YAN BOARDING COMPLETE

 YAN BOARDING COMPLETE 

Katafariyar makarantace dake mabera  cikin garin sokoto wato *Government Girls College* GGC.

Students kowa da abunda yake yi saka makon yau weekend ba class fitowar sukenan daga hostel an gama inspection kowa ta kama harkar gabanta sae himarsu sukeyi

Yan mata ne guda uku zaune a cikin kwanar suna fira hankali kwance waccen ke kan up bonk ta leko tace”sadixy wlhi na gaji da saka uniform da hostel wears ni yanzu burina kawae murubuta exams ace munyi candy”

Wacce aka kira da sadixy ta kalleta tace ” kae uwar kwana baki da dama kice ke uniform din ma ke damun ki”

😄 Dariya tayi btace ba kedae wlhi abun ba’a mgn wae nikam yau me su farcy sukayi ne na gansu gurin mama principal tana musu fada”

Sadixy tace wlhi ban sani ba

Aaj ta bata yi mgn ba tunda suke firar su sae yanzu tace “wae marin wata Junior tayi shine takae karar ta”

Sadixy tace ” wlhi matar nan na jamana raini hmm ni bari na daki wata taga mae min mgn”

Dariya sukayi gaba daya Raj tace kae diyar kwana shiyasa kike burgeni

Aaj tace ba wnn ba kun manta on monda muna da test din mai nika biology kuma gashi wnn matar mal Aysha Adila zata karba assignment din chemistry din ta

Raj tace kae ku bari sae gobe ko anjima wlhi duk na gaji da wnn inspection din na yau

Sadixy ta gyara kwanciya tace hmm ni bari na danyi bacci kafin ayi sallah”

Har ta kwanta ta mike ta fita wasu juniors ta gani tace” kar gaba dayan ku ku zo nan”

Da gudu suka nufi kofar dakin suka tsaya sae da ta gama kallon su gaba daya kana ta zabi yara biyu tace sauran ku tafi.

Juyawa tayi ta koma daki sae bayan ta kwanta tace ku min fitara har nayi bacci

Nan yaran suka duka suna yi mata fitara sae da suka tabbatar da tayi bacci kana suka fita

2

********★

Da dare bayan sun gama dinner gaba daya students din suka koma hostel wasu students ne yan jss3 suka taru a kwanar daya daga cikin yan class din su suna fira can sukaji ance *all j3 class* da gudu suka fita suna zuwa bakin kofar dakin suka hau layi wata yarin yace a karshe dan haka ita aka zaba.

Wannan dabi’ar bosa kenan idan tana bukatat wani zata tara gaba daya class dinda ta ga dama na hostel din duk wanda yazo a karahe to fah shi zaeyi duka aikin

Bayan sauran sun tafi tace yauwa so nake ki gyara min gadona kuma ki share dakin nan so goma bayan kin gama ki debo min ruwa a bucket” tana gama fadar haka ta juya tayi gaba

Nan yarin yar ta hau gyaran gado gashi gaba daya duk gadon kayane haka ta linkesu ta gyara gado tayi shara kamr yanda akace ta debo ruwa ta tsaya jira dawowar bosa dan tasan halin ta idan ta tafi toh ko jaki sae yafita jin dadi

Zama tayi tana tunanin test din da garesu on monday gashi ko karati batayi ba kuma teacher din mugu ne baya bada simlpe questions kuma idan kayi failing ya zane ka hade kanta tayi da gwiwa tana tunani can sae ga bosa da sautan yan dakin su sun dawo tare da wata junior tana ganin su ta mike tsaya ita bosa gaba daya ta manta da ita sae da taga gadon kana ta kalla yarinyar tace “sau nawa kika yi shara”

Yarinyar tace “sau goma”

Bosa tace “ina ruwan da na aikeki debowa”

Tace “gasu can”

Sae da ta zauna ta kalla Junior dinda suka zo tare tace ” ke kneel down kuma ki sani a haka zaki kwana”

Hawaye yarinyat ta goge tayi yanda akace tayi

Bosa kuma ta kalli dayar tace jeki ta fita tana tunanin waccen da akace a haka zata kwana gashima js1 take abun tausayi Allah ya isa ta dinga jerawa acikin ranta har ta kae daki…….

…Yau sunday gaba daya students din sun fita sanitation kowa an bashi portion dinda zae gyara basu gama ba sae kusan 12 kowa kuma ya kama harkar gaban sa masu wanki nayi masu kitso ma haka wasubkuma karatu aukeyi wasu ko assignment wasu kuma zaman banza gaba dayavkowa na rayuwar sa.
+
Bosa ce ta kira yarin yar da suka shigobdaki tarw jiya tace ga uniform dinta ta wanke su tas idan suka bushe ta kawo yarin yabkaram ba yanda ta iyavdan tasan halin bosa sarae duk acikin seniors dinsu tafi kowa mugunta da cin amana.
Raj sadixy da Aaj zaune suke a dakin su rabash suna fira gaba dayan su Aaj na ma zee kamaila kitso mar kuma na musu kwadon cornflakes da sardine bayan ta gama suka zauna sukaci bayan sun gama  Rasheedo ta ska aka kira mata dika dikan yan mata na ss1 ta tarkato gaba daya kayan wankinta ta bada harda sabuku da kiln ta hada musu suka kwasaa tafi Rag ta aika aka kira mata skl dota dinta Asma’u santali ko da ka je sae akaga tana wanki hakan yasa aka dawo aka sanar ma Ruqayyah asma’u na wanki kuma senior bosa ce ta bata tace idan ta gama zata zo4
Da sauri sadixy da Raj suka tashi suka fita a tare Aaj tace ke sadixyvina ruwanki wlh kidae na siyan fada
Tsakibkawae tayi taja hannun Raj suka fita basu tsaya ko ina ba sae gurin bosa sadixy tace ke bosa mae haka yanzu ki rasa duk cin yan matan dake skl din nan wa zaki saka ya wanke miki kayanki sae wnn jaririyar yarinyar dako kashi bata isa gama wanke ma kanta ba toh wlh idan kika kara sae mun saka kafar wando daya dake ke kin sanni na sanki ta juya ta kalli asma’u tace ke kuma ajiye kayan nan ki tashi mu tafi tunda bana uwarki bane jiki a sanyaye ta mike ta buya a bayan Raj
Bosa da ranta ua gama baci tace wkh sadicu ki fita daga idona oh su sauran yaran da akae sakawa aiki ba mutane bane
Saidicu tave oho wnn kuma ke kika sano amma wlh kika kara saka wnn yar gold in aiki haduwar mu baza tayi kyu ba
Gaba daya yan sauran dakin su bosa suka taso da fada dama su kowa yasan basu mkuma duk student sunfi tsoronsu akan kowa sadixy tace dan gin mahaukata zuri’ar mugaye yan uwan azzalumai wlh kuji tsoron Allah kuna tunanin addu’ar da yaran nn keyi muku baza ta kama ku wlhi sae daya daga cikin ku ta rubuta ecams taga flat f9 baku saka komae gaba ba sae cinzali da iskanci gaba dayan ku da za’a kara muku interview inada tabbacin da primary kalar brain dinku ya dace
Tana kae nan t suka wuce abunsu sauran kuma suka rakasu da zagi.
*ASALIN RUQAYYAH RAJ*
Sunan ta Ruqayyah Ahmad Jega zuwanta skl ne aka mae da mata da suna _RAJ_ sadixy kuma tana kiranta da uwar kwana
Ya ce ga babban lawyer mae zaman kasan wato Barrister Ahmad Y. Jega aslin babanta dan garin jega ne amma gaba dayan su suna zama a sokoto ne gaba daya rayuwar au a sokoto suka santa matan shi biyu hjy Rabi wacce auke kira damamar birnin kebbi sbd ita a can ta koma da zama yanzu kuma itace uwar gida tana da yara  7 sae hjy Hassana wato amary kuma maman Ruqayyah tana da yara 8 itama amma shida ne kadae a raye Aunty sha itace first born sa ya kabeer sae aunty hafsa sae ya zainab sae Ruqayyah sae sumayyah sae wta ameena amma allah ya mata rasuwa sae autansu abdulnaseer
Suna zama na mutunci gaba daya basa fada dansu basu dauki wani abu wae shi kishi a zaman su sae dae son barka
Mama sokoto da babansi auren zumunta ne auren dangi
Maman sokoto sun kasan ce sune first born a gdan su ita da yar uwarta ya’ya ga late musa Habeeb kuma asalin su ba yan nan bane kakan mamansu wato Habeeb ya dawo jega da zamane sanadiyyar wani fada da akayi a chan wata kasa guraren sudan su uku ne a gurin iyayen su toh sanadiyyar wnn gusun ne yasa dukan su suka rabu sae daga baya habeeb ya gane dan uwanshi dake zama a zamfara amma shi na ukun har yau ba wanda yasan shi sunyi nema har sun gaji suka barwa Allah.
Matarlate musa ita hjy Hadeeza mata mai mutunci da karamci yaranta 8 hudu mata hudu maza hasana da husaina ne farko sae Ameen sae Basheer sae zainab murtala Mukhtar Asma’u gaba dayan su sun taso cikin gata da so da kauna har Allah ua dauka ran baban su basu raba kansu ba ko a tsakanin yaransu baka gane waye dan wnn kona wnn sbd kansu a hade yake komae basa yi sae da shawarar junan su.
Itama Ruqayya ta taso cikin tsantsan so da kauna daga gurin mamanta da babanta bata da hayaniya ko kadan kuma ba ruwanta she is so silent baka taba jin bakinta idan ana fira kuma kyakykyawa ce ajin karahe though bata da tsowo amma kuma baza ka saka ta a jerin guntaye ba black beauty ce sosae ga gashi ga ilimi Allah ya bata shi yasa iayayenta ke sonta ko acikin yan uwanta gaba daya halayyar mamatr ta ta dakko ta cika sanyi bata son fada shiyasa mutane ke ganin kamar dan bata da karfi ne shi yasa amma sam ba haka bame Allah dae bae yita da haya niya bane gaba daya.
Aaj sunanta Aysha Ahmad Jega kanwar Ruqyyah ce amma few months ne kawae a tsakani Aysha tafi Ruqayya tsawo sosae kuma kansu a hade yake ko kayan sawa basa yi sae iri dayabharta da underweara dinsu iri dayane shi yasa wasu ke ce masu yan vmbuyu duk da basa kama ko kada……………Ruqayyah suna ss1 aka maida su GGC sabodan son boarding school da takeyi ita da yar uwar ta anan ne suka hadu da sadixy ita kuma real name dinta Khadeeja Abdullahi Gobir farkon zuwanta skl din ba mae shiga harkar ta gaba daya yan class din basa kula ta ganin haka yasa itama ta kama kanta bata shiga harkar kowa kuma gata da kokari da maida hankali akan karatu.+
Ganin haka yasa Raj ta fara janta ajiki acewarta bae kamata ba abunda yan class dinsu keyi da haka suka saba sosae kuma itama yar skt ce babanta babban mai kudine abunda yasa take skl din ma yanzu sbd mamanta bata gdan baban kuma gasu da yara da yawa kowa da mamanshi suka dae yaran wani katon part ya ware musu iya su da masu musu aiki set by set wani shi kadae ne bashi dan uwa wasu kuma su biyu haka dae ba wanda ya damu da tarbiyyar su hakan yasa maman sadixy ta maidata boarding bayan tayi aure.
Acikin su uku din Raj ce bata da fada ita data ga an fara ma kuke take saka musu idan kuma fadan da ita akeyi toh su zasu siya sae daga baya kuma suyita mata masifa wae ita wawiua ce ta cika tsoro sae dae taji su kawae ta share…
Wannan kenan
*MONDAY*
Hmm ranar da kowa ne mutum ke tsoro tindaga masu zuwa skl har masu zuwa aili kuwa.
Assembly aka bayan an gama kowa ya koma class dinshi ss3B mai nika ne a class dinsu wato biology teacher (haka suke kiranshi da) kamar yanda ya fada test  zae musu  hakan kuma ba’a fasa ba yana shigo yace morning all submit ur books b4 i count 3
Da gudu kika ga suna submintting dinshi a kan desk sbd sun san halin sa baya wasa bayan sun gama ya zaro paper daga cikin envelope ya fara rabawa abunda basu ta tsammani ba suka gani gaba daya kowa da kalar questions dinsa kafin kisamu mai irin naki sae kin kirga mutum biyar wadan da basuyi karatu ba duk suka sha jinin jikinsu bayan ya gama yace u can start now and u give i only 15mins
Kowa na iya kokarinsa yaga ya gama wadan da are not seriois kuma in banda kallon sama ba abunda suke yi sae cin marfin pen
Wata student gaya tana kallonshi yace ye look at me wel wel maybe u find the answer in my face will u write something my frnd kasa tayi da kae tacigaba da abunta
Hmmm maryam  (em jamil) ya gani tana bacci hankalinta kwance paper ya samu ya tura mata a hanvi da sauri ta mike tana hafa hancinta ganin shi yasa ta gyara zamanta tana hamma tace sir i dont kniw what to wirte cn i just give u ur paper kallonta yyi yace ehhh see ur nose like shortnika if i trash u here ko baki san komae ba sae bacci everyday u will be sleeping in d class sleeping master just ask ur papa ya miki aure cause he is just waisting his money ne baban gwaza big for nothing ba yan class ba ko readers sae da sukayi dariya 😆
Ruqayyah ta fara submitting sae class captain kana sadixy da AAJ ma sukayi
Yana fita malam Aysha Adil ta shiga dama sun san policy dinta idan ta bada assignment kafin ta shiga class toh kowa ya tabbatar yyi submitting idan ba haka ba toh na kowa baza karba ba kuma zatace shine test dinku over 40 shi yasa kowa ke bayar wa kafin ta shigo.
Bayan sun tashi hostel suka koma bayan sallah daga can suka wuce dining da bayan sun gama kowa ya fada kan gado dan sun san halin manyan nasu.
Basu tashi ba sae da aka fara kiran sallah daya daga cikin yan ss2 ana kiranta da rumeey ta daura abincin kan stove tana jin alamun ss3  ta dauki duka stove din da tukunyar ta saka acikin locker dinta ta fita sae da akayibsallah kana kowa ya shiga class gurin evening prep.
Su Raj da wasu yan class dinsu kuma suka zo satar ruwa suka ga dakin su rumeey na hayaki da gudu suka fita suna ihun gobara…….
….. Da sauri staffs dinda ke quaters suka fito mama principal ranta gaba daya ya baci bayan an kashe wutar ta tara duka students din emergency Assembly fada ta musu sosae ta dora da fadin wlh baza ku kara cooking ba gaba da na hana zuwa da wani kayan abinci fatan kunji me na fada kuma wadan da hostel dinsu ya kone suyi squatting a hostel din yan uwansu+
Bayan assembly kowa ya koma class nan fa aka samu topic of discussion duk inda ka kutsa magnar akeyi hmmm abunka da boarding harda kari
Da dare bayan sun dawi daga night prep nan fa wadan da hostel dinsu ya kone suka fara neman gurin kwana da kyar kowa ya samu ya kwanta har zuwa gari ya waye
Washe gari bayan sunje class yan ss3A babban R ne yashiga class dinsu wato mathematics teacher dinsu bayan sun gaida shi suka zauna malamin ba ruwanshi ya cika sakin fuska sosae ya juya ya kalli board ya fara rubutu *MEASURATION*  ya juya kalli students din yace our today’s lesson is measuration with full confidence Bosa tace but sir u wrote *MENSTRUATION* dariya aka saka duka class din hakan ya bata mishi rae ya hade fuska yace am not here for joke i know u were thought this topic in ur ss1 or 2 mine is just to revise so ols concentrate dariyar suja tsagaita ya cigaba da da musu explaining sae bayan ya gama lesson din gaba daya farcy tace excuse me sir juyowa yayi yace yes how can i help you tace sir i dont understand  yace where tace from the beginning wani kallo ya watsa mata kana yace u mean  all di time i wasted  u re saying u dont understand sha dat is ur own  cuo of tea i have done wat i can dat y i like ss3A they don’t play with their studies but u dis class gaba daya an hada masu fish brain a guri daya tsaki yyi ya fita abunshi nan suka dinga zaginshi suna tsine mishi
*SS2A*
Biology teacher dinsu ne a ciki Nawaaz explanation yake musu akan  *EVOLUATION* abinka da students kuma masu tashen balagar tsuntsaye sae dariya suke yi dama tunda suka fara hormones shikenan yaran suka maida abun dariya da anyi abu daya sae wnn ta kalli wannan sae kaga sunyi dariya hakan yasa malamin daure fuska.
*Breakfast*
Bayan an fita break daddy 501 (haka suke kiranshi) mugune sosae shi acewar shi ma cinzalibakwae dadi shike yanka portion idan kayi laifi.
Wasu students jss3 sukayi laifi wani uban katon portion ya yanka musu koni abun ya bani tsoro dan wlh ko maza aka saka sae sunsha wuya kagin su gama kuka suka fara suna rokonshi shiko mugu sae faman dariya yake ba yanda suka iya dole suyi gashi suna da test din B/tech.
Bayan an koma class malam Aysha Adil ta shiga ss3B  bayan ta gama lession ta basu assignment dan ita kullum ta shigi sae ta bada gata muguwa har ta kae bakin kofa tace And failure  to do eat  entiltle to punishment.
Dama sulopiyp na jiranta a bakin kofa tana fita ya shiga suna ganinshi suka fara dariya tafiyavyake kamar mace har ya kae bakin teacher’s desk yace wash am so tired
Dariya suka su kace dat how u re always sir smiling yyi kana ya rubuta sunan subject akan board physics hannun shi daya na kan board dayan kuma ya kama kunkuru dashi dama haka yake abu kadan yace ya gaji shi yasa suke kiranshi da *sulopiyo* saboda mugun sakarae ne Allah dae ne yyi shi teacher amma wlh hmm.
*Boiling Point And Melting Point*
Ya kwashe more than 1 hour yana rubutu a board kuma abun haushi so daya ya goge board ya cigaba da rubutu 😆gsky wnn ya cika sulopiya kuwa bayan ya gama lession aka tashi dama shine last period.
Bayan sunyi lunch suka koma hostel da yamma suka fita evining prep tsabar iskanci irin na ss3 kan wata kasa da aka tara suka koma suka zauna hausa novel suka dakko suna karantawa Raj ce maiyi dan duk ta fisu iya karatun hausa a gefe kuma kwadon gari ne cike da roba suna ci……..
Washe gari bayan assembly Raj ta fara neman hanyar guduwa dan bata gama copying assingment dinta ba su Aaj duk sun gama dan tare sukayi amma Raj da ta fara copying sae tace bacci zata yi bayan salahr asuba baccibya kara kwashe ta.+
Riketa su sadixy sukayi kamar mara lpy suka kae ta pharmacy dan ta san halin Aisha Adil ba raga mata zatayi ba bayan sun isa pharmacy suka kwantar da ita suka ce ma dr din marar ta ke ciwo nan ya bata mgn ta koma ta kwanta.
Dasu sadixy suka koma class malam ta tanbayesu ina dayar frnd din tasu sukace tana pharmacy ba lpy smiling kawae tayi dan tasan karya ne assignment ne dae batayi ba amma zatayi maganin ta dama bata wahalar da kanta gurin yin karyar ciwo ba da ta kyale ta dan tasan Raj na assignment amma karya da rainin hankalin da tayi ne yasa tace zatayi purnishing dinta.
Bayan lesson ta fita daga class din direct pharmacy ta wuce zaune taga Raj da ka ganta kasan lpyr qalau wani wawan mari ta bata guda biyu sae da Raj ta fadi kasa da sauri ta dagi sukayi ido biyu da malam Aysha nan take gabanta ya fadi tace malam am sick dat why.. A tsawace tace shot off ur dirty moth before i loose my  temper on u ni zaki raina ma hankali see me in d offce now.
Tana kae nan ta fita Raj gaba daya hankalinta ya tashi sae kuka take gashi gurin da malam ta mareta shatin hannunta ya kwanta.
Office dinta shiga jiki a sanyaye malama Aysha ta kalli Sargent tace gata nan kamata bulala 50 wani kuka Raj tasa sargent kam waje ya fita yace ta bishi haka ta fito sae kuka takeyi dukanta yake tana ihu dan Ruayyah akwae tsoron duka ihu take sae kace wacca za’a yanka yana mata goma ta fadi sume ganin haka yasa sargent tsayawa da sauri ya koma office ya gaya wa malama Aysha halin da ake ciki da sairi ta mike ta fita kwance ta ga Ruqayya bata motsi da sauri ta koma ta dakko ruwa ta dawo ta yayyafa mata sae gata ta kawo numfashi ai bata tsaya bata lokaci ba ta kamata suka wuce pharmacy da ita (sae ga Raj da ciwon gsk😆).
Allunran bacci dr ya mata kana hankalin malama aysha ya kwanta.
Su sadixy basu san abunda ke faruwa ba sae da aka tashi suka je pharmacy koda suka shiga Raj ta tashi daga bacci amma duk tayi so week nan suka tambayeta meke faruwa ta labarta musu komae tana sharar kwalla da sauri sadixy ta mike  sae office din mama principal tayi sa’a kuwa tana nan ta gaya mata komae tace ta tafi zata suyi mgn da malamar.
Sadixy na fita mama principal Ta kira malama Aysja masifa take mata ta idan take shiga bata nan take fita ba daga karahe ta bata 2weeks suspension akan sumar da yar mutane………
 Wasa wasa Raj sae da tayi jinya amma alhmdllh taji sauki dan sae faman shirye shiryen visiting suke yi masu yin kitso nayi masu wanki ma haka kowa ya matsu Saturday tayi. Tun ranar Friday suke faman gyara compound din skl sosae kuma gurin yayi kyau.
+
*Visiting Day*
Yau take sallah agurin boarders kowa Kika kalli face dinshi zaki ganshi cikin farin ciki sbd ganin yan gdan.
Su Raj ne zaune a kasan wata bushiya dasu da yan gdan su a gefe kuma yan gdan su sadixy ne fira suke sosae suna kallon pics din bikin da akayi basa nan a wayar ya Bg Asma’u skl dota din Raj ce tazo bayan sun gaisa da kowa na gurin tace”aunty Ruqayyah maman mu tace kizo ku gaisa”
Tashi tayi itada sadixy suka tafi.
Bayan sun gaisa maman Asma’u tace”aunty Ruqaayah mun gode sosae fah Allah ya saka da alkairi auta ta gaya min gaba daya alkairin da Kika mata naji dadi sosae dan kin san sha’anin boarding irin wnn sae a hankali”
Smiling kawae Raj tayi tace”ba komae mama”
Hafiz yayan Asma’u dake tsaye tun dazu yana kallon Raj Kamar an dasa shi sae smiling yake cikin ranshi yace” hmm love at first sight
Kudi maman Asma’u taba ma Raj amma taki karba ba yanda bata yi tace aa ta gode suma suka kara yimata godiya Asma’u ta karba wayan mamanta tace”mama dan aramin phone dinki in karba no din aunty Ruqayyah idan akayi hutu zan dinga kiranta muna gaisawa” maman tace kafin mu tafi zamu zo mu gaisa da ummanki”
Raj tace to
Ta bata wayan Raj ta saka no dinta suka tafi. A hanya sadixy ke cema Raj”Kinga yanda guy din nan ke kallon ki”
Raj tace”hmm ni ban ma kula dashi a gurin ba”
Sadixy tace”wlh ya hadu yama fi Asma’u kyau sosae Kinga elder sisters dinta my Allah gaba dayan su suna da kyau sae dae wnn yafi wnn”
Raj tace”ba dole ba maman shuwa baban su fulani”
Sadixy tace”wlh idan yace yana sonki karki tsaya kallon ruwa kado ya miki kafa da irin wnn kallon daya miki shi ake Kira love at first sight baki ga yanda yake smiling kae wlh ya roller miki ne fa”
Cikin mamaki Raj tace”shi ya fada miki hakan kawae daga ya kalleni ai naga ba shi kadae yake kallona a gurin ba dukan su all their eyes is on me”
Sadixy tace”dalla matsa an gaya miki bana saurin gano irin wnn ne kin sanni da saurin harbo jirgin mutum especially samari”
Raj tace”Allah ya shirya ki to”
Tace ameen
Haka suka karasa gurin suna fira bayan sun zauna ya zainab tace”wae ya naga dis visiting bakuyi complain ba”
Da sauri Raj tace”wlh akwae babba ma kuwa mal Aysha ta saka baba Sargent duka na har sae da na suma”
Suma? toh laifin me kikayi nan ta Basu lbrn abunda ya faru mamanta tashiga mata fada inda take shiga bata nan take fita ba”meyasa bakiyi assignment din ba bayan kin san halinta ai gashi yanzu kinja ma kanki zanje in samu principal din taku tunda yanzu dukan da akeyi harda sumar da yaran mutane akeyi””
Suna zaune sae ga Asma’u da mamanta kallon kallo sukayi da maman Raj tace dama kina duniya hajiya Atta
Maman Asma’u tace”hmmm hajiya Hassan dama kece maman Ruqayyahn auta
Maman Raj tace”Allah sarki naga kama kam ya gda da bayan rabo”
Maman Asma’u lpy alhmdllh ya su shafa da zainab
Maman Raj tace shafa na lpy ai ga zainab nan” maman Asma’u tace Allah sarki kin san koda muka bar gari itace goye alokacin Hafiz nada 6yrs
Maman Raj tace Allah Ina Hafeez din na san ya rima yanzu
Maman Asma’u tace gashi nan fa yanzu baki gane shi ba
Maman Raj tace Ina ko zan ganeshi yaro ya rigirma aa masha Allahu kace sae aure yanzu
Shikam kunya ta ishe shi a gaban su Raj ana cemishi ya girma..lol
Nan fa suka zauna fira da tuna baya sae da aka kusa tashi suka rabu.
Madam ataimaka plss wlh transfer muka samu kuma nasan yaran zasu iya covering kafin ayi exams tunda suma duk abunda ake a nan shi ake a can
Principal tace gsky baza nu karbe su ba sbd term yayi nisa har anyi second test
Nan suka shiga roko dakyar suka samu ta yarda akace gobe za’a kawo jss1
Da dare bayan kowa ya koma hostel suka shiga shirya kayan su yanda ya kamata fuskan kowa cike da farinciki.
Asma’u ce ta shigo kwanar su Raj ta zauna bakin bed dinta tace” aunty Ruqayyah gashi wnn mama tace na baki” ta mika mata 5k sae kuma wata leda tace wnn kuma ya Hafeez me yace na baki kuma yace idan kika koma gda zaku gaisa”
Aaj tayi saurin karbar ledar ta bude tarkacen chocolate ne kala kala sae dan wani wrist watch mae kyau. Shewa suka saka ita da sadixy suna tapa wa sadixy tace bana gaya miki ba hmm an gode Asmeey Raj banza ta musu ta kama hannun Asma’u suka tafi ta gyara mata kayanta ta shimfida mata sabon bedsheet dinda aka kawo mata mae zanen Micky mouse ajiki. Bayan ta gama ta koma daki suka cigaba da fira .
“Wlh kin san idan ba kaewa skl moda na wani abuba zamu bata da ita” ai ko Bata l rufe baki ba sae ga ta wae zata taya ta gyaran kayanta nan ta raba provision din biyu tace zata ajiye mata wnn har bedsheet dinta ta dauka suka tafi.
Washe gari aka kawo new student mata twins baza su wuce shekara 12 suna kama sosae dan baka iya banbance su. Mama principal ta hangi sadixy ta kirata ta hadata dasu aka basu daki dan yau Sunday ba class bonk daya baka komae nasu iri daya.
*Aljanu day*🤣
Wata Asiya ce aljanunta suka tashi zoku ga duka wayya students sae gudu suke dan kowa yasan idan aljanunta suka tashi ba sauki komae tasamu kwadama zatayi. Nan fa sisi baby ta zube kuzo kuga style din tafi gaba daya jikinta ya lankwashe tafiya take kamar spaghetti sae yanga take tana kwasar dariya nan fa kallo ya koma gunta tsayawa tayi cak sae ta fara rawa Kamar yar bori da kaga kalar rawar kasan bata masu hankali bace. Asiya ma na can sae gudu take zabgawa tana isa area classes ta zube tana buga kanta ga kasa.
Aaj kuma da nata ya tashi ihu kawae take tana kuka dan ita idan suka tashi bata hauka sae dae tayi ta kuka idan ta gama kuma ta kwanta baccin da bawanda yasan ranar tashinta.
Gaba daya students hankalin su a tashe yake nan aka hargitsa makaranta gaba daya abunka da mata liman ne yazo ya fara taimakon su yana musu ruqiyya wasu kuma sae zubewa kasa suke.
*Monday* _Busy day_
Tunda students suka tashi suketa shirye shiryen zuwa classes bayan an gama assembly kowa ya shiga class.
Da  dare bayan sun gama  lunch suka shiga prep 9:27pm generator ya mutu abunda basu taba gani ba nan fa suka saka ihu suna fitowa waje tsoro ya kara kamasu gashi jiya anyi rawar aljanu baka jin komae sae ihu wasu Kam har sun fara kuka new students dinda aka kawo Nabeela da Fadeela kam ae kuka kawae suke daga zuwan su jiya anyi wasan aljanu yanzu kuma ga wuta ya dauke cikin wnn dajin ga nisa hostel da nisa. Ai fah daga nan kowa ya gudu hostel prep dinda ba’ayi ba kenan……….
.washe gari mama principal ta hada musu assembly na kansu fada take tayi sosae kan abubuwan dake faruwa nan ta bama SS3 punishment for 2 days shara compound din makaranta 2times a day hmm Juniors abun so ya samu daddy 501 aka saka ya yankawa kowa portion dinshi mae shegen fadi sae dariyar mugunta yake.
+
Da yamma sauran students suka fita prep jss1 sae shige ma twins sukeyi note din Asma’u da wata fareeda suka ara suna copying note.
Da dare Nabeela tazo wuce wa bata kula ba ta dan bangaje bosa juyawa tayi tace”kan bura uba wace yar iskar ce mae ido a tsakiyar Kae ba bugeni”
Haba Nabeela na Jin haka ta zuba da gudu duk Kiran da ashar dinda bosa keyi bata juyowa ba.
Washe gari suka hadu da Fadeela Nan ta hau dukanta tace”ke dan ubanki ni zaki buge juya ki gudu ba’a taba yar iskar yarinya irinki ba wlh zaki sani ungu karba cigaba da sharan”
Share hawayenta kawae tayi dan tasan Nabeela ce dama duk inda suka je sae ta nuna halinta kuma ta gudu sae dae karshe a kama Fadeela a jibka.
Bayan kwana biyu ss3 sun gama punishment dinsu kowa na class ana evening prep zeey ce tace”guys Kun San zamu iya fita skl din nan ba tareda kowa ya sani ba”
Suka ce tayaya tace”wancen hanyar ruwan da akayi idan muka duka ta cikinsa muka rarrafa shi zae Kae mu waje kuma idan Kuka lura staff basa fitowa during evening prep”
Ihu sukayi suka ce shegiya zeey shi yasa nake sonki yanzu yaushe zamu fara fita danni wlh dama na gaji da zama ko gda bazan je ba zan dae je ganin gari”
Faty tace”Ni bani da problem da ba Yar gari bace Kinga ko ba Wanda zae ganni” haka suka cigaba da shawaran yanda zasu fita skl din.
Bayan kwana biyu zee da faty suka shirya duk wani Mae sako ya bada haka suka saka zani da T-shirt sae hijab suka dinga crolling kasa har suka fita kana suka mike……..
………. Sae da suka tabbatar an shiga night prep kana suka dawo cikin skl bayan an tashi prep kowa ya kwashi kayan karatunsa ya koma hostel. A can suka yada zango nan fa suka fito ma da kowa sakon shi suka bashi sae ihu sukeyi nan suka yanke shawara duk bayan kwana biyu zasu rika fita idan suka ce kullum to za’a Kama su ne.
Dare mahutar bawa kowa kwanta a gadon sa sae sharar bacci suke. Aaj sadixy nuwaira da faty ne suka fito zasuje toilet Aaj mae touch light a hannu mistakenly ta haska wata yar ss1 Zubaidah gaba daya jikinta a bude gashi ko pant bata saka dagani ma maybe wanka tayi bacci ya dauke ta dan towel ne a jikinta amma ya koma gefe blanket dinta kuma ya fado kasa. Da sauri Nuwaira ta daka mata duka a cinya a gigice ta tashi tana neman towel dinta kasa Aaj tayi da touch din sae da ta daura towel kana sukace ta saka kaya bata tsaya b’ata lkc ba ta saka sukayi gaba.+
Ruwa suka tsaya zasu debo a bucket faty ce mae pumping ruwan haskawan da Aaj zata sukaga jini na zuba haba sae ihu suka kwasa da gudu zasu bar gurin wata classmate dinsu Laila suka gani zataje debo ruwan sukace mata jini banza ta musu ta wuce abunta tana waka. Bayan ta fara pumping ruwan taga jini haka ta cigaba har sae da ya cika kana ta dauka ta wuce area classes dama sune Yan cult sunan group dinsu *pink Ladies* su 15 ne ss3 biyar sae sauran yan ss1 and 2 ne.
Su sadixy bacci ma gagaran su yayi gaba daya tsoro ya shige su zafin da suka fara jine yasa sadixy tashi ta bude window dama akwae bushiya a kusa da room dinsu budewan da zatayi taga Shafa’at sani a gurin ana mata kitso ihun da tayi ne yasa su Aaj Kara tsorata Raj da Husna dake bacci suka tashi gaba dayan gurin window suka nufa suma suna ganin abunda ke faruwa suka saki ihu gaba daya suka fita dakin da gudu hakan yasa wasu students tashi daga bacci a hostel dinda ke kusa da nasu kuma gudun kato ake gaba daya students sun haukace sae ihu suke hakan yasa wasu staff da basu kwanta ba Jin hayaniya suka fito da gudu amma ba’a samu nasarar kama katon daya shiga hostel din ba.
Washe gari bayan sun tashi breakfast su sadixy sukaje office din mama principal suka mata reporting abunda suka gani fada tashiga musu tana kiran karyane ita bata yarda ba haka suka dawo class sunata zaginta Shafa’atu sani Kam bata ma  san sunayi ba.
Bayan an koma class B/tech teacher din jss1 ne ya shiga bayan sun gaida shi suka zauna kallon twins din yayi yace su tashi haka kuwa akayi bayan sun mike ya maida Nabeela gaba ita kuma Fadeela baya Nabeela sae antaya mishi harara take akan ya raba su.
Haka da suka cigaba da rayuwar ta y’an boarding gaba daya kowa ya matsu ayi hutu especially su sadixy da suka ganiwa kansu tashin hankali.
Bayan kwana biyu Asma’u skl dota din Raj ta kwanta ciwo sosae kamar bazata rayu ba ganin ciwon nata yayi worse yasa aka maidata gda a gidan ma ba sauki sunje hospital dr basu gane matsakanta ba aka basu shawaran komawa na hausa wata kanwar mom dinsu ce tace a kaeta gurin masu maganin mayu a gani sbd harkar boarding sae a hankali.
Bayan sunje mutumin yace”hajiya Allah ya taimaka kun kawota da yuri jininta ne ake sha hakan yasa kuga ciwon nata ba sauki a ciki nan ya basu wasu magunguna yace kuma a tabbatar an kama masu Shan jinin idan ba haka ba zasu rasata.
Direct skl dinsu suka wuce suna zuwa office din principal suka shiga nan maman Asma’u ta Mata bayanin komae tasa aka kira mata Raj.
Su biyu sukaje itada faty bayan sun gaisa suka tambaya jikin Asma’u tave da sauki. Mama principal ta musu bayanin abunda ke faru da sauri faty tace”mama ranar da dare munje dibo ruwa bayan mun fara pumping muka ga jini sae muka bar gurin da gudu a hanya muka hadu da Laila da muka mata bayani banza ta mana”
Mama principal ta aika aka kira Mata Laila da taji abunda ke faruwa hankalinta ya tashi batayi tunanin Asma’u zata Kae wnn lkcn bata mutu ba. Da sauri tace”karyane ni ruwa na gani ba jini ba” mama principal ta kalli maman Asma’u tace” kiyi hkr hajiya zamuyi bincike yau komae ake ciki zan gaya Miki.
Bayan an tashi class mama principal ta kira gaba daya su sadixy da suka je dibi ruwa a daren amsa daya take samu a gurinsu nan ta kira Laila bayan tazo ta fara kawo Mata gardama ta aika aka kira nata Sargent ya dinga dukan Laila amma taki fadan gsky sae da tasha wahala kana tace ehh sune ke Sha mata jini gaba daya hankalin kowa na gurin ta tashi dama duk class din ba’a yarda dasu biyar din ba shi yasa ba Mae shiga harkar su. Nan take principal ta kira iyayensu a waya ba duka suka zo ba dan sauran ba Yan gari bane sae da aka tabbatar sun daena shama Asma’u jini kana akayi expelling dinsu daga skl din nan kayi emergency meeting.
As usual da dare lkcn prep biology teacher din ss3 yazo gurin hauwa dama itace buduwar shi can cikin daji sukaje yau Kam zuwan nashi yazo da sabon salo dan sae da yayi romancing dinta sabanin da fira kawae suke. Hmm nan gaba kowa yasan abunda zae faru🤔..2 weeks ago*
Exams suka fara Nan kowa ya dage da karatu sosae marasa son karatun kuma na shashanci a hostel basa nan basa chan.
Ranar da yan jss zasuyi B/science dama shi Fadeela tafi iyawa Nabeela kuma mathematics bayan ta gama nata ta mikawa Nabeela paper dinta tayi submitting ta fita ita kuma ta zauna rubutawa Nabeela nata.  Haka ma ranar da sukayi math Nabeela ta musu exams din kae twins sun iya iskanci yasin😆……
…..Bayan sun gama exams suka fara Shirin komawa gda murna Kam ba’a mgn bakin kowa ka gani a washe Kamar gonar auduga. Ko Ina ka leka hifimar hada kaya ke *daga yau sae gobe jibi gda koda tsallen kwadi sae munje* 🤸🏻‍♀🚴🏻‍♀
Kae yasin boarding da dadi alkur’an idan akace za’ayi hutu jikake Kamar an gafarta ma ne😆
+
Ranar Friday da yamma suka shirya wasan da zasu da yamma kusan duka rabin skl suka hallara a skl compound wanda hakan dabi’arsune duk zasuyi hutu ana gobe gda zaka gansu suna wasar gada kowa zae daura zanin sa da Yar t-shirt ya fito suyi circle suna wakar ayye yaraye Oga *Bosa* ce ta fara bude musu fili da wakar _idan da Allah sae nayi aure gdan nera Ina taka ne in juya nera in hau nera sae tommorow Allah bamu kairin masoya inada yata da baza na baewa fulani ba meye dalilin da bazaki baewa fulani ba kwana a daji yini a daji Kamar kura sae tommorow Allah bamu kairin masoya_ wannan ce best wakar Bosa shiyasa da ta shiga dandali da ita take fara budewa.
Haka suka dinga wasan su yayin da wasu kiwa suna cen suna karasa hada kayansu wasu kuwa kitso sukeyi haka dae kowa da abunda yake keyi
_yasin idan bakiyi boarding ba an barki a tashar dan hauwa_⛹🏻‍♀
_Washe gari_
Ta kama Saturday kowa yatsuke cikin wankan shi na hostel wears da suka Sha guga suna Kiran kwae a zo daukan su su Raj Kam 9am Yaya kabeer yazo daukan su dama tare suke tafiya su uku Raj, Aaj, sadixy hakan yayi dae dae da zuwa daukan Asma’u santali wacca Hafeez ne yazo daukanta Raj na ganinshi tayi kasa da Kae sadixy kam dariya abun ya bata matsowa yayi musa da su yace “sannun ku Yan makaranta hope kun ganeni”
Sadixy tace”sosae ma ba Kae bane yayan Asma’u santali?”
Yace”ehh nine ya exams”
Tace”lpy alhmdllh”
Aaj dake tsaye tace”sannu”
Yace “yauwa”
Hakan yasa itama Raj dole tace mishi sannu sae da ya kalleta sosae kana yace”aunty Ruqayyah ya exams”
Tace” alhmdllh yasu mama”
Yace”suna lpy what’s is ur position ko ba’a baku result bane”
Kasa ta karayi da kanta dan Ruqayyah na dae kunya ba tace”an bamu Ni nayi na 3rd”
Smiling yayi daya bayyana dimple dinsa yace”wow Masha Allah may Allah bless your knowledge”
Tace”ameen”
Sadixy tace”oh aunty Ruqayyah kadae aka sani mu baza a tambayemu ba ballantana Musa ran addu’a”
“Ohh sorry sis ba haka bane ai ban gama tambayar bane”
Tace”ba wani ko Aaj”
Tace”ehh”
Dawowar Yaya kabeer daga office din principal ne y katse musu fira bayan sun gaisa da Hafeez suka wuce shima ya dauki ma’u suka wuce
A mota sae tsiya suke ma Raj a haka har suka isa gda sae da suka Fara ajiye sadixy kana suka wuce gda
Asma’u ma a mota tana ta bawa Hafeez lbrn aunty Raj sbd itace 1st tana gaya mishi ne yanda Raj ke sakata karatu sosae ta kuma bashi lbrn twins dinda aka kawo musu da irin shakiyancin da Nabeela keyi a kana fadeela a daka..
Da murna suka shiga gdan aunty zaunab na nan dama ita unguwar take shi yasa kullum zaku ganta a gda da gudu suka shiga cikin parlourn suka makale mama da itama take musu lale da zuwa maman birnin kebbi ma nna wato maman Aaj itama tarbansu tayi sosae cike da jin dadin da wowar yaran nasu Nan fa suka baje a parlour ana fira bayan da mama batayi da su ba akan su tashi suje su cire Kaya amma sunki…….
_nima daga haka naje nawa hutun sati ukun kafin mu koma makaranta muga abunda zae faru Amma kafin nan zamuji a gdan ma abubuwan zasu tafi_
*Manage pls kwana biyu sae a slow wlh ku tayani da addu’a sisters* 
Bayan kwana biyu da hutu su Raj aka shirya sae birnin jega gaba daya farinciki suke dan rabon su da jega tun sallah suna so suje suga y’ar kakarsu abokiyar fadan su.
+
Tafiyar awa daya da rabi ta kaesu jega da gudu Raj ta fita sae cikin gda hakan yasa yan gdn suka gane sun iso Yan matan gdan suka fita tarbo maman skt tun a waje aka fara oyoyo ana murna da farincikin ganin juna bayan sun shigo da kayan suka shiga dakin hajiya domin gaidata
Raj ce ta fara shiga tace”hajiya Ina yini”
Kallonta kawae tayi tace”uhmm ai ba yanzu Kika shigo ba Ina Jin lkcn da yan uwanki ke Miki oyoyo to shina ni sae yanzu Zaki zo gaida Ni bana so tafi abunki”
Gajeran tsaki Raj tayi tace”hmm matsalar ki”
Hajiya tace”me kike cewa”
Raj tace”aa Yar tsohuwa bada ke nake ba”
Hajiya tace”ga uwarki can da ita kikeyi ja’irar yarinya”
Mama ce ta shigo bayan sun gaisa ta hajiya tace “Ina husae?”
Hajiya tace”ta tafi argungu amma gobe zata dawo”
Mama tace”Allah ya kaimu goben lpy”
Hajiya tace “ameen ya hanya”
Mama tace”lpy hjy mun same ku lpy”
Hajiya tace”toh lpy Kam kin San jiko da jini”
Mama tace”haka ne Allah dae ya mana afuwa” ta amsa da ameen.
Da dare bayan sallah isha duka Yan matan suna zaune a dakin su da suke zama idan sunzo family hause din nasu fira suke abunsa sae kwasar dariya suke
Yaya bg tace”Ruqayyah Ina yaron da muka gani gurin visiting dinku”
Dariya kawae tayi tace”Kae ya Bg Ina na sani nifa ko kanwar shi bamuyi waya da ita ba”
Salma dake gefe tace”su y’ar ruqucy manya to wa aka samu kuma”
Dariya sukayi gaba daya sumayya kanwar Raj tace”help me ask”
Raj tace”Kae nifa ba Wasa nake daku ba tam”
Dariya suka saka gaba daya dakin Asma’u dake gefe tace”dadina dake sis shegen son girma dudu bae shekara uku Kika bama sumayya”
Tace “ehh naji ai ko ban bata shekara dari ba na Bata kwana dari marasa kunyar yara”
Ya Bg tace”Kae amma dae Kun San ba’a dakin Nan zaku kwana ba ko”
Shewa sukayi Aysha tace”kinji Yaya Bg da wani zance to a Ina kike so mu kwana idan ba’a nan dinba so kike hjy ta cinyemu gaya ba miya ne yau?”
Dariya sukayi Raj tace”daga zuwana dazu sae da mukayi fada ita hajiyar nan ba Mae iya Mata ba y’ay’an ba ba jikoki ba kowa yi take dashi”
Dariya sukayi aunty maimuna dake zaune tana jinsu sae yanzu tayi mgn tace”toh banda cin fuska” da yake yarinyar kanin hjiy ce
Ya Bg tace”ba wani cin fuska dazun na gama Jin kina complaining ta Miki wani abu”
Aunty maimuna tace”ehh naji amma dae yanzu bazan bari ku hayayyaqo ta ba nasan da mutum daya cikin ya fara sauran ma zasu dauka ne”
STORY CONTINUES BELOW
Dariya sukayi Asma’u ta dauki wayar ta kunna waka Nan fa suka fara competition din kumma waka dama dabi’arsune da mutum daya ya kunna zakiga kowa ya fiddo wayar sa ya saka tashi aunty maimuna ta ciro earpiece dinta ta saka tace”matsala na daku ke Nan wlh yanzu zaku maeda Mana da daki Kamar tasha”
Dariya kawae sukayi.
Hajiya da tazo wuce wa taji sautin kida na tashi taja tunga ta tsaya abakin kofar dakin nasu labulen ta daga cikin fada tace”ga kaza uba, wane irin iskanci ne Zaki maida Mana gda kamar tasha wlh yanzun nan xan koreku gaba daya sae dae kune wani gurin ku kwana sbd tsabar iskanci da tashe balagar tsuntsaye zaku wani sakar mana kida to bari iyayen naku maza su shigo naji wannan gdan gadona ne Ni kadae daga ku har iyayen naku sae na koreku Naga ta tsiya yanzu”
Gaba dayansu shiru sukayi suna dariya kasa kasa Salma tace”wae hajiya kin manta da Musa Habib din zae mutu ya gaya Miki kishiyoyin ki zasu zone sae faman fadan kike ke daece da gda muma ae munda gado tunda mune kishiyoyin naki koya kukace sisters”
Dariya sukayi suak hakane sumayya tace”Allah baki hkr hjy ae ba sae kin koremu ba zamu bar Miki gdan nan da kwana biyu”
Karasa shigo dakin tayi ta nufi inda Salma ke zaune zata maketa tayi saurin barin dakin da gudu tana dariya hajiya tace”kudae kuka sani yara sae rashin kunya gaku duka Kun isa aure amma kun tsaya wae sae kunyi boko to ae saemu ga ta tsiya bokon ya kawo muku mijin aure mu gani”
Ya Bg tace”wlh Allah sae zae kawoshi wae hjy kin manta aure lkc ne dashi idan lkcn yayi ae dole sae anyi”
Tace”ehh ammaae da niya”
Asma’u tace”nifa hajiya ba wani aure da zan karayi bazan yaudari mijina ba tunda ya rasu Nima aure a gurina ya rasu”
Hajiya tace”ungo nan maras kunyar yarinya gaba daya Kun fandare kunfi karfin kowa bari dae yayan naku ikraman ya dawo”
Dariya sukayi Aysha tace”to me zae mana shine ya haifemu ne ko shi zae Basu mijin auren?”
Hajiya tace”aa ubanki me zae bada”
Tsaki tayi tareda murguda baki”
Hajiya tace”bani kikama ba uwarki kikama”
Tace”wlh ba dae uwata ba hajiya ki fita idona fa tom”
Dariya sukayi duka dakin hajiya tayi kanta gadan gadan ta ruga da gudu waje”
Tace”Yar isiya da Kin tsaya ai”
Fita tayi ta bar musu dakin tana masifa.
_washe gari_ tun a gurin tashin asuba suka fara fada da hajiya bayan ta shigo dakinsu ta kunna bulb din ta fara tashin su a lkcn ana batun Kiran sallahr farko dama sun san halinta shi yasa ba Mae kwana dakinta dan yun karfe uku zata tadaki wae ki tashi sallah ki gayawa Allah bukatarki shi yasa ba Mae kwana dakinta.
Bayan sun tashi ta fita tana masifa “yara sae shegen son kwanan wahala shiyasa ai kuke ma mutane rashin kunya son ranku na tabbata duk wani dan musulmi koda jaririne idan akayi Kiran sallah sae y motsa ballanta ku godan godan daku ace sae an tadaku” haka tayi ta masifa.
Bayan sunyi sallah suka zauna fira masu komawa bacci suka koma.
Da misalin karfe 7am hajiya ta shigo ta taras dasu wasu suna bacci wasu kuma suna fira sae da ta gama kallon su tsaf kana ta shiga tada masu bacci gaba dayan sae magahin bacci suke Mata ganin haka yasa tace”Bari na debo ruwa Zaki sani”
Ai ba shiri suka tashi suna misika ido tace”manyan banza kannin ku duk sun tashi Amma ku kuna Nan kuna baccin asara ku tashi ju gyara min gda kun san bana son kazanta sakarkarun yara kawae”
Ya Bg tace”hajiya kenan bazaki ko Bari mu gaisa ba kin hau fada da uwar safiyar Nan”
Hajiya tace”uwar kice mai fada ba Ni ba zaku tashi ko sae na Saba muku”
Tashi sukayi suka fito tsakar gdan a cike iyayen su maza na zaune bayan sun gaida su suka raba aeki wasu sukayi wanke wanke wasu kuma shara da mopping Mai aiki tayi musu breakfast.
Bayan sun gama suka dawo tsakar gda suka zauna gefe daya kan tabarma suna fira hajiya ta kallesu tace”aikin kenan zaman banza”
Ya Bg tace”oh ni Bilkisu hajiya wae Dan Allah me muka tsare Miki ne?”
Baba Aminu dake zaune kusa da hajiya yace”gidanku kuka tsare Mata yanzu uwar tawa kike ma haka a gaba anya kuwa y’a balla kina so mu shirya”
Dariya kwae tayi tace”Allah baba tun jiya take takura mana dama hajiya da taga an cika gda sae ta hau fadan rashin dalili”
Baba Aminu yace”Allah ya shiryaku.. ya kalli hjiy yace”Ni zan tafu hajiya sae kuma anjima idan Bashiru yazo kice ya kirani”
Tace”toh shikenan Allah ya bada sa’a”
Yace”ameen” ……….

…….Da misalin karfe 11am mama Husae ta sauka gaba daya gdan ya kuma kicimewa da hayana Kamar ana biki ko sallah tsayawa fada muku irin kaunar da wannan dangi kema junansu bata lokaci mutanen waje ma basa gane dan wannan da na wannan haka suka taso cikin so da kaunar junansu tundaga iyayensu har kansu yaran.
+
Bayan an gama gaisawa Yan matan gdan akalla sun Kae set hudu kowa da grp dinsu haka sukayi wanka suka shirya cikin wani rantsatstsen lace iri daya sae dae kowane gda da kalar nasu Su suke da Mae background black da touch of baby pink sae ya Bg ita kadae ce mace a gidan su nata gray sae Yaran baba Aminu suke da orange da lemon green sae Yaran baba Bashiru suke da ash and red sae Yaran baba Murtala kuma green da toch of pink haka ma yaran aunty Asma’u da aunty zainabu red and black gaba dayan su sunyi kyau dama Yan matan gdan badae baya ba gurin wanna kowa so yake ace yafi kyau.

Shiryawa suke dan su fita da wuri idan ba haka ba yanzu hajiya zata jajibo musu wani aiki Aysha dake zaune bakin gado daure da towel dagani fitowar ta kenan daga wanka ta tsaya tana kallon su gaba daya sun wani baza kayan makeup a daki sumayya dake shafa eyeliner ta juyo ta kalleta tace”kut lallaima wato ko Mai Baki shafa ba bare aje ga maganan Kaya zauna kina kallon mutane Allah tafiya zamuyi mu barki a Nan yarinya.

Itadae Aysha dariya kawae tayi tace”so nake na gama ganin wankan kowa ne kana nasan wane iri zanyi ni”

Dariya duka Yan dakin sukayi Asmeey tace”dan ki tashi ki shirya kin San ke Zaki daura min dankwalina”

Nasma dake gefe tana kallon mirror tace”Asmeey daga ke sae ni”

Ramla ma tace “nasma bayanke”

Haka suka dinga jera layi itadae Aysha sae dariya takeyi sumayya tace”wae ana Miki mgn dan Kinga suna binki ne kome?”

Bata ce komae ba sumayya ta cigaba da cewa”shiya kukaga Ni na daura kayana ban tsaya jiran kowa ballanta a rainamin hankali”

Asmeeey tace”ai wlh ko sama da kasa zasu hade sae ta daura min shi”

Itadae Aysha dariya ne kawae nata Mae ta dakko ta shafa bayan ta gama ta saka kayanta kana ta Shiga daura musu dankwali simple one ta musu Zarah Buhari  san da tagama musune kana ta shafa powder sae wani pink lipstick da tasa kadan sae liner da mascara ta zauna daurin dankwalinta itama Zarah Buhari tayi sae flat shoes dinda tasa da veil a waje ta taradda su suka sae pins sukeyi itama tayi joining.

Chann na hango muku Raj sae wani glowing takeyi tayi kyau abunta sae wasu hills da ta saka 6 inches abunka da mutum mara tsawo pics sukeyi gaba daya gdan har aunty Ameena data fito saeda tayi joining dinsu.
Hajiya ce ta hango ta window din dakinta ta fito waje sae da ta gama kallonsu tsaf kana tace”aikin kenan ayi wanka abi titi yanzu wannan tsinannen abun zaku saka ku fita a ganinku wae Kun rufe jikin ku”

Ba Wanda yabi ta kanta sae ma saurin da suke su fita karta tsaresu .
★★★★★
Bayan kwana *Asma’u santali* (skl doata din Raj) ta kirata a waya bayan sun gaisa  take tambayar ta ina mama Asma’u tace”tana lpy tace a gaida ke”

Raj tace”toh Ina amsawa ki Mika min sakon godiya gurin yayanki na kayan da ya bada”

Asma’u tace”toh aunty Ruqayyah sae mun Kara waya”

STORY CONTINUES BELOW

Nan sukayi sallama

*****
Da dare suna zaune a daki sae ga Kiran waya unknown number banza tayi da call din harta tsinke aka kuma Kira nan ma banza tayi sae da aka kira a na uku da Kamar bazata dauka ba sae kuma tayi picking bayan ta saka wayar a kunnenta tayi shiru tana jiran ayi mgn daga dayan bangaren aka ce”Aslm Alkm”

A hankali tace”wslm”

“Da fatan kina lpy”
Tace”lpy”

Yace”Masha Allah” sae kuma tayi shiru
Tace”who am I unto plss?”
Cikin wata murya yace”Hafeez”
Sae da gabanta ya fadi Jin wanene a hankili tace”wane Hafeez din?”
Yace”yayan Asma’u santali”

Tace”ohh yauwa dama inaso na gode ma thanks for ur gift”

Yace”my pleasure dama nace ne Bari nakira mu gaisa”
Tace”ok thanks Ina gaida su mama”

Yace”zasu ji”

Nan sukayi sallama Aaj dake gefe ta sheke da dariya ta dauki wayarta ta dannama Sadixy kira tana dauka tace”hmm lbr da d’umi d’uminsa baby”
Cikin zakuwa sadixy tace”ban na sha meyene?”
Aaj ta kuma shekewa da dariya”tace mutumin Raj ne ya  kirata yanzu”

Da sauri sadixy ta mike zaune daga kwancen da take tace”dan Allah”

Aaj tace”wlh yanzu suka gama waya”

Jin haka yasa Raj gane mgnr da sukeyi tace”munafukae kawae a hakan Zaki kare”

Aaj tayi dariya tace”wannan ke kika sani”

Nan suka cigaba da firar su da  sadixy bayan sun gama sukayi sallama
Ya Bg dake zaune tace”Aisha Allah ya shiryaku keda sadixy’

Aaj tace”ameen ya Bg”

_____★

Haka suka cigaba da hutunsu gdan hajiya kuma yanzu a kullum Hafeez sae ya kira Raj da safe as early as possible zae tura Mata message hakama da dare..

Yau Saturday sae shirye shiryen koma sokoto suke sae da yamma suka tafi cike da kewar Yan uwa.

Bayan sun isa suka bada kayan su a na skl a wanke sbd gobe zasu fara shiri.

Washe gari suka shirya sukaje gdan su sadixy bayan sun gaisa suka shiga fira Nan take gaya musu mamanta tayi wani aure gaba daya sae sukayi wani iri sadixy tace”Kae nifa nafi son haka wlh”
Aaj tace”toh muje mugaida aunty”

Sadixy tace”Bata gdan tunda na dawo wae sun tafi umarah”

Raj tace”toh dawa kuke zama a gdan?”

Tace”masu aiki Mana Ni Allah yasa ma banida Kani ko kanwa a gdan Nan”
Raj tace”toh Allah ya kyauta”

Nan suka shiga tattauna akan abunda zasu siyo idan zasu koma dan idan suka tafi yanzu baza su dawo ba sae sun gama suka tsaeda jibi zasuje kasuwa. Sae dare suka koma gda.

Ranar da zasuje kasuwa tun safe suka fita a gda sukaje gdansu sadixy dan driver dinsu ne zae kaesu haka suka dinga yawo cikin kasuwa Basu koma gda ba sae kusan magrib.

…………..•°•

Yau ta kama Saturday  kuma a yau ne su Raj zasu koma skl sun shirya komae nasu tsaf suka fito da kayansu suka ska a mota dan sae da yamma zasu koma.

Gaba daya sunyi wani kalar tausayi Kamar basu ba sumayya da Abdulnaseer sae dariya suke musu akan zasu koma haka ma Aunty zaynab sae tsokanar su take Raj harda hawayenta.
Da yamma.ya Habeeb yazo daukan su Dan shi ne zae Mai dasu skl din.
Bayan ya ajiyesu akayi musu checking kana suka ja kayansu zuwa hostel tundaga nesa Yan uwansu ke musu sannu da zuwa Nan suka hadu da sadixy tama rigasu dawowa daki suka Shiga sae da sukayi settling kayansu kana suka shiga room by room suka gaisawa da classmates dinsu cike da Jin dadin ganin juna……

………washe gari Sunday sauran students suka dawo ciki ko harda Asma’u santali duk yanda Hafeez yayi su hadu da Raj taki bari dole ya hakura amma ya bada sako a Bata.
Da yamma suna zaune suna firar gda da abunda ya faru sae ga Asma’u tazo hannun rike da leda sae da ta gaidasu kana ta bama Raj leda din hannunta tace gashi inji Yaya karba tayi tace”nagode”
Itadae Asma’u smiling kawae tayi ta tafiyanta
Sadixy ce ta karba ledan ta shiga budewa perfumes ne guda uku masu tsada sae chocolate kala kala da hard cover guda biyu masu kyau daya pink dayan kuma red sae wasu pens da pencil masu kyau na Yan gayu sae wata paper.
Da sauri ta saka hannu ta wabce paper din daga hannun sadixy dake korakin budewa.
Dariya suka saka gaba daya ta mike ta bar musu dakin.
____________★
Hajiya Bosa ce zaune ta hakimce a kan gadonta daga dawowar wata yarinya yau harta fara cin zalinta akan wae ta bugeta da blanket dinta Bata sani ba kneeling ta saka ta tareda daga hannunta sama ta daura Mata wani karamin fashion bucket cike da ruwa kuma idan ya zube tasan sauran.
Duka da hawayen da yarinyar keyi baesa ta hakura ba sae ma lbrn ta da suka cigaba dayi.
Sae guraren 4pm ta barta ta tafi sae kuka take yarin bayan ta koma dakinsu ta gaya musu abunda akayi nan suka shiga planing yanda zasuyi ma bosa Dan ss2 sun tsane ta kuma tsabar iskanci harda su da suke immidiate juniors dinsu basu kyale ba. Dariya sukayi dukan su suna Kae Linda Baki da mutunci
Wacce aka kira da Linda tace”haka kawae zamu zuba ido ana cin zalinmu baza nu rama ba”
Amina Ado tace”wlh Ni na matsu a bamu shadow”
Dariya sukayi duka
____________★
Haka rayuwa ta cigaba da tafiyar masu yanda suka Saba irin rayuwar su ta *Yan Boarding*
Ranar Tuesday da dare Bayan sun dawo night prep ss2 suka da dama sun gama shirya plan dinsu suna jiran Bosa tazo wuce dan Bata tafiya da wuri sae a Yan karshe.
Tana tafiya cikin sauri tana Kiran Yan dakinsu su jirata taji yani wup da ita cikin blanket sae janta sukeyi har sukayi nisa da matane Nan suka shiga jibgarta babuji Babu gani sae ihu takeyi amma a banza haski su dinda akayi ne yasa su gudu a 360 metron dinsu ce ta karaso tana subhanallahi waye suke duka haka koda ta bude sae taga bosa bakinta yayi suntum ga face dinta ya kumbura sae fitar da numfashin walaha takeyi tana kuka.
Da taimakon Inna A’ee suka karasa hostel Yan dakinsu sae dariya suke mata cikin kuka tace”wlh sae naci uban Mae blanket din Nan wlh”
Daya daga cikin su ne tace” aikin banza sae dae kici ubanki dan blanket naki ne”
Kara kallonshi tayi sae kuma ta fashe da kuka Kamar wata yarin me Yan dakin zasu in ba dariya ba…..
..Washe gari da kyar Bosa ta shirya ta tafi class fuskarta tayi suntum gaba daya a class ma da teachers suka tambaya sae tace faduwa tayi.+
Bayan break mai can CPU (computer teacher) ya shigo kallo daya yama Bosa ya kwashe da dariya sae da yayi Mae isarsa kana ya tsagaita yace”what happened to you”
Kuka Bosa ta saka Nan fa yan class suka shiga dariya sae da malamin ya tsawata kana sukayi shiru ya fara lesson.
_____________★
Daddy 501 ne ya shigo class dinsu Raj yana checking trousers dinsu Yana kawowa kan Raj ta bude window ta zuba da gudun bala’i Bata tsaya ko Ina ba sae hostel gaba daya yan class din kallo suka bita dashi dan sun San dae ba Wanda ke matse wandon shi amma Mae yasa ta gudu.
Hakan ya tunzura Daddy 501 ya fita fuuuuu Kamar zae tashi sama  shi kadae yasan me zae mata bae tsaya ko Ina ba sae female staffroom malama shafa ya gayama abunda ya faru itama dama ta sakama Raj Ido neman abu kadan takeyi ta hukunta ta. Tace”karka damu daddy zanyi maganinta Allah ya kaimu gobe assembly”
Yace”toh shikenan”
……………★……………..
Raj Kam tunda ta isa bakin gate din hostel ta tsaya tana haki sae da numfashinta ya koma normal kana ta zauna tana mgn ita kadae”kut Raj what have you done lallai na jama kaena bala’i nasan gobe sae an min assembly na kaena wlh 🤣 kae Raj kina wuta wlh hmm mgnr cin ubana ne gobe” haka ta dinga mgn ita kadae Kamar wacce ta zare sae da aka tashi kana suka shiga  hostel *topic of discussion* gaba daya lbrn abunda Raj tayi yabi hostel kowa da abunda take cewa.
“Wlh gobe zakici ubanki  Raj shegiya ga tsoro ga rashinjin mgn”
Dariya Raj tayi tace”hmm wlh Ni kaena na sani gobe sae nayi gashi”
Dariya suka koma shekewa da ita Raj ta Bata fuska tace”wato ma dariya zakuyi ko”
Aaj tace”toh da kuka kike so muyi idan ba iskanci ba ubanme ya kaiki saka wannan wandon”
Kwantawa Raj tayi tace”kudae kuka sani dadin abunma aiba Ni kadae na rage wandon ba harda ku”
           _____★_____
Washe gari da safe kowa ya shirya zuwa assembly  su Raj kuwa wandon da ta saka jiya shi ta kuna sakawa yau taci uban acuci mazanta harda su saka powder da kwalli aka bada turare suka fita tareda su sadixy suna ta Mata dariyar mugunta ita kuwa Raj ta rantse da Allah bazata Bari a dake ta ba.
Bayan sun je assembly ground aka fara national anthem Bayan an gama akayiduk abunda za’a yi malama shafa ta fara checking Raj na ganin haka taja hannun ma’u suka koma can baya tace”Dan Allah ban Aron wandon ki nasan idan kece bazata tsaya checking da kyau ba” haka kuwa akayi a cikin layi t cire wandon ta Bata tana sawa ta koma gurin ta a lkn saura mutum hudu akawo kanta.
Malama shafa na zuwa ta daga hijab din Raj ga mamakinta sae taga wandon ta palingo babba Mae Fadi duk dama tsayin ya Mata yawa kallonta tayi ta kasheta da Mari tace”ubanwa zakima makeup a Nan tell me who is ur guy among ur teachers da Zaki mishi makeup?”
Raj dake dafe da face dinta tace”wako xanma kwalliya do u think har akwae staff dinda zanma makeup ne”
Zata koma Kae Mata wani slap Raj ta zuba da gudu sae class mamaki ya kama malama shafa dan tasan Raj akwae tsoro kodae Aljanu ne da ita? Suma su Aaj mamaki ne ya kamasu haka dae aka karasa assembly din kowa ya tafi class dinshi………..
……..kwana biyun nan Raj gaba daya ta tubure Kamar ba ita ba sae ka ranste da Allah Aljanu me damunta da anyi Abu zata zuba a guje sae idan sun koma daki ta bama su sadixy lbr akan wae Bata so a daketa ne so idan ba haka tayi ba baza su shafa Mata lpy ba .+
Yau ta kama Saturday basuda class Bayan sun tashi daga baccin sage suka kwashi kayan wanki si sae laundry wanki suke su hudu Raj sadixy Aaj da zeey Raj harda karbo kayan Asma’u suka wanke gaba daya.
Bayan sun gama Koda suka koma hostel mutane duk sun tashi kowa na harkar gabansa daki sukaje suka gyara komae nasu da suka gama sukayi wanka suka shirya sae dakin sauran Mayes dinsu Nan sukaji ana bada sako sbd yau za’ayi sneaking out zuwa kasuwa suma kudi suka bada a siyo musu waya karama da SIM card guda biyu sbd zasu saka a kawo musu waya idan za’a visiting tunda ba komawa gda zasuyi ba.
Da misalin karfe 12 sadixy ta zagaya baya Dan kwaso kayan da suka shanya Koda taje an matsar muau da Kaya gefe tace” kutumar Ina wace shegiya ce ta matsar Mana da Kaya geje toh koma wace yar iskan ce ta sameni”
Ta hada kan Kayan da aka shanya gaba daya tayi daki dasu tana masifa Koda taje daki su Raj suka tambaya ta gaya musu abunda ya faru dariya sukayi Aaj tace”sadixy case”
Tace”wlh sae Naga Kaya wace yar iskan ne……
……..yau ta kama Sunday kuma yau ne ake inspection a hostel dinsu kowa sae faman gyara yakeyi Dan ganin yazo na daya. Da khadeeja Hausa aka fara. Wata khadeeja da tunda safe take kukan yunwa wae Bata lpy ta tada fitina sae an dafa Mata indomie shine suka dakko stove suka dora. Ana haka ne suka ji ance ga madam Ruth Nan ta shigo da gudu suka dauki stove da tunkunyar sukayi waje a 360.
Ya mutsa face dinta tayi tana kallon kowa Kamar taga Kashi sae da ta zagaya ko Ina kana ta dawo with serious tune tace”Ina stove dinda aka kunna a hostel din Nan?”
Tsuru tsuru sukayi Kamar wadan da aka kama suna sata Maimaita tambayar tayi a tsawace kowa yace shi bane Kneeling ta saka su duka tace”kafin na dawo make sure Kun fito dashi if not…hmm”
Ta juya ta fita Yan Ameena house da sukaji lbrn abunda ya faru a khadeeja House da sauri Faty bombom cikin daga murya tundaga bakin kofa tace”Y’an small room madam Ruth na zuwa ku dauke stove dinku wlh” Nan fa aka fara rididdar boye rough food da sauri su Raj suka dauke duk wani abu da na cooking da suka San an hana su zuwa dashi sadixy da Rabash suka kwasa cikin Ghana mazgo sukayi jumping ta window din Yan large room Basu tsaya ko Ina ba sae cikin Bush inda suka ramin da suka Saba ajiye kayan suka tono suka zuba kana suka saka zani suka rufe suka mayarda kasar suka koma a time din har madam Ruth ta shiga hostel din da Sanda suka shiga ta window.
Ko Ina kamshi me tashi na room freshener komae na hostel din blue and white sbd kalar kayan y’an Ameena house kenan. Kallon Faty bombom tayi tace”kuma kuma da stove dinne?”
Tsuru tsuru tayi Kamar Mara Gaskiya kana ta girgiza kanta a tsawace Madam Ruth tace”da Kae na Miki mgn ne da Zaki bani amsa da ka”
Da sauri tace”sorry ma’am”
“Sorry din uwar ki if you repeat it again you will see what I would do to you Bush girl” ta juya ta fita, gwalo faty bombom tayi tana dariya tareda kwaikwayar yanda madam Ruth tayi duka suka saka dariya.
Sadixy tace”Allah ya taimake mu da mun yabama Aya zakinta yau”
Aaj tace”wlh kuwa Allah sarki Yan khadeeja House”
Madam Ruth bayan sun fita nana House suka je Suma komae nasu tsaf ko Ina sae kamshi yake sunyi decorations da yellow and white kalar house dinsu Suma. Fateema house ma ko Ina green and white sae kamshi ke tashi. Haka ma Aisha House duk nasu yafi kyau sbd Red and white kuma kunsan dole zaifi kyau(saura kuma wani yace sbd sunana ne nace yafi kyau😎)
Jameela hause kuma suke da pink and white komae nasu tsaf dan House dinsu yafi girma.
__________★
Madam Ruth bayan sun gama inspection din sukankoma khadeeja House da mamakinta Koda ta shiga kowa harkar gabanshi yake wata uwar tsawa ta daka musu da tasa sae da naji tsoro a razane kowa ya juyo da sauri sukayi Kneeling wasu ma har sun fita harkar gabansu.
Wayarta ta ciro ta Kira discipline master ba jimawa sae gashi ya zo ya kirata yace gashinan bakin gate Dan baa Bari su shiga hostel din. Korasu tayi gaba daya students din skl compound suka je Nan aka kira sargent ya fara dukansu Kamar Allah ya Aiko shi bayan an gama masu kuka nayi masu kunkuni nayi punishment aka basu dukan su duk da haka Basu fito da stove din ba juniors din house sae Allah ya isa suke Dan ba halin fada sbd sun San ubansu zasu ci a gurinsu bosa…….
…..Haka rayuwa ta cigaba da tafiya da dadi da ba dadi rayuwar birding dae kowa yasan sae kayi hkr azalunceka a hanaka kuka kuma dole kayi hkr Dan ba yanda ka iya.
+
Zaune suke gabada dayan su suna kallon wani India film a laptop din hafeesha gaba daya attention dinsu na gurin sae da sadixy ta kalli kowa kana tayi dariya sae ta Dan fita waje ta dawo da gudu tana “ku boye malama shafa da sauri suka cusata kasan pillow kowa ya kama gabansa dariya ta tuntsere da ita sae da tayi Mae isarta kana ta tsagaita tace” matsoratan banza gaba dayan bakwa tsoron Allah”
Chaaaaa sukayi kanta suna masifa akan ta katse musu kallo da sauri ta zauna kan gadon tace”dama dazun bana gani da kyau yanzu kuma dole gani fa Hafeesha Zan zauna”
Kowa ya fara wlh sadixy Baki isa ba kawae kowa ya koma gurin daya zauna.
Hade fuska tayi tace”wlh sae dae a gas kallon Nan Dan yanzu sae na Kae Kara gurin mama principal”
Hafeesha tace”abun bae Kae chan ba nikam Dan Allah ku zauna mu karasa kawae”
Bosa tace”aikin banza ki Kae Kara din wlh sae dae asirin kowa ya tonu sbd kema ae kinzo da waya”
Dariya tayi tace”da ake cewa bakida wayo ban taba sani ba sae yau a tunanin ki Dan kinje kin fada shi zae saka ache na fito da wayar besides bama yarda da mgnrki akeyi ba ko kin fada kinyi a banza yarinya Dan Allah Kama hanya ki tafi yanzu sauri sauri me Kika tsaya jira kuma”
Hafeesha tace” Kinga sadixy nikam ya wuce Dan Allah ku zauna mu karasa inaso idan aka kawo wuta Zan saka chargy”
Ba yanda suka iya sae dae suka zauna a hakan har aka gama kallon Dan sun san halin sadixy rass basae an fada musu ba.
_____________★
Yau ta kama visiting gaba daya makarantar ta kicime da hayaniya ko Ina kaje wannan Karan Hafeez bae samu yazo ma Ma’u visiting ba sbd ya tafi service sae dae ya bada sakonta Dana Raj.
A lokacin ne kuma ake gayawa su Raj basa nan za’ayi aure wata cousin sister dinsu Rasheeda abun bae damesu ba Dan ba shiri suke sosae ba.
*R* ayuwa sae tafiya take dan yanzu students suna Fara shirye shiryen Fara exams Amma Banda ss3 sbd su zasuyi mock ne kafin suyi jamb……..
……..Yau ta kama Monday kuma yaune zasu fara exams bayan an gama assembly kowa ya Shiga yana jiran invigilator yazo Bayan Kamar 30mins aka fara raba papers English…
+
Ss3 kuma suna hostel kowa da abunda suna sharholiyarsu wasu na bacci  wasu kuma shara wasu kuma fira. Kowa dae da abunda yakeyi.
Malama shafa ce tashigo ta fara korasu class sae turo baki suke suna aika Mata da zagi. Bosa Kam kwance take ragajab tana bacci sae saukar duka taji a cinyarta a firgice ta  tashi tana missika Ido malama shafa tace”dallah tashi ballagaza kawae kin kwanta kin wani saki jiki gaki kwatuwa”
Turo baki tayi tace” yoo Naga ai malama ba exams zamuyi ba meye kuma na tadamu”
Maka ta Kae Mata ta kauce tace”Dan ubanki class zaku je wannan zaman banzan baza kuyi shi ba sae kace ba exams zakuyi ba”
Tashi tayi tana turo baki dukansu suka fita sae class suna zuwa kuwa suka kulleshi ta ciki Dan basa so ko wane teacher ya shigo blanket suka shifida Nan f fira ta barke sae tsif suke abunsu duk malamin da yazo yayi knocking basa budewa”
_______★
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya watarana suje class wani lkc kuma suna hostel sauran students kuma ana Shirin tafiya gda.
Yau Friday hostel duk ya kitsime yayi dirty sbd masu tafiya gda gobe. Raj tace”Ni wlh yunwa nake ji kamar Zan mutu”
Aaj tace”Bari na Mana socking indomie”
Ushe tace”Bari zanyi kawae”
Koda ta duba dakin ba ruwa sae ta wuce dakin dake kusa da nasu kasan bonk ta fara dubawa ko zata samu ruwa dayake magrib ta gabato kuma duhu ya fara sauka sae kawae ta karkata kan bucket din ta diba kuma direct cikin indomie Dan already ta zuba a roba tana neman ruwane kawae.
Rufewa tayi ta mike ta koma daki sae gashi an zo korarsu sallah hakan yasa ta ajiye akan idan sun dawo sae suci kana tayi.
Bayan an gama sallah suka dawo kowa da yunwarsa Koda sadixy ta kunna torch light dinta ta haska sae kawae gani sukayi ruwan wanki ne gashi indomie din ya jika kuwa kowa tsaki ya fara wasu kuwa dariya suka saka Raj Kam ae kuka ta saki Dan wata irin yunwa takeji kamar me..
Sadixy ce ta fita da sauri sae gata ta dawo da golden morn a hannun ta mikawa Raj da sauri ta karba ta fara sha Kamar Bata taba cin abinci ba.
Washe gari aka fara kwasar students ranar ne kuma za’ayi ma su Raj visiting ae kuwa duk anzo musu sae wadan da iyayen su keda uzuri.
Zaune take gaban mama tana”mama Ni wlh bana son irin wanna sardine din Allah Kamar zarni yakeyi”
Mama tace”to ku barshi Mana idan na koma sae na bama yayanku ya Kae a chanza wanne kuke so”
Aaj tace”Titus Dan yafi dadi”
Tace”toh shikenan fatan dae ba wani matsala”
Suka ce aa Raj tace” wae Ina ya Bg?”
Mama tace”ta tafi argungu last week maybe ma ta dawo Monday”
Tace” Dan Allah mama idan ta dawo kice tazo”
Mama tace “to Zan gaya Mata”
Haka suka cigaba da firar su har lkcn tashi yayi suka watse.
Bayan sun koma hostel suka gyara duk abunda zasu gyara suka shirya komae.
Daya daga cikin metron dinsu ce ta shigo suna kiranta da baba sa’a tace” ku tashi ku gyara hostel din Nan ko Ina yayai dirty”
Chaaa sukayi Kanta suna su bazasu yi ba tunda Basu suka Bata ba.
Dole ta hkr ta koma suka nema masuyi…
*EXTENSION*
💃💃💃💃💃💃💃…..Zaman extension suke cikin jin dadi dan yanzu ba wani malamin da ke takura musu duk abunda suka ga dama shi skueyi. Waya kuma sun dae na boyewa fito da kayansu suke masu sneaking kuma sunayi kuma ikon Allah har yau ba’a kamasu ba.+
__________★
A gidan su Raj twins sister din mom dinta ba lpy sosae mma Hassana kariya ta samu a kafa kuma har India akaje gyara bayan sun dawo alhmdllh kafar tayi sauki saw dae tana yawo da sandar dake taimaka mata.
Macece Mae matukar son mutane kowa natane gaba daya tundaga siblings dinta har y’ay’ansu sun mai data kakarsu sbd yanda suke wasa da dariya kuma hakan baesa raini ya Shiva tsakani ba duk wani Mae matsala toh mama yake gayawa a duk cikin gdansu kowa ya tashi Neman shawara toh mama yake nema.
Tunda ta karye lpy ta mata karanchi bata kwana biyu bata kwanata ciwo ba yau lpy gobe ciwo hardae abun ya kae ga kwantar da ita hospital din Sokoto kuma.
Ba wani chanji da aka samu a tattare da ciwon ita kadae tadan abunda take ji a jikinta. Su yaya BG ne suka shigo dawowarta kenan daga abuja shima dan an gaya musu anyi admitting mama ne. Tunda taga condition dinda mama ke ciki hankalinta ya tashi itama sae kawae taji zazzabi na Neman rufeta har dare suna asibitin sae da Dr yazo yace ya kamata su tafi yanzu Dan basa bari a kwana da patient.
Was he gari haka suka kara dunguma sukayi asibiti sae dae ba’a bari a shiga gurinta haka sukaci zama har kusan 6pm Dr S. Jegah ne ya fito gaba daya hankalinsa a tashe da Sauri yabar gurin ganin haka yada aunty fareedah (step sister) din Raj bin bayansa dan tasan tunda taga mijinta haka tasan ba lpy ba a bakin mota ta same sa tsaye ya jingina Kansa a jikin motar dafasa tayi ya jiyo yana share hawayen da suka zubo masa Jiki a sanyaye tace”my dr lpy?”
Hawaye na zuba yace”fareedah mamah gaba daya komae ya tsaya oxygen dinma ya daena bazata bazata wuce 10mins ba yanzu haka”
Zama tayi dabas a gurin tana inna… Wasu hawayene suka zubo mata sae kuka ya barke kokarin yake ya danne NASA ya rarrasheta amma ina gaba daya tq burgaye sae kuka takeyi cikin tsananin tashin hankali.
A gurin su BG kuma ganin Dr ya fito ya wuce yasa ta mike tana tafiya a hankali sbd gaba daya bata da wani karfin jiki yanzu ita kadae tasan yanda take ji. A hankali ta tura kofar dakin ta shiga a kujerar dake bakin gadon ta zauna ta daura kanta a kan gadon kana ta kama hannun mama cikin nata hawaye na zuba non stop haka Drs biyu suka shigo Dr Aysha ta kama ta suka fito waje Dr Jabeer kuma ya dubata cikin tashin hankali ya fito sbd ganin gaba daya komae ya daena aiki Neman taimakon wani Dr yake nan ya hadu da dr Yusuf suka shiga tare shima gaba daya ya kideme a hankali ya kulle mata ido kana yaja zani ya rufe mata fuska gaba daya ya sun kada fitowa waje sbd basu San ya zasu gayama wnn a halin rasuwar baewar Allahn nan ba.
Sun kusa 30mins kafin dr Yusuf yayi ta maza ya fito da sauri uncle murry ya karaso yana tambayar dr halinda ake ciki dafa shoulder dinshi yayi hawaye na zubo masa yace”sae dae muyi hkr…”
Bae karasa ba ya wuce dan bazae Iya tsayawa ya masa bayani ba a duk zamansa hospital din nan bae taba jin mutuwar data ratsada kamar wnn ba.
BG nan take ta sulale saka sume gaba daya hankalin yan gidan ya tashi maman Raj ma sae da ta fadi dan wani irin sone suke ma junansu abun gwanin tausayi nurses ne suka zo suka tafi dasu aka basu taimako.
Tsaywa fada muku tashin hankalin da wnn family din suka shiga bata lkc ne.
Sae dare su BG suka farka a time din ana shirye shiryen tafiya da gawar mama duk da dare yayi haka suka dunguma cikin high speed zuwa jega uncle murry daya dakko gawa dakyar yake tafiya dan harda kaucewa titi yake sae karfe 1am suka isa Hajiya kam gaba daya kukama yaki zuwa mata idonta yayi jajir sosae sun kafe  hmmm tashin hankali dae sun shigesa haka aka zauna zaman gaisuwa gaba daya BG ta zabje kamar wacce ta shekara tana ciwo.
______________★
Gaba daya Raj ta sauya ta kamar ba ita ba haka ma Aaj sadixy ma ganin frnds din Nata cikin wani hali yasa itama duk sae ta koma so silent.
Sannu a hankali ciwo ha fara cin Raj amma daure sosae haka dae suke zaman extension din Nash cikin wani yanayi.
Bayan sati daya ciwo ya rufe Raj sosae ganin haka yasa aka mai data gda koda taje su mama har sun Dawo daga jegah data ji lbrn mutuwar mama Hassana ba karamin tashin hankali ta shiga ba tayi kuka harta gaji a haka har mutuwar ta same masu jiki Raj taji sauki aka maedata skl da Aaj taji itama ta shiga tashin hankali sosae haka suka cigaba da zaman Nasu. 2 days later.+
Zaman su kam yanzu ya chanja sosae suke sheke ayarsu a hostel da kuma suka fara jamb registration aka fara kwasar students zuwa gda yayinda wasu kuma a skl zasu dan sunyi nesa sosae.
Zaune suke a hostel sun gama lunch sallamar sadixy ne yasa suka mike da gudu sukayi hugging dinta Jakarta ta ajiye tana”wash Allah wlh banso dawowa ba yau”
Faty tace”shegiya da kinyi zamanki ai dan wlh ni if to say naje gda to sae an gama jamb zan dawo”
Dariya sukayi Raj tace”INA sako na?”
“Ohh karki cinyeni daga dawowa zaki dameni”
Raj tace”atoh aiyafi waya gaya miki ana wasa da sakon masoyi”
Dariya suka sheke da ita Aaj tace”wato Ruqayyah green sneka ce “
“Ba wani green snake bazaki gane bane baby dazun bakiji yanda ya kasheni da romantic words dinsa bane oh my gosh am dying”
Daka mata duka Sadixy tayi tace”saeki gaya mana waye bashida soulmate din da zaki zo kina cika mana ears da zancen ki”
Dariya tayi irinta shakiyanci tace”ko baba da babansa in gaya miki Hafeez yayi ma Shuraim zarra kama kanki”
“Ahh wlh kinfi karfina yarinyar nan haka Hafeez ya lalataki ban Sani ba”
“Hhhh sae kiyi baby”
Kiran sallar asr ne yasa suka tashi gaba days xasuje masjid suna tafe suna fira abunsu dan basuda wani yawa sbd ba gaba daya suka Dawo ba
Alwala sukayi kana suka wuce cikin masallacin suka dasa wata fira ganin har 4:45 ba’a tada sallah ba yasa suka mike Aaj taja su sallah suna cikin 3rd raka’a ne Malam yashigo tsaye yayi Kansu yace”kae Ku katse sallar nan tunda nazo”
Banza suka mishi suka dago daga rukuu na last raka’a a tsawace yace”bada Ku nake mgn bane?”
Ina sallah suka cigaba dayi yana tsaye Kansu har suka idar ya cika yayi fam kamar xae fashe. Kallon Aaj yayi yace”ke shugaban marasa kunya Dawo nan kiyi kneeling “
Kallonsa tayi tana smiling kana ta mike tayi hanyar waje fizgo hijab dinta Malam Shafa tayi tace”ke Mara kunya rashin kunyar taki har ta kai kiyima Malam sbd bakida tarbiyya gidanku ba’a Baku tarbiyyar girmama na gaba da kuba toh ni xan baku
Fixge hijab dinta tayi tace”nikam malama inada tarbiyya ban Sani ba dae ko da wancen bangon kike yi”
Rike baki tayi tace”ahhhh lallai yau zaki ci ubanki a makarantar nan sae kin San yau kinzo GGC heeee bari na kira daddy wlh yau sae kinyi aiki kamar jaka”
“Nikam Malama ba jaka bace kuma wlh sae dae muci urban juna dan bana tunanin a wannan era din akwae malamin da ya isa ya dake ni na barsa”
Mari ta kae mata Aaj ta kauce kafin Malama Shafa tayi wani yunkuri ta zube kasa aljanunta sun tashi gaba daya yan masallacin kanta sukayi ganin tayi wata irin zabura ta mikene kamar snake yasa suka tsaya cak fa gudu tayi hanyar waje Malam yayi saurin tareta ta kai masa maka a fuska sae da hakorinsa daya ya fita Ashanty da zata shigo kenan sukaci karo Jan hannunta tayi da gudun masifa ihu Ahsnaty ta dingayi kamar ranta zae fita dan ita kadae tasan mafisar data hango dan wani irin gudune Aaj keyi kamar zasu tashi sama gaba daya yan masallaci hankalinsu ya tashi Raj da idonta ya kawo hawaye sbd tausayin Yar uwarat dan tasan halin aljanunta idan suka tashi ba sauki kallon sadixy datayi tsaye tayi tace”wayyo ban San ya zanyi ba wlh” shrr sae kuka itama sadixy hawayene suke sintiri .
Sae da tayi nisa sosae ta kusa gate kana ta saki Ashanty ta fadi kanta ya saki wani dutse sae suma…….Da kyar securities din bakin gaye suka samu damar kamata haka suka dakko ta duk ta sankare sae faman fisgewa take tanaso ta gudu amma saboda rikon da suka mata bana wasa bane yasa ta kasa kwacewa.
Malam kuwa tunda yaga an nufo masjid da Aysha ya kama hanyar gabansa ya gudu sae dae aka samu aka kunna mata karatun alqur’an kana tayi lakau ta koma ajiyar zuciya da haka har wani nannauyan bacci ya tafi da ita.
Bayan kwana biyu
Zaune suke a common room din red house kowacce da abunda yake yi su raj sae fira suke kasancewar Saturday ne yau students suka fara dawowa hakan yasa hostel din ya fara hargitsewa da hayaniya kowa sae murnan jin dadin ganin frnd dinshi yake da haka har sauran students din suka gama dawowa aka cigaba da skl life.
Bayan dawowar students da sati ss3 suka fara waec haka suke exams din cikin jin dadi Dan answer ake basu shi yasa ko karatu basayi sae dae zaman banza a hostel da hayaniya haka dae suka cigaba har suka gama kullum sae anyi fama dasu tunda sukaga barin makarantar zasuyi yasa suka fara bannar cin rae ba wacca bata rubuta sunan ta ba a jikin bangon skl ko ina saeda suka maka sunan su acewarsu sun bar record. White board dinsu ma sae da suka saka compass suka rubuta sunan su.
Daddy 504 ne yazo wucewa yaga an rubuta *Platonic yan aljannah* yasan ba aikin kowa bane sae ss3 Dan haka yasa aka Tara masa su sae da ya gama kallonsu kaf kana yace “Platonic yan aljannah” kallon kallo akayi tsakanin Raj da su sadixy banza suka mishi sae da ya koma maemaetawa kana sadixy ta daga hannu Raj ma haka da Aaj yace”oya pack one side so ss3 u guys are trying to prove to us dat u are stubborn you went on writing your names everywhere listen and listen attentively wlh non of you will ho out of dis skl har sae kun kawo mana one one bucket of milk paint and one one white board then back to u Platonic I don’t want to see dat name were I saw it use your tongue and wipe it before the sun set am I clear” suka amsa da yes sir kana ya kara gaba dariya suka sanya Hanifa ta fito tana Mae Maeta abunda ya fada cikin shakiyanci suka koma saka dariya kana suka watse
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya su  Raj sae fama da exams  sukeyi amma duk da haka basu daena shakiyancunsu ba Saema abunda ya karu malamansu sae dae hkr kawae sukeyi dash.
Yau Wednesday da dare sun fita night prep shima Dan an korosu ne da bazasu fito ba. Kida kawae sukeyi suna waka da rawa wasu kuma na tsifa wasu karatun novel kowa da abunda yakeyi dae mama principal ce tamusu shigar bazata dan dama ana kae karansu kullum akan rashin karatunsu sbd sunga ana basu answer  shi Yasa.  Ranta ya mugun baci wata uwar tsawa ta Daka musu dayasa kowa ya shiga hanakalinsa “so you are trying to prove me that what your teachers are saying is true ss3 am very disappointed with you wlh banyi tunanin abun naku har yakae haka ba but don’t worry we will meet  on Friday  no one will give you any answer  u will write it yourself ” tana Kaenan ta juya ta fita .
Dariya bossa ta sanya tace “dama ae kune kukaga zaku iya bamu answers  to yanzu wane karatu akeso muyi kuma raenin sense shan tea da cokali mae yatsu 😂😂 dariya duka suka sanya suka cigaba da harkar gabansu
Kamar yanda mama principal ta fada ranar Friday kuwa ba’a basu answer ba gashi chemistry ne sae dae sukaeta cizon yatsa masu wayon cikinsu ne kwae sukayi karatu gaba dayansu exams din ya basu haushi da suka fito sae zagin mama principal suke.
Bayan suna gama WAEC suka koma gida suka bar sauran students dan jss3 ma suna shirye shiryen  fara  JSCE  watan su daya da sati suka koma skl zasu fara NECO  haka suka fara exams duk basa jin magana kullum sae an samu matsala dasu.
    *Agurguje*
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya su Raj  sae shirye shiryen graduation party  akeyi tareda jss3 dinsu ranar Saturday  aka gudanar da kayataccen graduation cikin farin ciki iyayensu duk sunje taya y’ay’ansu murna Hafeex ma  yaje  farinciki gurin Raj ba’a magana pics kam anshasu kamar ba gobe bayan an gama aka watse washe gari Sunday akayi hutu su Raj an zama graduate present ss3 kuma sun fara shirin muguntar da zasuma Juniors dinsu.
THE END

GORAN DUMA BOOK1 PART1👇

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *