WANNAN RAYUWAR CHAPTER 4
Sam rayuwar bariki batai ba. Ina cikin cin duniya ta da cinke na fara wani irin zazzafi sai kuma zubar jini da na dinga yi wanda yasa naje asibiti suna dubani sukace sai an min aiki domin a cire mahaifata saboda yadda nake yin planing ko ta wanne hanya ya sa Mahaifata ta lalace kuma in ba a cire min ba zan ta ciwo ne ko in rasa rai na.
+
Ina ji ina gani aka ciren mahaifata bayan na warke na koma ruwa. A lokacin in bariki sam bana tunawa da Allah da azabar sa dan kudi sun gama rufen ido da ruda ta. A lokacin na zama babbar yarinya wacce manyan alhazawa ke nema na amman sai naga dama.
Har da kafurai mu’amala nake dan na hadi da wani Kizz wanda mukai rayuwar sosai dan shi in zai amfani dani sai ya ban kayar da zata haukatani ta dada min feeling wanda sai yadda yayi dani karfi ne dashi gashi yana shan abu dan haka in yana amfani sani bai gajiya sai mu yini yana abu daya da yake nima bana cikin hayaci ba ganewa nake ba sai abun ya saken nake gani a lokacin da muka diba bai ruwan sa ta gaba da baya cina hake in ya ga dama. Sai da ya fattakani dan lokacin da na koma wajen wadan da muke mu’amala sai suka fara gudu na dan duk na bude sosai. Daman ga kuruciya ta ta tafi dan har na manyan ta, nan aka fara daina nema na da rubibi na wani ma in naje gun sa kallo na bazai ba. A haka na rasa manyan Alhazawa da samari sai dai tsamaye. A haka na zama ba mai kallo na gashi banyi karatu ba ga girma yazo min a haka nake yawo ina neman sadaka har unguwar da nake suke kyamata dan yadda na rame nayi baki kuma duk wanda yazo da nufin yana so na sai a fada masa abinda nayi a baya daga nan shikenan.
Wannan yasa na saida gida na na dawo nan, kuma bani da aiki dan duk gidan da naje neman aiki ba sa bani si suce suna da masu aiki a haka na hakura na koma yawon bara har na tsufa haka. Nayi da nasani da rayuwar bariki dan bata tsinanan min komai sai bakar rayuwa daga baya. Dan da aure nayi ko mijin ne ya mutu ina da ya’yan da zssu na taimako na ko na mutu kuma suyi min addu’a yanzu kuwan fa bani da baya ba mai mun addu’a.
Rayuwar bariki rayuwa ce wacce bata dadadi daga ka bar rayuwar zakai ta fuskantar kalubale, in ka barka kenan in baka bar ta ba kuwa zaka kwaso ciwo ko bakin jini da wulakanci kala kala daga baya. in aure kayi rayuwa ya’yan ka gori in ka shiryu ma mutane suna maka kallon tuban muzuru kayi abubuwa da yawa.
Ta dago ta kalli Fauwaziyya tace
“Nayi rayuwa cikin bariki wadda yanzu nake danasi. tinda na ganki nake son ki da tausayin ki wannan yasa nake baki labari na ko zai zama izina a kanki. Dan Allah ki daure ki bar *wannan rayuwar* domin rayuwar mace kalilan ce, ki duba rayuwar yan bairikin da sukai shura kamar ta cikin littafin *Yar jagora Na _Xaharkel da Oum KHADIJA_* Wanda kina ganin sanadin son zuciyar mahaifin ta ya kai ta rayuwar da ta tsinci kanta rayuwar da sam bata tsinana komai ba har ya shafi rayuwar ‘yar ta to dan Allah ina amfanin wannan ‘yar ka ma ta zama karuwa. Ta zo a haka ta koma a haka kaje ka fadawa Allah me? Ya zina ita ma baka kula da ita ba bayan ya’ya amanar Allah ne a wajen mu ko yaya suka baci sai Allah ya tsida mu ranar gobe kiyama ya tambaye mu yadda muka kula dasu muka tarbiyar dasu. (kuje ku biya littafin dan jin tayaya ta tsinci rayuwar ta a karuwanci har ‘yar ta ma ta gado ta.)
STORY CONTINUES BELOW

Sannan ki duba rayuwar *Yar barki littafin Maryam Obam, kalubalen da Zainab ta shiga da ta zabi rayuwar bariki* kuga yadda tayi rayuwar ribar me ta samu in banda danasani wanda har karshen rayuwar ta take yi. In kinga a littafi tayi rayuwar wata tayi kyau to wallahi taki ba dole ne tayi ba. ita duk da ta samu soyayyar mijin ta amman ai tana fuskantar kalubale dan har a last page sai da yayi abinda ta tuna da rayuwar ta ta baya wacce in ta tina dole komai ya tsaya mata ta shiga kunci wallahi rayuwar bariki bakar rayuwa ce duk da kaddara kan jefa mutum amman muna guje mata ta hanyar addu’a akan Allah ya kare mu ya tsarkake zuciyar mu da zuri’ar mu.
Bayan nan ki duba littafin *Agola na Nabila Rabi’u Zango* ya rayuwar Jidda ta kasamce bayan ta zabi rayuwar bariki ya karshen ta ya kasance ta kamu da cuta mai karya garkuwar jiki. Na mata kuka sosai dan ta ban tausayi tata kaddarar kenan saboda son abin duniya ya sa mahaifiyar ta daure mata gindi wanda a karshe ta kwaso HIV.
Wallahi duk wanda ya zabi son duniya a *wannan rayuwar* zai ga ba dai dai ba. Domin ance *Son zuciya bacin ta.* a lokacin da ka zabi abinda zuciyar ka ke so karshe ka fada a nadama. In kin bi yadda kike ganin ana rubibin ki a yanzu zaki ga babu yake amman daga baya in aka yasar dake kallo baki ishe su ba. Zakiga yanzu namiji dan shekara hamsin yanemi yarinya kamar ki amman kinsa me? Wallahi ke da kinyi shekara hamsin ba me kallon ki domin cewa zasuyi kin tsufa ko kin taba ganin yaro dan shekara ashiri a harkar bariki yana bin mce yar shekara sama da hamsin. In ma yabi ta to biyan sa zatai kuma wani lokacin zai gudu ko bai gudu ba dan samun kudin ta zai na bada labarin shifa hakuri kawai yake da ita. Wannan rububin da kikaga maza na miki duk gaibu ne nasan a yanzu ba za a rasa masu son ki da aure ba, shawara ki tsaya kiyi karatun ta nutsu dan wallahi kina ji kina gani nan gaba zakina neman wanda zai aure ki amman ki rasa. kina zaune wanda bai isa ya kalle ki ko ya fada miki magana ba sai ya fada miki wani ya zage ki wani har da bugu. Aure shi ya dace dake, ban san me ya ja ra’ayin ki ga *wannan rayuwar* ba amman ina mai baki shawara da ki barta dan babu ribar da zaki samu a ciki. In kaddarar da jarabawa ta sameki ki koma ga Allah. Allah zai dube ki insha Allah. Baki san ta yadda zakije ki hadu da Allahn ki ba gwara tin yanzu ki guji wannan rayuwar. Wallahi duk wanda ya bar Allah yana tare da tabewa, da asara. Dan haka ki koma ga Allah shi maji rokan bayin sa ne.
Kuka Fauziyya take kamar ranta zai fita shin me ya kai ta aikata zina bayan lokacin da Kamal yai amshi budurcin ta cewa tayi ba zata kara ba shin me ya rude ta har ta biyewa shaidan take aikata zina. Innalillahi waina illahir rajiun kawai take fadi wai yau ita ce ke aikata zina kenan ta zama karuwa wai ita ke bin namiji ta kwana dashi ta bashi kan ta a bata kudi. Duk yadda take tsara rayuwar auren ta kenam ta rushe shin wa zai aure ta a haka shin tayaya zata tunkari mahallicin ta da wannan kazantar da take ciki. Shin da ta mutu bata samu wannan matar ba da ya rayuwar ta zata kasance da ta mutu innaliahi wainna illahir rajiun. Ita bata da kwadayi da son abin duniya amman mahaifiyar ta duk ita ta jefa a wannan harkar baza fadi wata mummunar kalma ga mahaifiyar ta ba dan uwa ce gare ta kuma itama halin mahaifin su ne ya jefa su. Lallai suna cikin halaka da bata. Allah ka yafe min Allah ka yafemin.
Abinda take fadi kenan. Mikewa tayo ta kalli Tsohuwar nan zatai magana taji ba zata iya ba dan wani kuka ke taso mata dan haka da sauri ta bar wajen tana toshe bakin ta. Tana zuwa gida ta fada kan gado tana mai cigaba da kuka.
Tana wannan halin wayar ta ta hau kara amman ko kula ta batai ba da taji zata isheta ma kashe ta tayi tin yamma take kuka har magariba da kyar ta mike tai sallah tana rokar Allah yafiya da shiriya.
Tana zaune akan sallaya ta hada kai da gwiwa hannun ta rike da carbi sai kuka take tana kai kukan ta ga Allah akan ya yafe mata abun da tayi. In ta tuna abinda tayi ta tuna da ta mutu a wannan halin ina zata tafi sai ta kara girgiza ta kara fashewa da kuka. Tana mai fadin
“Astagafurullah Astagafullah. Allah ka yafen ba dan hali na ba Allah ka tsare ni ka kare ni Yaa Allah. Allah na tuba ka yafe min!”
STORY CONTINUES BELOW

Ba abinda take sai istigifari tana mai zubar da hawayen da sun kasa tsayawa jikin ta yai sanyi ga kan ta dake ciwo dan tin jiya take kuka da wannan bawan Allahn yazo mata ga wani kukan wanda baya ganin akwai ranar daina shi. Tana wannan halin su Farisa da Hafsat suka shigo dakin. Kallon ta Hafsa ce tace
“Anty Fauziyya lafiya kuwa kar dai kice min tin jiya kike kukan nan!”
Farisa kuwa wanka ta shiga tayi a toilet din dakin ko ta kan Fauziyya bata bi ba dan taga Antyn tata ita kamar tana son ta daina harka ita kuwa yanzu ta fara. Dan haka nema bata ko kalle ta ba ta shige wankan ta dan dawowar su kenan kuma yanzu zasu kara fita dan wani party ba zasu wanda kwana za ayi till down kenan.
Sam bata kula su ba dan a halin da take ciki bata tunanin zata iya wata magama. Tana a durkushen nan suka gama shirin su cikin kananun kaya suka fice dan har kofar gidan aka zo daukar su. Wani kuka ta fashe dashi tana mai takaici ace su uku a gidan su duk rayuwar su ta lallace. Wa’iyazubillah shikenan za ana ce musu karuwar. Ina ma tana da halin hana su suma amman ina Farisa tayi nisa bata jin kira.
Mikewa tayo ta tada kabbara dan kara mika wata sallah da yanzu ba ta da abin yi sai sallah da lazimi.
****************************************************************************************************************************************************************************
Sosai Muhammad yaji faduwar gaba amman ya danne yace
“Nagode Allah saka da alheri.”
Ya mike ya tafi a ransa sam ba zai iya bijirewa bukatar Abba ba. Gida ya koma ya fadawa Hajiyarsa duk abinda ya faru. Hajiya tace shikenan. Washe gari yaje ya kaiwa Abba takardar sakin. Abban yace
“Ina jiran su fa.”
Ranar da ya saki Rukayya a ranar wani lectures su ya samar masa scholarship a can saudiyya zai je yayi PHD dinsa dan sun gama karatun su wata daya da ya wuce. Murna wajen Muhammad kamar ya zuba ruwa yasha a kasa.
Wannan yasa yaje gun Abba. Bayan sun gaisa Abba yace
“Ince dai ba wata matsala bace!”
Kai ya gyada. Abba yace
“Yaushe zasu zo?”
“Suna nan zuwa.”
“Muhammad ka sani bana bukatar komai na auran nan zan bada sadaki sai daukar matar ka da zakai kawai.”
Kansa a kasa ya fadawa Abba duk abinda ake ciki. Abba ya tayashi murna yace wannan ba matsala a daura auren ya tafi tinda itama service zata fara in ya dawo ta tare.
Da fadawa Hajiyar sa ta sanar da yan uwan uban sa. Tace
“Ai Alhaji Ibrahim sirikun kwarai ne yar ce dai bata dauki halin sa ba. Amman ba abinda zamuce sai godiya.”
Washe gari yan uwan iyayen Muhammad sukaje akan neman aure a take yaje ya kira abokan sa da makwabta aka daura auren suka tafi da goro da alawa da Abba ya bayar. Sai da suka tafi ya shiga gida ya samu Mama na aiki Umma na shara. Nan ya mika musu goro da alawa yana fadin
“Yau na daurawa Ummu da Muhammad aure!”
Turus Umma yayi tace
“Rukayyan fa?”
Takardar sakin ta ya zaro ya mikawa Mama yace
“Gashi nan ya baku takadar da kuke bukata.”
Nan Umma ta gane kenan sakin Rukky akai dan haka tace
“Allah tabbatar da Alheri.”
Mama kuwa tayi shewa tace
“Tafi nono fari yanzu ‘yata zata auri dai dai da ita.”
Ta kalli Umma tace,
“Na fada miki kece kalar talauci da tsiya dan haka yanzu kuka fara!”
Umma batai magana ba dan ita jimamin sakin Rukky ma take. Aikin ta ta karasa ta koma daki.
A gidan Anty Sailuba ta cigaba da zama. Acan ta hadu da wani abokin mijin Sailuba. Nan ta fara zawarci dan Sailuba sai gyara ta take inda watan Baby Junaid Bakwai suka cire shi a nono suka aika da ya’yan can wajen Hajiyar sa. Ita ta cigaba da kula da su.
Muhammad kuwa bai kara wata a kasar ba ya tafi ya fara daukar karatun sa. Inda ya samu wani aiki yana karatu yana aiki kuma ba laifi yana samin kudi sosai. Shi da kannin sa suka kulla business ya aiko kaya ya siyar ya turo Kudin ya fitar dashi. Sai gashi cikin wata biyar ya fara tarar kudade.
Alhaji Kamis Abokin mijin Sailuba ne yana daya daga cikin wadan da ke son Rukky. Amman ita ba ta son sa wai ta fison saurayi. (Kuji fa tayaya zata samu saurayi bayan ita ba budurwa bace.)
Haka ta cigaba da zawarci ganin Alhaji Kasim yafi wadan da ke son ta kashe mata kudi sai ta fara sauraron sa. Ba abinda baya bata ko ya siya mata. Nan ta fara jin dadin itama zatai auren gidan dadi. Uwar ta kuma tana mai yar wa da Umma habaici kullum wai ya’yan ta kalar arxiki ne nata kuma kalar tsita ce. Umma kuwa bata ko tanka.
*Toh gashi nan dai, ina son na gama chapter One din nan before azumi, in Allah ya kaimu, toh amman sai dai yadda ta yiyu gaskiya in na gama kan lokacin toh? In kuma ban gama sai ku tara in Allah ya kaimu bayan sallah da rai da lafiya. Allah ka kare dukkan musulmai akan wannan annobar.*
Washe gari ma da azumi ta tashinta kasa daina kuka da ta tina abinda ya faru da ita a baya sai hawaye. A haka ta yini daki ko tsakar gida bata fita. Da tasha ruwa ma ruwa kadai tashan ta kwata dan bata jin son cin komai sai can dare taji yunwa ta dan hada tea ta sha.
Tunanin yadda kannen su zasu tashi take sam iyayen ta su basu da kula shin sun manta su amana ce a gunsu ranar gobe kiyama sai Allah ya tambaye su yadda suka tarbiyyar dasu. Yau kwanan ta nawa bata gidan mahaifiyar ta bata damu ba bare mahaifiyar ta da tin da ta dawo kwana biyu ma bata saka uwar a idon ta ba ko ina ta tafi.
Washe gari ma azumin ta dauka tana mai cigaba da kai kukan ta ga Allah. Sam ta fitar da rai da rayuwar komai tsoron yake bata kwana take ta yini sallah da karatun al kur’ani ko falo bata fita iya karta dakin ta.
Da Yamma tana zaun taji kannen ta na ta kukan yunwa iyayen ma basa nan wannan yasa ta kira kanin ta ta bashi kudi masu yawa tai masa list din kayan abinci dan dubu dari ta bashi taje ya siyo tace su daura abinci suci.
A yanzu ta dauki damar yin karatu ko business dan ta tallafi kannen ta kar suma su fada irin rayuwar da suka shiga. Dan haka yanzu ta ina zata fara. Dole ta tsarkake kan ta wannan yasa sim din ta ma ta karya wayar ma ta cilla cikin jakar ta. Mukullin motar ta ta dauko tana juya shi yanzu sam mota ma bata bata sha’awa dan haka siyar wa zati ta samu shago ta siya ta zuba kaya ta maidashi provision store tana taimakawa kan ta a harkar karatun ta da kamnen ta. Bata kawo aure dan tasan ba me auren ta a yanzu.
Satin ta biyu bata ko fita tsakar gida bare falo tana dakin ta ko abinci bata iya ci daga tea sai lemo ko cake shima sai taji uwar bari wato yunwa. Sam Farisa bata shiga harkar ta sai Hafsa ce ta damu da halin da yar uwar tata take.
Kamal yazo gun Farisa amman tace ya kara hakuri yanzu Antyn tata tana wani hali. Duk ya damu donin ya kira ya kira wayar a kashe yazo ya aiko ta ce batazo ba dan bama ta tambayi waye ba tace aje ace bazata zo ba. Wannan yasa ya nufi Farisa dan ta taimaka masa domin Allah ya sani yana son Fauziyya bai taba haduwa da yarinya kamar Fauziyya ba kyakyawa ga kyan diri da ni’ima.
Tana kwance tana jan carbi kanin ta ya shigo dakin durkusawa yayi yace
“Ina yini? Anty Fauziyya!”
“Lafiya lou Amir me kuke so?”
“Babu komai daman wani ne a waje yace nazo na kira ki.”
“Kaje kace ba zanzo ba.”
Mikewa yyi yace
“Toh!”
Tsaki ta saki tana me fadin
“Sai dai fa ka mutu!”
Muhammad da yau sau biyu kenan yana zuwa yasa ai masa sallama da ita ake fada masa tace ba zata zo ba sai ya juya ya tafi ba dan yana so ba sai dan ba yadda zaiyi. Kwanakin da yayi baya ganin ta ya daga masa hankali dan daman ganin ta kadai na rage masa damuwa ko da kuwa ba zatai masa magana ba. Lallai zuciyar sa ta kawo shi inda aka fi karfin sa har take shan wahala amman duk da haka bai jin haushin ta sai karin son ta da yake ji.
Sakina kuwa ta kware a harkar da kawar ta ta saka ta dan cikin lokaci kadan ta kware a harkar dan yanzu manyan mata ke neman ta dan ya’yan gidan su kyawawa ne suna da sura mai kyau abinda ke rudar masu mu’amala dasu kenan. Yanzu ma Abuja ta tafi dan kawar wata hajiyar ta ce ta neme ta akan tazo tai mata kwana biyu. Bayan taje sun sheka ayar su ta dauke ta ta kai ta shopping daga nan suka biya gidan Hajiya Mariya wacce itama ta kasance tana bin maza a harkar saboda yadda mijin ta ke nuna halin ko in kula dan yadda ya fifita aikin sa akan hakkin aure dan in ya tafi sai yayi wata hudu bai dawo ba gashi ita kadai a gida dan ta yana waje acan yake aiki.
STORY CONTINUES BELOW

Tin tana bin maza ta daina dan tace kar asirin ta ya tonu dan hajiya Bilkisu ita ta fara kawo mata bin mace har sukai lesbian ta kuma ji dadi taga in mace aka ganta dashi ba mai zargin ta ba, ba kamar in yaga na miji wannan yasa Hajiya Bilkisu ke aiko mata da duk wanda yazo wajen ta yanzu ba gidan Hajiya Mariyar suka nufa da Sakina.
Suna zuwa hajiya Mariya ta kafe Sakina da ido dan tana ganin ta taji wata sha’awar ta dan haka a fara wani mammatse kafa take hajiya Bilkisu ta gane me yake faruwa dan haka tai dariya tace
“Ya dai hajia ko na ara miki ita tai kwana biyu a gun ki!”
“Da kuwa kin kyauta ina fatan bata da natsala zata riken sirri na.”
Fuskar Sakina Hajiya Bilkisu ta shafa tace
“Baki da matsala da wannan nutsatsiya ce.”
Bata bari ta gama magana ba ta mike ta kamo hannun ta sukai daki tin a hanya ta fara rumgume ta hade da kissing nata a haka suka shige daki. Hajiya Bilkisu tayi dariya ta mike tana kiran yarinyar da ta xama kamar matar ta acewar ta kenan dan har aure an musu da ita daga nan tayi gida.
Tin lokacin Sakina da Hajiya MARIYA suka dinke domin kuwa Hajiya Mariya sosai take kashe mata kudi kamar bata san zafin su ba wanda ita kuma Sakina ke jin dadi ga cima da makwanci a gidan Hajiya Mariya ga yadda take tarairayar ta kamar me? Wannan yasa bata kwana biyu bata zo Abuja wajen Hajiya Mariya ba dan ita da kanta kan aika mata driver ya dauko mata ita dan haka yanzu sakina ta zama babbar yarinya.
Wannan zuwan nata gida taga ta jima bata ga Fauziyya ba wannan yasa ta shiga dakin ta. Zaune taganta rike da alkur’ani duk ta rame baki ta tabe tana bin dakin da ya cika da akwati nan ta wanda ada kayan su bai fi kala goma ba. Zama tayi tace
“Sister ya gidan?”
Dagowa Fauziyya tayi ta saki murmushi ana fadin
“Sakina kwana biyu!”
Murmushi tayi tace
“Ke dai bari business ya boye ni!”
“Business kike yi?”
“Wallahi ke kuma fa? Dan aga yadda dakin nan naki ya cika da kayan arziki nasan kin tara da yawa!!
Tsaki ta saki a ranta tana fadin ina ma ita ce ke business ba abunda ta zaba a baya ba. Kallon Sakina tayi taga zobe a babban dan yatsan ta sai sarkar kafa a kafar ta sakale kan ta ne ya kulle tasan dai ance masu wannan abun lesbian suke amman tasan Sakina batayi meyasa ta saka kuwa.
“Tinanin me kike yi ne?”
“Sakin meyasa kika sa sarka a kafa da zobe anan kisan kallon yar lesbian za ai miki kuwa? Dan Allah ki dauna sakawa kinji.”
“Naji!”
Ta mike tana fadin
“Zan tafi dan zani Abuja zany sati sannan na dawo need ur prayer!”
“Safe journey sis!”
“Tnc!”
Tayi waje tana wata irin tafiya da kallo Fauziyya ta bita tana fadin
“Yaushe Sakina ta koma haka.”
Sharewa tayi kawai ta koma ta kwanta tana mai cigaba da karatun ta.
Yaya Babba kuwa ta mai da bara sana’ar ta ya’yan ta take deba subi gida je yan matasan wadan da basu fi shekara goma sha daya zuwa biyar ba kuma take cewa suma suje suyi amman ita tana tare da yan yaran. Haka suke ko yaushe suna yawon bara gashi da sun samo abin ke karewa.
Samira ma kuwa da auren ta ta zage tana bin maza ba ruwan ta bare tsoro wanda ta zama hajiyar kan ta dan ta dada kiba tai haske tayi kyau ka bakace ita bace a da. Idon ta ya bude wani lokacin dan har kwana takeyi a waje, yanzu ko ta kan Alhaji bata bi shima kuma bai damu ba gani yake kamar an sauke masa nauyi bama yanzu da yaga ba’a tambayar sa kudin abinci sai ya kara makalewa yana cigaba da tara kudin sa.
Wata rana Halima da Hajara sun fita yawon bara kamar yadda uwar ta koya musu sun shiga wata kasuwa, sukai wani loko, Inda samari ne kala kala. Wani yaro Isma’il dake kusa da abokin sa Kabir yace
“Kai kaga wasu yan shila.”
Dagowa Kabir yayi ya kure su da ido, yana ganin Halima yaji yana son ta har ga Allah duk da yarinya ce bata fi shekara goma sha biyar ba. Sanin halin abokinsa baya kula yan mata sai da harkar lalata yasa yace
“Wadan nan ai yara ne please kar ka lalata su!”
Wani kallo yabi Kabir dashi yace
“Ina ruwan ka wallahi tinda na ganta nake jin sha’awar ta kuma wallahi sai na lashi zumar ta.”
Mikewa Kabir yayi dai dai karasowar su wajen halima cikin muryar ta mai dadi tace
“Dan Allah a taimaka mana da sadaka saboda Allah da Annabi.”
Dari biyar Kabir ya zaro ya mika musu. Amsa suka yi suna godiya sannan shi kuma yayi gaba ya barsu. da kallo Halima ta bishi dan daga kallo daya taji ta kamu da son sa amman tayaya wannan kyakyawan mai kudi zai kula ta sai jikin ta yai sanyi. Juyawa sukai zasu tafi Isma’il ya kira su.
“Yan mata!”
Suka jiyo ya kalli Hajara yace
“Kanwata jeki can ki siyon lemo mana.”
Amsa tayi ta tafi Halima kuma.ta tsaya tana jiran ta.
“Yan mata ya kike ya sunan ki?”
“Halima!”
Ta bashi amsa.
“Suna mai dadi sunana Isma’il Halima tin da na ganki naji ina son ki please Halima kar kice a’ah!”
Kunya ce ta kamata ta rufe fuska. Dadi yaji ganin tana kunyar sa dan yasan daga kunya ake fadawa soyayya.
Gano kanwar ta taho yasa yace
“Gobe ma kuzo kinji?”
Kai ta gyada ya zari dubu daya ya mika mata yace
“Ku gaida gida.”
Ya amshi aikin ya basu biyu suka tafi. Hajara tace
“Allah sarki yana da kirki kuwa!”
Ita dai Halima shiru tayi dan ta tafi tunanin itama zata auri mai kudi ba zatayi rayuwa irin ta yan gidan su ba. A haka suka gama bin kasuwar sannan suka koma gida da kudi da yawa dan sun samu sadaka.
Farisa da Hafsa ayar su suke shekewa bame kwaba bare harara. Wata rana Hasfat ta dawo daga gidan saurayin ta da ta dawo tin tana titi taga wata mota ta faka a bakin titi, da ido tabi motar sai kuma ta dauke kai. Nan ta tsaida Napep ta hau ta tafi amman abin mamaki tana sauka ta kara ganin motar ita sai abin ya bata tsoro dan in har da irin mazan da take kulawa ne a take zai nuna abinda yake so in tayi niyya ta bishi amman wannan bata ga ko wake cikin motar ba ma bare ta kai da sanin waye. Gida ta shige.
Yana daga cikin motar ya saki murmushi yana cije baki ya tada motar yayi gida. Tin daga lokacin kullum sai yazo kofar gidan yaga fitar ta. Sam Hafsa bata shigar banza ko zatayi zata daura katon hijab abinda shi kuma abinda ya ja hankalin sa da ita kenan. Dan ko gidan samarin nata zata bata zuwa ba hijab sai taje can take cirewa ta sheke ayar ta. Gata a fuska kamila wannan yasa yaji ya kamu da son ta.
Yanzu ma yana tsaye cikin wata mota daban dan ya gane ta gane dayar motar duk da tint ce a ciki wannan yasa ya canja mota yana tsaye ta fito ta tsaida Napep ta shiga binta yayi har gidan saurayin ta da suke masha’ar su. Kullum yana ganin shigar ta gidan wannan yasa ya kawo ko gidan yan uwan su ne.
Parking yayi ya jingina kan sa a jikin kujera yana sake ajiyar zuciya, A ransa yana fadin tayaya zai tunkaro yarinyar nan sannan tayaya zai jewa Momyn sa da maganar ta bayan ta makale sai ya auri yar ya kanwar ta Hannah.
Hannah kyakyawa ce amman kuma shi yana da kishi yana son mace mai kame kai da suturta jikin ta abinda yaja hankalin sa ga Hafsat din ma kenan har ya kamu da son ta dan sau dama yana ganin ta tazo wucewa sanye da hijab har kasa. Hannah kuwa tai ta saka kaya damammu abin shi kuma ke bashi haushi kenan dan baya son maza na kallan masa abinda yake so.
Ahmad kenan ‘da wajen Alhaji Aminu Babban likita ne a AKTH kuma shi kadai ne ‘da namiji gun iyayen sa, sauran duk yayen sa ne mata har su hudu sai kanwar sa mace, wannan yasawa iyayen son sa bama uban sai abinda yake so yake masa kanwar sa daya mace. Momyn sa ba tin yau ba take fada masa ya auri yar kanwar ta Hannah wacce yanzu ta dawo gidan su Ahmad din ma dan yadda itama take son sa amman duk abunda take masa na kyautatawa a banza domin kuwa shi ba son ta yake ba. Yadda take shige masa tace zata rumgume shi na kara bata masa rai.
Shekarun sa talatin da biyu yayi degree har master din shi a bangare tattalin economic wanda yake aiki a bank na can Abuja. Dalilin ganin Hafsat yazo unguwar wucewa ne idon sa ya sauka akan ta lokaci daya yaji yana son ta da gaske abinda yaja hankalin sa kuma shigar ta, wannan yasa kullum yake hanya unguwar su ganin ta.
Ajiyar zuciya ya sauke ya bar unguwar. Gida ya nufa yana shiga ya nufi bangaren sa. Part din sa yayi yana shiga kanwar sa Basma ya shigo dakin tace
“Yaya ka dawo ashe?”
Mikewa zaune yayi yana dafe kai. Tace
“Yaya baka jin dadi ne?”
“Basma mikon ruwa”
Mikewa tayi ta dauko ruwa a firij sannan ya koma kan kujerar da yake zaune ta bashi amsa yayi ya sha sannan ya koma ya kwanta ba komai yake gani ba sai Hafsa cikin shigar ta mai kyau da burge duk wani ‘da mai hankali.
STORY CONTINUES BELOW

“Yaya Momy fa ta saka ranar bikin ka kai da Anty Hannah nan da one month!”
A zabure ya dago yana bin Basma da kallo.
Basma ta ce
“Wai yaya meyasa baka son Anty Hannah ni sam ban ga aibun ta ba wallahi.”
“Basma ba Hannah ce bana so ba sm halayar ta ce bana so. Ni mutun ne ma kishi wanda bana son kaya na ya zama kowa yana iya ganin min su ina son sirri da boye tsuraici amman ki kalli Hannah da kalar kayan da take sawa sam bata da kamun kai.”
“Haka ne Yaya amman fa kar ka taurara nuna kyamar dabi’un ta dan Allah sai ya jarabce ka da samun ta. Ni dai nasan Anty Basma na son ka dan haka nasan zata bi dukkan abinda kake so dan haka ko kunyi aure ba zaka samu matsalar gyara ta ba.”
“Basma kenan baza ki gane ba kowa na son samun mace kamila mai tarbiyya.”
“Yaya kabi zabin Momy nasan bazata taba cutar da kai ba.”
“Shikenan amman gaskiya Basma dole nima na auri zabin raina wacce nake so dan haka xan fadawa Dady in har an yadda nima zan yadda da auren Hannah!”
“To kai Yaya da ba kula yan mata kake ba!”
“Bana kula yan mata saboda banga wacce tai min ba wannan yasa yanzu da naga wacce tai min ma na kasa tunkarar ta!”
Ido ta zaro dan tai mamaki Yayan ta sam mata basa gaban sa.
“Iyeee please Yaya tell me something about her.”
Zama ya gyara yace
“As I tell you na kasa tunkarar ta Basma but she is my type ai you know the type of ladies I like to be my wife she is perfect, beautiful and intelligent, innocent she take my heart away I can’t do without her I really love her.”
Tafi Basma ta saka tana fadin
“Na yadda now my bro is in love!”
Kai ya jinjina yace
“Wannan haka yake!”
“Allah bada sa’a toh!”
“Ameen! Amman kasan me Yaya?”
“A’ah tayaya zaka tunkari Momy!”
“Ba ruwa na da wata Momy Dady zan sama ya shigen gaba in Momy ce wallahi sai dai na mutu!”
“Zan taya ka da addu’a!”
“Tnc uhw Little!”
Mikewa tayi tace
“Kaci abinci ne?”
“Me akayi?”
“Tuwo Momy ta sa akayi dan Oga yace shi yake so!”
Fuska ya tabe yace
“Samar min wani abu naci ba zan iya cin wani tuwo ba gaskiya!”
“An gama!”
Ta fice
Isma’il da Halima kuwa sun dinke soyayya yake nuna mata bai taba kawo mata zancen batanci ba. Wannan yasa in sun fito suke raba hanya ita da kanwar ta kanwar tayi wata hanya itama haka amman da karfe biyar zasu hadu a inda suke haduwa su koma gida da abinda suka samo.
Wanda yanzu sam Halima ta ba inda take zuwa in ta fito bara wajen Isma’il take zuwa su sha soyayyar su. taci abinci mai kyau ta sha lemo da ruw in zata tafi dubu daya biyu uku haka yke bata.
Kabir kuwa duk lokacin da yazo ya ganta bai zama ma yake tafi dan baya son Isma’il ya lalata yarinyar wacce shi ma son ta yake amman fa da aure.
In dai yazo ya gansu zai tafi wannan yasa Halima tace
“Meyasa baya zama naga ko kuna tare nazo sai ya tafi.”
“Miskili ne haka yake wani lokacin!”
Sai dai tayi shiru amman itama wata zuciyar na mata nuni da kara asassa mata son Kabir sai dai dannewa kawau da take.
A haka Isma’il ya fara kawo mata ‘kudirin sa ranar hannun ta ya rike nan ta kalle shi tace
“Menene haka Isma’il?”
“Wallahi Halima son ki nr yai min yawa ina son ki kullum na kwanta kwana nakr mafarkin ki, ki tausaya min Halima!”
Tausayin sa ne ya kamata dan tana son Isma’il dan bai taba mata haka ba kuma kullum nuna mata yake shi na Allah ne bama da yaga cewa ya halaiyar ta yake.
STORY CONTINUES BELOW

“To ni dai ka bari!”
“Baby ki ban dama na aiko gida ai yi komai within 2month!”
Ido ta zaro tace
“Isma’il ina da yayen da ba a aurar ba tayaya kake ganin za a aurar dani ina karamar su!”
“To menene? Indai kin amince zan turo ayi komai a gama.”
Shiru tayi can tace
“Matsalar Abban mu ne ba zai min aure yanzu ba.”
Shiru yayi yace
“Gaskiya Baby a matse nake gashi ni ke nake so ba zan taba aure ba in bake ba.”
Lokacin aka kira la’asar wannan yasa ta mike tace
“Zanyi tunani Isma’il sai anjima zan tafi!”
Dubu uku ya zaro ya bata yace
“Zanyi kewar ki sai gobe ko?”
Kai ta gyada tace
“Sai goben!”
Sukai sallama ta tafi. Zata fita kenan Kabir ya shigo gaishe sa tayi ya amsa ta fita kai ya girgiza sannan ya shiga shagon Isma’il din yace
“Muje muyi sallah!”
Suka je sukai sallah. Bayan sun dawo a hanya Isma’il yace
“Aboki na na kusa mata fa!”
“Mata kuma? Aure zakai?”
Kai ya girgiza yace
“Ba aure zan ba a sama zan samu mata.”
“You means abinda ka saba zaka karayi ko? Dawa kuma?”
Gashin bakin sa ya shafa yace
“Halima mana!”
“Ta yadda ne?”
Ya fada a zabure. Kallon sa Isma’il ya tsaya yi yace
“Lafiya?”
“Lafiya lou!”
“Naga ka damu da Haliman nan fa shin meyasa?”
“She is innocent that why ba kalar matan da ka saba deceiving bace.”
Dariya yayi yace
“Zan ci ta naji yaya dandanon ta yake if she is testy hhhhh nayi mata!”
“Kana son kace zaka aure ne?”
Tsaki yayi yace
“Kai ana maganar arziki kana maganar aure ni na aure ta nayi kalar auren ta just yadda na saba ne ina amfani da ita kan na samu sabon hannu again!”
“Isma’il wallahi ka sani duk abinda kayi sai an maka ina mai baka shawara da kaji tsoron Allah kar ka lalata rayuwar wannan karamar yarinyar da ba ruwan ta please!”
Kallonsa Isma’il ya tsaya yi can ya cije baki kawai yayi shagon sa.
Kabir kuma yayi supermarket din su dake can gefen shagon Isma’il dan Kabir mahaifinsa mai kudi ne katon waje suka samu sukai ginin bene suka loda kaya atama shadda less da kayan mata wanda shi ke kular da dukiyar Mahaifin su dan shine babba kuma da namiji a gidan su.
Yana da manyan supermarket da yawa a cikin garin kano waje waje kuma duk Kabir ke kula dasu.
Isma’il kuwa mahaifin sa ya rasu wannan shagon da yake kasuwan ci ma gadonsa ne shi da kanwar sa yake juya musu, Daga shi sai Maman sa sai Kanwar sa.
Halayar sa kenan bin yan mata ya lalata su shine aikin sa. Yana da gida anan Sharada. Madaidaicin gida ne mai two bedroom da falo da kitchen. Wanda gidan ya tsaru anan yake kai yan mata yana sheke ayar sa dasu.
Tana tafiya ta shiga neman bara har karfe biyar sannan ta koma inda suka hadu da Hajara suka koma gida.
Kwance take karfe goma sha biyu na dare lokacin kowa yai bacci wayar ta taji ta fara kara wannan yasa ta mike ta dauke ta a karkashin shinfiddar ta, dauka tayi taga Isma’il ne wannan yasa ta saki murmushi ta dauka tana fadin
“Bakai bacci ba!”
“Tayaya zan iya bacci bayan kewar I tai min yawa. Wallahi Halima mutuwa zan yi kwanan nan kisan me?”?
Kai ta girgiza kamar tana gaban sa tace
“Sai ka fada!”
“Ina matukar bukatar mace a rayuwa ta kuma ni ba zan iya auren kowa ba sai ke. Ke kadai nake so domin na jima da miki kyauta jiki na dan haka ba zan taba iya bari na je gun wata ko na auri wata ba gashi kince a gida ba za ai miki aure ba. Halima ya kike so nayi? Ki fada min dan Allah mutuwa kawau zanyi!”
“Ka daina cewa zaka mutu ba zaka mutu ba sai lokaci yayi yanzu ni me zan iya yi!”
“Ke kuwa kike da abinda zaki iya yi min”
“Me kenan!”
“Ki bari gobe in kinzo zamuje unguwa acan zan fada miki koma menene!”
“Shikenan Ya daren?”
“Ba dadi babu ke a gefe nah!”
“Uhmm in ina gefen ka me zan maka?”
“Jin dumin jikin ki kawai zai kwantar min da hankali ya sa min nutsuwa. Halima ki yadda dani wallahi ina sonki ba zan taba cutar dake ba zan iya baki rayuwa ta da komai nawa. Ina son ki kinji!”
Murmushin jin dadi tayi dan ta gama yadda da shi yana son ta zai iya bata rayuwar sa.
Hamma tayi yace
“Bacci ko?”
Kai ta gyada yace
“Kije ki kwanta amman kan nan kiyi min kiss!”
Ido ta rufe da hannu kamar yana kallon ta dan taji kunya yace
“Ina jinki!”
“Yaya zan maka?”
“Muaahhh zaki ce!”
Yadda ya fada tayi tace
“Muaahhh!”
Ido ya lumshe yace
“Yauwah kinji dadi kuwa nagode Baby na sai da safe I miss u bye.”
Washe gari bayan sun fita bara kamar yadda suka saba Hajara tayi hanyar ta itama tayi wajen Isma’il. Tana zuwa ya hau murmushi. Fuska ta dan rufe da mayafin jikin ta tace
“Ina kwana?”+
Baki ya lashe ya kura mata ido har ta dago fuska ta dan bata yace
“Ina gaishe ka baka amsa ba.”
Murmushi yayi yace
“Kin tafi da nine. Wallahi ina son ki Halima in na rasa ki mutuwa zanyi ban san tayaya zan iya rayuwa babu ke ba. Please kiso ni ko rabin wanda nake miki ne.”
Murmushin jin dadi tayi tace
“Haba Isma’il sau nawa zan fada maka ina son ka nima.”
“Tayaya zan yadda.”
“Zan iya baka komai nawa akan ka ba zan kula kowa ba. Ka sani ban taba soyayya ba da kai na fara kuma ina fatan ka zama miji na.”
Ido ya lumshe alamar yaji dadi yace
“Tashi muje yau hirar bata nan bace sai an fadan matsayi na a cikin zuciyar ki.”
Mikewa sukai ya kira wani yaron sa ya barwa jura suka bar wajen. Sannan suka tafi dn zuwa suka hau motar sa. Ta kofar wajen su Kabir suka bi zuwan Kabir kenan suka hadu da ido yabi Halima dan yana son yarinyar kamar zai yi me? Amman bai san ta ina zai fara ba ga wannan dan iskan yazo ya hure mata kunne.
Har ya shige kamar bai gansu ba Ismail yace
“Au abun yar haka ce!”
Juyowa yayi yace
“Am sorry ina sauri ne da yake fita zanyi ne!”
Ya mika masa hannu suka gaisa. Yace
“Ina zaka ne?”
Ido daya ya kashe masa yace
“Zamuje musha soyayya ne!”
Baki ya tabe yace
“Sai ka dawo!”
Kace
“Allah bada sa’a!”
Dan tsaki yayi ya shige cikin wajen. Da kallo Isma’il ya bishi yana dariya yace
“Big Alhaji kazo kaji dadin rayuwar ka ga kudi ga kyau ka kuruciya ka xauna a haka.”
Kallon Halima yayi yace
“Muje ko!”
Sukai gaba tace
“Wai meyasa Kabir baya son ya ganmu tare ne?”
Kafada ya dage yace
“Shi ya sani.”
Daga nan suka karasa inda yake parking. Cikin motar sa suka shiga ya tada ta suka bar kasuwa, gidan sa ya nufa da ita kai tsaye a hanya ya tsaya ya siya mata abinci da lemo.
Tin a gate gidan yai mata kyau duk da karami ne amman yayi kyau har suka karasa falon ta zauna a two sittet shima zama yayi gab da ita sai ta dan makale jikin ta. Dariya yayi yace
“Haba Baby menene dan na zauna a kusa dake kada ki manta fa auren ki zanyi kuma ba mai ganin mu anan fa.”
“Nasan aure na zakai Isma’il amman hakan bai dace ba. Kuma in ba mai ganin mu ai Allah na ganin mu ko?”
“Haka ne amman ai ba wani abu nayi ba ko?”
Shiru tayi nan ya mike ya matso mata da abincin da ya siyo tace
“Yanzu ban jin yunwa sai dai ko anjima!”
Mikewa yayi ya kamo hannun ta yace
“Zo mu zaga gidan ki gani yai miki ko a canja wani!”
STORY CONTINUES BELOW

Binsa tayi suja zagaye gidan sune har bedrroom din sa sunje na farko a na biyun ya zauna a gefen gadon yace
“Zo ki zauna!”
Daga gefe ta zauna ya mike ya sshiga bandaki ya jima sai gashi ya fito daga shi sai boxes da towel yana tsane ruwan kan sa. Mikewa tayi ta juya baya. Karasowa yayi ya hade jikin sa da nata wata ajiyar zuciya suka sauke dukkan su a tare. Kokarin barin wajen take ya matse ta a jikin sa yana shafa masa mai danshi a jikin ta. Tsigar jikin ta taji tana tashi.
Dadin abun take ji duk da jikin ta na rawar tsoro amman kuma tana jin dadi da kyar ya kwace kan ta tayi falo. Binta da kallo yayi yana cije lebe yace
“Halima kenan a juri zuwa rafi wata rana tulu zai fashe. Baki san waye Illah ba in naga abu naso na lashi zumar sa sai na sha ko da zai zame min ajali na. Dan haka time is coming dake zaki na kawon kanki ma.”
Kaya ya saka
Halima kuwa tana fita falo ta zauna kai ta jinkina a jikin kujera tana mai da ajiyar zuciya, jikin ta duk wani iri take ji dadi dadi da akasin haka. Nan ta lula wata duniya dan a rayuwar ta ba wani da namiji da ya taba, taba mata ko da hannu bane bare jikin ta.
A wannan halin ya shigo falon ganin ta a wannan halin yasa ya matsa kusa da ita da sauri, ya kamo hannun ta yace
“Ya dai Leemat?”
Ido ta bude a kasalance wanda ya canja kala alamar tana jin wani yanayi.
“Menene?”
“Ba komai bana jin dadi ne kawai!”
“Ayyah sorry!”
Hannun ta ta zare daga nasa saboda yadda taji yana aika mata da wani salon sa. Murmushi yayi yace
“Ni kam bana son abinda kike min Leemat shikenan ban da damar taba ki naga nan da dan lokaci jiki naki nawa zai dawo mallaki na kuma”
“In lokacin yayi ya zama!”
Fuskar ta ya dan shafa yana fadin
“Wallahi Halima sonki ke sawa naji kamar na hadiye ki. Surar ki na fusga ta in har ban same ki nan kusa ba da matsala.”
“Isma’il kenan na fada maka nima fa ina son ka wallahi nima ina jin abinda kake ji!”
“Me nake ji ni to?”
“So na mana!”
Dan murmushi yayi yace
“Gaskiya ne. Na yadda dake dan haka bari na fada miki wani abu. Yanzu haka shekarata talatin Halima dan haka dole na bukaci mace a baya ban samu wacce tai min har nake son auren ta ba sai akan ki dan haka Halima kome kikaga inayi ina dauriya ne. Dan ina matukar bukatar mace ni kuma gaskiya ba zan iya auren wata bake ba.”
Hannun ta ya kama yana kissing take tsigar jikin ta ta tashi ga tausayin sa yace
“Shekarar ki nawa?
“Sha bakwai!”
Ta fada muryar ta na rawa saboda abinda taji yana mata har bargon ta da tsigar jikin ta.
A ransa yace
“Zan more so swt baby!”
A fili kuma yace
“Zaki iya dani kuwa?”
Fuska ta rufe da mayafin ta yayi dariya yace
“Serious fa!”
“Dan Allah ka bar wannan maganar!”
Dariya yayi yace
“Na bari!”
“Kunyar ki burgeni Baby!”
Hannu ta sa ta kare fuska. Yai murmushi yace
“But soon zan cire ta dan in banyi da gaske ba zata na cutar dani.”
Kiran sallah la’asar akai wannan yasa ya mike yayo alwala yace
“Bari naje nai sallah kici abinci kiyi sallah ko zaki watsa ruwa ne!”
Ido ta zaro tace
“A’ah sai ka dawo!”
Ya fita itama ta mike tai alwala tai sallah sannan ta zauna cin abinci sai wajen hudu da kwata ya shigo ta kalle shi tace
“Mu yafi ko?”
“Eh!”
Nan suka fita. wani supermarket ya kai ta yai mata siyayyar kayan kwalliya da ciye ciye sannan suka wuce gidan dan lokacin haduwar su da Hajara ya wuce tasan kila yanzu ta tafi gida ma.
STORY CONTINUES BELOW

Tana shiga suka hadu da Fauziyya ta fito dan tana son ta bada aiken a siyo mata pad. Kallon ta tayi tace
“Anty Fauziyya baki da lafiya ne!”
Murmushin yake tayi tace
“Lafiya ta kalou!”
“Amman duk kin rame fa!”
Murmushi tayi tace
“Leka kiga Amir yana nan yazo ya siyon Pad!”
“Haba kawo na amso miki kawai!”
Ta dire kayan ta fita. Ganin tana son ta shiga daki ne yasa ta daukar mata ledar tayi daki tana shiga daki ledar a subuce a fadi kayan ciki suka zube. Kallo tabi kayan da shi a ina Halima ta samu kayan nan masu tsada dan tasan kayan tana siyan turaren da ya kusan dubu goma banda mayuka da sabulai. Kwashewa tayi ta leka dayar ledar nono ne da ice cream da shawarma da lemuka dukka.
Kai ta girgiza tace
“Allah kada ka sa abinda nake zargi ne. Allah ka tsayar a iya mu!”
Ta goge hawayen idon ta. Dai dai lokacin da Halima ta dawo ta bata mika mata kayan tayi ta shige bandaki. Wanka tayi ta saka sannan a fito.Ta shirya.
Halima na shiga daki ta bude kayan ganin da naci ta dubar wa Anty Fauziyya ta nufi dakin.
“Antu Fauziyya gash!”
Dagowa tayi ta kalle ta tace
“A ina kika samu wannan kayan Halima?”
“Wani saurayi nane ya siya min!”
“Angode amman please Halima ana kula kar ki biyewa rudin samarin nan. Ni wai ina kuke zuwa kullum ku dasu Mama da Hajara?”
“Bara muke zuwa!”
“Bara?”
Ta fada tana zaro ido.
Kai ta gyada mata. Kai Fauziyya ta dinga girgizawa tana mai zubar da hawaye, ko da yake gwara bara akan abinda su suke yi amman kuma illar barar shin dawa zasu hadu hannun wa zasu fada.
“Anty lafiya?”
“Lafiya lou!”
“To gashi!”
“A’ah kuje kuci da kannen ki ni nagode!”
Mikewa tayi ta fita jiki a sabule cike da tausayin yar tata wacce duk gidan suke son ta, dan itama tana son su da taimaka masu ta jima bata ganta ba gashi ta ganta a lokaci daya duk ta rame tayi duhu.
Kullum suna tare a kasuwa soyauuar su tayi zurfi sun shaku kullum zai mata siyayya sannan ya bata kudi wanda sam bata barar yanxu ta kara kyau tayi dumimi da ita a hankali yake isar mata da sakon sa dan yanzu zai kama hannun ta yai wasa dashi har yai huging nata bata hanashi sai dai ma taji dadi har ta lunshe ido.
Kabir kuwa kullun addu’ar sa Allah kubutar da Halima daga Isma’il wanda ya rasa tayaya zai sanar mata amman ya dauki aniyar dakile cutarwar da Isma’il ke son mata.
Watan ta uku rabon ta da fita kuma tin daga lokacin kullim Muhammad zai aiko ana sallama ko da wasa bata taba fita ba. Ta maida komai nata ga Allah da ibada daman Umman ta bata nan.yau watan ta hudu rabon ta da gida da ta tambayi Farisa sai cewa tayi ta tafi saudiyya.
Yanzu ko magana ba sayi da Farisa dan tayi nacin akan Kamal na neman ta amman taki ta yadda su hadu kuma duk abinda zata bata ba ci take ba ko ta amsa ma batayi.
Ji tayi tana son fita dan bata da mai da sabulun wanka da na wanki gashi gashin ta ya dame ta tana son a wanke mata. Wanka tayi ta saka doguwar rigar atamfa ta dauki hijab har kasa ta saka.
Tana fita ta tsare napep ta hau can kasan su taje aka gyara mata kai akai mata kitso sannan ta fito ta wuce wani super market tayi siyayyar ta ta taho. Lokacin da shigo unguwar karfe biyar da hamsin da biyar tafiya take a hankali har tazo gun wannan almajirar nan tace
“Baba ina yini?”
“Lafya lou Fauziyya ya gidan kwana biyu bana ganin ki?”
“Ina nan wallah nagode Baba kin ceci rayuwata na dawo kan hanya Allah saka miki da alheri.”
Murmushin jin dadi tayi tace
“Alhamdulillah Allah ya kara kare ki Allah baki miji na gari!”
Ido ta zaro tace
“Miji kuma? Anya kuwa ni kam ba wanda zan iya aura. Rayuwa ta bata dace da ta mutumin kirki ba gwara na zauna a haka har na mutu!”
“Allah maji rokan bawa ne tare da yafewa bawa kurakuren sa. Ki sani Allah na son ki da rahama da har kika daina abinda kika daina. Ki sani Aure shine martaba da shigar ko wacce mace. Ki sani Allah yana son ki kima zai jikan ki duk wanda yazo miki ki amshe shi Allah zai duba zuciyar ki ya jikan ki kema gana kiga ya’yan ki kinki.”
Kai ta gyada tazaro dubu daya ta baya tace
“Nagode Baba sai anjima zan shigo har gidan yanzu nagaji.”
“Sai kinzo ki gaida gida.”
Tayi gaba tana tafiya. Tazo kofar gidan su kamar Daga sama taji an Mata sallama. Juyawa tayi. Gaban ta taji ya fadi dan bata manta da fuskar sa ba. Tin da ta ganshi ranar da yazo kullum sai tai mafarkin sa.
Nace
“Assalamu Alaikum!”
Ya fada yana kallon ta. Dibibicewa tayi. Dan ya mata kwarjini sosai tace
“Wa’alaikum salam!”
“Dan Allah ki ban minti daya mana zuwa biyu.”
Shiru tayi. Hannayen sa ya hade yace
“Please!”
Dagowa tayi ta kalle shi tai saurin yin kasa da kanta tace……..Tayi gaba yabi bayan ta. tsayawa tayi shima ya tsaya, yace
“Dan Allah ki saurare ni da abinda nazo miki kwana ki na fada miki wallahi son ki nake kuma da aure dan Allah ki amshi soyayya ta kada ki duba rashi na…..”
Kanta a kasa kanwar ta ta shigo daga waje tace
“Anty Fauziyya wai kizo?”
“Inji wa?”
“Inji wani a waje!”
“Je kice ba zan zo ba.”
“A’ah!”
Muhammad ya dakatar da yarinyar daga shirin fitar da take yace
“Nima haka ake min kuma wallahi kasa bacci nake! Dan Allah kije kiji me zai ce miki!”
Dagowa tayi tana kallon sa. Son gaskiya take gani a cikin idon sa. Yace
“Jeki ki dawo ina jiran ki!”
Fita tayi a kofar gidan ta tsaya tana kallon motar dake kofar gidan wacce bata gani na ciki saboda tint ce. Dan haka ta tsaya tana kallon motar da tsana duk da bata san waye ba tasan irin samarin ta na baya ne wanda ba son Allah suke mata ba sai jikin ta.
Kamal ne tinda ta fito ya zuba mata ido bai taba ganin ta da Hijab ba amman ta masa kyau wannan yasa ya kasa ma fitowa a motar ya tsaya yana kare mata kallo.
Ganin yaki fitowa ne yasa ta daka tsaki ta juya zata shige cikin gidan. Da sauri ya dannan horn tare da bude kofar motar ya fito da sauri har yana tuntube ya karaso yana fadin
“Haba ranki yadade ayi hakuri laifin me nayi ne?”
Jin muryar kamal yasa ta juyo kallonsa tayi taji wata tsanar sa na karuwa a zuciyar ta. Wani banzan kallo ta aika masa sannan ta juya zata shige gidan hannun ta ya kamo da sauri, a fusace ta juyo ta daga hannu ta kwada masa mari sannan ta zare idanu hadi da daga hannun ta ta nuna shi da yatsa tace
“Ka kiyaue ni, ba Fauziyyar da bace wannan!”
Fuska ya dafe amman bala’in da yake ciki na rashin ta yasa ganin zata shige yace
“Naji please kiyi hakuri minti biyu dan Allah ba dan ni ba.”
Jin ya hada ta da Allah yasa ta juyo tace
“Ina jinka menene?”
“Fauziyya wallahi na kasa jure rashin ki dan Allah ki taimaka min please kome kike so zan baki.”
Wani kallon kasa da sana tai masa sannan tace
“Kasan me ya yi silar haduwa ta dani? Baka sani ba to ka sani ni a wajena ba kudi ya sa na aikata abinda na aika a ba kaddara ta ce ta saka ni a ciki kuma ina mai son fada maka yanxu kaddara ta ta canja.”
Tai shiru sai kuma tace
“Kasan me?”
Tsaki ta saki tace
“Bai da amfani kaji amman ka sani kaji tsoron Allah. Minti biyun da ka nema ya kare dan haka ka bar mana kofar gida.”
Tana fada ta shige soro idon ta na zubar da hawayen abinda ta aikata wanda duk Kamal shi ya fara lalata mata rayuwa. tana shiga soron gidan tayi turus ganin Muhammad a tsaye. Hijab din ta ta saka tana goge hawayen idon ta sannan tace
“Please kayi hakuri. Ni yanzu ba aure a gaba na. Ko da aure zanyi ban dace da kai ba.”
STORY CONTINUES BELOW

Nan tayi ciki da sauri saboda wani kuka da yazo mata. Kai ya girgiza a ran sa ya ma rasa tunanin da zai in har bai samu Fauziyya ba yasan mutuwa zai yi. Shin ko dan bai dashi Fauziyya ke kin sa. Dan yaga yadda manyan Alhazawa ke neman ta su bata musu haka ko dan su zasu bata kudi.
Kai ya girgiza dan baya son zuciyar sa ta kawo masa aibun Fauziyya dan son ta yake son Allah kuma da aure yayi bincike an fada masa wasu halayar nata na da da yanzu duk da a yanzu ba wai tana rashin mutunci ko shigar banza bane ance dai daga wannan motar ta dauke ta sai waccan ta dawo da ita. Wanda ake zargin bin maza take to shi yaji ya gani yana son ta. Dan Allah shi ya daura masa son ta daga kallo daya da yai mata. A haka ya ja kafa ya bar gidan jiki a sabule.
Kamal da ido ya bita bayan ta shige gidan son ta na nukurkusar zuciyar sa dan son ta yake da gaske wanda tsawon lokacin da suja debe basa tare shi kadai yasan wahalar da yasha. Da ya zata jikin ta kadai yake so dan bayan ta daina zuwa gun sa ya dinga bin wasu yan matan amman sam bai jin nutsuwa da gansuwa in bai hasaso da ita yake mu’amala ba ko zai yi sex sau nawa ma ba zai yi releasing ba.
Juyawa yayi ya shige motar sa ya bar wajen ran sa na suya. Yau kadai da ya ganta ta dada hargitsa masa tunanin sa.
Yana tuki yana tunanin abinda yasa shi fadawa wannan harkar bin matan.
Shine da na fari a wajen iyayen sa, sai kannen sa mata da maza. Mahaifin sa tsohon ambassador ne.
Yayi karatun sa na primary zuwa secondary a Abija inda ya tafi can Sudan dan yayi Degree din da. Acam Ya Hadu da Fatisha wanda ita kadai iyayen ta suka haifa dan haka yar gata ce bama da mahaifin ta ya kasance mai kudi sai abinda take so yake mata haka Maman ta.
Tin haduwar su taji tana son Kamal dan Kamal wayayye ne da gayu ga ilimi ga kyau wannan yasa har ta amshi tayin soyayyar sa. Nan suka kulla soyayya wanda bayan sun gama karatu akai musu aure ya cigaba da master din sa a can kasar itama haka.
Yana son Fatisha dan shi akwai shi da son kyawawa wannan abin ya kara masa son Fatisha gata yar gayu boko ya ratsa ta. A auren su sam bata san ma menene auren ba, bare wani hakkin sa. Ba abinda ta iya komai yi musu ake masu aiki ba anan kadai ta tsaya ba dan ko hakkin aure na jikin ta bata bashi dan in zai neme ta sau goma bai fi ta yadda sau daya ba wanda shi kuma mutun ne mai sha’awa. Wannan yasa yace zai aure amman sai ta tada hankalin ta ta kuma ce wallahi ba zai ba in har zai aure to sai dai ya sake ta. Shi kuma yana son ta.
Ganin sa kai kyau ga kudi yasa yan mata masa rubibi wanda tin yana kin kuka su har ya fara kula su da wata yar Nigeria ya fara zina wanda ita ta rinjaye shi a lokacin ba a son ran sa ba wanda jiki da jini da shaidan gashi mabukaci wannan yasa ya yadda da ita. Tin daga lokacin ta zama tamkar matar sa dan duk lokacin da zai kai bukatar sa bata kin yadda da hanzarin ta take bashi hadin kai.
A haka ta gama karatu ta tafi wanda yai kata alkawarin da ya gama nashi zai biyo ta nan Nigeria dan itama anan Abujan take.
Bayan tafiyar ta ya dinga bin yan mata kala kala suna biya masa bukatar sa har lokacin da ya gama karatun sa suka koma gida Nigeria wanda anan Abuja mahaifin sa ya damka masa gida bayan lokaci kadan ya samu aiki acan Kano. Da yace Fatisha ta bisa su koma tace ita ba inda zata yana zuwar mata weekend.
Abinda ya kara bawa Kamal damar bin yan mata a haka ya hadu da abokai wanda suka kara saka shi a hanya.
Wata rana suna zaune aka kawo musu su Fauziyya wanda tin daga daura idon sa akan ta yaji yana son ta. Sai kuma lokacin da ya same ta a virgin da abinda yaji na ni’inar ta wannan ya kara sawa ya mace mata.
Ta sha kyauta agun Kamal gida, mota, kudade masu yawa wanda duk a account take aje su.
Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya kai karshe a tinanin sa ya danna horn mai gadi ya bude ya shiga.
Hakika duk Fatisha ita ta ja masa wannan bala’in wanda bai san tayaya ya fada halaka haka ba. Yana rokar Allah yasa Fauziyya ta yadda ta aure shi ko ya huta amman yaga tsanar sa karara a kwayar idon ta.
STORY CONTINUES BELOW

Bai taba samun wata mace a bariki budurwa ba sai Fauziyya haka nan bai taba samun mace mai ni’ima irin tata ba. Lallai Fauziyya daban ce ya jyau ga kyan diri kan kujera ya fada yana dafe kansa.
Yarinyar da ta kwana a gidan ce ta fito daga bedroom jin ya dawo ta hau kan cinyar sa tana shafa shi. Ido ya bude ya janye jikin sa daga nata. Kara makale shi tayi da sauri ya mike yana fadin
“Bari mana!”
Amman sai kara shige masa take. Mari ya tsinka mata ya zare ido yace
“Get out!”
Ya nuna mata kofa, ai da sauri ta shige ta debo kayan ta, ta saka ta fice saboda yadda taga ya canja mata lokaci daya.
Mama ce tafe ita da yan yaran ta sina bara daya baifi shekara bakwai ba dayan shekara goma tara. Suna gefen titi taga wata mota mai nunfashi a tsallaken titi nan da nan ta tura dan shekara tara tace
“Maza Nasir jeka ka yo bara agun motar can!”
Da sauri ya mike ya tsallaka titin yaje yai bara.
“Dan Allah ka taimaka mana da abinda zamuci wallahi yunwa nake ji!!
Mai motar ya kalli Nasir tausayin sa ya kama shi yace,
“Ina maman ka?”
Titi ya nuno masa. Kallan wajen da take yayi ya girgixa kai ya zaro dubu daya ya mika masa nan ya yi Nasir yace
“Angode Allah saka da alheri.”
Ya juya ya nufa titi yana murnar sa sam bai kula sa kallan titin ba sai jin karar burki sukai wata mota ce ta bugeshi yayi sama ya fado kan sa ya hau zubar da jini da gudu mai motar ya bar wajen nan Mama ta taso sa gudu tana ihu tana kiran sunan sa amman ina jini ne ke zuba ta hanci da baki ga kansa ma dake zubar da jinin.
Nan da nan motar kwana kwana tazo aka tafi asibitin murtala emergency aka amshe shi nan suka shiga dashi mama na gefe sai kuka yake Yusuf dan shelara bakwai yana gefe ta yaa ta wasan sa. bayan minti biyar suka fito suna fadin
“Wa ya kawo wanda aka buge da mota?”
Mama ta tashi da sauri tayi wajen nurse din tace
“Nice!”
“Allah yayi masa rasuwa ki shigo ki dauki gawarsa.”
Ihu Mama ta saki tana fadin
“Na shiga uku!”
Kuka take a haka ta dauke shi suka tafi gida. Nan aka kira mahaifinsa yazo akai masa sutura aka kai shi gidan gaskiya. Mama ta sha kuka kamar ba gobe haka aka fara amsar gaisuwa.
Sakina kuwa tana can tana harkar gaban ta tayi kyau dan hajiyoyin da take tare dasu kudi suke sakar mata sosai sumata siyayya saboda yadda suke jin dadin ta bama Hajiya Mariya da ta xama kamar matar ta ayar su suke shekewa ba tare da sanin ‘dan ta ko mijin ta ba.
Tafiye tafiyen nata da take yi ma ta rage domin yanzu kullum tana gun Hajiya Mariya. Mama in tace ina taje sai tace aiki ta samu take yi a wani gida ganin tana zube mata kudi sai ta rufe mata baki bata fadan dan taje ta kwana.
Farisa kuwa ta zama kwankwarar ra dan Hafsat kan ta ta sara mata dan yanzu a cikin kano da wajen ta har neman Farisa ake ana rubibin ta inda ita kuma sai taga dama wannan yasa take abinda take so san ranta dan manyan Alhazawa sun tsaya mata.
Zaune take a falon wani Alhajin ta sanye da wani wando wanda iyakar sa cinyar ta sai yar half vest da ta kamata ta giyace a gaban ta tana sha kanta ya sha gashin doki. Saurayin ta Salim wanda ya kawo ta gidan ne ya fito daga ‘daki gefen ta ya zauna yana janyo ta jikin sa, wata mika ta saki abinda ya bashi damar shigewa jikin ta kenan. Daga nan ya mike ya dauke ta sukai cikin dakin sa.
Basu fito ba sai da suka dauki awa uku sannan ya fito rike da hannun ta suna dariya.
“Wai ke sai kinji gidan uwar dakin nan taki ne?”
“Haba Sameer kai kadai nake yadda nayi kwana biyu a wajen sa amman ba wanda ya isa ya sameni yau ya kuma kara samu na gobe, amman hakan ma bazaka gode min ba!”
Ta fada tana daukar jakar ta.
“Baki san yadda nake ji bane in bana tare da ke! Ji nake kamar na mutu dan Allah ki dawo anjima!”
“Zan duba na gani sai anjima!”
Tayi waje ya bita, mota ya bude mata ta shiga ya zagaya yashiga suka bar unguwar can gidan magajiyar su ya kai ta da zata fita yace
“Please Farisa ina jira dan Allah!”
“Ba komai! Bye!”
Ta daga masa hannu tayi gaba. Da kallo ya bita dan ta gama tafiya dashi.
Tana shiga gidan ta tarar da ansaka waka ana cashewa ai nan da nan ta shiga fili tana kada jiki yadda take kaa jikin ta yasa kowa ya bata waje ana kallon ta sai da tayi ta gaji sannan ta koma wajen magajiyar su suna magan kasa kasa daga nan ma suka mike sukai daki.