UNCLE DATTI COMPLETE

 UNCLE DATTI COMPLETE

Yarinya ce y'ar kimmata shekara tara taci ado cikin English wear na gown an tufke mata kai da baby pink d'in ribbon mai kyau.
Ba wata fara bace cen amma ba laifi kakkyawa ce son kowa kin Wanda ya rasa, tana da dimple a kummatun ta da suke lotsawa a duk sanda take murmushi ko dariya hakan ba karamin kawata fuskan ta yake yi ba.
" Aunty aina!!!! Aunty aina ki bani chocolates d'in da uncle datti ya sayo min", ta fad'a a lokacin da take nufar parlorn da mugun guru saboda har ga Allah tana mugun son chocolates hakan ya sa a kullum tazo gidan sai ta saka uncle Datti ya saya mata.
" Allah Khadija ba zan bayar ba, wai shin ba na hana ki shan zaki ba? ko zo kike yayi miki illah ne? ta fad'a a takaice tare da d'an had'e rai".
"Eeeyyaaaa aunty na yi hakuri ki ban, yau d'aya kawai ki ban nashi daga yau ban k'arawa.
" Hmmmmm nana kenan ke yarinya ce ba za ki fahimci illan shan zak'i ma mace ba but tunda kin ce haka mik'a min eye glass d'ina na saka sai muje na d'auko miki", domin Rana mugun fama da chronic ciwon ido bata gani sai da glass medicated, idan babu wuri duhu baka kirin yake koma mata hatta tafukan hannayen ta ma.
Kamar dama jira take yi ta d'au glass d'in a kan glass table ta mik'a mata ta karb'a ta kafa daga nan ta jawo hannun k'anwar ta suka shige d'aki tace ta tsaya a waje dan kar taga mab'oyan.
Guda d'aya ta fito dashi ta mik'a mata ungo wannan tafi kar ki kuma damuna.
Maimakon ta k'arb'a ta turo baki ta tare da sakin kukan shagwab'a wai ita baza ta k'arb'a ba sai an kara mata.
Jin kukan nata yayi yawa uncle Datti ya fito ranshi a b'ace, shi dai bai san me ya saka saffffff baya k'aunar b'acin ran baby angel ba balle kukan ta, a duk ran da ta saki kukan rigima bai da tsukuni a zuciyan shi har sai ya biya mata bukatunta tayi shiru.
So tari idan yana rawar k'afa a kan Nana Aunty Aina har mamaki take wai shin tsakanin ita da Nana was yake aure? Me yasa baya tarairayanta kamar yanda yake yi mata? ko dai Uncle Datti son Nana yake, duk wannan tunanin su suke mata yawo a kwakwalwar ta ba tare da ta samo amsar su ba.

Gani tayi ya nufo wurin Nana ba duk ya gigice ya susuce kamar wani wawa yana lallashin ta" shiru, yi shiru my angel fad'a min me ke damun ki, wa ya tab'o min ke", ya jero mata tambayoyi a tare.
Baki wangalau aunty Aina ta bud'e tana kallon shi da mugun mamaki, abunda ya dad'a bata mamaki ji tayi Nana ta kuma rushewa da kuka har tana shid'ewa ala dole ita tayi fushi shi kam sai ma gabaki daya ya fita a hayyacin shi ya rasa ina zai saka kanshi yaji dad'i.
Zumb'uro baki tayi cikin shagwab'ar ta tace "Uncle chocolate zan sha, aunty Aina tak'i ta k'ara min", ta fad'a cikin kuka tana langab'e kai.
" To to to yi shiru zo muje na saya miki, fita suka yi daga gidan shi da Nana suka bar Aina a tsaye jigum kamar gawa tana mamakin Datti.
Da taga abun ba mai k'arewa bane ta fad'a kitchen ta dafa had'add'iyar shinkafa jelof wanda yaji kayan had'i, ga wani uban k'amshi da ya gama gauraye kitchen d'in, tana gamawa ta fad'a d'aki ta rage kayan jikin ta kana ta fad'a bathroom. Tana gamawa ta fito ta shirya tsaffff cikin leshi mai ruwan toka d'inkin riga da zani. Kallo d'aya zaka yi mata ka san cewa ta had'u ba k'arya domin kyaun ba daga kayan jikin ta bane daga itan ce, cuz she is a kind of beautiful.
Parlour ta koma ta zauna shiru- shiru babu su babu alamar su har aka fara k'iran sallar Magrib, tayi alwala ta gabatar da sallar ta, tana idar da sallar kenan sai taji sallamar Datti a d'akin ta, ta amsa tare da juyowa sai ganin Aina tayi da kaya niki-niki a laida ta tare ta da ido tana kallon ta".
"Heeeee madam wannan kallon na mene ne?, Datti ya fad'a yana tapping d'inta da hannu."
DOWNLOAD PART 1 HERE👈
DOWNLOAD PART 2 HERE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *