MISBAH BOOK 2 CHAPTER 6 BY SA’ADATU WAZIRI

MISBAH BOOK 2 CHAPTER 6 BY SA’ADATU WAZIRI

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Deeni kwanakin baya, asibitin Doctor Mislihu. Ni matarsa ce da muke aiki tare, bayan rasuwar sa ni na ci gaba da kula da asibitin.
Kafin ya rasu burinsa ya ga ya taimaki Deeni, sai dai burin nasabai kai ga cika ba ta Allah ta kasance akan sa. Ina fatan cika masa wannan burin, don haka nake son taimakon Deeni da dukkan kokarina har sai naga ya samu lafiya”.
Ba ma bukatar taimakon ki”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Suka ji muryar Alhaji kamar daga sama.
Dukkansu suka mai da kallon su kanAlhajin, ya ci gaba da fada.
“Yau ce rana ta karshe da zaki sake tako gidan nan, kowa yasan irin yadda ku ka kara

dagula rayuwar Deeni, ku ka yi wasa da lafiyar sa. Ku godewa Allah da ban yi karar ku ba”. Cikin sadda kai da girmamawa Bahijja tace
“Alhaji dukkan mu ba wanda yaso abinda ya faru, kuma bamu yi haka da gangan ba sai don wata kaddara da ta fada mana. Burin mu ne daga ni har marigayi maigidana mu ga muna taimakon mutane, haka taimakon danka yana daya daga cikin burin, don haka nake me rokon ka da ka kara bamu dama, inshaa allah zamu yi kokarin mu akan danka ya samu lafiya”.
Alhaji dai ya dage Bahijja ma ta dage da kyar da kyar ta sha kansa ya yarda, sai dai ta dinga zuwa duba shi har gida. Bata musa masa ba saboda tana son taimaka masa, don tasan an musu laifi, sannan zata karasa abinda mijinta ya fara kamar yadda ya umarce ta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Hajiya ce tayi mata jagora har zuwa bangaren Deeni, ta nuna mata kofar dakinsa. Nan ta cewa Hajiya ta koma ita zata shiga. Hajiya bata musa mata ba ta juya, ita dai addu’ar ta Allah Ya bawa danta lafiya.Tura kofar dakin tayi wanda yake mamaye da duhu, duk da rana ce amma ya rufe ko ina kif, yanayin garin kuma dama in ba a kunna

wuta ko bude (window) ba babu ta inda haske zai shigo. Hakan yasa ta kara bude kofar don taga haske, nan ma ta hango (window) din dakin.
Kai tsaye ta nufi wurin (window) din ta sa hannu ta zuge labulen tare da bude (windows) din dakin duka, tuni haske da wani irin iska mai sanyi ya dinga ratso cikin dakin, nan ta maida kallonta gare shi, yana zaune tsakiyar gado kamar kullum ya hada kai da gwiwa yana kife wuri daya.
Cikin nutsuwa ta matso gare shi ta tsaya tana kallon sa tare da nazarin halin da yake ciki. Kamshin turarenta tare da iska mai sanyi ne suka soma ziyartar sa, wannan ya dawo da shi daga wata duniya da ya fada.
“Assalamu alaikum Nuraddeen”. Ta fada cikin sassanyar murya.
Jin murya da bakon yanayi yasa shi dago kai suka hada ido, tayi masa murmushi, shi dai kallonta yake.Ta sake kiran sunansa, “Nuraddcen, na maka sallama baka amsa ba, kasan kuwa shaidanun mutane ne kawai ba sa amsa sallama? Kai kuma nasan ba ka daya daga cikin su, kai salihi ne, Bawan Allah (you are a gentleman) nasan nan gaba in na shigo zaka amsa sallamata. Ni sunana Doctor Bahijja, amma zaka iya kirana da Bahijja. Ni sabuwar kawarka ce, abokiyar ka, naji baka da aboki haka kake rayuwa kai daya, nima bani da kawa don haka na cewa Hajiya me zai hana mu zama abokan juna ni da kai? Ka fada min damuwar ka in fada maka nawa, mu bawa juna shawara. Ina fata zaka amshi abota ta?”  Www.bankinhausanovels.com.ng
Kallonta yake fuskar sa daure, sannan kuma da alamar mamakin ganinta duk da yana jinta amma bai kulata ba, daga karshe ma ya kau da kai daga gareta saboda Allah Allah yake ta fita ta bashi wuri, saboda ba abinda yafi kauna irin ya zauna shi daya ya fada wata duniya daban wacce take da bambanci da wacce mutane ke
rayuwa. Ganin ya juya kai yasa ta sake zagayawa ta fuskance shi, ta ce.”Hakan na nufin baka amince da abota ta ba? Duk da baka amince da ni ba ni dai ba zan fasa zama abokiyar ka ba, saboda Nuraddeen shi kadai ne abokin da nake son nayi a duniya, saboda daga ji da ganin Nuraddeen (is special).
Zan fara aikina daga yanzu kafin ka amince, shawara ta farko ka dinga barin (fresh air) yana ratsowa cikin dakinka, zai baka (good company) kuma zai kara maka lafiya (it will keep you healthy and cheer you up).
Na biyu ni bana abota da kazamai, wannan dakin da kake zaune cikin kura ga kayan ka a zube, (toilet) dinka datti, kai baka gyara sannan ka hana a gyara maka. To in kana so mu zama abokai sai ka koyi tsabta, kasan mu likitoci bama shiri da kazamai, don haka ka tuna kai abokin likita ne”. Tana maganar tana tattara dakin.
Ba shiri ya dago kai yana kallonta, da ta ishe shi yaji ranshi ya baci, ya mike a zuciye ya fisgi hijab dinta yaja ta har kofa murtuke yake.yace
“Waye abokin ki? Bana son kowa, bana bukatar kowa a rayuwata, bana son kowa, ina so in rayu ni kedai. In kika sake zuwa inda nake zan kashe ki”.
Bata yi mamaki ba, dama ta zaci haka daga gare shi.
Murmushi ta masa, ta ce, “Shi yasa nake son ka zama abokina, zan dawo gobe in Allah Ya kaimu sai ka fada min damuwarka (and yes) bana so in dawo in same ka da kazanta, ka tabbatar da kayi wanka”.wanki
Rufe kofar ya yi da karfi, ta jima tana tsaye tana kallon kofar, yayin da kwakwalwarta ta shiga zarya tana tunanin ta hanyar da zata bullo masa har taja ra’ayinsa.
Alama ta farko ta nuna mata yana cikin fushi da zafi, na biyu kuma kamar yana cikin wani fargaba. Na uku, alama ya nuna ya yanke kauna daga dukkan wani farin ciki da rayuwar duniya. Wannan ya nuna rauninsa akan zahiri.
Ta jima tana nazari kafin ta juya samu Hajiya tana kaiwa da kawowa alanur jiran fitowar ta take, tana ganinta kuwa ta ni wurinta da auri. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Likita yaya kika ganshi?” Bahijja ta ce, “Kwantar da hankalin ki Hajiya, zauna zan miki bayani”.
Ta ce, “Inshaa Allah Deeni zai samu lafiya, zai samu sauki. Sai dai sai na danyi fama da shi, saboda na lura mutum ne me zafin zuciya da zafin rai, sannan yana tattare da wani fishi da ɓacin rai a tare dashi.
Sannan akwai wani (memories) a kwakwalwar sa da yake son shafe su, ya mance da su. Yana so ta shafe wani bangare na rayuwar sa a baya wanda suke masa ciwon gaske. A kokarinsa na wannan yasa kwakwalwar sa ta kamu da ciwo, rashin lafiya. Ba wai hauka ya yi ba, kamar yadda kai, ko zuciya, ko ciki suke yiwa mutum ciwo a jikinsa, haka kwakwalwa ma tana ciwo wanda dole sai ya sha magani zai samu waraka da yardar Allah. Sannan kuma wannan tunanin.
Na biyu, matsayin sa na Musulmi ya samu rauni  na uku na lura yana da matsala da duk wata dangantaka ta duniya wandaya jawo yasa ya tsanikowacce irin dangantaka, har yasa baya kaunar kulla dangantaka kowacce iri ce da kowa, yafiso ya yi ta rayuwa shi daya.Don haka Hajiya Deeni na bukatar taimako kwarai wanda zan yi iya kokarina nayi, sai dai ba mai sauki bane. Mutum ne mai taurin kai da zafin zuciya, tankwara shi ko juya shi abu ne mai wahala. Ina son jin tarihin Deeni kakaf da halilin shigar sa wannan halin, saboda in san ta ina zan soma bi in taimaka masa”.Hajiya ta ja dogon numfashi ta kalleta ido
cike
da tsammani, ta ce.
“Zan fada miki komai, tabbas Deeni danmu ne amma bamu kyauta masa ba, bamu masa adalci ba. Zan baki dukkan wani hadin kai dakika nema domin inga dana cikin walwala.
Deeni mutum ne wanda yake (full of life) kullum yana cikin dariya da zolaya gami da kyautatawa kowa, duk da yana da zafin rai yana da zuciya da fushi da kuma ra’ayi amma yana wuyar gaske ka fahimci haka, saboda kullum yana cikin wasa da dariya.
Duk wani abu da Deeni yake so mu ma shi muke so masa  don haka muka sa shi yin abinda muke so musamman mahaifinsa ya danne abinda yake so yana yin abinda muke so saboda biyayya. Sun sha samun sabani da mahaifinsa akan abu da yawa, amma daga karshe zai hakura yayi abinda mahaifinsa ke so.
Deeni bashi da raunin addini, asali ma sanin Addini yasa shi yi mana biyayya duk da mun fi ba da karfin mu ga neman ilimin duniya shi da kansa ya dage da neman lahira, don haka anan mu muke da rauni ba shi ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya yi amfani da iya ilimin da ya nemawa kansa na addini, yana kokarin neman ilimin ne kuma muka raba masa hankali tare da daga masa hankali akan karatun jami’a, don haka ya watsar ya koma bokon. Raunin Deeni guda daya ne a rayuwa FARIDA”.
Sai a lokacin Bahijja ta ce wani abu tunda ta fara magana, ta ce.
“Farida?”Mama ta gigirza kai, ta ce, “Kwarai Farida, in akwai abinda Deeni yake so a rayuwa da muradi a rayuwar sa to Farida ce. Dukkan ZURI’AR mu ba wanda bai san da haka ba, tun yana yaro har ya girma ya mallaki hankalin kansa, abinda yake so daya ne Farida, ita ce rauninsa…”.A hankali Hajiya ta labarta komai tin daga farko har karshen abinda ya faru.Bahijja taji jikinta ya yi sanyi, ta matukar tausaya masa sosan gaske.
“Allah Sarki bawan Allah”. Ta fada tana kallon Mama.
“Tabbas ba ku kyauta masa ba, mahaifansa, dan uwansa da masoyiyar sa, tabbas wannan cin amana ne mai girma, dole ya ji dukkan wata Dangantaka ta fita ransa.
Tabbas ya yi kokari ma da ya tsaya a haka, Deeni jarumi ne, na jinjina masa, kuma inshaa Allah zan taimaka masa ya fito daga cikin wannan kejin ya zo yayi rayuwar sa kamar kowa.
Saidai Kila da mutuwa Farida tayi zai iya daukar kaddara ya jure, da Farida ce tace Deeni bana sonka wani zan aura zai jure ya hakura, amma wannan abinda ku ka masa ya masa ciwo wanda ciwon da cin amanar shi yafi zama a zuciya da kwakwalwar sa fiye da Farida.
Yana jin cewa iyayensa basa son sa, ba sa kaunar sa, sun ci amanar sa. To in iyayenka za su ki ka su ci amanar ka zaka dinga jin to kai ina zaka shiga? Ya zaka yi da rayuwar ka?Abin da ciwo matuka, zaka iya jure tsana da kiyayyar kowa amma ban da mahaifanka, saboda mahaifanka, ‘yan uwanka su ne kai, su ne rayuwar ka. Www.bankinhausanovels.com.ng

Abin da Deeni yake ji, ciwon da ke cikin cikinsa da ni da ku duk ba zamu iya sani ko fahimta ba sai shi sai Allah Ina fata Allah Ubangiji Ya bashi lafiya, Ya bani iko da taimakon iya taimaka masa, Ya cire masa wannan ciwon da ke zuciyar sa”.
Ta mike, “Ni zan wuce, zan dawo gobe in Allah Ya kaimu. Sannan zan ci gaba da bincike akansa daga gare ku, da fatan za ku bani hadin kai”.
Mama da ke sharar kwalla ta ce, “Inshaa Allah za muyi duk abinda ya kamata, mungode”. Nan suka yi sallama ta fita.
Alhaji dake tsaye yana jinsu hankalinsa ya matukar tashi, tsananin nadama ya kara shigar sa, tausayin dansa ya kama shi. Ya iso falon hankalinsa a tashe, ya kalli Hajiya.
“Ki yafe min abinda na miki, abinda na yiwa danmu ban kara fahimtar illar da na yiwa yara na ba sai yanzu”.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *