WAYA SAN GOBE? CHAPTER A
Zaune take dirshan bisa carfet din dake mamaye da qaton dakin nata,ta tanqwashe qafafunta yayin data tallafe kumatunta da dukka tafin hannunta,lokaciguda kuma ta zubawa food flask din abincin dake gabanta ido,a zahiri idan ka dubeta zakayi tsammanin flask din take kallo sai dai sam ba haka bane zuciyarta da ruhinta sun lula wata duniya ne ta daban,da yunwa ta shigo gidan saidai sam ta kasa sa koda loma guda ta abincin a bakinta,cikin kwanakin tana cikin wani yanayi wanda ta kirashi da jarraba ko musifa dake tunkaro rayuwarta
Wannan ne karo na hudu a rayuwarta da idaniyarta tayi tozali dashi saidai ya zame mata masifa,tun daga ranar da ta dora idonta akansa wani baqon lamari ya ziyarci zuciyarta da gangar jikinta,zata iya kiran lamarin da zazzafan so wanda ya zamto mata tamkar harara a duhu,dalikinta na fadar haka kuwa shine wanda zuciyarta ke budurin a kansa baisan Allah yayi ruwan halittarta ba a doron duniyar subhana,tayi kukan tayi takaicin yadda zuciyarta tayi mata rashin adalci ta hanyar kamuwa da soyayyar wanda batasan koshi waye
ba?,meye sunansa?,a ina yake?,taja doguwar ajiyar zuciya sannan ta jawo flask din ta bude da niyyar taba wanu abu a ciki kota tsira daga fadan umminta,ilai kuwa tana loma ta biyu taji sallamar ummin tana daga tsaye ta dubeta tace”yanzu fadila tun shigowarki kika damemu da zancan jin yinwu amma kusan aqalla awa guda banga wani abun kirki da kika ci ba?,tadan yamutsa fuska tace wlh ummi da yunwar na shigo amma kinga na kasa ci”ummi tace ,haka dai kika iya kullum kamar wata qanqanuwar yarinya sai anyi fama dake akan cin abinci ko?,yayi miki kyau ai kinsan ulcer dai ba gidanku daya ba bare kice idan ta kamaki zata miki sassauci,tayi dan murmushi tace kiyi haquri ummi insha Allahu yanzu zan kawo miki flask din empty,ummin tadan harareta tace ai jikina kunne ne,fadila tadan qumshe dariyar da keson subuce mata,har takai bakin qofa ta juyo tace”af na manta ki shirya yanzun zaki kaini gidan alh salim kwana biyu su shiru muma shiru”tadan sosa kanta dake a tsefe saidai ta tufke shi da band tace anya ummi zan gane ma gidan?,ungo wannan ja’ira cewar ummi da ta watsa mata daquwa yace”nima in banda abbanku yace in tafi dake zaki maku siyayyar kayan make up da da driver zanyi tafiyata”tayi ko saurin miqewa tace yauwa ummi dama jiya nayi masa zancen kayan,tace ato minti goma ki sameni ina falo ina jiranki,ta amsa tana qoqarin shiga toilet dinta dake manne da bedroom din
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Tsaf ta shirya cikin abaya baqa mai sulbi saqar qasar dubai wadda aka mata ado da jajayen dutsina masu sheqi,ta nannade tulin gashinta tayi a cuci dashi sannan tayi rolling da wani dan kyakkyawan jan mayafi,simple make up tayi amma kasancewarta tana da wani sassanyan kyau sai ta fito gwanin sha’awa,ta daura agogo na fata ja sai plate shoe da tasanyawa qafarta mai ja ne mai baqaqen igiyoyi,wayar hannunta kawai ta dauka hade da key din motarta ta sake kallon kanta a madubi,cikin zuciyarta ta qaryata masu cewa abu mai duhu baya giwa baqi kyau,duk da cewa ita din ba baqa bace irin matan nan ne masu launin fata(chaculet colour)wasu kuma suce black beauty,fatarta batayi haske can ba kuma kai tsaye ba zaka kirata baqa ba tamkar irin black american haka yanayinta yake,fadila nada wani irin kyau mai sanyi wanda tashin farko bazaka gama tantance kyawunta sai kuna tare wato qananun kyau ne da ita,ba abu mafi daukan hankali a tare da ita irin qirar jikinta cocacola shape,idanunta manya masu dauke da gazar gazar din gashi wanda hakan ke taka muhimmiyar rawa gun tafiya da zuciya gami da ruhin mazaje da dama,goshinta kam irin qananun Gashinnan ne kwance luf wanda ko tayi dauri basu boyuwa,muryarta a sanyaye take cike da wani sirri wanda idan tayi magana take janye hankalin jama’a da dama,fadila tako ina Allah ya bata zubi da tsari wanda yasanya take burge mutane ba maza kawai ba hatta ga yan uwanta mata ma,sai dai gwanar miskilanci ce,sam magana bata dameta ba,tafi ganewa tayi karance karance maimakon zaman tadi,fadila yanzu haka daliba ce a jami’a bayero kano tana karantar mass com,duk da cewa abbanta yayi mata sha’awar karantar medicine ganin cewa mass com bana mutum ne mara son magana ba amma data nuna masa tafi sha’awar mass com din sai ya barta da zabinta kasancewarsa mutum ne mai sauqin kai,sai ya maida zabin nasa kan ‘yar uwarta farida,alh abbas ahmad shine mahaifin fadila dan kasuwane mai rufin asiri,domin Allah ya bashi wadata irin wanda ko wane dan adam ke fatan samu ba abunda aka nema a gidansa a ka rasa,asalinsa bafulatanin bauchi ne,yana sana’ar sai da shaddodi da yadiddika cikin kasuwar kwari,yakan tura babban dansa wasu lokutan china ko india domin shigo da kayan su kuma zuzzuba a shagunansu dake cikin kasuwar,ya auri mahaifiyarsu haj amina a maiduguri cikakkiyar shuwa ce wadda Allah ya qaddari aurensu tun bayan da yayiwa manemanta dintinkau a zuciyarta,anan garin kano suka ci gaba da zama tunda anan kasuwancin nasa yake,haihuwar farko suka sami da namiji inda yaci sunan ahmad,baiyi wani tsawon rai ba Allah ya karbi abinsa,shekara daya tsakani suka sake samun wani yaron aka mayar masa da sunan ahmad din,daganan haihuwar tayi musu dif tamkar aun daina,wanda a tsakanin har amina ta soma fuskantar qananun maganganu irin na dangin miji duk da cewar ba a kusa suke ba,sai bayan shekaru goma Allah ya sake qaddara musu samun wata haihuwar,ta haifi ‘yar kyakkyawar budurwa taci sunan fadila,shekara biyu tsakani Allah ya sake kawo wani rabon nan ma mace ta haifa aka sa mata farida,kasancewar fadila mara saurin girma sai suka taso kai daya da farida idan ka gansu zakayi tsammanin twince ne don kamarsu daya saidai farida tafi fadila garin jiki da kuma farar fata,tasowarsu tare yasanya komai daya ake musu hatta makaranta tare aka sanya su,sai da suka shiga jami’a ban bancin course ya raba su,shekara shidda da haihuwarsu umminsu ta sake haihuwar da namiji inda aka sa masa muhammad tun daga lokacin kuma haihuwar ta musu bankwana
Babban wansu ya ahmad yayi aure tuni da matarsa anty hafiza harsun samu albarkar twince duka mata ,rayuwar gidan rayuwa ce mai ban sha’awa cike take da son junansu suka taso girmama juna da qaunar juna,sai dai tsakanin fadila da farida akwai tsokana fada da wasa na tsakanin sakuwa da sakuwa sai dai duk da haka farida na respecting din fadila
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
S.A huguma
[10/16, 12:18 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Wa yasan gobe?
Safiya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶2⃣
Sun fito kenan daga gidan farida ta shigo da motarta layin (da yake ya ahmad yayi qoqari bayan kammala secondry sanda suka samu admission a jami’a ya sai masu yan qananan motoci rio,yace tunda fadila baqace ta dauki fara farida kuma ta dauki marun)farida ce ta soma jan burki ta tsaya don tasan halin mutuniyar zata iya shigewarta tace”ummi ina zaku je?” “Gidan alh salim kwana biyu haduwa tayi wuya shine zanje dubasu”cikin tsokana ta kalli fadila tace “wlh ummi gwara da kika banbaro kifin rijiyar nan kika fito da ita inaga tafi shekara dubu bata je gidan uncle abba ba”fadila ta watsa mata harara tace”ni sa’arki ce”ta qyal qyale da dariya tace sorry yaya fadila”fadila tayi saurin yiwa motar key suka wuce,suna tafiya a hanya suna hira jefi jefi da ummi abinsu gwanin sha’awa har suka isa gidan,gidan na jerin gidajen kundila housing estate dake maiduguri road,gidane irin na masu naira da suka ci suka tada kai,mai kula da qofa ya dage masu wakeken get din gidan cikin fara’a suka shige kasancewar akwai sanayya mai yawa tsakaninsa da ummin
Ummi ce a gaba fadila na binta a baya har suka isa tafkeken falon gidan ,haj maimuna na zaune bisa luntsuma luntsuman kujerun dake kewaye da falon kallo suke ita da yaranta sumayy da rabi’ah,sallamar su ita ta dauki hankalin su suka juyo hade da amsa musu,haj maimuna ta miqe cikin girmamawa tana cewa lale marhabin haj kune tafe da yammarnan ,ummi tayi murmushi tace ai kuwa dai kam”ta sake fadada fara’arta tace sannunku da zuwa ai……,maganar haj ta katse ta kama baki tace”a’ah yarannan yau yaushene?,ta fadi tana kallon fadila,dukkansu sun fahimci me take nufi suka qyal qyale da dariya suka ce momi yau laraba,ta gyada kai tana cewa lallai ba shakka ta bawa ranar samu,wlh haj bazan iya lissafa yaushe rabon fadila da gidannan ba,”ummi tace”hmmmm to wlh yauma da qyar na banbarota don taji zamu biya store ne zata kwaso kayan make up shine ma qarfin biyonin”momi ta sake gyada kai cike da mamaki tace lallai yau mun tashi da bismillah haj ku zauna mun tsaya zance na barku a tsaye,dukkansu suka zauna sannan suka fara gaisawa fadila ta gaida momi a kunyace ,ta amsa mata tana cewa”kyaji kunya mana mara zumunci ,sam farida ta fiki zumunci “sumayya dake kusan sa’a ga farida tace”wlh anty fadila faridammu ta fiki zumunci”fadila ta dan harareta da taga idonsu ummi baya kansu tace”ta dai fini qafar yawo yaufa sai da zamu fita ta dawo tun azahar wai ta tafi gidan qawarta “sumayya tace “to ai zumunci taje”fadila ta dan tabe baki tace”ke ni qyaleni yawon farida yafi qarfin qafata ko ina a kano kika kwatanta mata ta sani “sumayya da rabi’ah sukai dariya suka ce “kai anty don dai ke bakison fitarne shi yasa kikace sister ta fiya yawo”
Hira suke suka tsinci qanqanuwar muryar yarinyar na sallama ,ta saki hannun wanda ya riqota da gudu ta fado falon,momi ta cewa wanda ya kawota din sannu isah,yace yawwa haj ya juya ya fice,rabi’ah tace oyoyo ifti na,muga kitson,da gudu ta fada cinyarta ta janye hular da ka rufe mata kanta da ita tana nuna mata,kalbace mai kyau twisting wadda aka lafe jelar ta da beads masu kyau,kasancewar yarinyar nada tsawon gashi sai ta kwanta lub tayi kyau har dokin wuyanta,tace anty sumy tayi kyau”sumayya tace gsky qawata ba magana “ta bata hannu suka tafa,ta miqe tayi gun momi ganin ummi yasata duqawa ta gaidata,ummi ta amsa fuskarta dauke da fara’a momi tace”har yanzu fushi ake kenan da ni shi yasa ni baza’a nuna min kitson ba”cikin magana irin tq shagwababbun yara tace “ba cewa kikayi ayimin mai zafi ba”sai kuma ta juya ta koma gunsu sumayya tana bata lbr,ummi ta kalli momy tace”wai iftihal din Aliyu ce wannan?”momi dake tsiyayawa ummi lemo a cup tace”itace mana kinga yadda ta girma ko?”ummi ta jinjina kai tace”ba shakka gata nan kuwa masha Allah,ina zaton ai ba zata wuce shekara bakwai ba ko?”momi tace “idan watan nan ya mutu sabon wata ya kama yakai ashirin zata cika shida”,sai bayan sunyi magariba suka fito,tuni iftihal ta maqale wa fadila domin cikin qanqanin lokaci suka saba,don fadila ba daga baya ba gun son yara,bare iftihal yarinya ce kyakkyawa ga wayon tsiya,har bakin mota suka rakosu sumayya na yaba kyawun motocin nasu,fadila tace idan kina so ki amsa mana,sumayya ta kama baki tace rufamin asiri kada kisa yaya aliyu ya babbalani kina ganin abba zai sai mana ma ya hana wai har yanzu bamu da hankali sai randa muka qara nutsuwa?fadila tayi dariya tace “sai kace yau aka haifeku””kema dai kya fada sister cewar rabi’ah,dai dai nan ummi da momi suka qaraso momi ta miqawa fadila baqar leda tace”to ga kayan kwalliyarnan aje ayi tayi ana samo mana sueukai”a kunyace ta amsa tana mata Godiya,momin tace to sai wata shekarar kenan,fadila ta sadda kai qasa tace”a’ah momi insha Allahu zaku dinga ganina”Allah yasa inji momi,ummi tace”wai ni kuwa ina Aliyu ne,na kwana biyu rabon da na ganshi fa”fuskar momi ta canza zuwa yanayin damuwa tace”hmmmm,mtsw,ke dai bari kawai haj kwanan nan zaki jiyomu da shi,Aliyyu fir ya guji aure yaqi fidda mace yayi aure,yafi ganewa kasuwancinsa kawai nayi har na gaji hakanan abbansa kullum zancen kenan amma yaron nan sam yaqi mai dakansa”ummi tace”addu’a kawai zaku ci gaba da yi masa Allah ya kawo ta gari kada a kuma komawa ‘yar gidan jiya a bata goma daya bata gyaru ba”momi ta gyada kai tace hakane,Allah ya zaba mana abinda yafi alkhairi”tace amin
Daqyar iftihal ta rabu da fadila harsai da ta laluba cikin motarta ta samo mata chaculet sannan ta yarda ta barsu suka tafi,basu tsaya ako ina ba sai a shop rite dake ado bayero mall,ta nufi parking space ta gyara tsayuwar motarta sannan ta kashe,ummi ta zaro kudi cikin jakarta ta miqa mata,tace maza kiyi da jiki ki fito”tasa hannu biyu ta amshi kudin tana qoqarin maida murdin motar ta rufe ne ummi tace”saura ki kwaso kayan zaqi da sanyi ki koma gida ki guji maqiyin naki abinci”tayi murmushi kawai tace baza’a siyo ba ummi ta rufe motar ta shige,cikin nutsuwa take daukar musu abinda tasan suna da buqatarsa ita da farida har ta kammala,har zata nufi kanta ta tuna bata dauki turarenta ba blue lady,cikin sauri ta koma,hankalinta yatafi ga turarurrukan tamkar ance ta kalli gefanta,tsaye yake shima yana zaban nasa kalan,yana sanye cikin shadda dinkin tazarce blue Black ce ta haska farar fatarsa matuqa,ta gefan tana iya hango qaya taccen sajensa dake kwance luf bisa tsararriyar fuskarsa,ga tsinin hancinsa nan yayi das qasan farin qal din glass dake bisa fuskarsa,kyakkyawan idonsa wanda gashin idon suka yiwa rumfa suna juyawa cikin farin glass din nasa yan karanta rubutun dake jikin kwalin turaren,kansa ba hula sai sumarsa dake kwance an dan saisayeta,ya zari turaren kwali uku cikin sassarfa ya juya yabar gun,samun kanta tayi da bin bayansa zuwa inda zai biya kudinsa ,kusan tare suka biya sai dai sam shi bai lura da ita ba ya juya ya fita ta sake bin bayansa,tafiyansa ma abar kallo ce tamkar wani saraki haka yake takawa,daga nesa tadan tsaya a harabar adana motocin don batason ya ganta,cikin aljihunsa yasa hannu ya zaro key ya bude wata baqa sidiq din mota qirar range rover ya shiga yayi mata key ya jata da gudu ya bar gun,jan ajiyar zuciya tayi gamida lumshe idonta hadi da dafe goshinta da tafin hannunta”inna lillahi wa inna ilaihir raji’un allahumma ajirni fi musi bati wa akhlifni khairan minha”abunda take ta nanatawa kenan,wannan wace iriyar musibace zuciyarta ke son jefata ba gaira ba dalili?,ta bude idonta ahankali jikinta ba laka ta soma lalubar inda tayi parking
Cikin motar tayi dif zugi da radadi take ji,ba abunda zuciyarta keyi sai zillo cike da dimbin qaunarsa,shi wa?,ita kanta bata sanshi ba,ummi nata mata hira tana cijewa tana amsa mata har suka isa gida,farida na falo ta baje kolin takardu da alama assignment takeyi,batason ta dameta da hira don haka tadan daure fuska,itama faridan data fuskanci hakan bata ce mata komai ba illa sannu da zuwa ya kuka barosu?,ta amsa mata ta haura sama inda dakinsu ita da farida yake,ta watsa siyayyar tasu kan gado zuciyarta cunkushe ta cire kayan jikinta ta fada toilet da niyyar sakarwa kanta ruwa ko zataji sanyin zuciyarta
Muje zuwa
S.A.M huguma✍🏻
[10/16, 12:19 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
WA YASAN GOBE?
▶3
SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Lotion kawai ta shafa bayan ta fito ta feshe jikinta da body spray ta lalubi rigar bacci doguwa har qaurinta ta zura don bacci take da muradin yi, ta daura zani a sama ta sanya hijabin sallarta ta gabatar da sallar isha’i, ta dora da shafa’i da wutiri, bayan ta shafa addu’o’inta tabi lafiyar gado, a maimakon bacci yazo mata sai tunani ya mamaye gurbinsa, ba zato ta tsinci kanta da zubarwa kanta da kanta hawaye na tsananin tausayin kanta, a cikin jikinta da zuciyarta take jin ta shiga halin tsaka mai wuya, zuciyarta na bulayi da lalube cikin duhun son wanda bai ma san tana yi ba, farida ta shigo dakin hade da sallama hakan ya sanyata saka hannu tana goge hawayen cikin dabara don bata son faridan ta gani, faridan tadan kalleta jikinta yaso ya bata tamkar yar uwarta na cikin damuwa, don haka jikinta sai ya danyi sanyi ta shigo ne da niyyar tsokana don flask guda ummi ta ciko da abinci tace kada ta sauko da shi sai ta cinye Farida ta ajjiye flask din a gefan gadon ta janyo dressing chair ta zauna tana fuskantar fadilan tace”sister lafiya naga kamar fuskarki ta nuna kamar kina cikin damuwa? ,ta qaqalo murmushi sannan tace”ba abunda ke damuna just na gajine fitar nan da nayi”farida ta girgiza kai ba don ta yarda ba tace”ok,to ga abincin ki nan ,ummi tace ” kada ki sauko mata da shi sai kin cinye tana daga kwancen ta zubawa flask din ido tace”har gabana ya fadi wlh, ina zan kai wannan abincin? ,farida ta qyalqyale da dariya tace”ni dai yar aikece kuma na isar da saqo,qafafunta tayi saman tiles din daya mamaye da qaton dakin nata
Ta daura zani a sama ta sanya hijabin sallarta ta zari flask din, farida ta kalleta tace ” a’ah ina zuwa? “Ba tare data kalleta ba ta juya tana shirin fita sannan tace”jirani ina zuwa”farida ta bita da kallo tana dariya ciki ciki ,ta qofar baya fadila ta fita ta bulla bakin get din gidan,kai tsaye ta nufi gun idi mai gadinsu, mutuminta ne dama da hangota kuwa ya miqe yana cewa ” uwar dakina”miqa masa flask din tayi tace”yi sauri ka juye idi”cikin qanqanin lokaci kuwa ya juye abincin ya bata flask din yana zuba godiya Ta tarar da fadila na waya da alama da saurayinta take, ta koma gefan gadon ta zauna tana kallon faridan har ta kammala tsaki fadilan tayi, farida tayi murmushi tana kallon flask din da fadila ta dawo dashi don tasan kwanan zancan, bata son idan zatayi waya tayi mata a dakinta,fadila ta harareta tace”bana gaya miki ki daina shigomin daki idan zaki shirmen wayarki ba? ,tace tana gyara kwanciyarta akan sofa qwaya daya dake dakin ” sorry anty na”tana dan murmushi tace kiyi haquri
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Tun bakwai na safe take a kitchen dama haka al’adarta take, idan bata da lecture to Itace mai shirya musu breakfast haka da rana ko da daddare,girki yana daya daga cikin hobby dinta hakan ya sanya ta zama gwana ta fannin abubuwan ci da na sha,
Awa daya da rabi ta kammala komai ta koma dakinta tayi wanka ta shirya kasancewar tara da rabi tana da lacture,dakin ummi ta shiga bata nan sai muhammad ta tarar yana kan gadonta yana bacci,dala masa duka tayi tace”tashi malalacin banza eight thirty amma kana bacci ina school din?”cikin magagin bacci yake murza ido yace”wlh nayi wanka bacci ne ya daukeni”tace”oya tashi ka shirya idan zan wuce na sauke ka na baka eight minute”da sauri kuwa ya duro daga kan gadon ya shige toilet
Bangaren abbansu ta wuce tare da diba masa breakfast dinsa ta tafi masa da shi,yana zaune kan kafet din falon hannunsa dauke da jaridar daily trust,haka yake a al’adarsa bayan ya dawo a masallaci yakan yi azkar da tilawar qur’ani idan gari ya dan sha kuma sai ya karanta jarida kafin ya fita aiki,fadila ta shigo da sallama, ya masa yana dubanta fuskarsa dauke da murmushi,ta dire kayan abincin ta rusuna tana gaidashi ya amsa yana fadada fara’ar shi yace”sannu fadila da qoqari hala yauma anada da lacture din safen”kanta a sunkuye tana qoqarin hada masa kunun shinkafa da yasha madara tace”eh Abba”,ummi ce ta fito daga bedroom din Abban hannunta dauke da doster da alama goge goge ta gama,fadila ta gaidata tana qoqarin tashi tace”abba zan tafi”ya dubeta sannan yace”ai banga kin ci komai ba haka zaki tafi?””abba zan karya a capteria idan na……….
Ummi tayi saurin katse ta da cewa”yi mana shiru wlh abbansu idan taje ma bacin take ba farida ai ta gaya min wai ba zata iya cin abinci a waje ba,wannan yarinya na rasa meke damunki anya lafiyarki qalau kuwa?”,abban yayi murmushi yana dakatar da ita”dakata umminsu,fadila lafiyar ta qalau,kin manta yawon asibitin da muka dinga yi da ita tun tana qarama?,haka dai halittarta take”ya juya ga fadila yana tura mata cup din da ta hada masa kunun yace”maza zauna kici wani abu kada ki qara bata ran umminki kinji ko?”tamkar zata sa kuka😟 ta zauna tana cewa”to abba”yaci gaba da cewa”gashinan fadila tafiki abin arziqi shi yasa ta rainaki tana ganin kanku daya,ummin tace sai rawar kai da gwanintar yin girkin amma saidai wasu su ci mata,abban yayi murmushi yana kallon yadda take tura abincin kamar magani😣
Kafin ta kammala muhammad ya shigo don haka abban ya sallamesu suka fita tare,suna mota muhammad ya dameta da surutu,ta daga masa hannu ✋🏻hadi da cewa kaga malam bafa aku na dauko ba🐔idan kuma kai aku ne ka gayan”ya qyalqyale da dariya😂 yace”anty ke dai ba dama mutum yayi hira dake sai kice ya dameki shi yasa yaya farida ke burgeni ke halin ya ahmad kikayo kun fiya kwafsawa wlh,ta harareshi sannan tace”ai da itan da kai duk zamuce ta tadda mujemu idan mutum baiyi surutu ba baya burgeku,kada Allah yasa mu burgekun muyita kwafsawar,idan ka qara magana kuma sai na saukeka anan” take ya rufawa kansa asiri yayi shiru🤐
Taso makara saboda ajiye muhammad da tayi don ita ta saba da wuri take zuwa don ta samu sit din gaba,bata da wata qawa bare ta tarar mata hakan ya jawo batayi parking din motar ta daidai ba ta nufi ajin cikin sauri
Lacture din ta daukesu awa uku har da mintina,kanta ya dauki chargy sosai,don haka da fitowarta ta samu wani guri dake nesa kadan da ajinsu bashi da yalwar jama’a sosai yafi kusa da inda suke ajjiye motocinsu idan sunzo,gurine mai wadatar shuke shuke ita kuwa ma’abociyar son tsirrai ce
[8/8, 3:24 PM] LOADING……
gun na burgeta saboda son tsirran da take dashi,tamkar a cikin iska ta ke jiyo qamshinsa,gabanta ya tsananta faduwa,ta gefan ta ya wuce saidai bayansa kawai take iya gani,ahigar suit ne a jikinsa masu dan karen kyau da sheqi,kayan baqaqene sai tsintsiyar hannunsa da ta gani wadda yake daure da agogon fata baqi,gefansa wani ne ke biye da shi riqe da takardu da brief case,sam sai ta kasa dauke idanunta daga kanshi👀,hakanan gabanta yaci gaba da faduwa cikin zuciyarta take fadin inna lillahi wa inna ilaihir raji’un”har ya danyi nesa da ita sai taga ya waiwayo,cikin wani irin sauri ta dauke kanta tayi wani sashen da shi zuciyarta kamar ta tsinke ta fado,ganin yayi gaba tayi hamdala da Allah yasa bai lura da ita ba,tana tsammanin jikinsa ne ya bashi ana kallonsa👀,a sace taci gaba da kallonsa har ya bacewa ganinta,taja ajiyar zuciya sannan ta dauke idonta daga kallon hanyar ta jawo jakarta ta zuge ta fiddo da wayarta tana danne danne,ta doshi kusan minti aahirin a gunbtana hutawa sai sannan ta tuna zata fa gidan ya ahmad,da sauri ta miqe tana gyara yafen gyalenta,atamfa ce ajikinta dinkin riga da skirt ne,atamfar England ce dark green mai ratsin yellow,sai mayafinta da takalminta agogo da jakar hannu duk yellow,fadila ba qarya ta iya daukan wanka don duk munin atamfa takai aka mata dinki ya saka komai kushe da hassadarka baka isa kace batayi kyauba haka Allah ya bata wannan baiwar,tana tattare komatsanta tana sanyawa a jaka taji ana kwada mata kira,a nutse ta dago tana neman daga ina wannan kiran mafarautan ke fitowa?,wata class mate dinta ce binta auwal fadila taci gaba da binta da kallo har ta qaraso,”fadila abbas yaufa kinyi tabargaza”abinda ta soma cewa kenan,fadila tace”kamar ya fa?”tana dubanta tace kinyi wrong parking kin toshewa A.s mai tama hanya”ta sake dubanta cikin rashin fahimta tace”waye haka kika bi kika rude?’binta ta zaro ido😳 tace”kar dai kice min baki san a.s mai tama ba,hadadden guy din da duk nigeria bama kano ba ansan da zamansa”fadila ta dakatar da ita ta hanyar cewa”na gode”taci gaba da mayar da kayanta jaka
Iya dube dubenta ba wanda ta gani sai mutum daya👀,a tsammaninta idanunta ke mata gizo,sai dai har ta qaraso gun shi din dai ta gani,yana tsaye hannayensa harde a qirjinsa fuskarnan a murtuke,ta qaraso ne da niyyar bashi haquri sai dai lura da irin kallon qasqancin da yake mata mata yasa tayi banza da shi kai tsaye ta nufi motarta ta bude,ta zauna a seat din tana qoqarin jan murfin ta rufe taji an dafe murfin motar,ta dago ta dubeshi,yana tsaye yana mata irin kallon dazun,cikin qasaita taji yace”baki da ladabin bada haquri ga wanda kika aikatawa laifi?”duk da yadda zuciyarta ke sake ninqaya a zuciyarta,muryarsa mai sanyi ta kwanta a zuciyarta,amma ta dake gami da cewa cikin zuciyarta”duk da dumbin qaunar da nakeji taka a zuciyata hakan bazai sa na bada girma da jan aji irin na ‘ya’ya mata,ta dauke kanta sannan tace”ai shi wanda akawa laifin baisan darajar bil’adama ba”ya saki murfin motar hadi da watsa hannayensa yace”ok,ba laifi”ya saki murfin motar,cikin wata iriyar gaggawa taga ya amshi key din tasa motar daga hannun wanda suke tare ya bude motar sa ya shiga cikin gwaninta ya take motar ya kurda ya matse motar fadilan ta yadda itama bata isa ta fita ba harsai da ya gogeta,ya kashe motar ya zare maqullin ya rufe motar ya fito yana cilla maqullan yana cafe wa ya danyi tsalle ya haye bayan motar ya zauna,da hannu ya kirashi yadan yi masa rada ya amshi tak ardun hannayensa shi kuma ya juya da sauri ya bar gun
Sarai fadila ta fahimci abunda yake nufi saboda haka ta zaro wayarta ta nemi number farida ta kirata”hello farida kin shigo school?”tace”eh ya akayi?””kizo ina parking space ki daukeni mu wuce”farida tace”me ya sami motar ki?””kinga idan zaki zo kawai kizo malama””ok sister gani nan”
Cikin ‘yan mintina sai ga farida horn tayi mata ta miqe ta fito ta kulle motar ta gabansa ta shige ta nufi farida,dai dai lokacin ta jiyo saukowarsa daga bayan motar,wata yar qaramar mota ce tayi parking a gabansa kusan tare suka shige motocin,ta madubin motar farida suka hada ido ta sakar masa tsaki hadi da murguda baki,cikin zafin nama ya balle murfin motar ya fito da sauri tacewa farida”yi sauri ki bar gurinnan,tamkar kuwa tasan meke faruwa ta figi motar ta bar gun
Muje zuwa
[10/16, 12:21 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Wa yasan gobe?
Safiya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶4⃣
Sai da motar ta saitu akan titi sannan tace mata”gidan ya ahmad fa zamu”ok” inji farida,”sister wai me ya faru naga kamar wadda aka biyo a guje?”taja tsaki tace”wani dan rainin hankali ne yaso wulaqantani bai san bana daukan wulaqanci ba”ta bata lbr yadda sukayi da shi akan toshe ma juna hanya da sukayi,me farida kuwa zatayi idan ba dariya ba,”kefa ‘yar wulaqanci ce shi yasa ban fiya saki cikin lamarina ba,a yar madaidaiciyar harabar gidan sukayi parking,kai tsaye suka nufi falon gidan,ba kowa cikin falon da alama matar gidan na ciki don haka suka dinga kwada sallama,daga kitchen matar gidan ta fito anty hafiza kenan kyakkyawar bafullatana,tana ganinsu ta saki fara’a😊 cikin barkwanci tace”lallai yau baquntar tamu ce”suka saki dariya😀dukkaninsu suka gaidata cikin girmamawa ta amsa musu cikin kulawa tana tana tambayarsu ummi,suka ce tana lpy tana gaidata,fadila ta zaro packet na chaculet tace gashi injita a baiwa twince,wai ni ina suke nema anty?””tace yau ai ranar school ne suna can amma suna hanya don bala ya tafi dauko su,””na manta wlh”ta fada tana qoqarin kwanciya bisa doguwar kujera”anty hafiza tace”ah ya haka ina murna kuku tazo kuma naga tana neman bin lafiyar kujer?”fadila ta dan murmusa 😊tace ” anty yau saidai amin afuwa yau kasala nake ji””na miki”inji anty hafiza,farida dake canza tasha a t.v tace”qyaleta anty muje na canjeta yau tsokano fada tayi sauran kadan taci na jaki badan Allah ya kawoni na ceceta ba””tab wucenan wlh wa ya isa yayi gangancin taba mana ita?😳””fada mata dai anty😏”cewar fadila,suka shige kitchen nan suka barta a falon
Gyara kwanciyarta tayi don taji dadin yin tunaninsa,shi wa?,idan bata manta ba A.S mai tama binta tace da ita,A.S mai tama ta shiga maimaita sunan ita da zuciyarta,”to me A.S mai tama take nufi?”A dai duk inda aka zaga farkon sunansa ne,to ahmad ne ko ko abubakar ko abdul?,oho itama bata sani ba,wani murmushi ne ya subuce mata😊 sai tunaninta ya dawo kan abinda ya faru tsakaninta dashi dazun,sassanyan muryarsa ta dinga yi mata amsa kuwwa a kunnenta,kyawawan idanunsa yanayin zubinsa da tsarinsa,sai ta tuna sanda ya fito a fusace lokacin data murguda masa baki ta harareshi,nan ma dariya ce ta subuce mata,”lafiya kuwa?”ta tsinci muryar farida na tambayarta,ta hade rai tace”lpy lau me kika gani?”farida ta dan tabe baki tace”hmmm tun dazunfa kike murmushi har da dariya ke kadai kamar wadda ta fara soyayya”da sauri fadila ta kalleta tace”lallai yarinyar ni kikewa wannan titsiyen?to gyada na zama na soye qarewar soyayya”anty hafiza dake zaune saman kujera bata sa baki ba sai yanzu tace”um um yaya fadila wannan fa sign ne na falling in love😜”fadila ta miqe daga kwanciyar tana cewa”kai anty,please kada ki biyewa shirmen farida,ita ‘yar sa ido ce komai ta gani idonta na kai,kuma sai ta sanya ma question mark😏”,ta gyada kai sannan tace ” alright idan tayi wari maji,Allah yasa alkhairi ne””amin amma ba abinda zaiyi wari ma anty”,nan gidan suka wuni har ‘yan biyu suka dawo suka yini tare da su,suna son yaran sosai ko dan su kadaine jikokin gidan nasu,sai bayan magariba sukayi sallah sukaci abinci har yaya ahmad ya dawo ya tarar da su,bayan sunyi shirin tafiya ne ya ahmad ya baiwa ko wacce 4000 anty hafiza kuma ta basu turarurruka.
to daren ranar sam fadila bata samu bacci ba,kusan kwana tayi tunanin A.S maitama,duk da ta danji dadi don aqalla tasan yanzun yasan da fuskarta a duniya,koda bazai iya shaidata ba bare tana tunanin mawuyacine ace yayi saurin manta ta ko dan irin karon da suka yi,har washegari da taje school bai janye motar tasa ba,sun dauki aqalla sati guda a haka sannan taje ta tarar ya cire,a gida tace ne kawai tana tana garage ana duba mata ita
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Cikin wannan yanayin suka soma attachment,ranar laraba aka turasu domin tattaunawa da wani fitaccen dan kasuwa,ita da abokiyar karatunta ne hafsat sai wani ma’aikacin gidan radion khalid da zasu tafi tare qarfe hudu na ranar larabar.
cikin yellow din atamfa ta shirya mai zanan blue din qananun taurari,skert ne rafa da riganshi wanda dinkin yayi mata cif a jikinta kamar don ita aka qera atamfar,ta maqala qananun fashion na dutse masu kalan blue,ta daura dan siririn agogo na fata ,qafanta blue din hill shoes ne mai madauri sai mayafi data yafashi a kafada bayan ta soka daurinta wanda ya fito da dogon gashinta ta qasan daurin,jakarta ta dauka ‘yar madaidaiciya wadda ake maqaleta a gwiwar hannu ta feshe jikinta da turaren shamsul imarat,shigar ta haska fatarta sosai ta fito dagwas da ita,farida dake nade a tsakiyar gadon fadilan tana charting ta dago ta dubeta”gsky yaya fadila kinyi masifar kyau,tsiyar abun daya da baki kula kowa,sai ance anasonnki kuma ki kama mita bayan laifinki ne saiki yi shiga ta janye hankali kuma kice ba wanda ya isa ya kalaki”banza tayi mata ta dauki wayarta dake kan dressing mirror ta fice,farida ta dan daga murya yadda zata jiyota tace”a dawo lpy antyna Allah ya hadaki da mannau ya biyoki har gida😜”bata dai ce mata ci kanki ba ta wuce dakin ummi don tasan a wannan lkc tana daki tana azkar,daga bakin qofa ta tsaya don ta kusa makara tace”ummi zan tafi””to Allah ya tsare hanya ki kula sosai kuma kuna kammala abinda kukaje yi ki taho gida kada ki yadda kiyi dare a waje”tace insha Allah ummi”,acan gidan radion suka hadu,bata shiga ba ta yiwa su Hafsa waya su fito su wuce don a motarta suka tsara za suyi tafiyar,Hafsa na zaune a baya yayin da khalil ya shige gaba,tsaf fadila ta gama karantar manufarsa saidai tayi banza da shi tamkar bata fuskance shi ba,tun zuwanta gidan yake rawar qafa a kanta saidai ya kasa furta mata kamar sauran maza da yawa,tana da wani irin kwarjini ne a idanunsu ita sam baya burgeta,ya fiya surutu shi yasa sam bata son ko aiki ne a hada ta da shi,kamar yanzun ya takura mata sai zuba yake shi ala dole sai ya burgeta,Hafsa na baya tana ta tuntsira dariya 😂don tasan halin kayarta sarai,daqa qarshe c.d plate ta dauka tasa sannan yayi shiru
A hankali suke binkwatancen har suka gano gurin,qaton get din gun aka bude musu gu ne a tsare ahankali aka dinga nuna mata inda zata bi har taje inda aka tana da don ajiyar motoci tayi parking suka fito,ta jingina jikin motar tata tana qarewa gun kallo,tamkar ma’aikata gun yake saidai ya tsaru sosai komai neat,khalil ya qarso gunsu bayan yaje yayi tambaya yace muje can sunce mu jirashi yana fitowa,wani dan gune da ka qawatashi da flastic din kujeru da teburinsu kowanne yaja kujera guda ya zauna
sun dan dauki mintina har fadila ta soma qosawa da zaman jiran
Tun daga nesa da ta hangoshi qirjinta ya hau luguden bugawa,ji tayi tamkar ta tashi ta bar gurinsai kuma taga idan tayi hakan ta bada kanta,don haka sai ta basar ta zarme da bude jakarta ta soma fiddo da kayan aikin da zasu buqata,qashin mayen tutarensa da taji ya mamaye gurin shi ya tabbatar mata da qarasowarsa,sallamarsa ta same tabbayr mata da hakan dukkansu suka amsa saidai ita ta kasa dago ido ta dubeshi ta fake da laluben jaka,ya .iqawa khalil hannu sukayi musabaha hafsat ta gaidashi,sai a sannan ta dago kanta caraf suka hada ido👀 saidai ga mamakinta dauke kansa yayi tamkar bai taba ganinta ba,a hankali ta radawa hafsa”da wa za muyi hirar ne?””gashinan a gabanki a.s maitama “inji hafsat”take taji ta dan rude amma cikin dabara ta gayyato dakiya da nutsuwa ta yafawa kanta,kasancewar Ita ce mai tambayoyin jfsat da khalil na tayata da rubutu dolenta ta jawo kujerarta ta sake matsowa daura da shi ta sanya ‘yar qaramar recorder dinta a tsakiyarsu suka sake zama verry close aunyi face to face sosai,wani yanayi ya dinga shiga zuciyarta da gangar jikinta wanda hakan ya haifar mata da kasala,tanason tayi.masa tambaya ta farko saidai ta kasa,har sai da hafsat ta dan dungure sanna tayi ta maza ta dago ta fuskanceshi👀,saidai ga mamakinta hannauensa na harfe ne bisa qirjinsa yana mata wannan salon jallon rainin nasa😏,da fari munason muji ainihin cikaken sunanka,ta fada yayin da ta mayar da dubanta kan radio dinta taga tana nadar sautin yadda ya kamata,shiru taji har yayi yawa ta dago ta sake dubansa a karo na biyu,saia taga ya saki hannunsa ya dauke idonsa daga kanta ya kalli khalil yace”ko zakuyi musayar aiki ita ta ta karbi rubutun kamar ba zata iya aikin ba”khalil ya dan rusuna yave ranka ya dade zata iya haka tsarin aikin yazo”ya kalleta cikin gatsali yace”zaki iya?”batayi qasaaqwiwa ba tave aisai an gwada aknsan na qwarai”ta mayat masa da irin yanayim yadda ya yi mata tambayar,cikin ransa yake jinjina rashin kunyarta tare da fafin nasan maganinki” a zuciyar sa ya fadi hakan
Ku biyoni muje……
[10/16, 12:21 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Wa yasan gobe?
Safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
▶5⃣
Ya dan gyara zamansa cikin isa ya amsa mata”Aliyyu salim maitama shine cikakken sunana””sunan ya dace da maishi”ta fadi a ranta,cikin nuna qwarewa da gwaninta ta shiga jefa masa tambayoyi daya bayan daya,sai da suka kwashi kusan awa guda sannan ta saurara masa,ta katse abun recording din nata ta jefa a jakarta,ta miqe tayi gaba abinta,saidai can qasan zuciyarta farinciki ne fal ranta,yau ta zauna daf da shi ta shaqi qamshinsa ta saurari muryarsa son ranta,shi kam bin ta yayi da kallo cike da mamaki da takaicin raininta don a gurinsa wannan raini ne.
Zaman ta tayi cikin mota tana dakon zuwansu hafsat
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Dukkaninsu suna gidan alh salim,kasancewar yau ake birthday din iftihal,rabi’ah sumayya farida da fadila anty hafiza sai anty hauwa’u(babbar yar haj maimuna)duk suna bedroom din momi,fadila na kwance bisa gadon momin,dakin ya kaure da hayaniya amma banda ita,sam gun ma baya mata dadi,tun jiya da Abba yayi mata da ya ahmad suka yi masu magana ita da farida kada su kammala attachment dinau ba tare da sun kawo mijin aure ba,farida kam ko ajikinta tunda dama irin wannan damar take jira ita da masoyinta mubarak
Ta sake juya kwanciyarta hannun damanta kanta yayi mata gingirin zuciyarta a cunkushe,anty hafiza ta juyo ta kalleta “fadila ki saki ranki don Allah kiyi addu’a shine kawai mafita “fadila ta lumshe idonta hadi da sake qanqame pillow tana sake jin nauyi cikin qirjinta,anty hauwa tace “me ya sameta ne tun dazun na lura bata cikin sukuni”,anty hafiza ta gaya mata hadi da cewa”na rasa irin farida kwata kwata bata kula kowa,nan da kika ganta bata da wani gwani”farida tace ” anty itama fa da laifinta ya za’a ce duk mazan dake mutuwar sonta ace babu daya da ya mata”a fusace fadila ta kalleta😡”anty kinganta ko ko da ita ake magana?😫”dama zuciya kusa a kusa sai hawaye wani na bin wani😭”anty hauwa’u tace”duk ku tashi ku fita ku bamu wuri”tsam suka fice dakin ya rage daga ita sai fadilan sai anty hafiza,anty hauwa’u taja ajiyar zuciya tace”sai nake gano dacewa tsakanin fadila da Aliyyu Abban iftihal ba don kada nayi muku shishshigi ba da na hada wannan alkhairin”gabanfadila yayi matsananciyar faduwa💔 jin an ambaci Aliyyu,inama ace shine aliyyun da anty hauwa’u ke magana akai?,ina ma ace shine zai taho da neman soyayyarta?,ina ma ina ma………taci gaba da zancen zuci
Anty hauwa taci gaba da cewa”shima anyi anyi da shi ya fidda mata tayi aure ya qi,sai jiya ya kawo wata yarinya mai zubin yare ba alamun tarbiyya a tattare da ita wai ita yake son aura,hafiza yarinyar bata da maraba da matarsa ta farko,amma sai ya kakkareta da cewar wai zaman cikin yare ne yasa aka ganta haka amma da nutsuwarta.
Fadila tayi hanzarin tashi don batason zancan da anty hauwa’u ta dauko yayi ma wani nisa,tayi qasa da idonta😪 tace”anty ba wai inason watsa miki qasa a ido bane a’ah,bansan ya Aliyu ba sani na da shi tun ina qarama ne wanda a yanzu na manta shi gaba daya,shima kuma nayi imanin ba sanina yayi ba,ba ta wannan ba anty a zamanin nan auren soyayyar ma ya aka cika bare auren hadi,matar cushe anty ba ta daraja,kawai ku tayani addu’a Allah yayi min zabi mafi alkhairi”suka amsa da amin suka kuma bar maganar suka shiga wata badan maganar ta bar ran anty hauwan ba
Kwana biyu da yin maganar anty hauwa na juya maganar cikin ranta sai ta kasa hadiye maganar har sai da ta niqo gari ta dawo gidan don tattatunawa da abba”tana zaune gaban abban bayan sun gama taba hira tace”abba nazo maka ne ne da wata muhimmiyar magana”abban ya bada dukkan hankalinsa kanta sannan yace”uhm ina jinki maijidda”ta dora”abba kasan fadila ‘yar abba abbas tafida?”yayi murmushi irin na manya yace”banda abinki maijidda idan ban san su farida ba ai kuma bansan kuba,”tayi dariya ita da momi tace hakane abba”tiryan tiryan take gaya masa halin da yanzu fadila ke ciki game da zancen fiddo da miji,sannan ta dora”abba inason ne na haska muku abinda tuna nina ya hasko min game da wannan lamarin””uhn”cewar abba,anty mai jidda ta dora”abba Ali ya kawo muku yarinyar da azahirin gaskiya baku yadda da halaye da nagartarta ba,ali abba ya riga ya fada soyayyar yarinyar wadda da zarar kunce zaku hana shi auren ta dama ce tq zo masa ta yaci gaba da zama babu zancen aure,zai kafa hujja da cewa ai tun tuni ya kawo ku kuka qi abun”abba ya gyada kai cikin gamsuwa maijidda ta dora da fadin”to abba mai zai hana ku bashi damar ya aureta amma abba ku hadashi da fadila?,abba kai ganau ne ba jiyau ba ka fini sani kasan fadila kasan irin kyakkyawar tarbiyyar da suke da ita,mai zai hana muyi kwadayin hada zuri’a da su abba?,abba kada mu bari ta subucewa family dimmu saboda fadila macace ta gari wadda nake da yaqinin samun alkhairai masu tarin yawa da zuriyya dayyiba tattare da ita?”
Shiru sukayi gaba dayansu bayananta na ratsa su tabbas duk abinda maijidda ta fada gaskiya ne,sun gamsu matuqa da bayananta,abba yaji dadi matuqa sosai tare da sawa maijidda albarka gameda zurfin tunanin da tayi akan makomar rayuwar dan uwanta
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Washegari alh salim da kansa ya taka ya nufi gidan amininsa alh abbas tafida,suna babban falon sa bayan sun gam gaisawa alh salim yace”abbas nasan zakayi mamakin ganina ko da daddarennan bayan jiya da azahar ma muna tare”alh abbas yayi murmushi yace ai nasan akwai dalili,kuma ma mene a aciki don dan uwa ya ziyarci dan uwansa aduk sa’adda da yaso?”alh salim ya gyada kai yace”hakane dalili ne kuwa babba ya taso da ni”alh abbas ya vyara zama yace”ina jinka Allha yasa lpy”alh salim yace”danka Aliyyu nazo nemawa auren’yata fadila”alh abbas yace”fadila?”ya gyada kai qwarai fadila ko anyi mata miji ne?”alh abbas ya girgiza kai yana murmushi yace”ko daya wlh,rigimar da nake ma da ita kenan a ‘yan kwanakinnan kenan akan sai ta fito da miji,maganarka alh ta yimin dadi sosai wlh,amma ina fatan da amincewar alin?”a’ah ko daya wannan hasashe nayi na son hada zuriyya da aminina”alh abbas ya saki dariya yace”yayi wlh wannan tunani naka yayi kyau qwarai da gaske,domin samun nagartacce kamar Aliyuna a wannan zamanim abune mai matuqar wuya qwarai da gaske,fadila’yar ka ce halak malak kuma ko wani kaso bata wlh zaka iya bashi bate aliyu,na bawa aliyu ita har abada abokina”alh salim yace”a’ah abokina kada kayi saurin yanke hukunci ba tare da kaji ta bakin ta ba ka bari su gana taga idan har yayi mata”alh abbas yace”haba salim Haba salim yaya zaka ce haka bayan kasan yarinya budurwa ubanta ne ke da ikon zaba mata mijin aure ballantana duk yaron da zata zaba mawuyacine yakai nagarta da ingancin aliyyun,ai magana ma ta qare dama dab suke da kammala attachment dinsu nafison ace da zarar sun kammala su tafi dakunansu”
Alj salim yaji dadin maganar yace”amma fa wani hanzari ba gudu ba,akwai yarinyar da aliyun zai hada su ya aura tare,to ya kamata a sanar da ita kasan yaran yanzu basa son abokiyar zama kaga ya kamata ta sani kafin ayi”alh abbas yayi dariya yace”shirmen banza ne iri na ‘ya’yan yanzu zan sanar da ita kada ka damu,bamu buqatar duk wasu kaya na bidi’o’i”alh salim yace”a’a kaima ka sani momimta haj maimuna ba zata yarda ba yadda za’a yiwa dayar itama sai an mata”suka sa dariya gaba dayansu cikin farinciki,cike da godiya bisa karamcin da amininsa yayi masa”alh abbas yace ka daina godiya da Aliyu da fadila duk daya ne a gurina”alh salim yace”na sani amma duk da haka godiya ta zama dole duk wanda yayi ma jininka kyautar da sukutum da guda ai ba qaramin masoyi bane,cikin girmamawa da mutuntuna juna sukayi sallama
Safiyya(mra muhammad bello)
[10/16, 12:22 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Wa yasan gobe?
Safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶6⃣
Cikin daran alh abbas ya sanar da mai dakinsa,tayi murna qwarai don tasan amincin dake tsakanin mazajan nasu da irin tarbiyyar dake gidan alhj salim,sai dai tace wani hanzari ba gudu ba alhj ba lallai yaran su so junansu ba fa?,abba yayi dariya yace”duk soyayyar yqnzu shirme ce,ina soyayyar take zuwa?daga anyi auren ta mutu sai ki rasa ranar da tayi musu,wani auren hadin ba yafi qarko da albarka ba,ga auremmu ya isheki misali sai da aka kawo ki muka ga juna ko kin manta,gashinan haryau shekara kusan talatin da biyar ba fada bare yaji”ya dan kalleta ta sigar tsokana yace”nasan dai abu daya kikayimin kin shanye ni na kasa qaro miki abokiyar zama”kunya ta kamata tadan rufe fuskarta da tafin hannunta🙈tana cewa”kai alhaji”shina dariyar yayi😄 yana bude mata fuska yace”ai gaskiya ne”
Misalin goma na safiyar washegarin ranar alh salim da kansa ya sanya aliyu a gaba ya tuqoshi zuwa gidan aminin nasa alhj abbas don kawo sadakinsa,aliyun yayi kyau abinsa cikin shadda gezna dinkin tazarce farace qal sai maiqo take,ya saye idanunsa cikin farin glass wanda bai hanaka tozali da farar qwayar idanunsa,takalminsa baqi ne na kamfanin batozi sai baqar hula duk da bai sanya ta ba tana riqe ne ahannunsa,kana nazaratar fuskarsa zaka karanci damuwa a tattatare da shi,sam alh salim bai bi ta kansa ba don yasan kwanan zancan,ya sani cewa gata ne yake son ya yiwa aliyun wanda ko bayan ransa zaiji dadinsa.
A nutse yake murza sitiyarin motar har suka iso cikin gidan,alhj abbas da kansa ya fito yayi ma abokin nasa iso zuwa cikin gidan bayan sun gaisa da Aliyu suka barshi cikin motar,ya dan kwantar da kujerar motar yayi rigingine yana kallon yanayin ginin gidan,
Alhj salim ya fiddo da daurin bandir na dari biuar biyar rafa daya ya ajjiye a gaban alhj abbas yace “ga sadakin aliyu ga ‘yata fadila”alhj abbas yace “amma ai a yimin kara ko ni na biya ai”alhj salim yace”ni da kai ai duka dayane babu komai wlh”alhj abbas yace”Allah to ya yiwa auren albarka yasa ya zamo farinciki a gurimmu da gun yaran gaba daya””ameen”ya amsa masa”auren zai kama nan da sati shida dai dai lokacin da zasu kammala attachment dinsu”alhj salim yace”anya ba’ayi gaggawa ba?””wani irin gaggawa kuma me zasu zauna su yimin agidan ?”to shikenan abbas Allah yasa ayi a sa’a””amin dama ban sanar da yarinyar ba niyyata dama yau ta sani amma munyi zancan da mahaifiyarta,to tunda ga sadakinta ga kuma mijin sai a kirata tasan komai””to ba laifi”inji alh salim
Tana ysaka da baccinta😴 taji ana dukan saman qafafunta,ta daga kanta idanunta cime da bacci tana kallon muhammad da ya tashetan cikin jin haushin tashin nata da yayi tace masa”meye?,ba nasha gaya maka idan ina bacci ka daina damuna ba”ya hade hannayansa 🙏🏻yace”am sorry anty,abba ne ke kiranki””abba kuma?😳”ta ta tambayeshi cike da tsoro saboda ta tuna agender su,ya gyada mata kai cike da tabbatarwa,tace jeka ina zuwa”tuni ragowar baccin da take ji ya gudu daga idanunta,ta dirgo daga gadon ta shige toilet ta wanke fuskarta tayi brush sannan ta dawo cikin dakin ta daura zani kan rigar baccin ta ta fesa turare sannan ta zira zumbulelen hijabinta mai hannu,a falo taci karo da umminta tana saka turaren wuta,ta gaidata sannan fuskarta kamar mai shirin rushewa da kuka😟 tace”ummi wai abba ke kirana”ta kalleta tace”to kije mana na ganshi da alhj salim”gabanta ya qara faduwa ta juya ta bar falon
A salube tayi sallama a sitting room din,dukkansu suka amsa mata,ta samu gefan kujera ta gaida uncle abba(hka suke ce masa)kasancewar sun gaisa da abbanta tunda asuba,uncle abba ya amsa yana mai qara nazaratar nutsuwa da ladabinta,abbanta ya kalleta yace”fadila ina son ki bani aron nutsuwa da hankalinki “tace”to abba😔””kin sani cewa shekarunki sun isa ace kina dakin mijinki tunda an aurar ma da wadanda basu kaiku shekaru ba,sannan na baki dama ki fito da wanda kikeso kamar yadda qanwarki ta fiti da shi amma har yanzu baki cemin komai ba,na qyaleki har lokacin da nabaki ya qare ban tanka miki ba duk da cewa ina da iko in zaba muku miji amma na baki damarki “ta gayada kai “hakane abba yace”fadila”ta amsa “na’am””abbanki ya nemawa yayanki aurenki kuma na bashi”wata mummunar faduwar gaba ce ta risketa tamakar an daddaure jijiyoyin jikinta taji,hakan yasa ta kasa dago idanunta ta kalli kowa bare su fahimcin halin da ta shiga,ya dora da cewa “yanzu haka ga sadakinki a hannuna”jin hakan yasa ta qarasa rikicewa sauran dauriyarta tuni tayi qaura,addu’o’i ne barakatai suka dinga zuwa bakinta tanayinsu cikin zuciyarta,shikenan na rasa aliyuna?shikenan zuciyata ta rasa muradinta?shikenan mafarkina ya zama hasashe?,abinda take jujjuyawa kenan kawai a zuciyarta,duk maganganun abba ba wanda ta ji ko ta fahimta sai maganarsa ta qarshe wadda sauran qiris ta sa numfashinta ya dauke”kije kuga juna yana falon waje duk da shekarun baya kun sanshi amma saboda tsawon shekarun zaki iya mantashi ya kwana biyu baya qasar”uncle abba ne yayi saurin cewa”a’a saurara✋🏻ina da magana ke fadila gayamin gaskiya idan bakiso kina da wanda kike so”tabbasa da zata iya da ta fayyace musu sirrin dake zuciyarta ko zasu tausaya mata su bar zuciyarta taji ma da masifar da take ciki,amma ko kusa batajin zata iya kunyata abbanta,bayan ya isa da ita yana da iko da ita fiye da yadda take da iko da kanta yayi mata komai a rayuwa ya bata dama masu yawa a rayuwa irin wadda kowane mutum ke son samu,duk ma a ture wannan gefe baza iya daga iso ta budi bakinta tace da aminin mahaifinta wanda yake tamkar uba a gareta cewa batason dansa jininsa ba,hakan yasa tayi saurin girgiza kai tace”ko daya abba na gode da zabin da kukayimin,Allah ya saka muku da alkhairi”ita kanta ta jinjinawa kanta kan namijin qoqarin da tayi na furta haka,uncle abba har zuciyarsa yaji dafi matuqa tare da sake gode ma allah da zata zamo daya dqga cikin ahalin gidansa,albarka suka sa mata sannan abbanta ya umarceta taje su gana
Takai kusan minti biyar a qofar sitting room din ta kasa shiga,gaba daya a rude take zuciyarta a cunkushe take,daga qarshe taga tsayuwar batada wani amfani don haka ta tattaro dukka nutsuwarta da dauriyarta ta kutsa kai hade da sallama kanta a qasa😔 ta lalubi kujera daya ta zauna cikin fargabar wa zata daga kai ta gani,muryar da taji ta masa mata ita ta razanata da sauri ta dago kai ta gani ahin da gaske ne ko kunnuwanta da zuciyarta ke yaudararta yadda suka saba?idanunsu suka hadu da juna👀 wanda hakan ya tabbatar mata da tsammaninta,ba qaramar razana tayi ba duk da bata nuna hakan ba,A.s mai tama Aliyyun uncle Abba?,take ta jera sunayan a zuciyarta,komai tsaya mata cak yayi,tunaninta ya kasa gaba ya kasa baya,shiru daki ya dauka ba wanda ya tankawa dan uwansa wanda hakan ya sanya fargabarta daduwa,bata kuma sake kallonsa ba bare taga a wane irin yanayi yake ciki ba,sun jima a haka sannan ta jiyo alamar miqewarsa,har ya kai bakin qofa yayi taku uku ya dawo da baya,kallon nan nasa da ta fari gani a qwayar idonsa ta kuma tsaneshi shi yayi mata sama da qasa sannan yace cikin izza da qasaita”ban iya qarya ba kuma bazan fara taba saboda ke,bazan iya tafiya ban amayar da binda nake ji cikin zuciyata ba,bakimin ba baki dace dani ba,baki ma dace da tsarin rayuwata ba,ke da kanki shaidace ce idan dq zaki iyq yiwa kanki adalci bamu dace da juna ba,baki ma da zubi da tsarin da nake so gun mace,idan banda tsaurin ido ma irin naki taya zaki hada kanki da ni?kinga nayi kala da ke?gaskiya kin cuceni,god forbid ki zama matata,kada kuma ki soma yaudarar kanki ta hanyar zato ko tsammanin nan gaba zan iya sonki harki cuci kanki ki aure ni,wannan maganan daga cikin zuciyata direct take fitowa
Wani mugun takaici da baqinciki ne lokaci guda ya rufeta,tunda take babu wani da namiji da ya taba mata munanan furuci makamanta wannan,ta tuna uawan samarin da ke kara kaina a kanta,samari masu ji da kudi kyau nasaba isa da qasaita,ba wanda ta bawa dama a cikin su,wasunsu dama suke so ta basu koda ta friendship ne amma basu samu ba,samari da dama sun sha kuka a gabanta kan ta mallaka musu zuciyarta,amma yau wani daya daga cikin jinsin maza ke gaya mata wadannan kalaman,ji take a rqntq matuqar ta barshi ya tafi haka ba ta da ta mayar masa da martani ba wanda zai dade yana cizon zuciyarsa ba to ba shakka tayi faduwar baqar tasa”hey🙋🏻”tace da shi sanda ya sanya kai zai gice daga falon,ta miqe tsaye ta yi masa kallon sama da qasa ta yatsina fuska😏 ta tofar yawu a gefanta sannan tace”see you wane mashahurin maqaryacin ne ya gaya maka ina maraba da kai da zaka zo kanata soki burutsu,ni dinma ba yimin kayi ba don baka wuce dan aiken gidana ba a tsarina,amma ni nasan darajar dan adam banga a gidammu ana tozartashi ba kuma na iya darajatta zancan magabata na shi yasa ban tozarta mutumin da mahaifina ya zabamin ba,idan banda qaddar ina budurwa sabuwa dal a leda mai zanyi da bazawari ragowar wata……….
Wata iriyar wafta ya kawowa bakinta wanda ta tabbatr da ya sameta sai lebunanta sun fashe,da gudu ta bude daya qofar falon da zata kaita cikin gida ta baya ta shige ta bankowa aliyu qofar ta batshi tsaye zuciyarsa kamar zata fito saboda fushi,ya ga alamar akwai rainin wayo tattare da yarinyar,yayi qwafa cike da zafin zuciya ya fice,kai tsaye daķinta ta nufa ta kulle qofarta gam tayi zaman dirshan saman carpet dinta,wani irin kuka ta saki😭tayi qasa da kanta😪,ta rasa me zayayi farinciki ne ya kamaceta ko baqinciki?ta jima a zaune tana kukan tate da tambyat kanta da kanta shin dama baqinciki da farinciki na haduwa lokaći guda cikin zuciyar bil’adama?yau kam ta fahimci hakan na faruwa tunda gashi yau ta tsinci kanta a ciki
Aliyyunta mafarkinta na kullum?burin zuciyarta muradinta yau shine zai zama mijin aurenta babban burinta kenan dama anan duniya,sai dai kash yazo mata ta wata iriyar fuska da sigar da bata tsammatar mata ba,baya sonta baya qaunarta abin har ya kai tsananin da bazai iya boye qinta a zuciyarsa ba harsai da ya tsaya a gabanta ya fesar mata,baya ga haka ba ita kafaice zata zama mallàkinsa ba?zata yi sharing aliyunta da wata?ga ahi har waya ma ta rigata samunshi(maman iftihal)
Da qyar ta iya janye jikinta ta gada saman gadonta,ba abinda ke mata amsa kuwwa akunnenta irin kalaman aliyu,kafin azahar zazzafan zazzabi ya rufeta,sau biyu farida na shigowa dubata tana ganinta a duqunqune tayi tsammanin bacci take,a shigowarta ta uku ne tace”kai yaya fadila wani irin bacci ne haka tun ten o’clock har one thirty?”tasa hannayenta ta janye bargon tana fafin”ba sanyi ake ba ba komai ba kuma kin…….
maganar ta maqale mata sanda idonta yakai kan fadila ta zaro ido😳 tana cewa”kinga idonki kuwa?”ta juyar da idonta daya side din sannan tace”kaina ke ciwo”
Mrs muhammad bello
✍🏻✍🏻✍🏻📝📝📝
[10/16, 2:39 PM] +234 706 914 1005: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Wa yasan gobe?
Safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶7⃣
Fadila ta juyar da kanta daya barin tace”kaina ke min ciwo”farida ta gefanta ta zauna tace”kinyi dai kuka wanda ya haddasa miki ciwon kai,sis ni ‘yar uwarki ce,bai kamata ki dinga boyemin wasu abubuwa da ya kamata ace na sansu ba,yadda nima bana boye miki komai bana boye miki damuwata nake neman shawar warinki akan komai,ko dan tsokanarki da nake ne yasa kikemin kallon am too young?,komai ai da tym dinsa,amma idan kina ganin na takuraki am sorry sister”ta fada tana shirin tashi,sai ta bawa fadila tausayi,farida na sonta sosai,tana damuwa da damuwarta any time,ta riqo hannunta tace”is not lyk dat sister baki takurani ba,I will tell yuh everything,but b4 den bani paracetamol nasha,and kimin alqawarin daga ni sai ke babu maijin wannan sai wanda na amincewa hakan”ta gyada kai tace “I promise sister”
To fadila dai sauqi bai samu ba har sai data kwana biyu a kwance tana jinyar jiki da zuciyarta sannan ta samu qwarin jikinta da taimakon farida ta hanyar bata shawarwari da kwantar mata da hankali,ba abinda ke sake daga mata hankali irin lafuzan da suka fito daga bakin abinda tafi so a duniyarta har yau sunqi bacewa daga dodon kunnenta
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Yammacin talata ne wanda ya zamto dukkaninsu suna da abinda za suyi cikin makaranta don haka suka tafi a amota daya suka kuma dawo tare kasancewar lokaci guda kowacce ta gama uzirin da ya kaita,tare sukayi sallama suka shigo suka tadda umminsu a falo ita da muhammad dake gefanta yana ta kumbure kumbure,ta musu sannu da dawowa suma suka mata sannu da gida sannan suka haura samansu kowacce ta nufi dakinta don watsa ruwa,farida ta riga fadila kammalawa har ta sauko ta shiga kitchen ta ciko plate da couscous da vegetable soup wadda ta wadata da hanta,fadila ta sauko sanye da pakistan riga da wando irin shigar farida kenan saidai bambancin colour na fadila dark pink ne na farida kuma light blue
Itama kujera ta samu dake kusa da ummin ta zauna,ta dubin sashen da muhammad yake wanda tunda suka dawo ya musu sannu da zuwa bai qara cewa qala ba tace”ummi halan yau akwai abinda ke damun parrot dinki naji yau gidan so silent gwanin dadi ba hayaniya”ummi tace”rabu dashi,haka kawai yazo ya tarar dani ina kallon labarai shi wai dole sai ba canza masa tasha zai kalli qwallo”farida ta kalleshi”meye amfanin t.v din dakinsa”ummi tace”duk yabi ya lalata socket din dake dakinsa wai shi koyon gyara an canza masa wasu ya sake kuncesu to ba sai yaje yayi ta yi ba nidai ba mai takurani ni da falona idan mutum yaji haushi ya tashi ya bani guri”ta fadi hakane don dama ya isheta ta koreahi tun dazun yaqi tafiya,ai kuwa ya tashi ya bar fallon yana shirin sa kuka,fadila ta gimtse dariyar dake son qwace mata don tsakanin ummin da muhammad ba’a shiga tasan kuma nan da anjima shi zata lallabo tace yayi mata tausa,fadila tace”ummi mun hadu da haj barira fa?”ta juyo ta dubeta tace “a’ina?,dama tana gari ne uwar tafiye tafiye?”farida da takai lomar abinci bakinta ta karbi zancan”a danja ummi,danja ta tsayar da mu sai da tasa mukayi parking gefan titi,farida ta qyalqyale da dariya😂 tace”kai matarnan ummi Allah ya zuba mata surutu”ummi ta mata daquwa tace”ungo wannan mamarku ce,da Allah yayi ma ke farida ai da tuni ta zama surukarki”farida ta sake kecewa da dariya😂ta kama haba tace🤔”Allah ya tsare,wai shi abdus-samad ma idan banda abunsa ummi qawata fa rumana yace yqna so amma don ya raina ni yaje ya cewa hajiya ni yakeso,ni bansan ma inda tasan labarin bikimmu ba take tambayata nace mata saura three weeks,ai kauwa har zancan abdus-samad din.ma tayimin wai na dai qishi”ummi tace”ato kunya ma ta isheki”
Ummi ta juya ta dubi fadila wadda ta zubawa t.v🖥 ido tayi shiru tana sauraransu ,duk da fadila miskila ce amma ta sake zama so quiet fiye da da,ga wani rama da take dan kumarin da a da take dashi yanzu ya zabge babu shi duk a cikin kwanakin ummin na ankare da ita,abun ya dameta sosai har take sanar da abbansu,ya kwantar mata da hankali ta hanyar cewa”kada ta damu ai dama yawancin ‘yammata idam aurensu ya taso gadan gadan hakan na faruwa sai tace amma ai bata ga hakan a gun farida ba yace mata ai kowa da irinshi wani ma qiba yake yi maimakon rama,ummi ta yanke tunaninta tacewa fadila”ki shiga kitchen ki sami abinci ki ci”ta dan noqe kafada “ummi sai anjima”ta bata rai😠 tace”wani anjiman kuma?,kinga tashi ki debo abinci kici tun kafin ranki ya baci”tasan ummi ba wasa don haka a kasalance ta miqe ta nufi kitchen ummi tace mata”ki taho min da kunun aya”
Taliya ta zuba da miyar kifi(haka umminsu take gwanar girki shi yasa da wuya kaje gidan ka tadda abinci kala daya a kitchen dinta takanyi kamar kala biyu dai dai yadda zasu iya cinyeshi)kusan sili dai dai fadila ke zara tana ci ummin na kallonta tayi banza da ita,yayin da farida ke mata kallon tausayi😒,
Wayar ummi ta soma ruri alamun ana kiranta tasa hannu ta qmsa hadi da yin sallama,”haj maimuna lpy lau……..lpy qalau wlh……..ah mun gode Allah”fadila dake gefe gabanta ta fadi ta tabbatar kiran daga mahaifiyar Aliyu ne ,ko yaya ta ji wani abu da ya danganci gidansun sai ta shiga fargaba,tana tsoron mai zai biyo baya ne a nan gaba?.
Tsinto.muryar ummi tayi tana cewa”yanzu da nufinki haj sai dai naji a gari?ai Aliyu dana ne don zai auri fadila sai na kasa zuwa rakiyar lefansa gidan wasu?ita fadilan ba’a zuwa kaiwa za’a zo kawo nata
Wata mummunar faduwar gaba ce ta shigeta,lallai ya tabbata Aliyu nasu ne ita da wata,ji tayi wani daci ya mamaye mata halshenta abincin ya qarasa ficewa a aranta don haka ta zame ta shige kitchen ta maida shi cikin cooler ta rufe,taja plastic din kujerar dake kitchen din wadda sukan ajjiye saboda zaman aiki ta zauna a kai,daganan din tana iya jiyo muryar ummin nata na mata sallama tana cewa”Allah ya kaimu goben,Allah ya nuna ma……….bata qarasa ji ba tayi saurin saka hannunta ta toshe kunnenta qwalla nabin fuskarta😢
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Washegari gaba daya jikinta a mace yake murus ta kasa fita ko ina tana kwance a daki komai ya cakude mata,har la’asar tayi ummi ta shirya tacewa farida itama ta shirya ta kaita tana jiyo farida na mitar ita fai bazata ba ummi idris kawai ya kaiki,”kinci uwaki ja’irar yarinya to naqi idris din ya kaini ke zaki kaini idan kuma ba zaki ba bani maqullan ni nayi driving din da kaina”,haka farida ta shirya babu son ranta suka fita sukabar fadila ita daya a gidan,fitarsu sai taji kamar an qara mata kasalar,kimanin awa guda da tafiyar tasu tajiyo sallama daga bakin falon qasa,ta miqe ta yafa mayafinta ta fito bakin verandar saman benan sani mai gadinsu ne yace”uwar dakina yallabai ne yazo”gabanta yadan fadi saboda wanda zuciyarta ke raya mata shine”wanne yallabai?”ta tambayi malam sani ya saki dariya😃 yace”yallabai Aliyu jan zaki”tayi jim kamar tace baxata ba,sai kuma ta tuna da maganganun da Abbanta yayi mata daran shekaran jiya ta juya ciki tana cewa”kace ya jirani ganinan zuwa”bata wani jima da yin wanka ba don haka body spray ta fesa ta dauki hijabinta ta sanya ta zura slippers din wankanta ta fito,yana cikin sitting room din bakin get,ya dan kashingide akan kujera three sitter waya yake da alamu kuma yana jin dadin wayar don har wani lumshe idanunsa yake,bata ce uffan va ta samu gu ta zauna zamanta da minti biyar ta fuskanci da wadda yake wayar jin zancan wadanda suka tafi kai.lefe da yayi,ya doshi kusa minti ashirin yana wayatsa ba abinda ya shalleshi kamar shi kadai ne a dakin sanann ta jisu suna sallama da juna cike da tsantsar soyayya,wata allurar kishi ce ta soketa ta kauda kanta gefe tayi kamar batasan budurin da yake ba,
Bayan ya kashe wayar sai shiru ya baqunci dakin,bakajin motsin komai sai qarar a.c “ke”taji yace,banza ta masa kamar ba da ita yake ba taqi ko da kallon sashinsa,taji ya sake cewa”da ke nake”ta dago ta watsa masa wanu kallo na baka isa ba,bata mai da kanta ba taji yace”baki isa na roqeki ba amma ina baki shawara da umarni kije kice bakya sona,idan ta kama ma zance miki please ko dan nima ki barni in samu peace of mind da wanda nake son aura”sai taji zuciyarta ta karye gaba daya tausayin kanta sai ya kamata lokaci guda,tabbas aliyu baya qaunarta ko qanqani,batasan sanda hawaye ya subuce mata ba,ta sake tabbatarwa da kanta so bala’ine kuma masifane,haqiqa tana cikin jarrabawa mai girma,musamman irin wannan son na SON MASO WANI,sai taji bata da wani zabi da ya wuce ta tashi ta bashi guri,ta miqe tsam ta fice tana lalauben hanya,tabbas ba shakka yau da ita ta zabawa kanta Aliyu ta tabbatar da a yau ta rabu da shi koda sonsa ai zama ajalinta,da kuna zata iya duban mahaifinta ta roqeshi ya janye maganar aurensu da Aliyu da tayi hakan
ta jima tana kuka a dakinta sanann daga baya tabi ahawarar da zuciyarta ke bata na ta nemi matemaki mana a cikin lamarinta?,ta wanke fuskarta ta shafa hoda ta zizara kwalliya a idanunta donbta rage musu kodewar da sukayi,after dress ta zira ta dauki key din motarta,tana saukowa taci karo ba daqar leda a falon,bata bi ta kanta ba ta fice,tana bude motar ta ta dannawa mlm sani horn akan ya bude mata qofa sai da tazo saitinsa sannan ta tambayeshi wa ya shigo falo da kaya?”nine yallabai ne yace a kawo miki,inata sallama ma naji ba’a amsa ba sai………,ta daga masa hannu kawai ta fice
Cikin minrina qalilan ta isa gidan ya ahmad saboda gudun da ta tsula anti hafiza na falo ita da biyunta taganta tamakar wadda aka jeho ta zube a kujerar falon tana haki sai kuma qwalla ta fara sintiri a fuskarta,kallo daya anty hafizan tayi mata ta tabbatar ba lafiya ba ta cire yan biyu da suka zube jikin fadilan sunata murnar ganinta ba tare da lura da halin da take ciki ba,ta kiu ra maqociyarta zainab tace ta turo ‘yar aikinta ta wuce dasu gidanta tayi baqi
Kusa da ita anty hafizan ta zauna ta kamo hannayentabta riqe sannan tace”lpy me ya faru haka?”fadika ta sake fashewa da kuka tana cewa”na shiga uku anty,innalillah,anty zuciyata bata yimin adalci ba ta jefana cikin mawuyacin hali,anty ki taimakamin,me yasa zuciyata ta yimin hka anty?why?why?,
Anty hafiza ta dafa kanta tana shafawa tana cewa”calm down ki nutsu ki gayamin meke faruwa?”
Tasa bayan hannunta tana share hawayen dake kwararo mata sannan ta saki ajiyar zuciya tace”anty tun kafin na San shi waye zuciyata ta dade da kamuwa da matsananciyar soyayyarsa💘,tun daga lkcn na rasa sukuni a zuciyata kwata kwata,kullum kwanan duniya qaunarsa na qara ninkuwa ne a zuciyata kamar jaraba abun,ina cikin wannan haline muka fara face to face da shi saidai abu na farko da ya fara shiga tsakaninmu fada ne,hakan ya zamana har zuwa lkcn da mahaifin Aliyu salim maitama ya nema masa arena gun abbammu ba tare da nasan shine ba,na shiga matsananciyar damuwa😣 a lokacin da ta bayyana an bada arena ga wani,sai dai sanda nayi tozali da aliyu a matsayin wanda aka bawa ni sai farinciki😊 ya mamaye damuwata
Sai dai kuma me?anty ga tarin mamaki na sai kalaman qiyayya suka zamo kalaman farko da na fara samu daga masoyina,kalaman da suka kusa tarwatsa zuciyata💔,qarara aliyu ya nunamin bai qaunata ba nice choice dinsa ba samirah ce muradinsa,meye aibuna naty?wane naqasu nake da ahi wanda ya janyo aliyu ya tsaneni?ban can can ci so bane daga gurinsa bane anty?
Aliyu yana sonki zai kuma soki fafila”ta fada tana girgiza kafadarta,kukanta ya tsaya cak sai hawaye dake shatata ta ski baki tana kallon anty hafizan da itama ido ta zuba ma ta tashiga girgiza kai tana cewa”bazai soni ba naty baya kuma sona din ya fada anty da bakinsa fa yace”kada nasan ran wata ran zai soni”anty hafiza tayi saurin tarar numfashinta tace”✋🏻ke da’alla can rabu da shi shike da kansa?WA YASAN GOBE?ai sai allah”ta karyar da kai cike da neman agaji da mafita😧”amma anty haka zamu rayu da shi?rayuwar aurece naty wadda ba yau ko gobe za’a yita a watse ba”
anty hafiza tayi murmushi😊 tace”ki kwantar da hankalinki,abu na farko da nake so gareki shine ki miqawa allah lamuranki babu abinda ya gagari allah,abu na biyu ki zamo mai juriya haquri gami da kawaici ki zamo mai controlling din anger dinki ,ni kuma insha ‘allah nayi alqawatin doraki akan step na gaba,nayi alqawarin baki shawarwari na gari harsai inda burinki ya gama cika
Cikin hikima da dabara ta zauna tana bude mata babi babi na hikima da dabarun zaman tare gamida kwantar mata da hankali har fadila ta ji nutsuwa ta shigeta tace ni anty abinda ke dada tayr min da hankalin ganin yadda nake jin zallar soyayyarsa a zuciyata to shi haka yake jin zallar qiyayyata”tave cool down sister na gaya miki kada ki damu irin wananna ita take fa juyewa wata rana ta zama zazzafar soyayya ke dai ki dinga yiwa soyayyar tasa linzami kada ki bari ya fuskanci akwaita a ranki don kada ya samu jin dadi da sakewa na wulaqantaki harsai lokacin bayyanatan ya yi
Daf da sallar magariba yaya ahmad ya dawo bayan sun gaisa yake zolayarta”lpy kuwa amarya nàga tana ta qarewa haka?”tayi murmushin yaqe tace lpy lau yaya”anty hafiźa tayi saurin tare tambayar ta hanyar cewa”abban twince aì kasan fama haka na faruwa ga mutum idan aurensa yazo”ya girgiza kai xikin gamsuwa da bayaninta yace”hakane aure yaqin mata,Allah yasa ayi a sa’a”anty hafiza ta masa amin
Bayan isha’i tayi haramar tafiya bayan anty hafiza ta tsareta dole ta sata cin abinci ,antyn ta rakota bakin mota tana sake kwantar mata da hankali fadilan ta dubeta tace”anty unason don Allah ya zama sirei wannan zancan””haba fàfila kada ki damu dake da aysha daya nake daukarku(qanwarta ce aysha)fadila tace anty na gode
Tana driving tunani ne fal cikin ranta duk da tana jin ta samu relief sosai cikin ranta,ita kanta mamakin kanta takeyi tasha jin yadda mata ‘yan uwanta ke yaba kyau da ajinta👰🏻 bare maza wadanda ita kanta batasan adadin masoyanta na dili da na bòue ba wadanda ke jatumtar sanar da ita da wadanda take musu kwarjini suke batin abuna zuciyarsu,wadanda ke kuka akanta bazata.iya tuna yawansu ba don ita dama Allah bai dora mata kule kulen samari ba amma yau kamar almara sai gata a wata wawakekiyar qofar jarrabawa,ta saki ajiyar zuciya sanda ta iso bakin get din gidan malam sani ya budw mata qofa ta shige ta tsaida motarta bayan ta daidait parking,a gefabta taga motar farida hakan yasa ta gane sun dawo,ta saki doguwar ajiyar zuciya tafito daga motar ta kulle ta tunkari falon nasu
MRS MUHAMMAD BELLO
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻📝📝📝
07066139278
[10/16, 2:39 PM] +234 706 914 1005: 8:39 pm
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Wa yasan gobe?
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
▶8⃣
Bata nemi kowa ba kai tsaye dakinta ta nufa ta shiga wanka ta hado da alwala ta gabatar fa shafa’i da wutirinta tunda tun a gidan ya ahmad tayi isha,ta dauki kimanin minti goma ta azakar dinta sannan ta ninke sallayar ta sauko qasa ta nufi dakin ummi,ummin ta amsa sallamar bayan ta mata sannu da zuwa ta sanar da ita anty hafiza na gaisheta ummi tace “kinje kenan?”ta gyada kai tace”bayan fitarku ne ummi gidan shiru ba dadi😒shine nace bari kawai na leqa biyu”har ta bude baki zata mata fadan fita ba tare da ta tambayeta ba sai kuma ta tuna fadilan ba gwanar yawo bace banza bata kai zomo🐇kasuwa,ta tabbatar ba’a banza ta fita ba,dama farida ce to tasan hali,sai kawai tace”ina amsawa”fadila tace “ummi bari na wuce na kwanta na gaji”ta dubeta tace”au yau ba zaki jirayi dawowar abban naki ba?”ta gyada kai”um ummi abincinsa na dining area na parlour dinsa ni dai sai da safe”ta miqe ummi tace”Allah ya tashe mu lpy nima wanka zan shiga ki jamin qofar”tana qoqarin fita taji ummi ta kirayeta ta dawo da baya tana amsawa”bayan fitata wa ya kawo kaya a baqar leda suna nan a parlour?”,sai a sannan ta tuna da kayan da aliyu ya aiko a kawo mata,ta sunkuyar da kanta😔tace”ummi yaya aliyu ne ya kawo to sai na mantasu a parlour”ummi ta gyada kai tace”yayi miki kyau,fadila ki maida hankalinki fa,gidan kishiyafa zaki,ba ke kadai zaki zauna ba ballantana kice zaki dinga abinda ranki keso……ta danyi jim,jin fadila bata ce komai ba ta Dora”sai kije ki debe tun kafin abbanki ya zo ya gani ranki ya baci”ta qarasa maganar tana shigewa bandaki ,jikinta a salube ta fita,ta isa inda ledar take ta dauke ta tayi sama da ita
Hannu biyu ta tallafe habarta da su ranta a jagule,yaushe su ummi zasu fahimci tsananin da take ciki?,har ga Allah tana son ali yana burgeta a rayuwarta komai nasa yana bata sha’awa,yau da za’a ce aliyu yana sonta a sai ta fi kowa farinciki,to su su ummi suna tsammanin ita ke son kawo cikas,ta share hawayenta ta daga ledar tana zazzage kayan ciki
Bandir ne na ‘yan dubu dubu sababbi fil a miqe💶 guda hudu sai chocolate packet hudu manya🍫,sai turare guda hudu designers,sai awarwaraye banguls da zobensu na gold guda biyu💍,sai agogon hannu na azurfa guda biyu shima,komai tsada ne da tsari,cikin zuciyarta take fadin”yadda Aliyu na ke da kyau da tsari haka everything na shi yake,yadda aliyu yake special haka komai daya dangaceshi yake,komai nashi special one ne hakanan abun ban sha’awa ne,ina ma aliyu zai soni?,ina ma Aliyu zai rufeni da da so da qaunarsa da na zamo daya daga cikin mata masu tsananin sa’a a rayuwarsu”hawayen tausayin kanta suka ziraro mata,ta dauki daya daga cikin rapper din kudin tana shinshinawa,ta lumshe idonta don qamshin turarensa kawai ke tashi a jikinsu(haka aliyu yake saboda yadda turare ya zaunar masa a jikinsa duk abi da yayi gogayya da shi sai yayi qamshin turarensa)
Farida ta shigo dakin da sallamarta,fadila ta amsa tana janye mata kayan dan faridan ta samu gun zama,cikin tsokana faridanke tambayarta kayan,tace”duba ki gani ya Aliyu ne ya kawo dazun ki zabi abinda kike so(haka ummi ta koyar da su tun suna qanan idan daya ya samu abu to zai raba tare da dan’uwansa )ta yaba kayan sosai ta dauki turare biyu tace sun isheta,fadila tayi tayi da ita ta qara taqi,ta turo mata kudaden gabanta hadi da yage ‘yar paper da taga anyi rubutu a jiki kamar haka”kiyi hidimar biki idan basu isa ba zansa a adado miki”tadan tabe baki ☹cikin ranta tace”nafi buqatarka da su da zaka gane hakan””farida ga kudin hidimar bikinan inji aliyu idan basu kai ba a mishi magana”farida ta dauki kudin tana juyawa tace”har dubu dari hudu😳”fadila tave”hmmm ni da ua ban su nasan mai zanyi ma da su”farida tace”ni da anty hafiza munsan me zamuyi miki da su,ko iya wadannan ma sun isa ya sallameki”ta miqe tana cewa”bari in nunawa ummi,sai da safe sister”ta fita taja mata qofar tana ayyana abubuwan da zasu yiwa fadilan masu amfani
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Duk cikin satittikan da suka biyo baya cikin hidamar shirye shiryen biki suke,ita kam fadila bata da wani zabi na kanta,da zasu yarda ma da sun qyaleta haka don bata da sha’awar yin komai kama daga gyaran jiki zuwa kan duk wasu events da ake yi yayin bikin aure,don duk abinda zatayi wanda za’ayi don shin abun bai dada shi da qasa ba baya gabansa hakan yasa itama ta tsani komai,sai da anty hafiza ta zaunar da ita ta nuna mata duk abinda tayi idanun👀 duniya na kanta,zata tona asirin kanta da kanta ne sannan ta amince da tsare tsaren da suke zuwar mata da su,hatta magunguna tanajin farida na sha da qyar tana mita ita kam nata ido👀karba kawai take ta daddake tunda tana ganin babu wani amfani da zasu yi mata
To fa masu karatu ga fadila Abbas na shirin shiga gidan Aliyu salim maitama,gidan da aka gargade ta da shigarsa tun kafin ta kai ga shigarsa,shin mene shawararku gareta????
10:34 pm
07066139278
✍🏻✍🏻✍🏻📝📝📝📝
🌺🌺🌺
[10/16, 12:25 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Wa yasan gobe?
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶9⃣
Ranar laraba 12 ga watan biyu aka soma da kamu👰🏻,ba dan qaramin kyau amare sukayi ba,kai kaso kazo kaga yadda kamun ya qawatu matuqa da gaske,an zubar da dukiya sosai kasancewar wannan ne bikin ummi na farko kuma na qarshe,tamakar tagwaye haka suka zama komai iri daya suka sanya hatta da awarwaro da zobe
Kasancewar abban su babar bare umminsu bafulatana sai aka raba abun biyu shigar farko sukayi shiga irin ta bare bari cikin wata lafiyayyar lafaya wadda kudinta ya tasamma kimanin dubu ashirin kamu aka musu irin na bare bari sosai sannan daga bisani kuma suka canza shiga irin ta fulani cikin kayan saqi nan ma aka musu kamun fulani,shida na yamma aka tashi bayan sallar magariba kuma masu kidan qwarya suka zauna zuwa goma na dare
Irin cikar da gidan yayi yasa su fadila haqura da zaman gidan su da qawayansu suka koma gidan maman zainab maqociyarsu ce kuma babbar macace don idan batayi sa’ar umminsu ba to zata girmemeta,zainab din yarinyarta ce kusan sa’ar farida ce
Fadila nabin kowa da ido don a yanzu kam jikinta ya qarasa mutuwa murus,bata da kuzari ko qanqani komai cikin dakiya da qarfafa mata gwiwa da anty hafiza ke mata take yinsa,ga wani ciwon kai da ya addabeta,ta riga ta saba ita ko da can bata saba da shiga hayaniya ba ko bikin dangi ne bata kwana sai dai farida ta kwana ita kam komai dare zata dawo gida ne,ko hayaniya tayi mai yawa to yanzu kanta zai fara ciwo ko qirjinta ya dau zafi
Kwance take kan gadon zainab din ta juya ma tarin ‘yammatan dake dakin sunata hayaniyarsu baya ta fuskanci fuskar gadon,yawancinsu duk qawayen farida ne sai ‘ya’yan ‘yan uwa,farida tayi sallama ta shigo dakin ita da aminiyarta ruqayya hannunsu dauke niqi niqi da ledoji na take away wanda aikin mubarak(angon faridan) ne shi yace a tazo suje tayi musu take away,ta zube musu nan hayaniya ta qaru kowacce tana daukar tata,ta iso kan gadon hannunta da ledoji biyu,ta dan taba qafafun fadilan tace”sister tashi”fadila ta miqe daga kwanciyar ta zauna tsakiyar gadon ta tanqwashe qafafunta tana kallon farida,qasa-qasa muryarta tace “yayaa ga abinci ki daure ki ci sai ki sha maganin ciwon kan ko dan idon mutane ida yaso sai ki kwanta ki huta,”tana maganar tana bude ledar da ta shigo da ita din ta tura mata gabanta,ta sake bude dayar ledar tana cewa”ga dinkimmu na dinner din gobe ta can muka biya da mubarak muka maso”ta soma fito da su
Wani dan ubansun material ne mai azabar kyau wanda ko makaho ya shafa yasan cewa ba qananan kudade aka sa aka siyeshi ba,milk ne da ja(milk and red),ita kanta faridan da tunda ma anty hafiza ta bawa ya ahmad da zashi india ya siyo musu bata ganshi ba sai yau da aka karbo dinki faridan ce ke zuzutashi sai yau taganshi yayi bala’in tafiya da ita ,ta jinjina kak tace”an gode miki sister farida”farida tayi dariya tace”ai wannan aikin anty hadiza ne ragowan su earings ma da zamu sa suna gunta”fadila tace”Alla ya saka mata da alkhairi”ta jawo ledar da faridan ta bude mata,gasashshiyar kaza ce🍗 da hanta wadda aka mata gashi mai ruwa ruwa da albasa,shawarma🌮 sai kuma ice cream roba biyu🍧🍧,tayi murmushi ta kalleta kafin tave komai faridan ta rigata magana”ke dai yaya ki ci kawai,kina tsammanin bansan abinda kime boyewa bane a dan qaramin fridge dun gefan gadonki ba wanda ke hanaki maida hankali kici abinci?☺”sai dariya ta kama fadila,lokaci guda kuma tausayin rabuwa da junansu da qaunar ‘yar uwarta ya kamata,lallai ne dan uwa rabin jiki,naka nakane qwalla ta ziraro mata ita ma faridan sai ga qwallar,dai dai nan rumasa’u(yar qanwar umminsu ce(ta shigo dakin,ganin haka ta saki dariya”😄a’ah kaga twince sisters wato ku daga fara biki har kun soma gunsheqen kukan rabuwa tun kafin aje ko ina?”yawan hayaniyar da yammatan keyi ya hanasu jin abinda take cewa,farida na dan murmushi ta goge hawayanta,ita kuwa fadila da yake sa’annin juna ne saita harareta”to ina ruwanki ‘yar sa ido?”cikin dariya tace”🤗a’ah Allah ya huci xuciyarki bani na kar zomon ba ratayar ma ba’a bani ba ni ummi ce ta turoni tave inzo inga kinci abinci don tasan hali”ta fada tana leqen ledar gaban fadila,fadila ta muwa lanqwashe ledar,tana cewa”kuma duk kwadayin mutum bazaici ba ba?”cikin son zolaya rumasa’u tace”haba aminis ni dake fa bata baci”fadila ta zaro kazar ta nannde mata tace “ungo a banni na hadiyi yawu”tafice tana dariya,farida da tun dazun take ta musu dariya tace”hoo 😂yaya ruma akwai zolaya da abun dariya yanzu fa idan kika bibiya itama bacin zatayi ba baiwa wani zatayi”fadila tayi murmushi tace”ta ji dai
Shi dai gundura kawai”
Da taimakom farida fadila ta saki jikinta sosai don har ta samu ta shige cikin ‘yammatan aka shiga hirar harda ita,hakan ya taimaka mata ta samu sauqin takurar da zuciyarta tayi sosai kafin dare yayi kowa ya kwanta
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Washegari gidan kwalliya anty hafiza ta debesu suka tafi,cikin wasu awoyi aka qalqale wa kowacce fuskarta da kwalliya ta garari dubu ashirin aka ajiyewa matar,itakam anty hafiza tsayawa tayi tana kallon sarautar Allah kyansu ya qara bayyana qarara,daga baya ta kasa ahiru sai da tace”ashe haka kuje da kyau yammatan ummi musamman fadila ashe hasken fata kawai za’a nuna miki?”dariya dukansu sukayi har da ita mai kwalliyar wadsa itama tinda tayi musu take kallo fuskarsu tace”dama ai ba fari ne kyau ba don wani choculet din yafi fari kyau nesa ba kusa ba”
sai bayan idar da sallar magariba aka kammala kwashe yammatan zuwa royal tropicana,amare sun gama shirinsu kayan kam sun amshi jikinsu don tamkar saboda su aka halicci yadin da shi kansa dinkin,kiran mubarak ya shigo wayar farida yana sanar mata isowarshi qofar gidan,ta kashe wayar fuskarta na bayyanar da damuwa ta kalli anty hafiza da ta luea tun dazun ta kasa zama sai kaiwa da komowa taketana kiraye kirayen waya ta fuskanci akwai abinda suke boye mata,farida tace”anty ya za’ayi gashi har mubarak ya iso?”hafiza vikin damuwa ta kalli fadika tace”fadila kibi motarsu farida kawai kije”ba abinda tace mata kawai tabi bayan farida suka fice,ko ba’a gaya mta ba itafin ai ba yarinya bace qarama ta sani koda wasa aliyu ba zuwa zaya yi ba,ko da yazo ma tana fargabar kada ya yi mata wani abun da zata kunyata a idon duniya,shi yasa tun usuli ta so su shiryawa farida dinner din ita kadai abunta,mubarak ke driving motar da kansa don haka suna fitowa da kansa ya bude mata kujera mai zaman banza ta kusa da shi ta shiga ya rufe sannan ya koma ya shiga nasa gun,ita kuwa tana baya ita kadai,tunani ya cika zuciyarta tana sha’awar soyayyar farida da mubarak dinta,yana matuqar nuna mata qauna da kukawa ko da a gaban waye,tunda aka fqra hidimar bikinannan kusan tare suke jigilar shi da ita,duk da tana da moyar ta amma ba ruwansa da wannan,
da yake basu fito da wuri basun dan bata lokaci gun jira jiran da fadila ta samasa jiran gawon shanu don tasan ba komai bane face jiran tsammanin zuwan Aliyu ya dauketa ita damata ahekara da sanin ba zuwa zaiyi ba,a farfajiyar farko kafin ka shiga tafkeken hall din mubarak yayi parking,saiga anty hauwa anty hafiza da tuni ta iso sumayya rabi’ah da ‘yan biyu,fuskar anty hawa da alamun bacin rai ta kalli su mubarak”kama hannunta ku shiga su fadila zasu shigo daga baya”yace “to”ya kama hannun farida su sumayya suka take musu baya su da wasu yammata cikin anko codelace milk dake tsaye bakin qofar ahiga hall din,cikin son kauda ahitun da gun yayi antu hauwa tace”gsky hafiza mun tsinci dami a kala fa,irin wannan tsaleliyar budurwa haka?”duk sai da ta basu daroya,anty hauwa ta budewa fadila motarta gun kujera mai zaman banza tace zauan fadila,wayarta ta zarota shiga kira”muna qofar hall inda ka shanya mu muna jira”ta fada cikin fusata sannan ta kashe wayar,sundebi kusan minti ashirin suna zaman jiran har fadila ta qosa sosai tayi kamar ta nemi alfarmarsu akan su qyaleta ta koma gida tana ahirin yin hakan waau jerin gwanon baqaqen motoci motoci suka danno kai cikin harabar gurin,anty hafiza ta sake feshe fadila da turare sannan duk da qamshin da take zubawa fuskarta fes take kamar yanxu aka gama kwalliyar sai alamun damuwa da suka bayyana a fuskar anty hafiza ta rada mata”be free and comfortable you have to invite happiness in you face even its not true, zaku shiga cikin mutane ke zaki bawa kanki confidences na zaki zaki zama amarya kamar farida da mubarak right?”fadila ta gyada kai tana qoqarin daidaita yanayin din fuskarta,ta maida turaren cikin hamarta tana cewa sai kun shigo “ta wuce ciki,daganan tana hango anty gauwa yadda ta nufesu tana wurwurga hannu da alama masifa take nasa shì kuwa ya yi kicin kicin ya hade ransa sanye yake cikin wata dakakkiyar shàdda milk colour yar ubansu komai na aliyu classic ne yayi wani shegyan kayu dinkin babbar riga da yar ciki ne da wando sai takaminsa half cover na kamfanin mister,daga bisani tafa tana nuno masa ita da hannu itama ta juya tayi shigewarta
Duk takunsa daya shike qaŕa bugun da zuciyarta keyi ta dauke idanunta ta ditasu kacokam kan sitiyarin motar kunnanta na jiyo mata takun tahowarsa gun hancinta na shaqo mata daddadan turarensa,sau biyu taji yayi knocking glass din motar bata da zabi illa ta fuskanceshi sabida haka ta dago razanannun idamunta ta saukesu cukin nasa idanunta da nashi suka hadu gu guda👀,zuciyarsa taďan kai ta jawo kadan duk da yaga kyaunda tayi amma sau yaga batakai kyan da samira ta masa ba,cikin halun ko in kula yace mata”les go”fuska a tsuke ya juya😠,ta bude murfin motar tana qoqarin fitowa ta gurde ta tafi luu zata fadi saboda yadda jikinta ke rawa,yasa sangalalun hannunsa na hagu ya tare ta sannan ya miqar da ita tsaye ya saki tsaki yayi gaba,ta yi qoqarin daidaita natsuwarta sannan ta bishi suka jera
Shigarsu mawaqin ya sauya kidan zuwa wani take na musamman aka bisu kuma da abin qyalli ana fesa musu🎊 ga gayyar yan rakiya a bayansu da suka sasu a tsakiya,suna zama aka maida waqar da shahararren mawaqin nan yayi musu nura m inuwa(anyi aure biki na’ya’yan girma ‘ya’yan alhaji abbas bashir sunyi aure)aka dan cashe kadan sannan m.c ya amshi abun magana🎙ya soma zugasu kamar yadda aka sani sunawa amare da angwàye,lokacin mubarak da aliyu suka gaisa cikin mutunta juna,mc bai qyalesu haka ba har sai da ya samo musu kyautar mota daga gun Aliyu mubarak ya bada dubu dari hajiya shatu yayr alh salim maitama ta basu wata qaramar motaŕ dangin mubarak kuma suka qara musu da dubu hamsin,tunda suka samu abinda suje si suka bude fa bakin gangat zamar da bikin qayatacce a idon duniya,biki kam ya qawayat ta kuma nishadantar musamman farida da angonta,don da aka kira amare da angwaye su shigatsu sukayi filin rawa suka taka sosai itakam ita da aliýu sun tsaya ne kurum suna facing juna ita kanta na qasa ma aka musu ana cikin yi aliyun yaja hannuta suka koma sit din su umarni ma yabi da tafiyarsa zaiyi ya barta ita kàdai tsaye a filin sai akan kujerunsu aka qarasa musu liqin,wayrsa ta dauki wani daddadan ringin,ya daga yar kyakkyawar wayar a kunnensa sannan u
yace”oh baby I already told you sai na fara zuwa gun daya dinner din ko idan kuma nabar nan din can zan taho tunda na da wuri zaku tashi ba……ok take care”ya kashe wayar yaja dan siririn tsaki
Farida da mubarak ne suka soma yanka nasu cake din sannan dan gaa kadan nasu fadila mai hawa shidda ne milk sannan red milk sannan red haka haka har step shida🎂,bayan su farida sun koma aka kirasu gabanta na ta duka,suka tsaya gaban cake din maimakon ua fara daukar wuqar saboda tsorata ita tà fàra daùka akasa tagi mc yace yau zamuga sabon salon soyayya uwargida zata fara ci da mai gida wata wuta tayi tsiri saman cake din lokacin da tasa yar qaramar wuqar tana yanko cake din hakan ya sake sa jikinta rawa tadan tsorata
duk da ta saba gani ammada yake a rude take sai hakan ya sake duburburtata,tayi qasa da idonta sanda ta kai cake din bakinsa ,ya kuwa basar ya sa bakinsa ya karba cikin mugunta ya hada da hannayenta ya datse mata sutaji zafi sosai amma kasancewar tasan da gayya yayi sai ta basar kamar baþa ji zafin ba,bai damu da qanqantar bakinta ba ya yanko qaton cake da tasan yafi qarfin bakinta ya danna mata duk da haka itama tayì namijin qoqarin lalubo yatsunsa ta ganyara masa cizo maimakon ya cire hannun nasa sai kawai ya birkitota ya mannata da jikinsa ya maqure ta sosai duk a zuwan rungumeta ya yi ya sanya bakinta cikin nasa yana tsotse butter din da ta bata dan qaramin bakinta,duk gurin ya dau sowa da tafi masu hotuna📸 da video🎥 suka yo ca suna aikinsu saidai fafila ita tasan azabar da take ji domin tsotsar mugunta ce su kuwa a tsammaninsu tsantsar soyayya ce,ta tabbatar lebunanta idan basu tsage ba to daf suke da au tsage din,kunya da takaici suka dabibayeta cikìn dinbin jama’a saboda rashin kunya irinta aliyu ya mata irin wannan abun?ya saketa sannan ya jata zuwa gun zamanta ya zaunar da ita ya dan ranqwafa mata yace”matuqar idan nayi miki abu kikace sai kin rama u wil b suffer”yana gama gaya mata ya juyà yabi ta cikin mitanen ya bar halla din sai jiyowa tayi ta cikin macros phone mc na sanarwa cewa ango yace a masa afuwa kayansa sun bavi zaije gida ya canza yana kuma yiwa kowa fatan alkhairi godiya da kuma ban gajiya amarya kùma tadan daure taje zasu tafi,kasa tashi tayi kuka kurum take na takaici da kunyasam Aliyu bashi da kunya ya rasa tame zai rama saita irin wannan hanyar?idan su sunsan abinda ke zuciyoyinsu ai ragowar jama’a basu sani ba ko?,harsai da text din anty hafiza ya shigo mata kamar haka sannanta iya tashi”malama kukan ya isa haka ki taahi ki bishi yana wahan hall din yana jiranji isan kùna so kike ki tona abnda muka binne to bismillah”ta miqe tana kare fuskarta da purse👛ta fice
Wannan saurayin da ta saba ganinsu ko yaushe da aliyu shi ya fito ya bude mata gidan baya ta shiga sai da ta zauna ta lura da aliyu ahima zaune gefanta bai ko kaeta ba yavi gaba da abinda yake bako motsin mutum cikin motar sai qarar fitar ac har suka qaraso ni’ima guest place,motocin sukayi parking na ciki suka firfito suka tsaya jiran fitowar Aliyu tuni drivan ya fice aliyu ya zube wayoyinsa bayan ya kashesu yà fice shima a motar ya kulleta tare da sa security
Wucewarsu cikin hayaniya ta tawagar ango yasanya gun komawa tsit kamar yadda yake ,tun tanajin tsoro har ta dake tana ta addu’o’i,a hankali abinda ke wakana agun ke isowa kunnuwanta ta hanyar lasifiqan da suke amfani da shi,sunan samira da ta ji hade da na Aliyu shi ya tabbatà mata gun bikinsu ne,wani kishi mai zafi ya shaqeta,ta jingina sosai da makarin kujerar tana ambatar sunan Allah tà lumshe idanunta tana ci gaba da sauraren abinda ke wakana cikin gun dinner din,gajiya tsoro kishi da takaici suka mata taron dagi, tun bata gaji ba har ta sare da zaman gashi ba damar fita bare tayi tafiyarta yabi ya kulle matar,zaman jira na kìmanin awa uku tayi a motar sannan ta fara hango tawagar aliyu
Mrs muhammad bello ce
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 12:29 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Wa yasan gobe?
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶🔟
Tamakar ya manta akwai wata halitta da ke cikin motar ya shigo abinsa driver yaja motar suka bar gun,ganin haka yasa tayi kamar ta tuna masa su sauketa a gida fa sai taga ai ya ma raina wayonta duk inda zai kaita ya kaita,ganin sunyi hanyar gida yasa ta sake tabbatarwa yana sane kenan
A daidai qofar gidansu driver yayi parking yana tsayawa tasa hannu ta bude motar tayi ficewarta ba tare da tace masa kanzil ba haka shima baice komai din ba dama kuma tasan ba cewar zaiyi ba bata kuma dada ta da qasa ba maganarsa,ahankali take tafiya saboda kasala da bacci ga takaici da ya rufeta ya dan bita da kallo yana mamakin haqurin da tayi bata ce masa komai ba ua juya ya bawa nasiru umarnin ya ja motar su wuce
Kai tsaye gidansu zainab ta tafi don kwanciya kawai take buqatar yi a halin yanzu,dakin da aka basu ta tura ta shiga wasunsu yammatan sunyi bacci wadanda suka rage kuma kowacce na maqe da waya tana tadi kamar yadda farida tabi sahu itama ganin shigowar fadilan ne ya sata katse wayar ta dubeta tace”ya naga kin jima sosai haka”sai kuma ta danyi murmushi😊 tace”um mace da mijinta meye nawa?”,tabe baki fadilan tayi☹ta jawo jakar kayanta ta dauki towel ta kwabe mayan jikinta tadaura ganin haka yasa farida ta gane tambayarta bata da amsa kenan,ta sake dariya bayan taga shigewarta toilet tace”ya fadila tawa……miskili kafi mahaukaci ban haushi
Washegari ummi tayi mother’s day,cikakkiyar shigar hausawa sukayi ranar don hatta mayafi na atamfa sukayi,kwatsam sai ga momin Aliyyun a gun da mutanenta sunzo wai za ta yi wa fadila nata kamun,gun yayi armashi sosai don kidan qwarya akayi zalla bayan lecture ga amare wadda aka shafe fiye da awa ana musu inda daga baya kuma gun ya karade da waqoqin da irin nasu mamman shata sani sabulu dan qwairo dan indo audu wazirin dan duna da sauransu suma iyaye aka tuno musu da da tunda dama ranar ta iyaye ce,
Washegarin ranar sukayi kuma wuni a gida,wata Washegarin kuma ta zamto ranar daurin aure,daurin auren da ya tara jama’a na ban mamaki garin ranar unguwar ba masaka tsinke,jama’a ne tako ina na nan qasar dama maqwaftan qasashe har da na qetare
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Misalin takwas na daren ranar daurin auren fadila da farida na durqushe gaban umminsu sanye cikin atamfa super England lemon grean ce da pink sai adon fari dinkin riga da zani an nannade masu jikinsu da wata danyar lafaya fara tas mai dige digen pink a jiki,dan kunne da sarqa sai banguls duk na azurfa ne ,babu abinda ke tashi jikinsu sai wani rantsatstsan qamshin turaren humra yar gasken ta bare barin usuli
Da fari ummi kasa magana tayi saboda tausayi da qaunar yaran nata sai jimamin rabuwa da zatayi da su,daga baya ta daurw ta musu yar tunatarwa saboda ita damacan koda yaushe mai dora yayanta ce kan tarbiyyar zaman gidan aure ce,ta kammala nasihar tata da addu’a da fatan alkhairi a garesu,umma A’i yayar ummi ta leqo tana cewa su fito angwaye nata jira fa,wani kukan suka sake saki suka ruqunqume ummin suna neman yafiyarta,tace ta yafemusu burinta kawai su zauna da mazajanasu lafiya kada taji kada ta gani shine farincikinta,ana riqe dasu amma suna waiwayowa suna kuka idanunsu a kanta kamar zasu qwace su dawo,itama sai ta kasa jurewa suka sata qwalla duk sai suka karyar da zuciyar kowa sai muhammad shima ya dauki masa kukan da ya bawa mutane tausayi kasa zama yayi yabi yan uwan nasa yana ta kuka kowa ya tausaya mai saboda tunda ya taso suna tare da su ya saba su ya saba gani gashi yau an dauke masa su duka biyun
Cikin wata arniyar mota qirar sail akace a shiga da fadila suna qoqarin sa farida a dayar ta riqeta gam tace bata yarda ba saidai a hadasu a mota daya,ganin da gaske take yasa suka sasu a mota gudan,lokaci guda motocin suka tashi suka kuma jeru reras bisa titi tamkar motocin rakiyar shugaban qasa,duk da cewar darene amma duk inda suka bi sai sunja hankalin mutane saboda kyawun motocin,kai tsaye yahaya gusau suka fara nufa inda anan gidan farida yake,a nutse suke shiga gidan saboda ba yara ko daya sai manya da yammata tun la’asar aka kai yara suka gama gani aka dawo da su gida tsarin gidan farida gwanin sha’awa ya burge jama’a da dama atsare ginin yake kana kallonsa kasan sai da aka sa nutsuwa aka fidda masa fasali
Sai da suka ajiyeta a bedroom dinta su umman abuja(itama qanwar abba ce)suka sata tayi addu’o’i sannan sukayi haramar tafiya,fadila na nanuqe da farida har yanzu kukan suke sunqi sakin juna harsai da umma a’i tq fusata dama akwai lafiyar fada ta hau sababi tace”ku kunga bamason isknci,kanku aka fara aure ai kowa da haka ya sabatun dazun ake fama da ku ki fito kin noqe to kada ki sake na qaraso dakinann baki fito mun tafi ba”suka sake rushewa da kuka 😩ganin lallai dai rabuwar za suyi,mama sadiya(abokiyar wasan abbansu ce)tazo ta kama fadilan tana rarrashinta tafito da ita tana jiyo kukan faridan kamar yadda itama take jiyo nata
Cikin nasarawa G.R.A motocin suka kutsa qofar wani katafaren gida suka tsaya,kewaye yake da dogayen kuma qawatattun katangu da fitulu masu tsananin kyau makeken get wanda saboda tsananin girmansa sai kayi tsammanin qofar shiga garice suka tsaya,duk yawan motocin sai da kyakkyawar harabar gidan ta lamushe su,sai ma suka tashi yan tsurut harabar wadace ta take da haske tamkar rana sai ka rantse da Allah rana ce ba dare ba
“Kai jama’a yanzu kamar ba za’a mutu ba?,wannan gidan dai…..inda ni kadai na shigo wlh ihu zan sak na ce gidan yankan kai nazo,kamar ba mutuwa a duniya?”kakarsu fadila hajja gana mahaifiyar abbansu ke wannan santin,su kam me za suyi idan ba dariya ba😂,sai da suka nufi sashen fadilan masu yaba kyau da tsaruwar gidan suka dadu,ginine wanda kaf garin kano baifi ka qirga masu irinsa da hannu ba,ginin part hudu ne sai boys quarters makeken lambu swimming pool gun wasanni kala kala,basketball table tennis,football boxing,tokwand da sauransu baya ga haraba biyu da gidan ke dauke da shi harabar farko dakin mai gadi da parking space take dauke da shi,sun dan tarad da jama’a a gidan acan part din samira suna jira a kawota,ba abinda ke tashi sai kida da yan uwanta suka ware mai barazanar fasa kunnuwa ganin haka hajja gana ta hana su koda guda suyi ta shiga gidanta da addu’o’i bakinta
“🤔wai ni Allah wannan gida naki fadila idan baka da qarfin imani zai iya saka ka manta Allah “gaba dayasai da hajja gana ta sake sa kowa dariya a gun😂 duk da suma sun lalace ne gun kallon tsaruwar gurin nata falone two in one wanda kan ka shigo main falo akwai varender a farkon sashin sannan ka tadda falon,dukka falukan sun qawatu da kayan qyale qyale na falo babba da qaramim falon kowanne ansa masa abinda falo ke buqata ba abinda aka rage masa,acikin main falon anan daga hannun damanka matattakala ce masu fadi guda hudu zaka taka ka haye gun dining wanda ke daume da wasu hadaddun labulaye masu kacar kacar anan qofar kitchen s dinta take wanda duk wayewarka sai quyancinka ya fito,gaban gun dainin kadan wata yar qoface mai kyau ta glass wadda ke dauke da corridor shimfide da lallausan carfet da hadaddun labulaye dakunan bacci ne guda uku daya furniture ne yan Saudi pink da purple daya dakin kuma yan italia ne ash da pinch yayin da daya dakin kuma aka malaleshi da carfet da manyan tuntuna aka zagayeshi da labulaye masu shegen kyau aka rarrataye mata kayan kaba da kumbuna tamkar jeran qauye sai wani dan gado irin na qauye mai rumfa amma wannan an zamanantar da shi kowanne daki da toilet dinsa sai public toilet dake varender da kuma wani a falo,daga kitchen akwai qofa da zaka zagaua bayan part dinka(ventilation)wanda akayi dan qaramin lambu da wata rumfar bunu sai yar qaramar qorama da aka qirqira da doguwar kujera ta siminti qwaya daya,a falo aka ajiyeta,ido kam ya raja’a da kallom kyawun gidan,sanyi a c da qamshin freshener ya game ko ina ga qamshin sabunta,gidan ya kaure da hayaniyar yammata dake ta zuba santi da yiwa kansu fatan samun koda makamancin wannan gidan ne,
Wata hayaniya da suka ji ta kunno kai gidan ya saka su yin shiru suna sauraron daga ina take?,guda ce da aka cakudata da kirari iri iri hafe da habaice habaice”taka lpy uwar gida sarautar mata,isaahshiyar mace a gidan aliyu maitama ,eh anqi Allah yaso,qaryar mahassada ba zasu iya da ke ba wallahi sama ta yiwa yaro nisa saidai ya tada kai yayi kallo,an buga da ke an barki wlh yarinya ko yar sankin santanbul ce kinfi qarfin ta kara da ke saidai tayi iya nata salon ta haqura,”
hakane ya tabbatar musu masu rakiyar samira ne mama sadiya suka hana kowa fita har suka qaraci ahewarau da shegantakarsu suka shige da ita,zuwa wani lokaci kuma sautin sabon kida na kujerar tsakar gida ya karade gidan tamkar wani club,Allah ya kayuta abinda suka ce kenan
Qarfe tara aka soma kwashe yammatan ana maida su kafin tara da rabi gidanta babu kowa,kadaici ya kama fadila,tsoro ya cikata,bata jin sautin komai sai hayaniya da kidan yan uwan samirah,zuciyarta tayi rauni sosai tunanin irin zaman da zatayi a gidan take,Aliyunta bai sonta,kishiyarta kuwa salon da ka rakota da ahi ya tabbatqr mata ba zaman lafiya tazo ayi da ita ba,hawaye ya balle mata😭 zuciyarta kaar tayi tsalle ta fito saboda zullumi da radadin da take mata
Horn din motoci ya sake cika gidan,ta daga kanta ta kalli agogon bangon dake falon sha daya na dare ya nuna mata🕚 ba shakka angone da abokansa suka shigo zuciyarta ke gaya mata haka,sannu taji hayaniyar jama’ar na raguwa hakan ya tabbatar mata ana debe su ne tafiya suke,ga tarin mamakinta sai ta jiyo muryar samira na cewa”ku gaida gida na gode Allah ya huta gajiya,ina jiranku gobe da safe,kuma wlh kada ku yarda sai sun vika muku kudin siyan bakin”fadila ta jinjina kai tana cewa cikin zuciyarta lallai ba shakka kowane tsuntsu kukan gidansu yake
Cikin qanqanin lokaci gidan ya sake zama tsit,ba komai cikinsa sai hasken fitilu daya gauraye da kukan tsintsaye da kuma gyare jefi jefi,haka ya sake assasa tsoron dake zuciyar fadila ta runtse idanunta gam😣tana ambaton sunayan Allah hadi da addu’o’in tsari,sannu a hankali taji idanunta da jikinta sun fara nauyi ,gajiyar kwana da kwanaki suka fara sauko mata,taji bata da buqatar komai illa kashingida,ta zame ta dogara gwiwar hannunta a hannun kujerar,tsananin gajiya yasa bacci har ya dauketa bata sani ba💤
ASUBA TA GARI AMARYAR ALY😊😊
Firgigit ta farka kamar an tasheta,ya zame mata jiki tun a gida assalatun farko take tashi tayi yan nafilfilu kafin assalatu na biyu daga nan idan ta idar tayi baccin mintuna idan tana da lacture ta shiga kitchen ta shirya breakfast,yauma gajiyar bata hanata tashin ba saidai ta sabawa lkcn da ta saba tashi sai kiran a kiran sallah na biyu ta tashi,cikin kasala ta miqe don har yanzu tanajin nauyin jikinta tayi miqa hadi da salati idanunta suka kai kan wata farar leda babba mai dan duhu guda biyu tsoro ya darsu a zuciyarta ta katse miqar a iya saninta sanda zata kwanta babu ledar a gun to ya akai ta samu?cikin sanda ta isa inda ledar take kamar wadda akace za’a kama,saidai tunkan ta bude ledar qamshin turarensa ya ziyarci hancinta,hakanne ya bata amsar tambayarta lallai aliyu shi ya shigo da ledar tayi mamakin yadda har ya shigo ya fita bata sani ba,
Ta bude ledar gasashshiyar kaza ce wadda akai wrapping dinta guda uku sai ice cream da ya gama narkewa saboda an ciroshi daga ma’ajiyarsa sai fresh milk manyan roba har uku,sai yoghurt shima roba uku tayi ajiuar zuciya ta mayar da kayan,kasala ta sake kamata taja da baya ta koma bisa kujerar ta zauna tana aheqar daddadan turarensa tamkar yanzu yake a gun,ta shiga hasashen fuskan aliyun a cikin wadannan awoyin da yake angon mutum biyu,kishi ya taba zuciyarta,tafan bata waau lukuta a zaune ta kasa tabuka komai sannan ta miqe ta lalubi corridor din nan ta zabi bedroom daya ta shiga,tana alwala tana qarewa tsaruwar toilet din kallo,tabbas dole hajja gana tace kamar ba za’a mutu ba,bayan ta idar sa sallar ma tana lazumi dakin taci gaba da bi da kallo tana yaba irin namijin qoqari da iyayenta da yayansu Ahmad suka yi,bata kammala ba wani daddan bacci ya rinjayi idanunta nan bisa dardumar sallarta
Hasken rana da ya soma shigowa ta window yana taba fuskarta shi ya farkar da ita,da addu’ar tashi daga bacci ta miqe a bakinta ta dubi agogon dake ajjiye kan bedside ya nuna mata goma da minti sha biyar na safe batayi mamakin awanni data shafe ba tana baccin ba,toilet ta shiga ta kunna water heater dake manne a kusurwar bandakin cikin mintina qalilan ruwan ya tafasa ta kunna shower ta daidaita zafinsu ta shige kwamin wankan🛀🏼,tsaf ta shirya cikin atamfa mai zanan manyan ganye mai kalolin pink da ja sai light blue,dinkin da ita atamfar kanta tayi.masifar karabarta duk da ba wani make up tayi ba hoda ce kawai sai man lebe da kwalli,dinkin ya lafe mata sai kayi tsammanin fitted gown ce daurinta yayi das wanda ya awa gashinta damar kwanciya bisa dokin wuyanta
Ta fito falo ta kwashe siyayyar jiya ta kaisu kitchen,tsayawa tayi kallon kitchen din tana jinjina kai da dan guntun murmushi akan fuskarta😊ba shakka ummi tasan tsarinta game da kitchen kuma ta san maitar kitchen irin tata don haka ta cika mata ahi da dukkan wani nau’i na kayan amfanin kitchen babu ce kawai babu,abun nema ya samu nan ta bata lokaci gun tsara da shirya kitchen dinta yadda take muradi,tana tsaka da aikin ta jiyo ringing din wayarta wadda ita sam ma ta mance da ita ta fito galin tana laluben inda take,tsakiyar filalluka ta hangota tasa hannu ta dahota tana duba mai kiran garida ta gani tayi yar dariya sannan ya daga hadi da sallama,muryar farida a qasa ta amsa fadila tace lafiyanki qalau kuwa?”ta masa mata da “hmmmm,ai dole ki ce min lpy qalau tunda ke naji miryarki garau da ke “fadila da bata fuskanceta ba tace”kamar yaya? Wani abu ya faru ne a gida?”farida ta sake ajiyar zuciya tace”mubarak bashi da tausayi Allah sister fadila jiya kada kiso kiga rashin imanin da ya gwadan,anty hafiza tasan haka amma ta dinga dirka mana magani”fadila data dau haske a zancan nata tace”to Allah ya kyauta””wlh kin ga na kasa tashi sister”ta fada cikim karyewar murya,wani yarrr fadila taji tausayinta da tsoro suka kamata tace”ai ke likita ce saiki kula da kanki Allah ya bada lpy”tace”amin na gode ina ya Aliyu”
“Baya nan”
Cikin sauri farida tace “kada dai ace samira kika miqawa uwargidan bayan ke aka fara daurawa aure kuma ke aka fara kaiwa?”
Fadila cikin son abar zancan tace”ban sani ba ‘yar jarida kije ki fara jinyar kanki tukun idan kin warke sai kiji amsa”ta katse wayar,jikinta yayi sanyi sosai a salube ta zauna agefan kujerar,ashe har faahin matsayinta ma sai da aka mata?ita idan banda yanzun ma bata san itace gaba da samiran ba tasa hannayanta biyu ta dafe kanta cikin wani irin yanayi da ta kasa tantance ame take?,ganin ba mafita yasa ta koma kitchen taci gana da gyare gyarenta zuciyarta cike fak da tunani,
Da azahar baqi suka soma zuwa mata sallama din komawa gidajensu yan maiduguri ne da yan gwambe,zuwa qarfe uku suka tafi sai su rumasa’u sa’adah minah rahama da hafsah duk cousins dinta ne rumaisa tace’?”wai ke ya ne?”fadila ta kalleta da alamun tambaya ,sa’adah ta karbi zancan “gidan farida muka fara zuwa tana can kwance mubarak nata hidima amma ke gaki dungur gur a zaune”fadila ta juya idanunta🙄tace”lallai yarannan”da yake ta basu tazarar yan kwanaki ta Dora”kuce kawai uawon sa’ido yau kuka fito ko”dukkansu suka sheqe da dariya😄,suka ce”to ai gwara kafin mu wuce muga lamira sun daidaita ” tace”to Allah ya qara muku himmar sa’ido”ta fada tana shirin shigewa toilet rahama tace”to ai sai ki kira mana angon mana mu gani ko shi aka dorawa jinyar”ta jiyo ta harareta tace”baki isa ba kuma kwa qaraci zaman gulmarku ku tattara yammatan qafafunku ku koma inda kuka fito”suka sake aheqe mata da dariya😂,ita kuwa ta shige toilet din tana fadi a ranta”koni bancin arziqin samun ganinshi ba rabonku da ganinsa tun a dinner to nima hakan take”
La’asar gidan ba kowa duk sun yoye sun mata yan gyare gyaren da suka ga ya dace na game da jere da yan goge goge sukayi sallama cike da kewa tabi kowaccensu da dan dasheshan turare,turaren wuta ta zuba a bin turare mai amfani da wutar lantarki ta daidaita sanyin a.c falon yayi wani dadi qamshi da sanyi auka hafe guri guda,turare na musamman da hajja gana ta musu da kanta kuma ya tsumu sosai don ya jima a ajjiye ta musu tanadinsa,don haka qamshin har farfajiyar gidan,wajajen biyar ta sake gyara fuskarta ta feshe jikinta da turarurruka don dama babdaga baya ba fadila gun qamshi ta gabatar da la’asar da ta kufce mata,tana linke sallayarta tana ci gaba da jiyo hayaniyar dangin samira don tun farkawarta da safe wajan goma da rabi ta fara jin zuwansu,ta gama ta koma falo ta kama mbc bollywood dan ta samu ta debe mata kewa,kafin takai ga zama kan kujerar taji ana knocking din qofarta,ta nufi qofar tana cewa “waye?”saidai shiru ba’a amsa ba,don haka tasa hannu ta bude idanunta a waje don ganin waye,a subhanallah,ta fadi a zuciyarta saida bugun zuciyarta 💓ya dadu sosai fiye da qima,Aliyu ne tsaye a bakin qofar yana sanye cikin wani lallausan farin yadi qal(tissue),yadin nada shara shara don hakka hatta farar vest dinsa kana iya hangota,dinkin yarbawa aka masa(boda)iya gwiwa da dogon wando yana sanye da baqin takalmi idanunsa saye da farin gilashinsa na qa’ida kansa ba hula sai kwantacciyar sumarsa kamar mai sa mata relaxer saidai natural ce haka sumarsa take,qamshin turarensa ke dukan fuskarta,tsintar muryarsa tayi yana cewa”su bar maka a nan ka dinga daukowa kana ahigowa da su”hakan yasa ta tabbatar bashi kadai bane,tayi niyyar yin sauri ta koma ciki don ba hijabi a jikinta saidai ta kasa moysa qafafunta,sai jan jiki da tayi ta rakube a bayan qofa,nasiru n yake shigowa da kayan abinci duk wani dangin abunci da nasha na har ya kammala shigewa da su tsaf aliyi na tsaye tsakiyar falon hannayansa zube cikin aljihunsa yana facing qofar store yayin da ya juyawa qofar shigowa baya,ta haka fadila ta morewa kallonsa ba tare da ya sani ba,ingarman namiji ne wanda siffar qarfi ta bayyana atare da shi bayansa kawai ka kalla zaka fassara hakan,nasiru ya fito yana kade hannayansa ya dan russauna yace”yallabai na gama”yana qoqarin zaro kudi a aljihunsa yace”yauwa ya miqa masa kudin yace”raguna zaka samo guda biyu ka biyaau su gyara komai su wanke acan ka duba motar zuwa kasuwa ka tafi a ita””to yallabai”ya fada yana shirin wucewa”nasir”aliyu ya kirashi a aladabce ya juyo yana amsawa”ka biya ta gidan gona su gyara kaji ka taho da su””an gama sir”cewar nasiru ya fice da sauri
Ya juyo yayo tattaki har zuwa bakin qofa,fadila ta saci kallonsa sai taga hankalinsa na waje,cikin sanyin jiki da sanyin mutya tace masa”ina wuni”yqdan kalli sashin da take ya kauda kai,cikin wata dakakkiyar murya yace”kada ki qara zama haka bayan kin san cewa ba ni kadai bane,in kunne yaji……”tace”to”har yasa qafarsa awaje yadan dawo da baya ba tare da ya dubeta ba yave”qarfe takwas ki sameni a gefena”to ta sake cewa,”shikenan babu abinda kike da buqata?”ya fada yana duba agogon hannunsa,”babu”tace
“Ok ki duba saman kujerarki”kawai yace yasa kai ya qarasa barin sashin aransa yana cewa”ta wani labe sai kace wadda ake kora”
Hannayansa harde bisa qirjinsa yake bin harabar gidan da kallo ,ko ta ina dangin samirah ne kamar wani sabon bikin suke sakewa,ba bainda auke illa aikin dafa abinci da kade kade,shiba wannan ne damuwarsa ba hayaniya ce baiso sam ko kadan,musamman wannan lokavi da tun daren jiya zuciyarsa ke a cunkushe,lamarin na taba ransa sosai yanayin da ya samu samira a daren jiya tun daren bacci ya qauracewa idanunsa,yaja siririn tsaki a ransa yace”wai duk haka matan suke ne?”bashi da mai bashi amsar tambayarsa don haka ya nufi sashensa
Damuwa ita ta haddasa masa gajiya da kasala ya zauna bisa kujera ya miqe duka qafafunsa kan kujerar ya hardesu yasa hannunsa na dama yana shafar sumar shi,tunani ya masa yawa ya rasa da wanne zai fara,yana a haka yaji knocking kafin ya nada izini har ta shigo,tafiya take tana wani karairaya kamar mai ahirin tsinkewa ta kafa masa ido tana murmushi,sam ko kusa bata burgeshi ba hasalima wani tsanarta da baqinta yake gani,ta haue kujerar da yake kai kamar zata koma cikinsa”sweet aly ina ka shiga tunda ka kawo kayan abinci ka fice”ya dauke kansa yana qoqarin janye jikinsa yace”na koma kasuwa ne”
Ta dan bata fuska ganin yadda yake nuna kamar yana qanqyaminta tace”haba sweet wai meke damunka tun daren jiya fa ma lura da sauyawarka,bayan wannan lokacimmu ne da ya kamat ace mun moreshi,pls kada ka bari wani dan qanqanin abu ya tarwatsa mana jin dadin wannan lokaci da muka dade muna tanadin zuwansakada ka lalata mana suitable moments dimmu”kallon da ya watsa mata shi ya firgitata ya kira sunanta da wata murya da ta qara razanata
“Kin dade da wargaza farincikin wannan lokaci tuntuni da hannunki”ta dan zaro ido cikin duniyanci😳 tace “kamar ya wai me ya faru?”ganin tana shirin raina masa wayi yasa ya.miqe gami da jan tsaki yace”ni zaki mawa silly question irin wannan?”ta kama gefan rigarsa tana shirin kecewa da kukan kirsa tave”din Allah ka gayamin me na maka?”,ransa tafasa da suya kawai yake,ya dawo da baya yana huci ya ranqwafo kanta tamkar maiahirin fadowa kan nata har tana jiyo hucin numfashinsa,ya ware sexy eyes dinsa soaai a kanta wadanda bata san suna da girma ba haka miuyarsa a shaqe yace”u mean bakisan kinyi loosing virginity dinki ba,u did not know u r not a virgin!! A ina kika bada kanki samirah!!!”ya qaraahe cikin qaraji saboda wani kishi dake sukarsa,
Wani kuka ta rushe masa da ahi harda dora hannu a ka🙆🏻 kasancewar tasan halinsa baisan kuka ko da na yaro ne qarami yanzu zai dameshi,gunji take sosai hakan yasa temper dinsa ta fara raguwa,ya koma da baya ya zauna sosai,ta qasqantar da kanta tamkar wadda zata masa sujjada ta muzanta sosai,ta tsara masa qaryar fyade aka mata tun tana qanqanuwa”inna lillahi wa inna ilaihi raji’un”ya dinga mabata ahankali har yaji zuciyarsa ta fara sanyi duk da wani bangaren na zuciyarsa ya kasa gasgata labarinta,ya amince haka qaddararsa take,shi kam ya sani bai taba koda kusantar zina ba bare ya aikata ta amma Allah ya jarabceshi da samun mata har biyu da suka zo masa babu budurci,harda matarshi ta fari
“Ya isa,is ok “yace da ita,”hakan baza ta sake faruwa ba”yaci alwashin hakan,ta ruqunqumeshi tqna ta zuba godiya xikin zuciuarta tana godewa allah da asirinta baitonu ba don bazata iya jure rashin aliyu ba,baiga alamun tayi wanka ba don haka ya tambayeta,ai kuwa ta narke murya tave”na manta yadda ka koyan jiya da daddare”cike da madaukakin mamaki yake kallonta mace yar kimanin 25yrs amma ace bata iya wankan janaba ba ya koya mata ta kasa daukewa ?tun asubar jiya kuma tana zaune da janaba ajikinta bata damu ba to ina ga ban sallah kuma?ya jin jina kai yana hamgo girman aikin da ya sameshi,duk kuma yawan yanuwanta da sukazo a rasa wanda zai kwatanta mata harkar gabansu kawai suke,ya fuskanceta sosai ya sake koya mata ,nan toilet dinsa yasa ta shiga bai barta ta fita ba sai da yaga ta kammal ta kuma rama dukkan sallolin dake kanta
Tofa masu karatu muje zuwa
Mrs muhammad bello
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 12:30 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Wa yasan gobe?
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶1⃣2⃣
Har magariba fadila na bisa kujerar ta kasa tashi,kudin da ya jiye mata na gefanta tafa ce ta dubu dubu guda biyu,tasa hannu ta sake juya kudin a karo na barkatai “nafi buqatarka Aliyu fiye da kudinnan fiye da komai ma,me zaniyi da kudi”ta raya haka a ranta,kiran sallar magariba da aka qwalo a masallacin qarshen layin shi ya kawo qarshen zaman dirshan din da take,wanka ta soma dama ita gwanar sa ce don wani lokacin farida kan tsokaneta da agwagwa sarkin wanka ta hado da alwala bayan ta fito ta sa hijab ta gabatar da magrib sannan ta zauna tana azkar tana kuma jiran kiran isha’i
Minti arba’in tsakani ta jiyo kiran isha’in saboda haka ta tashi ta bada ita ta kammala da addu’oi ta shafa sannan ta isa madubinta dake cike da kayan kwalliya,kwalliya ta yi mai qayatarwa bata hauka ba mai cika fuska da yake ba baya bace gurin kyau sai kayi tsammanin bata lokaci tayi gurin yinta ta amsheta sosai ta kuma dave da yanayinta,ta bude duk sif dinta ta zuba mata ido tana tunanin wanne kaya zata saka?,hankali take shafa su har hannunta ya kai kan wani material
Pink ne mai adon dark blue da dark green din zare da golden sai wasu dutsuna da aka caba ado da su masu sheqi suma golden colour,dinkin doguwar riga ne da mayafinsa material din yake zuwa,yana da sulbi da taushi ba santsi ba yana shaking kadan a jiki don haka da tasa sai yabi jikinta ya lafe ya kuma haska kyakkyawar chaculet din fatarta fashion na dutse ta dan madaidaici ta maqala a kunnenta sai siririyar sarqarsa data lafe a dogon wuyanta sai zobe blue shima qwaya daya da ta saka a yatsan tsakiuar hannunta,ta shafe jikinta da tutaren asaal da ahlamul arab tame suka gauraya suka bada wani daddadan qamshi mai sanyi ta zura plate shoe pink ta dau mayafin kayan ta nade kanta da shi
Sannu ahankali tame ratsa gidan sai yanzu ta qarewa gidan kallo ita kam ya burgeta tsarin sosai,tamkar kana turai,ta sauke ajiuar zuciya sanda zuciyarta ta raya mata dama ita da Aliyunta ne kadai ke rayuwa cikin gidan rayuwa kuma irinta soyayya
cikin takun nutsuwa ta nufi qofar da zata sadata da bangaran nasa ido ta saki tana kallon ko ina,tako ina bangaran nasa yafi naau kyau da tsaruwa sosai,tun daga varender dinsa take jiyo sassanyan qamshinsa,ta shiga falon a nitse falone da ya tafi da gaba daya tunaninta tamkar gadar shugaban qasa,haduwarsa da tsaruwarsa tafi gaban kwatance
Idanunta suka sauka kanta tana hakimce kan kujera tana fuskantar t.v tana sanye ne da riga body huge da wando na jeans wadanda suka mata dam dam,ta baza kitson attachment din da aka jibga mata aka har gadon baya,fara ce sosai don har wani kore da yalo gefe da gefan fuskarta yake tabbacin kaso saba’in cikin dari na farin nata ya qara shi ne da man kanti,tana da jiki amma ba can ba da alama nan gaba kadan ta samu hutu zata narja qiba ne,tabbas ba don farin da ta aro daga kanti ba kana mata kallon farko zaka saka ta a sahun muna na amma sai farin ya boye kaso hamsim cikin dari na munin nata
Fadila ta sake jadda da sallamarta a karo na biyu sai Aliyu ne dake zaune bisa step kan dining ya amsa yayin da samira tayi saurin dago idanunta tana kallon mai shigowar idanunta suka fada kan fadila wani faduwar gaba taji amma ta maze don bata son fadilan ta fuskanci ta razana da ganin da ta mata,maimakon haka ma sai ta mata wani kallon raini na sama da qasa sannan ta janye idanunta ba tare da tace kanzil ba
Bata ma lura da kallon ba tana qarasowa cikin falon ta yiwa kanta matsugunni bisa tattausan carfet din da ya malale dakinta jingina jikinta da kujerar dake bayanta,wani abu ke tsunkular zuciyarta game da kishi duk da ta godewa Allah da ta tarar samirah bata fita da komai ba sai farar fata don ta tsammaci aliyu zai so matar da ta fi samira ne ba kamar samiran ba cikin ranta take cewa lallai so hana ganin laifi,to ganin samiran ko sashen da take bata kalla bayasa itama ta dauke mata kai sai ma ta zaro wayarta ta shiga latse latse
To shima Aliyun sai da ya kammala abinda yake ya shiga bedroom dinsa ya dan jima sannan ya fito ya samu kujera daya ya zauna ai kuwa tsam samira ta bar gurinta ta dawo jikinsa ta lafe kamar mai shirin komawa cikin sa ta gefan ido take satar kallonsu wani abu mai daci na damunta,amma a haka idan ka kalleta sai ka rantse da Allah batasan Allah yayi ruwansu ba don bata fasa danne danne a wayarta ba
Da bismillah ya fara yayi salati ga fiyayyen halitta yaja dogayan addu’oi wandabhar samira ta fara nuna masa tafa gaji,fadila ita mamakin yadfa Aliyu ke zuba addu’a take tamakar ba daga bakinsa suke ba(hmmm fadila kenan bakisan waye Aliyu bane😜)ya kammala sannan ha shafa,ina godiya ga Allah bisa ni’imomi da ya yimin a rayuwata tun daga haihuwata har kawo yau,ya kalli samira yace ga abokiyar zama nan Allah ya qaddara tare zan aureku sai kj zauna lpy bana buqatar hayaniya ko tashin hankali a gidana kowacce ta kama kanta ta tsaya inda Allah ya ajjiyeshi….
Ya dan sarara sannan yace idan da mai magana bismillah ya koma ya jingina da kujera yana jiran cewarsu,samira ta saci kallon fadila tana jiran taga zata tanka sai taga ma Sam idanunta bai kansu ta aza su ne bisa carfet,ta gayara zama cikin iyayi da kisisina tana kuma yatsuna 😏 tace”to nidai bana son shishshigi kuma bana son raini ehe…..kuma kowa ya kwana lpy shi yaso,sweet banji kayi rabon kwana ba?”ya daga kafada yace”its un 2 u ai”tayi wani fari da ido🙄tace”zamu raba kwana dai dai ne yayi aiko?”ta tambayeshi ya sake faga kafada yace taakaninku ai nikam ban iya yawon bin bangare bangare ba,”hmmm shegen girman kan tsiya”fadila ta fada a zuciyarta,duk da idan ka kalleta zakayi tsammanin bata tare da su,yauwa sweet ina kuma da buqatar masu aiki do…..cikin dakiya ya tari numfashinta,ba’a gidannan ba☝🏼,inji aliyu,ta narke murya,please sweet pls mana”bani buqatar roqo✋🏻ra’ayina ne”shiru tayi don tasan Aliyu idan yace eh babu mai sashi yace a’a,bare ita da take lallabawa tasan har yanzu lamarinta bai saki zuciyarsa ba
Dakin yayi shiru har ta gama kidanta tayi kuma rawarta ita kadai,ba wanda ya nemi jin ta bakinta Aliyu ya rufe da addu’a,ita din ma bata zaton ko sun ce tace dinma zata tsinka wani abu,suka shafa addu’ar ta miqe ta fice ba tare da ta cewa kowa komai ba,samira ta bita da kallo ranta cike fal da kishi saboda komai hassadarta bata gano abun kushewa tattare da fadilan ba
Shima kallon gun da ta tashin yayi yana dan mamakin sauyawarta yayi tsammanin za susha artabu ne kamar yadda suka saba a gida sai kuma yaga b sabanin hakan
A bangaranta fadila dana sanin zuwanta tayi gun sosai don bai qareta da komai ba sai hanata bacci da ya yi duk yayin da ta runtse ido da niyyar baccin sai hoton fuskar Aliyu ya bayyana cikin duhuwar idanun nata,wata iriyar soyayyarshi ke mamaye ruhunta cikim tsakiyar daren kewa ta kamata ga kadaici da ya hanata sakat,so ne da bata yaba jin irinsa ba a rayuwarta qauna ce ta musamman,hakanne ya zama sanadiyyar karyewar zuciyarta duj yadda takai ga bawa kanta qwarin gwiwa,kuka ne matsananci ya sarqeta,daren tayi kuka mai yawa a kwancan tana tausayawa rayuwarta da makomarta,tasan tabbasa son Aliyu na daya daga cikin jarabobin rayuwarta,tanajin sa a jiki jini jijiya da ruhinta
Cikin taimakon Allah bata manta da ambatonsa ba hakan yasa bacci yayi nasarar daukarta
👏🏻👏🏻👏🏻 ayimin afuwa a danyi haquri da wannan sai Allah ya kaimu gobe
Mrs muhammad bello ce
✍🏻✍🏻✍🏻📚📚📚📖
[10/16, 12:31 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Wa yasan gobe?
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶1⃣3⃣
Kwanakin da suka baya ta yisu ne cikin kadaici da kewa,ita kadai ke wuni a bangaren nata,bata da aiki sai wanka da sallah da shi dama abinci ba gwaninta bane saidai tayi ta jiyo muryar baqin samira da har yau suka qi qarewa,wani lokaci kuma ta kira farida su sha hirarsu
Ranar da ta cika kwanaki bakwai a gidan ranar tana kwance a falo hannunta riqe da littafin sahihu muslim mujalladi na daya tana karantawa da yake mayyar hadisi ce ita ta jiyo ana knocking din qofarta ta dora littafim a saman kujerar taje ta bude
Anty hauwa ce da yaranta bilkisu kausar Ibrahim sai qaramin su muhammad sai kuma madina qanwar momy da yaronta hamid sai iftihal,farinciki sosai fadila tayi don tasan yau babu wunin kadaici,nan falin ya kaure da hayaniya su suna hirarsu yana na nasu,ta shiga kitchen ta hado musu kayan motsa baki sannan daga bisani ta nufi kitchen don dora girki iftihal da bilkisu suka bita zasu tayata don sune yan manya madina ma binsu tayi aka bar anty hauwa da ragowan yaranta suna kallo fadila tayi tayi madina ta bari amma taqi don haka tare suka kammala komai,tare suka ci a babban plate guda yaran ma aka hada musu anti hauwa ce tace ayi haka kada a bata mata kwanunka,bayan sun gama madina ta hada kan kwanunkan ita da su bilkisu suka gyara mata komai,ganin ba kowa a gun anty hauwa ke tambayarta ina fatan dai baki da matsala da Aliyu ko dan kishiya wannan kam ita ba’a rasa ta da matsala saidai haquri ,dan murmushi fadilam tayi tace”ba wani matsala anty lpy lau muke”ta jinjina kai tace to saidai a yita dai haquri don kinsan zaman aure ya gaji yau fari gobe tsumma,tayi mata nasiha sosai tare da bata shawarwari masu gamsarwa fadila sosai taji dadin maganganunta hakan ya sake qara mata qwarin gwiwa da nutsar mata da zuciya
Bayan sun idar da sallah ne ta la’asar wajan biyar da rqbi suka soma haramar tafiya,iftihal tace da naty hauwa mummyn kausar nidai anan za’a barni ko?,antu hauwa ta girgiza kai tace a’ah ai ba haka kukayi da mummy ba,bazan iya da wannan rigimarba tate zamu tafi da ke,ta soma diddira qafa tana maqale kafafa tana cewa nidai anan zan zauna mummyn kausar gaskiya,fadila tace da anty hauwa”anty don Allah ku barmin ita mana dama ni kadai zaman ba dadi wlh”anty hauwa ta zaro ido😳 tace”wai rufamin asiri ai mummy bazata iya zama ba iftihal ba ko na barta da kanta zatq zo ta dauki abarta baki ji yadda aka kafa mana sharadi ba kan a bamu mu taho da ita kamar tasan za’ayi haka”jin haka yasa fadila ta haqura
Ta tako.musu har waje bakin part dinta yara nata tsalle kowa da packet na chaculet dinsa a hannu ta bawa su anty hauwa turarurruka da qyar ta karba tace ita lpyrsu kawai ta zo gani,ganin suna shirin yin gaba ba tare da sun shiga gun samira ba tace”antu baku leqa gunta ba kun gaisa”anty hauwa tace o’o’o ni kam tun shigowarmu muka gaisa da ita a harabar gida ta rako baqinta sai dai ko madina ita da yara,madina ta tabe baki tace nima bani zuwa anty ina kallo fa sanda muka shigo tana ganinmu tayi saurin sallamar baqin ta juya ciki kema sai da kika kirata kusan sau uku sannan ta amsa miki,sai dai su kausar maza kuje ku gaidata ku fito mu tafi ungoshi bilkisu ga hamida ma aje da shi ai ya wakilceni
Suna tsaye suna jiran yaran sai kuwa gasu jiki a salube sun dawo Ibrahim sarkin zuciya hadda guntun hawaye madina na amsar hamid daga hannunsu tana tambayarsu me ya samesu,bilkisu tace anty koromu tayi wai ba mun gaisa a waje ba meye kuma na wani biyota,ibrahim da ya fisu shekara yana kusan 12yrs yace”har tsawa fa tayi mana wai masu qwala qwalan ido sai kallonta muke wa ya sani ma ko turo mu kayi mu cinyeta”iftihal kam fuskarnan a turbune tqma kasa cewa komai,anty hauwa tace ya ‘isa haka is ok bata mata rai baqinta suka yi ku wuce muje,sukayi gaba fadila da mamaki ya kamata tana biye da su mamakin samira take sai kace wata mahukaciya yara zata tsaya tana gayawa irin wadannan magan ganun sai ka ce wasu manya,suna gab da get suka ji ana kwararo horn mai gadin ya tashi da azama ya bude wawakeken get din wata farar motace sol qirar range rover ta shigo ta samu gun parking ta tsaya da gudu iftihal ta kwasa tayi bakin motar
Ya bude motar ya fito sanye yake da suit masu bala’in kyau baqaqe sunyi masifar yi masa kyau da kwanciya lif a farar fatarsa tas da shi kamar yanzu ma yake ahirin fita aikin ba wai ya dawo bane,iftihal na qarasawa ya cafeta ya daga ta sama ya jujjuyata yayi kissing kumatunta sannan ya direta ta tsugunna da alama gaidashi tayi,madina tayi dariya😀tace “oh uwar wayon tsiya wai har motocin Abbanta ta sansu wannan yarinya “anty hauwa tace”ke ai iftihal da wayinta aka haifeta don.mummy tace duk cikin jikokinta bata ga mai wayonta ba”da hirar iftihal da suke suka qarasa gurinsu ,cikin motoci fadila ta dan rabe bayan wata mota tana ganinsu tana kuma jina binda suke cewa,ya dago yana masa sallamarsu.lokacin da yake tambayar iftihal”ashe tare kuke mummyn yara”anty hauwa ta mayar masa ta sigar da ya fada”😊mummyn yara tun dazu tazo kuma yanzu zasu koma”ya juyo yana kallin madina yadan hade rai yace”au da waccar kima zo”anty hauwa dake danne dariya tace”eh duk tare muke”tasan yar tsamarsu da Aliyu don tun ranar da take fadin ita babarsa ce tunda qanwar mummy ce bata san yana gun ba suke yar tsama ya daina sakar mata
Ya miqawa su ibrahim hannu suna musabaha haka halayyarsa take dama yana dan tsokanar ibrahim din kasancewar sunan kakansu ne shi kuma ibrahim na murmushi ya karbi hamid daga hannnun madina yana duban anty hauwa yace ba wanda ya rakoku ne?,anty hauwa tana dube dube tace tare da fadika muke ina tayi ne?,fadila data dora hannayenta saman motar tana game a wayarta har dankwalin kanta ya zame bata sani ba ta dago jin an ambaci sunanta idanunta suka fara sauka kan aliyu cikin sa’a suka hada ido harara taga ya balla mata wani abu taji ya caki zuciyarta ta lumahe idanunta am ta kasa budesu wani sinsa taji na mamayar zuciyarta da gangar jikinta kamar ana zira ra mata ruwan sanyi bugun zuciuarta ya sake qaruwa,bata san me tayi masa ba yake harararta,sai tq sunkuyar da kanta😔 tana kallon yatsun qafarta dake saye cikin slippers,sai da iska ta watso mata gaahin kanta gefen fuskarta sannan ta gane ma’anar hara rar da aliyu ke mata don bata manta ba rabi’ah ta taba fada mata ya aliyu baison yawo a waje ba dankwali idan ya ganki kuwa kin shiga uku,da sumauri ta jawo mayafin data yafa ta lullune kanta sosai
Duk daga idon da zatqyi a rayuwarta ta kalli aliyu sai taji an qara manna mata sonshi ji taje kallomsa ma kawai jaraba yake zamewa rayuwarta sai dai koda tayi niyyar qin kallon nasa sai ta kasa jure haka domin zuciyarta bata lamunce mata ba,ba abinda ke sata nishadi irin kallon kakkyawar qayatacciyyar fuskar tasa
To fadila za mu wuce sai an kwana biyu kuma,cewar anty hauwa tana dan murmushi😊 ta taso daga jikin motar da niyyar sake yi musu tattaki suka sake hada ido da shi sanda tayi niuyar satar kallonsa wata hararar mai zafi ya sake watso mata wadda ta sata tsayawa daga nan cak,yaram suka taho suna kama hannunta suna cewa anty bye bye,itama ta daga musu hannu✋🏻 tana dan murmushin yaqe😇 tana cewa”bye”sai kuma iftihal ana su taho ta ja tunga ta tsaya ita allan katafar ba zata bisu ba aliyu dake karbar takaddu daga hannun nasuru ya juyo yana tambayar meke faruwa anty hauwa ta masa bayani,kallo daya tak yama iftihal din tabi bayansu jiki na rawa
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶1⃣4⃣
Bata sake sha’awar kallon inda yake ba don ta gaji da ganin wanna hararar tasa da kallon qiyayya da yake jifanta da su sai ta juya da sassarfa don barin gurin “ke”taji dakakkiyar muryar Aliyu,batason irin wannan kiran sam don haka tayi banza bata juyo ba bata kuma amsa ba kuma bata daina tafiyarta ba ya sake daga murya yace”dake nake”sai ta tsaya cak saboda tsoron da ya bata muryarsa ta canza tayi fakare tana jin yadda zuciyarta ke bugawa,da tsawa yake mata magana bayan ya sha gabanta”ki baki isa a kira ki ba kenan ki tsaya”tamkar tace wani abu sai kuma taga bai kamata ba tunda a harabar gida suke wani zai iya zuwa giftawa ya jisu
Aliyu ya kafeta da ido yana huci a zuciyarsa yana fatan ta tanka masa ko zai samu ya huce mata haushinsa amma ko kallon fuskarsa taqiyi hasalima sadda kanta tayi qasa,ganin da ya yi bata da niyyar ko alamun tanka masa sai ya dora mata baqar leda mai dan matsakaicin girma bisa qafarta yaja tsaki gami da hura mata hucinsa akan fuskarta ya wuce,sai sannan ta dago tabi bayansa da kallo tana sheqar iskar wadda ke bada qamshin lemon fresh na mouth fresh,ta kauda idonta sai kuma ta hango samirah na tsaye bisa varender dinta ta zuba musu ido don haka sai ta saki murmushi ta kuma yi saurin dauke ledar tayi bangarenta tana qara hasko fuskar aliyu qamshin turarensa maganarsa komai nashi unique ne mai tsari ba baunda tafi buqata a yanzu irin aliyum saidai tasan samun nasa ba baune mai sauqi ba wanda zata cimmawa cikin qanqanin lokaci
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Kamar ko yaushe a irin wannan lokaci tana kwance kam dogowar kujera a main parlour kunnenta maqale da earpiece tana sauraron suratu baqara cikin qira’ar sheikh Abdurrahman assudais taji ana mata knocking kafin ta bada izini tuni an bude an shigo,ga tarin mamakinta samirah ce ,ta tashi zaune tana qoqarin cire earpiece samirah ta qaraso tana kallon yadda take qarewa parlour din kallo zuciyarta cike da kishin yadda parlour din fadilan yafi nata tsaruwa da kyau,fadilan nata biye wa wanna ba ta nunawa samirah gun zama tace bismilla ga guri zauna😒”ta wani tabe baki tace”ba zama na zo yi ba don nima gidana akwai gun zaman “jin haka yasa fadila ta gane ba mutuncine ya kawota badon haka sai ta koma tayi kwanciyarta kamar yadda take da ta kuma maida earpiece dinta kunne ba tare da taci gaba da sauraron karatun ba
Da samira taga haka sai ta yatsine fuska sannan ta fora da cewa”nazo ne don na tuntubeki bakiyi shirya fara zuwa turakar miji bane?,sai tambayar ta bawa fadila mamaki ta kuma ji wani bawai tana daga kwancan ta dubeta”kamar ya?,me kike nufi ne?”samira ta juya ido👀 tace”a….to gani nayi har yau baki fara zuwa ba shi kadai yake kwana nima ba zuwa nake ba tunda lissafe kwanakin amarcinki ne”mamaki ya sake kama fafila don ko a lbr bata taba jin ko ganin raahin kunya irin wannan ba wato ma idonta na kanta kenan
Tilas ta miqe ta zauna sosai don nuna wa samira ba ita ce kawai mara munya ba itama ta iya barikancin nan,”da farko baiwar Allah ajiyata aka baki?,ko kuma da mai gidan kukayi maganar bana zuwa gunsa?,to idan ajiyata aka baki ina mai baki shawarar kiyi gaggawar maidawa wadda ya baki ajiyar don wannan aniyar tafi qarfin ki wlh ba zaki iya ba idan kuma shi mai gidanne ya gaya miki bari na sake tambayomiki shi…..,ta fada tana jawo wayarta tana shirin shiga contact cike da barazana don bata tsammanin ko number dinsa akwai cikin wayarta😜
Ganin da samirah tayi da gske kiransa zatayi kuma ta san sarai halin Aliyu bare tana cikin case har yanzu lallabawa kawai ake sai tace”dakata ni ba gangami nace kiyo ba magana ce iya kacina da ke”ta juya tana shirin barin falon fadila ta dan daga murya tace”ai da kin tsaya an sake jin ta bakinsa ko kinga maji dadin qarasa maganar,mu amarci muke mai lasisi ba irin naki ba”bata ce uffan ba ta fice ta ja mata qofa,wani takaici ya kama fadila taja wani dogon tsaki tana cewa”banza ballagaza ko angaya miki ke daya kika iya bariki ne kina ganin kin girmeni ko,da auren so mukai da aliyu wlh kallonki ma kace yayi sai yaji an hada shi da aiki”ta koma tayi kwanciyarta yadda take taci gaba da bin karatunta
Kwanaki nata tafiya da fadila cikin gidan,ba wani qiba da zaka ce ta qara sai fatarta da tayi lumi lumi ta sake fresh saboda zaman guri daya
Watanta biyu kenan da sati yakwas kwankin da take jinsu kamar waau shekaru saboda zaman kadaici,Allah allah take sakamakonsu ya fito bata da sha’awar komai illa ta fara fita aiki,ta jawo wayarta ta soma neman nafisah classmate dinta ce suna gaisuwar mutunci da fadila don har bikinta tazo tave cikin zuciyarta bari ta kira ta tambyaeta ko sakamakon ya fito saidai nata sameta ba number dinta a kashe don haka ta maida akalar kiran layin anty hafiza sunsha hira aosai ta kuma yi mata qorafin sunqi leqota ba ita ba yan biyu gsky tayi fushi tace tayi hqr insha Allah zasu zo su yinin mata,bayan sun gama sai ta kira hafsah da aukayi attachment tare sun gaisa sosai take tambayar hafsa ko result ya fito tace yana dai hanya da ya fito insha Allah zata sanar mata tayi mata godiya suka kashe wayar
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Zaune take alambun dake bayan part dinta kan kujerar siminti under wear dinta take wake wa su brassiere pant da skert gun tsit yake shima kamar yadda gidan nasu yake saidai ahi akwai kadawar ganyayyaki da kuma kukan tsintsaye jifa jifa wadanda take zubawa gero shi yasa suka dadu kuma suka fi yawa alambun nata fiye da ko ina a cikin gidan tana son gun sosai saboda yawancin lokuta yakan zamo daya daga cikin abinda ke debe mata kewa ko da yaushe gun luf yake dauke da inuwa mai sanyi
bata barin undies dinta wanna ma kwana biyu ne da bata jin dadin jikinta dama cutarta ciwon kaine ko ciwon mara shi yasa suka taru haka ita dama can ko a guda da wahala kaga kayanta cikin kayan wanki ko za’a mai saidai kaga na fatida tafi ganewa tana cire maya ta sabesu ta shanya sannan ta shigà wanka,tana cikin shanya ne taji takun taviya sai tayi sak don dai tasan ita kadaice a gun kuma ta kulle sashen nata da idanunta take bin gun da kallo don gane daga ina takun yake,Aliyu ne ke taho wa hannayensa harde a qirjinsasanye yake da jar t.shirtmai gajeran hannu sai dogon wandon jeans mai kalar black blue sau ciki ya sanya balck blue idanunsa saye cikin glass dinsa na qa’ida fari qal zuwa lokacin fadila ta soma tsammanin medical ne bana gayu bane,tayi saurin dauke idonta dag kansa zuciyarta na wani das das das har ya qaraso gabnta ta kasa moysawa tamkar ta nutse saboda irin kayan dake jikinta ta tabbatar babu mai shigo mata ne don ta kulle qofarta shi yasa ta saka su rigane da akery sosai sai dai maau roba ne iya qibarka iya yadda zasu fidda shape dinka gashi gaba daya hannayen ta da skrt din anbi an tsaga ko ina babu inda ya tsira wuyan rigar mai fafi ne son ana hango saman qirjinka sosai kanta kuwa ba dankwali sai tafkeken ribbom da ta saka ta mate gashinta ya sauka mata a kafada duk da ya danyi tauri sabida raahin zuwa saloon kwana biyu
A dabarance take duba jikinta tana sa hannu tana gyara inda hannunta fuk yakai saidai ina duk In da ta sa taja ta rufe sai wani gurin kuma ya bayyana shikam hannàyensa na harde ya jinggina jikin qarfen da ta ware tan shanya kayan idanunsa duka ya zuba mata duk dabararta na tattare jikinta sai da ya ganota shi sai abin ma yaso bashi da riya duk da a fuaka sai ka ranyse rufeta ma zaiyi da duka”bari nayi maganin yarinyarnan’ya fadi haka cikin zuciyarsa”ni da waye a gun kiketa wani aikin rurrufe jiki?,gabanta ya fadi kunya ta sake kamata sai taji ya ja tsaki wanda yasa ta dago ta kallo shi ba tare da ta dubi qwayar idanunsa ba don tana kaucewa hakan bataso au hada ido sam don tana tsammanin yana da wani asiri ne cikin qwayar idanunsa aduk sanda qwayar idanunsa auka hafu da nata takan kwana ne ta wuni cikin begensada kuma aAbar aonshi da take ta yaqin ganin ta bunneshi cikin babin rayuwarta,wa ya gaya miki an damu da jikin naki da kiketa qoqarin killaceshi ne?…… Ba wannan ba na duna store naga yadda aka Uba kayan abinci haka suke ba’a taba ba kamar wadda ka bai wa rancansu sannan fridge ma haka yake abu qalilan ne suka ragu mekike nufi? Salon kija min bala’i ko?wannan wankin kuma da kika hafo na meme?duk masu wankin gidannan suma basu miki ba ko gulmar azo a tarar kina wanki ace wuya kike sha?burinki dai kawai na zama mai lafi
Ya tsagaita da fadan ya kafeta d ido ko zata ce wani abu amma yaga ba alamu duk da zuciyarta ta baci da yadda aliyu ke mata a cikin gidan ba dama inuwa daya ta haasu sai fada tsakaninta da shi?cikin zuciyarta taja tsaki gami da cewa”shikenan kuma sai akace mutum bàshi da aiki sai dirkar abinci kamar tsohon jaki?kuma ma wane aiki nake don na dwbo yan kayana na wanke da hakan zai zama laifi agun wannan mutumin?
Bata tsammci a fìli tayi maganar ba sai da ta ji yace”duk basu zama laifi ba amma ki shirya duk ranar da aka tuhumeni da wani laifi akanki kisan yadda zaki kanki don daukar ki zanyi cancankat nakai musu ke”ya maida kansa gun agogon dake daure atsintsiyar hannunsa 😠 yace”me dame kike da buqata?a gajarce tace masa”ba komai”yayi tattaki ya sake qarasowa gabanta ya ajiiye mata kudi kamar yadda ya saba ya rabe ta gefanta ya wucè tana sheqar daddadan qamshinsa wanda yaja mata kasalar da ala dole ta tattara ragowar da bata wanke ba ta maida ciki
Mrs muhammad ce
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 12:33 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Wa yasan gobe?
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶1⃣5⃣
Washegari misalun takwas na dare tana zaune a falo tana kallon wani film gabanta plate ne ta yanka kankana apple da gwanda tana sha dama abincin bai wuce ire ire wadannan qwaqwaso qofar taji anayi ta dauki hijabinta dake gefanta wanda ta idar da sallar isha’i da shi ta zura sannan ta miqe tana tambayar wane?ki bude mana,taji ance bata dau murya ba amma ta gane maca ce,ta bude ba yare da ta kauce daga hanya ba,samirah ce tsaye cikin kwalliya rakacau a fuskarta tana sanye da doguwar rigar atamfa tayi rolling dawani siririn mayafi sai uban turare data bulbule jiki da shi tana taunar chewing gum qas qas qas, tana wani ya tsina fuska tace sweet yace ki fito zamu siyayya,fadila tace😏 waye sweet kuma?,ta wani juya ido tace my aly,
Tabe baki fadila tayi tave kice bani buqatar komai,bata jira cewarta ba taja qofarta ta rufe,wani kishi ne ya motsa mata ita kanta tasan tana da tsananin kishin aliyunta amma ya ta iya?,ta jiyo muryar samirah na masifa”aikin banza wa ma ya damu da ke
?kada Allah ubangiji yasa ki je din dama sho ya takura ayi kiranki waishi mai adalci toga abinda ya jawo mana nan wulaqanci agun wadda bata isa ba”fadila dai murmuahin uaqe tayi wanda akace yafi kuka ciwo,ta dauki plate dinta taci gaba da cin fruit din ta ba tare da tana jin dadinsu ba kamar da
Knocking ta sake ji ana mata ta maida plate din kitchen sannan tazo ta bude yana tsaye a bakin qofar hannayensa zube cikin aljihun jeans dinsa fuskarnan kamar hadarin dake shirin zub da ruwa😠ba tare da ya dubeta ba ya kalli agogon hannunsa kana yace”nan da minti biyar ki sameni a mota,abindabya fada kenan ya juya yayi tafiyarsa,cikin qanqanin lokacin kuwa ta shirya kasancewar ita dama koda yaushe bata taba yarda ta zauna babu wanke bare uwa uba qamshi da yariga ya kama jikinta kida muwa bata sanya turare ba,shigar doguwar riga abaya tayi baqa wuluk mai sheqi saqar qasar dubai an mata ado da dutsuna masu kalan sararin samaniya(sky blue)rigar tayi bala’in amsarta musamman da tayi rollinga da wani dankwali madaidaici shima sky blue ta nannde gashinta tayi acuci da shi,ta saka zobe qwaya biyu a yatsunta na tsakiyar hannu plate din takalmi ta saka baqine mai light blue din igiyoyi,ba wani make up tayi ba hodace kawai da weet lips amma kada kaso kaga kyawun da tayi kamar wata baqar balarabiya kasancewarta mai zagayayyar fuska da cikakken gshin gira ga yalwar sumar kai wadda ta bayyana har a gaban goshinta
Suna zaune shi da aamirah cikin motar tana ta faman mitan dole wai sai da gadilan za’a tafi ne ya daga mata hannu✋🏻 fuska ba walwala kamar kullum yace”ya isa fa mitarki tayi yawa,for god sake,zaki taimakeni ranar da na tashi barin jiki na ashanye?,anje da ita kamar yadda kaje da ke ruwanta ne ta siyi abinda take ruwanta ne ta barshi fine an fita haqqinta,cikin salon jan hankalinsa tace da tuni ni kadaice taka sweet,an tashi an.manna maka wannan baqar yarinyar,wani kallo ya sakar mata wanda ya tilasta mata tsuke bakinta don kuskuren da taso tafkawa,baya ga haka ma aliyu shi tun usulinsa bai iya yi da mutum ba gaskiya daya ce zai fade ta ne agaban mutumin koda zai mutu ko zai kasheshi
Sukayi tsai suna sauraron isowarta aliyu nebya faa hangota ya glass din gefansa,sai ya samu kansa da qarewa shigarta kallo tabbas tana da kyau babban abun ma iya dressing na nutsuwa bana hauka ba fuskarta babu tarin kwalliya irinta ta samira hakanan babu qamshin turare har sai da ta ahigo motar gidan baya ta zauna sannan yaji nata qamshin,shigar tadauki hankalin samirah tamkar ta fito itama ta canza irinta haka ta ji tunda ita fara ce ai zata fi karbarta haka ta gani,amma a fili sai ta wani tsaki,aliyu ya tashi motar ya yi ribas ya nufi get tun kafin yayi horn salisu mai gadin ya dage grmet din gidan nasiru da suke zaune tare da slisun ya taso ya iso saitin da aliyu yake ya fan ranqwafa yace yallabai kai kadai yau zaka fita,ya girgiza kai ina tare da matan gidan ne,nasirun ya dan sake ranqwafawa yace barkanku da dare hajiya an quni lpy,fadila ce kawai ta amsa samirah kam dauke kai tayi kamar batasan yana yi ba takaici ke cin ranta da dab banzan kishi sai tayi banza da shi
Aliyu ya qare maganar da suke yi da shi da”sai na dawo kaima zaka iya wucewa gida sai gobe insha Allah”nasiru ya dan ja baya yana cewa to yallabai a dawo lpy Allah ya tsare,har ya saoma jan motar ya tsaya ya dannawa nasiru horn ya dawo da sauri yace masa”nasiru kayi qoqarifa gobe ka fita da wuri ka fara zuwa gunsu haruna ka b tabbata a gobe an gama sa kayan duka cikin store qarfe sha biyu zan qaraso insha Allah ,yace to da yarda Allah goben za’a kammala,aliyu yace sai ka wuce gida ka kwanta da wuri don ka samu tashi da wuri Allah ya bamu alkhairi,ya ja motar suka fice
Yanayin tuqinsa salon da fadila bataso ne sau tari sukanyi fada da frida akan haka wato gudun tsiya ne da su,ya iya gudu da keta motoci,motar ta dauki shiru sai sanyin raba dake ratsa kowanansu kowa kuma da abinda zuciyarsa ke saqa masa,a sace fadila ke kallon aliyu ta mirror,fuskar nan ahade tan shaqar qamshin turarensa na chastity sai ta kasa dauke idonta a kansa sonsa na mamayarta,ji take tamkar ta kamoshi ta rungumeshi a qirjinta ko zaiji yadda zuciyarta ke bugawa saboda shi ya tausaya mata,a yanzu ba abinda tane buqata illa soyayyarsa,tana ji ne kamar ta furta masa abinda ke danqare a a zuciyarta ,don kanta ta dauke idonta tana sauke boyayyar ajiyar zuciya
Tafiyar mintina qalilan suka isa katafaren kantinnan na shoprite,ya dauki wayarsa iPhone 6 yayi yan danne danne sannan yayi kira da bai wuce na second goma ba ya maida wayar gefensa ya kashe motar minti ashirin na bayar kada kuma a wuce haka,samirah tace cikin murmushi”ok sweet”ya maida mata da cewa”ok dear”wani dadi ya rufe samiran kamar ta taka rawa💃🏽 domin ta dade bata samu hakam daga gareshi ba duk da tsan ba laifinsa bane ita ta barar da damarta,ta kama hannunsa ta masa kiss sannan ta fice,abinda bata sani ba tuni fadilan ma ta rigata ficewa
Ta kwashi kusan minti goma bata dauki komai ba tana zaune duniyar tunani sai da taga giftawar samiran a inda take sannan ta ankara ta miqe,wani abu ya darsu a zuciyarta,nana da nan ta soma zabar vest ta maza cotton fala qal mai kyau da taushi ta dauki gajerun wanduna dozen sai hand kerchief dozen agoguna na kamfanin gucci uku azurfa biyu takalma hudu budaddu biyu rufaffu biyu sai turarurruka na kamfanin rasasi sai rezar aski ta maza tare da shaving cream na nair,ta daukarwa kanta turaren blue lady sai relaxer,sannan ta amshi mutuminta wato ice cream manya robobi guda hudu,leda biyu aka mata kayan sai tata ledar ta tashi shafal babu wani abun kirki da ta dauka,kayan basu da wani nauyi don haka da kanta ta dauka ta fito,tana kusantar motar gabantana dada faduwa bata ga alamun samira ta dawo ba don haka ta iso motar ta sanya hannu ta bude gidan baya ta zuba ledojin hannunta sam sai ta kasa zama cikin mitar kasancewar aliyun na ciki don haka sai ta tsaya jikin motar ta jingina da ita ta harde hannayanata bisa qirjita tana bin harabar gun da kallo gamida qare masa nazari na yadda matasan yan birni maza da mata keta kara kainar shigowa gun da motocinsu
Sai fadila ta soma qosawa da tsaiwar gun ganin yadda duk naminin da zai gifta sai ya zuba mata idonsa,taja tsaki tana jin takaicin matsanancin kallo irin na waau mazan,kamar daga sama ta jiyo dakakkiyar muryar Aliyu yana cewa”malama koma.mota ki zauna tun ke bakisan me ya dace ba” a sanyaye ta juya ba tare da ta kalleshi ba ta shige cikin motar zuciyarta na mata quna da jajen yadda aliyu ke mata mu’amala tqmkar wata mara rai kunnuwanta basu taba jiyo mata kyakkyawar kalma daga bakin aliyu ba akanta,zuciyarta ta fara tafasa saidai ta danne bacin ran nata da kiran sunayen Allah,dama ta tsammaci fiye da haka ma daga gurinsa
A hankali ta soma jiyo maganganun aliyu dake tsaye jikin mota sai ta tsinci kanta da kasa kunnuwanta cikin qaqanin lokaci ta fuskanci da mace yake hirar,kai tsaye ba zata fassara hirar data soyayya ba amma zaka fuskanci cewa akwai alaqa tsakaninsu ,mai da bayanta kawai tayi ta jingina da makarin kujerar ta lumshe ido tana sauraron bugun da zuciyarta keyi ta dauki tsaqon mintina a haka ba tare da ta tantance halin dabm take ciki ba sai da aka gama zubawa samirah siyayyarta a but qarar rufe buut dinne ya dawo da ita duniyar data Lula
Muryar samira ta karade gun cikin tuhumar aliyu da wace yake waya cikin rashin ladabi bai kulata ba sai da ya gama wayarsa tsab yayi sallama dabwadda yake wayar ya kashe bai ko kalleta ba ya bide side dinsa ya shiga itama cikin sauri ta zagayo tana huci ta shiga itama ta bame qofar yana yiwa motar key ta sake jaddada masa tambayarta “na ce ma da wakake waya?”aliyu bai iya qarya ba don haka kansa tsaye ba tare da shayin komai ba yace”da maman iftihal kin gane?”ba samira da tayi tambayar ba hatta fadila da amsar ta daketa,samira ta hadiye abinda ya taso mata don bin qwaqqwafi ta sake jeho masa wata tambayar daidai sanda motar ta saitu akan kwalta”ro mw kake nufi da yin magana da ita gidanka take nufin dawowa koko ya aka soma?””duk yadda ta kama haka za’ayi”ya mayar mata kansa na kallon kwalta,saiga samirah ta dora hannu aka tana shirin zunduma ihu🙆🏻,da sauri aliyu ya sauka gefan kwalta ya taka birki yace”bari na sauke ki idan kin gama ihun saiki tari mota ki biyo ni tunda lasheki nayi ko kuma satoki nayi”ba tare da ta sauke hannun ba ta hau maganganu bai kulata ba ya figi motar ya koma hanya,fadila kam na baya ji take kamar babu jini a jikinta babu abinfa kunnanata da qwaqwalwarta ke ganewa har suka iso gida ita dai taga ficewar samirah fit kamar walqiya bata ma jira motar ta gaa parking ba don saura kadan ta fadi,ita kam bata da kuzarin yin hakan don haka ta jawo ledar da ta yiwa kanta siyayya tabar wadda ta masa,ta fara tafiya ta jiyo maganar sa abayanta yana tambayar ledar meye ta bari?ta sadda kai qasa😔cikim sanyin murya tace kayanka ne,ya sake damqe rai😠 yacekayana?na sanar da ke ne ina da buqatarsu?”dum dum taji atsakiyar kanta wadda tamkar an buga mata guduma a tsakiyar kanta taji,batasan sanda ta isa sashenta ba ita dai ta tsinci kanta ne kwance bisa carfet din falonta
Aliyu yabi inda ta wuce da kallo ganin bata tanka masa bailla ma ledar hannunta da ta saka ta wuce tana raba hanya,sai yaji wani iri a cikin zuciyarsa yake jin kamar bai yi abu mai kyau ba ya sunkuya ya dauki ledar da ta saki din ya bude mota ya hada da tasan ya wuce sashensa don ko kusa baiyi sha’awar neman samira ba don yasan bazai tainci komai ba illa qarin damuwa da koke kokenta na tsiya,kai tsaye ya wuce bedroom dinsa ya dora ledojin bisa center table din dake gaban gadon ya cire kayansa ya shiga wanka bayan ya fito ya ciro kayan bacci ya feshe su da turare su haka nan jikin sa,ya shimfida sallayarsa yayi shafa’i da wutiri sannan yayi addu’o’insa ya shafa,ya murzawa qofan dakin key yasa hannu zai kashe wutan dakin din kwanciya idanunsa suka fada kan ledojin da ya shigo da su,bayan ya kashe ya koma ya dauki ledojin ya koma saman gado ya kunna fitilar gefan gado ya zazzage kayan dake ledar farko,daya bayan daya yake daga kayan sannu a hankali yake binsu da kallo,sai yaji kayan aun nurgeshi kamar ta san zabinsa,kayan sun masa sosai ya maida su cikin ledarsu,ya jawo tata ledar ya bude wani dan qaramun murmushi ya saki😊hadi da wani abu mai kamar tausayi da ya kamashi,sam list din siyayyar da aka turo masa nata bai kai daya bisa biyar din siyayyar samira ba,ya tashi ya bude dan qaramin pridge din dake dakin ya debe ive cream din ya zuba aciki ya hade ragowar kayan ya dora bisa bedside
Kwananta biyu kenan tana fama da matsanancin ciwon kai da yaqi saukar mata ta wani rame tunani biyu ne ya addabeta,yiwuwar qara masu abokiyat zama wanda take ganinhaka wabi babban qalube ne da zai qara nisanta ta da aliyu sai kuma raahin sauki na qiyayyar ta da take gani qiri qiri atsakiyar idanun Aliyu
Mrs muhammad ce
Yauma tana kwance saman carpet ta kanta bisa pillow kwanciyar rub ciki tayi saboda yadda take jin kan nata kamar zai tarwatse doguwar rigar bacci ce a jikinta iya gwiwa,gashin ta yayi dai dai kan pillow din,idanunta runtse suke ciki n haka ta jiyo sallamarsa,ta kadu sosai wanda hakan ya sake haifar mata da wani ciwon ko motsi ta kasa yi bare tayi yunqurin barin falon,tana jinsa har ya qaraso kanta yana sake maimaita sallamarsa,sai dai dif ta kasa amsawa sai wani bari da jikinta yake yi,yasa qafarsa ya dan bigi gefan pillow din da take kai ga zatonsa bacci take saidai nan ma yaji shiru,hakanne ya danso taba tunaninsa,ya sunkuya a hankali yasa hannayensa biyu ya birkitota gaba daya ta dawo rigingine fuskarta cikin tasa saidai idanunta na runtse don wani tsoron ne ya sake mameyeta,hawaye ya gani sharkaf a fuskarta ga wani dan banzan zafi da jikinta ya yi har haqoranta sun fara haduwa da juna”subhanallah😳”aliyu ya fada,surarta gaba daya ta bayyana har baisan sanda ya fadi hakan ba kyakkyawan gashinta ya sauko ya rufe fiye da rabin fuskarta,sai kuma yadda jikinta yayi zafi da yawa da yadda idanunta suka tasa,ya sunkuceta kamar wanda ya dauki tsinken sakace yana laluben bedroom dinta
Saman gadonta ya ajjiyeta ya zuba hannayensa cikin aljihun wadonsa yana kallonta ya rasa mai ya kamata ya yi mata wane taimako ya kamata ya fara bata,don da gaske tanajin jiki rashin lpyr na damunta,a hankali ya bude labbansa yace”relieve ur self and stop d crying “sai da ya kwashi kusan minti biyar sannan yace”already dama baki da lpy?”ta gyada kai ya sake tambaya”meke damunki?”ta nuna masa kanta,bai sake cewa komai ba ya shiga toilet dinta ya hada mata ruwan wanka mai dumi a bathtub sannan ya fito “kishiga ki shirya kanki likita zata zo”daga haka ya fice,ta daddafa bango ta shiga toilet din ta sabe jikinta ta dawo ta saka doguwar riga ta atamfa mai dogon hannu ta fesa body spray ta hade kanta da band qarami ba tare da ta taje shi ba ta koma ta kwanta,bata dade da kwanciya ba taji ana knocking aliyu ne ya tura ya shigo bai dubeta ba taji yana bada umarnin a shigo
Likitace sanye da kayan aiki,aliyu dama bai lamunci hurda da likita namiji ba akan matsalar iyalinsa tun usuli tun maman iftihal doctor sa’adah itace family doctor dinsa ta qware sosai akan aikinta tasan me take tamakar mayya haka take akan cuta da maganinta,da sallama ta shigo farar macace dirarriya wadda aqalla shekarunta ba zasu haura talatin da biyar zuwa arba’in ba doctor sa’adatu akwai ta da fara’a don.mawuyacine kaga fuskarta babu murmushi yanzun ma da fara’ar a fuskarta suka gaisa da fadila tana mata sannu yayin da Aliyu ya jawo dresaing chair dinta ya zauna hadi da zaro wayarsa ya soma danne danne,doctor sa’adah ta ajjiye kayan aikinta a gefan gadon ta fara fito da su tana tsokanar fadila”Allah dai yasa qaruwa muka samu madam😃”kunya ta kama fadila don a haife doctor ta haifeta,ta dan saci kallonsa sai ta ga ma sam hankalinsa bai kansu
Cikin qwarewa ta soma aikinta tana gwaje gwajen tana hada mata da tambayoyi,tambayoyinta har suka so rikita fadila domin tamakar doctor na son karanto zuciyarta ne ,fadila tayi ajiyar zuciya lkcn da doctor ta tsagaita da tambayoyin ta zauna a gefan gado yadda zata iya fuskantar aliyun sosai tace”gsky a.s maitama damuwa ce fal a zuciyar madam wadda itace musabbabin wannan ciwon nata wanda Allah ya gani da ace tana fa qaramin ciki da tuni tayi miscarriage dinsa,aliyu ya maida wayar sannan ya kalli😒sa’adatu ba tare da yace komai ba tasan bazaiyi maganar ba don ba komai yake bada amsarsa ba saboda haka sai kawai ta dora da bayaninta”ya kamata ka binciki abinda ya sanyata damuwa mai yawa haka,ya dauke idanunsa daga kan likita yana duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa yace”doctor iya sanina bata da wata matsala amma gaki gata ai u can ask her”ya dago kyawawan idanunsa masu tafiya da zuciyoyin miliyoyin ‘yammata ya zubesu fes bisa fuskar fadila,tayi gaggawar yin qasa da kanta don kada tana fama da kanta ya baro mata wani aikin,tasan cewar a yadda take jinta dinnan matuqar ta yadda suka hada idanu to la shakka qaryarta ta qare domin daga shi har sa’adah ba zasu sja wahalar gano mai ke dawainiya da zuciyarta ba”meye damuwarki?,ya furta cikin dakakkiyar murya ba tare da ya dauke idonsa a kanta ba ,da zata iya ba shakka da tace masa kaine!,kishinka da qaunarka aliyyu sune damuwata!!!,sai fainkash ko kusa bata jin zata iya,abinda take jin zata iya kuma ahi yafi dacewar tayi din shine shiru kuma shi tayi din
Shiru din kuwa ya ratsa dakin doctor sa’adah tace”mai tama ba haka ake ba,it can be d screat ne she dnt wanna share it with another person so ka bari idan na tafi ta gaya ma a nutse”ta qarasa maganar tana yago pepper daga memonta mai tambarin asibitinta a jiki ta soma rubutu bayan ta kammala ta ajjiye takardar kusa da fadila da har yau kanta ke sunkuye tace”to madam Allah ya qara sauqi but pls kiyi qoqarin rage damuwa”kai ta daga ta mata godiya,sa’adah ta kalli aliyyu tace ga magungunan da za’a siya mata a nemo.yanzu ta soma sha zata samu relief insha Allah amma ta dan ci wani abu before ta sha din,ta miqe tana hada kayanta tqna musu salllama aliyu yace”thanks sa’adah a gaida yara
Mrs muhammad ce
📚📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Wa yasan gobe?
▶1⃣7⃣
Fitarta da yan mintina aliyu ya dauki pepper din maganin ya fice ba tare daya ce mata kanzil ba,shima ba dadewa da fitar tasa wayarta dake qarqashin pillow ta dau tsuwwa alamun shigowar kira,a kasalance ta daga wayar tana duba mai kiran sister farida ce ta daga hadi da yin sallama farida tayi dan jim sannan tace sister ya naji muryarki ta canza ne?fadila cikin muryar marasa loy ta masa mata wlh bani da lpy ne farida ya gida ya kuma mubarak?cikin yar qaramar dariya farida tace duk muna lpy sister ko ta samu ne?,samuwa kamarbyaya? Ta tambayeta,farida tayi qasa da murya tace ian nufin fa juna biyu,ta dan basar tace abinda kika bugo ki tambaya kenan?,a’ah anty dama ina ceqa ne gibe ki duba haya ina nan zuwa harda result dinki tun last week ya samu,duk da bata jin da lafiya hakan ya mata dadi sosai har ta nuna zumudi,jin bata da lpy yasa farida qyaleta akan sai tazo goben,ta amsa don dama kantabhar ya soma sarawa ta maida kanta saman pillow ta kwantar tana addu’ar Allah yasa ta samu damar aiki
Ya shigo hannayensa biyu riqe da ledoji ya shigo ya zubesu kan bedside ya maida hannayanaa aljihu kamar kullum,ji tayi kamar ya cika mata dakin wani kwarjininsa ya cika mata gu jikinta yayi sanyi tanajin kamar ko hannuta ba zata iya dagawa ba ta shiga satar kallinsa duk fa batayi niyyar yin hakan ba zuciyarta ce ta tursasata kansa na qasa ne yana kallon carfet kamar mai nazari,sai ya mata kyau sosai fuskarana fes kama ganinta kasan tasan hutu tabbas maza irin aliyu sai ka tara dari zaka samu biyu cikinsu ga tsawo da qaqqarfan gangar jiki mai murdadden damtse mai cike da qarfi faffadan qirji mai cike gargasa wadda ta bayyana har hannayensa yana da jiki amma ba zaka kirashi mai qiba ba domin tsawonsa ya shanye ta,kusan ko yaushe fuskarsa a haka take ba fara’a sam don ita a iya saninta da shi bata taba ganin haqoransa ba,
Saura qiris ya kamata tana satar kallonsa tayi gaggawar janye idanunta daga kanshi a hankali taji yace dazun na tambayeki meye damuwarmk yanzun ma na maimaita karo na biyu”shiru ta sake yi.masa hakan yasa ya kausasa.murya yana sake tambayarta,cikin cool voice dinta tace babu komai,ya dago kamar zai kalleta sai kuma ya lumshe ido ya budesu kan.ledojin da ya shigo da su sannan yace idan tashin hankalinki da damuwarki sun ta’allaqa ne kema kan dawowar maman iftihal to kiyi saurin taimakawa kanki ki nemi sassuci a gun zuciyar ki don zata dawo ne amatsayin mata ta karo na biyu ba wata baquwa bace……sannan ki bawa zuciyar dai taki again shawara da kada ta cika kanta da damuwoyi masu yawa tun yanzun……ya danja fasali sanna ya miqa hannunsa ga wayarta dake gefanta abinka da giant tuni hannun yakai ba tare da ya hau gadon ba ya lallatsa sannan ya ajjiye mata yace”ga abinci nan da magunguna ki sha,then ga number ta if there is any problem contact me”daga haka ya juya ya fita ba tare da Saura ron komai ba
Sai abun ya zamewa fadila wani iri ta jima akwancen kafin ta samu damar miqewa zuciyarta na qarfafa mata gwiwa ta tashi ta taimaki kan nata kamar yadda aliyu ya shawarceta,tq shiga toilet tayi fitsari sannan ta daura alwala wai ko zata ji sauqin zugin dq zuciyarta ke mata,ta dawo bakin gadon ta bude ledojin daya magunguna ne a ciki daya kuma gasashshiya,ta dinga zare tsokar tana ci zuciyar ta dauke da addu’o’in samun sauqin daga quncin zuciya(inda Allah ya taimaki fadila kenan bata mantawa da add’a duk irin situation din da take ciki,muyi koyi da ita yan uwa domin hatta qaddara babu abinda yake tareta sai add’u’a,mu dinga tuna Allah a yayin da muke cikin jin dadi da walwala sai Allah ya tuna da mu lokacin da mu kuma muke cikin qunci da neman taimakonsa wannan fadar annabi ce s.a.w,kai ta addu’a da sannu Allah zai isar maka,take note pls!)jin naman take kamar magani mai daci haka taci gabada dannashi har tqji kamar zata yi amai,ta balli.maganin adadin yadda aka rubuta tasha sanna ta dan zauna na mintina don abincin ya fada mata sanna ta ja pillow ta kwanta,cikin ikon Allah ta dinga jin sassuci a zuciyarta,ta jawo wayarta sai taji tana qamshin aliyu ta soma duba contact dinta taga number din da yace yasa mata ai kuwa a rukunin A taci karo da sunansa full name dinsa ya saka mata ta bude numbers din tana qare musu kallo suma special ne don cikin taqaitattun daqiqu zaka iya haddacesu,(mrs muhammad nace ko na sato muku numbers din A.s maitama ne cikin wayar fadilan?to gasu 0803344…….😜😜 to naqi don naga wata har tana saurin kwafa ba ruwana ku da fadila😜)ta zuba musu ido kamar tana son ganin fuskar mamallakin numbobin da ta gaji da kanta ta rufe wayar ta maida ta qarqashin filon ta lumshe idonta tana maida numfashi cikin zuciyarta ta soma tilawar suratu yusuf tana yi tana bin labarin annabi yusuf din da Allah s.w.a ke bayarwa cikin surar,zuciyarta ta mata sanyi damuwarta ta ragu sosai lallai Allah yayi gaskiya da yace(ala bi zikrillahi tadma’innal qulub/ku saurara da ambaton Allah ne kadai☝🏼 zukata ke samun nutsuwa)
To fa makaranta na labari yanzu muka soma shigarsa kuci gaba da jumurin bina insha Allah zamu cimma gaci😊
Dumbin godiyata a gareku
Mrs muhammad ce
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻……..
[10/16, 12:35 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Wa yasan gobe?
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶1⃣8⃣
Washegari misalin sha biyu na rana tana kitchen tana tafasa ruwan lipton so take ta dan sha ko zai warware mata ciki don tun tashinta yau ba abinda ta iya ci,muryar farida taji tana qwali mata kira da gudu ta fito suka rungume juna suna dariyar farincikin ganin juna😄,farida ta dan janye fadila daga jikinta tana cewa sister yi a hankali kada ki mana asarar baby,fadila ta ballamata harara tace”wai ke wa ya baki wannan labarin qanzon kuregen?farida tace bayan mun gama waya jiya da ke da daddare rabi’ah ta kira ni take gayan again,fadila na qoqarin komawa kitchen din tace uhm sai ki zauna ai kiyi ta jiran cikin,farida tayi dariya ta bita,maimakon daba lipton sai ruwan zafin ya koma na girki,suna yi suna casar hira,suka kammala suka zuzzzuba su a warmers suka wanke kwanukan hadi da gyara kitchen din
Wash! Inji farida bayan ta zauna fadila ta kalleta tace kin canza sister fa sosai kinga qibar da kika fara yi?farida tayi murmushi tace ke dai bari ya fadila ina tsammanin ciki ne fa?,fuskarta cike da fara’a 😄tace ke dan Allah,tace wlh da jibi ko gobe mubarak ya matsa sai naje an min test wai kada na jawo masa asara cikin rashin sani ni sai naga kamar ba shi ba,kasala kawai fa nake da yawan bacci,fadila tace,a’ah nima fa ina bayan mubarak sister kije a dubakin meye amfanin zaman haka,kina likita ai kinfi kowa sanin alfanun abin,tace insha Allahu gobe zamu je
Farida ta janyo jakarta ta bude ta miqawa fadila takardunta,cikin zumudi ta buda tana duba result din ba abinda bakinta ke fada sai alhamdulillah,domin kuwa yayi kyau fiye da yadda ta tsammata cikin farinciki tace da farida”burina na gaba farida inga na soma aikin media shine burina tun ina qarama”murmushi ta sakar mata tace”kwantar da hankalinki ya ahmad yana can yana miki wannan aikin don kuwa freedom da express tuni sun karbi takardunki jira yake kawai yaji daga garesu,wani farincikin da qaunar yan uwanta ya sake kamata
Tana toilet tana wanka ta bar farida a afalo tana kallin arewa 24 suna haska maimaicin shirin boyle bitmesin wato kyautata rayuwa da yake jiya tace tayi missing bacci ya dauketa bata kalla ba,ta jiyo hayaniya sama sama ta tsinci dai muryar anty hauwa din haka a gurguje ta gama tana fitowa ta shirya kanta cikin shigar doguwar rigace ta shadda wadda aka mata paint work mai tasadar orange ce akayi mata kwalliyar light blue,body spary kawai ta fesa ta daura dankwalinta ta debo magungunanta wadanda zata sha da rana ta fito falon,rabi’ah ce da sumayya da anty hauwa,cikin fara’a suka gaisa suka mata sannu da jiki”tace ai na samu sauqi ina momy da iftihal mutuniyata,anty hauwa tace suna gida gurin momyn nace ne ba da wanda zanzo duk har su kausar suna gunta muhammad ma tunda ba nono yake sha ba acan na barshi don suna zamu wuce dqga nan wata maqwafciyata ce ta haihu to kuma da yake haihuwar ta danzo da matsala a gidan su take acqn za suyi taron,tace eh Allah ya qara mata lpy,amin inji anty hauwa
Nan suka shiga hira abinsu minti talatin suka miqe suna shirin tafiya fadila dake ta qoqarin zuba musu abincin tace anty ga abinci don Allah ku tsaya kuci,anty hauwa tace bayan lemo da cake da kika cika mana ciki da shi alhamdulillah wlh,rabi’ah tace nikam anti fa na fasa rakiyar nan gidan sunan kuce da maman hidaya ina mata barka na taho anjima farida ta saukeni a hanya,sumayya tace”dama na sani anti ba rakaki zata yi ba ina ji tana cewa yau ana rana da yawa nasan dama daga nan gidan ba inda zata dara”aishikenan muje mu gaisa da samirah sai.mu wuce,inji anty hauwa,sumayya ta coge😒sannan tace a’ah anty nikam zan jiraki cikin mota ki shiga ki fito tayi saurin yin gaba damma kafa antin ta tsayar da ita,fadila tace “baki kyauta ba sumayya idan kika wuce baki gaidata ba”rabi’ah dake zaune tace wlh anty ko nice ba zan je ba,farida dake ta faman cin abincinta abunta tace qyalesu sister mai daki shi yawan inda yake masa yoyo✋🏻,ai kuwa dai sister farida sai.kaje kayi ta bugu taqi budewa gashi fa kana kallo ta tana kalloka qiri qiri,bayan kuma ta bude sai tayi.bake bake a bakin qofa ta tsare ka da ido tana wani ce maka meye?kamar wanda kazo maula gurinta,duk suka kwashe da diyar yadda rabi’ah ta gwada yadda samiran keyi banda fadila da ta dan murmusa gami da girgiza kai tana mamakin halayya irinta samirah
Biyar da rabi farida ta dauki rabi’ah suka tafi suma sashen sai ya dawo sai ita kadai ta so ta yiwa farida zancan dawowar maman iftihal sai kuma taga mai hakan zai dadeta da shi iyaka ta taya ta jimami sai shawara wadda a yanzu ita ma bawa kanta da kanta take,tunanim data fara yin zurfi a ciki ne yasa barin kanta ya soma ciwo bata yada hakan yayi zurfi ba ta tashi ta jona home theatre dinta ta saka cd plate na karatu ya karade falon
Takwas da mu
mintina na dare nasiru ya turo hancin motar ogan nasa cikin gidan,ya samu parking space ya daidaita tsayuwar motar sanna ya kasheta,a hanzarce ya fito ya budewa aliyu shima ya fito sannan ya miqa masa keys din motar yana fadin gashi sir ya amsa yana cewa debo min files din nan na sit din gaba,ya debosu ya bashi sukayi sallama aliyu ya sallameshi,hankalinsa gaba daya ya yi gaba burinsa kawai ya isa sashen nasa ya watsa ruwa a jikinsa ya samu ya kwanta ya huta,ya soma tafiya idanunsa suka kai kan sashen nata babu wadatar haske kamar bangaren samira dake tarwai da haske harda qarar abin kida ya dauke kai ya shige
Yana fitowa daga toilet ya zabi doguwar riga jallabiya fara sol.mai yankakken hannu ya saka ya feshe jikinsa da turarukan baccinsa masu sassanyan qamshi kan sofa ya fada ya miqe qafafunsa sannan ya hardesu ya kansa na kallon sama yasa daya hannun nasa ya shafi cikin sa,yunwa yakeji amma ya rasa inda za shi ya samu abincin da zai gamsar da shi,mutum ne shi.mai tsan tsami ba ko ina yake iya saki jiki ya ci abinscinsu ba sai ya yarda da ingancin tsaftarka hakan ne yasa ya tsani masu aiki hakan yasa tun yana gida ya yi ruwa yayi tsaki ya hana mominsa daukar masu aiki yace meye amfani su sumayya duk da suma bai yarda ko kadan yaci girkinsu sai na mominsa
Ya tashi ya qarasa fridge ya bude ya dauko yoghurt na l&z ya hado da fura ya samu cup ya dama ya sha ,ya sake tashi ya maida cup din kitchen sannan ya qarasa window dinsa yana bude glass din don ya bawa iska daman shigowa duk da iskar a.c da ta mamaye dakin kasancewar mutum ne shi maison natural air,idonsa ya sake fadawa kan bangaren nata duk da yaune ya shigo bashi da niyyar ganin kowa bacci yakeso ya samu isashshe don haka har wayoyinshi ya kashe su gaba daya
Ya saki labulen yana ajiyar zuciya saboda tunawa da yayi haqqine a kansa ya kula da lafiyarta don rabonsa da ita tun jiya da ya batta da magungunan da ya siyo mata ,ya zari keys dinsa ya zura slippers dinsa ya fice
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶1⃣9⃣
Tana kwance a miqe sambal bisa kujera three sitter don tunda tayi sallar isha’i bata tashi ba agun falon tsit yake ba komai sai sanyin na’urar sanyaya daki wanda ta gauraye da qamshin freshner mai dadi idanunta na lumshe ne tamkar mai bacci saidai ba bacci take ba tayi nisa ne a wata duniya mai wuyar fassarawa duk da ciwon da kan yake mata das das das amma hakan bai dameta baqarar bude qofan falon da qamshim mayen turarensa dake rataye da zuciyarta shi ya dawo da ita,ta bude manayan idanunta akansa yayin da shi kuma ke qoqarin tura qofar tayi namijin qoqarin tashi ta zauna kanta na sunkuye a qasa don ba zata iya jurewa kallonsa ba,hannayensa ya goye a bayansa ya qaraso falin yana kallonta da qayatattun idanunsa ya lura kamar ta dan rame duk da ba sanin ainihin kamanninta ya yi ba”ina yini”tace still kanta na qasa,cike da qasaitarsa da izzarsa ya dauke kai ya maida mata gaisuwarta da tambayar jikinta,da sauqi ta fada cikin sassanyar muryarta data sanya yaji wani dan yam ajikinsa
Bata zata ba bata kuma tsammata ba sai jinsa tayi zaune kan kunerar da take kai.kuma dab da ita ya sanya bayan hannunsa a wuyanta da niyyar jin temperatures din jikinta ba komai aransa,sai dai baisan illar da ya sake yiwa fadila ba a zuciya da gangar jikinta ba,kasala mai tsanani tashi guda da kuma wani irin shauqi taji ya saukar mata numfashinta ya tsaya cak na wucin gadi,sam bai kulaa ba yace”still jikinki da ragowar dumi ya kamata ki warke kafin isowar abokiyar zamanku right?ya qare maganar da sigar tambaya,ya.miqe yana cewa babu abinda kike buqata,tamkar ta ce masa”kai nake buqata aliyyu ka qarashe awoyin wannan daren naka tare da ni,maimakon haka sai ta sake gyada masa kai,yace ” alright gudnyt”ta bishi da kallo idanunta fal cike da qaunarsa da kewarsa har ya fice daga part din nata ya rufe mata part din,ta koma da baya ta jingina jikinta da kujerar hadi da runtse idanunta hawayen dake maqale a idonta suka gangaro mata wani radadi da zugi zuciyarta ke mata lallai kishi masifa ne
Cikin daren bacci gagararta yayi juyi take kawai akan makeken gadonta cike da sha’awar aliyu tunda take bata taba jin makamanciyar sha’awa arayuwarta irin wannan ba
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Sannu a hankali ta miqa dukkan lamuranta ga Allah cikin ikon sa kuwa ta fara samun sauqinsu saidai fa har yanzu babu sauqi ta bangaren soyayyar Aliyu dake maqare cikin zuciya ,cikin lokacin sam ta daina bari idanunta suga aliyyu duk da tarin zugi da zullo da zuciyar keyi na son ganin nasa amma ta danneta
Cikin lokacin aikinta ya samu freedom da express din duk suka buqaci yin aiki tare da ita,ya ahmad dinne ya kawo.mata da kansa bayan ya sanar da aliyu da kansa ya kuma amince mata da fara aikin nata,tayi murna tayi tsallae tun a gaban ya ahmad din ya sha godiya sosai har da qwallar farinciki saboda yadda take masifar son aikin jarida shikam dariya yayi yace Allah zata godewa,bayan tafiyarsa ta kira farida dake fama da laulayi suka sha murnarsu tare,nan fa ta zauna ta soma tsarawa kanta yadda zata tafi da rayuwar aikinta
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Cikin satin Aliyu ya shirya musu fita wadda ta farko ce agun fadila don bata taba fita ba wani gu da sunan unguwa ba bayan shopping da suke zuwa duka qarshen wata za suje ne gaida hajiyarsa
Tun rana fada ke zumudin fitar tana tunanin mai zata kaiwa momin,akwatunan lefenta dake shaqare da kaya wadanda kamar ba’a taba amfani da komai a ciki ba ta bude ta zabi turarurruka designers guda uku ta warewa abba,ta duba akwatinta da ta adana gift da ta samu na biki ta cirarwa momin atamfofi super Holland da England guda biyu,da kanta ta aiki yaron dake musu gyaran flowers ya samo mata kilishi mai kyau da zuma
Tun magariba ta yi wanka ta shirya kanta cikin atamfa dinkin riga da zani kamar light grean da milk sai ratsin baqi dinkin ya mata cas kamar a jikinta aka qirqireshi yari da sarqa ta saka ma dutse masu kalan milk sai farin agogon hannu tq zuba awarwaro mai 24 farare takalmi da jaka milk sai laffaya data nannade jikinta da ita milk ce mai adon baqi ta debi tsarabarta ta dawo falo ta kunna arewa 24 tana kallon shirin matasa at 360,tayi wani masifar kyau ta fito sosai a babarbariyar ta
Ya qarashe karin hular sa yana daidaita ta a kansa shaddace fara qal a jikinsa dinkin tazarce sai walwali take ta sake fidda sirrin kyawunsa mutum ne shi ma’abocin iya ado ta wannan fannin kam ko mace haka ta ganshi,komai nashi fari ya sanya hatta da agogo,ya sanya glass dinsa sanna fesa turarensa ya rufe sashen
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶2⃣0⃣
Bangaren samirah ya nufa wanda sai ta kama dole yake shigar sa,ga mamakinsa aai ya taddata sirshan tana zaune abinta zaninta da rigarta daban daban kanta da ta tsefe shi yana tsaitsaye kamar tabarya😜dama ita ba wani tsawon gashi gareta ba sai qarfi da gashin yake da shi,ba abinda falon keyi saiqarnin kifi sardine ta tara gwangwanayen a gabanta ua daurw yadda qarnin ke bugar hancinsa yana tayar masa da zuciya cikin bacin rai yace mata zaman me kikeyi baki shirya ba tun dazun?ta dan yatsina fuska tace qawatace wlh ta kiarani a waya ta kwasheni da jira ya gyara tsaiwarsa cike da qosawa da azababben qarnin kifin yace mata is ok sai ki nemi wanda zaku tafi tare kinsan bana jira yana kaiwa nan ya sanya kai zai fice yana jan tsaki cike da takaici ,ta yi saurin shan gabansa tana cewa haba sweet kayi haquri mana pls ka bani minti uku kaya kawai zan canza,ya kauce ya fice yana cewa wataqila idan kinyi sauri kin tadda ni kafin in ciro mota is ok,ya barta nan baki a sake ta bishi da kallo sai kuma ta zabura tayi cikin daki don ta shirya
Knocking taji anayi don haka ta zira hill shoes dinta fari ta rataya jakarta ta dauki ledarta don jikinta ya bata aliyu ne shi dinne kam idonsa na bisa screen din wayarsa yana danne danne bai dube ta ba ya juya taja part din nata ta kulle tabi bayansa tana qare masa kallo”ya gaji da haduwa”ta zanta hakan a ranta,tana jingine da rumfar ajiyar motoce har ya gyara parking qa’idarsa ne indai tare zasu fita baya neman driver duk da dama nasiru ne kawai.ke driving dinsa,wanni dogon hirn ya ja da sauri ta daidaita nutsuwarta ta nufo motar tun kafin ta qaraso taji an bangaji kafadarta da mamaki ta dago don ganin waye samirah tana ta zuba sauri zani a hannu tana gyara daurinsa,duk saurin da take gidan gaba aahe takewa,abun ma sai ya baiwa fadila dariya ta saki murmushi😊
Cikin mintuna da basu gaza talatin ba suka qaraso gidan,harabar gidan tsaf kuma fetal da haske ba kowa sai mai gadi shi da wasu mutum biyu zaune kan benci suna sauraron duniya tumbin giwa suna cin gyada jefi jefi suna taba hira,cikin girmamawa ya gaida aliyu sannan ya gaida su fadila ta amsa masa fuska a sake tunda dama da yar sanayya tsakaninsu ya samirabko kallo bai isheta ba bare tasan yana yi,ya dage masa get din ya wuce ya yafitoshi yayi masa ihsani kamar yadda ya saba shi da wadanda ke zaune a gun suka hau zuba godiya abinsa shi kuma baiso
Samira da aliyu suka jera suka fara yin gaba zuwan falon gidan fadila bin bayansu tayi ,sumayya da rabi’ah ne zaune a falin da hijabai ajikinsu da alamar sallar isha’i suka idar,suka juyo suna amsa sallamar sannan suka miqe tsaye cikin farin ciki suna gaida su hankalinsu na kan fadila itama su take kallo suna gaisawa sabanin samirah da ta riqe qugu tana qarewa falon kallo tana yaba tsaruwa da dukiya da ya lashe kamar wadda aka bawa kwangila sannan daga bisani ta zabi kujerar da tayi.mata ta zauna akai,cikin dakiya irin ta babban wa yake tambayarsu ina momy sumayya tace tana sama ya nufi benan taku biyu uku sukayi kacibus da iftihal na saukowa kamar yadda ta saba ta tsugunna ta gaidashi sanna ta daneshi ya sabeta a kafada yana tambayarta momi
Tare suka sauko shi da momin yana take mata baya iftihal na hannunshi ganin fadila ya sata ta zille ta diro ta nufeta a guje cikin murmushi fadilan ta tareta ta dora ta bisa vinyarya dukkaninsu suna dariya ta gaisheta,duskar momi washe da fara’a take.musu barka da isowa samira dake zaune dare dare bisa kujera kamar tata tave yauwa fadila dama.na qasa ne kan carpet ta duqar da kanta qasa tana murmushi cike da kunyar momin,gaisuwa aukai da samirah kamar qawa da qawa yayin da fadila ma ta kasa hada ido da ita a haka suka gaisa,ganin taqi sakin jiki ya sa momyn tace su rabi’ah su kaisu dakinsu itama zata gun abbansu yanzu ya shigo gidan,hira suke abinsu da fasika yayin da samirah ta zaro wayarta ta hau danne danne tana ganin duk ta girmesu tafi qarfin zama cikinsu ai,ga takaicin yadda aujewa fadila haba haba itq aunqi mata haka cikin ranta take cewa hmm dangin miji kenan tsinannu(kunji fa?)
A haka bacci ya dauki iftihal akan cinyar fadila aliyu ne ya leqo hukarsa a hannu yace ke sumayya ku taho dining”samrah ce ta fara miqewa tana cewa dama yunwa nake ji ta fice,qememe iftihal taqi kwanciya dole iftihal na nishi ta sabota a kafada suka fito su sumayya nata dariyar yadda ta dauki ifrihal din da qyar,momy ce da abba sai aliyu bisa dining din kusa da abban abba na dariya yaceyau ban dawo da wuri ba bare a murqushen tsohon
qashi na shine aka rama akanki ko?
Duk sukayi dariya kowanne ya samu kujera daya ya ja ya zauna banda fadila dake tsaye sabe dà iftihal wani baccin nason daukarta amma ta qi yarda tayi don kada a sauketa
Mrs muhammad ce
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Wa yasan gobe?
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶2⃣1⃣
Momy ta kalli aliyyu tace alii rabata da rigi mammiyar yarinyar nan don idan ba kai ba ba wanda zata yarda ya sauketa,ya miqe ya nufesu yanayin yadda ya tsaya gab da ita yana yunqurin karbar iftihal ya haifar mata da wani yanayi cikin jikinta,ya sa hannu zai dauketa cikin rashin sani hannunsa ya shafi qirjinta wani abu taji ya tsirga mata tun daga kanta har tafin qafafunta hakanan shima yaji tsigar jikinsa ta tashi wani shocking yaji kamar an jashi da wutar lantarki,ya sabata a kafadarsa ta miqe zata soma rigima suna hada ido da shi tayi gum da bakinta🤐 ta mayar da kanta kafadarsa ta kwantar ya sauka da ita cikin falom ya kwantar da ita bisa doguwar kujera ya karanta mata addu’o’in bacci na tsari ya tofa mata sannan ya koma
Ta tsugunna ta gaida uncle abba ya amsa mata cikin kulawa yana cewa lpy lau diya ta,sannan ta ja kujera itama ta zauna,sumayya tayi serving din kowa🍽🍴 sannan akai bismillah aka fara ci,kwata kwata kasa sakewa fadila tayi ta kasa kai koda loma guda bakinta sai juya cokalin kawai take a cikin abincin ,amma ga tarin mamakimta sai taga samira ta saki jiki tana ta kaiwa uwar hanjinta🍜 harda tsiyaya lemo 🍹🍾da ruwa da kanta,tayi sakewar da ko ita da uncle abba yake kamar uba a gareta ba zata iya irinta ba
Abinka da mata momi na ankare da yanayin nutsuwar kowaccensu tana kuma sake godiya ga sarki Allah da ya qaddara fadila ta zamo daya daga cikin family dinsu,afakaice rabi’ah ta qarewa samirah kallo uadda take lodar abincinta ko aliyyu da yake dan gida baiyi haka ba,ki saki jiki mana fadilan ummi kici abincin ki mu fa iyayenki ne ko babu aliyu baki ga yadda yar uwarki ya saki jikinta ba?,cewar ummi,samirah ta amshe cikin tabe baki tace momi kinsan wani akwai qauyanci da rashin wayewa atare da shi”sai kowa yayi dif rabi’ah da takaici ya cikata tace ba rashin wayewa bane kowa dai da irin yanayinsa,ta sake tabe baki tace uhmm,ita kuwa fadila dariya ma ta bata sai daga qarshe ne taga kada suji ba dadi ta kurbi lemon da rabi’ah ta zuba mata
Bayan sun kammala momi tasa rabi’ah da sumayya suka gyare gurin suka kwashe kwanukan,suna shirin wucewa don su basu guri momi tace su dau iftihal su wuce da ita,falon yarage daga fadila aliyu samirah sai momi da uncle abba
Abba yayi gyaran murya yayi bismillah sannan ya kirawo sunan aliyu ya amsa masa”naam abba”ya dora “aliyyu girma yanzun ya hau kanka duk da a baya kwatan kwacin wannan girman ya taba hawa kanka kuma kayi namiji qoqari wajen riqeshi yadda ya kamata amma bai kai wannan ba,a yanzu dole na sake jaddada maka saboda zama ne da zaka yishi tsakanin iyalinka har su uku wanda ko ni mahaifinka banyi duk da komai tsarin Allah ne
Daga samirah har fadila babu wadda gabanta bai fadi ba har sai da samiran yabdaga kai ta kalli abban,uncle abba yaci gaba “lamarin mata ali sai da haquri kawaici da kuma jajircewa halitta ce su maau wuyar sha’ani amma idan ka duba Allah sai komai ya zo maka da sauqi ,aliyyu ina horarka da kaji tsoron Allah ka tsaida adalci tsakanin matanka duk wadda ka cuta wlh wlh sai allah ya bi mata haqqinta sai kuma ya tambayeka,kuma ko ni ban lamunci rashin adalci ba acikin gidanka ka riqe Allah ka kuma ji tsoronsa
Ya juyo gunsu fadila da kansu ke qasa kowa da abinda ke cikin zuciyarta yace “dukkaninku ina kallonku ne a matsayin ‘ya ‘yana na na cikina da na haifa nasihar da zan muku itace kuma ku ji tsoron Allah kuyi zamqn aure a matsayin ibada kuyi biyayya ga mijinku.ku kyautata zamantakewar ku domin kuwa shine muqullinku na shiga aljanna ko wuta idan kuka saba masa Allah ya tsare mu,magana ta biyu kuma na dakatar da shi ne daga gaya muku don inason na gaya muku ni da kaina ta hanyar da ta dace,nasan kowacce mace haka Allah ya halicceta da kishi kuma ba zaku so abokiyar zama ba a yanzu amma ba yanda muka iya da hukuncin ubangiji kuma aure rai ne da shi matuqar bai qare ba komai dadewar zamani sai an dawo anci gaba da yinsa to ina mai baku haquri a madadin aliyyu,mahaifiyar khadija(sunan iftihal na gsky haka abba ke kiranta yawancin lokuta)zata dawo dakun aurenta ina fata zaku hada kanku ku zauna lpy,samirah ta dago kanta a gigice tana fiddo da idanu waje😳tace”abba mai kake fada ne?dama da gaske aliyu yake da yafara zancen?” aliyyu ya juyo ya kalleta wani huci ya saki abba ya lura da yadda yanayinsa ya canza ya san yadda fishin aliyyu yake don haka ya danne shi,cikin tausasawa ya kalli samira yace ki kwantar da hankalinki yata insha Allahu ba zaku fuskanci rashin adalci ba daga gun aliyu ni kaina bazan lamunci hakan ba shiru tayi tana muzurai idonta ya kada yayi ja saboda ganin yadda aliyu ke gasa mata hara ra tamkar zai cinyeta danya,itakam fadila gabq daya jikinta ya saki tunaninta daya ta ina zata samu aliyyu bayan ga wasu na farautarshi ? Jin sunyi shiru dukkaninsu abba yace da momi”kina da magana momin yara?” Ta danyi murmushi tace” aikace komai abban yara,saidai nace aliyu kaji tsoron Allah kamar yadda abbanka yace sannan ku kuma Allah yayi muku albarka kuyi haquri kuma kuyi biyayya sai.kuci riba”suka amsa da amin banda samira da ta kasa furta komai sai tafasa da zuciyarta keyi,abban ya sake basu dama akan idan da mai magana ya yi,ba wadaa tace komai sai aliyu da yace”abba da momi na gode muku kuma insha Allah zaku sameni mai amfani da duk nasihar da kuka yimin zan zamo mai adalci da yardar Allah”Allah ya amince suka ce,fadila ta fito da kayan data taho musu da su ta dorawa abba nasa a gabansa sann ta dorawa momi nata
Duk da ranta babu dadi amma ta ji dadin yadda suka nuna jin dadinsu suka sa mata albarka,aliyyu kansa can qasan zuciyarsa yaji dadin hakan don shi mutum ne mai dake qaunar wanda ke kyatatawa iyayensa,haushi ya sake cika samira tayi dana sanin zuwan ta gidan yafi sau cikin carbi bata son taga wani yana yabo ko son fadila kwata kwata
Cikin mota ma kowa da irin zaren da yakr saqawa zuciyarsa shikam ya dake abinsa kamar bashi ya sanar da mata har biyu zai qara musu abokiyar zama ba tuqinsa kawai yake a nutse,fadila tata saqar na yadda zata juyo da hankalin aliyu take bata so kuma bazata so ace kishiyoyi har biyu su fuskanci raahin qauna da jituwa dake gudana tsakaninta da shi ba,samira kuwa wani mahaukacin kishi ne ke taso mata zuciyarta namata saqa da baqin zare,tana shirya mata irin mummunan matakin da ya kamata ta dauka abu guda ke taka mata burki idan ta tuno yadda aliyyu ya birkice mata da yanayin da ya sameta a daren farkonsu tasan har yanzu dafin na sukar zuciyarsa somin kuwa duk wani tanadin soyayya da sukayi wa juna tn daga ranar ya rushe,duk kuma waa qauna tata dake zuciyarsa wadda ta rage tuni ta rushe
Cikin satin komai ya fara kankama abubuwa suka cedewa baiwar Allah fadila ga zirga zirgar shirye shiryen fara zuwa aikinta ga kuma lamarin na dake mintsinin zuciyarta duk da shiryr shiryenta ya tafi da kaso.mafi tsoka daga damuwar dake cin xuciyarta,tuni tayi waya gidan an ma motocinta service daya tsohuwar tata ce tun ta gida aka sake mata fenti da wasu abubuwa sai ta tashi ta dawo sabuwa dal don tana qaunar motar bata son rabuwa da ita yanzu sai kuma wadda aliyyu ya sa musu a lefe wadda ta sam ira tuni ta dade da cin uban tata ta mora qawaye su ara suma su mora
Kira ta dinga samu daga su anty hauwa anty hafiza har da farida kowannan su nasiha ce da jan hankali ne nasa har farida ta so karayar mata da zuciya saidai tayi qoqari matuqa wajen nuna dakiya da mai da komai ba komai ba
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Wa yasan gobe?
▶2⃣1⃣
Samira kuwa abun nata sai ya zamto tamkar mai qaramin ciwon hauka kamar a kanta aka fara kishiya kasancewar ta samu gudun mawar zuga daga qawaye da yan uwa kala daban daban duk da wasu ba don Allah suke bata basuna baqinciki da rufin asirin kawai da take ciki ne(qalubale a garemu mata sai azo ayita baki shawara akan za’a miki kishiya ko wani harkar wani ahaka kamar mai sonki amma da zaki ga cikin zuciyarsa game da ke tsoronsa ma zaki koma ji,sanin haqiqanin mutum sai Allah,sai ki auna da hankali da Allah ya baki a matsayinki na mutum mai tunani)sai ta sake zama kamar zararriya ita kadai ma abangarenta sai ka jiyota tana bala’i tana zunduma ashariya(wa’iya zu billah)cikin satin baqi ta dinga yi kala daban daban kowanne da tasa guzuri da salon hudubar waccan ta shiga waccar ta fita
Tun Aliyu na zuba mata ido idan tana salon rashin mutuncinta da haukanta har sai da ya zamto idan tazo sai dai ta gajibda bugun sashen nasa ta juya da haukanta ta koma inda ta fito,tuni fadila tabgama tsarawa kanta yadda zata tafiyar da rayuwar aurenta ta gama tanadar komai,tana hango cewar itama fa maca ce tana da duk wani abu da da duk wata ya mave maiji da kanta ke taqamar tana da shi,tana da duk wasu qualities da ake buqatar mace da su kafin ta amsa sunan ta na mace,to me yayi saura banda itama ta shiga fagen a dama da ita?? Me zata jira banda ta shiga ta karbo aliyyunta? Ta gaji kuma lokaci yayi da take ganin ya kamata ace ta kasance da da shi ta gaji da dako da rainon soyayyarsa ita kadai
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Biki ya zamto saura kwana uku wanda yayi dai dai da sauran kwanaki bakwai fadila ta soma zuwa aikinta
A ranar ne bayan sallar magariba aka shigo mata da akwatina set shida masu matuqar kyau maqarenda kaya nasiru yace mata inji maigida,ta jinjina kai ta rufe qofar sashen nata ta koma kan kujera ta zauna daya bayan daya ta budesu ta zubawa kayan ido duk budurin da ake sai yanzu zuciyarta ta tsinke hawaye suka soma zarya a kuncinta a hankali take sa yatsunta tana sharesu tabbasa an jarrabci rayuwarta da jarabta mai girma ta sani cewa son aliyu jarabta ce daga ubangiji acikin jininta yake kuma bata fatan Allah ya dandanawa wata mace kwatankwacin yadda take ji a zuciyarta,nan saman kujerar ta lafe tana hawaye a hankali take furta HASBUNALLAHU WA NI’IMAL WAKIL har taji zuciyarya ta soma sanyi
Haya niya da hargowa take jiyo wa maau qarfi suna karade filin gidan hakan ya sanya kukanta katsewa ta tashi kamar mai sanda ta isa window dinta da yake cikin balcony dinta ta yaye labulen ta riqeshi a hannunta,daga nan tana iya hango dukkq sararin gidan samira ce ke wannan hayaniyar cikin hargowa da babat tanajanyo akwatina irin wanda nasiru ya kawo.mata dazu daga part dinta daya bayan daya tana cillarwa anan tsakiyar filin gidan ko nauyinsu bata ji ,aliyyu na tsaye hannayensa harde a qirji ya zuba mata ido bai ko motsa ba
Sai da ta gama lodesu sanna tayi cikin gidan nata a fusace sai gata da gallon da ashana ta daga tana qoqarin bulbula musu fetur din da yake ciki sai a lokacin aliyyu yasa hannu ya fincikota baya a fusace ya nunata da dan yatsa yana cewa kul kada ki soma,ta dubeshi duk da ta tsorata da yanayinsa amma sai ta dake cikin bala’i take cewa” sai na qona aliyu sai na qona wallahi kayan fadar kishiyan wata tsiya ce,sai dai idan na qona idan ka so nima ka qona ni” ta sake zabura tayi kan kayan da nufin idar da niyyarta cikin qaraji da tsawa ya ambaci sunanta wadda sai da hantar cikinta ta kada amma sai ta waiwayo tace”ko kasheni zakayi ba zan fasa ba” tadai sake nufar kayan cikin azama a karo na uku,cikin fusata yasa hannu ya janyota baya harsai da ta zube warwas a gun tamkar ya bita ya tattaka haka yake ji,don da namiji ne ya masa haka to yanajin ba shakka sai ya nuna masa qwarin qwanjinsa
Ta sani cewa idan taci gaba da abunda take hukuncin da zai yanke mata ba mai sauqi bane hakan yasa tana daga zaunan ta hau borin kunya cikin surutai da maganganu marasa kan gado daga baya ma da taga ya qi kulata sai ta fashe da kuka
Ko kallo bata isheshi ba ya dinga siban akwatunan bibbiyu bibbiyu ya shigewa da au bangarensa yana gamawa ya rufe qofarsa ya barta a nan,data waiga ta waiga taga ba kowa ba wanda ya gansu sai ta goge idonta ta miqe tana kade zaninta tana wa allah godiya da ba wanda yaga abinda ya faru tana yi tana tsinewa hannatu qanwarta gashinan ta jawo mata asarar akwatinan ma dungurun gum dan ita ta bata shawarar tayi haka
A falon sa ya zube ya dafe kansa hannu bibbiyu yana tsananin jimanta al’amarin to haka mata suke ne basu da hangen nesa ya jima a haka sannan ya tuno bai ma shiga bangaren dayar ba kamar yadda yake ce mata a ransa”itama idan ka shiga wataqila haukan da zata yi maka kenan”wata zuciyar ke gaya masa,ba yadda ka iya tunda itama aqarqashinka take kuma ka shigarwa ‘yar uwarta indai adalcin kake son yin
Da sallama ya shiga ta amsa a sanyaye tana zaune ne kan kujera hijabin da tasa ta budewa masu shigo da kaya har yanzu shine a jikinta saidai sabanin da yanzu akwatinan a rufe suke,a fakaice yake dan nazarin falon komai tsaf yake cike da tsafta da qamshi hakanan komai a killace yake a muhallinsa da kyawunsa kamar yau aka jerashi sabanin falon samira da komai ya fita hayyacinsa saboda rashin kulawa duk da dama tsadar kayan ma ba daya bane don iyayenta basu da qarfin iyayen fadilan,kanta na qasa ta dam zamo daga kan kujerar tace ina wuni? Duk da bata sa ran masawarsa ba don bai taba amsa gaisuwarta ba ga mamakinta wannan karon sai taji yace “lpy ga kaya nan abinda babu ko baiyi ba sai ki yi maga ko ki rubuta ta girgiza kai tana cewa😔 komai yayi mun gode Allah ya qara arziqi” ya lumshe idanunsa don har zuciyarsa ya ji dadin addu’ar “madalla” yace ya zaro bandir na dubu dubu guda uku ya dora saman akwatinan ya juya ya fice sai yaji wani sauqi na radadin da zuciyarsa ke masa addu’ar ta faranta ransa don tunda yake bai taba samun kwatan kwacin wannan ba daga bakin wani abu wai iyali ba
Muje zuwa yanzu aka soma
Mrs muhammad
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
12:45 pm 03/11/1437
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
WA YASAN GOBE?
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶2⃣2⃣
Ana ya gobe daurin aure su anty hafiza anty hauwa farida sumayya rabi’ah har da rahama suka zo wa fadila,farida ta zube dinkunan da fadila ta bayar aka mata sunyi matuqar kyau da gaske duk da tana da sababbin din kunan ma da bata taba sa su ba,kala ashirin farida ta zabar mata aka dinko su lace biyar atamfa biyar shadda biyar material ma biyar ne,anty hafiza ce ta taho mata da mai gyaran jiki gashi da lalle takanas sai hade haden magunguna namu irin na mata imgantattun na ‘ya’yan itace,anty hauwa sai dariya take tana cewa o’o’o fadila ‘yar gata to ai ko kece amaryar sai haka,sai dai tayi dariya ta sunkuyar da kanta qasa cike da kunyarnan ta ta,anty hauwa ta zuge jakarta ya fito da littattafai tace ga saqon momi nan,hannu biyu tasa ta amsa tana godiya litttafai ne kusan goma na addu’o’ine da kuma gyara zamantakewar aure,
Zuwansun ya sake debe mata kewa taji dadi nan suka fara tsara yadda za su gudanar da yinin su na gobe wanda ko wacce mace da za’a qarawa abokiyar zama ke gudanarwa,wuni akai ana qalqale mata jiki yayin da su rabi’ah sumayya da rahama suka zage wajen qal canzawa gidan fasali,sune canza labulaye canza carfet goge goge da ahare share duk da komai na fadila tsaf yake sai abinda ba’a rasa ba,cikin qanqanin lokaci kuwa gidan nata ya canza kamar ba shi ba,hatta qamshinsa sai da aka canza kalarsa ya zama na musamman abinka da diyar bare bari
Rahama ke tambayar fadila samirah fa?fadila tace wlh tun safe dai naji tashin motarta amma ban sani ba ko qunshin itama ta tafi “Allah ya kyauta inji anty hauwa ,bayan isha’i komai ya kammala anty hauwa tace zasu wuce sai gobe kuma idan Allah ya kaimu anty hafiza da yake kwana za suyi ita da farida tace”dama kwanciyar ku muka yi maman kausar wlh ,a’ah hafiza na bar yara su daya a gida daga su sai Abbansu wunin yau fa duka?”anty hafiza tace to don Allah ga laila(mai qunshin da ta dauko)ku sauke min ita a dorayi
Suna kan gado duk su ukun sunyi shirin yin bacci hafiza ta zubawa ido dake qoqarin shafa addu’a tace wai yau wa kuka barwa mijin ne?samira fa bata dawo gidannan ba haka kuke masa?”cikikin son rufe sirrinta da son gyara rayuwar aurenta ba tare da taimakon kowa ba tace “girkin samira ne anty bana son neman rigima da tashin hankali me zani in masa tunda ba girkina bane?salin inje mu raba dai abun fada?”daga haka suka qyale zancan
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Washegarin aka zo akawa salima jeranta da yake aikin maza ne nan da nan yayi sauri amma akwai wasu daga cikin yan uwanta mata da suka zo da su,girkinsu su fadila sukayi sosai suka zuzzuba a manyan warmers suka aikawa yan uwan salima da wani wasu kuma suka barshi nan cikin kitchen dinta saboda mutane yan uwa da maqota da keta zuwa Allah ya sanya alkhairi har a lokacin sashin samira na kuelle ne alamar bata dawo ba kenan hakan yasa kowa ya shigo gun fadila yake yowa idan suka tambayeta samira sai tace ta tafi gidan qunshi
Ba qaramin kyau fadila ta zuba ba tamakar ita ce amaryar daga wayewar garin zuwa yanzu ta sanya kaya kusan kala takwas kenan har harabar gidan jama’ace don babu laifi yan taru duk da ba wanda suka gayyata
💔💔💔💔
Qarfe sha daya da rabi na rana aka daura auren Aliyyu salim maitama da salima tukur Abubakar,kasancewar gidansu salima na na unguwar dake daura da g.r.a ne yasa yanuwan fadila na jiki da suka halacci daurin auren suka dinga zuwa ana gaisawa suna tafiya ciki kuwa harda abbanta da muhammad da ya ahmad taji dadin zuwan hakan kuma ya faranta mata ranta don tun da aka daura aurenta rabonta da taga abban nata kuma shima yaune zuwansa na farko gidan nata,ya mata nasiha sosai da ta qara mata nutsuwa ta kuma sata kuka ta sake tabbatar da cewa ba qaramin zumunci bane tsakanin abban nata da uncle abba mahaifin aliyyu tabbas babu abinda zata wa abban ta aduniyar nan fiye da ta jure zaman aure da aliyyu,anan suka bar mata muhammad zuwa yamma abban zai turo a daukeshi
Qarfe sha biyu da rabi ta sake wanka ta sanya wani Swiss lace pink ne mai dan turuwa kadan sai kore aka masa da ratsin silver din zare sai manyan dutsina masu walqiya sarqarta abun hannu da dankunne mayafi da takalmi duk silver ne dinkin riga da skert aka mata skert din eight pieces ya bude daga qasa sosai ,yayi matuqar karbarta ya haska chaculet din fatarta gashinta mai tsawo da santsi da baqi ya sha parking da pink and green din ribbom sai ya kwanta a bayanta sai sheqi yake tayi daurinta das wanda ya ta qasansa gashin nata ya fito,ta dauki turare tana fesawa taji ana kiranta maqotanta sun shigo kuma wasu na nemanta a harabar gidan saurin da take yasa ta manta bata dauki mayafi ba,suka gaisa da baqin tasa aka kawo.musu abinci sannan ta qarasa harabar gidan, nasiru ne da wasu mutane suke neman gun jibge abincin da ake ta shigowa da su,ta nuna musu store dinsu dake harabar gidan ta farko kusa da parking space
Tana shirin shigewa ciki motocin suka soma danno kai suna parking daya bayan daya,bata fuskanci su waye a ciki ba sai da suka cika harabar gun dukkaninsu cikin fararen kaya suke,Aliyyu ta hango a tsakiyarsu fuskarsa nata fitar da wani annuri cikin wata rantsatstsaiyar shadda babbar riga da yar ciki sai wando zata iua cewa bata taba ganinsa da irin wanna shigar ba ya qara wani kyau da kwarjini sosai ta shagala da kallonsa har suka hada ido
Haushi ne da takaici suka cika shi ganin yadda tayi kwalliya kuma ta fito har kusa da get a haka na tare da tayi lullubi ba,yayi mata kallon nan nasa data tsana wanda ya saba yi mata hakan yasa ta tuna a uadda ta fito fa tayi saurin shigewa cikin jama’a ta bacewa ganinsa
Tana zaune cikin baqinta sumayya ta shigo tace anty kije inji yaya sai taji maganar banbarakwai gabanta kuma ya fadi tace yana ina?yana cikin garden,dakinta ta shiga ta sake fesa turare sannan ta lulluba mayafinta,tunda ta nufo lambun zuciyarta ke dukan uku uku a haka har ta cimmasa,yana tsaye ya goya hannunsa a baya ya juyawa qofar shigowar baya,batasan yadda akayi ya gane ta shigo ba don gurin gaba daya grass carfet ne bare tace yaji takun tafiyarta ne sai ji tayi yayi gayaran murya gayaran muryan sai ya zamo kamar ya mata luguden guduma a qirjinta🔨,me ya fito dake harabar gida babu lullubi?shiru tayi muryarta na dan rawa tace ka…..kay……kayi haquri”ya dan dauke wuta na dan lokaci kana ya juyo da azama kar mai shirin waftar wani abu,hakan ya sa tayi tsammanin duka zai kawo mata tayi baya da sauri cikin tsautsayi ta taka wani dutse sai kuwa ta tadeta tayi baya luuu zuciyarta na bugawa da sauri don ta gama saddaqarwa sai ya sha qasa,sai kuma ta jita jikin mutum aliyu ne ya sa singalalin hannunsa ya tallafeta ta bude idonta data lumshe tana jiran ta jita ta sha qasa sai ga idonta cikin nasa,ya tsuke mata fuska 😠kana yace meye haka tashi” tayi azamar zare jikintata tana cewa kayi haquri,sai ya harde hannunsa aqirji ganin yadda duk tabi ta duburburce yabi gashinta wanda ya bi wuyanta ya dawo kafadar ta ta dama da kallo lace din ya zauanar mata caras cas yabi lafiyayyar fatarta chaculet,ya dan dauke kansa yabi gefansa da kallo yana jan tsaki a fili
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
WA YASAN GOBE?
▶2⃣3⃣
Sai da ya gama shan qamshinsa sannan yace ina da baqi dame dame kuke da shi a kitchen?cikin dai rawar muryar tace akwai sinasir masa funkaso da miya fried rice sai white rice da miya,ya danyi shiru sanna yace cikin sweet a bamu sinasir da masa sai a hado da white rice tace to har ta juya yace hey! Tadan waigo idonta na kallon qasa yace idan min kawo kiyi knocking kawai ki barsu a bakin qofa ta gyada kai ta wuce
Bayan isha’i gidan ua dade ba mowa sai anty hafiza da farida suma suna gama kintsa mata ko ina suka turare shi sannan sukai haramar tafiya,godiya ta musu mai yawa su kuma suka cikata da nasiha ta rakosu tana bawa naty saqo don allah ki kawo min yan biyu tunda kika kaisu gida yaye anty minqi karbosu tace yayanku ma mita yake amma shekaran jiya munyi waya da mama sun kusa dawowa insha allah da haka suka rabu ta dawo ta koma bedroom dinta ta hada ruwan wanka wanda ya wadata da turarukan wanka,bayan ta fito ta shirya kanta ckin wani lafiyayyen material kalar qwanduwar qwai wanda aka masa ado da qyalli silver da ratsin fari kadan kadan ,shima yana daya daga ckikim dinkunan da aka kawo mata jiya riga ne da skert amma wadannan sun kamata sun muma fito da shep din ta sosai,tana gyara kayan kwalliyar dake kan madubin nata ne taji gudar yan kawo amarya jikinta ya saki ta zauna bisa dressing chair
Tana kwance bisa kujerar qaramin falonta agogon bango ya kada qararrwar qarfe goma tayi ajiyar zuciya ta gayar kwanciyarta goma da ashirin da biyu qarar intercome ta tada ita daga bangaren aliyu ne hakan yasa ta fahimci hadasu yake sonyi kamar yadda al’ada ta tanadar gabanta ya tsanata faduwarsa💔,cikin nutsuwa ta sake feshe jikinta da turare turare ta lulluba mayafi a lallausan gashin kanta wanda bata daura dankwali ba
Da sallama ta tura qofar falin nasasu biyun ne suka amsa amaryar na tsaye gaban fridge tana ciro ruwan roba da lemo yayin da gogan ke hakimce bisa kujera two sitter shigar jikinsa ta yanzu ta babbanta da ta dazu duk da dai babbar riga ce yanzu ma a jikinsa ta shadda milk colour ya ajiye babbar rigar a hannun kujerar da yake kai,salima ta dan zubawa fadila ido na yan sakanni sannan ta dauke kai ta dauki plate saman fridge din ta dora kayan fadila ta samu one sitter dake gefansu ta zauna ,saluma ta janyi centre table dan madaidaici gaban aliyun ta dora masata tsiyaya ya masa ta jiye ta koma kusa da shi kan kunerar da yake kai ta zauna,fadila ta saukar da idanunta qasa tana cewa cikin ranta “ni kadaice bani da irin wanna damar me yasa why Aliyu?,na kusa samota na kusa da qarfin zuciyata insha Allah” muryarsa ta jiyo yana fadin kefa mume jira ko?,shiru na yan mintina sanna ya qara cewa”yayi miki kyau” ya ajiye wayar ,saluma tace kawai ka qyale ta ni na gaji bacci nake so nayi,fadila ta dago kai suka hada ido sai kuma kowacce ta dan saki fuskarta fadila tace sannu amaryarmu”itama da dan murmushin a fuskarta tace sannu kuna lpy”a taqaice fadila ta amsa mata da” lau”ta dan saci kallonsa shi lemonsa ma yake kurba idonsa na kan qofa
Banko qofar akayi aka shigo samirah ce sanye da baqar doguwar riga babu ko alamar hida bisa fuskarta sai dan kwalun atamfa da ta dauro a kanta wanda tayi masa daurin ture kaga tsiya,ta kama qugu tana cuno baki gaba tace da aliyu “gani” wani banzan kallo ya jefeta da shi sanna yace “ga gurin zama nan ko ina idan kuma bai miki ba…..ya nuna mata qofa da hannu👉�,sai da ta qarewa ko ina kallo sanna ta nufi kujerar da aliyun ke kai kusa dashi a daya side din ta dora qafa daya kan daya tana girgizata harara salima ta makawa samirah itama kuwa batayi jinkiri gun ramawa ba,taja tsaki sanna taci gaba da jijjiga qafarta,hara rarta aliyu yayi ya kalli qafar da take jijjigawa ta fuskanci abinda yame nufi kuma tasan ba magana zai.mata ba don haka ta sake zumbura bakinta sannan ta sauke qafar tata
Godiya ya far yiwa Allah sanna ya dora dukkaninku a qarqashin iko na kume kuma tsarin Allah ne shi ya tsara hakan kamar yadda yame da ikon tsara rayuwar ko wane bawa nasa to ma gode masa akan duk yadda yayi da tawa rayuwar “daganan ya dora da yi musu gargadi da jan kunne sannan ya tunasar dasu tsarinsa na zama a bangarensa mai girki ta biyoshi”salima ta kanne masa ido tave” dear ani dama na nasan da wanna tsarin naka tuntuni saidai kawai ya zamto kamar tunasarwa a gareni”murmushin shima ya mayar mata yace “yes”
Zuciya ta kawowa samirah iya wuya sai da ta tanka” a banza ai wai talaka ya girmi sarki dolen mutum yanzu shinr qarami ko yaqi ko ya so”cikin fusata salima tace “👉�ke nifa ba dake nake ba,ban gayyatar irinku a zancena don ni idan banda qaddara ba ma baki kai matsayin ma ki zama kishiya ta ba wlh don ko yar wanke wanken gidammu ta fiki kwarjini sai kuwa samira ta nuna ta da yatsa tace”👉�don kutumar uban mutum ya qara gaba mana don ni duwa wuce dole ne a zauna da ni zama daram wlh “sai suka so su kacame
Cikin wata gigitacciyar tsawa aliyu ya dakatar da su sannan yace kowacce ta bace masa agun ba zasu haddasa masa ciwon kai ba haka kawai”salima ta miqe ta shige bedroom dinsa samira kuwa ta fice tana gungunin a qyaleta wlh taci uwar mata,ita kuwa fadila abun nasu tsorata ta yayi don bata taba ganin fadan kishiyoyi ba hasaluma ma ba’a taba yiwa umminta kishiya ba gidansu daga ita sai farida sai muhammad ko a tsakaninsu ba fada suke ba don haka tun ma kafin ya kammala bada umarni su fice din ita tuni ta riga su fita yana juya lamarina ranta
Ransa abace ya shiga dakin duk yadda taso lallashinsa yayi banza da ita ta san halinsa tun ba yau ba kuma bata manta da shi din ba don haka da taga yayi banza da ita yana shirin shiga wankà sai ta qyaleshi sai da ya fito yana shirin kwanciya sanna ta langabe a jikinsa tana bashi haquri,ya dan kalleta ya basar sannan yace matuqar kika ce haka zaki dinga biye mata kunayi a cikin gidana to na rantse babu wadda zan saurarawa acikinku,idan banda raini ma a gabana? Ta sake marairaicewa tana cewa “Allah na lura ita wannan kanta na hayaqi ne da kamar dayar ce da babu ruwana da ita,su auremin mijin kuma suce bazanyi kishi ba” shi sai a lokacinne ma ya tuna da fadila baima san sanda ta fice a dakin ba donsanda yake musu jawabin ka ta na sunkuye ne sai ya tuna rana shigen irin wanna da ya hadasu ita da samirah ba wanda ta kula a ranar ma ahi ko samiran harta wuce” ya kauda wannan yace mata” am telling uh indai kina son zama da ni cikin kwanciyar hankali” “baza’a qara ba dear”
Ganin yadda yaqi sakin jiki da ita yasa ta dinga masa wasu abubuwa wanda suka sa ala dole ya ajjiye fushinsa abinka da dama wanda yake cikin wani hali nan ya bada kai bori ya hau aka tuno da tsohuwar zuma don salima dama idanunta a goge take ta wannnan bangaren to haka shima aliyyun yake dalilin da yasa saliman ma ta kasa auren kowa kenan tayita naci har sai data dawo masa
Mrs muhammad
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
WA YASAN GOBE?…….
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶2⃣4⃣
Cikin kwanakin amarci kawai ake ta ballewa a gidan ,salima wayayyar gaske ce ko da wani lokaci tana manne da A.s maitama samira kuwa ta kasa tsaida hankalinta gu guda,yiwa salima itada da aliyyu labe kuwa ya zamo.mata kamar ibada mintina kadan sai ka hangota tana ta safa da marwa tsakanin sashenta da na Aliyu,fadila baiwar Allah lissafinta yafi ga kwanakin da zata soma shiga office da kuma ranar da zata zamo itace ranar girki a gareta
Kwana uku kenan da tarewar salima fadila ta soma zuwa aikinta ya kama ranar laraba,shiga tayi ta hausawa atamfa ce dinkin riga da zani wadatattu yayin da tayi lullubi har kanta cikin yalwataccen mayafi komai nata cikin kamala yake da nutsuwa haka nan halittarta take kamar wata babbar mace duk da shekarun nata qana na ne,ta bude sabuwar motarta fara qal wadda bata taba shigarta ba saiyau,ta zauna a sit din zaman driver ta kunnata ta wana ta sosai sanna ta sauke hannunta daga kan key din ta hada tafukanta ta soma addu’a🙏🏻,sai da ta gama tana shirin tasar motar ta tuna da hand bag dinta data manto kan gadon ta da sauri ta bude motar ta koma ciki
A hanyar dawowa ne sukayi kacibus da shi kasancewar ta gefansa ne zata wuce din sai tayi tsammanim bai ganta ba don haka ta dauke kanta cikin sauri ta wuce don ta kusa makara ta ajjiye jakar a asit din baya tasa hannu zata kunna motar taji an janye hannun gami da zare key din ta daga kai tq bishi da kallo bai ko kalleta ba ya zagayo sit din mai zaman banza dake kusa da ita ya zauna sosai sannan ya maida qofar ya rufe,ta dan sunkui da kanta😔 ya dan kalleta sannan ya basar don ya lura kamar al’adarta ce hakan,ya tabe baki cikin muryar nan tasa ta isassun maza mai cike da izza ya soma ce mata”ko banza a qarqashin mulki da ikona kike saboda haka u must obeying my statute and order if kina son aikinki,ya dan qara tsuke fuska 😠duk da yawancin lokuta haka fuskar take ya dage kafadunsa sannan yace” I don’t know why aka wani tsiri yin aikin bayan ban gaza komai a gidana ba……
Ya dan sha qamshi sannan ya dora firstly ya zama dole kanki shiga ta kamala idan kin tashi fita,sannan ban lamunce da yawace yawace abu na gaba kada ki kuskura na ganki da number din wani qato a waya ko receiving calls ba and d last one kuma mafi girma wanda zai iya causing loosing din aikinki mu’amala da maza,kada ki dauki damar da na baki na fita aiki lasisi ne da na baki da zaki dinga ganin kina da right na yin duk abunda kika ga dama,take note👉,yana qoqarin ficewa tace insha Allahu zan kiyaye”duk da ranta a abace yake da irun dokokim da yake kafa mata da ita a karan kanta ai tasan ya kamata,baice komai ba ya cilla mata key din yaja qofar ya fice ya tafi abunsa,ta miqa hannunta ta rufo qofar sannan tabi bayansa da kallo yanayin yadda yake taku kamar zabar masa inda zai taka ake,ranta babu dadi ta ja motar ta fice a gidan ,yanayin motar yana da dadin tuqi hakan ya taimaka mata wajan dawo mata da walwalarta,a hankali temper dinta take sauka sai ta dora da fadin la’ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalim cikim zuciyarta,da haka har ta qarasa gidan radiyon freedom don can ta tafi sha’awa amma duk da haka akwai wasu privet ayyuka da zata dinga yi da express radio din
Yanayin yadda ta samu karbuwa ya sake sa mata interest akan aikin sosai,su biyu ne kawai a office din ita da wata fauziyya kusan za tayi sa’a da fadilan amma ita nada yarinya daya iman,fauziyya shekararta uku da soma aiki da tashar,sosai fadila taji dadin samun fauziyya da tayi wayayya mai faran faran da son jama’a duk da ita miskila ce,wunin ranar tayi shine tare da managing director da wasu ma’aikatan tana arranging din ayyukanta ciki harda tsara sabin shirin da suka qirqiro wanda za’a fara gabatar da shi a asabuwar shekara wanda itace mai gabatar da shirin da taimakon fauziyya ta sake fuskantar yadda abubuwa suke duk da dama tasan da wasu lokacin attachment dinta
Kwana biyu tayi tana tsara komai ta mai da kanta busy sosai ta hana kanta sukuni hakan yasa bata da wani lokaci na tunani ,da ta koma gida tayi wanka tayi sallah sai ta samarwa kanta abunci simple ta ci sai kwanciya idan da wuri ta dawo kuma takan yi tilawar alqur’ani tunda dama ta jima da kammala haddarsa tun lokacin da tayi candy,idan ta gama taga tana da wani lokcin sai ta dauki wani aiki da zai taimaketa a office ta yi ko tayi amfani da laptop dinta tayi research na wasu abubuwan masu muhimmanci,a rana ta uku ne da taga komai ya kammala ta nemi hutu na kwana biyu ba wani matsala suka bata tunda dama bata soma gabatar da ayyukan ba cikin shirye shirye dai take,tayi hakanne don a lissafinta ya bata yau itace zata karbi girki ,kuma dama tuni ta shiryawa zuwan ranar
Da wuri ta koma gida ruwa kawai ta watsa ta zura doguwar riga har qasa mai hannun shimi ruwan hoda ta saka,ta taje dogon gashinta ta daureshi da ribbom shima ruwan hodar ne,farin hijabi ta saka wanda iyakacin qirjinta kawai ya rufe,ta wuce locker dinta ta lalubi inda ta adana muqullan da bata amfani da su ta debesu gaba daya ta zira farin silifas na fata ta fito,a falonta ta soma tsayawa ta bude fridge ta dauki lemon chi exotic nectar na pineapple da yayi sanyi sosai ta sha ta maida sauran ta rufe sashen nata,
TO FADILA SAI INA?🤔
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶2⃣5⃣
Kai tsaye sashen Aliyyu ta nufa gabanta na dan faduwa kadan kadan har ta isa qofan,addu’a fal bakinta ta ke sanya muqullan daya bayan daya take gwadasu har ta dace da na qofar,ta tura babbar qofar ta shiga sanyin a.c ne da daddadan turaren aliyyu ne yayi mata maraba,ta dan lumshe ido kadan sannan ta waresu sosai kamar mai neman wani abu,a hankali take bin kowane sashi na falon da kallo tabbas yana buqatar gyara,bata shakka cewa har bedroom dinsa ma na buqatar a kintsashi,ba tare da tsayawa wani dogon nazari ba ta dauko dust bin dake falon ta ajjiye a tsakiyar falon ta zare dan hijabin nata ta jefashi kan kujera ta fara tattare ta fara tattare leda takarda gwangwani da duk wani abu da ya zama datti ne tana jefashi cikin kwandon sharan
Tana tsaka da aikin ne taji ana taba qofar alamar an shigo a tsorace ta dago tana tsammanin aliyu ne sai dai kuma maimakon haka sai taga ashe salima ce tayi tsaye a abayanta tana qare mata kallo ,fadila ta tsani yadda matar me mata naci nkallo haka,dama ita tun da can ta tsani mutum mai azabar kallo,to haka saluma ke mata a duk sanda hanya zata hada su ,abinda ita fadila bata sani ba shine kishine taf cike a zuciyar saliman don so tayi ta samesu gaba daya babu mamora kamar yadda taga samira bata da qira sam,saidai ance gwano baijin warin jikinsa ne ita dinma da tayi dogon nazari da tsinkaye da ta fahimci yadda tata qirar take irin matan nan ne masu azabar tsawo da sirantaka sai wani azababben fari da take da shi irin me gauu din nan to duk da babu laifi tafi samirah amma ko kusa bata kamo qafar fadila ba,tsawonta da azabar sirantaka su suka sata take a miqe kamar number 1 ba wani shape sai tsabar iyayi da yauqi
Ta kau da kai.daga kallon fadilan ta tabe baki sannan tace”oh nayi tsammanin mai gidan ne ya dawo da naga gun a bude” a taqaice fadila ta amsa mata da”A’a” taci gaba da aikinta,sai kawai salima ta bude fridge ta dau maltina hadi da kunna t.v ta nemi gu ta hakimce,sarai ta gano ba abinda yasa saluma zama a gun banda bin qwaqawafin taga me take yi hakan yasa ta sa key ta bude bedroom dinsa ta shige tare da rufe qofar da muqullin ta ciki,salima tabi qofar da kallo cikin takaici don ba haka ta so ba,nan ta zauna tana ci gaba da shan maltinan tana dakon fitowar fadila wadda batasan ma tana jiran ba
Ta qarewa shima bedroom din kallo sannan cikin nutsuwar nan tata ta fare tattare shi shima tana kintsa komai a muhallinsa tanayi tana mamakin kamar babu wasu mata dake kwana a dakin komai a yamutse?towel ne underwear ne comb ne mayuka ne turaruka ne kai tarkace dai wanda da alama a safiyar yau kafin ya fita yayi amfani da su warwatse bisa gadon bedsheet din kansa duk da babu datti amma ya yamutse,kowanne abau ta maidashi inda ya kamata cikin qanqanin lokaci dakin yayi fes komai ya dawo cikin hayyacinsa ta kunna kaskon turaren wuta electric ta zuba irin turaren wutan da take amfani da shi a bangarenta sanna ta wuce toilet
Toilet ne qaton gaske wanda yakai girman ciki da falo na mata da yawa yana dauke da duk wani kayan amfanin toilet na zamani,cikin lokaci qanqani shima ya dau haske komai na cikin sa farine sai da ya dawo daidai tamkar ka zuba abinci a qasan ka ci,sai da komai ya mata yadda take so ya wadatu da sanyayyan qamshi sannan ta bude qofan ta koma falon don ta qarasa aikinsa
Salima ta bar falon saidai ga gwangwani nan da tasha malt cups da qarin ledojin cake da na wasu tarkacen ciye ciyen nata watse a agun da ta tashin,baki ta tabe cikin ranta tana cewa”Allah ya sawwaqe an san yadda za’a bata amma ba’asan yadda za’a gyara ba sai kace ba mata ba,tana wanna zancan zucin tana kammale falin duk da girmansa kuwa,har kitchen bata barshi a baya ba sai da ta gyareshi ,”haba duk kyan abu ai yana buqatar gyara”inji fadila tana riqe da qugunta ta fada bayan ta gama aikin tana qarewa bangaren kallo yadda ya koma tamkar ba shi ba
Aikin ya ja mata lokaci sosai kuma ya gajiyar da ita,tana kimawa bangarenta nan ma dai ba zama din kitchen ta shiga ta kama habarta🤔 cikin tunanin me zata girkawa aliyyu wanda zata iya kammalashi kafin kiran sallar magariba ganin gashi hudu tayi har da rabi,abu mafi muhammancin ma bata san choice din aliyyu ba ,sai ta yanke a ranta bari ta fara gwadashi da tuwo ta gani din ta fuskanci wasu mazan ba sonshi suke ba in yaso idan yayi masa shikenan an wuce gurin
Tuwom shinkafa ta daura miyar danyar kubewa wadda ta dagargaza mata zallar tsokar kaza sanna ta sa tantaqwashi ya wadatu a ciki,misalin qarfe shida komai ya kammala ta soma mulmula tuwon da yayi fari sol cikim farar leda ya tuqu sosai ya hada jikinsa,sababbin warmers masu kyawun tsari ta dauko ta jerashi a ciki,ta gama ta gyara ko ina kamar bata yi aiki a kitchen din ba,ganin tana da ragowar lokaci yasata ta dora farfesun danyan kifi ragon ruwa maimakon zaman jiran dahuwarsa sai ta hada zobo wanda ta markada wadatacciyar abarba ta zuba a ciki ta hada da citta da kanunfari ta dafa,shima ta zubasu a mazubi ta wanke tukwananta,cikin azama ta shiga toilet ta silla wanka
😂😜 na gano su maman sa’ida fa na son jin qwaqwaf an baza👀👂🏻👄 anason aji ya aka kaya ko
To🤔🤔🤔kada dai ku gaji ku biyo safiyya insha Allah don jin kanun labaran
Mrs muhammad dinku ce 07066139278
📚📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 12:38 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
WA YASAN GOBE?
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶2⃣6⃣
A bakin mudubi ta yada zango ta fara shafe loko da saqo na jikinta da turare dama ta saba da yin hakan kwalliya irin ta zamani mai tsari ta shiryawa fuska fuskarta bata cikata da jagwalgwalo ba ta taje gashinta mai tsaho da sulbi ta daureshi da ribbon ja swiss lace ta saka orange mai adon ja riga da skirt dinkin rafa wanda yayi masifar fito da sharp dinta,ta bata lokaci tana zana dauri a kanta ya zauna gwanin sha’awa fashion ta saka na dutse na sarqa da dan kunne sannan ta cika hannunta da awarwaro irin na india ja mai ashirin da hudu ya ahmad ne ya taho musu da tsarabarsa sati biyu da suka wuce,plate shoe ta saka orange and red ta sake feshe jikinta da turaruka sanna ta kalli kanta a mudubi,masha Allah ta fadi ba tare da tasan ta fadi ba sai murmushi ya subuce mata ita kanta yau ta sake gasgata kyawun da ake fadar tana da shi,kiran sallar magaribar da taji shi ya sata saurin fitowa ta shiga kitchen ta shirya kayan abincin ta kulle sashen nata ta fito tana tunanin qila ma aliyyu har ya dawo,ta cikin balcony din ta ta isa sashen ba alamun ya dawo don haka ta sa key dinta ta bude tana shirin shiga tajiyo alamun tsayuwa mota ta waiwaya sai taga samirah ce ke shirin fitowa daga motar tata wani irin kallo samiran ta watso mata wanda fadila ta gaza gane mai take nufi,dauke kanta tayi abinta ta shige don ba ita bace a gabanta tana mamakin masifaffen yawo irin na samira
Cikin qwarewa ta shirya table din sannan ta sauko cikin falon ta kunna tafkekiyar t.v plasma din dake manne a bango cikin sa’a kuwa malaminta ne ke karatu a saudi qur’an ta dan qaro volume matsakaici ya game falon ta koma gefe ta tada sallarta cikin nutsuwa bayan ta idar ta koma ta zauna tana kallon yadda mahajjata ke dawafi
Mintina biyar da zaman nata taji ana bude get jikinta ya bata Aliyyu ne jikin window taje ya dage labulen tana kallonsa har ya fito daga motar dukkan alamun dake nuna gajiya ga mutum sun bayyana a tare da shi,duk da ya gajin amma a nutsenshi yake kyawunsa na nan saidai fara’a da tasake yiwa fuskarsa qaura hirar da fadila keyi kenan ita da zuciyarta nasiru ne ya kulle motar bayan yafito sanna ya miqa masa kayayyakinsa da muqullan cikin rusunawa kamar ko yaushe aliyu ya karba yana cewa👉kada kowa ya jirani gobe ka sallamesu don bazan fito da wuri ba idan ka sallamesu sai kuci gaba da list din suna yan wadanda suka karbi kayan amma a cire sunan alhaji hamza wannan mun gama da shi✋🏻,nasiru yace ok insha Allahu ya juya yana shirin wucewa yace Allah ya tashe mu lafiya,ameen ya amsa masa
Burinsa ya isa gida yayi wanka ya samu abinda zaici ko da tea ne donshi kam har yau cikin matan gidan babu wadda zai nuna👉�yace girkinta ya masa har gwara salima yakan qoqarta yaci indomie dinta don kore yunwa,yayi mamakin ganin qofar tasa a bude amma sai yayi zaton ko salima ce,ba wani dadi da yaji don ason ransa so yayi ya zauna shi daya ya samu hutu
Saidai yana tura qofan wani daddadan qamshi ya daki hancinsa wanda ya tilasta shi lumshe ido kasancewarsa ma’abocin son qamshi sai ya shiga tunanin inda ya taba jin qamshin amma ya kasa cankowa idanunsa suka sauka a kanta bata anakara da ya shigo bane ko tsorone ya hanata motsi?ya dan tabe bakinsa 😠yana tunanin mai ya kwao ta kuma? Ya qarasa shiga falon yana sallama a nutse ta dago tana amsawa ya dan zubawa fuskarta ido zuciyarsa na son yaba wani abu amma ya rasa meye shi?ita kuwa gabanta ke faduwa cike da fargabar kada ya wulaqanta aniyarta yadda ya saba ganin yaddda ya hade rai kamar ya ga kashi,sai kuma taga ya dauke kansa ya nemi kujera can gefe ya watsar da kayan hannunsa sannan ya zauna har baisan sanda yace wash! ba ya sake lumshe ido yana ci gabada sheqar qamshin da ya ji yayi masa har cikin zuciyarsa ya rasa kuma ta Inda ya samu don dai shi har ya bar falon baiji qamshin ba sai yanzu da ya dawo
Sannu da zuwa tace cikin cool voice dinta,ya bude idonsa tana durqushe gabansa riqe da cup da jug na glass baice komai ba yabi hannun nata da kallo dake riqe da cup din tana tsiyaya masa lemon zobon dake ta tsatstsafar sanyi da qamshin abarba ta janyo center ta dora a kai sanna ta balle murfin gorar ruwa na c’bon ta cika masa shima cup da shi ta ajjiye masa duk baice komai ba cikin dari darin kada ya gwasaleta ta miqe ta dauki briefcase dinsa safa takalmi key dinsa da duk ya wurgar din ta yi cikin daki da su
Tana shiga tayi maza ta maida qofar ta jingina jikinta ta dafe qirjinta tanajin yadda yake bugawa da sauri da sauri idanunta a lumshe tana dan murmushi☺, cikin zuciyarta tana cewa wai Allah na! Sai da ta dan nutsu sannan ta ajjiye kayan a inda ta tsara musu kai tsaye ta wuce toilet ta kashe makunnin heater din don har jar danja ta kama alamar ruwan ya tafasa ta hada masa ruwan wankan a bathtub ta saisaita shi ya zamo mai dumi sosai yadda zaiyi saurin saukar da gajiya sannan ta zuba masa turarukan wanka a ciki
A hankali yasa hannu ya dauki cup din zobon yana tunanin meye wannan? Ya kai bakinsa da niyyar dandanawa sai gashi ya shanye har da qari sai da yasha cup uku sannan ya saki ajiyar zuciya saboda yadda dadinsa da sanyinsa ya ratsa shi sai yaji kaso goma na gajiya da qishirwarsa har ma yunwar sun fara sakinsa ya samu relief har a qwaqwalwarsa ya jingina bayansa da makarin kujera
Sai a yanzu ne ya lura da canjin da falon ya samu ko ina tsaf tsaf kamar yadda yake so,tunanin wa ye yayi aikin yake don shi kqm daga samira har salima yasan cewa matane masu azabar ganda da ko ruwan sha sai ya tambaya ake iya tashi a dauko masa,ga ruwan wanka can a toilet ko kana da buqatar yin wanka,ya dago da kansa tuni har tayi hanyar kitchen fadila tayi hakanne don gujewa baqar maganarsa ko da ziyi mata ta maqale a window din kitchen tana leqensa
Sai da ya bata lokaci sosai har fadila tayi zaton bazaiyi wankan bane ta soma dana sanin shishshiginta sanna ta hangoshi yana kwance agogon hannunsa hadi da cire suit dinsa ya riqesu a hannu ya shige dakin tabi bayansa da kallo,ta janye idanunta hadi da lumshesu ta dafe goshinta da tafin hannunta tana cewa a can qasan maqoshinta”wo hoho Aliyyu badai miskilanciba?…. sai kuma ta sake sakin murmushi tana cewa”Allah ka mallakamin Aliyyu”tayi saurin dafe bakinta tama zare ido saboda ta fuskanci maganar zuci ce ta fito fili
Sak yayi ya tsaya yana kallon dakin baccin nasa komai kamar yanzu aka jerashi ko tsinke babu a farin tiles din dake mamaye da dakin ya jinjina kai ya ajjiyr kayan hannunsa a gefan gado ya fara binciken inda ya ajjiye rigar wankansa sai ya bude wardrobe donnya dubata a ciki,canji idanunsa suka masa karo da shi,wardrobe ce ta jikin bango mai hangar komai ya canza bangaren shadda daban yadi daban suit dinsa haka kai hatta socks dinsa da handkerchief an masu nasu tsarin bai san sanda ya saki murmushi ba don tsarin ya burgeshi kasancewarsa dan gayu ya tabbatar babu tsarin rigar wankansa a gun don haka ya haqura ya wuce toilet cikin ransa yace wonderful cikin wani glass dake manne a kwanar bandaki ya hango rigunan a tsare jikin hanger bai bata lokaci ba ya shige cikin ruwan wankan duminsa da qamshinsa suka ratsashi sai yaji kamar kada ya fito,ya shafe kusan minti talatin sannan ya sabe jikinsa ya dauraye ya fito bisa gefan gadon ya zauna ya tsane jikinsa ya nemi farar jallabiya yasa don yafi son sata idan ya dawo daga aiki ya taje kansa ya feshe jikinsa da turare sanna ya bude jakar computer dinsa ya cirota yayi waje da niyuar shiga kitchen ya tafasa ko tea ne ya sha
Ganin ya zauna yana aikinsa ya sanyata debo kayan ta shimfida babbar ledar cin abinci a gabansa baisan me takeyi ba sai da yaji qamshin abinci nata shiga hancinsa sanna ya dago kansa ya dubi gabansa ta jera tuwon a farin kyakkyawan plate miyar na wani dan kwano na tangaran shima fari ne tasha man shanu ta cika wani plate din da farfesun ragon ruwan ta zuba ruwa na sha da na wanke hannu ta tsiyaya masa lemo sanna ta janyo tissue box ta ajjiye masa tace bismillah ya kalleta 😠yace ” ce miki akayi da yunwa na zo? Ko an baki labari ina buqatar abincinki kinga malama kwashe abincinki ki ban wuri,
Ba qaramin sosa mata zuciya maganganun suka yi ba bata san sanda hawayen da take boyewa suka silalo mata ba😭karo na farko kenan tun sanda ya fara mata cin kashi,batayi qoqarin maidasu ba ta barsu suka ci gaba da zuba
Cikin zuciyarsa addu’a yake allah yasa kada ta kwashe din don tunda yaji qamshin sha’awar cinsa ta kamashi ai kuwa aadu’arsa bata karbu ba don a zuciye ta soma maida abincin cikin warmers din
😜😜😜
Kuyi haquri da wanna yau bani da chargy wadatacce
Mrs muhammad na muku fatan alkhairi👏🏻
📚📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 12:39 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
WA YASAN GOBE?
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶2⃣8⃣
Sai da yaga da gaske take cikin daurarriyar fuska yace kinga malama zuba kada a qarani gaba ace bani da adalci tunda kin kawo kanki” ya fadi kamar wanda da gasken tilastashi akayin,kalmar tunda kun kawo kankin tayi matuqar bada gudun mawa wajan qona mata rai don haka hawayen da suke zuba suka qara gudu😭
Malmala daya ta saka masa da miya ta miqe wata zuciyar na zugata kiyi tafiyarki kawai wata kuma na lallashinta da hanata tafiya tana gaya mata saurin fushi ba nata bane yanzu da sauran lokaci dai,kujerar da ta tashi a kai can ta koma ta zauna tana qoqarin maida kukanta ta canza tasha zuwa mbc boollywood ta tarar suna film din kuch kuch hotahie tsohon film ne amma bata gajiya da kallonsa
Ta kasa hankalinta kusan gida uku kason farko na kan aliyyu ne da taga ya ci gaba da danne dannensa a computer ya shanya abincin,na biyu na kan matan gidan da ta ga har yanzu ba wadda ta leqo da niyyar yi masa barka da dawowa ashe haka suke masa har ita din?,na uku kuma ta dorashi kacokam ne bisa t.v dake gabanta sai ka rantse da Allah ta bata hankalinta ne gaba daya
Ta gefan ido taci gaba da satar kallo da nazarinsa sanda taga ya rufe computer din ya sauko qasa mamakinta zaman da taga yayi zamane irin wanda annabi yake yayin cin abincinsa mamakinta ya sake qaruwa ne sanda taga yayi bismillah ya sa hannunsa ba tare da ya nemi cokali ba
A hankali taci gaba da bi biyarsa da idanunta,yanayin yadda yake cin abincin a nutse yq burgeta tana ankare da shi har sanda ya cinye ta biyu ya soma cin ta uku,ranta yayi mata dadi ganin yadda yake cin abincin bisa dukkan alamu yayi masa dadi
Hankalinsu dukkansu ya kai bakin qofar jina naturo ta,saluma ce ta shigo da yalwar fara’a a fuskata amma sai taja tayi turus ganin fadila a falon,cikin iya tsabar duniyanci da iya waskewa ta gayyato fara’a fuskarta ta dubi sashen aliyyu tace” a’ah dear inacan ina zullumin yau ka jima baka dawo gida ba”ya miqamata hannu sanda ya sa lomar tuwo a abakinsa yana mata nuni alamar ta taho ,ta taho din kuwa ta zauna kusa da shi sai da ya hadiye sannan yace almost one hour da wani abun da dawowata na gajine shi yasa ba wanda na nema”da ido ta nuna masa fadila tana masa nuni da ita ya akai tasan da dawowarsa har ta rigata zuwa?,dauke kai yayi kamar bai fuskanci abinda take nufi ba don ba’a haka shi da shi,itama tasan hali don haka ta bar maganar
Murya a anarke tace dear dama zancan ankon lubabatu ne qawata da nayi maka,kudin nakeso na karba don banason in zama a qarshe saboda baka fiya samun mai kyau ba”ya gyada mata kai yana ci gaba da cin abincinsa,ta tsare shi da ido ganin baice komai ba bayan gyada kan sai tace sake cewa naji kayi shiru baka”ya dago cikin qosawa yace ba munyi maganar ba tuntuni ba kuma ana amsa miki kuma yanzu baki ga abinci nake ci ba” tace cikin son wayancewa ok takai dubanta ga abincin gaban nasa sannan tace” dear yaushe ka fara cin tuwo?”kai tsaye yace “yau”cikin mamaki ta maimaita yau” ya gyada kai yace “yes”sai kuma tace ammafa nima abincin ya burgeni bari muga”ta tsoma hannu a plate din nasa,aliyu ya tsaida cin abincin ya bata fuska ya dago yana dubanta “repeatedly am telling you duk sanda kika soma cin abinci ba tare da kinyi bismillah ba kina cine tare da shaidan ko?” Ta dan dafe kai tace oh sorry na manta bismillah amma fa abincin nan dear yayi sosai a wane restaurant ka siyo” na gida ne ya bata amsa ya dan dubi sashen fadila wadda idan ka kalleta a zahiri zakayi tsammanin kallin film dinta takeyi haiqan sai dai duk tana jinsu tayi kunnan uwar shegu da su,salima ta fuskanci abinda yake nufi don haka ta tsuke bakinta😷tana da na sanin yabawar da tayi wa abincin din bata yi tsammanin fadilan ce tayi ba
Salima na ta zubawa aliyyu surutu jefi jefi yakan tanka mata har suka kusan tashi da abincin gaba daya har farfesun kifin,suka gama aliyyu ya koma kan computer dinsa ya ci gaba da lissafe lissafensa na kayyayakin dake cikin store da wadanda za’a zuba sababbi da kuma wadanda ya saba rabawa yan kasuwan
Har kusan tara na dare salima na zaune taqi tafiya,cikin haka saiga samira itama ta shigo yanayin samira ne yasa sauran kadan farida ta tuntsure da dariya duk da quncin da zuciyarta ke ciki,nikam safiyya kasa daurewa nayi sai da na dara😂😂 har sai da maman walid ta rufemin baki don kada su ganni
Zanin shadda ne a jikinta rigar atamfa dankwalin material,har abada ba zaka ga kwalliyar samirah cikin gidanta ba idan har kana son ganin kece ado tofa saidai idan fita zatayi cikin qawaye takan ce kada a raina min wayo ina gidan nera dole na dinga keta shiga da kowacce mace zata kiyayi kanta tasan tana tare da matar Aliyyu salim maitama(kunji wata toshewar basira fa)
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
03:15 pm
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
WA YASAN GOBE?
▶2⃣9⃣
Salam! Samirah tace cikin daga murya tana tafiya tana wani budewa babu wanda ta kalla direct ta wuce gun maigidan hannunta dauke da zungureriyar farar takarda,ya dan bar abinda yake kana ya dubeta yana masawa,ta qaraso inda yake ta zauna hannun damansa yayin da salima ke hannun hagunsa takardar ta miqa masa ya amsa kafin ya duba yace” kada ki sake min irin wannan sallamar da kikamun yanzu don ba sallama bace take note,ok?”ta gyada kai tana buntsuro baki,ya bude takardar yana dubawa,ya qare dubawar sannan ya dago kai yana kallon fuskar samiran idanunsa da alamun neman qarin bayani,ta dan yatsine fuska sannan tace”eh abu uwan amfani ne da suka qare nake da buqatarsu” ya dan gayara zamansa ya jingina da makarin kujerar ya sanya idanunsa sosai cikin nata,sai ta kasa kallonsa ta dan soma rikicewa tana son janye idonta ta kasa tasan shi tamkar maye yake wajen naqaltar mutum tasan yanzun nan ba qaramin aikinsa bane ya harbo jirginta,da zarar aliyyu yayi ma irin wannan kallon yake gamawa da kai,sai da yayi shiru na muntina sannan yace”ina zaton yau ko sati biyu ba’ayi ba na karbi list na dukkan abunda baku da shi na kawo…..ya akqi naki ya riga na kowa qarewa bayan ko sati biyun ma ba’a cika ba?”
Ganin tayi shiru ta kasa bashi amsa yasa ya maida kallinsa ga salima wadda tayi kasaqe tana sauraronsu zuciyarya cike da farinciki tana mai addu’ar Allah yasa a ci mata mutunci”nawa ne kudin naki ankon”tawani yi fari da ido sannan tace😊 atamfa dubu arba’in ne lace dubu sittin aai gudun mawar da zan bata dubu dari”(kunji tsabar rashin hankali irin na wasu matan mutumin da duk qarshen wata yake fita da su suyi siyayyarsu idan akwai abinda sai anshiga kasuwa ake samu zai sa su su rubuta ya bayar a akawo musu haka nan kayan abinci da na ciye ciye zaisa a sabunta miki koda basu qare ba kuwa ruwanki ne kisan yadda zakiyi da su shi dai duk qarshen wata zai miki haka,hakanan zai kawo kudi masu kauri ya baki bayan wanda kullum zai baki koda ba ranar girkinki bace )baiji komai ba kasancewarsa mai hannun kyauta ne koda ba ga iyalinsa ba,amma ya lura barnar ta soma yawa don haka ya sake waiwayawa ga samira yace”uhm….am waiting for d answer
Ta yatsina fuska tace” kasan ni maca ce mai jama’a ‘yar dangi kuma duka dangina anan garin suke ba baquwar haure ka auro ba wannan ya shiga ne wannan ya fita”salima tasan da ita take kasancewar iyayenta da danginta ba a garin suke ba a hannun qanwar mamanta take anan kanon amma ba yan garin bane,cikin hasala tace “da uban wa kike?”kamar dama jira samiran kuwa take tace da ubanki nake👉,kinji na kasa da ke ne bare ki dauka banza kawai😙 mtswee!”ai kuwa salima tayo kukan kura tayi kan samira da niyyar shaqota dama da qullin samiran a ranta
Wata gigitacciyar tsawa ali ya daka musu wadda hatta fadila dake gefe sai da ta miqe tsaye saboda razana bare su salima da suka koma sukayi zamqn dirshan ba tare da sun shirya ba,ran ‘yan maza ya baci fa zuciyarsa ta tabu take idanunsa suka kada
Cikin tsananin bacin rai ya kallesu “wadanne irin mahaukata ne da baku da burin da ya wuce kuyi kokawa?”salima da ta shaqa da yawa ta nuna kanta👆🏼 tana cewa aliyyu nice mahaukaciya?” Ya dora da cewa “kun
wuce hakanne?bai sauraresu ba ya murza yatsunsa suka ce das das das ya nuna su👉� sannan yace dis is d last worning kunyi na farko kuma kunyi na qarshe dambe a agabana…..☝🏼bazan dauka ba don ni ba shasha sha bane” salima da idonta ya ciko da qwalla😢 tace”amma fa kana gani fa tana shigowa ta hau habaici daga qarshe ta hau zagina…..samirah ta tari numfashinta da cewa”tambaya kimayi na baki amsa daidai da tambayarki” shut up!” Ya sake dakawa samira tsawa ya nuna mata qofa😡👉� sannan yace da ita get out of my room,jiki a salube ta juya zata fita ya ce hey🖐🏽ta juyo ya nuna mata paper dinta👉� take your rubbish neman tashin hankalinki ya siya miki ya bita da “stupid” wani takaici ya sake turnuqeta ai kuwa buguzum buguzum ta qarashe ficewa
Ya dawo da idonsa kan salima yace”ni bani da kunne sanda tayi zagin ba zaki bari kiga hukuncin da zan dauka ba sai ke sarkin iya hukunci?,sai kuma alokacin ta soma shagwabe masa da sunan bashi haquri ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu”🖐🏽dont disturb me please leave me alone”ta san bacin ran aliyu bashi da dadi do haka ta ja qafafunta ta fice cikin takaicin asarar da sira ta jawo mata na kudaden da take son karba a gunsa,yaja tsaki mai qarfi cikin ransa yace”silly girl” ya juya a hanzarce ya shige bedroom dinsa
Ransa ya baci sosai mutum ne da baison hayaniya yanzu haka qirjinsa zafi yake haka yake ko hira yayi mai tsaqo yanzu kansa zai fara ciwo shi yasa ko musu bai iya ba,ba ruwanshi da shiga wata harqalla ko abokai bai fiya tarawa ba baifi ka qirge abokansa ba da hannu,to da shi da fadilan bansan wanda yafi wani ba🤔
Mrs muhammad dinku ce
[10/16, 12:39 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*wa yasan gobe?*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Writting by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶3⃣0⃣
Kai tsaye bedroom dinsa ya nufa ya canza kayansa zuwa na barci farare ne sol masu taushi mutum ne shi ma’abocin son fararen kayan amfani ya fada bisa gadon yayi rigingine qafafunsa na qasan gadon ranshi a cunkushe yake
Fadila da ke tsaye sai yanzu ta motsa ta saki ajiyar zuciya gami da fadin Allah ya kyauta ya iya mana abinda ba zamu iya da shi ba,ta isa inda suka baje kolin abincinsu suka ci suka tashi bar kwanukan ta tattare su ta gyara gun kamar ba’a yi hada hadar abinci ba agun
Ta isa kitchen ta zubasu cikin sink ta kunna gas ta hada ruwan bununsa wanda ya wadatu da citta kanunfari da lemon grace ta saka lipton daya sannan ta rufe tukunyar,ta koma ta saki fanfo ta wanke duka kwanukan ta adanasu sannan ta juye mishi tea din cikin wani dan qaramin flask mai kyau ta dauki cups guda biyu na tangaran ta dora a saman plate ta hada masa da spoon,ta rufe qofan kitchen din ta doshi bedroom din nasa
Ta tura qofar tana dar dar don tana tsoron kada ya maimaita mat abinda ya mata dazun,ya canza kwanciyar tasa zuwa barin hannun damansa yayin da ya juyawa qofar shigowa baya,qafarshi da yake dan kadawa kadan kadan shi yasa ta fahimci idanunsa biyu a hankali ta ajjiye tire din a asaman bedside sannan ta koma saman kujerar madubi ta zauna tana fuskantar bayan nasa,dakin ya yi tsit kamar ba wata halitta a dakin sai qarar agogon bango dake maqale a abangom dakin yana ta aikinsa,ita batace komai ba bareshi da tasan dama ba maganar zaiyi ba
Zuwan can ta dan ja numfashi sannan ta tattaro dukka dauriyar da ta rage mata bayan ta gama wassafa da tsara maganar da zata fito a bakinsa,tayi yar gajeriyar gyaran murya a dan tsorace sanann tace” nazo ne baka haquri game da bata maka rai da mukayi dukkaninmu mu ukun,zan ari bakin yan uwana na ci musu albasa ince kayi haquri da mu baki daya,idan ban manta ba haka Abba ya gaya maka a ranar da mukaje masa _lamarin mata sai da haquri da kuma jajircewa halitta ce maau wuyar sha’ani amma idan kasa Allah a gaba sai komai ya zo maka da sauqi_”kayi haquri da mu Allah kuma ya huci zuciyarka😔,ga black tea nan ko kana da buqata sai da safe
Ta miqe tana barin dakin ya dan waiwayo yana dan kallon ta har ta fice,yana cike ne da mamakinta dama tana da saurin sauka a fishi ne?,at least ya samu relief ainun daga damuwarsa,hakan ne ya bashi dama har ya jawo flask din ya murda murfinsa ya bude qamshinsa ya taso ya mamaye hancinsa ya dan lumshe idonsa take kwadayin tea din ya kama shi,yasa kofi ya tsiyaya ya sanya zumarshi ya kurba qamshin cittan da kanunfarin da lemin grace suka hadu a abakinsa suka masa dadi
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Tana idar da sallar asuba bayan kammala al’adarta ta kullum wato azkar na sabahi wal masa wanda annabi ya koyar ta koma ta jingina da gefan gadonta idanunta a lumshe ta soma tilawa kamar yadda ta saba cikin sassanyar muryarta,sai da tai izifi biyar sannan tayi addua ta shafa,ta linke sallayarta sannan ta soma gayara bangaran nata duk da ba datti ko kadan sai ‘yar qura da ba’a rasa ba wadda hadarin da ake tayi kwana biyu idan ya hado sai kuma ya zama iska mai sanyi wadda ke tashi hade da yar qura,tana kammalawa tayi wanka sannan ta shirya cikin doguwar rigar yan kanti mai roba roba red ce ta sauko mata har qasa ,daga gaban rigar wajen qirji an kamata an mata tattara yayin da ta bude sosai daga qasan aka jera wasu irin dutsuna manya guda uku masu garai garai da qyalli hannun vest ne da ita saboda haka ta sanya long sleeve shirt fara ,tayi rolling da farin mayafi wanda acucin da tayi da gashinta ta mai doughnut ya taimaka wajan qarawa rolling din nata kyau iya kafadunta mayafin ya tsaya,qananun fashion na barima farare ta saka sannan ta jawo takalminta slippers na fata shima fari ne,wayarta ta dauka ta kulle bangaran nata
Yauma da keys dinta tayi amfani ta bude gurin,shiru yake ba motsin komai hakan yasa tayi tsammanin bacci yake,hakanne kuwa ta gani sanda ta leqa bedroom din nasa cikin sanda,yana kwance tsakiyar gadon duqunqune cikin farin lallausan bargo ,gefansa daga qasa dardumarsa ce qur’ani da kuma carbi 📿akai,yayi mata kyau sosai aliyyi gwanin kyau kome yakeyi kyansa fita yake,baccinsa yake verry calmness fuskarsa tayi fresh,sai ta lumshe ido tana tuna da yadda daren jiya tayi nata baccin cike da kewa da azaba,amma shi yanzu gashi yana nasa hankalinsa a kwance har da qarin wani na bayan sallar asuba kenan,ta dauko wayarta ta kashe plasher dinta tayi snapshot din fuskarsa,ai kuwa ta fito shar zara zaran gashin idanunsa sun kwanta luf,tayi kissing din hoton sannan ta juya ta yi kitchen
*mrs muhammad ce*
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*wa yasan gobe?*
▶3⃣1⃣
Chips ta soya hade da wainar qwai sannan ta dama masa kunun gyada da ya sha madara yayi fari qal sai zuba qamashi yake,sannan ta bare indomie ta yi masa awarar indomie,nan fa qamshin abincin ya karade gaba daya falon har cikin gidan to wani ma yayi rawa bare dan makadi,fadila gwanar girki ce mayyar kitchen ce tun tana gida ma,tana saitin window inda kan famfo yake tana wanke kayan da ta bata ta ke jiyo motsi kadan kadan,windon na cikin lambun bangarenshi da ke bayan part din kowa,tana daga kai ta hangoshi qarfe yake dagawa🏋🏼ya hada gumi sosai,armless riga ce a jikinsa da shortnekeer damtsensa cike da qwanji a murde,ya ajjiye qarfen ya dau dan farin towel dake gefansa yana sharce gumin kana ya dauki bottle na ruwa ya daddaka ya rufe ya koma kan keken training kuma🚵🏻
Ta saki murmushi ta kada kai,da azama ta hada komai ta koma bedroom ta gyara masa ta wanke toilet ta hada masa ruwan wanka,ta budade ko ina da qamshin nan nata sannan ta dawo parlour ta zare rolling din kanta ta fara gyare falon shima ,yana daga can yake jiyo qamshi kala kala na shiga hancinsa da fari qamshin girki ya fara jiyowa ya bude dogon hancinsa yana shaqar sa saboda ya masa dadi daga bisanai kuma ya jiyo wani qamshin qamshin da ya kwana jiya yana sheqa,ya sauka daga kan keken shima ya dauki wayarsa da towel dinsa ya bude qofar bayan ya shigo ta cikin kitchen wanda yasa sauran kadan suyi karo,ta ja baya da sauri tana gaidashi kanta na duqe a qasa kamar kullum bai amsa mata ba dama ta zaci hakan ya dai daga mata hannu🖐🏽ya wuce
A bandaki ya tarar da ruwan wankan nasa,ya dan yi dam domin bai saba ganin hakan ba a tarihin rayuwar aurensa ba ganin tunanin zai bata masa lokaci yasa kai tsaye ya shige cikin ruwan🛀🏼yana sheqar qamshin da yake
Cikim suit ya fito baqaqe masu sheqi sunyi masifar fito da ainihin kyawunsa,takalmi ne half cover dan hasken marun kamar yadda tie dinsa yake marun da jakarsa a hannu fuskarsa saye da fari qal din medicated glass dinsa wanda bai hanawa mutum ganin kyakkyawan qwayar idanunsa,sumarsa a kwance luf baqa sidik sai sheqi take ita ba mai yawa ba kuma ba a aske ba qamshin nan nasa na musamman ke fita a jikinsa,ya dan zauna a hannun kujera yana qarasa taje sumarsa da brush dake hannunsa
👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻
Afuwa afuwa
Nayi rubutu mai yawa zan turo muku na ajjiye wayar ina dan wani uziri kafin na dawo ya goge,chargy kuma ya riga yayi halinsa,kuyi haquri da wannan ku bini bashi da yardar Allah
Na gode
Mrs muhammad ce
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 12:40 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*wa yasan gobe?…..*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶3⃣2⃣
Ganin wannan dama ya sanya fadila tayi saurin sauko da kayan breakfast din gabansa duk da cike take da fargabar kada ya gwasaleta,tayi saurin hada masa tea☕ ta daidaita masa zafinsa ta ajjiye masa sannan ta sa masa wainar qwai🍪 da farfesun kayan ciki🍲,taji dadi da baice komai ba ya sauko ya karya,bayan ya kammala ya dauki jakar laptop dinsa💼 ya ciro yan dubu dubu guda uku ya ajjiye mata kamar yadda yake ajjiye wa sauran matan ranar nasu girkin duk da kuwa babu abinda zasu siya komai diba za suyi yana ajjiye,ya yi gaba ta biyoshi a abaya gabanta na dukan uku uku bangaren samira ta ga ya shiga don haka ta ja tunga ta tsaya baifi mintina biyar ba ya fito ya shiga gun salima mintina takwas sai gasu sun fito yana gaba tana biye da shi ganin fadila na tsaye da alamum jiran fitowarsa take sai yanayin fuskarta ya sauya😠 take ta juya ta koma ciki
Har sai da ya shiga mota ya zauna sannan tace a dawo lafiya tayi saurin juyawa ba tare da ta jira cewarsa ba don tasan bazai ce din ba ma idan ma ua fadan to ba mai dadi zata ji ba,tana hango salima da ta yaye labulen falonta tana kallonsu don haka sai fadila ta qorqiro murmushi ta dora bisa fuskarta
Ta rasa hali irin na salimar mutum ce mai tsananin qyashi da hassada ga azabar sa ‘ido komai idanunta na kai kamar wadda aka bata aikin yin hakan ita dai samira barta da kishi masifa da tsokalar rigima kuma kana tabata za kuyi uwar watsi agun shikenan duk da haka kishin salima har yafi na samira ita kawai tanada duniyanci da yasa take iya boyeshi ba kamar samira da ba ruwanta ko a gaban uwar waye ayita ta watse ba munafunta
⚜⚜⚜⚜
Haka fadila taci gaba da tsara rayuwarta duk ranar da take da girki zata shiga bangaren ta gyara ko ina da ina,tana kuwa fama da aikin domin tsakanin samira ko salima babu mai iya yin cangal kowacce haka take fita daga girkin ta tabar sashen a ahautsine
Tsakaninta da aliyyu sai girki ta shirya masa daddadan abinci ta zuba masa ya ci idan ya kammala ta kwashe ta wanke kana ta ja qafarta ta bar sashen sai kuma washegari idan ta shigo hada masa breakfast,da zarar kuwa kwanakinta ya qare bata bi ta kan kowa da zarar ta taso a aiki ta shiga sashenta ta qulle qofa tofa sai washegari zata sake fitowa
Wai inji hausawa sunce jiki da jini kuma mutum da zuciya cikin lokacin sai sai qyamar girkin su samira ya fara kama aliyyun ransa ya soma sosuwa da ganin sam gyara bai damesu ba,har gwara ma.salima tunda at least akwaita da son ado da kwalliya zata yi wankanta tayi kwalliyarta hakanan zata qoqarta ta dafa masa koda jallop ce albarkacin masifar son sa da take duk da bata taba girki a gidansu ,amma samira kuwa babu daya qanwar biyu daga ciki
Cikin harshensa da zuciyarsa yana jin dadin girkinta sosai dandanon da bai taba jinsa ba gun kowa ba baya ga mominsa,miskilanci irin nasa yasa ko a fuska bata taba ganin alamun haka ba,takan tattare masa socks singlet handkerchief three quarters da duk inner wears dinsa harda jallabiyoyinsa da yake sawa ta wanke su tas ta goge su sannan ta feshe su ta turare ta jera masa su to ammafa insha Allahu bayan kwana hudu ta karbi girki zata zo ta tarar da su kamar kamar ba su ba komai an hargitsa shi sai ta soma fuskantar wani abu akwai gayya a ciki ta kuma san bazai wuce su salima ba don adawarsu gane da aikin nata a fili yake qara ra wani lokacin takan jiyosu suna yan qana nan maganganu takan sharesu taqi tankawa don basu tari gabanta sun gaya mata ba bare ta kula da shashancinsu
Abu daya ke qona mata rai aishi aliyyun na gani suke batawar shin bazai tsawatar musu ba idan su basu da tunani?
Ga misali a farkon fara aikin nata kafin su soma adawarsu takan tsince kayan aliyyu ne kawai a dakin a watse takan gyara ba tare da ta damu ba tunda tasan aikin ta ne dama,da tafiya ta soma nisa sai suka dinga barin brassiere panties sleeping dress underwear 👙👗musamman salima wadda kullum sai ta tsince nata tunda samira ke fara girki sai ita wanda a qa’ida fadila ce ya kamata ta zamo mai girki a farko amma suka maida ita ta qarshe ta qyalesu duka ta zuba musu ido ,tasan da gayya take zub da kayan,zuciyar fadil na matuqar baci da hakan,a duk lokacin da ta tsinci kayan takan bata lokaci mai yawa tana qissima dalilin barin kayan daga jikin mai su wanda hakan ke qara ta’azzara kishinta ga aliyyu
Wani sabon rainin hankalin kuma sai ta fuskanci ya shigo ta soma gyaran sai ta shigo tace”☺sorry fa don Allah,jiya na mance kayana akan gado wallahi dear ne ya rudani daren jiya shi yasa da safe na manta da su ban dauka ba,kinsan shi akawai nacin abun,sai dai fa ba sauqi shima fa gwani ne😉”wannan ya bata ranta fiye da abinda tayi mata,har ta soma hasashem anya basu da masaniyar babu abinda ya taba gilmawa tsakaninsu?
Akwai lokacin da ta zube har da magungunan mata maau dauke da hotunan banza,wannan fadila maganinta tayi ta dauko mata wasu wanda wata maqociyarsu a acan gida ta bata ita basonsu take bame ma zatayi da su tunda ta bata ta jawo locker ta watsasu sai yau ta tuna da su ta qara mata tace ga wasu sai ki qara naga naki basu kai wadanan tsada ba ni kinsan bana amfani da su halitta ta bata buqatarsu komai nawa yaji ba sai da kwaskwarima ba”jiki a salube ta karba duk da bata nuna mata hakan ba,ai kuwa da ta karanta kwalin sai taga tabbas sun fi nata kyau to tun daga ranar bata sake bari ba
samira nata rashin mutuncin yafi ysakanin falo da kitchen parlour zuwa kitchen,zata dauko plates ne🍽 kofuna ne🍶 da su spoon tayi ta batawa wani abun plate din ma leda ce ta chewing gum ko biscuit zata dora akai kuma ta barshi a nan tunda ta sani cewa babu mai aikin gyara gun sai fadilan,duk da wannan neman masifa da suke ba wadda ta isheta kallo a cikinsu
Su kansun so suke ta kulasun amma ta qi basu wannan dama
Mrs muhammad
📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
01:18 pm 05/11/1437
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*wa yasan gobe?*
▶3⃣3⃣
Lahadi daya daga cikin ranakun qarshen mako ne wanda yake zama ranar hutu ga ma’aikata to haka ne ya zama ga fadila hutun ya zame mata double babu zuwa office kuma bata da girki,la’asar sakaliya ta ranar ta shirya tsaf cikin doguwar riga shigar da tafi so kenan ta material ce ruwan qwaiduwar qwai dinkin rigar ya bude sosai dga qasa an mata dogon hannu tayi rolling dinta kamar yadda ta saba da jan mayafi,takddunta ta diba 📄📉📈 na aikin office da takeson dubawa zata yi wani aiki a kansu ta dauki yar madaidaiciyar dadduma da daya daga cikin matashin kujerarta ta zira takalminta ta firo harabar gidan,sai ta tarar da saluma da samira zaune kowacce a harabar sashenta bisa farar kujera plastic,novel a hannun salima📖 samira kuma na riqe da wayarta📱 tana tana ta faman danne danne,tun kafin fadila ta kai ga zama ta fuskanci zaman nasu ba na Allah da annabi bane don kuwa taba fitowa ta fara cin karo da baqaqen maganganun da auke jifan juna da shi a fakaice ba tare da kowa ya kalli dan uwansa ba
kamar ta koma ciki sai kuma ta duba agogon wayarta📱taga biyar harda rabi da minti uku bata da wani lokaci na duba takadddun idan ba yanzu ba cikin gidan kuma zafi yayi yawa sanadiyyar hadarin da keta hadowa ana yin yayyafi dan kadan wanda ke qara tada zafin garin,ga injinsu yayi tsiya yaqi tashi tun wajen uku bakaniken ke kansa yana fama da shi kasancewar ba dan qarami bane yana daukar dukka freezers dinsu heater a.c da sauransu sun riga sun saba da wuta ko yaushe 24 hours,sai kuma ta ahimfida dardumarta cikin ranta tana fadin _ina ruwan biri da gada?_,tayi bismillah ta zauna ta soma aikinta,ashe duk suna ankare da ita,minti goma bai cika ba da zaman nata samira ta soma receiving call “shegiya kina duniya?……heeeee wlh gamu a cikinsa muna gogawa…….hahahahahaha aike kinsan fa hali tun ba yau ba”ta danyi shiru sanna ta sake kecewa da dariya kamar wani gardi tace”a haba haba ke sai kace ba nice samira ba?…..k kinsan saidai a gaji aqyale mana,kowacce qaramar shegiya sai ta kama gabanta da qafafunta🏃🏽 ,salima ta bude shafin gaba na littafin dake hannunta tamkar da gsken karatun take tace”qaramin dan iska ma yaci uwatar ai yasan kansa,samira ta sake kecewa da dariya “wlh har mai share share da goge goge ita wannan ai ba wahala zata bani ba…..yo hannatu yar anacen ma ba komai bace a guna wallahi duk hasashen da take na ita wata ce a gunsa
Sarai fadila ta san da ita take amma sai taga ba mutuncinta bane tsayawa tana cece kuce da wadda batasan ciwo mutunci da kuma darajar kanta ba ,kan ta qare wannan tunani sai ji tayi tas!
Da sauri ta dago idanunta don ganewa kanta wanda ka zubawa wannan lafiyayyen marin,aikin salima ne tana tsaye a gaban samiran bayan ta kwasheta da marin tana huci,tuni samira ta katse wayar hannunta na kan kumatunta ta miqe tsaye salima ta dora mata da bayani👉shiru shirun da kike ganin ina miki ba fa tsoronki nake ba ki bar ganin kina min kina samun nasara wallahi kin kaini bango nifa ba sa’ar yinki bace don uwarki”tasa yatsanta tan nuna qirjinta👆🏼 tana cewa”ni kika mara?”😁an marekin kadan ma kika gani wata rana zaki ga abinda yafi marin ma,kina tsammaninke kaďaice tantiriyar karuwa ko?💁🏽to 👆🏼nima karuwace nayi nayi kuma yaqon duniya fiye da naki ke da kika local ma
😳😳mamaki da tsoro suka kama fadiladama har akwai abun tutiya gun mace don tayi yawon karuwanci?wannan wane irin zama nine da Allah ya kwomù da har karuwanci ya zama abun ado?ita takaici ma sai ya sata ta maida kanta kanrubuce rubucenta📝taqi kola kowaccensu tana jinsu cacar baki mai zafi ta barke tsakaninsu tamkar zasu cinye junansu 🎭
Duf taji gun yayi shiru kamar an sanya musu kwado a baki🔐,ta dago da hazari don ganin mai ya sanya su yin shirun ba tare da kowa ya raba su ba?,aliyyu ne ashe ya ahigo kuma baau ankara da shigowar tasa ba sai da ssuka soma daga hannu da niyyar kaiwa juna duka👊🏻,kowaccensu tayi sak saluma ce ta fara cewa 😢wallahi tallahi ban kulata ba itace ta fara takalatakuma ka tambayi fadila”jin sun sanyo sunanta cikin sha’aninsu ya sanyata azamar taahi ta soma linke sallayarta,daidai lokacin da ya kai dubansa😒 gun da fadilan take da salimar ke nuna masa,ga mamakinsa tana gama ninke sallayar a nutse ta duqa ta mwaahe takardunta ta juya ta shige sashen nata ba tare da ta kalli ko da daya daga cikinsu ba cikinsu ba sai aliyyu ya bita da.kallo👀 karon farko wani abu daga garetà ya fara burgeshi nutsuwarta ,sai da ta shige ta kulle qofarta sannan ya dawo da idonsa kansu tuni samira har ta gudu🏃🏽ta rufe itama qocarta cike da fargaba da tsoron fushin Aliyyu😡 a akanta don ta tabbatar In dai ya bincika ya tarar bata da gaskiya to la shakka fa kashinta ya bushe,ta ruwan sanyi yake ma hukuncin da zaka raina kankà babu duka ba zàgi bà baqar magana,ya juyo ya dubi saluma da jikinta ke rawa sai kawai shima ya gewayeta ya shige nasa part din
⚜⚜⚜⚜⚜
Kwana uku tsakaniya kamaqarshen wata ne,kamar yadda ya zama al’adar gidan fita aiyàyya a iřin lokacin don sabunta abu uwan buqata na amfanin yau da kullum
Yaune za auyi fitar farko tun bayan dawowar salima gidan gidan
Fadila ta shiryq cikin shigarta ta bare bari tana nannade cikin lafayarta ,ta kammalà komai ta kira umminta don su gaisa,hira suke sosai ta jiýo tashin horn ta tabbatar aliyyu ne don bai son jira kuma baya jira saboda haka shima bai bari a jirashi tayi saurin maqale wayar a kafada tan ci gaba da hirarta da ummin tasa daya hannunta dauki jakarta🎒ta sa mèy ta kulle sashin,ta qarasa jikin motar tana sallama da ummin ta ciro wayar daga kafadarta tana kashewa sai ga salima da samira tamakar an jehosu kowacce na qoqarin bude gidan gana ta shige don badon fadila tayi azamar matsawa ba da daita zasu yi awon gaba,ta rufe bakinta da tafin hannunta🙊 dariya na shirin subuce mata😂,cikin zuciyarta tana cewa sunan wani film *qauyawa* Allah kayi mana magani wannan ai kishin jahiliyya ne
😂😂😂😂😂
Ku biyo *mrs muhammad*
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 12:41 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*wa yasan gobe?*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶3⃣4⃣
Allah ya sawwaqe tace,ta bude gidan baya ta shiga tana kallon drama,aliyu ne ya juyo don ganin meke faruwa haka ake shirin cire masa hannun mota?cikin tsawa musu su matsa masa daga jikin mota,bai wata wata ba ya figi motarsa ya barsu a gun sake da baki😦,gudu yake zubawa abinsa bisa dukkan alamu ransa ya baci,duk sai fadila tayi tsuru-tsuru don da irin wannan gudu da yake zabgawa gwara ya sauketa salun alun ,
Qiiiii…taji ya taka burki,ya gangara gefan titi ya faka motar cikin shaqaqqiyar murya taji yace”fito ki dawo gaba don ni ba driver din gidanku bane😠”bata ce kanzil ba ta dawo gaban
Yanayin zaman yayi wa fadila kusa sosai,mayen turarensa ya soma raba mata hankali,lissafinta ya soma qwacewa take kasala ta saukar mata,wani shauqin aliyyun ya mamayeta duk da azahiri idan ka kalleta zaka yi tsammanin ko inuwar sa bata gabanta
Sun isa shoprite inda suka saba siyayyar duk qarshen watan,ta san tsarinsa bai shiga yana tsayawa ne a waje yayi zamansa cikin mota,da sun gama siyayyar ayi masa total a turo masa list da amount,da yake yana harka da su akwai kamfaninsa dake india wanda akwai hurdar kasuwanci tsakaninsu,”u have twenty minutes idan kima gota haka so sai ki nemi motar mai da ke gida”ta jinjina masa kai duk da idan da sabo yaci ace ta saba don duk sanda ya kawosu mintina ashirin din yake basu basa kuwa darawar domin dukkaninsu sun san halinsa yana iya tafiyarshi
A nutse ta shiga ta duba muhimman abubuwan da take buqata don tana lisaafin jibi ita zata karbi girki duk da ba wani tsiya bane a ciki banda tsabar bauta ta gyare gyare da dafa masa abinci wanda sau da yawa tare suke cinyewa da samira da salima ,sukan daidaici lokacin cin abincinsa ne su shigo da nufin sun zo taya shi hira sai kuma su taya shi lamushe abincin
A gurguje ta kammala zabar duk abinda tasan bata da shi ba wani kaya ne mai yawa ba tunda bata iya gama amfani da siyayyar tsohon wata suke sake sabuwa saidai ma wani abun ta bada shi,sai ta soma dibarwa salima da samira abinda ta lura sunfi siya yawancin lokuta idan suka zo,Allah ya taimaketa minti goma sha takwas ta gama komai,ta riqe leda daya ragowar aka biyo ta da su
Tana fitowa suka yi kacibus da shi yana tsaye a hanyar wucewar tata,shi da wata matashiya ce wadda a qalla shekarunta ba zasu gaza ashirin da shida ba,abunda ya bata mamaki shine ganin hawaye bibbiyu bisa fuskarta😭,ta maida dubanta garesu a karo na biyu daidai lokacin da aliyyun ya nuna ta da yatsansa yana cewa “👉 this is d last warnings da zaki sake bina wani guri ki kama kanki tun kafin ya gudu ya barki and respect ur self”
😳Sai taga kawai ya sa hannu ya rungumota kafadarsa sassanyan qamshinsa ya buwayi hancinta suka bi ta gabanta suka wuce,cikin mamaki fadila ta waiwayo still tana tsaye tana binsu da kallo hawayen na bin fuskarta😭,ta sake fashewa da kuka a guje ta nufi motarta ta fada ciki🚗🏃🏽,
Daf da zasu qarasa cikin motar wadda tuni an kammala zuba kayan taji ya tureta daga jikinsa ,ta tsaya a baya sai da ta bari yayi gaba sannan ta biyoshi,zaman kurame suka sakeyi cikin motar har suka isa gida
Ta kammala shirin baccinta ya sanya night gown sannan ta dora dogon hijabinta mai hannu da ya sauka har saman qafafunta ta sanya sannan ta kwashi ledojin da ta yima su salima ta su siyayyar ta nufi sashensu,saidai ta tarar dukkaninsu basa nan don haka zuciyarta ta bata amsar ba zasu wuce sashen aliyu ba
Can kuwa ta tarar da su kowacce ta debi fushinta akan ya wulaqantata ya tafi ya barta taje masa da shi ,basu san ya fisu fushin ba don haka ci kanki ba wadda ya gaya mawa a cikinsu ya watsar da su a falo ya shige dakin barcinsa ya shiga wanka,sun sani ba wadda tayi gigin binsa ciki tunda suka ga ya musu banza to da tashi da su nan suka jibge a parlour zaman jiran sa,har ya fito ba wadda ya kalla ya haye dining yana fama da girkin salima wanda,farar shi kafa ce tsura babu salad ko cabbage bare akai ga batun nama,cikin qufula ya kira sunan salima da suke zaune suna fama da ‘yar harare harare,bisa kansa ta tsaya ita dole wadda akayiwa laifi ce tace gani😼,ya dora gwiwar hannunsa saman table din ya hade yatsunsa cikin juna ya dora habarsa a tsakiya sannan ya kalleta yace”😒 sau nawa nake gaya miki I don’t like such cooking?,ko kayan cefanenki sun qare ne?ko sun qare ba zaki iya sanarmun ba kenan?,ta tabe baki ta kawar da kai tace “kayi haquri “ya danyi shiru ya dafe kansa kamar ba zaice komai ba,har ga Allah ba don yunwa ba baiga dalilin da zai sanya shi cin wannan abincin ba,ya shiga tuna irin dandano mai gansarwa da yake samu duk ranar girkinta,ya dago kai yace bude fridge dina ke debi cabbage da cucumber ki yankamin ki hada min da dafaffen qwai tunda yau ban isa naci nama ba”ba tare da ta amsa ba ta juya
Mrs muhammad👑👑
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
5:44 pm 5/11/1437
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*wa yasan gobe?……*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶3⃣5⃣
Da sallamarta ta shigo falon sam bata ma lura da shi ba bisa dining,ta dan dora murmushi bisa fuskarta🙂,salima ce ta masa sallamar itama ciki ciki kamar wadda aka cusawa tsumma a baki,ta qaraso gabansu ta direwa ko wacce ledarta🛍 a gabanta tana cewa”sannunku,ga siyayyarku nan Allah yasa na haso muku da abubuwan da kuke buqata ” salima shiru tayi saboda tafasa da zuciyarta keyi,yayin da salima yar takife tace” waye ya saki sarauniyar masu shishshigi ,kina murna kina rawar kai an koro mu ke an tafi da ke,shine don digimi da neman gindin zama harda wani yi mana siyayyar kaya ko?to ahir dinki wlh ni ba’a shiga gonata don kiji na gaya miki,har wata fada ce dake a gunsa banda ta shara da zaki mana rawar kai?ko an gaya miki sonki yake?”
“Hmmmm matar cushe kenan”cewar saluma da bata tofa ba sai yanzun,cikin wani irin mamaki da al’ajabi ta dago tana dubansu,meke faruwa?a ina suka san wannan ?haka aliyyu ya gaya musu cewar ba aonta yake ba?,wannan wane irin kwance zani a akasuwa ne?,wanne irin cin kashi ne haka yayi mata?”take idanunta suka sauya launi,wani irin fushi da bata tsammaci tana da shi ba ua sauko mata😡😣,kamar hadin baki suka miqe suna shirin barin dakim don dama haushin kaza ne huce kan dami,tunda sunsan ko giyar wake suka sha basu isa su juye haushinsu ba kan wanda ya musu laifin sai suka juyeshi kanta,suna shirin ficewa suka jiyoshi cikin lion voice dinsa yana kiransu “😠ku kwashe kayan nan daga gun nan ku bace min da gani”kunnen uwar ahegu sukayi niyyar yi a zafafe yace da su”👉�billahil azim duk wadda tabar ledarta a nan tamu ce ni da ita”tilas kowacce ta waiwayo ta dauki tata tabar sashen
Cikin matsanancin bacin rai ta dago kantasai suka hada ido,wani baqinsa ta gani wanda bata taba ganin yayi makamancin haka a idanunta ba,kafin ya janye idanunsa ta fara janye nata tayi azamar juyawa ta bar sashen
Kusan kwanan zaune tayi ,babu abinda ranta bai gaya mata ba,abunda take ta qoqari da fadi tashin bunneshi ashe ya dade da yin tsiro har yqyi yabanya?tabbasa aliyyu ya cutar da zuciyarta ya cutar da zuciya da ke cike da qauna gami da begensa cikin kowanne fitar numfashi na dan adam,tabbas a ayu badon mutum bai da ikon cire son wani daga zuciyarsa ba da itakam ta ciro har zuciyar ta wurgar ta huta ma gaba daya,ranar idanunta basu ga bacci ba sai tunani data takurawa.kanta da shi wanda ya haifar mata da da ciwon kai da zazzafan zazzabi,ba ita ta samu kanta ba sai washegari da la’asar bayan ta takurawa kanta ta cire damuwar ta ajjiyeta gefe
⚜⚜⚜⚜⚜
Cikin qyanqyami yake shiryawa,gaba daya dakin ya hargitse sun kuma barshi kamar yadfa suka saba,sai dan yakanji relief idan ya tuna zaije ya dawo ya tarar da komai ya zama neat,da hanzari ya kammala ya dauki jakarsa💼 ya fice ba tare da ya saurari breakfast da salima ta hada ba ruwan tea ne fari sol babu citta bare kanunfari sai soyayyen qwai wanda qarninsa ke hanashi hadiyarsa,shi kuma akwai qyanqyami yayin da su kuma basu maida tsafta 💄👠👒💅🏽da gyara wani abu mai muhimmanci ba
Sanda ya dawo ya tarar da sashen nasa yadda ya barshi yayi matuqar mamakin hakan,don bai saba ganin haka ba,yasan ranakun girkinta zai tadda komai a kintse hakanan yaji ransa ya baci da ganin haka,ya zube anan saman kujera yana fitar da iska mai zafi daga bakinsa,ya dubi agogon hannunsa qarfe shida da arba’in har da hudu,mintina qalilan suka rage a shiga masallaci sallar magarib,a kasalance ya duqa yana zare sau cikin qafarsa👞hadi da sabule safar,wata bahaguwar yunwa ke rarakarsa,yinin yau gaba daya ba abinda yaci banda maltina mai sanyi da ruwa da yake ta dirka,saoda yana da yaqinin zuwa ya tadda abinci mai kayau🍛,
Kai tsaye ya shige toilet ya dauro alwala ya dawo falon yana goge ruwan jikinsa da handkerchief,gidan🏛 tsit sai hasken fitilu da ya gauraya da duhu suhun magariba da ya soma kawo kai ,ya dan lumshe idanunsa kewar qanan yara na shigarsa👫,ya tabbata da yana da su da zai dinga jin koda hayaniyarsu ce da gilmawarsu ,ya riga ya saba da tsabar qwarewar.matan gidan wajen iya rashin kula da miji,ya katse tunaninsa sanda ya jiyo kiran salla a masallacin dake can farkon layinsu ya sanya silifas ya fice yana maìmaita abinda liman ke cewa kamar yadda annnabi ya horemu idan munji kiran salla
A can ya zauna ya jira sallar isha’i sannan ya dawo gidan,still gidan dai na nan kamar yadda ya barshi kowa na kulle a sashensa,ya dauki wayarsa ya kira nasiru ya gaya masa inda zaije ya samo masa masa da miyar ganye,cikin lokaci kadan saiga nasirun ya dawo ya amsa ya koma ciki yayi wanka ya sauya kayan bacci,ya zuba masar ya ci sai da ya qoshi sannan ya jawo computer💻 dinsa ya soma shigar da lissafinsa na yau,hankalinsa ya kasu kashi biyu,ko alama zaman gun ya gundireshi sabo da tsaftar gun bata masa ba,shigowar saluma ce ta saka shi tsai da abinda yake ,ba laifi salima indai ta bangaren qalqale jiki ne salima ta iya wannnan kam,yanzun ma ashirye take cikin dinkin lace baqine mai adon ja,ya sauke biron dake hannunsa
Ya sauke biron dake hannunsa🖍yana dan binta da kallo,tayi masa kyau sosai,fuskar sa ta dan sassauta daga dauretan da yayi ganin yadda take masa murmushi😃,gefansa ta zauna cikin salon kissa take cewa”barkanka da warhaka ranka ya dade”yadan janyota jikinsa yana cewa “barka kadai……sai yanzu aka ga damar zuwa yimin sannu da zuwan?”ta san tabe baki tace”girki na ne da zan taho daga dawowarka?” “Ko ba girkin ki bane ni ba mijinki bane?” “To ayi haquri ko” yace “ya wuce”ya maida kansa kan aikinsa tana tayashi da hira jifa jifa yana amsa mata
Samira ce ta shigo wannan karan harda sallama,abun arziqin nata yau yana da yawa🤔 don ba’ayi wari da.wari ba riga da zani ta saka na atamfa,kanta tsaye ta zauna daf da shi tana mata sannu da zuwa ba tare da ta nuna ma ta san da zaman salima ba agun,ya dan saki fuska bayan ya ja yatsun hannunta da nashi zara zaran yatsun yace”bana amsawa tunda kema sai yanzu” “bana shishshigi ne sweet kuma bana son maiyi shi yasa”ya dade da haddace wannnan kalma daga bakin samiran,don haka ya mele baki gefe sannan yace”lallaikam,da kun bani babies ai da sai nace kusha zamanku ni kuma insha hira da yara na ko?”
“Nikam ai na riga nabada tawa baby din”cewar salima”no she is belongs to momy,u already know…sabuwa nake so”cikin shagwaba ta dan bata rai sannan tace”haihuwa is not easy dear”samira sai ta tabe baki hadi da cewa”mukam ai ba yanzu ba,tunda sauran quruciyata🤔”aliyyu ya jawo ragowar takardunsa yaci gab da rubuce rubucensa ,kowacce yasan inda tasa gaba dama salima d tasu ai tun shekarun baya,shikam idan da abunda ya rage masa yanzu shine tara family babba
Cikin kwanakin fadika ta watsar da duk wata harka data danganci aliyun ta koma rayuwarta irin ta da,idan gari ya waye tayi ayyukanta na gida ta fice office sai ta dawo tan dawowa ta shige to sai washegari idan ta gaji sai fa kira farida ummi ko anty hafiza su sha hirarsu,ko muhammad yazo mata su wuni tare abinsu
Gaba dayan bangaren ya fita daga ran aliyyun saboda tsabar kacamewar da yayi,ko ina ba kyawun gani a hargitse,ranar da salima ta fita daga girki yaga tana shirin kulle sashen ta wuce nata sashen,cikin takaici ya kalleta ganin bata da niyyar kawar da ko cup din da ta hada masa tea bare akai ga batun gyara “jimana!” Yace da ita a zafafe ta dawo tace gani”bai ko kalleta ba ya daga intercom ya kira sashen samira ,sai da ta qara wasu mintina kana ta iso hakan ya sake hassala shi,ya dubesu cikin bacin rai yace
“Anya kuwa ky mata ne cikakku?ba ko wani jinsin bane ku?”a mamakance suka dago suna kallonsa,”kamar ya?”inji samira,da hannunsa ya soma yi musu nuni da falon suna binsa su kuma da kallo,”ku duba….dubi……haka ya kamata ace ya kasance?haka sauran mata suke barin turakar mazajensu?….abun naku ba ya yi yawa na lira ba hankali a ciki,ba tsafta ba iya kula da miji?kuma ni kuna son kyautatawa daga gareni?….it cant abun yayi yawa na gaji da tolerating bad attitude dinku….👉as from today ya zama dole a kanku kowacce kafin ta bar nan ta tabbatar ta gyara duk inda ya kamata ba ruwana da qazantarku ruwanku ne ku gyara naku ko ku barshi haka is not my own business…..
Ya suri briefcase dinsa ya fice,da kanshi yau zaiyi driving kasancewar nasiru baya nan ya tafi ganin gida ,ya juya kan motar ya danne horn yana jira a bude masa,ta kalli gilashin mudubin dake gefansa da niyyar gyara zamansa don ganin wanda kebin bayansa sai yaga wata motan na jira ya fita itama ta fita,ya duba sosai sai ya hangota zaune hannun ta saman sitiyarin fuskarta tayi fresh cikin safiyar,agogon dake daure a tsintsiyar hannunta take kallo da alama ta kusa maka rane don sai yatsina fuskarta take,material ne ajikintan yellow mai adon coffee,ba makeup ko kadan a fuskarta banda powder data shafawa soft chocolate skin dinta,sai lips balm data shafawa lips dinta sirara masu taushi,tayi lullubinta na mutunci har saman ka,ya dan tabe baki ya dauke kai itakam bata san ma yana yi ba,duk da ta ganshin
Ayimin afuwa kasancewar yau ina da uziri irin wanda ke kama ko wanne irin dan adam na turo muku shi late kuma ba yawa amma zamu hadu insha Allah,ina godiya a gareku👏🏻👏🏻
Mrs muhammad ce
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 12:42 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*wa yasan gobe?……*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
3⃣7⃣~3⃣8⃣
Fisgar motar yayi ya ficee daga gidan sannu sannu take binsa a baya har suka bar cikin layin suka hau babban titi,yana hangota ta qarawa motar gudu tayi over taking nasa ta wuce shi ba tara da ta dubi koda sashen sa ba,ya daga idanunsa yabi motar da kallo yana dan gyada kai cike da mamaki da jin izza shi zata nuna wa iyawa da qwarewar sarrafa mota?,yaushe ma ta fara kama sitiyarin
Wani girman kai ne ya kamashi,ya qarawa motar shi speed cike da qwarewa da gwaninta shima ya mata over taking,ta lura sarai da shi amma sai ka rantse da Allah batasan da wanzuwarsa akan titin ba,ta dan cije lebenta sannan ta dan daki saman sitiyarinta cikin zuciyarta tana dariyar mugunta,sai da ta barshi ya sakankance sosai ta take motar ta qara maya gudu sai ji yayi fit ta wuceshi ,cikin zafin nama da mazantaka ya qara wa tashi shima wutar don ya nuna mata bata isa ba saidai kafin ya qaraso har ta qaraso kwanar freedom ta sanya signal ta shige,ta morrow din gaba suka hada ido yana wucewa amma sai ya wuni mugun dauke kai kamar ma bata sanshi ba
Ya girgiza kai ya miqe kasancewar b.u.k zai shiga hanyar ta rabu cikin zuciyarsa yana fadin”zan koya miki hankaline kin maida ni abokin wasanki kenan
Qarfe biyu ya baro b.u.k din bayan ya kammala abinda ya kaishi,kai tsaye ya tashi motarsa ya bar makarantar,biyu da rabi ya iso freedom hakanan bai taba zuwanta ba koda hira suke son yi da shi yana basu appointment ne,ahankali ya gangara layin ya qaraso bakin gidan radio din ya yiwa mai tsaron bakin qofa horn ua taso don yaji me ke tafe da shi,da ganinsa ya fara fara’a cikin mutunci suka gaisa ba tare da jiran komai ba ya bude masa qofa yana jira ya shiga,da hannu aliyu yayi kiransa ya qaraso saitin window ya ranqwafo yana saurarensa,”wata sabuwar ma’aikaciyar ku nake nema ina fata bata fita ba”cikin tunani yake kalleshi,aliyu ya gyada masa kai da son tabbatar masa,sai kuma yadan saki murmushi yace “oh ko haj fadila?”aliyu ya gayada kai yace”yes itace”😃 tana nan ciki kuwa bata fita ba mutuniyar arziqi kuwa ranka ya dade…..ko kira maka ita za’ayi”aliyu ya dakatar da shi”✋🏻a’ah barshi zan dan jirata ba matsala”ya tada motar ya shiga security suka nuna masa gun parking”ya daidaita motar qasan bishiyun dake gun ya kasheta,ya miqar da sit din nasa ya kwantar da shi yadda zai masa dadin kwanciya,yayi sama gaba daya da glass din motar kasan cewarsu akwai (tinting)jikinsu,yasa hannu ya qaro qarfin a.c dake jikin motar ta gauraye masa ko ina ya kashe dukkanin wayoyinsa ya watsa su sit din gefansa,ya maida bayansa ya kwantar jikin kujerar yana fuskantar ginn gidan idanunsa akan reception,lokaci lokaci kuma yana bude mujalla yana dubawa
Zaman minti ashirin yayi ya ganta ta fito gefanta wata yar matashiyar ce sabe da baby girl a kafadarta ,ita tayi hanyar waje ita kuma ta nufi inda tayi parking tasa maqullinta ta bude motar tashiga,ya miqe ya gyara zaman kujerarsa ya jawo belt ya daura,ya kunna motar ya biyo bayanta sanda take ficewa daga ginin gidan radiyon
Ko kusa fadila bata lura da shi ba don bata kawowa ranta ba,cikin kwanciyar hankali take tuqinta,wani mahaukacin horn taji ana mata kafin ta ankara motar ta zo daf da ita tana shirin gogarta a gigice tayi gefe da motar tana ci gaba da kallon motar da ta kasa tantance waye a ciki?,kafin ta gama wannan tunanin har ya dawo daya side din data koma ya sake matsowa daf da ita yana shirin gogarta,sai ta tsorata 😳kasancewar titin da ta biyo ba mai yalwar jama’a bane bugu da qari kuma rana ce babu gilmawar mutane sosai a gun
Cikin lokaci qanqani ya gama rudata gaba daya ta tsorata dama da hugunta ya dinga komawa,tuni lissafinta ya qwacr tama manta sitiyarin na hannunta ne,sai ta taji motar ta soma yawo da ita saman titi idanun aliyu na kan motar,ya zubawa motar ido ganin ta soma yawo bisa kwalta a hankali yana nazari,ya saki ajiuat zuciya sanda yaga ta daidaita ta daina tangal tangal din da takeyi,ya qaraso saitin window dinta sai ya sauke glass ta juyo idanunta cike da taf da tsoro suka hada idanu,ya dauke kansa ya qarawa motar speed yayi wucewarsa,wani abu ya daki zuciyarta sai ta kasa tuqin,ta sauka a hankali ta gangara gefan kwalta ta kashe motar ta jingina da makarin motar idanunta a runtse😣 zuciyarta na ci gaba da bugawa💓,sai hawaye ya biyo rufaffun idanunta ta saki kuka silently,sai da taji don kanta ta samu nutsuwa sannan ta kunna moyar taci gaba da tafiya slowly a gefan titi don gaskiya ya dauki haqqinta
Tana isa parking space taga motar tayi tsammani ya shge cikin gidan saidai tana gama kulle motar ta ganshi tsaye jikin motar yana amsa waya,idanunsa suka shiga cikin nata wadanda suka dan kafa alamar tayi kuka takaici yasa ta sakar masa harara🙄 hadi da murguda masa baki😙ta shige jin alamun taku tayi ana bin bayanta,tana juyawa taga kuwa shi din ne,tasan mai yasa ya biyota cikin azama ta qarasa shigewa bangaren nata daidai lokacin da yakai hannunsa zai fincikota,tayi saurin sanya maqulli ta qulle qofar hadi da jingina a jiki,tana kallonsa ya juya ya koma” kawai”ta fada a hankali
Zaune take tana kallon wani Indian film hum dil de chuke sanam tana ganin son maso wani tamkar nata da aliyu,ta bada hankalinta kacokam bisa t.v din sai tsintat qamshinsa tayi yana yawo bisa hancinta,ta dago da sauri yana tsaye bisa kanta hannunsa harde a qirjinsa shima idanunsa na kan t.v din sai a lokacin ta tuna da abinda ta masa dazu da hanzari ta miqe ta jawo hijabinta ta zira tana neman guduwa sai alokacin ya dawo da idonsa kanta fuskarsa a dinke tsaf,da baya da baya ta soma tafiya yana binta har ta dangane fa qofar bedroom dinta ta fafa ciki tana shirin danno qofar,yasa hannu ya kare ta,yaci gana da binta sai da ta dangane da sif dinta ,qwalla ta cika idanunta idonta tuni ya raina fata,girgiza kanta ta soma yi tana cewa cikin tawar murya”donA….Allahh kay……yi…yih…..haquri….”yasa yatsansa ya dalle mata baki,taji zafi sosai ta sanya hannunta ta dafe bakin🙊,ya zare mata ido sosai yace”wa kika harara? Ni sa’anki ne?kin raina ni ko?,still tafin hannunta na dafe da bakinta ta girgiza kai tuni hawaye ya balle mata😭,ya saka hannunsa ya kama gashinta💆🏼 da ta tufke cikin hijabin har sai da tace “wayyo Allah na!……,hadi da wani dan guntun hawaye da ya silmiyo mata,ya saketa yana sake matsota har tana jin hucin numfashinsa,ta runtse idonta gam tana jiran jin hukunci na gaba,ta yarda aliyyun mugu ne,tasan yau Allah ne kawai zai qwaceta
Shirun da taji yayi yawa ya sata bude idonta,ba kowa a dakin hasalima an ja mata qofar dakin sai ita kadai dake tsaye jikinya na kakkarwa,ta sake sakin kukan ta kifa kan gadonta
⚜⚜⚜⚜⚜
Cikin kwanakin gaba daya ya gama tsanar bangaren nasa,bedroom sin da suke cikin corridor din wadanda bai amfani da su duk sai da ya budesu yayi amfani da su ,duk da alokacin su su samira suna ganin suna qure adaka gun gyaran amma shi sam bai masa ba,don ba wani qwarewa sukayi ba kamar na fadilan,yakan daure ne kawai ya nuna yabawarsa,ya tabbatar wa ransa nata yafi wannan kimtsuwa
Kowanne dan adam wani lokacin kakan tsinci kanka cikin rashin jin dadin rai hakanan to haka yau aliyu ya tashi,alhamis ce wadda aka wuni garin lullube da hadari da iska mai cike da qamshin qasa,mutane da yawa yanayin yayi musu amma banda shi,biyar saura yama yi dawowarsa gida,yayi cilli da jakar tasa a falo,gidan dai na nan a yanayinsa na kullum wato shiru,toilet ya shiga ya watsa ruwa ya fitar jallabiya mai sulbi irin ta maza milk colour mai dogon hannu ya saka,ya feshe jikinsa da shamsul imarat ya hada da turaren chastity ya dawo parlour ya fitar da computer dinsa ta tafi da gidanka(laptop)ya jona mata chargy ya jawota har kan kujerar da zai zauna ya dora ta a saman kujerar,ya daddanata ya bude bayan komai ya gama daidaituwa ya soma aikin da ya dawo da shi
Munti biyar goma sha biyar sai aikinbya soma gagararshi saboda yunwa,ya dafe kansa da hannu daya yasa dayan ya lallatsa comouter din ya kasheta,ya zubawa fridge dinsa ido yana nazarin me zaici a ciki?komai dai na nau’in ciye ciye akwai aciki🍏🍎🍐🍊🍋🍌🍉🍇🍓🍈🍒🍑🍍🍅🍆🌶🍠🍤🍟🍔🌭🍕🌮🌯🍕🍘🍦🍧🍨🍺🍷🍾
Saidai gaba daya sun gundireshi babu abinda yagi buqata sai abinci mai nauyi da gishiri,gaba daya taste din girkinsu salima bai gamsar da shi bare yasa su dafa masa wani abun,koda ranar gikinsu ne yana yin kawaici ne kawai yaci don kada suga rashin kyautawarsa
A nutse ya isa gaban freezer din ya bude yana sake kallonta kamar baisan meye da meye a ciki ba,hannunsa yakai kan madarar fresh yo da tayi sanyi sosai tanata fidda tsatstsafar sanyi yasa daya hannun ya maida murfin freezer din ya rufe,ya maida kallonsa kan robà dake riqe a hannunsa yana jujjuyata tamkar mai karanta rubutun dake jikinta
Ya saki tsaki hadi da cillar da robar kana yayi tattakì ya isa bakin window dinsa yajanye labulayen jiki gefe daya ya dora idonsa a harabar gidan,idanunsa suka sake kaiwa kan bangaren nata a karo na barkatai,tarwai yake da haske alamun tana nan,ji yayi yà gaji baAi iya jutewa ba sole ne yazo tayi masa aikin da tasabar masa idan yaci gaba da jurewar yana jin qila yunwa da tsantsami na iya illatashi,ya juya ya zira slipper dinsa ya fito….
Mrs muhammad ce👑
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 1:41 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*wa yasan gobe?…..*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
3⃣9⃣~4⃣0⃣
Ya juyabya zira slippers dinsa ya fito Gaba daya tana ma gida babu inda ta fita saboda ba ba abinda zatayi a gidan radiyon shi yasa bata shiga ba,zamanta tayi ta dinga bacci abunta sallar azahar kawai ta tashi tayi ta dan sha yoghurt ta koma baccinta
Qarfe hudu da rabi ta farka tayi wanka,tq gabatar da sallar la’asar din da ake binta,riga da skert ta saka hade da mayafinsu sannan tayi kitchen da azama saboda wata hadaddiyar yunwa dake sakadarta
A tsaitsaye ta hada jallop din taliya🍜 da tasha kifi ta watsa mata carrot piece da grean beans,da zaman jiran dahuwar abincin da zata yi sai taga gwara ta hada lemo,cikin lokaci kadan ta hada lemon kwakwa da yasha madara ta bude freezer din kitchen din ta sanya ta a ciki,bayan ta kammala ta juye a plate ta kalli plate din tana murmushi hadi ya tsina fuska don ita kanta tasan ba iya cinyeta zata yi ba ta mata yawa”let me try”ta fada tana gyada kai ta hado da lemonta dake cikin jug din ta taho dashi parlour ta zabi kujerar da zata zauna akai don haka ta jawo centre table ta dora su a samansa
Ta juya ta koma daki don daukar wayarta ta tashi ne ta tarar da missed call din fauziyya colleague dinta ta barshi da niyyar idan ta gama abinda take ta kirata
Ya kama handle din ya murda hadi da tura qofar ta bude ya shiga,qamshin freshner din parlour hadi da qamshin jallop din ya dunqule ya daki hancinsa wanda hakan ya sake haddasa masa yunqurowar wata matsananciyar yunwa,idanunsa suka kai kan plate din dake dauke da jallop din🍝😋dake ta tururi da qamshi,
Fadila ta fito hannunta dauke da wayar tana duba missed calls din data tarar ciki harda na rumasa’u da farida,,sam bata lura da shi ba agun sai da yayi gyaran murya,adan furgice ta dago don bata zaceshi ba,a dinke fuskarsa take kamar kullum ya cillo mata muqullai suka sauka a kusa da qafafunta,yayi gefe da kansa sannan cike da ginshira yace”ki gyara min bangarena sannan ki sama min abinda zanci yanzun nan tunda sai an koya muku abinda ya dace” ya nemi kujera ya zauna hadi da jawo wani dan qaramin table din na glass ya miqe qafarsa akai
A hankali ta sunkuya ta dauki muqullan,cikin zuciyarta tace”ka gama qunbiya qunbiyarka ka ma,mutum sai shegen jin kai ka fito kawai kace kazo neman taimako guna,ki banza dai ina da muhimmanci tunda.duk cikinsu babu mai iya maka haka sai ni duk da dan banzan jin kanka”ta shiga daki ta canza mayafin zuwa hijabi sannan tazo ta wuce shi yana zaune yadda ta barshi
Kamar jira yake ta fita din ya jawo abincin gabansa,ya dauki cokali mai yatsu yana jujjuyata yana qare mata kallo,a zahiri shi taliya bata dameshi ba don haka ya ture plate din gefe sai kuma qamshin ya addabeshi don haka dole ya jawo yakai loma daya bakinsa🍜
Lumshe ido yayi dadin na zagaya kunnensa👂🏻,ya tabbatar wannan ne taste😋 din da yayi missing kwana da yawa kuma shi yake nema wasa wasa saiga gashi ya tashi da plate din gaba daya,ya shafa cikinsa take yaji yana buqatar qari bai qoshi ba, ya miqe ya nufi kitchen kasancewar tsarin ginin nasu daya ne shi yasa ya fahimci inda yake,ya daga tukunyar gaba daya ya juye ta ciki ya cinye ya dawo falon dauke da ruwan roba na faro a hannunsa ,sai yaji ya samu nutsuwa ba shakka yunwa bata da hankali inji dan almajiri
Ya miqe a kan three sitter🛋saboda yanaji har cikin zuciyarsa yanayin qamshi da tsaftar falon sunyi.masa,idanunsa a lumshe yana tunane tunane har aka fara kiraye kirayen sallar magariba sannan ya miqe ya bar sashen,kafin ya qarasa nasa suka ci karo da samirah na shigowa da motarta,ya tsaya qam yana dakon qarasowarta hannunsa zube cikin aljihun wandonsa,tunda ta hangoshi tace da qawarta sa suka shigo tare “na shiga uku kubra mai gidan nan ya dawo”kubra da hankalinta ke kan waya ta ja tsaki tace”mtswee to sai me?ni wlh samira mamaki kike bani tunda.kika yi auren nan duk kin canza komai adarare duba fa dazu da zamu fita fitted gown fa kawai nace ki saka amma kika qi bayan kinsan gun manyan mutane zamu ji,tsoron mutumin nan kike ji kamar wani Allahn ki ke yadda ma kike tsoronsa baki tsoron Allahn naki ma,nidai gwara ma dai yau naga wanne dan mulkin nan ne wannan da.kike masa biyayya haka kamar shi ya tsuguna ya haifoki
Cike da gadara da rashin kunya kubra ta fito yayin da samira keta.rabe rabe don kuwa riga da skert ne a jikinta na shadda kana kallon shaddar kasan an kashe mata naira mai tsada ce saidai anci mutuncinta ta wajen kacalcalata da yi mata matsatstsen dinki,ga mayafin jiki ta sai kace wadda aka yiwa gorin lullubi
Kallo daya ya yiwa kubra da ta tsareshi da ido duk wata rashin.kunya da ta fito da ita tayi nata gun,hakanan aliyu yake Allah ya bashi baiwar kwarjini masifa,ta sake kallonsa karo na biyu”wow”ta fadi a hankali don gaba daya ya tafi da tunaninta,sai ta mance mission din ta fito da shi,ta zuba masa ido gaba daya,sai a lokacin idonsa ya kai kanta bayan ya dauke kansa daga samira,takaici ya kama Aliyu ganin irin kallon qurillar da take masa ya sake dinke fuska tamau,sai lokacin ta kula da ta bada kanta fa ashe,
Ta dauke kai cike da duniyanci da niyyar bin bayan samira dake ta zuba sauri jiki na rawa,tsawa ya daka mata😠 hadi da nuna mata qofar get sannan yace”get out of my house idiot kada na kuma ganin wadannan lalatattun qafa fun naki a gidana”murmushi ma ta saki ta juya ta fice cikin karairaya wai ko zata janyo hankalinsa, bata san wani takaicin ne ya sake qumeshi ba yaja wani dogon tsaki ya juya ya nufi sashen samira
Mrs muhammad👑
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
3:37 pm 8/11/1437
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*wa yasan gobe?…..*
4⃣1⃣~4⃣2⃣
Kubra ta tsaya a bakin get din tana jinjina kai ita daya take sumbatu”kut lallai yarinyarnan dole ta matowa gayen nan shi yasa take ta faman rawar qafa?ai kuwa wlh baza’ayi bani ba”tayi qwafa sannan ta ja qafa tayi gaba,
samira ta kasa zaune ta kasa tsaye tasan halinshi sarai yarjejeniya kuma suka qulla tun kan aurensu kan shi baison wadannan kwashen qawayen nata gashi yau ta saba yarjejeniyar,tana shirin guduwa dakin gadonta ya damqota ya maidata kan kujera,ya kalleta sosai sannan ya jefo mata tambaya”ina kika samo waccar shedaniyar?”ta dake duk da tsoro ne fal cikin idanunta tace”qawata ce fa”ya gane mai takeson yi duniyancin nata data saba don haka ya shirya nuna mata nasa salon,don haka sai ya saketa daga riqon da yayi mata,ya saki fuskarsa ya daga kafadarsa hadi da watsa hannayensa na nuna alamun rashin damuwa da abu kana yace”good….verry good tunda qawarki ce kinga abun zai zo min da sauqi kenan ko?,dama gani nayi tamun inason aurenta aikinga zaman naku zai miki dadi tunda kun fuskanci juna, bata san sanda tayi zumbur ta miqe ba tana zazzare idanu ba baki na rawa tace”iyi…mme…me kace”ya daga mata gira sannan yace”abinda kunnen ki suka ji shi nace”ya juya yana niyyar barin dakin,hankalinta a tashe ta riqoshi kasancewar tasan halinshi *fada da cikawa*ya dubeta fuska a turbune yace”meye haka”don Allah ka rufamin asiri wlh bazan qara ba kasan wace kubra kuwa?”ya sake dage kafada hadi da cewa”ni ina ruwana da koma wace ce tunda kin kawo min ita har gida ni kuma na gani kuma ta yimin”ya zare hannunsa yayi ficewarsa,yana jiyo kururuwarta sai ya tuna haukan da tayi masa sanda zai dawo da salima,murmushi🙂 ya subuce masa ba tare da yayi niyya ba,yasan cewa shikenan yayi abinda zai rabasu kenan har abada ba tare da ya wahal da bakinsa ba,(samira irin mai rawar kan tara qawayace ko wa qawarta ce kare da doki ga son birga da burgesu ita dole sai an san mijinta wani ne,kaya komai tsadarsa suka gani a gunta tofa take zata basu ko nawa aka siya musu ko na aliyyun ne kuwa,indai zata burge tofa magana ta qare,gata da saurin daukar maganarsu don yadda take jin zancansu nata jin na mahifanta haka ne yayi silar lalacewarta,wannan ne yasa aliyu ya rabata da kowacce qawa amma da yake akwaita da kafiya taurin kai da naci sai ta sake wasu sababbi wadanda aliyyun bai sansu ba)
Kai tsaye ya wuce sashen sa tun daga falin ya ga canji komai fes ya koma hayyacinsa,daddadan qamshin girki ya cika falon nasa,bedroom ya zarce ya daura alwala ya nufi masallaci,kan ta kammala aikin ta gama gajiya tubus don kuwa aikine ya gama taruwa ya cakude ita kanta wani gun cike da qyanqyami ta daure ta gyarashi to ina kuma ga aliyyu
Take tasha alwashin zata yiwa tufkar hanci don badaqalar data tarar a bedroom din tasa ta isa,tuni ta gane cewa fushinta bashi da amfani don yadda komai ya qazance ta sani cewa da duniya zata gani ba iya su samira kawai za’a zaga ba harda ita,don ba wanda yasan mekw gudana tsakaninsu,ta sake gayawa zuciyarta lallai ibada tazo yi ibada kuma mai wahala wadda itace tafarkin shiga aljannarta kuma ta dade da sani aljanna bata samuwa daga zaune ba tare da ka tashi kayi aiki tuquru ba kuma dole ka ninka haqurinka(wannan sune daya daga cikin lafuzan umminsu garesu ko yaushe,uwa ta gari kenan)
Aliyu bai shigo ba har sai da yayi sallar isha’i don haka tuni ta gama komai har ta jere a dining taje tayi wankanta ta shirya tsaf cikin dark blue din shadda doguwar riga wadda aka mata surfani mai kyau tun daga sama har qasanta ,hankalinta dai na kan taliyarta don haka ta nufi table din saidai wayam don ko plate din babu,ta juya ta shiga kitchen acan ma a bude ta tadda tukunyar wayam
Ta san babu wanda ya cinye abincin sai shi don ba wanda ya shigo din,wata dariya😂 ta subuce mata data tuno yadda ya shigo dazun rai a hade yayi wani kicin kicin da shi😠 ashe harda yunwa itama ta taimaka wajen dinkewar fuskar tasa,ta hade kwanunkan ta dauraye ta maida su muhallinsu cikin ranta tana cewa”babu rabona nasha ice cream🍧
Tana bisa carfet ta bude babbar robar ice cream din tana diba a hankali tana kaiwa bakinta lumshe ido take don babu abinda take jin dadin shansa kamarshi din,wayarta ta duba jin qarar shigowar text _kizo ki bawa mutane abinci_”haka taga an saka,ta duba sunan Aliyyu salim maitama kamar yadda yayi mata serving din ta ranar da bata da lafiya”ta miqe hadi da dauke ragowar ice cream din ta maida cikin fridge ta koma daki ta fesa turarenta na blue lady ta hada da asaal brush perform ta nade kanta da da farin hijabi ta zari wayarta ta fito hadi da kulle gun ta,a hanya suka hadu da salima ta rako baquwa suna tsaye da alama magana suke ganin fitowarta duk sai sukayi shiru suka bita da kallo ganin haka yasa tace musu salamu alaikum sanda zata giftasun,baquwarce kawai ta iya amsawa itama can xiki kamar wadda akayiwa dole,suka ci gaba da kallon nata har ta shige bangaran aliyun
sai a sannan suka dauke idonsu baquwar ta saki ajiyar zuciya tace “tab gaskiya salima tahir na janjanta miki don wannan kam banga ta inda zaki ci nasara akanta ba,saidai ban sani ba ko ta bangaren farar fata”salila ta kai mata duka hadi da cewa”banason iskanci sadiya kota farar fatar ai sai na yi yaqi da itan ,dadin abun ma miskilancin mai gidan bai bari ki gane wa yafi so cikinku ai da tuni inaga na dade da kamuwa da ciwo yanda nake bala’in a son my dear💘 “ta fadi tana dafe qirjinta”(abunda bata sani ba aliyyun irin mazan nan ne wadanda ke nunawa mace qauna wadda kan bawa mutane mamaki har adinga zaton kunya ce basu da ita ko mallakesu akai sunyi sake da damar da ya basu tun farko har ta subuce musu)sadiya ta dafa kafadarta tace”to Allah ya bada sa’a don ko nice a matsayinki gaskiya bazanyi wasa da aliyyu ba”salima ta juya ido tace “ashe kin fara gano gaskiyata🙄 “
Sadiya ta dafa kadar salima tace to Allah ya bada sa’a don ko nice a matsayinki gaskiya bazanyi wasa da aliyyu ba”salima ta juya ido tace ashe dai kin fara gano gaskiya ta🙄”
Sanda ta shiga yana zaune gaban na’urar tafi da gidanka yana qarasa aikin sa da dazun yunwa ta hana shi yi,sallama tayi ya amsa kansa na kan allon computer din,kujerar dake gefansa ta samu ta zauna,kusan mintina sama da ashirin bai ce mata kanzil ba don haka itama ta bude wayarta ta soma register din watsapp saboda yanzu as journalists tana buqatar wadannan kafofin sadarwar,
duk da basu dameta ba don ba yadda farida batayi da ita tun a gida ta bude koda watsapp ne kawai ba amma taqi tafi ganewa karance karancen magazines da wasu rubuce rubucen
Cikin yan mintoci qalilan ta kammala da account dinta na watsapp ta soma qoqarin hada na facebook,falon yayi tsit kowa ya sanya na’ura a gaba,lokaci lokaci takan daga ido ta saci kallonsa,qayatacciyyar fuskarsa da hasken screen ya sake hasketa tayi fresh,ta zubawa hannayensa ido yadda yake sarrafa computer din cikin qwarewa da da gwanancewa typing yake cikin sauri tamkar shi ya qera computer din yasan madannin kowanne abu abun sai ya burgeta sosai
Wayarsa ta soma ringing ya dauke kai daga kallon fuskar computer din ya maidaa idonsa kan wayar ba tare da ya daga ba,baquwar numbace kuma bai dagawa,kira aka ci gabaa da yi akai akai har ya gaji ya danna ok ya dora ta bisa computer ya sanya ta a hands free
Muryar mace ce “hello ranka ya dade” “salamu alaikum wake magana?”ya fada hannayensa na saman laptop dinsa yana aikinsa,”daga daya bangaren aka sake maqe.murya“suna na nadiya ina kiranka ne daga unguwar rijiyar zaki kano”bai maida hankalinsa ba kan wannan yace”me kike nema?”aka danyi jim har yana shirin kashewa sannan akace “don Allah ka rufawa zuciyata asiri kada ka kashemin waya domin kashe wayar tamkar kashe ni ne”ya tsayar da abinda yake sannan yace “uhm go on” aka saki ajiyar zuciya sanna tace “maitama Allah ya jarabceni da tsananin qaunarka wadda tasa na kasa jure hakan cikin zuciyata har sai bakina ya furta maka,ina roqonka don Allah ka taimakeni ka so……..” “hey!”ya daka.mata tsawa “stop that,rubbish!”tsit tayi,ya ware idonsa kamar tana gabansa yace”ke baki da ajine irin na mata?” Shiru ba amsa don haka ya dora “let me tell you baki da shi,and inason gargadinki wannan ya zama na qarshe da zaki kira numberta,I hope kin fahimta ko”ya katse kiran hadi da jan tsaki,fadila tayi saurin dauke kanta lokacin da ya dago kansa taga tamkar ita zai kalla zuciyarta na wani irin bugu,kishi ya tokare mata qirji,ta lumshe ido bugun zuciyarta na qara sauri…….
Mrs muhammad dinku ce😘
[8/25, 3:44 PM] +234 812 673 9684: 5:55 pm 16/8/2016
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*wa yasan gobe?…*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*PART 2*
3⃣~4⃣
Kusan kimanin minti biyar idanun nata na lumshe ta kasa budesu saboda wani abu da takeji a jikinta wanda tasan baya rasa nasaba da tsan tsar kishi,ta sauke boyayyar ajiyar zuciya sannan ta bude idonta ta dora su bisa screen din wayarta tana ci gaba da qoqarin kammala bude account nata na Facebook duk da wani bari na zuciyarta na ci gaba da mintsininta,cikin zuciya lallai ta godema Allah da bai qaddara ta zubda ajinta ta bayyana abinda ke zuciyarta ba har ta kai aliyyu ya fuskanta bare ta samu nata kason cin zarafin kwatankwacin wannan wanda it may break her heart
Tabbas ta sake yarda cewa so masifa ne musamman son da hausawa kema laqabi da son maso wani,babu irin baiwar da tabbas bata da ita iya kyau Allah ya mallaka mata shi ilimi hankali da nutsuwa,tasha jin mata yan uwanta da yawa na yaba ta bare tarin maza dake kara kaina a kanta
Ta sake satar kallon nasa wannan karon maimakon ta tadda shi yana aiki kamar dazun yanzun takardun na watse ne a gabansa ya jingina kansa harda bayansa a jikin kujera dukkanin tafin hannunsa ya tallafe bayan kansa da su idanunsa na rufe,gashin idonsa yayi ma idon rumfa tamkar an jera su
“Bani abinci”ya fada idonsa na a rufen,ta miqe ta shirya masa komai still dai idanunsa na arufen har ta gama ta koma ta zauna,a hankali ya bude idonsa ya kalli warmers din”u mean ni zan zuba kenan da kaina?”😒 ta girgiza kai sannan ta taso ta zuba masa white rice ce da miyan kaza sai hadin coleslaw tana kammalawa ta miqe da niyyar fita “ina zaki je?”ya tambayeta cikin izza,ta kawar da kanta sannan tace “sashina zan koma” yaci gaba da cin abincinsa sai da ya mula don kansa sannan yace “ban baki izini ba”cike da haushi da takaicin irin mulkin da yake mata ta koma da baya ta zauna kanta a qas
Cin abincinsa yake with calmness ba abunda ya dameshi ya shanyata abunsa,har ya kammala bai dubi sashenta ba already ta soma gundura da zaman ga bacci ya soma mamayarta ga kuma fita office gobe early,sai da ya kammala duk abinda yake har ayyukan da yake shigarwa cikin laptop dinsa apple sannan ya tattare kayayyakinsa ya maida jakar laptop din yana shirin shiga bedroom dinsa yace da ita”ki hadomin coffee ki kawo min”
Kamar zata fashe da kuka☹ ta shiga kitchen cikin mintina biyar ta hada masa ta juye cikin cikin wani set din butar shayi irin na larabawa na silver da cups dinsu yake hade da tray
Hade da sallama ta shiga dakin yana cikin lallausan bargonsa cikin shirin bacci ba haske a dakin sai na fitilar gefan gado,yana receiving call har ta shigo ta isa bed side ta dora plate din daidai lokacin da ya kammala amsa wayar ya kasheta gaba daya ya cillata bayansa tana tsaye har ya kammala addu’o’in bacci sannan ya juya mata baya yana gyara kwanciyarsa hadi da jan bargonsa “kina iya tafiya” dama a gundire take Allah Allah take ta bar masa dakin ta juya ta fice abinta
Tana shiga bedroom dinta nightgown kawai ta sanya ta fada gadonta tana addu’o’in kadan kadan har ta gama,a hankali ta lumshe idonta tana da muradin yin bacci amma ina sai tunanin da akullum yake zame mata na qarshe a rayuwarta shi ya lullube qwaqwalwarta,duk yadda taso bacci yayi awon gaba da ita abun ya faskara har sai da ta dade tana ninqaya a duniyar qaunar aliyyu haidar sanan baccin yayi awon gaba da ita bacci ne mai cike da mafarke mafarken aliyyun
⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Cikin hukuncin ubangiji rayuwar ke tafiya da bawa wani lokaci ta zo maka uadda kake so kake tsammaninta wani lokacin kuma ka samu akasin haka yau fari kenan gobe tsumma jibi nasara gata asara duk cikin hukuncin ubangiji ne da yadda yaso rayuwar bayinsa ta kasance,to bawa mai cike da tauhidi da imani sai ya godewa masa don kamar yadda haka yake ga fadila,shekararta guda kenan cikin igiyar auren aliyyu,shekarar da ta ga abubuwa daban daban ta fuskar qalubale da nasara
Zamu iya cewa babu wani abu da ya sauya dangane da salon mu’amala da alaqa dake gudana tsakaninta da shi baya ga wadda muka riga muka sani,nasara daya ce zata iya daga hannu🙋🏻 ta fadeta cike da alfahari shine duk cikin samira ko salima babu wadda take iya sarrafawa aliyyu girki da tsaftar muhallinsa kamar ita
Abunda suka fi qwarewa ciki sune kowacce ta fito tana tunqaho da hura hancin Aliyyu yafi sonta akan sauran ‘yan uwanta,takan kau da kai cike da yakanah tayi kamar bata san abinda suke yi ba,wani lokacin kuma sukan bata dariya har ma ta murmusa takan daukesu ne a matsayin wadanda basu san mai ya kamacesu ba duk da kuwa duk sun bata wasu shekaru sun kuma girmemata sosai tana ganin tutiya bata kamacesu ba a irin wannan rayuwa da suke,ta sanu da gayya suke mata wani abun ganin cewa bata taba daga ido ta kallesu ba bare suyi ‘yar tankiya
So suke ta zamo daya daga cikinsu domin kuwa fada tsakaninsu sun koma tamkar ‘ya’yam tumaki har bangarenta tana jiyo hayaniyarsu,sukan ji kasiririt ne idan aliyu yana gida don ko giyar wake suka sha a yanzun basu fada gabansa tun tuni yayima tufkar hanci ya kuma tauna tsakuwa don aya taji tsoro ta kuma ji din saidai su yita ‘yan habaice habaice wadanda shi da yake namiji me bai ma fuskantar me suke
Ta riga tuntuni ta saddaqar da cewa soyayayyar aliyyu wani gine ne daga Allah cikin zuciyarta,tayi imani koda bai sonta ba koma zai sota din ba kamar yadda yayi mata tunqaho Allah bazai taba wofintar da ita darajar biyayyar aure da take hidima a gareshi da kayutata gami da girmama buqatunsa,duk da babu wani sauqi da take ganowa a tattare da aliyyun amma har kulluma tana bawa kanta confidence kan hidimar da take masa especially a duk sanda haduwa ta hadasu da uncle abba momi abbanta ko umminta taga yadda suke nuna jin dadinsu har yau da wannan aure nata sai taga zata iya ci gaba da faranta ransu indai hakane
Saidai abinda bata sani ba shi kansa yakan samu kansa cikin nutsuwa a duk ranakun da suka zamo nata ne ko banza ya san yana sakewa yaci abincinsa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali kuma cike da gamsashshen dan dano irin wanda yake so duk da babu ruwanshi da ita,some times ma kafin ya dawo ta hada duka abinda yake so ta bar masa bangaren,mutum ne aliyyu maciyin abinci bao wasa da cikinsa ko kadan hakanan halittarsa take,duk qwaqwar mutum bai isa yayi indication wasu sign da zai nuna yana jin dadin hidimarta ba
Mrs muhammad dinku ce😘😘😘
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[8/25, 3:45 PM] +234 812 673 9684: 5:08 pm 20/08/2016
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?..*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*PART 2*
5⃣~6⃣
Cikin watannin da basu gaza biyar zuwa shida ba fadila ta samu gagarumar nasara ta bangaren aikinta,nasarar da bata taba tsammanin zata sameta in a few months ba,ta soma aikine cikin sa’a,farin jini sosai take da shi,sunanta ya fara fantsama cikin al’umma shirye shiryenta sun samu karbuwa matuqa da gaske,ki ina ka zaga zancan matashiyar ‘yar jarida fadila Abbas wakili ake,ita kanta tana mamaki with her few age ta samu daukaka haka,saidai da yake mai hankali ce takan godewa Allah domin tasan babu wanda ya isa yayi mata haka sai Allah,hakan yasa ta sake daura damarar riqo da aikinta cikin qwazo amana da kuma gaskiya da kuma manufa kyakkyawa da zata kawo gyara da ci gaban al’ummarta,bata mantawa da ya ahmad da abbanta wadanda su suka jagoranci samuwar ci gaban nata
Bayan ta kammala duk wasu ayyukanta kamar yadda ta saba,ta shirya masa komai hatta da tissue bata barta ba,sauri take ta yi ta fice daga gun kafin dawowar tasa,saidai kash bata ci nasarar hakan ba don kuwa a bakin qofa suka yi kacibus kadan ne ya rage basu bige juna ba,da sauri taja da baya tana shaqar numfashin ta dake gudu sakamakon tsoratar da tayi,qasa tayi da kanta tana murza tafin hannunta gami da cewa “sannu da zuwa”
Kusan minti biyu taji shiru shi bai wuce ba ba kuma alamun juyawa yayi,ita kuma ya bashi dama ne ya fara wucewa duk da sauri da take ta koma bagarenta ta cire pad din jikinta ta sauya wata,ta dago kanta don taga me yakeyi ne haka yana tsaye hankalinsa kwance kamar bai tsarawa kowa hanya ba don bashi da wani alamu na matsawa hasalima tie dinsa da coart yake cirewa a nutse
Ganin haka yasa ta raba gefansa don ta shige ashe bata sani ba ya sanya mata qafarsa dake saye cikin sau ciki👞sam bata lura ba don hankalinta yayi gaba,luuu tayi baya ya goce sai kuwa ta bugu da qofan falon ,cikin azabar radadi ta dafe gun ta dago a hankali ta kalleshi sai taga tamkar ma baisan mai yayi ba agogon hannunsa na gucci yake cirewa,malolon takaici ya kama mata maqogaro tuni kuka ya kufce mata tasa kai tanashirin bar masa gun tana dafe da goshinta
Ji tayi ya jawota baya ta dawo tayi kamar zata sake faduwa Allah ya taimaketa ta tsaya da qafafunta bayan taga tagar da tayi “sama fa qasa ya kalleta sannan yace “😠baki da kunya ko?,ni zaki buge ki wuce kenan?”tafin hannunta tasa ta kate fuskarta tana ci gaba fa kukanta shi kuwa ya zuba mata ido ba tare da ya sake cewa komai ba, sai da ya gama ikon nasa don kansa ya kauce tare da wucewa ya bar gurin
Da gudu ta fice tana ci gaba da kukan ta wuce bangarenta,dispenser ta kunna tayi heating gurin sannan ta koma bisa gadonta ta kwanta tana maida ajiyar zuciya,me ta masa?ma ta tsare masa banda tsabar cin zali kawai don ta rabe zata wuce sai ya mata wannan muguntar?” Ta danyi qwafa kadan a ranta tana ayyana zata rama
⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Su biyar ne zaune cikin office din fadilan sai fauziyya fa’iza aisha da halima dukkaninsu abokan aikinta ne matasa ne son saidai duk sun girmemata aqalla zasu bata shekaru uku zuwa hudu,amma nutsuwa da kaifin hankalin fadila yasa ta saje cikinsu suna jin dadin zama da ita sosai duk da miskilace saidai akwai karamci da mutunta mutum
Hira suke gaman da zamantakewar aure irin hirarmi dai mata da aka sani wadda matuqar mayan aure suka wuce biyu aka hadu sai an yita,hira ce ta qaruwa ba banzar hira ba wadda bata kamata ba,duk da haka fadila na gefe don bata da abun fadan saidai jifa jifa takan ce wani abu
Hira tayi nisa fa’iza ke basu labarin wata maqociyar yayarta ‘yaf nijar dake saida magungunan mata masu kyau na gargajiya wadanda basu cutarwa,dukkansu suka ce ayi kiran matar suna so fadila kawai ta rage,fa’iza ta kalleta”ke ba ki siya fadila wlh maau kyau ne”murmushi tayi tana neman qaryar da zata gilla musu,don ko ta siya me zata yi da su,ta kalli fa’iza “to a hado da ni ga nawa kudin”ta nude zif din jakarta ta fito da kudin,fa’izan ta kuma cewa idan ma bakiso akwai wani hadin tutare mai tada sha’awar mai gida sai a kawo miki shi”cikin basarwa fadila tace”a hadomin duka kawai”(kaji fa mai karatu kamar gasken tana da buqatarsun 😜😜)
Take fa’iza ta kirata ta sanar mata,ta kaahe wayar tana dubansu tace kun taki sa’a don gata nan ma anan kusa don tana ja’en,cikin minti talatin sai gata kowacce ta karbi nata ta sanya ajaka
Qarfe biyar ta soma hada kayayyakinta tana sallama da su zata wuce gida don ta kammala aikinta ,wayarta dake aljihun bayan jakarta ta dauki qara alamun ana nemanta *sister ta* ta gani bisa screen din hakan na nufin farida ke kiranta,da sauri ta daga hadi da yin sallama,”sister ki taho kiga baby girl mai kama da ke kamar copy naki akayi na haihu yanzu haka ina gida”wani tsalle fadila tayi hadi da qaramin ihun farinciki sam ta mance a office take ba a gida ba sai da taga su fauziyya sun taso suna tambayarta mai ya faru sannan ta tuna ta maida wayar tana dariya cikin doki tace junior sister na ce ta haihu wlh”suka mata barka hade da dariya suna cewa saura ke kenan,murmushi 😊kawai ta musu ta saba jakarta tana cewa”Allah ya bamu alkhairi”ta kama kumatun yarinyar fauziyya tana mata wasa har ta fice yarinyar nata kuwa bangala mata dariya don fadila akwai son yara yarinyar ta soma sabo da ita yauma sa’a akaci bata sa kuka ba da zata tafin
Da dokinta ta shiga motarta da niyyar wucewa gidan farida kai tsaye,har ta kunna motar ta tuna cewa sai fa ta sanar da aliyyu,take
murnarta ta ragu tamkar an zare mata laka ta kashe motar,ta jawo hand bag dinya dake kusa da ita ta ciro wayarta ta bude sannan soma searching number’n sa cikin contact dinta wadda yayi mata serving da kansa ranar da bata da lafiya,tayi attempting din kiransa yafi sau goma ta kasa,sai ta fara dialing sai ta katse da kanta,bata san answer da kuma result da zata samu ba
Daga qarshe taga hakan bazaiyi mata amfani ba sai kawai tayi shahada ta kira din,yadda wayar ke qara yin din din haka zuciyarta ke bugu,idanunta a rufe gam tana jiran wayar….
Mrs muhammad dinku ce👑👑👑
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*PART 2*
7⃣~~8⃣
“Assalamu alaikum” dakakkiyar muryarsa ta doki dodon kunnen fadila,numfashinta ya dan dakata na wucin gadi,komai da ya danganci aliyyi jinsa yake har cikin jininta da bargo komai qanqantarsa kuwa,”hello waye ne?” Ya sake maimaitawa, “idan mai kira baida abun fada zanyi rejecting I have a lot to do”dadi muryar tasa ke mata har can qasan zuciyarta,zata so ta dawwama tana sauraren muryar idan da halin hakan,din din din da taji sau uku shi ya tabbatar mata ya katse wayar kamar yadda ya fada tun farko,ta saki wani dan murmushi da ya tsaya a kuncinta tana kallon fuskar wayar tata,tazarar minti biyar ta bayar sannan ta redial din number tasa
Tana daf da tsinkewa ya daga wannan karon ita ta fara yin sallamar ,yayi dan dum sannan ya masa a daqile sanan ya dora da “who’s on d line?”cikin in ina ta soma magana don gaba daya dakiyarsa ta rudata “nice” “kewa”ya maida mata da tambaya,”fad…fadila”ya sake shiru na yan sakanni har tana tsammanin ko baya kan layi ta duba wayar sai ta ga yana nan
“What’s going on?”ya sake tambaya,wani abu ya dan taba ranta da gaske bai ganeta ba har sai da yayi analysing a qwaqwalwarsa,”sister farida ce ta haihu” “uhm labari kike ban kenan?”ya fadi cikin watsar da muhimmancin batun a gunta,tambayar ta quleta hakan yasa tayi shiru,”me kike buqata ne ina fa da aikin yi”ta daure tace “baby nake son inje na gani” “ban amince ba”ya fadi kansa tsaye,din din ya katse wayar,wani hawayen takaici ne ya sulmiyo mata,tayi wurgi da wayar kujerar gefenta,cikin takaici ta figi motar sai gida
Danja na tsaida su tana ganin wani wani saurayi dake gefan tata motar yadda ya zuba mata ido da alama yana mamakin me ya sanyata kuka ne,ta kawar da kanta gefe cikin zuciyarta tana ayyana in banda babu kyau fita babu izini tabbas da sai tayi wucewarta gidan farida saidai aliyyu yayi tsirenta,ta share hawayen sanda danja ta sake su ta sake figar motar,tana kallon yadda saurayin ke sa mata signa yana son tsaidata tayi banza da shi ta qarawa motarta speed,ita kanta bata san tayi gudu haka ba sai da ta iso gida agogon wayarta ya harba taga yan taqitattun mintocin da suka kawo ta gida,tana qoqarin shiga gidanne bayan mai jire bakin qaton get din gidan ya dage mata qofa ta soma shiga taji wani horn din,ta glass ta hangota motar samira ce wadda take cin ubanta da hawa ta tabbatar da motar mutum ce da tuni ta dade da guduwa,ba samiran ba hatta qawayenta sai suzo su ari motar su wuni sur suna cin ubanta ko a daddoke mata ita su kuma dawo su yasar mata ita ce mai kudin banza ta gyaro ta zuba musu mai gobe su dawo su sake ara ita kuma ba lissafi ta basu saboda tsabar neman suna irin na samira,shi uasa tayi nacin aliyyu ya canza mata mota qememe yayi buris da ita don yana sane da abinda takewa tatan
Mrs muhammad ce
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
12:36 pm 22/8/2016
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?..*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*PART 2*
9⃣~~1⃣0⃣
Ta ajjiye motar a parking space ta kashe ta tana mai dauke idanunta daga kansu samira zuciyarta na tur da irin halayen mutanen da samiran ke mu’amala da su,hakanan ko yaushe zaka gansu cikin shiga ta banza da rashin da’a,yanzun ma qawayenta ne su uki ta dauko cikin motar kowacce kuma cikin shigar tasu dai ta dabi’ar da suka dorama kansu ,tana jin shewarsu sanda take rufe motarta kasancewar suna bayanta ne tsaye jikin motar samiran su basu shige ba hakanan basu komacikin cikin motar ba,sun saba yi mata haka tun ba yau ba kula su ne sam bata taba yi ba don bata kallonsu ma a matsayin cikakkun masu hankali,tana ganin idan ya kula su ma tamakar ta basu wata martaba da daraja ne,kallon tsiya ma basu isheta ba bare su sa ran wataran zasu samu na arziqi bare fadilan dama miskilar kanta ce sai ka gama cin kashinka a gabanta idan bata ga dama ba quda bazata kore maka ba
Kamar ko yaushe yauma har ta bawa banza ajiyarsu tayi gaba abinta maganar da ta jiyo suna fada ita ta sanyata dawowa da baya ta tabbatar ya zama dole yau ta yiwa tufkar hanci bare yadda take cikin takaicin hanata zuwa gidan farida da aliyyu yayi shewa suka yi sanda take yin gaban sannan daya daga cikinsu tace”badi’a (sunan daya daga cikinsu ta kama)saiki dinga fakewa da fita aiki ana yawo a kwararo
Da baya ta dawo sannan ta fuskancesu,dubansu tayi daya bayan daya up to down ta saki wata ‘yar siririyar dariya tace “😏 ai karuwanci iyawa ne kuma karba karba ce,💁🏽wata hajar sai ta qaraci zamanta a kasuwa tasha qura tayi futu futu kullum kuma sai an fito da ita an kasa amma sai kiga ko kallonta al’umma basuyi bare su baqaci siya,kinga kenan inda wani yayi rawa aka bashi kudi wani idan yaje yayi dan banzan duka zaici
Ta sake watsa musu kallon raini sannan ta dora”ku ba abokan yina bane don ban hada sabga da ku ba wannan…..ta nuna samira da key din mota dake hannunta “itace abokiyar yina,ita din ma zata gaya muku inuwarta bata isheni kallo ba bare zahirinta,but…. well zan baku shawara guda daya hade da gargadi mai kama da jan kunne,shawara ta farko itace ku rufawa kanku asiri ku samu ku raba jikinku a dakin aure kafin a rasa mai kwasar ragowarku……😂🙊 au am sorry na manta yanzun ma fa hakance ta faru da ku fa shi yasa kuke gararamba da yawon kwadayi da maula agidajen matan wasu
And gargadina shine kada wadda👉 ta sake bude rubabban bakinta da niyyar shiga gonata don nikam duk cikinku babu wadda tayi isar da zan shiga gonarta,saboda haka nima akiyaye shiga tawa gonar👉”ta kama kunnenta daya da hannunta tace”idan kunne yaji……gangar jiki ta tsira”ta saki hannunta ta juya da niyyar shigewa dukkansu sunyi mutuwar tsaye don nasu taba tsammanin ta iya magana haka ba a yadda samira ke basu labarinta,samiran ce tayi yunqurin nuna jarumtarsu tasha gabanta ta kama qugu tana cewa”ke qaramar ‘yar iska mu kike nufin zakiyi wa rashin mutumci?”
Murmushi fadila tayi tace”🤗 a’ah sanin kanki ne fa ni ban iya hayagaga ba ke zaki fara baiwa wanda bai sani ba labari ,to kuwa akan wadancan👈🏼 shashashan bazan fara ba”ta gewayeta tayi wucewarta,tana jiyosu suna ci gaba da kuri da cika baki kala kala akanta har suka wuce sashen samira,cikin ranta take fadi Allah ya bawa daya daga cikinsu sa’a tace zata biyota taga yadda ake rashin albarka
Wanka tayi don taji sanyin zuciyarta tuni ta watsar da batun su samira don basu gabanta hasalima bata daukesu wani abu ba don tasan baya ga tsabar jahilci dake damunsu rashin tarbiyya na bibiyar rayuwarsu,tana mamakin tsarin rayiwa irin tasu sam basu damuwa da yanayin da rayuwarsu ke gudana,falo ta dawo ta hada yoghurt mai sanyi da fura ta dama ta koma saman kujera tana diba da cokali a hankali tana sha zuciyarta sam bata gidan,kira ne na anty hafiza ya soma shigowa wayarta tana neman farida ne tayi ta kiran wayarta busy shine ta kira ko suna tare ta bawa faridan,nan da nan ta tabo mata miki basu gama sallama ba ta kashe wayar don bata son taji kukan da ya qwace mata,kamar kuwa hadin baki yan uwa ke kiranta suna cewa ita zasu yiwa barka itace uwar ‘ya,hakan ya raunana zuciyarta sosai tasha kuka,sister faridanta guda amma wai a hanata ganin ‘yarsu?
Har magariba jikinta amace yake,sai sannan ta tuna bata kira umminta ta mata barka ba,jin muryar ummin bayan ta daga sai ya karyar mata da zuciya kuka ta saki,a tsorace ummin tace “meye haka lafiyarki kuwa?”cikin kukan tace “ummi ya hanani zuwa ya hana ni inje inga baby ummi”ummin ta saki ajiyar zuciya sannan ta ja tsaki”wlh harkin tayarmin da hankali na zaci wani abune ya faru ko ya sameki?” Ta sake marairaicewa cikin muryar kuka tace “ummi wani abune mana sister farida fa ummi” “to sai me idan baki je din ba?,idan kinje ma me zakiyi mata iyakaci kije kuyi ta surutu,tunda Allah yasa an sauka lpy bashi kenan ba abunda dama ake buqata kenan”ta sake sakin kuka tace “ummi ki masa magana don Allah idan ba haka ba baza ni ba”kama haba ummin tayi kamar fadilan na gabanta tace”🤔lallai bansan haryau quruciya na damunki ba fadila,to ba da ni ba wannan shiriritar,bana som sakarci ki maida hankalinki fadila kada na soma jin wani abu kuna jina ko?” A sanyaye ta gyada kai ta sani ummin bazata so ace bata je ba amma bazata taba bata goyon baya ba,halin ummimsu ne a gidan aure maca ce mai tsananin biyayya ga abbansu ko layi uaja yace kada ta tsallake to insha Allahu ba zata tsallake din ba hakanan kaf yaran babu wanda zata bari ya tsallaka hakan ne yasa har yau har gobe har ma jibi inji shi abban nasu yake alfahari da kuma ji da ita
Ta saki ajiyar zuciya bayan ta kashe wayar tana jan majina hadi da son maida kukan ta,alwala ta daura tayi sallar magariba ta zauna kan sallayar tana jiran a kira isha,hakanan fadila take tana da kwadayin wannan garabasa da ake samu ga duk wanda ya idar da salla bai kuma tashi daga gurin ba,jira ne baifi na awa daya da rabi ba aka tada isha’i ta gabatar da ita duka harda shafa’i da wutiri sanann ta sake zama ta karanta subhanallahi wa bi hamdihi subhanallahil azim,don kanta ta gaji da zaman ta ninke abun sallar ta maida shi muhallinsa ta baro dakin sa hijabinta a jiki don dumin cikin hijabin ya mata dadi
Cartoon ta maida tana kallo kan tashar m.b.c 3,lokaci lokaci tana sakin ajiyar zuciya saboda kukan da tayi,sannu a ahankali ta soma jiyo qamshinsa ,ta daga fararen idanunta ta maida su bakin qofar shigowa falon,cikin nutsuwa da sallama ya shigo yana sanye da jacket black blue sun haska farar fatarsa,sunyi amsarsa matuqa da gaske adorable structure dinsa ta fito sosai,sassanyan kyawunsa din nan ya bayyana cikin kamilalliyar tafiyarsa ya qaraso falon hannayensa sarqe a qirjinsa,can qasan maqoshinta ta amsa sallamar carelessness ya samu hannun daya daga cikin kujerun ya zauna ba tare da ya dubeta ba
With bounded face yace”ki fito na miqaki kiga baby”tamkar tayi banza da shi ko tace ta fasa sai taga idan ma tayi hakan ai kanta ta yimawa ba wani ba don shi kam bashi da asara,ta miqe kamar marar laka ta shige bedroom dinta tana qunquni qasa qasa”sai an ma gama qonawa mutum rai sannan za’a wani tasa shi a gaba akaishi kamar wani dan qanqanin yaro” “idan baki zuwa ba saiki zauna ba ke ya shafa”ya fada a tsawace,baki ta rufe da sauri ta qarasa shigewa bedroom din don batayi tsammanin ya ji ba,lallai shi kuwa wane irin kaifin ji gareshi take mamaki cikin zuciyarta
*NOTE*: assalamu alaikum masoya littafina saqonninku nata isheni da maganganunku game da littafina,duk da cewa na sani nayi muku bayani tun a farko na yadda rubutun zaici gaba da kasancewa sakamakon shirin fitar da shi kasuwa,na dauka tuni mun wuce gun saboda banyi zaton zanci gaba da baku shi littafin ta watsapp bama amma yanayin yadda kuke nuna qauna gameda da shi din yasa naci gaba da rubuta mukun duk da na rage yawansa kamar yadda na fada,
To amma naga rashin fahimta na son shiga ciki,na farko har ga Allah yadda wasunku ke min bana jin dadi yana bata zuciyata,saboda bani da wani uziri da zai taso min a matsayina na yar adam a gunsu abunda kullum suke buqata shine nayi musu kawai typing na turo musu,sannan wasu babu yabawa saidai qorafi da zarar sun gama karanta wanda na samu na turo,hakan da suke yana kashemin gwiwa ne,maimakon suyi abinda zai qarfafa min gwiwa ko saboda gaba kada ku manta hannu ne keyi ba fada muke wayar na rubuta mana,kuma yau da gobe ai sai Allah,ni ‘yar adam ce gsky da bana son abinda zai dameni ko ya samun damuwa a zuciyata nakan haqura da abubuwa da dama matuqar zasu jawomin damuwa,don Allah ina roqonki ku tsaya kuyi duba na fahimta game da ni,ni ba budurwa bace matar aure ce ku duba kuga yanayin hidimomin gida na kullum dake kan matar aure baya ga wadanda ka iya taso mata wadanda bata tsara da su ba a rana,ku dinga adalci kuna hukunci na gaskiya,mu fahimci juna don Allah wannan shi zaisa ni daku muci gaba da jin dadin alaqar dake tsakaninmu,wlh akwai abubuwa masu yawa da muhimmanci a rayuwata da nake yi kulluma da kafin fara muku rubutu amma a yanzu sun gagareni yi saboda rubutunku,na sani harka ta mutane sai kayi haquri tunda yadda muka banbanta a halitta haka Allah s.w.a ya ban banta mu a halaye da dabi’u,na gode Allah yasa mu dace👏🏻👏🏻
Na biyu kuma masu ganin abunda aliyyu yake yayi yawa kada kusa gaggawa a lamarinku kuma kada ku manta shi haquri shine jagoran kafatanin lamuran mu na duniya bare haquri ga ‘ya mace kuma acikin gidan aurenta hanyar shiga aljannarta riba ce ba kadan ba,ina so ne yan uwana mata muyi koyi da halinta koda cewa ba irin auren ta kikayi ba amma nasan baza’a rasa matsala daya ko biyu da kike iya fuskanta ba daga mai gida wadda shigen halin da aliyyu ya taba nunawa fadila ne to ga yadda ta shanyeta ga kuma ribar da ta samu,na godewa masoyana gana daya ,Allah yayi mana sakamako agidan aljanna ya hadamu dukkanmu a cikinta in kuma ci gaba da zama marubuciyarku ta gidan aljanna 😜😜😀😀👏🏻
Mrs muhammad din[truncated by WhatsApp]
4:50 pm 23/8/2016
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?..*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*part 2*
1⃣1⃣&1⃣2⃣
Powder kawai ta shafa a fuskarta ta shafawa kyawawan labbanta lip glosses,atamfa ta zaro cikin kayan nata dinkin doguwar riga ne mai umbrella ta bude sosai an mata dogon hannu simple style ne,ta ware dan madaidaicin mayafinta ta yafa shi har saman kanta kamar yadda ta saba yafenta sannan ta fesa turare ta fito
Yana tsaye a wajen motar yana amsar calling yayin da salima ke tsaye kusa da shi hannunta harde a qirjinta tayi kicin kicin da fusaka,sallama fadila tayi mata sai taga ta dauke kai don haka sai ta ja tunga itama tayi banza da ita,ya gama amsar kiran ya kashe wayar hannunsa na kan mabudin motar salima ta kalleshi tace”please dear”kai ya gyada yana cewa”dont mind” ya bude gidan gaba kusa da kujerar mai tuqi ya zauna ta bude baya itama ta shige,nasiru ya gaida ta cikin girmamawa a mutunce ta amsa sannan ya tada motar suka fice
Tafiya ce kamar ta kurame sai ka rantse bata cikin motar sai shi da nasirunne ke hira jefi jefi galibi ma bai wuce zancan kasuwa,idanunta na kan titi yayin da zuciyarta ta lula duniyar tunani
A bakin get suka dakata bayan mai gadin ya dage masu get aliyyu yasa nasiru yayi masa magana ya rufe ba shigowa za suyi ba,fadila ta tabe baki cikin ranta tana gulmar aliyyun,nasiru ya gyara parking din sannan ya fice daga cikin motar,fadila ta sa hannunta a kan mabudi zata fice “twenty minutes”haka ya fada cikin carelessness,ba abunda tace da shi tayi ficewarta “ko baka gaya min ba ai na sani uban masu tsari da qa’ida na duniya😙”tayi zancan cikin zuciyarta
Da yake takwas na dare ma ta dan gota gidan ya samu sararawa daga cincirundon ‘yan barka mutum hudu ta tarar Amina da mariya qannan mubarak ne sai maqociyarta guda daya sai kuma wata dattijuwa inna jummai wadda mahaifiyar mubarak ta kawo mata ita saboda kula da mai jegon da kuma jaririyar,alokacin da ta shiga ma tana kitchen tana kwashe tuwon da ta yiwa faridan,fadila nata qyalqyala dariya ganin inna jummai nata loda tuwon a flask tana ce mata”inna zanso naga dambarwar ku kam da farida don ba abincin da taqi jini irin tuwo,dama dai ni kika baiwa”innan da yake macace mai kirki da saurin sabo da jama’a tace”ai duk qinta kuwa da tuwo yanzu ya zama abokinta dole ta cishi tunda jego ya zo”
Tayi sallama ta shiga falon faridan dukkaninsu suka amsa mata cikin fara’a suna dariyar hirar fadilan da inna jummai,farida kam ture kayan jarirai dake gefanta take tana cewa sister taho nan daya hannun nata kuma cup ne cike da tea tana sha sai hada gumi take inna kuma taqi ma a kunna fanka bare a.c saboda wai jego faridan zatayi irin na da,fadilan ta qaraso tana cewa “🤔sister farida mai tsokana da yawon gidan qawaye yau gata dq baby” dariya ta basu dukkaninsu harda faridan,idanu fadila ta baza tana neman baby tace nifa baku nazo gani ba wlh ina ‘yata ku bani ita naji duminta”yarinyar na hannun maqociyar ta ta nannade cikin farin shawul mai taushi ta miqe tana miqawa fadila ita hadi da yi misu sallama ta ajjiyewa faridan 1000 kudin barka ta mata godiya ita kuma ta fice
Ta kammala shanye tea din tas ta dire cup din tana kallon fadila tace “sister da fa har nayi fushi kece ta farko da kika fara sanin haihuwarnan baya ga abbanta amma sai yanzu zaki zo mana tun dazu baby ke son ganin mummynta bata zoba sai da aka rigata gane mata ita” “hmmm lallai yarinyarnan kukan dadi fa kike da yaya yanzun ma ya barni tare ma fa muke”cikin zolaya wadda attitude din farida ne tun usulinta tace “wow kice har an fara boyonki lallai soyayya ruwan zuma”fadila ta harareta tace “wlh badan kin mun abun kaiba kin bani baby mai kama da ni ba da sai na bubbuge bakinki”su amina suka qyalqyale da dariya sannan suka miqe suka ce bari dai mu baku guri kada a buge mana anti a gabammu”dariyar suka bawa fadila su kuma suka fice kitchen gun inna jummai
Fadila ta sake zubawa yarinyar ido tubarkallah masha Allah qatotuwa da ita lallai kam wannan photo copy dinsu ce ta kalli farida tace sister sannu”farida ta ya da kai gefe tana tuno wuyar da ta sha”hmmm ke dai bari sister ansha gwagwarmaya ni kam dan ba qara”fadila ta sake rungume yarinyar a qirjinta tana sake jin qaunarta na shigarta bata qi ace tata bace,ta saki dariya tace “yanzun fa aka fara farida me akai da maza daga ihu daya sai kuma murya ta dashe?😜”ta qarashe ta sigar tsokana yau dai ta maida raddin tarin tsokana irin na farida da take mata ko yaushe,ko da can dama fadila Allah ya zuba mata son yara,sanda suka tashi muhammad ne kawai yaro a gidansu to har gidan maqofta take shiga dauko yara duk da yanayin unguwarsu irin unguwan nin nan ne da ba ruwa na da kai kowa na qulle shi da ahalinsa cikin gida amma haka fadila ke shiga ta taho da su,miskila ce ako ina magana bata dada ta da qasa ba amma banda kan yara hakanan zaka ga ta sasu a gaba suna ta wasansu,farida kam dama idan taga dama idan suka zo neman anty fadila sai ta korasu tace bata nan zasu zo su dameta ne
Farida ta girgiza kai da sauri tana juya ido tace “kai sister is hardly in sake ko zan qara sai after five to ten years,nikam na barmiki ki taba kiji”dariya ma ta bata ganin duk yadda tayi laushi duk rashin tsoro da dakiya irin na farida,murmushi fadila tayi tana ci gaba da kallon yarinyar tayi kissing dinta agoshi,”ina aliyyu ne sister?”🙄af yana waje ” farida ta miqe daga kashingidar da tayi tace “kada dai kice mun kuna tare yaushe ya aliyyu boss ya fara kai matarsa unguwa”fadila tace”saboda ya bata min ya fara ta kaina yau kina gani fa kamar gidqn nan yace min wai twenty minutes?”farida tace “wlh am serious ya aliyyu ko salima matarsa ta farko bai taba kaita wata unguwa ba idan ba monthly shopping naku ba(farida ta fi fadila sanin halinsa ne kasancewar tq fita shiga jama’a hakanan ta fita zuwa gidan uncle abba)kuma shine kika barshi a waje ga sitting room nan”fadila ta tabe baki tace “oho masa har get malam salisu ya bude masa yace a maida arufe ba shigowa za su yi ba” “gashi mubarak yanzu ya fita maida hajiyarshi gida da ya shigo da shi”farida ta fada tana lallatsa wayarta,”zancan kike so ki bar mubarak kada ki taso shi idan da rabon zasu hadu zasu hadun don ko mubarak ya zo idan bai ra’ayi ba bazai shigo din ba”
Minti goma sha biyar ta shude suna ta hirarsu farida na cin tuwonta a sake kasancewar su mariya sun bar masu dakin,dahiru yaron dake wa farida aike aike ne ya shigo karbar abincinsa bayan ya miqawa inna jummai kwanon ya tsaya bakim falon faridan yace”anty wai baquwa ta fito za su tafi”fadila ta bata rai don tasan aliyyu ne yayi aiken kuma aqa’ida tana da sauran minti biyar
Ranta a bace bayan ta bude camera din wayarta ta yiwa baby pic ta sake sumbatarta ta ajjiyeta gefan faridan ta dubeta tace sister zan dawo insha Allah me kikeson na kawo miki”murmushi tayi tace”sister fadila nayi missing din wainar shinkafarkin nan da kike mawa dady,idan zan sameta inaso”dariya fadilan tayi saboda ta tuna mata lokacin da suna gidan idan tayi insha Allahu kan ta gama shiryawa Abban a warmer taci na ci kuma ta bi ta har falon abban suci tare da shi tana hara rarta tana komai amma sai tayi biris,”insha Allah kamar kinci waina ta kin gama”sukayi sallama tamkar kada su rabu
Tana fita taga motar mubarak fake kusa da tasu shi dinne kuwa da alam yanzun ya iso don lokacin suke gaisawa da aliyyun ta qaraso suka gaisa ya juya yayi cikin gida yana cewa bari ya dauko ma aliyyun babyn ,hannu biyu yasa ya dauki babin mubarak na gyara masa riqon don da gani bai iya ba,ya riqe ta sosai yana kallinta hadi da fadin”masha Allahu la quwwata illa billah”(yan uwa gaka annabi ya horemu da fada a duk lokacin da muka ga wani abu da ya qayatar da mu to ko kana da kambun baka bazai kama abun ba domin wasu ma auna da shi amma basu san suna da shi din ba,sai kaga abu kayita kodashi ba tare da ka fadi hakan ba daga qarshe sai wani ibtila’i ya saukarwa abun ya lalace don Allah mu kula da wannan)
Fadila na satar kallonsa kadan kadan tana kallon yadda ya zubawa yarinyar ido ya lumshe idanunsa daga baya ya budesu ya sumbaci goshin yarinyar sannan ya miqawa mubarak ita yana sake cewa Allah yayi mata albarka,ya amsheta sukai sallama ya shige gida da babyn
Aliyyu ya yafito qasimu dake fitowa fitowa daga gidan hannunsa da robar abinci qasimu ya qaraso hadi da rusunawa aliyyu ya amshi bandir din kudin dake hannun nasiru ya miqawa qasimu yace ka kaiwa maman baby ya zaro 1000 daga aljuhun trouser dinsa ya bashi ya shige motar yabar qasimu nata zuba godiya yare da komawa cikin gidan don sada saqon aliyyu ya bawa nasiru umarni ya tada motar suka bar layin fadila nata satar kallonsa don kiwa dubu dari ce ya bayar a kaiwa babyn
Mrs muhammad ce 👑
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
2:08 pm. 24/08/2016
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
WA YASAN GOBE?..
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by masoyiyar buk din wayasan gone..*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*Part 2*
1⃣3⃣&1⃣4⃣
Fadila tacigaba da sake2 azuciyarta bata ankaraba taji ana bude get tana dago kaitaga harsun iso gida ashe,parking space ya nufa ya kashe motar,fadila dakekokarin bude motar setaji ya kulle motan ta waiwayo tadubesa suka hada ido tayi saurin dauke kanta zuwa gefe,shiko gogon sebinta ya ke da kallo can yace wai meye kiketa wani bata rai tamasa banza yacigaba damagana ,inatambayarki,kaikidanayine nayi lefi koso kike danabarki kikwana? nan ma shiru yaharzuka cikin tsawa yace wai badakenake maganaba salan wulakanci,
Se asannan fadila tadago kai da fuska cike da hawaye tace wulakanci? wulakanci yawuce wulakantani dakakeyi Wanda haka har matanka suka sami damar gorantamun,Aliyu nayi nadamar aurenka auren bakinciki Inatabbatarma dabadan mahaifinaba dana dade dabarin gidan nan,cikin kuka takemaganar yayin da Aliyun yatsinci kansa da tausayinta Yakuma kasa cewa kome illa binta da kallo.
Fadila tacigaba kodan matanka da ni ba irin su naso nayi kishi dasuba,naso ahadani da wayanda suka San mesukeyi😭 bawadannan da kake kallo amataba nibanga mata anan ba kuma duk ajin naka akan salima da samera yakare ragowar wasu,cikin bacin rai yadakamata tsawa,itako ta dannan motar tabude tafita da gudu tanufi sa shinta,tana shiga tafada kujera setaji ya akayi tayi wadannan magana,setaji kamar bats kyautaba cankuma wani bangaren zuciyarta tacemata garadakika masa haka yasan fa kinsan mekikeyi kuma yasan badan shikike gidanba Dan biyayyar iyayankine,tamike tashiga toilet tayi alwala ta fito ta tada sallar isha dabata samu tayiba.
Can Aliyu kuma kasa futa yayi daga motar jikinsa duk yamutu zuciyarsa ta cunkushe abinda yafi damunsa shine kalmanta datayi kansu samira da salima domin yakaratunawa da yanda yasamu samira adarensu nafarko,sannan Salima bayan rabuwarsu itama ba agida tayi rayuwaba,yadafe kansa karo na farko da naga A S metama na kwalla daya nazurarowa daya bayadaya😰 yace inna lillahi wa inna ilaihirraji un.tabbas jidakai bekama ceniba domin ina tare da wadanda basu cancanci suzama iyayan yayanaba,gashi inakallo se haihuwa ake Wanda akai bikinmu tare duk sun haihu,su naji kowacce tace batashiryaba itakuma wanan yarinyar banashiga harkanta,gashi du k ta gane kome,Aliyu yacigaba da hawaye yana maibakkincikin abubuwa kala kala yadaure ya fita daga mortar jiki akasalance yanufi bangaransa yanashiga ya kulle kofar yabar makullin ajiki sabida bayasan ganin kowa domin koda sunzo sunyi amfani da makullinsu bazebuduba.yashige bedroom yafada gado yacigaba da tunani aranar dai Aliyu beruntsaba Dan maganganun fadila kemasa yawo akwalkwaluwarsa,
Itako fadila cikin nishadi tayi barci domin tafidda wani tabo da kedamun zuciyarta.
*amun afuwa Mrs Muhammad nayi muki shishshigi amma haka mukeson buk yadawo munakara mikamiki godiya dayabawa Allah yakara basira kidora saga inda natsaya domin zansamu goyon bays amma kitambayi friends sunyarda kidora😀*bye nabarki Lfy Wanda sukaji haushi suyafemin kar azagen nima wlh soyayyar buk din yasa nayi👍🏻
Ba Mrs Muhammad bace👑
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 1:46 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?..*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*part 2*
1⃣5⃣&1⃣6⃣
Qarfe tara fadila tayi wa iftihal wanka itama ta shirya cikin riga da skert na atamfa a cikin qana nun kayanta ta cirowa iftihal wasu riga da skert dama sun mata kadan jajayene in and top ta raba mata gashinta gida biyu ta tufke mata da ribbon sosai iftihal tayi kyau suka yi break sannan ta soma gyara part dinta kafin ta isa ga na aliyyu don duty dinta ne duk inda ta shiga yarinyar na biye da ita ita ala dole sai ta taya ta aiki sai da fadila ta bata mopping din kayan kallo sanna ta rabu da ita
Fadila ta fito tana goge hannunta da duster bayan ta gama aikin ta iftihal dake ta fama da chocolate tace “anty ina daddy na?”murmushi fadila tayi ta kama kumatunta tace”kwantar da hankalinki ‘yar daddy yanzu zaki ga daddy shiga daki bakin gado ki dauko min hijabina”da gudu kuwa ta shiga sai gata da shi a hannu ruwan madara ne iya qugu wanda ya shiga da atamfar jikinta sosai,ta kama hannun iftihal din bayan sun rufe qofan
Tana sa kai falon taji hayaniyar sama sama muryar salima ke a sama,tana tsaye hannayenta harde saman qirji kan aliyyu shi kuma na zaune kan kujera yana sanye da kayan bacci na maza ruwan madara shima hannun nasa harde a qirjinsa😠,shigowar su yasa salima yin dif daga maganar da take yi din gami da sakin fuskarta daga tsukewar da tayi tana dan binsu da kallo(salima akwai duniyanci)sam bata lura da iftihal ba da suka shigo tare sai da yarinyar ta zame hannunta daga na fadila wadda ta shige kitchen ta ruga a guje tayi gun daddynta tana cewa”daddyyyy daddyyyy….”kamar yadda ta saba ta durqusa a agabansa kafin ta haye cinyarsa tana cewa”morning daddy sabahul khair”,murmushi ne sosai dauke a fuskarsa wanda bai bayyanar da haqora😊yasa hannu ya dagota yana kallonta yace”sabahun nurrrr my lovely khadija”tayi tsalle ta dane cinyarsa abinta tana wasa da maballan gaban rigar baccinsa tana cewa”daddy tunnjiya nazo da daddare kaqi zuwa na ganka” “wonderful,anan kika kwana ke da wa?””ni da anty fadila tare ma yanzu muka taho”ya daga kansa yana nemanta da idanunsa sai dai tuni ta jima a kitchen bata a gun sai salima dake tsaye ta zubawa ‘yar tata ido
Kallonta take tana jin wani alfahari na shigarta tana godewa Allah da bai bata damar rasata ba,wani dadi ne ke cikata ganin gudan jininta ita da halitta mafi soyuwa a gareta wato Aliyyu salim Abdallah maitama,tabbas iftihal abar alfaharinta ce yarinyar bata debo kammaninta ba ko kusa babu wani abu nata data dauko illa farar fata wadda aliyun ma na da ita,kowa ya ganta ya san jinin su ce family din alhaji salim Abdallah maitama ce jininsu ce
Ta dawo daga duniyar tunaninta hadi da miqawa iftihal din hannu alamar ta taho sanda suka hada ido fuskar salima dauke da murmushi,da taga kamar yarinyar bata fahimta ba sai tace”come on baby na come on my dear ” yarinyar ta noqe kafada tayi luf jikin mahaifinta kamar mai tsoron ta babu sabo ko kusa tsakaninsu,wani kishi ya kama salima don taga yadda suka shigo da fadila yarinyar a sake take kana ganinsu kasan akwai sabo mai yawa tsakaninsu
Ta sake gwada sa’arta ta miqa mata hannunkaro na biyu tana sake cewa”come on mana mai dear kin manta mominki ne iftihal? Me yasa baki zo guna kin kwana ba ina da chocolate da biscuit da yawa da zan baki”ta sake noqe kafada tace “um um nafison na kwana gun anty fadila she’s nice like daddy”sai salima ta maida hannunta ta rungume cikin jin haushi
Aliyyu na ankare amma yayi kamar baiga abinda ke faruwa ba,sai da yaji tana jan qwafa sannan ya tanka mata”duk uwar da bata yi showing mercy akan yaronta ba tayi abandoning duk wasu duty nata akansa no need to deceive her self akan shi zai iya jin qanta ya kuma ji tausayinta”idanunta sun kada sunyi ja kadan take jira ta fara malalar da hawaye tace”aliyyu abinda ya wuce ya riga ya wuce please”ta juya cikin zafin nama ta bar part din nasa kamar zata rushe da kuka
🔱🔱🔱🔱🔱
*TUNA BAYA*👈🏼
🔱🔱🔱🔱🔱
Aliyyu da salima sunyi aure ne irin auren da zaka iya kiransa na soyayya,karatu shi ya fara fitar da aliyyu india cikin garin mumbai dake qasar india,ya karanci fannin kasuwanci da masana’antu ne tun usulinsa,kusan binda ma ya zaunar da shi kenan a qasar bayan kammala karatunsa kafin daga bisani ya soma kai kawo tsakanin nijeria da indian
Tun kafin aliyyu ya kammala degree dinsa na farko yake siyan kaya yana turawa uncle Abba yace a siyar masa tun uncle abban na dariya yana dauka wasa ne abun nasa yakance”alii rigima idan banda abinsa mai ya nema ya rasa da zai takurawa kansa sai ya fara kasuwanci tun kafin ya kammala karatunsa?”shi kama aliyyu ya dage aiko kaya yake tun daga lokacin da uncle abba ya fuskanci son kasuwancin a jininsa yake sai ya qyaleshi ,sai gashi tun kan ya kai ga kammala degree dinsa na biyu ya mallaki kudade masu tarin yawa na qashin kansa tsantsar guminsa,sam yaqi amsar tallafin sisin kwabo dag dukiyar da Allah ya horewa mahaifinsa,kwata kwata aliyyu ba cima zaune bane akwai zuciyar neman na kai tun yana qaraminsa,bai damu da arziqin da mahaifinsa ke da shi ba
Wadannan kudade yaci gaba da juyawa har kawo yanzu matsayin da yake kai na mamallakin companies da share shares a gida nijeria da wadansu maqwaftan qasashen,aliyu ya zamo daya daga cikin matasa masu tarin dukiya mutumne shi da Allah bai bashi dagawar son a san wayeshi ba,yasha gayawa abban nasa tun kafin zuwan wannan lokacin shi yafison yasan ya san zafin neman na kai,sai gashi burinsa ya cika don ya tara dukiyar da shi kansa bai sa ran samun kamarta ba,darajar addu’ar mahaifa riqon gaskiya da amana tausayi da taimakon na qasa su suka kaishi ga wannan matsayin da yake kai
Haduwar su da salima ta kasance ne sanadiyyar hutun qarshen zangon karatu da daliban instute din pashwar suka samu ciki harda,wadanda ba ‘yan qasar ba kuma suke da sha’awar zuwa qasashensu hutu nata shirye shiryen zuwa gidan ciki kuwa harda saliman,wasunsu na ahiga kasuwannin dake cikin mumbai don yiwa yan uwa tsaraba
Cikinsu harda salima su hudu ne ita sai wata qawarta ‘yar nijeria sa’adiyya abikan karatunta biyu ‘yan qasar data nemi rakiyarsu don qasarsu ce sun fita sanin kan farashin kayayyakin shruti da arohi,sun ahiga shagon a sanda aliyyu ke ciki yana zaune kan daya daga cikin kujerun dake ajjiye a shagon suna lissafi ne shi da mai mai shagon kan wasu kaya da aliyyun ya sara a gunsu alokacin tun kafin ya bude kamfaninsa
Abu na farko da ya fara kama jan hankalinta game da aliyyun shine baiwar tsantsar kyau da Allah ya bashi da daddadan sauti ,abu na biyu ya bata mamaki jin yadda yake hira tar tar da indiyanci tamkar haifaffen can,tunda suka shigo shagon daga kallon farko na amsa sallama bai sake duban sashin da suke ba ya mai da kai yaci gaba da abinda ya kawoshi shagon
Ita din ma azahiri idan ka kalleta sai kayi tsammanin hankalinta bai kansa saidai duk siyayyar da take yi kusan qani abun ma bata san me zatayi da shi ba data dauke shi don hankalinta na kan alin
Tuni ya kammala abinda yake yayi sallama da raja ya wuce,sanda yake fita ashagon garin karkatawa ya wuce taga silmiyowar wani abu daga aljihun trouser dinsa ma baya amma bata zaci wani abu mai muhimmanci bane sai da ta sake matsowa ta sa idonta sosai sannan taga ashe wata ‘yar kyakkyawar wallet ce ,da sauri tasa hannunta ta bude ciki,rupees(kudin india) ne masu yawa aciki a miqe,sai dan qaramin hotonsa wato passport,sai kuma wasu kati guda uku biyu na wasu shaguna dayan an rubuta *adishwar garment* shagon na cikin *janta cloth market hawkers plaza*ta maida shi ta duba dayan shi kuma na shagon *ajmeri fashion* shagon shi kuma na *hazarat abbas road Samuel street*,duk cikinsu babu shagon da ta taba zuwa tunaninta na kan yadda Atayi masa da wallet da kuma yadda zata sake samun damar hanawa da shi,tana duba kati na uku uku na dauke da sunan hotel din da ya sauka haka jikinta ya bata tunda su muta nene da komai ka siya ko kayi mu’amalar ciniki da shi sai sun baka rasit ko card nasu,tasan hotel din tunda takan ziyarci cikinsa lokaci bayan lokaci nan kusa da makarantarsu yake
Ta maida duka kayan ciki tana sauke ajiyar zuciya,bayan sun kammala siyayyar suka koma cikin makaranta,da daddare ta canza shiga irin tamu ta hausawa atamfa ce saidai dinkin riga da skert ne tayi kwalliya sosai a fuskarta,ba wata tafiya ce mai nisa sosai ba tsakaninsu don haka irin keken nan nasu ta hau ya qarasa da ita,bata sha wahalar samunsa ba saidai da yake hotel ne na manyan mutane akwai tsaro sosai da kuma tsari duk magiyarta basu yarda sun bata number din room din ba sai da sika kirashi suka sanar masa,duk da yayi mamakin mai neman nasa kuma sunce mace yace a bata number din baisan me ya kawota ba ko da taimakon da zai iya bata
Ku biyo
Mrs muhammad👑😘
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 1:47 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?…*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*part 2*
1⃣7⃣&1⃣8⃣
Sai da tayi knocking sama da sau biyar sannan aka bude mata,fuskarta ta wadatu da murmushi😃 yayin da tasa take a tsuke😠 kamar hadari,”sannu ko?”tace da shi cikin fara’a”yauwa sannu” ya fadi adan dake yayi bake bake abakin qofar babu wata hanya bare ta sa ran shiga ciki don ko kalan labulen bakin qofan ba zata tantancewa ba,cikin qosawa ya gyara tsaiwarsa ganin tayi shiru yace “I hope lafiya dai ko?”ta sake yin murmushi a karo na biyu ya zaro wallet din daga cikin yar purse👛 dinta dake damqe a tafin hannunta sannan ta dubeshi tace”wannan ka yar dazun a mall din paras mahal collection”ta miqa masa tana dan murmushi,ya sa hannu ya amsa yana cewa”thank you verry much”ya juya yana qoqarin mai da qofarsa ya rufe
Da sauri ta dakatar da shi ta hanyar cewa”haaabaaa haabaa malam babu ko goron tsintuwa?😊” a qagauce ya dakata ya juyo yana cewa”nawa kike buqata?”t saki wani mayaudarin murmushi”ba kudi nake so ka bani ba,kawai passport nake so na cikin wallet naka sai kuma phone number dinka shikenan abunda nake buqata🤗”
Girgiza kai yayi hadi”it can’t ki zabi wani abun dai daban banda wadannan”ta kanne ido daya😉 tace”ni su din dai nake so”kafewa yayi kai da fata bazai bata ba”i told you ba zaki samu ba”itama kafewa tayi akan shi take so indai alherin da tayi masa yake son rama mata,daya lura tana da yawan taurin kai sai ya bude wallet din ya zaro rupee dubu daya kwatan kwacin kudin nijeria a yanzu naira dubu hamsin ya ajjiye mata saman qafarta ya juya karo na biyu yana shirin sake rufe qofarsa
Ta tabbatar idan ya subuce mata a yanzu mawuya cine ta sake samun dama kwatan kwacin wannan don haka cikin zadin nama ta tattara kalmomin”idan kamin haka baka min adalci ba zaka kashe min gwiwa ne na aikata aikin alkhairi,ni bana buqatar kudinka
Da haka ta kashe masa gwiwa don bazaiso ta zama mara kirki ba ta sanadinsa ya sani idan har hakan ta faru yana da tagomashi a agun Allah,dole ba dan yaso ba ya bude wallet din ya bata passport din hadi da karanto mata numbobinsa ta kwafe tsaf bisa wayarta tayi serving,tun daga lokacin hotonsa shi ya zama abokinta da zarar ta kadaice shi take sawa a gaba tayi ta kallo,kyan Aliyyu na qayatar da salima ya tafi da imaninta 100%
Takan bata lokaci tana gurin kiransa amma ba zai daga ba,ta jure hakan ba tayi zuciya ba tana ci gana da kiransa,yau da gobe tafi qarfin wasa har takai da idan ta kirashi sau goma zaoyi qoqari ya daga mata ko sau daya ne shima daga gaisuwa bai bari a wuce haka,an halicci zuciya abisa son mai kyautata mata to hakan yake don kuwa kulawa sosai salima ke nunawa aliyyun mutum ne dama da bai taba budurwa ba samun hakan yasa ta shiga cusa masa ra’a yinta sannu a hankali har ya minta da ita ya bada amannar zata zama abokiyar rayuwarsa
Asalin salima ‘yan katsina ne mahaifanta,yan boko ne na bugawa a jarida irin mutanen nan ne da ake cewa”yan boko aqida”wato ga karatun bokon ga kuma bin duk wasu aqidu nasu, bokon suke da gaske babu sirkin addini ko kada cikin mu’amalar rayuwarsu ta yau da gobe bokon kawai akasa agaba shine madubi,hakan yasa tun a nijeria salima ke alalace don babu kwaba balle hantara da zarar kin kai shekaru goma sha takwas a gidansu to kina da yancin yin komai da kika ga dama,iyayenta na da arziqi daidai gwargwado don su suka dau nauyin karatunta ta fita indian
Mutum daya ne salima ta yarda da shi ta sallama masa jikinta a nijeria suke harkarsu duk da tana bawa wanda taga dama kanta yayi tabe tabensa don a cewarta ita babbar harka take,sai kuma zuwanta india ne wani abokin karatunta rahul,shima din tunda ta hadu da aliyyu tayi mishi fata fata sukayi handing over don kuwa tunda ta ga aliyyun tayi amanna ta samu kalar namijin da take so ya zama miji a gareta ya hada komai hundred percent
Cikin lokaci qanqani salima ta dage a tada maganar aure don kuwa tsoron take kada ta rasa aliyyun saboda tana ganin yadda mata jinsin qabilu kala kala dake indian mazauna can yan asalin indian da kuma baqin haure ke kara kaina akansa abunda ya sauqaqa abun ma babu fara’a ma bisa fuskarsa ko yaushe tana daure ne tamau balle kice zaki kawo masa wargi
Bai damu ba suka koma gida nijeria aka gama komai sannn ya dauko ta suka dawo indian saboda business dinsa ita kuma ta samu ta kammala karatunta,dole salima ta yakice duk wani abokin shashancinta saboda matsananciyar qauna da take ma aliyyun
Ba qaramin tashin hankali aliyun ya shiga ba yadda ya sameta ba budurwa ba duk da bai san ya budurwar take ba hakanan tasha stitches duk don ta matse,yafi aqalla sama da wata abun ma dukansa amma kasancewar sa mutum mai tsananin kishi da baijin zai iya auren mace ya saketa wani ya aureta yasa ya qyaleta,bugu da qari tsantsar qauna da take masa tamkar ta fidda ranta ta bashi,yayi imanin idan ya rabu da ita mawuyaci ne taci gaba da rayuwa parfectly
Cikakkiyar kulawa aliyyu ya dinga samu sosai daga farkon aurensu duk da ya fuskanci qalubale da dama na wasu ayyuka na cikin gida wanda ya zama dole kowacce *cikakkiyar mace* ta iya su,kama da girki zuwa tsaftace gida amma sai yayi haquri da hakan yake koya mata wasu abubuwan da niyyar idan sundawo gida nijeria zai turata makarantar koyon irin wadannan abubuwan
Abu na farko da ya fara kawo babbar baraka a zamantakewarsu wanda shi ya zama sila kuma sanadiyyar barkewar alaqar dake tsakaninsu shine,wata uku da yin aurensu ta soma rashin lpy,tuni suka yiwa mumbai general hospital tsinke sabodancita take sosai ,ba bata lokaci likita ya fara aikinsa cikin dan taqaitaccen lokaci sakamako ya bayyana sun samu qaruwa Allah ya albarkaceta da samun juna biyu
Ba qaramin tashi hankali da razana aliyyu ya tsinkaya ba kan fuskar salima shi da ya tsammaci ganin farinciki,tun acikin asibitin take kuka wi wi har suka iso gida,duk da ya kawo abubuwa da dama cikin ranta game da kukan da take sai dai ya hani zuciyarsa da yanke hukunci bisa zato da zargi,don ya tabbatar ya matsa mata da tambayar mekw faruwa? Bata yi qasa agwiwa ba kuwa budar bakinta tashin farko ta ce masa”gaskiya darling ban shirya haihuwa ba yanzu babu abinda ke cikinta banda wahala da tsofar da mutum,just shekarata ma nawa da zan fara shiga rayuwar raino da wahalar ‘ya’ya?,am just 25 fa”ta qaraahe maganar idanunta na malalo da hawaye
Da fari ua dauka rashin fahimta ne saboda boko da ya dabai baye rayuwarsu don haka sai ta ma bashi dariya ya murmusa idanunsa akanta yace”that’s my salima,wannan tunanin naki fake ne it’s not real,haihuwa ai ni’imace daga Allah wanda kudi ko mulki ko wata isa basu isa su baka ita ba,tsufa kuma ai lokacine,idan yazo babu abinda ke tareshi,bama haka ba idan kika ga haihuwa tasa mace tsufa ya danganta ko daga gareta ne rashin gyara ko kuma daga yanayin kulawar da take samu daga mijinta,ke kam baki da wannan matsalar ko daya,come on baby dont bother your self kinji,I promise I wil be with you cikin ko wanne irin yanayi”
Wannan duk baiwa salima ba tun aliyyu na rarrashinta har ya gaji ya sanya mata idanu,daga qarahe ma ganin ya zuba mata idanu sai tayi tsammanin ko ya haqura ne gaba daya?,sai kuwa ta fito masa da aniyarta na son zub da cikin wai ko don ta samu taci gaba da yin karatunta cikin kwanciyar hankali da nutsuwa tunda tana final year dinta watanni kadan suka rage mata zata fuskanci exams
A ranar taga bacin ran aliyyu irin wanda bata taba ganin irinsa ba,yayi mata kaca kaca ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba ya mata jan kunne mai zafi akan kada ma ta yarda koda mistake wani abu ya samu cikinsa bazai lamunta ba bare kuma intentionally,ta tsorata ainun amma duk da haka ta kafe ta turje akan bata ga abunda zai sata zam da cikin ba tunda bata so ai ba’a dole shi kuma yace zai mata dolen kuma zata gani,kamar ta haqura amma zugar qawaye na sake tunzurata,cikin rikici ta dinga rainon cikin ji take kamar tasa hannu ta fisgo abinda ke cikin ta jefar ta huta,wani takunkumi ya kafa mata ya hanata fita ko ina hakanan ya hanaduk wani mai zuwa zuwa gurinta,makaranta ma shike daukarta ya kaita ya kuma tsaya a bakin inda da zata dau lecture din har sai ta kammala ya daukota ya maidota gida ya kuma kulleta sannan ya fice sabgoginsa
Da wannan rikici ta kammla karatunta yayi clearing din komai nasa ya dawo Nigeria shi da ita gaba daya sai dai idan wani abu ya kamashi na yaje indian sai ya tasata agaba suje tare su dawo tare don kada ma ya barta tsautsayi ya gifta tayi abinda ranta ke raua mata,don baijin idan ta aikata hakan zai iya qyaleta ko ya daga mata qafa,
Ita kuwa ta samu sake rigima harda mara dalili yinta salima take dom dai taga duk ya dora burinsa kan cikin,ya zuba mata ido ne saboda albarkacin yaronshi da take dauke da shi gashi mai tausayi ne qwarai da gaske kan mace mai ciki,hakanan tsakiyar dare sai ta tashi ta zauna ta kuma taahi aliyyun suyi kwanan zaune ta kuma kwana tana rusa masa kuka da ihu ita wai cikin ya dameta ya hanata sakewa
Cikin haka ne ranar wata juma’a aliyyubya fito a masallaci aka masa waya asibitin doctor sa’adah yazo salima ta haihu,yayi matiqar mamaki don kuwa cikin watansa takwas da sati biyu kuma lafiyar Allah ya fita ya barta a gidan babu wasu alamun naquda tare da ita don baccinta ma take shirga,baiyi qasa agwiwa ba ya isa asibitin cike da murna doki da koma mamaki,yana zuwa ya samu qarin bayanin zuwa tayi aka turo naqudar ta qarfin tsiya wai ta gaji da zaman cikin ajikinta don lafiyarta lau ta iso asibitin,yayi fada sosai don sunga doctor sa’adah bata nan ne da ko bakin salima zai cire don roqo bazata yi mata ba har sai da yarda da kuma izinin aliyyun
Ransa yayi mummunan baci saidai yana yin tozali da santaleliyar baby girl din da Allah yayi masa kyautarsa sai farin ciki ya mamaye gurbin bacin ransa tuni yama mance da abunda ya faru,sak kamammin family dinsu tayo ya rungume yarinyar tsam tsam a qirjinsa qaunarta na mamaye jinin jikinsa,ya dinga kissing din yarinyar da tofeta da addu’o’in tsari kala kala,tuni gidansu ya cika da yan uwa mominsa farin ciki tamkar akan yarinyar ta fara jika,duk wani uatsina da salima keyi da daga kai ita da yam uwanta hakan bai dami yan uwan aliyyu ba domin su gadon arziqi ne ba taka shi sukayi suka haye ba rana tsaka,harkar girma kawai sukeyi
Suna akayi na tserewa sa’a,yarinya tayi albarka sosai don daga salima jar aliyyin babu wanda bai ga hakan ba,khadijatu shine sunan da ya mominsa ta zaba mata don abba ya bawa zabi shi kuma yace ya bawa momin ta zabawa kishiyarta sunan da kanta tayi murmushi tace ta bata khadijatu tana fatan Allah yasa ta yi gadon hali irin na mai asalin sunan,salima dama wannan bai dameta ba ita dama ta rabu da cikin shine agabanta alaqaqai kamar yadda ta laqaba masa
Aka gama wannann ta wuce salima ta sake qirqirar matsala ta biyu wadda ta tunzurashi ta koma jawo igiyar aurensu ta guntule
Mrs muhammad ce👑
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 1:48 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?…*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*Part 2*
1⃣9⃣&2⃣0⃣
Yadda abun ya faru shine salima sam taqi shayar da iftihal,anty hauwa ita ta gani ta yiwa salima magana cikin nasiha da kuma fadakar da ita illolin dake tattere da qin shayar da yaro nonon uwa indai ba lalura ba mai qarfi wadda zata jawo hakan koda hakan ta faru wasu basu yarda da madarar suna kai dansu ne ga wata wadda suka amincewa halayenta ta shayar musu da yaro balle ita da lafiya lau ne babu wata lalura,qememe salima tayi da ranta taci gaba da dirkawa iftihal baiwar Allah madara ba tare da masaniyar aliyyu ba
Ranar da lamarin ya faru sati biyu ne da yin haihuwar cikin yan suna wata ta sanar da ummi halin da ake ciki don haka ta aiko anty hauwan takanas da roqo da kuma lallashin salima tayi haquri ta shayar da iftihal don abun ya daga hankalin momin tace ko lafiya ce bata da ita tayi magana sai a a samo mata magani cikin tsiwa da rashin kunya salima tace”ita momin ce ta aiko ki?to ki gaya mata babu dan iskan da ya isa ya jawomin abinda zaisa jikina ya lalace lafiyatq qalau saidai tun farko na gayawa ubanta ban shirya haifarta bane,don da na samu dama da tuni tabi rariya ba zata ma zo duniyar ba bare azo ana min iyayin banza da wofi akan………..
Bata qarasa ba taji saukar lafiyayyun mari hagu da dama na kumatunta,da sauri ya daga kai din taga wanda yayi mata irin wannan aika aikar,aliyyu ne tsaye bisa kansa cikin matsanancin fushi fuskarsa tayi jajur😡 abunka da fari huci kawai yake fitarwa kamar wani zaki ya dora da cewa”bansan baki da mutunci ba sai yau ashe ke ‘yar iska ce ban sani ba? Mahaifiyata kike fadawa wadannan mugayen kalaman?…..to bari kiji salima…..👉har yau ba’a haifi yarinyar da zata ci mutuncin iyayena ba wallahi duk son da nake mata,yarinyata kuma daga kin bar bata madara indai ni ke aurenki”
Cikin hasala ta miqe tana nuna kanta tace 👆🏼ni ka mara aliyyu?….ni ka mara?,to an fada din yarinya kuma wallahi ko sama da qasa zasu hadu ba zata sha min nono ba,ai kana da yan uwa mata kana iya basu ita su shayar maka ko ka samar mata wata uwar ko kuma ka maidata cikinka ka sake haifeta”ya harzuqa matuqa ya daga girarsa yana kallonta “oh haka kika ce! Indai kuwa haka ne baki da wani amfani” “to ba sai ka yiwa tufkar hanci ba”a zafafe ya gyada kai yace “ok,well kije na sake ki saki daya”
Maganar tayi matuqar girgizata tayi zumbur ta miqe ta dangwarar da iftihal da da take riqe a hannunta tace”tafi nono fari ai” ta shige bedroom dinta,yarinyar tamkar kuwa tasan meke faruwa ta tsandare da kuka,ko waiwayo ta bata yi ba,anty hauwa tuni ta qame hannunta aka 🙊🙆🏻saboda sakin da aliyyun yayi
Ta fito dauke da akwati tana shirin fita,sai lokacin anty hauwa ta samu bakin magana “kiyi haquri don Allah ki dauki yarinyar nan”ta juyo a fusace sannan tayi murmushin takaici ta dubi anty hauwa”ai burinku ya cika ko?kuma ina tsammanin kema macace akwai nono a qirjinki kamar nawa to kina iya bata naki”a fusace aliyyu ya sake tasowa da niyyar kai mata wani marin anty hauwa ta tare gabansa
“a’ah aliyyu kada ka sake dole taji haushi its our fault dont beat her again mu lallabata ta dauki yarinyar dai”cikin harzuqa da tsawa wadda baisan yayi ba yace da anty hauwan”ni👆🏼 ni zan lallabata don ta dauki iftihal god forbid anty”ya fada yana kada kai”ko zata nemi hakan ba zata samu ba”bai san ya sake tura ma salima wani baqincikin ba da sauri ta ja akwatinta ta fice,a sanyaye anty hauwa ta juya ta dauki baiwar Allah iftihal dake nannade cikin showel tana ta tsanyara kuka kamar tasan abunda mamanta ke yi ,sanyata tayi a kafada tana jijjigata tana kallon aliyyu dake zaune saman kujera dafe da kansa idanunsa alumshe jijiyoyin kansa sun fito sunyi rada rada tasan alamun tsananin fushin aliyyu kenan tun yana yaro ,a hankali tana shafa bayanta har yarinyar ayi shiru da yake mai haquri ce bata da rigimako kadan matuqar ta qoshi
Zaman sukayi tamkar na makoki na kusan minti talatin sanann tace”aliyyu tashi mu wuce gida dole su abba suji irin aika aikar da kayi,ya kada ki bayan ya bude idanunsa da suka koma ja ya kalleta”ban yi laifi ba wannan shine hukunci da yafi dacewa da ita,ni nasan me dame salima ta yimin bayan wannn tun alokacin ta cancan ci narabu da ita amma na daure”ya maida kasa kujera yana maida numfashi ya daga mata hannu alamun ta tafi kawai
Ta girgiza ki tace “a’ah bazaiyi na qyaleka ki kadai ba kana cikin irin wannan mood din”ita tayi driving shi kuma ta bashi iftihal din ya riqe,ido sosai ya zuba yana kallon yarinyar tausayinta matuqa ke shigarsa yana tausaya mata na rashin dacen uwa da bata yiba ya rungumeta tsam tsam a qirjinsa cike da qaunarta
Fa babu irin wanda momi bata yi ba tamkar ta ari bakin wasu,kamin abbansa ya dawo ya dora da nashi,ce masa auke ai haquri shine mafita ba saki ba,shi dai uffan bai ce ba don baijin koda salima ta dawo tofa ta rasa shi shi da ‘yarsa har abada
To kuma sai aka taki saa ko rashin saa zance ne?uncle abba me ya nuna dattako da kansa ya taka gidansu salima don yin bikonta,qara ra a gabansa abban ta ya nuna masa shifa ba ruwansa bazai tursasawa ‘ya ‘yansa ba don suna da ‘yancin yin duk abinda suka ga ya dace da rayuwarsu,amma zai kira salima atambayeta idan zata koma to,da yake a cikin zafin kanta take a lokacin bata ji kunyar budar ido tace da uncle abba ba itafa ba zata koma ba”abban nat ya kalleshi yace”to kaji mai zaman tac3 bazata iya ba”abba bai sake tofa kanzil ba ya bashi hannu sukayi musabaha ya dawo gida
Lamarin rayuwar gidan nasu yayi matuqar bawa uncle abba mamaki,rayuwar’yancin kai suke irin ta mai jan kunne?ba rayuwa ba irin ta addininmu wadda fiyayyen halitta ya koyar da mu ba?,wanna wane irin masifane da a yanzu muka qaqabawa kanmi?,bayan ya dawo ya sanar da momin yadda sukayi,ita kanta da ake mace abun ya daure mata kai amma kasancewarsu iyaye masu dattako da basu so dansu yayi saki sai ta nemi izini gun uncle abban akan ita ma zata je ko za’a dace”uncle abba bai hanata ba yadda mai akai da mahaifin salima exactly haka akayi da mahaifiyarta don aqidar duka iri guda ce
Saidai ita an samu dan bambanci kasancewar salima tafara saukowa har ta fara kewar aliyun sai mamarta tace wa momi saidai aliyyun yazo da kansa,nan momi ta saka shi gaba akan lallai lallai ya shirya yaje,shi dai kullum yana binta ne da to don kuwa ya riga ya gama yankewa ransa cewq ko itace autar mata yq haqure mata don gaa daya ta qarasa ficewa fit daga ransa,bata da wani abu a yanzu da zata burgeshi da shi
Ganin momi ta soma tsanantawa a al’amarin sai ya soma shirin komawa indiyarshi ba tare da sanin kowa ba bai so ba ba kuma a son ranshi ba don baiso yayi nisa da yarinyarshi sai da ya kammala ne suka sani,momin taso ta hana abba yayi mata magana aka ta tsagaita hakanan da Maganar dole sai salima ta dawo idan da rabo zaman bai qare ba zata dawo ne,aliyyu mai tsananin biyayya ne bashi da tarin kunne akan duk wani umarni da iyaensa suka bashi,yana dai da zurfin ciki ne da nauyin baki,tun yana yaro idan suk ce yayi abu ya kafe baiyi ba to yanada dalilinsa ne mai qwari wanda sai daga qarshe idan suka bincika sai suga lallai yana da gaskiya
Momi ta gamsu da bayanin abban ta kuma yiwa aliyyun fatan alkhairi da samun dacewa,aliyyu ya bar nijeria 🛫cike da kewa da qaunar ‘yar diyar tashi tsoka daya a miya khadijatul iftihal,ya tanadar mata duk wani abu da zata buqata daki guda ya ware mata yajibge mata komai hatta da ruwa da zata sha ya tanadar mata bai bari ya dorawa kowa wahalarta ba harda kayan banza ma da wofi wanda bata buqatarsa,hakanan ya bude mata account duk wata yana saka kudi a ciki yace da momin aje a cira ayi mata abinda tale da buqata,to kawai take cewa kamar yadda uncle abba ya umarceta don shi tuni ya karbe ragamar komai din kudin da aliyyun keta aikin turowa uncle abba yace abarshi cikin account din ta amfanesu idan ta mallaki hankalin kanta
Wata shida kacal salima taji ajikinta qaunar aliyyu da yarinyarta tamkar zata zautata cikin begensu take kwana take tashi,yayin d iftihal ke cikin walwala da samun gamsashshiyar kulawa gata da soyayya ta qannen uba kakanni na gun uba da kuma dangainsa,tayi bulbul abinta madarar dai ita taci gaba da karba don itama taqi nonon kowa zakaran da Allah ya nufa da cara sai gashi cuta mai taba yaro bata taba samun yarinyar ba don ko haqori tashi sukayi suka ganta da shi ya soma fitowa,ga wayo a gunta gane mutane da kaifin basira
Shekara daya da rabi salima ta kasa daurewa,ido ta rufe ta soma neman aliyyun,saidai ya riga ya toshe duk wata kafa da zata sada shi da ita,sai daga baya ta samu labarin ya koma india,ba bata lokaci tayi visa ta bishi don zamanta da aliyyu ta samu dukiya sosai kasancewarsa mai sakin hannu shi yasa hatta zaman gidansu take jin bai mata ba
Acan din ma bata sameshi da wuri ba don ya canza gari ma gaba daya sun zauna a mumbai ne shi kuma ya koma new Delhi taci wuya ka su hadun saidai haduwar tasun mabata haifar mata da d’a mai ido ba,kaca kaca yayi mat irin wanda bata tsammani ba ya kuma jamata kunne da idan har ta sake suka kuma hada hanya sai ya wulaqantata,ta samshi qwarai idan ya fusata baida dadi iya kuma qurewa ta sani ta qureshin don haka bashiri ta tattara ta dawo nijeria ba tare da ta cimma nasara ba
Aliyyu bai waiwayi nijeria ba sai bayn shekaru uku cike da nasarori da budi masu tarin yawa wadanda bai taba tsammatar samunsu ba,company nasa ya bude babba acan hadi da qulla harkokin kasuwanci kala daban daban da wasu manyan kamfanonin,yazoya taras salima naci gaba da bibiyar rayuwarsu shida yarsa taqi aure sam duk wadata tsaya da shi sai taga ba namiji bane ganinsa take kamar mace yar uwarta taqi sauraron kowa da komai,itace kira saqonni na email sms duk wata kafa da ta samu ya rabu da duk wasu layukansa saboda ita amma ya rasa yadda take samun sababbi,sunzo don a basu iftihal yafi sau hamsin tun yana india suke da muradin haka ya gaya masu su da iftihal saidai su ganota daga nesa don bata buqatarsu
🔱 🔱🔱🔱🔱🔱
*samira*
🔱🔱🔱🔱🔱🔱
Shekarunsa hudu da dawowa ya hadu da samira gun bikin abokin kasuwancinsa,tunda ta qyalla ido a kansa ta qwallafa ranta,ta rasa ta inda zata samu shiga domin kuwa baida walwala ko sakin fuska shi yasa take fargabar tunkararsa,da yake tare yake ta hidimar bikin abokin nasa da iftihal dinsata lura da yadda yake ta nan nan da yarinyar ta samu kuma information kanncewa ‘yarsa ve da yake tsananin qauna sai itama ta jata ajiki sosai tattali take nuna mata kamar babu gobe,shikam mai son wanda ke son iftihal dinsa ne don haka ya sakar ma samira duk da ya ja jikinsa sosai da fari saboda yakan tuna yadda ta kasance masa a baya tsakaninsa da salima
Itama tazo akan gaba don lokacinne tsananin ya sake aure ya masa yawa a gida ahi kuma a zahitin gaskiya a wannan lokacin bai da time na duba mace,ganin ya samu maison iftihal dinsa yasa ya amince daga qarahe ne ma momi ke masa albishir din itafa ba zata bashi iftihal ba donnta riga tazo kenan,ba yadda ya iya duk da son da yake wa yarinyar tasa
Sai da salima ta gasu sosai fiye da tsammaninta wanda tadinga jelen kamun qafa da momi da abban da a baya ta watsawa qasa a ido kullum tana cikin gidantana magiya sannan ta samu dawowa gidanta,gidan da ta tarar ya kubce mata har wasu biyun sun samu mazauni cikinsa,ya ta iya da ranta son da take masa yasa bata ji wani abu ba tayi zamanta duk da a baya tana daga cikin matan dake iqirarin basu ba kishiya don ba zasu iya zama tare da ita ba
🔱🔱🔱🔱🔱🔱
*_dawowa labari_*
🔱🔱🔱🔱🔱🔱
Washegari tun qarfe tara fadila ke shirin fita suna,tayi wanka ta shirya tsaf cikin shadda dinkin doguwar riga ne yasha aiki daga sama har qasa butter colour ta debi wadanda zata sauya a can kala biyu ne da tayi musu anko ita da faridan zasu sa tare ta shirya iftihal cikin itama doguwar rigar yan kanti wadda ajiya ta bada aka siyo mata hade take da takalminta da ribbons dinta red ce in and top ta tsaya mata iya qauri takalmin boot ne na yara fari qal tayi ma gashin yarinyar ado da fararen ribbon tayi kayu matuqa kasancewar yarinuar mai yalwar gashi mai tsawo da santsi
Hat ta tada motarta iftihal ta hango abban nata ta balle murfin motar ta fice aguje,bayan ta duqa ta gaidashi ya dauketa yana wulla ta a sama shiko nauyi bata yi masa”cewar fadila cikin ranta tana satar kallonsu,tana ganin iftihal na nuno mishi ita,ya juyo ya kalleta suka hada ido tayi maza ta sunkui da kai don kada qwayar idanunsu ta hadu ya saka mata dafin da ya saba jefa maya cikin zuciyarta na qarin qaunarsa,”verry neat ya fada sannan ya dauke kai”iftihal ta leqa fuskarsa “daddy munyi kyau kuwa”yayi kissing kumatunta yace kinyi kyau sosai my dear”tadan bata fuska tace “anty na fa?”yayi yar qaramar murmushi yace “both of you””thank you daddy”ya sauketa bayan ya sake kissing dinta tana daga masa hannu ta zura aguje ta dawo cikin motar tana dariya