WANNAN RAYUWAR CHAPTER 3

 WANNAN RAYUWAR CHAPTER 3

Karfe biyun dare taji ana shafata abinda yasa ta bude ido da sauri kenan. Wanda ya kawo ta gidan ta gani mikewa tayi tace

“Mu tafi ko?”

Idon sa dake a kankance tsabar jaraba ya bude yace

“Ina?”

“Gida!”

Ta fada a shagwabe. Fuskar ta ya shafa yace yanzu karfe biyu har da rabi ba ki bari sai gobe dazu nazo ina ta tashin ki baki tashi ba.”

Kai ta gyada tana matsa karshen gadon biyo ta yayi tace

“Dan Allah kayi hakuri wallahi wajen da zafi.”+

Tausayin ta yaji amman kuma a bukace yake da ita. Yace

“To naji amman ki Sani ba zan miki komai ba amma duk abinda nasaki kiyi min zaki min kin yadda.”

Nan ta gyada kai Dan tasan azabar da take ji a wajen har yanzu. Dole duk abinda yace tayi take masa duk da ba a son ranta take ba shi kam sai ihu yake a haka har ya samu yayi releasing. Amman fa kirjin ta kamar ya cire Dan ja bakin ta kuwa saboda kiss har zafi yake mata.

A haka bacci ya kwashe sa yana kanta itama Bata San lokacin da baccin ya dauke ta ba sai asuba sannan ta farka, ta shiga tai wanka ta Kara gasa jikin ta tafito ta tada shi tayi sallah. Tana zaune ya tashi ya shiga yai wanka ya fito daure da towel. Kai ta dauke. Ya fita tana zaune hade karfe bakwai ta mike ta fita a falo ta same shi. Kallon ta ya tsaya yi tace

“Ka kaini gida.”

“Tin yanzu?”

Kai ta gyada masa.

“Zo nan!”

Ya fada yana nuna mata gefen sa karasawa tayi ta zauna. Ya ce

“Bari ki karya sai in kai ki gida kinji.”

Kai ta gyada masa yana zaune ya mike ya shiga daki aransa Sam baya son ta tafi amman zai mata abinda baza taba rabuwa dashi ba. Wani Katon akwati ya janyo ya fito falon da shi. A gaban ta ya ajiye ya bude yana fadin

“Sauko kiga kayan sun miki ko a canja su.”

A ranta tace wai kai baka San na tsane ka bane. Ko da yake ba laifin ka bane laifin Mama ne da tasa a kawoni nan. Yanzu Mama da kanta take son na koma karuwa. Sai hawaye ta hau zuba a idon ta.

Yana gani yace

“Haba Sugar menene ko bakya so fada min abinda kike so, gida kike so ko mota ko hajji zan kai ki fada min.”

Shiru tayi ya mike ya shiga daki ya dauko bandir din kudi yan 1k guda hudu yazo ya ajiye su hannun sa dayan rike da kwallin wata sabuwar wata da a lokacin ta fito kasuwa ya ganta ya siyo mata. Ajiye mata yayi yace

“Nasa ayo min order motoci da sunzo daya taki ce. sannan akwai gidaje na da ake karasawa a rijiyar zaki in kin dawo zamuje ki zabi Wanda kike so.”

Duk yana mata haka ne Dan gobe ta dawo. Yace

“Ga waya nan da number in kina bukatar wani Abu. Yanzu daga yau sai yaushe.”

Shiru tayi ya ce

“Gobe inzo in dauke ki.”

Dan ya kyale ta tace

“Eh.”

Dai dai lokacin da akai knocking Kennan ya mike ya amso abun ya dawo ya bude musu chips ne da farfesun kayan ciki sai fulas din tea ya hada mata ya tashi ya bar ta a gun Dan ta sake taci. Ai kam ta danci Dan tana Jin yunwa bai fito ba sai sha biyu saura kuma taki ta koma daki tana zaune Dan tace bazata koma daki ya fita ta Kara kwana a gidan ba.

Kayan ya dauka yace

“Tashi muje.”

Ta mike tabi bayan sa. Shi ya bude mata mota ta shiga ya zaga ya shiga suna hawa titi yace

“ina zamu?”

Fada masa tayi da aka zo unguwar ta dinga masa kwatance har sai da yazo kofar gidan sannan ta fito. Shima fitowa yayi ya mika mata da kayan yana kallon ta kasa kasa yace

“Sai gobe?”

Kai ta gyada ta juya.

“Uhmmm please Fauziyya take care kinji.”

Haushi ya zo kirjin ta amman ya zatayi ya gama cutar ta Dan haka kai kawai ta gyada ta shige gidan. Dakin su ta shige ta fada gado ta sha kukan ta sannan bacci ya dauke ta.

Sai yamma su Hafsa da Farisa suka dawo Hafsa da kaya Niki Niki sai uban kudi da suka samo suka shige daki. Fauziyya suka samu tana bacci suka kalle ta suka sheke da dariya. Nan suka zauna suna maida maganar jiya da abinda ya faru. Abinda ya tada Fauziyya kenan.

Kallon su tayi sukace

“Sannu da zuwa Anty Fauziyya.”

Batace kala ba. Farisa ce tace

“Me kika samo mana.”

Ta janyo akwatin tana budewa tare da zaro ido tace

“Gaskiya ne Wallahi Anty Fauziyya ai daman ke daban ce irin wannan kyau da diri ai kila har da kujerar hajji aka hada miki.”

Tsaki tayi ta tashi zata fita kallon tafiyar ta Farisa tayi da yake Farisa ita idon ta a bude yake tin kan ta fara bin maza yasa ta ce

“Kai sai na gyara ki Anty Fauziyya kalli tafiyar ki. Hafsa jeki dauko min ruwan zafi.”

Dawowa tayi ta kwanta Farisa da Hafsa suka hada mata ruwan shiga hade da maguguna suka sa taje ta gyara jikin ta sai taji dadin jikin ta. Wani magani Farisa ta Bata guda uku daya na wankin mahaifa daya na Karin ni’ima da Wanda zai tsuke ta Bata San na menene ba tasha nan suka Samar musu abinda zasuyi.

Fauziyya ce ta dauki kudin wajen ta dubu dari ta basu tace

“Kuje ku siyo kayan abinci duk abinda Babu a siyo shi.”

“Sai Hajiya Anty Fauziyya.”

Suka fita komai sai da suka siyo bugun shinkafa guda hudu sannan taliya Katon biyar mai, macaroni, indomie, magi, gishiri har gas suka siyo a gidan. Sannan suka dawo nan da nan aka daura abinci a gidan yaran sai murna suka.

Sakina kuwa tana can Habee ta dauke ta zata kai ta gidan wata uwar dakin ta. Wacce wani gida ne, Katon gaske da sukaje Hajiyar Babba ce Dan ance Kawar matar gwamna ce ma haka suka zauna ta sallama Habee ta rike Sakina tace zata kai ta gida da kanta.

Wannan yasa duk abinda akai Bata gida. A jiya da Yaya Babba ta dawo taga Babu Hafsa tace tana ina sai akace Bata nan sunje unguwa da Farisa gidan yan uwan Maman ta. Wannan yasa tayi shiru.

Dukkan su wayoyin su suka kashe Dan Fauziyya daman Bata bude wayar ta ba. Suna zaune wajen isha’i sai ga Yaya Babba nan ta shigo tana kiciniyar daura abinda za’a amma sai ta tarar da abincin ta ma. Nan ta zauna tana mamakin inda aka samo abincin. A gajiye ta dawo da yara Dan haka tara nayi tai bacci inda sai a lokacin Jummai ta dawo tana shiga dakin ta ta hau washe baki. Mikewa Fauziyya tayi ta shige daki Dan bata son kallon fuskar Mahaifiyar tatama Dan komai da ya faru itace sila.

Kallo Mama ta bita dashi tana girgiza kai. Farisa ta ce

“Hajiya Mama Allah yayi albarka kinga arziki kuwa. Arziki na bin mu Ashe muna gudun sa.”

Nan suka dinga Bata labari tana ta dariya da murna nan Farisa ta Bata dubu dari sannan tace ga abinda Yaya Fauziyya tayi nan sai ga Mama na fada wai dan me zata karar da kudin ta har dubu dari ita take da hakkin ciyar da yaran gidan ko me.

Haka ta tashi ta shiga dakin da Fauziyya ta shiga tayi fadan ta tagama sannan ta fito Fauziyya ko kallon ta batai ba. Suna zaune akayi kiran Farisa ta tashi ta tafi Bata Dade da tafiya ba sai aka Kira Hafsa itama ta tafi. Mama sai murna take tana jiran taji Fauziyya ta fito ta tafi taji shiru wannan yasa ta leka daki sai ta tadda ta tana bacci ma.

Tsaki tayi tace

“Shegiya mai bakin halin tsiya.”

Daga haka ta wuce daki ta kwanta ita man.

Hafsat da Farisa kam sun kama kasuwanci sosai suke bin maza inda acikin sati daya har sun kware da harkar kamar ba farin shiga ba.

Kullum Kamal sai ya Kira Fauziyya wayar a kashe Dan haka yau ana magariba ya Iso unguwar sallama yasa akayo masa da Fauziyya lokacin Farisa zata fita tace

“Muje muga waye?”

Tana zuwa taga Kamal ‘Babban Alhaji. Nan suka gaisa yace

“Ina ta kiran Fauziyya wayar ta a kashe Lafiya kuwa?”

“Lafiya lou! Kasan Yaya Fauziyya sai a hankali halin ta daban ne. Amman kar ka damu zan hada mata abun da sai ta neme ka.”

“Nagode kanwata.”

Ya debo kudin da baisan adadin su ba ya Bata. Ta amsa ta tafi shima haka.

Washe gari da yamma ta shigo gidan da lemuka a daya ta saka maganin saka Sha’awa tana shiga daki ta mikawa Yaya Fauziyya da hadin nama. Amsa tayi har da godiya sannan ta fita. Ita da kannen ta suka raba sauran. Tinda Fauziyya ta gama ji taji jikin ta yai wani irin sanyi take ta fara Jin kirjin ta na bugawa daga haka sai taji wata matsanaciyar Sha’awa Dan har gaban ta harbawa yake yi. Idon ta lokacin daya ya canja ta rasa inda zata saka kanta.

Tin yamma take a wannan halin har akai magariba sai da tai wanka tayi sallah tana zaune ta dungule kafafun ta Dan yadda take ji sai ta Saki kuka.

Farisa ce ta shigo tana fadin

“Yaya Fauziyya lafiya?”

“Ina fa Lafiya Farisa abinda ban taba ji ba shi naji yau. Wai namiji nake bukata ya zanyi Farisa.”

“Ina Kamal dinki?”

“Wane kuma Kamal dina?”

Ta tambaya.

“Alhaji da aka hada Ku.”

Tsaki tayi tace

“mai zan masa to?”

“Ai shawarar daya shine ki Kira shi ya taimaka miki ki fitar da abinda kike ji.”

Wani kallo ta aikawa da Farisa tace

“Ai na tuba wancan ma tsautsayine bana fatan karawa Allah ya yafe mana wancan ma.”

“Oh haba? Shikenan ki zauna ki mutu.”

Ta mike ta fita. Wata hautsinawa da marar tatayi Bata San lokacin da ta kwadawa Farisa Kira ba tana zuwa ta hau cewa

“Farisa taimaka min zan mutu?”

Farisa tana danne dariya tace

“Ni ban da abinda zan iya taimakon ki dashi shawarar ce na baki kince ba haka ba.”

“Dauki wayata ki Kira min shi.”

Ta fada tana share hawayen idon ta.  Dariya Fauziyya tayi ta dauko wayar ta kunna text din sa ne suka hau shigowar Dan ko ba a duba ba tasan shine. Number da tagani tasan tashi ce ta dauka ta hau kiran sa. Tana fara ringing aka kashe daga haka ya kira. Farisa tace

“Kazo Yaya Fauziyya na Neman.”

“OK gani nan.”

Ba a dauki lokacin ba sai Gashi nan. Nan Farisa ta kamata takai ta cikin motar ya tada motar sai gidan sa.

Kasa tafiya tayi Dan marar ta ta daure shi ya dauke ta suka shiga. Yana daukar ta taji tsigar jikin ta ta tashi tin kan su shiga falo ta fara kissing nasa da kyar suka karasa bedroom nan ta haukace masa. A haka har ya samu ya kusanceta taji zafi amman a halin da take ciki Bata jishi sosai ba.

Shi kam Kamal sai mamaki yake sai da komai ya lafa Farisa ta Kira tana ce masa

“Ina jiran tukwici na.”

Yai dariya yace

“Kece kika taimaka min kenan. Ki cigaba zan na baki rabon ki ngd”

Sukai sallama. Sai bayan tai wanka nadama ta baibaye ta ta hau yin kuka nan yazo yana lallashin ta. Dole ta kwana Dan tayi dare.

A bangaren Sakina kuwa yadda wannan hajiyar nan ta tafiyar da ita ba karamin dadi yai mata ba Dan sai taji ta sakayauyau da ita, bayan cima da aka cika ta da ita da zata tafi hajiyar ta hada mata kaya masu yawa sannan ta daura mata da kudi mai shegen yawa Wanda sai da sakina taji tsoron amsa. Da murnarta ta koma gida lokacin har Baba tai bacci Dan ta kwaso gajiya. Inda ita kuma ta kwanta kan ta tashi Baba ta Kara dibar kananun ya’yan ta sun tafi bara.

STORY CONTINUES BELOW

Haka rayuwar gidan ta kasancewa Wanda Auwal garin sai da rake ga yan shaye shaye suka Fara koya masa shaye shaye Wanda duk a gidan basu lura ba saboda in Alhaji Kasim ya fita tin safe Bai dawowa sai dare Bai damu da sanin a wane hali ya’yan sa suke ba. Itama Baba bata dawowa sai dare Dan yanzu a gidan ba rashin abinci.

Haule ce dai take ta gwagwagwa da cikin da yanzu watan sa takwas kenan. Sai dai duk ta kumbura da taiwa Alhaji magana sai yace taje chemist ya hada ta da dari biyu. Inda da taje ya hada mata maganin dubu uku ganin bata da kudi ya hada mata maganin dari biyunta ta komo gida da ciwo na cin ta.

Samira kuwa sai da ta matsawa Farisa ta hada ta da wani Alhaji inda itama ta Fara bin mazan take samun na kashewa da nacin dadi.

Farisa da Hafsa Idon su ya fetsare kamar Wanda suka jima a cikin halin haka suka koma sam basa kunyar kowa dan duk wanda aka hada su yanzu ma ba sosai suke tare ba sai sun rokesu sannan suke zuwa dan sun samu manyan alhazawa wanda suke samun kudi dan yanzu sam basu da matsalar kudi a gida ma sai dai su taimaka.

Fauziyya ce take kyamar abin amman Farisa tinda ta gane haka ta sa take bata maganin sha’awa a boye wanda ko taje tayi zinar sam bata cikin nutsuwa damuwa tai mata waya amman da abin ya zamar mata jiki sai ta sake itama ba dan tana so ba.

Har wata kungiya Su Farisa suka kai ta wacce ta cikakkun yan bariki ne, inda a cikin su sai wani competition ake akan wacce aka fi rububi, wato wacce kadangarun bariki suke nema.

Sai dai Fauziyya Allah ya daura mata ibada da taimako duk inda ta ga mai neman taimako zata taimaka masa a haka har ta saba da wata almajira a kofar layin da take zuwa gidan Alhaji Kamal ko Sameer sabon wanda suke a tare kenan dan har yanzu Kamal sam bai kyale ta ba dan shi kadai yasan sirrin dake tare da ita wanda yace duk wanda ya dandani zumar Fauziyya bazai taba kyale ta ba wanda shima abinda yasa har yanzu yake bibiyyar ta wanda ita kuma a duniya shi tafi tsana dan har dashi a fara lalalata mata rayuwar ta.

Kamar Ko da yaushe bayan sun gama abunda zasuyi da Kamal ya ce zai fita tace ya kai ta gidan Magajiar su.  A kofar gidan yai parking yana aika mata da wani dan iskan kallo, ido ta lumshe tace

“Yaya ne kai ka fiya jaraba sam baka gajiya da zan zauna sai ka yini a kaina.”

Dariya yayi yace

“Baki san yadda kike bane, shin a cikin wadan da kuke tare a da ba wanda ya taba ce miki abinda na fada.”

Ido ta lumshe dan gaskiya ne sai dai batai mu’amala da mutum ba wanda indai tai ma’amala da mutun shikenan zai zame mata cingam dan yadda yake jin ta. wannan yasa a gidan su na karuwai da ita ake adawa dan kowa ita yake nema, sai dai basu ji labarin ta ba manyan alhazawa ke neman ta ido rufe wanda ita kuma Fauziyya sai ta ga dama dan ba da kowa take taraiyya ba. A zahiri su Farisa sun fita wayewa amman a badili tafi su komai.

“Kaga ni kam bari naje.”

“Please Fauziyya zaki zo anjima ko nazo na dauke ki ne?”

Murmushi tayi tace

“Zan nemeka.”

“Please sweerhrt kar naji shiru wallahi har na fara jin feeling naki again.”

Baki ta cije tace

“Ai na fada maka indai takai ne kwana zamuyi a daki.”

Murmushi yayi yace

“Me kike so?”

Baki ta tabe tace

“Wannan motar nake so da wannan gidan na GRA da mukaje rannan.”

Yadda take magana tana lumahe ido ya kara narkar da shi. Baki ya lashe yace

“Da dare mu hadu ki amshi takardun gidan shikenan.”

Fuskar sa ta shafo har zuwa kirjin sa zuwa gaban sa ta dago abar sa tace

“Ta shirya anjima sai tace ta gaji dani.”

Hannun ta ya rike a gun yana lumshe idon yace

“Bazata taba gajiyawa da dumi da zakin ki.”

Hannunta za ta kwace ya janyo ta ya hade bakin su waje daya sun jima suna romancing junan su sannan ta janye jikin ta tana me cewa

“Sai daren!”

Ta bude kofa ta bar shi a cikin wani mayuwacin hali.

Sai ta bishi iska tana zuwa gida magajiyar su. Tana shiga aka fara kwada ta dan a gaskiya in kaga Fauziyya xaka iya zaton ba yar kasar nan bace dan kyan ta da dirin ta. Nan yan bayan ta suka hau kawo mata gaisu nan ta amsa.  Nan yan wajen suka fara jin haushin ta. Magajiyar su wacce take ji da Fauziyya a yanzu ta kamo hannun ta tace

“Manyan hajiya ya kike ne? Ya jama’a?”

“Anty Magajiya ina lafiya ya kike ya yan koranki.”

Kallon yan dakin tayi tace

“Gasu nan sai a hankali kudi nake bukata.”

“Baki da matsala zan turo miki.”

Ihu dakin aka dauka. a cikin yaran dakin wata tace

“Please muma a bamu ko na kati ne.”

Magajiya ta kalla tace

“Zan turo miki kudi sai a raba musu.”

Ihu suka dauka, wasu yan mata dake dakin suka mike suna mata kallon banza, sauran yaran yan bayan ta ne suka mike zasu fara dambe. Sam Fauziyya bata son hayaniya dan haka ta mike tace

“Akan me zakuyi fada, a kai na? No please ku daina indai nice nan gani nan bari.”

Ta koma ta zauna. Komawa sukai suna fadin

“Sai Antyn mu.”

Murmushi tayi ta mike tace

“Bari na tafi sai kunji sako na.”

Nan ta mike har da…….

Nan ta mike har da magajiya a masu rakata har bakin kofa. Nan ta hau napep ta tafi gida. Akan layin su nan ta samu wannan almajirar gaishe ta tayi a bude jaka ta bata dubu daya sannan ta wuce ta da kallo matar ta bita dan ta gane me yarinyar takeyi. Tana shiga kannen ta suka yo kanta suna mata sannu da zuwa, dan suma suna jin dadin ta dan sai dai bata ga yaro ba sai abinda yake so take masa. Dan haka nan da nan ta bayar a siyo muusu kaji sannan ta shige daki. Wayar ta ta dauka tayiwa su Magajiya transfer kudi masu tsoka sannan ta ajiye wayar bata minti byar ba sai ga kiran magajiya nan da an dakin suna zuba mata godiya tace ba konai ta kwanta dan ta huta.
Kamal ne ya kira ta na ta dauka yadda suke wayar ka rantse da Allah da mijin ta suke waya sai wani karairaya take da juyi akan gado. tana cikin wannan halin Samira ta shigo yadda ta canja kai baka ce itace a kwanakin baya ba dan yanzu ta goge ta zama fara tayi kiba ganin Fauziyya na waya yasa itama ta janyo wayar ta a jaka text ta tura ta ajiye. Wayar ce ta hau kara ta dauka cikin murya mai sanyi ta amsa sallamar sannan tace
“Ah haba na gane mai magana ko ba Alhaji Bilya ba.”
Tai shiru tana murmushi tace
“Ah haba ka shigo gari kenan.”
Tai shiru tana jin abinda yake fadi sai kuma tace
“Kaga yamma fa tayi da dai zaka bari ko gobe da safe.”
Tai shiru tana sauraron sa sai kuma ta fashe da dariya tana fadin
“To gani nan kai kam akwai ka da jaraba ka baro matar ka xaka zo ka kwakuleni in nazo ma baifi kai round daya ba dan dare ya kusa kuma kasan yau a daki na mai gidan yake.”
Tai shiru sai kuma tace
“Shikenan gani nan.”
Dai dai lokacin da Fauziyya ta gama wayar kenan. Kallon ta Fauziyya tayi tace
“Allah Anty Samira ki daina abinda kike da auren ki.”
Hararar ta tayi ta mike tafice bata tamka mata ba. Itama kwanciyya ta cigaba dayi har akai magariba tai sallah sannan ta mike tai wanka ta hau kwalliya sai kace mai zuwa biki sannan ta fice a gidan a bakin layin su ta tadda matar Wannan almajira zata tafi gida tana kokarin tashi dan haka da sauri ta karasa ta taimaka mata tana mata sannu. Amsawa tayi tace
“A dawo lafiya Allah ya tsare.”
Sannan ta tafi.
Gidan Kamal ta isa tana zuwa yana falo yana jiran ta. kallon sa tayi a shekeke sannan ta samu gu ta zauna.
“Yau sarautar ce ta motsa ne gimbiyya ayi hakuri kisan yau a matukar matse nake tinda muka rabu a daddafe na karasa komai nawa.”
Fari tai masa da ido wanda ya kusan zautar dashi nan ya mike ya shiga daki sai gashi da wani yar jaka yazo ya xauna a gefen ta ya dauko wata takarda ya mika mata yace
“Ga takardar gidan nan.”
Ya kuma dauko wata yace
“Ga wata kyautar nan.”
Sai ya miko mata mukullin motar yace
“Ga abinda kika nema kuma. Wai ke ina kike kai motocin kine?”
“Ina ruwan ka.”
Ta fada tana tattare takardun da mukullin sannan ta mike tayi hanyar bedroom tana girgiza jikin ta wanda duk motsin ta kara jefa kamal take a cikin wani yanayin. Ido ya lunshe ya cije lebe yana jin wani iri a jikin da sa sauri ya mike ya bita dakin.
Yaya Babba kuwa wato Sa’adatu ta maida kananun ya’yan ta jari yau daga wacan unguwar gobe sai waccan zuciyarta ta gama mutuwa ta yadda yanzu ta wannan hanyar kawai zatai arziki wanda har tasa matasan yan matan take fito dasu daga baya ta barsu su shiga gari suna bin gida ana basu sadaka yan yaran kuma suna tare sai ta labe a wani gun suje su amso mata sadaka. Cikn ikon Allah sai gashi tana samu dan kudi yanzu take dashi sosai kullum a mai gidan ya fice itama take ficewa.
Maman su Farisa ma Jummai ma ta rika a yawon bara sun dinke ita da hajiya kaltum dan yanzu zance tafiyar su saudiyya na sukeyi dan itama yanzu kudi bata da matsalar sa sam.
Inda ita ma samira  abun da take yawon bin maza dan acan baruki suka hadu da masu aure irin ta suke rayuwar su tare. A cikin su akwai Rabi da Barira.
Rabi dalilin fara bin mazan ta mijin tane sam bai zama a garin kullum yana can yawon neman kudi bai fi yaxo yai mata sati a wata uku ba wanda ita kuma bazata iya jurewa ba shine ta fara bin maza dan ita da kananun yara yan unguwar su ta fara lalatawa inda daga baya ta shigo harkar sosai dan in taga babban Alhaji yai mata ma har gun malami take zuwa a ja mata hankalin sa. Ba ruwan ta da batsa a gaban kowa idon ta ya bude sosai tana da ya’ya amman har kwana take a waje sai ta dura musu maganin bacci suyi ta bacci ita kuma ta fice.
Barira kuma tana da mijin ta amman yau shekarar sa uku rabon sa da ita dan yayi balaguron samun kudi wannan dalilin ya jefata itama yawon bin maxa da auren su.
Inda Samira kuma mijin ne bai sauke nauyin cin su da shan su har ta fada harkar. Allah ka shirya ka sa mufi kafin zuciyar mu Ameen.
1
Fauziyya ce ta fito taci kwalliya sauri take zata je wata unguwa tana fitowa suka hadu da wannan almajirar kudi ta dauko ta mika mata sai almajirar tace
“Amman ina son ganin ki yarinya kinji?”
“Toh Baba sai dai in na dawo.”
“Ba komai Allah ya tsare.”
“Ameen nagode.”
Tana tsaye akan tit taji wayar ta na kara tana dubawa taga Kamal ne. Dagawa tayi tace
“Ya akai Kamal dina.”
“Please Baby wata tafiya ce ta sameni har london please kizo zamuyi wata magana.”
“Kamal unguwa zani gaskiya.”
nufashi yaja yace
“Kina ina?”
“Ina titin unguwar mu.”
“Ok ki tsaya ganinan.”
Ya kashe wayar. Tana tsaye tsaiwar jiran sa ai ga wani matashin saurayi nan yana sAnye da wani yadi wanda daga gani ba wani kudi ne dashi ba amman kyakyawa ne sosai. A gaban ta ya tsaya yace
“Assalamu Alaikum!”
Dagowa tayi tare da amsa sallamar wanda suna hada ido kirjin ta ya buga dan haka tace
“Wa’alaikum salam.”
“Barka da yamma!”
“Yauwah!”
Ya danyi murmushi da ya kara fito da kyan sa yace
“Wallahi tinda zan shige na ganki sai naga kin min ina son ki.”
Wani kallo tai masa zatai magana kenan sai ga motar Kamal nan taxo.
“Sorry!”
Ta fada tana daga masa hannu tayi gun motar ta tafi ta barshi a tsaye.
Motar yabi da kallo zuciyar sa na kuna ba tin yau ba ya ke ganin ta kuma yaji yana sonta da aure dan bai taba son wata a rayuwar sa ba amman ita kam yaji ya kamu da son ta da ya fara bincike akan ta sai yaji ance masa tana yawace yawace abinda ya daga hankalin sa kenan dan yadda yake wa Fauziyya addu’ar neman shiriya kanar shi ya haife ta ba dare ba rana addu’ar sa Allah ya shirya ta kenan yai sadaka yai azumi duk shi kadai.
Kamal daga nan Airport ya nufa a hanya yace
“Please Fauziyya once a rayuwar mu yau ki yadda ki rakani wannan aikin wallahi bazan iya nisa dake ba. Please ki yadda dani ba cutar dake xan ba.”
Murmsuhi tayi a ranta tace
“Ai cutarwa ka gamai min tinda har ka kwanta dani ba tare da aure ba.”
“Kinyi shiru.”
Ya katse mata tunanin ta. A ranta sai taji itama dai yau bari tabi shi ta bashi wannan chance din da yake nema dan haka tace
“Ba damuwa.”
Juyowa yayi yana kallon ta da mamaki yace
“Kin yadda sa gaske?”
Kai ta gyada masa. Jikin sa ya janyo ta yana aika mata da kiss sai da yaji motar zata kwace ne ya komar da hankalin sa kan titin. A take akai musu komai suka bar kasar.
A nan kuwa su Farisa an samu duniya ita da Hafsa sai yadda sukai da maza dan suma Samira ta koya musu bin malamai inda in sunga duk wanda suke so zasu kai sunan sa sai dai kwanan zancen.
Sakina kuwa itama ta zama yar lesbian sosai dan da manyan mata take hulda tayi kudi cikin kan kanin lokaci inda nan da nan ta zama hajiya yau daga tana waccan kasar gobe tana waccan kasar ko garin.
Auwal ma ya zama dan shaye shaye dan har a yar sata yake tabawa. Sabida zama dasu da yake a haka suka koya masa sosai yake shaye shayen sa.
Haule baiwar Allah ita kadai ce take zaune tana bautar Allah dan cikin jikin ta har yai wata tara amman bata taba zuwa awo ba sai fama take yau lafiya gobe babu lafiya.
Duk wannan abun da ake sam Alhaji bai farga ba.
Su Fauziyya yadda suka dirji junan su ko wasu ma’auratan sai haka. A satin da sukai ba abinda bata samu ba na daga dukiya da jin dadi sam bata da matsala duk wanda ya ganta da kamal sai ya zata matar sa ce. Dan daga shi har ita kamilai ne a fuska.
Baba Jummai mahaifiyar su Fauziyya kuwa da tafiyar saudiyya yazo ta fadawa mijin yace Allah kiyaye hanya haka ta tattara kudaden ta ta tafi ba tare da damuwa da ya’yan ta ba.
Tin daga ranar da ya ganta ya farai mata magana ta tafi kullun yana layin su sai dai ko kyallin ta bai kara gani ba amman duk da haka yana layin nasu.
Satin su biyu sannan suka fara shirin dawowa ana jibi zasu dawo take akai mata wani dinki a ake mai da mace budurwa wanda kudi masu yawa Kamal ya biya akai mata. Kwanta daya a asibiti aka sallameta inda suka shirya suka  dawo da abubuwa masu yawan gaske wanda bata taba xaton samun su a rayuwa ba. Duk da da bata son wannan rayuwar amman a yanzu ta fara jin dadin ta amman fa a zuciyar ta dan babu yadda zatayi ne. Kamar yasan da dawowar tata yana daga can nesa da gidan yaga anyi parking da ita ta shiga cikin gidan yaran suka fito suka shigar matasa manya manyan akwati nan ta. Tana shiga dakin su ba kowa dan haka wanka tayi ta kwanta dan ta huta. Sai dare ta dau wanka zata fita kenan aka aiko ayi sallama da ita. A soro ta same shi. Suka gaisa dan ita bata gane shi ba, shine ya fara magana.
“Da farko sunana Muhammad Abubakar ina nan kasan layin kune ina da yar tireda wacce nake dan siye da siyar wa. To ni dai…”
Sai yai shiru dagowa tayi ta kalle shi a karo na biyu dan har ga Allah yai mata kwarjini dogone bashi da jiki yana da hanci da idanu sai dai fuskar sa ba ta da haske amman hannusa da ta kalla sai taga fatar fara tas da ita. Dauke kai tayi daga kallonsa dan ba karamin kwarjini yai mata ba kanta a kasa tace
“Kana bukatar jari ne?”
Kai ya girgiza mata yace
“A’ah Fauziyya ni ke nake so, dan Allah ki taimaka min.”
Murmushi tayi ta kalle shi kamili da shi a ranta tace
“Ina ma fauziyyan dace da yau na samu miji dai dai dani amman yanzu ko na aure ka na cuce ka. Ba zan iya ba.”
STORY CONTINUES BELOW
Dagowa tayi ta kalle shi tai saurin dauke ido dan wani abu taga yana fita a idon sa yana shiga nata. Murmushi yayi ita kuma ta girgiza kai tace
“Dan Allah Muhammad kayi hakuri.”
Tana fadar haka ta shige gida kan gado ta fada ta fashe da kuka ba komai takewa kuka ba sai kanta dan daga Kallo daya taji ta kamu da son sa, ba yadda zatayi saboda in ta yadda ta cuce shi daga gani kamili ne in ta aure shi ta cuce shi sosai. Ina ma bata fada wannan harkar ba da yau ta samu mijin aure amman yanzu ba zata iya ba. Tana wannan halin Farisa da Hafsa suka shigo da yawon su. Akwatunan da suka gani ya sa suka san ta dawo da sauri suka shiga dakin a kan gado suka same ta tana kuka
“Lafiya Anty Fauziyya?”
Suka hada baki suna fada. Bata basu amsa ba dan kuka take sosai. Sai da sukai ta lallashin sannan tai shiru.
“Me ya faru ko kamal ne ya mutu ko bai da lafiya ne?”
Abinda Farisa ta fada kenan. Kai ta girgiza tace
“Hakika Farisa mun cuci kan mu aure ne ya dace da mu ba wannan rayuwar ba. Yau na hadu da wanda nake so da aure sai dai ba zan iya auren sa ba. Ni ba kalar sa bace da kamilar mace ya dace. Mama ta cuce ni ta sa na lalata rayuwa ta yanzu tayaya zan gyara rayuwa ta.”
Wani tsaki Farisa ta saka tace
“Akan haka kike kuka. Tinda kin san rayuwar ki ta lalace menene amfanin yin nadama ai kawai a cigaba da harka.”
Hafsa dai jikin ta yai sanyi dan abinda yar uwar ta fada gaskiya ne dan haka bata ce kala ba. Fariaa ce tace
“Kar ki manta dalilin fadawar mu wannan harkar mahaifin mu ne, da yana kula da mu da hakan ta faru ko so kike kije kiyi aure yanzu baki tanadi komai ba nan gaba rayuwar ya’yan ki ta dawo irin tamu. Kinga Anty Fauziyya ki farka daga baccin da kike ki tashi ki nemi duniya ko dan rayuwar gaba taki da ta ya’yan ki in kuwa ba haka ba kina zaune kamar yadda kike fadin rayuwar ki ta lalace haka ta ya’yan ki zata lalace ko kin fison haka. Kina ganin Anty Samira yanzu da auren ta take bin maza da kibi maza kina da aure ai gwara ki bisu a yanzu. Ki zauna ki karatun ta nutsu kina gani iyayen mu yadda suka tsofa duk dan rashi, Anty Haule kuwa da ba yadda zatai kullum cikin wahala take. Rayuwar gidan nan kadai ta ishe ki tunani Anty Fauziyya.”
Ta fada tana fadin
“ni sai da safe.”
Ta fice. Tana kwadawa Hafsa kira. Kwanciyya tayi ta rasa irin tunanin da zatai gaskiya Farisa ta fada mata amman kuma wata zuciyar na karya tata wata kuma na daura ta akan abinda Farisan ta fada mata. A haka baccin ya dauke ta wanda sai asuba ta tashi.
Muhammad kam da ido ya bita yaji zuciyar sa na bugawa. Allah ya daura masa son Fauziyya duk da yan unguwar na fada masa halin ta amman shi a haka yaji yana son ta kuma zai aure ta. Allah ne ya daura masa son ta kawai. Bai san ta yaadda zai cire ba in har taki shi ga kuma alama nan yana gani kamar zata ki shin. Shin menene dalilin ta nakin sa ko dan bai da kudi ko kuma dan me to? Da haka ya fita ya koma shagon sa ya kasa zaman ma sai gida ya koma gidan da ba kowa sai shi kadai. A dare bai bacci ba da yaga haka ya mike yayo alwala yazo ya nafila kara’a biyu sannan ya koma ya kwanta bayan yai addu’a sosai da ta neman zabin Allah. Bacci barawo ne ya dauke shi.
Washe gari da wani irin ciwon kai ta tashi wanda bata taba yin irin sa ba a zaune tayi sallah walha da take yi. Tana zaune ta mike ta dauko madara ta sha tasha maganin ciwon kai ta sha sannan ta koma bacci ba ita ta tashi ba sai karfe biyu saura. Da sauri ta shige ban daki tai wanka sannan tayi alwala tai sallah ciwon kan ya ragu amman da saura. Tana zaune ta gama shiryawa tai kwalliya wayar ta tai kara dauka tayi tana karawa a kunne. Kamal ne dan haka tai masa sallama wanda bai amsa ba sai cewa da yake hello.
Dan tsaki tayi tace
“Wai kai me yasa baka son amsa sallama ne?”
Dan murmushi yayi yace
“sorry Wa’alaikum salam!”
“Ya kake?”
“Ba lafiya ba, kewar ki jiya sam ta hanani bacci kinsan kwana na biyu rabo na dake amman dan meyasa jiya ma baki zo ba, ina son naji yadda aikin da akai miki yayi.”
Ido ta lumshe tace
“Kamal bana jin dadi wallahi.”
Yar dariya yayi yace
“Ina jin kema kewar tawa ce tai miki yawa, kizo naji me ke damun ki, ko asibiti zamuje.”
“Ok gani nan.”
“Sai kinzo!”
Ya fada yana kashe waya.
Mikewa tayi dogon siket ne a jikin ta sai riga mai dogon hannu da hula a kanta dan haka mayafi ta dauka kawai ta zari waya da kudin mota. Tana fita ta hangi wannan almajirar wajen ta ta karasa tace
“Baba kince kina son magana dani amman sai jiya na dawo.”
“Allah sarki kin dawo lafiya.?”
“Lafiya lou!”
Ta dan yi murnushi tace
“Yarinya shawara zan baki akan *wannan rayuwar* da kika zabawa kanki. A haka kamila ce ke ba wanda zai miki kallon mai yawon banza daga gani kina da addini da nutsuwa waccan rayuwar taki ta baya ita tafi dacewa dake sam *wannan rayuwar* gurguwar rayuwa kika zabawa kan ki. Hakika ina mai baki shawara da ki bar *wannan rayuwar* da kika zabawa kanki. Hakika cutar war da ke cikin ta tafi dadin dake cikin ta yawa, in da babu damuwa kizo muje gida na kiji.”
Ba musu Fauziyya ta bita dan itama jikin ta yai sanyi sosai akan maganar wannan almajirar. Gidan kasa ne wanda duk kasar ma ta zube, gidan duk ya rube abin tausayi. Wata tabarma ta dauko mata ta shimfidda wacce itana duk ta tsofa zama tayi dan Fauziyya bata da kyamkyami. Daki Fauziyya ta shiga ta fito hannun ta rike da wani envelope zama tayi ta mikawa Fauziyya. Amsa Fauziyya tayi, ta bude hoton wata kyakyawar Baby ta gani sanye duk tayi da kananun kaya kai yaci a attach ansha make up.
Dagowa tayi tana kallon almajirar tace
“Wacce wannan? ‘Yar kice?”
Dariya tsohuwar nan tayi tace
“Bani da ‘ya ko daya, nice nan!”
Ido fauziyya ta zaro tana bin ta da kallo
Har tayi arbain bata da shirin komawa. Dan tace ita tafi jin dadin zaman gidan Abba kuma ya zuba musu ido dan yace baza su saka masa hawan jini ba. Da Muhammad yazo ma Hakuri Abba ya bashi yace ya zuba musu ido. Da yaga zata doshi wata hudu a gida ne yace ta hada kayan ta, ta koma dakin ta. Mama tace ba inda zata da taga Abba ya dau zafi dole ta amsa da toh. Amman Mama tace ta hada kayan ta ta tafi gidan Sailuba.
Daga can ma gidan Anty Zainab taje tai sati biyu, da taje taga a daular da suke sai zuciyar ta ta kuma kwadaita mata son kudi. Dan ko bngaren Ummu ya fi gidan auren ta. Ga Ummu na karatu ta kuma wayewa sai ta fara danasin itama karatun tayi ba aure ba. Danasani dai kala kala. A ranta kuwa ta saka ba zata kona gidan Muhammad ba. Da zata tafi Yaa Suleiman ya bata 50k Zainab ta bata 10k da kayan sakawa sababbi nata da na Baby Jannat. Ummu ta bata takalma da jaka. Sannan ta koma gidan sailuba
Muhammad ganin shiru shiru har wajen wata shida ba Rukkaya ne yasa ya tafi gun Abba. Abba yai mamaki dan gani yake ai tafi wata biyu da komawa dakin ta.
Cikin gida ya shiga wajen Mama, yace
“Binta ina Rukayya?”
“Tana gidan ta mana!”
Mama ta bashi amsa.
“Binta bana son rainin hankali ina Rukayya? Ga mijin tanan yazo yace bata koma ba. Ina kika kai ta”
Ganin Abba ya riga yasan bata nan ne tace
“Kaga Alhaji, ana dole ne?  ba’ayi ko? To dan haka Rukayya batayi dan haka ka shaida masa ya saketa in ba haka ba wallahi har kotu sai munje an raba wannnan kaddararen aure.”
Abba cikin mamaki yace
“Abinda kuka zaba kenan?”
“Eh!”
Ta bashi amsa.
“Shikenan Allah ya bada sa’a!”
Ya sa kai ya fita. Mama ta hau mita daman ai shi ya cuci yar ta ya hada ta Muhammad amman ita Zainab ya bata miji mai kudi. Ni kam nace sai kace ba dariya akewa zainab din ba a da.
Abba ya samu Muhammad a daki ya kalle shi yace
“Muhammad kayi hakuri ina son ka hakura da Rukayya ka bani takardar ta, dan yanzu abinda suka fada min ko baka sake taba zasu kai karar ka kotu ba zan mata dole ta koma dakin ta ba dan nasan sam ba zakaji dadin ta ba.”
Kan sa a kasa ya kasa magana Abba yace
“Amman in kaga kana so aje koto ni zan tsayaa maka.”
Kai ya girgiza yace
“A’ah Abbah! Zanyi yadda kace!”
Ya mike yana fadin
“Nagode Allah ya saka da alheri.”
Abba yace
“Zauna kaji!”
Zama yayi Abba yace
“Alhamdulillah. Allah ya sani ina son ka a matsayin siriki na dan haka ba zan so na barka ka bar wannan zuri’ar tawa ba. Alah yaso ina da wata yarinyar in har kan kawon takardar sakin Rukayya ka turo magabatan ka zan baka auen Uwata Ummu!”
Wata faduwar gaba Muhammad yaji  amman ya danne yace
“Nagode Allah saka da alheri.”
Ya mike ya tafi a ransa sam ba zai iya bijirewa bukatar Abba ba.
(Shin me kuke ganin zai faru Muhammad zai auri Ummu kuwa? Need more comment here.)
STORY CONTINUES BELOW
******************************************************************************************************************************************************************************************************************************************************************
Dagowa tayi tana kallon almajirar tace
“Wacce wannan? ‘Yar kice?”
Dariya tsohuwar nan tayi tace
“Bani da ‘ya ko daya, nice nan!”
Zabura Fauziyya tayi. Almajirar nan ta ce
“Da farko sunana Na’ima, ni kadai ce wajen iyaye na. Sunan mahaifina Mal Alhassan da mahaifiyar ta Hadiza. Mahaifi na bai da kudi ko kadan dan yar buga buga yake yi ko dan faskaren itace dashi yake samo mana na abinci duk da haka ya tsaya tsayin daka akan yaga ya inganta rayuwar mu bama tawa wato nayi karatu a halin da muke ya sanya ni a makarantar gwamnati kuma kome aka nema zai nemo ya kai sai dai Mahaifiya ta ita kuma bata da hakuri da dangana dan duk kokarin da mahaifina zaiyi bata taba ganin yana komai duk da bamu da rashin ci wanda ita kullum burin ta taga munyi kudi.
Da farko na riki mahaifina da da akidar sa amman kinsa ‘ya da uwa haka ta dinga zugani har na biyewa abinda take so nan, wanda in mahaifi na ya tura ni makaranta sai tace na buya a gidan kawar ta in ya tafi na fito na dawo ita kuma sai ta daura min talla. Duk da bason tallan nake ba amman fada min da tayi zata na bani kudi in na dawo daga tallan wannan yaja ra’ayina, wanda na fara fita talla ina bin lungu da sako in na fita banyi ciniki ba Baba tai ta zagina a haka har na hadu da wata yar makwabciyar mu da take tallan itama. Muna zaune ta tashi daga inda muke siyar da abincin nace
“Ina zaki?”
Kallon yan gun tayi tace
“In har muna nan bamu fiya ciniki ba, baki ga yadda mukai yawa ba.”
“Haka ne amman ina zaki!”
“Taso muje kiga!”
Nan na bita har muka isa wata yar kasuwa wajen dandazon maza ne wani lungu muka je acan naga taje wajen wani nan suka shiga dan shagon sa ina zaune tafi awa daya sannan ta fito tana gyara rigar ta da zanin ta. Furkar ta dauke da murmushi. Dan haka nace
“Aman kin jima bakya ganin zamuyi kwantai.”
Murmushi tayi tace
“Tsaya kallo.”
Nan wannan mutunin ya fito ya kira almajirai aka juye musu abincin ta sannan ya ninka mata kudin da ta fito da abincin. Abin ya ban mamaki nace nawa fa. Tace
“Zan hada ki da wani Iro duk abinda yace kiyi, kiyi nasan shima zai siye miki.”
Nan na gyada mata kai a haka ta kai ni wajen Iron inda yana gani na ya hau washe baki, anan tace
“Ga wata kawa ta nan sabon hannu ce amman!”
“Kar ki damu.”
ya fada yace
“Ya sunan ki yan mata.”
“Na’ima!”
“Ah lallai sunan ya dace dake.”
Nayi murnushi nan Binto ta fita ta bar mu. Matsowa kusa dani yayi na dan matsa sai yai murmushi yace
“Haba yan mata ba abinda zan miki. Shin Binto bata fada miki ba.”
Kai na noke. Nan ya zaro da kudi daga aljihun sa ya ban dubu daya yace
“Rike wannan nawa ne alalan naki?”
Na kalli bukitin sannan nace
“Dari shida!”
“Zan baki dubu daya shima yayi?”
Nan na washe baki nace
“Eh yayi!”
Nan yaja hannu na yana tabawa tin in nokewa har na sake nan ya farai sumbatar hannu na, iya kar sa haka ya tsaya, yaban kudi na na taho gida. ina kawowa Inna ta kudin ta hau samin albarka bata damu da tambaya ta a ina na siyar ko me ya faru ba. Dan haka ta ban yar dari nayi wanka na shiga gari gun kawaye na.
Washe gari ma haka na tafi can kasuwa a haka kullun zai siye min kayan abincin ya ban kudi ya dauran wani abu akai. A haka har ya fara sumbatata da rumgume ni. Sam Inna na bata damu da sanin halin da nake ciki ba. Dan haka na cigaba dan nima yanzu na gane dadin abun.
STORY CONTINUES BELOW
Mun jima a haka inda ido na ya kara budewa a haka har wata rana ba zan manta tata ba ranar da na rasa mutunci na, anan ya rabani da budurci na, nasha kuka amman da ya daukon dubu biyar sai na nemi zafi da radadin na rasa nan na mike ya kawon magani na sha ya siye abincin ya ban kudin abinci na tafi gida. Sam Inna bata san me ya faru dani ba dan ita ta in kawo mata kudi kawai take. Haka nayi wanka na saka kayana koma na kwanta jiki na na ciwo.
Daga lokacin na zama babbar mai bin maza kowa na samu kulawa nake daga a bani dubu daya sai dubu biyu ko uku. A haka ido na ya bude saboda haduwa ta da wani Alhaji wanda shi ya fara bani dubu goma a rayuwa ta nan nai ta murna har Inna na nunawa inda ta amshe min kudin kuma kwandala bata baniba ba kuma ta tambayen dan me ya ban kudi haka ba. Daga lokacin na daina talla sai dai na fita ina bin maza in samo kudi in na samu dubu biyar nace dubu biyu na samu in na bawa Inna bata ban kwandala. Kuma bata taba tambaya ta a ina nake samu ba.
Allah sarki Baba na bai san me ake ba dan kullun zai ban dari ko hamsin kudin makaranta kuma yai ta tambaya ta ya makarantar nan bai san ba wata makaramta da nake zuwa ba sai bin maza.
A haka na shekara ina wannan harkar ido na ya bude sosai. Na yi kyau da haske dan ina samun kudi sosai ga jiki na na amsar abin da yake samu.
A haka na kwanta wani ciwo saboda zazzabi da nake yi, a ciwon kai mai tsanani sai da na kwana biyar bana fita ga amai da nake yi wannan ya sa Inna tace mu tafi asibiti muna zuwa aka dibi jina da fitsari na aka gwada nan aka ga ciki ne dani har na wata biyu.
Inna ta shiga tashin hankali ni kuwa kuka na dinga yi haka muka koma gida muka samu Baba yana jiran mu. Nan Inna ta fadawa Baba abinda nake dashi a take Baba ya yanke jiki ya fadi daga lokacin aka kai shi asibiti nan ya samu ciwon barin jiki, kwanan sa biyar a asibiti ya rasu dan ance jinin sa ya rufe masa kwakwalwa. Nan muka koma gida akai jana’idar mahaifina.
Bayan bakwai Inna ta kai ni asibiti wai azubar da ciki na nan aka zubar na dawo gida nai jinya. Bayan na warke Inna tace dole na koma talla tinda bata damai bata kudi ni kuma ganin da nayi talla gwara na koma abinda na baro dan haka na koma bin maza na.
Namiji in yana son wani abu a jikin ki ba abinda ba zai miki ba amman daga lokacin da ya gama dake kashi ma yafi ki daraja. Akwai wani Alhj Bilya wanda komawa ta ya amshe ni na zama tamkar matar sa ko wasu mazan ma bana son kulawa shi kada nake mu’amala dasu. A haka muka debe lokaci me tsawo wanda ba abinda baya min sai daga baya ya fara janye jikin sa daga waje na wanda ni kuma sam a ganina shi kadai ya dace dani.
Wata rana naje inda muke haduwa acan na tadda shi da wata yarinya suna masha a nan kishi ya debe ni nayi kanta zan dake ta amman sai cewa yayi in har na dake ta sai ya kira min yan sanda.
“Ke matata ce da zaki hanani kula wasu matan naga kema ba a budurwa na sameki ba a ragowar wasu na samu. Dan haka ki bace min a waje!
Jiki a sanyaye na bar Alh Bilya, wanda da nayi ciwo dan ban zata haka bariki yake ba sai da wata kawata tace a bariki kenan dan haka kar na soma yadda da kowa. kowa ta kama na kula na yaudara sannan nayi gaba. Bariki kenan ba amana bare tausayi a cikinta sai dibar zunubi da danasani a gana. sannu a hankali na fara bin wasu mazan a lokacin kowa ya ganni yasan na zama babbar yarinya sai dai ban kara bari nayi ciki ba saboda ina shan magunguna da allura komai yi nake yi kuma a lokaci daya.
A wannan halin nayi wata tafiya sai da nayi wata uku bana nan ina dawa wa na samu Inna ta ba lafiya da mukaje asibiti mukai ta jinya a haka har ta rasu.
Na hadu da Al amin wanda tinda muka fara harkar bariki yasoni kuma yaso ya aure ni amman sam naki a yanzu na fada miki bana yadda na zauna da mutum daya tin abinda Alhaji yai min sai na zata shima yaudarar zai minama kuma ya nunan da gaske yakenni kuma naki har so nayi na rabu dashi Amman Al amin yadda ya nace min yasa dole nake kula shi duk da nima ya min.
Kuma wani abin shi da kansa yake hada ni da manyan Alhazawa naje na samo kudi dan haka ban da damuwar komai a lokacin duniyata kawai nake ci da tsinke.
Sam rayuwar bariki batai ba. Ina cikin cin duniya ta da cinke na fara wani irin zazzafi sai kuma zubar jini da na dinga yi wanda yasa naje asibiti suna dubani sukace sai an min aiki domin a cire mahaifata saboda yadda nake yi planing ko ta wanne hanya ya sa Mahaifata ta lalace kuma in ba a cire min ba zan ta ciwo ne har ya iya zama ajali na.
*Kamar yadda masu karanta littafi na na _NI DA YAA FAUWAZ_ Sukaga ban hakuri na da uzurin da ya hanani yin rubutu har na tsawon wani lokacin to kuma haka zan baku hakuri da fatan zaku amshi uzuri na. Ba komai ya hanani typing ba sai wayata da ta lallace wanda shi yasa kuka ji shiru duk da nima ba haka naso ba. Dan lokaci na kurewa azumi yana tahowa. Amman zan yi kokari in Allah yasa muna raye zan yi concluding din chapter One din nan ko in summary ne dan in nace zanyi shi yadda ya kanata sai bayan sallah za a cigaba wanda ni kuma in Allah ya kaimu bayan sallahn nake son na daura chapter two. Littafin yanzu aka fara ko rabi ba ai ba dan akwai matsaloli da dama da zan tabo su kuna da nuna darasin dake a ciki insha Allah. In nace zai iya kai mu chapter Five ma kila ya fi. Zan iya cewa kudai cigaba da bibiyar alkami na dan jin mr nake tafe da abinda nake son isar wa. Sai dai kuma muyi fatan Allah ya ara maba lokacin in har mun kai lokacin da rai da lafiya zakuji sauran abubuwan dake ciki da yawa. Ina fatan ayi amfani da darasin dake ciki. Nagode har kullum taku _MARYAM S INDABAWA (ANTTY)_ ke muku fatan alheri da fatan Allah ya kare dukkan musulmai na duniya akan wannan annobar Amin Ya Rabb*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *