ITA CE QADDARATA CHAPTER 3
Noor na biye da ita har suka kawo dakin Ihsan “”Ihsan ta juyo ta kalleta tace ina so ki gyara dakin nan tas,ki wanke toilet ,akwai inners(bra,pant,vest,underskirt) dina nan a basket ki wanke su tas “”Noor tace Toh, Ta fice tare da buga k’ofar d’akin “”Noor ko a jikinta,dan ta riga ta saba da wahala tun gidansu,ta hau gyaran d’aki,ta gama ta wanke toilet,ta d’auki kayan ta fito “”Laundary taje,tana wankewa tana karatun Qur’ani,Wasu pants din ma duk tayi staining dinsu,dan haka Noor ta ajiyesu gefe dan bazata iya wankewa ba coz tana da bala’in kyankyami+ Imran bayan ya fito sashen Alhaji, Sashensu ya nufa Yayi wanka ,yana ta sauri zai fita,coz akwai wanda Daddynshi ya turashi wurin shi akan maganar aikinshi Rigar da zai sa yake ta nema bai gani ba, Yace nasan tana laundary bari naje na duba “”Noor nata wanki abunta “”Taji kamar mutum ne tsaye a kanta,d’agowar da zata yi suka had’a ido,tai saurin sunkuyar da kanta k’asa,saboda kwarjinin da ya mata Shi kuwa gabanshi ne ya fadi “”Ya dake yace Kee! Waya gaya miki anan ake wanke wa’innan abubuwan anan “”Kunya ta kama ta, ta kasa furta ko A,(ga pants din da suka yi staining ta cire su gefe ,kuma tasan definitely ya gani) “”Tsaki yaja yace in zaki wanke wa’innan abubuwan naki ,ki rik’a wanke su toilet ba nan ba “”Kai kawai ta iya d’agawa sama “”Ya duba rigarshi,ya d’auko ya fita(kwata-kwata bai d’auka itace matar Daddynsu ba,ya d’auka yar’aiki ce,dan dama ba duka yan’aikin ya sani ba) “”Noor kuwa wata irin kunya ta cigaba daji ,tace yanxu fah shikenan ya gani,kuma zai d’auka nawa ne,anyway da gani ba ruwanshi,ba kamar sauran yan’uwanshi ba, Ta gama wankewa,ta kwashi masu staining d’in A d’akinta(ihsan) ta sameta “”Murya a sanyaye tace ga wa’innan sun b’aci “”Ihsan dake kwance,ta tashi zaune cikin zafin nama tace me kike nufi ? Ai nasan yadda suke na baki su “”Noor tace Staining ne fah,kuma ba kyau,ka wanke ma mutum “”Ihsan ta daka mata tsawa tace kafin in k’irga uku ki fitar mun a d’aki,kije ki wankesu “”Noor ji tayi har ga Allah ba zata iya wanke wannan kayan k’azantar ba,Dan haka tace Dan Allah kiyi hak’uri bazan iya ba “”Ihsan tace me kika ce? Ba zaki iya ba “”Noor ta d’aga kanta sama “”Dirkowa tayi daga kan gado,Sai gata gaban Noor,Tasss Tasss kake ji saukar mari,mari biyu ta mata lafiyayyu,ta hankad’ata ta fad’i,Noor sai hawaye abun tausayi “”Ihsan tace kad’an na miki,Gobe na k’ara saki aiki kice ba zaki yi ba, Maza tashi ki fitar mun a d’aki kuma ki tabbatar kin wankesu,in ba haka hmmmm…….,ba sai na gaya miki me zan miki ba “”Noor ta kwashe kayan ta fita tana kuka,tsakar gida taje ta zauna,tana ta kukan bak’in ciki,duk wani mai imani ya ganta dole ta bashi tausayi “”Lami ce tazo ta dafa ta,tace lafiya ,me suka miki “”Cikin dasasshiyar muryata ta labarta ma Lami duk abunda ya faru “”Lami tace Allah sarki,yi shiru daina kuka,kema me ya kai ki cewa ba zaki yi,da kin sani kin wanke “”Noor tace Allah Lami ina da k’yank’yami bazan iya wankewa ba “”Lami tace muje laundary ki wanke a washing machine “”Noor tace ai Yayansu ya hana “”Wanne daga ciki Imran ko Yazeed “”Wani dai kyakkyawa haka da baya dariya “”Lami tace Imran kenan,wannan miskilin ko magana ma shi wahala take mai,muje ki wanke ,ai ba yanan ya fita “”Lami ta rik’e hannun Noor suka je “”Noor ta godewa Allah da ya had’ata da Lami,dan yau ba don Lami ba,bata san me zai faru akanta ba,dan bazata iya wankewa ba ko kasheta za’a yi “”Tana gamawa,taje wajen Iman,itama ta bata nata aikin “”Tun safe Noor ke aiki da ta gama wannan ,za’a ce yi wannan,tana yi ana zaginta,ana hantara Sai dare wajen k’arfe sha d’aya suka sallameta,ta masifar gaji Kayanta ta tattaro daga part d’in da Alhaji ya kai ta,ta maidasu d’akin da Lami take,dama ita kad’ai ce a d’akin,Sauran masu aikin biyu d’akinsu d’aya, kansu had’e yake “”Tayi wanka taji k’arfin jikinta,sannan Lami ta zubo mata abinchi taci,suka kwanta barci “”Alhaji nata tunanin ko wane hali Noor take ciki,yana so yaje ya dubata amma yana tsoron Hajiya “”Hajiya kuwa nata shige shigen(boka da mallam)yadda zata sa Alhaji ya tsani Noor,ya manta da ita “”Kiran sallar farko na Asuba,Noor taji saukar ruwan k’ank’ara a jikinta “”Firgigit ta tashi tana mutsittsika ido, “”Hajiya ta gani tsaye a kanta “”Hajiya tace Tashi Yar’iska an gaya miki hutu kike zo,da zaki kwanta kina ma mutane barci,Maza tashi kije ki wanke mototocin dake gidan nan,ki share tsakar gida “”Noor ta amsa da toh jiki na rawar sanyi Hajiya ta juya ta fice, tana masifa Lami itama ta tashi, hayaniyar hajiya ta tada ta,Noor tama kasa yin kuka,tashi tayi ta cire kayan jikinta,tasa wasu “”Har zata fita taji muryar Lami nace mata kiyi hakuri Noor,komai yai farko yana da k’arshe,watarana sai labari “”Noor tayi murmushin takaici tace ba komai Lami wannan *itace k’addarata* “”Lami tace hakane itace k’addaraki “”Bari na tafi kar tace na d’ade “”Lami tace toh,tana mai jin tausayin Noor……….. …………………… Tsintsiya ta d’auka ta fara share tsakar gida, Mai sharar tsakar gida,da wanke mota duk Hajiya ta sallamesu, tace Noor ce zata rik’a yi Tana yi tana hutawa,kasancewar gidan k’ato ne,ba ita ta gama ba Sai k’arfe 8am Ta nufi parking space inda Cars din gidan suke,mototoci 20 ne a gidan “”A ranta tace ni kadai zan wanke duka motocin nan,gashi ta masifar gajiya Ruwa ta debo,ta Zuba car wash,ta d’auko soson k’arfe,duk aikin da ake sata gidansu ba’a taba sata wankin mota ba,dan haka ta d’auka da soson k’arfe ake wankewa, Wata hadaddiyar mota k’irar Bugatti ,ta fara wankewa,Tana gurza soson,Paint din ya goge,wurin ya k’oje(gashi sosai ta gurza,wurin ya k’oje da yawa),Tana ganin haka hankalinta ya tashi “”Innalillahi wa inna ilai hir raji’un ta furta,tace Yau na shiga uku,k’ila yau hajiya sai ta yanka ni “”Nan ta kifa kai tana kuka,tama rasa me zata yi,ko taje ta gayawa Hajiya b’arnar da tayi,ta gaya mata a bisa rashin sani ne,sai kuma taji tsoro kar ta gaya mata ta kasheta,ita yanzu ya zata yi,addu’o’i kawai take karantowa+ Can taga kukan bazai fissheta ba,dan haka ta tashi,ta cigaba da wanke motocin ba da soson k’arfe ba,Zuciyarta cike da tsoron kar a gano b’arnar da tayi Tana yi tana hutawa,har ta gama “”Ko Lami bata gayawa b’arnar da tayi ba,Addu’a kawai take Allah yasa kar a gane “”Tare da Lami suka yi breakfast(kunu da k’osai) “”Hajiya tace Noor taje sashenta,ta gyara ko’ina lungu da sak’o a sashen daga kan dakuna,toilets,falo “”Noor na jin haka sai hawaye(saboda ta masifar gaji,bayanta har ciwo yake,ta ya zata iya gyaran Sashen,ita dai ta rasa gata,ba mai sonta,ba mai tausayinta) “”Kukan da take ko a kwallar rigar Hajiya,kwata kwata bata ji tausayinta “”Babban falon take gyarawa,da kyar take shara,Duk wanda ya kalleta yasan a gajiye take,Haka take ji kamar zata fad’i,A zaune ta koma yin sharar “”Hajiya ta daka mata tsawa tace Maza tashi,wane aiki kika da har zaki gaji,kin manta ke Baiwa ce a gidan nan,baki ba komai ba tukunna “”Noor ta mik’e jiki ba k’wari,Tana shara da k’yar “”Yazeed ya shirya zai fita,yana da lectures “”Duk zai fita sai ya dudduba Motarshi,yaga bata da wata matsala,ko kadan baya so yaga datti jikin motarshi ko wani k’warzane shiyasa kullum cikin painting car dinshi yake,ko kad’an yaga datti jikin motarshi,to Mai wankin motar ya boni “”Dubawar da zai yi,yaga k’aton k’warzane jikin motar, A fusace yace What d hell is diz ?? Ya cije lab’e,ya buga motar da k’arfi yace Damn it!,tare da harbin tayar motar, “”Iro You must pay for doing this ya fad’a A fusace yake kiran Iro! Iro ! Iro! “”Mai gadi ne ya rugu da gudu,ya durk’usa gabanshi yace Ranka ya dad’e,Iro baya nan “”A fusace yace Gidan uwar wa yaje ?? “”Mai gadi yace Ai hajiya ta sallame shi “”Toh Uban wa ya wanke motocin gidan nan yau “”Wata yarinya ce “”Yana huci yace ko yar gidan uban waye,Yau sai ta gane kurenta infact yau sai ta bar gidan nan “”Yana huci ya nufi sashen Hajiya “”Da k’arfi ya tura k’ofar falon, Yana huci ,ya had’e girar sama da ta k’asa ya shiga “”Hajiya kanta ta tsorata da ganinshi,tasan duk abunda aka mishi ba k’arami bane,kafin ta tambayeshi me ke faruwa “”Yace Wa ya wanke cars din gidan nan Yau ?? “”Noor hanjin cikinta ne ya kad’a,tsintsiyar dake hannunta ta fad’i,kunnenta taji ya d’au ruwa tsabar tsoro “”Hajiya tace wani abu ne ?? “”Yace mum,imagine motata fah aka k’urje,kuma wallahi daga gani da gangan aka yi “”Hajiya Salati ta rafsa tace Noor ashe ke muguwar yarinya ce ban sani ba,yar hassada,wato tunda na saki wankin mota bari ki k’warzane motar “”Noor murya na rawa tace wlh…..ba…da Yazeed ya katse ta tare da daka mata tsawa da k’arfi yace Enough!! ,dama kina cikin case d’ina,kafin in hukunta ki akan wance,kin k’ara wani, ki rasa motar da zaki ma haka sai tawa,Duk yawan motocin gidan nan “”Iman tace da gangan tayi ,dama daga ganinta sai tayi k’eta “”Yazeed yace yau kuwa zan koya mata hankali Belt ya zare “”Ya fara zabga mata ,yana k’wallo da ita “”Su hajiya na zuga shi,suna cewa yawwa k’ara ma shegiya “”Shikuwa ya zage sai dukanta yake,Tana kuka tana bashi hak’uri amma kamar rok’onshi take ya k’ara Imran ne ya shigo,idonshi straight suka kai inda Yazeed ke dukan Noor(bai ma lura wacece ake duka ba), Yai saurin k’arasawa wajen,ya rik’o shi yana cewa lafiyar ka,sai kashe yar’mutane “”Yazeed yace k’yaleni kawai Bro,in kasheta in kashe banza “”Imran yaja shi ya zaunar dashi,Yana ta huci Yace Haba Yazeed! Ka rage zuciyar nan taka “”Barni kawai da shegiya,motata fah ta k’uje mun “”Imran yai dariya yace to me ye a ciki,ni na d’auka ma wani babban laifin ta ma, “”But kasan bana son,ko kadan mota ta ta b’aci “”Toh ba sai an chanja paint din ba,me ye na b’ata ranka a banza “”Yai shiru yana haki Noor bakinta da hanci ya fashe sai jini yake ,tana kuka “”Imran ya kai dubanshi gareta,ta bashi tausayi,Yace ke kuma tashi kije ki wanke bakin ki Me ma ya kai ki wajen motarshi “”Hajiya tace daga na sata wankin mota,shine tayi wannan muguntar “”Imran yace Mum ban da abunki, ina mace ina wankin mota “”Hajiya tace to akanta za’a fara kuwa,ba ita ta auri mai kud’i tazo ta huta,zata ga hutu “”Imran cike da mamaki yake kallon Hajiya a ranshi yace dama ita ce matar Daddy,yarinya kyakkyawa da ita,ta auri tsoho dan kud’i,dama ya sani bai rik’e Yazeed ba,ya barshi ya cigaba da dukanta,Hakan shine dai dai da ita,Da ace duk yan’matan nan masu auren tsofaffi dan kud’i ,zasu rika samun haka gidan mazajen su,da an rage auren kud’i,mata yanxu sun lalace da sun kud’i,sai su jefa kansu wani hali saboda kud’i Yaja tsaki,ba tare da ya sake kallon saitin ta ba, a fusace yace Oya Get out,dan baya son ma sake sata a ido _A rayuwarshi ya tsani mace na banzarta da rayuwarta a banza a wofi,Yana so yaga mace tana daraja kanta,kuma shima yana matuk’ar daraja mace_ Noor jiki a sanyaye da k’yar ta mik’e dan duk ta galabaita, tana mamakin why the sudden change daga Imran,taga shi ba ruwanshi da ita amma lokaci daya ya hayayyak’o mata “”D’akinsu ta shiga,a tsorace Lami tace Lafiya Noor,me suka miki “”Noor tai saurin mayar da hawayen dake k’ok’arin xubo mata tace manta ba komai “”Haba! Noor ya zaki ce ba komai,bayan ga jini duk jikinki “”Noor tace bari ina zuwa lami “”Toilet ta shiga,ta wanke jinin dake zuba bakinta,da hancinta Ta fito,har yanzu jinin bai bar zuba ba “”Lami tace tashi muje chemist Noor,jinin nan yak’i tsayawa “”Noor tayi murmushi takaici tace ko munje chemist bani da kud’in da zan biya “”Tashi muje ni ina da kud’i Noor tace a’ah Lami,barshi kar na d’aura miki wahala “”Ba wata wahala wallahi,me ye amfanin zaman tare,tashi mu tafi “”Noor ta tashi,tana mai jin k’aunar Lami a ranta “”Chemist d’in kusa dasu suka je,aka mata dressing tare da bata maganguna,Suka dawo gida “”Tana ta ma Lami Godiya “”Lami tace ba komai,tun farkon da taga Noor taji tana k’aunarta+ “”Ranar Hajiya,Gaba d’ayansu suka fita,dan haka Noor ta samu sarari Ta kwanta,tana ta barci,tana huce gajiya Sai ana kiran Sallar magriba ta tashi,Tayi wanka da ruwa masu d’umi,Sosai taji dad’in jikinta,dan ta huce gajiya sosai Tana jin dama ace haka kullum take samun hutu,amma ina ba zata samu ba Alhaji kwata-kwata ya fidda Noor a ranshi,yaji baya ma son sake sata a ido(aikin asiri)sai sun had’u da mahaifinta wurin caca ma yake tunawa da ita, kuma ba wai mahaifin nata ,na tambayarshi bane ina take, a’ah,Mahaifinta shi harkokinshi ma yake,ji yake kamar an cire mai k’aya Noor kuwa rashin kula ta da Alhaji ba yayi,ba k’aramin dad’i ya mata ba,amma sai dai kuma ta rasa gane me ya kawo sudden change d’in,Sai kuma can zuciyarta ta bata hajiya ta hana shi,saboda a yadda ta lura mijin hajiya ne “”Tana aiki a kitchen,Iman ta lek’o Tace kee!! Kije Ya Yazeed na kira “”Murya a sanyaye tace toh Ta ajiye yanke alayyahun da take,tace Lami Dan Allah ki k’arasa mun ina zuwa “”Gabanta nata fad’uwa ta nufi sashensu Yazeed,wannan ce rana ta farko data fara zuwa,a ranta tana cewa ko me zai mun “”A hadadden falonsu ta same shi zaune shi da Imran,Suna kallon k’wallo(Ball) “”Ta duk’a nesa dasu,tace Sannunku gani “”Imran ya gane muryata dan haka bai juya ba,Dan baya son sake sata a ido,Dan a duk sanda ya kalleta sai gabanshi ya fad’i ,kuma yanzu ga haushin auren daddynsu da tayi saboda kud’i “”A fusace yace me kike yi anan? “”Yazeed yace ni na kirata aiki zata mun “”Tsaki kawai Imran yayi,ya tashi ya bar falon,ya koma d’aki,Ya kwanta kan gado yana cewa i want to get rid of this girl,bana son sake kallonta ko jin muryarta,haushi yake ji,ya tsani mace mai irin halinta(wato auren kud’i), “”Yazeed ya kai dubanshi gareta,Yace kar ki d’auka dukan da na miki jiya shi kad’ai ne punishment d’inki,yanzu kika fara,dan haka weeding(noma)zaki yi,na grasses dake bayan d’akunan mu Duk grasses d’in da suka fito,ina so ki cire su “”Noor gabanta ya fad’i tace na shiga uku ni Noor,weeding abunda ban tab’a yi ba, a gidanmu,me zai sa su rik’a sani aikin da ban saba dashi ba “”Yazeed ya daka mata tsawa yace kinji ko “”Ta d’aga kanta sama,yace fice mun da gani “”Ta tashi sumi-sumi ta fita Bayan rooms dinsu taje,anan taga hoe “”Ta d’auka ta fara cire grasses d’in wurin “”Da k’yar take cirewa “”Imran yaji kamar motsin mutum ta window’n d’akinshi “”Ya tashi ya lek’a,yaga sai weeding take duk tayi zufa “”Yayi murmushi ya dawo,ya zauna yace Shege Yazeed baka da dama wlhy,Anyway hakan shine daidai da ita,ko wata taji zata yi auren kud’i,zata bata shawara kar tayi “”Yama kawar da tunanin,ya jawo system d’inshi yana operating “”Tunda take,ba aikin da aka tab’a sata ya wahalar da ita,kamar na yau “”Sai nishi take tana sweating “”Ta ciccire grasses d’in,ta ajiye hoe, zata tafi taga Yazeed tsaye gabanta, A tsawace yace Ina zaki ? Murya na rawa tace na….ga….ma(dan masifar tsoron shi take tun dukan da ya mata) “”Yace nace idan kin gama ki tafi “”Ta girgiza kai alamar a’ah Ya wuce,yana dudduba,saura sauran grasses dake can k’asa,Ya nuna yace wannan fa ,wa kika bar wa ya cire “”Maza zo ki cire su kafin na k’irga uku “”Jiki na rawa ta d’auki hoe “”Ya daka mata tsawa yace ajiye shi,da hannu zaki cire “”Ba musu tasa hannu,tana tsige grasses d’in,Yazeed na tsaye kanta Sai da ta tsige shi tas,kai kace machine ne ya cire shi,ba mutum ba “”Yace oya tashi muje akwai sauran aiki “”Idonta suka yi narai-narai suka cika da hawaye tace Dan Allah kai mun rai,ka barni na huta,ko me kace inyi zanyi “”Kawai yaji ta bashi tausayi yadda yaga ta galabaita tana hawaye Yace na baki 15mints,ki huta,ki sameni sashenmu “”Nagode nagode “”Bai sake tankawa ba,Ya wuce Imran na jin su ta window,Yana dariya duk da cewa yana da tausayi sosai amma kwata kwata baya jin tausayinta,dan a ganinshi kome aka mata, ita taja ma kanta “”Da k’yar ta kai d’akinsu,ta fad’a katifa tana maida numfashi ga yunwar cikinta ma ta isheta “”Tsawon minti biyar tana kwance ta kasa yin ko k’wak’waran motsi,Bayanta taji ya rik’e yana ciwo “”Iman ta gani tsaye kanta,rik’e da k’ugu ,tana juya key’n mota da d’an yatsa,tace lallai samun wuri,har kina ma da lokacin hutu, baki gyara mun d’aki ba,shine kika zo nan kika kwanta “”Noor bata tashi daga kwanciyar da tayi ba,tace Dan Allah,ki d’aga mun k’afa yau Iman,wlhy bayana ke ciwo “”Iman tace wannan kuma ke ta shafa,ba matsalata bace,all i know shine ki tabbata kin gyara mun d’aki,kafin naje na dawo,ta kad’a kai ta fice “”Noor kuwa gyara kwanciya tayi,in less than 2min barci ya saceta ……………………………