, rigima tasamai akan ita bata amince ba, ahankali yaita lallashin, tare da nuna mata matsayin doctor Abdulmajeed agurinsa, sannan ya shawo kanta ta amince”
   Daddy da kansa ya amsowa Abdulmajeed maganin miyagu gurin hajiya yasha ya turara wani sannan yabashi wani ya bawa abokin tafiyan sa”
    Washegari tunda asuba sukayi Sallama da kowa, suka dauki hanya, sosai sukasha addu’a agurin iyayen su”
    Tun dare Abdulmajeed ya zuba duk wani abu dayasan zai bukata acikin mota”
   Sudanyi nisa da gida Abdulmajeed yaja ya tsaya”
   Sadiq ne ya kalleshi yace”
   Muje mana yanaga ka tsaya ko har ka gaji ne??
    A’a ina jiran Nafisa ne”
   Nafisa kuma, mezaka mata Nafisa acikin halin yanzun?
   Juyar dakai Abdulmajeed yayi yana kallon waje, sannan yace”
   Munyi da ita Zata min rakiya ne”
   Subuhanallahi, Abdulmajeed wai meke damun ka?, ta yaya zaka dauki yariya budurwa kayi tafiya da ita, ina hankalin ka yaje?
STORY CONTINUES BELOW
    Kaga, Sadiq karka damu, ta riga ta sanar da iyayenta kuma sun amin ce, dan haka ka kwantar da hankalin ka, danni idan ban tafi da itaba hankalina bazai kwanta ba”
    Wani kallo Sadiq ya wurga mai, sannan shima ya dauke kanshi”
    Basu jima ba, Nafisa ta sauka amashin tare da jakar kayanta”
   Ganin Sadiq agaban motar yasa jikinta yai sanyi, kamar tace ta fasa tafiyan, domin tasan ba sakewa zasuyi ba”
    Bayan motar ta bude ta shiga, tana zama Abdulmajeed ya figi motar”
    Cikin saririyar muryarta ta gaida Sadiq,
   Yana dadaure fuska ya amsa, sannan ta gaida Abdulmajeed shiko kala bece mataba”1
    Jan ajiyan zuciya tayi tare da rufe ido, dan tasan indai yai haka toh akwai abinda tamai”
    Zuwa can ta bude idonta ranka ya dade nayi wani abu ne?
   Ke dallah malama karki dameni, kina sane sarai raini ne ke damun ki, tuntuni nake miki mgn ki daina hawa mashin amman saboda tsaban iskanci kinki bari, toh ni bazan dauki iskanci ba, fada ya cigaba dayi sosai dan haka Sadiq ya zuba mai ido yana kallon shi, ganin inda ya tada jijiyoyin wuya yanata masifa, yasa Sadiq yace”
   Abdulmajeed ya isheka haka, haka kurun kabi ka ishe mutane da masifa, matar kace ita?, zaka hanata hawa Mashin?, ka aureta ne?, kajimin wata fitina sabo da Allah?
    Sadiq babu ruwanka badakai nake ba, karka kara samin baki”
    Saina saka, masifaffen banza kawai”
    Girgiza kai yayi sanna ya dauke kai yaci gaba da tukin sa”
    Shiko Sadiq yanajin yadda Nafisa keta bawa Abdulmajeed hakuri kamar tana bawa Ubanta, amman yayi banza da ita”
   Gaba daya haushin su ya kamashi ji yake tamkar ya shake su, acikin zuciyan shi yace ‘yan iskan banza da wofi,
    Sunyi tafiya me tsayi damma suna tsawa Sallah”
  
   Gashi sunayi ne suna tambaya dan acikin su babu wani masanin hanyar, dan haka Abdulmajeed ya fara gajiya da tukin”
     Kusan karfe 6:00pm Sadiq ya amsheshi, amemakon ya shiga gaba saima ya koma baya”
   Kallon shi kawai Sadiq yayi sannan ya ja motar, batare daya sake kallon suba”
    Shiru motar tayi na wasu awannai zuwa can hankalin Sadiq yakai kan madubin dake makale agaban motar”
    Abdulmajeed kwakume da Nafisa tare da kara manne wa jikinta”
     Cikin sauri ya dauke idon shi, zuciyar shiko kamar ta fito sabo da haushi be sake kallon madubin ba barema ya kara jin baccin rai”
    Suna isa daidai wani kauyi aka kira mangariba dan haka Sadiq yaja ya tsaya cikin sauri yabar motar”
    Shima Abdulmajeed sakin nafisa yayi, yabi bayan Sadiq tare da fadin”
    Shine kuma zaka tafi ka barni”
    Tsaki Sadiq yaja yai gaba abinshi”
    Buta ya dauka cike da ruwa, shima Abdulmajeed butan ya dauka ya nufi cikin ciyayi domin kama ruwa”
   Bin bayan shi Sadiq yayi da kallo cikin tarin takaici”
   Abdulmajeed na dawowa Sadiq ya sake kallon shi tare da cewa”
    Badai alwala zakayi ba?
    Yana kokarin nade hannun rigarshi yake fadin”
    Alwala zanyi mana”
STORY CONTINUES BELOW
    Cikin zare ido Sadiq yace”
    Har kamanta zinar da kukayi acikin mota?
   Yamutsa fuska Abdulmajeed yayi, zina kuma Sadiq?, kasan me kalman zinah take nufi kuwa?
    Hmmm ina kallon fah iskanci da kukaitayi cikin mota, kuma nasan daganin yadda kake rawan jiki wanka yahau kanka”
    Tsaki Abdulmajeed yaja angaya maka kowa ragone irinka, kawai daga na dan tabata sai wanka yahau kaina, niba dan iska bane kamar yadda kake tunani”
    Alwalan shi yayi ya tashi yabar Sadiq agurin ya zuba tagumi”
    Tare suka fito masallaci suka nufi motar babu mema wani mgn”
    Hanya suka sake dauka sai kusan 2:00am suka shiga cikin garin Niger, lokacin kowa yagaji tubus”
    Gashi basusan wacce hanya zasubiba, dole suka tsaya gefen hanya, dan babu kowa agurin”
   Sosai Abdulmajeed kejin sanyi, gashi sauro duk sun cincijeshi”
    Juyawa yayi ya kalli Nafisa yadda ta miki sosai abayan motar dare da rufa da bargonta datayo guzuri tun daga gida”
   Juyayawa yayi ya kalli Sadiq, badan yana kudun korafin saba, da babu abin da zai hanashi shiga cikin bargon Nafisa”
    Haka yaita rawan sanyi, kallon shi Sadiq yayi yace”
   Wai duk sanyin ne haka?, kanadai dajin sanyi ne, amman banji sanyin da kake mgn ba”
    Haka bacci barawo ya sace su”
     Kiran sallane ya tada su, sakkowa sukayi suka nemi masallaci bayan sunyi Sallah suna fitowa Sadiq yama wani mutumin sallama”
   Tsayawa mutumin yayi suka gaisa, Sannan Sadiq yace”
    Mu bakine, daga Nigeria, dan Allah muna tambayan hanyar wani kauye ne, ana kiransa *BAKIN YANKI*
    Toh🤔 Aiko kuna da sauran tafiya, tafiyace mikakiya tayi rabin wadda kukayo, sannan kafin ku shiga kauyen ma akwai tafiyar kafa me matukar nisa, Amman kukuwa me zakujeyi *BAKIN YANKIN*?
  Sadiq ne ya fada masa dalilin zuwan su”
  Nan mutumin ya jinjina kai, sannan yace”
   Gaskiya bazan boye mukuba, tunda tambayata kukayi,azahirin gaskiya garin bashi da kyau, akwai hatsari shigarsa, sannan hanyar ta kasu kashi biyu, amman mutane nacewa wai baki takewa gizo, sannan dabi’ar su bata dakyau kwata kwata, ga tarin mayu”
  Kai Sadiq ya shafa sannan sukaiwa mutumin godiya”
    Ahakali suka fara tafiya Sadiq ya kalli Abdulmajeed yace”
     Anya kuwa maje?, kanaji fah kowa ya bude baki sai yace garin bashi dakau, ni ina ganin xuwa garin nan tamkar saida rai ne?, anya kuwa bazamu juya ba?
    Duk abin da suke cewa Nafisa najin su, dan haka itama ta shiga nadama tare da data sani bata biyosu ba”
    Shiko Abdulmajeed wasu jijiyoyi kawai kake gani agefen kansa rudu rudu”
   Bakomai ke bashi haushi ba irin nisan garin daya gani, amman duk da haka Ummi ta yadda tabi Mukhtar, yasan kafin taje tasan garin, yana da nisa,  toh meyasa tabishi?, jibemu muna maza amman muna jinjina tafiya cikin wannan garin, amman ita amatsayinta na mace ta yadda ta bishi, ita ‘yar dadi soyayya, shine ni zan sai da raina nabita?, bayan ta fada agaban kowa, cewa bata sona?, mezanji inyi mata?, mayar yariya kawai”
    Afali yace”
   Sadiq na fasa bazanjeba, mukoma kawai”
    Wani irin kallo Sadiq din ya masa, sannan yace”
   Kamanta munyiwa Su daddy alkawarin zamu dawo musu da Ummi? idan muka koma yanzun muce musu me?, sannan ita kanta Ummin ai abun tausayi ce, dan wannan tafiyan dole ta bukaci mataimaki, bazata iya yinta ita dayaba, duk inda take yanzun tana cikin mawuyacin hali, ga jimamin  mutuwan mijita, gashi yabarta agarin da ba dangin iya bare na baba, sai tarin mayu da kowa ya bude baki yake fad’a
   Amman Sadiq tasan haka garin yake meyasa ta biyoshi?, ita ‘yar dadi soyayya ko?, wlh har bana son na hada ido da ita, haushi zata bani, inbanda wawuya wacece zata yarda akawota nan gurin ma bara cancikin wanne wani daji?
    Hmmm Abdulmajeed har yanzun dai kishin Ummi ke damunka, kayi hakuri karka zobe ladan ka, ka tausaya mata ‘yar uwarkace ta jini, ayanzun ummi abin tausayi ce”
Naji Sadiq, zanje, amman wlh tace zata kawo min iskanci zanci ubanta, kasan me za’ayi?, kuku tsaya daga nan, zan karasa ni daya, kaga Nafisa macece, idan muka shiga da ita zata wahala, kuma ina gudun kar wani abu ya faru da ita, dan haka katsaya da ita ni zan karasa”
   Bazai yiwu ba Abdulmajeed, ni kaina rako ba Nafisa ba, dan haka kafata kafar ka”
    Amman kasan bekamata mushiga da Nafisa ba ko?, tafiyar awa 10 fa ace kuma da kafa”
   Cigaba yayi da cewa, idan wani abu ya sameta mukoma muce da iyayenta me?, sannan kaima fah kana da mata da yariya, idan wani abu ya sameka, bazan yafewa kaina ba, dan haka ni kadai zan shiga wannan dajin”
     Sosai jikin Sadiq yai sanyi, ahakali suka karasa inda Nafisa take, tana zaune tana share hawaye”
  Kallonta kawai Abdulmajeed yayi, kobata fada ba yasan tunanin shiga wannan garin takewa hawaye, amman ita waccen mayyar taje tashige, Kiran sunanta yayi yana me kurawa idota kallo”
   Ahankali ta taso ta tsaya agaban shi, ki dauki jakarki Sadiq zai neman muku masauki ni zanje na dawo”
   Harta dauki jakar tana rawan jiki, Sadiq ya shiga motar ya zauna, sannan yace muje bakin yankin inyaso sai mu dawo da motar”
    Hakama yayi Abdulmajeed ya fada, sannan nafisa ta shiga motar suka wuce”
    Babu wani me kwarin guiwa acikin su, kowa da abin da yake sakawa”
    Sai kusan 4:44pm suka isa bakin yanki, bayan sunci Uban tambaya kafin suka kawo”
   Gaba daya suka sakkowa sukayi daga cikin motar, bayan Abdulmajeed ya gama karewa mikekkiyar hanyan kallo ya koma cikin motar”
   Zuwa can ya fito ya sauya kaya, daga manyan kaya zuwa kanana masu dan duhu saboda gudun kura jakace daure bayan sa wadda tayi kama da jakar makaranta, kafar shi ko takalmi ne wadda bahaushe ke kira taka teba”
    Hanyar ya kalla sannan ya kalli Sadiq yace zan wuce”
   Hannu Sadiq yasa aljihun sa, yaciro layin waya ya mikawa Abdulmajeed sannan yace
   Kasa wannan awayar ka, idan ka fito akwai numbar ta aciki saika kirani
   Murmushi Abdulmajeed yayi domin shi yama banta ya kamata ya canza layi”
    Hannu ya dagawa Nafisa, sannan yama Sadiq murmushi tare da fadin saina dawo, juyawa yayi ya nufa mikakiyar hanyar da duhun yamman ya fara sauka tare da kukan tsuntsaye bakin shi dauke da addu’oi yake tafiya”
    Sadid ko kasa kyaucewa yayi tsayawa yayi wai saiya daina hango Abdulmajeed…54 PM] ~🇭 🇦 🇺 🇼 🇦✨: 🔥 🔥🔥🔥🔥🔥
*KOWANNE BAKIN WUTA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
( da nashi hayakin)
💨💨💨💨💨💨💨
Story & Written by
*Fadeela Lamido*
*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*
Wattpad @fadeelalamido
*25 -26*
Saida duhun ya fara bayyana, Sadiq ya daina hango kellin Abdulmajeed, dan haka ya kara tabbatar da nisan garin”
Sosai yaji hankalin sa ya tashi, Nafisa ko fadi take”
Doctor inajin yunwa fah”
Kad’a kai yayi ya shiga cikin motar tare da alkarin indai Abdulmajeed ya kwana 3 aciki ya zama lallai yabi bayan shi”
Shiko Abdulmajeed tafiya yake tayi amman bega alaman akwai mutum acikin wannan dajin ba, anya kuwa ya biyo hanyar daidai?, cikin wannan tunanin duhu ya baiyana, bakajin komai sai kukan tsuntsaye”+
Sosai Abdulmajeed kejin fargaba tafiya yake batare da yasan inda yake jefa kafar shiba”
Acikin zuciyan shi yake tunanin anya kuwa ba yau daren su akayi ba, kodai Mukhtar ne ya hada baki da wani domin wani yazo su cutar dashi, wata kilama Ummi bata raye”
Yin wannan tunanin yaji wani kwarin guiwa ya tasan mai, inma haka ne zai so ya tabbatar wa idonshi haka, idan ma mutuwa ce ta kawoshi kwanan shine ya kare”
Jefa kafa yakeyi tare da karanta duk wata sura da tazo bakin shi”
Tafiya yayi sosai wadda atunanin shi yakejin ta wuce ta awa goma, wani irin zugi kafar shi kemai, kai gaba daya jikinshi ma ciwo yake ga fargaban dake cinkushe azuciyar shi”
Mugun gajiya yaji wadda yake ganin indai be tsaya ya hutaba komai na iya faruwa dashi, tafiya yake yana lalube domin neman gurin zama, ji yayi tamkar ya taba gini sabanin da da yake cikin ganyaye da bishiyoyi, kara tabawa yayi, tabbas gini ne, acikin zuciyar shi yace kodai nashigo garin ne?
Hannu yasa a aljihu ya lalubo wayar sa ya kunna haskenta ya haska hanyan”
Gidaje ya gani barkatai wadda akayiwa shafe da bakar laka, hanta randunan su anyi musu bakin fenti”
Ajiyan zuciya yayi sannan ya nemi guri ya zauna, yana me addu’an Allah yasa garin ne”
Ya zauna babu dadewa yaji ankira Sallah”
Sosai yaji mamaki dan a Tunanin Abdulmajeed mutanan gari nan basu sallah, dan bega alaman rahama ba”
Mutsin mutane yaji suna ta fitowa wasun su dauki da fitilan acibalbal, wani fili suke nufa wadda atunanin shi nan ne masallaci su”
Goran Faro ya ciro daga cikin jakarshi yayi alwala sannan yamaida ragowan shima ya nufi cikin su”
Yana isa gurin suka fara hasko shi da fitilan acibalbal din su”
Aduniya babu abin da Abdulmajeed ya tsana kamar yaga ana haska shi, duk da cewa fitilan tasu bawani haske gareta ba amman yaji haushi sosai, acikin zuciyan shi yace”
Kagamin ‘yan iskan mutane, ni bance zan haska suba sai sune zasu haskani, fitalan wayanshi ya kunna ya dallare musu idanu”
Arikice suka fara fadin bako ne wlh wannan badan garin nan bane”
Wasu daga ciki har sun fara daukan sandina, yayin da wasu suke kara matsoshi da fitilan su”
Abdulmajeed bebar haska suba ganin suna dada shigoshi yasashi fadin”
STORY CONTINUES BELOW
Eh ni bako ne, daga Nigeria, kuma na shigo gurin nan ne ina neman wani kauyen da ake kira bakin yanki”
Sassauke sandinan sukayi sanna daya daga ciki yace ka iso bakin yanki, zumuje muyi sallah tukuna”
Bayan sun ida Sallah, suna fitowa, mutum biyu ne suka biyo bayan Abdulmajeed lokacin garin ya fara haske”
Suna tafiya ne mutumin ke tambayan Abdulmajeed gidan wa yazo?
Eh to gaskiya bazan iya cewa ga gidan wadda nazoba, dan bansan sunan me gidan ba, amman akwai wani yaro Mukhtar daya zauna a Nigeria wadda muka samu labarin cewa ya rasu anan”
Shiru mutumin yayi zuwa can yace”
Ai inajin duk kyauyen nan bamu da me wannan sunan, akwai dai wani yaro Muntari wadda saran maciji yakaishi ga rasa rayuwan sa, shima naji ance daga Nigeria yazo, har yanzun ma matar sa nanan tare da dan da suka haifa”
Cikin kosawa Abdulmajeed yace ai inajin shine ma, dan Allah ka taimaka ka kaini gidan”
Toh toh ba damuwa muje ko”
Suna tafi mutumin na tamai hira tare da bashi lbrn garin, duk da cewa Abdulmajeed bashi da son mgn ya saurari wasu, har suka isa gidan hira yake mai”
Akofar gidan mutumin ya tsaya sannan yace”
Kaga gidan nan, kayi sallama aciki, dan Allah koda antambayeka waye ya maka jagora kace bakasan shiba, domin matar gidan masifaffiya ce”
Sosai Abdulmajeed yayi godiya sannan ya tambayi mutumin sunan sa”
Sunanaa magaji duk sadda ka bukaci tai mako zaka sameni acikin masallacin”
Godiya Abdulmajeed ya kara masa”
Sannan ya nufa kofar gidan”
Sallama ya rangada sau Uku, sannan aka amsa acikin irin hausan Magaji”
Muryan mace ne dan haka ya tsanmaci macece zata fito, amman saiya namiji”
Saminu naganin Abdulmajeed ya shaida dan uwan ummi ne saboda tsananin kama da suke yi”
Fara’a yayi mai sosai tare da fadin sannu da zuwa maraba”
Fuskan Abdulmajeed daure yake amsawa daman shi ba me dariya bane sannan ga tasananin gajiya da tarin yunwa, duk da cewa ya riko abin da zai tare mai yunwa, amman be samu yaciba sabo da far gaba”
Cikin daure fuska yace ni bakone, nazo daga Nigeria, ina neman gidan su wani yaro Mukhtar dayayi zama acan”
Murmushi saminu ya sake mai, ai kazo gidan tunda naganka na shaidaka saboda kama da kukeyi da matar Muntari, sai dai wani hanzari ba guduba, dan Allah koda munje gun Ummayo karkace waya aka muku, kace kawai kunji shiru ne kuka biyo sawo, labarin mutuwan sa ko kace acikin garin nan ka samu labari lokacin da kake neman gidan nan”
Yamutsa fuska yayi wai meyasa kowa sai yace ayi shiru wai garin nan kowa gudun laifi yake ne”
Girgiza mishi kai yayi sannan suka shiga saminu nagama Abdulmajeed abayan sa, kayan sa sunyin duku duku kamar ba Abdulmajeed ba”
Dakin Ummayo Saminu yakaishi, tsugunawa Abdulmajeed yayi ya shiga gaida Ummayo ina kwana?
Tasowa Ummayo tayi daga kishin gidan da tayi tana kallon Abdul cikin ido”
Sannan tace kagamin mara kunyan yaro mara tarkiya?, ni kake cewa ina kwana”
Wani irin kallo shima yai mata sannan yace”
Idan bance miki ina kwana ba me kike son nace miki?
Saminu ne yai gyara murya sannan yace”
STORY CONTINUES BELOW
Bako, mu anan idan kacewa babba ina kwana tamkar ka raina sane saidai kace ankwana lafiya?, juyawa yayi ya kalli Ummayo yace”
Ummayo wannan bako ne daga Nigeria dan uwan matar muntari ne, bakiga suna kamaba”
Tashi tayi ta zauna sosai sannan tace”
Ai naga alama itama gaisawata da ita ta farko cikin wayar muntari haka tace dani saboda yaje ya aure mara tarbiya”
Cikin zafi Abdulmajeed yace nifah banzo nan dan amin wata doguwar magana ba naxone na dauki kanwata, kuma ni inada tarbiya kar asake cemin mara tarbiya”
Atsorace Ummayo ta kalleshi, eh lallai muntari ya hada iri da tsiya”
Juyawa Abdulmajeed yayi ya kalli saminu yace”
Ina Ummin take???
Muryan Ummayo yaji Bazan baka daman ganinta ba”
Mikewa yayi cikin zafi, inason nasan dalilin dazaki hanani ganinta, kanwatace ‘yar uwatace tajinina, wlh indai tana garin nan banga mahalukin daya isa ya hanani ganin ta ba”
Zaro ido Ummayo tayi tare da fadin kagamin jarabeben yaro, ni kake zarewa idonu?
Ni bansan ke ko wacece ba, kamar yadda nima bakisan ni ko waye ba, kawanta kawai nasani kuma ita nazo nema”
Hadiye yawo Ummayo tayi sannan tace”
Haka ne, muje ka ganta”
Shiya fara fitowa saminu nabin bayan sa, sanna suka jira Ummayo tai gaba sannan sukabi bayanta, harara Abdulmajeed yaita xubawa bayan Ummayo”
Wani lungu sukabi da babu kowa agurin saida sukayi tafiya me nisa sannan Ummayo ta nufa dakin dake karshen gida, kafa tasa ta tura kofar dakarfi”
Dagowa Ummi tayi ta kalli Ummayo idonta duk busheshshen hawaye sannan tasadda kanta kasa”
Wucewa Ummayo tayi ta tsaya cen gefe sannan saminu ya shigo, Abdulmajeed nabin bayan shi”
Kafafuwan su kadai Ummi ke iya gani dan haka ta kawo tunanin yau kuma da wacce Ummayo tazo mata kafar farko dai ta shaida ta saminu ce”
Abdulmajeed zuba hannuwan shi yayi duk biyu cikin Aljihun shi yanabin Ummi da idanu”
Ganin sun dade tsaye basuce komai ba yasa Ummi ta dago ta kalli Ummayo ta juya gurin saminu, gani tayi ya sakar mata murmushi dan haka tajuya gurin da Abdulmajeed yake”
Arikece ta miki tabishi da idanu wanni irin hakin farincikin ne ya tasar mata tashiga yi babu kyautawa, saidai tana ganin kamar mafarki take dan bata tunanin Abdulmajeed zai iya zuwa nan gurin sabo da ita, dan haka ta karasa gaban shi tare da murza idanunta, yaya Abdulmajeed nake gani ko mafarki nake ne, idan mafarki ne Allah kabarnin acikin sa👏🏻”
Banza yayi da ita tare da daure fuska, ya juyar da fuskan shi can gefe, acikin zuciyan sa yake tunanin ranar da akace za’a hadasu aure haka tamike cikin tashin hankali gaba kowa tace”
Allah kayi gaggawan farkaddani daga wannan mummunan mafarkin, yau kuma ke kike cewa Allah yabar ki acikin sa?
Saminu ne yace”
Mmn Amadu gaske ne ba mafarki bane, dan haka Ummi takara matsawa, ta taba jikin Abdulmajeed, har yanzun yana tsayi kam”
Arikece ta rungumeshi sosai, tana kuka me tsuma zuciya”
Sosai tabawa Abdulmajeed tausayi, dan haka beyi yunkurin hana taba barinta yai tai kwace akirjin shi, gaba daya gaban riganshi ya jiki da hawayen Ummi, saida dagaji dan kanta sannan ta daga ta kalleshi tare da fadin”
Yaya zoka zauna”
Girgiza kai yayi sannan ya kalli Ummayo yace”
Banga gurin zama ba, Meyasa aka ajeta nan?, wannan gurin bashi da maraba da dakin kaji”
Subuhanallahi mukuma nan shine dakin takaba, duk wata mata da mijinta ya mutu agarin nan nan ake kawota harta cike takabanta”
Aiko ban da ita, yanzun nan zaku fitar da ita daga nan wajen, muba haka mukeyi ba, dan danku ya mutu saiku huce akan dan wani?
Wani irin kallo Ummayo tamai sannan tai gaba tare da fadin muje”
Hannun Abdulmajeed Ummi ta rike tana kuka take fadin”
Yaya Abdulmajeed dan Allah karka tafi ka barni anan”
Ke, dallah tafi can nina kawoki dazakice wani karna tafi nabarki, idan naga dama tafiyata zanyi, mayyar yariya kawai, wadda ma ya kawokin ya tafi ya barki bareni”
Hannu tasa ta share hawaye, sannan ta rike hannun sa katam, gaba yayi tana binsa, sai faman sauri yake, yayin da ummi ke binsa dan gani take kamar zai gudu yabarta”
Dakin da suka sauka ita da Mukhtar Ummayo ta bude sannan tabawa Abdulmajeed hanya ya wuce tare dabinsa da kallo”
Ummi ma Ummayo tabi da kallo dan sai take ga kamar tana shakkan Abdulmajeed”
Zama yayi abakin gadon bonon dake dakin, fuskan nan kicin kicin kai kace be taba dariya ba”
Saboda tsabar tsoron sa da Ummi keji zamewa tayi ta zube akasa ta zuba mishi idanu”
Ganin ta kureshi da ido yasa ya kauda kansa yana kallon gefe”
Ummi ko har yanzun mamaki take, wai Abdulmajeed ne agabanta?, shine ya iya keta dajin nan domin ya tsamota daga cikin balakin da ta shiga?, kafar sa ta kallah taga yadda tai futu futu da kasa, takalmin dake kafarshi ko, bata taba tunanin zai saka irin saba, gashi ya nannade kafar wandon sa almar ya shiryawa tafiyan, sosai taji farin ciki ya baibayeta Abdulmajeed yau ya aje gayonsa da takama, acikin zuciyarta tace, ko Mukhtar da yake da mahaifiya, da danginsa, ba’ason ransa yake zuwa garin nan ba, amman Abdulmajeed ya shiryo mussamman saboda ni😭 fuskanshi ta kuma kallo taga yadda yake huhura hancin, cikin hawaye tare da majina tace”
Yaya Abdulmajeed nagode, wlh naji dadin zuwan ka, dan Allah karka barni….
Bebari ta karasa ba yace”
Ke, kama bakin ki, ni badan ke nazoba, nazo nan ne domin farin cikin iyayen mu, dan uban ki sanda zaki taho kinyi shawara dani ne?, karki karamin godiya badan ke nazoba, ‘yar rainin hankali kawai”
Dukda wannan fadan Ummi bataji hushiba, acikin zuciyanta tace”
Koma badan ni kazoba nagode maka yaya Abdulmajeed”
Shiru dakin yayi na wasu dakiko, babu wadda yayiwa wani mgn, Ummi nason ta tambayeshi Ummanta da Abba tare da sauran mutanan gida amman babu fuska zama kawai tayi ta kuramai ido bubu ko kiftwa domin gani take data kefta ido zata nemeshi ta rasa”
Saminu ne ya sake dawowa dakin dauke da kwanon abinci, agaban Abdulmajeed ya ajiye tare da fadin”
Ranka ya dade amman dai bayau zaku wuce bako?
Cikin ciccijewa yace”
Naso hakan, sai dai nagaji matuka, jikina na bukatan hutu, amman da asuba zamu wuce”
Jin ya fadin haka Ahmeed ya fado mata rai dan haka ta kalli Saminu tace”
Saminu Ahmeed fah?, ka amsomin shi dan Allah, ga yayana yazo amman ba’a kawo shiba, nufin Ummayo bazata ni shiba??
Waye Ahmeed? cewar Abdulmajeed yana kallon cikin idon Ummi”
‘Dana ne, Ummayo ta dage wai saina barmata shi, yaya Abdulmajeed dan Allah ka taimake ni intafi da d’ana”
Tamin daidai, har kin iya bude baki ki cemin danki??, waye zai miki jigilar shi?? Ashe ko zantafi na barki agarin nan, angaya miki ni bawan gidan kune, wannan idan ke mayyace kika kama mutum saikin kaishi lahira, ke, duk yadda aikai kema mayya ce, shiyasa kika nace saikin hada iri da mayu, fitinanniyar yariya kawai……*KOWANNE BAKIN WUTA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
( da nashi hayakin)
💨💨💨💨💨💨💨
Story & Written by
*Fadeela Lamido*
*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*
Wattpad @fadeelalamido
27- 28
Kuka Ummi ta fara sosai tare da share hawaye, ganin haka Saminu ya juya yai waje, azuciyar shi yake fadin, wannan mutumin masifa tamai yawa”
Shima Abdulmajeed ganin Ummi ta dameshi da kuka yaja tsaki yai waje”
Waigowa Ummi tayi ta kalleshi ko kadan bataso ya matsa daga kusa da ita, sabo da ayanzun gani take shine gatanta, karya gudu ya barta”
Gashi yace bazai tafi da Ahmeed ba, wa zatasa ya rokar mata Abdulmajeed ta tafi da danta?, wlh idan har na barshi agarin nan ciwan zuciya zai kashe ni”
Sosai taci kuka ta koshi, har dare Abdulmajeed be dawo ba dan haka hankalinta ya tashi matuka”+
Sosai take kuka dataji motsi saita waiga”
Saican dare ya shigo lokacin Ummi na raira kuka”
Tsaye yai akanta ya gama kare mata kallo, sannan yace”
Meya faru kuma??
Cikin kuka tace naga ka dadene baka dawoba”
Hmmm lallaima yariyar nan kin rainamin wayo, dan kinason ki cuceni dole kiga dadewata, tsaki yaja sannan ya wuce ya zauna yana cigaba da girgiza kafa”
Ummi ko sai faman nonnukewa take”
Abdulmajeed ko kallonta yake afaikai ce, tananan yadda take sai rama da tayi da baki,dan haka yace kina wanka kuwa”
Girgiza kai tayi sannnan ta buki tace”
Tsoron yin wanka nake agarin nan sabo da Mukhtar daga wanka Maciji ya sareshi”
Wani guntun murmushi Abdulmajeed yayi matsoraciya, ai bekamata ki dinga jin tsoroba ‘yar rainin hankali kawai”
Shiru sukayi zuwa can Ummi ta sake cewa, yaya Abdulmajeed dan Allah ka taimake ni, intafi da Ahmeed, wlh idan nabarshi anan hankalina bazai kwanta ba, tunani zai kamani watakilama ciyon zuciya ya shige ni, kaga garin yayi nisa kuma yaron ko wata hudu fah bekai ba sannan ……….
Ke karki dameni, ko bakisan kyawun d’a gidan ubansa bane, kisan bashi da tushen da zaki iya barin musu jikan su meyasa kika aure shi??
Yaya wlh basan haka garin yake ba, Mukhtar betaba bani lbrn garinsu ba”
Toh ai yayi kyau kankankan kenan, ni banga lefiba dan tace kibata jikanta, kinga wannan saiya kuya miki darasi, idan zaki kumayin aure dakanki zaki tafi bincike, aike kinzaci inkinason mutum kawai shikenan, baruwan ki da dangin sa, gashi dalilin son zuciya kinjawa d’anki tasowa acikin wahalalliyar rayuwa”
Sosai Ummi ke rusa kuka, tasan duk abin da Abdulmajeed ya fada haka ne, amman ita burinta kawai ya amsan mata Ahmeed”
Cikin kukan tace”
Yaya nidai ka taimakeni, wlh inason dana kuma Babashima kafin ya rasu cewa yayi karna barshi anan”
Ok shiyasa kika dage saikin tafi dashi? Toh bari kiji ni bazance komai akaiba, ke mijiki yabarwa wasiyya baniba, dan ni be isa ya juyani ba, nakula har yanzun bakiji jikiba da sauranki, indai har kika matsa saikin tafi da yaron nan tafiyata zanyi, zan gayawa Abba kin zabi danki akansu, yariya banda fita baki iya komai ba”
STORY CONTINUES BELOW
Kuka Ummi taita rusawa zuwa can Abdulmajeed ya mike zaibar daki”
Cikin sauri Ummi ta muke ta rikeshi katam”
Tana kuka take fadin yaya ina zaka, kayi hakuri karka tafi ka barni kaine gatana, idan katafi bansan inda zansa raina ba, idan ma zance Ahmeed ne baka so na daina bazan karaba, kadawo ka zauna dan Allah”
Wani irin tausayinta ne yaji ya saukar mai, dan haka ya kauda idonsa can gefe, sannan yace ba tafiya zanyi ba zanje dakin saminu na kwata bacci nakeji, da anyi sallah asuba zamu wuce kizama cikin shiri, kuma kicira tunanin yaron nan azuciyan ki”
Sukuyar dakai tayi tare da cewa toh yaya zan cire”
Juyowa yayi yakalla yadda ta rikemai hannu, kara kaudakai yayi sannnan yace”
Sakeni zan wuce ne”
Hawaye Ummi ta share, murya kasa kasa tace”
Ka kwanta anan mana, idan ka kwana awani guri bazan natsuba”
Inkwata anan? ke kuma fah??, waike kinada hankali kuwa??
Sukuyar dakai tayi kasa sannan ta sake shi ahankali”
Har ya fita tana tsaye awajen, sannan ta koma kan gado ta kwata, gashi yau kwata kwata Ummayo bata bata Ahmeed ba, kome hakan ke nufi??
Abdulmajeed da saminu suna dakin dake jikin na ummi dan haka cikin dare kukan Ummi ya hanshi sukuni, tashi yai ya zauna yanata zuba tsaki, jin inda take sheshshekar kuka yasa ya sakko daga gadon, kokarin bude kofa yake saminu ya bude ido arude yace ina zaka??
Cire sakatar yayi yana rike da kofar yace”
Bakajin kukan Ummi??, takusa awa 3 fah tana kuka, ina zuwa barin je na dawo”
A’a karka fita, wannan garin ba’a fitarshi da dare, sannan akwai bakon machiji wadda ake tunanin shine ya sari Mumtari”
Tsaki Abdulmajeed yaja, tare da fadin kai dallah bari, yawan cin irin wannan maganar duk can fine, babu wadda ya isa yayiwa mutum abinda Allah besomai ba, barin dawo”
Sosai saminu ya tsorata, yana jin yadda Abdulmajeed ke buga kofar Ummi tare da kiran sunanta”
Budemai kofar tayi ya shiga tana kokarin boye hawayenta”
Meya sameki kike kuka??
Bakomai”
Ammiki wani abune??
Nan ma girgiza kai tayi”
Juyawa yayi ya kalli kan dago, sannan yasa wayarshi ya haska”
Kayan karamin yaro yagani ta jejjera akan gadon harda hula da safa, tajere shi tamkar tsayon yaro, juyawa yayi ya kalleta acikin zuciyan shi yace, duk kewan yaron ne haka??? Lallai wannan idan ba’abata dantaba tana iya haukacewa, kuma su daddy zasu shiga damuwa sosai wata kilama lokacin su matsa saina dawo na amso mata danta, kai ya kama tare da fadin wannan yariyar akwai bakin naci, amman zakici ubanki bari mukoma gida”
Cikin ido ya kalleta sannan yace”
Kina tunanin d’anki ko??
Sukuyar dakai ta sake yi, tare da wasa da yatsun hannunta”
Hannun shi ya zuba a aljihu sannan ya kalli sama yace, waike wacce irin mayyace? Toh shikenan, zan amsan miki danki amman ki shirya yadda zakiyi dawainiya dashi gurin fita daga kauyen nan, kin dai san yadda hanyar take, basai na fada miki ba, kuma karki ga kamar zan tausaya muki bare inji tausayin ki, niba bawan gidan ku bane “
STORY CONTINUES BELOW
Wani irin farin cikine ya kama Ummi, fuskanta dauke da hawaye da murmushi tace, naji yaya Abdulmajeed nayadda nakuma gode”
Juyawa yayi ya fice, sai dai Ummi ta fahimci ba’ason ransa bane”
Washegari bezo da asubaba, kamar yadda ya fada, dan haka ummi tayi tunanin koya canza shawara ne?
Saida gari ya waye taji sallamar shi akofar dakin Ummayo”
Mikewa tayi ta leka, lokacin harya shiga ciki illah takalmar shi dake bakin kofar”
Gaidata yayi kamar yadda ya saba, sai dai Ummayo kin amsawa tayi, Abdulmajeed bebi takantaba, cigaba yayi da cewa”
Nazo nagaya miki yau zamu tafi”
Wani irin murmushi tayi, sannan tace toh yayi kyau”
Abdulmajeed ya sake cewa saikuma mgnr danta Ahmeed, tace kince bazaki bataba kozan iya sanin dalili??
Bude ido Ummayo tayi sosai ta kalli Abdulmajeed tace”
Kai yaro kallanni dakyau, kaida gani kasan ni ba kanwar lasa bace, inace jiya cemin kayi badan kowa kazo ba sai dan ka dauki kanwar ka , har kana cewa ita kadai ka sani agarin nan, dan haka na maka duk abin da kakeso, shine kuma zaka billo min da wani zance???, toh bari kaji duk garin nan babu wadda ya isa ya kwaci amadu ahannuna, balle kai bako dabakasan komai ba”
Haka kike gani?, nikuma zan nuna miki nasan komai, zan nuna miki ni bako ne wadda yafi dangari iya iskanci”
Kana nufin ni yar iskace, wannan wanni irin tantirin yaro ne? haka kurum zakuzo ku fitine ni, yazama lallai in mike tsaye domin wannan yaron fitsaran shi tayi yawa, ina bazan barshi ba, dole indauki mataki”
Ficewa yayi adakin yana huci, dakin da Ummi take ya nufa”
Itako Ummayo goya Ahmeed tayi tai waje cikin sauri tanayi tana hararan dakin da Ummi ke ciki”
Bayan Abdulmajeed ya shiga dakin ko Sallama bema Ummi ba, domin ji yake haushinta ya karu azuciyar shi”
Zama yayi abakin gadon, yana cigaba da huci, tare da zubawa guri daya ido, bakomai ke damun sa ayanxun ba illah yadda zaiyi ya amsa d’an Ummi, sannan tunanin sadiq da Nafisa ya dameshi yana son yasa su a ido”
Ummi dake zaune can gefe ta zuba tagumi tace”
Ina kwana yaya?
Saida ya dad’e kamar bazaiyi mgn ba, zuwa can, ya dago ya gallah mata harara daban kwana ba zaki ganni ne?
Sunkuyar dakai tayi kasa, tasan yin mgn da Abdulmajeed amman tanajin tsoro, daka masa magana sai ya lalubo me zafi yake fad’a dan haka ta sunkuyar da kanta kasa”
Shiru dakin ya kuma dauka zuwa can Abdulmajeed yace”
Jita kawai, wawuyar yariya, haka kurum kinjawo ma mutane balaki, nina taba tunanin zan shigo irin wannan wajen, bama wajen ba, jifa yadda kika hada kanki da waceen taurikikin matar? Ke wlh idan ma nadage saina amsan miki d’anki nazama wawa wlh, dan ubanki bake kika dage saikin aure uban shiba, ina ruwana mani aciki?, haka kawai banci nanin ba nanin tacini, ke wlh idan har muka koma gida sai kinci Ubanki, dan bazaki wahalar dani abanza ba”
Cikin kuka Ummi ta tashi ta matsa gaban shi tana kokarin rike hannun shi yace”
Wlh karki sake ki tabani, kina tabani saina miki matsiyacin duka, dan kin rainani saikita dakunani?, ko angaya miki ni gwajone?, bake ‘yar dadin soyayya ba”
Banda kuka babu abun da Ummi keyi acikin zuciyarta ko fadi take”
Ni idan ma zaka min matsiyacin dukan, ka amsan min d’ana saiyafi min komai dadi”
STORY CONTINUES BELOW
Komawa gafe tayi taita kuka bayan ya gama hucin shi ya waigo ya kalleta, tare da fadin mayya kawai me bakin nacin tsiya, tunkina ‘yar karamar ki abin da kike so dole sai amki, wlh badan anki bani dama ba dasai na koya miki darasi, dan ni kinyi kadan namiki abinda ranki keso, ‘yar rainin hankali kawai, afusace ya juya yai waje”
Bin bayanshi Ummi tayi da kallo, acikin zuciyarta tace”
Gaskiya yaya Abdulmajeed masifaffe ne,😭😭😭 Hannu ta daga sama tare da fadin”
Allah ka yayyafawa zuciyar Abdulmajeed ruwan sanyi👏🏻 insamu ya taimakeni ibar garin nan, Allah kafini sanin halin da nake ciki, Allah kamin maganin abin da ke damuna😭😭😭👏🏻
Bata sakejin muyarn saba sai yamman, kuma har lokacin Ummayo bata dawo da Ahmeed ba, yau hankalin Ummi yafi na kullum tashi”
Tana daga daki ta hango Saminu ya wuce da ruwan zafi cike da bokiti ya nufa bandaki”
Kara matsowa tayi domin tanaji ajikinta kamar Abdulmajeed zakaiwa ruwan wankan”
Bayan ya Saminu ya ajiye ruwan ya fito ya wuceta, zuwa can saiga Abdulmajeed yana kokarin bin hanyan ban dakin”
Gaban Ummi ne ya buga sosai, afirgice tace”
Yaya”
Waigowa yayi ya kalleta da sauri domin beyi tunanin tana kallon shiba”
Karasowa tayi aguje tace”
Yaya ina zaka??, kardai kace min wanka zakayi??
Kauda kai yayi sannan yace”
Wanka zanyi, wani abune??
Eh Yaya, ai bayin gidan nan akwai wani maciji me kashe mutane, dan Allah karka shiga haka yayiwa Mukhtar daga……
Hannu Abdulmajeed ya daga mata, shi kwanan sane ya kare, babu abin da zai sameni da yardan Allah”
Juyawa yayi yacigaba da tafiya yana tunani acikin zuciyar shi, wai ummice yau ke kukaren kareshi?, jinjina kai yayi tare da cewa rainin hankali ne irin nata, zan nuna mata nafita iya iskanci”1
Harya kule Ummi na kallon shi, kasa juyawa tayi dan haka tabi bayan shi, daf da bakin ban dakin ta nemi wani dutse da zauna tanajin karan ruwan wankan sa”
Idonta firgai firgai daka kalleta kasan hankalinta tashi yake, takasa zama guri daya tamike ta zauna haka taitayi, zuwa can taji batajin karan ruwan, shiru tayi tare da dad’a saurara wa, tabas babu karan ruwa dan haka ummi ta daura hannu akai ta fasa ihu🙆🏿‍♀”
Abdulmajeed dake gurza jikinshi da soso yaji ihun Ummi sosai ihun yaba yabashi tsoro, mikewa yayi ya dauko 👖yasa, jikinsa duk kunfa ya nufa waje”
Tsayawa yayi ya tsure Ummi da ido sannan yace”
Ke! dan kutumar ubanki mekikeyi anan?1
Dagowa tayi ta kalleshi, cikin sauri ta kunshe bakinta sannan ta maida kanta kasa saka makon ganinsa babu riga”
Badake dakeba?, me kikeyi anan gurin?
Haryazun kanta nakasa tana share hawayen fuskanta”
Tashi kibar nan wajen, kagamin shegiyar yariya, ni d’anki ne?, dazakizo kina gadina, inna fito nasame ki anan wajen saina karya ki”
Sumsum Ummi tabar wajen, acikin zuciyar ta tana mematukar kosawa ya fito”
Daki ta shige, tazauna daga bakin kofa, zuwa can taga wucewan shi, ko kallon dakinta beyi ba”
Ajiyan zuciya tayi, sannan takoma kan gado ta kwanta”
Gaba daya nonota ciyo yake mata, yau kwana biyu kenan Ahmeed besha nono ba, dan haka zazzabi ya rufan mata”
STORY CONTINUES BELOW
Sai dare Ummayo ta dawo, dakin Ummi ta leka ta kureta da ido, sannan tace”
Zanga karyan naci, wato kuna nan har yanzun baku wuceba ko?, goyon Ahmeed ta juyo mata dashi, tare da fadin wannan yaron yafi karfin ku, haka zaku gama nacin ku kubar min jikana, kenan adole me dan uwa, toh ni dashi muzuba, fitsararren yaro kawai, afusace Ummayo ta juya ta fita”
Ummi ko tagumi tayi tare dajin wani irin zafi atsakiyar kirjinta, ji take tamkar ana suka mata kibiya, ga zazzabi dake shirin rufar mata, dan haka idonta yai jawur tamkar garwashi”
Shiko Abdulmajeed bayan yayi Sallan isha’i kwaciya yayi domin yagama tsara yadda tafiyan su gobe zai kasance”
Rashin gani Abdulmajeed ya kara ruda jikin Ummi, dan idan bata ganshi ba gani take kamar ya gudune ya barta”
Washegari da misalin 7:12am Abdulmajeed ne ya shigo dakin Ummi goye da jakarshi, Saminu na binshi abaya, dagowa Ummi tayi ta kalleshi, cikin sauri ya kauda kansa kamar bazaiyi mgn ba”
Sunan Saminu ya kira, sannan ya mika mishi wasu kwayoyi guda 4, cikin sauri Saminu yakarba yabar dakin”
Cikin takun kasaita Abdulmajeed ya zauna abakin gadon sannan yace”
Tashi mutafi”
Dagowa tayi ta kalleshi sannan ta maida kanta kasa”
Ko bakiji me nace bane?
Jiki na rawa tace naji, akwatin su tanufi jawowa, cikin sauri ya dakatar da ita, me kuma zakiyi?
Zan canza kaya ne?
Hmmm, bazaki canza ba, dashi zaki tafi, ko kin manta takaba kike?, dallah malama tashi mutafi”
Mikewa tayi ta gyara dauren zaninta sannan tajawo rigar zuwa daidai kugunta, kayanta kallah sosai, sai ayanzun take iya tattace kalar kayan, kayane irin na fulani nasaki, saidai wannan bakine ba fariba”
Duk abin da take Abdulmajeed na kallonta dan haka tai sauri rufa bakin mayafita”
Mikewa yayi yana kokarin fita Ummi tai saurin bin bayashi, hartakai kofa, tajuya takalli akwatin kayansu ita da Mukhtar, kukane yaso kwace mata sai dai babu hali, dan haka ta share hawayen tare da bin bayansa”
Abakin dakin Ummayo Abdulmajeed ya tsaya ya nunawa Ummi hanya tare da fadin”
Shiga kiyi mata Sallama”
Shiga dakin tayi, ta durkushe akasa tagaida Ummayo, sannan tace zamu tafi”
Cikin wanne irin murya mekama dana maye Ummyo tace”
Madallah, ku gaida gida”
Mikewa Ummi tayi tana hango yadda Ahmeed keta wasa agado saima daga kafa yake tare da hannayen sa”
Tana tafiya tana waiwayen Ahmeed batasan nufin Abdulmajeed ba, ya mata Alkawarin zai karban mata danta, amman taga bece komai akan Ahmeed ba”
Tana tafe tana kuka, mutanan uguwa sai sallama suke musu dan zamanshi garin nakwana 2 jama’a da dama sun shaida zuwan shi”
Har sukai nisa, suka fita daga gidajen Ummi kuka take, bakomai ke kona mata zuciyaba illah barin Ahmeed da zatayi agarin nan”
Basu hango komai agaban su sai bishiyoyi, dan haka Ummi ta juya ta kalli garin sosai ta fashe da kuka”
Wuceta Abdulmajeed yayi batare da yace mata kalaba”
Sunyi nisa sosai sun fara shiga cikin bishiyoyi Abdulmajeed yazauna abayan wata bishiya yana cigaba da hura hanci”
Cikin rashin kuzari Ummi ta tsaya tana kallon shi”
Sun dade agurin daga can ta hango Saminu yana tahowa rugume da bakin zanin goyon Ahmeed”
Zabora tayi tare da kura masa ido taname son tabbatar da abinda take zato”
Saminu na karasowa ya Mikewa Abdulmajeed Ahmeed”
Mikewa yayi tare da girgiza kai, sannan yace, bata kayanta”
Jikin Ummi na rawa ta amsa Ahmeed, idonta cike da kwallah take fadin”
Nagode Saminu”
Goya Ahmeed take jikinta na rawa, gaba tayi domin gani take tamkar Ummayo zata biyosu ta kwace Ahmeed, tafiya take tana waige waige”
Shiko Abdulmajeed Tsayawa yayi suka yi Sallama da Saminu sannan yabi bayan Ummi”
Gani inda take zuba sauri, taso tabashi dariya, daga ganin shigarta zuwa tafiyanta kasan taji jiki, dan haka ya bude baki yace”
Ke! bazar bazar, sauri me kike?, dallah zoki koma baya” dan idan nacigaba da kallon ki firgita zan dingayi cikin dare………
1
*Mmn Yazeed**KOWANNE BAKIN WUTA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
( da nashi hayakin)
💨💨💨💨💨💨💨
Story & Written by
*Fadeela Lamido*
*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*
Wattpad @fadeelalamido
29 – 30
Komawa bayanshi tayi amman gani take kamar baya sauri, wanni irin tafiya yake ta takama gabanta”
Dole haka ta hakura tabi bayan shi, cikin tsananin fargaba, sosai Abdulmajeed ya kara kima a idonta, nan ta daukan makanta alkawri, duk zagin da Abdul zai mata bazataji haushi ba, domin tasan ta wahalar dashi”+
Sunyi kamar tafiyan awa 4 zazzabi me zafi ya rufe Ummi, ban da rawan jiki babu abun da jikinta keyi, Abdulmajeed besan me take cikiba, domin shi yayi gaba, jin da yayi bejin takunta abayan shiba yasa shi juyawa”
Hangota yayi acan baya tana tahowa jikinta sai kerma yakeyi, sosai ta bashi tausayi, tsayawa yayi yana kallon ta harta karaso, ahankali yace”
Lfy kuwa??
Sanyi nakeji sosai Yaya”
Kauda kai yayi sannan yasa hannun sa ya taba jikinta, zafi rau yaji, dan haka yaji babu dadi ko yanzun yaya za’ayi kenan?
Cikin sauri ya Sakko da jakarshi ya dauko wasu magani tare da goran ruwa ya mika mata cikin rawan jiki ta karba ta rike ahannu, tare da fadin muje toh”
Muje ina??, magani fah na baki kisha kuma kina cemin wani wai muje”
Yamutsa fuska tayi nifa bana shan magani”
Ke! Karki kawo min iskanci maza kisha mu wuce mubar gurin nan”
Saka maganin tayi abaki, sannan ta zuba ruwan, kokarin kakarin amai take dan haka Abdul yace”
Wlh kikamin Amai saikin shanye shi”
Kara kunshe bakinta tayi, tare da zamewa kasa”
Kamar bazai taretaba, ahankali ya tsuna tare da kokarin dagata, amman Ummi kara kudundunewa take tamkar zata shiga cikin kasa”
Ganin haka yasa Abdul ya tsorata, rike cewa yayi saidai yana kokarin dannewa, cikin tausasasiyar murya yace”
Menene haka?
Sanyi nakeji yaya, bazan iya tafiya ba, dan Allah ka rufeni”
Dame zan rufeki Ummi, kin dai san babu wani abu anan gurin dan haka ki tashi muje”
Kara dunkulewa take guri guda, gashi yaron dake bayan ta ya dara kuka, babu yadda zaiyi dole ya dauke shi, hannunsa yasa ya kwace goyon ya dauki yaron, sannan ya mike ya rufeta da zanin, kin kallon fuskan yaron yayi duk da cewa yanata ma zuciyar shi fada ta bari ya kalli yaron amman ya gagara yin haka”
Akirjin shi ya kwantar dashi tare da buga bayan shi, harya samu yai shiru”
Juyawa yayi ya kalli inda Ummi take, tana rufe da bakin bayafi kalar kayan jikinta, amman jikinta bebar kermaba, kamar ma karuwa yake, tausayin ta yaji ya kamata, dan Allah wannan wacce irin rayuwa ce?, ahankili ya fara takawa inda take”
Tsugunawa yayi agabanta sannan yasa hannun ya taba jikinta, har yanzun zafin nanan “
Dan haka hankalin shi ya kara tashi, zama yayi agurin sannan ya dagota kwantar da ita yayi akan kirjinshi, sannan yasa hannun shi zagayeta, daga ita har Ahmeed lafewa sukayi akan kirjinshi, bayan ya gama kare mata kallo ya kwantar da kanshi akan nata”
Wani irin tausayinta yakeji wadda betabajin irinsaba, dan haka yaji kwala ta cika mai ido”
Mannewa Ummi tayi ajikin shi sosai, bakajin komai sai numfashin su”
STORY CONTINUES BELOW
Kafin wani lokaci, Ummi ta fara zufah, wani irin ajiyan zuciya Abdulmajeed ya sauke, sosai zufa ke karyo mata Abdulmajeed na goge mata”
Dagowa tayi ta kalleshi, cikin sauri ya kauda kanshi tare da hade fuska”
Tashi Ummi tayi ajikin shi, tana me kallon fuskan shi, tace”
Nagode yaya”
Daure fuska yayi tamau yana kallon guri daya sannnan yace”
Ki daina min godiya, domin ni badan ke nayi ba”
Wani gutum murmushi Ummi tayi, sannan hawaye ya zobo a idonta, cikin siririyar murya Ummi tace”
Yaya dan Allah idan wani abu na maka ka yafemin,👏🏻 wlh banajin dadin yadda kake min”
Ke! Ummi tashi mu tafi, karki nemi ki raina min hankali nasan abin da nake, dole kice zakiban hakuri sabo da babu wannan wawan mijin naki”
Shiru Ummi tayi, domin ta kula Abdulmajeed da gaske yakeyi, sai yanzun take hararo Abin da Mukhtar yake fadin mata, akullum fadin yake yayanki fah Son ki yake, shiyasa yakejin zafinki”
Hawaye Ummi ta share tabbas ta fara gano haka, domin bata tabajin yakira sunan shiba, sai dai yace wancen wawan, ko kuma ya kirasa dan cirani, gashi har bayan mutuwan sa be canza mai sunan ba, har yanzun yana kiran sa da wawa, nikuma bansa me nayi masaba yakejin haushin, amman koma menene, idan Allah ya kaimu gida, zansa su Abba subashi hakuri”
Juyawa tayi ta kalleshi ganin inda yake huci shi kadai yasa tacigaba da fadi acikin zuciyarta”
Wannan irin su matansu zasusha wuyan zama dasu, gashini haka kurum yanata fushi dani kuma ni bansa me nayi masaba, adacen babu ruwansa dani, ko magana bata hadani dashi, hannu tasa tasa tana share hawaye”
Mikewa Abdulmajeed yayi ya fara tafiya har yanzun Ahmeed na bacci akirjin shi”
Saida yayi nisa sannan ya waigo yace”
Idan kin gama zagin nawa saiki taso muje”
Mikewa tayi cikin gudu tabi bayan shi tana cewa wlh ban zageka ba”
Tsaki kawai yaja yai gaba dan haka taitabin shi abaya”
Har yamma suna tafe sai dai Abin da yabata mamaki har yanzun Abdulmajeed be nuna ya gajiba, tafiyarsa kawai yake kamar yadda ya fara da farko”
Sai yamma likis suka isa Bakin yanki, lukacin kafar Ummi banda zugi babu abin da take, wa wani ciyo akafarta, wadda bata lura dashiba sai yanzun”
Tsayawa taga Abdulmajeed yayi dukda tarin motocin dake wucewa agurin”
Waya ya ciro ya dannan kiran Sadiq”
Tunkafin wayar takai kunnensa yaji Sadiq na fadin”
Doctor kana ina ?, ka fito ne ?
Sadiq kuna lfy?
Kai zan tambaya doctor kaida ka shiga jeji, kana lfy ko?
Ina lfy Sadiq nafito yanzun nan”
Kardai ka cemin baka samu nasaran fitowa da Ummi ba??
A’a muna tare tana kusa dani”
Toh Alhamdulillah, gani nan zuwa”
Sadinq ina ganin ku gayamin inda zamu hadu kawai, tsayawa anan wajen hatsari ne, domin Mahaifiyar wannan wawan bamu rabo da ita ta arzikiba, dagewa tayi wai sai dai ta rike yaron, ita kuma Ummi dayake mayyace itama tanace saita taho da yaron, dan haka tana iya sawa abiyomu”
STORY CONTINUES BELOW
Shiru Ummi taji yayi zuwa can ya kashe wayar yasa a aljihu, sannan yai gaba abin shi”
Bin bayan shi tayi, tun kan takarasa taga yatsaida wata mota yana musu bayanin inda zai kaisu, sai dai abin da yabawa ummi Mamaki irin babban motar nance ta daukan kaya, tana karasawa taga saura gurin mutun daya ne agaban motar”
Bude mata murfin motar yayi sannan yace shi”
Batai musuba ta shiga ta zauna, sannan ya daura mata Ahmeed akan cinyanta”
Juyawa yayi ya nufa bayan motar, dan haka Ummi ta leko taga me zaiyi kuma”
Kwallah ce ta cika mata ido lokacin da taga Abdulmajeed ya kama karfen motar yana kokari darewa bayan motar”
Sosai take zubar da hawaye, gaskiya Abdulmajeed mutum ne, mezan mishi na sakamai da abin da yayimin???, hawaye ta share sannan tace”
Kai koma mezan mishi bazan iya biyanshi wahalar dayasha ba, sai dai nace mishi Allah ya sakamai da Alheri👏🏻
Kwarara gudu motar keyi, bakajin komai sai karan iska, sosai Ummi kejin sanyi, dan haka ta shiga tunanin Abdulmajeed, ko wanne hali yake ayanzun?
Da misalin 11:34pm suka shigo cikin garin Niger Ummi ta gane hakan sadanin haskin fitilu da tafara gani”
Abakin wane Hotel drive ya tsaya, sannan yacewa Ummi anan zaku sauka ko?
Cikin rashin sani tace ni ban saniba saidai na tamboyoshi, sakkowa tayi tana me kallon bayan motar”
Abdulmajeed rakube ya tura hannuwan shi tsakiyan kafafunshi alamar sanyi yakeji”
Ganin Ummi yasa ya dago kansa ya kalli gurin sannan ya sakko, kudi ya ciro ya biya memotar sannan yaciro waya yasa akunnen shi”
Zuwa can yace gani agurin”
Cikin mintin da befi 3 saiga Sadiq da Nafisa suna fitowa daga cikin Hotel din”
Sadiq kadai Ummi ta iya shaidawa dan haka ta shigawa Nafisa Kallon rashin sani”
Abdulmajeed da Sadiq kuwa rungume juna sukai, Sadiq sai bashine baki yake, shikuma Abdul yana yamutsa fuska”
Gurin Ummi Nafisa ta nufah tare da fadin”
Sannu da zuwa Ummi, hannu ta mika ta amsa yaron tana cigaba da cewa Ya hakuri?
Cikin kallon rashin sani Ummi tace”
Alhamdulilahi”
Tafiya suka fara Abdulmajeed da Sadiq suna gaba, yayin da Ummi da Nafisa suke baya”
Bayan sun isa dakin dayake masaukin nafisa, Ummi ta zauna ta zuba tagumi”
Sadiq da Abdulmajeed ma dakin suka shiga, ko zama Abdulmajeed beyiba yace”
Wanka zaiyi domin yana jin kyamar jikin sa”
Ya dade a toilet zuwa can ya fito yana goge jikin sa, wayarsa ce tai kara dan haka yai saurin dubawa”
Nafisa ce, dauka yayi ya kara akunnen sa”
“Oga nace yakamata asawowa Ummi kaya ta sauya”
Hmmm Nafisa wannan yariyar barta yadda kika ganta, wanne halallen ne zaije sawo mata kaya??, katse kiran yayi tare da ajiye wayar”
Sadiq ne ya sakko daga kan gadon yana fadin gani ai sai naje na sawo, yariyar taban tausayi, gata ‘yar karama jarabawa, irinta rayuwa ta sameta”
Sadiq kar kaje ko ina, wlh ko ansawo mata kaya bazata sakaba, nafi son kowa yaganta ahaka, ahaka zata gida, wannan kayan da kagani wai sune kayan takaban garin, idan kaga dakin danaga Ummi aciki kuwa ko almajiri yafita galihu”
Mikewa Sadiq yayi yana fadin Allah sarki, nasan dataganka zataji dadi”
Hmmm ‘yar banza ba, kamani tayi taita dakunani, kasan Allah?, badan taban tausayi ba alokacin data rugumeni so nayi inmaketa”
Dariya Sadiq yayi sannan yace”
Adai dinga hakuri, yanzun barin insamo mata kaya, kaga be dace taje gida ahakaba , ahakalin su zai tashi idan sukaga Ummi da wannan shigar”
Hmmm kasan Allah Sadiq?, dole sai Ummi taje gida ahaka bazata canja kayaba, inma kasawo Mata kayi asaran kudi ne”
Sadiq be sake cewa komaiba ya koma ya kwanta domin yafi kowa sanin kafiyan Abdulmajeed”
Bayan Majeed ya gama shiryawa’ bashin sallolin da ake binsa yayi, sannan yadan kishingida, zuwa can ya mike yajawo jakar shi, Sigari ya dauka guda daya yana kokarin kunnawa Sadiq yai saurin cewa”
Doctor karka kunnamin Sagiri anan, wai har yanzun bakabar wannan dabi’ar ba?
Batare daya kalli inda Sadiq yakeba yace”
Kayi hakuri kara daya zan sha, kaga tunda nashiga jejin can ban shaba, ahankali zan bari”
Cikin matsanancin Haushi Sadiq yace”
Abdulmajeed kasan ni ban son warinta, karka kunna, ida kuma ka bari nashaki warinta Allah ya isa”
Allah ya isa??, tsaki yaja sannan ya mike yai waje”
Dakin Nafisa ya nufa, tun ahanya ya kunna sigari yana tafe yana sha, da karfin ya tura kofar”
Dan haka Ummi dake kwance akan gado tai saurin juyowa”
Runtse ido tayi tare da fadin Subuhanallahi, sai yanzun ta tuna ta tabajin warin sigari adakin sa, ashe hancinta gaskiya ya gayamata, abin ma ko kyau be masa ba, cikin takaici ta kuresa da ido”
Yana busa hayakin yace”
Meye kike kallona”
Dauki idonta tayi, amman ganin Nafisa tai saurin sauka daga kan gadon yasa ta kara kallon gurin”
Ummi na kallo Nafisa ta nufi gurinsa, hannu tasa ta dan ruko nasa hannu”
Kara bude ido Ummi tayi tana kallon ikon Allah”
Akan kirjinshi ya kwantar da Nafisa, tare da zame dan kwalin dake kanta”
Duk da cewa babu wani gashin arziki akanta amman Abdulmajeed sai tura hannun shi yake yana yamutsa gashinta”
Wani kululun abu ne ya tsayawa Ummi atsakiyan kirjinta, acikin zuciyarta tace”
Yaya Abdulmajeed yai aure ne, bayan tafiyata? Koko karuwansa ce nake zaune da ita?
Wani irin kallo ta sake musu me ciki da tsana, har yazun Abdul bebar abin da yake ba, kamar ma nafisan ce take nukewa, zuwa can yajata zuwa toilet”
Cikin mummunan tashin hankali Ummi tashi ta zauna, tarasa abin dayasa ta kasa natsuwa, Abdulmajeed da take ganin shi haka ashe tantirin dan duniya ne, wata zuciyar ce tace, kika sani ko matarsa ce?
Sun kwashe kusan minti 15 aciki, sannan Nafisa ta fito, kanyan dake jikinta duk sun ya mutse”
Kallonta kawai ummi tayi sannan ta kauda kai, ji take kamar ta shageta”
Zuwa can Abdulmajeed ma ya fito cikin tsare gida saidai idon shi yayi jawur kaman garwashin wuta, wanni irin kallo yayiwa Nafisa sannan ya girga kai yace zaki sani, juyawa yayi gurin Ummi yace”
Ke kuma karki yadda naji wani lbr agida, baruwanki da sha’nina”
Kasa magana Ummi tayi, sai faman ajiyan zuciya tayi, tare da dafe kirjinta……..
*Mmn Yazeed*
[KOWANNE BAKIN WUTA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    ( da nashi hayakin)
💨💨💨💨💨💨💨
Story & Written by
    *Fadeela Lamido*
*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*
    Wattpad @fadeelalamido
              31 – 32
Juyawa yayi ya fice, yayin da Ummi ta juyar da kallonta ga Nafisa”
   Cikin wanne irin yanayi nafisa ta juyar da kanta, da alama kamar tanajin kunya, wanne irin sanyi jikin Ummi yayi, yayin da ta kosa dubar gurin”
           **  *** ****
Ummayo kuwa sai dare ta farka, agigice ta tashi tana dube dube akan gadonta, ganin babu Ahmeed babu zanin goyonsa yasa ta wuntsulo da kan gadon”+
   Tsakar gida ta nufa tana uhu tare da kururun waye ya daukan mata Amadu”
    Gaba daya gidan tarowa akayi akan Ummayo kowa fadi yake besan inda yaron yakeba”
    Cikin matsanancin Kuka Ummayo tayi waje tana cigaba da kiran jama’ar gari, bayan kowa ya hallara, Ummayo tace”
    Tanason Samari majiya karfin subi mata hanya, domin tasan babu wadda zai dauki yaron sai matar muntari da d’an uwanta”
       Dayawa daga cikin mutanen garin sheda suka bayar kancewa sunga wucewan Su babu yaro ahannun su, kuma ko kayama basu dauka ba”
    Cije lebe Ummayo tayi sannan tace ina saminu???
    Arikice ta juya ta nufi dakin saniu, kara damke idonshi yayi kamar me bacci domin duk abin da suke yana jin su”
   Wani wawan duka ta d’aka mishi, arikeci ya mike yana sosheshe, ina Amadu???
    Cikin yatsuna fuska yace”
   Ina nasan inda yake, ai ni yau kwata kwata ban dauki amaduba, ki duba cikin gida mana”
    Mike Saminu, maza tashi, duk gidan nan babu Amadu”
   Haba Ummayo garin yaya haka ta faru?
   Hmmm nifa nakwanta bacci tare dashi, bansan yadda akayi ba bacci ya kosheni”
   Sakkowa Saminu yayi arikice tare da fadin”
   Tun yaushe hakan ya faru??
    Saminu tun lokacin da ka amso min kunu gurin babandi nasha, ba jimawa na farajin bacci, ban kwantaba sai bayan su Zainabu sumin sallama sannan nahau gado na kwanta tare da Amadu”
    Toh aini Ummyo kin manta tun lokacin namiki Sallama na wuce gona?, banga tafiyan su mmn Amadu ba, kuma lokacin dana dawo banga yayanta ba, nashigo dakin ki domin intambaye ki saina iske kina bacci”
   Ajiyan zuciya Ummyo tayi shiko saminu sunkuyar dakai yayi kamar me nazari”
   Zuwa can ya zabura ya mike tare da fadin”
  Ummayo babu wadda zai dauki yaron nan sai bakon Zainabu, dan haka mubi hanya kawai”
    Ficewa yayi arikice yanata faman hoci, suna fitowa ya nufi hanyar Bakin yanki”
  Wani dake cikin mutanan ne ya kirashi tare da fadin, karka wahalar da kanka domin yanzun na tabbatar sun dade da barin kauyen nan tun safe fa suka tafi kuma kasan bazosu tsaya wasaba”
   Cikin mummunan tashin hankali Ummayo tace”
   Yazama lallai inje Nigeria domin bazan bar gudan Jinjina awani waje ba, bare jinin Muntarina wlh bazan barmusu shiba”
STORY CONTINUES BELOW
   Hawaye saminu ya share tare da fadin Eh eh Ummayo haka za’ayi yazama lallai mubi bayan su, kodan musan takamai man inda suke”
   Cikin matsanancin kuka Ummayo tace”
   Bazan sake farin cikiba sai ranan danaga Amadu, haka kuma bazan sake dariyaba sai lokacin danaga amadu, daman wannan yaron daganin sa tantirine,  baya shakkan kowa, ji inda ake girmamani agarin nan amman shi fadi nake yana fada, saboda rashin tarbiya, toh nikuma zan gwada masa nacina, wlh sai anbani jikina, kanada wayar megidan muntari ko?
    Jinjina kai Saminu yayi alamar eh, dan haka Ummayo ta sallame kowa, tare da alkawarin zuwa Nigeria”
   
                **  ** **
Ummi kuwa kasa kwanciya tayi da Nafisa guri daya, tunda nafisa tahau gadon ita ta fara kokarin sauka kasa”
    Ganin haka nafisa tabar mata gadon ita kuma ta koma kan kujera”
   Washegari, ma bayan gai suwa basu sake mgn ba”
   Har sukayi wanka suka shirya Fuskan Ummi daure take”
     Zuwa can taga Nafisa na waya, sai dai batasan dawa take ba, bayan ta sauke wayar ta mike ta canza kaya, kallon Ummi tayi tace”
     Ina zuwa Ummi”
    Dakai Ummi ta amsa mata”
   Bayan fitanta ba jimawa Ummi ta kasa hakuri, dan haka ta tashi ta leka window dake dakin”
    Abdulmajeed taga ya bude motar ya shiga, zuwa can ta hango Nafisa itama tashi cikin motar, sosai takarajin damuwa”
    Kusan minti 5 motar bata tashiba, dan haka ta kara gyara tsayowarta, saida ta kwashe sama da minti 30 bataga fitowan suba, dan haka ta fara tunanin me sukeyi acikin motar haka, yaushe yaya ya zama dan iska, ko daman abin da yakeyi kenan shiyasa yakiyin aure?
    Hawaye taji yana zobo bata, shafowa tayi ta kallah, acikin zuciyarta tace”
   Kukan me nakeyi?? Ina ruwana da iskancin sa, tunda basonsa nake ba, meya dameni dashi, tsaki taja sannan takoma gefe ta zauna, acikin zuciyarta tace toh kima idan ya dauko wani ciwon aita shafeni”
    Bayan minti 10 ta kasa hakuri, sake komawa tayi har yanzun motar nan agurin”
    Hakanan taji azuciyanta bata son tasake hada ido da Nafisa, Har ga Allah ta tsaneta, kwata kwata bata son ta sake ganinta, da ace tana da kudin dazaitai kudin mota wucewarta zatayi”
   Huci taitayi ita daya, gaban iyayenta kawai take son ta ganta dan intacigaba da zama anan akwai matsala, tunanin Sadiq ne ya fado mata dan haka ta mike ta goya Ahmeed sannan ta nufa dakin dataga sun shiga jiya”
   Kwankwasa kofar tayi, daga ciki Sadiq yace waye??
    Cikin siririyar muryanta tace nice Ummi”
    Tasowa Sadiq yayi, ya bude kofa, bayan sun gaisa yaga Ummi na kokarin shiga ciki, cikin sauri yace”
    Abdulmajeed din bayanan yadan fita, wani abu kike so???
     A’a daman gurin ka nazo?
    Gurina?, bude kofar yayi yabata hayan ta shiga ta zauna akan kujera, sannan ya zuna abakin gado, tare da fadin”
   Inajin ki Ummi yaya akayi???
    Hawaye ne ya fara zubo mata daker ta iya bude baki tace”
    Dan Allah so nake ka taimaka min da kudin mota zan wuce gida”
   A’a Bangane zaki wuce gidaba, muma ai yau din zamu wuce, ko Abdulmajeed din begaya miki ba?
    Dagowa Ummi tayi ta kalli Sadiq sannan ta sake cewa”
STORY CONTINUES BELOW
   Eh be gayamin ba, amman ninafi son natafi ni daya”
   Saboda me? Mu da mukazo mussaman dan mutafi dake sai kuma mukoma daban daban??
   Kukan da Ummi takeyi yasa Sadiq fadin”
   Ummi ko wanni abu aka miki ne?
   Girgiza kai tayi, alamar a’a”
   Jiba Ummi, karki boye min komai, nima dan uwanki ne kamar Abdulmajeed, duk abin da yake damuki ki gaya min, karki boyemin komai”
    Share hawaye tayi, tare da sunkuyar dakai ahankali tace”
    Yaya Sadiq ni waccen Nafisan ce ban yadda da itaba, inason nasan wacece ita, ko matar sa ce?, nina kasa fahimtan abin”
    Gutun murmushi Sadiq yayi sannan yace”
   Kinga Ummi, bansan me zance miki akan alakar su ba, yadda kika gansu haka nima na kansu, dan haka kiyi hakuri har mukoma gida”
   Wani hawayen ta sake sharewa sannan tace”
    Yayana yazama mebin mata kenan? Kuma fah har sigari naga yanasha, alhalin ada ba’sanshi da wannan halayen ba”
    Ummi kiyi hakuri kawai, lokaci daya Abdulmajeed ya sauya halayen shi, kullum cikin mai fada nake amman bayaji”
    Kuka Ummi tayi sosai tanajin takaicin halin daya saka kan shi aciki, tare da tsanar Nafisa me tsanani”
   Kuka Ummi kiyi babu ji babu gani, Sadiq yaita lallashinta bayan ta lafa da kukan yace tashi ta koma dakin su”
   Fafur Ummi takiya, dan haka Sadiq ya mike ya kama kugu”
   Ummi kitashi ki wuce dakin ku kishirya”
   Cikin kuka tace”
  Ni bazan koma dakin ba, banason ganin Nafisa da duk wani abin daya shafeta, ka taimakeni kabani kudin mota na wuce gida, ko kuma ka kiramin Abba ko daddy awaya,  domin bazan shiga mota daya da waccen ‘yar iskan ba”
   Cikin ido Sadiq ke kallon Ummi, lallai akwai aiki, acikin zuciyarshi yace ashe Ummi ma rigimammiya ce??
   Daidai lokacin Abdulmajeed ya shigo ganin Ummi yasa ya kara hade fuska, tare da fadin ita kuma wannan me takeyi anan??
   Juyawa Sadiq yayi ya kalli Ummi sannan ya kalli Abdulmajeed yace”
    Yakamata ka sallami Nafisa”
   Yamutsa fuska yayi bangane insallameta ba?
   Eh ina nufin kabata kudin mota tai yi gaba”
   Saboda me?, motar bazata ishemu bane?, juyawa yayi ya kalli Ummi, cike da tuhuma sannan ya juya ya kalli Sadiq yace”
   Metace maka??
  Ajiyan zuciya Sadiq yayi sannan yace”
  Akan Nafisa ne, tazo tana rokon inbata kudin mota ta wuce gida dan batason ta jera tafiya da Nafisa”
    Hmmm, lallai ma yariyar nan kin raina min hankali, dan Ubanki kin samu na cetoki daka bakin kura har kina da bakin mgn? Na lura duka kike so, tashi kibar nan wajen dan Uwar ki”
    Acikin zuciyarta tace Uwata ta gode, amman banga wadda ya isa ya kuma hadani da Nafisa ba”
   Kanta yayo badake nake mgn ba?
    Sadiq ne yai saurin shiga tsakiya yana fadin karka tabata, tana da gaskiya ai, yayi maka kyau hakan, kuma ina baka shawara kaje ka sallameta”
  Kadaina min irin haka Sadiq, ummi kawanta ce ba uwataba, ita bata isa tasani inyi abinda ranta kesoba, wlh tayi kadan ta juyani, ina ruwanta da Nafisa meya dameta da ita?
    Kallon shi kawai Sadiq yayi, sannan ya juya ya kalli Ummi yace”
   Ke Ummi kiyi hakuri ki koma cen din”
    Yi tayi kamar bataji ba, tacigaba da share hawaye”
    Sadiq ya dad’e tsaye yana jiran ummi, amman sam taki tashi, duk da hararan da Abdulmajeed yake gallah mata”
     Sadiq ban da kallon su babu abin da yake, idan ya kalli fuskar Abdulmajeed saiya juya ya kalli ta Ummi”
     Zuwa can yayi Murmushi sannan yace”
     Toh shikenan Abdulmajeed tunda Ummi taki komawa can saika tashi mushirya mutafi”
    Bata isaba wlh, kai ni nama fasa tafiya yau, sai gobe, kuma nabaki nan da minti biyar kibar dakin nan”
     Kallon shi kawai Sadiq yayi sannan yace”
    Ok shike nan, ke Ummi tashi muje nasamar miki naki dakin”
    Cikin sauri ta mike tabar dakin, Sadiq nabinta baya”
     Jinjina kai Abdulmajeed yayi, tare da fadin lallaima yariyar nan, waini zata nunawa taurin kai, ashe haka take da shegen kafiyar tsiya?, zan nuna mata niba irin mazan da ake juyawa bane”
     Cikin kankanin lokaci Sadiq ya shigo yana dariya, tare da fadin”
    Wlh al’amarin ku wani zubin yana bani dariya, kai kullum cikin haushi kake, kana cewa Ummi bata sonka, amman ni sai naga kamar Ummi kishin ka take, abin da na lura dashi, ita kanta batasan meye so ba”
    Ba waninan, tsabar iskanci ne, yariyar da har taje aka mata ciki, kake fadin batasan so ba?, ai ita ma tafi kowa sanin So tunda har tabi wannan wawan yaron kauyen su, ai inkaji ana cewa ‘yar gani kashenin soyayya toh Ummi ce, sai da ranta fa tayi, ai duk wadda ya sake ya aureta ya aure gaibu dan bason Allah da annabi zatamai ba”
      Hmmm doctor kenan, ya kamata ka aje makaman ka, dan karka rasa Ummi akaro na biyu”
   Sadiq kenan, kana abu kamar bakasan halinaba?, mezan ci da Ummi?, jifa yadda ta dawo saikace kazar mayo, idan na aureta ainaci baya”
     Dariya Sadiq yayi sosai sannan yace”
   Wlh Abdulmajeed kai hankali da kanka, kuma ka kiyayi bakin ka, duk kabi ka tsangwami yariya kasata gaba, da zagi da hantara?, ina guje maka ranan kin dillaci fah, domin ni bazani rarrashi ba”
   Lallai Sadiq kama raina min hankali, wai ina hauka ne zan aure Ummi? Acikin bainar jama’a fah ta bude baki tace bata sona, sai nine zan furta mata kalmar so?
   Indai nine wlh bazan taba furta mata soba, kuma wlh bazan aureta, sai da ta zama shaura”
      Hmmm, Abdulmajeed kenan, yanzun dai Ummi tace bazata shiga mota daya da Nafisa ba, dan haka kasan yadda zakayi da ita”
    Ai bata isaba Sadiq, kuma nasan abin da tagani jiyane yabata yaushe, ina sane nayi, sai dai ta mutu wlh, idan wani ya kika ai wani zai soka, shiyasa na nuna mata, kuma ni Nafisa ta gama min komai”
     Eh, dole kace tagama ma komai, tunda kana samun biyan bukata da ita”
   Wanne irin mgn ne wannan Sadiq?, kafi kowa sanin niba dan iska bane”
Da ba, amman banda yanzun, d’an iskane kai tunda kake tare da ‘yar iska, mara tarbiyya lalattaciya”
     Cikin fushi Abdulmajeed ya mike, karka sake ce mata ‘yar iska, domin aurenta zanyi, kuma ni bantaba zinaba, dan haka karka kara cemin dan Iska……..[9/1, 8:59 PM] ~🇭 🇦 🇺 🇼 🇦✨: 🔥 🔥🔥🔥🔥🔥
*KOWANNE BAKIN WUTA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    ( da nashi hayakin)
💨💨💨💨💨💨💨
Story & Written by
    *Fadeela Lamido*
*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*
    Wattpad @fadeelalamido
              33 – 34
Azuciye Sadiq yabar dakin, domin ya fara gajiya da halin Abdulmajeed, sosai yaji ransa yabaci, wai har Abdulmajeed ne yake tutiyar zai auri nafisa, yariyar da bata da mutunci bare tarbiya, daga shigarta zaka gane batasan darajan kantaba, kuma ya lura abin da yake rudan Abdul kenan, ya rasa yadda akayi Abdulmajeed ya zama haka, bayan ada duk kwarkwasan da mace zata masa ko kallo bata isheshi ba, amman rana tsaka ya sauya halin sa”+
    Takaici ne ya isheshi, ji yake kamar yai tafiyan sa yabar su sukarata, amman kuma Ummi na bashi tausayi, koda ya koma dakin beceda Abdulmajeed komai ba, har Washegari, tunda suka dawo sallah asuba kowa yahau shiri, sai dai babu wadda kewa wani mgn, dan haka Abdulmajeed ya kalli Sadiq yace”
    Wai gaba kake dani ne?
   Cikin daure fuska Sadiq yace”
   Yaya zanyi gaba dakai kawai banajin yin mgnr ne”
    Hmmm, Allah yabaka hakuri, ni ban ma mgn dan kai fushi dani ba, kawai nagayama abin da ke cikin zuciyata ne”
   Banza Sadiq yayi dashi zuwa can Abdulmajeed ya sake cewa”
   Daman abin da nake son nace ma, dan Allah karka karasa saka mana baki tsakanina da Ummi dan hakan zaisa ta raina ni”
    Toh bazan kara ba, cewan sadiq alokacin daya kawar da kansa gefe”
    Abdulmajeed da Sadiq ne suka fara fitowa Nafisa ko ta tsaya wai tana jiran Ummi”
    Zuwa can Ummi ta fito rungume da danta, wuce Nafisa tayi tamkar bata gantaba, cikin sauri tabi bayan ta”
    Cugewa Ummi tayi agefe, Nafisa ko harta shiga motar ta zauna, juyowa sadiq yayi ya kalli Abdulmajeed sannan yace, kai zaka jamu?
    A’a sai dai kai, Danni har yanzun gajiya bata sakeni ba”
    Ba musu Ya wuce ya bude dayan gefen yacewa Ummi yi hakuri kizo ki zauna agaba”
Wani irin kallo abdul yamai bangane ta shiga gaba ba, nikuma fah??
     Kai ku zauna da Nafisa, ina ganin hakan zaifi”
    Kafada ya dage alamar  ku kukassani🤷🏼‍♂ sannan ya  zagaya ya zauna, kusa da Nafisa”
     Ummi ko har yanzun bata shigaba tana tsaye awaje dan haka Sadiq yace”
    Ke! Wai badake nake mgn ba?
    Kokarin bude baki take, dan haka Sadiq yai saurin cewa karkice min komai, indai kina ganin kimata kishi muje”
     Share hawaye tayi sannan ta shige motar da zauna”
  Hanyan suka dauka kowa da abin da yake sakawa”
    Nafisa ko ayanzun ta shiga fargaba, domin sauyawar Ummi abaiyane yake, dan haka abin duniya ya isheta, ita da take fatan kowa cikin dangin Abdulmajeed su sota, sai gashi akaron farko ta faracin karo da kiyayar Ummi”
    Abdulmajeed ma ganin inda Ummi ta dauke kai daga inda suke abin ya fara bashi haushi, ko kadan taki yadda ta waigo, gabanta kawai tasa gaba, dan haka yaita neman abin da zaiyi ya bataran Ummi”
STORY CONTINUES BELOW
    Har karfe 9:34pm suna bisa hanyan gaba dayan su sunyi wujuga wujuga, cikin ikon Allah 12:44am suka shiga cikin Kano”
     Sadiq ne ya waigo yacewa Abdulmajeed yanzun ina muka nufa, gidan Abba zamu ko gidan ku??
    Inaganin mufara aje Nafisa tukuna dan bason aganta agidan mu, alokacin daga Nafisa har Ummi bacci suke”
    Sadiq beyi musu ba, har kofar gidan su Nafisa sukaje sannan Abdulmajeed ya tasheta”
   Da kanshi ya sauke mata kayanta sannan yaciro kudi ya mika mata, suna tsaye harta fara buga gidan su, ba jimawa aka bude mata tashiga tamai dago musu hannu”
    Tirr, Sadiq ya fada lokacin dayaga shigan Nafisa gida, sannan ya sake cewa Allah ka shirya mana zuriya👏🏻
    Gidan su Ummi suka nufa, suna shiga harabar gidan Umma tafito da gudu, tsaye tayi agefe tana hakin farin ciki tare dason tasa Ummi a idon ta”
   Abdul ne ya tashi Ummi sannan yafita acikin motar itama fitowa tayi daidai lokacin Abba ya fito yana fadin”
   Alhamdulillahi
  Umma ko tuni ta rungume Ummi tare da danta tana kukan farin ciki, Abba ko kan Abdulmajeed ya dafa sannan yace Allah yama Albarka”
    Cikin babban palon dake gidan suka rankaya Ummi sai raira kuka take kamar sabowar amarya, bayan Sadiq sun gaisa da Abba yace shi zai wuce gida”
    Dagewa Abba yayi akan yabari sai da safe amman ya kiya, domin ya kosa ya koma cikin iyalin shi, agidan yabar Abdulmajeed, duk da Abdulmajeed din ma yaso ya rakashi gida amman sadiq din yace a’a
  Ummi ko tunda ta saka kanta akafadar Umma taki dagowa sai raira kuka takeyi”
    Agidan Abdulmajeed ya kwana, sai dai yana dawowa daga masallaci ya dauki daya daga cikin motocin Abba ya nufa gida”
     Duk gidan bacci suke, dan haka be samu kowa apalon ba, harya nufa hanyar dakin sa, yaji bazai iya ba dumin kwana 6 da yayi bega momy ba ji yake kamar ya shekara”
    Dakin Ummi ya nufa ya fara buga kofar ahankali”
    Waye??
   Cikin tausasassiyar muryan shi yace nine momy”
   Abdulmajeed??, Shigo
   Yana tura kofar ya hango momy zaune akan sallaya tana sanyi da hajjab, daf da ita ya zauna sannan ya kwantar da kansa agefen cinyanta”
   Cikin sauri ta dafah kansa kwalla cike da idonta tace”
    Ina Ummin??
   Ummi tana gidan su, tun dare muka dawo”
   Kanshi ta kara shafawa sannan tace”
   Alhamdulillahi Allah kaine abin godiya”
    Abdulmajeed ta sake kallo tace amman meyasa baka fara kawota nan ba?
  Momy wannan yaron Nata ne ke firgita ni, da nayi tunanin inkawota nan, amman dana tunashi saina fasa”
   Hmmm, Abdulmajeed har yanzun dai kana nan da halinka, dan iskanci jaririn ne yake firgitaka?
    Hmmm, Momy dan baki ganshi bane, idonshi dakwa dakwa kamar na ubanshi”
    Dariya Momy tayi, sannan tace, ai kuma baban shi ba mummuna bane Abdulmajeed sharri ne kawai irin naka, toh ya gajiyar hanya?, hankalin mu ya kasa kwanciya kullum tunanin ku muke”
   Momy hanya babu dadi inda kika san zaka bayan duniya haka garin yake, nasha wahala sosai jijiyoyin jikina duk ciwo suke min, bakina kuwa kamar na cire na ajeshi agefe, saboda tsabar gajiya da nayi da mgn , kai Ummi tana da abin haushi wlh”
STORY CONTINUES BELOW
   Allah sarki Ummi, kaga d’aga ni, insami Daddy ku mutafi nasan zasuyi tunanin kagaya mana shiyasa basuyo mana waya ba”
    Mikewa yayi ya nufi dakin sa, yanajin fitan su  lokacin har yayi wanka ya sauya kaya”
       *****”**
Gidan su Ummi cika yayi makil da jama’a dangi nata zuwa ganin Ummi tare dayi mata ta’aziyar mijin ta”
   Tunda tayi wanka ta sauya kaya ta danyi kyau Ahmeed ko Momy ce tamai wanka sannan tabashi madara dan kwata kwata yaki amsan nonon , bayan tagama bashi  ne ta goyashi abayanta”
    Sosai Ummi takejin dadin yadda yan uwa suka nuna tsantsan farin cikin su da dawowarta, sai dai har yanzun hawaye ya kasa daina zuba daga idon ta, dan haka ta zama abu kadan kuka”
   Rannan datacika kwana biyu da dawowa ranan aka kawo Hajiya iya, dagudu Ummi taje ta rungumeta”
   Kuka hajiya tafara tana fadin haka kika dawo Zainab jibi kasusuwa awuyan ki?
   Hmmm, Hajiya damma baki ganniba ranan dana dawo, da kila bazaki ganeni ba”
   Toh barka tunda Allah ya yanke wahala, kuma baza asake baki daman zabin mijiba, nan gaba baki da wani zabi, kina gama takaba zansa adaura miki aure da Bawan Allah”
  Kirjin Ummi ta dafe, da sauri, sannan ta bude baki tace, hajiya dan Allah karki kirkiro da wannan mgn, nibazan kuma yin aure bama”
    Umma ce tace ai aure yazama dole Ummi zama ki barine”
    Rabu da ita zancen banza take, kuma ai Bawan Allah ya gama miki komai tun……
   Cikin sauri Ummi tace kinga nidai ki daina min zancen wani bawan Allah”
   Baki hajiya iya ta bude, hakama Umma tsaye tayi tana kallon Ummi, zuwa can tace”
    Ai Ummi har yanzun kina nan akan bakanki, nakin Abdulmajeed ko?, ca nake wannan ya wuce kuma tsakanin ku”
   Umma nifa bana son ne inji kuna dangantani dashi, nasan yamin kokari kuma nagode amman ni koda wasa ku daina cewa zaku hadani aure dashi”
    Iyeeee, eh lallai, aikuwa baki da mijin daya wuceshi, kuma ina baki shawara karki kara furta kalmar ki ga bawan Allah, domin cike yake da haushin ki, nayi mamaki da Bawan Allah ya tafi neman ki, domin yaji haushin cewan da kikai baki son shi awancen karon, ya shiga halin damuwa matuka, duk da zurfin cikin shi sai da ya furtamin damuwan shi, anan nafahinci ya dade acikin son ki, zurfin cikin shine ya hanashi ya nuna, inda ace nasan yana sonki bazan yadda ki auri bareba”
   Sosai hawaye ke zubawa daga cikin idon Ummi, ayanzun ta yadda da mgnr da Mukhtar yake fada tunda taji daga bakin hajiya, amman meyasa betaba nuna mata alamar soba? Kuma yake yawan kyaranta?
   Hawaye Tashare sannan tace”
   Hajiya nifa koda bacewa nayi ban son shi ba, aurenshi ne dai nace bazan yiba”
   Tu daga yau ko ba bawan Allah ba, karki sake yin wannan furucin, mutum be mancewa Zainab, cikin hikima da dibara zakiyi, har ya fahimci bakiyin sa, amman kice ni ban son wane, abun akwai ciwo, bare shi dayake cewa sai da kika kalli tsabar idonshi kikace baki son shi”
   Cikin share hawaye Ummi tace toh naji, in Allah ya yarda bazan sake ba, daman shiyasa ya tsaneni ?  Sai yai ta gayamin bakaken maganganu tare da duramin zagi?, aini ban dauke wannan abin haushi ba, amman shikenan kice masa yayi hakuri, ni ba nufina kenan ba”
   Murmushi Hajiya iya tayi tare da fadin Yauwa ko kefa, Allah ya muku Albarka”
   Ameen Ummi ta fada tare da kauda kai”
STORY CONTINUES BELOW
     Ko bayan tafiyan Hajiya, Ummi tagumi ta xuba tana addu’ar Allah ya cirewa iya tunanin had’ata da Abdulmajeed aure, domin ita sam batason Abdulmajeed amatayin mijinta, bashi da zubin irin mazan da take son aure”
    Duk da cewa auren Mukhtar tasha matukar wahala, amman rashin bincike a aure shiya kawo haka, wannan kuskure ne babba, wadda ya zama jarabawa arayuwarta gashi yanzun saboda son zuciya tajawa danta rayuwa babu dangin Uba, dan tasan koshi Ahmeed idan ya girma yaji suwaye dangin uban sa, sai yayi kuka da ita”
   Hawaye ta share sannan tace, Allah karka kaddara Abdulmajeed ya zama miji agareni, domin zamana dashi babu alheri, kai zaman ma bazai yiyuba, ta yaya zamu fara rayuwa matsayin miji da mata ni da Abdulmajeed?”
   
         ***********
Tundaga wannan lokacin ba’asake tada zancen ba har Ummi ta gama takaba, da wata Uku”
   Kyau tayi ba kadan ba, har so take dafi dacen kyau, tayi fari ta kara cika na ban mamaki”
   Idan ka kalketa baxaka taba cewa ta taba aure ba”
   Ahmeed ma yayi wayo sosai har ya fara takawa kadan kadan”
   Umma ke kula dashi dan haka suka saba da ita sosai, idan ba sani kayiba bazaka taba cewa Ummi ce ta haifi Ahmeed ba”
   Yanzun farin cikin Ummi ya dawo kamar da, kuma ganin ba’a mata zancen aure, hankakinta ya kara kwanciya, rabon dasa Abdulmajeed a idonta ko, tun ranan da suka dawo”
   Be zuwa gidan su kwata kwata, zuwanta gidan su ko yafi a kirga amman bata samun shi agida”
            *****
Shikuwa Abdulmajeed alakarshi da Nafisa kullum Dada gaba take, duk da cewa yana son ya yakece abin amman ya gagara hakan, kuma baya iya kula kowacce yariya sai ita, dan haka ya fara tunanin sonta yake, dan baya tunanin gashi yana tana wata yariya sai ita, akullum wutan sha’awarshi kara ruruwa take akan Nafisa, ayanzun ji yake abin da yake samu daga wajenta yayi kadan, daker yake iya sarrafa kanshi dan karya kusanceta, nan yafara daya sanin fara wannna d’abi’ar da yayi, kashi yanzun yana son ya zamar mai masifa, ji yake kamar idan be kusance taba mutuwa zaiyi, dan haka ya yanke shawaran aurenta cikin kankanin lokaci”
   Cikin jan idanun shi ya nufa gida, apalo ya samu Momy tare da daddy bayan ya gaidasu ya zauna ya sunkuyar dakai”
   Daga momy har daddy kallon sa suke”
   Zuwa can daddy yace”
   Yau ko lfy kake?
  Lfy lau daddy, daman nazo ne inason zamuyi mgn”
   Cikin kwaciyar hankali daddy ya tattaro hankalin shi yace”
    Ina sauraron ka”
   Kasa Abdulmajeed ya karayi dakai, sannan yace”
  Daman nasamu yariyar da nake sone, kuma mun gama daidaitawa”
   Murmushi Daddy yayi tare da fadin”
   Alhamdulillahi hankan yayi kyau, amman kadan bani lokaci, akwai wata magana da makayi da Hajiya, dan haka kabari harsai na tuntubeta”
   ‘Dagowa Abdulmajeed yayi suka hada ido da daddy, cikin sauri ya maida idon shi kasa sannan yace”
    Daddy ni inason ne kar auren ya wuce sati 1 nan gaba”
  Daga Ummi har Daddy ‘Dagowa sukayi suka kalle shi, cikin fada daddy yace”
    Sati daya? Wanne irin sauri kake haka? Meke damun Kane??
  Cikin shafa keya yace, daddy mun dad’e fah da yariyar, mun riga mun gama daidai tawa, kuma gidan suma ashirye suke”
STORY CONTINUES BELOW
    Katseshi daddy yayi, ta hanyar daga mai hannu sannan yace”
    Lallai watoh kana son mu kuma aikata kuskuren da mukayi abaya akan auren Ummi ko?, ta yaya zakace zakayi aure acikin sati guda, baka da hankali ne?, toh idan kai baka dauki darasiba mu mungani dole muyi bincike akan iyayen yariyar, sannan ita yariyar kanta, sai munsan mutananen wanne garine kuma yaya tarbiyan su yake, kafin muje maka neman aurenta, kana nufin har ka manta abin daya faru da Ummi???
   Cikin dasheshshiyar murya yace Daddy nifa na miji ne, kuma inda ban yadda da itaba ai bazan je ba”
     Shiru daddy yayi zuwa can yace”
      Naji, tashi kabani guri, kuma ina kara jandada maka andaina bada aure agidan nan sai anyi cikaken bincike, kuma muma bazamu dauko ba sai munyi bin cike, dan ba yadda bata kasan cewa”
    Momy batasa musu bakiba har sukayi suka gama”
   Abdulmajeed dakinsa ya nufa yana mai huci tare dajin haushin furucin  daddy”
    Har dare be sami fitowa ba, saboda wani irin mugun zazzabi dayake ji, da misalin karfin 8:00 pm Momy ta kwan kwasa masa kofa, tare da Sallama”
   Amsa mata yayi sannan ya tashi ya zauna”
    Fuskar Momy awashe tace taso maza ga Abban ku nan sunzo tare da Hajiya iya”
   Mikewa yayi suka jero tare da Momy”
    Suna isa palon ya kara tamke fuska saka makon cin karo da yayi da fuskan Ummi, zaune wajen kafafun Hajiya”
    Tayi kiba, ta kara fari kamar ba Ummin Bakin yanki ba, Tabe baki yayi sannan ya dauke kai daga kallonta, sai dai yanayin ta ya nuna kamar cikin tashin hankali take”
   Bayan Abdulmajeed ya gaida su, Abba yace”
   Abdulmajeed  dazon nakejin sakonka ashe ka samu mata?, gashi da har mun yanke shawaran Zamu hada auren ku da Ummi, amman duk da haka bata baciba, ranan Juma’a me zuwa za’a daura maka aure da Ummi, ita kuma waccen idan mungama bincike zamu nemar maka aurenta”
   ‘Dagowa Abdulmajeed yayi ya kalli Abba, acikin zuciyan shi yace abin da baxai taba yiyuwa ba kenan, saida ta zama saura, dagowa yayi ya kalli Ummi cikin sauri ta sunkuyar da kanta, tsantan kanshi yayi yana fadin”
    Abba ni gaskiya bana son ta”
    Babu wadda ya tsammaci wannan furicin daga bakin shi, dan haka duk suka dago kai suna kallon sa”
    Cikin mamaki Momy tace azuciyarta, yaron nan gaba daya ya canza halin sa, ada yana da kawaici tare da zurfin ciki, meyasa zaiyi haka?, nasan Abdulmajeed yana son Ummi mugun ruko ne dashi, idan Ummi ta fadi haka wancen karon saboda kuruciya aishi da hankalin sa, meyasa zaiyi wannan furicin gaban kowa, lallai sainayi wa Abdulmajeed da gaske, tana cikin wannan tunanin taji hajiya iya na fadin”
    Aiba shawaran ku muka nemaba, Umarni muka Baku, kuma bama bukatar ra’ayin ku”
    Kauda kai Abdulmajeed yayi zuwa can ya sake kallon Ummi ya gallah mata harara”
    Cikin sauri tamaida kanta kasa”
   Dahaka su hajiya iya sukayi sallama, bayan sun kara jaddada musu su shiryawa auren”
    Abdulmajeed mikewa yayi yabi bayan hajiya, gafe yajata, cikin jan ido yace”
    Hajiya karku hada wannan abun, bazan iya zama da itaba, wlh idan kuka dage duk abin da ya faru kuyi kuka da kanku”
     Kallon shi Hajiya tayi asheke sannan tace”
    Bawan Allah saidai kayi hakuri bakin alkami ya riga ya bushe Insha Allahu sai dai muga alhri”
   Juyawa yayi afusace ya shige gida, dakin momy ya shiga yana ji ranta ta dawo daga rakiyar su Umma”
   Zuwa can ta turo kofar tana shigowa tace”
    Sai yau na tabbatar da baka da hankali Abdulmajeed ko kunyan Abban ku bakajiba??
   Momy wannan ai zalinci ne, dan me za’a tursasani saina aureta, mayasa ita lokacin da tace bata sona basu tursasataba saini?, inba zalinci ba meye wannan?, ina namiji zasu dinga juyani, lokacin da tace bata sona ba wadda yai mgn, kuma wlh idan har aka dage sai an hada wannan auren Baza taji dadin zama daniba, dan ni ban sonta inada wadda nake so”
    Ganin Ummi bata da niyyar tanka masa ya juya yai dakin sa, yana cigaba da huci”
    Itama Unmi tun amota take kuka, Bakomai ke damunta ba sai yadda zata fara zama da Abdulmajeed amatsayin mijinta”
    Abdulmajeed masifaffe, ga bakar xuciya, ga daure fuska, ko zaman minti 5 bana fatan nayi dashi, dan nasan kafin minti biyar din sai ya harareni tare da hantaran ta, yau shine zanyi zaman dindin dashi?? Lallai ciwon zuciya zai kamani, gashi zagi baya wuya abakin shi, nidai nashiga kuna🙆🏿‍♀😭
Mmn Yazeed
[9/2, 8:48 PM*KOWANNE BAKIN WUTA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    ( da nashi hayakin)
💨💨💨💨💨💨💨
Story & Written by
    *Fadeela Lamido*
*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*
    Wattpad @fadeelalamido
                  35 – 36
Ummi kuwa Kuka taitayi cikin motar”
   Har suka isa gidan Hajiya suka sauketa babu wadda yace da ita kala, haka taita kumo2 da hawaye”
    Bayan sun shiga gidane tabi Umma dakinta, cikin kuka ta durkushi agabanta, sannan tace”+
   Umma yanzun shike nan auren ya tabbata dani da yaya?
    Ummi ki kwatar da hankalin ki, duk wannan abin da kike gani komai zai wuce, kuma saikin dage da gyara jikin ki tunda kinga shi saurayi ne betaba aure ba, sannan bayan ke akwai budurwa wadda zai aura, kinga akwai aiki agaban ki, idan har kika tsaya wasa zaki zama ‘yar kallo”
    Hmmm, ai shima Umma bawani nan, ba saurayi bane, tunda dan iska ne, neman mata yake yi, kune baku saniba, wlh ya aje wata yariya yawo yake da ita tamkar matar auren shi”
   Kama baki Umma tayi ta zubawa Ummi ido sannan tace”
    Abin kuma harda sharri? Ina ki kaga ma Abdulmajeed din bare kisan wannan abubuwan da kike lissafowa, tare kuke yawo?
   Umma wlh da gaske ne lokacin dayaje taho dani fah da mace ya tafi, kuma bakiga iskancin da suke yi ba, wlh har Sigari ma yanasha”
    Subuhanallahi, kinga Ummi ina baki shawara ki daina daukan zatukan mutane Abdulmajeed dinne yake shan Sigari, ina baki shawara ki dinga saukaka kiyayyar ki ga a Abdulmajeed, kuma ai daman *KOWANNE BAKIN WUTA* danashi hayakin”
    Ummi kallon Umma kai wai take, tana zubar da hawaye, Allah ya sani balakin tsoron Abdulmajeed take, ayanzun ko tuna fuskan shi tayi sai gabanta ya fadi”
    Acikin zuciyarta tace”
   Nasan Abdulmajeed yana da kyau duk wace ta ganshi kallo daya zataso kasacewa dashi, amman datamai kallo na biyu saita fahimci bashi da fara’a ga shegen fadin ran tsiya, wani lokacin ma idan yana mgn tamkar an matsa masa ne sabo da yadda zakaga yana ciccijewa”
    Haka Ummi taita tunanin yaya aureta zai kasan ce ita da Abdulmajeed”
   Shima Abdulmajeed din gidan Sadiq ya nufa cike da korafi abakin shi, bayan ya gama zayyane wa Sadiq dine, Sadiq ya zuba mai ido, sannan yace”
    Idan na fahimce ka, kana nufin tunda tayi aure ada ka fasa son nata kenan?, indai haka ne, ashe ba soyayyar gaskiya kake mata ba, ai shi so be tsufa, daman wani abu kake so ajikin ta? Yanzun babu dan haka shike nan ka fasa?
   A’a ni karkamin Sharri, wlh wlh koda can bantajin inason wani abu ajikinta ba, nidai nasan ina sonta, shima daga bayane na lura da haka, kuma tunda ta zabi wani akaina nai Alkawarin nima nabarta har abada, koda kuwa sonta zai kasheni, kuma idan haka sukeji meyasa tun lokacin basu tursasata saita aureni ba, sai nine za’adinga juyawa?
   Hmmm Abdulmajeed ni dai shawaran da zan baka kayi hakuri kawai wata rana komai zai wuce”
  Bawani wucewa da zaiyi yaya za’ayi bantaba aure ba sannan dauki gundumemeyar bazawara abani, wannan ai zalinci ne”
   Cikin sauri Sadiq ya kalli Abdulmajeed sannan yace”
   Ummin ce gundumemeya? Naga bawani girmane da itaba dan ma ammata auren wuri ne, atunanin ai har yanzun batai 20 ba, Nafisar kama aita fita girma da shekaru”
STORY CONTINUES BELOW
    Amman dai ai bazawara ce, wadda mijinta ya mutu, kuma anrabu ne dan dole badan ranta naso ba”
   Dariya Sadiq yayi sanna yace”
   Abdulmajeed da gangan kake gurbata tunanin ka, idan zaka saki ranka kasake, ka aje wannan bakin kishin naka”
        *******
Duk gidan guda biyu shirye shirye ake, gashi yakama saura kwana biyu daurin auren su, dan haka daddy ya matsamai yaje gurin Ummi yaji bukatun ta”
    Cikin jin haushi ya fice agidan, sai da ya biya ya dauki sadiq  dan shi baxai iya duguwar mgn da Ummi ba”
    Ahabar gidan suka samu Ummi ita da kawarta Sadiya, da alama rakiya take mata dan babu mayafi ajikin ta sabanin Sadiya da take sanyi da mayafinta”
   Ummi naganin shigowar motar Abdulmajeed gabanta ya yake ya fadi, jitayi kamar ana tsuntsunka hanjin cikinta, dan haka ta rike Sadiya tare da fadin”
   Wayyo Allah na, nashiga Uku”
   Sosai Sadiya ta kalleta sannan tace”
  Haba Ummi meye haka saikace kinga mala’ika? Mijin dazaki aure ne fah”
   Ajiyan zuciya Ummi tayi sannan tace”
   Dan bakisan halin shi bane Sadiya, wlh bashi da kyau”
   Matsawa Sadiya tayi gurin motar tana gaidasu, Abdul dauke kansa yayi Sadiq ne kadai ya amsa”
   Hakama gaisuwa Ummi Sadiq din ne ya amsa”
   Cikin sauri Sadiya tayiwa Ummi sallama ta wuce, dan haka Ummi ta nufi komawa gida, sai dai duk adar dar take dan babu mayafin ajikinta kuma kayan jikinta sun kamata”
   Harta fara tafiya Sadiq yakirata”
   Ahankali ta dawo ta tsaya, Abdulmajeed kuwa sai satan kallonta yakeyi”
  Cikin fara’a Sadiq yace”
  Gurinki fah mukazo, kuma naga kina kokarin guduwa gida”
    Sukuyar dakai Ummi tayi tana wasa da hannunta tare da faduwan gaba, zuwa can hawaye ya fara zubo mata”
   A’a Ummi yada kuka kuma? daga mgn saiki fara kuka?
   Waigowa Abdulmajeed yayi ya kalleta sannan yaja tsaki ya dauke kai”
   Ganin haka kukan Ummi ya kara karuwa”
    Daker Sadiq ya shawo kanta ta daina kukan sanin da yayi ko tana son wani abu bazata fada ba yasa ya ciro kudi me yawo ya mika mata, tare da fadin gawannan nasan kila zaku shirya mana wata ‘yar walima keda kawayen ki”
   Nuke hannuta tayi tare da fadin ni babu abin da zanyi”
   Shiru Sadiq yayi na wani lokaci zuwa can yace toh ansa nabaki kyauta”
   Hannu tasa ta share hawaye sannan tace ni babu abin da zanyi dashi”
    Eh ko babu abin da zakiyi dashi ki karba ki ajiye kudina ne bana doctor ba, wata rana zasu miki amfani”
   Hannu tasa ta karba tare da fadin nagode”
   Girgiza kai Abdulmajeed yayi tare da fadin”
   Lallai ma yariyar nan ta raina ni, kwafa yayi tare da cewa Zaki sani, jeki dauko mayafin ki kizo muje”
   Muje ina ? Tafada azuciyarta, daidai lokacin taji Sadiq yana fadin ina??
    Zan kaita Asibiti ne amata gwaji  H.I.V
STORY CONTINUES BELOW
   Daga  Sadiq har Ummi dagowa sukayi suna kallon shi, yayin da ya kauda kanshi gefe”
   Hawaye ne suka sake zurarowa Ummi Wanne irin mugun alkaba’ine?, sosai ranta ya bacci jikinta ya fara rawa, wata irin zuciya ce taso mata, wadda batasan tana da itaba, har bata ganin meye agabanta”
    Badake nake ba, kin tsaya kina kallo na”
    Cikin tsananin fushi tace”
   Ni bazani ba, kuma aniyarka tabika, kai da kake bin matan ban…..
   Batasan yadda akaiba sai ganinshi tayi agabanta kantayi wani yin kuri ya Kwashewa da mari”
   Wanne irin taurari taita gani suna shawagi asararin Samaniya, muryan Sadiq taji yanawa Abdulmajeed fada”
    Daker ta iya bude idonta ta kallesu”
   Sadiq ta gani yana kokarin saka Abdulmajeed acikin mota, ganin yadda yake rawan jiki tare da kokarin dawowa, yasa ta kwasa aguje tayi gida”
     Jikin Umma ta fada, tare da fasa sabon kuka, arikice Abba ya mike yana fadin kedawa, hannu yasa ya daga kanta, shedan hannun ne wance akan kumatunta juwur gurin yayi sannan ya kunbura sutum”
    Cikin fada Abba yace sam bazan yadda ba, waye yayi miki haka???
    Tana shashshakar kuka tace”
    Yaya Abdulmajeed ne”
  Abdulmajeed?, Abba ya fada cikin sanyin jiki, sanna ya kara cewa Abdulmajeed din ne ya mareki?, me kika masa?
   Abba cewa yayi wai zai kaini Asibiti, amin amin gwajin H.I.V
    Sunkuyar dakai Abba yayi yana nazari zuwa can yace”
   Toh meyakawo duka kuma, daga wannan mgnr sai ya dake ki??
   Sukuyar dakai tayi cikin kasa da murya tace”
    Cewa nayi niba zani ba, shida yake niman matan banza  bance sai angwadashi ba, sai nine zaice min haka😭
    Ummi Abdulmajeed din kikacewa haka? Sa’anki ne shi?, yaushe kika zama fitararriya?  Idan baki saniba barin fada miki, kusan shekara 20 ne tsakanin ku, dan haka ba tsaranki bane, karna sakijin kiyin musu dashi, dan ba sa’an ki bane”
    Shuru Abba yayi yana huci zuwa can yace”
Abdulmajeed nada gaskiya, daman ya kamata akaita asibiti tai gwaji, yanzun zamani ya canza, ko budurwa ce akanje ayi wannan gwaji bareke da kika taba aure”
   Waya Abba ya dauka ya kara akunne zuwa cen taji yana fadin”
    Abdulmajeed ga Ummi na jiranka kazo ka dauketa ku tafi”
    Lokacin Abdulmajeed ya sauke Sadiq kenan agidan sa, dan haka ya juya shikadai, har cikin falon ya shiga bayan sun gaisa Umma ta kalli ummi tace”
    Dauko bayafin ki kutafi”
   Tana shiga dakin ta jawo gyalen, cikin haushi tayo palo, samu tayi ya ruga ya fita sallama tama Umma, harta fara tafiya Umma tace”
    Kuma inkin fita kibashi hakuri”
    Toh kawai tace sannan tai waje”
    Tunkafin ta isa wajen ya tada motar, ko kafin ta gama zama harya figeta, cikin mugun gudu yabar gidan”
    Gaban Ummi ban da faduwa babu abin da yake,tana kallon yadda yake juyowa ya kalleta sannan yayi tsaki ya juyar da kanshi, zuwa can taga ya faka agefen hanya”
    Dago idonta tayi tana kallon shi, adaidai lokacin daya miko hannun shi, jikinta tabi da kallon me wannan ki shirinyi?
    Jitayi hannun shi ya sauka akirjinta, kan ta ankara yasha kwalarta sosai, wani mugun radadi taji agurin sadin kayan sun matseta, ji take kamar zai rabata da numfashinta”
STORY CONTINUES BELOW
    Cikin ido ta kalli shi, sosai idonsa ya bata tsoro, cikin karaji yace”
   Ni sa’an wasan kine?, ina wasa dakene dahar zanyi mgn ki zageni?
    Cikin zubar hawaye tace ni ban zageka ba, kayi hakuri ka matsemin kirjina”
    Kara matsewa yayi cikin zazzaro ido yace”
    Daga yau in ina mgn karki kara sakamin baki, ni ba tsaran ki bane, idan kin saba kina ma wannan wawan rashin kunya yana barin ki, to ki sani, ni bazan dauka ba, yaushe aka haifeki dahar zanyi mgn ki mayar min?
    Haki kawai Ummi keyi sabo da tsabar wahala cikin wani irin numfashi tace nace kayi hakuri wlh ka matseni zaka kasheni fah”
    Kamar kara zugashi take, har wani girgizata yakeyi sai da ya gama hargaginshi dan kansa ya saketa, sannan ya kuma gurin zaman shi yana huci”1
    Itako Ummi dafe kirjinta tayi sosai yake mata ciwo tare da bugawa, babu abin da take so yanzun illa tacire kayan jikinta ta kwanta ko zata samu dadai tuwar numfashi”
    Cikin wanni Asibiti ya shiga bude motar yayi ya fice yabarta aciki”
    Binshi da kallo tayi gaskiya bazata iya zama da Abdulmajeed ba”
    Ta dade zaune sannan ya dawo, gefenta ya bude, gani tayi ya ciro Allura tare da finciko hannunta”
   Batare da wani bata lokaci ba ya suka Alluran, runtse ido tayi tare da sakin kara”
   Acikin zuciyanta tace”
   Nacewa daddy Abdulmajeed mahaukaci ne, yace min da lfyr sa, idan ba mara hankali ba waye zai aikata abubuwan da yake aikatawa ? Ace mutum beda tausayi beda imani”
   Yana gama diban jinin yace saukar min a mota ki wuce gida”
    Bata bari ya gama rufe bakiba ta sauka amotar sannan ta fice daga cikin Asibitin ko Waiwaye babu”
 
    Dakafa ta fara tafiya dan bata dauko ko sisiba, gidan su Abdulmajeed tai niyyan zuwa dan yafi kusa da Asibitin, amman ganin yadda takejin jikinta yasa ta tare memashi tahau”
    Suna isa tace”
   Inazuwa barin anso maka kudin”
    Tana saka kafarta ta hango motar Abba, Afalo ta same su harda Ummata, dan haka bayan
Ta gaida Abba sannan ta cewa Umma ta bata kudi taba me mashin”
   Gaba dayan su kallonta sukayi Daddy ne yace bake da Abdulmajeed kuka fitaba?
   Sukuyar dakai tayi, sannan tace”
   Eh shine yace in tafi gida”
    Shiru Daddy yayi be sake cewa komai ba, sanda Ummi ta shigu ma ido ya zuba mata sannan yace”
    Dukan ki yayi ne?
   Girgiza kai tayi, alamar a’a, aciki ranta tace tabar matsane kawai danasha”
   Dakinta ta nufa, yayin da Daddy yacewa Abba kaga irin abin da naguda kenan tun farko, ji inda idanunta suka kunbura dalilin dayasa waccen karon bangoyi bayan amata dole ba kenan, kuma dan tsabar rashin kunya irinta Abdulmajeed sai ya turota gida, meye dalilin dazai kasa kawota, yana son ya nuna mana cewa beso auren kenan?, wlh idan yai wasa zan hanashi auren ko wacce yariya”
   Duk da shima Abba beji dadi ba, haka yai tabawa Daddy hakuri”
    Ummi ko dakinta ta kule ta cire kayan jikinta wani mugun ciyo kirjinta yake mata lallai Abdulmajeed yasan kan mugunta, har yanzun ji take kamar yanzun ne yake cin kwalarta, ji take tamkar hannun shine akan kirjinta”
STORY CONTINUES BELOW
   Kusan minti 30 tana kwance, ban da numfar fashi babu abin da take, zuwa can Umma ta shigo dakin ganinta haka abun ya bata tsoro”
   Ummi menene kuma haka, ya zaki kwanta babu riga”
   Umma kirjina ne yake min ciwo sosai, idan rigata ta gugi gurin yana min zafi, kuma inajin kaman ana su kamin alura acikin kirjina”
   Subuhanallahi, me yafaru?, gashi nan kirjiki yayi jawur, ina zuwa barin kira Abban ki muje Asibiti wannan wanne irin ciwo ne haka lokaci daya”
   Cikin sauri Ummi tace”
   A’a Umma, karki kirashi basai munje Asibitiba, yaya Abdulmajeed ne yasha min kwala, shine ya hada hadda fatan jikina, tundaga lokacin kirjina ke ciwo”
   Zare ido Umma tayi acikin zuciyanta taji babu dadi, cikin takaici tace kin sake yi masa wani abune??
     Ba abun da na mishi”
   Kai Ummi ta daga samma, sannan tace anya kuwa Auren nan zai yiwo?, bari insamu Abban ki akan mgnr”
   Juyawa Umma tayi, tai waje zuciyarta cike da damuwa”
   Bata sakejin Umma ta tada zancen ba, har washegari wada ya kama gobe ne daurin aurenta da Abdulmajeed”
    Ganin suna cigaba da shirye shiye, yasa tai tunanin kila Abba yaki bawa Umma goyon baya ne, haka ta wuni sukuku cikin damuwa da tarin takaici”
    Tanajin lokacin da ‘yan uwan Umma suka dawo daga kai kayanta gidan Abdulmajeed acikin zuciyarta tace”
   Yau kayan ma kansu sai sun san sunshiga gidan jarababbe domin ta tabbatar sai yaita hararan kayan tare daja musu tsaki”
   Ayanzun babu hawaye ko daya daya ke iya zubowa daga idon Ummi sai tsabar radadi zuciya, zama kawai tayi ta zuba tagumi tare da karantu addu’in neman tsari, daga masifar Abdulmajeed”
     Washegari tunda safe gidan ya rincebe da aikace aikace, wada  dangin Umma ne akan abun, tana jiyo yadda suke shewa tare da guda, itako gabanta sai faduwa yakeyi”
   Da misalin karfe 1:44pm Abba ya dawo daga masallaci tare da wasu daga cikin abokan sa, wannan na nuna ta tabbata matar Abdulmajeed, sai yanzun hawaye ya zubo mata sannan tasa hannu ta share”
   Sai kusan karfe 3 tai wanka, bata wani tsaya kwalliyaba dan bata da nutsuwa, suma mutanen gidan basu neme taba dan sunsan halin da take ciki”
   Kusan karfe 8:00pm Umma ta shigu, wanka tasa Ummi tayi da wani irin ruwa me mugun Kamshi ita kanta basan sadda ta lunshe idoba saboda sanyin kamshi,
   Harta fito wankan tana jin kamshi ajikinta, Sannna bayan ta guge jikita Umma ta kara shafa mata wasu turaruka da hannuta, baka taba iya tantace kamshi sanna ta dauko kaya ta mika mata”
    Sosai Ummi ta fito, kyau ta zubashi ba kadan ba”
    Sannan ta rufa kanta da farin mayafi”
    Ita kadai ce zaune bata gaiyaci kowa ba, ko Sadiya tasan dai da zancen, amman batasan ranan ba”
    Har kusan karfe 10:00 ana jiran Abdulmajeed ya kawo mota amman shiru kakeji, dan haka Abba ya buga masa waya”
    Yana dagawa Abba yace kaifa muke jira ka turo adaukan maka matar ka”
        Cikin siririyar muryan shi yace”
  Abba jira nake mutan nan gidan su ragu sai nazo na dauketa”
   Jim, Abba yayi, zuwa can yace, au, toh, baka bukatan ‘yan rakiya kenan?
   Ahankali ya sake cewa eh Abba”
   Toh, toh, shikenan kazo ka dauketa kawai”
    Suna gama waya Abba yai kiran Umma yadda sukayi da Abdul ya fada mata, sannan yace taje ta sallami mutananta, Abdulmajeed yace dakan shi zaizo ya dauki matar sa”
   Sosai ran Umma ya bacci, gaskiya Abdulmajeed yanayin abin da yaga dama”
  Sai kusan 11 ya iso, cikin farar shadda babban riga yana sayin da hula, sosai kayan suka karbeshi, kai tsaye falon Abba ya shiga, bayan sun gaisa, Abba ya kira Umma yace su taho ita da  Ummi”
    Zuwa can, saiga su, bayan Ummi ta zauna Abba yaita musu nasiha, zuwa can yace su tashi su tafi”
    Abdulmajeed ne ya fara mikewa sannan Ummi ta mike, harta fara tafiya Abba yace”
   Ummi karki yadda naji wani matsala daga gareki, Abdulmajeed danane kamar yadda kike, idan nagan shi ajikin farin ciki kece, kuma zanyi fari ciki dake, dan haka ki kiyaye baccin ranshi”
    Wanne irin mgn ne wanan Abba keyi?, nidai na shiga Uku na😭😭
    Gaba daya suka fito harda Umma da Abba, wani abu dayai mugun bawa Ummi mamaki, Abdulmajeed da kansa ya bude mata kofar motar,
    Tana zama kuwa ya tsuna ya kamo kafafuwata ya dagamata tare da gyara mata mayafinta daya zamo daga kanta, murmushi yayi sannan ya rufe motar”
    Sakin baki tayi tana kallon shi, harya zagayo ya shiga motar ta kasa daina mamaki”
   Ahankali yake tuka motar tare dayiwa su abba godiya har ya fice’  ummi ko har yazun satan kallon shi take domin yabata mamaki’
    Suna fita agidan ya kwashe da dariya, kallo ummi tabishi dashi dashi daman Abdulmajeed na dariya ne?😳
   Mmn Yaxeed
[9*KOWANNE BAKIN WUTA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    ( da nashi hayakin)
💨💨💨💨💨💨💨
Story & Written by
    *Fadeela Lamido*
*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*
    Wattpad @fadeelalamido
               37 – 38
Hade ido sukayi nan danan ya daure fuska, tare da fadin”+
    Ke! Dakin mike kafa ne kina jira azo daukan ki, saikace wata amaryan kirki”
    Sunkuyar dakai tayi tana sauraran shi, acikin zuciyarta tace ai me haki baya barin halin sa”
    Shiko Abdulmajeed sai satan kallonta yake azahirin gaskiya tamishi kyau, gawani sanyayeyyen kamshi dayake tashi ajikinta, bude hanci yai tayi yana shakar kanshinta”
    Zuwa can ya waigo ya sake kallonta tare da fadin”
    Ina fatan zuwa yanzun kin shiga hankalin ki, kamar yadda kika sani, ni ba sonki nake ba, dole akamin aka hadani dake, da ace nasan za’ace za’a hadamu aure bazanje neman ki, barin ki zanyi acen, ki bace batt, sai yanzun nasan nayi kuskure zuwa neman ki, dan haka kibi ahankali nafisa nan shigowa”
    Wani irin haushi taji tunda ya ambaci Nafisa, wlh badan tanajin tsoron shiba dayau saiji mgn, amman tasan ita zatasha wahala, dan haka ta kama bakinta”
   Dahaka suka isa gidan cikin sauri ya wuce yabarta, ahankali tabi bayan shi, wucewar shi yayi yabarta tsaye afalon dankata ta neman ma kanta dakin ta, tundaga lokacin bata sakejin duriyarsa ba har washegari, da yuwan ta kwana dan bata samu arzikin da za’ai mata tayin wani abu ba”
    Da misalin 11:30am Sadiq yayi sallama agidan, Abdulmajid ne ya amsa mai, wadda fitowan sa kenan”
    Tafawa sukayi, bayan barkwanci irin na abokai Abdulmajeed yace, muje daman fita zanyi wunwa nakeji”
   Zama Sadiq yayi, tare da fadin, saika dawo niba gurinka nazoba, jiya ka koreni don baka son adauko ma Amarya, toh yanzun ni gurinta nazo”
   Ok toh ai shikene nan kana iya kiranta ni babu ruwana, ina tare dakai amman kana munafuntata”
   Allah ya shiryeka, Sadiq ya fada, sannan ya daga murya yana kiran Ummi”
    Daidai lokacin da take fitowa Abdulmajeed yai waje yana fadin inka gama ka sameni gidan su Nafisa, na matsu insata a idona”
   Ko daga ido Sadiq beyi ba, cikin dasheshshiyar Murya Ummi ta gaida shi”
   Amsawa yayi fuskan shi dauke da murmushi, acikin zuciyan shi yace”
    Abdulmajeed besan me yakeyi ba wlh ji yariya son kowa kin wadda ya rasa, Amman ya tsaya hauka banza da wofi, ‘yar karamar mgn ya maidata babba, saboda shegen taurin zuciya iri nashi”
     Ummi ko zaune tayi ta sadda kanta kasa”
   Zuwa can Sadiq yayi gyara murya yace”
    Ummi nifa gurun ki nazo, ba gurin doctor ba, amman naga kamar kina dari2 dani, ki saki jikin ki ki dauka kamar kina mgn ne da Yayan ki, domin nazo na baki shawara ne akan yadda zaku zauna da Abdulmajeed”
    Ni abokin sane da muka dade tare, nasan sa ciki dabai, dasan halinsa nasan neyafi so kuma nasan abin da baya so”
   Sannan basai nafadin miki ba, Abdulmajeed rigimammene nasan kinsa wannan”
     Nisawa yayi, sannan yaci gaba da cewa, dan haka ida kikai wasa zakisha wahala azama dashi, abu nafarko shine ki rage jin tsoron sa, ba ina fufin ki masa rashin kunyaba, a’a tsoronsa zaki aje agefe, idan ba hakaba zaki cutar da zuciyan ki, Abdulmajeed yana matukar son ki, duk abin da kikaga yanayi da gangan yakeyi sabo da taurin kai, duk halin da kikaga Abdul aciki ayanzun asanadin rashin ki ya shiga, bazan boye mikiba Ummi Sanadin ki Abdulmajeed ya fara shan Sigari, wai atunanin shi itace zata ragemai damuwa, ada baya kula kowacce yariya sai asanadin rasaki ki”
STORY CONTINUES BELOW
    Dagowa Ummi tayi tana kallon sadiq, cikin ido, jin zantukan daya ke kamar amafarki”
     Sadiq ne yacigaba da cewa, dan haka nakeson ki ajiye tsoron shi ki nunamai so dan ki rabashi da mummunan dabi’ar daya fada, atunanin shi bazaki taba son shiba ne, ni kuma nasan kema kina son shi yakasa fahimta ne, kamar yadda kema baki fahimta ba”
    Cikin zuciyarta tace ni ban wani son shi”
       Sadiq kallon Ummi yayi sannan yace”
    Ummi inason duk wani hakki da kikasan nashi ne akan ki, kirinka sauke shi yadda ya dace”
   Ki bashi abinci koda ace bazaiciba karki nuna kinji haushi anjima ki sake ajemai wani, ke macece wata dubaran basai na fada miki ba, Abu na gaba wadda shine muhimmi inason ki dinga kai ziyara dakin sa kowanne dare, hakan zaisa yayi saurin sakkowa, dan Allah karki biyi mishi ku zama maso girman kai dukkan ku, kinji ko?
    Kan Ummi a sunkuye ta daga kai, alamar eh, sanna tace”
   Naji duk abin dakace kuma zanyi, abu daya ne bazan iyaba, shine bisa dakin sa, Allah ya sani bazan iyaba”
  Haba Ummi? Abdulmajeed fa mijinki ne, zaki iyayin komai domin kijawo hankalin mijinki gareki, ko Nafisa da kike gannin su tare fitsaranta yasa ta rinjaye shi, idan har kika zauna haka abu me walane ya nemeki, amman idan kina zuwa gurinsa ina tabbatar miki lokacin dazai karkato bema sani ba”
   Cikin kasa da murya tace, nidai indai saina bishi dakinsa ne toh karya karkato”
      Sosai kalaman Ummi sukabawa Sadiq dariya, bayan ya gama kyajewa yace”
   Watoh karya karkato ko?, lallai Ummi zanga yadda wannan wasan  naku zata kare, kowa rigima baken ba, ba Abdulmajeed din ba, toh ni zan wuce, mikewa yayi tare da fadin sai gani nabiyu “
   Yana fita Ummi ta mika acikin zuciyanta tace”
   Haka kurun, inbishi dakinsa ya wulakantani, wlh bazan kai kaina ba, banje dinba ma yana kare?
    Kitchen ta shiga ta samawa cikinta abin da zataci, tana cikin cine Kiran momy ya shigo wayarta”
    Dauka tayi tare da sallama”
   Cikin fara’a momy ta amsa mata”
    Ina kwana Momy”
   Lafiya lau Ummi ya kwanan bakunta?
   Kasa Amsawa tayi, tai shiru, yau daya taji tanajin kunyan momy”
    Yar dariya Momy tayi sannan tace”
    Ashe har kinshiga kitchen, Abdulmajid yazo ya samu Hassana zata taho kawo muku breakfast yace tabarshi kin riga kin karya”
   Acikin zuciyanrta tace kaji bakin mugu ko?, afili kuwa tace”
    Eh eh Ummi nayi”
   Toh yayi kyau, Ummi Allah ya muku albarka, amman daga yau idan zaki girka wani abu yazama lallai kisa da mijin ki,  bazan sake bashi abincina ba, dan yace wai keka dai kikacinye kayan ki”
   Jim,  Ummi tayi ,zuwa can tace”
   A’a Momy shine fah yace bayaci”
    Umhunm ai daman ban yaddaba, shiyasa nafada masa zan miki mgn, nasiha momy tamata nawani dan lokaci, sannan sukayi sallama”
  Sai dare Abdulmajeed ya shigo, lokacin gidan ya hade da kamshi”
    Palon ya tsaya yabi da kallo, wannen kamshi meye haka? Kasa barin falon yayi dan haka ya nemi guri ya zauna tare da kunna TV”
STORY CONTINUES BELOW
    Karan TV ya tabbatar wa Ummi Abdulmajeed ya shigo, dan haka ta mike ta fitoh”
     Tunkafin takaro yajin wani sabon kamshi na dososhi dan haka yabi hanyar da kallo”
    Suna hada ido da Ummi ya dauke kansa, zama tayi akujeran dake kallon nasa sannan tace”
 
     Barka da shigowa”
    Kallonta kawai yayi sannan ya kauda kai, acikin zuciyar shi yace yariyar nan akwai iyayi, ji inda take mgn tana wani karkata min baki”
    Shiru nawani dan lokaci, sannan Ummi tace”
    Ga abincika cen  kona kawo maka nan ne?
     Bazanci ba, dan kin raina ni, na fadi mgn kicewa momy karya nake yi?
   Allah ya baka hakuri, mikewa tayi ta dauko teren abincin ta ajiye gaban shi, sannan ta fara zubamai”
    Cikin sauri ya lumshe ido yana satan kallon abincin, yuwace acikin shi sosai, amman idan yaci girkin Ummi ai shikenan ta raina shi gashi yaje gurin momy ita kuma ta hanashi abinci”
    Dago kanshi yayi daidai lokacin da Ummi ta juya baya tana kokarin wucewa dakinta yace”
    Ke kizo ki kwashe kayan ki, Danni ban iya cin jagwalgwalo ba, idan ba hakaba kuwa almajiri zan bawa”
     Batace kalama ta wuce abinta, acikin zuciyarta dake addu’an Allah ka yayemin wahala, ace duk wahalar danasha Almajiri zai bawa? Kuma ace wai gobe insake girka wani?, gaskiya bazan iya ba, irin yadda yaitawa Umma kenan, lokacin dayake zuwa gidan mu, inta musu dariya, ashe abin zai dawo kaina”
   Harta kwanta ta tuna tabar wayarta afalo, dan haka ta mike ta fito
  Sai dai tana kokarin karya kona ta farajin karan cukali kamar dai anacin abinci”
     Dakatawa tayi sannan tasa idonta guda daya ta leka”
   Abdulmajeed ne zaune yanacin abinci tare da lunshe ido”
   Dawowa tayi da baya tai murmushi tare da fadin acikin zuciyarta”
   Ji mutumin dayace baxaiciba jagwalgwalo ba, sai gashi yana zuba loma, hadda wani lumshe ido, wata yar guntuwar dariya tayi waddda batasan lokacin data subuce aba”
    Cikin sauri ta toshe bakinta, tare da rike cikin ta, ashe duk burgace, har yana cewa wani sai dai yabawa almajiri, Ashe shine almajirin”🤣 ganin dariya tana shirin kubuce mata tai saurin barin gurin”
    Tana shiga daki ta sheke da dariya, abaka abu kace bakaci, sannan ka labe kana zuba loma, dariya taitayi kamar wadda ta zauce”
   Tunda take bata taba ganin sa yanacin abiciba, sai yau taga yadda yakecin abinci, idonshi rufe kamar jaririn dake shan nono, kasa daina dariya tayi, tana cikin wanna halin taji anturo kofar”
   Azabure ta dago kanta, ido biyu sukayi da Abdulmajeed dan haka ta daure fuska”
    Cikin murtuke fuska yace”
     Ke dawa kike dariya??
    Bakowa”
  Bakowa? kina nufin ke kadai kike dariya?, kin zare ne?
   A’a wani abu nake karanta wa awata”
   Karya kikeyi, makaryaciyar banza, baga wayar kin barta apalo ba, ni ban son shirme banza kinaji ko?
    Gyada masa kai tayi, cikin sauri ya saki kofar ya juya”
   Sai dai yana shiga d’akinsa yaji wani iri, ji yake kamar ya koma palon ya kwanta, saboda kamshi dake tashi acen din, hakama dakin Ummi daya fito yanzun wanne irin kamshi ne ke tashi na musamman, zaiso ace dakin sama yayi irin wannan kamshi, koda wanne turare Ummi take amfani?
     Tunanin dayai tayi kenan, zuwa can ya tuno kamshin dayaji lokacin da Ummi ta doso falon, gaskiya ko wanne irin turaren ne wannan ya hadu, dazai san sunan sa daya saiwa Nafisa”
     Cikin irin wannan tunanin bacci ya dauke shi”
     Washegari tun 8:35am kamshin girkin Ummi ya hanashi bacci, sai juyi yake, dan haka ya yanke shawaran barin gidan gaba daya”
   Misalin 9:00am ya fito domin tafiya Office, adaidai lokacin da Ummi take fitowa”
    Ina kwana?
   Wanni irin kallo ya mata dakile yace”
    Lafiya?
   Ga breakfast dinka can”
   Banci, inace nagaya miki bazanci jagwalgwalo ba ko?
    Shiru tayi tare da sunkuyar dakai”
    Shiko cikin sauri ya kada kai yayi waje, yana kokarin shiga mota yaga drive Hajiya iya ya shigo, dan haka ya dakata”
     Karasowa yayi tare da fadin”
   Hajiya sannu da zuwa”
  Yauwa sannu Bawan Allah”
    Ganin ta dauki ledoji niki niki yasa ya karbe daga hannunta, yana fadin hajiya da rigima kike, me kuma kika kawo mana?
    Adaidai lokacin da ta kinkimo galandin dake bayan motar take fadin a’a bawan Allah nidai taimamin kashigar min dashi ciki, kayi tafiyar ka, yau ba gurinka naxo ba”
     Dauka yayi ya nufi palon yana cigaba da nazari tare dason sanin meye wannan? Kuma me hajiya zatayi dashi?, badai irin tarkacen da mata suke dirkawa cikin su bane wai da sunan gyara?
  Yana ajiye kayan hajiya na shigowa, zama yayi tare da fadin hajiya meye wannan??
    Zama tayi tare da fadin”
     Idon matambayi ne”
   Murmushi yayi ganin fitowan Ummi ya hadiye sannan yabita da ido”
    Eh babu laifi tayi kyau amman fa tayi kandan ta firgitashi dan yaga alamar kamar nema take ta zautashi, dan haka ya dauki alkawarin bazai sake kallon inda takeba bari ta tayar mai da hankali”
      Ummi ko hannun kujeran da hajiya take ta zauna, sannan ta kwanto jikinta tana fadin amman ahajiya kinzo kinan ?
    Allaha kiyaye, nazone ganku, ban zaun agidan iyayenku ba mezai kaini inzauna agidan ku”
   Mikewa Abdulmajeed yayi yace”
    Hajiya ni zan wuce idan na dawo anjima na mayar dake gida”
    Toh bawan Allah ina jiranka Allah ya maka Albarka”
       Yana mikewa Ummi ta dauki abin cin da tagama hadawa tabi bayan shi, ya shi mota ya zauna ummi tai saurin bude dayan gefen ta ajiye abinci”
     Cikin sauri yace”
  Ke! ke! Wai mena gaya miki? bason rashin kunya fah, nace banci ko dole ne?
     A’a badole bane, daman cewa nayi ka kaiwa almajirin daka kaima  na jiya”*KOWANNE BAKIN WUTA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    ( da nashi hayakin)
💨💨💨💨💨💨💨
Story & Written by
    *Fadeela Lamido*
*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*
    Wattpad @fadeelalamido
               39 – 40
Kallonta yayi, cikin ido, itama kallon shi tayi tare da murmushi, sannan ta juya zata kama ciki”
   Ke zonan”
    Dawowa tayi ta tsaya, tana kallon shi”
   Ni d’an aiken kine?
    A’a kayi hakuri naga idan aka barshi ne saiya lalace  azubar, kuma babu kyau almubazaraci”
     Ok, kinsan da haka kike yinshi da yawa, daga yau ki dinga dafa iya cikin ki”+
    Yana fadin haka yaja motar sa yai gaba, yayin da Ummi ta tintsire da dariya, sannan ta juya ta shiga gida”
    Tabe baki Hajiya tayi tare da fadin”
   Marasa kunyan yara, da kunata kunci, kowa cikin ku nunawa yake beson auren, amman dan tsabar nunafunci kwana biyu rak sai gaku kund’inke, munafukan banza”
   Gutuwar dariya Ummi tayi, sannan tace”
   Kai hajiya, ai ga babban munafuki can ya tafi”
     Zaro ido hajiya tayi mijin naki kike kira muna fuki?”
       Toh hajiya inbace mai hakaba me zance mar, jiyafa dana bashi abinci cewa yayi shi becin jagwalgwalo, amman dayaga nashiga daki saiya dauka ya faraci”
     Daga Ummi har Hajiya tintseriwa sukayi da dariya, bayan sun sarara Hajiya tace”
    Kice dai kin masa labe, ai daman cen shi haka yake, becika son ci abu gaban mutane ba, so dayawa idan kabashi abu gaban wani tashi yake yabar maka, kuma dan Allah Ummi karki biyewa halin sa, kisaki jiki dashi, koba komai dan uwanki ne, kumashi ko yana son abu ba nunawa zaiyi ba, dan Allah kar ace za’a masa jan aji irin naku na yaran zamani, kinji ko”
   Hmmm Hajiya kina nufin inyi shishshigi babu kwarjini, kinajifa ranar da aka cemai za’a hadamu cewa yayi fah besona, nikuma Hajiya dan ban da hankali saina shige mishi yamin wulakanci?”
   Ai wannan furucin da yayi Ummi na shirmene, ramawa yayi, ko kin manta kintaba fadan haka abaya, har yanzun fah abin na damun sa, aishi Bawan Allah ma kidaina saka zance shi azuciyarki “
    Kedai kawai kiyi kokarin jawo hankalin shi gare ki, yanzun ma ga wasu kaya nan nataho miki dashi, ki boye su sosai kar ajesu a inda Bawan Allah zai gani, ga yadda zakiyi amfani dasunan kowanne arubuce ajikin sa”
   Turo baki Ummi tayi, nifa Hajiya ban son wannan kayayyakin “
   Auto yayi kyau, kina nufin haka zaki zauna, har inacewa ai kisan mahimmancin su baza kiyi wasaba, naga lokacin Mukhtar dakanki kike zuwa neman su?, bare wannan daba ke kadai zaki zauna ba, budurwa nanan zuwa, ko ranan auren ku sunturi yaitayi akan wancen mgnr gurin babanshi”
   Wani irin haushi Ummi taji ya kamata, yanzun wai sabo da lalacewa Nafisa zai aura?, yariyar da take yawo kamar tsirara, yanzun hakama wajenta ya tafi dan taji jiya yana cewa Sadiq ya samesa gidan su Nafisa, wato shima Sadiq din munafuki ne kenan”
    Tagumi ta zuba tare da fadin”
   Gaskiya bazan yadda Nafisa ta shigo gidan nan amatsayin matar Abdulmajeed ba, jifa fitsaran da sukeyi, tun atiti, idan suka shigo gidan nan kuma ai kashina ya bushe”
STORY CONTINUES BELOW
    Hajiya ce ta kalleta tace, ke mene yai miki zafi kika zuba tagumi?
  Cire tagumin tayi, sannan tace”
   Hajiya amman idan yayi auren banan gidan zata zauna ba?
    Anan zata zauna mana, ai gida biyu babu dadi”
   Haba Hajiya, nikam wlh baxan iya zama da itaba, idan ya kama dole sai yayi auren sai dai ya neman mata wani gidan, wlh nikam ancuceni da aka hadani da shi, ni ban son kishiya”
    Bode baki Hajiya tayi tana kallon, Ummi sannan tace baki son kishiya?
    Toh hajiya koke fa har Alhaji yarasu be miki kishiya ba, kuma daddy da Abba ma basuyi aure biyu ba, saini ‘yar karamata dani?
     Murmushi Hajiya tayi sannan tace”
   Toh aike ki kikai sake tun farko, yanzun babu dalilin daza’a hanashi auren shi”
    A Wani iri hajiya ta karasa wuninta, dan Ummi tundaga wannan mgnr ta fada cikin zullumi”
     Shiko Abdul bayan ya zauna Office ya aika adauko nasa abinci cikin mota”
   Ya bude kenan yana kokarin kaiwa baki Sadiq ya shigo, cikin murmushi yace”
   Toh ko kaifa, yanzun ne zakasan me duniya ke ciki, da baka san komai ba”
    Dagowa Abdul yayi ya kallesa sannan yace”
   Kai dallah gafara can, zo kaci gaji, ina Ummi ta iya wannan girkin?, gidan Momy naje ta hadu ni dashi”
     Cikin dariya Sadiq yace”
   Amman Momy ta kyauta, tanaji dakai, kuma bata taba hadoka da abinci ba sai yanzun dakayi aure?
    Banza Yayi da Sadiq saida suka gama ci, sannnan Sadiq ya mike yana fadin”
        Gaskiya Ummi ta iya girki, yakamata adinga bamu irin wannan kullum”
   Cikin sauri Abdulmajeed ya kallesa sannan yace”
    Waiwa yace maka Ummi tayi shi”
    Dariya Sadiq yayi sannan yace ni zakama karya wanne halinka ne ban saniba, makaryacin banza”
    Hmmm toh naji, ita tayi, saime? dan naci abincinta”
    Me kuwa?, babu kumai mutum da matar sa”
   Eh mata tace, amman dan Allah koda wasa karka nuna mata naci abincin nan, bani tayi nace, ban ci, shine tace nabawa almajiri danabawa najiya, kasan jiya databani cewa nayi banci, sai dai nabawa almajiri, bayan shiganta daki saina dauka naci saboda yunwa ta dameni, gashi momy ta hanani abinci”
    Dariya sosai Sadiq yayi zuwa can yace”
  Amman gaskiya kaban dariya, dan Allah malam ka saki jikin ka kuci amarci kawai, tunda gashi tun ba’aje ko inaba ta fara rudaka da kirkinta”
  Hmmm kadai bari kawai, bakama san wani abuba, akwai wani turare da take amfani dashi, gaskiya bazan boye maka ba, kamshin shi namin dadi, kuma wani abu dayake bani mamaki, koda yake ba abun mamaki bane, daman idan mace da nimiji suka kasance guri daya, na Ukun su shed’an ne, wlh idan tana zaune a inda nake, wani iri nake ji cikin jikina, kuma bawani kwalliya fa dake cikawa ba, amman dai jikinta acike yake”
    Hmmm ai kaine shed’an d’in, idan ba hakaba kana zaune da matar ka, ka dinga kira mana shed’an, kaine babban shed’ani da kake kokarin haramta abin da Allah ya halasta maka”
   Mikewa Abdulmajeed yayi tare da fadin”
   Au hakama zakace?, dana sani ban gaya makaba, kai badaman nagaya maka abin dake zuciyata sai kaita min dariya, kuma nasan ka da shegen surutu, yanzun naga har wani kebewa kukeyi kaida Ummi kuyi gulmata, karkace zaka gaya mata ni naci abincin nan fah”
STORY CONTINUES BELOW
    Sabowar dariya Sadiq ya fara, bayan ya jima yanayinta yace”
   Ai ina tabbatar maka wata kila Ummi ta leko taga kanaci shiyasa ma yau da tabaka tace ka kaiwa Almajirin jiya”
   Shiru Abdulmajeed yayi, eh kuma fah haka ne, domin tun ina zaune afalo na farajin dariyarta, kuma dana shiga daburcewa tayi, tarasa takamaimai abin da zatace tana ma dariya”
    Dagowa yayi yacewa Sadiq kuma fah haka ne, domin najita tanata dariya ita daya adakin, aiko zataci ubanta ni take kira almajiri?
     Cikin daure fuska ya karashe aikin sa ya nufi gida, acikin zafi ya shiga falon”
   Ganin hajiya yasashi yai ajiyan zuciya domi ya manta tana gidan”
   Ko zama Hajiya bata bari yayi ba tace ya maidata gidan ta”
    Lokacin da ya dawo Ummi tana kwace agadonta har bacci ya fara dibanta”
    Dan haka ya tsaya yana kallonta, tayi kwance rashe2 dagani tanajin dadin baccin”
    Tsintan kanshi yayi da kara matsawa kusa da ita yana kare mata kallo”
   Idonta arufe yake, sosai tamai kyau naban mamaki, yadda yakejinta zuciyar shi haka take kullum betabajin sonta ya raguba, saidai wani lokacin tana matukar bashi haushi, badan beson taba saidan kinsa da tayi afarko, sannan taje tabawa wani dama yayi wasa da abin da ya dade yana kiwo acikin zuciyan sa, dan haka yakejin haushin dan da suka haifa”
     Tsugunawa yayi agabanta, adaidai lokacin data juyo masa baya, hakan yayi daidai da zamewan dan kwalin dake kanta”
    Ya Subuhanallah, yafad’a acikin zuciyar, sakamakon wani dogon gashi daya gani, daman Ummi tana da gashi haka? daganin sa zaiyi laushi, acikin zuciyan sa yace”
    Zanso naga karshen gashin nan, sai dai ta kwanta akansa babu daman yagani”
   Ahankali ya daga hannun shi ya shafi gashin tare da kai masa sunba, take ya mance abin da yazo yi, kasa hakuri yayi, dan haka ya zarce da shinshinata tare da lumshe idon shi”
    Ganin Ummi na motsi yasa yai saurin mikewa, falo ya koma ya fara sintiri, gaskiya akwai matsala, bazai taba nunawa Ummi tana da wani abun burgewa ba, ya zama lallai ya gaggauta kawo Nafisa gidan nan, domin ya gujewa fadawa tarkon Ummi”
     Cikin dare kasa bacci yayi” dan haka ya tashi ya zauna, babu abun da idonsa ke hango masa sai bakin gashin ummi, wadda har yanzun be dena jin sulbinshi ahannun shiba, dan haka ya yake shawaran zuwa ya same daddy akan mgnr Nafisa”
    Tun 6:30am ya fice agidan batare da Ummi taga fitan shi ba”
    Yana isa gidan su dakin Momy ya dosa, Momy naganin shi kuwa ta mike azabure tare da fadin”
    Lfy mene ya faru?, ganin ya sunkuyar dakai idonshi jawur yasa momy karasowa tare da fadin”
   Abdulmajeed mutuwa akayi ne?
    Cikin sauri ya girgiza kai sannan ya dago ido ya kalli Momy tare da fadin”
   Nazo ne, inason inyi mgn dake”
     Zama Momy tayi abakin gadon sannan tace inajin ka?
    Emm, daman akan mgnr yariyar danayi mgn ne kwanaki, sosa keyarsa yayi, sannan yacigaba da cewa”
    Daman ku kawai iyayenta suke jira, kuma naga har yanzun Daddy bece komai ba”
    Kauda kai Momy tayi tana nazari, zuwa can tace”
    Hmmm, daman akan wannan mgnr ka dako wannan uwar sammakon?, meyayi zafi haka?, wlh ka fad’ar min da gaba, nina dauka ma mutuwa akayi ko kuma wani babu lfy”
STORY CONTINUES BELOW
    Kauda kai Abdulmajeed yayi, tare da mazurai, kallon shi Momy tayi taga yadda idonshi yayi juwur tabe baki tayi sannan tace”
    Toh yanzun me kake nufi?
    Dagowa yayi sukayi ido biyu da Momy sannan yai saurin maida idonshi kasa, Momy inason ajemin neman aureta ne”
     Toh aibani ya kamata ka taraba, dan kasan dai mata masa zuwa neman aure, sai kaje kasamu baban ka ka gayamai”
    Momy ninaga kamar bakwa son auren nan ne, shima Daddy be wani dauki mgnr da mahimmaci ba, kuma kufa kuke cewa naki aure, yanzun kuma nace zanyi anki kulani”
    Wani irin kallo tamai sannan tace”
    Towai Abdulmajeed saurin me kakeyi?, dan Allah ka natsu, abi komai ahankali, yaufa dukka kwana Ummi 3 agidan ka”
     Shiru yayi kusan Minti 20 zuwa can ya mike saida yakai kofa yace nawuce”
    Hararashi Momy tayi tare da fadin ka gaida gida”
    Tana cikin jimami taji ya tashi motar da karfin tsiya”
    Afali tace, yau naga fitinannen yaro, inajin bayan Sigari ma akwai abin da yake sha, jifa wannan uwar sammako kamar ankoro sh, Allah ka shiya mana”
     Abdulmajeed kuwa yana fita ya kira nafisa awaya, kamar bazata daukaba domin tunda yayi aure take mai ‘yan kunbure kunbure, sai da ta kusan katsewa ta dauka”
    Nafisa kina inane?
    Yanzun fito wata kenan zan wuce Office”
   Ok muhadu a inda muka saba haduwa yanzu nan”
    Ok tam”
   Ajiyan zuciya yayi sannan ya kashe wayar ya kwanta akujiran motar”
    Nafisa ko cewa tayi jarababbe, yanzu haka jarabar ce ta motsa, yayi aure kamar beyiba sai yazo ya fitini mutum, saiya gama tada hankalina ya tafi yabarni da fitina, Wlh idan satin nan ya wuce be turoba daina kulasa zanyi”
    Kusan minti 20 yana jiranta sannan ta iso, bude ido yayi ya kalketa sannan ya lumshe idon shi, bashi ya budeba sai da yaji shigowanta cikin motar, cikin sauri yakai Hannusa jikita, batare da tayi wani yinkuri ba, ta sallama masa komai, ya juma yana wasansa da ita, amman beji natsuwa tazo masaba, jiyake kamar yana dada tasowa kansa da fitina ne, dan haka ya janye jikin sa tare da fadin”
    Maida rigarki, ki wuce, ni zan koma gida nayi wanka, sai mun hadu anjima”
    Cikin kissa Nafisa ta kara rukoshi tare da fadin”
    Yunwa nakeji nafito ban karya ba”
    Ok, kudi yaciro ya mika mata, gashi keje kici abinci”
   Narkewa tayi sannan tace ninafin son muje tare”
   Cikin fada yace, ke! Idan zaki wuce ki wuce nagaya miki banyi wanka ba”
   Zunbura Baki nafisa tayi, sannan ta sauka, harta fara tafiya yaji tabashi tausayi dan haka ya kirata”
    Dawowa tayi tana cigaba da kunbura baki”
   Shiga muje gida, nasan yanzun Ummi ta kammala breakfast, idan ki kaci nikuma nayi wanka saimu fito tare”
    Zama tayi tare da cewa, amman ranta bazai bacciba ko?
   Ina ruwanki da ita, abin dama kin kusan zuwa gidan din din”
    Murmushi tayi tana cigaba da kwarkwasa”
    Damisalin 9:30 Ummi tagama hada breakfast, bayan tayi wanka ta gyare jikinta ne taji tsayawa mota, Mikewa tayi ta leka ta window”
    Hassana tagani kanwar Abdulmajeed rungume da Ahmeed akan kirjinta, drive ya sauke su”
    Cikin mamaki tace yaya akayi Hassana suka hadu da Ahmeed?, cikin dauki dasun ganin yaron tayo waje aguje”
   Hassana ta fara runguma sannan ta durkusa ta dauki Ahmeed ta dagashi sama tana tana me farin ciki”
     Adaidai lokacin Abdulmajeed ya sako hancin motar shi cikin gidan”
    Ganin Hassana yasa yai saurin zuge gilashin motar, sanna ya juya ya kalli Nafisa yace”
    Karki sakko waccen kanwa tace, ina zuwa barin dawo”
    Sakowa yayi cikin motar sannan ya nufa gurin su, adaidai lokacin da suke kokarin shiga cikin palon”
    Hango Ummi rungume da Ahmeed yasashi jin wani haushi, dan haka ya d’aga murya yace ke Ummi?
     Cikin sauri ta waigo ta kalleshi”
    Karki shigar min da yaron nan cikin gidana”
    Cikin idon Ummi ta kalkeshi sannan tace”
     Saboda me??
    Kina tambayata ne?, juyawa yayi ya kalli Hassana yace”
    Ke, amsheshi ki maidashi gida, karki kara zuwa min dashi, idan ba hakaba wlh wata rana saina karya ki”
    Arude tamikawa Ummi hannu, saidai kememe Ummi taki bata shi”
     Jinjina kai yayi, sannan ya nufi cikin gidan, yana fadin, ki amsheshi kibar nan gidan karna fito na same ki”
   Daga Ummi har Hassana kuka sukeyi, zuwa can Hassana tace”
      Kawoshi mutafi, kiyi hakuri, kin san halin yaya, daman Momy ce tace idan zan taho nabiya na dauko shi”
    Hawaye Ummi ta share, sannan tace bazan badashiba, jiki abin ki, gidanshi din banza, saidai yayi abin da zaiyi, idan ya sake min mgn saidai mutafi tare”
    Karkiyi haka, kiyi hakuri idan na koma zan fadawa Momy, kinga ita zatai maganin abun, kinsa halinsa idan yai mgn kamar fadan Allah”
    Hannu tasa ta karbesa ajikinta da karfin tsiya, kuka yaro ya fasa, dan haka Hassana ta wuce da sauri”
    Ummi na tsaye na kallonsu har suka fice, banda hawayen tausayin yaron babu abin da take, takasa abarin wajen, agaskiya Abdulmajeed ya fara kaita bango, sam bazata jure wannan rashin mutuncin ba, tana cikin wannan tunanin ya fito”
    Wata uwar harara ya buga mata, itama cikin ido ta kalleshi hawaye na sakowa daga cikin idanunta, ganin bata da niyar cire idonta akansa yasa yayi kwafa ya wuceta”
     Gurin motarshi ya nufa, gefen da nafisa take ya bude tare da fadin sakko muje……..
   Mmn Yazeed🔥 🔥🔥🔥🔥🔥
KOWANNE BAKIN WUTA
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    ( da nashi hayakin)
💨💨💨💨💨💨💨
Story & Written by
    Fadeela Lamido
​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​
    Wattpad @fadeelalamido
     
                59 – 60
Jikinta asanyaye ta fita, dan haka Abdulmajeed ya ya dauko jallabiya ya saka sannan ya nufa gado, cikin matsanancin hali, kwata kwata bacci yaki zuwa idon shi, gaba daya jikin shi ya dauki dumi, Cikin shi namai wani irin cewa, dan haka asubar fari ya kira Sadiq yamai bayanin halin da yake ciki”+
    Karfe 7:55am Sadiq ya shigo gidan, lokacin Ummi ta gama breakfast tana kokarin jerawa”
    Ganin Sadiq ta washe baki cikin fara’a ta gaida shi”
    Wuceta yayi, ya nufi dakin Abdulmajeed, dan haka abin ya bata mamaki, dan idan yazo zama yake afalo sai dai yai masa waya”
    Zama tayi tai tagumi kodai, ya fada masa abin da namai jiya ne?, kuma ai inda ya gaya masa nasan magana zai min”
    Cikin irin wannan zullumin ta zuba tagumi”
   Shiko Sadiq yana shiga ya samu Abdulmajeed nannade agado, cikin son yin dariya ya karasa ya zauna tare da fadin, doctor abin kuma har yakai ga haka?, kuma duk da haka ka kasa saduda, ka nuna mata abin da kake so?
    Cikin rawan Sanyi yace”
   Sadiq wlh ba yadda banyi da itaba amman taki, har mamakin kaina nake yadda na kwantar dakai ina rokonta amman wlh taki ta saurare ni”
    Kana nufin ka nemin hakkin ka Ummi ta habaka?
    So nawa kuma? Idan kaga yadda nake rokonta wlh saika tausaya min, ni da inada yariyar dazan aure wlh bazan sake kula Ummi ba, amman yanzun kona memo wata su Abba cewa zasuyi sai sunyi bincike”
    Shiru Sadiq yayi wannan karon ransa ya fara bacci da halin Ummi, tunda yanzun ya nema bekamata ace Ummi ta hanasa ba”
    Dago yayi ya kalli Sadiq sannan yace”
   Yanzun tasan halin da ka kwana ciki?
    Bata saniba, kuma ban son ta sani, taje ta cinye kayanta, kuma wlh tace darajan ‘yan uwantaka dayau dinnan Wlh saita bar gidan nan, dan banga dalilin dazan zauna tana  tayar min da hankali ba”
    A’a nasan bata kyauta ba, Amman kayi hakuri, yanzun ga magunguna nan nakawo maka, ka tashi kasha, maganin ya Ajeye sannan yace barin je inga Ummin”
      Sadiq ka barta kawai, dan Allah karkai mata mgn kyaleta kawai”
    Sadiq be sauri Abdulmajeed ba yai waje abin sa”
    Afalo ya sami Ummi, zama yayi nesa da ita, sannan ya dago ya kalleta”
    Amman dai kinsan abin da kikeyi bedace ba ko?, agaskiya baki kyauta ba, idan da kince be nemiki bane, nima ban goyi bayan akaron farko kibishiba, amman tunda yafito ya gaya miki yakamata ki saurara shi, wlh kin ban mamaki, ban dauka haka kike ba, dan haka kiji tsoron Allah ki gyara hakin ki”
    Hawaye Ummi ta share takasa cewa komai, illah hawaye dake sintiri Afuskanta”
  Sadiq ne ya kalleta yace aiba kuka zakigyi ba, mijiki nacen beda lfy kitashi kije kibashi hakuri kuma karki sake irin wannan abin kinji ko?
      Kai ta gyada, bayan Sadiq ya fice Ummi ta mike ta nufa dakin tana cigaba da share hawaye”
     Sai dai tana tura kofar tajita akulle, meya yasa rufe kofa, tunda take bata taba zuwa ta samu kofar akulleba”
STORY CONTINUES BELOW
   Ahankali ta shiga buga kofar, ji tayi kaman babu mutum dan haka ta shiga kiran yaya, dan Allah ka budemin kofar”
     Haka ta kwashe kusan minti 30 tana buga kofar tare da kiran sunan shi amman shiru, dan haka ta juya ta koma dakin ta, gado ta haye tare da fashewa da kuka”
     Meyasa nake bata masa rai?, alhalin fushin shi na damuna,  wlh ban son naga yana fushi dani, yaya zanyi inbashi hakuri?, nashiga Uku
    Har azahar be fitoba dan haka hankalin Ummi ya kara tashi, wuni tayi cikin kuka”
     Misalin biyu na rana ummi ta fito falo taitagumi, zuwa can tqga fitowan Abdulmajeed da alama masallaci zashi
        Mikewa tayi da sauri ta rikeshi yaya dan Allah kayi hakura……
    Cikin zaro ido yace ke karki rainamin hankali dallah sake ni”
   Sakinshi tayi harya juya zai fita ya juyo afusace”
    Ki wuce ki tafi gidan ku, karki yadda na dawo na sameki anan”
    Natafi gidan mu?, yaya naface maka kayi hakuri”
    Ficewa yayi afusace dan haka Ummi ta saki kuka, dagudu ta nufi daki ta dauko gyalenta, wani irin haushine ya kamata, cikin matsanancin baccin rai tabar gidan”
     Memashin ta tara tahau gidan Abba ta nufa amman tana tunawa da kalaman Abba jikinta yai sanyi”
     Idan naga d’ana acikin farin ciki kece, haka idan nagansa cikin bakin ciki zanyi kuka dake, karki yadda Abdulmajeed ya kawo min karanki”
    Sannan ta tuna ranan da Umma tazo har gida ta mata dukan tsiya saboda Abdulmajeed yakai karanta, nashiga Uku ta fada afili, mebashin dinne ya waigo tare da fadin yaya akayi hajiya?
   Bakomai muje, amman nafasa zuwa can, sunan unguwar su Momy ta gaya mai”
     Suna isa ta biyashi kudinsa sannan tashiga ciki, jikinta amatukar sanyaye”
    Momy da anty kadai afalo, cikin siririyar muryanta tai musu sallama”
   Amsawa sukayi tare da zuba mata ido, ganin inda idonta suka kode yasa Momy take fadin lafiya?
     Zama Ummi tayi akasa wajen kafafun Momy tare da fashewa da sabon Kuka”
       Hannu Momy tasa ta dago Ummi ta zaunar da ita akusa da ita sannan tace”
     Meya faru?, kedawa da yamman nan?
   Bubu amsa sai kuka kawai da take, dan haka momy tacewa anty Salma, kiramin number Abdulmajeed”
     Tana kira taji duk layinsa kashe yake, dan haka tacewa momy wayar sa akashe suke”
     Girgiza kai tayi, zuwa can ta juya ta kalli Ummi, shiya sauke ki?
     Cikin kuka Ummi ta girgiza kai”
     Shiru Momy ta sake yi zuwa can tace”
    Ummi kun yi rigima ne?
      Girgiza kai Ummi tayi tare da fara wasa da yatsun ta”
    Anty ce tace, ke Ummi ki bude baki kiyi mgn mana”
     Hawaye ta share Ahakali tace”
     Anty cewa yayi intafi gidan mu”
     Kitafi gida?, Momy ta tamya, Anty ko kwashewa tayi da dariya tare da fadin, Abdulmajeed manya, inajin fushi yayi Momy”
    Fushin banza, ban da haukan shi Ummin zaicewa taje gidan su?, inma wani abu tamai ai sai yazo ya fada, wawan banza kawai”
     A’a Momy itama fah Ummi tana da laifi, tsakani da Allah Momy, jiya fah kinajin abin da yake fada”
STORY CONTINUES BELOW
     Tabe baki Momy tayi sannan tace, ai kome tamai shirmen shi yaja mai, yaro beda aiki sai fadin ran tsiya, dayake idonshin sun fitsare har yana iya fada, mara kunyan banxa kawai, ai tuntuni akecewa yayi auren ya ki, sai yanzun zaizo ya damemu da masifa”
     Toh Momy kiyi hakuri, sannan amasa adalci dan Allah, dan nasan be wuce akan mgnr daya fara jiya ba, tun jiyan ma idan kin lura afusace yake”
     Dauke kai Momy tayi, zuwa can ta dauki wayarta ta latsa number Sadiq”
     Bayan sun gaisa Momy tace”
    Ina abokin ka?
   Momy rabona dashi tunda safe, yanzun ma ina kan hanya ne zanje gidan sa”
    Toh idan ka sameshi kace mishi nace yazo ya dauki matar shi, dan wlh idan yabari ta kwana agida ransa zai mugun baci”
      Toh kawai Sadiq yace, sannan ya aje wayarsa agefe, acikin zuciyan shi yace yanzun nan Abdulmajeed korata yayi kenan”
     Bayan Sallar mangariba saiga Sadiq da Abdulmajeed sunyi sallama”
     Ummi nadakin Momy itada anty Salma, fada taita mata akan gudun Abdulmajeed da take, nasiha ta mata me shiga jiki, duk jikinta yayi sanyi dan haka tai tagumi”
    Tana cikin wannan halin taji shigowan Sadiq da Abdulmajeed dan haka taji cikinta ya murda”
Acan falo kuwa bayan sungaisa da Momy ta kalli Abdulmajeed tace”
  Me Ummi ta maka kace ta tafi gidan su?, wai kai kana da hankali kuwa?
       Momy aiba nan nace tazoba, gidan Abba nace taje, danni gaskiya nagaji da halinta, rashin kunya take min bata ganina da mutunci”
      Bawani rashin kunya da take maka, karya kakeyi, kaje ka kirata adaki ku wuce gida, ban son inkarajin ka kuma ce mata ta tafi gidan su, inace danan gidan, da gidan ka, da kuma gidan Abban naku duk daya ne, ko bata auren ka dole ta shiga takumayi abin da take so aciki”
    Hmmm toh amman momy nida gidana kuma saita takura min “
     Kadaiji abin dana gayama ko?
    Mikewa yayi ya nufa dakin Momy cikin daurefuska, ya gaida anty sannan ya juya ya kalli Ummi yace”
      Tashi muje”
   Har mota Anty ta ranka su, tana kara basu shawarwari, anan Abdulmajeed ya lura Anty tayiwa Ummi fada sosai, dan jikinta yayi sanyi ba kadan ba”
        Nan gidan sukabar Sadiq, suko har suka isa gida babu wadda yai tari”
      Kowa dakinsa ya nufa, damisalin karfe 9:30pm Ummi ta gama shirin kwanciya cikin kananan kayan bacci ta daura hijjabi akai sannan ta nufa dakin Abdulmajeed”
    Tura kofar tayi tare da sallama”
     Kallo daya ya mata ya dauke kai, yana kwance agado yayi rigingine yana kallon sama”
     Jikinta asanyaye ta karasa bakin gadon, sannan tasa guiwarta akasa tare da kwantar da kanta akan kirjin shi, Yaya nayi laifi amman dan Allah kayi hakuri”
   Lumshe ido yayi har cikin zuciyan sa yaji dadi amman saiyace”
   Naji, d’agani, kije abin ki”
   Kara mannewa tayi zuwa cen ya farajin dumi akirjin shi, nan ya tabbatar wa kansa kuke take, idan akwai abin da ya tsana aduniya toh kukan Ummi ne, dan haka yaji hankalin sa ya tashi”
    Cikin kukan take fadin yaya kayi hakuri, daga yau duk abin da kakeso zanma, bazan karama musuba bare kayi fushi dani, wlh idan kana fushi dani bana iya bacci, dan Allah ka saki ranka, ka daina fushi dani, ayanzun haka kirjina zafi yake min”
STORY CONTINUES BELOW
     Sosai yaji dadin kalamanta, ahankali yazame dan kwalinta, besan lokacin daya fara shafa gashin kanta ba, tare da fadin”
    Da gaske kikeyi Zainab?, kirjiki nazafi kamar yadda nawa yakeyi idan kina kuka?, Zainab fadamin gaskiya
Kina nufin kema kina sona?, daman akwai ranan daxanji irin wannan mgnr daga bakin ki?
    Lomo ta sakeyi akirjin shi, tare dasa hannunta ta shafo sumar kanshi”
   Lumshi ido Abdulmajid yayi tare da fadin”
   Masha Allah”
   Dagota yayi ta hayo gadon ta kwanta rugumeta yayi tsama ajikinsa, tare da binta da sumba”
   Haka suka kwana saboda dadin bacci yau ko kiran sallah basujiba, kusan 7:30am suka tashi”
    Koda Abdulmajeed yaga gari ya waye mamaki yayi sosai, daman akwai dadin baccin dazai kaini wannan lokacin?
    Juyawa yayi ya tada Ummi, itama mamaki tayi sosai da ganin garin”
    Cikin ido Abdulmajeed ya kallita, tare da fadin meyasa baki tadani ba?
   Sunkuyar dakai tayi sannan tace nima ai ban san lokaci ya tafi ba”
      Ok toh tashi kije kiyi wanka”
    Mikewa tayi ta nufa toilet, tana kokarin shiga taji murya shi yana fadin”
   Ko naxo na cud’aki?
Jimm, tayi sannan tace a,a yanzu nan kai yaya sai ka iya?, nifa kanwarka ce”
     Hmmm kanwata kuma matata ba, kina son kimin wayo ki cuceni ko?
    Murmushi tayi sannan ta Shige”
   Koda tana wankan tunanin Abdulmajeed taitayi, daman zai iya sakin jikinsa dani, kenan wata rana zaimin wanka, tunda nagano shi simimi kasau ne, ko mukhtar be taba min wanka ba”
    Da wannan tunanin ta karasa ta fito”
   Abdulmajeed ma ya shiga”
  Ko bayan daya gama shiryawa, ji yayi kamar karya fita, amman fitan nashi nada matukar muhimmanci dan akwai wasu muhimman abubuwa dazai yi”
    Tare da Ummi suka fito tana manne ajikin sa, dagowa tayi ta kallishi haka zaka tafi bayi breakfast ba?
  Cikin murmushi ya daga kansa eh, anjima idan na dawo zanci”
     Kwanciya tayi ajikin sa, tana dan shafashi ahankali”
     Kollo ya bita dashi aranshi yanajin farin ciki, make murya yayi, Zainab anya kuwa yau zanje aikin nan?
     Kara narkewa tayi ajikin shi, dan haka yace”
  Gaskiya badan akwai masu jiranaba yau bazan je aiki ba”
    Kara kallonta yayi tare da fadin ko akwai abin da kike so ne?, nagoyaki ne?
  Ko rufe baki bata bari kayiba tace eh”
     Murmushi yayi sannan ya tsuna yace hau”
    Ba kunya Ummi ta dare🤔 lallai duk wadda ya shiga tsakanin mata da miji shi zaiji kunya”
   Mikewa yayi kamar ya goya karamar yariya yai waje da ita”
    Agaban motar ya dirita, fuskanshi dauke da murmushi, cikin motar ya shiga ya zauna sannan yace”
   Toh ki saki ranki mana”
  Kara lafewa tayi ajikin motar tare da ya mutsa fuska”
      Zainab ko goyon ne be ishekiba?
    Da ido ta amsa masa, dan haka yayi dariya, sannan ya sakko yace toh hau muje na maidaki palo”
   Hayewa ta sakeyi akaro na biyu🤔 kai wannan yariya kwai munafuka, anaso ana kaiwa kasuwa”1
    Yana ajeta yace toh saina dawo ki nemi abinci kici kiji”
    Aguje yabar gidan, ji yake kamar yafi kowa farin ciki”
   Ahaka suka kwashe kusan sati, kullum zatazo dakinsa su kwana tare, Abdulmajeed daurewa yayi wai harsai Ummi ta nemi wani abu da kanta,
  Ganin bata da niya yasa ya fara gajiya”
   Acikin zuciyarshi yace”
Watoh itadai Ummi uwar ‘yar son banza ce, mukwana tare, mutashi tare babu abun da ya dameta, ita dai ayi wasa da ita sama sama abarta, sannan kuma da safe tace agoyata, yau zanga karshin wayon ki”
     Kamar kullum yauma suna kwace rungume da juna, ahankali Abdulmajeed ya kira sunan ta”
   Amsawa tayi ahankali”
   Nace yau za’a bani hakkina?
     Jimmm🙄😳 tayi, zuwa can tace”
    Mezai hana Yayana”
     😴Hmmm nagode kanwata”
   Yaya?
   Na’am yaya akayi kanwata?
   Daman cewa zanyi dan Allah karka tabamin kirjina……
1
    🤔🤔
        *Mmn Yazeed*🔥 🔥🔥🔥🔥🔥
KOWANNE BAKIN WUTA
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    ( da nashi hayakin)
💨💨💨💨💨💨💨
Story & Written by
    Fadeela Lamido
​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​
    Wattpad @fadeelalamido
                 61 – 62
Toh fah😕, daman akwai wani guri dazaki min shamaki?, Ummi to kodai har yanzun baki sona ne?
    Bahaka bane yaya nidai haka nake bon so ataba min”
  Jimm, yayi zuwa can yace”
Kina nufin tun tuni haka kike?, koko daga baya ne, naga ai kin taba aure?
   Yaya, wlh tuntuni haka nake shima baban Ahmad haka yake hakuri dani”+
   ‘Dagowa yayi ya kalli idonta sannan yace”
    Toh nidai gaskiya ban miki alkawarin ba”
   Cikin sauri ta fara kokarin matsawa, cikin tsanin mamaki Abdulmajeed yabita da kallo”
    Ganin tana shirin guduwa, yasa ya rukota tare da fadin naji, na amince bazan taba ba”
    Sannu ahankali Abdulmajeed ya shiga sarrafata, kan kace me ya rikece tare da watsar da akawarin daya dauka, ganin haka yasa na fice nabasu waje”
     Ban sake komawa ba sai da asuba, Abdulmajeed ne tsaye yana goge gashin kansa da alama wanka ya fito”
   Zuwa can ya juya ya kalli Ummi, dake zaune akujeran dake gefen gadon ta turo baki gaba, yace”
    Tashi kije kiyi wanka”
   Bazanyi ba”
   Toh Allah ya baki hakuri, har yanzun baki huce ba?, ni danaji kince kar intaba miki na dauka hannu ne bakiso yakai gurin, ban dauka sharadin naki har da baki ba, juyar dakai yayi gefe, yana matse dariyar sa, sannan ya kara cewa”
    Amman kinga yanzun nafahimta wani lokacin zan kiyaye,  banzan kuma ba”
    Kara turo baki tayi gaba, sannan tasa hannu ta share hawaye, mikewa tayi tana hararan gefen sa tashige toilet din”
     Murmushi Abdulmajeed yayi, akullum son Ummi kara shigan sa yake, yanajinta sosai acikin zuciyan shi”
    Bayan Ummi tayi wanka ta gama shiryawa tsaf, ta nufa kitchen domin taga kwana biyu haka Abdulmajeed yake fita batare daya karya ba”
     Karfe 7:00am tagama komai, dan haka ta zauna zaman jiran sa”
    Sai 7:39 ya fito, cikin kana nan kaya da gajeran wando, daidai guiwa, kallon shi tayi ta dauke kai”
    Bayan sun gama breakfast din ne ya kalli ta, Ummi har yanzun kina fushi ko?, bayan nagaya miki kuskuren fahimta ne”
    Kara turo baki tayi, dan haka Abdulmajeed yace”
    Ok toh shike nan, tashi muje muyi wasa, yau babu inda zani, sai na tabbatar kin huce”
    Tunkafin ya rufe baki ta mike, ganin haka Abdulmajeed yace”
   Amman fah bazan daukeki da wannan kayan ba, kije ki canza kaya tukuna”
   Jikinta ta kallah riga da siket ne na atamfah, sun kamata sosai, juyawa tayi ta kalleshi”
   Ai zan iya hawa dasu tattare siket din zan yi”
     Malama kije ki canja, kanan kaya zaki saka”
STORY CONTINUES BELOW
   To aini bani dasu”
    Ok toh muje kisa nawa, anjima idan na fita zan sawo miki”
     Naka kuma?, yaya zansa kayanka ai ma sun min yawa”
   Nasan irin wada zan baki, zasu miki”
   Ganin tana mai musu yasa ya sunkuceta sukai daki, acikin zuciyan sa yake fadin”
   Angaya miki nima wawa ne, kamar wancen mijin naki, ni bazan dauki wannan halin naki ba, riga ya dauko mata mara hannu tare da gajeran wando”
    Rigar ta zura sannan ta tsaya tana kallon wandon”
     Yaya ni gaskiya muje haka, wannan yamin yawa”
   Toh sai dai mubar wasan, danni bazanyi wasa dake kina lullube ba, nace miki anjima zan nemo miki naki”
    Amsa tayi ta saka sannan suka fito suka nufi filin wasan”
    Kallon gurin Abdulmajeed yayi tare da fadin”
    So nawa kike son nazagaye wajen nan dake???
   Sau goma”
   Sau goma ko? toh nikuma sau nawa zaki zagaye dani???
    Bude baki tayi🤔🙄 au kana nufin kaima saina rama maka?, aini bazan iya goyaka ba, baka ganin kai kato ne, wlh ko Ahmeed bazan iya zagaye gurin nan sau goma dashi ba”
    Toh ke dah meye nufin ki?, kina tufin abati zan yi?
    Matsawa gafe tayi, ta turo baki, acikin zuciyarta tace”
   Wlh wannan Abdulmajeed din, Mukhtar yafishi kirki, shi da yake min kyauta, amman shi wai sai na rama mai ko kunya baya ji, katoto dashi”
    Shima Abdulmajeed acikin zuciyan shi fadi yake”
    Kajimin yariya da shegen wayo, angaya miki nima nakashshene kamar tsohon mijin ki, kedai kawai burin ki agoyaki, baki damu da halin da mutum yake cikiba”
     Juyawa ya sakeyi ya kallita sannan yace”
     Me kikace?
   Nifah yaya gaskiya bazan iya goya kaba jibeni fah”
     Kallonta yayi, naganki, ba dole saida goyo zaki biya niba, inzabi wani abun dazaki biyani dashi?
    Eh na yadda amman ka fara goyani tukuna”
    Yauwa ko kefah zo ki hau”
    ‘Darewa Ummi tayi yaita zagawa da ita, babu wadda yakai ummi farin ciki awannan lokacin”
     Ji take tamkar ba’a taba goya taba aduniya, domin ji take tamkar goyonsa yafi na kowa dadi, ko yaron da yake bayan mahaifiyar sa, aganinta bekaita jin dadi ba”
    Ta dade abayan Abdulmajeed, ita kanta bazata iya kirga saunawa ya zagaya da itaba, zuwa can yace”
    Har yanzun be isheki bane?, akwai zafin rana fah, ko baki ji?
    Toh saukeni haka ammam fa gobe ma zaka min?
   “Eh zan miki mana indai kina biyan bashi”
    Jimm tayi sannan tace”
   Yauwa baka fadamin abin da zan biyaka dashi ba?
   Sosa kai yayi sannan yace”
   Yauwa kanwata, hakkina zaki bani”
     Kai! 🙄 shiru tayi tana nazari zuwa can tace”
   Toh naji amman sai dare ko?
      A’a na dare ai wannan wajibun ne, wannan ko bashi zaki biya, ina son ki biyani tunkafin gumina ya bushe”
       Nan danan idon Ummi suka kada zuwa jah cikin matso hawaye tace”
     Amman ni Baban Ahmeed kyauta yake min be cewa saina biyashi, kuma kaima da nasan haka zakace wlh bazan yadda”
    Bata rai Abdulmajeed yayi karki sake kira min sunan wannan wawan, karki sake kiramin sunan shi agidana, kinji na gaya miki karki sake hadani dashi, ni lafiyayya ne, ba nakashashshe ba”
     Sunkuyar da kai Ummi tayi, itama batasan yadda akayi zance ya fito ba”
     Tasan tana hana shi fushi zaiyi Gashi idan yana fushi da ita bata jin dadi, dan haka tace”
    Shike nan muje na yadda, amman karfa kace ka manta”
     Dauke kai yayi, bazan manta ba”
 
     Daukanta yayi cak be dareta ako inaba sai toilet, cikin ido ya kalleta, yi maza kiyi wanka nima barin je nayi”
    Cikin kankanin lokaci ya dawo, ya sameta tagama gyara jikinta dan haka suka shiga wasannin, tun tana ganin abun kamar wasa har ya fara wuce gona da iri, acewar Ummi”
  Abdulmajeed be saurara mata ba, har saida yaji natsuwa tazo mai”
     Yana kankame da ita yake fadin”
   Ummi baki da lafiya gaskiya, kina matukar takura min, kije ki gayawa Umma ko Momy su nema miki magani, kin takura min da yawa”
    Tureshi Ummi ke kokarin yi, amman ta kasa, ganin haka yasa ya kyauce gefe”
    Toilet ta shiga, zuwa can ta fito tana goge jiki tare da share hawaye”
       Waigawa tayi taga Abdulmajeed yabita da kallo, dan haka ta gallah mai harara”
      ‘Dazon kace baka fahimceni bane, yanzun kuma kace me?
    Murmushi yayi, sannan yace”
    Kiyi hakuri to, zuciyata ce takai hannayena wajen, bani da kaina ba”
     Juyar ta kanta tayi bata sake kallon inda yake ba, tunani take acikin. Zuciyarta gaskiya yaya Abdulmajeed yafi Mukhatar bukata, ni ko Mukhtar din ma wani lokacin takurani yake bare kuma wannan dabaya gajiya, yanzun duk ilahirin jikina cewo yake min, gashi kuma yace wai na dare wajibun ne, yanzun haka zan zauna ina kallon sa yana wahalar dani?
   Kai ina karyan ciwo zan yi bazan iyaba”
    Mikewa yayi ya wuce dakinsa, zuwa can ya dawo ya samu sai rawan sanyi Ummi keyi”
   Subuhanallahi, ya fada yana kokarin karasowa, Zazzabi ya kamaki har kina rawan sanyi haka shine bazaki kirani ba”
     Bata ce Ufan ba, sai rawan baki take irin tana jin jikin nan”
      Kallonta yayi sannan yace”
   Barin yi Sallah na dawo kinji?
    Yana fita Ummi ta mike, ragowan abincin da ta bari na rana shi ta fara ci, domin tana son ta nunawa Abdulmajeed bazata iya cin abinci ba”
    Tana tsaka dacin abincin taji takunsa, dan haka ta mike aguje batare da ta rufe abincin ba, gashi ta riga ta cika bakinta dashi”
        Lokacin da Abdulmajeed ya shigo dakin Ummi na kokarin gyara bargon dumin ya rufe mata kafa”
    A’a Ummi sai naji kamar ana gudu adakin nan”
   Cikin rawan dari da girgiza kai”
    Toh Sannu ya jikin?
Kasa amsawa tayi saboda bakinta cike yake da abinci”
     Abdulmajeed ya kula da kamar da wani abakinta dan haka ya juyar da kansa gafe”
   Nan yaci karo da kwanon abincin Ummi abude”
       Kallon abincin yayi sannan ya juya ya kalli Ummi”
    Murmushi yayi sannan yace”
     Kinga, Ummi tashi kici abincin ki, ni babu abin da zan miki”
  Ganin taki kulasa yasa ya haye gadon fuskanshi dauke da murmushi ya jawota jikin shi, kitashi kici abincin ki, ai na fahimci matsalar ki, gobe zamuje gidan Umma, zan gaya miki abin da zakice mata, dan aneman miki magani…….
   
     Mmn Yazeed🔥 🔥🔥🔥🔥🔥
KOWANNE BAKIN WUTA
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    ( da nashi hayakin)
💨💨💨💨💨💨💨
Story & Written by
    Fadeela Lamido
​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​
    Wattpad @fadeelalamido
                     63 – 64
Juyowa tayi ta kalle sa, sannan ta cire hannun sa daga jikinta ta nufa toilet”
     Jimawa kadan ta fito da alama bakinta ta dauraye sannan ta koma gadon tana kokarin kwanciya”
   Kirki kwanta jiki karasa abincin ki”+
    Kwanciya tayi tare da fadin”
   Nakoshi”
    Hmmm matsoraciya karki karamin karyan ciwo, kingama guje gujen kuma kin koma lambo?
       ‘Dan turo baki tayi batare da tace komai ba”
    Dan haka Abdulmajeed  yace”
    Maida bakin ki, ni babu abin da zan miki, amman ya zama dole ki fadawa Umma dan ta nema miki magani”
      Yaya nifa bazan iya fada ba gaskiya, kuma ni lafiyata lau”
   Hmmm ai ko dole ki fada, dan bazan iya zama haka ba, kuma ai cikin dibara zaki fada, ba gatso tsoba”
     Kasa tayi da murya sannan tace”
     Allah yaya bazan iyaba”
     Shiru ya mata har aka kwashi tsayon wasu lukaci, besaka ce mata kala ba, amman zuciyan shi cike yake da zullumi”
    Ahaka suka kwashe tsayon sati biyu yana hakuri da Ummi, yama rasa ta yaya zai billowa abun”
       Tuni anty Salma ta koma, bayan ta kara basu shawarwari”
    Ummi kuwa awannan lukacin tayi kyau tayi kiba na ban mamaki, amman Abdulmajeed yana nan yadda yake, duk da cewa yana samun kulawa ta bangaren abinci da sauran su”
  
           ** ** ***
Yau Abdulmajeed ya tashi da damuwan halin Ummi, bayan sun gama yin breakfast yace”
     Dauko gyalen ki in sauke ki gidan Umma”
   Cikin dauki ta mike domin tunda aka akai auren su bata taba zuwaba, hakama gidan momy zuwan da tayi bana dadi bane”
    Koda suka dauki hanya Abdulmajeed be kallon inda take, dan haka Ummi ta kalleshi tace”
    Yaya nayi maka wani abu ne? Sai naga kaman kana fushi”
   Juyowa yayi ya kalleta ba fushi nakeba”
    Hmmm toh shike nan, bata sake cewa komai ba har suka isa”
   Tare suka sakko sannan suka nufi cikin gidan dayake safiya ne Abba nanan”
    Da Sallama suka shiga falon, Abba da Umma ne suka amsa, sosai sukaji dadin ganin su”
    Ummi jikin Umma ta zauna cikin fara’a da nuna farin ciki”
    Yayin da Abdulmajeed ya zube akasa agaban Abba sunkuyar dakai yayi sannan ya shiga gaida su”
   Bayan sun gama gaisawa Abba yace tashi ka hau kujera mana Abdulmajeed, kaida gidan ku”
   Cikin fara’a yace”
  Nan ma ya isa Abba, hakanan yaji yau yana jin nauyin su, dan haka bazai iya hawa kujera ba”
    Abba ne ya juya ya kalli Ummi sannan yace”
STORY CONTINUES BELOW
   Yanaga ke kinyi kyau Abdulmajeed kuwa yananan yadda yake, anya kuwa baki cutar sa?
   Dan Murmushi kawai Ummi tayi tare da sunkuyar dakai”
    Abban ne ya sake kallon Abdulmajeed yace”
    Toh badai wata matsala ko?
    Ba komai Abba, daman zan tafi Office ne, shine nace barin ajeta anan”
   Toh yayi kyau Allah ya muku Albarka”
   Har Abdulmajeed yayi sallama zai fita ya tuna bega Ahmeed ba dan haka yadan juyo yana fadin”
    Umma banga Ahmeed ba?
   Cikin fara’a Umma tace Ahmeed be tashiba yanata bacci”
    Ok toh saina dawo”
   Dadi sosai Ummi taji, jin ya tambayi Ahmeed, har saida taji kwallah ta cika mata ido”
    Fita yayi yana jiran Ummi amman shiru shiru bata fito ba, gashi yabar awayar shi cikin mota”
       Ya kusan minti goma atsaye, acen ko Umma tayi tayi tabiyo bayan Abdulmajeed amman sai tace ai sunyi sallama”
   Suna cikin haka suji shi cikin daga murya yace”
      Zainab
    Cikin sauri ta amsa sannan ta fito”
  Umma ko fadin take ato bakijin mgn ne, nace ki bishi kince ke kunyi sallama”
    Ficewa Ummi tayi, ta  sameshi tsaye agaban falon, hannunta ya roko sannan yace”
  Idan na taso zanzo na dauke ki muje gidan momy, kafin na dawo ki fadawa Umma matsalar ki”
      😳 Yaya?, nifa gaskiya bazan iya ba”
   Zaki iya Ummi, haka kike son naita zama da wahala”
Yaya toh kai kazo muje ka fada mata, ni wlh bansan ta yaya zan fad’a ba”
     Zainab ki daure koma ta yayane ki fada”
    Shiru tayi, zuwa can tace, toh shikenan naji zan fada”
     Harta juya Abdulmajeed yace me zakice mata”
     Toh ba dai kace infada mataba, kaje abin ka”
    Ke! tambayan ki nayi kibani amsa”
     Shiru tayi kamar Bazatayi mgn ba, zuwa can tace”
    Cewa zanyi, ka ce anema min magani wai bani da lfy”
      Kara daure fuska yayi, sannan yace”
   Karki sake ki kira Sunana aciki, ki bakisan baki da Lafiyan bane? Karma ki nuna mata nasan da zancen”1
    Tabd’ijam yaya to bakai ka fadaba?
    Tafiya yafara cikin fashi yake fadin wawiyar yariya kawai, wlh karki sake ki kira Sunana, so kike ace min bani da kunya?
     Saida taga fitanshi gidan sannan ta koma ciki, cike da haushi”
   
Yana isa Office dinsa ya samu Nafisa agurin”
   Kallonta yayi akaikaice sannan ya wuceta ya shige ciki”
   Yana kokarin zama ta shigo ta zauna”
    Cikin ido ya kalleta sannan yace”
   Ke kuma daga ina?
    Sun kuyar dakai tayi sannan ta shiga gaida shi”
    Cikin daure fuska ya amsa, sannan ya jawo wasu takardu ya fara rubutu akan su”
STORY CONTINUES BELOW
     Gagowa Nafisa tayi ta kalle shi sannan tace”
   Doctor nazo ne ina son zamuyi mgn”
    Hankalin shi akan rubutun shi yace”
    Inajin ki”
   Shiru tayi zuwa can tace”
    Daman nagane kwana biyu kamin shiru, kuma ka daina kulani, ko kirana ma awaya ka daina, karka manta fan kamin alkawarin zaka aureni”
    Batare da ya dagoba yace”
    Eh ada na miki alkawari, amman ayanzun babu wannan zancen, dan iyayena sun hanani, kuma kisan bazan bijire musu ba”
    Hawaye ta matso tare da fadin kar kamin haka Oga, kaikace zaka aureni shiyasa ma harna Bar maka kaina kai yadda kaga dama dani,😭 dan Allah kamin adalci, ka tausaya min”
    Sosai jikin shi yai sanyi, dan haka ya dago ya kalleta, cikin nuna damuwa yace”
    Nafisa ni kaina naso na aure ki, amman babu yadda zanyi”
    Kuka Nafisa take sosai harda shashshaka, dan haka hankalin Abdulmajeed ya kara tashi, mikewa yayi cikin tashin hankali, binta yayi da kallo, acikin zuciyan shi yace”
    Yanzun meye anfanin irin wannan abun?, yaya zanyi da ita?, hakika idan nabarta haka na zalinceta, bansan wata irin kaddara bace ta debeni har idanuna suka rufe”
    Juyawa yayi ya sake kallon Nafisa, sannan yace, ya isa haka kitashi ki je gida zansan yadda zanyi
    Kasa tashi tayi, sabo da kuka dayaci karfinta, duk abin da take Abdulmajeed na binta da ido, sosai yakejin tausayinta, dan haka ya yanke shawaran zai shawo kan su Daddy domin su amince ya aureta, kodan kwanciyar hankalinta”
    Tashi muje nakaiki gida”
   Kaman daga sama taji zancen, dan haka ta mike tana layi tabi bayan shi”
      Har suka isa kofar gidan, babu wadda yai magana, bude motar tayi zata fita Abdulmajeed ya kira sunan ta”
     Ja tayi ta tsaya kanta sun kuye akasa, zuwa can yace”
    Ki kwantar da hankalin ki, kibar zubar da hawaye, zanyi iya bakin kokarina naga cewa na aureki”
     Hawaye ta share sannan tace”
      Nagode doctor, dan Allah karkaja lokaci, domin agida an matsamin da mgnr, amman kana ganin….
     Shiru tayi, ta kasa karasawa dan haka Abdulmajeed yace”
    Ina jinki?
     Cewa nayi amman Kana ganin Ummi zata amince kuwa???
   Shiru yayi, acikin zuciyar shi yace”
      Eh Ummi fah masiffafiyar yariya ce, afili kuwa cewa yayi”
   Karki damu da Ummi, kedai kawai kiyi addu’a’
   Shikenan doctor amman zan iya kiranka awaya”
   Cikin murmushi yace”
    Duk lokacin da kiga dama zaki iya kirana babu damuwa”
     Kudi ya dauko ya mika mata”
    Amman taki karba, karo na farko kenan daya bata kudi taki karba”
     Shigewa gida tayi tare da fadin nidai ka cikamin alkawari”
            ***
Lokacin da Abdulmajeed ya koma daukan Ummi kwace ya sameta afalo shame shame, dan haka yaji gaban sa ya fadi”
      Ita kadai ce afalon dan haka ya isa dafda ita ya zauna tare da fadin yaya dai?
    Kara dunkulewa tayi dan haka ya sake cewa”
     Ina mgn kinmin shiru?
Umma ce ta fito, cikin sauri Abdulmajeed ya mike tare da sosa kai, sannu da gida Umma?
   Yauwa Sannu Abdulmajeed, ka dawo?
    Can gefe ya zauna tare da fadin eh”
    Zama Umma tayi, sannan tace”
    Ai Ummi tunda ka tafi babu lafiya, wuni tayi amai”
    Acikin zuciyar shi yace amai kuma?, da dai wani ciwon ne, dana ce lanbo ne, amman kamar bazata kirkiro aman karya ba”
     Afili kuwa sosa kai yayi, tare da fadin kinci wani abu ne?
      Kauda kai Umma tayi domin ta kula Abdulmajeed ya daburce”
    Zuwa can tace Ummi ki tashi ku tafi gida ko”
     Daker ta iya mikewa tana dafa bango, ganin Abdulmajeed kuya ta kamasa ya rasa abin yi, yasa Umma da kanta ta rakasu mota”
     Suna hawa titi Abdulmajeed ya juya ya kalli Ummi, zuwa can ya mika hannu ya taba jikinta tare da fadin”
    Wannan ciwon na gaske ne?, ko kuma lanbon da kika saba ne?, koda yake bari muje gidan Momy, inbincike ki, idan ma dan kinki gayawa Umma matsalar ki ne, ni zan gayawa Momy…….
    Mmn Yazeed

🔥 🔥🔥🔥🔥🔥
KOWANNE BAKIN WUTA
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    ( da nashi hayakin)
💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by
    Fadeela Lamido
​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​
    Wattpad @fadeelalamido

                     65 – 66
*Afwan Yan uwa Kun jini shiru kwana biyu Kun San jiki da jini.ina yaba muku masoyana abin gudun mawar da kuke bani ngd* 😘😘😘😘

Juyowa tayi ta kalle sa, sannan ta cire hannun sa daga jikinta ta nufa toilet”

     Jimawa kadan ta fito da alama bakinta ta dauraye sannan ta koma gadon tana kokarin kwanciya”+

   Kirki kwanta jiki karasa abincin ki”

    Kwanciya tayi tare da fadin”

   Nakoshi”
    Hmmm matsoraciya karki karamin karyan ciwo, kingama guje gujen kuma kin koma lambo?

       ‘Dan turo baki tayi batare da tace komai ba”

    Dan haka Abdulmajeed  yace”

    Maida bakin ki, ni babu abin da zan miki, amman ya zama dole ki fadawa Umma dan ta nema miki magani”

      Yaya nifa bazan iya fada ba gaskiya, kuma ni lafiyata lau”

   Hmmm ai ko dole ki fada, dan bazan iya zama haka ba, kuma ai cikin dibara zaki fada, ba gatso tsoba”

     Kasa tayi da murya sannan tace”

     Allah yaya bazan iyaba”

     Shiru ya mata har aka kwashi tsayon wasu lukaci, besaka ce mata kala ba, amman zuciyan shi cike yake da zullumi”

    Ahaka suka kwashe tsayon sati biyu yana hakuri da Ummi, yama rasa ta yaya zai billowa abun”

       Tuni anty Salma ta koma, bayan ta kara basu shawarwari”

    Ummi kuwa awannan lukacin tayi kyau tayi kiba na ban mamaki, amman Abdulmajeed yana nan yadda yake, duk da cewa yana samun kulawa ta bangaren abinci da sauran su”

 
           ** ** ***
Yau Abdulmajeed ya tashi da damuwan halin Ummi, bayan sun gama yin breakfast yace”

     Dauko gyalen ki in sauke ki gidan Umma”

   Cikin dauki ta mike domin tunda aka akai auren su bata taba zuwaba, hakama gidan momy zuwan da tayi bana dadi bane”

    Koda suka dauki hanya Abdulmajeed be kallon inda take, dan haka Ummi ta kalleshi tace”

    Yaya nayi maka wani abu ne? Sai naga kaman kana fushi”

   Juyowa yayi ya kalleta ba fushi nakeba”

    Hmmm toh shike nan, bata sake cewa komai ba har suka isa”

   Tare suka sakko sannan suka nufi cikin gidan dayake safiya ne Abba nanan”

    Da Sallama suka shiga falon, Abba da Umma ne suka amsa, sosai sukaji dadin ganin su”

    Ummi jikin Umma ta zauna cikin fara’a da nuna farin ciki”

    Yayin da Abdulmajeed ya zube akasa agaban Abba sunkuyar dakai yayi sannan ya shiga gaida su”

   Bayan sun gama gaisawa Abba yace tashi ka hau kujera mana Abdulmajeed, kaida gidan ku”

   Cikin fara’a yace”

STORY CONTINUES BELOW

  Nan ma ya isa Abba, hakanan yaji yau yana jin nauyin su, dan haka bazai iya hawa kujera ba”

    Abba ne ya juya ya kalli Ummi sannan yace”

   Yanaga ke kinyi kyau Abdulmajeed kuwa yananan yadda yake, anya kuwa baki cutar sa?

   Dan Murmushi kawai Ummi tayi tare da sunkuyar dakai”

    Abban ne ya sake kallon Abdulmajeed yace”

    Toh badai wata matsala ko?

    Ba komai Abba, daman zan tafi Office ne, shine nace barin ajeta anan”

   Toh yayi kyau Allah ya muku Albarka”

   Har Abdulmajeed yayi sallama zai fita ya tuna bega Ahmeed ba dan haka yadan juyo yana fadin”

    Umma banga Ahmeed ba?

   Cikin fara’a Umma tace Ahmeed be tashiba yanata bacci”

    Ok toh saina dawo”

   Dadi sosai Ummi taji, jin ya tambayi Ahmeed, har saida taji kwallah ta cika mata ido”

    Fita yayi yana jiran Ummi amman shiru shiru bata fito ba, gashi yabar awayar shi cikin mota”

       Ya kusan minti goma atsaye, acen ko Umma tayi tayi tabiyo bayan Abdulmajeed amman sai tace ai sunyi sallama”

   Suna cikin haka suji shi cikin daga murya yace”

      Zainab

    Cikin sauri ta amsa sannan ta fito”

  Umma ko fadin take ato bakijin mgn ne, nace ki bishi kince ke kunyi sallama”

    Ficewa Ummi tayi, ta  sameshi tsaye agaban falon, hannunta ya roko sannan yace”

  Idan na taso zanzo na dauke ki muje gidan momy, kafin na dawo ki fadawa Umma matsalar ki”

      😳 Yaya?, nifa gaskiya bazan iya ba”

   Zaki iya Ummi, haka kike son naita zama da wahala”
Yaya toh kai kazo muje ka fada mata, ni wlh bansan ta yaya zan fad’a ba”

     Zainab ki daure koma ta yayane ki fada”

    Shiru tayi, zuwa can tace, toh shikenan naji zan fada”

     Harta juya Abdulmajeed yace me zakice mata”

     Toh ba dai kace infada mataba, kaje abin ka”

    Ke! tambayan ki nayi kibani amsa”

     Shiru tayi kamar Bazatayi mgn ba, zuwa can tace”

    Cewa zanyi, ka ce anema min magani wai bani da lfy”

      Kara daure fuska yayi, sannan yace”

   Karki sake ki kira Sunana aciki, ki bakisan baki da Lafiyan bane? Karma ki nuna mata nasan da zancen”

    Tabd’ijam yaya to bakai ka fadaba?

    Tafiya yafara cikin fashi yake fadin wawiyar yariya kawai, wlh karki sake ki kira Sunana, so kike ace min bani da kunya?

     Saida taga fitanshi gidan sannan ta koma ciki, cike da haushi”

  
Yana isa Office dinsa ya samu Nafisa agurin”

   Kallonta yayi akaikaice sannan ya wuceta ya shige ciki”

   Yana kokarin zama ta shigo ta zauna”

    Cikin ido ya kalleta sannan yace”

   Ke kuma daga ina?

STORY CONTINUES BELOW

    Sun kuyar dakai tayi sannan ta shiga gaida shi”

    Cikin daure fuska ya amsa, sannan ya jawo wasu takardu ya fara rubutu akan su”

     Gagowa Nafisa tayi ta kalle shi sannan tace”

   Doctor nazo ne ina son zamuyi mgn”

    Hankalin shi akan rubutun shi yace”

    Inajin ki”

   Shiru tayi zuwa can tace”

    Daman nagane kwana biyu kamin shiru, kuma ka daina kulani, ko kirana ma awaya ka daina, karka manta fan kamin alkawarin zaka aureni”

    Batare da ya dagoba yace”

    Eh ada na miki alkawari, amman ayanzun babu wannan zancen, dan iyayena sun hanani, kuma kisan bazan bijire musu ba”

    Hawaye ta matso tare da fadin kar kamin haka Oga, kaikace zaka aureni shiyasa ma harna Bar maka kaina kai yadda kaga dama dani,😭 dan Allah kamin adalci, ka tausaya min”

    Sosai jikin shi yai sanyi, dan haka ya dago ya kalleta, cikin nuna damuwa yace”

    Nafisa ni kaina naso na aure ki, amman babu yadda zanyi”

    Kuka Nafisa take sosai harda shashshaka, dan haka hankalin Abdulmajeed ya kara tashi, mikewa yayi cikin tashin hankali, binta yayi da kallo, acikin zuciyan shi yace”

    Yanzun meye anfanin irin wannan abun?, yaya zanyi da ita?, hakika idan nabarta haka na zalinceta, bansan wata irin kaddara bace ta debeni har idanuna suka rufe”

    Juyawa yayi ya sake kallon Nafisa, sannan yace, ya isa haka kitashi ki je gida zansan yadda zanyi

    Kasa tashi tayi, sabo da kuka dayaci karfinta, duk abin da take Abdulmajeed na binta da ido, sosai yakejin tausayinta, dan haka ya yanke shawaran zai shawo kan su Daddy domin su amince ya aureta, kodan kwanciyar hankalinta”

    Tashi muje nakaiki gida”

   Kaman daga sama taji zancen, dan haka ta mike tana layi tabi bayan shi”

      Har suka isa kofar gidan, babu wadda yai magana, bude motar tayi zata fita Abdulmajeed ya kira sunan ta”

     Ja tayi ta tsaya kanta sun kuye akasa, zuwa can yace”

    Ki kwantar da hankalin ki, kibar zubar da hawaye, zanyi iya bakin kokarina naga cewa na aureki”

     Hawaye ta share sannan tace”

      Nagode doctor, dan Allah karkaja lokaci, domin agida an matsamin da mgnr, amman kana ganin….

     Shiru tayi, ta kasa karasawa dan haka Abdulmajeed yace”

    Ina jinki?

     Cewa nayi amman Kana ganin Ummi zata amince kuwa???

   Shiru yayi, acikin zuciyar shi yace”

      Eh Ummi fah masiffafiyar yariya ce, afili kuwa cewa yayi”

   Karki damu da Ummi, kedai kawai kiyi addu’a’

   Shikenan doctor amman zan iya kiranka awaya”

   Cikin murmushi yace”

    Duk lokacin da kiga dama zaki iya kirana babu damuwa”

     Kudi ya dauko ya mika mata”

    Amman taki karba, karo na farko kenan daya bata kudi taki karba”

     Shigewa gida tayi tare da fadin nidai ka cikamin alkawari”
            ***

Lokacin da Abdulmajeed ya koma daukan Ummi kwace ya sameta afalo shame shame, dan haka yaji gaban sa ya fadi”

      Ita kadai ce afalon dan haka ya isa dafda ita ya zauna tare da fadin yaya dai?

    Kara dunkulewa tayi dan haka ya sake cewa”

     Ina mgn kinmin shiru?

Umma ce ta fito, cikin sauri Abdulmajeed ya mike tare da sosa kai, sannu da gida Umma?

   Yauwa Sannu Abdulmajeed, ka dawo?

    Can gefe ya zauna tare da fadin eh”

    Zama Umma tayi, sannan tace”

    Ai Ummi tunda ka tafi babu lafiya, wuni tayi amai”

    Acikin zuciyar shi yace amai kuma?, da dai wani ciwon ne, dana ce lanbo ne, amman kamar bazata kirkiro aman karya ba”

     Afili kuwa sosa kai yayi, tare da fadin kinci wani abu ne?

      Kauda kai Umma tayi domin ta kula Abdulmajeed ya daburce”

    Zuwa can tace Ummi ki tashi ku tafi gida ko”

     Daker ta iya mikewa tana dafa bango, ganin Abdulmajeed kuya ta kamasa ya rasa abin yi, yasa Umma da kanta ta rakasu mota”

     Suna hawa titi Abdulmajeed ya juya ya kalli Ummi, zuwa can ya mika hannu ya taba jikinta tare da fadin”

    Wannan ciwon na gaske ne?, ko kuma lanbon da kika saba ne?, koda yake bari muje gidan Momy, inbincike ki, idan ma dan kinki gayawa Umma matsalar ki ne, ni zan gayawa Momy…….

    Mmn Yazeed🔥 🔥🔥🔥

*KOWANNE BAKIN WUTA*

🔥🔥🔥🔥🔥

  _( da nashi hayakin)_

💨💨💨

               _Story & Written by_

    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*

*_Inafarincin sake kasancewa daku masoya wannan Novel nawa KOWANNE BAKIN WUTA (danashi hayakin) kuma inabaku hakuri akan jikirin danayi bankarasa sa ba, na dakata ne dalilin nauyin dana yi, Alhamdulillahi nasauka lafiya, wasu sun sani, wasu kuwa suna cigaba da kurafin naki karasawa, toh amun uzuri kunji dalilina, insha Allahu daka yau zan daura daga inda natsaya_*🌹🌹

2

             *65 – 67*

Kallon shi kawai Ummi tayi ta dauke kai, domin ita kadai tasan abin da takeji”

    Shima Abdulmajeed be sake kallon inda Ummi take ba, banda hura hanci babu abin da yake”

    Suna isa gidan Momy kuwa ya juyo ya kallita, tare da fadin”

    Ki saurareni dakyau kiji abin da zan fada miki, kinajina ko”

   Ganin inda ya tsareta da jajayen idanun shi yasa ta sunkuyar da kanta kasa, tare dayin raurau da ido tamkar zata zubar da kwallah”

     Shiko Abdulmajeed bayan ya gama kare mata kallo yace”

    Karki yadda mu fito gidan nan baki gayawa mommy matsalar da kike tattare da itaba, idan ko har kika bari muka fito wallahi zan baki mamaki”

   Dagowa Ummi tayi ta kalleshi, tare da rasa abin da zata cemai,  cikin sauri ta fice ta shege gidan”

    Bayanta yabi da kallo sannan ya sakko yabi bayanta”

    Afalo ya same su ita da Mommy sai dai Ummi na ganin shi tai sauri ta nufi dakin ‘yan biyu”

    Zama yayi bayan sun gaisa da Mommy be sake cewa komai ba illah ido daya zubawa hanyar da Ummi tabi”

     Ya dade yana kallon hanyar, ga dukkan alama besan yanayi ba”

    Wai lafiya kuwa? Mommy ta wurgo mai tambayan”

   Cikin inda inda yace”

    Am daman zamu wuce ne”

    Toh ai gidan ba bakon ka ne sai kaje ka kirata”

    Mikewa yayi ya nufi dakin yayin da Mommy tabishi da kallo”

      Can tsakiyar gado ya hangota, ta nannan nade, da alama rawan sanyi take yi, hakan ya tabbatar mishi da ciwon na gaskiya ne, bakin gadon yaje ya tsaya, idanu ya zuba mata, ganin zuciyar shi na neman karaya yasa ya dauke idanun shi, domin matakin da yake shiri dauka shine kadai zaisa Ummi tayi abin da yake bukata”

    Dan haka cikin kausasarsiyar murya yace”

    Ke tashi mutafi”

    Duk da cewa tana jinshi kara dunkulewa tayi guri guda, domi tafarajin haushin halin ko inkula daya nuna akan ciwanta”

     Yayin da wata zuwaciyar ke ingizata da aidama bake yake so ba, yana da wacce yake so”

   Muryanshi ya katseta badake nake magana ba?

    Kokarin saukowa ta fara ahakali cikin sauri ya kyauda idonshi beson ya nuna tausayawan shi akanta, koma menene insunje gida ya dubata”

    Ahankali ta fara tafiya, Abdulmajeed nabinta abaya, har suka isa falo adaidai lokacin da momy ke fitowa”

    Dauke idonta tayi daga garesu sannan ta zauna”

   Shiko Abdulmajeed bakin shi yakai kunnen Ummi, karki yadda mukoma gida baki fadin mata ba, cikin sauri ya nufa hanyar fita tare da fadin”

STORY CONTINUES BELOW

    Momi saida safe”

    Allah ya tashemu Lafiya, juyawa tayi taga Ummi tsaye kamar an dasata dan haka ta daga murya ta kira Abdulmajeed”

       Bayan ya dawo ya tsaya tace”

    Batare zaku tafi bane naga kafice ka barta?

   Rasa abin cewa yayi dan haka ya daga hannun shi ya shafo keyarsa tare da fadin”

    Eh……..am……daman tun safe ta matsa na kawota, wai tanason yin  magana dake”

     Juyawa tayi ta kalli Ummi cikin sauri ya fice”

    Itako Ummi sunkuyar da kanta tayi, daman Abdulmajeed ya iya karya ko kunyar idona bayaji yamin kazafi agabana”

    Tana cikin wannan tunanin taji Momy ta riko hannunta, bakin kujera ta zaunar da ita, sannan itama ta zauna tare da fadin”

  Ummi ina sauraron ki kunada matsala ne?

   in hankalinta sunyi dubu sun tashi, gaskiya Abdulmajeed bashi da kirki”

   Ummi inajin ki kinyi shiru kuma, ko kinajin nauyina ne?

    Kwallah ce ta cika mata ido, kokarin maida hawayen take taji Momy ta sake cewa”

  Ummi ki daukeni tamkar uwar da ta haifeki ke da Abdulmajid duk daya ne agurina kinji ko”

   Kusan minti biyar Ummi ta kasa magana dan haka Momy tasake cewa”

    Sai ki tashi kutafi, yana jiranki, tunda bazaki yi magana ba, amman zan gayawa Umman ki ai nasan ita bazaki ki gaya mataba”

   Cikin sauri tace”

    Momy nifa babu komai ba abin da ke damuna”

   Amman kika matsa masa ya kawoki?

    Wlh karya yake min, ni bance mishi haka ba”

    Dan murmushi Momy tayi sannan tace”

   Ai shikenan, nasan dai koma meke damun ki be wuce akan halin Yayan ki ba, ki kara hakuri kuma shima zan mai fada, tashi kuje yana jiranki”

    Abdulmajeed dake bakin kofa labe yace kashhhhh😬

     Yariyar nan saida ta wargaza min shirina, tsaki yaja sannan ya isa motar ya zauna”

    Be jima da zama ba Ummi ta fito, ido ya bita dashi, gashi bazai iya fushi da ita ba, sabo da halin da take ciki”

     Bayan tashiga ta zauna ya tada motar satan kallonta yai tayi zuwa can yace”

    Meke damun ki??

   Kara kauda idonta tayi daga gareshi tare da zunbura baki”

     Ina magana kin min shiru, meye ke miki ciwo?

    Batare da ta kalleshi ba tace Zazzabi”

Hannu ya mika ya taba jikinta, tare da fadin sannu Allah ya sauwake

    Juyar da kanta tayi can gefe, acikin zuciyarta take fadin daman nasan zama da Yaya Abdulmajeed bawani dadi zaiyi ba, kanshi kawai ya sani, sai yanzun ne zai tambaye ni meke damuna dan yana tunanin nagawa Momy sakon shi, yanzun da zan ga yamai ban fadaba masifa zaimin meye amfanin auren wadda be damu dakai ba? gaskiya ni ancuceni wlh, hawaye ta share tare da jan tsaki”

    Daidai lokacin da suka isa gida yace”

     Zainab wai me aka miki ne yau?

     Tana kokarin sauka take fadin bakomai”

     Sauka yayi yabi bayanta ta rigashi shiga dan haka be sameta afalo ba”

     Dakin shi ya nufa be  juma ba ya fito hannun shi dauke da magani ya nufa dakin Ummi”

STORY CONTINUES BELOW

    Kan gado ya sameta ta kudundune  kusa da ita ya zauna Zainab tashi kisha magani”

   shiru tamai dan haka ransa ya fara baci cikin fada yace”

    Ke wai ina wasa dake ne dazan dinga mana kina banza dani”

    Kokarin Sakkowa ta fara fuskarta murtuk har Mukhtar yabar duniya bata tabajin haushin shi kamar yadda takejin haushi Yaya Abdulmajeed yau ba”

    Watoh Mukhtar so yake mata domin Allah badan wani abuba, shiyasa ma ya iya hakuri dani iya rayuwar sa betaba nuna natakura masaba, amman wannan dan fadin ran zaice wani wai ban da lfy”

    Tana cikin wannan tunanin taji yasa hannunshi ya bude idonta zuwa can ya sake sannan ya mika mata maganin tare da ruwa”

     Bayan tasha ya mike ya fice, gidan ya bari gaba daya, be dawoba sai karfe 9:30pm”

   Itako Ummi tunda ya fita kuka take, dukda Zazzabin ya sauka amman haushin Abdulmajeed ya hanata sukuni, lokacin baban Ahmad yana darai idan bani da lfy daker yake iya matsawa daga kusa dani beson yabarni nikadai amman shi jiba har yanxun be shigoba haushine ya kamata sosai, dan haka taketa zubar da hawaye babu kyaukyautawa”

   Acikin wannan halin ya same ta tunkafin ya shiga dakin yake jiyo sheshshekan kukanta

Dan haka ya shiga da sauri, Ummi Lafiya?, meya faru, kusa da ita ya zauna tare da mika hannu ya taba jikinta, Zainab jikin ne?

     Kaita girgiza, Ahankali ta shiga share hawaye”

   Shiko Abdulmajeed cikin mamaki ya zuba mata ido, Ummi toh meya saki kuka?

   Kanta ta sunkuyar kasa sannan ta sake share hawaye”

   Ina jinki ki?

   Kanta akasa tace”

  “Ni banjin dadin zaman gidan ne”

    Bangane bakajin dadin zaman gidan ba, meya kawo wannan maganar kuma?, ko namiki wanni abu ne?

    Shiru tayi har yanzun kanta nakasa”

    Shima Abdulmajeed bayan yagama kare mata kallo yace”

   Ina jinki”

   Dagowa tayi ta kalleshi sannan ta maida kanta kasa, cikin kasa kasa da murya tace”

    Aini Baban Ahmeed ba haka yake min ba, idan bani da lafiya baya tafiya ya barni ni kadai”

   Cikin sauri Abdulmajeed ya mike idonshi rufe tare da dunkule hannunsa yace”

      me kika ce?

        Batare da ta kula da halin da yake cikiba tace”

    Ni Mukhtar ba haka yake min ba idan bani da Lafiya”

   Hannu ya daga da niyyar zai kai mata mari, adaidai lokacin da ta maida idonta kansa”

    Cikin sauri ta rufe idonta, tana jiran jin saukan marin, jin karan kofar ya tabbatar mata yabar dakin dan haka ta bude idonta, tare da maida numfashi, domin yadda taga ya zuciya batai tunanin zai bantaba”

     Kujeran dake gefen gadonta ta nufa, bayan ta zauna ta zuba tagumi” waishi da dukana zai yi?, toh meyasa ya fasa?, tsaki taja afili tace, yazama dole innemi hanyar da zan rabu da mutumin nan, domin idan ina tare dashi baxan taba farin ciki ba”

    Haka ta shirya kwaciya bacci ta kwanta, zuciya cike da tunani, dan haka batai baccin kirkiba”

    Shima Abdulmajeed kasa bacci yayi bakomai ke batamai raiba sai idan ya tuna har yanzun Ummi takasa mantawa da *Uban danta*

STORY CONTINUES BELOW

    Idonshi jawur sai zagaye yake adakin babu alamar bacci a idonshi, baya jin komai cikin kunnensa sai sautin muryan Ummi, alokacin da take fadin”

   _Ni Baban Ahmeed bahaka yake min ba, idan bani da Lafiya baya tafiya ya barni ni kadai_”

   Kanshi ya dafe, domin ji yake tamkar zai rabe gida biyu, kan gado ya koma ya zauna tare dasaka hannusa cikin aljihun sa ya fito da kwalin sigari, batare da fata lokaciba ya shiga kunnawa yana sha babu kyaukyautawa💀

   

     Koda gari ya waye bayan yagama shiryawa bebi tagan Ummi ba ya fice abinsa”

     Ummi najin fitansa tafito dan daman tuni take son fitowa amman batason ahaduwanta da Yaya Abdulmajeed dan hakama ta rufe dakin ta”

    Ganin be neme taba ta tabbatar shima fushi yake da ita”

    Duk da batajin dadin jikinta haka ta shiga gyaran gida, bayan ta gama gyara ko ina ta nufi dakin Abdulmajeed”

   Tura kofar ta keda wuya, warin Sigari ya daki hancin ta, cikin sauri ta toshe hancinta, sannan ta karasa ciki”

    Guntayen ta tagani barkatai, jinta kawai tayi ta zube bisa kafafunta”

    Wato Abdulmajeed kwana yayi shan sigari, wannan wacce irin rayuwa ce, niwai haka rayuwata zata kare?

     Waccen karon daga karshe auren Mukhtar nasha wuya, har ana ganin naki Abdulmajeed, toh ai shima gashi ba mutumin kirki bane, me ake da mashayi tunda yasha wannan agida, Allah kadai yasan wadda zai sha awaje, wlh bazan cigaba da zama dashiba

    Kitchen ta koma cikin sauri ta dauko leda ta dawo, guntun sigarin ta fara tattara wa ta zuba cikin leda

Sannan ta koma nata dakin”

   Misalin 5:00pm Abdulmajeed yawo gida har yanzun da haushin Ummi azuciyar sa dan haka be nemeta ba”

    Bayan yayi wanka ya sauya kaya Wata zuciyar ke umartan sa da yaje ya dubata, kodan saboda ciwon dake damunta, tsaki yaja sannnan ya nufin dakin ummi fuskarsa murtuk babu alaman rahama”

   Ahankali ya tura kofar, idon shi akan gadonta ganin bata agurin, yasa ya tsaya atsakiyar dakin xuwa can ya taka zuwa kofan  toilet din, ahankali yace”

      Zainab, shirun da yaji yasa ya tura kofar ahankali tare da kara Kiran sunanta”

   Cikin sauri ya fito domin beji alaman mutum ba”

    Cikin sauri ya fito adakin yana tafe yana kiran sunanta har ya isa bakin kitchen”

   Bayan ya fito daga kitchen tsaye yayi yana faman share zufa dabesan dalilin karyowan Sa ba”

    Wayarta ya shiga kira Amman ba’a dagawa, dan haka ya shiga zullumin inda ta shiga”

    Gani yayi tsayiwan bazai mai ba dan haka ya koma daki ya dauko key din motar sa ya fice”

    Rasa ina zai nufa yayi, gidan Mommy ko gidan umma besan ina ta nufa ba”

   Addu’a yaitayi Allah yasa gidan Mommy taje, koma menene candin zaifi”

   Koda ya isa gidan tsit yaji dan haka zuciyar shi ta fara karaya dakin Mommy ya nufa da sauri”

  Babu kowa aciki dan haka ya saki kofar ya fara kira Mommy”

   Daga kitchen yajiyo muryan Mommy dan haka ya karasa da sauri”

   Suna hada ido yace”

    Zainab bata zonan bane??

    Cikin rashin fahimta tace”

    Bata zoba yaya akayi?

    Yamutsa fuska yayi tare da fadin toh ina taje??

   Kai zan tambaya ina taje

      Kaida kuke gida daya baka sani ba bare ni”

    Mommy ni nadawo ne kawai naga gidan bakowa, kuma bamuyi zataje ko inaba”

    Shiru Mommy tayi tana kare masa kallo, zuwa can tace”

    Kunyi rigama ne?

    Jim yayi zuwa can yace, a’a ina zuwa, juyawa yayi ya fice da saurin shi”

     Girgiza kai Mommy tayi, tare da fadin Allah ya kyauta”

     Abdulmajeed kuwa gidan su Ummi ya nufa bayan sun gaisa da Umma ya zauna jigum, zuwa can yace”

    Ummi ta wuce ne??

   Cikin mamaki tace”

   Ai Ummi batazo gidan nan ba, kunyi zatazo ne?

   Eh a’a daman nakaita wajen Mommy ne tace min daga can zata yo nan, ko ta cenza shawara ne”

  Murmushi Umma tayi tare da fadin toh kila”

    Mikewa yayi yaiwa Umma sallama yabar gidan”

    Gida ya sake komawa, babu inda be duba ba dan haka ya shiga damuwa banda tsaki babu abun da yake ja, gashi yamma tayi sosai ana dafda kiran mangariba”

     *BAKIN YANKI*

Ummyo nace ki kwantar da hankalin ki, insha Allahu Ahmed zaizo da kafar shi, Wata rana zai nememu, Saminu ke fadin haka lokacin da yake rike da hannun Ummayo yana lallashinta”

  Cikin kuka yake mata fifita, sosai hankalin sa yake tashe, suna cikin haka akayi sallama adaki”

    Azabure Ummayo tafara kokari tashi tare da fadin”

   Yauwa Amadu na sannu da zuwa, kokarin mika hannu take ta kamu matar da tashigo”

   Hawaye saminu ya share tare da fadin”

  Ummayo ba Amadu bane, tabawa ce tazo gaidaki”

   Sabon kuka Ummayo tasa domin ahalin yanzun Ummayo ta rikice duk muryan da taji saitace Amadu ne, sai anyi da gaske take fahimta”

   Kusa da Ummayo tabawa ta zauna, tana kukarin kwantar mata da hankali wata yariya ce tashigo aguje wacce bazata wuce shekara 12 ba”

   Gudune take na ban mamaki tare da haki, tabawa ce ta miki ta rike yariyar tare da girgizata ke lafiya kuwa”

   Cikin zare ido take nuna mata kofa, sakin yariyar tabawa tayi ta nufi fita yayin da yariyar ta shige karkashin gadon Ummayo”

Shiko Saminu yana rike da Ummyo tare da zubawa kofa idanu yana jiran dawowan tabawa”

   Zuwa can saiga tabawa aguje tana rada ihu dare da numfarfashi, tana shigowa ta maida kofar ta rufe……….

  

       *Mmn Yaxeed*🔥 🔥🔥🔥

*KOWANNE BAKIN WUTA*

🔥🔥🔥🔥🔥

  _( da nashi hayakin)_

💨💨💨

               _Story & Written by_

    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*

            *68 to 69*

Sakin Ummayo Saminu yayi Tabawa wai lfy kuwa?

     Bakinta narawa ta nuna kofa tana fadin Muntari”

   Muntari? yayi me?

    Ya dawo”

  Ya dawo ina?

   Kofar take nunawa adaidai lokacin da aka fara buga kofar”

   Fitsari ne ya fara zubuwa tabawa yayin da Cikin saminu ya murda”

     Ummayo ce ta taho tana kokarin budewa, yayin daga can waje ake cigaba da bugun kofar”

     Ganin Ummayo na kokarin budewa yasa yaminu ya rike Ummayo sannan ya karasa bakin kofar yace”

    Waye??

   Nine

Jim Saminu yayi yanason ya tattace muryan dan haka ya sake cewa waye?

    Nine ka bude kofar mana”

   Eh muryan tayi kama data muntari saidai ya jin shine din ahankali ya sake cewa kaine Wa?

    Shiru yaji zuwa can yaji ance wai waye ne, Ummayo bata nan ne?

   Jin haka ya tabbatarwa kansa ba Muntari bane dan haka yacire sakatar ahankali ya bude kofar

   *JAFARU*

Ummayo ta ambata tare da rungume mutumin”

    Shima Saminu jin Ummayo ta ambaci sunan Jafaru yasashi tonawa da yayan su Jafaru da yabar gari tun bashi da cikkaken wayo”

     Tabbas kamar su da Muktar tabaci saidai Jafaru yafi Muktar baki kuma Jafaru fuskar shi akwai tabbai na yanka alamar anyi rashin ji”

    Shima rungume jafaru yayi, sun dade suna koke koke yayin da tabawa ta zama yar kallo”

    Bayan sun sarara daki Ummayo ta Jawo Jafaru har yanzon taki sakin sa”

    Kallonshi kawai take zuwa can tace Jafaru daga ina kake”

    Cikin wata irin murya yace”

    Kinaji KO Ummayo, ki basar da wannan zancen yanzun dai yaya kuke, ya kowa da kowa”

   Kowa Lafya Jafaru, saidai Muktar ya rasu tuntuni”

   Mikewa yayi cikin azama, nan danan ya fara tsiyayar da hawaye”

   Hakuri Hajiya ta shiga bashi tare da bashi labarin Muktar”

    Bayan ta gama faiyace mai komai ya fara share hawaye tare da fadin”

     Kinaji KO Ummayo ki kwantar da hankalin ki, bawani shegen dazai tabaki nabarshi, kin gane KO Ummayo, Ahmad zai dawo cikin kankanin lokaci, dama baki zubar da hawaye ba Ummayo, dama bakiyi kokaba, nake gaya miki KO bangon duniya suka kaishi sai sun kawo shi dan Uwar su”

      Sosai hankalin saminu ya tashi, cikin in ina yace”

     Ai Yaya ka kwantar da hankalin ka ma, indai jinin mune zai biyomu watarana”

     Jafaru ne ya kalleshi, banni dasu Saminu duk wani dan iska nine baban shi, kin gane KO Ummayo kibani sati biyu nake nake gaya miki, komai zaizama tarihi”

STORY CONTINUES BELOW

     Jikin Saminu na rawa yabar dakin yadda yake ganin Jafaru babu abun da bazai iyaba, ya zama lallai ya nemin Abdulmajid akan mgnr”

   Abdulmajeed kuwa ya kasa zaune ya kasa tsaye, Nan yaji wayarsa na kara yana dubawa yaga nomber Hajiya, sai yanzun tunani ya duba gidan hajiya yazomai, cikin gudu gudu ya nufi gidan”

    Cikin gudu gudu ya isa cikin gidan, Sallama yayi sannan ya shiga dakin hajiya”

    Hajiya dake zaune tsakar dakinta ta dago ta dubeshi sannan ta juya ta kalli kujeran da Ummi ke kwance”

    Juyawa ta sakeyi takalli Abdulmajeed tare da daura dan yatsanta kan lebenta alaman yai shiru”

   Murmushi yayi sannan ya karaso ya zauna gaban hajiya adaidai lokacin da hajiya ta mike tana leka fuskan Ummi”

    Duk abin da Hajiya ke Ummi na kallonta dan haka ta mike azuciye ta shige daki”

     Komawa hajiya tayi ta zauna sannan ta zubawa Abdulmajeed idanu”

   Kai kuwa kana ina naita kira baka dagaba, gawannan rigimammiyar yariyar tanason ta tayar da tsiya”

    Ajiyan zuciya yayi, bana kusa ne hajiya, me tace miki??

    Ai Bawan Allah nan ita ta tsareni ne insa araba aure”

    Wanne auren za’araba?, Abdulmajeed yai tambayan lokacin da ya tsare hajiya da kallo”

   Naku mana, tace ita araba bata yi, kuma agaskiya bawan Allah idan bera na sata daddawa ma na da wari”

   Hannu ya dagawa Hajiya alamar ta dakata,  tace miki na mata wani abu ne”

  Meye ma be faruba, Bawan Allah, kaida ‘Yar uwanka kuma ka kamata da duka sabo da Allah, wlh karka bari Baban ka yaji wannan labarin”

   Cikin tsananin mamaki yace”

   Hajiya yanzun ke kin yadda na daketa ne?,  shiryawa tayi dan tana da wani nufi azuciyarta”

   Hmmm, kana nufin har gutayen sigarin da ta kawo shima sharri Tamaka??

     Guntun sigari kuma Hajiya??, kina nufin dashi tazo gidan nan??

Dashi tazo bawan Allah, yazun kai sabo da Allah abun da baka yi da yarinta ba shine zaka tsiro dashi yanzun da girma yazo ma, kuka Hajiya ta saka wiwi”

    Hajiya duba, kinaji, wlh duk halin dana shiga Zainab ce ta sani aciki, wlh hajiya kasa sarrafa kaina nake idan ta bata min rai, ita take sani acikin damuwa”

     Haba, bawan Allah kana nufin tabar ce zatama maganin damuwa?, inbanda batan basira ina taba zatai maganin damuwa, idan kana cikin damuwa kakai kukanka wajen Allah, amman ka zauna kana shirmen banza da wofi”

      Share zuba yayi shikenan hajiya zan gyara, yanzun turo min ita mutafi”

  A,a sam kaje can Ku karata, bani cewa kala dan bani nakawota ba kafarta takawo ta”

      Sanyi jikin Abdulmajeed yayi sosai, yanabin hajiya da kallo yace”

     Hajiya nine fah”

      Mikewa tayi tana kokarin ficewa daga dakin take fadin eh kai din”

    Binta da kallo yayi bayan ta kule ya nufa cikin dakin hajiya”

       Yana daf da shiga dakin kiran Mommy ya shigo wayar sa cikin sauri ya dauka

     Kasami Ummin?, kabarni cikin zullumi”

    Eh gidan jaya tazo, yanzun haka ma ina gidan”

    Toh idan ka daukota ka kawo min ita”

     Dahaka sukayi sallama ya nufi cikin dakin”

STORY CONTINUES BELOW

    Samunta yayi kamar me bacci wadda yake da tabbacin baccin karya ne, ahankali yace”

   Tashi muje gida Zainab karki batamin lokaci”

    Kamar dai yana magana da dutse dan haka yaciba da cewa, badake nake magana ba, KO sai kin wahalar dani kamar yadda kika saba koda yaushe, tun kina ‘yar tatsitsiyarki kike wahalar dani, kin takurawa rayuwata kin hanani jin dadi, yau ki dauko wancen rigiban gobe ki daukko wancen”

    Sosai kalaman shi suka bawa Ummi haushi, acikin zuciyarta tace kaji wai tun inna yarta tsitsiyata nake wahalar dashi, alhalin lokacin da nake primary school da mun hada ido yake zare min idanun shi, kuma harna gama secondary gaisuwa kadai ke hada mu, ko cikakiyar amssawa bayayi dayace Lafiya besake cewa komai, amman dan kuturon gulma zaice wani  wai ya wahala dani”

    Tana tsaka da wannan tunanin taji ya sake cewa kitashi muje Mommy nakiran ki”

     Barkon taja ta rufe fuskanta sannan tace”

   Bazani ba, kuma ka lissafa wahalar ka dasha dani  tanawa ce nabiya ka”

    Jimm yayi domin shi bemasan lokacin da wannan zancen ya fito ba, kallonta yayi kinga Ummi taso dare fah yayi”

    Aina gayama bazan koma ba, kuma wlh wannan karon koza’a kasheni bazan koma ba”

     Ni kike gayawa wannan maganar?, ina zuwa, gayamin mena miki?

      

      Oho kaika sani”

     Wani haushine ga kamashi, wai yaya akayi Zainab ta rainani haka ne, cikin huci yace, ke, ki shiga hankalin ki niba sa’anki bane ki daina gayamin abun da kiga dama”

Kargiga Ina barin Ki kice zaki min iskan cin banza, wacece ke?, wallahi sai in tattakaki”

      Cikin kunkunai tace”

     Ai daman bance ni wata bace, nasan niba komai bace agurin ka, shiyasa ma nace ka fadi wahalar dakayi na biya ka”

     Hannuwan shi ya zoba cikin aljihun wandon sa, sannan yace”

     Himm zaki sani, juyawa yayi cikin sauri ya fice dakin”

      Tsakar gida ya samu hajiya, cikin rashin kuzari yace”

     Hajiya Zan wuce, amman dan Allah Ki amshe abun nan ahannun yariyar nan, karki batta dashi”

     Kai meya hana ka amsa? kaga bawan Allah, nacire hannuna acikin wannan maganar, itama takwarar idan ta isheni koranta Zanyi”

     Haba Haji kema zafin zaki hada min?

    Toh ya bazan hadama ba, aini nadawo daga rakiyar ka kuma, banga laifin takwaraba Sam, zama da mashayi ai sai dole”

   Haji nine mashayin??

   Eh kai fah, yama zafi ne?

    Girgiza kai kawai yayi ya fice, cikin tsananin bacin rai”

   Koda ya isa gidan Mommy sai huci yake

   Kallo daya tamai ta dauke idonta, zuwa cen tace”

        Ina Ummin?

  Taki biyoni”

   Akan wani dalilin zataki biyo ka?, kace min bakuyi rigima ba”

   Mommy ni bansan abin da namata ba, kwata kwata taki bari hankalina ya kwanta, tunda akayi auren nan take tsuro da tsurfa iri iri, daga wancen sai wannan, ‘yar karamar yariya taringa juyani?, dan taga ina kyaleta, badama wani abu yadan faru saita dinga kiramin sunan wannan wawa dolon”

    Zaro ido Mommy tayi, Wa kake kira haka?, Abdulmajeed, da wadda baya duniya kake kishi haka?

     Hannuwa ta fara tafawa tare da sallati”

STORY CONTINUES BELOW

    Sanyi jikin shi yayi ganin Mommy ta kafeshi da ido yace”

   Niba kishi nake dashiba amman ai bedace ta dinga kiramin sunan wani kato agidana ba, idan har yanzun sonshi take ai saita……

   Mommy ce ta katseshi da fadin kai bason ji, ya isheni haka tashi kabani waje, mutum sai zafin kan tsiya”

    Shiru yayi tare da sunkuyar dakai, kusan minti 5 bece uffam ba sannan ya mike tare da fadin saida safe”

     Allah ya tashemu lafiya, ta fada tana bin bayan shi da kallo, d’a da mahaifi sai Allah jitayi ya bata tausayi, tasan yana son Ummi duk da yana boyewa, amman kalaman shi sunyi tsauri, idan yana son ya goge Muktar  azuciyan Ummi ya fito ya nuna mata so, dan wannan nuku nukun bazaimai ba”

      Koda Abdulmaneed ya koma gida, kasa runtsawa yayi, dan haka washegari karfe 6:34am agidan Hajiya tamai”

   Beji motsen kowa ba, hakan ya tabbatar mai bacci sukeyi, kan duguwar kujera ya kwanta, ba jimawa wani nannauyan bacci ya dauke shi”

      Misalin 9:18am Hajiya tafito falon, ganin Abdulmjeed kwance abun ya bata mamaki, wani mugun tausayin shi taji ya kamata”

      Juyawa tayi zuwa daki, bargon da Ummi ta rufa dashi ta jawo, cikin sauri Ummi ta rike, Hajiya ban tashi ba fah, kuma sanyi nakeji”

     Tana kokarin fita tace, A’a tashi maza rana tayi”

    Sakkowa tayi badan ranta yaso ba, tana fitowa falon ta hango mutum nannade cikin bargo”

   Wanene wannan, nasan dai wannan ba hajiya bace, domin tsayin nan bana mace bane sai dai namiji, kuma sanda natashi sallar asuba babu kowa agurin”

    Bargon ta kalla taga ai wanda Hajiya ta cire ajikinta ne yanzun, kitchen ta nufa suna hada ido Ummi tace”

     Yauwa takwara taho ki taimaka min”

     Itako fadi take Hajiya waye wancen kwace falo??

    Murmushi Hajiya tayi sannan tace”

   Baki ganeshi bane, dan uwanki ne fah”

   Ya zanyi inganeshi bayan  yana rufe”

   Dariya Hajiya tayi ai nadauka idan kasan mutum sosai ko yaya yake zaka gane shi”

     A’a ni tunda nake bantaba ganin wadda yakai tsayin shi”

    Juyawa hajiya tayi tana fadin toh Allah ya kyauta miki kuwa”

   Juyawa Ummi tayi ta nufi tsakar gida, tana tura kofar taci karo da takalmin Abdulmajeed”

  Komawa tayi ta kalli gurin dayake kwance”

   Nan ta tabbatar wa kanta shine”

    Turbune fuska tayi sannan ta koma kitchen ranta ahade”

    Hajiya shine kika hanani kwanciya kika kuma kwace bargon dana rufa dashi kika bawa yaya, cewa fah kikayi rana tayi amman shi har kina bashi bargo”

    Ayya takwara ai shi kwana yayi be rutsaba, nan nafito na sameshi ya takure yana bacci, bemasan nasa mishi bargon ba”

    Wani sabon haushi ne ya kama Ummi nan danan hawaye ya fara zobo mata, acikin zuciyanta tace”

  Wai sai yaushi hajiya zata daina nuna tafi son abdulmajeed duk cikin jikokinta, mutum gotai gotai dashi ta wani dinga kula dashi kamar ta samu karamin yaro”

    Tahowa Hajiya tayi ta dafata Haba takwara, ki tausaya mishi mana, kinga ya  kasa bacci gidan sa saida ya biyoki inda kike, rabon da bawan Allah yai bacci gidan nan bazan iya tunawa ba, dan Allah ki huce haka  idan ya tashi kutafi gida”

STORY CONTINUES BELOW

    Hannun hajiya ta ture daga jikinta sannan ta share hawaye nifa hajiya bazan koma ba, koke fah jiya cewa kikayi bazan koma ba”

  Eh ai cemin kikayi ya dakeki, kuma yace min be dakeki ba”

     Cikin sauri Ummi ta kalli hajiya, to dan yace miki be dakeni ba saiki yadda ke kuma”

     Eh na yadda aishi bawan Allah baya karya be dakekiba, inda ya dakeki zai fada”

     Wani sabon haushi ne ya kamata dan haka ta fice tana zunburan baki”

    Bayan hajiya ta   gama aikinta ta fito, har yanxun bawan Allah bacci yake, Allah sarki hajiya ta fada afili, sannan ta wuce gurin Ummi”

     Zama tayi tana kallon Ummi daketa faman hada kayanta”

     Bayan tagama kare mata kallo tace”

    Ina zuwa kiketa hada kaya?

     Tafiya zanyi, daman tsautsayi ne ya kawoni, mantawa nayi abokin ki ne”

    Murmushi Hajiya tayi sannan tace”

     Toh ina zaki takwara?, bayan ga Mijin ki anan, ni abin da nake so dake, ki ringa hakuri, wannan laifin bekai ace an raba aure ba, ki kwantar da hankalin ki mijinki nason ki, yadda kika dauki abun ba haka bane,  duk wanda yaga abin da yayi yau, zai tabbatar miki yana sonki”

    Bawani nan kedai Hajiya kina tare masane, ai daman aminin ki ne, nima tsautsayi ne ya kawoni, ko jiya ma sai da yace wai ni wacece”

     Nagaya miki ki daina biyewa halin bawan Allah, wannan zancen banza ne yake yi, haka dabi,un sa suke duk abin da yake so be fada tun yana karamin Sa”

    Mikewa Ummi tayi tare da fadin naji duk abin da kikace amman ni ban son zama dame irin halin Sa, kuma nagadai auren ba dole bane, nace banso shi kika nace saida kika kullah, nazo nagaya miki halin shi, ni banjin dadin zama dashi, jiya da bakinki kikace bazan koma ba amman daga ganin shi kika canza magana”

     Hmmm takwara, rigimarki fah ta isheni, ni daman wannan tabar ce ta dagamin hankali, kuma yace min bashi yasha

Bako yayi abokin sa ne yazo kinga ba yadda zaiyi dashi”

    Caf bashi yashaba?, haka yace miki?,, ke kuma kika yadda, wallahi Hajiya shine yasha, so nawa inaganin shi yanasha”

     Subuhanallahi takwara kiji tsoron Allah”

   Kuka Ummi tasa domin ta tabbata hajiya ce kadai zata iya mata abun da take so, damarta ta karshe ko daddy”

     Tana cikin wannan halin taji hajiya tana fadin”

    Dan haka ki miko min abun da kika taho dashi nasa abola tunkan na saba miki”

    Cikin kuka sosai tace’ wlh bazan bayarba sai na nunawa su daddy”

    Kukan da take ya tada Abdulmajeed mikewa yayi ya nufu dakin”

    Abakin kofar ya tsaya ya rungume hannun sa akan kirjin sa ya zuba musu idanu”

     Kusan minti biyar yana tsaye sannan yace”

    Hajiya me aka mata haka ne?

    Gidanka ne bazata koma ba, wlh bansan yaryar nan bata da mutunciba sai yau, juyawa tayi ta kalli Ummi tace”

       Duk inda zaki kin dade bakijeba amman ki tabbatar kin fito da ledan nan inba hakaba na mangare ki, so kike ki hadasa da iyayen shi”

     Wlh bazan bayarba”

     Ni kike gayawa bazaki bayarba mikewa hajiya tayi tana kokarin isa gurin Ummi Abdulmajeed ne ya taho ya shiga tsakiya hajiya rabu da ita kawai kije ki zauna abunki”

      Kallon Ummi yayi yace”

    Zomuje nakaiki inda zaki”

     Kokarin fita take tana fadin banaso”

     Harta fice afalon yana kallonta tare da tunanin yadda zai bullowa abun”

     Kansa ya dafa, hajiya ce ta karaso da sauri gani ko bawan Allah, dafashi tayi ka kwantar da hankalin ka wannan auren babu me rabashi matsawar ina raye”

    Yana dafe dakai yace”

    Ni nayanke hukuncin zan Mata abun da take so, tuntuni take furta bata kyaunata gashi har yanzun bata bariba har yanzun, ni bansan dadin aure ba, nakai shekara 10 ina dawainiya da ita acikin zuciyata, nagaji hajiya Zan Mata abunda take so”

    Kul karka fara, domin itama ai tana kaunarka, kawai akwai abun da bataso ne dakai, kuma kaga maganar taban nan itama zata iya sawa taji batason zama dakai, abun yayi yawa bawan Allah, kuma acikin gidan ka dan Allah ka gyara halinka”

     Mikewa yayi yana fadin zan gyara hajiya, barin je sai anjima”

  

           ******

   Tunda Ummi ta fito layin su Hajiya take tsaye bakin titi bata samu abun hawa ba”

    Zuwa can ta waiga bayanta, wani mutumin tagani yana boye fuskan sa”

    Ta kula kamar ita yake boyewa, toh ko mahaukaci ne, jikin shi akwai alamar wahala da gani baya cikin jin dadi”

     Tafiya ta fara domin ta fara tsorata dashi”

     Gani tayi shima ya biyo hanyar cikin sauri ta waigo”

   Tsayawa yayi cak tare da juya bayansa”

    Cigaba tayi da tafiya gashi unguwar babu kowa sai motoci dake wucewa jefi jefi”

    Ta gefen ido take kallon bayanta, gani tayi yacigaba da biyo bayanta”

     Tsayawa tayi cak sannan ta juyo bayanta”

     Basarwa mutumin ya sake yi, sosai jikin Ummi ya soma rawa cikin sauri ta fara tsayar da motocin dake wucewa ganin basa tsayawa yasa Ummi ta kwasa aguje”

    Mutumin ma bayanta yabi da mugun gudu, yayin da Ummi takara gudunta tana matsanancin haki……

      *Mmn Yazeed*

🔥 🔥🔥🔥
*KOWANNE BAKIN WUTA*
🔥🔥🔥🔥🔥
  _( da nashi hayakin)_
💨💨💨

               _Story & Written by_
    *Fadeela Lamido*
*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*

           *70 to 72*

Abdulmajeed tafe cikin motar sa, sake sake kawai yake bayajin zai iya rabuwa da Ummi”

    Wata zuciyar ce tace ka mata abin da take so kawai”

   Tsaki yaja afili tare da fadin”

    Hakan na nufin nina gaza kenan? Kai ina bazai yiwu ba, bazan saketa ba, Ummi tawace danni akayita, shima Muktar din gangaci yayi harya aureta”

     Zaro ido yayi lokacin daya hango Ummi tana gudu agaban shi, ko tantama bayayi Ummi ce”+

     Meyasata gudu haka?, meya sameta? Wuta ya kara wa mutar , cikin kankanin lokaci saiga shi agaban ta”

    Arikece ta nufo motar tana mata mata mahaukacin bugu”

    Shima Abdulmajeed arikecen ya fito ya rukota, Zainab meya same ki?

    Kirjinsa ta fada mutafi muyi sauri mubar nan wajen”

     Hannuwan shi yasa ya rungumeta ki natsu kinji KO, ki gayamin menene ya firgitaki haka?

     Ban da yarawa babu abun da jikinta keyi, nidai mutafi wani mutum ne yake bina”

     Hanyar yabi da kallo yana shafa bayanta yace”

    Bakowa anan gurin Zainab, daman haka kike da tsoro?, duba fah kafarki babu takalmi”

    Umm mutafi dan Allah”

    Rabata yayi da kirjin sa sannan ya nufi motar da ita”

    Bayan ta shiga ta zauna ya rufe motar sannan ya zagaya yana kokarin shiga motar, tare da waiwayen bayan sa, jakar Ummi ya hango can nesa, dan haka ya karasa gurin ya dauki jakar”

     Lekawa cikinta yayi komai nata naci har phone dinta, amfani yayi da wannan damar yasa hannu cikin ya fara lalubawa, nan yaje ya tabo wata leda ahankali ya zarota”

   Tunkafin ya budeta ya tabbatar wa kanshi sune dan haka yayi jifa dashi sannan ya taho”

     Samun Ummi yayi tanata zazzare ido tana waige waige”

     Jakar ya mika Mata sannan ya zauna, har suka fara tafiya batabar waigen bayanta ba”

   Shikuwa Abdulmajeed dariya yake kyalkyatawa acikin zuciyar shi, kai mata suncika tsoro yanzun hakama mahaukaci ta gani”

    Juyawa yayi ya kalleta, ki natsu mana ki daina irin wannan tsoron waye zai biyo ki?, ke dai kin firgita ne kawai”

    Cikin zare ido tace wlh wani ya biyo ni, kuma yamin kama da wadda nasa ni, banga fuskan shiba amman wallahi kamar nasan shi”

    Jim Abdulmajeed yayi, yana nazarin maganarta, zuwa can yace”

      Toh kiyi tunani da kyau”

    Itako.Ummi tsoron furtawa take gaban Abdulmajeed Amman yanayin jikinsa yayi kama dana Muktar”

    Suyi nisa atafiya yace”

     Ina zan kai ki?

   Gidan Mommy zani”

    Kauda kanshi yayi can gafe tare da fadin ko kunya babu”

STORY CONTINUES BELOW

      Itama kauda kanta tayi, har suka isa gidan hankalin ta be kwanta ba”

      Mommy tayi murna da ganin su, hartai tunanin sun shirya kansu, sai dai ganin inda kafar Ummi tai futu futu yasa Mommy tadan zaro ido, lafiyar ki kuwa?

    Abdulmajeed da shigowan shi kenan ya shiga fadin”

    Wlh Mommy atiti taita gudu ita kadai wai wani mutumi na binta”

    Wani mutumi?, toh kaikuma kana ina?

       Daman ita kadai ta taho nayi nayima ta Bari nawata taki, dana sanima na wuce nabarta”

      Ina ai baxai yiwuba, daman yanxun nake shirin zuwa gidan hajiyan”

   Abdulmajeed ne yace Mommy ni zan wice Office saida yamma”

     Toh adawo Lafiya”

      Yana fita Mommy ta kalli Ummi tace”

    Ke kuma daman nemanki nake, meyasa zaki fita bada izzinin mijinki ba, wannan ba halin kwarai ban, baki kyautaba Sam, ko kunyi fada ne?

     Sunkuyar da kanta tayi tare da rasa abin fada”
Hmmm inajinki Ummi ke nake sauraro”

     Cikkin murya kasa kasa tace”

   Bazan iya zama adashi bane”

     Akan wani dalili, Ummi daman haka kike da rigima”

    Hawaye Ummi ta Fara sharewa

    Ke, Ummi idan kinada wani dalilin ki fada amman wannan ba dalili bane”

     Tana share hawaye tace”

    Mommy yafiye son kansa da yawa, sannan kuma har sigari yake sha”

    Jim, Mommy tayi domin itama kanta wannan shan sigari yana bata takaici”

     Zuwa can ta dago kinaji KO Ummi, kije ki kara hakuri, wannan bekai dalilin daza,a raba aure ba, kema kuruciya ke damunki, kiyi hakuri kowa ma hakuri yakeyi”

      Inyi hakuri inzauna dame shan sigari? wai meyasa kowa baya ganewa ne, cikin zuciyarta take wannan tunani”

      Hakuyi Mommy taita bata suna zaune har lokacin sallah yayi”

   Bayan sun ida sallah Mommy ta  shiga dakinta yayin da Ummi ta zuba tagumi”

      Ba abun da yake damunta kamar Idan  ta tuna kalaman Abdulmajed dayake fadin bata da lafiya, haushi kalamin ke bata”

     Yanzun haka Zan koma yacigaba da gayamin abun da yaga dama, tana tsaka da wannan tunanin taji muryan Ummanta tana sallama”

     Farin ciki sosai taji azuciyarta, bayan ta gaidata ta shige gurin Mommy”

     Sun dade sosai acikin dakin sannan Umma ta fito”

     Kusa da Ummi ta zauna tare da fadin”

     Naji duk abun dake faruwa, kije kiyi hakari, shima Abdulmajeed din ai yana hakuri  dake, kuma daga yau inkinajin rashin mutuncinki ki daina yowa nan”

     Cikin kuka tace ai gidan hajiya naje ita kuma ta goyi bayan sa”

   Waya ai keki gidan hajiyar?, yayi kyau data goyi banyan sa, meya kaiki, kina tunanin wannan auren zai mutune?, to kaddara ma zai mutu ai gidan wani zaki ko?, toh bari kiji duk inda kike sai kinyi hakuri, idan kikaji labarin wata cewa zakiyi ke a aljanna kike, domin *KOWANNE BAKIN WUTA* _da nashi hayakin_, dan haka duk inda kika sami kanki ki kiyi hakuri kuma ki godewa Allah”

STORY CONTINUES BELOW

     Wani irin natsuwa ne yazo mata, dan haka tai shiru tai kasa da kanta, haka Umma taita mata nasiha harna tsayon wani lokaci”

     Zuwa can Umma ta mike zata koma gurin Mommy, nan Ummi ta tuna da mgnr Abdulmajeed, cikin sauri tace”

    Umma wai da gaskene yaya ya wahala dani lokacin danake karama?

       Waye ya gaya miki wannan mgnr kuma?

   Umma shi ya gayamin wai tun ina karama nake wahalar dashi, nikuma naga ko gaisuwta baya amsawa”

     Ikon Allah, wannan zancen ku ne Ummi ke dashi ni bansan komai ba”

     Kawai dai beyiba Umma inda yayi ai zaki sani”

     Hmmm Allah ya shirye ki wucewa tayi ta barta agurin”

   
        Misalin karfe  5:00 pm Abdulmajeed ya dawo, a kitchen ya same Ummi da Mommy lokacin Umma ta dade da tafiya”

    Jin sallaman sa Gaban Ummi ya fadi, har ya gaida Mommy ya fita bata dawo da nutsuwarta ba”

     Juyowa Mommy tayi ta kalli Ummi tace”

Ummi barshi haka, ki wanke hannunki ku wuce gida”

     Badan ranta yasoba ta wanke hannuta ta fice”

      Dakin Mommy ta nufa ta dauko mayafinta ta fito tana kokarin yafawa adaidai lokacin da Mommy ta fito fuskanta murtuk, tace gatanan ka tashi ku tafi gida”

     Abunne yai matukar daure masa kai yaya akayi Mommy ta shawo kan Ummi da wuri haka”
     Mikewa yayi yanabin Ummin da kallo, sai dai ya kula bata cikin walwala”

    Har suka dauki hanya yana cigaba da mamakin halin Ummi, KO bata gayawa Mommy abunda ta kudirta bane?

     Itako Ummi ganin fuskarshi asake tai tunanin  ko dan yana tunanin tagayawa Mommy abun da yace ta fada ne, juyar da kanta can gefe tayi sannan tace”

      Kuma abun da kace na fadawa Mommy rannan ban fada mata ba”

    Juyowa yayi ya kalleta, dukda cewa yasan bata fadaba abun ya bashi haushi, rainin ya farayin yawa”
Ji yayi kamar ya koreta daga cikin motar, daker ya iya daurewa yace,

     Ai nasan baki fada ba, nabar miki kayan ki ne”

    Ji tayi tamkar ya watsa mata ruwan zafi, me yake nufi dayabar min kayana?

      Tunani tai tayi cikin zuciyarta domin sosai take tunani akan xancen”

    Shima Abdulmajeed ya kula kaman zancen bemata  dadiba, tunani ya shiga me zurfi, meyasa naga kamar zancen be mata dadiba? Idan ko har zancen be mata dadiba toh abun da yake zuciyarta bashine abakin ta ba”

     Suna isa gidan ta fice amotar, shiko juyawa yayi yabar gidan domin gidan ba dadi zai masa ba”

      Gidan faruk ya nufa sukaci hirar su cikin kwanciyar hankali, nan yaci abincin daren sa, sai gurin karfe tara ya baro gidan batare daya gayawa Faruk abin da ke faruwa ba”

    Yana isa kofar gidansa yaji ransa ya fara baci, cikin rashin kwarin jiki ya shiga falon”

     Ko ina gyare tsaf ga abinci jere dagani kasan abincin dake ciki na musasman ne”

    Tsaki yaja sannan ya nufa dakinsa”

     Wanka kawai yayi ya nufa gadonsa ya kwanta”

    Ummi KO tun shigowan Abdulmajeed tajishi, atunaninta zaizo ya nemeta amma sai taji shiru har kusan goma na dare, kome ya hanashi shigowa kamar yadda ya saba?

     Mikewa tayi ta fito falon, abincin sa tagani yana nan inda yake, ga dukkan alama beko taba ba”

    Jikinta taji yai sanyi sosai harta zauna ta sake mikewa, dakinsa ta nufa tana daf da shiga ta kuma jah ta tsaya, me zanjeyi?, inna shiga ince me?, wata zuciyarce tace, aidaman kin sabashiga da wannan tunani ta karasa cikin dakin”

    Ganinshi tayi kwace yana dannan waya fuskansa babu alamar damuwa”

   Waigowa yayi ya kalleta sannan ya maida hankalin shi kan wayarsa”

    Rasa abinyi tayi nan taji kamar ta juya amman ta dake, zagayawa dayan gefen tayi ta kwanta, har tsayon wani lokaci be waigoba”

    Jikinta taji yayi sanyi sosai, harta fara danasanin shigowanta

     Zuwa can Abdulmajeed ya mike ya dauki filo, kan kujera ya aje sannnan ya haye ya kwanta, yaso yace mata saida safe amman ganin batace mishi komai ba har yanxun yasashi ya shareta”

    Itako gabanta taji ya fadi, me wannan mutumin ke nufi ne?, daurewa tayi tai gyaran murya sannan tace”

     Yaya anan zaka kwana?

    Eh kanwata anan zan kwanta akwai wani abu ne?

    Babu tace sannan ta dada gyara kwanciyarta, zuwacan ta mike ta fice cikin rashin kwarin jiki”

    Shikuwa yana ganin fitanta yai murmushi sannan ya mike ya koma gadosa tare da fadin tana gani in na barta zan takura ne, daman sawa zuciya ne, iyakacin idan nagaji nai Aure”

    Kwaciya yayi, zuciyar shi cike da farin ciki, bacci me dadi yayi, yayin da ummi ta kwana tunanj”

     washegari karfe 7:55am Abdulmajeed ya fito, cikin shirin zuwa Office”

     Yana kokarin fita wayarsa tai kara, Abba ne ya kirasa, cikin sauri ya kara wayar akunesa”

    Yana kokarin mika gaisuwa Abba ya katseshi da fadin”

    Abdulmajeed kana ina ne?, Ahmed ne ba’a ganshi ba”

    Innalillahi Wa Inna ilaihir raju’un ya ambata Abba garin yaya haka tafaru?

    Anshirya shi za’kaishi makaranta muka nemishi muka rasa”

    Ganinan Abba, ganinan zuwa…..

     *Mmn Yazeed*🔥 🔥🔥🔥

*KOWANNE BAKIN WUTA*

🔥🔥🔥🔥🔥

  _( da nashi hayakin)_

💨💨💨

               _Story & Written by_

    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*

         

            *73 to 74*

Yana sauke wayar suka hada ido da Ummi, afirgice ya ganta dan haka yai kokarin saita kanshi”

    Yaya Lafiya?

    Lafiya lau, tafiya ya fara tare da fadin barin je na dawo”

     Bin bayan sa ta sake yi, tana kira yaya yaya dan Allah ka gaya min neye ke faruwa?

     Nace miki ki jirani ina zuwa ko, cikin motar ya shiga ya zauna  sannan yace ki koma ciki yanzun Zan  dawo karki sake kice zaki fito”

    Jikinta babu kwari ta koma cikin gida”

    Atunanin ta Abbane bashi da lafiya domin taji ya abbaci Abba”

    Abdulmajeed na isa ya samesu cirko cirko, aharabar gidan duk su Mommy da daddy suna gurin”

    Karasawa gurin yayi ya tsaya cikin yanayin dake nuna yana cikin rudu yace”

   Wai yaya akayi haka ta faru, shi kadai yake tafiya makarantar ne?

    Ai ba ama kai ga zuwa makarantar ba, duk yadda akayi acikin gidan nan aka dauke shi, Umma ce ke fadin haka adaidai lokacin take share hawaye”

     Juyawa Abdulmajeed yayi ya kalli me gadin yace”

    Wani ya shigo ne?

   Babu wadda ya shigo gidan nan me gida, tuda nadawo masallaci nake zaune aguri na babu wadda ya shugo kuma babu wadda ya fita”

    Dakata Baba, kana nufin shi kadai zai dauki kanshi? Karka raina min hankali mana, duk yadda akayi kanacen kana gyangyadin ka natsiya wani ya shigo gidan nan, ko kuma yaron yafita”

    Abba ne yace”

  Bana tunanin haka Abdulmajeed domin yaron nan betaba fita gidan nan shi kadai ba, duk yadda akayi anshigo gidan nan ne aka dauke shi”

    Hannu Abdulmajeed ya dunkule sannan ya bugawa dayan hannun sa, zuwa can ya shafa kanshi cikin neman abin yi, afili yace ta ina Zan fara ne”

    Abba ne ya dafashi tare da fadin”

    Ka kwantar da hankalin ka Abdulmajeed mubi komai ahankali, Allah zai kawo mana mafita”

   Abba hankalin Ummi zai tashi ban son taji wannan maganar”

   Wani irin kallo duk suka mai Daddy ne yai karfin halin cewa”

    Kai ka nutsu bamu san shashanci, idan ta kama ta sani ai dole ta sani, idan har bamu sameshi ayauba dole za’a gaya mata, domin addu’an uwa akan danta babban sinadari ne”

   Jikin Abdulmajeed sanyi yayi sosai zuwa can ya nufa motarsa tare da fadin ina zuwa”

    Abba ne yace”

  Ina zaka?

  

    Har ya tada Motar Mommy ta tuna jiya fah Ummi tace wani mutum na binta, dakatar dashi tayi tare da fadin”

     Jiyafa Ummi tace wani mutumi ya biyota aguje”

   Dakatawa Abdulmajeed yayi bayan gajeran nazari yace”

    Bana tunanin haka Mommy waye zai kama binta haka kawai, nafi tunanin mahaukaci ne ya biyota”

    Ba lallai mahaukaci ba, akirata domin muji daga gareta”

STORY CONTINUES BELOW

     A’a Mommy ni bana son ta sanni, dan Allah Ku bari idan ban samoshi ayauba gobe saiku fada mata, da haka ya fice yabar su jigum jigum”

   Abba da Daddy ma ficewa sukayi, daga Umma sai Mommy sau kuma Mutan dake shigo musu jaje”

     Har dare babu wadda ya dawo, da misalin karfe, 8:30pmUmmi ta kira wayar Umma, bayan ta gaidata tace”

   Umma wai Abba bayi da lafiya ne?

    Lafiyarsa kalau   Ummi me kika gani?

     Dasafe ya kira yaya Abdulmajeed awaya kuma naga ya fita arikece, shine nayi tunanin ko Abba ne babu lafiya”

    Saurin Umma tayi tasha kwana,  eh dazon yazo ya dubashi akan ciyon kan dake damun shi”

    Addu’an samun sauki tamai”

     Bayan ta kashe tunani taitayi akan meya hanna Abdulmajeed dawowa gida har wannan lokacin”

    Itama Umma addu’a taitayi Allah yasa aga Ahmad domin ita kanta cikin damuwa take”

   Misalin karfe 9:30pm, Abdulmajeed ya dawo gidan lokacin su Abba ma basu jima da dawowa ba, jikin shi babu kwari fuskan shi da alamar damuwa karara”

    Abba babu wani labari KO?

    Babu Abdulmajeed nidai yaron nan kawai daukan shi akayi, duk yadda akayi akwai wani boyyen al’amari wadda bamu sani ba, amman inaga idan ka koma gida ka sanar da Ummi cikin hikima, kuma da safe ka daukota ku zo”

     Toh yace sannan ya mike  yai masu sallama ya tafi”

     Ya isa gida kusan karfe goma, ji yake kamar karya shiga gidan, cikin dakewa ya shiga falon, mamaki sosai yayi ganin Ummi zaune afalon”

   Tana ganin shi ta mike ina ta kiranka baka dauki wayar ba”

     Aljihushi ya fara shafawa tare da fadin ni bamma san inda wayar take ba, me kikeyi har yanzun bakiyi bacci ba?

    Nata jiranka ne ka dawo naga ka kira sunan Abba kuma ka fita arikice”

    Zama yayi akujeran dake kallonta sannan yace”

    Toh kuma sai akace miki Abba ne, wani abokina ne fa ya kirani”

    Hmmm kawai tace domin a tunaninta zai boye mata ciwon Abba ne”

     Ganin tashiga tunani ya miki zanje na kwanta agajiye nake kema kije ki kwanta”

    Mikewa sukayi kusan atare”

    Aranan Abdulmajeed be iya bacciba, kawai tunani yake waye ya dauki Ahmad karamin yaron da besan komai ba, so uku yana zuwa duba Ummi sai yaga tana shirgan baccinta”

    Washegari ma wanka kawai yayi ya fitoh ya leka dakin Ummi, bayan ta gaidashi ya rasa yadda za’ayi ya gaya mata, ya dade tsaye zuwa can yace saina dawo”

     Koda ya isa gidan kallon bayan shi suke ganin dai tabbas shi kadai din ne Daddy yace”

    Ina Ummin?

    Tana gida, nace mezai ahana abari yau idan baganshi ba sai afada Mata”

    Kai, karka kawo min shashanci banza, wuce kaje ka kawota”

    Mikewa yayi badan ransa yasoba ya nufa gida”

   Tana zaune tana danna waya yacin mata, zama yayi kusa da ita ya rasa ta ina zai fara ne”

     Itama dawowan shi ya bata mamaki kuma daganin yanayin shi akwai zance abakin shi’

     Hannunta taji ya rike da sauri ta dago ta kalkeshi, idonshi jawur tagani tana shirin bude baki tai magana yace”

    Ummi ki dauko gyalenki kizo muje Ahmad ne ba’a ganshi ba tun jiya”

    Da saurita ta mike tare da salati, nan danan hawaye suka fara sintiri a idonta”

    Tashi muje Ummi ki daina kuka za’aganshi, kasa tashi tayi saida ya dagata”

    Shi da kansa ya dauko mata mayafinta da tai makon sa ta shiga motar suka tafi”

    Afalon gidan duk suka same su, zama Ummi tayi akasa tare da sukuyar da kanta tana cigaba da share hawaye”

    Daddy ne yace, ai ba kuka zakiyi ba, addu’a zakiyi Allah ya baiyyana shi,

  Insha Allahu yana hannu nagari, yanzun mu abun da muke sonji ance wani mutumi ya biyoki shekaran jiya, kin masa wani abune koko a’a hakanan yake binki?

   Babu abun da na masa kawai dai naga ya fara bina”

    Zaki iya gane kamannin shi?

    Hawaye ta share banga fuskansa ba amman yanayin jikin shi yamin kama da na wadda na sani”

   Kiyi tunani da kyau Ummi domin inaganin mutumin dake binki yana da hannu acikin batan Ahmeed domin yaron nan daukan shi akayi”

   Nan Ummi ta kara rikicewa akwai kamshin gaskiya kuma fa mutumin yayi kama da Mukhtar, bazan iya boyewa ba anzo gurin da yazama tilas na fada, dago jajeyin idonta tayi daddy mutumin dake bina yayi kama da Mukhtar”

    Cikin sauri Abdulmajeed ya kalleta, Abbane yace”

  Kikace kuma bakiga fuskan shiba?

   Eh bangani ba amman ni……

    Abbane ya katseta da fada dole ta rufe bakinta”

    Haka suka wuni kowa zuciyar shi babu dadi, suna cikin wannan hali kira ya shigo wayar Abdulmajeed, daganin number ya gane Saminu ne, da saurisa ya nufa waje”

    Dannawa yayi Shannan yasa akunne, daga cen cikin wayar akace”

    Saminu ne”

  Eh nagane”

   Naso nakiraka tun tuni nasanar dakai dawowan yayanmu jafaru da furucin sa, amman ban samu fitowa bakin yanki ba har haka ta faru, beyi muku bannaba dai KO?

    Rudewa Abdulmajeed yayi zuwa can yace”

    Wanene kuma Jafaru?

   Nan Saminu ya sanar dashi atakaice, sannan ya kara da cewa walahi banso yai nasaran tahowa da Ahmad ba”

   Kana nufin Ahmad yana wannan bakin garin”

    Yana nan basu jima da isowa ba”

  Innalillahi wa inna ilaihir raju’un Abdulmajeed ya furta”

    Karkace min bakusan da zuwa Jafaru ba?

    Saminu mudai kawai mun neme yaro ne mun rasa, tun jiya muke neman shi”

    Basu jima da isowa ba ni zan koma kar su fahimci nafito Bakin yanki su tambayeni dalili, kuma Yaya karkace zakazo garin nan Jafaru shu’umin mutum ne”

   Abdulmajeed na kokarin magana yaji ankatse kiran, sauke wayar yayi tare da tarin takaici, falon ya koma ganin shi wani iri yasa duk suka juyo suna kallon shi”

   Daddy ne yace lafiya ka samu wani labari ne?

  Eh Daddy, Ahmad wan babanshi ne ya dauke shi”

    Cikin rudu Umma tace yakai shi ina🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀????

    

     *Mmn Yazeed*🔥 🔥🔥🔥

*KOWANNE BAKIN WUTA*

🔥🔥🔥🔥🔥

  _( da nashi hayakin)_

💨💨💨

               _Story & Written by_

    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*

           *75 to 76*

.

Duk ido suka zubawa Abdulmajeed “

     Cikin kauda fuska yace”

   Yana can garin su can ya kaishi”

   Ina ka same wannan labarin?, cewan daddy cikin mummunan tashin hankali”

    Nan Abdulmajeed ya warware musu, hankalin su duk ya tashi, Umma da Mommy kuwa har sun fara hawaye, ganin Ummi sukayi ta mike ta wuce dakin Umma batare da tacewa kowa komaiba”+

     Umma kuwa komawa tayi kan kujeran ta zauna tare da fadin shikenan sai muyi hakuri kowa ya koma yaci gaba da harkokin sa”

     Mommy ma tagumi tacire gashi gari ba kusaba bare muje mu rokesu subamu shi”

     Gyaran murya Abba yayi ai kusa azuciyar ku ya mutu kawai shine zaifi kwanciyar hankali”

      Ai bazai yiyuba KO kowa zai iya ita Ummin bazata iyaba daddy ne ke fadin haka”

    Toh ya zatayi aiko dole ta hakura dan Ubanta, duk ba ita ta jawo mai ba, mikewa Abba yayi yafice yana cigaba da fada, dan haka Abba yabi bayan sa”

  Mommy ko tashi tayi tabi bayan Ummi”

     Daga Abdulmajeed sai Umma aka bari, kowa da abun da yake sakawa “

    Zuwa can Umma ta kalleshi tace”

   Kai tashi kaje kacigaba da harkokin ka”

      Jikin sa asanyaye ya mike ya fita, Umma ma dakin ta nufa domin ganin halin da Ummi take ciki”

     Ajikin Mommy ta sameta tanata sharban kuka”

    Aiko kina da aiki, garama kibar zubar da hawayen ki, domin dai hakuri ya zama dole, bamu da hujjar dazamu ce subamu da, garama ki cireshi axuciyarki”

      Hawayen ta fara sharewa wani irin kulolon bakin ciki ne ya tsaya mata awuya, yaya Zanyi da rayuwata ne ina zansa kaina”

    Shikuwa Abdulmajeed Office ya nufa”

    Ya shiga babu jimawa faruk ya shigo”

  

     Ganin Abdulmajeed dafe dakai yasa shi dakatawa cikin kasa da murya yace”

     Abdulmajeed badai matsalan ka da Ummi bace har yanzun?

    Dagowa yayi da sauri domin KO shigowan sa bejiba”

    Karaso ga zauna mana”

    Shikowa faruk yayi yana fadin mutumina gaskiya matsalan gidanka tanayin yawa fah kuma har yanzun ka kasa dakatar da ita”

   Bama wannan ke damuna ba Faruk duk da cewa itama tananan har yanzun, nan ya kwashe halin da ake ciki ya gayawa faruk”

     Sosai faruk ya tausaya sannan yace”

     Tafiya ta sameka domin zama agida be gankaba”

    Tunkan ya rufe baki, Abdulmajeed yace”

   Babu inda zani wallahi, aini ba wahalalle bane dazan kwashi kafa na tafi”

    Aiko zuwa ya zamar maka dole dama kayi, bare yanzun dazakayi me dalili, gaskiya lokacin na jinjina maka ka iya kasada da rayuwan ka akan soyayya, kagani ban shigama cikin kyauyen ba, Amman wuyan dasha bana fatan Allah ya maimaita min”

STORY CONTINUES BELOW

   Nima kaina bana fata, amman ni KO awancen lokacin saboda su Abba naje badan Ummi ba”

     Hmmm har yanzun dai bazaka ganeba Abdulmajeed wallahi sabo da ita kaje, kuma yanzun ma dole ka koma”

    Wallahi bazanjeba faruk kana nufin a wahala rayuwata xata kare, akan dan daba nawaba?,

Zan ta wahalar dakaina ne”

    Idan ba danka bane ai dan matarka ,

ne kaga ko yazama naka”

   Hmmm ni ba dana bane wlh, idan na tuna waye ubanshi sai naji raina na bacci”

     Ummm haka dai zakuyi ta daurewa kuma yakamata kazo ka daura niyya tafiya”

    Tsaki Abdulmajeed yaja tare da fadin ban son iskanci fah”

     Sai dare Abdilmajeed ya koma gidan Abba domin daukan Ummi”

   Tunkafin ya shiga falon yajiyo muryan hajiya tana mgn cikin fada”

     Aiko babu me zuwa kauyen nan, wlh duk cikin zuri’ata ban yadda kowa ya tafiba, inna ai bazai yi yuba, KO bawan Allah da yiyi shahada waccen karon saboda naga ‘yar uwansa ce a can, amman wannan karon be shirya yin shahada ba”

    Kwata kwata jiyayi kalamin hajiya basu dace ba, atunanin shi zai sami Ummi tana kuka amman sai ya ganta zaune”

    Kwayan idonta fari tas gefen idonta ya kunkunbura dagani kasan taci kuka”

     Sai da yayi mamakin dayaga hajiya tanata ma Ummi suruntun da inda dane da tuni sun haura sama, amman tai  shiru sai kallo da take binta dashi”

     Kansa akasa badan kunyan Umma ba daya dakatar da ita”

    Gajiya yayi dajin sutun hajiya ya mike ya musu sallama ya fita”

    Bajimawa Ummi ta fito bayan ta zuna ya kama hanya”

    Sai satan kallon Ummi yake, mamaki yake sosai ganin Ummi bata kuka yayi tunanin yau bazata barshi bacciba, amma saiya ganta azaune idonta akan hanya”

    Suna isa ta bude kofar tafita, bin ta da kallo yayi zuwa can shima ya fito ya nufa ciki”

    Tana shiga yana shigowa dan haka ta juyo ta kalle shi tace”

     Sai da safe”

   Wanni irin kallo ya mata sannan yace”

     Allah ya tashemu lafiya”

    Beji me tace ba amman bakinta ya motsa sosai yaji tabashi  tausayi gaskiya abun da ciwo”

   Zama yayi afalon ya kasa shiga dakin sa ya kwanta, har 11:34pm yana zaune falon ya kasa shiga sai najin kamar zai jiyo kukanta, kamar yadda ta saba idan tana cikin damuwa”

   Zuwa can ya mike ya nufi dakin sa, bayan yayi wanka yahau gadonsa badan yanajin bacci ba”

    Kasa bacci yayi har kusan daya, dan haka ya sakko ya nufa dakin Ummi”

     Yana tura kofar ya hangota zaune Saman gado ta hada kanta jikin gado”

    Ji yayi kamar tana magana dan haka ya kara kasa kunne sa”

     Wayyo, wayyo Allah na nashiga uku”

   Hannu sa yasa ya taba  kafadarta, tare da fadin ke Zainab”

     Dagowa tayi da sauri suka hada ido, cikin sauri ta maida kanta kasa”

    Menene haka kuma kikeyi Zainab?

      Bakomai”

      Shiru yayi yana jin yadda numshinta ke sauka sama sama, ajiyan xuciya yayi sannan yace”

     kiyi hakuri kidawo cikin hankali ki”

    Ai nayi hakuri yaya, babu abun da yake damuna baccin ne dai yaki zuwa”

     Hmmm taya bacci zaizo Ummi bayan kina cikin damuwa”

    Tana sauke numfashi sama sama tace”

   Bana damuwa yaya bakagama bana kukaba”

   Juwata yayi ya rungumeta ajikin shi sannan yace”

   Gara kuka Zainab, gara ki yi kuka da wanna halin da kike ciki”

    Kara lafewa tayi ajikin shi tare da sauke ajiyan zuciya”

   Ahankali yaita shafa bayanta sannan tana maida ajiyan zuciya, zuwa can bacci ya dauketa”

     Washegari Ummi tana kitchen tana hada breakfast tunani me zurfi ta tafi, inama Allah zai zamar dani tsuntsu na tashi sama farrr inje indauko dana na dawo,😭 inama nina mijice natafi kyauyen bakin yanki, koda ace zan mutu acen  hamman nasan hakan bazai yiyuba, ayanzun nasan duk wadda yaje garinsu ba lallaine ya dawoba”

 

    Tana tunanin tana cigaba da aikinta dan haka harta gama taje ta jera abincin batare da ta sani ba, tana zaune a kitchen din Abdulmajeed ya fito, ya dade akanta bata sani ba”

     Zainab me kike yi anan?

    Zabura tayi tare da fadin”

      Girki zanyi?

  Girki?, wancen dake falo fah

Jim tayi  Au na manta ne”

    Kina tunani KO?, tashi muje”

    Falon suka fito bayan sun zauna ta bude abincin”

    Gabanta taji ya fadi, menene wannan, ganin ta dakata Abdulmajeed ya mike ya leka”

    Mayar da kallon shi yayi kan fuskanta menene wannan kuma kika dafa?, Ummi bazaki kwantar da hankalinki ba KO?

   Ajiyan zuciya tayi, sannan ta koma kankujera ta zauna, yaya inaji tamkar inzama tsuntsu inje in dauko Ahmad”

  Idonu ya zuba mata sosai tabashi tausayi ahankali yace”

   Ki daina irin wannan tunanin, shiru yayi sannan yace”

     Zainab kinason ne naje Bakin Yankin na amso Ahmad?….

🔥 🔥🔥🔥

*KOWANNE BAKIN WUTA*

🔥🔥🔥🔥🔥

  _( da nashi hayakin)_

💨💨💨

               _Story & Written by_

    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*

           *75 to 76*

.

Duk ido suka zubawa Abdulmajeed “

     Cikin kauda fuska yace”

   Yana can garin su can ya kaishi”

   Ina ka same wannan labarin?, cewan daddy cikin mummunan tashin hankali”

    Nan Abdulmajeed ya warware musu, hankalin su duk ya tashi, Umma da Mommy kuwa har sun fara hawaye, ganin Ummi sukayi ta mike ta wuce dakin Umma batare da tacewa kowa komaiba”+

     Umma kuwa komawa tayi kan kujeran ta zauna tare da fadin shikenan sai muyi hakuri kowa ya koma yaci gaba da harkokin sa”

     Mommy ma tagumi tacire gashi gari ba kusaba bare muje mu rokesu subamu shi”

     Gyaran murya Abba yayi ai kusa azuciyar ku ya mutu kawai shine zaifi kwanciyar hankali”

      Ai bazai yiyuba KO kowa zai iya ita Ummin bazata iyaba daddy ne ke fadin haka”

    Toh ya zatayi aiko dole ta hakura dan Ubanta, duk ba ita ta jawo mai ba, mikewa Abba yayi yafice yana cigaba da fada, dan haka Abba yabi bayan sa”

  Mommy ko tashi tayi tabi bayan Ummi”

     Daga Abdulmajeed sai Umma aka bari, kowa da abun da yake sakawa “

    Zuwa can Umma ta kalleshi tace”

   Kai tashi kaje kacigaba da harkokin ka”

      Jikin sa asanyaye ya mike ya fita, Umma ma dakin ta nufa domin ganin halin da Ummi take ciki”

     Ajikin Mommy ta sameta tanata sharban kuka”

    Aiko kina da aiki, garama kibar zubar da hawayen ki, domin dai hakuri ya zama dole, bamu da hujjar dazamu ce subamu da, garama ki cireshi axuciyarki”

      Hawayen ta fara sharewa wani irin kulolon bakin ciki ne ya tsaya mata awuya, yaya Zanyi da rayuwata ne ina zansa kaina”

    Shikuwa Abdulmajeed Office ya nufa”

    Ya shiga babu jimawa faruk ya shigo”

  

     Ganin Abdulmajeed dafe dakai yasa shi dakatawa cikin kasa da murya yace”

     Abdulmajeed badai matsalan ka da Ummi bace har yanzun?

    Dagowa yayi da sauri domin KO shigowan sa bejiba”

    Karaso ga zauna mana”

    Shikowa faruk yayi yana fadin mutumina gaskiya matsalan gidanka tanayin yawa fah kuma har yanzun ka kasa dakatar da ita”

   Bama wannan ke damuna ba Faruk duk da cewa itama tananan har yanzun, nan ya kwashe halin da ake ciki ya gayawa faruk”

     Sosai faruk ya tausaya sannan yace”

     Tafiya ta sameka domin zama agida be gankaba”

    Tunkan ya rufe baki, Abdulmajeed yace”

   Babu inda zani wallahi, aini ba wahalalle bane dazan kwashi kafa na tafi”

    Aiko zuwa ya zamar maka dole dama kayi, bare yanzun dazakayi me dalili, gaskiya lokacin na jinjina maka ka iya kasada da rayuwan ka akan soyayya, kagani ban shigama cikin kyauyen ba, Amman wuyan dasha bana fatan Allah ya maimaita min”

STORY CONTINUES BELOW

   Nima kaina bana fata, amman ni KO awancen lokacin saboda su Abba naje badan Ummi ba”

     Hmmm har yanzun dai bazaka ganeba Abdulmajeed wallahi sabo da ita kaje, kuma yanzun ma dole ka koma”

    Wallahi bazanjeba faruk kana nufin a wahala rayuwata xata kare, akan dan daba nawaba?,

Zan ta wahalar dakaina ne”

    Idan ba danka bane ai dan matarka ,

ne kaga ko yazama naka”

   Hmmm ni ba dana bane wlh, idan na tuna waye ubanshi sai naji raina na bacci”

     Ummm haka dai zakuyi ta daurewa kuma yakamata kazo ka daura niyya tafiya”

    Tsaki Abdulmajeed yaja tare da fadin ban son iskanci fah”

     Sai dare Abdilmajeed ya koma gidan Abba domin daukan Ummi”

   Tunkafin ya shiga falon yajiyo muryan hajiya tana mgn cikin fada”

     Aiko babu me zuwa kauyen nan, wlh duk cikin zuri’ata ban yadda kowa ya tafiba, inna ai bazai yi yuba, KO bawan Allah da yiyi shahada waccen karon saboda naga ‘yar uwansa ce a can, amman wannan karon be shirya yin shahada ba”

    Kwata kwata jiyayi kalamin hajiya basu dace ba, atunanin shi zai sami Ummi tana kuka amman sai ya ganta zaune”

    Kwayan idonta fari tas gefen idonta ya kunkunbura dagani kasan taci kuka”

     Sai da yayi mamakin dayaga hajiya tanata ma Ummi suruntun da inda dane da tuni sun haura sama, amman tai  shiru sai kallo da take binta dashi”

     Kansa akasa badan kunyan Umma ba daya dakatar da ita”

    Gajiya yayi dajin sutun hajiya ya mike ya musu sallama ya fita”

    Bajimawa Ummi ta fito bayan ta zuna ya kama hanya”

    Sai satan kallon Ummi yake, mamaki yake sosai ganin Ummi bata kuka yayi tunanin yau bazata barshi bacciba, amma saiya ganta azaune idonta akan hanya”

    Suna isa ta bude kofar tafita, bin ta da kallo yayi zuwa can shima ya fito ya nufa ciki”

    Tana shiga yana shigowa dan haka ta juyo ta kalle shi tace”

     Sai da safe”

   Wanni irin kallo ya mata sannan yace”

     Allah ya tashemu lafiya”

    Beji me tace ba amman bakinta ya motsa sosai yaji tabashi  tausayi gaskiya abun da ciwo”

   Zama yayi afalon ya kasa shiga dakin sa ya kwanta, har 11:34pm yana zaune falon ya kasa shiga sai najin kamar zai jiyo kukanta, kamar yadda ta saba idan tana cikin damuwa”

   Zuwa can ya mike ya nufi dakin sa, bayan yayi wanka yahau gadonsa badan yanajin bacci ba”

    Kasa bacci yayi har kusan daya, dan haka ya sakko ya nufa dakin Ummi”

     Yana tura kofar ya hangota zaune Saman gado ta hada kanta jikin gado”

    Ji yayi kamar tana magana dan haka ya kara kasa kunne sa”

     Wayyo, wayyo Allah na nashiga uku”

   Hannu sa yasa ya taba  kafadarta, tare da fadin ke Zainab”

     Dagowa tayi da sauri suka hada ido, cikin sauri ta maida kanta kasa”

    Menene haka kuma kikeyi Zainab?

      Bakomai”

      Shiru yayi yana jin yadda numshinta ke sauka sama sama, ajiyan xuciya yayi sannan yace”

     kiyi hakuri kidawo cikin hankali ki”

    Ai nayi hakuri yaya, babu abun da yake damuna baccin ne dai yaki zuwa”

     Hmmm taya bacci zaizo Ummi bayan kina cikin damuwa”

    Tana sauke numfashi sama sama tace”

   Bana damuwa yaya bakagama bana kukaba”

   Juwata yayi ya rungumeta ajikin shi sannan yace”

   Gara kuka Zainab, gara ki yi kuka da wanna halin da kike ciki”

    Kara lafewa tayi ajikin shi tare da sauke ajiyan zuciya”

   Ahankali yaita shafa bayanta sannan tana maida ajiyan zuciya, zuwa can bacci ya dauketa”

     Washegari Ummi tana kitchen tana hada breakfast tunani me zurfi ta tafi, inama Allah zai zamar dani tsuntsu na tashi sama farrr inje indauko dana na dawo,😭 inama nina mijice natafi kyauyen bakin yanki, koda ace zan mutu acen  hamman nasan hakan bazai yiyuba, ayanzun nasan duk wadda yaje garinsu ba lallaine ya dawoba”

 

    Tana tunanin tana cigaba da aikinta dan haka harta gama taje ta jera abincin batare da ta sani ba, tana zaune a kitchen din Abdulmajeed ya fito, ya dade akanta bata sani ba”

     Zainab me kike yi anan?

    Zabura tayi tare da fadin”

      Girki zanyi?

  Girki?, wancen dake falo fah

Jim tayi  Au na manta ne”

    Kina tunani KO?, tashi muje”

    Falon suka fito bayan sun zauna ta bude abincin”

    Gabanta taji ya fadi, menene wannan, ganin ta dakata Abdulmajeed ya mike ya leka”

    Mayar da kallon shi yayi kan fuskanta menene wannan kuma kika dafa?, Ummi bazaki kwantar da hankalinki ba KO?

   Ajiyan zuciya tayi, sannan ta koma kankujera ta zauna, yaya inaji tamkar inzama tsuntsu inje in dauko Ahmad”

  Idonu ya zuba mata sosai tabashi tausayi ahankali yace”

   Ki daina irin wannan tunanin, shiru yayi sannan yace”

     Zainab kinason ne naje Bakin Yankin na amso Ahmad?….

🔥 🔥🔥🔥🔥🔥

*KOWANNE BAKIN WUTA*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥

    ( da nashi hayakin)

💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by

    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*

  Salam mabiya KOWANNE BAKIN WUTA a page din baya nayi kuskure wajen sunan Abokin Abdulmajeed *Sadiq*, nasa Faruk to ayi hakuri kuskure sunan sa *Sadiq* ne ba Faruk ba👏🏻

    *77 to 79*

Girgiza kai tayi da saurin ta tare da zobowan hawaye”

      Kallo yabita dashi dashi na tsayon wani lokaci, sannan ya mika hannun shi ya rungume ta”

     Wani irin kukane yazo mata me karfi Abdulmajeed be hanataba domin yana ganin kukan zaizama sauki azuciyarta”

    Bude baki tayi sosai tana raira kuka, duk da cewa tuni taso tai irin wannan kuka yaki zuwa amman kalamin Abdulmajeed ya fittar dashi”

     Yana nufin idan inaso yaje zaije ne?,  indai ko hakane wancen karon ma danni yaje badan su Abba ba kamar yadda yake fada ko yaushe, kuma indai zai min haka lallai bakaramin sona yake ba, daman andade ana gaya min sona yake yi bana yadda”

     To shi me yasa baya son nasa ni?, me yasa yake boye son da yake min?

    Adai dai lokacin da take wannan tunanin taji yana shafa bayanta tare da fadin”

    Ya isah haka Ummi, indai kina son inje zanje, amman karki sake yiwa kanki fatan komawa wata halitta daban, in kika koma haka mu kuma ‘yan uwan ki yaya zamu yi?, koko mu bakya tuna nin Mu?, eyye Ummi Ahmad ne kadai azuciyar ki KO ???

   Tana kwace akirjin shi take girgiza Kai, tare da share hawaye”

      Shiko kara shafa bayan ta yake, tare da fadin hakane mana”

     Wani irin sanyi taji azuciyarta ganin inda Abdulmajeed yake rarrashinta, ji tayi tamkar duk duniya bata da wadda yafishi, son shi me zafi taji yana shigarta, samun me irin halinsa sai Antona”

    Ahankali tace”

  Bahaka bane yaya, kawai ban son ya kasance agarin ne, wlh yaya daya kasance agarin gara nasan mutuwa yayi”

     Shiru yayi zuwa cen yace”

  Zainab nasan idan ba ganin yaron ki kayi ba hankalinki bazai kwanta ba, kin dole zan tafi”

   Girza kai tayi a’a yaya baxaka ba, bon son kowa yaje, domin nasan yanzun sun gama shirya mana, babu abun da baxasu yiba akan duk wadda yaje, Yaya wallahi jiya nayi dana sanin auren Mukhtar”

    Wani irin sanyi yaji axuciyar shi, dan haka ya kara rungume ta, lamo tayi tamkar me bacci har na tsayon wani lokaci sannan ya dagota yana kallon fuskanta Ummi ina son na leka Office, amman bazan dadeba zan dawo”

    Mikewa sukayi tare yana tafe yana waiwayen ta kasa cewa komai tayi yana fita tace”

   Allah sarki, Ashe yaya Abdulmajeed yana da kirki haka?, hawaye ne sukayi ta zubo mata tana sharewa nan ta zauna tacigaba da tunani, harta dauki tsayon lokacin da bata sani ba”

    Sallaman Mommy ne ya katseta, cikin sauri ta mike tana yake”

   Mommy ma tana murmushi tace”

    Kin samu sana’a KO? hannunta ta ruko suka zauna akan kujera, daidai lokacin Abdulmajeed ya dawo, dan haka duk suka maida kallon su gareshi”

Mommy ya gaidar sannan ya nemi guri ya zauna”

STORY CONTINUES BELOW

Mommy kuwa Ummi ta kallah tace,

  yau da tunanin ki nakwana Ummi, nasan kinan cikin damuwa dan haka nazo inkara baki hakuri abun babu dadi amman ya zama dole kiyi hakuri indai muna raye wata rana zakisha mamaki domin dole Wata rana zai nemeki, ki kwantar da hankalin ki kinji KO?

   Daga kai tayi tare da fadin Bana damuwa Mommy ki tambayi yayama kiji”

   Wani irin kallo ya mata idonta aduk akunbure amman tana cewa bata da damuwa, kwana daya tal harta zuge”

     Kauda kai yayi dan haka Mommy tace”

   Ki daiyi hakuri Ummi duk wadda ya kalleki yasan kina cikin damuwa, nasiha gaita mata daga karshe tayi sallama tafito”

   Abdulmajeed ya bita suna fita yace”

  Mommy Ummi fah bata bacci, wlh tana cikin damuwa dan haka na yanke shawaran zanje kyauyen nan na dauko mata danta”

  Wani irin waigowa Ummi tayi tare da zaro ido😳 cikin sauri ta daga hannunta ta zabga mai mari”

   Yana rike da kuncin sa yake kallon Mommy, fuskanta ciki da tashin hankali, idan kai mahaukaci ne to ni da hankali na, ban amince ba Sam”

    Wallahi wallahi bazakaba ka gaji da duniyar ne ?, to nima inason naga kwanka fah,  kullum kana fadin ummi tana  wahalar dakai taki Bari azauna lafiya amman ka iya sadaukar da rayuwanka akan soyayyar yariyar da batasan ma kanayi ba” to maza ka shiga hankin ka, kuma karna sakejin zancen kauyen nan abakin ka bazaka ba, dadin auren kaji???

    Sosai Mommy tabashi mamaki betaba zatan hakaba daga gareta, domin hakan ba halinta  bane

 

   Juyawa tayi ta shiga mota tana cigaba da fada”

   Shima cikin gidan ya koma Ummi bata falon dan haka ya wuce dakin sa”

    Tunani yai tayi barka tai harna tsayon wani lokaci, jin kiran Sallah yasashi mekewa da sauri”

   Tunda ya fita be dawoba sai wajen karfe tara, dakin Ummi yafara shiga, tana kwance tana kallon sama

     Ahakali tace sannu da zuwa”

   Yauwa Zainab ya gida

    Lafiya lau

   Alhamdulillahi, kindai ci abinci ko?

    Eh naci”

   A’a ban yadda ba Zainab me ki kaci?

    Abinci mana gama nakacen afalo”

   OK tam barije naci daga cen Zan wuce na kwata saida safe kenan?

     Daker ta iya daurewa tace mukwana lfy”

    Yana fita tace azuciyarta, yaya ya cenza hali baya san kasancewa kusa dani ayanzun ba kamar daba, baya son kwana kusa dani, tunawa tayi da kalmar daya fada mata nabar miki kayanki ne, yana nufin har yanzun yana kan bakanshi, alhalin awannan lokacin ina bukatar kulawan shi, tunani taitayi har 12:30am ta  buga, kwata kwata ta kasa bacci dan haka ta tashi ta zauna ina zuwa cen ta mike ta nufi dakin Abdulmajeed, cikkin sanyin jiki ta tura kofar”

   Waigowa yayi ya kalleta domin shima tunani ya hanashi bacci”

  Murmushi yayi mata kin kasa bacci ko?

   Sukuyar da kanta tayi sannan ta karasa gefen gadon ta zauna

    Zaki kwanta anan ne?, saukowa yayi yace”

hau ki kwata”

   

Babu musu ta tahau ta kwanta bargon ya jawo ya rufe mata jiki sannan ya koma kujera ya kwanta”

    Jefi jefi yana waigowa ya kalleta, har bacci ya dauke shi”

STORY CONTINUES BELOW

    Itama Ummi bacci barowo ne ya saceta”

Washegari har Abdulmajeed ya gama shirinshi Ummi na kwace sai dai idonta biyu ba bacci take yiba”

     Bayan yagama shirin sa tsaf ya kalleta, Yau yaya dai naga har yanzun baki tashi ba?

    Lafiya lau kawai dai banjin dadi ne, jikina babu kwari”

    Ayya sannu ko, ki daure ki tashi ki nemi wani abu kisa abakin ki”

   Toh yaya, amman  kaifa bakayi breakfast ba”

   Karki damu idan na fita zanyi”

    Dahaka ya wuce yabarta adakin sa yana cigaba da waiwayenta”

   Yana cikin motar ma tunaninta yake, tare da neman hanyar dazai taimake ta”

   Yana isa  Office din Sadiq ya wuce hannu ya mika masa suka tafa, cikin murmushi Sadiq yace”

  Mutumin yaya dai?

   Zama Abdulmajeed yayi yana fadin “

Banjin dadi Sadiq ina tunanin zuwa garin nan domin Zainab tasa zuciyanta akan yaron nan tana neman zaucewa”

   Hmmm ai dole ne Abdulmajeed bazaka gane hakan ba saika kwatanta abin da kanka, sai dai fa garin akwai wahala”

Hmm aini bama wahalar ke damuna ba, kawai ina tunanin yadda zanyi intaho da yaron ne, ina tunanin babu wata hanya da zanbi, su yadda dani bare har suban yaron , kuma nasan ayanzun suna dakon jiran zuwa wani akan karban yaro”

   Sosai kuwa Abdulmajeed da ace zata iya hakuri da hakurin shi yafi”

  Bazata iyaba Sadiq ita fatan ma komawa tsuntsu takewa kanta wai data dauko danta, kaji wani shirme dan Allah, karasa maganar yayi idonshi cike da kwalla”

   Dariya Sadiq yayi tare da fadin Allah sarki, taban tausayi lallai tana cikin tashin hankali mutum yai ma kanshi fatan komawa wata halitta, dariya yasake kwashewa dashi”

  Kai dan isa ne Sadiq, maye abun dariya anan kuma”

    Kaine kake bani dariya Abdulmajeed, yanzun dai ba wannan ba, yaushe zaka tafi?, sai najima tamkar na rakaka”

   Hmmm bakasan wani abuba wai jiya Mommy daga nace mata zani ta fara fada hartana marina, wai bata yadda ba”

   Zaro idanu yayi tare da fadin Mommyn”

  Hmmm ai nima taban mamaki wlh”

  Toh yanzun yaya kenan?

   Ni inaga zan lallabeta ne kawai na tafi, sai daga baya ma nai dana sanin furtawa dana shiryawa kaina tafiya kawai batare da kowa ya saniba”

     A’a karkai haka, wannan tafiyan ba irin wadda akeyi aboye bace”

    Hmmm yace, tare da mikewa Mikewa Abdulmajeed din yayi ina zuwa barin je indawo yanzun nan”

   OK toh saika dawo”

     Gidan su ya nufa domin ya kara lallashin Mommy  yana shiga ya samesu su biyu da hajiya, wani dadi yaji domin yasan hajiya zata sa baki”

  Bayan ya mika musu gaisuwa yazauna”

   Muryan hajiya yaji tana fadin”

  Bawan Allah ashe baka da hankali, yanxun kai saika koma wannan garin kaifa ka dawo kana fadin akwai dan karan wahala kuma fah kana kallon yadda suka dauki yaron nan cikin sauki kamar sun hada da tsafi ashirye suke duk wadda yaje bana tunanin zasu bashshi ya dawo darai”

   Hajiya kenan kinji ki da wata magana duk fa wadda ya mutu kwanan sane ya kare”

   Salati hajiya ta fara tare da tafa hannuwa, wa ka ajiye mana makwafin ka da zaka fara neman mutuwa”

   Dariya yayi sosai hajiya saina ajeye wani?

   Mommy ce ta zubamai harara tare da fadin”

   Wlh badan Ummi kake aure ba danace asiri aka maka, kuma zanga ikon Allah zan gani tsallake magana ta zakayi ka tafi”

   Mommy dan Allah kiyi hakuri, wlh Ummi tana nuna muku cewa bata damu bane amman wallahi bata bacci”

    Abdulmajeed nasan dai bana wasa dakai wallahi zan saba maka”

   Jan bakin sa yayi ya tsuke, zuwa can ya mike ya fice”

      Yana kokarin shiga mota Daddy na shigowa, suna hada ido da Abdulmajeed ya fahimci akwai matsala, dan haka yace”

    Kai yaya akayi?

    Dakatawa yayi tare da sunkuyar dakai yace”

   Daddy daman nazo neman shawara ne akan zuwa wannan kyauyen amman Mommy taki saurarata”

   Shiru Daddy yayi, zuwa can yace”

   Toh ka bari zamuyi magana nima abun da yasa banyi magana ba ina tunanin zuwan bashi da amfani, idan nasameta din zan neme ka, ya Ummin bata dai matsawa kanta da tunaniba ko?

   Wlh Daddy bata wani baccin kirki duk da tana boye damuwar tata”

   Kacigaba da bata hakuri jarabawa ce da Allah ta kwantar da hankalin ta komai zai warware”

    Dahaka sukayi sallama da daddy,  sosai yaji dadin maganar daddy”

    Yana dafda isa gida yaji wayarsa na kara yana dubawa yaga Ummi ce, be dagaba dan ya kusan isa gida”

    Cikin gudu ya karasa, tunkafin ya fito cikin motar Ummi ta fito , daidai lokacin da yake sakkowa”

     Hannunshi ta rike, yaya wai Zakaje kyauyen su Mukhtar???

    Dagowa yayi ya kalle idonta duk sun ciko da hawaye yace”

   Waye ya gaya miki?

   Hajiya ce “

  Eh ina tunanin yin hakan dai”

  Hawayen ne suka gangaro kan kumatunta tana kallon cikin idonshi tace”

   Yaya kabarshi dan Allah karkaje”

   Da mamaki ya kalleta Ummi baki son na dawo miki da Ahmad din???

Inaso amman bason katafi wannan garin, yaya ina tsoron karka mutu kai ma acen yaya kabarshi kawai na hakura karnazo nayi biyu babu idan narasa ka bansan yadda zan yiba……..

   *Mmn Yazeed*🔥 🔥🔥🔥🔥🔥

*KOWANNE BAKIN WUTA*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥

    ( da nashi hayakin)

💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by

    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*

       *80 to 81*

Wanni irin dadi yaji azuciyan shi wadda rabon da yaji irinsa ya jima, sunbatan ta ya fara batare da yasan me yake ba”

    Gaskiya rabon da yaji wata magana me dadi kamar haka ya manta”

Ashe Ummi ta damu dani irin haka”

    Ita kanta Ummi yadda taga yana nayi sai da tayi mamaki tare da gasgata lallai yayanta yana son ta nunawan ne dai beyi”

     Mannata yayi ajikin sa tare da kura mata ido, fuskan shi warkan yace”

    Bakomai Zainab insha Allahu lafiyata lau zan dawo, duk wadda kikaga ya mutu kwanan sane ya kare”+

    Hannun shi ta sake rukowa, a’a yaya nace maka bana so, garin bashi da kyau haka Mukhtar daga shiga wanka, maciji ya sareshi kuma tundaga ranan bekara samun lafiya ba”

    Jinta fara zancen Mukhtar ya saketa da saurin sa ya shige cikin gida”

    Biyo bayan shi tayi, lokacin da ta shigo baya falon domin wani irin sauri ya ke zafgawa”

    Dakinsa ta bishi nan ma ta samu ya shiga wanka, dan haka ta nemi guri ta zauna tare da tunanin kodan ta ambaci Mukhtar ne dalilin sauyawar sa, indai hakane kuwa toh yaya yacika kishin tsiya”

   Wani guntun murmushi tayi wadda bekai zuciya ba”

    Zuwa can ya fito yana  kallonta tare cigaba da goge jikin shi”

   Kallon shi tayi, sannan tace, yaya ka fasa tafiyan?

   Hmmm Kinfi son na fasa ko?

   Kaita daga masa”

    Nafasa toh amman fa ki kwantar da hankalin ki daina damuwa ki kuma saki jikin ki”

   Dakai ta amsa sannan ta Mike ta fita”

     Washegari yana Office Abba ya kirashi awaya bayan sun gaisa yace naji labarin wai zaka tafi kauyen su Mukhtar, to karka soma,  muyi hakuri haka nan, idan kaje kace musu me? mutanan fah abun tsoro ne kasani amman kana yi kamar bakasan halin su ba”

    Abba nasani wai daman zan jaraba zuwa din ne ingani “

    Kai Abdulmajeed kabar maganan tafiya nan kaji ko, bamu yadda ba dan haka baxa kaba”

    Toh Abba shi kenan”

    Bayan ya kashe wayar yaja tsaki”

    *BAKIN YANKI*

  Tunda aka kawo Ahmad yake kuka tare da kiran sunan Umma, Ummayo tayi tayi ta rarrasheshi ta kasa domin tureta yake, yi”

   Hankalin ta ne ya tashi yaron da ta koyar dashi shan madarar shanu har ya fara mantawa da nonon uwarsa amman yau shine yake gudunta sai kira sunan wata Umma yakeyi, ko wacece Umma, kila Zainabun ce”

   Jafarun ne yai sallama ya shigo Ummayo ta kalleshi tace”

   Jafaru yaron nan fa yaki yadda dani yau kwanan sa Uku amman yakicin abincin mu daker ma ya yadda yaci na, Saminu shima dan yace zai maidashi gida ne”

    Hmmm ai Ummayo dole yaki zama domin idan kinga gidan dana dauko yaron nan zakisha mamaki gidane babba me kyaun gaske, wlh nake gaya miki Ummayo gidan ya burge ni”

STORY CONTINUES BELOW

   Tokai Jafaru yaya kayi ka gane gidan?

  Da adireshin da kika bani na me gidan Muntari dashi nayi amfani na gano komai, itama Zainabun har tayi aure, dana ganta naso ace ina nan komai ya faru, yasin da karya ne tabar garin nan”

     Wani irin kallo Ummayo tamai mezaka mata?

    Matse kawai Ummayo amman dai yariyar fah tayi ne ba karya Ummayo

    Kai jafaru kana da hankali kuwa”

     Garass nake “

   Hararan shi tayi sannan ta mike tai waje”

   Dai dai lokacin Saminu ya shigo da Ahmad yana kwance kan kafadan shi, ganin Ummayo yasa shi fadin Ummayo yaron nan fa bashi da lafiya taba jikin sa kiji”

    Hannu ta mika ta tabashi zafi taji rau dan haka ta ruga daki aguje ta dauko jikon magani ta fito tana fadin kawoshi nan saminu”

   Bata

shi yayi, sai dai duk dubaran ta yaki shan maganin, nan ta matseshi ta dura mai amman ya feso shi tare da fashewa da kuka yana bisun da kallo kamar yaga wata halitta”

   Ummayo ce tace”

   Waiyawo nikam nashige su, wai Amadu ne ke guduna yana kallo na kamar yaga dodo”

   Tun daga lokacin yaki yadda da kowa sai Saminu, yana zaune ajikin sa yana fadin ka kaini wajen Umma”

    Kwalla ne cike da idon shi, yaron nabashi tausayi, wani abu me daci yaji ya tsaya mai awuya”

    Kwanan Ahmad Uku yana zazzabi dan haka Ummayo ta takai shi wajen tabawa domin tafiso sanin kan maganin”

    Tabawa na kallon yaron tace”

   Wi wannan yaron ai ya riga ya fara shan maganin nasara namu bazai mai ba, wannan yana daya daga cikin abun da yasa maganin mu beyiwa muntari aiki ba, dan haka sai kin tashi tsaye kin lalata na nasaran sannan namu yamai  aiki”

    Nashige su tabawa, yazon meye abun yi”

  Mafita daya ki nemin sassaken baidu kina bàshi cukali daya kullum har tsayon sati guda,  sannan mu bashi na Zazzabin”

*****

Daga Office gidan Hajiya Abdulmajeed ya wuce”

   Tunda taji sallaman Abdulmajeed ta hade fuska, daker ta amsa gai suwan shi”

  Murmushi yayi sannan ya zauna tare da fadin”

  Yanaga kina shamin kamshi ne kona koma ne”

   Ka koma man mara hankali kawai”

  Haba hajiya nine ban da hankali?

Ina kaga hankali ban da abun ka ai duk wadda ya tausayawa takwara yaso ne, ni yaron ma yafi bani tausayi”

   Hajiya kina nufin mutum baya kuskure ne, kuskure tayi kuma wlh hajiya ta gane kurenta, kisa baki Mommy ta barni mana”

   Eh lallai bawan Allah kana nufin harka manta yadda taita wulakanta ka?

  Kai Hajiya ina ruwanki da wannan maganan kuma

   Eyyeee🤔🤔 eh lallai kam ba ruwana, tashi ka tafi  kaban waje, bakin kuma da kace nasaka bazan saka ba, sai dai inkara basu umarnin kar su barka, fitsrarre kawai”

   Murmushi yayi, Hajiya ni kike zagi

   Eh kai din”

  Shiru yayi yana tunanin, in dai  ko babu bakin Hajiya tafiyar bazata yiyuba, dan haka ya sakko gaban hajiya ya zauna, Haba hajiyata, ni dake ai bama haka, Zainab tana cikin damuwa wani abu fan zai iya faruwa da ita, kuma ai inace Ummi ma takice kamar yadda nake agurin ki

  Hararan shi tayi,  nifa bawan Allah zancen tafiyan nan ne ban kyaunar jinta, amman nima ina tausayinta”

  Yauwa hajiya kuma kingani ma ba ita kadai bace, tana da ciki, ita kanta bata sani ba”

     Alhamdulillahi bawan Allah baka taba min mgn me dadi irin wannan ba, wata nawa ne bawan Allah”

   A’a hajiya bekai ma wataba nakega shiyasa itama bata fahimta ba, nima banso fada ba”

   Murmushi tayi, gaskiya yau ina cikin farin ciki, kasan yanzun abun da zamyi, addu’a zamuyi tayi zan saka malamai suyi saukan alkur’ani domin su kasa zama da yaron da kansu su dawo dashi”

  Tabe baki yayi, domin ya kula dai har yanzun tana nan kan bakanta”

   Hajiya ai wannan bazai hana tafiyan ba, ni inason naje ne, abu me wahala ne fa su dauko shi su kawo shi kama yadda kika ce

Shiru tayi zuwa can tace”

   Kai amman dai gaskiya bawan Allah bana son tafiyar ka”

   Hajiya kiyi addu’a kawai shi yafi, insha Allahu lafiya lau zan dawo”

   Hmmm to kaje  zanyi shawara”

    Toh amman karkiyi dasu Mommy kiyi da zuciyar ki kawai, sai ki yanke hukunci”

    Jeka naji”

      Daga nan gidan sa ya wuce haka nan yake jin zuciyar sa babu dadi wani iri yajeji komai ya tuna bayajin dadi dan haka ya dauko Sigari yana tafe yana busawa”

  Koda ya isa kofar gidan sai da ya tsaya ya karasa sannan ya fesa turare ya nufi cikin gidan”

   Ummi ya gani zaune a falon, ta zubawa TV ido ga dukkan alama ba TV take kallo ba, dan guri daya taima kuri, gawani farin shedan hawaye daya bushe idonta”

     Ya dade tsaye batasan ma ya shigoba, tahowa ya sake yi cikin dakin ya tsuguna agaban ta duk da haka bata san yana yi ba, ahankali yace”

    Ummi”

   Har yanzun dai batasan yanayi ba dan haka ya taba kafadan ta, zabura tayi tare da mikewa tsaye

    Shima mikewa yayi yana kallonta kinan  aikin tunani in anyi maga kice bakiyi ko?

    Wasu sabbin hawaye ne suka zobo mata tasa bayan hannuta ta share, kasa tsaida su tayi, haka sukayi ta zubowa”

   Cikin sanyin jiki Abdulmajeed ya karasa gaban ta sannan ya fara share mata hawayen”

   Kiyi hakuri ki daina wannan kukan, wlh ban son ganin ki cikin wannan halin, kina cikin damuwa amman kina boye min ko?

    Ba haka bane Yaya kawai yanzun ne na tuna Ahmad, yaya duk halin da yake ciki ayanzun fa nice na jawo mai, yaya wlh na cuci Ahmed saboda son zuciyata😭😭😭

   Jawota Abdulmajeed yayi ya rungume ba laifinki bane Zainab kawai kaddara ce”

    Shafa bayan ta yai tayi, yayi da acikin zuciyan shi yake yanke shawa ran tafiyan sa gobe batare da sanin kowa ba, ciki harda Ummi…….

*Mmn Yazeed*🔥 🔥🔥🔥🔥🔥

*KOWANNE BAKIN WUTA*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥

    ( da nashi hayakin)

💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by

    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*

       82 to 84

Lallashin ta yaita yi harta daina kukan, sannan ya nufi kujera da ita”

      Kallon ta yai tayi tare da neman hanyar da zaisa ta farin ciki”

   Washegari yana ta dakon kiran hajiya kona Daddy akan maganar tafiyan shi”

   Amman har ya taso aiki babu wadda ya kira shi, gida ya nufa domin ya gaji da rokon su, acikin zuciyar shi yake fadin wato har yanzun bani da yancin kaina, har yanzun kallon karamin yaro suke min, shekarata nawa amman sai wani tattareni suke yi kamar sunsamu dan karamin yaro”+

   Iri irin wannan tuna nin ya fara harna tsayon wani lokaci, daga karshe yaja tsaki sannan ya mike ya nufi dakin Ummi”

       *******

Jikin Ahmad ya kara zafi duk jike jiken da take bawa Ahmadu basu saukar da zazzabin ba, tun yana kukan kiran Umma harya daina Ayanzun baya iya cewa komai, kawai yana kwace ne yana bin mutane da idanu”

     Ayanzun gurin kowa zuwa yake, domin baya iya tafiya duk wadda ya miko masa Hannu zashi”

    Ganin jikin Ahmad na kara Zafi, hankalin Ummayo yafi da tashi “

  Ahmad din ta goya sannan sannan ta leka kofar gidan ta kira Saminu”

    Jajayen idonta ta zuba mai, Saminu ina Jafaru?

   Naganshi ya nufi jeje”

    Ton jeka min kiran shi, yaron nan jikin shi kara zafi yake yi, gara musan abun yi”

    Juyawa yayi ya tafi, babu jimawa suka dawo tare da Jafaru bayan Ummayo ta gama zayyane mishi yace”

    Toh ai kamata yayi mufitar dashi cikin gari sai akaishi asibitin”

    A’a jafaru ba gara amai irin namu na gida ba”

   Inace tuntuni na gidan ake mishi  beyi ba?

   Kawai mu shirya mu kai shi cikin gari aduba shi, sabo da kar mu rasashi Ummayo hakan shine mafita”

   Toh shikenan Jafaru muje din, tunda babu mafita”

    Washegari suka hau shiri Harda Saminu za aje dan haka ya yanke shawaran kiran Abdulmajeed dazaran sun fita”

  Cikin ikon Allah suka isa bakin yanki Ummayo na goye da Ahmad yayi lamo abayan ta”

   Kwallah ce take ta cika idon Saminu yana fakan idon su yana shareware”

   Mota suka tare suka shiga cikin domin isa Asibitin”

   Koda suka isa Saminu Zamewa yayi yabar Ummayo da Jafaru”

   Can waje ya fita ya nemi layin Abdulmajeed”

 

      ******

Shiko Abdulmajeed yana shiga ya samin Ummi tafito wanka tana shafa mai”

     Yana kokarin zama kiran Saminu ya shigo wayarsa”

    Cikin rawan hannu ya amsa sannan ya mike cikin sauri yayi waje”

     Koda ya fita haraban gidan saida ya waiga yaga babu kowa  sannan yace”

   Saminu inajikin ka, wani Hali Ahmad ke ciki”

STORY CONTINUES BELOW

   Ahmad babu lafiya yanzun haka ma mun fito dashi wajen gari ne domin neman masa magani”

    Meye ke damun sa?

Zazzabi ne ke damun shi, kuma ya matsa masa sosai, yanzun haka ma ko tafiya baya yi”

   Kanshi ya dafe sannan ya sake cewa, kaida waye?

   Ni da Ummayo da kuma Jafaru”

   Cikin tsananin rudewa Abdulmajeed yace”

   Toh kanaji ko? dan Allah kasan yadda zakayi karku koma cikin wannan kauyen da Ahmad ni kuma ayanzun zan san  yadda zanyi na kamo hanya”

   Ai Yaya bani da wata dibara dazanwa Jafaru, duk yadda kake tunanin Jafarun ya wuce nan”

    Yana shirin yin mgn yaji kiran ya katse dan haka ya cije baki tare dabin wayar da kallon”

     Bayan ya tabbatar da katsewan kiran hannu ya zuba cikin aljihu tare da neman mafita, iska yaita fesarwa, domin wani irin daci zuciyar sa ke masa”

    Sadiq ya kira ya sanar mai halin da ake ciki domin ya rasa wa zai gayawa wa”

    Bayan ya kagama waya da Sadiq kiran Saminu ya sake shigowa karo na biyu”

  Hannun shi na rawa ya dauka, daga can Saminu yace”

   Sun kwantar dashi sunce sai Ankara masa jini”

    Toh, Saminu kanaji ko? Kabar wayan ka akunne kowani lokacin zan neme ka”

   Cikin gidan ya nufa da gudun sa yana shiga falon ya tsaya ya saita kansa, sannan ya nufi dakin Ummi”

    Tana kokarin saka kaya ya shigo, ganin sa wanni iri yasa ta karasa saka rigar tace lafiya?

  Murmushi yayi lafiya lau, hannu ya mika ya dan jawota jikin shi, cikin kunneta yake rada mata tafiya ce ta taso min babu shiri”

  Tafiya?, Ina zaka?

Wani Asibiti suke nemana Amman bazan wuce kwana 4 zuwa 5 ba”

   Fuskanta babu yabo babu fallasa tace toh Allah ya kaika lafiya yaushe zaka tafi?

    Eh to ina zuwa barin je indawo”

    Ko da ya fita gidan su Sadiq ya nufa suka kara tattaunawa, nan suka yanke hukuncin zasu  tafi tare”

   Daganan gidan Mommy ya wuce, itama karya ya mata kamar yadda yayiwa Ummi”

    Taso ta dagoshi amman jin yace kwana 4 Zai yi ta cire zargin komai, addu’a tamai sannan ya koma gida”

   Ya samu Ummi kwace lamo adakin ta, zama yayi gefenta yana yin shi Ummi taso ta fahimci akwai abun da ke damun sa”

    Washegari tun da ya dawo massalaci ya hau shiri, bawani kwalliya yayi ba, dan haka Ummi ta kalleshi tace”

    Ka fasa tafiya ne??

  A’a ahaka zan tafi”

   Mukhtar ne ya fadu mata, ranan da zasu tafi kyauyen su, shima Haka yace ko wanka ma beyi ba dan haka ta kalli Abdulmajeed da saurinta tace”

   Kauyen su mukhtar zakaje ko?

   Da saurisa ya kalleta sannan ya girgiza kai bacen zani ba me kiga gani”

    Kuka ta fara, sannan ta karasa gaban shi ta rike hannun sa, nasan can zaje shiyasa ma baka yi wanka ba, karka min haka yaya, baban Ahmad haka yayi min ranan da zamu tafi, yakiyin wanka sabo da yasan wahala akesha ahanyar, ya barni inata shiri”

STORY CONTINUES BELOW

   Bacen zanje ba Ummi, kinga ni ai nayi wanka”

  Hmmm yaya wlh ban yadda dakai ba, wayo kakeson kamin”

    Akan me zan miki wayo bayan nasan da wayon ki idan baki  yadda ba ma toh shirya mu tafi tare, daman naso tafiya dake Hajiya ce ta hana”

     Shiru tayi zuwa can tace toh ka rantse bacen zakaje ba”

     Inrantse?, hmmm hadda sani rantsuwa kuma, murmushi yayi sannan yace toh na rantse

    Kwanciya tayi akirjin shi, lumshe idanu yayi ya rugume ta tsam, kunneta yakai bakin shi yace, me zan suyo miki?

   Duk abun da ya birge ka”

   Wani irin sanyi yaji azuciyan shi  domin alamu sun fara nuna Ummi ta fara sonshi”

   

    ‘Yar karaman jakan shi ta dauka suka fito tare suna rike da hannun juna”

  Bayan ya zauna amotarYa kalleta idonta cike da hawaye”

   Ji yayi tamkar ya fasa tafiyar ya zauna yaita kwantar mata da hankali, wata zuciyar ce tace”

    Ai duk kwantar mata da hankalin dazaka yi be wuce taga gata ga danta ba”

   Da wannan tunanin yaji kwarin guiwa dan haka ya mika hannu ya riko hannun ta, ki koma gida haka nan, kuma ban da tunani bazan dadeba zan dawo”

    Kaita daga sannan ta juya idon ta cike da kwallah”

    Ji yayi kamar kar ya tafi, ya dade tsaye  harta shige gida, sannan yaja motar shi ya tafi”

    Gidan su Sadiq ya nufa daukan shi kawai yayi suka dauki hamya”

     Suna tafe suna hira jefi jefi, sun kusa isa Abdulmajeed ya kira Saminu ya gaya mai sun kusan karasu wa”

    Sai dare suka isa, sai da sukayi tambaya sannan suka gano sunan asibitin dan su ba ‘yan gari bane”

       Koda suka isa asibitin Abdulmajeed Saminu ya sake  kira”

    Ta can baya ya bullo, cikin sakin fuska suka gaisa, sannan ya sake jajjada musu halin da ake ciki”

    Hana cikin Magana Abdulmajeed yace”

   Duk kabar wannan mgnr yanzun dai ina yaron yake?

    Kwatan ta musu yayi domin beson agan su tare bare har a fahimci wani abu”

    Cikin sauri Abdulmajeed ya nufi hanyar, dan haka Sadiq yabi bayan shi”

        ******

   Ummayo na kwace kusa da Ahmad bacci ya kawashe ta, adai dai lokacin su Abdulmajeed suka shigo”

    Bakin gadon Abdulmajeed ya tsaya saitin kan Ummayo dan itce afarko yana leka fuskan Ahmad”

     Yayi baki ya rame hannun shi ya mika ya taba jikin yaron”

     Har yanzun jikin da zafi dan haka yaji wani bacin rai ya kamashi”

    Ya sake leka fuskan Ahmad akaro na biyu Ummayo ta farka”

    Ido hudu suka yi da Abdulmajeed afigice Ummayo ta zubomai ido, zuwa can ta zunduma ihu”

     Wayyo wayyo gashi nan, gashi nan”

     Ja dabaya Abdulmajeed yayi yana kallonta, nan danan mutane suka taru”

    Riketa suka yi suna tambayan ta meyake faruwa?

     Abdulmajeed take nunawa tana cewa”

    Wai mafarki nake ne ko idona biyu?, inaganin wannan dan iska yaron agabana”

     Abdulmajeed ne ya kars matsawa kusa da ita yana fadin”

    Ba mafarki kikeba nazo ganin Ahmad ne kuma indoba jikin shi”

     Tashi tayi ta zauna sannan ta dauki dan kwalinta akasa ta daura”

      Ganin haka mutanen da suka fara shigowa suka fita”

    Wani irin kallo Ummayo tama Abdulmajeed sannan tace”

     Uban wanene ya gaya maka bashi lafiya?

     Murmushi Abdulmajeed yayi sannan yace”

    Naji ajikina ne”

    Ido ta dan zare sannan tace”

   Wai ina Jafaru ne? Jafaru kana  ina”

   Sadiq ne yace”

  Mubada tashin hankali mukazo ba, zamu ganshi ne kawai mu wuce”

    Ni zaku rainawa hankali, Ku zauna har Jafaru yazo  zakuga rashin mutunci, wlh rashin kunyar da kamin da ka kwana lafiya yanzun bazaka min shi ba, bari gari ya waye Jafaru zai min maganin ka”

    Ban da murmushi babu abun da Abdulmajeed keyi, Ummayon kuwa hakan ne ke kara bata tsoro”

  Haka suka kwana tsaye Ummayo na  zaune daf da Ahmad yayin da Sadiq da Abdulmajeed suke tsaye ko wanne rungume da hannun sa”

      ******

Tun dare Mommy ke kiran number Abdulmajeed amman  bata shiga

Dan haka ta fara tunanin kodai Niger din ya tafi, number Ummi ta kira, lokacin Ummi na zaune a kitchen tana aikin tunani taji kira daga Mommy”

   Cikin sauri  ta dauka, bayan sun gaisa Mommy tace”

    Kunyi waya da Abdulmajeed tunda ya tafi?

      A,a da daddare ma na nemi layin shi basu shiga ba”

     Ina yace miki zashi?, na manta ban tambaye shi garin da zashi ba”

   Mommy wlh nima be gaya min ba”

   Shiru tayi zuwa can tace”

  Toh ai shike nan”

   Katse kiran Mommy tayi sannan tace “

   In dai kuwa Abdulmajeed kauyen nan ya tafi zai hadu da fushi na wlh”

    Ranta ne ya bacci sosai sabo da tsabar takaici har kwalla sun taro a idonta”

   Mikewa tayi cikin Zafin rai ta nufi dakin Daddy sa, yana ganinta yasan babu lafiya, dan haka yace”

   Meye yake faruwa?

   Abdulmajeed ya tafi wannan kauyen kamar ni zai tsallake magana ta ya tafi batare da izzinina ba

     A’a a’a dakata ban son hayaniya wanene yace miki cen ya tafi?

   Alhaji tun jiya layin shi basa aiki, tunda ya tsallake maganata wlh sai ya hadu da fushina, kwata kwata auren ma ya sire min, na daina sha’wan auren shi da  Ummi”

    Hannu Daddy ya daga mata sannan ya shiga kiran layin Abdulmajeed “

     Duk basu shiga ba, dan haka Daddy ya mike ya fice cikin sauri”

   Itama Ummi ganin har dare be kirata ba, gashi in ta kira basa tafiya, yasa ta fara kuka domin tabarwa zuciyan ta kawai can ya tafi ko tantama batayi”

    Cikin kuka sosai ta mike ta dauki gyalenta ta nufa gidan Mommy “

    Dare ya fara yi dan haka abun hawa yayi karanci tana  tsaye bakin titi sai faman share hawaye take …….

    *Mmn Yazeed*🔥 🔥🔥🔥🔥🔥

*KOWANNE BAKIN WUTA*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥

    ( da nashi hayakin)

💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by

    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*

    *88 to 90*

Sadiq kasan fa babu wadda yasan da zuwan mu nan, naso ne kawai na koma da yaron, hakan zai rage fushin su”

     Toh Abdulmajeed ai yanzun yazama dole akira su domin Susan halin da ake ciki”

      Bazan iya kiran shi ba, ka kira shi kawai”

    Shiru Sadiq yayi zuwa can ya  miki ya yabar wajen”

   Ba jimawa ya dawo, kallon Abdulmajeed yayi, yace nagayawa Daddy yace zasu taso yanzu nan”

   Da sauri Abdulmajeed ya kalleshi zasu taso?, me zasuzo suyi?, kace musu subar shi kawai, muma yau zamu taso”

   A’a kabar su suzo din kawai”+

  Sadiq meye amfanin zuwan su akwai nisa fah”

   Sadiq ya bude baki zaiyi mgn wayar Sadiq tai kara, cikin sauri ya dauka ya kara akunnen sa”

    Sadiq Ahmad ya rasu ko?

  Eh Abba”

  Toh ina Abdulmajeed din hadani dashi”

   Abdulmajeed din ya mikawa wayar yana fadin ga Abba”

    Abdulmajeed tun da babu yaron ai sai ku dawo gida ko?, zaman me kuke yi agarin”

   Cikin kasa da murya yace”

   Yau zamu taso Abba, amman sai anyi zana’ida”

   Abdulmajeed ban son rigima, ku taho kawai, wannan garin ban yadda dashi ba”

   Toh kawai yace yana mikawa Sadiq wayan ya mike ya koma dakin”

   Ganin Ummayo yayi rungume da Ahmad tanata kuka yayin da jafaru da Saminu suke bata hakuri suma idon su dauke da hawaye”

    Sadiq ne yace”

   Yanzun meye Abun yi, lokaci na tafiya banga anfanin zaman ba”

   Saminu ne ya kalli Ummayo yace”

    Ummayo barin samu mota mu isa gida”

    Cikin kuka Ummayo ta gyada kai, Sadiq ne yai karfin halin cewa”

    Me zai hana arufeshi anan domin muna son ayi zana’ida shi damu”

    Fuskan Ummayo face face da hawaye tace”

    Saminu miko min zani nagoya shi mutafi ka daina sauraran wadan nan mutanan”

   Mikewa Saminu yayi ya isa inda Abdulmajeed yake,”

   Yana zaune yayi tagumi yace”

   Kaji wai cikin kyauyen nan zasu kai shi”

   Mikewa yayi da sauri tare da fadin bazai yiwu ba sadiq, mezai hana arufe shi anan?

    To haka dai suka ce”

   Komawa dakin sukayi tare nan sukaci gaba da ja inja tun suna yi ahakali har suka daga murya”

   Nan mutane suka fara ta ruwa, ko wanne na tufa albarkacin bakin shi”

    Ganin inda Abdulmajeed yayi zuciya yasa Saminu yajashi waje yana fadin”

STORY CONTINUES BELOW

   Abdulmajeed ba fada mukazo ba tunda basu yadda da mu wuce kawai”

  Wlh bazan tafiba ni sonake ma subamu shi mutafi dashi can mahaifiyar shi ta gan shi”

   Abdulmajeed kaima kasan fah bazu yadda ba kayi hakuri kazo mutafi”

    Sadiq wlh kaji na rantse bazan taba tafiya ba, zanga wadda zai fita daga wajen nan”

   Nan fa mutane suka taro inda Ummayo ta taho da Ahmad tana kokarin fita”

    Abdulmajeed ne ya tareta yayin da Jafaru ya taso mai, nan tsiya ta barke kowa kaiwa dan uwansa duka yake”

    Ana cikin haka saiga wani malamin yazo, da alama kiransa aka yi, daker aka janye Jafaru”

   Kowanne yaji jiki, kuma dukkan su haki suke hadda Sadiq dake rabasu haki yake”

    Malamin ne yace”

  Menene haka yake faruwa”

   Ma’aikatan asibitin ne suka shiga karontawa dan haka malamin yace aje akira me Umguwa”

   Cikin kankanin lokaci ya taho da mutanan sa, bayan yaji abun dake faruwa, Gyaran murya me Unguwan yayi sannan yace”

    Tunda abun haka ne kowa bazai sami abun da yake so ba, anan za’a rufeshi, duk wadda yace zai kawo min taurin kai zan dauki mummunan mataki akan sa”

     Har acikin zuciyan Abdulmajeed yaji dadi domin daman yasan baza su yadda su bada yaron ba”

   Bagaba daya gidan me Unguwa aka nufa kowa da abin da yake sakawa har da ‘yan kallo”

    Acikin gidan aka masa sutura bayan an sallaci shi aka kaishi ma kwancin shi”

   Duk lokacin da jafaru ya hada ido da Abdulmajeed hararan shi yake yi, shiko Abdulmajeed jikin shi yayi sayin sosai ayanzun wani irin mugun tausayin Ummi yakeji”

    Koda suka koma gida me uguwa godiya suka mai sosai sannan suka kama suka mai Sallama”

   Suka kokarin wucewa Ummayo ta fito Jafaru ne ne ya fara kunduma Abdulmajeed zagizagi”

   Ita kanta Ummayo taita gudumawa Abdulmajeed, zagi, dan iska bazan taba daina tsine maka ba”

   Jafaru ma aika mai da zagi yake dan haka me unguwan yace su koma su zauna sai bayan su Abdulmajeed sun tafi da minti 40 sukuma su tafi, wannan hukunci bema Jafaru dadi ba, ji yayi inam be nuna komai ba”

    Har suka isa inda motar su ta ke ajiye jikin Abdulmajeed babu dadi, dan haka ya koma bayan motar ya kwata”

   Sadiq ne yaja su, sunyi tafiya me nisa yaji yana ta Jan ajiyan zuciya, dan haka ya juya kadan ya kalle shi Abdulmajeed wai meye haka ne”

   Sadiq banjin dadi ne kawai”

   Juyawa yayi yaci gaba da tafiya tare da fadin”

    Allah ya kyauta”

      Sunyi tafiya me nisa Sadiq ya kara waigowa”

   Gani yayi yanata rawan sanyi dan haka yace”

    Zazzabi ne kuma?, bari mu tsaya mu nemi magani”

   A’a karka tsaya muje kawai”

   Sosai Abdulmajeed kejin jiki amman yaki yadda su nemi magani,  lokaci lokaci suna waya da daddy da Abba, Tun suna cen Umma ta kira tana kuka amman Mommy har yanzun babu kiranta”

    Karfe 6:24am suka iso, gidan Abba suka dusa nan suka sami mutane cike wannan ya tabbatarwa Abdulmajeed Ummi taji labarin rasuwan danta”

    Sannu da zuwa akaita musu, duk sunyi wujiga wujiga”

    Shi ko Abdulmajeed ko magana baya so, dan haka ya wuce falon Abba ya kwanta”

    Ba jima Abba da daddy suka shigo Abba ne yace”

   Yaya babu lafiya ne”

   Sadiq dake shigowa yanzu nan yace”

   Tunkan mu baro garin zazzabi ya rufeshi”

  Daddy ne yace”

  Toh Allah ya tsare, Sadiq ka rubuta masa magani, sai asiyo”

   Labari ne ya isa cikin gida su Abdulmajeed sun dawo amman bashi da lafiya”

    Sosai hankalin Ummi ya tashi Allah Allah take tasa shi a idon ta, amman bazata iya tsallake mutane ta tafi gurin shi ba”

   Mommy ma ta samu labarin amman ko alama bata nuna damuwanta ba bare tace xata duba shi”

   Shi kuwa Abdulmajeed kowa murnan ganin shi yake yi, amman babu Mommy babu Ummi dan haka hankalin shi ya fara tashi”

   Jikin sa kuwa kara zafi yake yi, zuciyar shi cike fal da damuwa, yana me addu’an Allah yasa Mommy ba fushi tayi dashi ba, ita ko Ummi dama bawani kula dashi take ba, dan haka dole ya rage shige mata

    Itako Ummi tana tsakiyan jama’a amman hankalinta yana gurin mijin ta, kosawa tayi sosai ta sami hanyan dazata fice domin taje gurin sa”

    Sallar la’asar aka kira dan haka da yawa suka miki domin yin alwala”

    Da wannan damar tayi amfani ta mike ahankali ta nufi falon Abba”

    Duk abin da take Mommy na kallonta dan haka taja tsaki ta  mike tabi bayan ta……..

*Mmn Yazeed*🔥 🔥🔥🔥🔥🔥

*KOWANNE BAKIN WUTA*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥

    ( da nashi hayakin)

💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by

    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*

       85 to 87

Daker ta ta samu mota ta Shiga”

    Ana kiran sallan mangariba ta isa gidan”

   Ganinta Mommy tayi wujiga wujiga, kallonta tayi akai kaice tace daga ina haka”

    Zama tayi sannan ta jawo gyalan ta ta goge fuskan ta tace”

    Mommy Yaya fah har yanzun wanyan shi baya shiga kuma ina ganin kaman kyauyen su mukhtar ya tafi”

     Wani irin kallo Mommy ta wurga mata tare da fadin”

    Au abun daya shirya mi ki kenan, bake kika turashi ba”

    Da jajayen idonta ta kalle Mommy ganin inda Mommy ta daure fuska yasa tace”

   Mommy wlh bani na turashi ba, basan inda zashi ba, be gaya min ba, sai da nace mishi karya je kuma har rantsuwa ya min bacan zaije ba”

    Kauda kai Mommy ta sake yi a karo na biyu sannan tace”

   Toh ai shikenan ku kuka sani, Allah yasa bashi kadai gareni ba bare nace zanyi bakin cikin rashin shi, kema inkin gama takaba saiki aure wani, shi ya ma kanshi asara”

    Wannan zancen ya daga hankalin Ummi dan haka ta rasa me zata ce, hawaye ne yaita tsiyayo mata tana sa hannuta tana sharewa yadda taga. Ummu tayi tasan kome zatace bazata fahimceta ba”

   Duk kukan da Ummi ke yi Mommy naji batace mata komai ba, dan haka da Mommy ta shiga dakinta Ummi ta mike ta fice agidan”

    Gidan su ta wuce tana shiga ta rugume Umma dake zaune ita da  Abba suna tattauna zancen damin tuni labarin ya wada dangi”

    Duk kallo suka bita dashi  tare da tambayan ta abun da ke faruwa”

    Cikin kuka ta gaya musu halin da ake ciki”

    Shiru sukayi zuwa can Abba yace”

   Toh ya isa haka share hawayen ki, shima Abdulmajeed din yayi kuskure be kyauta ba”

   Abba to ai bani na turashi ba, wlh nace mishi karya je yanzun gashi Mommy tana ganin laifina”

    Cikin rarrashi Umma tace”

  Ke kibar kukan nan haka insha Allahu zai dawo, bar kuka kinyi sallah ko?

   Hawaye ta share sannan tace”

   Banyi ba”

  Toh maza kije kiyi sallah ki ruki Allah ya dawo dashi lafiya “

    Mikewa tayi ta nufa daki, Umma ko juyawa tayi ta kalli Abba tace”

    Alhaji kaji wulakacin da Hajiya taiwa Ummi ko, taje mata da matsala bazata saurareta ba saita fara fadin mata zancen da zai kara tada mata da hankali jifa inda ta lalace acikin yan kwana biyun nan”

   A’a kar muyi haka dake, kiyi mata uzuri, Abun da yayi be dace ba kuma ko kece ma ranki zai baci, kamar yadda Ummi batason danta ya kasan ce awannan garin itama haka bazata so danta yaje ba, ki yi tunani dakyau ki gani”

    Mikewa Umma tayi ta shige dakinta batare da ta saurari Abba ba”

  

          *****

STORY CONTINUES BELOW

Tunda gari ya waye Ummayo ban dan hararan su Abdulmajeed babu abun da take, shiko Abdulmajeed yama rasa me zai yi ne, gaba daya besan hanyan da ya kamata yabi ba”

   Zuwa can sai ga Saminu rike da leda, nunawa yayi kwata kwata besan da zuwan Abdulmajeed ba”

   Nan ya nuna mamakin sa, Ummayo kuwa tambayan shi take ina ya baro jafaru”

   Jafaru na baro shi yana saran itace acikin gari”

    Murmushi kawai Abdulmajeed yayi sanan ya kalli Sadiq yace ina zuwa bari je inga doctor na dawo”

   Nan ya fice ya barso yayin da Ummayo tacigaba da hararan Sadiq”

    Sadiq ne ya kalleta yace”

   Mama kin ga yaron nan yana jin jiki, kuma shi Abdulmajeed likita ne, dan Allah ki bashi dama ya duba shi, bada wata manufa mukazo ba, kawai mun nemi yaron mun rasa ne kin ga dole mu nemi inda yake, alhamdulillahi kuma muji dadi da muka same shi ahannun ki, koda ma baku sace shi ba inkukace mu baku ai zamu baku”

   Indai haka ne ai sai ku kama gaban ku, eh yaro na hannu mu ai nazo har garin wancen dan iskan yaron ya raina min hankali”

   Murmushi Sadiq yayi sannan yacs”

   Rashin lfy yaron yasa mu tsayawa  amman da zaran munga ya fara samun sauki zamu tafi, amman zaku bamu dama lokaci zuwa lokaci zamu dinga lekowa muna ganin shi”

   Sakin fuskanta tayi kadan sannan tace”

  Kai na kula kana da hankali ba kamar wancen ba, wlh bason shi duk sadda na hada ido dashi gabana faduwa yake yi”

   Dan murmushi yayi sannan yace mama sai hakuri kinsan kowa da halin sa”

     Abdulmajeed ne ya dawo ranshi ajagule ya zauna, zuwa can yaje ya leka fuskan Ahmad yayi mamaki da Ummayo ta kauce ta bashi hanya”

   Kallon shi yayi jikin yaron duk ya sake, sai ayanxun ya bude idoshi ya ganshi, sosai ya  kafe Abdulmajeed da ido yana mishi kallon sanayya, Kwallah ne suka cika idon Abdulmajeed tsintan kanshi yayi da lallashin yaron, kayi hakuri kaji ko, kana son ka koma gurin maman ka?

    Sakin fuska yayi tare da mutsa bakin shi dan Abdulmajeed ya kai kunnen sa saitin bakin Ahmed ahankali yaji ya furta Umma”

    Umma?, gurin Umma kake son kaje”

    Daga kai yaron yayi tare da murmushi”

    Shafa kashi Abdulmajeed yayi sannan yace”

  Zaka koma gurin Umma  dazaran kaji sauki, Ummin ka ma tana gaida ka”

    Gyada kai yayi har Abdulmajeed ya koma gurin Sadiq Ahmad na kallon sa tare da murmushi”

    Daidai lokacin Jafaru ya shigo ganin Abdulmajeed abun ya bashi mamaki, dan haka yace”

   Uban waye ya gaya maka Ahmadu na hannun mu, zan batar da mutum fah, wlh za’a daina jin labarin ka”

   Dauke kai Abdulmajeed yayi tare da dan murmusawa”

   Badakai nake mgn ba zaka dauke min kai karya kake ka manna min hauka, kana ji ko wlh zan batar dakai”

    Bismillah, ina kiran ka”

  Haka kace ko, zan nuna maka niba kanwar lasa bane billahillazi sai kun rasa hanyar garin ku, zan nuna maka fada damu sai dan gado, kallon Sadiq yayi yace”

    Kai kuma kai waye?, waye kai?

    Sadiq na kokarin mgn Abdulmajeed ya hanashi, ta hanyar tabashi da hannu dan haka yaja bakin sa ya tsuke”

   Duk zakuci uwar kune yasin”

   Cikin sauri Abdulmajeed yace”

   Karka kara zagin mu dan mu ba yaran ka bane kanaji ko ka shiga hankalin ka”

   Cikin tsananin fushi Jafaru yayi kan Abdulmajeed adai dai lokacin Ummayo ta fara ihu dan haka duk suka juya suna kallonta”

    Ahmad ne ke wani irin numfashi, tuni Abdulmajeed yayi kan shi yana kokarin bashi taimakon gaggawa koda daman likita ya gaya mishi daker yaron ya rayu, duk iya kokari shi abun yaci tura, dan haka ya fara salati tare da bin yaron da kallo”

    Ba Ajima ba yace ga garin ku nan, tun da Abdulmajeed ya tabbatar da cewa Ahmad ya rasu ya ajiye shi ya mike”

     Ummayo ko aguje ta tafi tana kiran likita”

  Kowa ya rikice Saminu ma kuka kawai yake yi, koda likitan yazo ya duba Ahmad cewa yayi  sai dai kuyi hakuri babu shi”

   Hannu biyu Ummayo ta daura aka tana zunduma ihu tare da birgima”

    Shikuwa Abdulmajeed waje ya koma ya zauna cikin tsananin tashin hankali”

   Sadiq ne ya dafashi tare da fadin”

   Abu beyi dadi ba, yau Ummi zataji mummunan labari”

   Bazan iya gaya mata ba Sadiq,

Ai ya zama dole su sani, ina ganin abun da za’ayi akira Daddy asanar mai…..

   *Mmn Yazee*🔥 🔥🔥🔥🔥🔥

*KOWANNE BAKIN WUTA*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥

    ( da nashi hayakin)

💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by

    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*

    *91 to 92*

Ummi na shiga ta hango Abdulmajeed na kwance idon sa rufe*

    Kusa da kujeran daya ke kwance ta zauna akasa sannan ta kamo hannun shi tana me zubar da hawaye”

   Cikin baccin daya dan fara diban shi yaji ana taba hannun shi, bude ido yayi ahankali ya kalleta”

   Wani irin sanyi yaji azuciyan shi, dan haka ya lumshe ido”

   Ummi kiwa tana kuka ne tana murza hannun shi”

    Zuwa can  ya bude idon sa yace”

    Zainab kinji mummunan labari ko, kiyi hakuri jarabawa ce daga Allah, duk abun da ya tsara babu me iya canzawa”

    Hawaye na tsiyaya afuskan ta tace”

    Yaya ba komai Allah yasa haka shine mafi alheri”

   Amin ya fada ahankali, shiru sukayi na wani lokaci, zuwa can Ummi tace”

    Nagode Yaya Allah ya saka maka da alheri, domin abin da kamin arayuwa bazan iya biyan kaba”

   Hawaye sosai yake zuba a idonta, dan haka Abdulmajeed ya tashi ya zauna tare da kama kafadun ta, yana kallon cikin idonta yace”

   Ai ba nayi bane dan ki biyani, zuciyata ce bata son ganin ki cikin damuwa dan haka daga yanzun bazan kara takura miki ba, duk abin da kike so shi zan miki”

   Wani irin kallo tamai, acikin zuciyanta tace ban gane duk abin da nake so ba?, afili kuwa binsa da ido take”

    Kula tayi har yanzun rawan sanyi yake yi, dan haka tace”

    Kasha magani kuwa??

   Nasha amman kinga har yanzun be sauka ba”

    Shiru tayi zuwa can ta kara yawan kukan ta”

   Mene ne kuma?

   Yaya ni tsoro nakeji”

Tsoron me?

  Yaya inajin tsoron kar wani abu ya faru dakai”

  Murmushi yayi kamar me misali?, mutuwa?

  Kaita daga mai alamar eh”

   Murmushi ya sake yi sannan yace”

   Ai mutuwa dole ce Ummi idan tazo babu yadda zamu yi”

   Kanta ta hada da kujera tare da sheshekan kuka”

   Kallon ta yayi yana me son ya gano wani abu, bayan ya gama nazari akanta yasa hannun sa ya dagota sannan yace”

   Ke wasa nake miki ba yanzun zan mutuba,  gajiya ce tamin yawa dazaran na samu bacci zan warware”

   Hannu yasa yana share mata hawaye, dan haka Mommy dake tsayi bakin kofa taja tsaki sannan ta juya tana kokarin fita tare da fadin,

   Banza salla mamme, ya zauna yar kankanuwa yariya tana mai abun da ranta keso, shiko kullum burinsa ya faranta mata rai, zanyi maganin ku in kusan wata ai bakusan wata ba”

  Itama Ummi fitowa tayi ta koma cikin jama’a”

  Shiko Abdulmajeed sai yamma ya samu zazzabin ya sauka dan haka ya fice babu wadda ya sani yabar gidan”

STORY CONTINUES BELOW

  Kwana uku akayi ana zaman makokin Ahmad, kuma aranan Mommy ta koma gida, har yanzun basuyi ido biyu da Abdulmajeed ba domin tunda ya koma gidan shi be fitoba dan har yanxun jikin shi be gama watsakewa ba”

   ******

Itama Ummi ayau taita baza ido taga zuwan Abdulmajeed domin ya dauketa su wuce gida amman shiru har dare babu shi babu labarin sa”

   Tun tana zuva idanu harta gaji tai shirin kwanciya, zuciyan ta cike fal da kewan sa”

   Washagari da safi yayi shirin Office tunda ya shigo gidan be fitaba sai yau, iyakan sa masallaci sabo da wani irin ciwon kai dake damu sa”

Gida Mommy ya nufa zuwa kafin ya wuce”

  Yana shiga falon suka yi ido biyu da Mommy”

   Gaba daya dabur cewa yayi besan lokacin daya tsuguna yana gaida Mommy ba”

  

    Dauke kai tayi tamkar bata san dashi agurin ba”

   Har Abdulmajeed ya gaji da magana, Ummi bata tankashi ba”

   Sunkuyar dakai yayi cikin matsanan cin tashin hankali”

   Sun dade ahaka zuwa can ta mike ta shige dakinta”

    Zama yayi yai shiru, zuwa can ya mike yabi bayan ta, sai dai yana taba kofar yaji ta kulle”

    Komawa yayi jikin sa asanyaye, ko da yaje Office din be iya aikata komai ba”

    Misalin 4:34pm ya sake komawa gidan,  magiya yaita mata bayan ya gaida ta taki amsawa”

   Mommy dan Allah kiyi hakuri wlh banayi bane dan ranki ya bacci, Mommy wlh dan naji ance yaro beda lfy ne, kuma ai ba cikin kauyen tajeba, dan Allah kiyi hakuri ki yafi min”

    Waigowa tayi ta kalkeshi tare da fadin”

   Fita kabani guri

Banson ganin ka agaba na”

   Haba Mommy dan Allah kiyi hakuri mana”

   Hannu ta daga mishi alaman dakatar wa”

  Dan haka yaja bakin shi”

   Zuwa can ya mike ya fita waje, saman motar shi ya zauna cikin mummunan tashin hankali”

  Nan Abba ya dawo ya same shi, kai Abdulmajeed Lafiya kuwa?

   Lafiya lau Abba, sakkowa yayi suka jera nan Abba ya sake cewan sai naga kamar kana cikin damuwa”

   Daddy Mommy ce take fushi dani nagaida ta taki ta amsa”

     Shiru daddy yayi har suka shiga falon, kira ya fara kwalawa Mommy”

   Amsawa tayi, tare da fitowa tana ganin Abdulmajeed ta hade fuskan ta”

    Zama tayi Daddy ma ya zauna sannan yace”

  Ke meyasa kike haka ne? Abun da ya faru ya riga da ya faru, duk mu taro muyi hakuri”

   Alhaji dan Allah karka sa baki ka, barni dashi, badai yace ban isa ba”

    A’a a’a bana son haka, kefa uwa ce, kin sa masifan da fushin ki zai iya jawo mai kuwa?

    Dauke kai Mommy ta sake yi, dan haka Abba yaci gaba da cewa”

  Kimai hakuri sai ya kuma, juyawa yayi ya kalle Abdulmajeed yace”

   Kai kuma ka kiyaye kaji ko”

   Kai ya daga da sauri”

  Muryan Mommy yaji tana fadin”

   Alhaji idan har zan yafe mai sai dai idan ka yadda zaka cire takunkumin hana karin aure ga Abdulmajeed dan banga amfanin wannan auren ba, tun da na fahinmci yana son Ummi ban kara gane kansa ba”

STORY CONTINUES BELOW

   Hannu Daddy ya daga tare da fadin”

   Naji idan ya samu yariya me hankali kuma in yana da ra’ayi yayi, ko waccen ma yariyar ce bata min ba”

   Alhaji ko yana so ko baya so sai yayi shi”

   Wanne irin kallon ya mata sannan yace”

   Anawa namiji auren dole ne?, karfa ki manta, yana da matar sa, kuma kara auren sai kice dole sai ya kara idan bazai iyaba fa, koko ke zaki zauna masa dasu”

   Nifa Alhaji ina son ya kara aure dan ni wallahi ban mai kallon me mata”

   Juyawa daddy yayi ya kalli Abdulmajeed yace”

   Hmmm to kai kaji”

  Muryan shi kasa kasa yace”

  Naji Daddy zan yi, amman abari na huta tukun dan Allah”

   Murmushi kawai Daddy yayi da haka ya musu sallama ya fita”

   Kamar zaije ya dauko Ummi wata zuciyan tace”

Kila bazata biyoka ba, tun da kusan kwana uku bata ganshi ba kuma bata nemeshi ko awaya ba”

   Gidan Sadiq ya wuce can yaci abincin dare sannan ya wuce gida ya kwanta”

    Itako Ummi taita baxa idon ganin Abdulmajeed amman babu shi babu alamar shi, har kusan 11:30pm idonta babu alamam bacci, meyasa baxai zo mu tafi gida ba?, yau kwanan sa Uku da dawowa amman ace ko ya kirani awaya?

   Wata zuciyan ce tace”

Ki kira shi kiji mana, cikin sauri ta girgiza kai na kira shi yace na damu dashi?

   Mikewa tayi ta dauko ruwa ta kurba domin kirjin ta wani irin zafi yake mata”

   Gani tayi bazata iya hakuri ba dan haka ta yake shawaran ta kirashi”

   Number shi ta dannan sannan ta kara akunneta, sai dai harta yanke ba adaga ba, kira taitayi har sau uku babu amsa dan haka ta wurga wayan kan gado sannan ta mike tsaye, me wannan ke nufi?

   Tsaki taja sannan ta koma gadon ta kwanta tare da fadin”

   Wlh sabo dashi bazan ki bacci ba, bacci na zan yi, kwaciya tayi ta jawo bargo ta rufa, sai dai har kusan minti 30 babu alamar bacci a idon ta Abdulmajeed kawai take tunawa “

  Shikuwa Abdulmajeed  har wannan lokacin yana sharan baccin sa dan haka bemasan ta kira shi ba”

   Washegari bayan ya dawo masallaci ya duba wayar shi, wani irin dadi yaji daga ta kirashi, har yayi niyyan kiranta sai kuma ya fasa dumin zuciyan shi taba shi kodai ta kasa bacci ne?

    Itama Ummi zuwa wannan lokacin ta yanke hukuncin yaga kiranta bazai dai kirata bane, toh me yake nufi?, kulewa tayi iya kuluwa”

   Sai da Abdulmajeed ya isa Office sannan ya kirata”

   Kin dauka tayi harta katse, yaso yayi naci ya kara kira sai kuma ya fasa, ajeye wayar yayi agefe sannan yaci gaba da aikin sa, fuskan sa dauke da murmushi”

   Sosai Ummi taji mamakin ganin be sake kira ba, hankalinta yai mugun tàshi’

   Duk abun da Ummi keyi Umma na kallonta ta kula sai kallon wayarta take da alama tana tsan manin kira ne”

   Acikin zuciyanta tace”

  Ikon Allah da alama Ummi ta fara kewan yayan ta”

  Ganin damuwan tana yai yawa yasa Umma tace”

   Ummi yaya akayi ne?, kamar wani abu na damun ki”

    A’a Umma ba abun dake damuna”

    Shiru sukayi dukkan su, zuwa can Ummi tamai da takumin ta, dan haka Umma tai nufin ta zulayeta dan tasan inda ta dosa”

  Kallonta tayi tace”

  Ummi Abdulmajeed kuwa lafiya har yau be leko gidan nan ba?

   Tabe baki tayi Oho mishi shiya sani, mikewa tayi da sauri ta shige daki”

    Murmushi Mommy tayi tare da fadin”

     Kyagawa me garin ko, ba dai kin ki kwatar da hankali ba”

   ***

Sai dare Abdulmajeed ya sake kiran Ummi”

   Gabata taji ya fadi, dan haka bata dauka ta wuriba sai da ta natasa kanta”

    Sallama tamai ya amsa, tare da cewa”

     _Ya kike?_

   _Lafiya, ya jikin ka?_

_Naji sauki ai Ummi”_

   Shiru suka yi zuwa can ya sake cewa”

   _Toh yaya akayi, jiya naga kin kirani, lokacin nayi bacci, sai da safe naga ni, nakira kuma baki daga ba”_

    Tsintan kanta tayi tana fadin”

  _Ni kuwa?, gaskiya ni ban kiraka ba”_

OK toh shike nan, sai da safe ke nan???

   *Mmn Yazeed*🔥 🔥🔥🔥🔥🔥

*KOWANNE BAKIN WUTA*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥

    ( da nashi hayakin)

💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by

    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*

     95 to 96

Sosai yaji mamakin zancen abakinta, cikin ido ya kalleta waye ya gaya miki?

   Ni agari naji”

    OK yayi kyau juyawa yayi ya koma kan gadon ya kwanta yayin da Ummi ta kara hade fuska”

   Yaya baka fah ce komai ba”

    Me kike son nace miki?+

   Ai tambayan ka nayi kuma baka bani amsa ba”

    Murmushi yayi sannan yace”

  Eh da gaske ne”

   Wani irin kallo tamai nan da nan idonta sukayi jah cikin matsanan cin haushi tace”

    Ashe shiya kake shashshare ni, baka kulani kana min mgn daker kaman me ciwon baki, ashe kana can kanacin amanata”

Kyalkyalewa yayi da dariya sannan ya tashi ya zauna, amanar kuma nakeci Ummi?, me nayi miki?

    Kauda kai tayi tana mejin wani irin daci azuciyan ta”

   Kallon fuskanta yayi yaga idonta jawur ya kara kwashe da dariya”

   Waigowa tayi ta kalle shi domin bata taba ganin yana irin wannan dariyar ba”

   Shikuwa Abdulmajeed acikin zuciyan shi yake fadin”

   Mata karshene awajen kishi”

    Dariyar ce ta fara bata haushi dan haka ta mike axuciye tana kokarin fita”

    Rikota yayi tare da fadin meye haka?, 

   Ka  Sake ni”

   Ki zauna inason muyi mgn ne”

   Komawa tayi ta zaune sannan ya kura mata ido yace”

  Ummi inason ki fahici wani abu da kika kasa fahimta, ni fa ba dutse bane, mutum ne ni, kuma ba waliyyi bane ni, kinga dole innemi abokiyar rayuwa”

   Wani kululun abone ya tsaya mata awuya ta kasa hadiye yawu, zuwa can tace”

    Shi kenan ka nemi abokiyar rayuwa, nikuma sai aka gaya min inda ka ajiye ni….

  

   Bata gama rufe baki ba yace”

   Na ajiyeki agurin da kika ajeye ni”

   Shiru tayi zuwa can tayi ajiyan zuciya sannan tace”

  Amman tsakani da Allah yaya kazo ne nahanaka kaine fa kace min wai kabar min kayana”

  Eh nina ce, ashema kingane abun da nake nufi, nan fa gida nane, nina kashe kudina na gina shi, nazuba abubuwan more rayuwa acikin sa, sannan na ajeki aciki, ki kwana a inda kike so, ki kuma ci abin da kike so, na miki shamaki da wani abu agidan nan???

   Girgiza kai tayi da sauri acikin zuciyan ta take cewa me kuma ya kawo wannan maganar”

    Ji tayi yace,

   Ki bude baki ne ki bani amsa”

   Ahan kali tace a’a”

  Alhadulillahi, , cikin idonta ya kallah Ummi dan me ke zakimin shamaki da wani abu??, dan haka zan fada muki da babban Muryar ina so nayi wadaka acikin gidana gida nane dan haka inason nayi abin da raina yaso”

STORY CONTINUES BELOW

  Sanyi jikinta yayi sosai dan haka ta sunkuyar da kanta kasa ta fara kuka kasa kasa”

   Ganin haka yasa Abdulmajeed ya mike ya shige toilet “

  Kuka taitayi kasa kasa nan ta fara ganin rashin kyautawanta, amman ai bada gangan nakeyi ba”

   Fitowan shi yasa ta share hawaye tare da fadin”

   Yaya dan Allah kayi hakuri ka yafe min, wlh bada gangan nake yi ba, ko lokacin da nake gidan baban ahm……

    Karki kiramin sunan wani acikin gidana, nariga na gogeshi azuciya ta karki tuna min dashi”

  Hannun tasa ta rufe bakin ta tare fashewa da kuka”

    Gadon yahau ya kwanta, tare fadin to meye kuma abun kuka kije kiyi hakuri”

   Kin tashi tayi kuma batabar kukan ba”

   Kukan ke damun sa sosai, dan haka yaji ya rasa sukuni, sokkowa yayi akan gadon sannan yace”

   Tunda bazaki wuce dakin ki ba ki hau gado ki kwanta, ki daina wannan kukan ban son jin shi”

   Kama kafadan ta yayi yana kokarin kwatar da ita akan gadon ta zame ta rike kafar shi”

   Yaya dan Allah kayi hakuri, kayafen min yaya ka daina fushi dani dan Allah

    Bana fushi dake taso ki kwanta”

   Yaya wlh kanayi dan Allah kayi hakuri zanyi kokari nagyara”

   Hannu yasa ya dagota sannan yace”

   Ya wuce muje ki kwata, dare fa yayi, karki kara kuka kisan ba’ason mace me ciki tana yawon damuwa, kir kisa komai azuciyan ki”

   Gadon ya kwatar da ita sannan ya zauna abakin gadon yana duba wasu ta kardo”

    Baya ya juya mata dan haka taita kallon shi  tare da tunani barkatai azuciyata”

   Kasa bacci tayi har tsayon wani lokaci”

    So take yaxo ya kwanta amman taga bashi da alama rubuce rubuce kawai yake, dan haka ta matso daf dashi dare da zagayo da hannunta duk biyun cikin sa”

   Jita yayi abayan sa sannan ya kalli hannayen ta akan cikin sa, dakewa yayi ya cigaba da rubutu sa”

   Zuwa can yaji tana juya hannayenta, nan danan jikin shi ya fara rikicewa, dan haka yace”

   Ummi baki yi bacci ba?

   Banaji bacci yaya”

   Kiyi addu’a ki rufe idonki baccin zaizo”

   Shiru tamai zuwa can yaji taci gaba da abu n da take”

   Jikin shi yaji ya soma rawa cikin muryan sa data fara shakewa yace”

    Bari, Ummi ki kwata kiyi bacci”

    A’a ta fada ahankali sannan ta cigaba da abin da take”

   Ajiyan zuciya yayi sannan ya ture takardun, hannayen ta ya kama sannan ya hau gadon ya jawota jikin shi”

  Kan kirjin shi ya kwatar da ita sannan yasa hannun shi ya rukun kumeta, gaba dayan su ajiyan zuciya suke saukewa har bacci ya dauke su”

Bacci me dadi suke wadda har yakai su ga makara rana gatse gatse Abdulmajeed  ya bude idon sa”

  Subuhanallahhi, zame Ummi yayi, ya tashi ya fada toilet “

    Zuwa can ya fito ya daura alwala, adai dai lokacin da Ummi ma ke kokarin tashi”

   Sai bayan sun ida Sallah Abdulmajeed ya duba agogo karfe 7:14am

   Yayi mamaki sosai ahankali ya juya ya kalli Ummi kingani kin sa na makara ko?

STORY CONTINUES BELOW

   Hmmm ai ni ma kai kasani  makara”

  😉OK dai dai kenan, jeki, hada min ruwan wanka inason nafita da wuri”

  Mikewa tayi tashiga toilet ba’jimawa ta fito, mikewa yayi zai shiga yayin da Ummi ta nufi fita”

   Ina kuma zaki?

   Zanje in hadama break fast”

   A’a bazan jira ba Ummi sauri nake, ki zauna kawai ki taimaka min”

   Toh tace sannan ta dawo ta fara gyara dakin”

   Bayan ya gama wanka ya fito yana goge jikin sa, kin kallon shi tayi domin har yanxun bawani sabawa suka yi ba”

    Ta gefen idonta take kallon shi, yayin da gabanta ke dukan uku uku, gaskiya yaya gafjeje ne baka gane han saiya tube🤭 , Allah Allah take karya kirata yana cikin wannan halin, zuwa can kuwa ya kira sunanta  dan haka tai saurin zabura tare waigowa”

   Zo mana”

   Dakewa tayi tare da karasawa gaban shi acikin zuciya take addu’an Allah kasa duk abin da yace namishi ya zama me sauki agare ni”

    Tunda bazaki taimaka min ba to ki dauko min kayan da zan saka”

    Wucewa tayi ta dauko kayan ta dawo gaban shi ta tsaya, sannan ta ajiye kayan agefen gado, hannu ya miko mata dan haka ta dauki wandon ta mika masa, kanta akasa taga ya sake miko mata hannu, rigar ta dauka ta sake mika masa”

    Bayan ya saka yace”

   Ko zaki taimaka ki ballemin boturan?

    Matsawa tayi ahankali ta fara sakawa, idonta na kasa alamar tanajin kunya”

    Shiko tuda ta fara sakawa kallonta yake yana murmushi, inama ina samun haka kullum ai da tuni nayi kiba, idon shi akanta yace”

   Ummi yanaga kamar kunyata kikeji ne??

    A’a

    Toh dago idon ki kikalle ni,

  Ahankali ta dago ta kalle shi”

  Murmushi yayi sannan yace”

   Ni dai na hango kunya a idonki”

   Juyawa tayi tare da fadin”

   Idonka be gaya maka gaskiya ba”

   OK toh zangani ai Allah ya kaimu anjima”

    Yau Abdulmajeed cikin anna shiwa ya gama shirin sa tare suka fito har ya shiga motar shi ya zauna Ummi tace”

    Yaya dan Allah inason zan fita”

    Nan danan ya hade fuska, ki fita kije ina”

    Gidan Hajiya zanje, da yamma saikazo gidan Umma ka dauki ni”

  OK kice gantali zaki, to bari kiji nifa ban son yawo, komai nawa atsari yake, idan zaki fita ki gaya min tun ana saura kwana 3, idan bakiyi hakan ba karma ki tambaye ni dan bazan bari ba”

    Bata nuna komai ba, tace tam kawai fuskan ta dauke da murmushi ta sake cewa sai kadawo Allah ya tsare”

   Ameen yace, harta juya yaga kamar be kyautaba dan haka atake yaiwa hajiya waya”

    Hajiya mutuniyar ki fa bata da lafiya tun jiya, kuma tace ke take son gani”

  Kirji hajiya ta dafe kardai zancen dana mata jiya ya tada mata hankali”

   Wanne mgn kenan Hajiya?

   Zancen karin auren ka mana”

   Toh kudai kuka sani ni bana ma gida……

STORY CONTINUES BELOW

   Katse kiran tayi dan haka ya tabbatar zatazo sannan ya fice agidan, tare da addu’a Allah yasa Ummi ta iya jure Ummarni sa domin so yake yagani tayi hankali ko har yanzun da saura”

   Be dade ta fitaba Hajiya ta iso”

   Samun Ummi tayi tana ta aikace aika centa dan haka ta saki baki”

   Murmushi Ummi tayi tare da fadin”

    Sannu da zuwa hajiya kamar kinsan inason ganin ki, dazon ma fa nacewa yaya zanzo ya hana”

   Hmmm lallai bawan Allah ya baci da karya, cemin yayi baki lafiya”

  Murmushi Ummi tayi lfyta lau hajiya

   Wlh harna dauka zancen dana miki ne jiya”

   A’a hajiya aina tambaye shi, kuma ya gaya min da gaskene, kwalkwal tayi da idonta sannan tace”

   Hajiya wallahi ina tausawa kaina, banso kishiya hajiya natsani kishiya”

   Toh ai kinga irinta Ummi tuntuni nake  gaya miki, ki sake jikin ki kijawo hankalin miji ki gareki kika ki”

   Hajiya to aini da gani nake be sona”

Ke dalla can, ke makauniya ce?, Bawan Allah ya dade yana sonki kuma na tabbatar inda kin bashi hadin kai bazai amince da wannan auren ba, gashi lokaci ya kure, kinyi nadama alokacin dabe da amfani”

  Nifa Hajiya ba tun yau nayi nadama ba, kawai sakin mun fuskan da bayayi ya hana ni sakin jiki dashi Hajiya ko fah dariya bayayi, sai yaga dama”

   Wai ni takwara ina ruwanki da rashin dariyar bawan Allah ne??, kowa fah da halin sa, baki mai abin dariya ba sai ya kama dariya?, koko so kike yana tafe yana washe baki saika ce sabon mahaukaci?

    Hmmm Hajiya baki fahimce ni bane”

  A’a takwara mijin kine idan kina son yayi dariya kiyi masa abun dariyar ki gani, ke idan kin so cikin kwanaki zaki canza shi, karki yadda wata tazo ta kwace miki miji”

   Toh haji ni yanzun yaya zanyi”

   Hmmm kedai takwara kwata kwata baki da wayo, duk abin da kika kula yafi so shi zaki masa, karki kula rashin mgnr sa, ba ruwan ki da daure fuskan sa, kedai yimai abin da ya kamata kiga ikon Allah, wlh ko rawa kikace yayi yi ze yi”

   Hmmm Yaya ne zai min rawa?

Duk wani daurewan shi da zaran kin shige mishi zai bari, kina abu sai kace wacce bata taba aure ba”

  Hajiya bazaki gane ba, shifa Mukhtar yana da sanyi, yaya ko ya cika zafi, kuma lokacin ina gidan Mukhtar komai shi yake min, girkine kawai nake yi wani lokacin ma tare mukeyi, Hajiya ko ruwan wanka shi yake hadamin”

  A lallai kice shiya bataki, to in zaki datse damtse gara ki datse dan bawan Allah bazai yadda da wannan iskancin ba, yaushe zaki zauna miji ya miki komai?  Maza ki  canza tunani ki lura da abin da yake so ki ringa yi masa karki yadda daidai darana daya kimai musu, kinaji ko?

   Naji hajiya nagode insha Allahu zan gyara”

   Mikewa tayi ni zan koma

  Itama Ummi mikewa tayi tabi bayanta toh hajiya ki gaida gida”

     Bayan hajiya ta wuce komawa tayi taci gaba da aikinta tana tsaka da aikin wayarta tai kara”

   Umma ce dan haka tai saurin dagawa”

   Ke Ummi kina da labarin Abdulmajeed zaiyi aure??

    Eh Umma naji”

   Au kinji fa kika ce?, tun yaushe kika ji baki fadamin ba”

   Ai Umma nima jiya Hajiya ke gaya min da daddare kuma shima ya fada min”

   Tabb, lallai Ummi baki da hankali, shine kika zauna hankalin ki kwance?

   Kwalkwal tayi da ido sannan tace”

  Umma wlh hankalina ba akwance yake ba, kawai ban san yadda zan yi bane?

    Tabb lallai to daya gaya miki me kikace masa?

   Hawaye ne ya zubo daga idon Ummi tasa hannunta ta share sannan tace”

   Toni me zance masa Umma, ban isa na hanashi ba Umma bance komai ba”

   Maza maza kizo ina son ganin ki?

    To ai baya nan ya tafi aiki”

  Shiru Umma tayi zuwa can tace”

   Shikenan ina jiran ki gobe”

    Ahankali tace”

   Umma gobe ma bazan zoba dan bazai bariba, yace min inzan fita infada mai kwana uku kafin ranan”

   Salati Umma tayi sannan tace”

   Lallai Abdulmajeed ya karo wulakanci tun kafin ayi auren ma kenan?, wato har ya lura kin kamu da sonshi, katse kiran tayi tana cigaba da fada”

 

      *****

Shikuwa Abdulmajeed daga gurin aiki gidan Momy ya wuce”

    Yau ne ya shirya zai fara shiryawa Momy dabaran shi”

  Cikin dakinta ya sameta bayan sun gaisa ya zauna tare da rasa ta ina zai fara”

   Muryan Momy yaji tace”

  Kana zuwa wajen Bilkisun kuwa ?

   Eh Mommy ina zuwa, yauma naso naje, amman inason na koma gida da wuri dan nabar Ummi bata jin dadi”

    Ayya Allah ya sauwa ke”

  Ameen yace, sai dai Ba haka yaso ba,  so yayi ta tambaye shi abin da yake damun ta”

  Shiru suka sake yi ganin Mommy bata da niyyar mgn yasake cewa”

   Mommy kusan sati 2 kenan bata da lafiya”

   Wanne irin kallo tamai sannan tace”

   Allah sarki gobe ka daure kaje ka dubo Bilkisun, inka koma gida kama Ummi sannu”

   Shiru yayi domin shiba haka yaso ba, ina mata  mgn tamin wani zance daban, juyawa yayi ya kalli Mommy ta dauke kai can gefe”

   Yanke shawara yayi da zuciyar shi kawai ya gaya mata”

    Sun kuyar dakai yayi sannan yace”

   Mommy Ummi fah ciki gareta”

*Mmn Yazeed*🔥 🔥🔥🔥🔥🔥

*KOWANNE BAKIN WUTA*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥

    ( da nashi hayakin)

💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by

    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*

    *93 to 94*

Shiru tayi dan haka ya sake cewa”

    Ko akwai abun  da kike so ne?

   A’a ta fada ahankali”

   OK to sai da safe”

  Kashewa tayi batare da ta amsa ba”

   Wayar yabi da kallo fuskan shi dauke da murmushi”

   Ga dukkan alamu akwai alamun nasara, tunuwa yayi da mgnr Mommy gaskiya inda ace Ummi tana kula dani yadda ya kamata bani da ra ayin tara mata barkatai, Nafisa ma dana ce zan aure tausaya mata nake kawai, ya zama lallai inyi auren kamar yadda Mommy ta fada, Dan Ita Ummi ta fiye son jikinta da yawa”+

   Da wannan tunanin bacci ya kwashe shi”

    Washe gari bayan ya tashi aiki ya wuce gidan Su Ummi”

  Umma ya samu afalon bayan ya gaidata ya kara mata ta’aziyar Ahmad “

   Cikin sakin fuska ta amsa sannan taitamai godiya tare da sa mai Albarka”

   Zuwa can ta mike tana kwalawa Ummi kira”

   Ba jimawa ta fito suna hada ido tace”

  Sannu da zuwa yaya”

   Yauwa sannu Ummi ya gida, ya kuma karin hakuri”

  Alhamdulillahi”

   Ido ya zuba mata zuwa can yasake cewa”

   Yanaga kin rame kina tunani ko?

  Sunkuyar da kanta tayi kasa sannan tace”

Bana tunani yaya, zuciyata tafi jin dadi yanzun akan sadda yake garin nan, natsuwa ne dai kasan sai ahankali, karashe mgnr tayi cikin zubuwan hawaye”

   Ajiyan zuciya Abdulmajeed yayi sannan ya tashi ya koma dafda ita ya zauna tare da jawota jikin shi”

    Yana shafa bayan ta yake fadin kiyi hakuri kinji ko, komai mukaddari ne daga Allah, Allah yasa hakan shine mafi alheri”

   Kara fashewa tayi da kuka tana cewa”

  Shine ma yaya”

   Ya isa haka, ki daina kuka, wlh natsana inga kina zubar da hawayen ki, kisan abin da nakeji kuwa?

      Cikin sauri ta kalle shi , acikin zuciyanta tace”

  Gaskiya yaya mutum ne, samun me irin halin sa sai antona, abun da Yaya Abdulmajeed yayi min Mukhtar bazai iya yin irinsa ba, a da na jahilce shi ne kawai, matsalar sa kawai bashi da sakin fuska ne, kafin kaga dariyar sa da wuya, sabanin Mukhtar da ko da yaushe fuskan sa asake take”

   Tana tsaka da wannan tunanin ya dagota daga jikin shi ya kalleta tare da fadin”

   Dan Allah Ummi karki sake zubar da hawayen ki, kiji ko?

   Dakai ta amsa mai, sannan ya sake cewa”

    Wani abu na damun ki?, baki jin ko ina na miki ciwo?

    Kai ta sake daga mai alamar eh”

   Ki bude baki kiyi min magana mana”

    Ba inda ke min ciwo”

STORY CONTINUES BELOW

   OK toni zan tafi insha Allahu gobe zan zo”

    Wani irin taji azuciyan ta memakon yace tazo suje gida, towai me yake nufi ne?

    Har yakai bakin kofa yayi tonanin be dace yana barin ta da damuwa ba akalla tana bukatar kulawa dan haka ya waigo yace”

    Yaushe zaki koma gida ne?

    Sunkuyar dakai tayi tana wasa da yatsunta har saida ya sake cewa”

    Dake fah nake”

   Kanta akasa batare da ta dagoba tace”

     Duk randa kace”

    Shiru yayi sannan yace”

    A’a nafi son ki fada da bakin ki, dan bana son na takura ki”

   Yaya ka fada kawai duk ranan da kace shikenan “

   

    OK toh jibi yayi miki?

  Kai ta daga alamar eh”

   Sallama ya sake mata ya fice”

   Tsaki taja sannan ta mike tabar falon tana kara tura baki gaba

   Abdulmajeed kuwa yana tafe yana murmushi cikin motar sa da alama Ummi ta fara hankali”

   Gidan Mommy ya nufanufa, ganin yaddda ta tarbeshi abun yaba shi mamaki, domin shi yazo ne ya dada bata hakuri amman sai yaga tanata murnan ganin shi”

   Bayan sun gaisa ya zauna tare da sunkuyar dakai”

   Kallon shi Mommy tayi tace”

   Kanaji ko Abdulmajeed daman ko bakazo ba zan kiraka, akan mgnr auren dana maka, inason gobe kaje ka gano yariyar dana zaba maka”

   Cikin sauri ya dago ya kalli Mommy yace”

  Mommy amman fa na roka abari tukuna akwana biyu kafin afara mgnr auren k…..

    Dakata Abdulmajeed, ka huta?, kajiya kayi?, inaso na nuna maka na isa dakai ne, gobe nake son kaje kaga yariyar   kuma umarni nabaka”

    Shiru yayi zuwa can yace”

   Shikenan Mommy goben zanje a ina yariyar take?

    Nan ne makota bawani waje bane me nisa, nayi magana da mahaifiyarta kilama zaka santa yariyar nan gidan alhaji Bala sunan yariyar Bilkisu”

   Bansan ta ba Mommy, ni ina zan santa kallon mata nake yi”

  Cikin ido Mommy ta kalle shi Bilkisun Alhaji Balan ce baka sani ba?

   Toh aini Mommy ko alhaji Balan ma bansan shi ba”

   Zaka san shi ai dan ubanka, mikewa tayi tana fadin”

    Inajiran ka goben”

    Mikewa yayi ransa ajagule ya nufi gida, koda ya isa gida tunanin sa kenan, afali yace”

   Ina kokarin shawo kan Ummi Mommy kuma ta tsiro da rigima, kwata kwata mani tunanina bekai wajen karin auren ba, idan ma auren zanyi ai gara in aure nafisa koba komai mun saba, yanzun ta wacce hanya zan bulowa Mommy ta janye zancen auren nan”

    Shiru yayi sannan yace”

   Nasan hanyan da zan bolo mata”

   Washegari bayan ya dawo aiki gida ya wuce, wanka ya sake sannnan ya dauki dalleliyar shadda ya sanya tare da feshe jikinsa da turare”

    Gidan Mommy ya isa, kallo daya tamai ta saki murmushi domin rabon da ta ganshi da manyan kaya ta manta”

   Bayan ya gaidata tace”

STORY CONTINUES BELOW

  Haba, ko kaifa, gashi tun kafin ma ayi auren ka fara kyallin goshi”

   Murmushi yayi tare da sunkuyar da kai”

   Itama cikin fara’a tace kwatan tama zanyi koko Hassana ta raka ka”

   A’a kidai kwatanta min kawai”

    Kwatan tamai tayi nan yace yagane gidan ya tashi ya fita cikin sauri”

    Kallon bayan shi tayi tace”

    Kaga min munafukin yaro, yana nunawa beso amman ya ciwo uban kwalliya, sai kace zashi dauri aure”

    Yana fita ya maida fuskan shi ya daure, har ya shiga haraban gidan fuskan tamau take”

    Megadin yama mgn cewa yace ga bako yazo, ba jimawa ya dawo yace tana zuwa”

   Motar shi ya koma ya zauna, ba jimawa wata buduwar yariya ta fito, kallonta yai tayi harta iso gaban shi tare da sallama”

    Daker ya amsa sallamanta”

   Wani irin kallo tamai sannan tace”

   Ina wuni?

   Lfy”

   Dagowa tayi ta sake kallon shi, nan sukayi ido biyu domin Abdulmajeed kure ta da ido yayi yana kare mata kallo”

   Cikin sauri ta maida idonta kasa”

   Abdulmajeed kuwa azuciyan shi yake cewa”

   Babu laifi tana da kyau, amman ni bata min ba,  batamin ba kwata kwata ban son ta”

    Ganin ta sunkuyar dakai yasa ya dauke kan shi sannan yace”

   Nasan kinsan da zuwa na ko?

    Dakai ta amsa domin tsoron hada ido take dashi”

    Toh idan an tambaye ki saiki fada musu nazo nakuma ganki”

    Dakai ta sake amsawa, motar shi yake kokarin ja dan haka tai sauri ta shige gida”

   Gidan Mommy ya koma sai da ya tsaya ya kirkiri murmushi sannan ya shiga”

   Mommy ma naganin sa cikin wannan halin farinciki ya kamata”

   Ka dawo?, ka ganta ko?

    Yana Sosa kai yace”

   Naganta mommy”

    Toh ina fatan dai tayi ma”

   Cikin yana yin dake nuna yanJin kunya yace”

   Tayi Mommy yariyar tana da kunya sosai, shiyasa ma kiga ban dade ba, ta kasa mgn sai jin kunya ta take”

   Kara washe baki Mommy tayi ai tun kafin ka dawo mahaifiyarta tamin waya cewa kaxo”

  Allah sarki,  gaski dagani gidan suna da tarbiya”

  Ai Abdulmajeed abun da yaja hankalina kenan, kaga sai kuyi zaman ku, itama Ummi n ai bawai ban sonku tare bane, zaman naku ne naga tamkar ba aure koke yi ba, abun da nakula kai kadai ke son Ummi, kuma ni inason naga jikokina”

   Kamar zaiyi mgn sai kuma yace, karna lalata shiri na”

   Mommy ce taci gaba da cewa”

   Yaushe kake ganin za’ayi auren”

   Sunkuyar dakai yayi, Mommy inason kibar min komai ahannu na, inason mu fahimci juna sosai dan bosan asamu Matsala, dazaran mun gama fahimtan juna zan gabatar dakaina gurin babanta da kaina

STORY CONTINUES BELOW

    Shuru Mommy tayi kamar bazatai magana ba zuwa can tace”

   Shikenan amman duk abun da zaka yi ga gama shi cikin watan nan”

   Insha Allhahu Mommy komai ze warware”

   Daha suka rabo da Mommy tana ta samai Albarka”

    Gidan su su Ummi ya wuce”

   Sai dai yau be shiga cikin ba, yana zaune cikin motar sa ya kirata awaya, bayan ta daga yace ki fito ina jiranki a mota”

   Toh kawai tace”

    Sannn ta mike ta dauki mayafinta, kitchen tashiga ta sanarwa Umma sannan ta fito”

   Gaban motar ta tsaya ta gaida shi bayan ya amsa tace”

   Toh meye kuma natsaya awaje, kasan idan Abba ya samemu anan zaiyi fada ko?

  Hannun shi ya mika alaman kira yace”

  Xo, matso nan”

   Ahankali takara  matsawa”

  Karaf yayi ya riki hannunta, cikin ido ya kalleta, na cenza shawara ne Ummi, kizo mu koma gida yau”

   Shiru tayi tana tunani, ita kanta ta kosa ta koma gida, ahankali tace”

   Nariga nacewa Umma sai gobe fah, bakai kace haka ba?

    Nina ce, Na zanza shawara ne, kuma ai ita Umma ba ruwanta, je ki mata sallama kawai mutafi gobe na dawo na dauki kayan ki”

    Juyawa tayi ta koma gidan, wannan karon afalon ta samu Umma”

   Suna hada ido tace”

   Umma kinji kuma yaya wai yaxone mutafi gida”

   Murshi Umma tayi sannan tace”

   Toh Ummi ku gaida gida, kayan ki fah?

   Cikin jin kunya tace”

   Yace gobe zaizo ya dauka

   Toh yayi kyau sai da safe”

  Juyawa tayi ta fita, tararwa tayi ya bude murfin motar yana tsaye tana shiga ya mayar ya rufe sannan ya zagaya ya shiga”

   Koda suka isa gida dakisan ya Shiga yana fadin bari na dan watsa ruwa”

    Tunda ya shige bata sake ganin keyarshi ba sai washegari da safe bayan ya gama shirin fita aiki”

  Karyawa kawai yayi ya mata sallama ya fice”

    Mamaki tayi sosai atunanin ta matsuwa ce tasashi ya daukota amman taga ya shareta”

  Tun daga ranan ya tsuri yin haka, gurin cin abin ci kawai suke haduwa, har suka kwashe tsayon wata daya’

    Zuwa wannan lokacin Ummi ta fahimci tana da ciki wadda take tunanin zaiyi wata 2 sai dai ta rasa yadda zata yi ta sanarwa Abdulmajeed, ganin inda yanzun yake tsare gida tamkar bashi bane yake mata magiya adah”

    Ta yaya zanyi na sanar mai, me zan fara cewa😔”

   Tana cikin wannan tunanin taji ana kiranta awaya cikin sauri ta dauka tare da fadin”

    Hajiya kinan? Ni nama manta dake”

   Shiru tayi tana sauraran Hajiya, zuwa can ta dafa kirji tare da fadin”

   Hajiya waye ya fada miki?

    Shiru ta sake yi, bayan tagama sauraran hajiya ta kashe wayar sannan ta nufi dakin Abdulmajeed “

STORY CONTINUES BELOW

    Lokacin 9:30 na dare dan haka ya riga yayi shirin kwanciya”

   Ganin Ummi yasa shi yadan zaro ido, domin ya dade yana tsammanin shigowanta”

    Zama tayi abakin gadon shikowa ya daure fuskan sa tare da fadin”

   Lafiya kuwa”

  Lafiya lau, nazo ne inason muyi mgn”

   Tashi yayi ya zauna tare da fadin”

    Ina jin ki”

  Shiru tayi tare da sunkuyar dakai”

   Ke nake sauraro?

   Murya kasa kasa tace”

   Dama zan gaya maka ne, shiru ta sake yi”

    Me zaki gaya min?

    Kasa ta kara yi da idonta tace”

   Ina da ciki”

   Da sauri ya kalleta da murmushi akan fuskan shi yace”

   Na sani ai, wani abu ne?

   Itama cikin sauri ta kalle shi tare da mamaki to yaya akayi ya sani?

   Matsowa ya kara yi kusa da ita ina nufin akwai inda yake miki ciwo ne??

    A’a nadai gaya maka ne”

   OK na sani ai”

   Shiru tayi zuwa can tace”

   Yaya wai dagaske ne zakayi aure?

*Mmn Yazeed*🔥 🔥🔥🔥🔥🔥

*KOWANNE BAKIN WUTA*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥

    ( da nashi hayakin)

💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by

    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*

    *93 to 94*

Shiru tayi dan haka ya sake cewa”

    Ko akwai abun  da kike so ne?

   A’a ta fada ahankali”

   OK to sai da safe”

  Kashewa tayi batare da ta amsa ba”

   Wayar yabi da kallo fuskan shi dauke da murmushi”

   Ga dukkan alamu akwai alamun nasara, tunuwa yayi da mgnr Mommy gaskiya inda ace Ummi tana kula dani yadda ya kamata bani da ra ayin tara mata barkatai, Nafisa ma dana ce zan aure tausaya mata nake kawai, ya zama lallai inyi auren kamar yadda Mommy ta fada, Dan Ita Ummi ta fiye son jikinta da yawa”

   Da wannan tunanin bacci ya kwashe shi”

    Washe gari bayan ya tashi aiki ya wuce gidan Su Ummi”

  Umma ya samu afalon bayan ya gaidata ya kara mata ta’aziyar Ahmad “

   Cikin sakin fuska ta amsa sannan taitamai godiya tare da sa mai Albarka”

   Zuwa can ta mike tana kwalawa Ummi kira”

   Ba jimawa ta fito suna hada ido tace”

  Sannu da zuwa yaya”

   Yauwa sannu Ummi ya gida, ya kuma karin hakuri”

  Alhamdulillahi”

   Ido ya zuba mata zuwa can yasake cewa”

   Yanaga kin rame kina tunani ko?

  Sunkuyar da kanta tayi kasa sannan tace”

Bana tunani yaya, zuciyata tafi jin dadi yanzun akan sadda yake garin nan, natsuwa ne dai kasan sai ahankali, karashe mgnr tayi cikin zubuwan hawaye”

STORY CONTINUES BELOW

   Ajiyan zuciya Abdulmajeed yayi sannan ya tashi ya koma dafda ita ya zauna tare da jawota jikin shi”

    Yana shafa bayan ta yake fadin kiyi hakuri kinji ko, komai mukaddari ne daga Allah, Allah yasa hakan shine mafi alheri”

   Kara fashewa tayi da kuka tana cewa”

  Shine ma yaya”

   Ya isa haka, ki daina kuka, wlh natsana inga kina zubar da hawayen ki, kisan abin da nakeji kuwa?

      Cikin sauri ta kalle shi , acikin zuciyanta tace”

  Gaskiya yaya mutum ne, samun me irin halin sa sai antona, abun da Yaya Abdulmajeed yayi min Mukhtar bazai iya yin irinsa ba, a da na jahilce shi ne kawai, matsalar sa kawai bashi da sakin fuska ne, kafin kaga dariyar sa da wuya, sabanin Mukhtar da ko da yaushe fuskan sa asake take”

   Tana tsaka da wannan tunanin ya dagota daga jikin shi ya kalleta tare da fadin”

   Dan Allah Ummi karki sake zubar da hawayen ki, kiji ko?

   Dakai ta amsa mai, sannan ya sake cewa”

    Wani abu na damun ki?, baki jin ko ina na miki ciwo?

    Kai ta sake daga mai alamar eh”

   Ki bude baki kiyi min magana mana”

    Ba inda ke min ciwo”

   OK toni zan tafi insha Allahu gobe zan zo”

    Wani irin taji azuciyan ta memakon yace tazo suje gida, towai me yake nufi ne?

    Har yakai bakin kofa yayi tonanin be dace yana barin ta da damuwa ba akalla tana bukatar kulawa dan haka ya waigo yace”

    Yaushe zaki koma gida ne?

    Sunkuyar dakai tayi tana wasa da yatsunta har saida ya sake cewa”

    Dake fah nake”

   Kanta akasa batare da ta dagoba tace”

     Duk randa kace”

    Shiru yayi sannan yace”

    A’a nafi son ki fada da bakin ki, dan bana son na takura ki”

   Yaya ka fada kawai duk ranan da kace shikenan “

   

    OK toh jibi yayi miki?

  Kai ta daga alamar eh”

   Sallama ya sake mata ya fice”

   Tsaki taja sannan ta mike tabar falon tana kara tura baki gaba

   Abdulmajeed kuwa yana tafe yana murmushi cikin motar sa da alama Ummi ta fara hankali”

   Gidan Mommy ya nufanufa, ganin yaddda ta tarbeshi abun yaba shi mamaki, domin shi yazo ne ya dada bata hakuri amman sai yaga tanata murnan ganin shi”

   Bayan sun gaisa ya zauna tare da sunkuyar dakai”

   Kallon shi Mommy tayi tace”

   Kanaji ko Abdulmajeed daman ko bakazo ba zan kiraka, akan mgnr auren dana maka, inason gobe kaje ka gano yariyar dana zaba maka”

   Cikin sauri ya dago ya kalli Mommy yace”

  Mommy amman fa na roka abari tukuna akwana biyu kafin afara mgnr auren k…..

    Dakata Abdulmajeed, ka huta?, kajiya kayi?, inaso na nuna maka na isa dakai ne, gobe nake son kaje kaga yariyar   kuma umarni nabaka”

    Shiru yayi zuwa can yace”

STORY CONTINUES BELOW

   Shikenan Mommy goben zanje a ina yariyar take?

    Nan ne makota bawani waje bane me nisa, nayi magana da mahaifiyarta kilama zaka santa yariyar nan gidan alhaji Bala sunan yariyar Bilkisu”

   Bansan ta ba Mommy, ni ina zan santa kallon mata nake yi”

  Cikin ido Mommy ta kalle shi Bilkisun Alhaji Balan ce baka sani ba?

   Toh aini Mommy ko alhaji Balan ma bansan shi ba”

   Zaka san shi ai dan ubanka, mikewa tayi tana fadin”

    Inajiran ka goben”

    Mikewa yayi ransa ajagule ya nufi gida, koda ya isa gida tunanin sa kenan, afali yace”

   Ina kokarin shawo kan Ummi Mommy kuma ta tsiro da rigima, kwata kwata mani tunanina bekai wajen karin auren ba, idan ma auren zanyi ai gara in aure nafisa koba komai mun saba, yanzun ta wacce hanya zan bulowa Mommy ta janye zancen auren nan”

    Shiru yayi sannan yace”

   Nasan hanyan da zan bolo mata”

   Washegari bayan ya dawo aiki gida ya wuce, wanka ya sake sannnan ya dauki dalleliyar shadda ya sanya tare da feshe jikinsa da turare”

    Gidan Mommy ya isa, kallo daya tamai ta saki murmushi domin rabon da ta ganshi da manyan kaya ta manta”

   Bayan ya gaidata tace”

  Haba, ko kaifa, gashi tun kafin ma ayi auren ka fara kyallin goshi”

   Murmushi yayi tare da sunkuyar da kai”

   Itama cikin fara’a tace kwatan tama zanyi koko Hassana ta raka ka”

   A’a kidai kwatanta min kawai”

    Kwatan tamai tayi nan yace yagane gidan ya tashi ya fita cikin sauri”

    Kallon bayan shi tayi tace”

    Kaga min munafukin yaro, yana nunawa beso amman ya ciwo uban kwalliya, sai kace zashi dauri aure”

    Yana fita ya maida fuskan shi ya daure, har ya shiga haraban gidan fuskan tamau take”

    Megadin yama mgn cewa yace ga bako yazo, ba jimawa ya dawo yace tana zuwa”

   Motar shi ya koma ya zauna, ba jimawa wata buduwar yariya ta fito, kallonta yai tayi harta iso gaban shi tare da sallama”

    Daker ya amsa sallamanta”

   Wani irin kallo tamai sannan tace”

   Ina wuni?

   Lfy”

   Dagowa tayi ta sake kallon shi, nan sukayi ido biyu domin Abdulmajeed kure ta da ido yayi yana kare mata kallo”

   Cikin sauri ta maida idonta kasa”

   Abdulmajeed kuwa azuciyan shi yake cewa”

   Babu laifi tana da kyau, amman ni bata min ba,  batamin ba kwata kwata ban son ta”

    Ganin ta sunkuyar dakai yasa ya dauke kan shi sannan yace”

   Nasan kinsan da zuwa na ko?

    Dakai ta amsa domin tsoron hada ido take dashi”

    Toh idan an tambaye ki saiki fada musu nazo nakuma ganki”

    Dakai ta sake amsawa, motar shi yake kokarin ja dan haka tai sauri ta shige gida”

STORY CONTINUES BELOW

   Gidan Mommy ya koma sai da ya tsaya ya kirkiri murmushi sannan ya shiga”

   Mommy ma naganin sa cikin wannan halin farinciki ya kamata”

   Ka dawo?, ka ganta ko?

    Yana Sosa kai yace”

   Naganta mommy”

    Toh ina fatan dai tayi ma”

   Cikin yana yin dake nuna yanJin kunya yace”

   Tayi Mommy yariyar tana da kunya sosai, shiyasa ma kiga ban dade ba, ta kasa mgn sai jin kunya ta take”

   Kara washe baki Mommy tayi ai tun kafin ka dawo mahaifiyarta tamin waya cewa kaxo”

  Allah sarki,  gaski dagani gidan suna da tarbiya”

  Ai Abdulmajeed abun da yaja hankalina kenan, kaga sai kuyi zaman ku, itama Ummi n ai bawai ban sonku tare bane, zaman naku ne naga tamkar ba aure koke yi ba, abun da nakula kai kadai ke son Ummi, kuma ni inason naga jikokina”

   Kamar zaiyi mgn sai kuma yace, karna lalata shiri na”

   Mommy ce taci gaba da cewa”

   Yaushe kake ganin za’ayi auren”

   Sunkuyar dakai yayi, Mommy inason kibar min komai ahannu na, inason mu fahimci juna sosai dan bosan asamu Matsala, dazaran mun gama fahimtan juna zan gabatar dakaina gurin babanta da kaina

    Shuru Mommy tayi kamar bazatai magana ba zuwa can tace”

   Shikenan amman duk abun da zaka yi ga gama shi cikin watan nan”

   Insha Allhahu Mommy komai ze warware”

   Daha suka rabo da Mommy tana ta samai Albarka”

    Gidan su su Ummi ya wuce”

   Sai dai yau be shiga cikin ba, yana zaune cikin motar sa ya kirata awaya, bayan ta daga yace ki fito ina jiranki a mota”

   Toh kawai tace”

    Sannn ta mike ta dauki mayafinta, kitchen tashiga ta sanarwa Umma sannan ta fito”

   Gaban motar ta tsaya ta gaida shi bayan ya amsa tace”

   Toh meye kuma natsaya awaje, kasan idan Abba ya samemu anan zaiyi fada ko?

  Hannun shi ya mika alaman kira yace”

  Xo, matso nan”

   Ahankali takara  matsawa”

  Karaf yayi ya riki hannunta, cikin ido ya kalleta, na cenza shawara ne Ummi, kizo mu koma gida yau”

   Shiru tayi tana tunani, ita kanta ta kosa ta koma gida, ahankali tace”

   Nariga nacewa Umma sai gobe fah, bakai kace haka ba?

    Nina ce, Na zanza shawara ne, kuma ai ita Umma ba ruwanta, je ki mata sallama kawai mutafi gobe na dawo na dauki kayan ki”

    Juyawa tayi ta koma gidan, wannan karon afalon ta samu Umma”

   Suna hada ido tace”

   Umma kinji kuma yaya wai yaxone mutafi gida”

   Murshi Umma tayi sannan tace”

   Toh Ummi ku gaida gida, kayan ki fah?

   Cikin jin kunya tace”

   Yace gobe zaizo ya dauka

   Toh yayi kyau sai da safe”

  Juyawa tayi ta fita, tararwa tayi ya bude murfin motar yana tsaye tana shiga ya mayar ya rufe sannan ya zagaya ya shiga”

   Koda suka isa gida dakisan ya Shiga yana fadin bari na dan watsa ruwa”

    Tunda ya shige bata sake ganin keyarshi ba sai washegari da safe bayan ya gama shirin fita aiki”

  Karyawa kawai yayi ya mata sallama ya fice”

    Mamaki tayi sosai atunanin ta matsuwa ce tasashi ya daukota amman taga ya shareta”

  Tun daga ranan ya tsuri yin haka, gurin cin abin ci kawai suke haduwa, har suka kwashe tsayon wata daya’

    Zuwa wannan lokacin Ummi ta fahimci tana da ciki wadda take tunanin zaiyi wata 2 sai dai ta rasa yadda zata yi ta sanarwa Abdulmajeed, ganin inda yanzun yake tsare gida tamkar bashi bane yake mata magiya adah”

    Ta yaya zanyi na sanar mai, me zan fara cewa😔”

   Tana cikin wannan tunanin taji ana kiranta awaya cikin sauri ta dauka tare da fadin”

    Hajiya kinan? Ni nama manta dake”

   Shiru tayi tana sauraran Hajiya, zuwa can ta dafa kirji tare da fadin”

   Hajiya waye ya fada miki?

    Shiru ta sake yi, bayan tagama sauraran hajiya ta kashe wayar sannan ta nufi dakin Abdulmajeed “

    Lokacin 9:30 na dare dan haka ya riga yayi shirin kwanciya”

   Ganin Ummi yasa shi yadan zaro ido, domin ya dade yana tsammanin shigowanta”

    Zama tayi abakin gadon shikowa ya daure fuskan sa tare da fadin”

   Lafiya kuwa”

  Lafiya lau, nazo ne inason muyi mgn”

   Tashi yayi ya zauna tare da fadin”

    Ina jin ki”

  Shiru tayi tare da sunkuyar dakai”

   Ke nake sauraro?

   Murya kasa kasa tace”

   Dama zan gaya maka ne, shiru ta sake yi”

    Me zaki gaya min?

    Kasa ta kara yi da idonta tace”

   Ina da ciki”

   Da sauri ya kalleta da murmushi akan fuskan shi yace”

   Na sani ai, wani abu ne?

   Itama cikin sauri ta kalle shi tare da mamaki to yaya akayi ya sani?

   Matsowa ya kara yi kusa da ita ina nufin akwai inda yake miki ciwo ne??

    A’a nadai gaya maka ne”

   OK na sani ai”

   Shiru tayi zuwa can tace”

   Yaya wai dagaske ne zakayi aure?

*Mmn Yazeed*🔥 🔥🔥🔥🔥🔥

*KOWANNE BAKIN WUTA*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥

    ( da nashi hayakin)

💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by

    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*

 

Dedicated👇🏻

     *Classic Feedoh*👌🏻

            

             97

Daga sama taji maganar dan haka tai saurin juyowa ta kalle shi, kana nufin Ummi ce ke da ciki??

   Kasa yakara yi sosai da idon sa sannan yace”

    Eh”

Shiru tayi zuwa can tace”

   Toh Allah ya rabasu lafiya”

   Can kasan makoshi yace ameen”

  Shiru suka sake yi, sai dai abin daya bashi mamaki Mommy bata wani nuna murnan ta ba, bayan kuma tace tana son taga ‘ya’,yan shi”

   Zuwa can ya mike Mommy sai da safe”

   Toh Allah ya tashe mu lafiya”

   Ficewa yayi dan haka Mommy tabi bayan shi da kallo, tare da fadin”+

Allah sarki, Allah ya jarabce shi da son Ummin nan, jiba shi ko kunya babu wai Ummi fah ciki gareta, duk zufin cikin nashi yau ya ajeshi gefe, sai wani murna yake”

   Murmushi tayi  sannan tace”

  Dana sani na tambaye shi wata nawa ne, mikewa tayi ta nufi daki tana mejin annan shiwa acikin  zuciyanta”

  

      *****

Shima Abdulmajeed gida ya nufa tare da addu’an Allah ya sausauto da zuciyan Mommy”

   Da wannan tunanin ya isa gida, Ummi najin tsayon motar shi ta fito”

   Adai dai lokacin da shima ya fito, kureta da ido yayi  sosai dan haka kunya ta dabai bayeta”

    Fuskan ta dauke da Murmushi takara tare da kokarin amsan jakar dake hannun shi”

   Maza yayi ya mika mata sannan ya hada su ya rungume tare da lumshe idon sa”

   Ahaka suka shiga gidan, afalon ya tsaya zuwa can yajata kan kujera ya zaunar sannan ya kafeta da  ido”

   Kanta a kasa jefi jefi tana tana dagowa ta kalle shi fuskanta dauke da kunya

    Ganin bashi da niyyar bari kuma fuskan shi babu murmushi ko fara’a yasa Ummi ta rasa inda zata yi”

   Dagowa ta sake yi ta kalle shi, dariya ce ta kama ta tai saurin toshe bakin ta tare da fadi”

   Yaya meye haka cinye ni zaka yi ne?

  Idon shi daya ya make mata tare da cigaba da kallon ta”

   Murmushi tayi sannan ta sunkuyar da kanta, zuwa can ta sake dagowa, har yazon be dauke idon shiba dan haka tai saurin saka hannunta ta rufe idanun shi”

  Murmushi yayi sanna yasa hannun shi ya cire nata tare dacigaba da kallonta, cikin dariya tace”

   Yaya wallahi kabari”

  Kafadan shi ya make  guda daya dan haka ta dage ta huramai iskar bakinta”

  Dole yasa ya rufe idon shi, ummi ko mikewa tayi aguje ta bar wajen”

   Yanajin gudunta ya bude idosa fuskan sa dauke da murmushi, mikewa yayi ya wuce dakin sa yana mejin wani irin farin ciki”

   Itama Ummi tana zaune abakin gadon ta tana murmushi tare dajin wani irin son sa me zafi cikin zuciyanta”

STORY CONTINUES BELOW

   Ayanzun ta fara gani mgnr hajiya  na dauka idan narufe mai fuska fada zai min tunda naga fuskan shi babu alamar wasa, sai gashi yana dariya, wato dai ita Hajiya tagama ganu halin sa wata kilama shiyasa take cemai Bawan Allah”

   Wanka ta sake yi duk da cewa kafin Abdulmajeed ya dawo ma tayi wanka, amman hakanan taji tana so ta sake”

   Bayan tagama shiryawa ta nufi dakin Abdulmajeed “

      Zaune ta same shi ya baje takardu agaban shi yana dubawa yana ganin ta ya dago idonsa ya sa akanta kamar yadda yayi dazun”

   Zama tayi tare  dasa hannuwanta ta rufe fuskanta tana fadin”

    Yaya dan Allah ka daina mana”

   Idan kina son na daina saikin daina jin kunya ta”

  Aini daman banjin kunyan ka”

OK toh dago idon ki ki kalle ni”

   Dagowa tayi ta kalkeshi sannan ta maida kanta kasa”

  Ba haka nake so ba, inason ki tsayar da idonki akai nane”

Can kasan makoshi tace”

  Toh ka gama abin da kake tukuna”

  Ina ruwan ki da abin da nake yi”

  Dagowa tayi ta kalle shi, sannan ta mike tsaye toh ina zuwa barin je indawo”

   Hannunta ya rike tare da fadin”

  Ai na rigaki zuwa duniya ni zakima wayau, zo nan ki zauna”

  Murmushi tayi alokacin da yajawota kusa dashi, sannan ya juya ya fara hada takardun sa”

Tare da fadin”

   Hajiya tazo?

   Eh tazo ka fita ba dadewa”

   Ta kyauta, Mommy na gaishe ki”

   Ina amsawa kaje ne”

   Yana kokarin hawa gado yake fadin”

  Daga can nake”

   Shiru tayi yayin da wata zuciyar ke kitsa mata kilama saida yaje gurin yariyar da zai aura”

   Wani kululun bakin ciki taji ya tsaya mata awuya yaki gaba yaki baya”

   Ko yaya yariyar ma take oho, wata kilama tafini kyau, tunanin da Ummi taitayi kenan cikin zuciyanta”

   Yaya zanji ranan danaga yaya da wata, innalillahi wa inna ilaihir raju’un’

    Ahankali taji yace”

  Ummi tunanin me kike?

Mikewa tayi tare da fadin”

   Babu komai”

   A’a Ummi nakula akwai abin dake damun ki”

  Yaya babu abin dake damu na”

   Murmushi yayi sannan ya kalleta yace”

  Kodai kina tunanin wannan tsohowar ne, Ummaye take kowa?, mema kuke ce mata?

  Turbune fuska tayi tare da fadin Allah ya min tsari da ita, wlh ka daina tuna min da ita, dan ko alahira bana fatan Allah ya hadani da ita”

   Can cikin zuciyar shi yayi dariya dan ya tabbatar Ummi tayi nadaman auren Mukhtar”

   Kallon ta ya sake yi, sannan yacije leben sa alokacin da ya tuna lokacin baya, da Ummi taki sa,

  Gyara kwaciyar shi yayi sannan ya jawata jikin shi ya kwantar”

    Kwaciya tayi sannan ta fara hangowa cewa yanzun wata rana yaya zeyi haka da wata, agabana, wata zuciyar ce tace kilama yayi abin da yafi haka”

STORY CONTINUES BELOW

   Innalillahi wa inna ilaihir raju’un ta fada a zahiri”

   Kumatunta ya taba ke menene haka”

   Babu komai yaya”

  Akwai komai Ummi kina salati kina gayamin bako mai, baki da lafiya ne, kare mgn yayi yana taba wuyanta dan haka tai saurin cewa”

Bacci  nake ji”

   Kara rugume ta yayi ajikin shi tare da fadin”

   Yi baccin nata”

   Rufe ido tayi badan baccn takeji ba, ahankali baccin yazo mata”

    Baccin ta yayi nisa, sosai takejin dadin baccinta, can cikin baccin ta farajin wani irin nishi nafita ahankali”

   Kokarin watsakewa ta rafa, sai da ta kasa mutsawa sakamakon wani irin mugun runguma da yayanta ya mata tamkar zai maidata ciki”

    Nan ta fahimci abin dake faruwa dan haka ta fara addu’an Allah ya bata juriya ga  duk abin da yaso yi”

   Yadda abdulmajeed ya rike ce yasa Ummi ta ce azuciyarta yau kashina ya bushe”

    Sai dai abin da yabata mamaki ji tayi ya tsaya cak, dan haka ta bude idonta”

    Sakin ta yayi sannan ya tashi ya sauke kafafuwan shi akasa tare da dafe kanshi da hannuwan shi duk biyun”

    Kallo Ummi tabishi dashi tare da rasa abun yi, zuwa can ta mike ta zauna shiru tayi tana nazari”

   Bayan ta gama kare mishi kallo ta karasa ta kwanta abayan shi”

   Ummi kina baccin ki me dadi nahanaki ko, jeki kwata abunki”

   Acikin raunanan niyar murya tace”

   Yaya inason muyi mgn ne”

  Jeki kwata Ummi sai da safe”

   Kwalkwal tayi da ido yaya ni yanzun nake so”

  Mikewa yayi inazuwa barin shiga toilet “

   Gyara zaman ta tayi tana jiran dawowan shi”

   Koda da ya fito takardun shi na dazon ya kwaso ya fara dubawa”

  Duk abin da yake Ummi na kallon shi acikin zuciyanta tace”

   Har yanxun akwai wani abu azuciyan yaya, daman fa naji su Hassana na cewa yacika rokon tsiya, girgiza kai tayi tare da fadi acikin zuciyanta”

   Dole nasan yadda zanyi domin nashawo kan yaya”

    Kwaciya tayi har bacci ya kwasheta,,

   Washegari da misalin 8:30, Abdulmajeed ne ke sallama da ummi zai wuce aiki”

   Sallaman Umma ne ya maida hankalin su gurin kofar”

    Gadayan su sannu da zuwa suke mata, yayin da take amsawa fuskanta daure”

   Shigowa falon tayi ta xauna yayin da Abdulmajeed ya russuna ya gaidata, 

   Amsawa tayi ba yabo babu fallasa, abdulmajeed ya kula yanayi Umma ya canza amman be kawowa zuciyan shi komai ba, ya juya ya nufi fita”

    Itama Ummi mikewa tayi ga dukkan alama rakiya zata mishi, cikin sauri Umma ta finciki hannun Ummi tare da gallah mata harara”

   Tsayawa tayi cak, tare da fadin”

   Saika dawo, daidai lokacin da Abdulmajeed yasa kafa waje Umma tasa Hannu ta make bakin Ummi”

   Kara tayi tare da rike wajen tana fadin Umma me nayi ne?

   Ubanki kikayi kaga min wawuyar yariya yau na tabbatar baki da hankali, Abdulmajeed din kike yakewo hakora, inace aure zai kara?

   Zama tayi sannan ta yamutsa fuska tace”

  Umma toni ya zanyi?, bansan yadda zanyi ba, dan haka nake addu’an zabin alheri”

  Ahankali Umma tace”

    Ummi kina nufin kin amince zaki zauna da kishiya?, ta yaya zaki fara rayuwa da kshiya Ummi alhalin koni bantaba zama da itaba”

   Hawaye ne suka zobo mata tasa hannunta ta share sannan ta ce”

   Umma in ban zauna ba ina zani”

  Kamota Ummi tayi ta kwatar ajikinta sannan ta ce”

   Ba nufina kibar gidan ki ba, Ummi, kawai ban son ne naji ance wai kece da kishiya”

   Ni abin da nazo nagaya miki shi ne”

    Kije ki ki samu hajiya  ki tasata gaba har sai anjanye zancen auren, ita kadai ce zata iya hanawa”

  Shiru Ummi tayi zuwa can tace”

   Toh Umma ai idan nasa hajiya ta hana auren ban masa adalciba, abu daya kawai nake tsoro, ina gudun kar yaya ya wulakanta ni, badan hakaba babu abin da zai dame ni”

  Baki Umma ta kama lallai Ummi, wato ke ko ajikin ki, tun jiya nake tausaya miki, na kasa bacci ko abinci daker nake hadiya, amman ke kina nan kina mai murmushi”

   Sukuyar dakai Ummi tayi  lokaci tana share hawaye”

   Wasa da hannuta ta fara sannan ta sukuyar da kanta tace”

   Umma ki kwantar da hankalin ki, nina hakura, na lura, yaya duk abin da nake so shi yake min, koda kuwa beson abun, dan haka nima inason na kwatanta mai irin wannan abun, Umma addu’an ki kawai nake bukata, Allah yabani ikon jure wa”

  Mikewa Umma tayi tare da Jan tsaki, shikenan Ummi ni na tafi”

   Har gaban mota tama Umma rakiya sannan ta koma gida”

  Tunani Ummi ta wuni yi yau, inda take kiyasta harma yayi auren, komai take gani a idonta harda yana yin yariyar, tare da hango Abdulmajeed suna cin soyayya da yariyar”

   Tunanin da ya dauketa tsayon lokaci, hawaye shabe shabe a idonta”

Ahaka Abdulmajeed yacimmata har ya isa gabanta bata sani ba”

    Dangwalo hawayen yayi tare da fadin”

   Ke Ummi meke damun ki haka?

   Zabura tayi domin sai alokacin ta kula dashi”

   Kukan me kike?

  Hawaye ta fara sharewa tare da fadin tunani nake”

    Tunani shine harda kuka?, ke, kar dai kice min har yanzun baki shafe Ummayen nan ba azucjyar ki”

   A’a ni ba tunani Ummayo nake ba”

  Toh tunani wa kike”

   Kallonshi tayi ta sauke idota, wani irin masiffen kishinsa ne ya taso mata, dan haka ta matso hawaye sannan ta ce”

   Yaya wai meyasa zakayi aure??

  Mmn Yazeed🔥 🔥🔥🔥🔥🔥

*KOWANNE BAKIN WUTA*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥

    ( da nashi hayakin)

💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by

    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*

                98

Rufe idon sa yayi domin be tsan maci tambayar ba, zuwa can ya bude tare da fadin”

   Wacce irin tambaya ce wannan ?

    Eh nidai ka bani amsa kawai”+

  OK toh zan baki amsa, dalilin shine”

   Inason na aure wacce take sona nake sonta, ma ana auren soyayya bana hadin iyaye ba”

    Kasa cewa uffan tayi ta juya baya gaba daya ta rasa mema yake nufi ne, ahankali ta juyo ta kalleshi  yaya kana nufin wanan auren na kiyayya ne ke nan?

  Ni bance ba, amman in baki manta ba kin furta agabana cewa baki sona, bakuma sau daya kika fada ba, kuma da akayi auren gashi nan kina nuna min kiyayya abaiya ne”

   Kash😬 gaskiya yaya ya cika naci, acikin zuciyar ta tai maganar, sannan ta dago ido ta kalleshi tare da cewa”

   Ka daina wannan maganar  yaya, ya kamata ka fahimce ni, idan haka ne ai kai ma  ka taba cewa baka sona”

  

Kau da kai yayi tare da fadin ai ke kika fara cewa”

 

   Murmushi tayi tare da share kwallan dake idonta tace”

   Toh kayi hakuri yaya ka fahimce ni, ko alokacin ba kinka nake ba, kawai lokacin akwai wadda na shaku dashi ne, har nai nufin auren sa, da aka kawo mgnr ka banbarakwai naji mgnr domin bantaba kawo aure atsakanin mu ba, asali ma lokacin ni tsoron ka nakeji, matsayin yaya nake kallon wadda muka fito ciki daya amman yaya wlh yanzon komai…..

Hannu tasa ta to she bakinta yayin da Abdulmajeed ya tsare ta da ido yana son yaje me zata ce”

   Ganin ta dakata yasa ya kara kafeta da ido tare da cewa ina jinki”

   Wasa ta fara yi da ya tsunta tare da fadin”

  Komai ya canza yaya ba inda kake tunani ba, kasa ta karayi da murya sannan ta ce”

     Wlh ina son ka

     Dadi yaji sosai azuciyan shi , afili kuwa cewa yayi ban shaida ba”

   Yarfa hannunwata tayi tare da sunkuyar dakai acikin zuciyarta tace bansan kuma me zance maka ba amatsayi na na mace na mutsuke kunya amman yace be gane ba, daman su hassana sunce, ka cika naci”

   Jinshi tayi yana fadin”

   OK wato har hirata kike yi dasu ko, salon su raina ni”

   Rufe bakinta tayi da sauri tare da zare idonta”

    Gani tayi ya mike ya shege dakin sa”

   Tsaki taja afili sannan tace”

   Narasa yadda zanyi inshawo kan mutumin nan, ban son yayi auren nan muna cikin irin wannan halin”

     Tashi tayi tabi bayan shi amman saita samu ya rufe kofar”

    Ahankali ta buga kofar

Sai dai harta karace bugunta be bude ba”

   Juyawa tayi jikinta asanyaye, me yasa yaya yacika zuciyan tsiya ne, zama tayi tayi tai tagumi daga karshe ta wuce dakin ta”

   Gaba daya hankalin ta ya tashi ta rasa yaya zatayi ta shawo kanshi, har mgnr shekara da shekaru yaya be mantawa dashi, yana nan azuciyar shi”

  Kuka ne yazo mata dan haka tai tayi tana goge hawayen wani na zubowa”

STORY CONTINUES BELOW

   Acikin zuciyan ta take cewa”

   Haka Allah ya jarabce ni, da gani, tun da nai aure dadin da naji be wuce na shekara daya ba, daga wance  sai wanccen babu wani cikkaken kwanciyar hankali”

  Gashi yaya ya cika taurin kan tsiya ban son me yake nufi ba ko so yake saina bude ba kina na bashi dama sannnan zai kula ni”

   Kuka Ummi ta raba dare tana yi, dan haka bata samu ishashshen bacci ba”

   Ko da safe data tashi jikinta babu kwari dan ko abincin dare bataci ba”

   Jira taitayi taji fitowan Abdulmajeed amman har kusan karfe 9 be fito ba dan haka taitunanin kila bazai fita bane”

    Tana cikin wannan tunanin zuciyanta ya fara tashi nan ta fara yunkurin amai da gudu ta nufi toilet”

   Amai taita kwarawa tana cikin wannan halin ta farajin Sallaman su  Hassana da Hussaina”

   Sundade suna sallama saidai bazata iya amsa wa ba, koda ta gama aman daker ta iya dauraye bakin ta, tana dafa bango ta isa bakin gado ta kwanta”

   Ba jimawa Abdulmajeed ya shigo bayan Ummi yabi da kallo wato ma har yanzun tana kwace ne, ahankali yace”

   Ga kawayen ki nan sunzo gaida ki, Mommy ce ta turo su dan nace mata baki da lafiya so insun gaidaki ki amsa, kuma idan kikayi gulmata dasu Allah ya isa, idan kawayen ki ne ni kannai nane”

  Shiru yaji bata ce kamai ba kuma bata motsaba, dan haka yace”

  Ina magana kinyi banza dani?

   Cikin dakushashyar murya tace”

    Bazan iya tashi bane, banjin dadi”

   Da saurin shi ya karasa gurin tare da laken fuskanta”

   Lfy meya sameki, idonta yagani akunkunre dan haka yace”

  Subuhanallahi Kuka kikayi ko?, kokarin dagata yake nan ya kula jikinta babu kwari”

   Ummi bude baki kimin mgn meye ke damun ki, kin tsokalo ciwo ko?

    Amai dai nayi”

    So nawa kikayi a man??

    Sau daya ne”

   Shine jikin ki yayi laushi haka gaya min so nawa kika yi?

   So daya ne?

   Ido ya kura mata, sannan yaja tsaki tare da fadin”

    Ina zuwa?

   Ya fita ba jimawa su hassana suka shigo, ko wanne fuskan sa dauke da murmushi”

   Abakin gadon suka zauna, Hussaina ce tai saurin  cewa”

    Sannu Ummi ya jikin”

   Da sauki ta fada ahankali yayin da su ‘yan biyu suketa kunshe dariya”

   Ummi ta kula ita sukewa dariya dan haka tace”

    Dariyar me kuke yi?? Ni kukewa dariya??, to wlh ku bari idan yaya yagani zaice zancen shi muke”

   Hassana tace ta fara to she bakinta tare da fadin”

   Hussaina tashi mutafi dana san yana nan ma bazan zo ba”

   Lallai daga zuwa ai Mommy wuni tace miy……

   Shigowan shi ya katseta, tsayawa yayi agaban su ya fara balle magani guda 4 sannan ya mikawa Hussaina yace”

   Mika mata ga ruwa nan ku bata tasha”

   Da taimako hassana ta tashi ta zauna tare da jin gins ajikin gadon”

STORY CONTINUES BELOW

  Ko da aka bata maganin kinsha tayi ta rike ahannunta dan haka yace”

   Kisha mana”

  Kallon shi Ummi tayi sannan tace”

   Toh ka tafi ai zansha”

   Bazan tafiba sai kin sha ina kallon ki”

    Guda daya ta dauka sannan ta mikawa Hassana sauran tare da fadin”

    Rike min”

Ai dika yace kisha”

   Abdulmajeed ne yace”

  Batta tasha hakan idan yafi mata”

  Sakawa tayi abakinta sannan tasha ruwan   ta kuma karban wani, yunkurin aman ya kara taso mata, da gudu ta nufa shi cikin azama Abdulmajeed ya riketa adai dai lokacin da ‘yan biyu ma ke kokarin riketa”

    Ku saketa yace, sannan ya dauketa cak ya nufi toilet da ita”

   Tun kafin su isa ta fara amai ajikin sa”

   Amai tayi sosai, daker ya tsaya, sannan ya fara zuba mata ruwa ta wanke bakin ta tare da dauraye mata fuskanta”

   Rigarta ta jike gaba daya dan haka ya kira Hassana yace”

   Kawo mata Riga”

    Tabdijan Hasssana ta fada azuciyan ta abun mamaki, jibi yaya kamar bashi ba, abu kadan ya nuna yana jin kyama amman jibi amman Ummi ajikin shi kamar ma begani ba”

    Rigar ta dauko ta mika mishi sannan suka hau gyara gadon ita da Hussaina yayin da sukaci gaba da dayin kuskus din su”

    Zuwa can ya fito da Ummi ta kwanta akan dagon, sannan ya koma toilet din”

   Zuwa can ya fito babu riga yana fadin”

   Ke, Hussaina shiga ki dauki kayan ki shan ya ke kuma Hassana dama min maganin nan”

   Lokacin da Hussaina tashi toilet din Tass ta sameshi lallai ma yayan nan, wato har wanki yake wa Ummi muko yazo yaita zare mana ido, indan Mommy tayi mgn yace ai kannasa ne, ita Ummin ba kanwarsa bace?? Ai mun ma girmeta”

    Bejima ba ya dawo, ya tarrar Hassana ta gama damawa dan haka yace”

   Ajiye min anan gurin kije falo ku jirani”

   Tana fita yace”

   Amsa kisha ko kuma na matseki na dura miki”

   Amsa tayi ta rike numfashi sannan ta juye abakinta ta hadiye”

    Ya mutsa fuska taitayi, duk abin da take yana kallon ta”

Bayan yaga ta nutsu yace”

  Ki kwanta kiyi baccin barin je na dawo”

   Ba’ajima ba taji kwari ajikinta  dan haka suka shiga hira dasu Hussaina “

    Sai yamma Abdulmajeed ya dawo, tunda sukaji shigowan shi kowa ya shiga cikin nutsuwar shi”

    Sai dare Abdulmajeed ya maida su gida bayan suci abinci da su suka girka”

     Nan Ummi ta sake yimai zancen auren tare da nuna mai tsananin son da take yayi auren cikin fada take magana sannan ta kara da cewa tana son yau yau yaje yaga Bilkisu”

   Wani iri yayi zuwa can ya yamutsa fuska jikin shi asanyaye yace”

   Mommy wlh bazan iya zuwa yauba Ummi nacen gida bata da lafiya”

   Abdulmajeed Umarni nabaka bashawara na nema ba”

  Shike nan zanje”

  Mikewa yayi ya mata sallama ya fita”

   Hayan ya dauka  yana tafe yana tsaki”

   Yana isa gidan me gadin, ya taho yace mai aiko bata nan”

  OK na gode juyawa yayi ya fita sannan ya kira wayar mommy ya gaya mata yaje batanan”

   Toh amman gobe ka koma fan”

Fuskan shi ayamutse yace toh Mommy zan je”

  Gida ya nufa ya samu Ummi  zaune zaune afalo, da gani jikinta yayi sauki sosai sai idonta daya dan tasa”

    Hannuta ya ruko ya wuce dakin sa da ita, suna zama yace”

   Ki gayamin abun dake damun ki, jiya kin kwana kina kuka gaya min meye matsalan ki??

  Murya kasa kasa tace”

   Yaya ni ina son ne ka yafe min komai ya wuce, nagaji da irin wannan rayuwar, wai kai baka yafiya ne, inata baka hakuri kaki hakura”

   Murmushi yayi sannan yace”

   Na yafe miki sai kuma me??

  Kasa tayi dakai sannan tace”

  Maganar auren ka na tayar min da hankali”

   Runtse ido yayi acikin zuciyan sa yace”

  Allah yasa kishina take, afili kuwa cewa yayi saboda me?

   Hawaye ta share yaya aiba wata mace da mijinta zai kara aure tace hankalinta be tashi ba”

  Harda ke??, ummi kina nufi kishina kike??

Hawaye taci gaba da hashare da haka yace”

   Shikenan na fahimta nima ba ason raina bane, Umarnin Mommy ne, kuma danaje naga yariyar tana da hankali  dan haka na  naji ta kwata min”

  Gabata ne taji ya fadi, wai ta kwanta mishi wannan ai cin fuska ne”

  Mikewa tayi tana huce, adaidai lokacin da yake cewa kuma yariya tana da kyau sos….

   Wani mugun haushi ne ya kamata dan haka bata san lokacin da  ta dauki wani cufin dake kusa da ita ba ta wurga mai”

  Kaucewa yayi da sauri dan haka ya fada bayan shi ya tarwatse”

   Kallon yafi Ummi dashi tana huci ta shige daki, juyawa yayi ya kalli cufi ya tarwatse, fashewa yayi da dariya sosai, daker ya iya tsayar da dariyar sannan yace”

    Lallai kin kamo yariya,

  Bayanta yabi azuciya n shi yake fadin”

    Kinci darajan cikin dake jikin ki yariya amman duk da haka ZAKI GANE KURAN KI angaya miki DAUKAN FANSA wasa ne, ina raga miki ne sabo da tsoron BUGUN ZUCIYAR ki…..

Mmn Yazeed

🔥 🔥🔥🔥🔥🔥
*KOWANNE BAKIN WUTA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    ( da nashi hayakin)
💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by
    *Fadeela Lamido*
*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*

          Dedicated👇🏻
*Meelat Musa*
     
    *99 to 100*

Samun ta yayi ta kudun dunai agado, amman xuk da haka huci take yi, yana tsaye akanta yace”

   Ummi yi hakuri kitashi muyi mgn”

  Ni bawani mgn dazan yi dakai duk wani abu dazan fada na riga na fada kaje kayi duk abin da kaga dama”

  Dariya yayi sannan yace”

  Nifa ba fada nazoba hakuri zan baki dan nace yariyar na da kyau saiki jefeni ai ba ina nufin tafi bane, ke fa ta daban ce bana hadaki da ko wacce mace afadin duniyan nan, idan kin natsu zaki fahimci hakan+

   Ko karya Abdulmajeed yayi mata to taji dadin mgnr dan haka natsuwanta ya fara dawowa”

   Ahankali ya sake cewa tashi ki zauna”

   Tashi tayi ta zauna tana mutsuke ido”

Abdulmajeed ya bita da ido sannan yace”

  Gaya min abin da kike son ayi indai hankalin ki zai kwanta”

  Ni bawani abin da nake so, tunda kace Ummarnin Mommy ne ai shike nan, amman karka sake min zancen ta ban so, kuma idan kana son zaman lafiya karka hada mu gida daya”

Murmushi yayi sannan yace to naji Allah ya baki hakuri”

   Ameen ta fada sannan ta juya ta kwanta”

   Shima fita yayi ya nufi  dakin sa, yana me farin cikin Ummi ta fara sonshi dan yaga kishinta me tsanani akan shi”

      ****

Su Hassana da Hussaina ne zaune agaban Mommy bayan sun dawo daga Gidan Abdulmajeed, dukkan su kuwa fuskan su dauke da murmushi”

   Kallon su Mommyn tayi tace”

   Ya dai naga kunata faman yake baki, wani abu ne?

   Hussaina ce ta fara cewa Mommy ashe duk zare idon da yaya yake mana da gangan yake yi, wlh ji yake da Ummi sosai, baya wani zare mata ido”

   Ina fah zai  zare mata ido ai daman irin su haka suke, dan ma taki kwatar da hankalinta kullum cikin tashin hankali”

  Hassana ce tace”

   Aiko Mommy yanzun dai basa wannan fadan ko Hassana ?

   Eh wlh basa yi Mommy dan wlh maganin ma sawa yayi Hassana ta dama mishi sannan ya kore mu, nasan dura mata zaiyi shiyasa ya kore mu, karashe mgnr sukayi cikin dariya”

    Hmmm yanzun kuna nufin Ummi ma ta kwantar da kanta”

    Ai Mommy mudai lfy lau muka gansu gidan dadi kamar kar mu dawo, kuma da yaya ya ganmu acen be wani zare mana ido ba”

  Murmushi Mommy tayi to ai kunga haka yafi sai suyi zaman su, Allah ya kara hadda kan su”

   Ameen suka amsa ta sannan  ta kara cewa jikin dai be matsa mata ba ko?

   Eh sanda mukaje dai tana jin jiki amman kafin mu taho taji sauki sosai”

      Allah kara sauki, nima zanje na dubata”

STORY CONTINUES BELOW

   Shiru tayi zuwa can tace”

    Kungani tun da Ummi ta samu cikin nan Abdulmajeed be sake zuwa wajen Bilkisu ba, kullum namai mgn daga yace wannan sai yace wancen, wlh ban son naji kunya mun riga munyi magna da mahaifiyar yariyar”

   Bata rai sukayi gaba dayan su yayin da Hussaina tace”

   Toh Mommy ki barsa mana ai ba dole bane”

   Hassana ma karaf tayi tace”

    Toh Mommy wai daman ba kince dan Ummi taki nutsuwa bane?, ai yanzun sun daidaita dan Allah abar zancen”

   Dakuwa Mommy tayi mata sannan tace”

   Kin ganki?, daman tuni na fahimci baki son laifi Ummi, ta yaya za’a fasa bayan mun gama shirya komai”

   Toh Mommy shi yayan ya yadda da bilkisun ne?, nidai wlh yariyar bata min ba wannan yariyar ai tama girmi Ummi”

   Hararanta Mommy tayi sannan tace”

   Eh ta girmin Ummin sai me? Kun ga Ku fita ido na, ko kuna taya Ummi kishi ne?

   Shiru sukayi tare da kunkunai, zuwa can suka bar wajen daya bayan daya”

   Kallon tabi su dashi tare da fadin kaga min yara dai”

 
    Washegari da daddare  Abdulmajeed yayi nufin zuwa gidan su Bilkisu kamar yadda Mommy tace”

   Bawani shiri yayi ba dan azahirin gaskiya baya son auren nan, yafi son ya shawo kan Ummi su zauna lfy, hakan ne zaj bashi daman nuna mata soyayyar da take ganin be iya ba, idan yayi aure yanzun hankalin shi bazai natsu guri daya ba, Allah yasa Mommy tabar zancen Auren nan amman intaki dole na yi dan  babu yadda zanyi da Mommy dole navi Ummar nin ta”

   Fitowa yayi ya samu Ummi afalo ta tasa TV agaba”

   Ahankali yace”

  Ummi ina zuwa barin je na dawo”

  Sarai ta gane inda zaije domin indai ya dawo sallah isha’i babu inda yake zuwa”

  Sakin fuskanta tayi sannan tace”

   Nazo muje ka ajeni gidan Umma idan ka gama sai kazo ka dauke ni”

   Shiru yayi zuwa can yace”

  Me zakiyi da daddaren nan?

    Akwai kaya na acan ina son zan dauko ne”

   Kauda kai yayi meyasa baki gaya min ba ai da na dauko miki, dan gaskiya dare yayi ki bari gobe zan dauko”

    Mikewa tayi tare da fadin”

   Ni dai zan bika yanzun nake so zanyi amfani da shi”

    Tafiya ya fara tare da fadin zo muje”

    Aguje yake tafiya dan haka cikin kankanin lokaci suka isa gidan”

    Bude motar tayi ta fita kasa tayi da murya sannan tace “
  Ka kaida ta”

  Akunnen shi radau dan haka yace”

  Ni gidan Sadiq zani”

   Gaba tayi abunta batare da ta saurare shi ba”

    Umma taji mamakin ganin ta da daddare daga ina haka”

    Daga gida Umma ina wuni?

  Lafiya lau ke daya ko tare da Abdulmajeed kuke?

  Eh shiya sauke ni zaije ya dawo ne”

    Zaije ina da daddaren nan?

   Oho masa kila tadi zashi”

STORY CONTINUES BELOW

   Baki Umma ta sake wai Ummi kina da lfy kowa ko irin kishin nan na mata wai baki dashi ne?

   Hmmm Umma toh ni ya zanyi?

  Yaya zakiyi ma kike tambayata?, zai tafi dadin ne ke kuma ya kawo ki gida”

  Umma nifa nace ya kawoni zan dauki kayana daker ma fah ya yadda”

   Tabe baki Mommy tayi sannan tace”

    Daman ina neman ki, naje wajen hajiya akan mgnr tama bani sako na baki”

   Toh Umma, Abba na nan ne”

   Eh yana ciki”

  Mikewa tayi bari je mugaisa”

   Toh kar dai ki dade”

  Cikin fara’a suka gaisa da Abba sannan ya tambayeta daga ina?

  Nan da gaya mishi kamar yadda ta gayawa Umma, nasiha yaita mata akan hakuri daga karshe ya koma kan biyayya”

   Ya dade yana mata nasiha, sosai taji dadin nasihar Abba dan ta ganu wasu abubuwa da take wadda basu dace, wajen mgn, wadda atunanin ta bawani abu bane”

   Suna cikin haka Abdulmajeed ya dawo, tunkafin ya shigo ta wuce hada kayanta

   Abdulmajeed kuwa zama yayi gurin Abba sukaci gaba da hira”

   Ummi kuwa kayanta ta hada tana kukarin fitowa Umma ta shigo hannunta rike da wata leda”

   Mikawa Ummi tayi sannan tace”

   Gashi Hajiya tace nabaki, tace ki kirata saita gaya miki abin da zakiyi dashi”

   Amsa Ummi tayi sannan ta bude ledan ta leka turare ne kala uku acikin ledan”

Muryan  Umma taji tana cewa karki ki amfani dashi fah kiyi, inba haka ba sai dai ki zama yar kallo”

   Acikin zuciyanta tace bazan zama yar kallo ba insha Allahu”
  Umma ko juyawa tayi tana fadin kiyi sauri Ku tafi fah”

   Toh tace, lekawa tayi ta tabbatar da wucewan Umma sannan ta dannan number Hajiya”

    Gaisawa sukayi da hajiya sannan tace Umma ta bani sako”

    Saurawa tayi zuwa can tace”

   Zanyi mana Hajiya”

  Shiru ta sake yi zuwa can tayi Murmushi tare da fadin”

   Ai zan yi ma”

    Da haka sukayi sallama, sauke wayar tayi tare da fadin”

   Hmmm zaka sani ne”

   Jakarta ta dauka ta fito sallama sukayi sannan suka fito Abdulmajeed rike da jakar Ummi”

   Magana sama sama sukeyi har suka isa gidan”

  Ta riga shi shiga ciki kai tsaye dakinta ta wuce ta shige toilet”

   Abdulmajeed ne ya shigo ya ajiye jakar , wajen kofar toilet din yaje “

   Ummi idan kin gama kizo ina son ganin ki”

   Acikin zuciyarta tace aiko baka ce bama zanzo ne, murmushi tayi afili tace”

   Hajiya Allah yabar min ke”

  Ba jimawa ta fito.tana wani irin kamshi🤔 ita kanta bude hanci take sabo da dadin kamshin”

    Maita shafa sannan ta bude jakar ta dauko rigar data ware tun daga gidan Umma”

   Rigar iyakanta cinya bawani hannun kirkice da ita ba, duk halittan jikinta baiya ne yake”

    Koda ta gama shirita tsaf tsayawa tayi taitai addu’an Allah ka haneni jin kunyan idon yaya Allah ka bani ikon aiwatar da abin da nai niya”

   Dakin ta nufa ahankali ta tura kofar tare da sallama”

   Amsawa yayi idon shi akasa”

    Ahankali Ummi ta fara takowa cikin dakin”

   Idonshi akasa ya hango wasu kafafuwa farare tas

    Kafar yabi da kalo tare dabin tsayon kafar har ya dago gaba daya”

    Sandarewa ya nemi yi a daidai lokacin da wani irin kamshi ya daki hancin sa”

  Baki ya bude cikin tarin mamaki”

   Yace Zainab meye kuma haka”

  Tana kokarin zama dafdashi tace meye kuwa, wani abu ka gani”

   Murmushi yayi sannan yace”

     A’a banga  komai ba, gyara zaman shi yayi ya juyo ya kureta da ido”

    Itama ido ta zuba mishi tamai wani irin kallo”

    Ganin tana neman rikita shi dauke idon shi, zuwa can ya sake dagowa ya kalleta sannan ya kara kauda idosa tare da fadin”

   Hmmm kai, murmushi yayi sannan yace”

    Wannan wanka Amman dai ba adakin nan zaki kwana ko”

    Anan zan kwana”

   OK to jeki saka kaya sannan ki dawo dan bazaki tayar min da hankali abanza ba”

   Wani irin kallo Ummi tamai sannan ta mike ta nufe shi…..😳🤔

Mmn Yazeed🔥 🔥🔥🔥🔥🔥

*KOWANNE BAKIN WUTA*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥

    ( da nashi hayakin)

💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by

    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*

   Wattpad @fadeelalamido

         *101*

Duk abin da take idon shi na kanta, sai da tai kamar zata zauna jikin shi sai kuma ta kauce ta zauna gurin data tashi tare da kara matsan shi”

   Hadiye miyo yayi daker tare da kara karkata idon sa yana kallon ta”

   Ahankali tace”+

   Ni daman ba anan zan kwana ba wasa nama, kai nake jira bakai kace inna gama nazoba, shine nazo”

    Ajiyan zuciya yayi sannan yace”

   Ni mema xaki min ne?

   Sauri tayi tace”

   Toh barin je idan ka tuna kamin mgn”

   Juyawa tayi zata fita Abdulmajeed ya zuba mata idanu tamkar ya dakatar da ita”

    Harta fita kamshin na makale adakin afili yace”

   Wanne irin turare ne wannan yariyar take amfani dashi, gaskiya yana da daddi sosai”

   Ji ma wata shiga da tayi na neman magana, kana nurfar ta kuma tace, karka taba min kirji na, tsaki yaja sannan yace”

   Duk abin da naji zan daure harsai ranan data salla ma min komai”

    Tashi yayi ya nufi gado domin duk tunanin shi sun kyauce, har yanzun Ummi yake gani cikin idon shi, nan da nan hankalin shi yayi matsanan  cin tashi”

   Tsaki ya karaja afili yace”

   Kaga min muguwar yariya zata hanani bacci”

  Har gurin 12:00am ya kasa bacci, tashi yayi ya zauna bakin gadon tare da fadin Yau zan sha wahala, wata zuciyar ce tace”

   Kaso ne karfinka tafi haka kawai ka kwana da wahala”

  Da wanannan tunanin ya mike tare da fesa turare ajikin sa ya fice”

   ****

Ummi ma tana komawa dakin ta gadon ta haye acikin zuciyan ta take fadin”

   Wlh na rikita shi, dan tsohowa tace min sai ya manta nutsuwan shi, dariya tayi sannan tace”

   Zaka sani ne”

   Tun tana ganin zaizo har bacci ya mamaye ta, ba jimawa Abdulmajeed ya shigo”

   Ganiin Ummi kwace akan agado yayi ajiyan zuciya tare da karasa wa abakin gadon”

   Kallo yabita dashi yau bata rufa ba sabanin da da indai tahau gado saita rufa da bargo”

   Zama yayi agefen ta yana kallon ta yana ajiyan zuciya”

    Besan sanda hannun shi yakai gurin da Ummi ta tsana ataba mata ba, domin shiyafi komai tsole masa ido”

    Acikin baccin da beyi nisa ba tafara jin wani bakon yana yi”

    Dakewa tayi domin azahiri bata son hakan sai dai dole ta jure koma beye”

   Zuwa can ta farajin abun nayi nisa”

    Mimmikewa take kamar me baccin gaske yayin ta Abdulmajeed ya sake rikicewa”

STORY CONTINUES BELOW

   Ganin ya gama fita hayyacin shi yasa Ummi ta bude idonta tare da fadin”

    Yaya menene kuma haka?

  Cikin lumshashen idonsa yace”

   Ummi yi shiru karki sake mgn

   Yaya ?

Na’am Zainab

  Kaface kabar min kaya na”

   Ai wannan kayan banaki bane zainab kaya nane😜”

   Yaya ?

  Ganin bazata mai shiru ba yasa ya rufe bakinta da nashi”

   Daga nan abun da be taba faruwa ba ya faruba ya faru tsakanin Ummi da Abdulmajeed domin tsintan kanta tayi tana mayar da martani”

   Rikicewa Abdulmajeed yayi ya fita hayyacin sa daga can naji yana tambayn Ummi wai daidai ina kunnen sa yake😱 cikin sauri na barsu dan kudun kar nawa kunnen ya toshe”

   Washegari da Misalin 9:34am Abdulmajeed makale da Ummi ta shige jikin sa”

   Kara rungumeta yake yana lumshe ido”

   Itama Ummi lumshe ido take tana tunu sambatun Abdulmajeed adaren jiya”

   Murmushi tayi tare da dan leka fuskan shi tace”

   Yaya yau bazaka fita bane”

   Umm babu inda zani, ranar ki ce”

   Duk wayoyin shi ya kashe sannan ya dauko ta Ummi ya kashe, nan bacci ya dauki su domin daren jiya basu run tsaba”

   Ranan wuni sukayi suna abu daya, tun tanajin far gaban taba kirjinta da yake har tazo ta gyare, watoh daman rashin sabo ne?, ayau ta daina jin abin da take ji, shi kan shi Abdulmajeed yaga banbaci har ya fara tunanin kodai zaman da tayi agida anbata magani ne?

   Aranan sallah kadai ki fidda Abdulmajeed da ya dawo yake komawa su manni wanka kuwa bana iya kirga sau nawa suka yi”

    Har washegari Abdulmajeed be kunna wayoyin sa ba ko tuna tama baya yi”

      ****

Mommy tun jiya take kiran wayar Abdulmajeed Amman akashe take dan haka hankalinta ya fara tashi, nan tace bari ta kira Ummi nan ma akashe take”

   A’a ta fada afili sannan tace toh ina suka shiga anya kuwa lafiya”

   Agogo ta kallah karfe  biyu na rana dan haka tai tunanin kila suna tare da Sadiq Number sadiq takira ba ajima ba ya dauka, bayan sun gaisa tace”

   Wai mutumin ka fah? Tun jiya neki kiran sa wayarsa kashe ta matarsa ma haka”

   Eh Mommy rabon shi da Office tun shekaran jiya nima ita neman sa ban samishi ba, ayanzun haka inakan  hanyata ta zuwa gidan sa”

   Toh Allah yasa dai Lafiya”

  Ameen dai Mommy sai kinjini”

     ****

Yana isa gidan ya sauko ya shiga tare sallama”

   Ya dade tsaye cikin falon babu wadda ya amsa dan haka ya koma bakin kofar ya fara bugawa hankalin sa tashe”

   Abdulmajeed yana rukunkume da Ummi suna bacci yaji kamar ana bugun kofa”

    Bude ido yayi eh kofar ake bugawa sakkowa yayi da sauri ya fito daga shi sai gajeren wando”

Ido biyu sukayi da Sadiq sakin baki yayi yana kallon Abdulmajeed tare da fadin meye kuma haka”

    Tahowa Abdulmajeed yayi yana cewa”

STORY CONTINUES BELOW

    Bangane meye haka ba, wani abu ka gani?

   Dubeka fah wannan ai tsirara kake”

   Zama sukayi kusan atare adaidai lokacin da Abdulmajeed ke fadin”

    Toh gidan ka na shiga? Kaifa ka same ni agidana”

   Eh gaskiya ne me gida, yanzun dai meye ya hanaka fitowa Office yau kwana biyu”

   Hutu nake yi”

   Hutun?, hutun me?

   Kasan lokacin danayi aure banyi hotuba”

   Eh ina jin ka”

   Shiyasa nake dan hutawa”

   Juyowa Sadiq yayi yace”

  Toh baka isa ba, Uban wa ya hanaka yin hutun tun a lokacin?

   Ban isaba fah kace?

  Eh baka isa ba dole ka fito danni

Ma aiki ya min yawa dan me zaka kwanta agida kace hutu, hutun me?

  Ai sai kazo kajani ka kaini”

  Kallon shi Sadiq yayi tare sakin baki”

   Fari yaga ya kara tare da wani irin kwarjini dan haka yace”

   Kai karka raina min wayo gaya min sirrin naga kayi wani fari ne”

  Toh ba ina gaya maka ba kaki saurarata ankwanci nake ci kawai”

   Angonci da cikin??

   To se me, ai cikin ma Allah ne kawai ya kawo shi, amman ni yanzun ne nasan nayi aure gaskiya aure yayi ba karya”

   Au haba?, dariya sukayi tare da tafawa sannan Sadiq yace”

   Watoh shine har kana kashe waya ko?, toh Mommy nata neman ka”

   Kai ya dafa sannan yace”

   Wlh na manta munyi da ita zanje gidan su wannan yariyar, kasan me, sai gobe zan kunna wayata idan ta kiraka kace mata bani da lafiya ne”

   Dariya Sadiq yayi sosai sannan yace”

  Lallai ma Abdulmajeed kana nufin makale mata zakayi kenan dan Allah kabar ‘yar mutane ta huta rabon ka fah da fita tun shekaran jiya”

  Hmmm tashi ka tafi gobe zan leko ka”

    Dariya Sadiq yayi tare da fadin”

    Abdulmajeed kana da hankali kuwa intafi fah kace?

   Eh jeka gobe zanzo”

  Mikewa Sadiq yayi tare da fadin”

  Zan rama ne ai aure befi aure ba, ficewa yayi ya bar gidan, saida ya hau titi ya kira Mommy ya sanar mata kaman yadda Abdulmajeed yace ya fada”

   Sosai hankalin Mommy ya tashi, Ummi babu lafiya kuma Abdulmajeed ma haka toh wa zai taimaki wani”

    So tayi ta tashi ta tafi gidan idan ta kama ta dauko Ummin ko kuma acikin ‘yan biyu daya ya tsaya a can, amman saita vari daddy ya dawo tukuna”

   Koda daddy ya dawo ta sanar mai shima shawaran da yabayar kenan”

  Dan haka Mommy tasa Hassana ta hado musu abinci atafi dashi ko Abdulmajeed yaci ita kuma Ummi su taho da ita”

    

        *****

Da misalin 5:00pm Ummi na rugume ajikin Abdulmajeed yana samata albarka”

   Ahankali tace”

   Yaya

  Na’am, Ummi”

   Kai bakajin yunwa ne wai?

   Banji Ummi ke kina ji ne

   Kaita daga masa”

  Zamewa yayi barin yi wanka na nemo miki abin da zakaci”

    A’a ninafi son na girka da kaina”

OK toh yi wanka kije ki yi”

    Mikewa tayi ta nufi toilet

  Abdulmajeed kuwa murmushi yai tayi, tare da mamakin yaya akayi Ummi ta sakar mai komai kodai, lokacin da ta zauna gida tafada ne antsuma ta”

   Har Ummi ta fito yana irin wannan tunanin kallon ta kawai yake yana mamaki, harta gama shiryawa ta fita”

  Shima mikewa yayi ya shiga toilet domin tsarkake jikin shi”

   Be jima ba ya fito yana goge jikin shi, kamshin girkin Ummi ne ya daki hancin shi, hakanan yaji yana son yasata a idon shi dan haka yai saurin goge jikin shi tare da saka gajeren wando ya nufi kitchen din”

    Har ya shiga Ummi bata san da shigowan shiba sai dai ji kawai tayi ya rungumeta ta baya”

   Juyowa tayi ta kalle shi tayi murmushi shima Murmushi yayi tare da fadin”

   Kamshin girkin ki ya hana ni natsuwa”

   Hmmm yaya kai da kake daki”

   Har can yabi ni ai, kuma daman inason na tanbaye ki?

   Allah yasa na sani”

   Wai waye ya gyara min ke ne, naga da baki yadda ataba nan gurin, kai hannun shi yayi dan haka Ummi tayi murmushi tace”

   Haka nan ba maganin dana sha haka nan natsin ci kai na”

  Daga gaske?

  Wlh”

Toh indai haka ne daman can wannan dolon ne ya barki har kika canfi abun, tun farko be sabar miki ba, ko da yake daman  shishigi ne ya kawo shi cikin rayuwan ki shiyasa Allah bebashi sa’a  ba”

   Wai yaushe Yaya zai daina kiran Mukhtar da sunayen da basu dace ba?, kawar da zancen tayi da cewa”

   Yaya wai ko kaga kunnen ka??

   Me ne?, wanne kunnen???

Murmushi tayi sannan ta matsa can gefe tace”

   Shekaran jiya ne naji kamar kana cigiyar kunnen ka”

   Sai yanzun ya gane inda ta dosa  dan haka yayi Murmushi sannan yace”

   Kin fara raina ni ko?, zo in nuna miki inda yake”

   Binta yayi yayi da ta fara neman hanyar gudu tare da dariya”

   Shima yana murmushi yake binta”

  Dai dai lokacin su Mommy suka iso, Salama sukaita yi babu amsa dan haka suka shigo cikin falon”

   Nan ma sallama suka cigaba dayi tare da fadin ina masu gidan ne….….

*Mmn Yazeed*🔥 🔥🔥🔥🔥🔥

*KOWANNE BAKIN WUTA*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥

    ( da nashi hayakin)

💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by

    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*

          102

Jin shiru yasa Mommy ta nemin guri ta zauna sannan ta dube Hassana tace”

    Ajeye kanyan kije dakin Ummin ki duba ta”

   Ajewa tayi sannan ta juya nan Mommy ta  kara cewa kiyi sallama  ki tabbatar an amsa miki kafin ki shiga”

   Toh tace

Sannan. ta wuce”

    Ta wuce kenan Mommy ta  fara jin kauri a binci na dukan hancinta”

Bude hanci tayi sosai tabbas kauri ne, kuma daga kitchen yake fitowa dan haka Mommy ta mike da sauri tana fadin”+

   Girki kuma ta daura ta kuma shige daki ta kwanta”

    Cikin sauri ta shige batare da ta kalli ko ina ba”

   Har takai tsakiyar kitchen din, taji motse abayan ta wai gawar da zatayi 🙆🏽‍♀ ta hango  Abdulmajeed ya hada Ummi da bango yana kokarin saka bakin shi cikin nata yayin da Ummi ke dariya tana kokarin gudu”

   Rasa Abun yi tayi, dan haka batasan sanda tai gyaran murya ba, sannan ta wuce ta sauke tukunyar”

  Tun da sukaji gyara murya zabura sukayi suka rabu da juna suna zare ido”

   Itako Mommy kanta akasa ta fice”

    Koda ta koma falon ji tayi kamar kasa ta bude ta shige, tare dayiwa kanta fadan me ya kawota”

   Daidai lokacin Hassana ta fito Mommy basanan fan, kuma har dakin Yaya ma na duba”

   Taho ki zauna Ashe suna nan”

   Zama tayi sannan Mommy ta sake cewa ko zamu tafi ne Hassana?, nifa shiyasa ban son zuwa gidan yara”

  A’a Mommy meye toh?, ba munzo gai dasu bane, kuma ai kince da Ummi zamu koma ko”

   Hmmm Hassana bar wannan mgnr kinji, ai bama zai yadda adaukar mai mata ba”

  

     *****

Abdulmajeed da Ummi a kitchen sai zare idon suke”

   Zuwa can ya kalli Ummi yace”

   Jeki dauko min jallabiya ta adaki “

   Hawaye Ummi ta matso sannan tace”

  Ni bazan iya fita ba fah”

   Dariya ce ta kwace masa bayan ya tsagaita yace”

   Meye haka?, wannan bawani abu bane, jiki dauko min ban son ne na fita ahaka”

   Fuskanta cike da hawaye tace”

   Nima ai bazan iya fita ba, jifa kayan jikina”

  Mur yasha dan yaga idan ba haka yayi ba bazataje ba, ke, wuce ki dauko min rigata”

   Buga kafa ta fara akasa tana fadin”

  Wlh yaya bazan iya fita ba, da dai akwai wata kofar ne ta baya”

   Dariya ya kuma yi sosai yayin da Ummi keta faman share hawaye”

   Tsagaitawa yayi sannan yayi kokarin saita kansa tare da kallon jikinsa, juyawa yayi zai fita dan haka Ummi tace”.

STORY CONTINUES BELOW

   Ka dauko min hijjabi na”

  Bazan dauko ba, ya fada sannan ya fice”

   Ido biyu suka yi da Hassana, sauri tayi ta kauda idonta, ita ko Mommy ta juyawa kitchen din baya”

  Kujeran ya dafa da hannun shi sannan yace”

  Mommy Sannu da zuwa”

    Batare da ta juyo ba tace”

  Yauwa ya jikin naka?

   Ji yayi tamkar ya nutse can kasan makoshi yace”

  Lafiya lau”

  Madallah

Juyawa yayi ya shige ciki  ba jimawa ya dawo sanyi da Jallabiya”

   Zama yayi akujeran dake kallon ta Mommy sannan suka kara gaisawa sosai”

   Hankali Abdulmajeed yana gurin Ummi dan haka bini bini ya juya ya kalli kitchen din, zuwa can yacewa Hassana”

   Dauko min wayata a Kitchen “

  Mikewa tayi ba jimawa ta dawo tace banga ni ba”

  OK to barshi, juyawa tayi ta nufi dakin Ummi adai dai Lokacin Mommy tace”

    Ina Ummin take ne? Ko bazata fito bane”

   Keya ya shafa sannan yace”

   Wai kunya take ji”

  Mikewa Mommy tayi ta nufi kitchen din tana fadin”

   A’a niba bakuwar zafi bace”

    Mommy na shiga ta samu Ummi manne ajikin bango, Hannu ta mika ta ruko nata sannan tace”

    Zo muje me yayi zafi, manna ta tayi da jikin ta suka fito falo”

   Sai alokacin wani sabon kunya ya sake tasowa Abdulmajeed ganin shigar dake jikin Ummi”

   Sukuyar dakai ya fara tare da shafo keyar shi yana dan Murmushi yana kallon Ummi da Mommy”

   Suna kokarin zama Hassana ta fito ta mikawa Ummi hijjabinta” a?murmushi  Mommy tayi sannan ta kalli Ummi  tace”

    Yaya jikin ki?

   Can kasa tace naji sauki”

   Allah ya karo sauki, juyawa ta kalli Abdulmajeed tace”

   Kaima ance baka da lafiya amman ni banga alaman ciwo atare dakai ba, gara Ummi ta dan fada, kai ko kiba ma kayi”

   Cikin yana yin dake nuna yaji kunya yace”

   Nadai samu sauki ne yau, amman jiya akwance nake”

   Murmushi tayi sannan tace”

  Allah ya sauwa ke”

  Daman nazo ne na tafi da Ummi tunda kace baka da lafiya kaga babu me temakon wani kenan”

   Kai ya shafu sannan yace”

    Ai na warke Mommy, kuma itama ai ta samu sauki”

   Toh ai shike nan mu bari mu koma”

   Mikewa Mommy tayi dan haka duk suka mike Ummi ko har yanzun bata iya hada ido da Mommy sabo da tsabar kun dataji”

   Har mota suka raka Su sannan Ummi ta koma gida tabar Abdulmajeed  da Mommy”

   Mommy na ganin wucewan Ummi ta kalli Abdulmajeed tace”

   Gobe ka tabbatar kaje gidan su Bilkisu, ahanan ka zauna agida ka kirkirowa kanka ciwon karya,  toh gobe ka fita ya isheka haka”

   Ya mutsa fuska yayi, Mommy ni da zakiji shawarata adan tsayar da zancen auren nan har Ummi ta samu Lafiya kinsan dai halin mata akan kishi kar wani Abu ya shafi abin dake cikin”

  Kai Abdulmajeed ka fita idona, wannan auren banga abun da zai dakatar dashi ba sai anyi shi”

   Kasa yayi dakai nima ba cewa nayi kar ayi ba ai, amman ai…..

    Karka ce min komai ina jiran ka goben”

   Shikenan Mommy sai na zo”

    Komawa gida yayi yayin da Mommy suka wuce”

  Harta isa gida yadda ta sami su Abdulmajeed yaki bace mata”

   Watoh Abdulmajeed angoncin sa yake ci shine yace beda lafiya har da wani kashe waya saika ce waddah ya aure sabuwar budurwa”

   Toh idan kuma Bilkisu ta shigo sai Allah yanzun ma abinci na kauri basu sane ba”

   Da irin wannan tunanin ta koma gida”

  Shikuwa Abdulmajeed cikin damuwa ya koma gurin Ummi domin ya tsani yaji anyi zancen bilkisu musamman yanzun da suka dai daita da Ummi”

    Daker ya iya cin abin cin da Mommy ta kawo musu, Ummi ma ta kula yana ciki Damuwa amman sai tai tunanin ko halin da Mommy ta same su ne ya dame shi”

     Washegari da yamman bayan ya taso aiki yai nufin ya koma gida yaga Ummi sannan ya wuce gurin Mommy “

   Sai dai suna hada Ido da Ummi yaji bazai iya fita ba”

    Rungume ta yayi, yayin da Ummi ke waigen bayanta tana fadin yaya karfa wani yazo”

   Babu wadda zaizo Ummi saki jikin ki”

   Janta yayi zuwa daki, daker ya rabo da ita yai wanka”

    Koda ya dawo kallo ya bita dashi, besan meyasa ba begajiya da kallon ta, sosai take dauke hankalin sa har mamaki yake acikin ‘yan kwanakin nan ji yake tamkar ya hadiye ta”

   Yana saka kayan yana kallonta, duk abin da yake tana kallon shi ta gefen idonta”

   Yayin da take addu’a acikin zuciyanta Allah yabar mata Abdulmajeed ita kadai domin bazata iya jure ganin shi da wata ba” wallahi mundin naga Yaya Abdulmajeed da wata zan iya hadiyan zuciya”

    Kallo tabishi dashi yayin da shima ya zuba mata ido, tare da fadin”

   Ya dai karfa ki cinye ni”

  Hmmm wai ina zaka ne naga alamar fita zakayi”

   Zanje gurin Mommy daga can kuma zani wani guri amman bazan dade ba karki damu”

   Ina ne wani guri ko dai tad’i zaka?, karaahe zancen tayi cikin baccin rai, dan haka ya karaso ya zauna agabanta”

   Ummi yanaga kin bata rai”

   Ba komai”

  Shiru yayi zuwa can ya miki yanzun zan dawo, badan ma zani gidan Mommy ba da muntafi tare”

   Dauke idonta tayi dan haka yaji bazai iya tafiya yabarta ba”

   Dawowa yayi ya tsaya yana kallonta zuwa can yace”

    Taso muje”

  Ina zamuje ?

Na dai ce ki zo, muje duk inda zani tare zamuje”

   A’a ni bazani ba, Kana son Mommy taji haushi nane”

   Wannan kuma babu ruwanki nine nace kizo muje ai”

   Turo baki tayi tare da make kafada”

    Mamayanta yayi ya sungumeta yai waje da ita ya tura ta cikin mota”

   Turo murfin take tana fadin ni bazani da  Allah kabarni”

   Rufewa yayi sannan ya zagaya ya shiga ya hada motar……

Mmn Yazeed🔥 🔥🔥🔥🔥🔥

*KOWANNE BAKIN WUTA*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥

    ( da nashi hayakin)

💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by

    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*

           103

Har suka isa gidan, Mommy magiya take mai aka ya mayar da ita gida”

   Ganin ya bude motar ya fice yasa tai zaman ta amotar”

   Har ya kusa shiga falon ya juyo yace”

   Wai baxaki fto bane?, kin dade bakiga baccin raina ba ko?, girgiza kai yayi ya wuce abin shi, dan haka Ummi ma ta fito ranta abace”

   Mommy zaune ita da Daddy suka samu, dan haka duk suka zube agasa suna deban gai suwa”

   Daddy yaji daddy ganin Ummi da Abdulmajeed da alama yaxun komai ya daidaita atsakanin su, Abdulmajeed din yaga yazama magidanci sosai, yayi kiba tare da fari ga wani cikan zati da kamala daya sameshi lokaci guda”+

   Juyawa daddy yayi ya kalli Mommy sannan yace”

   Toh gafa mutumin ki yazo”

Hmmm Alhaji kenan wai mutumina juyawa tayi ta kalli Abdulmajeed kai sai yanzun kaga damar zuwa?

   Mommy Ummi ce ta hanani fita sai kunci take yi”

   Cikin sauri ta sunkuyar da kanta ahankali tace”

Ni babu ruwana azuciyarta kuwa haushin Mommy ne fal azuciyanta, ni take son awa kishiya sabo da ba ita ta haifini ba dasu Hassana ne ai bazata so amusu ba, saita dinga nuna tana sona ashe munafunci ne”

   Tana cikin wannan tunanin taji Mommy na cewa”

   Sai kayi maza kaje kaga dare nayi”

  Mikewa yayi tare da kallon Ummi yace taso muje”

   Ina zakuje?, tare zaku?

    Yana kallon kofa yace”

   Eh Mommy”

Daddy ne ya kwashe da dariya adaidai lokacin da Mommy ta mike ta nufi dakin ta tana fadin kai zonan”

  Bayan ta yabi, suna shiga dakin tace”

   Abdulmajeed kana da hankali kuwa?, aina ka taba ganin anyi haka?, ka dauki matar ka ka tafi da ita zance, koko so kake fitina ta tashi tun ba aje gayin auren ba”

   Mommy babu komai fah daman ban son ne nabarta ita kadai agida, babu abun da zai faru”

   A’a sam bazai yiwu ba kai kadai zakaje, dan nasan kuka tafi tare ba hiran arziki za’ayi ba”

  Mommy babu fa wani ab…..

   Hannu ta daga mai sam ban amince ba, ka barta anan kaje ka dawo, karka sake ce min komai”

    Shiru yayi tare da sunkuyar dakai sannan ya juya ya fita tare da fadin”

Na tafi?

Biyo shi tayi nan ta same shi afalo yana cewa Ummi ki jirani barin je na dawo”

  Itako Ummi kule take domin taji haushi Mommy sosai da sosai”

   Dan haka kai kawai ta daga mishi dan bazata iya magana ba

  Har yakai kofa daddy yace”

Kai, dawo ka dauki matar ka Ku tafi duk in da zaku, in kunga dama ku wuce gida abin ku asa wata ranar”

STORY CONTINUES BELOW

   Juyawa Abdulmajeed yayi ya kalli Mommy fuskanta ba yabo babu fallasa”

   Dan haka yace”

   Ummi taso muje”

   Sallama suka musu suka fito”

   Suna fita Daddy ya kalli Mommy yace”

   Ke kiji tsoron Allan abin da kikeyi sam be dace ba”

   Hmmm alhaji laifin Abdulmajeed ne mutumin da zashi zance sai kuma ya tattaro matar sa?, wai Abdulmajeed lafiyan sa kalau kuwa?

   Lafiyan sa kalau, kawai yana nuna miki beson auren ne, tunda bazai iya bude baki ya fada ba, kuma ina son na baki shawara akan zancen auren nan, amman fa inzakiji”

   Inajin ka alhaji”

  Kinga idan bakibar maganan auren nan ba toh acikin biyu za’ayi daya”

Kinga mgnr Gaskiya Abdulmajeed yana son Ummi tun ba yau ba nasan kinsan wannan, kuma yaga ‘yan mata kala kala amman babu wadda ya saurara ko yace yana so har sai da ya jira Ummin dai, kin ga wannan kalmar da kikayi wai kodai beda lafiya ne, toh itama Ummi tasha fadan shi abaya, so da yawa in munyi waya takance wai akai yayanta asibiti dan yace mata kaza, mgn mara dadi yake yaba mata, nace mata lafiyar shi lau iskanci ne, to awannan lokacin ina sane sarai kishi ne ke sashi furta irin wannan kalamin shiya lokacin da mukaji lbrn rasuwan mijinta a wannan kauye banyi mamaki ba daya daki kirji ya kama hanya, nan nafahimci bakaramin so yake mata ba, dan haka yanzun ma daukota da yayi nuna muki yake beson aure inda yana so sanda zai sulale ya tafi bata da labari, mundin kuma kika dage, toh acikin biyu za’ayi daya”

   Ko dai ayi aure kwana kadan auren ya mutu, ko kuma aita rigima dan zaiyi wuya ya iya adalci”

   Bayan Mommy ta gama sauraran Daddy tace”

  Nima ai nasan yana son ta, amman ina mishi kwadayin auren budurwa ne, domin shima yabar tarihi, sannan son da yake wa Ummi yayi yawa ina son ya rabashi gida biyu kila zaifi samun kwanciyar hankali arayuwar sa”

  Dariya Daddy yayi ai kwanciyar hankali ta same abin da take so, kije ki kara tunani karkije ki daukowa yaro fitina”

  Mikewa yayi ya fice afalon”

   Tunani Mommy ta shiga me zurfi, gaskiya ina son ya kara aure wata zuciyar ce tace”

  Meyasa sai Abdulmajeed ne kadai ke gaban ki bayan ga ‘yan mata nan Har biyu aga gaban ki ai su ya kama ta kiyi kokari kiga kin aurar da su”

   Da wannan tunani ta mike tabi alhaji dakin sa, tana daga tsaye tace”

   Daman alhaji wani tunani nayi, nace su Hassana yakamata afara mgnr auren su”

  Dariya Daddy yayi sannan yace”

   Aini abun na zuciyanta dan harna amshi zancen auren su kallon ki dai nake yi”

  Au kace ni ina can na saki baki sai naji abu kwatsama, aiko da baka kyauta ba kuwa”

   Ai naga basu bane agaban ki kinfi maida hankalin ki gurin Abdulmajeed ne kad’ai”

   Murmushi tayi sannan tace”

   To yanzun me ake ciki”

   Shiru yayi sannan yace”

  Yauwa ni da Abban su muka zauna mukayi shawara, domin dai kinga ansha mu mun warke akan auren Ummi dan haka nasa a kamin bincike akan yaran nan dake zuwa wajen su”

    Bayanin da aka bamu akan su be gamshe mu ba dan haka muka yanke bada su ga tagwayen nan dake nemam su”

   Ya mutsa fuska Mommy tayi sannan tace”

STORY CONTINUES BELOW

   Alhaji aiko ita Hussaina bata son ‘yan biyun nan garama Hasssana ita kamar tafi sauraron su”

   Rabo da Hussainan nan ta cika rawan kai, tana son tayo halin Ummi ne, dan haka bazamu saurari zancen su ba, tunda dai munyi bincike yaran suna da asali me kyau kuma suna da tarbiya daidai gwargwado toh alhamdulillahi”

   Toh shike nan Alhaji Allah ya tabbatar da alheri”

  

      *****

Tun da Ummi ta zauna amotar take kunbure kunbure har suka isa gida”

   Ganin yadda take bata fuska yasa Abdulmajeed  ya sungumeta yayi cikin gida da ita, be dareta ako inaba sai akan makeken gadon sa, dukawa yayi kanta sannan yayi murmushi yace”

   Nine na bata miki rai sabo da na tafi dake gidan Mommy da karfi da yaji, ni kuma nayi haka ne dan naga kina fushi zan tafi zance, yanzun da bantafi dake ba ko nace miki banje ba yadda zakiyi ba”

Eh din, ai dan anganni ne akace karkaje, ni bani nace zan mika ba, kai jani da karfi

   Bakin ta ya kalla yadda take karkata shi tare da hararan sa, acikin zuciyar shi yace”

   Har yanzun dai rashin kunyar na nan, afili kuna yace”

    Wannan da naje dake zance bansan abin da zai faru ba”

   Toh ko zamu koma ne?,  nima ai naso muje din”

   Dariya yayi sannan yace”

   To shike nan ya wuce, ni daman nasan ba zance zani ba, yanzun taso muyi hira”

   Bacci nakeji”

   Ni kuma banajin bacci hira nake so”

  Kaga yaya karabu dani fah”

   Kallonta yayi sosai sannan yace”

  Jiba Zainab bason mu fara haka dake”

   Yaya mufara babu komai tunda Mommy na turaka wajen wata, gara intayata yiwa amarya tanaji,

   

   Wani irin kallo ya mata, sannan ya mike tare da fadin toh mubar mgnr haka nan, kuma idan kina mgn indai bata arziki bani karki kara kiran sunan Mommy aciki

   Kwaciya yayi kusa da ita zuwa can ya mike ya sauya kaya zuwa na bacci, sannan ya koma gadon ya kwanta”

    Ahakali ya mika hannun shi ya jawota ya rungume tare da lumshe ido”

   Itako Ummi wani irin kishi ne ya tasar mata tare da haushin Mommy me tsanani da takeji azuciyan ta, dumin ta lura ita take tura Abdulmajeed neman aure, tana cikin wannan tunanin taji ya fara lalubarta, cikin wani mugun haushi ta tureshi ta mike”

    Zainab meye haka?

  Hawaye ne yazo mata tasa hannu ta share sannan ta hadiye wani miyau me zafi tace”

   Ka jira har wadda Mommy ta zaba maka tazo mana ai, tunda kai dan gata ne a na maka kwadayin auren budurwa”

   Rufe ido yayi sannan ya bude ranshi ne ya bacci sosai dan haka ya nan danan jikin shi ya fara rawa besan sadda ya kwasheta da mari ba

   Hannu tasa da sauri ta dafe gurin shikuwa dunkule hannun sa yayi tare da binta da idanu, kash ya furta domin besan sadda hannun shi yakai jikinta ba”

Ummi kuwa bayan ta gama kare mai kallo wucewa tayi afusa ce tabar dakin”

   Bayanta yabi da kallo sannan yaja tsaki”

   Komawa gadon yayi ya zauna, meyasa na daketa ne, kai ya shafa sannan ya runts idon sa, zuwa can ya bude bazan iya kwana babu Ummi ba, amman dan me muna mgn zata dinga soko sunan Mommy sa’arta ce?

  Yin wannan tunanin yasashi ya kira wayar Sadiq”

   Sadiq din yana dauka yace”

  Lafiya kira da daddare?

   Tsaki yaja sannan ya shiga fada mishi abin dake faruwa”

   Kai Abdulmajeed wai yaushe matsala zatabar gidan ka ne, nifa nagaji wlh, ka dinga hakuri mana, dan macce tayi haka akan mgnr kishi ai bawani abubane”

   Amman muna mgn saita dinga sako sunana mahaifiyata”

   Amman ai ba zaginta tayi ba ko, ni kwata kwata yanzun agidan ka be kamata asako zancen kara aure ba aganina, inta kaice maka ni yariyar ma tausayi take bani dan ita kanta har yanzun hankalinta be kwanta ba, ni abin da nake so dakai ka dinga hakuri da ita da Mommy zata hakura kuma da anbar zancen auren sai wani lokaci”

    Tsaki yaja sannan ya shike nan saida safe”

   

    Yana kashe wayar ya mike, Dakin ta ya nufa domin ya rarrasheta”

  Itako Ummi batai tunanin zuwan shi wannan lokacin ba, tana kan gado ta zuba dagumi, ba marin da Abdulmajeed ya mata bane yafi bata haushi, illah yadda taga Mommy na nuna kiri kiri so take yayi aure harda wani hana shi yaje dani”

   Tana cikin wannan tunanin Abdulmajeed ya shigo jikin shi asanyaye”

   Daf da ita ya zauna sannan ya mika hannu ya roko kafadanta”

   Ummi kiyi hakuri raina ne ya bacci”

    Dauke kai tayi ahankali ya sake cewa kiyi hakuri kinji, nima ba fah bason auren nan nake ba, kuma ina iya bakin kokarina danna kyauce masa”

   Hmmm ai gara kayi tunda ni na taba aure kaje ka aure wadda bata taba aure ba kaji abin da akeji, karashe mgnr tayi cikin kauda kai”

   Murmushi Abdulmajeed yayi sannan ya kara jawota ya rungumeta tsam ajikin sa sannan yace”

   Ni bashi bane agabana, ni ke nake so domin komai inba daga gurin ki bane baya burge ni, ki yadda dani Ummi wlh babu wata ‘ya mace dake gabana nan gaba kadan zaki tabbatar da haka, irin wannan kala min yaita mata har ya samu ta sakko, ba kunya suka shiga faranta ran junan su”

   Washegari 6:30am yana makale da Ummi tamkar wani zai kwace mishi ita yaji wayar shi na kara”

   Tsaki yaja sannan yace mesa ma ban kashe wayar ba”

  Kallon wayar yayi tare da zaro ido sabo da sunan Nafisa da yagani”

   Cikin sauri ya dauka dan gudun kada karan ya tada Ummi”

    Abdulmajeed dan Allah kafito yan zun gani acikin agidan ka……

 

   Mmn Yazeed🔥 🔥🔥🔥🔥🔥

*KOWANNE BAKIN WUTA*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥

    ( da nashi hayakin)

💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by

    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*

          104

Cikin gida na???

   Kallon Ummi yayi sannan yayi sauri ya kashe wayar, tare da shafa kanta”

    Ahankali ya sunkuyo daidai goshin ta ya subbaceta sannan ya ya zameta ahankali ya ya kwantar”

    Ahankali ya sauka a gadon sannan ya jawo bargon ya rufeta”

   Sunbatanta ya sake yi sannan ya juya ya fita”

   Cikin tashin hankali ya fito tare da waiwayen bayan shi”

   Can Mesa ya hangota tsaye sanye da hijjabi”

   Da saurin ya karasa cikin rawan baki yake fadin”

   Nafisa me kikazo yi agidan nan?

   Hawaye ne ya zubo

tana shirin yin mgn yace”

  Kinga, Nafisa jeki gida zanzo na same ki, banson Ummi ta fito ta same ki”

  Ka bari muyi magana anan dan  gidan mu Babana ya hanani fita”

   Waigawa yayi ya kalle bayan shi sannan yace”

  Yi sauri ina jinki?

  Wasa ta fara da hannunta yayin da hawaye ke zubo mata tace”

   Babana yayi fushi dani doctor har ma yayi ikirarin aurer dani ga duk wadda yaga dama

  Ina cikin tashin hankali narasa inda zansa raina, kaika min alkawarin aure amman ka dauke kafa da zuwa wajena”

  Ji yayi hankalin shi ya tashi sosai dan haka yace”

   Kash😬 Nafisa kije ki gida zanzo na same ki, wannan mgnr bazai yiyu agidan nan ba”

   Ko kazo gidan mu baza abarni na fito ba, Babana yariga da yayi fushi, ‘yanzun ma besan da fitowata ba”

   Kai Abdulmajeed ya shafa sannan yace”

   Nafisa jeki gida zanzo”

   Kanata maimaita mgn daya doctor dan Allah ka taimake ni, karkaci amanata kayi min alkawarin aure”

   Juyawa Abdulmajeed yayi ya kalli cikin gidan sannan yace”

    Yanzun me kike son ayi?

   Dukar dakanta kasa tayi sannan tace”

   Inaso ne kagabatar da kanka awajen Babana amatsayin wadda zai aure ni”

   Bazai yiwuba Nafisa, ayanzun haka ina cikin wata matsalar ne, dan nima Mommy na ta dage saina kara aure kuma ita ta nemo min yariyar da kanta, kinga kuwa ban isa kuma nakai wata mgn gidan ba”

   Kuka NAfisa ta saka wiwi harda sheshsheka idanu kawai ya zuba yana kallonta, zuwa can ta dago ta kalleshi sannan tace”

Kana nufin dai bazaka aureni ba kenan?, ka manta alkawarin daka min, indai ko hakane ka cuceni bazan yafe maka ba…..

   Hannu ya mika ya ruko hannunta cikin sauri ta hankade shi tare da fadin karka tabani, daman ku maza haka kuke baku da amana sai da na sallama maka kaina ka gama jin dadin ka, yanzun dan kayi aure saika watsar dani?

    Gaba daya tunanin Abdulmajeed kullewa yayi burin shi kawai tabar gidan dan haka yace”

  Kinga Nafisa kije gida zanyi tunani akai anjima zanzo na same ki, kinsan halin Ummi bana son ta samemu anan wajen”

STORY CONTINUES BELOW

   Girgiza Kai Nafisa tayi wota doctor baka son bacin ran matar ka ni kuma ko oho, har wani tsoron fushinta kake”

   Shiru yayi yana kalllonta harta gaba sannan yace”

  Kije zanzo”

  Sai kaita cewa wan…..

Tsawa ya buga mata ki wuce ki tafi zanzo nace ko”

  Firgita tayi dan haka hawaye ya fara zubo mata”

   Cikin gudu gudu ta fita agidan, dan haka Abdulmajeed ya juya zai koma gida”

  Mamaki yayi sosai ganin Ummi tsaye abakin kofar, yaushe ta fito?, ya tambaye kanshi sannan ya karasa tare da sakar mata Murmushi”

   Sai dai ita bata mayar mai da Murmushin ba, cikin ido ta kalleshi sannan tace”

   Waccen wacece?

  Murmushi yayi sannan yace”

   Wata mata ce wai tazo neman tai mako ne”

    Taimako da sassafe?

  Wlh nima abin yaban mamaki”

   Shiru Ummi tayi zuwa can tace”

   Naga yariya ce ba wata babba bace, kuma kamar babu wahala ajikinta”

   Oho ni ban kula da wannan ba Ummi, hannunta ya kama suka shiga falo suka zauna, yana kallon idonta yace”

   Anya kuwa baccin nan ya isheki?

   Eh dakaina fa na tashi”

   Mikewa yayi ya danyi nesa da ita sannan ya ya daura kanshi kan cinyanta tare da fadin”

   Ni dai baccin be isheni ba”

   Wayyo yaya zaka karya ni fah”

Hmmm wai ke meyasa kin faye son jikin ki ne, kaina kawai na daura fa, Oya sosa min ya dameni da kaikayi”

    Hannunta tasa ta fara sosawa duk da tasan bawani kaikayi dayake mai”

   Shiko idonshi ya lumshe tare da ajiyan zuciya”

    Sun dauki tsayon minti dalatin haka sannan Ummi tace “

    Yaya?

  Na’am

   Gakiya ya isheka haka”

   Shiru yayi dan haka ta sake kiran shi”

   Amsawa yayi batare daya bude baki ba”

   Nifa nagaji ka

tashi”

   Cikin murya kasa kasa yace”

   Banjin ki bacci nake”

   Murmushi tayi sannan tace”

   Kana baccin ne ka iya amsa min?, ka tashi to muje daki ka kwanta”

  Kafada ya make, dan haka Ummi tayi dariya”

   Sannan ta zuba mishi ido fuskanta dauke da murmushi”

   Muryan shi can kasa yace”

  Meye kike kallo na?

   Dariya tayi sosai sannan tace”

   Kai da kace bacci kake, yaya kasan ina kallon ka?

    A jikina naji, tashi yayi ya zauna bari nayi wanka nafita, tunda kin Hanni bacci”

     Bawani baccin da kake idoka biyu”

   Ai tunda kin fiye son jiki dole kice idona biyu”

   Turo baki tayi tare da fadin”

   Kaima ai son jikin gareka tunda baka goya ni”

STORY CONTINUES BELOW

   Yana kallon cikin idonta yace”

   Wai ke bakya girma ne? har yanxun baki bar lbrn goyon nan ba?, toh shi kenan, ki bari ki haihu zanta goyaki har ki gaji”

   Kara turo bakin tayi tare da fadin”

   Yanxun baka min bane zakace sai na haihu, in dai lokacin ne banso na yafe”

   Murmushi yayi sannan yace”

   Toh shike nan jeki shirya kizo na goya ki”

  Mikewa tayi ta nufi daki, zuwa can sai gata tafito cikin riga da wando”

   Idanu ya zuba mata yayin da wani irin farin ciki ne ya kamashi gaskiya inason Ummi har bana iya kwatan ta son da nake mata”

   Yana cikin wannan tunanin ta karaso”

   Tsaye tayi agaban shi sannan tace”

   Toh dan sunkuya na hau”

   Dariya yayi sannan ya kalleta”

   Na sunkuya  da gaske kike ne?

   Eh mana dakai wasa kake?, Bata rai tayi sannan ta juya tana zobura baki”

   Zo, zo muje, tunda da gaske kike mu zagaya baya sai ki hau”

    A’a ni daga nan zaka goya ni, indai ba hakaba abar shi, juyawa ta sake yi dan haka ya riko Hannunta tare da fadin”

   Kinga, kina son wani ya ganmu ne?, yanzun idan na goyeki daidai mun fita wani bako yazo fah?

   Ya mutsa fuska tayi tare da fadin to meye?

  Murmushi yayi sannan ya sake cewa”

   Ummi muje baya, duk abin da kike son nayi zanyi amman yanzun zan iya goyaki mu na fita kuma mucikaro da wani, kinsan ko su Hassana suka ganni goye dake raina ni zasuyi ko?

   Dagewa Ummi tayi duk abin da ya fada mata bata yadda ba sai da yayi mata yadda take so sannan hankalin ya ya kwanta”

  Sai kusan 11:00am ya lallabata suka shiga gida duk jikin shi zufa, yayin da Ummi ke haki”

    Abakin gadonta ya zaunar da ita sannan yace”

   Hankalin ki ya kwanta yanzun ko?, hannun shi yakai kan cikin ta daya dan fara tasawa kadan yace”

   Wai bakijin nauyin wannan ne?

  Murmushi tayi tare da kyauda idon ta”

   Ahankali ya sake cewa”

  Ki rage son wasan nan kodan abin da ke cikin ki, kibari har ki haihu sai kiyi duk wasan da ranki ke so”

   Komawa tayi ta kwanta, matar da tazo nai man taimako ce ta fado mata, kamar tasan matar, yana yin jikinta kamar ta taba ganinta”

   Shiru tayi tare da zurfafa tunani har Abdulmajeed ya kula da hakan”

  Ummi tunanin me kike?

   Dan zabura tayi tare da fadin”

   Yaya daga yanzun duk matar da tazo nemen temako ka daina zuwa da kanka, sai in namiji ne saika je”

    Daga sama yaji zancen, dan haka yayi Jim zuwa can yace”

   Shike nan naji”

  Shiru tayi zuwa can ta sake cewa nifa kamar ma nasan matar”

   Gaban shi ne ya fadin, mikewa yayi”

   A ina zaki santa?, dan Allah kibar mgn nan koma dai wacece bata wuce ba, juyawa yayi ya shige toilet da saurinsa”

  Ko acikin toilet tunani yake wai me yasa beson Ummi ta fahimci wani abu”

   Wata zuciyar ce tavashi amsa sabo da baka son ranta ya baci”

   Yana tsaka da wannan tunanin yaji Ummi tace”

     Yaya?

   Tsayawa yayi cak na’am Ummi ya akayi?

  Daman cewa nayi matar da tazo neman temakon ka bata wani abu ne?

    Jim yayi sannan face”

   Eh na bata kudi”

   Cikin tuhuma tace daman da kudi ajikin ka kayi baccin??

   Kash 😬 wai Ummi wacce irin yariya ce?, me zance mata ?, wai duk kishin ne haka?

    Yaya bakace komai ba”

   Dakewa yayi Ummi kijira harna fito kinsan bakyau mgn a toilet ko?

   Komawa tayi ta zauna jikinta babu kwari, yayin da ta fara wani irin tunani mara dadi, ni banga lokacin daya bata kudi ba, zanfi yadda idan yace shawara tazo nema dan naga sumyi mgn me tsayi da ita, toh ma wai meyasa banje gurin ba menene ya hanani zuwa?, wacece wannan kuma me tazo nema agurin sa dan baxance gurina ba”

    Fitowan Abdulmajeed yasa ta juya tana kallonsa, bata son yayi mata kallon me neman fitina dan haka bata sake tambayan shi ba, amman a zuciyan ta tunani take sosai”

      *****

Abdulmajeed kin zuwa gidan su nafisa yayi domin ko yaje din besan me zaice mata ba”

   Yana tashi aiki gidan Mommy ya wuce, yaji mamakin da bata mai zancen auren ba, harya tashi yayi sallama da ita bata cemai kalaba ko da besan meye azuviyarta ba, yaji dadi sosai”

    Itako Mommy yana fita tace”

   Ja iri gaskiyan daddyn su ne, be kyaunar auren nan Sam, ni tunda nake bantaba ganin me irin halinsa ba, she ko sha’awan Auren budurwa be yi?

   Ummi kuwa har dare tana tunanin matar da tazo dazon domin har yanzun abun da yagaya mata be shigeta ba”

   Shima Abdulmajeed ya kula da hakan dan haka ma yau beson hirar tasu tai tsayi domin ya kula rigima take son yi, dakin sa ya zauna yana me addu’an Allah yasa Nafisa ta hakura dashi, Allah yasa tayi fushi tabar ni”

   Sallaman Ummi ne ya katse mai tunani, juyowa yayi yana kallonta fuskan shi dauke da Murmushi”

   Itama murmushi ta mayar mai, adai dai lokacin wayar sa tai kara”

   Juyawa yayi ya kalli wayar Nafisa yagani, dan haka cikin sauri yai kasa da wayar tare da kasheta gaba daya”

   Duk abin da yayi Ummi na kallon shi, jikinta taji bebata ba, dan haka ta mike tare da fadin ina zuwa”

    Window taje ta yaye labulen, daga can nesa ta hango wata mata wadda take kyautata zaton matar dazon ce….

Mmn Yaidan ex🔥 🔥🔥🔥🔥🔥

*KOWANNE BAKIN WUTA*

🔥🔥🔥🔥🔥🔥

( da nashi hayakin)

💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by

*Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM🐄​*

_*Wannen page din tsaraba ne gareku masoya na aduk inda kuke😘❤❤❤*_

105

Hada kanta tayi da kirjin da domin buye murmushin ta”

Shima cikin murmushi ya rungumeta tare da jin wani irin farin cikin na shirgar shi, acikin zuciyar shi yace”

Wannan wannan Mukhtar din yaso maida ta naka kashashshiya”+

Yana cikin wannan tunani Ummi tace”

Ko baka so ne??

Niko nake so Ummi, suma sukafi komai Jan hankali na”

Toh ina jin ka”

Ajiyan zuciya yayi sannan ya dagota yana kallon cikin idonta yace”

Ummi nakasan ce ina son kallon ki tun baki wuce shekara 9 ba, haka nan nake zuwa gidan ku kawai dan inkalle ki in dawo, gashi ni ban iya wasa da yara ba, tun ina makaranta harna fara aiki ya zamar min jiki kullum na tashi aiki gidan nake fara zuwa, har zuwa lokacin da kika fara girma, alokacin ne na fara tunanin kodai sonki nake?, domin duk wata mace da zata min kwarkwasa bata burge ni, aduk lokacin da wata mace zata tsaya gaba na kece kike fado min azuciya, dan haka nayi tunanin nafara janki ajikina, lokacin dana zo da niyyar hankan saina same ki ke dasu Hassana kunata hayaniya duk cikin kinfi su rawar kai, dan haka nafasa dan gudun zubar da girma na, nacigaba da zuwa gidan ku har ki ka zama budurwa, kwatsam sai Daddy yazo min da zancen aurenki ban ce a’a ba ban kuma ina son ki ba, har saida kikace baki sona, ni ina ganin baki

Kaiba ashe kina can kina soyayya awaje”

Cikin sauri, Ummi tace”

Ayya yaya bafa awaje bane acikin gida ne fa, kuma ai Abba ya sani, da izzinin sa na fara fita, kai dai kawai baka zuwa lokacin ne”

Hmmm Ummi kin wahalar dani da yawa, nasha wahala sosai lokacin da kikace baki sona, narasa inda zansa kaina, ke har kwakwalwata juyawa tayi, alokacin ne nafara shan sigari gashi har yanzun na ka kasa barinta, sannan wannan lokacin ne nafara mu’amala da Nafisa domin su kadai suke rage min takaici”

Hawaye ne shabe shabe fuskan Ummi tana share hawayen tace”

Yaya toh meyasa alokacin baka gaya min halin da kake ciki ba?, ko su Abba daka gaya masa nasan bazai tsallake kaba dan lokacin ya nuna beson aure na da mukhtar, ni kuma lokacin bantaba kawowa kana sonaba, baya ga haka kuma kallon wani mutumi me wuyar sha’ani nake maka, ga wani balakin tsoron ka nada nake ji”

Yanzun fah? Ko har yanzun ma kinajin tsorona?

Na daina ai da kaine kake hararana, sunkuyar dakai tayi sannan ta sake cewa”

Dan Allah yaya karka kara shan sigari, kai kasa kanka dan Allah daga yau kace kabarta”

Zanyi kokarin hakan ummi insha Allahu”

Kuma dan Allah ka yafe min ka dauki komai amatsa yin kaddara ce”

Ya wuce ai, hawaye ya fara share mata yana fadin”

Toh meye kuma na kuka, rungume ta yayi, dan haka taita sauke ajiyan zuciya, natsuwa takeji sosai na shirgarta ashe haka yayana yasoni ban sani ba?, dadine ya kamata dan haka ta shiga murmusawa”

Zuwa can taji Abdulmajeed na fadin”

Ina jinki nima fada min abin da kika fara fada”

Tana kwance ajikin shi tace”

STORY CONTINUES BELOW

Kasan me?, idan kaxo kullum Umma sai tace na kawo maka abin ci, kai kuma kullum din baci kakeba, ita kuma bata fasa baka, kai kuma kanaji zatace akawo amman baka cewa baxa kaci ba sai ankawo ka gama zaman ka saika mike kace Umma barin je, karashi mgnr tayi tare da fashewa da dariya”

Murmushi ne sosai akan fuskan Abdulmajeed yace”

Ina jinki?

Daker ta tsaida dariyar tace”

Nikuma hakan ke matukar bani dariya kana fita zanta ma Umma dariya tare da bata shawaran ta daina baka abincin ta kai har cewa nake wlh Yaya Abdulmajeed dinnan zararre ne, kara fashewa tayi da dariya”

Dan haka ya rike kunnenta daya ya murde, har saida ta saki kara”

Dariya yayi sannan ya saki kunnen yace”

Angaya miki cin abinci ke kawoni?, mantawa ma nake da wani abinci agabana”

Murmushi tayi sannan ta koma kan kirjin shi ta kwanta, shikowa Abdulmajeed hannun yasa yajawo bargon ya rufe su, daga can naji yana cewa oya cika alkawarin da kika dauka”

Washegari Abdulmajeed kasa zuwa ko ina yayi dan haka ya kashe wayar sa, sai yamma ya fita badan ya gaji dajin dubin Ummi ba, sai dan yabarta ta sarara”

Gidan Sadiq ya nufa domin yasan yanzun yabar Office “

Tunkafin ya isa ya kirashi awaya cewa ya fito ya rakashi wani waje”

Bemai musu ba ya fito ya sameshi kamar yadda yace, sun dauki hanya kenan yace”

Ina zaka kai ni babu baya ni?

Gidan su Nafisa zaka rakani”

Me zakayo acan din?

Nan ya kwashe komai ya fada mishi”

Shiru Sadiq yayi sannan yace”

Yariyar taban tausayi wlh, irin abin da naguda kenan tun farko, ninasan ba aurenta zakayi ba dama ace baka samu Ummi ba toh wata kila ka aureta, gaskiya abu beyi dadiba, dazaka daure ka aureta tunda ka riga ka lalata ta”

Wani irin kallo Abdulmajeed yayi masa sannan yace”

Nina lalata ta?, ai dama can alalacen ta take, ina ce lokacin kai da bakin ka kake cewa ba natsatsiya bace”

Eh nina fada, yanayin ta na duba kuma yariyar bata da kamun kai sannan mutane nacewa tana yawo amman ai duk wannan zargine tunda bangani ba, naka ko nagani da idona kana tattaba musu yariya”

Sadiq daman fa nafisa tasan komai, wlh ita takowa min lokacin mani bansan komai ba, kuma nima ina tausayita amman gaskiya bazan iya aurenta ba”

Hmmm to yanzun me zakaje yi gurinta?

Hakuri zan bata kawai”

Da haka suka isa kofar gidan awaya ya kirata ta”

Bayan ta dauka yace”

Gani akofar gidan ku”

Tajima bata fito ba har suka gaji da da zama harya fara tunanin kara kiranta ta fito”

Bayan ta gaishesu Abdulmajeed ya zuba mata ido, zuwa can yace”

Nafisa nazone nabaki hakuri, sannan nabaki shawara kibi zabin iyayen ki, danni iyayena tuni suka min gargadi akanki, dan haka basu karbi zancen auren ki…….

Hannu ta dagamai naji wannan sai kuma me?

Shiru yayi yana kallonta, zuwa can yace”

Daman abun da ya kawoni kenan, hannu yasa a aljihu yaciro kudi masu yawa ya mika mata”

STORY CONTINUES BELOW

Murmushi tayi sannan tace “

Bana so duk wani abu daya fito daga hannunka, kuma tsakanina dakai Allah ya isa”

Wani irin kallon ya mata sannan yace”

Ke kibar ganin ina baki hakuri ina ce ke kika min tallan kanki ta hanyar nuna min tsaraicin ki, idan kin manta ne ki tuna bada karfi na miki ba, juyawa yayi ya shige motar shi batare da ya waiwayi bayan shi ba”

Har sukayi nisa Sadiq kallon shi yake tare da fadin meye amfanin irin wannan rayuwar”

Abdulmajeed bece komai ba har yakai Sadiq gida huci yakeyi”

Daga nan gida ya wuce, domin tsoro yake kar Mommy tamai zancen auren nan”

Ya shiga gida cike da bacin rai, amman yana hada ido da Ummi yaji bakin cikin shi ya yaye, wani irin sanyi yaji yana ziyartan shi dan haka ya riketa ya kankame”

Tun daga ranan Abdulmajeed da Ummi zama suke me dadi gwanin ban sha’awa Office kadai ke fitar dashi daga gida, ko yana can din Allah Allah yake atashi yasata a ido kullum sonta karuwa yake azuciyar shi”

Haka itama Ummi kullum son Abdulmajeed kara shigarta yake, har takaici take inama shita aura tuntuni, abun da bata taba tunani ba, yaya Abdulmajeed yana kula dani yadda ya kama ta, bayason duk wani abu dazai dame ni, kullum ji yake kamar ya hadiye ni, ashe Hajiya tayi gaskiya ta take kiransa Bawan Allah

Washe gari ya samu lbrn auren da maifin nafisa ya daura mata da wani mutumin wada matarsa ta rasu”

Haka sukai tacin soyayyar su har tsayon sati uku batare da Abdulmajeed ya leka gidan Mommy ba”

Yau Abdulmajeed nagi dan haka yayi nufin zuwa gidan Mommy”

Saidai har tsoron hada ido yake da Mommy dan tunda yaga bata nemeshi ba yasan tayi fushi ne gara ma Daddy suna waya”

Yana cikin wannan tunanin Ummi ta fito daga kitchen da dan matashin cikinta, wani irin tafiya naga tayi tamkar dai ba Ummi dana sani ba”

Kallonta Abdulmajeed yayi ya fashe da dariya tare da fadin”

Kin fetse da rashin kunya ko?

Jikin shi tahau ta zauna sannan ta shafo gemon shi tare da fadin baka so ne?, kaifa kace sunfi komai jan hankalin ka koba dalili kenan da kwanaki kace kabar min kayana ba?

Inaso mana kawai dai mamaki kike bani sai na dinga ganin kamar bake bace”

Nice ina tuna maka abin da kafi so ne”

Murmushi yayi sannan yakai hannun shi yana fadin”

Kin kyauta Allah ya miki albarka”

Wasa suka shiga yi zuwa can yace”

Dauko mayafi muje yawo”

Cikin murna Ummi ta mike ta canzo mayafi shima kaya ya canza ya fito suka fice gwanin ban sha’awa”

Har suka shiga mota murmushi ne akan fuskan su, Abdulmajeed na zama ya riko hannun Ummi, sunyi nisa ya juyo ya kalleta ina zamu fara zuwa?

Gidan hajiya tace da sauri”

Beyi musuba akofar gidan ya tsaya

Ummi ce ta fara shiga dan haka Hajiya na ganinta ta fara fara’a tare da fadin”

Kagamin marakunyan yariya ni banyi kishi ba nabaki sirin sai ki yi mulumbukui ko godiya babu”

Hannu tasa abaki alaman tai shiru tare da fadin kari fa nazo ne ma”

STORY CONTINUES BELOW

Ban bayarwa mara kunya kawai kina banso banso ji inda kika zama ‘yar lukuta”

Daidai lokacin Abdulmajeed ya shigo yaji abin da Hajiya ke fada dan haka ya fara dariya”

Hajiya naganin fuskan Abdulmajeed tace eyyye eh lalllai dole ka manta da uwayen ka BAWAN ALLAH”

Dariya yayi sosai sannan yace”

Haba Hajiya bama haka dake fah, daidai lokacin daya zauna, Ummi ce ta matsa kusa da shi tamkar zata shige jikin shi dan haka ya fara tureta”

Lahh wai kunyar hajiya kake ji ne?

Murmushi hajiya tayi tare da kama bakinta🤔 a’a kar yaji kunyata fitsararriya, aike daman can haka kike”

Murmushi Abdulmajeed yayi sannan ya matsa daga kusa da Ummi ya riko hannuta ya shiga gaida hajiya”

Bayan sun gaisa tace”

Kai kuma sai kaje ka labe agida Uwayenka nata cigiyar ka, ni nace musu ma subar ka lfy ke buya”

Hajiya aiki ne yamin yawa kwana biyu”

A’a Bawan Allah ban sanka da karya ba, kace dai takwara ta rika”

Murmushi yayi tare da sosa kai”

Nan hajiya ta shiga fada musu ansa ranan auren su hassana da hussaina wata biyu masu zuwa”

Suna cikin mgn da Hajiya yaji Ummi Ummi ta fara tsungulin sa da daya hannun ta”

Murmushi yayi sannan ya kalketa yaya akayi??

Mutafi”

Kingaji ne?

Eh

Hajiya ya kallah yace Hajiya bari muje zan dawo musha hira”

Toh 🤔ku gaida gida tace bakinta a wangale

Abdulmajeed ne ya fara fita dan haka Ummi ta koma kusa da Hajiya tace”

Yaushe zan turo akarban min”

Ke shiga hankalin ki, babu abun da zan kuma baki saikin haihu, hanya ta tuna mata tare da fadin wuce kibani waje”

Ficewa tayi tana kunkunai Hajiya ko hannu ta daga tana ma Allah godiya daya hada mata kan jikokin ta”

Amota Ummi ta samu Abdulmajeed ganin ranta bacce ya fara fadin”

Hajiya ce? rabu da ita yi hakuri”

Hira suke yi sama sama har suka isa gidan Mommy”

Duk da Ummi tana jin haushin Mommy da fara’arta ta ta shiga gidan”

Abdulmajeed kuwa atsorace yake saidai beson Ummi ta gane”

Ummi nayin Sallama Mommy ta amsa da sauri tare da baza ido”

Murmushi tayi lokacin data hada ido da Ummi”

Zama Ummi tayi sannan ta gaida ta tana cikin amsa mata Abdulmajeed ya shigo cikin dari dari”

Murmushi Mommy tayi sannan tace”

Idon ka kenan?

Sukuyar dakai yayi Mommy kiyi hakuri inata cewa zan zo na gaishe ki, abubuwa ne suka min…..

Ka gaishe ni bani da Lfy ne???

Toh Mommy sai baki da lfy zan gaida ki?

Eh aina dauka saina kwanta ciyo”

A’a Mommy kiyi hakuri”

Toh ai shike nan kuna nan dai lfy ko?

Lfy lau Mommy”

STORY CONTINUES BELOW

Toh yayi kyau, ke Ummi ya jikin naki?, koda yake naga har wani kiba kika yi”

Sunkuyar dakai tayi tare da murmushi”

Maida Kallon tayi gurin Abdulmajeed tace”

Sannun ka”

Murmushi yayi sannan yace”

Kai Mommy nafa ce kiyi hakuri”

Me nace maka nace ma wani abu ne?

Mikewa Ummi tayi ta nufi dakin su hassana dan tunda ta shigo takejin motsin su”

Dan haka Mommy ta samu daman cewa Abdulmajeed ai basai ka dauke kafa zan san baka son auren ba, kasha zaman ka da Ummi, idan Allah ya nufa nan gaba zakayi ka nema da kanka”

Dagowa yayi ya kalleta Mommy yace da gaske?

Ina wasa dakai ne?

A’a nagode Mommy”

Acikin zuciyarta tace”

Lallai Abdulmajeed nason Ummi harda godiya, amman da alma ya samu kwanciyar hankali dan gashi yayi fari yayi kiba”

Zama sukayi sukaita hira shida mommy tare da shawara akan auren su Hassana

Fara ganin Mommy ta joya mata baya Abdulmajeed kuwa yana kollonta”

Hankalin shine ya dauke daga wajen hiran ya koma kallon Ummi, yana yi yana basar wa duk da haka Mommy ta fahimci duk yadda akayi shida Ummi ne dan haka taki waigawa”

Karasowa tayi cikin dakin amman duk da haka kallonta yake”

Zama tayi agaban Mommy kusa da kafarta, duk da haka bata daina kirkizan ba shiko sai Satan kallon ta yake yana murmushi ya kasa dauke idonsa akanta”

Ganin haka Mommy takali Ummi, me yakewa Murmushi haka ne, duk iya dobawan ta bataga me Ummi keyi ba, amman da takalli Abdulmajeed har yanzun santan kallon ta yake yana boye dariyar sa”

Murmushi mummyn tayi sannan tace”

Ku kuka sani, mikewa tayi tabar su awajen dan haka Abdulmajeed yace”

Ummi baki da kunya ko?, dan Allah ki daina min wannan girgije girgijen kibari har mu koma gida”

Make kafadan ta tayi dan haka ya kara fashewa da tariya”

Daidai lokacin Mommy ta fito acikin zuciyarta tace”

Wato duk daurewan da Abdulmajeed yake iskanci ne, tunda nake bantaba ganin fuskan shi washe na tsawon minti 10 ba sai yau”

Wuni sukayi har gidan Umma sukaje suka gaida ta sosai iyayen su sukaji dadin ganin su tare dasa musu albarka”

Agajiye suka koma gida tunda ranan suka shiga shirye shiryen auren Hassana da Usaina”

Bayan wata biyu akasha bikin ‘yan biyu lokacin cikin Ummi ya fito sosai dan haka Abdulmajeed yaita kafkaf da ita bini bini ya shigo yace”

Mommy Ummi fah”

Anty Salmace tagaji da tambayan Ummi da yake dan haka wannan karo daya shigo yana baza ido tabishi da ido”

Zuwa can yace Mommy Ummi fah?

Cikin sauri anty Salma tace”

Kai dallah karka damemu, kai ko kunya bagaji ka dinga tsallake mutane kana tambayan Ummi, Ummi jaririya ce?, ko ance maka bacewa zata yi?

Kai anty nemanta neke akwai abin dazan ansa ahannunta”

Ka fada me kake so a anso maka?

Juyawa yayi ya fice domin ya rasa me zaice”

STORY CONTINUES BELOW

Yana fita akasa dariya anty Salma ma murmushi tayi tare da fadin”

Haba ya dame mu, ya dame yariya, bada n karnayi karya ba dasai nace ya kirata yayi sau goma”

Kome yake cemata oho”

Dariya duk akayi Ummi dake can cikin daki tana jinsu dan haka ta kira shi awaya yana dauka tasa dariya tare da fadin”

An kore shi😂

Shima dariya yayi sannan ya kashe wayar dan gundun karta xarar dashi domin atsakiyar mutane yake”

Haka aka kare biki lfy cikin farin cikin da walwala Abdulmajeed da kansa yakai Ummi gidan Amare dan haka kowa yayi mamakin sauyawar halin sa, ayanzun bashi da wuyar dariya yayin da mutane suke rasa me Ummi take yi ne take sashi dariya koda yaushe, ko ya daure fuska wani lokacin daya kalli Ummi zai fashe da dariya”

Bayan bikin ‘yan biyu da wata Uku Ummi ta sunkutu danta na Miji zarkadede tamkar babanshi”

Abdulmajeed baki har kunne”

Asibiti ta haihu dan haka daga can gidan Mommy aka wuce da ita, ba da sonran Abdulmajeed ba”

Sosai Mommy take kula da jaririn da Ummi ta haifa tamkar ta lasheshi harji take ma kamar tafi sonshi akan Abdulmajeed din”

Hajiya ma gidan ta dawo ita kewa Ummi wanka tare da jaririn ranan suna ta zagoyo yaro yaci sunan Muh’d”

Mutane Abdulmajeed ya tara sosai jaririn yakai cikin abokanshi tare da tambayan su dawa yaron yayi kama?

Wani irin farin ciki gaba daya Family suka shiga yayin da Abdulmajeed da Ummi suka kara mannewa junan su”

Mommy gajiya tayi da yadda Abdulmajeed yake makalewa agidan dan haka tace”

Sau daya zai dinga zuwa arana”

Hakan ba karamin takurashi yayi ba”

Dan haka idan yazo yake dadewa yaita wasa da Muh’d “

Kwanan su 41 Mommy ta tattara ta maida su gida Abdulmajeed kasa boye farin cikin sa yayi sai washe hakori yake haka yacigaba da rainon Ummi da Muh’d tamkar ya hadeye su yauma kamar kullum bayan Abdulmajeed ya dawo daga aiki suna zaune shi da Ummi daker su ka lalaba Muh’d yayi bacci”

Abdulmajeed jawo ta yayi ya rungume tare da yi mata rada akunne”

Murmushi tayi sannan tace”

Yaya yaushe zakayi aure?

Aure kuma?, Ummi baki kishina ne?

A’a niko nake kishin ka, amman nafison indai zakayi ka min tunda kuruciya ta ba sai na tsufa ba”

Dariya yayi sannan yace”

Ni Ummi ke kadai kin isheni babu auren dazan yi”

Wani kallo ta wurga mai yaya baka son ka aure budurwa aleda??

Murmushi yayi, haba Ummi ki daina wannan tunanin danni baya kagabana ke din dai nake so ba wani abu ba, kuma tunda na mallake ki Alhamdulillahi insha Allahu mutuwa ce zata rabamu”

Rugume shi tayi sosai domin har zuciyarta ta amince dashi”

Suna cikin haka Sadiq yayi sallama”

Mikewa Ummi tayi da sauri tabar jikin Abdulmajeed “

Bayan Sadiq ya shigo tafawa suka yi sannan Sadiq ya nemi guri ya zauna”

Ummi ma gaida Sadiq tayi sannan sannan ta mike zata basu guri”

Wani irin kallo tama Abdulmajeed sannan tamai abun da ta saba mai koda yaushe”

Murmushi yayi tare da kawar dakai”

Gani yayi har yanzun bata wuce ba dan haka ya sake kallonta”

Tintsirewa yayi da dariya tare da cewa jiki gani nan zuwa”

Ummi na wucewa Sadiq yace”

Wai me Ummi keyi ne yake saka dariya haka?

Murmushi yayi sannan yace rabo da ita Sadiq tsokana ta take yi”

Gaskiya ina son sanin abin da ke saka dariya haka, ka gaya min mana meye sirri”

Dariya Abdulmajeed yayi sannan yace”

Wannan sirrine tsakanina da ita banson gulma dasa aido

Alhamdulilahi

Anan kawo karshen wannan lbrn na KOWANNE BAKIN WUTA sai mun hadu a nagaba idan idan Allah yabani iko, Allah yasa anfahimci darasin dake ciki,

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *