WANNAN RAYUWAR CHAPTER 1
*ABINDA YAJA HANKALIN MU WAJEN RUBUTA WANNAN LITTAFIN MAI SUNA _WANNAN RAYUWA💐💐💐_ SAI IRIN RAYUWAR DA MUKA GA TSINCI KAN MU A CIKI, YANZU WATO WANNAN ZAMANIN KO A INA ZAKAJI MAGANAR AKE, DAGA GIDAJEN TV, RADIO, DA ALUMMA. BA AKAN KOMAI BA SAI AKAN MATSALAR DAKE DAMUN MU A WANNAN RAYUWAR TAMU TA YANZU SON ABIN DUNIYA, RASHIN GODIYAR ALLAH, RASHIN HAKURI, ZARGI, RASHIN TAWAKALLI, ZINACE ZINACE, BARACE BARACE, DA DAI SAURANSU. TO WANNAN LITTAFIN NAMU ZAI YI DUBA YAYI BINCIKE AKAN WADAN NAN ABUBUWA DA WASU DA YAWA MA INSHA ALLAH. MUNA FATA DA ADDU’A ALLAH YASA WANNAN RUBUTUN NAMU YAZAMA SILAR SHIRIYAR DA GYARUWAR RAYUWA MUTANE DA YAWA DA SUKE AIKATA MAKAMANCIN WA’DAN NAN ABUBUWAN. AMEEN*
******************************************************
Zaune yaran suke sun kai su goma sha a tsakar gidan, ko wacce ta hada kai da gwiwa yan yaran kuma sai kuka suke, saboda yunwar da suke ji. Uwar gidan su ce ta fito daga bandaki tana kallon su tare da girgiza kai ta rasa yadda zatayi.
Dakin mai gidan ta nufa tare da yin sallama a falon ta samu matar sa ta uku tana jiran ya fito, muryar sa suka jiyo daga bedroom din sa yana fadin
“Kinga Haule ni Bani da kudi yanzu fita nake son nayi na samo kudin, ku kenan kullum abani abani shin wai kudin debowa ake yine ko me? Haba Dan Allah.”
Muryar Haule suka jiyo tana fadin
“Gaskiya Alhaji ni ba zan iya ba, wallahi yunwa nake ji tun jiya fa rabo na da abinci ai ko baka tausaya min ba ka tausayawa abinda ke ciki na.”
Baro ta yayi ya fito falo nan ya samu Samira da Sa’adatu wani kallo ya bisu da shi sannan ya ce
“Lafiya?”
Uwar gidan ce wato Sa’adatu ta ce,
“Alhaji gani mukai har sha daya ba a daura sanwar safe ba ga lokacin na rana na yi…”
STORY CONTINUES BELOW

Bata karasa ba ya katse ta, ta hanyar cewa
“To me zanyi?”
Samira ce ta ce
“Alhaji amman kasan dai kayan abincin duk ya kare ko, ko kwayar hatsi Babu a gidan nan.”
“To uwar ci, yanzu ni ya kike so inyi ne, ni me naci? ita ma waccan ga ta can ta saka ni a gaba yunwa take ji to da wanne zanji ne? Na fada miki Bani da kudi bari na fita naga ko zan samo wani Abu.”
Sun San in har ya saka kafa ya fita to sai dare zai dawo, kuma su a yadda suka San Maigidan nasu bai da rashi Sam sai dai mammakon sa, da aure zai yi zai kashewa yarinya kudi ita da iyayen ta amman da an shigo gidan ba cin yau bare na gobe ba kudin ne bai dashi ba fitar dasu ne bai son yi.
Wanda in ya ajiye kayan abincin a shekara sau daya anci sa’a, kullum sai dai ya jefe su da dari biyar ko bakwa yace suyi girki bayan ya’yan gidan sun doshi su ashirin Dan wasu iyayen su basa gidan. Haka kullum suke fama shiyasa wani lokacin har gwara sun siyo garin kwaki sun sha da suce zasuyi wani abincin Dan kudin shinkafa ma Kadai kudin ba isa zai yi a siyo ba, Dan a wannan zamanin namu yar hausar ma kwano ta doshi dubu daya, to kudin da aka basu ko dubu dayan baya kai wa, wai nan kuma tin safe, rana da dare.
Sa’adatu ce tace
“Toh Alhaji Ko Auwal zan aiko ko garin kwaki ne a amso mana a shagon bulama yaran nan su samu su sha kan a samo abinda za’a girka Dan sai kuka suke mana tin safe.”
Shi kansa yasa ‘Babban Alhaji ne Dan haka Kunya da nauyi yake ji a ganshi yaje yace a bada garin kwaki wannan yasa ya ce,
“Alhaji Imran ya Bani ajiyar wasu kudi bari na dauki aron dari biyar na Baku kuyi girkin.”
“Amman Alhaji kasan dai dari biyar ba abinda zatayi mana a gidan nan ko?”
Samira ta fada.
Juyowa yayi yana kallon ta yana fadin
“To uwar ci, dayake ke runbu ce a ina dari biyar tai muku kada, kuna dai godewa Allah wallahi wani gidan ma kalar dari biyar din ma Saba samun damar ganin ba. Kina ji dai nace ranta zan yi tinda haka ne bari na fita in na samu na aiko muku da shi.”
Sa’adatu ce ta ce
“Kayi hakuri Alhaji bada dari biyar din Allah ya sanya albarka a ciki.”
“A’ah da ku bari mana.”
Ya juya yai cikin dakin. Haule ce ta fito tana tura ciki ta zauna a daya daga cikin kujerun falon tana fadin
“Ina kwana Yaya Babba?”
“Lafiya Lou Haule ya karfin jikin?”
“Alhamdulillahi!”
Ta fada tana dafa cikin Dan ji tayi Dan cikin nata yana zillo Dan shima yunwa yake ji.
Sa’adatu ce ta kalli Samira ta ce
“Kina son ki ja mana a ki bamu dari biyar din da Yaya zamuyi da wadan can yaran dake ta kuka kenan.”
Tsaki tayi tace
“Gaskiya Yaya Babba ni na gama Hajiya da halin Alhaji, kalle mu fa Dan Allah duk mun rame munyi baki ba cima me kyau ba sabulu mai kyau haba Dan Allah.”
Murmushi mai ciwo Yaya Babba tayi ta ce
“Samira kenan, sai hakuri ai.”
“Ina wallahi hakuri na ya kare, ‘ya daya gareni Dan haka ba zan zauna a gidan nan in mutu ba gwara tin wuri nasan inda dare yayi min.”
Yaya Babba da Bata son ko kadan wata a cikin su ta Kara cewa zata tafi Dan tasan kula da wasu ya’yan za’a Kara. bar mata duk da yanzu ma ita ke kula dasu ko iyayen nan.
“A dai ta cigaba da hakurin wata rana sai labari.”
“Kullum haka kike fada Yaya Babba yanzu kusan shekara ta hudu fa a wannan halin.”
Can karkashin gado ya duka ya dauko wani akwati pin ya saka ya bude bandir din kudi ne cire a cikin akwatin, dubu d’aya ya dauko a ciki dan duk yan dubu dayan ne a ciki, rufewa yayi, yayi addu’a sannan ya tottofa a jikin akwatin ya maida karkashin gadon Wanda haka yake yi duk lokacin da zai dauki akwatin.
Falon ya dawo ya tadda su suna maganar su, suna ganin shi sukai shiru, dubu dayan da ya dauko ya mikawa Sa’adatu ai nan da nan Samira ta ce
“Amman ai nice da girki ko?”
“Na Sani amman kar ki manta ita ce uwar gida na wacce take zaune dani duk da babun nan, kuma take rike min ya’yan na Wanda nasan ke da wuya zaman da mukai da ita ki jure mu zauna tare.”
Ya kalli Yaya Babba ya ce
“Ki bawa Auwal ya siyo garin kwano biyu nasan zai ishe ku har dare ko? Watakila har gobe da safe ma, sai a siyo muku siga in kuma kuli kuli zaku siya dai Gashi nan dari biyar na yadda a dauka a ciki Dan na fada muku itama bashi na ciyo.”
Karba Yaya Babba tayi tana fadin
“Allah Kara budi.”
“Ameen!”
Ya fada ya saka kai ya fice.
Bayan sa Yaya Babba tabi a tsakar gida ta tadda Auwal Dan shekara goma sha biyar ta ce
“Auwal zo ka siyo mana garin kwaki kwano biyu sai ka taho da kuli kulin saba’in da gishin ashirin sai a baka canjin dari biyar da tamanin.”
Amsa yayi da gudu yaje ya siyo ya dawo nan da nan Yaya Babba ta hau hadin kwadan Wanda da, daga zallar garin sai dan ‘kuli-‘kulin da kamar ba a saka ba sai dan banzan gishiri kanar yai magana ko arzikin mai bai samu ba haka ta gama ta zubawa yaran a ‘Babban faranti sanna ta zubawa iyayen su hudu kowa nashi, haka yan matan yaran ma ta zuba musu kowa nashi.
Zo kuga yadda ake cin wannan kwadon Wanda daba kuli kuli sai gishiri da kamar zai magana ne a ciki amman ci suke kamar suna cin kaza har da Loma da abincin ya kusan karewa kowa sai ya hau dunbuza a hannun sa Wanda har fada akai aka dau Katon farantin aka kwadawa daya daga cikin yaran akai akam take ta fara ihu Dan wajen har ya kumbura tana ta ihu.
Yaya Babba da ta Zama uwar kowa a gidan ita ta lallashe ta. Yan matan kuwa duk suna daki suna ci sai mita suke su wannan abin kamar suyi amai amman haka suke tura shi Dan in basu ci ba basu San yadda zasu yi ba.
Alhaji Kasim Babban ‘Dan kasuwa ne Wanda yake kasuwanci kala kala, ba abinda baya siyar wa zaiyo order kaya daga waje ya kawo ya siyar wa da yan kasuwa, bayan shagu nan da yake dasu Banda Wanda ya bada haya, haka nan yana da gidaje da ake masa haya sannan yana da filaye da yake siya in sun shekara ya siyar lokacin sun Kara kudi. Alhaji Kasim dai mai kudi ne kuma Allah ya rufa masa asiri.
Sai dai duk wannan abun bai kula da iyalan sa bare ya dauke nauyin su. Tin yana saurayi ya auri Sa’adatu wacce yanzu ya’yan ta shida dasu, tinda sukai aure take shan wahalar sa Dan a lokacin ma ba wani Hali ne dashi sosai ba. Inda da yaga budi yazo masa sai ya fara aure aure.
Wanda in ya tashi aure yan mata masu kyau da jini a jika yake aura a waje zai kashe miki kudi amman da kin shiga gidan sai hakuri bama
aka gama cin amarcin kika fara laulayin ciki. A haka yake wasu da yawa sun fita kuma in zaki fita ba inda zakije masa sa ya’yan sa.
Akwai wata Yarinya da ya aura Hibbatu sunan ta a waje sun sha soyayya inda har ya aure ta bayan ya jika iyayen ta da kudi, gidan ta da ban ya saka ta bayan aure daga kuma ya ce zai hada ta da matan sa da ta tada hankali iyayen ta sukai mata fada tinda tana zaune Lafiya kuma tana ci da sha tai hakuri haka ta hakura aka kai ta gidan sa. sai da tazo gidan taga yadda yan gidan suke jikin ta yai sanyi, Wanda Bata Jima a gidan ba ta fara laulayin ciki sai ya yasar da ita kamar ba ita ce suka sha soyayyar nan ba inda batai kwana kadan ba ya Kara yin wani aure.
Haka ta cigaba da rayuwar a wannan halin har Allah yasa ta sauka Lafiya da taga baza ta iya ba ta sa ya sake ta dole, da kyar ya sake ta dalilin sakin ma Dan ya gano wata ne. Bayan ya sake ta taso ta tafi da yarinyar da ta yaye amman yace tinda ta yaye ta ba inda zata da ita Dan ta ce yana Bata kudin abincin yarinyar har koto akaje amman da yake mai kudi ne har alkalin ya siye haka suka hakura amman hankali ta na kan yar ta dan sai da dana sanin Neman sakin da tayi saboda taga irin rayuwar da yaran gidan ke ci ba kula ba ci bare sutura. Wannan ya tada hankali ta duk ta kasa sakewa. (Shiyasa wani lokacin ba wai sakin ne ba a so ba makomar ya’yan ka wani lokacin da dadi da ba dadi gwara ka zauna ko Dan tarbiyar ya’yan ka.)
STORY CONTINUES BELOW

Babar ta ce daman kullum in ta kawo kuka take lallashin ta da ta dage aka sake ta tazo tana kukan take mata nasiha kamar haka
“Hibba ba wahalar da kike sha nake Jin dadi ba Sam bana Jin dadi amman nasan Alhaji Kasim ba bar miki yar ki zai ba ko Dan kar ace yana bada kudin kayan abincin ta, Wanda ke ganau ce kinga irin rayuwar gidan yanzu Gashi can kin baro yarinya yar shekara biyu gidan da yara suke da yawa ita ma Sa’adatun abun yai mata yawa ita ke kula da ya’yan goma sha da zaman ki kikai da dadi ba dadi kika kula da tarbiyyar ‘yar ki da yafi amman yanzu duk inda kike hankalin ki na kan ‘yar ki sai dai ki dage da mata addu’a Allah ya kiyaye ta ya shirya ta amman nima ina Jin ciwon barin ‘yar kankanuwar yarinyar can addu’a dai zamuyi tayi mata.”
Haka ta hakura ba dan taso ba da yawa matan haka suke barin ya’yan su dawo suna danasi Dan sun San irin rayuwar gidan.
Yanzu a gidan daga Sa’adatu uwar gidan wacce suke Kira da Yaya Babba sai Jummai mai bi mata sune Kadai suke zauna Dan ya’yan su Dan sune masu ya’yan da yawa Sa’adatu ya’yan ta shida sai Jummai mai ya’yan takwas ban da wadan da yake aura daga haihuwa daya su fita wasu biyu wasu uku, ga Samira na da ‘ya daya ga ciki nan a jikin ta Wanda Bata San da zaman sa ba sai amaryar sa Haule da ke da ciki itama haihuwa yau ko gobe.
Duk gidan ba mai Jin dadi duk a kare suke a rame, ba cima bare makwancin mai kyau Sam bai San halin da suke ciki ba. In ance wane ba Lafiya kan ai magana zai janyo wani kwando da yake zuba tarkacen magungunan sa ya dauko duk Wanda Allah yayi ya baryar wani in ansha Allah ya taimaka aji sauki wani kuma asha jinyar in Yaya Babba ta samu taimako ta kai yaron asibiti wani kan haka zai gama jinyar ya hakura.
Yan matan sa sunkai su takwai Dan wadan da zasuyi shekara goma sha tara sun kai su biyu sai yan sha bakwai su uku yan sha biyar su hudu haka abin yake bi da bi. Inda yake da Babban Dan sa Dan shekara ashirin da biyu amman duk ya’yan ba Wanda yaje makaranta Dan da ance kudin PTA sai dai su zauna sai in anja lokacin su koma inda bawani karatun kirki suke samu ba Sam.
Shikan Lawan Babban Dan nasa ya gama secondary school amman har yanzu yaki ya Samar masa makaranta ya karasa, yan matan sa kuwa da yawa an fito ana Neman su da aure yace bai da kudin da zai aurar dasu.
Rayuwar gidan dai sai Wanda ya gani abin tausayi.
Jummai ce zaune ita da Sa’adatu, Sa’adatu tace
“Jummai ni dai na gaji da rayuwar gidan wallahi.”
Nunfashi Jummai taja ta ce
“Haba Yaya Babba keda kike bamu kwarin gwiwa yau ke kike wannan maganar.”
“Ai baki Sani ba wata mafita na samo ne.”
Gyara zama jummai tayi tace
“Wacce mafitar fa?”
“Gani nayi da wannan rayuwar wahalar da muke mai zai hana mu fara fita yawon bara mu da yan matan nan namu kinga daga nan ma na samun na abinci ke har aure mayi wa yan matan tinda dai ba karatun suke ba amman Yaya kika gani.”
“Yaya kina ganin za a dace wannan shawarar taki.”
Jummai ta fada tana kallo ta.
Kai Sa’adatu ta gyada tace
“Ai baki Sani ba wallahi ‘kawata Hanne ita tazo gidan nan jiya take fada min har gida ta siya ana mata haya da kudin bara fa.”
Ido Jumma ta zaro ta ce
“Kai haba dai?”
“Wallahi tallahi haka ta fada min kuma na yadda da maganar ta. Yanzu dai kinga in Alhaji ya fita kan zuwa dare ya dawo ai munje mun samo abinda zamu samo ko ya kika ce.”
Da sauri Jummai tace
“Hakan ma yayi ki mata maganar sai mu fara fita gobe ni da ke yadda mukaga tsarin wajen yaran namu ma sai duk mu shiga gari tare.”
“To shikenan.”
Wani Yaro Dan shekara uku ne ya karaso wajen Yaya Babba yace
“Mama yunwa nake ji.”
“To ishaq ka Kara hakuri bari baban naku ya dawo mu gani.”
Ta janyo shi jikin ta. Dan ita akwai tausayi ba kamar Jummai ba da iya ya’yan ta kawai take rikewa amman Yaya Babba duk wacce ta fita ya’yan gun ta suke to wa.
Washe gari gidan Hanne suka nufa bayan mai gidan ya fita samun ta sukai ta fito rike da ledar ta tana rufe kofar dakin ta, Sa’adatu tace
“A’ah Badai har kin fito ba kace da mun Jima da baza mu same ki ba.”
Hanne tace
“Ke dai bari ai da sauri ake fita.”
Ta fada tana kulle kofar ta gama ta ce
“Ya na ganku ku Kadai.”
“So muke mu fara ganin ya hanyar abin yake.”
Tsaki tayi ta ce
“Ai wallahi da kun taho da ya’yan ku ko da har mazajen aure zasu samu, ke nifa Allah ne yasan manufar jaki da baiyo shi da kaho ba amman da ina da yara ko wacce hanya ce zan daura su Dan su Samar min na kashewa ni ina gida ina hutawa.”
Yaya Babba ta ce
“A’ah ba dai ko wacce hanya ba Hanne.”
Jummai da Bata tanka ba tinda suka fara tafiya ta ce
“Wallahi Yaya Babba indai zamu samu kobo da sisi zan tura ya’yan na, Hanne fada min shin da wata hanya bayan wannan abin ya ishe ni Naga in bamu tashi tsaye ba wallahi zamu mutu mu bar ya’yan mu a bala’i Dan wannan rayuwar ta gidan mu bala’i ce.”
Da irin wadan nan maganganun har suka karasa bakin hanya inda suke zaman.
Zaune yake a kofar shagon sa, wanda yake na provision ne duk da ba wasu kaya ne masu yawa can ba amman akwai kayan ba laifi. Dan dashi yake rufawa kan sa asiri da mahaifiyar sa
+
Kyakyawa ne ajin farko, dan fari ne dogo ga hanci yana da manyan idanu dan gayu dashi mai tsafta. Ba zai wuce shekara ashirin da takwas ba zuwa da tara dan bai kai shekara talatin ba.
Sam ba zaka ce bai dashi ba dan yadda yake cikin gyara da tsafta zai saka kayan sa masu kyau, kuma ya shafa turaren mai dadin kamshi.
Yana karatu anan Federal college of Education Kano yanzu haka sun fito Teaching practics wanda da sun dawo zasuyi second semester sun gama.
Yana daga kofar shagon nasa ya hango su ita da yan uwan ta, yan mata biyu wanda suka girme ta sai ita sai mai bi mata da yayen ta maza biyu suma sai wani karamin su. Wanda kullum suke shigewa ta kofar shagon nasa in zasu isilamiyya ko sun dawo. Dukkan su sanye suke cikin uniform dinsu sky blue karamar cikin su ce sanye da nikaf da safar kafa.
Dukkan su kyawawa ne bafulatanai dasu, wacce yake kalla ta ukun su ce, itama fara ce tas mai kyau da ita. Sam bai da dabi’ar kallon mata, amman inda zai hange su sai ya kalle su, wanda in har ya daura idon sa akan ta sai yaji kirjin sa ya buga, wanda yake rasa nutsuwar su har sai sun bacewa ganin sa sannan zai daina kallon inda suke.
STORY CONTINUES BELOW

Yaran suna da tarbiyya dan sam baka gansu suna fada ba ko suna kula mutane a hanya ba ko kule kulen mazan nan. A nutse zaka gansu sun fito kuma a haka suke komawa gida.
Yanzun ma da kallo ya bisu har suka bacewa ganin sa sannan ya sauke wata ajiyar zuciya tabbas yanzu ya yadda ya kuma gane son yarinyar yake, wacce bai san sunan ta ba amman yasan gidan su dan yar gidan Alhaji Ibrahim ce, dan duk wanda ke unguwar yasan da gidan dan mahaifin su dan boko ne duk da yanzu yai ritaya mutum ne mai ilimi dukka biyun da sanin ya kamata da dadtako da mutunci da tarbiyya dan yan ya’yan sa ma yana kokari akan su sosai ba inda suke zuwa daga makaranta sai makaranta sai kuwa zaman gida. Ba wani mai kudi bane sai dai akwai rufin asiri wanda yanzu yake harkar kasuwanci kuma abin ya amshe shi sosai.
Matansa biyu Hajiya Binta ita ce uwar gida, mahaifinta yana da kudi sosai auren ta da Alhaji Ibrahim ya faru ne dan d’an abokin mahaifin ta ne, ta tsani talaka, sam bata kaunar talaka, dan ko harka da talaka batayi ya’yan ta uku, Sailuba ce babba wacce take yar shekara ashirin da biyu sai Alkasim dan shekara ashirin sai autar ta Rukayya mai shekara goma sha tara.
Sai matar sa ta biyu Hajiya Amina mai hakuri da ilimi dan malama ce tin tana budurwa ta haddace alkur’ani, dan mahaifin ta ma malami ne, haka a fannin boko ma tayi karatun ta zuwa NCE gata da amfani da ilimin ta. Ya’yan hudu Zainab mai shekara ashirin da daya sai Abdullahi mai shekara sha tara sai Ummulkursum mai shekara goma sha bakwai sai Autan ta Ibrahim da suke kira da Khalil wanda shekarar sa goma sha biyar.
Sam ba zaman lafiya a tsakanin su dan Hajiya Binta bata son Hajiya Amina, haka ta daurawa ya’yan ta tsanar su Hajiya Amina, wanda a ciki Rukkaya ce kadai bata da wannan halin ita tana son yan uwan ta. Dan babbar su Sailuba ko gaisar da Hajiya Amina batayi, Rukayya kuwa kamar yar dakin Amina dan kullum tana dakin ta bacci ne kadai ke kaita dakin su duk yadda uwar ta ke fada har ta fara gajiya sai tace ta asirce mata yar ta.
Rukayya da ummulkursum tare suke duk da ta girme mata amman komai tare suke yi, Rukayya na SS 3 ita kuma Ummulkursum tana SS 1, inda Zainab da Sailuba suke university level 300 Abdullah da Kasim kuma suna level 100 sai Kasin dake JSS 3.
Komai na Ummulkursum da Rukayya daya ne, sai dai banbancin halaiya. Dan Ummulkursum ita ta dauko dabi’un mahaifiyar ta, dan haka ita tana da sanyin hali ga hakuri dan ko a isilmiyya ajin su daya da Rukayya dan sun sauke suna maimaici ne kan ayi bikin sauka. Akwai ta da kula da addini dan ko da yaushe cikin hijab da nikaf take har da safa.
Dukkan su yan gidan kamar su daya dan kama suke da mahaifin su wanda yake bafulatani gaba da baya. Haka ma Hajiya Amina ma bafulatana ce, dan haka yaran kyawawa ne sosai sai dai Ummulkursum ta fisu kyau wannan yasa Hajiya Binta ta kara tsanar ta.
Zaman dai sai a hankali ya’yan Hajiya Amina sam basu da hayaniya wanda Ummulkursum duk ta fisu hakuri kullum su Sailuba su ta tsokanar su sai dai su kau da kai. Ga biyayya da sukewa Mama (Hajiya Binta) duk da abinda take musu kullum sune a zage amman sam basa damuwa.
Haka Umma (Hajiya Amina) take basu hakuri a ko da yaushe tare da musu nasiha hadi da nuna musu mai hakuri shike da riba a ko da yaushe. Sosai take fuskantar da su halin rayuwa.
Sailuba tana da saurayin ta da yake son ta, mai kudi ne sosai dan itama halin uwar tane da ita komai da Mama ta dauko. Indai mutum bai kudi ko kallo sa batayi wannan yasa Alhaji Lukman na fitowa tayi na’am da shi dan yadda yake kashe mata kudi da siyan waya da kayan kwalliya ban da turo mata kudi ta account. Duk da uban ta yana yi amman son hada da kwadayi ita da mahaifiyar ta.
Ita kuwa Zainba mijin da yake neman ta ma lecturing yake yana da rufin asiri amman ba kudi ne dashi ba, sai dan kasuwanci da yake yi, wannan yasa su Sailuba suke daukar kan su a masu sa’a saboda wanda yake neman auren ta.
Karfe biyu duk yaran dake gidan sai hada hadar tafiya makaranta suke, Zainab da Ummulkursum sun gama dan Ummulkursum tana cikin saka nikaf din ta Rukayya ta shigo dakin sanye cikin uniform dinta dan itama ta shirya.
“Kun gama mu tafi?”
Rukayya ta tambaya. Anty Zainab tace
“Eh mun gama ina Anty Sailuba?”
“Ta fita yanzu!”
Rukayya ta bada amsa.
“Muyi sauri muje kar tai mana nisa.”
Anty Zainab ta fada tana kwadawa Abdullahi da Khalil kira nan da nan suka fito suka fice su biyar sunawa Mama sallama.
A dan nesa suka hango Sailuba da Alkasim dan haka da sauri suka karasa suka tadda su suka jera a tare sai ka xata a tare suka fito. Dan duk da abin da ke faruwa a tare suke tafiya sai dai su Sailuba in fara shirya suka fito to basa jiran su, amman indai su Anty Zainab ne suka fara shiryawa sai sun tsaya su sun fito sannan suke tafiya.
Kamar kullun yau ma yana zaune a gefen shagon nasa yana sanye da wani yadin yasha guga sai kamshi turare yake kan nan nasa ya sha aski an masa gyaran fuska sai kyan sa ya kara bayyana. Idon sa na kan Rukayya tinda suka karyo kwana har suka gota masa, ya rasa ta inda zai tunkari yarinyar nan. Wata shawara ce ta fado masa wanda nan da nai ya mike yayi cikin shagon sa. Littafi ya dauka ya fara rubuta wasika sai da ya gama sannan ya nannade ya zura a aljihun sa.
Karfe shida saura suka zo zasu wuce ta gaban shagon sa wannan yasa ya kira Khalil, Khalil da sauri ya karasa yana fadin
“Ina yini?”
“Lafiya lou!”
ya amsa. wasikar a ya rubuta ya zaro a aljihun sa ya mikawa Khalil yace
“Ka bawa Antyn ka waccen!”
Ya fada yana nuno masa Rukayya amsa yayi ya tafi gun su. Sannan ya mika mata amsa ta mikawa Ummulkursum tace
“Ajiyw min!”
Amsa tayi ta saka a jakar makarantar su.
Suna shiga gida kowa yayi bangaren su suka cire kaya sannan sukai alwala dan suyi sallah magariba da aka fara kira. Suna zaune akai isha’i dan haka kowa yayi.
Bayan sallah isha’I mahaifin su ya dawo dan haka kowa yaje yai masa sannu da zuwa, inda mai matsala ya fada masa sannan su baro wacce take da girki. Yau Mama ce da girki dan haka ita suka baro kowa yai bangaren Mahaifiyar sa. Rukayya da tasan Mama ce da girki har murna take dan tasan zataje Bangaren su Umma dan in tana nan bata barin ta taje.
Ummulkursum ta sama zaune a dakin su rike da littafin ta na makarantar boko yana dubawa. Ummulkursum ba dai kokari da maida hankali akan karatu ba wannan yasa kowa a gidan ke son ta ba ga iyayen ba baga yayen taba. Zama tayi a gefen ta tace
“Ina abinda na baki ajiya?”
Mikewa tayi ta dauko jakar makarantar ta ta mika mata wasikar. Amsa tayi ta bude ta zubawa rubutun nasa ido sai kace wanda computer ta rubuta dan yadda rubutun yake da kyau da tsari.
Ido ta lumshe da ta fara karanta wasikar sai da yayi sallama ya yabe ta sannan ya miko mata kokon barar ta a gaskiya duk mutum mai hankali bazai ki tayin soyayyar Muhammad ba dan bashi da aibu dan haka take taji ta kamu da sonsa.
Ummulkursum bata san halin da yar uwar ta take ciki ba dan ta dukufa akan karatun ta. Rukayya ce ta mika mata tace
“Karanta kiji!”
Amsa tayi ta karanta sannan ta maida kallon ta kan yayar tata dan taga wane irin yanayi take sai ta ganta cikin farin ciki abinda ya tabbatar mata da ta amshi tayin nasa kenan. Dan haka tace
“Allah ya sanya alheri!”
Rukky ta amsa da
“Ameen!”
Littafin ta ta rufe ta shiga bandakin dakin ta dauro alwala Rukkaya na zaune ta zo ta canja kaya zuwa na bacci ta haye kan gadon. Kallon ta Rukkayya tayi tace
“Ba dai bacci ba? Tin yanzu?”
“To me zanyi Antu Rukky?”
“Kalo mana ko hira!”
“A’ah ni kallon nan ba damuna yayi ba kyale ni nai bacci. Sai da safe!”
Ta fada tana jan bargo.
Mikewa Rukayya tayi ta tafi gun yan uwan ta dake falo suna kallo suna hira har goma tayi kowa yayi makwancin sa.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda soyayya ta kullu tsakanin Rukayya da Muhammad amman fa duk abinda ake a wasika suke yin sa sai dai sun tazo wucewa ya bita da kallo ita kuma kunya ta kasa kallon sa.
A lokacin kuma an sanya ranar auren su Anty sailuba da Anty Zainab Mama sai rawar kai take yar ta zata auri mai kudi dan ta samu labarin wanda zainab zata aura har da murna wai ba mai kudi bane.