SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 4

SILAR GIDAN AIKI




CHAPTER 4



Gaban Mubin ne yai mugun faduwa da yaga faeez ya fito daka dakin, Nan take fuskarshi ta chanza idonshi yai kanana dan Radadin da zuciyarshi takemai +

Haleema ne ta kalleshi tace” why d sudden change? Kona bata maka Raine? Kirkiro murmushin dole yayi yace” Nop at all is just that I need some rest ne kainane ke ciwo!

Ohh sorry tacemai kaje tom ka kwanta kasha magani

“OK yace Mata”

Kallonshi tayi cike da so da kauna tace mai I love you dear take good care of your self…yace” OK love

Daki ya wuce ya kwanta a gado yaji kwanciyar bazatai ma ya tashi ya dafa Kai tinani barkatai yake tayi, kardai ace faeez soyayya suke da Nazeefa, Kanshi yaji yana saramai ya tashi ya dakko Panadol extra yasha

Yadan sama relief but zuciyarshi Sam ta kasa natsuwa balle idan ya tina sanda faeez ya fito dakin Nazeefa yana smiling

Subhanallah yace Dan zuciyarshi Sam bata masa Dadi

Tinani ya tsunduma sosai Kawai sai naji ya furta haba Nazeefa ki soni Dan Allah duk irin abubuwan da nakeyi Kishinki nakeyi

Jan tsaki yayi yace” aikin banza ashema ba kowa a dakin

Wani tinani yayi yace” Bari ya Kira abokinshi Ibrahim ya sanar dashi halin da yake ciki

Har yai dialing numbernshi sai kuma ya katse aranshi yace if I call him mezancemai? Brother na dating da Yar aikin gidanmu no no yace

Nan Wata hikima ta fadomai tace Bari ya kira kanin nashi yaji ta bakinshi, Dan KO soyayya sukeyi Nazeefanshi

Fita yayi ya kirashi yace” yanzu zasu fita

Faeez bemai musuba yace” OK a shirye nake

Ya kalleshi yace to ka fita ganinan zuwa

Fita Chan gate yayi sannan Mubin ya fito ya sameshi, tafiya sukeyi a unguwa kamar abokai, Faeez yaga tafiyarsu bana kare bane yace” buh yaya sorry to ask you Ina zamu haka kasan akwai rana ko?

Mubin a kule ya kalleshi yace kaimun shuru nan ma rashin kunya zakaimun, nima ai inajin ranar, Faeez ya Kama bakinshi yayi shuru

Mubin KO kafe shi da ido yayi yace” Dama I wanted to ask you whats the relationship between you and Nazeefa

Faeez mamakine ya isheshi yace I don’t get you ya Mubin, mubin cikin bacin rai yace” dama ai you’ll never get ba soyayya kukeyiba ko? Jiya uban me yakaika dakinta?

Faeez ne ya zare ido yace” Wallahi ba abun dake tsakaninmu, is just that tausayi take bani

Wani ajiyar zuciya yayi ko banza zuciyarshi ta natsu kuma yasan Faeez bazaimai karya ba, yace nasani ai, kawai I’m giving you last warning ne Kar inkara gani kunama magan Dan I want to marry her, kabar ganin Kai kaninane, Nazeefa is mine alone, banso kowa ya rabeta!

Jin maganar Faeez yayi wani iri, aranshi yace Dan kanasonta seka dinga treating dinta wani iri hmm

Yana cikin tinanine mubin ya katseshi yace bakaji bane? Yace” ya mubin naji kuma inshaa Allah zan kiyaye, Mubin yace” OK sannan suka jiyo suka dawo gida kamar batare suka fita ba

*********
Bayan kwanaki Nazeefa taji sauk’i abunta, Haleema kuma hutunta ya kare ta koma Abuja gidan iyayanta, da zata koma an hada mata sha Tara ta arziki, Tayi kuka sosai dan Kaf duniyar nan tana bala’in son mubin itadai,

********
Haka rayuwar Nazeefa ya kasance yau farin ciki gobe bakin cikin, ta rasa yanda zatai a rayuwarta, gashi Yar number wayan data zo dashi na mahaifinta ya bace bata ganshiba,

Mubin kuwa son Nazeefa sai ruruwa yakeyi a zuciyarshi

……WASA FARIN GIRKI
*Bayan Shekaru 4*
Nazeefa ta zama cikakkiyar budurwa, a school kuwa jumping aketa Mata cos Tanada kokari sosai Ga speaking a bakinta kamar a kasar waje tai karatu yanzu haka tana ss3 zata zana waec dinta, kullun ta fita sai maza sun Biyota saboda yanayin halittar da Allah yai Mata, Mubin kuwa sunsha gwagwar Maya da maza Dan kashe Mata kasuwa yakeyi yace matarshine, School ma yanzu shi yake kaita ya dawo da ita amma ita a wajenta a banza yakeyi, +

Shape na jikinta kuwa ba inda be fitoba
Ita kanta idan ta tsay a gaban mirrow har mamakin kanta takeyi Wai itace tazama fine baby haka Lol

Mubin kuwa yagama karatunsa na Doctor Ya zama babban likita

Faeez da faeeza kuwa yanzu suna alqalam university a katsina

Komai na tafiyawa Nazeefa yanda takeso Dan bala’in gwarama Mubin Kai takeyi, Yanzu tinaninta daya tayaya zata koma hannun iyayanta, ita sam hankalinta ba kwance yakeba, Balle dataga Mubin yanzu ya zama wani iri tsoronshi takeji sosai Dan haba haba yakeyi da ita

******
Gidansu Haleema kuwa!
Mahaifiyar Haleema ne zaune tayi tagumi Tace” ita sam abunnan ya isheta wai ace Yaro yanason yarinya amma a shekara 4 befi sau daya yazoba se dai kullun suna cikin vedio call da chat din tsiya

Haleemace ta tirke mahaifiyarta da ido ita lalle sefa an aura Mata mubin ko aga ba daidai Ba

Mahaifiyar Haleema ne ta zaro waya cikin jakarta ta Kira numbern Hajiya Asmau

Ringing biyu ta dauka tai Mata sallama taji Hajiya Hadiza (Mahaifiyar Haleema)na amsa Mata wani iri

Tundaga maganar Hajiya Asmau taji alamun akwai magana a bakinta, tace” Hajiya lafiya kuwa?

H.Hadiza tace wani lafiya kuwa kinsan dai ke nake jira muyi magana, yara sungama karatu kowanne da aikinshi to me ake jira? Ko kinsa man Mai watace? Hajiya Asmau ta nunfasa tace” KO daya Hajiya idan ya dawo Zanyimai magana kuwa!

Hajiya Hadiza tace” to kafin dai na nemeki Ki nemeni Dan KEDA ALHAJI karku manta akwai SIRRI me karfi tsakaninmu, idan hakan bata yuwuba wallahi Saina TONA kowa yaji

Hajiya Asmau jikinka na rawa tace” OK angama!!

Wacece Hajiya Hadiza? Hajiya Hadiza mahaifiyar Haleema ce, Kuma at the same time Aminiyar Hajiya Asmau ne Komai na Sirri tare sukeyi saboda mazajensu abokai ne, Ita hajiya Hadiza mijinta ya rasu, y’arsu daya Haleema, tun kafin rasuwar mahaifinta sukai alkawarin Zasu aura ma yaran junansu Dan kobayan Ransu Wannan Sirrin dasuka boye bazai fitoba….Hmmmm

Hajiya Asmau se zagaye takeyi a cikin parlor, Hankalinta a tashe yake

Mubin ne ya dawo daga aiki, Ta Hangoshi ta window tace” Alhamdulillah gashinan yadawo

Tana zaune a parlor ya Shugo da Yar jakarshi a rataye ta gefen hannunsa

Sannu Hajiya yace”

Tace” Mubin kadawo? Yace yes my 1st love tace to zauna muyi magana, zama yayi ya kasa ita kuma tana kan kujera

Bude bakinta tayi tace” Kaga yanzu kanada abunyi dama maganar aurenkune da Haleema ya kamata Musan abunda muke ciki zuwa nan da January ayi agama

Mik’ewa tsaye yayi yace” What? Yace Mummy ni gaskiya I can’t marry her, Nazeefa nakeson aura!!

Itama mik’ewa tsayi tayi ta balla Mai mari, tace” Yar banzan yarinyar nan zaka aura? to Wallahi baka isaba Bari na Kira babanka na fadamai duk halin da ake ciki ya dawo

Ashe baka da kunya? Duk kudin mahaifinka ace Yar Aiki ka auro mana a matsayin Suruku? Wacce ma tinanin da ake iyayanta basu da rai dan da sunada rai da yanzu sun biyota

Nazeefa na daki tanajin ance kila iyayanta basuda rai ta fashe da kuka!

Mubin kuwa barin Hajiyarsu yayi ya shige daki! Kwance yake yanajin kanshi namai ciwo Sosai, Su Sam basuimai adalci ba danme za ace za a hadashi da Haleema itasam da batada kamun Kai ga rashin kunya sai kishin banza

Tsaki yayi ya dakko wayarshi yai ma Haleema text kamar haka! _Hello Naji abunda kikeso ai auranmu KO? To inamai baki shawara tun yanzu kice bakyasona kin hakura Dani_ yai Mata sending

Jikinta na rawa ta bude dataga Sunanshi a screen din wayar, budewa tayi taga text din dayai Mata, Tsaki tayi dukda zuciyarta na zafi itama tamai reply kamar haka _Aikin banza ma kenan AI tubda maganar a Hannun iyayanmu take Kai kasani, nidai I love you ya mubin_ ta turamai

Ya bude Dan bacin rai kasa reply ma yai Mata direct kiranta yayi taki picking, Kara kiranta yayi sai a na biyun ta dauka, tace Hello”

Gaya Mata magana son ranta yayi yace” I told you Nazeefa nakeso kuma ita Zan Aura

Kashe wayan tayi gaba daya tahau kuka kamar an aiko Mata da mutuwa!

Shi kuma ya sake kirin number yaji a kashe tsaki yayi yace Chan ta matse maki nidai Nazeefa nakeso!!

Hajiyarsu Tahau sama Dan kiran Alhaji

Mubin ne ya fito Parlor ya fada dakin Nazeefa tana kwance saiga mutun ya fado, mik’ewa tsaye tayi idonta jajir tace” get out of my room malan Ka fitaaaaaaaaaa!!! Da karfi tayi maganar

Ya ce Zan fita amma ai bakiji me yakawoni, ta daga mai hannu irin she don’t want to hear anything from him

Ki saurareni Kiyi hakuri yace” Nazeefa inasonki, I love you, I want to spend the rest of my life with you yana magana yana hawaye!!

Kallonsi tayi tace…………..🤣🤪 Nima Bari najirata naji me zatace😂
Da jajayen idonta Nazeefa ta ke kallonshi cik’e da mamaki tace Mubin I told you to go out banason Ganinka ka fitaaa tana magana tana kuka muryanta na rawa

Yace” i’ll go out but… Sai kuma ya tsugunna yana rokonta akan ta temaka ta soshi, shi Sam beson Haleema, Kara kallonshi tayi tace inhar bazaka fitaba ni Zan fitan maka a dakin, kasan dai matsayina a gidan, mezakai da Yar aiki

Bata gama rufe bakiba saiga Hajiya ta sakko daga Sama! jin hayaniya tayi a dakin ta leka, Ganin mubin tayi a dakin ranta a bace ta saukar Mai da Mari, Sannan ta juya kan Nazeefa itama ta mareta tace” yan iskan yara, Wannan iskancin ba anan gidan za’ai ba

Ta kalle mubin tace” Kai Dan bakada hankali ka Tina wacece Nazeefa nan da bakinka kake yawan kawomun karar Tana bin Maza, this n that sai yanzu kuma zakace kana sonta nidai na fada maka a anan gidan ba!

Nazeefa saboda tsaban bakin ciki Kasa komai tayi in banda innalillahi wa inna ilaihir rajiun da take ambata a zuciyarta

Hajiya tace ma Mubin wuce muje! Auranka da Haleema ba fashi Wallahi, Mubin saboda bacin rai yace” anwani andama mutane sai kace banine Zan zauna da Mata na ba a barni na aura Wanda nakeso mana

Hajiya ko sauraranshi batai ba ta wuce ta zauna a parlor shi kuma daki ya shiga ya kulle, Nazeefa kuwa suna fita ta Kafa sabon kuka tace” aranta wannan wani irin tashin hankaline, Ta roka Allah daya kawo mata mafita

***********Chan Gida Kauye

Baban Nazeefa ne Zaune a waje yanashan iska yana jin radio Saiga wasu matanan guda biyu sunzo wucewa ta kofar gidan, Dayan tana ganinshi ta Fara rufe fuska

Kyalla ido yayi Malan Nalado mahaifin Nazeefa, Yace Malama sahura kidena rufe fuska naganeki sarai Ina yarinyata???

Inda inda ta farayi yace” Mu shiga ciki

SAHURA itace me Kai yara aikatau birni, ita tazo ta ziga mahaifiyar Nazeefa akan yanda take dakyau dinnan akaita akatau Zata samo musu kayan arziki masu yawa

Samun Waje sukai suka Zauna a tsakar gida, Saiga Maman Nazeefa ta fito tana ganinsu tace” Alhamdulillah, Malan Nalado yace ki rufemun Baki se yanzu kika sama bakin magana?

Malan Nadalo ya kalle sahura yace Ina yarinyata daya tilo Kika kaita? Nan ta Fara magana muryanta na rawa tace” tsaya kuji, Malan yace” A zaune ma muke, Sannan ya Kara maimaita Mata ina d’iyata?

Sahura tace Malan kaimun aikin gafara yanzu haka bazance ga inda takeba, ainihin gidan da na kaita, Shekarun da suka wuce naje Ance sun tashi, Sunyi sabon gida a garin Kaduna

Tana Magana tana kuka tace Dan Allah kuyafemun, Maman Nazeefa najin haka ta tashi ta chakumo rigarta tace Wallahi Ko ki nemonin y’ata ko ai biyu babu, Kakari ta Fara Malan Nalado Yace wa matarshi ta saketa

Nan ta saketa amma tanata wurga Mata harara

Malan yace” Sahura kodai kinsaida mana yarmuce Mu hakura

Idonta yai kananu tace Wallahi bantaba saida kowani yaro ba, Yace” shikkenan Ki tafi akwai Allah, indai tanada rai da lafiya zata dawo wajenmu Dan Addu’a gaskiyane kuma munanan munayinta

Tace Nagode Sannan suka fita suka wuce da kawarta

Maman Nazeefa ta fashe da kuka ita dole tanason yarta

Malan Nalado yace” kinyi shawara danine? Wai meyasa sau tari Mata saisu dingayin Abu batare da mazajensu sun saniba?

Nan itama yai Mata nasiha akan addu’ace kawai mafita Dan Malan nalado mutun ne me tawakkali da Allah, Komai nashi addu’ane Kawai

   ******Kaduna

Kwanan biyu Mubin da Nazeefa basuga juna ba dukda suna gida daya, Nazeefa kuwa ta dau kudirin duk wani abun da za’ai mata bazata daukaba, Shi kuma mubin gaba daya baya cikin hayyacinsa Dan bala’in son Nazeefa yakeyi kamar kullun karamai akeyi

Washe gari MONDAY Mubin ne ya tafi wajen aiki, Yana cikin office kanshi namai ciwo, yace Bari yadan fita cikin hospital din yaga make faruwa

Fitowarshi keda wuya yaga yan Mata yan practical cik’e a Kofar office dinshi, Good morning sir sukai Mai ya amsa sannan yace me kukeyi anan? Sukace Kai muke jira ka fito muje ward round!!

Oh yace musu, kun fito da kayan? Sukace yes sir, Kowaccensu da a bun da take sakawa a zuciyarta idan anbarsu sai suce suna son mubin Haha

Tafiya yake suna binshi a baya kanshi na ciwo but hakanan ya kokarta har suka gama!  bayan yadawo office ne ya zauna wata Mufeeda me shegen kaudin tsiya ta Shugo office din tayi tace” Doctor sannu kasha magani? shouting yai yata yace” get out of my office yanzun nan ke wacece? Aranshi yace ance maki Ina dealing da yarane, Ko manyan ma Inba Nazeefa banga wata Mace ba

Fita office din tai ranta a bace, kawayenta Suka kwashe da dariya alamun ba market, Wata a cikinsu tace kuma in banda abunku high class Guy kamar Doctor zaku tusa kanku? Nikam ban iyawa, kunsan ma Dan wanene kuwa?

Sukace waye ubanshi? nan ta zayyana musu komai AI mahaifinshi babban mutun ne yanada kudi da companies da dama rike baki sukai

Mufeeda ta taba baki tace I love him Kuma sai ya soni nan suka kwashe da dariya suna Mata kirari Dan a cikinsu itace bataji SosaI…..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *