KOMA KAN MASHEKIYA CHAPTER B

 KOMA KAN MASHEKIYA CHAPTER B

Ai kuwa da dare  ya kira ta kamar yadda ya sabar mata.

Kafin ta tafi ckul xai kira acam ma yana kira yaji lafiyar ta. Haka in ta dawo sannan da dare kafin su kwanta ma zai kira.

Yanzu ma da ya kira  labarin abinda Yasmeen ta fada ta bashi. murmushi yayi ita kuwa dariya take, tana cewa,

“Wai Yaya sai suna mana kallon masoya wai ya ake soyayyar nan ne ma. Har da ake cewa haka.”

Shima dariyar yayi, ya ce,

“Nima ana yawan fadan hakan amma ni na cewa ke kanwata ce, soyayya kuma ni da ba budurwa ba da wa zanyi soyayya.”

Dariya tayi ta ce,

“Yauwah Yaya Allah ya kamata ka fito da mata da ka dawo musha biki dan Allah na matso naga Matar ka tinda baka fada min batun ta ba.”

Dariya yayi, ya ce,

“Kema kinsan da ina da budurwa kece farkon sani ko?”

Kai ta gyada, sannnan ta ce,

“Eh ina Sadyn ka kuwa?”

Ta kece da dariya saboda tini dramar da ya fada mata sunyi akan wai tana son sa dan Allah ya aure ta.

Kwafa yayi ya ce,

“Ni kike wa dariya ko? Zan rama ne, bari kema nasan yadda zanyi dake.”

Ya danyi shiru, Amina ta cigaba da dariya.

“Yauwah ina Garbatin ki?”

Ya fada yana dariya shima.

Fuska ta bata kamar yana gaban ta tai shiru. Duk maganar duniya yayi amman tai shiru wannan yasa ya hau bata hakuri dan sam baya jurar fushin Amina. Sai da yai ta lallashin ta sannan ta sauko suka cigaba da hirar su.

Sai da zata kwanta ne sannan sukai sallama.

Ahmad har aiki yake koya mata ta waya ko online.

Sosai suke mu’amala duk wanda yaga yadda suke mu’amala ko yaji labari zai ce soyayya suke.

Dan daga baya kowa kishin kowa yake bama sa son daya acikin sun ya ce, yayi budurwa ko saurayi daga ya fada za su fara fushi da juna har sai ya bada hakuri.

Haka rayuwar su ta kasance,  Ahmad kuwa wani amininsa da suka tafi daga Nigeria tare shi ne ya fahintar dashi da son juna suke.

Lokacin da shima ya tinkare shi da maganar son Amina yake musu yai masa.

Sai da ya tambayeshi yadda yakeji game da ita sannan ya ce masa.

“A gaskiya nasan shakuwa ce ke tsakani na da Amina wacce ta kai har ake mana kallon soyayya muke.”

“Yadda kuma nake jin ta araina nasan tana da matsayi me girman gaske. Kasan abinda baka sani ba shine wallahi ko rashin lafiya take nima sai nayi haka nan jikina na fada min a halin da take ciki na dadi ko akasin haka. Ina jin ta kamar Na’ima.”

Dariya Muslim yayi ya ce,

“Karya kake yanzu in Na’ima na rashin lafiya kaima kana yi? Ina Na’ima na wani halin kai ma kana ji a jikin ka. Duk abinda kake ji game da Amina kana jin shi game da Na’ima kullum ka kwashe lokaci baka kira ta ba ko bakuyi chat ba.”

Ido Ahmad ya lumshe tabbas yasan duk ba haka bane ga Amina kawai yake jin kuma yake iya haka.

Ya jima kafin ya ce,

“Ni fa duk da haka ban yadda ba.”

STORY CONTINUES BELOW

Dariya Muslim yayi ya ce,

“Abokina sauran shekara ko nace be kai shekara ba mu gama karatu. Ya kamata ka kama dahir dan girma kake kuma ya kamata kusan a wane hali kuke. In ita Amina bata gane ba kai ya kamata ka gane.”

Wayar sa ya dauke ya ce,

“Na tafi da ita ka kwana daya baka kira Amina ba da gida naji wane yanayi ka shiga dawa kafi tunawa.”

Ya mike ya fita. Kwanciyya Ahmad yayi ya lumshe ido Amina yake hange farkon haduwar su.

Ya jima yana tunanin lokutan da suke tare da mu’amalar su.

Amina kuwa tana can a school Allah Allah take a fito lecture ta kira Ya Ahamd.

Suna fito ta hau kiran sa amman number a kashe. Muslim ta kira shima wayar a kashe.

Duk kasa sukuni tayi da haka ta koma wata lecture har la’asar wayar sa a kashe take bayan tasan ba abinda zai sa ya kashe waya.

Addu’a take Allah yasa lafiya. Haka ta koma gida sukuku da ita.

Mama na ganin ta tasan ba lafiya. Ko da ta tambaye ta ai cewa tayi ai gajiyar makaranta ce.

Wasa wasa sai da Amina ta kwanta zazaabi na rashin jin ya Yaa Ahmad yake, damuwar ita ta haifar mata da zazzabin.

Ta bangaren Ahmad kuwa shima sosai ya kwanta ciwo dan Ya nemi Muslim ya rasa.

Jinya yake sosai, a kullun tunanin sa halin da Amina ke ciki.

Duk da haka be yadda da son ta yake ba yafi yadda da son sanin a wane hali take shi ya jawo masa haka.

Yau kwana uku be kira ta ba wanda kullum sai yai mafarkin ta.

Fita yayi ya siyi sabuwar waya ya siyo sim ya zauna agun ya kira ta.

Wayar ta a kashe wannan ya dada tada masa da hankali.

Kira ya dingayi ba kakautawa amman abu daya take fadi wayar a kashe.

Haka ya koma daki ya zauna shi be hadace number ibrahim ba.

Dady ya kira ya ce yana son ya bashi ibrahim. Dady ya ce ya fita sai dai in ya dawo.

Gida ya koma da zazzabin rashin jin muryar da ganin Amina.

Yana komawa ya samu Muslim zaune a dakin shi.

Yana ganin Muslim ya daure fuska ya samu gun zama da kyar ya kalle shi ya ce

“Bani waya ta mugu kawai.”

Dariya Muslim yayi ya ce,

“Naji kuma ba zan bayyar ba sai munje asibiti an duba min kai.”

Sanin Halin Muslim tinda ya fadi haka sai ya kai shi asibitin zai bashi yasa ya mike da kyar jiri na dibar sa.

Hannun sa ya kama suka je asibiti. Kallon sa yayi ya ce,

“Kai masa bayani.”

Muslim Ya fadawa Ahmad. kallon sa Ahmad yayi ya ce,

“Ciwon kai ke damuna da jiri sai dan zazzabi.”

Jinin shi ya auna ya dago ya kalle shi ya ce,

“Ahmad me yake damun ka da karancin shekarun ka jinin zai hau.”

Shiru yayi ya ce,

“Ahmad ko dai soyayya ce *sila.”*

Kasa yai da kai. Ya ce, tunanin me kasa a ranka Haka. Shawara daya zan baka in soyayya ce gwara in son ka ne ba ayi ka hakura da ita. In kuma bata san kanayi ba gwara ka sanar da ita.

Dan nasan samari irin ka masu ji da kyau da kudi da ilimi ba abinda zai sa su damuwa in ba soyayya ba.”

Magunguna ya rubuta masa ya mika masa ya ce,

“Ka sha wannan sannan ka cire damuwar dake ranka.”

“Thank you Dr!”

Muslim ya fada yana mika masa hannu su gaisa.

Fita sukai, ya siya masa maganin sannan suka koma gida.

Sai da ya tabbatar da yaci abinci yasha magani sannan ya ce,

“Kayi hakuri dan na san nine silar rashin lafiyar ka. Kayi hakuri ban san halin da kake ciki bane. Ban san kuma haka zai faru ba. Amman kayi hakuri.”

Yai shiru kafin ya ce,

“Yanzu ka yadda da abinda na fada maka. Tukkuna ma tunanin me kasa a ran ka.”

Tsaki Ahmad yayi ya ce,

“Kaga ka ban wayata.”

“Allah sai ka fada min abinda ke damun ka.”

Shiru yayi kafin ya ce,

“Ni wallahi ban san damuwar me nake ba. Amman ina tunanin Amina tabbas dan bansan halin da take ciki ba. Jikina ya bani ba ta da lafiya. Dan Allah kaban wayata na kira naji.”

Mika masa yayi yai  yana guntse dariya. amsa yayi ya bude ta

Sakonnin Amina ya dinga arba dasu. Ido ya zaro yana girgiza kai.

Number ta ya latsa ya kira Amina. har yanzu wayar a kashe take.

Tsaki ya daka ya kwanta. Hawaye ne ya ziraro daga idon sa.

Ya jima a kwance kafin ya mike ya shiga ban daki. Wanka yayi ya fito ya kwanta.

Bacci ne ya dauke shi. Da mafarken Amina a ransa.

Amina kuwa tin lokacin da tai ta kiran wayar Ahmad bata samu ba ta akashe ta ta ajiye.+

Mama tayi tayi da ita suje asibiti amman taki.

Auwal ne da yazo duba su yaga halin da take ciki ya kira Dectorn da yake duba ta.

Ko da yazo ya dubata yagane damuwa ce a ranta.

Nan ya dinga kwantar mata da hankali duk da besan damuwar ta ba.

Wani magani ya bata wanda zata samu bacci dan sam bata iya bacci.

Yana komawa ya kira Ahmad ya fada masa komai.

Sosai hankalin Ahmad ya kuma tashi.

Haka ya dinga trying number ta amman a kashe.

Sai washe gari da ta tashi ta dan ji dama dama.

Wanka tayi ta taya Mama da wasu abubuwan.

Daki ta koma ta dauki wayar ta ta ga ashe a kashe take.

Kunnawa tayi ta zauna ta zuba tagumi ta rasa tunanin me take.

Can sai ga kiran Wayar ta nan. Firgita tayi dan bata cikin tunanin ta.

Daukar wayar tayi taga Yaa Ahmad akan ne. Da sauri ta dauka, ta kara a kunnen ta.

“Yaa Ahmad!”

Ta fada tana fashewa da kuka.

Rasa abinda zaiyi yayi, yai shiru kafin ya fara magana cikin sanyi muryar, muryar sa na rawa ya ce,

“Yi hakuri Meenal. Kiyi hakuri…”

Jin muryar sa ba dai dai ba yasa tai saurin katse shi ta ce,

“Yaa Ahmad lafiya kuwa.”

Ajiyar Zuciya ya sauke ya ce,

“Yanzu dai ya kike? Jikina ya dade da bani baki da lafiya me yake damun ki.”

Kuka ta saka ta ce,

“Nima ban sani ba. Ban san me yake damuna ba. Nasan dai rashin ka na daya daga cikin abinda ke damuna na. Ka manta dani na tsawon kwana ki.”

“Ba haka bane!”

Ya fada a sanyaye dan ya kasa ma maganar.

“To menene?”

ta tambaye shi.

Nan ya bata labarin duk abinda ya faru. shiru tayi ta kasa magana ma.

Daga na ta kashe wayar tana tunanin wai kenan son Yaa Ahmad take.

Tab amman kuma ta yaya ta fara son sa.

Ta jima a kwance kafin ta kira number Yasmeen.

Yasmeen dake bacci ta dau wayar cikin sanyin jiki.

Ganin Amina yasa tai saurin daukar wayar tana cewa,

“Meenal ya dai ko jikin ne?”

Murmushi me sauti Meenal tayi ta ce,

“Aah jiki ai ya warware gobe ma zan shigo ckul.”

“To shikenan Allah kara sauki.”

“Ameen!”

Yasmeen ta ce,

“To menene? Naga kin kasa magana.”

“Haka ne. Gobe dai ma hadu.”

Ta bata amsa tare da cewa,

“Sai da safe.”

Tana dire wayar kiran Ahmad ya sake shigowa.

Tana gani ta kasa dauka dan wani nauyin sa take ji.

STORY CONTINUES BELOW

Yasan idon ta biyu dan haka ya turo mata da sako kamar hka.

‘Meenal, Allah ya dauran sonki a lokacin da ban san son naki nake ba. Son ki zai iya illatani in har bakya so na. Dan na sha wahala a kwanakin nan. Ina fatan zuciyar ki kema na son na. Sai da safe ki kular min da kanki.”

Murmushi Amina ta saki tana rumgume wayar.

Lallai ta tabbatar da son Ahmad take. Dan wani sanyi take ji na shiga zuciyar ta.

Washe gari da suka je ckul ta fadawa Yasmeen duk abinda Ya  faru.

Sosai Yasmeen ta tayata murna. Ta ce,

“Ai na fada miki kuka ‘ki yadda yanzu da kuka ji jiki kun yadda ko? To Allah tabbatar da alheri ya sa ayi damu.”

“Ameen!”

Amina ta ce tana dariya.

A lokacin Ahmad ya kira amman sai ta kasa dauka dan kunyar sa take ji.

Sai text ya kara tura mata.

Tin daga lokacin suka fara soyayya me ciki da tsabta da kaunar juna.

Duk wanda zai ga Amina da Ahmad sai sun burge ka.

Dan sun dace da juna. Kowa na son dan uwan sa haka nan kowa na burin farantawa dan uwan sa.

Dady da Ibrahim ne sai Auwal kawai suka san da soyayyar tasu.

Sai Mama da tun kan su san suna soyayya ta san son juna su suke.

Wannan shine abinda ya faru tsakanin Ahmad da Amina wanda ya san son ta ya zama jinin jikin sa bazai iya rayuwa babu ita ba.

*Cigaban labarin*

***********

Ahmad dake zaune yana tuno rayuwar su da Amina ya sauke wata nan nauyar ajiyar zuciya.

A ransa ya ce,

“Bazan taba iya barin Amina ba dan Amina ita ce rayuwa ta. Bazan bar wani ya mallake ta ba sai ni dan nafi kowa sanin wace Meenal nafi kowa cacanta da Meenal. Ni kadai zan iya kula da Meenal wanda bazata taba kuka ba.”

Hawaye ya zubo daga idon sa, ya goge yana mikewa yayi dakin sa da bacin rai a zuciyar sa.

Yana kwance Dady ya shigo dakin sa. Kallon sa yayi ya ce,

“Ahmad ya na ganka cikin wani hali ne haka lafiya?”

Ya fada yana zama a gefen sa.

Ahmad ya mike zaune ya ce,

“Dady. Mami ce dai akan maganar nan take ta repeating taki amincewa.”

Dady ya kamo hannun sa, ya ce,

“Kayi hakuri. Kasan mata da tunanin su,”

Kai Ahmad ya girgiza idon sa jajir ya ce,

“Dady wannan karan Mami na matsamin sosai. Abin yazo da wata kala daban.”

Kallon sa Dady yayi, ya ce,

“Dady abin na damuna ganin gashi har uncle dina suna wata magana akai.”

Dady yayi murmushi ya ce,

“Mubar wannan maganar tukkuna ya Aminan?”

Murmushin shima Ahmad yayi, ya ce,

“Tana nan kalao. Kwana biyu banje ba ma.”

“Saboda me to?”

Dady ya tambaye shi.

“Mami ta hanani fita gaba daya.”

Kai Dady ya girgiza ya ce,

“Shikenan ka kwantar da hankalin ka anjima zan kai ka. Tinda sun dawo ma zan san yadda za ayi. ayi komai a gama.”

Murmushi Ahmad yayi ya ce,

“To Dady na. Nagode Allah kara budi.”

“Ba komai son.”

Ya rumgune Dadyn yana murmushi.

Da yamma Dady da kan sa ya zabar wa Ahmad kayan da zai saka, wata Dark blue din wando ya saka sai farar riga.

Kafar sa kuma ya saka wani booth shima blue me adon fari.

Sai agogo da ya saka fari. Yayi kyau sosai.

Wani turare Dady ya miko masa ya saka. Hannun sa Dady ya kamo suka fita.

Mami da ke zaune a falo, ta mike ganin sun fito tare.

Kallon su tayi ta mike ta ce,

“Ina zaku?”

Tura ta Ahmad waje yayi, ya ce,

“Je ka fito mana da mota.”

Ahmad ya fita da sauri yana murna. Kallon sa Mami tayi ta dawo da kallon ta ga Dady.

“Ina zaku ne?”

Ta kuma jefar Dady da tambayar.

Da kamar bazai ce komai ba sai kuma ya ce,

“Ni danki ne? Ko me? Ki kiyaye ni fa. Ki kiyaye ni wallahi.”

Ya nuna ta da yatsa ya fita. Ahmad da ya fito musu da mota yana jiran Dady.

Dady na zuwa ya shiga ya tada motar suka hau titi.

Kallon sa Dady yayi ya ce,

“Haba Ahmad ga wancan store din muje ka siyo musu wani abun man.”

Karkata kan motar Ahmad yayi suka shiga tare da Dady.

Dady da kansa ya dinga dibar musu kaya. Sai da sukai siyayya me yawa sannan suka fito suka kama hanya.

Suna zuwa Ahmad yai mata waya cewar shi da Dady ne.

Gidan dama a gyare yake kamar kullum dan haka ta shimfida musu tabarma a tsakar gidan sannan ta sanya katon hijab ta fadawa Mama zuwan su. Sannan ta fita dan shigo da su.

Tana fita ta karasa gefen Dady ta amshi ledar hannun sa. Ta ce,

“Dady barka da zuwa”

“Yauwah Amina.”

suka shiga gidan tare.

Sai da suka zauna sannan Amina ta gaida Dady.

Dady ya amsa cikin so da kulawa. Mama ce ta fito sanye da hijab din ta har kasa ta gaishe da Dady tare da masa godiyar abinda yake musu.

Mikewa Dady yayi ya ce,

“To ni zan tafi. Ahmad sai anjima kai ko?”

Kai Amina tai kasa dashi. Ahmad kuma ya ce,

“Dady bari na raka ka kofar gidan.”

Kama hannun sa sukai suka fita. Sai da Dady ya tafi sannan ya koma.

Sun sha hira da Amina dan sai bayan isha’i bayan yaci abinci sannan ya yafi da kewar ta kamar yadda itama take kewar ta sa.

Alhamdulilah Komai yana tafiya dai dai dan har an kai lefen Amina wanda Dady ya dauki kanwar sa da Ahmad suka tafi Dubai dan hado kayan lefe.+

Sosai suka yo mata kayan dan akwati set biyu suka ciko mata da kayan.

Kanwar Dady da yake ta saba fita sarin kaya ta san kaya masu kyau da tsada yasa ta zabo.mata kaya masu kyau na kece raini.

Dan kananun kaya ma daban ta hado mata a kwati biyu.

Kaya sunyi kyau dan shi kan sa Dady ya yaba da kayan.

Suna dawowa su Dady ya sa abokan sa sukai lefe dan yace bazai sa mata ba dan mata akwai tsegumi.
Bayan an kai kaya Dady ya dankawa Ahmad wani makullin gida yace akaiwa Mama dan gyara mata gidan za’ayi kafin biki. Sanna yasa ya tambayo Amina wane kalar kaya take so.

Koda ya kai wa Mama. Mama kuka ta dinga yi tana shi musu albarka da addu’a.

A ranar aka kwashe komai nasu suka koma can.

Dady da ya aika Ahmad  da yaje gun Amina ya tambaye ta kalar kayan da take so shiru tayi ta kasa magana.

Kyale ta yayi ya kira Yasmeen ya tambaye ta.

Ita ta fada masa da yake suna maganar zabin Amina a tsakanin su.

Nan ya fadawa Dady aka yi mata su. Katon gida Aka ginawa Ahmad.

Wanda yake me kyau da tsari.
Gidan Mama an maida shi ginin zamani dan da ginin kasa ne ma.

Har da gate akai mata gidan yayi kyau sanna Dady ya zuba mata wasu kayan sababbi.

Mama dai kuka Amina kuka dan Dady ya musu abinda ba kowa zai musu ba.
Lokacin bikin kuwa Anty kanwar Dady da kanta tasa aka zo aka gyara mata amarya inda ta biya kudi mai yawan gaske.

Dan Dady ya ce duk abinda ake bukata shi zai yi kuma a tambaye shi ko nawa suke bukata.

Event daya Amina ta ce za’ayi amman Ahmad ya ce sam.

Dan shi ya riga da ya tsara komai har ya fitar da kati.

Zasuyi kamu sai yinin Mami, sai dinner.

Ana sauran kwana uku biki Anty da kanta tazo ta kawo mata wani akwatin kayan fitar biki.

Material ne masu kyau da tsada wanda ya’yan manya ke sawa a bikin su shi aka dinku mata.

Anty da kanta ta dauki Amina ta kaita duk inda za ai mata gyara da lalle da gyaran kai.
Tin ranar kamu Anty ta kawo mata me kwalliya wacce zata zauna har a gama bikin.

Ranar kamu akai mata kwalliya me kyau inda ta saka wani purple material tai ado milk head da net.

Kwalliyar da akai mata ta kara mata kyau dama aba ce me kyau.

Kowa ya kalli Amina sai ya yaba da kyan ta. Makobta da kawayen ta yan makaranta dana Yasmeen duk sun zo.

Kowa ka gani anan taya ta murna da farin ciki ake.

Mafici da turaren wuta da kasko a ka raba sai Snack da lemo da aka raba
STORY CONTINUES BELOW

Ranar yini ma amrya ta shirya cikin wani bakin material me golding stones nan ma an mata kwalliya tayi kyau kamar ba gobe.

Ango yaje cikin shirin shi wata golding kalar shadda. Shi da abokan sa.

Anyi ruwan kudi. Ansha hotuna Ibrahim kuwa sai murna yau burin su ya cika.

Ranar asabar kuma akai dinner inda amarya ta shirya cikin wani dark blue din material. Ango ya saka shima blue shadda me kayu.

Ba karamin kyau sukai ba sunyi matching da juna. An sha hoto Ibrahim da Auwal kannin ango sai rawar kai ake.

Ranar Lahadi aka daura aure Amina Suleiman da angon ta Ahmad Muhammad akan sadaki naira dubu dari.

Da dare amarya ta shirya cikin wata maroon kalar atamfa me adon milk a jiki. Milk Alkeba aka yafa mata akai mata ruwan turare. Daga nan aka kai ta wajen Mama tai mata fada sai aka dauke ta zuwa gidan ta.

Dan Dady ya ce sam kar a kai ta gidan Mami.

Duk wanda zai je gidan sai ya yaba da gidan dan ba karamin kyau gidan yai ba.

Farkon gidan katon haraba ce wacce za ta iya dibar motoci a kalla guda bakwai. Sai flower da aka zage gidan da su.

Da ka shigo zaka tadda baban falo wanda aka saka masa dark brown din kujeru masu ratsin milk kala.

Wanda bangon ma kansa pentin dark brown da milk aka kala akai.

Haka wallpaper dakin ma ka saka mata brown kala.

Daga gefen hagu dakina ne guda biyu ne suna facing junan su.

Dayan aka saka mata gado kalar kayan falon ta. Dan har handaki da kalar kayan cikin dakin a kai masa ado. Inda dayan kuma aka saka orange kala me adon ash. Hatta fentin dakin ma orange an ash ne.

Daga can karshe falon kuma daining space ne inda akai masa ado da jajayen labulaye da kayan ado. Bangaren dama kuma kofofi biyu ne.

Daya kitchen ne wanda aka saka.masa komai dark pink an milk hatta durowar dakin ma dark pink an milk ce.
Daya kofar kuma wani dan korido ne inda aka saka wata kujera da kayan gargaji a wanje aka saka masa milk labule. Sai kofofi guda uku. Daya barander daya kuma ban daki. Dayar kuma falo ne dauke da dakuna biyu.

Falon an masa ado da arabian kujeru pink kala inda labulayen ma kansu pink kala ne.

Sai bedroom din ma ado akai masa furniture pink kala dakin yai kyau sosa. Sai bandaki a ciki.

Dayan dakin kuma akai masa ado da kafet ja da tumtim suma jajaye da gado.

Kowane daki da bandaki a cikin sa. Kawayen ta suna mata murna bama Yasmeen da tafi kowa taya yar uwar tata murna.

Rayuwa kenan wai nan gidan Amina na ne, duk da fuskar Amina a rufe take tana mamaki dan taji yadda ake fadan haduwar gidan.

Sai da yan kawo amarya suka tafi sannan kawayen ta suka shirya mata gidan suka kara turare shi.

Yasmeen na ta tsokanar amarya. Haka ma sauran kawayen su.

Sai wajen karfe tara sannan Ahmad da abokan sa suka shigo.

Alkeba suka sakowa amaryar suka fito ffalo da ita.

Bayan anyi addu’oi ne aka bige da barkwance daga karshe akaiwa ango da amarya nasiha me ratsa jiki.

Inda daga nan suka mike dan tafiya rakasu ya tafi yi. Inda Yasmeen ta kama Amina ta maida ita daki.

Tai mata sallama kan sai gobe in sun zo cin kazar amarci.

Ahmad na dawowa ya rufe ko ina ya nufi dakin Amina.

Tana zaune kanta a kasa ya shiga dakin.
Murmushi ya saki ya kira sunan.

Kin dagowa tayi kamar yadda ta kasa amsawa.

Murmushi yayi ya ce,
“Tashi kije kiyi alwala kizo muyi sallah ta godiya ga Allah da ya nuna mana wannan ranar.”

Mikewa tayi a hankali ta nufi ban dakin da ke cikin dakin.

Bayan ta ya bi shi ya kunna mata famfo tayi alwala sannan shima yayi ya same ta a dakin tana saka hijab.

Sallaya ya shimfidda musu suka tada sallah.
Sai da suka idar sannan yai dafa kanta ya karanto addu’a.

Bayan ya gama ya mike ya nufi falo. Ledo jin da suka shigo dashi ya dauke hade da cup da plate.

A ciki ya zubo gasassun kajin tare da zuba mata madarar a kofi.

“Bismillah!”
Ya ce da ita.

Shiru tayi hade da dukar da kanta kasa. Murmushi yayi ya dauko ya mika mata hannu ta kawo zata amsa.

Hararar ta yayi ya janye ya nufi bakin ta da ita.

Cikin jin kunyar ta amsa taci cikin dabara da wasa ya dinga dura mata har sai da ta koshi.

Ban daki suka nufa ta wanke baki shima haka.

Dakin sa ya tafi dan dauko kayan bacci. Tinda ya shiga dakin yaji wata faduwar gaba.

Kirji ya dafe yana salati. Sai da ya saka kayan bacci sannan ya haye gadon sa.

Yana son zuwa gun ta amman wani barin na zuciyar sa na mai hani da zuwa.

Har ya mike yayo kofar daki sai kuma ya koma. Ya rasa me yake damun sa.

A zakirin gaskiya yana matukar bukatar ta kuma yana son yaji ta a jikinsa. To amman kuma da yayi hanyar dakin sai yaji kamar kar yaje
Da haka ya kwanta. Wayar sa ya janyo ya tura mata da sako. kamar haka.
‘Meenal ki kwanta kiyi bacci ki kular min da kan ki sai da safe.’

Ya tura mata. Ko da Amina taga sakon bata kawo komai ba ta kwanta amman wani barin na zuciyar ta na ce mata haka akeyi to.

Da haka tayi bacci cikin kwanciyyar hankali.

Washe gari tin asuba da ta tashi tai sallah ta koma bacci dan bata wani samun bacci tinda aka fara hadahadar bikin nan.

Ahmad kuwa bayan ya dawo daga massalaci ya shiga dakin ta.

Gani ta yayi can tsakiyar gado ta cure gu daya sai kace me jin sanyi.

Wani murmushi ya saki yana jin tausayin ta a ransa.

Yasan ko wace amarya tare take kwanaa da mijin ta a daki daya ko da ace ba abinda zai shiga tsakanin su.

To amman wai shi me ya hana shi zuwa wajen sahibar sa abar kaunar sa.

Kansa ya buga yana yin tsaki. Kan gadon ya hau ya janyo ta jikin sa.

Ya jima yana kallon ta kafin daga karshe shima baccin ya dauke shi.

Karfe goman safe ta farka. Jin ta jikin mutum yasa ta tai saurin rufe idanun ta.

Kwanciyya ta cigaba dayi har shima ya farka. A hankali ya zare jikin sa gudun kada ta tashi.

Bangaren sa ya nufa inda yana fita ita kuma ta mike ta fada ban daki.

Wanka tayi ta fito ta saka wata doguwar riga mara nauyi.

Hijab ta saka har kasa ta fara aikin gayaran gidan.

Sai da ta dauki awa biyu sannan ta gama. daki ta koma  ta shiga ban daki ta kara yin wanka.

Fitowa tayi tana shafa mai. Tayi kwalliya me kyau sannan ta bude akwatin ta.

Wani less ne orange kala me adon purple ta dauko.

An masa dinkin riga da zani. Kayan sun mata kyau sosai. silvern dan kunne da sarka ta saka sanna ta dauko turare ta bade jikin ta dashi.

Wayar ta ce tai kara ko da ta duba sai taga Anty ce

Dauka tayi da sauki ta ce.

“Ina kwana Anty?”

“Lafiya lou Amarya ya kuka tashi ya mai gidan naki.”

Kasa Amina tai da kai ta amsa da

“Duk lafiya lou.”

“Ok daman aiken abinci zan muku na ce bari na fada miki.”

Murmushi Amina tayi ta ce,

“To Anty angode Allah kara girma.”

Anty ta ce,

“Ba komai Amina na dauke ki kamar yadda na dauki Ahmad ne da Basma yar ta.”

“To Anty Nagode. Allah saka da alheri.”

“Ameen sai anjima,”

Sukai sallama. Zama tayi a gefen gado a ranta ta na tuno Mama ko ya take.

Sai kuma ga hawaye nan. Gaskiya ta yi kewar Mama wacce kullum suke tare Amina bata taba yin tafiya ko barin Mama ba.

Tana cikin kuka Ahmad ya shigo dakin. Ganin halin da take ciki yasa yai saurin karasawa gun ta.

Kamota yayi inda a take ta ji wani shock ya shiga jikin ta kamar yadda shima Ahmad din yaji.

Da sauri ya janye hannun sa. Kara kamo hannun nata yayi ya ce,

“Haba Meenal mene na kukan da wannan safen. Me nayi miki. Dan Allah kiyi hakuri in nai miki laifi.”

STORY CONTINUES BELOW

Kai ta girgiza masa, janyo ta jikin sa yayi, take yaji wani sanyin dadi na ratsa shi.

Haka ma Amina a take ta manta da komai lamo tayi a jikin sa abinda bata taba yi a jikin wani ‘da namiji ba.

Kallon ta yayi ya ce,

“Me nayi miki?”

Kai ta girgiza. Kallon ta ya tsaya yi take tai saurin dauke idon ta daga kallon sa.

“Meenal!”

Ya kira suna ta cikin wata murya mai sanyi da dadi.

Tsigar jikin ta ce ta tashi inda ta kuma lumshe ido tana shakar kamshin turaren sa.

“Meenal dan Allah ki fadan me yasa ki kuka in nine me nayi bazan kara ba. In wani abu kike bukata kuma ki fadan yanzu zan samo miki shi.”

Idon ta bude ta ce,

“Yaa Ahmad. Mama.”

Sai kuma ta kara fashewa da kuka. Murmushi yayi ya ce,

“To Mama’s gal ayi hakuri ko muje ne?”

Ya tambaye ta yana danne dariyar da take son fito masa.

Kai ta gyada ya ce,

“To shikenan bari mu karya in baki sun tafi sai muje. Ki daina kuka duk lokacin da kika tuno Mama ki fada min kinji, sanna duk abinda kike bukata ki sanar dani da wuri kinji Meenal din Yaa Ahmad.”

Fuska ta rufe da tafin hannu kafin ta dan janye jikin ta daga nashi ta ce,

“Ina kwana?”

Dariya yayi ya janyo ta jikin sa ya ce,

“Naki na amsa din.”

Ya harare ta. Sannan ya ce,

“Baby na ya kika tashi.”

Shiru tayi masa, Kansa ya kai wajen wuyan wani kamshi yaji yana tashi.

Shinshina yake idon sa a lumshe, ba tin yau yake son wannan kamashin jikin Amina nan ba sai dai babu yadda zai yi ne. Amman yanzu ai komai ya kau Amina tashi ce yai duk abinda yake so yayi da ita

Jin yana son yayi wani wajen yasa Amina kokarin fara janye jikin ta.

Kamo ta yayi ya ce,

“Ina zaki”

Knocking ta jiyo wannan yasa tai masa Wayo ta ce,

“Lah kaji ana kwankwasa kofa”

Mikewa yayi, ya ce,

“Ina zuwa.”

Ya fita. Kwanciyya tayi tana lumshe ido. Wani yanayi ta dinga ji a jikin ta wanda bata taba jin kamar sa ba.

Ahmad na zuwa yaga Anty ce ta aikon ‘yar ta Basma.

Murmushi yayi ya bata hanya ta shige cikin falon.

Sai da suka gaisa sannan ya ce bari na kira ta.

Ya mike da saurin yayi dakin ta. Tana kwance ya zo ya same ta.

Zama yayi a gefen gadon ya dago ta a hankali.

Kallon sa tayi suka sakar wa juna su da wani murmushi.

“Basma ‘yar gidan Anty ce ta zo.”

Da sauri ta mike tsaye.

Kallon ta yayi shima ya mike, bayan ta ya bi suka isa falon.

Basma sa’a ce ga Amina dan lokacin biki tana daya gada cikin kawayen Amina da aka sha hidimar biki da ita.

Murmushi Amina tayi ta zauna a gefen ta. Sai da suka gaisa sannan take tambayar ta ya gajiya.

Murmushi Basma tayi ta ce,

“Gajiya sai ku.”

Duk da Amina ta gane me take nufi sai ta kawar da zance.

Ahmad kuma ya mike ya koma daki ya bar su suka dai.

Basma ma mikewa tayi ai kuwa nan da nan Amina ta riko dan ta ce,

“Baza ta tafi ba bayan Yaa Ahmad fita zai yi. Kuma anjima zasu zo da abokan sa.”

Duk da haka kin yadda Basma tayi sai da Amina ta kira Anty a waya sannan

Abincin ta kaiwa Ahmad ta mike zata fita ya janyo ta.

Ya ce,

“Ina zaki je? Ki bar mijin ki.”

Kasa tayi da kai. Ta ce,

“Basma ce kadai a falo fa.”

“Ba da kayan kallo ba. Dan Allah zauna muci abinci fita ma na fada miki zanyi.”

Sauka zatayi daga cinyar sa amman sai ya kara riko ta.

Kallon sa tayi. Ta ce,

“Ya Ahmad zuba maka fa zanyi.”

Mirmushi yayi ya zaunar da ita a gefe sannan ya hada musu abincin.

Farfesun kayan ciki ne da dankali sai kunun gyada da yaji madara.

Da kan sa ya dinga bata sai da ta koshi shima ya hau ci.

Sai da suka gama tsab ta kwashe kayan tayi kitchen dasu.

A wajen Basma ta zauna suna hira jifa jifa.

Sai da ya shirya sannan ya fito wai zai fita.

Mikewa Amina tayi ta raka shi har bakin kofa sannan tai Masa Allah ya kiyaye hanya.

**********

Mami kuwa lokacin da taji batun auren Amina tayi duk iya yin ta abu ya faskara wannan yasa taje gun bokan ta dan kar ‘dan ta ya soma kusantar wannan yarinyar.

Dariya Bokan yayi ya ce,

“Aiki me sauki. Kar ki damu ba abinda zai shiga tsakanin su.”

Godiya tai wa Bokan ta koma da farin ciki. Wannan yana daya daga abin da yasa Mami bata damu da batun auren Ahamd da Amina ba sosai.

********

Bayan Ahmad yaje gidan Mama ya gaishe ta ne ya tambaye me take bukata ta ce masa bakomai.

Daga nan ya mike yayi office din Dady sun jima da Dady. Dady na kara masa nasiha da jan hankalin sa.

Ko da ya mike zai tafi Dady ya ce yaje ya gaishe da Mamin sa.

Kamar yadda Dady ya umarce sa haka ya tafi.

Tin daga gate me gadi yake masa Allah sanya alheri.

Da Ibrahim ya ci karo. Ibrahim ya ce,

“A’ah Yaa Ahmad kai ne. Sannu da zuwa ina Antyn nawa.”

Murmushi Ahmad yayi ya ce,

“Tana lafiya ai kasan inda take ma dai “

Dariya sukai. sannan suka shige gidan a tare.

Mami na zaune a falo kafa daya kan daya sai jijjigata take yi.

Ahmad na shiga ya nufi wajen ta. Zama yayi a gefen ta.

Ya dukar da kai kasa ya ce,

“Mami ina kwana na sameku lafiya.”

“Lafiya lou. Ya amaryar?”

Mami ta tambaye shi cikin sanyi.

Da sauri ya dago kan sa yana kallon Mami. Jin abinda ta tambaye shi.

Murmushin jin dadi yayi ganin Mami ta yadda da Amina.

Ya ce,

“Tana lafiya ta ce agaishe ki ma.”

“Ina amsawa. Ya gajiyar biki.”

“Alhamdulilah Mami.”

“To masha Allah.”

Daga nan ta dinga jan sa da hira har aka kira azahar.

A massalcin cikin gidan su sukai sallah sannan ya koma ciki dan yiwa mami sallama.

Amman sai Mami ta kira Na’ima akan ta hado kayan ta su tafi gidan Yayan Ta.

Na’ima ta koma ciki ta hado wata katuwar akwati ta fito.

Sallama yai wa Mami yana mamakin hali irin na mahaifiyar sa. Ace ayi aure yau kwana daya ta hada shi da yarinya su tafi.

Ba yadda zai yi haka suka tafi gida.

Lokacin har Yasmeen ta je. Dan tare sukai girkin da Amina da Basma suna zaune suna hira abin sha’awa sai ga sallamar Ahmad nan.+

Da sauri Amina ta mike tayi wajen sa. Na’ima ta gani janye da akwati.

Murmushi ta dan yi ta ce,
“Na’ima sannu da zuwa.”

Hannu ta sa zata amshi akwatin tai saurin kawar dashi.

Murmushi tayi ta maida kallon ta ga Ahmad. Ta ce,
“Sannu da zuwa.”

“Yauwah!”
ya fada yana kallon Yasmeen.

“Ah Yasmeen kin zo kenan.”
“Eh wallahi.”

Suka gaisa yai cikin dakin sa.

Bin bayan sa tayi ta shiga taga yana cire kaya.

Har ta juyo yai saurin kamo hannun ta.

Dawo da ita yayi ya ce,
“Ina kuma zaki?”

Kasa tai da kai ta ce,
“Naga kana canja kaya ne.”

“To shine me? Zo ki tayani cirewa ma.”

Kai ta kawar daga kallon sa.
Kukan shagwaba yayi ya ce,
“Allah ni kizo ki ciren kayan.”

Mikewa tayi a hankali ta soma dage masa rigar,

Shi ya taya ta dan ya fita tsayi ba zata iya cire masa ba.tana gamawa ta juya.

Janyo ta ya kuma yi ya daura hannun ta akan kugun sa.

Wani yarr yaji kamar yadda ita ma haka taji a jikin ta.
“Sauran wannan.”

Ya fada yana zura hannun ta cikin wandon. saurin janye hannun ta tayi ta shige ban daki.

Ruwan wanka ta hada masa. Tana fitowa ta ganshi kwance a kan gado da sauri tayi bakin kofa kafin ta ce,
“Yaa Ahmad na hada maka ruwan.”

Ta fice da sauri tana murmushi. gun Basma ta koma taga Na’ima zaune daga gefe sai kallon dakin take tana yatsina.

Murmushi Amina tayi kafin ta ce,
“Basma ki kawo wa Na’ima wani abun ta ci.”

Wani kallo Nai’ma ta watsowa Amina. ta watsa mata ta ce,
“Wa ya ce miki yunwa nake ji. Ko kinga nayi kama da mayun wata ne.”

Shiru Amina tayi ta maida hankalin ta ga Yasmeen da Basma suna hira abin su.
Ahmad be jima ba ya fito cikin shigar kannanun kaya.

Ba karamin kyau yayi ba. Mikewa Amina tayi ta matsa gefen sa ta ce,
“Barka da fito, Abinci ko?”

“Eh! Amman gasu Auwal nan zuwa zan jira su.”
Murmushi tai masa kawai.

Zama yayi a falon shima. Na’ima ya kalla ya ce,
“Ki dau dakin can.”

Ya nuna masa wani dakin dake can gefe a cikin falon.

Sannan ya kalli Amina ya ce,
“Ga kanwar ki nan tazo ta taya ki zama na kwana ki.”

STORY CONTINUES BELOW

Murmsuhi Amina tayi ta ce,
“Nagode kuwa.”

Suna zaune yaji an kira sa. Mikewwa yayi ya ce,
“Meenal sun karaso.”

Mikewa tayi ta ce,
“To Yaya bari na miko muku can site din.”

“Toh!”
Ya fada yana murmushi ya shiga bangaren sa ta kofar Babban falo.

Basma da Yasmeen ta kalla ta ce,
“Sis kuzo muje ku taya ni kai musu abincin.”

Mikewa Basma da Yasmeen sukai suka nufi kitchen Amina kuma tayi daki ta dauko mayafi.

Shinkafa da miyar kaji sukai. Sai hadin kabeji da yaji kwai. Sai lemon da suka hada musu da na kwali hadi da peper chicken. Sai dambun nama da snack da suka hado musu.

Abincin suka hada musu akan katon faranti sannan Amina ta hado musu plates da kofi na da cokali.

Da sallama suka shiga dakin Basma na gaba  sai Yasmeen, Amina na bin bayan su.

Ajiye wa sukai a kan kafet sannan suka durkusa suna gaishe su.

Amina dai kanta a kasa, Ahmad ne ya ce,
“Meenal Wannan shine Auwal ai kin san shi dai.”

Dan hararar sa tayi ta ce,
“Kaji ka Yaya.”

Murmushi sukai. Muslim ya ce,
“Ai in bata san Auwal ba kai ma bata sanka ba.”

Auwal ya ce,
“Eh man!”

Dr ne ya yi dariya ya ce,
“Amina ai nidai kin san ni ko?”

Dago kai tayi, tai.murmushi ta dukar da kai.

Nan ma Muslim din ne yayi magana ya ce,
“Dr kai ma akwai neman magana fa.”

Dariya suka kara yi. Ahmad yayi gyaran murya ya ce,
“To wannan fa. Akun nan.”

Ya fada yana nuna Muslim, dagowa tayi. Ta dan kalle shi sannan tai kasa da kai.
Tabbas ta san shi, amman ta san agun biki ya nuna mata shi.

“To da alama dai bata sanni ni ba.”
Muslim yai maganar.

Ahmad ya ce,
“To aku. Sai kai bayanin kan ka dan kai din nan ko?”

Ya fada yana kwafa. Dariya yayi ya ce,
“Nine Muslim. Muslim dai da kike jin labarin sa. nine wanda na fara nunar da Ahmad son ki yake. Na muku laifi lokacin da na dauke wayar sa ina neman yafiyar ki madam.”

Ya fada yana murmushi. Dariya duka dakin sukai. Amina kuma tai kasa da kai dan kunya ma ya bata.

Ahmad ya ce,
“wannan kuma shine Adanan.”

Ya nuna Adnan. Dan dagowa tayi ta kalle shi sannan tai kasa da kanta.

“Sai kuma wannan!’
Ya nuna wani abokin su danke gefe yana latsa waya.
Kallon sa tai tayi kasa da kanta. Ya ce,
“Wanan shi ne *Najib.* Abokina na abuja mijin *Najwa* “
(Na cikin littafin Najwa)

“Sai wannan kuma.”
Ya nuna dayan dake ta murmushi.

Dan kallon sa tayi tai kasa da kai ya ce,
” *Haidar ne, mijin *Hafsat”*
(Na cikin littafin *Mijin Ummu nah.)

Kai ta gyada masa. Ya ce,
“To kin gansu nan wadan nan sune abokai na, na jiki duk cikin su ba wanda be san ki ba. A zahiri ne dai basu sanki ba saboda bama kasar amman Auwal da Drn ki ai duk kin gane su ko?”

Dr ne ya ce,
“Yo in bata gane mu ba ai bata gane ka ba.”

“Inji wa?”
Ahmad ya tambaya.

Addu’a Muslim ya karai musu sannan suka mike suka koma falon su

Yasmeen ce ta mike ta ce,
“Meenal me zan miki ne?”

Kallon ta Amina tayi ta ce,
“me?”

Yasmeen ta ce,
“Kina nufin ba abinda za muyi miki?”

“Oh! Kuzo muje dakin can kuga.”
Ciki suka shige suka bar Na’ima na cin magani.

Dayan falon suka zauna suna hira abinsu har akai magariba sannan suka yi sallah.

Fitowar su Falo kenan zata raka Yasmeen da Basma. Ahmad ya shigo.

Kallon ta yayi cikin so da kauna ya ce,
“Kizo kuyi sallama.”

Amsa masa tayi ta koma cikin dakin ta.
Atamfa turmi dai dai ta dauko hade da kayan kwalliya da turaruka ta hadawa su Yamseen da Basma.

Godiya sukai mata. Amina ta harare su ta ce,
“Muje.”

Dakin Ahmad suka nufa. Suna shiga suka tadda su Muslim a tsai tsaye.

Amina ta ce,
“Ah har kun tashi bakuci abincin dare ba.”

Baki Muslim ya rike ya ce,
“Kuma mu zuba a wane cikin,”

Auwal ya ce,
“Wallahi dai.”

Haidar kuma, ya ce,
“So kike Hafsta tayi fushi yau banci abincin ta ba.”

Najib ya ce,
“Tab ai ni ko nace na koshi sai tai min dora to ina dalili.”

Suka saka dariya. Ahmad ya ce,
“Gauraye kuma fa.”

Muslim ya ce,
“Muma mun kusa ko Yasmeen!”

Dagowa Yasmeen tayi da ita bata san yasan sunan ta ba.

Kai ya gyada mata alamar ‘Eh da ita yake,’

Kasa tayi da kai. Auwal ya ce,
“Au haka ne, nima kwanan nan ne tinda na samu mata ko Basma.”

Murmushi Basma tayi ta ce,
“Eh man.”

Amina ta ce,
“To shikenan nagode ku gaida gida. Ku kuma Allah tabbatar da alheri.”

Duk suka hada baki wanje cewa
“Ameen ba komai mun gode .”
Kudi suka dire mata kowa dubu ashirin sannan suka fita gaba dayan su.

Ganin su Yasmeen zasu tafi yasa Muslim ya rage mata hanya.

Auwal kuma ya ragewa Basma hanya suka tafi suna masu jin dadin haduwar da sukai.

Ahmad ne ya kalli Amina ya sakar mata murmushi ita ma. Murmushin ta sakar masa.

Bangaren sa suka shige. Kwanu kan ta diba shi ya taya ta diba suka kai kitchen.

Kara komawa tayi dan dibar kayan. Kudin Ya kwaso suka tafi daki.

Dire mata kudin yayi ya ce,
“Wannan sai a saka miki a account.”

Kallon sa tayi ta ce,
“Haba honey. Wane account kuma ka rike a gun ka kawai.”

Ido ya zaro ya ce,
“Me kika ce. Please repeat the name. (Dan Allah maimaita sunan)”

Ido ta rufe ta mike zata fita. Jayo ta yayi ya ce,
“Ina zaki?”

“Kaji fa. Kiran Sallah ake.”
Ta fada tana nuno waje.

Ido ya kanne sannan ya mike ya shiga bandaki dan yin alwala.

Itama daki ta shiga tai alwala tai sallah. Ta jima akan sallaya kafin ta mike ta shiga ktchen.

Wanke wanke ta farayi tana cikin yi Ahmad ya shigo.

Kuyi hakuri naji na da kukai shiru. Nagode*

Juyowa tayi ta kalle shi sannan ta juya wajen aikin ta.

Karasowa yayi ya rumgumo ta, ta baya. Da sauri ta dauke wuta.

Ido ta lumshe kan sa ya langwabar a wuyan ta yana sinsina.

“Yaa Ahmad!”

Ta kira sa cikin wata irin murya.

“Na’am!”

Ya amsa yana ‘kara shige mata.

“Ka bari na karasa aikin.”

“Uhm kawo nai miki.”

Ya karba.

“A’ah dan Allah ka bani.”

Hannu ya daura akan lips din sa ya ce,

“Je kiyi wani abun.”

Murmushi tayi ta fita falo. Falon a gyare yake tsab dan kafin tafiyar su Yasmeen sai da suka ggyara mata.

Dan haka turaren wuta ta juna ta tafi falon da su Ahmad suka zauna.

Gyara shi tayi ta kunna turare sannan ta shiga bedroom din sa ma ta gyara. Ta wanke ban dakin.

Dakin ta ma ta kara share shi sannan ta koma kitchen.

Ya gama wanke wanken yana goge mata kayan kitchen din ta shiga.

Ido ta fito da su waje ta ce,

“Wai Yaya ya sha aiki.”

Karaf a kunnen Na’ima da fitowar ta kenan.

Kwafa tayi ta shige daki da sauri waya ta dauka ta kira Mami.

Mami na dauka ta ce,

“Mami wallahi Amina ta mallake Yaa Ahmad wai har aiki yake mata daga yin auren.”

“Aiki? Aiki fa kika ce.”

Mami ta fada.

“Wallahi Mami aiki aiki dai da kika sani sai ka ce wani mace.”

Na’ima ta fada.

“Barni da shi. Zai zo ya same ni.”

Ta kashe wayar ranta a bace.

Su Amina kuwa suna kitchen tana dafa musu jallop din tafiya wacce taji kaji da kayan lambu.

Ahmad na gefen ta sai santi yake zubawa tin kafin su ci.

“Uhmm uhmm kamshin nan har ya cikan ciki ma.”

Kallon sa tayi ta ce,

“Kai Yaa Ahmad.”

“Wallahi da gaske nake.”

Shiru tai masa tana gamawa ta zuba musu a plate daya ta daura akan daining din dake cikin kitchen din.

Lemo ta dauki musu a friji ta ajiye dukka a daining din.

Fulas ta dauko ta zuba abinci sannan ta dauki lemon kwali da ruwa ta nufi dakin Na’ima da shi,

Ahmad kuwa kallo ya bita dashi yana yaba halin Amina ba ruwan ta.

Tana shiga taga bata dakin wannan yasa ta dire mata ta dawo kitchen din.

Abincin suka fara ci suna ci Ahmad na zuba mata santi har ta ce ta koshi. Shi kuwa sai zurawa yake.

Sai da suka gama suka koma falo suna kallo. Janyo Amina dake gefen sa yayi jikin ta.

Langwabewa tayi, a haka suka dinga kallon.

Na’ima da tafito dan ganin me suke ta hango su a haka da sauri ta koma daki tana me jin haushin Amina.

STORY CONTINUES BELOW

“Wannan ta fiya son miji. Ina gidan ma sai ta zauna kusa da shi.”

Ta fada tana tsaki.

Su Amina kuma sai karfee goma suka mike Ahmad yayi dakin sa itama tayi dakin ta.

Wanka tayi ta shirya cikin doguwar riga ta haye kan gado bayan ta kashe fitila.

Ahmad kuma kamar jiya tinda ya shiga daki ya kasa fitowa.

A zahirin gaskiya yana son yaje ya ga Amina ya kwana kuma akusa da ita. Amman kuma da yaso yaje sai yaji kamar an maida shi.

Da haka ya koma ya kwanta bacci ya dauke shi.

Washe gari yin asuba da ta tashi bata koma ba.

Gidan ta kara sharewa ta kara saka turaren wuta bayan ta feshe freshner.

Kitchen ta shiga ta feraye dan kali sannan ta bude firij ta dauko kifi a ciki.

Bayan ta feraye ta tsane shi. Sannan ta daura shi akan wuta ta soya shi.

Kwai ta fasa ta yanka albasa da tumatur ta soya.

Sannan ta yanka kifi ta wanke ta daura farfesun kifi wanda yaji kayan kamshi.

Daki ta koma, tai wanka, ta shirya cikin wata brown din atamfa me adon blue da milk.

Dinkin riga da siket ne, ya mata kyau sosai.

Kwalliya mai kyau ta yi, ta feshee jikin ta da turaruka.

Kallon madubi tayi, sai ta hango Ahmad tsaye sanye da blue din shadda sai kyalli take.

Yayi kyau dashi ya kara kwarjini. Murmushi yake mata.

Itama murmushi tai masa ta juyo tana kallon sa.

Tana juyowa ya karaso ya rumgume ta.

Ido dukkan su suka lumshe, Kafin ta janye jikin ta.

Durkusawa tayi ta ce,

“Ina kwana yaa Ahmad?”

Dago ta yayi ya ce,

“Lafiya lou, ya kika tashi.”

Ido tai kasa da shi ta ce,

“Lafiya lou.”

“Masha Allah!”

“Muje ka karya ko?”

Kallon ta ya tsaya yi bece komai ba. Murmushi tayi ta ce,

“Yaa Ahmad!”

Shiru. Bai amsa ba dan jijiga shi tayi. Firgit yayi kamar wanda ya tashi daga mafarki.

“Yaa Ahmad lafiya?”

Murmushi yayi, ya ce,

“Meenal son ki yana neman zautar miki dani. Meenal kinyi kyau kin iya kwalliya me kara miki kyau. Ina kaunar ki Meenal dina.”

Ya fada yana kara rumgume ta.

Cikin sanyin murya ta ce,

“Nima ina sonka. Yaa Ahmad.”

“Meenal kimin alkawarin duk abinda zai faru baza ki taba bari na ba.”

Murmushi tayi wanda dimple din ta ya lotsa. Ta ce,

“Na maka alkawarin bazan taba barin ka ba. Nima ina son duk abinda zan maka zaka fahimce ni baza ka kallen da abin ba.”

“Insha Allahu Meenal zan kasance yadda kike so a gare ki.”

Murmushi tayi ta ce,

“Nagode!”

“Banda godiya.”

Hannun sa taja sukai falo. Na’ima suka gani zaune tana kallo.

Gaba sukayi, sai suka jiyo muryar ta tana cewa,

“Yaa Ahmad ina kwana?”

“Lafiya lou.”

Kallon ta yayi ko zata gaida Amina sai yaga ta dauke kai.

“Na’ima baki ga Antyn ki bane.”

Fuska ta hade kafin ta ce,

“Ina kwana?”

Amina tai murmushi ta amsa da

“Lafiya lou. Ya kika tashi?”

“Lafiy!”

Ta amsa mata.

“Ki taso ki karya.”

Ta fada suna karasawa wajen kayan abincin.

Banza Na’ima tai mata. Zama sukai ta hadawa Ahmad  kayan duk abinda tasan zai bukata.

Amman sai yaki ci ya ce, sai ya fara ciyar da ita. Ganin da Na’ima agun yasa ta ce

“A’ah!”

Amman shi ya nace daga karshe ma daukar ta yayi ya daura akan cinyar sa ya dinga bata a baki.

Na’ima da duk abinda suke tana jin su sai dai bata kalle su ba. Ranta yai masifar baci.

Ji take kamar ta tashi ta kwadawa Amina mari.

Amman ba halin yi. Shi kusa sai da ya tabbatar da ta koshi sannan ya ci nashi.

Suna gamawa suka mike suka nufi dayan Falon nasu. Na’ima ta bisu da wani irin kallo na tsana.

Suna shiga ya kunna musu kallo suka koma suka zauna akan kujera a hankali suka dinga hira cikin jin dadi.

Wayar ta dauka ta kira number Mama. Mama na dauka Amina ta ce,

“Mama ina kwana?”

“Lafiya lou. Ya kuke ya gidan?”

Mama ta tambaye ta.

“Lafiya Alhamdulilah!”

“To masha Allah. Amina ana hakuri da juna dan zaman tare zama ne na zo mu saba zo mu zauna. Ki kula da mijin ki mijin ki na son ki dan haka ki kula da shi. Haka nan mahaifin mijin ki shima me son kine. Duk abinda sukai miki na kayan daki an fada min. Amina nayi kuka sosai da Yasmeen ta nuna min awayar ta. Amina ki rike Ahmad dan ya zame miki uwa da uba. Ki ji tsorin Allah kada ki tauye masa hakkin sa. Allah miki albarka Allah baku zaman lafiya.”

“Ameen!”

Amina ta amsa muryar ta a sanyaye dan ba karamin sanyi jikin ta yai ba.

“Ina Ahmad din?”

Mama ta tambaye ta.

Wayar ta mika masa. Amsa yayi suka gaisa, shima godiya da nasiha tai masa.

Zamewa Amina tayi, ta kwanta tana ji suna waya da Mama suna wasa da dariya kamar yadda suka saba.

Sun jima suna hira kafin suyi sallama.

Dago ta yayi ya ce,

“Baby nah bacci ne?”

“A’ah!”

Ta fada

“To tashi muyi hira.”

Mikewa tayi.

Hira suka dinga yi cikin wasa da dariya. Sai karfe sha biyu da rabi ta mike.  Tayi kitchen kamar yadda shima yai alwala ya tafi massalaci.

Fried rice ta dafa musu wacce ta saka musu hanta a ciki. sannan tai musu gashin kaza ta saka dankali da kayan dandano.

Lemon kwakwa tayi ta saka a friji. Falon taje kan daining taga Na’ima bata ci abinci ba.

Hijab ta dauko ta dauki fulas din tayi wajen Baba mai gadin su.

Abincin ta bashi yana ta godiya. Ya juye ya bata kwani kan.

Wanke wanke tayi ta fito ta koma kitchen tai wanka, tai sallah. Ta shirya cikin doguwar rigar yar dubai.

Kayan abincin ta diba ta kai masa daki sauran kuma ta barshi a kitchen.

Tana daki tana gyara fuskar ta ya shigo dakin.

Mikewa tayi a hankali ta taro shi.

Murmushi yayi ya kamo ta sukai bangaren sa.

*Bismillahir Rahamanir Rahim*

Bayan wata daya.

+

Haka rayuwar su Amina da Ahmad ta dinga kasancewa cikin jin dadi da kwanciyyar hankali.

Sai dai abu daya ne Ahmad baya taba iyawa shine kusantar Amina dan da ya zo kofar dakin Amina da niyyar ya kwana zai ji kuma ya fasa baya son shiga.

Na’ima kuwa har yau tana gidan sai gulma da take kwashewa take fada wa Mami.

In kuwa Yaa Ahmad ya tafi aiki tai ta yin abubuwa a gida Amina kuwa in ta shige Daki bata fitowa in ba girki take ba ko wani abun.

Na’ima dai ta takura mata dan tai ta jifar ta da bakaken maganganu.

Bata taba fadawa Ahmad ba dan bata son hada shi da yar uwar sa.

Na’ima kuwa Tana jin haushin yadda take ganin Ahmad ke kula da matar sa duk da ita ma tana burin ana mata kamar haka.

Tana lura da rashin kwanan da baya yi a dakin ta a wannan ba karamin dadi take ji ba.

Dady kuwa har gida ya zo yaga dakin Amina. Ya saka musu albarka tare da bata kudi masu yawa.

Bayan har yanzu be dauke abinda akewa Mama ba.

Sosai yai musu nasiha ya kuma ce da Amina in da akwai matsala tana tarar sa kai tsaye ta fada masa.

Ta dauke shi tamkar mahaifinta sannan duk abinda Ahmad yai mata tana fada masa kar taji koma.

Daga baya yai musu addu’a da nasiha mai ratsa jiki.

*******

Yau kamar kullum tin asuba ta tashi sai dai yau bata jin karfin jikin ta.

Da kyar ta iya gyara gidan ta hada musu break.

Ta shiga tai wanka ta shirya cikin wani farin less wanda akai masa ado da jan abu.

Tayi kyau sosai tai dinkin doguwar riga. Sai dai da ka kalle ta za kasan bata jin dadi.

Bayan ta gama shiryawa ne tayi bangaren Ahmad. Shima lokacin ya fito cikin shirin shi na tafiya office.

Tana ganin sa ta karasa da sauri tana karasa ta saka masa maballi.

Tana gamawa ta durkusa ta ce,

“Ina kwana?”

“Lafiya lou. Ya kika tashi.”

Ya yambaye ta yana kamo hannun ta.

Mikewa tayi ta amsa da

“Lafiya.”

Kallon ta yayi ya ce,

“Meenal me yake damun ki?”

Kallon sa tayi ta ce,

“Me ka gani?”

“Haba Meenal kinsan dai ina gane ki ko ta murya bare kuma gani gaki.”

Murmushi tayi ta ce,

“Weather ce kawai.”

Ta kama hannun sa sukai daining. Sai da suka ci sannan ya mike zai tafi aiki.

Sai da ta rakashi har bakin mota sannan ta dawo.

Daki ta shiga ta kwanta sai bacci. Ba ita ta tashi ba sai karfe daya.

Alwala tayi tai sallah sannan ta fita dan samar musu abinda zasu ci.

Tuwo Ahmad ya ce yana so miyar allayahu wannan yasa aikin ya rike mata ga shi bata jin dadi.

STORY CONTINUES BELOW

Wannan yasa Amina fitowa dan kiran Na’ima ta taimaka mata da aikin.

Na’ima na falo ta saka waka tana kwance tana bi. Amina ta karaso dakin.

Kallon ta Amina tayi, ta ce,

“Naima dan Allah kizo ki kama min aiki. Yai min yawa ga shi bana jin dadi.”

Kallon ta Naima tayi ta ce,

“Ni zan taimaka miki. Kinga malama in baki iya ba ne ki fada kawai.”

Murmushi Amina tayi ta ce,

“Ai kin sani in na iya in ma ban iya ba. Kuma kisan ban taba cewa ki zo ki tayani ba. Gani nayi rana tayi nasan yanzu ma zai iya dawo wa gashi bana jin dadi shiyasa.”

Naima ta ce,

“Au dan baki da lafiya ne? To ki mutu man. Na ce ki mutu man.”

Ta fada tana kure karar wakar da take ji. Gidan ya rude kunnen ka kamar ya cire.

Remote ta dauka! Ta ce,

“Haba Naima ai a waje sai a zage ni.”

“Au a zage ki. To menene in an zage ki.”

“Ya isa kuma. Nan fa gidan mijina na ne ba gidan ki ba.”

Mikewa Na’ima tayi ta ce,

“Ohho to ai ban fahimta ba yanzu na fahimci me kike nufi. Sannu masu gidan miji sannu masu aure.  Ai banga abinda auren naki ya tsinana miki ba. Miji na can kina can shine auren ah lallai.”

Tayi shewa. Sannan ta ce,

“Gida kuma gidan wa nane duk yadda na ga dama haka zanyi kuma ba wanda ya isa ya hanani ko ya ta kura min. Kema kije ki yi takama da gidan ku ko gidan wan ki amman ba dai gidan wa na ba.”

Ran Amina in yayi dubu ya baci. Zuciyar ta tai mata zafi.

Na’ima ta ce,

“Sannan kuma ki maza ki kunna min kayan kallon nan.”

Wani kallo Amina tai mata, ta ce,

“To bazan kunna ba. Wai waya ce miki *durkusawa wada gajiya wa ce.* kar kiga ina raga miki wallahi dan ina auren wan kine.”

“Sannu. Nace sannu. Lallai samun waje. Shi daman dan matsiyaci bai iya cin arziki ba.”

Ido Amina ta zaro dan mamakin abinda Na’ima ke mata.

Bata taba zaton zata iya aika ta mata haka ba.

Cikin zafin rai ta daga hannu ta tsinka “mata mari.

Dafe kunci Na’ima tayi ta ce,

“Kika mare ni.”

Ta daga hannu zata mare ta kenan Ahmad ya shigo.

“Kai kai kai. Me zan gani haka?”

Ya tambaya ransa a bace.

“Yaya ba ita bace ta mare ni ba.”

“Rufe min baki mara kunyar banza da wofi ke in kina da hankali ma har ka ce zaki mari matar wanki. Kenan ma ni ma zaki iya mari na. Na’ima ina miki magana wallahi ki shiga hankalin ki. Ko da yake ai *duk abinda ka aikata kai ma za ai maka.* “

Ya fada yana huci dan ransa ya baci.

Amina tuna ta daura abu akan gas yasa ta koma kitchen da sauri.

Tuwon ta tuka ta wanke nama ta tafasa ta soya.

Kayan miyar ta daura ta dafa shi. Dai dai shigowar Ahmad kenan.

Bataji shigowar sa ba sai ji tayi ya rumgume ta. ido ta lumshe. Ta fara magana kamar haka.

“Kayi hakuri Yaa Ahmad wallahi rai nane ya baci amman hakan bazata kara faruwa ba.”

“Shittt!”

Ya fada hannun sa daure akan lips din sa.

Ya ce,

“Kar ki damu nafi kowa sanin wace Amina. Dan haka kiyi hakuri ki kara hakuri da yan gidan mu.”

“Ba komai Yaa Ahmad yan gidan ku ai sun zama yan gidan mu.”

Murmushi yayi ya ce,

“To ina zuwa bari naje na dawo.”

“To Yaya adawo lafiya.”

STORY CONTINUES BELOW

Ya fita. Falo ya koma gun Na’ima ya ce ta kwaso kayan ta.

Akwatin ta, ta dauko da duk abinda tasan nata ne.

A mota ya saka ta ya zagaya ya tada motar ya nufi gidan su da ita.

Suna zuwa gidan ya bude mata kofa ya sauka ya ciro mata akwatin ta.

Dady da dawowar sa kenan ya ce,

“A’ah lafiya?”

Ahmad ya ce

“Dady wannan yarinyar ce gaba daya ta fiti ne ni a gida. Masifar rana da ban da yamma da ban ta dare da ban haka ma ko da yaushe duk da Amina bata nuna damuwa amman tin da har yau Amina tai abu Dady kansan an kai ta bango.  Dan haka shine na dawo da ita.”

Dady ya ce,

“Bani na ce ki girmama Amina ba a matsayin ta na matar wanki.

“To Dady haka ake ai ta maida ni yar  Aikin ta,”

Mami ce ta fito wacce duk tana jin abinda ke faruwa ta ce,

“To kunji ko? Ya za ayi ta maida yar gida baiwa.”

Ahmad dai shiru yayi. Dady ya ce,

“Ai Amina yar gida na dauke ta tin kan ta auri Ahmad ma bare kuma da ta aure shi.”

Jan Ahmad yayi suka shiga cikin gidan suka bar Mami da Na’ima agun.

Na’ima ta ce,

“Mami wallahi kinyi sakaci. Kinga yadda ta mai da Yaya ya zama dan aiki sai abinda take so zai yi. Haka tace ita bata cin kaza sai kaza. Mami kinga kuwa.”

Mami ta ce,

“Na shiga uku yanzu ya zanyi.!”

“Mami baki gani ba shine kawo wannan kawo wannan. Kinga abinda yake kawo wa kuwa Mami wani abun ma ban san shi ba Wallahi.”

Mami dai duk ta rude. Naima ta ce,

“Mami wallahi ta asirce shi”

Mami ta ce,

“Ai daman na sani. Na shiga uku.”

Na’ima tayi cikin gida ta bar Mami na zageye ranta a bace kamar tayi hauka.

Amina kuwa tana gama girki ta shiga ta sake wanka. Shiryawa tayi cikin wata doguwar riga baka an mata ado da milk,

Rigar roba ce daga sama ta matse daga kasa kuma ta saki.

Ta mata kyau gashin kan ta, ta gyara, ta paka a taskiyar kan ta kamar baby.

Jikin ta, ta feshe da turare ta koma falo ta kunna kallo tana yi.

har akwai la’asar ta mike ta tada sallah.

Kwanciyya ta karayi. Ahmad be dawo gidan ba sai bayan magariba. Sai da yai har sallah isha sannan ya shigo.

Tana zaune akan sallaya ya shiga dakin ta. Tana ganin sa ta shafa fatiha ta mike.

“Sannu da zuwa Yaa Ahmad!”

Hanyar Ban daki ta shiga ta hado masa ruwan wanka. Sannan ta dawo ta taya sa rage kaya.

Wanka ya shiga inda kafin ya fito har ta bar dakin.

Sai da ya shirya  sannan ya fito a daining ya tadda Amina tana kara gyara wajen.

Zama yayi ta fara serving din shi abinci ta zuba masa ta tura masa gaban sa.

Kallon ta yayi yace

“Ke ma dai da son rigima zo nan.”

Matsawa tayi gun sa ya gutsuro yayo bakin ta dashi.

Kai ta kawar ta ce,

“Yaa na koshi naci dazu.”

Fuska ya bata ya ce,

“Me yasa kika ci?”

Murmushi tayi ta ce,

“To yunwah nake ji shi yasa.”

“Ah kinyi dai dai da wanna.”

Nan kuwa ba abinda ta ci.

Shi ya dinga cin abincin har ya koshi. Falo suka koma anan ta tambaye shi ina ya kai Na’ima

STORY CONTINUES BELOW

“Gida!”

Baki ta dafe ta ce,

“Gida kuma saboda me dan Allah?”

Kallon ta ya tsaya da mammaki ita da zatai murna amman ita ce me damuwa.”

Fuska ya daure ya ce,

“Saboda haka nayi niyya.”

“Allah baka hakuri banyi tambayar da niyar bata maka ba.”

Janyo ta yayi ya ce,

“Nima kiyi hakuri.”

Murmushi tayi. Daga haka kowa yayi bangaren sa.

Sai yau  Amina take tambayar kanta akan rashin kwanan Ahmad a dakin ta.

Da farko bata kawo komai ba sai yanzu da Naima ta fada mata magana.!

*MS Indabawa*07/07/2018

🌵🌵🌵🌵

*Koma kan mashekiya*

*(kaikayi)*

🌵🌵🌵🌵

*Almost true life story*

Na *Maryam S Indabawa*

*MANS*

🌐 *HAJOW*🌐

🌐🌐🌐 *Hakuri da Juriya Online writers* 🌐🌐🌐

Page *18*

*Bismillahir Rahamanir Rahim*

Bayan wata daya.

Haka rayuwar su Amina da Ahmad ta dinga kasancewa cikin jin dadi da kwanciyyar hankali.

Sai dai abu daya ne Ahmad baya taba iyawa shine kusantar Amina dan da ya zo kofar dakin Amina da niyyar ya kwana zai ji kuma ya fasa baya son shiga.

Na’ima kuwa har yau tana gidan sai gulma da take kwashewa take fada wa Mami.

In kuwa Yaa Ahmad ya tafi aiki tai ta yin abubuwa a gida Amina kuwa in ta shige Daki bata fitowa in ba girki take ba ko wani abun.

Na’ima dai ta takura mata dan tai ta jifar ta da bakaken maganganu.

Bata taba fadawa Ahmad ba dan bata son hada shi da yar uwar sa.

Na’ima kuwa Tana jin haushin yadda take ganin Ahmad ke kula da matar sa duk da ita ma tana burin ana mata kamar haka.

Tana lura da rashin kwanan da baya yi a dakin ta a wannan ba karamin dadi take ji ba.

Dady kuwa har gida ya zo yaga dakin Amina. Ya saka musu albarka tare da bata kudi masu yawa.

Bayan har yanzu be dauke abinda akewa Mama ba.

Sosai yai musu nasiha ya kuma ce da Amina in da akwai matsala tana tarar sa kai tsaye ta fada masa.

Ta dauke shi tamkar mahaifinta sannan duk abinda Ahmad yai mata tana fada masa kar taji koma.

Daga baya yai musu addu’a da nasiha mai ratsa jiki.

*******

Yau kamar kullum tin asuba ta tashi sai dai yau bata jin karfin jikin ta.

Da kyar ta iya gyara gidan ta hada musu break.

Ta shiga tai wanka ta shirya cikin wani farin less wanda akai masa ado da jan abu.

Tayi kyau sosai tai dinkin doguwar riga. Sai dai da ka kalle ta za kasan bata jin dadi.

Bayan ta gama shiryawa ne tayi bangaren Ahmad. Shima lokacin ya fito cikin shirin shi na tafiya office.

Tana ganin sa ta karasa da sauri tana karasa ta saka masa maballi.

Tana gamawa ta durkusa ta ce,

“Ina kwana?”

“Lafiya lou. Ya kika tashi.”

Ya yambaye ta yana kamo hannun ta.

Mikewa tayi ta amsa da

“Lafiya.”

STORY CONTINUES BELOW

Kallon ta yayi ya ce,

“Meenal me yake damun ki?”

Kallon sa tayi ta ce,

“Me ka gani?”

“Haba Meenal kinsan dai ina gane ki ko ta murya bare kuma gani gaki.”

Murmushi tayi ta ce,

“Weather ce kawai.”

Ta kama hannun sa sukai daining. Sai da suka ci sannan ya mike zai tafi aiki.

Sai da ta rakashi har bakin mota sannan ta dawo.

Daki ta shiga ta kwanta sai bacci. Ba ita ta tashi ba sai karfe daya.

Alwala tayi tai sallah sannan ta fita dan samar musu abinda zasu ci.

Tuwo Ahmad ya ce yana so miyar allayahu wannan yasa aikin ya rike mata ga shi bata jin dadi.

Wannan yasa Amina fitowa dan kiran Na’ima ta taimaka mata da aikin.

Na’ima na falo ta saka waka tana kwance tana bi. Amina ta karaso dakin.

Kallon ta Amina tayi, ta ce,

“Naima dan Allah kizo ki kama min aiki. Yai min yawa ga shi bana jin dadi.”

Kallon ta Naima tayi ta ce,

“Ni zan taimaka miki. Kinga malama in baki iya ba ne ki fada kawai.”

Murmushi Amina tayi ta ce,

“Ai kin sani in na iya in ma ban iya ba. Kuma kisan ban taba cewa ki zo ki tayani ba. Gani nayi rana tayi nasan yanzu ma zai iya dawo wa gashi bana jin dadi shiyasa.”

Naima ta ce,

“Au dan baki da lafiya ne? To ki mutu man. Na ce ki mutu man.”

Ta fada tana kure karar wakar da take ji. Gidan ya rude kunnen ka kamar ya cire.

Remote ta dauka! Ta ce,

“Haba Naima ai a waje sai a zage ni.”

“Au a zage ki. To menene in an zage ki.”

“Ya isa kuma. Nan fa gidan mijina na ne ba gidan ki ba.”

Mikewa Na’ima tayi ta ce,

“Ohho to ai ban fahimta ba yanzu na fahimci me kike nufi. Sannu masu gidan miji sannu masu aure.  Ai banga abinda auren naki ya tsinana miki ba. Miji na can kina can shine auren ah lallai.”

Tayi shewa. Sannan ta ce,

“Gida kuma gidan wa nane duk yadda na ga dama haka zanyi kuma ba wanda ya isa ya hanani ko ya ta kura min. Kema kije ki yi takama da gidan ku ko gidan wan ki amman ba dai gidan wa na ba.”

Ran Amina in yayi dubu ya baci. Zuciyar ta tai mata zafi.

Na’ima ta ce,

“Sannan kuma ki maza ki kunna min kayan kallon nan.”

Wani kallo Amina tai mata, ta ce,

“To bazan kunna ba. Wai waya ce miki *durkusawa wada gajiya wa ce.* kar kiga ina raga miki wallahi dan ina auren wan kine.”

“Sannu. Nace sannu. Lallai samun waje. Shi daman dan matsiyaci bai iya cin arziki ba.”

Ido Amina ta zaro dan mamakin abinda Na’ima ke mata.

Bata taba zaton zata iya aika ta mata haka ba.

Cikin zafin rai ta daga hannu ta tsinka “mata mari.

Dafe kunci Na’ima tayi ta ce,

“Kika mare ni.”

Ta daga hannu zata mare ta kenan Ahmad ya shigo.

“Kai kai kai. Me zan gani haka?”

Ya tambaya ransa a bace.

“Yaya ba ita bace ta mare ni ba.”

“Rufe min baki mara kunyar banza da wofi ke in kina da hankali ma har ka ce zaki mari matar wanki. Kenan ma ni ma zaki iya mari na. Na’ima ina miki magana wallahi ki shiga hankalin ki. Ko da yake ai *duk abinda ka aikata kai ma za ai maka.* “

Ya fada yana huci dan ransa ya baci.

Amina tuna ta daura abu akan gas yasa ta koma kitchen da sauri.

Tuwon ta tuka ta wanke nama ta tafasa ta soya.

STORY CONTINUES BELOW

Kayan miyar ta daura ta dafa shi. Dai dai shigowar Ahmad kenan.

Bataji shigowar sa ba sai ji tayi ya rumgume ta. ido ta lumshe. Ta fara magana kamar haka.

“Kayi hakuri Yaa Ahmad wallahi rai nane ya baci amman hakan bazata kara faruwa ba.”

“Shittt!”

Ya fada hannun sa daure akan lips din sa.

Ya ce,

“Kar ki damu nafi kowa sanin wace Amina. Dan haka kiyi hakuri ki kara hakuri da yan gidan mu.”

“Ba komai Yaa Ahmad yan gidan ku ai sun zama yan gidan mu.”

Murmushi yayi ya ce,

“To ina zuwa bari naje na dawo.”

“To Yaya adawo lafiya.”

Ya fita. Falo ya koma gun Na’ima ya ce ta kwaso kayan ta.

Akwatin ta, ta dauko da duk abinda tasan nata ne.

A mota ya saka ta ya zagaya ya tada motar ya nufi gidan su da ita.

Suna zuwa gidan ya bude mata kofa ya sauka ya ciro mata akwatin ta.

Dady da dawowar sa kenan ya ce,

“A’ah lafiya?”

Ahmad ya ce

“Dady wannan yarinyar ce gaba daya ta fiti ne ni a gida. Masifar rana da ban da yamma da ban ta dare da ban haka ma ko da yaushe duk da Amina bata nuna damuwa amman tin da har yau Amina tai abu Dady kansan an kai ta bango.  Dan haka shine na dawo da ita.”

Dady ya ce,

“Bani na ce ki girmama Amina ba a matsayin ta na matar wanki.

“To Dady haka ake ai ta maida ni yar  Aikin ta,”

Mami ce ta fito wacce duk tana jin abinda ke faruwa ta ce,

“To kunji ko? Ya za ayi ta maida yar gida baiwa.”

Ahmad dai shiru yayi. Dady ya ce,

“Ai Amina yar gida na dauke ta tin kan ta auri Ahmad ma bare kuma da ta aure shi.”

Jan Ahmad yayi suka shiga cikin gidan suka bar Mami da Na’ima agun.

Na’ima ta ce,

“Mami wallahi kinyi sakaci. Kinga yadda ta mai da Yaya ya zama dan aiki sai abinda take so zai yi. Haka tace ita bata cin kaza sai kaza. Mami kinga kuwa.”

Mami ta ce,

“Na shiga uku yanzu ya zanyi.!”

“Mami baki gani ba shine kawo wannan kawo wannan. Kinga abinda yake kawo wa kuwa Mami wani abun ma ban san shi ba Wallahi.”

Mami dai duk ta rude. Naima ta ce,

“Mami wallahi ta asirce shi”

Mami ta ce,

“Ai daman na sani. Na shiga uku.”

Na’ima tayi cikin gida ta bar Mami na zageye ranta a bace kamar tayi hauka.

Amina kuwa tana gama girki ta shiga ta sake wanka. Shiryawa tayi cikin wata doguwar riga baka an mata ado da milk,

Rigar roba ce daga sama ta matse daga kasa kuma ta saki.

Ta mata kyau gashin kan ta, ta gyara, ta paka a taskiyar kan ta kamar baby.

Jikin ta, ta feshe da turare ta koma falo ta kunna kallo tana yi.

har akwai la’asar ta mike ta tada sallah.

Kwanciyya ta karayi. Ahmad be dawo gidan ba sai bayan magariba. Sai da yai har sallah isha sannan ya shigo.

Tana zaune akan sallaya ya shiga dakin ta. Tana ganin sa ta shafa fatiha ta mike.

“Sannu da zuwa Yaa Ahmad!”

Hanyar Ban daki ta shiga ta hado masa ruwan wanka. Sannan ta dawo ta taya sa rage kaya.

Wanka ya shiga inda kafin ya fito har ta bar dakin.

Sai da ya shirya  sannan ya fito a daining ya tadda Amina tana kara gyara wajen.

Zama yayi ta fara serving din shi abinci ta zuba masa ta tura masa gaban sa.

Kallon ta yayi yace

“Ke ma dai da son rigima zo nan.”

Matsawa tayi gun sa ya gutsuro yayo bakin ta dashi.

Kai ta kawar ta ce,

“Yaa na koshi naci dazu.”

Fuska ya bata ya ce,

“Me yasa kika ci?”

Murmushi tayi ta ce,

“To yunwah nake ji shi yasa.”

“Ah kinyi dai dai da wanna.”

Nan kuwa ba abinda ta ci.

Shi ya dinga cin abincin har ya koshi. Falo suka koma anan ta tambaye shi ina ya kai Na’ima

“Gida!”

Baki ta dafe ta ce,

“Gida kuma saboda me dan Allah?”

Kallon ta ya tsaya da mammaki ita da zatai murna amman ita ce me damuwa.”

Fuska ya daure ya ce,

“Saboda haka nayi niyya.”

“Allah baka hakuri banyi tambayar da niyar bata maka ba.”

Janyo ta yayi ya ce,

“Nima kiyi hakuri.”

Murmushi tayi. Daga haka kowa yayi bangaren sa.

Sai yau  Amina take tambayar kanta akan rashin kwanan Ahmad a dakin ta.

Da farko bata kawo komai ba sai yanzu da Naima ta fada mata magana.!

Tana mamakin abinda ya hana Yaa Ahmad kwanan dakin ta.

Yaa Ahmad me zumudin ya ganshi a kusa da Aminan sa amman shine mai nisantar ta.

Ta bangaren Ahmad ma abin ba karamin damun sa yake ba.

Bashi da buri da ya wuce ya ganshi tare da Aminan sa.

Bai da buri da ya wuce ya kusance ta. Amman ya rasa me yake hana shi zuwa gare ta. Tinda yasan itama abin zai dame ta.

Haka suke zama suyi wasa da dariya suci abinci su zauna suyi kallo suyi hira amman daga nan ba abinda yake kara hada su.

Abin yana daure masa kai. Dan wani lokaci da kyar yake iya bacci.

Da dare suna zaune a falo suna hira Amina ta gyara zama ta ce,

“Yaya!”

Juyowa yayi ya kalle ta, ya ce,

“Na’am Babyn Yayan ta.”

Murmushi tayi ta ce,

“Yaya dan Allah ka kaini wajen Mama dan Allah.”

Kanta ya dafa ya yi murmushi ya ce,

“Duk abinda Baby nah ke so shi zan mata.”

Murmushin jin dadi tayi ta ce,

“Nagode!”

“To yaushe zakije.?”

Ya tambaye ta.

Baki ta bude ta ce,

“Lallai Yaya aai ko yanzu kace nazo muje zan je.”

Dariya yayi ya ce,

“To shikenan gobe yayi ko?”

Da sauri ta gyada kai ta ce,

“Eh! Yayi Yaya nagode.”

Fuskar ta ya shafa yana murmushi. Ya ce,

“Baby na ina son ki. Ina kaunar ki Allah ya barmin ke.”

Murmushi tayi ta ce,

“Ameen Yaya nah.”

“To me zaki kai wa Mama gobe?”

Ya tambaye ta yana wasa da hannun ta.

Kai ta daga tana tunani kafin ta ce,

“Sai dai goben in nayi tinani. Amman zan mata miya dai.”

Kai ya gyada ya ce,

“To sai muyi ko?”

“Nagode Yaya.”

Mintsinin ta yayi ya ce,

“Ba nace banda godiya ba.”

Kai ta gyada tana sosa gun da ya mintsine ta.

“Oh sorry!”

Ya fada yana kamo hannun. Iska ya dinga busa mata a hannu.

Washe gari tin asuba bata koma ba sai da ta gyara gidan sannan ta shiga kitchen ta daura breakfast. Sannan ta dauko kaji a firij ta yayyanka ta wanke ta daura akan gas ta zuba masa albasa.

Kayan miya ta diba ta gyara ta markada, ta daura ta tafasa su.

Soya su tayi ta hada miya. Dankali ta suya musu da kunun gyada.

Sannan ta dibi flour ta kwaba da butter dakwa ta zuba sugar ta kwaba cake.

Tana fara beaking ta kara dibar wata fulawar tayi kwabin meat pie.

Nama ta dauko ta gyara ta tafasa ta daka ta suya sannan ta hada ta suya.

Tana gamawa ta har hada a cikin wasu set don fulas.

STORY CONTINUES BELOW

Gida biyu ta raba duk abinda tayi sanna ta ajiye wasu a container da tayi amfani da ita.

Kitchen din ta gyara ta nufi dakin ta a gajiye.

Wanka ta shiga tayi ta fito ta saka wani dogon wando sai riga Wacce takai gwiwa.

Dan karamin Hijab ta saka ta feshe jikin ta da turare sannan ta fita falo.

Lokacin karfe sha daya. Yaa Ahmad ta gani zaune yana kallon TV.

Tana shigo ya dago kai yana kallon ta yana zuba mata murmushi.

Karasawa wajen sa tayi tana durkusawa.

“Ina kwana?”

“Lafiya lou! Baby na kin fito daga wankan?”

Murmushi tayi ta ce,

“Eh!”

“Kin tashi lafiya?”

“Lafiya lou. Muje ka karya ko?”

Mikewa yayi suka karasa daining din. Hada masa komai tayi sannan ta hada nata kunun.

Suna gamawa ta ce,

“Yaya in shiryi mu tafi.”

Murmushi yayi ya gyada mata kai shima ya mike yayi dakin sa.

Kayan jikin ta, ta cire ta saka wani material milk kala ne an masa ado da purple da orange kala.

Dinkin riga da siket rigar three quarter ce, ta zauna a kugun ta, Milk din mayafi ta dauko da milk din jaka da takalmi.

Akwatin ta dauko ta debo turmin atamfa guda biyu da shadoji yadi goma goma duda biyu sai turaruka masu tsada da kamshi da ta kwaso.

A wata babar jaka ta zuba kayan sannan ta debo kayan kwalliya ta watsa a ciki.

Daukowa tayi ta ajiye a falo.  ta shiga kitchen ta fito da kwanu kan.

Yaa Ahmad na fitowa ya fara jidar kayan yana sawa a cikin mota.

Sai da ya gama tsab sannan suka tafi.

A cikin motar yake tambayar ta me za a siyo wa Mama.

Ba komai Amina ta fada. Hararar ta yayi ya ce.

“Kin ma isa zakije gun Maman ki ‘ki siya mata komai.”

A wani store ya tsaya ya siyo mata kaya da su lemuka da sauran su.  sannan suka dau hanya.

Suna zuwa gidan ya fito ya bude gate din sannan ya shiga da motar.

Gate din ya kara rufewa sannan ya dawo.

Amina kuwa cikin gidan tayi da gudun ta, tana kira Mama.

“Mama nah! Mama nah!”

Mama dake kitchen ta jiyo muryar Amina da sauri ta fito.

Amina na ganin ta ta fada jikin ta tana murnar ganin ta. Ta ce,

“Mama nah nayi kewar ki wallahi.”

Murmushi Mama tayi ta kamo ta sukai Falo.

Yaa Ahamd suka gani yana shigo da kayan da suka siyo da wanda Amina ta zo da su.

Sai da suka zauna sannan Amina ta gaida Mama.

Mama ta amsa cikin kulawa. Ya Ahmad ma ya gaishe ta.

Amina ce kalli kayan ta ce,

“Yaa Ahmad wannan da wannan da wancan ba na Mama bane.”

Kallon ta yayi da mamaki. Kai ta gyada masa ta ce,

“Nasu Mami ne.”

Mama ta ce,

“Gaskiya kam kin kyau. To tashi kije ki maida mata cikin mota.”

Mikewa tayi Yaa Ahmad ma ya mike. Fulas din ta dauka guda biyu shi kuma ya dau jakar da dayan fulas din.

Sai da suka saka a mota sanna suka koma ciki. Tare da Yaa Ahmad suka kwashe kayan suka saka a kitchen.

Sai da suka zauna take fada wa Mama abinda ta yo mata.

Albarka Mama ta sanya musu, tana godiya.

Da rana Shinkafa kawai Amina ta dafa sukaci.

Sai da akai azahar sannan Yaa Ahmad ya fita ya ce, anjima zai dawo ya dauke ta.

Mama da Amina sun sha hira. Mama sai karai wa Amina fada take akan ta kula da iyayen mijin ta da mijin ta.

Tin karfe biyar Mama ta sa ta kira sa dan suje gidan Mami.

Amman Yaa Ahmad be tashi zuwa ba sai bayan magariba.

Yana zuwa Mama tasa ta kawo masa abinci.

Abincin ta kawo masa ci ya zauna yi inda sai da akai isha’i sukai sallah sannan suka tafi gidan Mami.

A hanya sai mita Amina take wai sai dare zasu gaida Mamin.

Ahmad kuwa yana sane duk dan su samu Dady a gida ne dan yasan in Dady baya nan Amina baza taji dadin zuwa ba

Suna zuwa Ibrahim ya kwashi kayan yai cikin gida dasu yana murnar zuwan su.

Da sallama suka shiga dakin. Dady ne zaune yana kallo gefen sa Mami.

Durkusawa sukai har kasa suna gaishe da su.

Dady ne ya amsa cikin kulawa da so da kauna.

Mami kuwa kamar baza ta amsa ba. Dady yana tambayar su,

“Ya gidan in ce dai ba matsala ko?”

Suka amsa mata da “Ba  komai.”

“To Allah yayi Albarka.”

Ibrahim, Dady ya kalla ya ce, ya kira Na’ima ta kawo musu lemo da ruwa.

Na’ima dake daki tana waya da saurayin ta Ibrahim ya kai mata sakon Dady.

Bata san su waye ba dan haka da saurin ta taje ta debo musu.

Tana zuwa Falo taga Amina sai ta hade rai. Direwa tayi ta gaishe da Ahmad ta juya zata tafi Dady ya kira ta.

“Baki ga Antyn ki bane?”

Dady ya tambaye ta.

Fuska ta kara batawa ta ce,

“Ina yini?”

Tayi ciki ba tare da ta tsaya amsawa ba. Mami ma mikewa tayi tai cikin gidan.

Dady ne ya girgiza kai yana mata addu’ar Allah ya shirya ta.

Ahmad ne ya matso da kayan da Amina ta kawo Bude fulas yayi yana nuna masa.

Dady sai dadi yake ji yana murna. Yana sa mata albarka.

Yana ganin miya ya ce,

“Amina daukon waccan shinkafa, inci da miyar ki.”

Daukowa tayi hade da plate. Abincin ta zuba masa, ta zuba masa miyar da nama da yawa.

Mikawa masa yayi yana sa mata albarka.

Ci yake yana santi sun sha hira. Har ya gama yaci snacks din.

Santi yake ya ce,

“Uhmm Ahmad ashe wayo kai min. Kullum wannan dadin kake ci, ka barni da abincin su Mamin ka.”

Murmushi Ahmad da Amina sukai. Dady ya ce,

“Amina Allah miki albarka Allah kara hade kan ku. Allah ya baki zuri’a ta gari.”

Ahmad da yaji maganar Dady sai jikin sa yai sanyi.

Dady ya kalle shi yace,

“Ahmad ya dai?”

“Ba komai!”

Ya fada yana yin kasa da kansa.

Amina ma kasa tayi da kansa. Dady yayi murmushi. suka dinga hira har tara da rabi.

Amina ce, ta ce,

“Ina Mami zatai mata sallama.”

Dady ya kalle su ya ce,

“Ahmad ka raka ta kuje ko?”

Suka mike sukai ciki. Mami na zaune akan gadon ta suka shiga da sallama.

Amsawa tayi tana ganin Amina ta dauke kan ta.

Dan durkusawa tayi ta ce,

“Mami mun fito zamu tafi sai da safe.”

Tsaki Mami tayi ta ce,

“To Mayya sai da safe wallahi kurwa ta da ta dana tafi karfin ki.”

Shiru Amina tayi ta mike, Mami ta bita da wani mugun kallo ta ce,

“Shegiya matsiya ciya. Mayya kin zama mana karfen kafa kin makalewa ‘dana kamar cingum.”

Amina dai bata juyo ba ta fice idon ta jajir.

Ahmad kuma da ransa yai mummunan baci yai shiru dan ba yadda zaiyi da mahaifiyar ta shi.

STORY CONTINUES BELOW

Mikewa yayi ya ce,

“To Mami mun tafi.”

“To wato dan na zage ta shine zaka tafi ko?”

Kai ya girgiza ya ce,

“A’ah ba haka bane, daman tafiya zamuyi.”

“To zauna zamuyi magana da kai. In kuma ita zaka bi ga hanya nan.”

“Allah baki hakuri.”

Ya fada yana yin kasa da kan sa.

Mami ta ce,

“Naji duk abinda kake mata wallahi Ahmad ka kiyaye ni wato kazama bawan ta ko? Sai abinda take so kake mata ko? Kai baza ka zama namiji ba ko? Kane ajiye mata kudi tai ta dauka ko?  Ahmad wallahi ka kiyaye ni.”

“Ayi hakuri Mami zan gyara insha Allahu”

Mami ta ce.

“Kar ma ka gyara nima zan gyara maka ne. Ka bi ka tsaya yarinya karama na juya ka. Ka zama soko. Abinda nake gudu kenan daman kuma an juyar min da kan ka.”

Shiru yayi. Mami ta gama bambamim ta. Sai da ta gama sannan Ahmad ya ce,

“Mami ayi hakuri.”

“Kaji zancen auren Na’ima ko?”

Kai ya gyada ya ce,

“Dady ya fada min. Me kuke bukata daga gare ni.”

“Zamu rubuto maka list din.”

“Shikenan.”

Ya zura hannu a aljihu ya mika mata kudi.

Amsa tayi tana godiya. sannan ya ce,

“Mami ga kaya can Amina ta kawo,”

Banza tai masa, mikewa yayi ya ce,

“To Mami sai da safe.”

“Allah tashe mu lafiya.”

“Ameen!”

Ya fita.

Amina kuwa tana fita falo Dady ya gane Mami ta mata tsiyar.

Hakuri yake bata yana mata nasiha.

“Amina kiyi hakuri da Mamin taki, Mai hakuri shi kan dafa dutse, kisan wata rana sai labari kiyi hakiri.”

Kawar da damuwar tayi ta ce,

“Dady ba komai wallahi ai Mami uwa ta ce.”

“To Allah miki albarka.”

“Ameen!”

Amina ta fada. Ibrahim ne ya shigo ya ce,

“Anty nah.”

Hararar sa tayi ta ce,

“Ni ba ruwana da kai. Dady kaga yaron nan zuwan sa daya fa.”

Dady ya ce,

“Kai kai kai, ai kam nagan ku a rana.”

“A’ah A’ah Dady baka gan mu ba. Ni da zan dawo gidan ma gaba daya.”

Da sauri Amina ta dago ta ce,

“Dan Allah da Gaske.”

“Wallahi!”

Ibrahim ya fada.

Dady, Amina kalla ta ce,

“Dady dan Allah ka bamu Ibrahim dan Allah.”

Murmush Dady yayi ya ce,

“Amina Indai ibrahim ne na baku shi. Ki ta

rike shi amana.”

Durkusawa tayi ta ce,

“Dady nagode Allah saka da alheri.”

“Ba komai ‘ya ta.”

ibrahim ya matsa kusa da kayan da Amina ta kawo ya ce,

“Dady me Antyn ta kawo mana.”

Dady ya ce,

“Gashi nan har naci abincin ta mai dadi.”

Murmuashi Ibrahim yayi ce,

“Ai Anty Ta iya girki kamar me?”

Suna cikin haka sai ga Ahmad nan ya fito.

Ganin su yai suna wasa da dariya gwanin sha’awa. Shima zama yayi suka dan taba hira.

Sanna suka mike suka tafi. Dady na sa musu albarka.

Har bakin mota Ibrahim da Dady suka raka su.

Dady yana ta sa musu albarka. Sai da suka ga tafiyar su daga gidan sannan suka koma.

A hanya ko da Ahmad yaso bata hakuri katse shi tayi ta ce,

“Yaa Ahmad kada ka sabar da bani hakuri dan Mami tai min abu. Mami uwa ta ce, dan haka komai tai min bazan ji haushin ta ba. Ina addu’a dai Allah ya dai dai ta mu nima naji son da uwar miji kewa sirikar ta.”

Sai kuma ga kuka nan. Tabbas abin Mami gaba yake karawa dan jin zuciyar ta take kamar ta fashe.

Motar ya paka a gefen titi ya ja ta jikin sa yana lallashin ta.

Har sai da ta daina kuka sanna ya samu damar mata magana.

“Hakika Amina ke mace ta gari ce yar aljanna. Halin na da kyau bansan me kikai wa Mami ba amman na tabbata wata rana Mami zata so ki zakuma tai alfahari da kasancewar ki sirika gare ta. Kiyi hakuri nasan kina dashi amman nima abinda Mami ke miki ban jin dadi dan ba yadda zanyi ne. Amman na tabbata nafi ki jin zafin shi. Ina son ki Amina ki sani bazan taba rabuwa dake ba sai dai in mutuwa ce zata raba mu. Ina kaunar ki son ki a jini na yake.”

Kamkame shi tayi, wani kukan na kara cin ta.

Fashewa tayi dashi, a hankali ya dinga jijinga ta yana kwantar mata da hankali har tayi shiru.

Sai da ya tabbata tai shiru sannan ya tada motar suka tafi.

Suna zuwa gida tai shiga ban daki wanka tayi ta fito ta saka kayan baccin ta.

Kitchen ta shiga ta hadowa Yaa Ahmad Snack da lemo.

Yana falo dan haka can ta kai masa. shima yayi wanka ya saka kayan baccin sa. Sai tashin kamshi yake.

Yana ganin ta ya saki murmushi ya mike ya amshi plate din hannun ta.

Zama yayi suka fara ci, cikin so da kaunar juna.

Suna gamawa ta mike tayi kitchen tana dawowa, ta kalle shi ta ce,

“Yaa Ahmad sai da safe!”

Kallon ta yayi cikin wani yanayi, a ka’ida fa su tashi suje su kwanta tare ne amman tazo masa sallama.

Yana jin tausayin Amina dan yasan yana danne mata hakkin ta.

Murmushi karfin hali ya yi ya ce,

“Allah tashe mu tafiya ko nazo na saki baccin ne?”

Kai ta girgiza ta ce,

“A’ah nagode!”

Ta juya ta tafi. Kallo ya bita dashi. Tafiyar ta ma kadai tada masa da hankali take.

Yana son Amina. Amina akwai hakuri tabbas ko haka ta cigaba da kasance wa a tsakanin su yasan to lallai zai zamo mai cutar ta da shiga hakkin ta.

Ya jima a zaune agun yana saka da warwara kafin ya mike ya nufi dakin sa.

*Bayan wata biyu*

Anyi sa ranar Na’ima inda yanzu ma sauran sati daya biki.

Amina baiwar Allah ita ke ta lissafe lissafen abubuwan da Yaa Ahmad zai mata.

Daga ta ce wancan sai ta ce wacan ko ta tata ma batayi sai ta Na’ima.

Da ya tambaye ta ita me take so zata ce ya fara gamawa da Na’ima.

Wani abun ma ba shi zai yi ba amman sai Amina ta ce shi ne zai yi.

Yana mamakin Amina halin ta daban ne.

Haka ta hada kudin ta dubu dari ta bawa Dady dubu hamsin ta ce gudumawar ta.
Haka ma ta bawa Mami, Mami ma dai ta karba, dan ta ce, ai a kudin ‘dan ta take samu.
Dady kuwa sai albarka yake sawa Amina.
Yaji dadin abinda Amina tai masa duk da yana da shi.
Haka tasa aka bugawa Na’ima Memo da calender, a jikin calender aka rubuta ayyatul kusriyyu da falaki da Nas da Ahad.
Dady ba karamin jin dadin abinda Amina tayi yayi ba.
Dan ko da mutum yana da hali ai ko yaya aka baka zzaka ji dadi.
Sunyi event kala biyu yini da kamu sai dinner da mijin ta ya hada.
Duk kan su Amina ta halar ta tare da Anty da Basma har da Yasmeen da ta gayata Amma ranar yini kawai taje.
Amina tayi rawar gani dan ko shigar da tayi sai an kalle ta an kara.
Tayi kyau dan kwalliya ma gidan kwalliya Ahmad ya kaita da kansa akai mata.
Haka kayan jikin ta ma da tsada ya siye su.
Ta yiwa amarya liki sosai dan ta kan karo musu girma bama a wajen dinner.
Anyi taro an gama lafiya inda aka kai amarya gidan mijin ta.
Su Amina kuma aka koma gida da gajiya duk wanda yaje bikin nan yasan da zaman Amina.
Dan kowa yasan tai rawar gani. Duk wanda ya ganta ssai ya ce mene aibun ta da Mami bata son ta.
Amina akwai farin jini dan dayawa dangin Mami sai nan nan suke da ita dan su basu ga wani ai bun ta ba.
*Bayan wata uku*
Anyi auren Na’ima da Naufal inda suke zaman lafiya sai dai a gidan uwar mijin suke tare da Kanwar sa Halima.
Halima yarinya ce amman tana da girman jiki sannan akwai rashin kunya.
Haka nan Ummah mahaifiyar Naufal ita ma bata da halin kirki.
Naufal mahaifin sa ya rasu ya bar masa dukiya me yawa ga aiki yana yi yana da dai kudi masu yawa.
Dan yafi karfin komai sai abinda yake so yake samu.
Tsarin gidan babban gida ne wanda yake da baban falo sai kuma kowa ta falon kofar bangaren sa yake.
Baban falon ya zama kamar wajen zaman su ne.
Dakunan Na’ima biyu falo sai bedroom uku. Kuma Dady duk abinda yaiwa Amina haka yai wa Na’ima dan wani abun ma na Amina yafi tsada.
Yau watan Na’ima daya a gidan tana zaune ttana kwalliya Halima ta zo ta tsaya akan ta. Ta ce,
“Me yasa kika taba min ruwa na?”
Na’ima ta ce,
“Ke Halima mene dan kin dauko ruwa nai amfani da shi.”
Wani kallo Halima tai mata. Ta ce,
“Haka kika ce? Haba shi yasa naga tinda kika zo gidan nan kike ta daukar kai kina nuna ke yar wani ce ko? To wallahi halin nan ba zai kai ki ba. Ki canja dan ke ba yar kowa bace ah toh!”
STORY CONTINUES BELOW
Dan kwalli Na’ima tayo gaba da shi ta ce,
“Uhmm kinga banda lokacin ku daga ke har babar taki.”
Dai dai fitowar Ummah daga daki kenan. Baki ta kire ta ce,
“Ai daman duk dan matsiyaci haka yake. An dauko ki a rana yanzu kinzo zaki nuna mana rashin mutumci ko? Duk dan matsiya ci bai gaji arziki ba. Dan kinga dana yana da kudi kika aure shi to wallahi bazan dauki rashin kunyar ki ba. Ki kiyaye ni dan ni ba kanwar lasa bace ah toh.”
Tsaki Na’ima tayi ta ce,
“Uhmm nifa bani da lokacin ku.”
Tayi gaba zata bar wajen. Ummah ta kalli Halima ta ce,
“Me kike jira da ita kamar ba jini na ba.”
Halima ta kamo ta, ta fara dukan ta haka ma Ummah ta sa hannu tana jibgar ta. Sai da suka zane ta tatas sannan suka bar ta a wajen tana ta zuba ihu.
Haka ta gama ihu ta tashi da kyar ta koma daki.
Dan a lokacin Naufal baya gari yayi tafiya. Ita kadai tayi jinyar ta.
Tin daga lokacin bata kara fitowa babban falo ba.
Bayan kwana biyu ana ya gobe Naufal zai dawo da yamma ta fita dan taje tayo siyayyar kayan da zatai amafani dashi.
Bayan taje ta dawo. Tazo tai knocking gate. Har Halima ta fito zata bude mata sai Ummah ta fito ta ce.
“Ke ina zaki?”
Halima ta ce,
“Ummah Na’ima ce ta dawo take knocking.”
Ummah ta ce,
“Rabu da ita kar ki bude.”
Halima ta kalle ta ta ce,
“Ummah saboda me to?”
Janyo ta Ummah tayi tai mata rada a kunne.
Kai ta gyada suka koma ciki suna dariya.
Na’ima kuwa sai knocking take tana cewa,
“Halima nice kizo ki bude min.”
Amman shiru har ta gaji ta zauna a bakin gate din.
Ta jima ta kara tashi ta bubuga amman shiru ba a bude ba.
Sai da ta kai karfe taran dare basu bude ba sannan ta tafi gidan kawar ta.
Washe gari kuwa tin karfe tara ta taho gida dan bata son Naufal ya dawo bata nan.
Amman abin mamaki tana shiga falo ta ganshi zaune a kan kujera.
Abinda bata sani ba shine saukar asuba yayi yana dawowa kuma Ummah da Halima suka hada karya da gaskiya suka fada masa.
Abin ya bata masa rai da kamar bazai yadda ba sai da yaga da gaske dai bata gidan sannan ya yadda da batun su.
Fuskar sa a daure ba alamar wasa. Tsoro ne ya kamata.
Yana ganin ta ya mike tsaye wani kallo ya bita dashi kafin ya ce,
“Daga ina kike?”
Ya tambaye ta cikin tsawa. Shiru tayi. Ya ce,
“Ba ta”
mbayar ki nake ba a ina kika je kika kwana?”
Ummah da Halima suka fito suna kallon su. Na’ima ta ce,
“Jiya naje kasuwa kafin na dawo naga an rufe kofa shiyasa.”
“Rufen baki. Yaushe aka rufe miki kofar?”
“Wallahi na dawo nai ta buga kofar ba a buden ba.”
Halima tai saurin cewa,
“Wallahi Yaya karya take ba inda wani a cikin mu yaje jiya da ta buga kofar da zamuji wallahi.”
Ummah ma ta ce,
“Kar ka yadda da yarinyar nan yar tasha ce kawai wallahi. Karya take fada maka wayo kawai take inda baka nan bata zama a gidan nan da mun mata magana kuma sai rashin kunya kai jima bata kyale ni ba …”
Na’ima da ido ya raina fata tayi kamar zatai kuka ta ce,
“Wallahi ka yadda da abinda zan fada maka wallahi ba karya zan maka ba nazo nai ta bugawa basu bude min ba.”
Naufal da ya rasa abinyi ya ce,
“Me ya faru to? Ina jin ki,”
Na’ima tana share hawaye ta ce,
“Shine naje gidan kawata na kwana.”
Ummah ta zaro ido ta ce,
“Gidan ‘kawa, ‘kawa ko saurayi, tsohowar makira, wace kawar taki kika kwana a gidan ta.”
Naufal ya ce,
“Gidan ‘kawa, to ni mene amfani na? Mene amfanin wayar ki kullum sai na sa miki kati mene amfanin ta? Mene bazaki iya kira ki fada min an rufe miki kofa ba. Koma bari na tambaye ki zaman wa kike a gidan nan. Ba zama na kike ba.”
“Wallahi abinda yasa ban fada maka ba dan kar kaga kamar na fiya ‘korafi ne, naga in nai maka zancen su sai ka nuna baka so ranka yana baci shiyasa.”
Ummah ta ce,
“To daman wacce kara zaki kai tinda maganar ki duk karya ce, kana fita daga gidan nan ita ma ta fita.”
Naufal ya ce,
“To naji. Na tabbatar dukkan su nan bawanda zai miki karya. In bakiyi abu ba ba wanda zai zo ya fada ya ce kinyi.”
Ummah da Halima kuwa sai murmushi suke, Naufal ya ce,
“Saboda haka ba kina jina kije gidan ku sai na neme ki.”
Ummah ta mike ta ce,
“Ai wannan baka dauki wani tsatsauran mataki ba. Ka sake ta kawai shine me kenan kayi?”
Naufal ya dan sosa kai ya ce,
“Ummah ai abin bai kai ga haka ba.”
Ummah ta ce,
“Au bai kai ga haka ba? Ka sake ta na ce da kai kawai. In kuma baza ka sake ta bane ni na sakar maka ita.”
Shiru yayi yana kallon ta. Na’ima kuwa da hawaye ya gama wanke mata fuska sai girgiza masa kai take alamar ‘yayi hakuri kar ya sake ta.’
Ummah ta ce,
“Baka ji nane?”+
Naufal kamar zai yi kuka ya ce,
“Kije gida na sauwake miki saki daya!”
Kuka Naima ta fashe dashi. Halima kuwa tai saurin mikewa ta yi wajen ta tana cewa,
“Tashi tashi ki tafi gidan ku.”
Tana tura ta tana kuka haka ta fita. Naufal ma daki ya shige yana kukan dan Allah ma ya sani yana son matar sa tana faran ta masa.
Ummah kuwa murna take haka ma Halima. Na’ima ta tafi gida tana kuka kamar ranta zai fita.
Napep ta tara a kofar gida da bata jin zata iyab tuku ma. Mai napep ya kai ta har can gida tana bashi kudi ta sauka tana kuka ta shiga gida tana kala ihu kamar wacce akace yau mahaifiyar ta ta mutu.
Mami ta fito da saurin ta kama ta ta ce,
“Lafiya? Ke me ya faru? Me ya faru? Lafiya?”
Mami ta jero mata tambayoyin nan gaba daya.
Kuka Na’ima ta cigaba da rusawa, Dady ne yai magana ya ce,
“Wai lafiya?”
Dady ya fito da sauri dan ganin me yake faruwa.
Cikin sheshekar kuka ta ce,
“Saki na yayi.”
Mami ta ce,
“Sakin ki yayi?”
Na’ima ta ce,
“Wallahi kanwar sa da Maman sa basa so na. Baki ga abinda suke min ba. Suka saka shi ya sake ni.”
Mami ta ce,
“Ashe wannan yaran bai da mutunci. ‘Yar tawa ta cikina zai wa wannan ya kuwa sanni kuwa.”
‘Yar dariya tayi ta ce,
“Lallai Naufal.”
Kallon Na’ima tayi. Mami ta ce,
“Daina kukan mana daina kukan. Dan Allah ki daina kina daga min hankali.”
Kukan Na’ima ta rage, amman duk da haka batai shiru ba.
Cikin kuka Na’ima ta ce,
“Ni wallahi Ummah shi nake so bazan iya rayuwa bashi ba.”
Mami ta ce,
“Ya isa. Menene haka maza nawa ne gasu nan waje barkatai.”
Kuka Na’ima ta kuma fashewa dashi ta ce,
“Ni wallahi Mami shi kadai nake so bazan taba aure ba in bashi ba.”
Dady dake gefe yayi dariya ya ce,
“A binda taiwa wani shi ya biyo ta yanzu. Tayiwa matar wanta ba wani abu bane wannan illa sakamako, daman an ce *duk abinda ka gina shi zaka girba.* sannan ance *in zaka gina ramin mugunta ta kina shi dai dai kai”*
Mami ta ce,
“Haba Alhaji me ya kawo maganar Amina kuma a cikin nan.”
Dady ya ce,
“Allah ba azalumi bane, duk abinda kayi sai ya bika. Kin san ance, *’Kai ‘kayi koma kan mashekiya* kun so mata hakan ta faru da ita sai gashi ya faru akan ku. Ke kuma sai ki shiga ki ta zaman gidan aure wata uku amman kina gida Allah ya shirya. Abin da ciwo na rasa ina tunanin ku ya shiga kwakwalwar ku ta dashe akan aikata laifi. Kuma ki sani makarantar da kika saka ta ta haddace komai tayi degree yanzu ga result nan. Kuma ke na fada miki.”
Ya fada yana nuna Na’ima ya ce,
“In da zaman gida ne gashi nan kiyi tayin sa.”
Ya shige ciki ya barsu anan. Na’ima kuma ta kara sa kuka tana cewa
“Mami dan Allah ki bashi hakuri dan Allah Mami.”
STORY CONTINUES BELOW
Mami da abin duniya ya isheta ta ce,
“Ke rabu dani.”
Cikin gida Na’ima tayi tana kuka kamar ranta zai fita.
Bayan ta Mami tabi tana lallashin ta.
***********
Mami na gani zaune gaban bokan ta ya bata bazan wuri din da yake ita ma tana yi.
Ga duk alamu dai Mami ta kauce hanyar Allah.
Dan wata kwarya nagani akan ta tana ambatar. su abubuwa
Sai da tayi da yawa sannan bokan ya umarce ta da ta sauke. Sannan ya ce,
“Hajiya kin burge ni. na zata baza ki iya bane?”
Dariya Mami tayi ta ce,
“Abinda ba a nema shine baza a iya ba. Wallahi ba abinda bazan iya ba in har dan in raba Ahamd da Amina ne.”
Dariya ya dauka wacce duk wajen ya amsa, ya ce,
“Kar ki damu zamu san yadda za ayi aikin nan ba zai taba yiyuwa ba sai in har Amina bata da tsarki. Dan haka zan tura aljannu ifiritu akan yaje yai ta gadin ta har lokacin da zai ga bata da tsarki sannan ya shige ta. Insha Allahu abinda kike nema zai faru. Dole Ahmad ya rabu da ita in tana masa hauka.”
Dariya Mami ta yi ta ce,
“Godiya nake.”
Wani kirari tai masa wanda daga ji haukan su ne ma. Sannan ta mike ta tafi.
*Allah ka shirya mu daga bin rudun zuciya da shaidan la’ananen Allah Ameen*
Amina baiwar Allah dake kwance dan tin jiya take fama da ciwon mara bata fadawa Ahmad ba.
Duk da Ahmad yai mata maganar cewa lokacin ta yayi sai cewa tai masa ai bai zo ba tukkuna.
Ta yanzu haka tana kwance marar ta ta rike mata dan bata jima da canja pad ba ta dawo ta kwanta.
Bacci ne ya dauke ta kamar daga sama na hangi wani irin abu yazo ya shiga jikin ta.
Mikewa tayi da sauri tana rike da marar ta. A hankali kuma ta zame ta kwanta.
Ahmad ne ya shigo yaga a halin da take ciki. Da sauri ya kira Dr.
Dr na zuwa yai mata allura sannan suka fito tare da Ahmad.
Kallon Ahmad yayi ya ce,
“Abokina kar dai kace har yanzu ba abinda yya shiga tsakanin ku da Amina.”
Kallon sa Ahmad yayi ya ce,
“Me ka gani.”
Murmushi Dr yayi ya ce,
“Kar ka manta farkon lokacin da Amina ta fara period na fada maka abubuwan da ke kawo su. Wanda nata nagano da sai tayi aure tukkunna in har mijin ta ya sadu da ita zata dai na. Abinda yasa nace haka shine na jima ina bata maganin infection dan da farko ina tunanin shine sai daga baya na gane irin matan nan ne da har sai sun sadu da mazajen su abin ke rage wa. Kaga kenan kai har yanzu baka je gare ta ba.”
Kai Ahmad ya dafe ya ce,
“To yanzu ba wani abin yi.”
Numfashi Dr ya sauke ya ce,
“Abin yi daya ne shine, ka kusance ta ko dan taimaka mata da wannan ciwon da take fama da shi. ciwo ne mai matukar azaba dan ita kadai tasan me take ji. Sai iya saukar mata da ciwon kafa ko hannu da baya, kai har amai da zazzabi da ciwon kai kaga kuwa abin ba wasa bane.”
Kai Ahmad ya jinjjina ya ce,
“To Dr nagode insha Allahu baza ta kara wannan ciwon ba.”
A ranar Ahmad da kansa ya gyara gidan tare da Ibrahim sukai girki. Da yake ibrahim ya kwana biyu da dawowa gidan.
Cikin kwana hudu ta warke lokacin kuma ta gama.
Tinda ta warke Ahmad yake fuskantar canji dan gane da ita dan wani lokacin sai yaga ta zauna ita kadai tai ta kuka.
Wani lokacin duk maganar da zai mata baza ta kula shi ba.
Haka dai ya fuskanci canji dan da farko yai ta mamaki dan har akai kwana biyu ma sai yaga da gaisuwa ba abinda ke sake hada su.
Haka ma Ibrahim shima daga gaisuwa gida ya zama duk wani irin.
In kuma sun tambaye ta ba lafiya ko wani ya taba ta sai ta ce a’ah.
Yau kamar kullum Ahmad na bangaren sa. Ibrahim na falo yana kallo ta fito sanye da hijab har kasa zata shiga kitchen kenan sai ta zube a gun.
Da sauri Ibrahim yayo kanta yana kiran ta. Amman shuru can kuma sai ta hau fasa ihu tana juyu a gun.
Da gudu yai bangaren Ahmad yana kiran sa. A tare suka karaso gun da gudun su.
Ihun ta cigaba dayi tana ta buga jikin ta A kasa. Ahmad da ya rike ta sai ta kwace jikin ta.
Haka tai tayi wajen sama da awa daya. Ahmad da duk ya rikice ya rasa me zai mata.
Sai daga karshe ya tofa mata ayyatul kursiyyu sannan ta lafa bacci ya dauke ta.
Daukar ta yayi ta kaita daki. Ya jima a dakin ya zuba mata ido kamar yai mata kuka haka yake ji.
‘To me yake damun ta mene hakan kenan’
Shi kadai dai ya dinga zancen zuci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *