HIKIMA
CHAPTER 8
*Russia*
“Like seriously yarinyar Kake jira Har tsawon wannan shekarun Maina, are you serious or you kidding me?”
Dr. Dalhat Ya tambayi Maina yana Kara sakin dariya Hade da tafa hannu, Maina dake zaune kawai kallonshi yake bai iya cewa komai ba, saboda shima yana ganin foolishness dinsa, ta Yaya zai zauna jiran abinda bai da masaniyar wanzuwar shi a duniya, it’s been 20years kenan tunda ya Wayi gari Ammiey tace masa an sace Lulu, yana ta kuka ya yini baici Abinci ba, da sukaje Maiduguri Dada tace mishi ai zata dawo, duk inda take zata dawo, kodan wannan alkawarin auren da akai. Wannan auren zai dawo da ita gida shidai Ya dage kawai da addua. So Dada ita ta saka mishi wannan hope din, ita ta Kara dasa mishi wannan soyayyar tareda rike alkawari amma kwana biyunnan bukatunshi suna neman fin karfinshi, shekarunsa sunkai yadda yake bukatar opposite gender Dan Ya cika mutum kuma namiji, so har ya Fara tunanin Anya bazaiyi aure ba idan yaso duk lokacinda Allah yasa ta dawo gida Dan shi jikinshi na bashi she’s coming, she’ll come for him. To amma tambayar ita ce yaushe? Se yaushe zata dawo? Ta Yaya kuma? Bai sani ba, Allah shi ya barwa kanshi sani.
“Abokina Ya zanyi? Nifa saboda yadda na sata a rai ko kallon Wasu matan banayi balle har naji Meye taste dina”
Wani kallo Dr. Dalhat yayi mishi sannan yace
“Seriously this is Delusional, ban taba tunanin zanji makamankciyar rayuwa irin taka ba Maina, how can you? ”
Se kuma yayi Tsaki sannan yace
“See, wata ya rage kawai mu gama komai, ka manta da yarinyar kawai kayi aurenka, ina wannan yarinyar dake stalking dinka? Ka aureta mana amma babu yadda zaayi ka zauna jiran gawon shanu, what if idan Tazo ka ganta gurguwa ko a nakashe? Zaka sota still”
Se a sannan Maina Yayi dariya tareda buga kafadar Dalhat yace
“Mutumina kana sha’aninka, wayace maka zan sota ne? Ai zuciyata da sonta ta ginu kaga I’ll accept her da duk yadda na ganta, as far as zata kauda Idanunta daga flaws dina bana tunanin akwai abinda zai gagara”
Kai Dalhat Ya Jinjina tareda kurbar coffee din da tuntuni ya dade da yin sanyi, Dan tuntuni akai serving dinsu amma saboda they’re heated up in a serious conversation shiyasa basu ma sha ba, seda ya shanye tas sannan ya aje tea mug din akan saucer yace
“Kafi karfina Maina, kasa yarinyar da yawa a zuciyarka. Allah ubangiji ya zaba muku mafificin alkhairi. Amma kayi Trusting rayuwa da yawa”
Kai Maina Ya girgiza yace
“Nagode sosae Abokina Kaima you have contributed so far. Amma Kasan ba rayuwa nayi trusting ba, Allah nayi trusting, nasan addua ta bazata taba tashi a banza ba. Kaidai mu hanzarta muje class”
Mikewa kawai sukai suka nufi inda zasuyi lecture din.
A hankali rayuwa ta cigaba da tafiya, by each passing day zuciyata tana kara karbar Abdallah, tana kara nuna min shi din shi ne abinda ya cancanta Dani. Gaba daya Abdallah ya siye min zuciyata banida wani tunani idan ba nashi ba, kome zanyi se na Fara fada mishi ya bani shawara kafin nayi. A hankali har wata guda Ya tafi anan naje weekends Kano, munjima muna hira da Mama sannan nayi wanka naci Abinci nayi sallah na dasa waya.
“Farin Cikina baki ganin ya dace su Papa suzo ayi formal magana, Nifa gwaurancin nan ya isheni haka”
Dan Murmushi nayi nace
“Kai Tun Yanzun ka bari idan na gama level 3 se ayi Maganar kafin azo bikin kuma na gama school gaba daya”
Wata dariya ya saki yace
“Haba? Da gaske kike? Tabdijam! I can’t wait gaskiya, Dan ni so nake nanda 4months ace kina gidana”
Idanuna na zaro tareda marairaice fuska nace
Story continues below

“Kai Sir….”
Cikin hanzari ya katseni da fadin
“Farin Cikina, me yasa bazaki daina cemin Sir ba for crying out loud? Se kace wata dalibata. ”
Toshe bakina nayi da tafin hannuna saboda kada nayi dariya nace
“To da ni mecece, Inace har useless and stupid girl ka cemin”
Nasan ya tsana na tuna masa Farkon haduwarmu, Yanzun nan zai fara fada, amma ranar se naji Ya kashe wayar. Dariya na karayi na mike na fito parlor daidai shigowar Hamma Mussadiq, Karo na farko da na saki Murmushi Tun bayan haduwar mu a Mota
“Hammana! Sannu da zuwa”
Shima murmushin Yayi yace
“Hikmata yaushe kika dawo? ”
Zamannan nayi gefen Mama tareda daura kaina akan kafadarta nace
“Dazun nan, kuma Mama bata siya min kaza ba”
Tabe Baki Mama tayi ganin mun saki jiki da juna, da kuwa tamkar Baki haka muke. Tureni tayi yayinda Hamma yake ta dariya, Hakan yasa nace
“Mama ki daina haka, kinga kina bawa su Hamma kofar yi mata dariya, Yanzun idan ban kwanta jikinki ba ina zani”
Dungure min kaina tayi tace
“Dadin baki ko?”
Mikewa Hamma Yayi yana dariya yace
“Grilled Ko roasted chicken kike so?”
Wani irin Murmushi na saki nace
“Hammana yafi na kowa, grilled nake so, sannan inason yoghurt da strawberry cheesecake”
Kallona Yayi yace
“Bafa Abdallah bane, Mussadiq ne”
Dariya nayi nace
“To ta Yaya zance Abdallah ya siyo min duk wannan, saboda Kai dinne shiyasa. ”
Ficewa yayi ni kuma na juya Kan Mama na fada mata sakon Abdallah, tana tamin tambayoyi akanshi sannan tace
“To Allah ya tabbatar muku da alkhairi, dama karshen satin nan zaa saka rana, Baffanki ke kadai yake jira. ”
Ance idan akai zancen Zaa bada Kai, kuka kake amma ni wani ihun murna na saki, Mama tasa pillon gefenta ta kwada min tareda fadin
“Ke dai Anyi ja’ira, Kunyar nan ta Fulani ke kam bakida ita. ”
A guje na wuce dakina a raina Ina fadin ta Yaya zanyi Kunyar Fulani bayan ni ba bafullatana bace. Dama ni tuntuni fullanci bai birgeni Dan Ko Yaren yinshi nake Dan dole Dan Ina cikinsu amma aladarsu gaba daya batai min ba, inda akwai culture da nake mugun so to barebari ne, sumin mutanen.
Gefen gado na zauna tareda janyo wayata na rubutawa Abdallah
_Galaxy, Mama tace next weekend Zaa saka mana official ranar bikinmu. I can’t wait na zama mallakinka. I love you_
Ina gama rubutawa na tura mishi lokacin yana gaban Anty Talatu da Papa, Anty Talatun ita ce wadda Papa ya aura bayan rabuwar shi da Ummiey. Wayar na dakinshi bai san na turo ba.
“Ai Prof sede ya hada ita Zainab din da Mupheeyda Ya aura Rana daya, tunda ni dai ban isa cewa Mupheeyda Abdallah ya fasa aurenta ba”
Da sauri Abdallah yace
“Nifa bani nace Ina sonta ba, Dan Haka babu uban Wanda ya isa Ya min auren dole a gidannan”
Wata tsawa Papa ya dakawa Abdallah yace
Story continues below

“Ubanka Babana, Ashe Bakada kirki, Talatun tana fada Kana mayar mata. Saarka ce? To tunda Hakane sede idan ka hakura da ita Zainab din amma dole ka auresu su biyu”
Wani murmushin nasara Anty Talatu tayi tana jijjiga kafa, Abdallah ranshi a matukar bace ya bude baki Zaiyi magana, Papa yace
“Bana son jin Wata magana kuma, ka dauka zancen nan an gama shi, ni zan fahimtar da iyayen Zainab din, saboda nasan kana sonta! ”
Abdallah bakin ciki yasa ya Mike tareda zabgawa Anty Talatu harara ya nufi dakinshi, yana zuwa ya Fara zagaya dakin, shi dai tunda yake karan farko da yaji yana matukar son Abu a rayuwarshi, shi baya son aure saboda yana daukar aure as liability, tuntuni abinda ya hana Ya auri Mupheeyda kenan. To amma zuwan Hikmah yasa yaji aure nima ce da Allah Ya saukar tsakanin mace da namiji. To kuma ta Yaya zai aure su biyu Wanda kwatakwata babu wata hanya da kamanninsu Ya hadu Ko halayarsu. Yana kallon yadda Anty Talatu ke juya Papa inhar tayi magana, Papa bai isa Ya Musa ba, sannan kawai ya auri yarta shima a asirce shi ya zama kan tace? Kanshi Ya dafe yana jin yadda kan ke Sara mishi.
Nikam nayi ta jiran reply dinsa amma har safe babu ko amsa balle kira, Tun anan nasan tabbas babu lafiya hakan yasa ina idar da Sallar asuba na Fara kiranshi amma wayarshi a kashe, gabaki daya se naji tsoro ya kamani, let it not be shima he’s breaking up, kada ya zamana ba zama yazo yi ba. Haka nayi ta sakawa Ina kuncewa tareda hasaso anything possible da zai iya faruwa. Amma iya tunanina babu abinda yazo raina. Baccin da ban koma ba kenan, na shiga shirts kayana Dan inason zuwa da wuri naga halinda Abdallah ke ciki.
Wajen azahar na tafi, gaba daya hankalina a matukar tashe, Hamma Mustapha Ya kaini Tasha na hau Mota Inata trying numbers dinshi amma amsar daya ce “It’s switched off, try again later”
A hankali hawaye ya Fara sauka min daga idanuna, shikenan Haka rayuwata zata cigaba, Haka zan kasance kullum zuciyata Shattered, idan na tattara pieces din na hade Se wani ya kara shammata ta ya wargaza, rufe kaina nayi cikin hijab Inata kuka a Haka barawo ya lallabo Ya saceni nayi bacci!
Ina tafiya da daddare masu neman aurena mawa Abdallah suka zo, wannan karan hadda Papa Wanda Yayi squeezing yazo, Ashe abokin Baffa ne Sunyi wani PgD tare. Se sabuwar gaisuwa da kuma hira Har Papa yaji Kunyar fada masa abinda ya kawoshi amma yazaiyi Haka ya mishi bayanin duk yadda ake ciki. Baffa yayi Shiru tareda Jinjina alamarin, can dai yace
“Babu yadda zaayi da hukuncin Allah, ina ganin mu barwa Allah zabi tunda shi ya kaddaro hakan. Se mu karba a matsayin kaddarasu. ”
Papa cikeda farin ciki ya karakace ya zaro kudi ya aje gaban Baffa yace
“To ai Abu yayi kyau ina ganin a kammalla komai kawai. Wannan kudin 100k na tambaya, 150k na sadaki, Allah Ya tabbatar da alkhairi”
“Bansan yadda zaki dauki Maganar ba, amma ni a gurina komai da sauki yazo. Baban Abdallah dinne yazo akan zancen saka rana. Mun tsaida watanni biyu Dan hankalina Zaifi kwanciya. Bana son Nesan nan da Uwata tayi damu, gwara idan tanada aure shikenan”
Cikeda farin ciki Mama tace
“Mashaaa Allah, jiya take cemin yace zasu turo Ashe shi bai sani ba suna hanya. To Allah ya sanya alkhairi. ”
“Amin ” Baffa ya amsa tareda gyara zama yace
“Akwai Dan damuwa, amma to me bawani abin bane, nasan Kema zaki fahimci hakan. Mahaifinshi yayi min bayani akan tuntuni akwai Agola Dayake riko a gidanshi, to Dama Yayi alkawarin zai aurawa shi Abdallah wannan yarinyar, shi ne yace sai Ya auresu su biyu”
Da sauri Mama tace
“Me kace musu? ”
Shikanshi seda yayi shayin bata amsa saboda yadda ta tsareshi da ido, Hakanan yace
“Nace musu duk tsarin Allah ne, babu damuwa”
Kai Mama ta dafe tana jin wani irin a kanta, me yasa maza suke haka ne. Ina Hikmah ina kishiya? Yarinya da bata san komai ba.
“Haba Malam, Yaya zakai haka. Me yasa Bakace zaka tuntube ni ba, me yasa ka yanke hukunci Baka tuna Yaya Hikmah zata karbi zancen ba, kana ganin bazata ga kamar Dan bamu muka haifeta bane? ”
Dan Tsaki ya saki, Dan shi ganinshi hakan ba komai bane, to Meye Dan Ya auresu su biyu? Shi Baiga wani abu ba.
“To Menene a ciki Dan Ya auresu su biyu? Ni banga wani aibu ba. Hikmah yata ce, I trust her nasan bazata taba bani matsala ba. Kede ki kwantar mata da hankali sannan kiyo list a Fara shirye shirye, Dan zan aurar da yata, zanyi gaggarumin bikin da Baa taba yin irinshi cikin gidannan ba!
Who saw This coming?
Bani na isa Zaria ba se gab da Maghrib, lokacinda na shiga dakina Kaina Kamar zai tsinke saboda azabar ciwo, ga wani palpitation daya sakani gaba, idanuna har dusudusu nake ganin wannan yasa nasan tabbas Bpna Ya hau. Bana sallah hakan yasa na kira Mama wadda tana zaune jugum ta rasa abinda ke Mata dadi gani take baayi min adalci ba, ta Yaya Baffa zai iya yin hakan, gani take an zalunce ni ne kawai. Tana cikin wannan yanayin Sega wayata tana shigowa, kasa dauka tayi dan gani take da zarar ta dauka zan fahimci halinda take ciki. Sau biyu ina kira bata dauka ba, hakan yasa na hakura na gwada number Abdallah, inajin ta shiga naji tamkar an tsoma ni cikin ruwa saboda yadda naji dadi a raina, amma har ta gama ringing Baa dauka ba. Kashe wayar nayi baki daya na kwanta tareda runtse idanuna, duk wani tunani daya taho min Se na kawar dashi saboda Ina bukatar adequate rest Ko na samu Bpn ya sauka. Cikin raina Inata maimaita Hasbunallhu wa niimal wakil! Cikin kamkanin lokaci naji komai ya Fara lafawa ban jima Ba bacci ya daukeni. Tunda na kwanta nake wani irin mafarki me tayar da hankali, a firgice na tashi Ina maimaita adduar Wanda Yayi mummunan mafarki Ko ya kasa bacci
_Audhu bikalmatillahi tammati, min gadabihi, wa iqamihi, Wamin sharri ibadihi, Wamin hamazati shayadin, wa an yahduru!_
Tashi nayi na kuuna standing fan sannan na tafi bayi nayo alwala, time na duba naga daf ake da Fara kiran Sallar asuba, hakan yasa na Fasa komawa kawai na hau sallaya Ina kaiwa Allah kukana. Seda nayi asuba sannan na duba timetable naga Se 9am nikeda class hakan yasa na koma na kwanta, bacci sosae nayi se takwas da yan mintuna sannan na tashi. Wanka nayi Nazo nadaura Abinci, kafin na gama na shirya na duba Bpna Naga ya sauka sannan naci Abinci.
Karfe Tara saura Minti biyar muna zaune nida Nanah, gaba dayanmu babu me magana Se Amjad ke ta janmu da hira ganin da gaske Shiru shirun muke ji yasa kawai ya rabu damu, amma ni bansan ya Nanah takeji ba, Nikam komai baya birgeni, lecture ma Dan dole na zota dan nasan Urinary physiology ba saan wasa na bane, if not da Bazan shigo ba.
Muna nan zaune se bayan awa daya sannan class rep yayi making announcement cewar bazai samu damar zuwa ba, Ko Damuwa banyi ba, inajin yadda mutane ke zaginshi amma hankalina yayi gaba, so nake kawai naga Abdallah naji dalilin da yasa ya shareni for good 3 days. Ko su Nanah Ban jira ba na tafi office dinshi. Ko knocking banyi ba, Ina zuwa na tura kofar da karfina na shiga ciki, yana tsaye Ya zura hannayensa cikin jeans pocket dinshi, Wanda color ya zama pale brown, top din jikinshi milk ce me taushi, babu rubutun komai a jiki se tambarin designer din, fuskarshi tayi fayau, idanunshi sun fada ciki kamar Wanda Yayi jinya. Kallona yake kamar yadda na zuba mishi ido, dauke kanshi Yayi tareda fadin
“Zan sameka a office, se mu karasa maganar”
Se a lokacin na fahimci Ashe bashi daya bane, Juyawa nayi naga wani mutum Wanda sun kusa sa’oi da Abdallah Ahmad ban taba ganinshi ba. Murmushi yayi min sannan ya fice bayan Ya ja mana kofar. Zagayowa Abdallah yayi gabana ya tsaya kamar 3 feet away,
“Hikmah please sit”
Ya fada a hankali Kamar me rada, dagowa nayi dukda kwarjinin da yayi min amma seda na zabga mishi harara nace
“Kanada wannan bakin Dama? Abdallah me Kake nufi? is that treatment a bye bye? ”
Kanshi Ya dafe yana girgizawa yace
“I’ve messed up Hikmah, kina tunanin cikin hayyacina zan iya cewa na fasa? duk ranar da aka ce miki Abdallah ya fasa aurenki, to kisa a ranki I’m insane, I’m possessed wallahi. Bazan taba yin hakan ba, Bazan taba cutar ki ba. Yanzun ki zauna muyi magana”
Yayi nasara Dan kalamansa Sunyi tasiri sosae cikin zuciyata, a hankali jikina a sanyaye na zauna inajin haushin Kaina da nayi tunanin cewar Abdallah zai iya rabuwa Dani, zai iya yaudarata. Se naji babu dadi.
“Zainab its very hard Kinji, amma I got you farin Cikina. Ban taba fada miki ba saboda da farko ban taba kawowa cewar hakan zata iya faruwa ba. Kinsan VC shi ne Mahaifina, Mrs Hassanah Uba ita ce Ummiey ta. Sun rabu Tun kafin na gama secondary school, I taught may be zasu maida aurensu but basu mayar ba, kowannensu yaje Yayi aurenshi abinshi. I came from a broken family, shiyasa Bana son aure , a da ina ganin duk aure haka yake ayi a rabu, later na gane namu ne Haka, saboda kaddarar mu kenan. Papa yayi auri wata lecturer Hajiya Talatu, matar nan is cruel ban taba ganin azzaluma irin ta ba, seda ta maida Papa se abinda tace shi yakeyi. Tazo da yarinyar ta Mupheeyda wadda take completely opposite of her sede Kinsan Hausawa sunce barewa bata gudu danta yayi rarrafe, she’s more poisonous than uwarta, shiyasa muka daina shiri, her only weakness is I, tana sona Hikma, so Wanda banda mugun halayenta da nayi dace. Anyi zancen Zamui aure na ki amincewa kuma daidai lokacin kika shigo rayuwata shiyasa na tabbatar kafin na shawo Kanki naje gidanku, naje komai ya tafi daidai, sede ranar da mukai waya last ina fitowa Papa ya kirani na sameshi parlonshi, tunda na Tarar da Anty Talatu zaune nasan akwai matsala, kafin naje ta gama mishi famfo akan sede na aureku ku biyu…… ”
Story continues below

“Mu biyu kace Sir, nida wa kenan? ”
Na katseshi da sauri ina ware masa idanuna, duk wannan kwarjinin Se naga babu ko daya, ban ma gani ba balle naji shayin abinda zan fada masa. Cikin sauri yace
“Hikmah Ki tsaya kiji Dan Allah ”
Ya fada yana hade hannayesnshi guri guda alamun roko, kaina na kawar ,Har idanuna sun cicciko da kwalla nace
“Bazan iya ba Sir! Zuciyata bazata dauka ba, Wallahi Bazan iya ba. Me yasa Se ni, me yasa rayuwa ba tamin adalci, me yasa kowa yazo se ya fasa min zuciyata, seda aka gani na fara sonka sannan wannan stupidity zai zo? ”
Mikewa nayi Ina jin yadda jikina yake Bari, Kamar zan fadi haka nakeji. Da sauri ya riko hannuna yana fadin
“Hikmah don’t leave me, ya kikeso nayi? Ya zanyi? ”
Kwace hannuna nayi cikin zafin Nama nace
“Tambayata Kake ne? Ni kake tambaya ya Zakayi? ”
Dariya nayi kuma kuka nake sannan nace
“Tun kafin na shiga kenan anamin zancen kiahiya, ina marainiya a salwantar min da rayuwa! A’a wallahi ”
Daga Haka Ko sauraranshi banyi ba na wuce daga office din, hijabina naja na rufe fuskata Inata sauri na tafi daki, saboda yadda jikina ke karkarwa dakyar na bude dakin, na fada gado, zuciyata Kamar zata fito Haka nake ji. Nayi kuka na rashin sanin ya zanyi, nayi kuka na rashin Gata, na tahumi rayuwa akan walagigi da takeyi Dani, kamar zan haukace haka nakeji. Ina nan akai azahar Har laasar ban tashi ba, ba kuma ni da niyyar yin hakan. Ina kwance Kamar ruwa ya cinye ni, Inata kwance har maghariba sannan hankalina ya fara kwanciya kawai abinda na yanke hukunci shi ne na hakura da Abdallah, Dan Bazan iya kishi ba, Bazan iya masifa ba.
Ina nan kwance na tashi zauna tareda Fara kiran number Mama, cikin saa ta dauka, yadda taji muryata a dashe yasa tasan na samu labarin abinda ke faruwa.
“Mama ki cewa Baffa na fasa auren Abdallah”
Gabanta taji ya fadi tace
“Subhanallah, lafiya Hikmah?”
Hawayena na share nace
“Mama Wai mu biyu zai aura, nida wata kanwarshi, Mama ni Bazan iya ba, ina zan saka raina? ”
Se na kara fashewa da kuka, Shiru tayi ita batace komai ba, ita bata lallasheni ba seda nayi Shiru sannan tace
“Kiyi hakuri Hikmah, bansan me ya hau kan babanki ba, sun mishi bayanin da Abdallah yayi miki amma ya amince har ya karba sadaki Anyi fixing date nanda wata biyu”
Hawayen na share Kamar zan fashe Dan kuka, Baffa saida ni Zaiyi? At least ya dace a bani option tunda ni zan zauna dashi ba wani ba, ta Ina zanyi hakan, ta Yaya ai baamin adalci ba ko kadan ba? Kuka sosae na dinga yi inajin Mama tana rarrashina tareda bani baki, amma ko jinta banayi saboda ni banida hakuri bana daukar abu da sauki komai a gurina me zafi ne shiyasa nake shan wuya kuwa. Can Mama ta kashe baafi mintina goma ba Aiman Ya kirani, Bazan taba ganin call din Hamma Aiman naki dauka ba, hakan yasa na dauka na fada mishi abinda ke faruwa
“Hikmah wannan abin is simply, is just that Baffa ya rigada yayi complicating abin. Amma bakina addua ba?”
Kaina na gyada, ban bashi amsa ba yace
“Then, kiyi Shiru kiyi istikhara for good three days. Amma Se kin fitar da komai a ranki daga ranki, se Kinsa a ranki Allah Kika bawa Zabin. To kuwa Allah zai zaba miki. ”
Ya jima yana min nasiha sannan mukai sallama, fuskata na shiga na wanke nayi wanka, na canja kaya sannan na rufe dakina na tafi wani clinic inda nake follow up, Doctor seda ya min fada saboda yadda Bpna yayi shooting, a Daren dai a clinic din na kwana.
Story continues below

Wasawasa Abdallah ya dauka da gaske zan hakura na sakko amma har yayi kwana uku bana amsa call dinshi. Da daddare Ina kwance daki Sega Nanah ta shigo, Ko zama Batayi ba tace
“Sir Abdallah yana waje yace kizo.”
Mikewa nayi saboda bansan further questions daga gurin Nanah shiyasa na fita, Ina Fita na ganshi cikin mota, gefenshi Umminshi ce kamar Ko yaushe Tasha gayu Har Daren ma Bazaa huta ba. Ina isowa dukkansu suka fito, gefenta na koma na gaisheta ta rike min hannu, shikam ko kallonshi banyi ba balle yasa ran zan kulashi, cikin wani Eatery muka shiga can VIP section, babu kowa muka zauna sannan Ummiey tace min
“Zainab, Kinyi jinya ne? ”
Da sauri na girgiza kaina nace
“A’a Ummiey”
Kanta ta gyada sannan tace
“Ni Zainab bansan me zance ba, ni mecece nasan pain din, nasan abinda kikeji, banyi niyyar saka baki cikin Maganar ba, amma Abdallah zai cinyeni indai banyi intervening ba. Nasan baayi miki adalci ba ace Zaa aureku ku biyu. Amma waye yake tsallake kaddararshi, wanene babu shi, komai Allah Ya tsarawa bawansa there’s wisdom behind it, so kada Ki damu, ki nemi Zabin Allah bazakiyi dana sani ba. Kuma bawai na goyawa Abdallah baya bane amma Bashida laifi, ki tayashi yiwa mahaifinsa biyayya”
Daga Haka ta Mike tace
“Kui hakuri da junanku, sannan ku fito se kuyi magana a waje”
Jikinmu dukka a sanyaye muka fita, Mussaman ni, ji nake kamar zanyi me. Seda ta tafi sannan yazo kusa dani yace
“Farin Cikina! Kiyi hakuri Kinji Yan Matana, kiyi hakuri”
Na tsinewa zuciyata yafi a irga da har son Abdallah ke Kara samun gurbi cikinta, naji haushi na kuma. Kasa bashi amsa nayi Illa kallonshi da nakeyi ina ganin how will life be without this being, Abdallah is my weakness. Da kyar yasahwo kaina na yadda naci Abinci, amma magana Ko sau daya ban iya mishi ba. Har kofar apartment ya rakani sannan ya tafi, na jima sosae sannan na koma ciki inajin kewarshi, wai ita zuciya Haka take da naci akan abinda take so.
Ina shiga daki na dauki qurani na karanta sannan na dakko books dina na Fara Karatu Dan idan banyi wasa ba zanyi CO semester dinnan. Har 1am sannan nayi bacci. Washegari Cardiovascular physiology muke dashi kuma Se 3pm hakan yasa na karfafa jikina nayi aiki sosae nayi Karatu. Bayan azahar Baffa ya kirani, duk haushi ma nakeji amma Haka na dauka muka gaisa sannan yayimin bayanin da na riga na sani, bakin cikin se lokacin yake tambayata opinion dina ni kuwa nace a mayar musu da kudin na fasa auren. Baice min komai ba ya kashe wayar, so guilt was eating me, AI Baffa ko Bera yace na aura ya kamata na mishi Biyayya balle mutum Wanda ni nace Ina sonshi, Anya kuwa ma nufin yar halak ce da zan ki musu Biyayya saboda son raina? Jikina Yayi bala’in sanyi haka na tattara na tafi class.
Ban jima da zama ba class din ya cika Dan missing din lecture Abdallah is like playing with a Dragon, Bashida kirki when it comes to that, he always says bazai bata time dinshi making lecture note and some useless people will just stay home, Wanda bai zo ba ya san Sauran.
Ina chatting da Najaatu wadda kemin jaje tareda dannar kirjin abinda ya faru, naji an buga desk din Dana daura kaina akai, a hankali na dago Kaina, nayi toxali da irin yan matannan ajebos, kyakyawa ta gasken gaske, fara ce kyakywa, tasa red lipstick Wanda Yayi mata kyau tareda haska fuskarta, tayi rolling da bakin veil hannunta na karkada car key,
“Kece Zainab? ”
Ta tambaya tana taunar chewing gum Tareda yin kas kas, kallonta nayi nace
“Eh! How may I help you? ”
Tsirtar da yawu tayi tana bina da kallon wulakanci tace
“Allah Ya isa amma! Ashe Kece Dama yake ta hankilo akanki, Kece Zaa hadamu kishi dake. Oh my gosh! Wannan abar”
Ta fada tana nuna ni, hade damin kallon wulakanci, bakina kasa budewa Yayi, se kallonta nake Dan na kasa figuring ita din Wacece, seda tace
“Nasan kina tunanin wacece wannan, sunana Mupheeyda, mace daya mallakin Abdallah Ahmad Abdallah, kin gane. You look innocent bana son kikawo Kanki makabarta, kiji da gurguwar kafarki….. ”
Anzo gurin, Babu wani da ya isa tanka halitta ta na kyaleshi
“Karki! Karki fara, Useless stuff wadda bata san kanta ba, idan da kin yadda ke Kece I don’t think zaki bata ma Kanki lokacin nemana, gurguwa ki rubuta ki aje ita ce kishiyarki, ita kadai a Zuciyar mijinki kuwa”
Dariya tayi dukda maganata ta mata ciwo kamar yadda tata tayi min zafi, cikin daga murya ga class din Anyi Shiru kowa hankalinshi akanmu, mutane including Nanah da Amjad yaushe muka hade da Abdallah ne?
“Ashe zanyi yawo tsirara kenan, ashe ma ba Mupheeyda bace yar Talatu. Ki rubuta ki aje matsawar kika auri Abdallah, kika zama kishiyata to ki sani na haukace ko kuma na mutu.”
Dariya nayi dukda gabana ya fadi nacr
“Gado ba karanbani ba. ”
Har ta juya taji na fadi haka, Aikuwa tace
“Dadinta ni nasan asalina, nasan waye ya haifeni, ba Shegiya wadda aka haifeta a titi ba kuma aka yarda ita a titi”
Da sauri na mike zuciyata Kamar zata fashe saboda yadda take wani irin bugawa
Dau!!! Naji saukar Mari…………..
Da sauri na saka hannuna na dafe kuncina dan dukkan tunanina ni aka mara, se kuma Banji zafi ba hakan yasa na waigo kan Mupheeyda wadda tuni hawaye sun bata saman kyakyawar fuskar da ake takama da ita, Abdallah ne a gabanta, idanunshi Sunyi jawur saboda bacin rai, ban taba ganinshi a Haka ba tunda nake.
“Get out! ”
Ya fada da karfi yana nuna mata hanyar waje, muryarta na bala’in rawa tace
“Yaya Abdallah, ni ka mara? ”
Hannunshi ya Kara dagawa zai sauke mata wani, nayi saurin rike hannun tareda girgiza mishi Kaina, itakam tama sadakar zata sha Mari Har ta runtse idonta.
“Get out nace”
Ya kara maimaitawa, bude idonta tayi tareda min wani mugun kallo sannan ta gyada kanta tayi gaba, Binta yayi a baya har suka fita, se lokacin na sauke Ajiyar zuciya tareda dafe Kaina Wanda ya Fara min ciwo, wayata na dauka batareda nace komai ba nayi hanyar fita Dan Ko na zauna I’ll understand nothing. Nazo tsakiyar hall din shima yana shigowa, turus na tsaya Har ya karaso inda nake, murya can kasa kasa yace
“Farin Cikina, are you hurt? ”
Dan Murmushi nayi na girgiza kaina nace
“I’m ok as you can see”
Ajiyar zuciya me nauyi wadda har seda na kalleshi ya sauke sannan yace
“please, Ki koma ki zauna, ko kwantar da Kanki ne kiyi, but at least Ina ganinki a class din zanji dadi”
Yadda ya marairaice yasa nayi Murmushi na juya na koma seat dina, kowa a class din banda mamaki babu abinda suke baki a sake, kowanne tambaya ce bakinsu. Komawa nayi na zauna tareda sunkuyar da kaina shi kuma ya cigaba da lectures dinshi, gaba daya fuskar Mupheeyda ce kemin kai kawo a idona, saboda takamar ta Tana da wannan shouting beauty dake fading matsawar zaka dinga kallonshi for long. Sunkuyowa Nanah tayi tana magana a hankali
“Ke fadamin yaushe kuka dinke keda abokin fadan naki? ”
Gyaran murya mukaji daidai saitin mu, a hankali na dago naji yana ce mata
“Nanah we need a rest fa, kada ki dameta da yawa”
Hararashi nayi shikuma ya dage min gira ya cigaba da abinda yake, Nanah kasa magana tayi Se binmu da kallo take. Can class din yayi nisa Sega level coordinator dinmu ya shigo, da dukkan alamu sun saba sosae da Abdallah yadda suke gaisawa sannan ya jashi waje sukai magana Se gashi ya dawo, inda nake yazo Ya tsaya yace
“Baffa yazo yana office din VC, go and meet him and please kada Ki damu… I love you”
Murmushi nayi na gyada Kaina na fita inajin ihun Yan class din amma baice dasu komai ba. Karo na farko da na taba tunkarar inda office dinshi yake, securities all over, seda na nuna appointment paper ta sannan na wuce. Basa main office din se wani Dan parlor like guri Wanda cushions suka kayata gurin, suna zaune su biyu gabansu Anyi musu serving juice se dariya suke najin dadi. Da sallama na shiga, lokaci guda Duka suka dago suna kallona, Kaina a kasa na tsuggunna na gaishesu, cikin faraa suka amsa, Baban Abdallah ya kalleni cikin sakin fuska Wanda anan na gano inda ziryan din kamannin Abdallah suke.
“‘Yata ya Karatu? ”
kaina na sake sunkuyarwa nace
“Alhamdulillah ”
Kanshi Ya gyada yace
“To Allah Ya bada saa, ina fatan Babana baya hanaki Karatu Ko? ”
Dan Murmushi nayi tareda girgiza Kai amma Bance komai ba, mikewa yayi bayan yasa na zauna dukda dardar da nakeyi ni a dole office din suruki! Sake gaisawa mukai da Baffa, gyara zamanshi Yayi yace
Story continues below

“Uwata kince na maida kudin auren kin fasa? ”
Shiru nayi na kasa yin koda kwakkwaran motsi balle na bude baki na bashi amsa, mun kusa mintina biyar sannan Yayi gyaran murya yace
“Kiyi hakuri, amma Bazan iya maida masu kudin ba. Nayi tunanin na isa dake shiyasa nayi hakan, Inada high expectations akanki nasan you won’t let me down, so kiyi hakuri Haka Allah ya tsara mana”
Kaina na gyada naji na hakura na amince nace
“Allah Ya kaimu Baffa”
Cikeda farin ciki ya dinga shimin albarka, daga nan yayimin sallama akan zai koma Kano Dama abinda ya kawoshi kenan saboda bazai yiwu muyi magana a waya ba. Dukda muna da lecture ban koma ba daki kawai na wuce bisa umarnin Abdallah, Dan yace indai naje class dinnan to shy babu ruwanshi da tambayoyin da zan amsa daga gurinsu.
Bamu hadu da Nanah ba se shida na yamma, ina kitchen ina girki tayi knocking, zuwa nayi na bude mata ta shigo tana wurga min harara tace
“Bakida mutunci wallahi…..”
Da sauri na katse ta nace
“Ayya Nanah, ba haka bane. Kinsan abinne yazo so sudden da ban fada muku ba”
Tabe Baki tayi irin bata yadda dinnan ba, tace
“Wannan kuma ke kika sani Malama, yaushe aka saka yace a tambayeki”
Dariya nayi wato Ya hadani dasu
“Yanzun muna August, October Inshaaa Allah”
Baki ta rike tace
“An kusa ma kenan. Wannan ballagazar ta Dazu what about her? ”
Dariya nayi nace
“Ballagaza kam! Kishiyata ce, tare Abdallah zai aure mu.”
Take yanayin Fuskarka ya canja tace
“Kidding me right? ”
Bance komai ba na wuce kitchen na sauke abincin tareda juyewa cikin warmer na fito, inda na bar Nanah nan na sameta. Se bina take da wani pitiful look Wanda kesa inajin babu dadi amma still Bance mata komai ba, se wayata Dana janyo nace
“Nanah, bamuda lokaci ya kamata duk Wasu shirye shirye muyi su. Idan ba Haka ba Zaa samu matsala. ”
Kanta ta gyada in agreement tace
“To Dame Zaa fara?”
“Anjima zamuyi Maganar event da Galaxy, so duk yadda ake ciki Se mu fitar da anko ”
A Haka muka rabu, bayan ishai Abdallah yazo shida abokinshi Usman , seda muka gaisa yace na kira Nanah. Komawa nayi muka zo da ita, cikin eatery dinmu mukaje aka Fara shirin biki.
Washegari da naje class mutane na tayi min murna, Wasu nasan babu yadda zasuyi ne Dan akwai wadda tace min na mata shigar sauri, da ta sani ita tayi mishi Tsaki ya korata suka dinke. Dariya kawai nayi mata Bance komai ba. Shirye shirye sosae ake ni ce ma nawa Ya lafa saboda exams da ta taho. Karatu nayi sosae har muka fara cikin saa. Kullum se nayi receiving messages din Mupheeyda na tsabar rashin mutunci da kuma warning, babu Wanda na fadawa balle na nuna mishi.
Ranar da zan tai Kano, yazo zamuyi sallama anan na bashi wayata yana ganin pictures din da aka turon na event centers Dan muyi finalizing Dan sati biyu kadai ya rage bikin. Gani nayi ya zare glasses dinshi tareda kallona,
“Farin cikina, Meye wannan? ”
Ya fada yana hasko min wayarshi, seda na tsura ido sannan na fahimci messages Ya shiga, bata rai nayi nace
“Me yasa ka shiga min messages, breach of privacy and trespassing ko? ”
Bata fuska yayi yace
“See this silly girl, me yasa baki fadamin Mupheeyda na miki irin texts dinnan, she sent one Ynxun naga pop dinshi, shi ne na shiga naga Sauran. Hikmah do you have to endure all this? ”
Story continues below

Dan Murmushi nayi nace
“Kasan I regretted exchanging words da ita ranar, ni Kaine zan aura ba ita ba so kaga banida wani case da ita, Ita taga wannan rayuwar Ko kuma yimin haka shi ne yafi mata. Banfa aureka ba so bazanyi fada akanka ba, Ko na aureka Bazan iya fada ba, banda wannan strength din. So Dan Allah ka manta da ita, tunda na yadda da aurennan, so just forget about her”
Yadda yake bina da kallo yasa nasan maganata ta shigeshi, Nifa da yadda na dauki kishiya Haka kowa ya dauketa may be da Zaa zauna lafiya, nasan as kuna zaune tare tabbas Zaa saba amma wannan ka zauna kuna fada Wasu Harda dambe ai an samu problem Babba kuwa.
“Hikmah I love you”
“I love you too”
Na mayar masa Ina dariya kasakasa, Hararata yayi yace
” Se na saita wannan bakin tukun zaki gane”
Zaro ido nayi nace
“To me nayi ni kuma? ”
Runtse idonshi Yayi sannan ya Mika min wayar yace
“Muje na kaiki park Ki tafi”
Kaina na gyada na wuce ciki, ban jima Ba na fito janye da karamar trolley. Shi ya karba ya saka cikin booth sannan ya bude min front seat tareda dukawa yace
“Always at your service Ma’am”
Dariya nayi na shiga, shima shiga Yayi nace
“Irin Gentleman dinnan ko?”
“Eh mana, nayi tunanin zaki kwashe kayanki duka, tunda next semester you moving out of empire”
“Ba Yanzun ba se Anyi auren tukun”
Harara ta yayi yace
“Kina abu Kamar ba kin fini daukin aurennan ba, kullum nasan addua kike na zama mijinki na baki honey”
Ya fada yana min wink, ihu na saki tareda rufe kunnena nace
“Karka lalatani”
Bai Kara cemin komai ba se dariya da ya dinga yi. Mun danyi nisa kadan zamu wuce wani Suya Hut yayi saurin parking tareda fadin
“Farin cikina Bari na karbo miki kaza, nasan kinajin yunwa”
Kallonshi nayi nace
“Se kace ni ce irinka, I’m not hungry Nidai sede Ko Kai Acici”
Rankwashi na yayi yace
“Yarinya bakiga komai ba, ina tason nace miki idan zaaje Jere please a rage miki warmers da tukunya a gida”
Cikin rashin fahimta nace
“For what? ”
Kanshi Ya shafa ya hade fuska a dole he’s serious yace
“Idan aka daura aure Kinsan ranar Zaa kaiki, so please ki dafa mana Rice and stew seki taho dashi, kinga basai min saya ba. Beb inason abinci”
Kasa magana ma nayi na dinga dariya Kamar zanyi me, har seda na Fara tari sannan nayi Shiru shima Abdallah ne yace min
“Farin Cikina, easy mana. Ynzun idan kika samu attack Ya zanyi. Ni banma ga abin dariya a Maganar nan ba, girki kawai zakiyi”
Kaina na girgiza nace
“A’a ka manta, lallai har wani na Fara maka girki, ai se Ayimin dariya”
“Ba wani dariya, umarni ne fa Kinsan ana daura aure na zama head”
Tabe Baki nayi nace
“Bossing me around! ”
Hararata yayi, Munata hira muna tafiya har ya kaini park sannan mukai sallama na shiga ya biya. Seda motar ta tashi sannan ya juya inajin Har na Fara missing inshi. Motar na tafiya na rufe idona, Abdallah na tayumin yawo cikin Kaina, Inasonshi kuma a kwannan abin yafi gaban magana, son nashi Yafi min zafi, inajinshi a ko ina na rayuwata.
Lokacinda na isa gida ban nufa gidan ba, Dan Mama tayi min text akan yan kawo Lefe sunan, gidan Anty Fadila na tafi, babu kowa na karba key data barmin gurin neighbors dinta. Tunda na shiga na kwanta a parlor Ina hutawa Abdallah kawai na fadawa na iso shima bamu wani jima Ba yayi min sallama zasu fita da Umar zancen events din Mupheeyda.
Sallamar Hamma Mussadiq naji hakan yasa nayi saurin tashi Ina gyara zaman scarf dina. Shigowa yayi hannunsa rikeda na Miemie, Tana ganina ta taho da gudu ta rungumeni, nima da murnata na ciro big bom na saka mata a baki.
“Yarki kadai kika gani Ko? ”
Gyara zamana nayi nace
“Oh Hamma Mussadiq Ina yini”
“Lafiya an gama exams lafiya? ”
“Alhamdulillah”
Na bashi amsa Ina sending message ma Nanah.
“Kinfi ganin dacewar Ki auri Wanda zai aureku ku biyu Hikmah?”
Dagowa nayi na kalleshi nace
“Ai Kaima Kanada Mata Hamma, kaga kaida Abdallah Tit for Tat ne. ”
“Amma Aini ina sonki kinsani ko? ”
“Shima yana sona Hamma, Dan Allah kayi hakuri ka bar Maganar Haka”
“Saboda me? ”
“Hamma Dan girman Allah I’ve gotten enough heart break, Kasan sanadinka na samu high BP Ko? Ko makiyina bansan ya dandani abinda naji so do me a favor ka rike matarka Dan Allah, kaga ni ba rasa mijin aure nayi ba, you’re confused bawai sona Kake ba tausayina kawai kakeyi”
Ina fadar Haka na Mike nayi cikin daki na tura kofar, maimakon nayi kuka se naji babu alamar hawaye se ma ji da nayi zuciyata ta zama very hard. Ina jinshi yana knocking nai masa banza seda ya gaji Ya tafi sannan na fito nayi gidanmu.
Koda na shiga duk an tattafi se tsiraru na jiki, Tundaga kofar parlon Aneeysa ke guda tana fadin
“Ta kusa ta kusa ta kusa, ta kusa dakko hula….. ”
Tureta nayi inajin wani weird feeling a jikina, Mama dake zaune ta tankwashe kafafunta ga akwatina an Jere su na lefen, kallo daya nayi nasan an narka kudi a cikinsu. Kanta na fada hade da rungumeta nace
“Mamata ta kaina”
Itama rungumeni tayi, Anty Muna ta tabe Baki da cewar
“Mun kusa ganin karshen karya dai ”
Dariya Mama tayo tace
“Bakwa gani ba, yan sa ido. Auta tashi kiga lefenki”
Bawai ina wani jin Kunyar Mama bane, haka na zauna aka kalla Inata yabawa daga karshe nayi masa text din godiya. Tabbas Lefe is a gift that meant to be a surprise!
Washegari aka Fara gyaran jiki, Mama nata complain an makara hakan yasa matar ta dawo gida baki daya da yaranta kowanne yana aikinshi, daga zaune ga shirin biki Wanda kullum ji nake kamar na gudu, idan Naga kudi Kamar na sata. Idan haka kowacce Amarya tayi aure to tabbas tayi kokari.
Saura kwana hudu Abdallah ya kirani, kwanakinnan Ko Yaya ya kirani ko na tuna shi se gabana ya fadi. Ina picking muka gaisa yace
“Farin Cikina, kinga Friends dina ne suka hada mana wani….. ”
Da sauri na katseshi da fadin
“Me? Badai wani event din ba. Wai ya Kake so nayi da raina ne? Yaushe na kammalla hada kan photographer, Me kunshi, Make up artist amma kana kawo zancen events. Sede kaje kai kadai”
Maimakon yaji haushi se cewa yayi
“Har nan Zamuzo da Mupheeydar ayi, Dan Allah kiyi hakuri Baby ”
“Don’t baby me, kaje da Mupheeyda tunda itama matarka ce. Ta Yaya kace da babu dinner, an saka and now Meye event din da? ”
“Tea Party ne fa, Haba Bebs kwana biu duk kin koyi rigima, komai fa da zakisa nayi order make up duk nai booking. Yours is only to attend”
Ajiyar zuciya na sauke nace
“Sure? ”
Da sauri yace
“100% sure my love”
Se naji a bit hankalina ya kwanta
Dariya yayi yace
“Allah barmin Hikmata… Uwargida sarautar mata. Sarka me rikicin gangan! “
Tea Party shi ne event na farko da muka farayi, shi ne ya kasance ranar Wednesday. Tun safe aka aiko min da outfit dina, Wata Kimolly gown ce ta wani rantsatsan Silver material, kasanshi black sequence ne. Ga komai accessories dina black. Ajewa nayi bayan na gama yabawa, a ranar akai min kunshina Yayi kyau Dan dawowata kenan na samu sakonshi. Karfen biyar na yamma muka tafi wajen make up wanda Yayi booking seda aka gama Allah Ya taimakeni period dina da safe yazo, Dama na dade ina wannan adduar yadda Bazan Je Ina missing sallah ba Har a kwashe albarkar auren ba. +
Misalin Karfe Takwas yazo daukata, friends dina Wanda rabinsu duk Yan ABU ne sunsha English gown dinsu, Sunyi kyau sosae abinsu. Sun fitar Dani kunya. Yana tsaye a jingine jikin wata black Benz, yana sanye da Grey tuxedo suit, yayi kyau naji tamkar na rungumeshi na nunawa duniya yadda nake jinshi a zuciyata. Tunda muka hada ido yake min Murmushi, haka na samu Kaina da Murmushi Wanda nakejin tamkar bakina zai yage saboda Murna. Shi ya bude min kofar na shiga, anan idanuna ya sauka akan Mupheeyda wadda ta hakimce ta baje. Tayi kyau babu karya kuma outfit dinta sak irin nawa, just that nata Baki ne sequence din ash. Sau daya ta kalleni ta maida kanta Kan wayar da take dannawa, seda na zauna sannan ya rufe ni ya koma gaba ya zauna, Umar ke driving. A ka’ida Wanda ya shiga guri shike sallama, nayi bata amsa min ba balle mu gaisa hakan yasa kowacce ta ja mutuncinta har mukaje wani Chinese restaurant anan akai Tea Party din saboda reserving gurin akai gaba daya. Mun sha hotuna, duk Wanda yazo daukar mu se nayi dariya because I was so and super excited, inajin Kamar wannan auren shi ne mabudin dukkan Wasu alkhairin rayuwata, dukda idan na Kalli Mupheeyda zuciyata bugawa take amma Ban Bari hakan Yayi clouding zuciyata ba, abinda ya zama dole Meye naka na fighting dinshi tamkar kana fighting da will din Allah kenan.
Ana kammalawa muka fito, I had lots of fun, abokansa are entertainers, sun bamu dariya sun sani farin ciki sosae. A cikin mota yace
“Hik zanyi dropping Mupheeyda ta kwana gurinki kafin zuwa gobe mu wuce kaduna”
Kafin na bashi amsa tace
“No, na rigada nayi booking hotel room, I’m spending the night there “
Baice komai ba muka cigaba da tafiya, seda muka ajeta a hotel din sannan muka tafi, shike driving ina gefenshi yana nuna min yadda wannan satin yakeda muhimmanci cikin rayuwa, a wannan lokacin Yayi min alkawari Wanda inhar da komai ya tabbata bana tunanin zanyi kunci a rayuwata, but Allah is the best and the most perfect planner. A Wasu lokutan idan ya hukunta abu a kanmu mukanji tamkar inama ba haka abin yake ba, kanajin dama Haka akai, amma later on se ka fahimci there’s reason and wisdom behind every will of Allah. Hakace ta faru dani.
Muna shiga gida naje na cire kayana nayi wanka sannan Nazo gaban window na tsaya, a hankali inajin yadda iska ke daddaga curtains din, Garin Yayi dadi ga damuna da bata gama sauka ba, inajin yan mata nata hayaniya kowa yana neman gurin da zai kwanta amma Ni tunani daya ke min yawo a raina, Friday Zaa daura min aure, ranar lahadi zan cika shekaru ashirin da uku a duniya, daidai shekaru ashirin da daya Dana aka sace ni kamar yadda Hamma Aiman yayi min bayani. I so long to see them, inason naji Yaya ‘Ya’ya sukeji gameda iyayensu, ban rasa komai ba amma duk lokacinda nayi sujadda Se nayi adduar reunion dinmu dasu.
Nayi zurfi sosae cikin tunani naji hannu ya tabani lokacin ruwan Sama me karfi ya Fara sauka, feshin shi ya bata min fuska da kayan dake jikina. Mama ce hakan yasa na kirkiro Murmushi nace
“Mama”
Kallona Tayi tareda rungumeni tace
“Zanyi kewar ki diyata, Allah Yayi miki albarka”
“Amin “
Na amsa inajin idanuna suna cikowa da kwalla. Dakin Hamma Mus’ab mukaje babu kowa a ciki, gefenta ta zaunar dani ta Fara min karatun aure
STORY CONTINUES BELOW
“Zainab! Kinsan Allah yace idan kayi aure mutum ya cika Rabin addininshi? Bakiyi mamaki ba? Ko daga wannan fadin Ya kamata kisan cewar aure abune me matukar girma, abune da yake bukatar juriya, hakuri da kuma dangana. Hikmah nasan bazaki bani kunya ba amma a matsayina ta mahaifiyar ki Yau Zan canja akalar yadda iyaye sukewa yayansu fada. Ni Uwa ce, ni mata ce nasan yadda aure yake, Abu ne me wuya Mussaman idan ka fada mummunan hannu. Muna cikin wata musiba ta yadda mata ke kashe mazajensu, saboda sun kaisu karshe bazasu iya jurewa ba, shiyasa nace miki mun yawaita a wuta, ga azabar miji a duniya gata Allah a lahira. Nasha ayyana cewar kamata yayi ace maza su suka yawaita a wuta ba mata ba, saboda su ke zaluntar mu, suna cutarmu, maimakon mu barsu da Allah Se mu saida imanin mu wajen bokaye, har takai ga kisa. A Yau nace miki idan Har kikaji bazaki iya hakuri akan mijinki ba ki dawo gida, Ki dawo mu zauna, da kije Ki tabe gwara ace kin kasa zaman aure. Ina miki addua ina miki fatan alkhairi a rayuwarki, Ki sani duk lokacinda kika kasa sarrafa Kanki, kikaji ya zakiyi ki tuna ni, zan zame miki kunnen da zai saurari kukanki. Se Abu na karshe nasan Kinada hakuri amma bakya daukar abu da sauki, komai a gurinki me zafi ne shiyasa kike shan wuya…. ” 1
In takaice muku ban taba jin nasiha irin wannan ba, kullum abinda ake nuna mana, dole kiyi zaman aure koda kasheki miji keyi, we’re in the era of female gender stigma, komai mukai we’re blamed, Baa duba me maza suke sede mata. Kinyi aure biyu Ance ta kasa zaman aure, se yayi aure goma yaje neman na sha daya a bashi, mijinki Ya mutu after iddah kince zakiyi aure, society bata duba sexual need dinki ba tace da yaushe mijin ya mutu? Shi bayan sati daya da rasuwar mata yace Zaiyi aure, society tayi backing dinshi. Kin kasa iya girki, Baki Shara Ance saketa ka auri wata, ko kuma ka Kara aure, kin kamashi red handed da mace on bed, kin nemi saki Ance kin kasa rufa asirin mijinki. We need to change, ke da kika fadi haka Kema mace ce, muma hallita ne, For me a woman is the most easy going creature in the universe, but if you mismanage her, you go see shege. 5
Tare muka kwana da ita, cikin dare na kalleta na shafata naji wani sanyi a raina, Allah shi ne abin godiya. Washegari mutane suka zo sosae musamman na Nesa, gidan Ya cika sosae, kawayena Wanda basu zo ba yawanci duk sun karaso. Ranar akai kamu a FABS dake Magajin rumfa. Lord nayi kyau, kamu akai na gargajiya hade da aladar mu ta Fulani, babu namiji Dan Ango Tun gurin me make up mukai hoto. Na dawo gida a matukar gajiye, babu abinda nake son nayi kamar bacci amma ina Abdallah bai bada wannan damar ba, bamu taba hira so much ba Kamar ranar, dukkan abinda yakeso da baya so seda yayi min narrating haka zalika Nima, a wannan Daren muka daura alkawarrika da Dama a rayuwarmu. Munyi alkawarin komai runtsi komai wuya muna mugun tare amma ina Allah yafi mu sanin gobe!
Washegari jumaa, jumaar da Bazan taba Mantawa ba, jumaar da komai ya Fara, Ya lalace ya kuma gyaru. *The Blessed Friday* Haka takenta yake a gurina. Tun safe masu Jere suka tafi Zaria, Tun safe ake gyaran jiki, kuma tunda aka Fara muke waya da Abdallah, na tsumu babu karya. Munata waya Har sha daya tayi nace yaje ya tafi Yayi wanka ya tafi massallaci kada yayi missing sallah Dan daurin auren Karfe uku ne na Yamma a Babban Masallacin Ibn Uthman Sahaba dake kundila. Daga nan mukai sallama, can wajen Karfe biyu na gama shiri cikin wani farin rantsatsan lace Yayi min kyau abinka da bakar mace, fuskata all dolled up. Nayi kyau anata hotuna Dani wayata Nanah ta mikon tareda fadin
“Ango na kira”
Ganin sunanshi yasa gabana Yayi wani irin bugawa, se naji Kamar ana zare min duk wani kuzarina amma a hakan na kara a Kunne nace
“Galaxy”
Murmushi yayi yace
“Farin cikina, na tashi a massallaci Zanje na canja kaya, mu tafi gurin daurin aure, I can’t wait ki zama tawa”
Cikeda jin dadi nace
“Awnnnnnn same”
Har ya kashe ya Kara kira yace
“Ki sani whatever the outcome ina sonki, Ina kaunar ki and I longed to have you as my wife”
Bai jira nace komai ba ya kashe wayar, se naji tamkar ya tafi da dukkan wani Sauran Hikma yabar Zainab a tsaye. Yadda nayi Shiru yasa muka koma ciki na wuce dakin Hamma Mus’ab na kwanta ba tareda sanin kowa ba, inajin yadda jikina ke rawa gabana nata faduwa, komai was beyond na fada.
Karfe uku dukkan Wanda ya kamata yaje gurin daurin auren ya hallara, banda Ango da waliyyansa. Tun ana jira cikin dadin rai Har mutane suka Fara kosawa, Baffa nata duba agogon hannunshi Tareda kallon kofa with the hope cewar Ango zasu shigo amma ina babu shi babu dalilinsu. Har hankalin mutane ya Fara tashi.
“Baffa ka kira Mahaifinshi kaji mana, mutane nada nasu uzurin munzo mun tsaidasu, AI wannan wulakanci ne”
Baffa tuni ya cire babbar riga ya mikawa Hamma Mus’ab, wayarshi ya ciro Sega kiran VC yana shigowa hannunshi har karkarwa yake wajen picking call din, sede baice komai ba wayar ta zame daga kunnenshi ta fadi ta tarwatse, banda Innalillahi wa Inna ilahil rajiun! Babu abinda yake maimaitawa, Aiman ne ya taho yana fadin
“Baffa me yace? “
Lumshe idonshi Yayi sannan ya bude tuni sun kada Sunyi jawur yace
“Sunce idan ta samu miji tayi aure”
Dif gurin yayi, atmosphere very tensed, Shiru bansan saukar numfashi, karar AC da fans babu komai. Bayan wajen 2 minutes gurin Ya kaure da hayaniya a take Hamma Mussadiq yace 1
“Baffa a daura mana aure da ita!”
*MAIDUGURI* +
Hafsa na zaune parlon Mom Tana shan Tea dukda zafin da ake amma ta maidashi routine, a cewarta gwara ta dinga shan hot Tea after kowanne meal ko ta samu tadan rage kibar da takeyi. Kuma a zahiri ba wata kibar Tashin hankali bace, kawai dai kana kallonta Kasan babu alamar wahala Ko Tashin hankali. Salima ce ta shigo hannunta rikeda waya Se bubbude nostrils take saboda yadda parlon yake kamshin abincin da Hafsa ta gama ci, Kamar Ance ta juya side din dining yake Abinci ne cikin warmers an cika table din dashi, cikin sauri Tayi wajen amma kafin ta kai tuntuni Hafsa ta rigata, ture ta ta shiga yi tana fadin
“Meye Haka wai ke Salima? “
Kai Salima ta dafe dawowata kenan daga Lagos, wata iriyar Yunwa takeji Kamar ana kwakular Hanjin cikinta, amma wannan wicked witch din bazata barta tayi tasting ba. Marairaicewa tayi tana fadin
“Haba In-law plate daya kawai wallahi Yunwa nakeji”
“Zancen banza kenan, kije main kitchen Anyi Abinci kici”
Bata rai Salima tayi tace
“Yanzun Inlaw bazaki bani ba, ko Yaya Aminu kika dafawa”
Kai Hafsa ta girgiza ta aje cup din hannunta tace
“Ba nashi bane ba, Kinsan ki hakura kawai”
Tsaki Salima tayi ta Bangaje Hafsa ta bude warmer daya seda yawunta ya kusan zuba cikin gurin. Daman tafi Hafsa kiba gashi sun girma amma wannan childish play din basu daina ba Har lokacin. Hafsa kanta ta girgiza tace
“Allah Ya isa”
Nafisa da Umaima dake parlon suka kwashe da dariya, Mom tace
“Allah Ya isa dai ta rago ce”
Salima na gama diba ta nufi dakin Hafsa Tana fadin
“In-law taho gist dey”
Ai da wurwuri suka fada kurya suna kulle kullensu Kamar yadda suka saba. Suna idar da Sallar Maghrib Hafsa na kan sallayar da tayi sallah tana lazumi, Salima na kan stool din dressing mirror tana instagramming ta hangame Baki tace
“Inlaw zo kiga wani Tea Party, wani yaro ya auri mata biyu Rana daya.”
Kafin Hafsa ta karba wayar taji ihun Nasiba yarinyar Ammar tana ihun
“Yaya Maina oyoyo!”
Da sauri Hafsa ta Mike tayi waje yayinda Salima ta sake baki Tana tunani, a ranta ta Ayyana Dama abincin Maina ne Hafsa ke hanata dauka, no wonder! Murmushi tayi tana ayyana soyayyar da Hafsa kewa Maina. Fita Tayi sukai karo dasu suna shigowa. Daga kofar bedroom din ta tsura mishi idanu tana ganin yadda yaron nata ke Kara girma, shekaru suna Hawa kanshi, a ranta ta ayyana inama yana da aure he would have been completely a man. Hannunta taji ya riko fuskarshi a sake yace
“Ammiey ta, surprise right? “
Bayanshi ta buga tace
“Really, banyi tunanin dawowarka ba, no wonder waccan wicked witch din keta aiki Tun safe “
Dariya yayi dan yasan dawa take. Zama yayi gefen Mom tareda kwantar da kafadarshi yace
“Mom yimin massage”
Ture kanshi Tayi tace
“Uwarka Hafsa ita zata maka massage, kaga da kayi aure basai kayi requesting massage ba. Da kanta za tayi maka”
Mikewa yayi yana dariya yace
“Ma, lemme take a shower, Nazo naci tasty dishes dinki”
Kanta ta gyada ya fice, seda ya leka Dada, Ummiey da Anty Yana sannan ya wuce yayi wankan.
STORY CONTINUES BELOW
Dukkansu suna parlor banda jikokin se Maina shi daya acan gefe yana kwasar Abinci. Hafsa na zaune a tare, kalla wayarta tayi tace
“Takwas Har tayi amma har Yanzun mutanen Kano Shiru”
Se lokacin Ummiey tace
“Aikuwa dai Maman Maina, Bari na kira Alhaji naji lafiya”
Amina matar Mubarak tace
“Kede Kice Hubby bai dawo ba, hankali yayi gaba”
Yadda ta fada kasakasa Hafsa da Salima kadai suka ji, kafin Hafsa ta bata martani se sukaji sallamar su Alhaji, cikin rada Hafsa tace da Salima
“In-law sallamar Yayanki tasa zuciyata melting”
Tsaki Salima tayi tace
“ke kam kin shiga uku”
Dariya sukai anata gaisawa tareda musu barka da dawowa, Dada da Hafsa suka kwaso Abinci aka jera kan dining mat dake malale a kasa, duk lokacinda aka hadu da yawa to Tare suke cin Abinci, dama Sunyi sallah kafin su shigo hakan yasa suka ci Abinci, suka gama aka daura da hira, Alhaji Nafi’u ya Kalli Hafsa yace
“ke da tuni An kashe Bakinki, Yau Aminu Yayi aure”
A zabure Hafsa tace
“kai Yaya Nafi’u wannan ba wasa bane wallahi, Alhaji kana ji ko? “
Ta fada tana bata rai, kowa seda yayi dariya a parlon Alhajin sama yace
“Hafsa kira min Danki, we have an issue dashi”
Mikewa tayi ta nufi dakin Maina, yana zaune kan Sofa Ya lumshe idonshi, yana jin sallamarta ya bude idanunshi yace
“MA”
Kallonshi tayi sannan tace
“You seems in a good mood yau, Meye sirrin”
Mikewa yayi yace
“MA, kawai tunda satin nan ya kama nake cikin farin ciki”
Kanta ta gyada Tana murmushin itama tace
“To Allah yasa alkhairi. Muje Alhaji na magana”
Mikewa yayi yabi bayanta yana ta bata labarin Russia, Mussaman sanyin Garin, suna shiga parlon ya samu guri ya zauna bayan Ya gaishesu, kowa na tambayar yadda karatun ya kasance tareda fatan samun nasara.
“Yau Kamar yadda kuka sani naje Kano, sede zuciyata ta tabu Munyi wani abu Wanda bansan yazan kirashi ba amma dai nasan will din Allah ne. Bayan Munje gaisuwa, muka tafi Sahaba masjid dan kaiwa Abokina ziyara, muna zaune yake ce mana Yanzun Zaa daura aure gurin, kafin wani lokaci an taru Dan daura auren, muna ciki a zaune, bansan me ya zaunar damu ba amma nafi tunanin rabo ne, Allah Yayi rabonmu ce”
Gyara zama Hafsa tayi Dan Bata fahimtar abinda Alhaji ke fada, Meye hadinsu da wannan Maganar
“Seda kowa ya taru amma Ango da shakikansa basu zo ba, daga karshe se suka Kira sukace sun fasa…..”
“Sun fasa? Innalillahi wa Inna ilahil rajiun! “
Ummiey ta fada, gaba daya parlon kowa Yayi Shiru kada Maina yaji labari, Dan Haka kurum yake jin Wasu irin uneasiness na mamaye shi , tareda faduwar gaba da baisan ta mecece ba.
“…..Abu biyu na tuna yadda mahaiyarta da kuma yarinyar, bayan nazarin da nayi na bada sadaki aka daura auren da jikana da nake jin na isa dashi aurenta. Wato kai Ibrahim Maina”
Kowa seda ya firgita tareda kallon Alhaji Mussaman matan, Maina Yayi Shiru Yana jin wani abu yana mishi yawo cikin jikinshi, tamkar an zare mishi laka haka yaji baya tareda kowanne guzari, kasa cewa komai Yayi Se istigfari da yake yi saboda baisan ya ayyana cewar Baa kyauta masa ba. Hafsa ce ta bude baki zatayi magana, Alhaji yace
STORY CONTINUES BELOW
“Kar na sake naji Bakinki, aure an rigada an daura, Babanta yace a bashi sati daya Zaiyi magana Se Kuje Ku ganta. But gaba dayanmu munji tamkar abinmu muka karbo. Maina Allah Yayi maka albarka”
“Amin”
Ya amsa kanshi a kasa, addua akai kowanne da nashi tunanin Haka kowa ya nemi makwanci, duk yadda Hafsa taso ganin Maina hakan bai yiwu ba saboda Alhaji Bukar na tsaye seda Hafsa ta tafi sannan ya tafi, ita tayi farin ciki ba kuma opposing zatai ba Kamar yadda suke tunani A’a, he surely needs someone Dazai lallashe shi amma tana shiga daki ta kirashi, yana dauka tace
“Son, are you ok”
Dan Murmushi ya saki yacr
“Babu komai MA, Munyi adduar Zabin alkhairi gashi Allah Ya zaba, to ai bazanyi jayayya ba. Allah ka tabbatar mana da alkhairi”
Cikeda jin dadi Hafsa ta dinga saka mishi albarka. Tana zaune Aminu Ya shigo jikinsa daga shi se singlet da short, gefenta ya zauna tareda riko ta yace
“I’m nervous Hubby”
Matsa hannunshi Tayi dake cikin nata tace
“Duk auren Mainan ne? “
Kai ya girgiza yace
“Ko daya, ni naji dadin hakan wallahi. But tunda muka shiga Kano nake jin kamar wani abu da yayi nisa Dani zai dawo gareni, na rasa Wanne irin unusual feeling ne hakan. “
Murmushi Hafsa tayi tana shafa kanshi tace
“Relax Dear, Bari na hado maka tea”
Kai ya gyada mata, ita kuma ta fice daga cikin dakin.
Bangarena tunda na shiga side din Hamma Mus’ab ban fito ba, sede lokaci zuwa lokaci Ina duba wayata ko text din Abdallah zai shigo cewar na zama matarshi Kamar yadda nake karantawa cikin novels. Amma har hudu tayi babu wannan text Ko kira,
A hankali naji tsoro ya Fara shigata saboda gidan ba Kamar gidan biki ba, is too quite than usua. Cikin gida Mama ana ta nemana ni kuwa Ina kwance Abuna kuma babu Wanda Yayi tunanin kirana. Har Karfe biyar babu wani Amo bare labari, nasan dole idan aka daura auren ai zaixo muyi hoto, to Kodai Abdallah ya mutu ne? Ko accident Yayi? Na ayyana hakan, babu shiri Na tashi daga kwance da nake na fito parlor, nan mukai kicibis da Hamma Mus’ab, ko a fuskarshi zakaga yana cikin damuwa amma ina ban lura ba saboda banma niyyar masa magana ba seda ya riko hannuna sannan na dago na kalleshi, hijabi ya Mika min yace
“Saka “
Daurin kaina na tuje na saka, muryarshi was so pitiful, Karo na farko da yayi min magana a Haka, Ina sakawa ya ja hannuna muka fita ta kofar baya, Nidai nasan tabbas babu lafiya amma saboda tsoron kunnena kada suji abinda zaisa zuciyata bugawa na kasa tambaya. Can gefe ya bude motarshi seda na shiga sannan ya zagayo ya shiga tareda fuzgar motar Yayi gidanshi, tare muka shiga ciki yace
“Zauna ina zuwa”
Yana fadar Haka ya fice a gaggauce. Shiru nayi Inata sake sake a raina, me ya faru? Menene matsayina, runtse idanuna nayi tareda kwantar da kaina a saman cushion ina jin yadda yanayin jikina ya canja. Bansan mintina nawa nayi a Haka ba se naji sallamar duk Yan gidanmu, Baffa, Mama, Hamma Musbahu, Hamma Mussadiq, Hamma Mustapha da Hamma Mus’ab. Se kannen Baffa su uku. Ina kallon fuskar Mama naji hawaye ya Fara sauka saboda Ko Baa fada min ba, I’m sure kuka take. Abinka da fari fuskarnan tayi pink. Babu Wanda yace ko na daina kuka, ko nayi Shiru babu, Illa kallon kallo da akeyi. Baffa ya dubeni yace
“Zainab, banida Baki Ko wani kalma da zan Baki hakuri da ita. Kince na mayarwa Abdallah kudin aurensu amma na sakaki dole se kin aureshi. Nasan da ban tursasa ki ba da banga wannan ranar ba”
Hawaye na sauka min Kan fuska nace
“Baffa ka daina fadar Haka, saboda ka isa ne shiyasa, ka isa Dani. Baffa ka fadamin Abdallah ya rasu ne? “
Kai Baffa ya girgiza yace
“Naso mutuwa Yayi da tozarcin da akai min, ya kirani yace kiyi aurenki ya fasa! “
Dif hawayen ya dauke
_Ki sani whatever the outcome ina sonki and I longed to have you as my wife_
Shi ne Maganar shi ta karshe gareni, Haka ta dinga zagaya min kwakwalwata amma abinda Baffa ya fada next shi yafi komai tarwatsani
“Wani bawan Allah a gurin Ya bada sadaki na aurawa jikanshi ke…. ” 4
AI tuni na Fara kuka wannan karan ba hawaye ba, kuka sosae ina fadin
“Baffa me yasa, Da da yace bazai aureni ba, da ka bari a hankali wani zaizo am…… “
Muryata gaba daya ta shake, kowa a parlon Yayi Shiru Banda Baffa dake ta rarrashina.