ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 3

 ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 3

Ummi ta ce, “Wallahi ita ce”. 

A dai-dai lokacin da Yaya Aliyu ya shigar da hancin motar A.B Bamalli Estate, ya yi kyakkyawan horn yaran dake kusa a kofar flat din Baba Barau suka rugo suka fidda kayan a boot suka shigar mana dasu gida. 

Yaya Aliyu Boys Qtrs dinsu ya wuce bai kara kula mu ba. Su Abba na jidon kaya suna ihu wai za su ci cornflakes din ‘yan bording school. Na ce, “Wallahi duk wanda ya bude mana kaya sai na kabari ya fishi jin dad’. 

Ina kwance gadon Hajja na ji shigowar su Ummi, suka shigo da kaya _ niki-niki, Ummi cike da tsegumi take ce da Hajjah, “Wai Hajja ki duba ki ga duk yawan kayan nan da muka shigo sai da Yaya Aliyu ya sake sayen kwatankwacinsu wa Fa’iza ita kadai ranta’’. 

Zanirah ma ta ce, “Kuma Hajja baki gani ba, wai don dan fadan nan da Ya Fa’iz ya yi mata dazu kafin mu fita ya yi ta lallaminta tana masa wulakanci da kada ido, ita ba ta yarda ba babba”. 

Hajjah ta yi kamar ba ta ji su ba ta shiga duba kaya, ta ce, “Ya ban ga kwaki ba bayan kun ce bakwa son wanda na sayo fari kuke so?” 

Ummi ta ce, “Tab! Waye zai sha miki kwakin? Ki jimu da tsohuwa da neman ta da zaune tsaye’”’. 

Hajjah ta dauki mafici ta yi kanta ta runtuma da gudu. Hajjah ta ce, “Ja’ira, gobe dai kun barni da ‘yan jikokina mu huta bakinmu alaykum. Haba! Yara uku duk kun bi kun isheni kamar ina zaune da zaratan “yammata”’. 

Ummi ta zo ta kwanta a gefena ina kwance rigingine na yi nisa cikin tunanin irin kulawar da Yaya Aliyu ke yi mani. Hakika shi dan’uwa ne mai matukar kirki da dabi’un kyakkyawar mu’amalar zumuncl. 

A lokuta da dama ina kwatanta kirkin Aliyu da wani cikin yayyenmu, amma ban ga kwatankwacin shi ba. Halinsa daban, simplicity dinsa daban da dukkan mazan Zuri’ armu. 

To amma kulawarsa gareni ta zarta 

wadda yake yiwa kowa, babban misali su Zanirah da tare muke rayuwa yana fifitani a kansu. Sai a hankali nake jin Yaya Aliyu na kwanta min a zuciya saboda kyawawan halayensa da kulawar da yake yi mun. 

Tunani na ya gangara ga abin da ya fadi dazu na cewa, wai ba zai iya barci idan ina fushi da shi ba, saboda abin da yaro baya ganewa sai ya girma. Shin mene ne wannan abun? I’m quite curious… 

Kamar Ummi ta san abin da nake tunani, ta yi murmushi sai cewa ta yi, “Princess har an soma tunanin Yaya Aliyu? Ayi hakuri dai muje kwalejin mu gama, in kuma auren za ayi sai a fada mana mu fara shiny’. 

Na mike a fusace na soma dukanta ina yakushinta ta sa ihu, nan da nan Hajja ta shigo za ni na zamewa kamar ta fadi. Ta ce, “Wai ke wacce irin masifaffiyar yarinya ce ne Fa’iza? Ke daya duk kin buwayi gidan nan, daga ki yi da wannan sai ki koma ki yi da wancan?” 

Na sa kuka na ce, “Hajjah cewa fa ta yi wai ina tunanin aure, “yar iska ta dauke ni 

ko me? Bayan ni tunanin su Walida nake 

299 

yi”. Hajjah ta ce, “To yi hakuri wasa take 

miki, ke kuma Ummi kada na kara jin makamanciyar wannan maganar ta fito daga bakinki zan saba miki fiye da zaton ki”. Ta juya ta fita. Zanirah ta bimu da kallo kurum, sai dai na lura tun shigowar ta dakin akwai abin da ke damun ta. 

2K Ag Ag 

Ranar da zamu tafi FGGC Gusau ta kama litinin ashirin ga watan Nuwamba, don haka sanyi ya yi tsanani ainun. Tun asuba muke ta shiri, murna kamar kanmu aka fara zuwa makarantar kwana. Mun yi tsaf cikin uniform abin sha’awa. 

Na hade gashina cikin (hair-bound) kalar tsanwa cikin sayayyar Yaya Aliyu ne. Hajja dake azkar din safiya a gefe bisa shimfidar sallarta ta shafa addu’a ta juyo ta dube mu. 

“Yanzu duk wannan azarbabin da kuke wa kuke zaton cikin yayyunku zai mike cikin wannan azababben sanyin ya kai ku 

makarantar?” 

Na ce, “Wallahi babu kam Hajjah, ai Isa direba ba zai ki ba. Ko ya kika ce Ummie?” 

Ummi ta ce, “Kwarai”’. 

Zanirah ma ta shirya cikin uniform na GGSS Giwa, kasancewar ita makarantar ta 

daban ta gwamnatin jiha mune a gwamnatin tarayyah. 

Riga da zani da hijabi shudi da fari, ta yi kyau abinta. Na tuna da banki na da nake tara kudi a ciki da na baiwa Yaya Aliyu amanarsa tun wancan satin. Na ce, “Hajjah ko Yaya Aliyu ya tashi yanzu? Bankina”’. 

Hajjah ta ce, “Tabdi! Aliyu makiyin sanyi ko na ruwan sha shine zai mike miki yanzun? Karfe shidda?” 

Na janyo farin cambas na daurawa kafata na yo tsakar gida da niyyar daukar suwaita ta a kan igiya da na shanya tun jiya. Cikin muku-mukun sanyin nan ma’abocin hazo da ya lullube sararin samaniya, sanye da bakar shirt da shudin wando jeans ya daura ‘thick-coat? doguwa har gwiwarsa, hannayensa duka zube cikin aljihun coat 

makarantar?” 

Na ce, “Wallahi babu kam Hajjah, ai Isa direba ba zai ki ba. Ko ya kika ce Ummie?” 

Ummi ta ce, “Kwarai’”’. 

Zanirah ma ta shirya cikin uniform na GGSS Giwa, kasancewar ita makarantar ta 

daban ta gwamnatin jiha mune a gwamnatin tarayyah. 

Riga da zani da hijabi shudi da fari, ta yi kyau abinta. Na tuna da banki na da nake tara kudi a ciki da na baiwa Yaya Aliyu amanarsa tun wancan satin. Na ce, “Hajjah ko Yaya Aliyu ya tashi yanzu? Bankina”’. 

Hajjah ta ce, “Tabdi! Aliyu makiyin sanyi ko na ruwan sha shine zai mike miki yanzun? Karfe shidda?” 

Na janyo farin cambas na daurawa kafata na yo tsakar gida da niyyar daukar suwaita ta a kan igiya da na shanya tun jiya. Cikin muku-mukun sanyin nan ma’abocin hazo da ya lullube sararin samaniya, sanye da bakar shirt da shudin wando jeans ya daura ‘thick-coat? doguwa har gwiwarsa, hannayensa duka zube cikin aljihun coat 

din domin kare sanyi, yana jingine jikin tagar dakin Hajjah. A hankali na ambaci sunansa cikin mamaki…. “Yaya Aliyu?”’ 

Ya lumshe idanunsa da suka kumbura suntum saboda rashin isasshen barci. 

“In kun kammala Fa’iza ku fito in kai ku, ku nake jira tun bayan fitowata masallaci sallar asubahi’”’. 

Ban ce komi ba na karasa na dauki suwaita ta na koma ciki. Da na gayawa su Ummi Yaya Aliyu ne zai kaimu duk sun yi mamaki suma, Hajjah ba ta ce komi ba. 

Zanirah muka fara rakawa kasancewar nan wajen gari ne, bayan an kammala mata (registration) an ba ta hostel an hadata da wata prefect muka juyo zamu tafi, idon Zanirah ya cicciko da hawaye. 

Ta ce, “Yanzu Yaya Aliyu don Allah kwana nawa zan yi a nan?” 

Muka yi dariya duka ganin yadda hawayen ya soma malalowa a kundukinta. Yaya Aliyu don ya kwantar mata da hankali ya ce, “Haba Zanirah? Ga ki ga gida meye abin damuwa ne? Bayan haka ma na yi miki alkawarin duk sati biyu zan rinka zuwa in ganki, zamu ke zuwa miki 

visiting duk wata har da Hajjah”’. 

Ta soma sharar kwalla muka rungume juna, sannan prefect din da aka hadata da ita ta ja hannunta suka shige ciki. Bamu tafi ba sai da muka ga kulewarsu. 

A kan hanyar Gusau Yaya Aliyu ke ta tsokanarmu ni da Ummi, sai dai jiki da bakin kowaccenmu ya yi sanyi, kai baka ce ‘yan karadin nan na Hajjah bane masu kama da jiniya don kwakwazo a falon Hajjah ba. 

Wala’allah hakan na da nasaba da rabuwarmu da Zanirah da tunanin sabuwar rayuwar da zamu je mu taras, ta doka da oda ba irin ta gida gaban kakarmu abin son mu Hajjah ba. 

Ya tsaida motar a wani masallaci muka yi sallah, ya ce, “Ku dan jirani ko?” Ya tsallaka daya titin ya dawo mana da gasasshen nama da gorar ruwa da ta pepsi, muka ci muka ci gaba da tafiya. 

Ummi na ta yi min hira na ki kula ta saboda kewar Zanirah. Ta yi tsaki ta ce, “Aikin banza ana ta yi miki magana kin yiwa mutane shiru ke wace ce?” 

Na ce, “Nice Pirincess Fa’iza Bamalli”. A hankali yadda Yaya Aliyu bai jimu ba. 

Ummi ta ce, “Umh! Ya Aliyu ka ji yau Fa’izah ta fadi sunan da ka rada mata?” 

Idonshi a titi ya ce, “Ki bari don Allah?” 

Ta ce, “Wallahi’’. 

Yace, “Kara fadi in ji Fa’iza”. 

Na sanya fuskata cikin tafukana ina dariya. Ni yadda Yaya Aliyu ke nuna mana kauna da kulawa irin haka sai nake jin zuciyata na kara kaunarsa a kowacce dakika. Ina ma a ce Yaya Aliyu ya ce yana sona? Ina ma ya zamo miji a gare ni? Da wace irin sa’a zan yi a rayuwata? 

Kamar ya san kallon shi da tunaninshi nake, sai kawai ya juyo muka hada ido, na yi saurin juyar da kaina ga titi. 

Ya yi murmushin da ya_ motsa kyakkyawan sajen da ke gefe da gefen fuskarsa, ya ce, “Kallon na mene ne?” 

‘A kan me zan kalle ka Yaya Aliyu?” 

“Nima abin da nake son sani kenan Fa’iza, dalilin kallon?’ 

Na zumbura baki na hura hanci. Ya yi 

dariya ya kara speed din motar, bamu kara tsayawa ba sai a FGGC Gusau. 

Bayan ya gama mana duk shige da fice da ake yi daga ofishin vice zuwa na principal, aka bamu hostel daki daya ni da Ummi, amma ba aji daya ba. Ina A tana B. 

Sai da Yaya Aliyu zai tafi Ummi ta ce, “Yaya Aliyu mai yasa aka raba mana aji?” 

Ya yi murmushi ya ce, “Saboda ku yi karatu sosai in bakwa ganin juna akai-akai, amma idan an hada ku za ku shagalta da hirar gida ku ki yin karatu”’. 

Ummi ta ce, “Wa ya ce dasu gidanmu daya? Ga sunanmu ba iri daya ba, ni Khadija Sabi’u Giwa, ita Fa’izah Ahmad A.B Giwa?” 

Ya nuna mata tsagin mallancinta, ya kuma ja dogon karan hancinmu da hannayenshi hagu da dama, ya ce, “Kowa ya ganku ya ga wadannan to ya san tushenku daya, kuma in har bazazzage ne to ya san zuri’ar A.B ne”. Jinjina kai na yi cikin gasmuwa da kalamansa. 

Bayan Yaya Aliyu ya mana sallama, har ya juya zai tafi sai kuma ya _ juyo, 

idanuwanshi sun sauya launi daga farare sol zuwa na damuwa, “FA’IZAH!” Da wata murya tamkar ba tashi ba. 

A hankali na juyo na ce, “Na’am Yaya Aliyu!” 

Ya ce, “Zo”. Tare da yafito ni da hannun daman shi. Na saki hannun Ummi na je gare shi muka tsaya muna kallon juna kamin in sadda kaina kasa a dalilin nauyin da kwayar idanunshi yai min. 

“Yan dakika kamin ya ce, “Ki daina kazanta, ki aje wasan da ke kanki ki tsaya ki yi karatu, ki zama mai kokari irin Zanirah kin ji ko?” 

Idona taf da hawaye na ce, “Yaya Aliyu kazantar me nake yi? Mene_ ne KAZANTA?” 

Bai bata lokaci ba ya dora da cewa, “Kula da tsaftar jikinki, kamar yadda zuciyarki take da tsabta. Ubangiji yana son tsabta ta yadda har ya mai da ita cikon addini. Tsafta ta hada da tsaftar jiki, da ta suttura, da zuciya baki daya. 

Tsaftar jiki ita ce, kula da baki (yin brush a kalla sau biyu a rana, wato safe da dare). 

Tsaftar fatar jiki (yin wanka da sabulu mai kamshi shima a kalla sau biyu a rana, da yawan amfani da sinadaran dake kashe warin jiki na _ halitta (body odour), wadannan sinadarai duk na sanya su cikin sayayyar da na yi miki (mouth wash, deodorant spray da roll-on) da turaren fesawa a tufafi. Tsefe kai da wankeshi da yin kitso duk sati, kina jina Fa’iza ta?” 

Na daga mishi kai ba tare da na iya duban shi ba sakamakon wata matsananciyar kunya da ta taso ta Yaya Aliyu ta lullube ni a dalilin kalaman shi. 

Ba tare da ya saurari cewa ta ba ya cl gaba da cewa, “Don Allah Fa’za ki tsaya ki yi karatu sosai kin ji? Wallahi bana son na ashirin din nan da na talatin da kike dauka a jarrabawar firamare ko na goma 

sha kaza…..” 

Na dago na dube shi idanuna fal da hawaye, na ce, “Insha Allah Yaya Aliyu zan dage ko don ka ji dadi ka daina jin haushi in Ya Fa’iz ya kirani Jaka! Insha Allahu ba zan kara kaiwa na ashirin ba ma har in kare makaranta….. insha Allahu ba 

zan baka kunya ba…. insha Allah sai ka yi alfahari dani fiye da yadda Ya Fa’iz ke alfahari da Zanirah!” 

Ya yi murmushi ya ce, “Alkawari….?” 

Na ce, “Eh, alwakari, kawo ma mu kulla”. 

Na bashi dariya sosai kafin ya miko min yatsarshi ta karshe ta hannun dama, na mika masa nawa muka sarke. Sannan muka kyalkyale da dariya ba tare da Ummi ta san abin da ya bamu dariya ba, ta janyo ni ta baya. Yana daga mana hannu muna daga masa har sai da muka kule cikin hostel. 

Rayuwarmu a makarantar Gwamnatin tarayyah ta ‘yammata dake Gusau ta ci gaba da tafiya yadda ake so, mun dukufa, ba ma tamkar ni da bani wasa da alkawari ko ya ya yake, fatana Allah ya fidda ni kunyar idanun Yaya Aliyu in kai mishi sakamako mai kyau. 

Duk da ba class daya muke da Ummi ba amma a hostel ko da yaushe muna tare, 

tare muke tafiya school arena, class, prep da hostel, dining da sauran extra-carricular 

activities da makaranta kan shirya bayan working time. Bamu yarda mun yi kawa ko guda daya ba, tsakaninmu da kowa sallamar musulunci da abin da ya hadamu. Mun samu exposure na zama da mutane kala-kala ‘yan garuruwa da yare daban

daban, masu halaye da dabi’u dabandaban. 

2K AK Ag 

Gabatowar karshen zangon karatu na farko muka fara gwaji wato (test), inda na kara zage damtse iyakar iyawata na yi dan abin a zo a gani. Wannan ne dalilin da yasa kafin zuwan jarabawa na dan rike wasu abubuwa da yawa, don haka da muka fara sai ta zo min da sauki, na cinye darasin Arabic da English tsaf, sauran subject din dai gasu nan dai la ba’asa ya fi la shai’in in ji Larabawa. Su Hajjah sun zo mana visiting (ziyarar dalibai) har da su Inna Kubra. 

Ranar hutu da murnar mu muka onufi bakin gate a zaton mu Yayanmu Aliyu ya zo daukar mu, don baki ganni ba fuska kamar gonar auduga don murmushi. Ina 

rike da (report card) dina wanda nake kyautata zaton na yi abin kirkin da zai faranta ran Yaya Aliyu, na sauke nauyin alkawari na yi abin a zo a gani. 

Amma murnata ta daka tsalle ta burma ciki sakamakon ganin mutumin da na tsana da gani a rayuwata, mutumin da na tsani jin muryarshi da ganin fuskarshi mara alheri a gare ni, dan uwan da da za a bani wuka ace in caka mishi ba komai da na yi saggawar aikatawa. FA7EEZ MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI GIWA. 

Sanye da makubar shadda ‘getzner’ dinkin samarin garin Kaduna masu ji da tashen samartaka, bakar dara mai gezar bakin gashi ya kara haske sosai ya yi fresh ta yadda ko ni da bani son shi a duniya na san Fa’ezz namiji ne abin so ga kowa, ba ga mata kadai ba har maza jinsinsa ba za su bar yiwa kansu fatan zama ko dakacen komawa kamar shi ba. 

Jingine jikin motar Yaya Aliyu kirar ‘Picanto’ (Kia), fuskar nan dinke babu alamun rahama kamar kullum, na damko hannun Ummi kam, kirjina na dukan taratara ba ma uku-uku ba. Fuskar Ummi 

kamar an aiko mata da Manzon rahama ta saki hannuna ta sheka da gudu aguje wai za ta rungume shi. 

Ya kuwa doka mata tsawar da ta sa ta tsugunnewa a kasa cikin gigicewa. Ganin yadda ya tsoratata ya _ gigitata ya yankwanata a gaban sauran daliban da ke gefe, ko me ya tuna? Ya yi dan murmushi gajere wanda ya fidda lotsawar gefen kuncinsa na dama. 

Ya ce, “To ai ke ce abin naki babu kan gado tsohuwa (sunan da suke tsokanarta don ita ce mai sunan Hajjah, shi kuma su Yaya Aliyu su ce mishi tsoho kasantuwar shi mai sunan marigayi Abubakar Giwa (A.B Bamalli Giwa). Ya ce, “Kai! Ummi ba a girma”. 

Sannan ne ta iya mikewa a darare. Ni dai ina daga gefe hannuwana sarke a kirji ina kallonsu, a zuciyata in ban da Allah ya kara ba abin da nake yiwa Ummi. 

Ya budewa Ummi kofa ta zauna a gidan gaba ya rufe, yana sanya kayanmu a boot din mota ya juyo inda nake tsaye ya dube ni, ina tsaye jikin bishiya kawai ina kallon 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *