KANDALA CHAPTER 8

KANDALA







CHAPTER 8






Toh bari na karanta miki kur’ani cikin murya mai tausa zuciya yafara karantawa….

” kallonsa take tayi lallai akwai bayin Allah aduniya ahankali tace to bazakaje gurin aikin kaba?

” wallahi bazan iya zuwa ba ganina akusa dake shine kwannciyar hankali na ko da na tafi tunanin ki zan dinga yi…..

” toh cigaba dayimun karatun ahaka bacci ya kwasheta….

” Abdul ke faman kallonta ayayin daya fahimce tayi bacci rufe kur’anin yayi ya nufe gidan sa…

” Har kadawo kenan?

” ba dake mukayi zakizo ki dubata ba?

” kayi hakuri sai zuwa gobe yau banason fitane…

    ” tsaki yayi yace ai yayi miki kyau…

     ” kawai kaje ka makalewa wata yarinya ba maharramar ka ba wai kai jinya adinga tunawa da Allah dai….

       ” ke Narasa irin jahilcinki wallahi….h

    ” Ai dama haka jakace nan ‘yarka batada lafiya ka tsalleki mu kayi tafiya, yanzu gawata bare can kama ajiye aikinka saboda ita…

     ” hmm Nusaiba kenan yakamata aci kinfi kowa fahimtar halina ayanzu! Kafin natafi ai dai nakaita asubuti wannan kuma sunanta humaira bansanta ba nazo Na bugeta ko ke ai kayimun fada Natsaya nakula da ‘yar mutane…

      ” haha wai kai mai tausayi ai sai kayi tayi…

     ” Dak’insa ya shiga ya dakko wasu sababbun kaya dogayan riguna ya huce asubutin…

   ” mame ce ta sakata agaba sai tambayoyi takeyi mata tambayar karshe tasa kande kuka..

      ” haba ‘yata kidaina kuka mana daga tambaya?

    ” cikin kuka tace Ne bansan inane garin mu ba in Allah yabani lafiya zan tabi ko’ina ne…

     ” aikuwa baza’ayi haka ba ki kwantar da Hankalinki kinje? Ki kuma d’aukeni amatsayin uwa kinje? Zan kula dake har ranar da yan uwanki zasu Nemi k’i…

     ” Hawayen da suka karasa sakkowa a fuskarta ta goge tace Nagode da irin karamci da tausayawar dakuka nunamin….

     ” ki daina godiya ‘yata ke godewa Allah daya jarraba miki wannan kaddara….

    ” har acikin ranta taje Dadin maganganun mamee hakan yasa ta saki jiki dasu ta kuma godewa Allah dayasa ta fada hannu nagari…

    ” Yanzu me kikeso Na dafa miki?

     ” Cikin sarkakkiyar murya tace duk Abunda kika dafamun mamee…

     ” Haba ‘yata Nace miki kidaina jin kunya wallahi Ne tamkar mum dinki zan zame miki….

    ” kande cikin ranta tace Ai sai dai tamkar iya habu domin tafi goggo sona…

   ” A hankali mamee ta rik’e hannun ta ki gayan abunda kike bukata ‘yata…

     ” Macaroni nakeso da salad…

     ” Tohm karbe wayata ko zakiyi game bari naje Nadawo….

     ” Kande ta karba tafara game bayan fitar mamee abdul yashigo fuskarsa ciki da fara…

    ” sai Da ya kalleta up and down yadda yaga tanata walwalah sannan yace my humaira?A hankali ta dago kanta tace shine ka gudu nace kayimun karatu ko? +

    ” yi hakuri toh bazan kara guduwa ba, ga kaya in mamee tazo sai ta canja miki…

     ” Tohm, ya baka kawomin minal da minat ba?

   ” karki damu zasuzo tare da mum dinsu, yanzu yaya kafartaki Naga ciwo k’an naki duk sun warke!..

    ” Eh yanzu ina iya motsa kafata Ne wallahi Nagaji da zaman nan….

     ” karki damu Nan da 2weeks zaki taka…

    ” Acikin ranta tace Allah yasa…

     ” my humairat yayanki nawa?

     ” cikin rashin son tambayar tace 3 ne duk maza sai kanwata sadiya….

      ” A’hh kice ke kande ce?

   ” bata ranta tayi tace banson sunan nan..

    ” murmushi yayi yace ai kuwa dole kiso domin acikin maza aka haifeki…

   ” hawaye ne yafara bin fuskarta…

    ” stop it ke dakike da sunan yan gayu babban suna humairat…

    ” Kallonsa takeyi yanayin nutsuwarsa tana burgeshi amma har yanzu bai kai ya haruna ba…

  ” shekarar ki Nawa?

      ” shekarata 20 babu wata 5 
  
” kice ke yarinya ce wanne uni kikeyi?

     ” ban faraba.. Ne kadamine bacci zanyi…

   ” Am sorry my humairat kwanta kiyi bacci tohm…

     ” cikin k’in kina tace Ne kadaina kallona to…

    ” murmushi yayi yace toh….

Birni

    Abu ya faskara gidan kullum rikeci da kananan magana haruna kullum ciwon kai ga firdausi ta saka shi agaba wasu shiga da takeyi kansa kullum  a k’ulle…

     ” firdausi ce azaune tana faman kada kafa ta saka wasu english wears riga da wando…

     ” mama farida ce ta sakko daga bene shigar da firdausi tayi ya sata tsayawa cikin bacin rai tace firdausi…

     ” daga kanta tayi tace Naam ya akayi?

      ” Wannan wacce irin shiga ce?

     ” me kuma shigata tayi, i think Nan gidan ubana ne i have the right nayi duk abunda naga is right for me….

    ” Mama farida tace Has i said it kudinga jin tsoron Allah wannan shigar babu abunda zai jawo muku sai fitana gidan nan akwai maza ku kama kanku sai Allah ya baku miji wannan shigar bazata saka so azuciyar haruna ba…

     ” Toh ne nagaya miki haruna nayiwa toh shima nayiwa sai me? Kije kiyiwa jahilai wanda basuda ilimi….

    ” kuje kuyi tayi duniya ce…

    Bayan haruna yayi wanka Nafila yayi sannan ya tsaya yayi sallar azahar sannan ya shiga kasuwa kaya ya rarraba kayansa a hankali ya huce office babu abunda yakeyi sai juya kujera wayansa ya kunna atake yakira d.p.o wai yanaje shiru ne?

     ” Haruna muna ta iya kokarin mu soonest muna fata za’a ganta inshaa Allah kudai kudinga yawan addu’a…

  ” munayi kuma zamu cigaba, yana karasa aikinsa ya huce gida wanka yayi ya zauna ya rike kur’ani a hannun sa bayan yagama karatun ya ajiye…

    ” Assalamu Alaikum yaya?

    ” wa’alaikis salam firdausi ya akayi?

     ” cikin Rangwada ta’isu inda yake zama tayi abakin gado kada idanuwanta tafarayi sannan tace wai har yanzu babu labarin kande ne?Kallon ta yafarayi yace eh wallahi kinga har na rame… +

       ”  wallahi Nema abun yafara damuna, Amma ni banga wata ramarka ba, Anya kuwa kande ba guduwa tayi ba?

    ” Shiru yayi sannan yace bazata taba guduwa ba…

     “Hmm haka dai kace good night…

      ” dauke kansa yayi yace gud nyt sai data fita sannan ya miki yayi sallah tare da Addu’ar Allah ya bayyanata…

     ” Dady kuwa kullum cikin neman kande yakeyi har yakai yanzu yafara sanar da malaman makarantar Allo domin a tayasu da Addu’a…

Abuja

  Ummi ummi fito kije labari mai dadi..

     ” maryam wannan wane irin kirane?

     ” kiyi juyi kiyi tsalle kande ta bata an nemita an rasa fa…

    ” idiot cewar abi ku wanne irin mutane ne kanwarku ce fa…

     ” Ne ba kanwata bace ba wannan jahilar yar talakawa…

    ” wanka mata mari yayi nikike gayawa haka ko dayake uwarku ce ta daure muku gindi toh wallahi akan maganar kande sai na sabawa kowa….

     ” ummi da yake tasan halin abi cikin kissa tace ke maryam banason sha shanci yar uwarku ce fa…

     ” Kuka ta saka sannan ta huce sama…

    ” ke kuma saura ke wallahi kiyi hankali dani…

     ” bayan fitarsa tace Naga ta inda zaka shigo indai ina raye hamza bazai taba auren kande ba ayi mugane….

Kauye

     iya habu kiyiwa Allah karkije birni inshaa Allahu za’aganta….

     ” kai Aliyu shiga tattayin ka banason hauka wannan ai iskanci ne ina haruna daba zaije ya dubota ba ahaba so sukeyi su kasheta hankalinsu ya kwanta!…

    ” Aliyu ne ya tsugunna karki damu iya kande bazata mutu ba har sai kwanan ta ya kare kuma kiyi fatan b’atan Datayi yazama Alheri…..

      ” kuka ta saka tace yaya kakeso nayi aliyu goggo batasan darajar yarta ba ‘ ya mace ce fa yanzu kowanne hali take?

    ” inshaa Allahu tana cikin koshin lafiya kuma nayi miki Alkawarin zanje birnin gobe zanje halin da ake ciki…

       ” Tohm na amince kakuma sanar da hassan wallahi haduwar mu bazatayi kyau ba indai bai nemomin kande ba…

     ” zangaya masa tashi naraka ki gida to…

    ” goggo ce tace har karakata wallahi iyah tafiye meta…

      ” Aliyu ne ya zauna kusa da’ita yace gaskiya goggo baki nuna damuwarki akan kande!…

     ” Aliyu kenan haka kuke gani wallahi kullum addu’a nakeyi kuma inata yin sadaka karfa ku manta kande ‘yata ce….

     ” Toh Allah dai ya Amsa mana ya bayyanata….

    Birni

     Brox hamza lafiya tun dazu kayi shiru?

     ” wane kallo ya watsa mata sannan yace tunani na bazai huce halin da masoyi yata take ciki a yanzu ba idan Na rufe idona ita kawai nake gani….

    ” mtsewww son maso wane kakeyi, Ne bantaba ganin inda ake wannan abu ba kande fa bata sonka kuma kasan mutane dayawa sun riga ka…..

     ” shoutup malama in bazakiyi Addu’a ba To kiyimin shiru kizuba mana ido….

      ” yi hakuri dear banyi haka dan nabata maka rai ba….

     ” Dakko min lemo afrige, mikewa tayi tanata iya yee…

    ” Tsaki hamza yayi yace kiyi duk wata rangwada ba sonki zanyi ba…

      ” Farida tace wallahi kayi da ‘yar halak sai kazo da kafafuwan ka neman soyayya ta ne kuma A lokacin kuma nariga nafi karfin ka….

     ” hamza ne yace see this mummu, ke zanso? Aikuwa kana cikin hauka, ita soyayya daya ce kauna ma daya anayi da mutane da ya dace…

      ” kuka tafashi dashi ta shiga dak’insu….

Kowa sai cigiya kande yakeyi a makaranta yau malam jabir ya tambaya ‘yan aji ko lafiya kande…

    ” Anan kowa yace bai saniba…

     ” Toh muna fata lafiya..

    Bayan fitarsa mlm umar ya shigo kamar yadda ya saba yauma tambaya ce amma ga mutum daya fatima idress inaso ki kawo mana hadisin dake magana Akan falalar kiran sallah….

    ” Assalamu alaikum acikin hadisi mai numba 614 cikin bukari
An karbo daga Jabir bn Abdullahi Allah ya qara yarda a gareshi cewa Annabi SAW yace:  Duk wanda yace yayin da yaji kiran sallah: *ALLÃHUMMA RABBA HÃZIHID DA’AWATIT TÃMMATI WASSALÃTIL QA’IMATI, ÃTI MUHAMMADAN ALWASEELAH WAL-FADHEELAH, WAB-ASHU MAQAMAN MAHMUDAN ALLAZY WA-ADTAHU* to cetona ya zazartu/tabbata a gareshi ranar alqiyama ….. +

Wato wannan addu’a na sanya bawa cikin ceton Manzon Allah SAW ana so mu ringa yin wannan addu’ar bayan mun amsa kiran sallah mun yi salatin Annabi SAW sai mu karanta ita wannan addu’ar sai kuma mu roqi Allah buqatunmu….

   Barakallahu fiyki Anan zamu tsaya, fatima kije gidansu Aisha kuje lafiya bata zuwa….

    ” Tohm inshaa Allah..

Jigawa..

    Yau sati Na hudu kenan kullum su mamee suna zirga zirgar asubuti, har sun bawa kande wata sandar koyan tafiya yauma kamar kullum mamee na ruke da ita a bayan asubutin tana dan tattakawa…

     ” mamee nagaji fah..

    ” ‘yata daure kikai can sai kihuta…

     ” kande ke kallon ta ciki da kauna dama bazata rabu da mamee ba…

    ” a hankali ta rungumota suka karasa gurin wata chair suka zauna…

    ” sannu ‘yata bari na dakko miki fruit a dak’in namu…

    ” Tohm, shiru ne yafara isar kande a hankali ta miki amma ina kokarin wad’uwa takeyi kuka ta saka Nan da nan idunta ya k’ada…

    ” abdul ne cikin sallama ya iso inda take a hankali yace my humaira…

    ” tana daga idonta yaga yayi jajir ga wane sabon hawaye yana bin kwancinta….

    ” my humaira please Don’t cry for your loss Allah won’t take any thing from a believer without replacing it with something better,
Allah said in the Qur’aan, “Perhaps you may dislike something which is good for you, and like something which is bad for you. Allah knows and you do not.” (2:216)….

  ” kalaman sane sukayi tasiri a zuciyar ta sai kuwa tatafi luuu zata wad’i…

    ” Hannun ta ya ruko sannan ya zaunar da’ita a kujerar kusa dasu….

    ” kallonsa kawai takeyi da jajayen idunta da hawaye bai daina zubo mata ba…

    ” kiyi hakuri my humairat Na rike hannun ki Naga zaki Wad’e ne….

      ” hannun ta tasaka ta goge hawayen fuskar ta…

      ” har cikin ransa yana jin tausayin humaira gashi taki tasanar dashi komai akanta ga zuciyar sa tana saka masa wasu abubuwa….

      ” a hankali cikin sanyin murya tace kaifa kace nadaina tunani mey isa kai kakeyi….

    ” cikin murmushi yace tunanin ki nakeyi…..Hannun ta tasaka ta goge hawayen fuskar ta… +

      ” har cikin ransa yana jin tausayin humaira gashi taki tasanar dashi komai akanta ga zuciyar sa tana saka masa wasu abubuwa….

      ” a hankali cikin sanyin murya tace kaifa kace nadaina tunani mey isa kai kakeyi….

    ” cikin murmushi yace tunanin ki nakeyi…..

” Tunani kuma? Ku Dan nazama gurguwa?…

    ” Subhanallahi my humairat wacce irin magana ce wannan….

      ” kuka tasaka masa sannan tace duk su suka jawomin kafin takarasa kuka yace karfinta…

      ” Sakkowa yayi kasan grass din yana kallonta haba my humairat nace miki kidaina kuka! Kuma ke ba gurguwa bace ba kafarki tana lafiya kalou kuma ko su wanene suka jawo miki Allah yariga ya kaddara ne…belive me i will also be there for u…..

     ” kallonsa tayi tace are u sure?

     ” yes i am, kinsan me za’ayi yanzu ki daina damuwa da komai ki daina kuka Ni kuma zanta baki labari kalakala….

      ” Toh inshaa Allahu, mamee ce tace ashi kazo yau ma bazakaje gurin aikin baniba?

    ” kashe mata ido yayi mamee har naji nagama duk abunda zanyi shine natawo nan….

    ” cikin halin girma mamee takalli kande ina fatan abdul baya damunki…

    ” dariya tayi tace mamee ya zaayi ya dameni?

     ” ah bakisan abdul ba kenan ballantana jinin ku ya hadu wataran dakanki zaki koresa….

     ” dariya yayi yace wai haka my humairat zaki koreni?

     ” murmushi tayi tace Ne naisah, ai in kowa yakoreka ni bazan koreka ba….

     ” hahaha to mamee kinje dai abunda tace ko?

     ” kwaji dashi ruke kande tayi shuka shiga asubuti Nan tayi Alwala ta kuma karanta alkur’ani tare da adduar Allah ya kwantarwa da iya habu hankali akan batan ta…..

      ” mamee tace ‘yata na zubo miki macronin?

   ” A’a sai yaya abdul yazo shima zaice sai yazuba mana….

  ” Lahhh abdul kuma? Shikenan yafara siyi ki! 

     ” kafin mamee ta rufe baki sai gashi ya shigo riki da ledojin ice cream ahannun sa….

     ” sannu my humairat bari na zuba miki abinci kice….

      ” toh ai kaima bakace ba tun safe babu abunda kace….

      ” Ai ne nakoshi ne, agabana su meenat sukace sha tea ni nafeson abinci shiyasa….

     ” To in baka zuba kace ba nima bazanci ba….

      ” sauri yayi ya zuba mata sannan ya dau nasa, Ai ko duka kikace nacinye sai nacinye…. 1

      ” mamee tayi dariya tace kudai kunfiye abun dariya, dazu matar mukhtar ta kirani tana hanya zuwa dubi ya…

    ” abdul yace Allah sarki su anty bazasu zo ba?

     ” suma suna tafi sunci mota guda zasuyi kasan cameeron banan baniba….

     ” dariya yayi cikin tsokana yace Allah yaso su da duk wanda bai zi ba bazan kara kulasa ba….
     ” Nan taje babu dadi dama da hali ta gudu kauye! sai kuma ta tuna zafa a iya komar daita birni…..

” murmushi yayi yace my humairat ai na hanaki wannan tunanin….

     ” kallonsa tayi tace toh ai Nadaina yi! In tambayi ka yaya abdul….

     ” inajinki my humairat, Allah yasa nasani yasa kuma balaifi nayi miki ba….

     ” Me isa Anty Nasiba batazo ba kuma kace zaka kawomin su meenal ba?

    ” diris yayi ya kuma fara tunanin sa’insan da sukeyi da Nasiba…

     ” ya kayi shiru ko tambayar batayi maka dadi bani?

     ” Nop kinsan me? Anjima dasu zan tawo kikwantar da hankalinki….

     ” mamee kinje dai yayimin alkawari ko? +

      ” Naji Dan haka abdul sai ka cika mata…

    ” I-S-A Ke dai karki damu kuma kicire komai Aranki…

      ” Tohm bari nadan kwanta…

     ” mamee ta rike baki ohh ne Ina jiyi muku irin wannan shakuwar da kukeyi…

    ” Duk’an su sukayi luff babu wanda yace mata uffan….
   
  Birni..

Tun lokacin da malam umar yasanar da fatima Akan taje taji lafiya kande kwana biyu? Hucewa tayi stright har gidan su tana zuwa ta samu mama farida a palour tanata gyarawa, cikin ladabi tace ina yini mama?

    ” har cikin ranta taji dadin sunan sai cewa tayi lafiya lou kuna lpya naganki kamar da kayan makaranta?

    ” lpylou wallahi kwana biyu ne mukaji Aisha shiru ko lafiya?

    ” ta gyara tsayuwarta to agaskiya ba lafiya ba domin kuwa yau kusan sati na 5 zamu shiga da b’atan Aisha ba’asan inda ta shiga ba!…

    ” fatima ce ta zaro idanunta tare da fadin innalilahi Allah ubangiji ya bayyanata….

     ” Ameen ‘yar nan…

       ” to sai anjima Allah kuma yajiyar damu Alheri…

    ” Ameen cewar mama farida dady ne ya fito lafiya kike magana?

   ” wallahi alhaji abun yafara bani mamaki batan kande yanzu kawayenta sunkai 5 sai zuwa sukeyi. …

   ” karku damu ai nasanar kuma anata addua Ne wallahi babu abunda yake tayarmin da hankali irin iya habu domin tabude mun huta…

   ” kaima dai kasan iya da kande soyayyace tun tana ciki, Amma kadaina saka kanka damuwa mijina za’aganta…

    ” shiyasa nake sonki saboda hankalin ki da tunanin ki….

     ” firdausi ke faman rawa a dak’insu ta saka eyepiece mumy ce ta shigo tace ke firdausi zo dak’ina…

    ” cirewa tayi ta amsa mata da toh shigarta dakin mumy ta tarar da farida tanata kuka cikin damuwa tace me kuma akayi miki?

    ” mumy tace naga alamun mun batar da kande amma zuciyarta tana cikin yarannan ku harma mahaifinku dan haka zamuje gurin boka nan da kwana uku ko ta halin yaya ne su soku…

    ” farida tace are u serious?

     ” eh mana kudai karku damu kiyita bani hadin…

    ” haruna ke fama da rungume filo sai juye yakeyi akan gado fuskar kande da murmushin kawai yake tunawa, tsewar da takeyi gayadda take kada hips yayin tafiya nan fa yamiki kai kai kai this is impossible ace kande ta bata! Wallahi i so much lurv her, you’re mine forever Allah kabay yanan kandeta wallahi am In  need of marriage Oh Allah yaragen abunda ke damuna at the end yatashi yayi alwala tare da sallah…F
” hamza kizaune a palour nan yadanna wayar suleiman hello suleiman wai DanAllah har yanzu ana satar mutane ne?

    ” kajika hamza me zaa hana har yanzu ba’a ganta bani?

    ” eh wallahi har yanzu…

    ” Toh Allah ya bayyanata dazuma naji naduba wacce abdul ya buge wallahi abun tausayi amma karayar ta dan fara karye wa har ta dan fara tafiya…

     ” wai abdul na nan jigawa?

    ” shimana bakaga yarinyar ba mashaa Allah ga nutsuwa…

     ” Allah sarki in nasamu time zanje nema kasan abdul abokine nagare komai namu yana tafi….

     ” hakane kam Allah yasa Aganta sai kuyita addu’a…

    ” Ameen nagode bye!!!..

     ” dady ne yafito yazauna kusa da hamza yace inason magama dakai!

     ” okay dady inajinki…

            ” yauwa maganar kande ce kun taba soyayya kokuma ta taba cewa tana sonka?

    ” hamza ne yayi tiriss yafara tuno maganganun ta nacewa bazata taba zama dashi ba gwara ma yadaina damun kansa!!!…

     ” Dady yace dakaifa nake magana hamza!..

     ” kwallar idanunsa ce ta kada yace bamu taba ba!…

     ” To me isa kakeso kasaka kanka cikin wahala da kuma bata lokaci!…

    ” cikin girmama wa yace dad u can’t understand the love am doing to her, please karkace haka please karka ce na hakura kataimakan wallahi zan iya shiga kowanne hali in babu kande!…

    ” ya ilahi, to naji amma inaso ku ajeyi komai agefe har Allah ya bayyanata sai muje ta bak’inta….

    ” Tohm dady, ya shige dak’insa cike da tunani yanzu in bai aure kande ba yaya zanyi da ransa? Baba mai gadi ke faman sintiri a cikin gidan sa can inna tafito tace wai malam meke damunka ne? +

     ” wallhi maganar yarinyar nan ce fa…

     ” To malam me zai hana kagaya masa gaskiyar magana!…

     ” Yace ai kuma nariga nagayamasa karya, gashi yanzu duk hankalina yana kan kande…

    ” Malam kadinga tunawa babu abunda wasu zasuyi maka face abunda Allah ya rubuta, sai wahalar Nemota sukeyi….

    ” ai bakisan wane abu baniba da bakinsa yace min in wane yayi masa karya ne bazanyi masa ba….

    ” To ai shikenan mai gida…

    Kauye..

    Iya ce ta shigo wai Aliyu har yanzu baka gama shiryawa bani ba?

    ” iya yanzu zangama…

    ” ah kabiru yaushe ka dawo daga lagos din?

   ” ina yini iya? dazu nadawo kuma na tadda wannan shedaniyar yarinyar wai ta bata!….

     ” kundun ubanka sha sha sha dolo kawai yar uwartaka?

     ” iyah kinfi kowa fasanin haukan kande kai daba’a hankali zakayi ne da kasan kande ba yanzu ba!…

   ” To Allah ya bayyana ta..

    ” yanzu naji magana Ameen, kai aliyu ayayin daka isa birni kasanar da hassan wallahi tun muna shiri yatabbatar ya fitomin da ‘yata kuma kacewa haruna ina son ganinsa idan kande bata dawo nan da wata1 ba to kotu zamu shiga dashi….i
    ” shi dai Aliyu toh yace mata yayi sallama da kowa ya dau hanya…

    Bai isa gidan ba sai gurin 8 nadare duk’a suna palour suna cin abinci sallama yayi sannan ya shigo….

  ” Dady ne ya mik’i  tare da bashi gurin zama sannu da zuwa Aliyu…

    ” Nan ya gaidasu..

     ” suka Amsa mumy tace kamar Dan uwan kande ko?

    ” ya kada kansa tare da murmushi…

     ” Dady yace iya ce ta aiko ka ko?

    ” ai Alhaji iya ta dau wuta da ita tace zatazo dakyar tabarni natawo duk ya gayamasa sakon…..

     ” Dady yace nikaina bansan yaya zanyi ba domin hankalina ba a kwance yake ba…

    ” Aliyu yace Allah Dai ya vayyanata sukace Ameen…

Jigawa

Sallamar abdul ce ta katse su meenal daga kallon dasukeyi da gudu suka tawo suna oyoyo abba oyoyo zamayayi akam gujera yana sakar musu murmushi ahankali ya sumbace kowanne koshinsu ciki da kauna da soyayya….

   ” meenat ce tace Abba ina kashiga tun dazu munata jiranka baka dawo ba?

    ” ahankali yace am sorry wane tsautsayi ne yasameni shine nake zuwa gurinta….

      ” meenal ce tace me isa baka kaimu munyi mata addua ba!…

     ” kuma kullum sai ta tambayi ku wallahi amma anjima zaku bine sai muje ko?

     ” Nasiba ce ta katse shi da cewa babu inda zasuje ihee babu inda zasu, bamusanta ba bamusan asalinta ba wama yasani ko mayyace ko aljana?

     ” meenal tace umma bafata da lafiya idan mukaje zamu samu lada sosai….

     ” meenat tagyara zamanta tace kuma umma munkaranta acikin hadisi manzon Allah saw yace idan mutum ya ziyarci mara lafiya dan uwansa musulmi da bashida da lafiya to yana tafiya ne cikin lambunan Aljanna yana tsinkar ‘ya’yan itaciyarsu, idan ya zauna sai rahama ta lullube shi, idan da safe ne mala’iku dubu saba’in zasu yi ta yi masa salati har ya shiga maraice, idan kuma da maraice ne mala’iku dubu saba’in zasuyi tayi masa salati har ya wayi gari… a cikin sahih ibn majah 1/244…

    ” meenal tace harda cikin sahih at tirmizi 1/286, inaji mantawa kikayi ko umma?..

    ” abdul ne ya rungumesu inasonku ‘ya’yana to kuje sama ku shirya kunje?

     ” yauwa dady we love u too…

     ” Nasiba da ta tsaya tana kallonsu, abdul yace ‘ya’yanka ma su fika hankali Allah yasawake kuma umarni na baki kishirya yanzu mutafi, tukunna ma ina abinci Na?

      ” tsaki tayi tace A asubutin bakaci bani?

      ” inada mata wane na asubuti zance, aine ba gwauro baniba…

     ” to mun cinye in zakaci babu sai kace kuma …

    ” hakuri wajen bin Allah ne, hakuri wajen barin sabon Allah ne, hakuri akan abin da Allah ya kaddara samun nasara yana tare da hakuri, kuma zan cigaba da yinsa…

      
  kande ce ta kalli mamee sosai dattijuwa mai mutunci gyangyadi ma takeyi a hankali tace mameeta….

    ” Naam ‘yata nefa nafeson kisha kunun kunun sai ki hadeye maganin kinje…. +

       ” sai da kwallah tafito idon kande (cikin zuciyarta tace ikon Allah ita tani ma takeyi)…tace toh zubamin nasha…

      ” babu shiri mamee ta zuba mata ta miko mata…
     ” mamee kiyi hakuri sai wahala nake sakaki….

     ” zama tayi abakin gadonta tace wahala neman ladan ne wahala? To wallahi kamar ‘yata na dauke ki….

     ” kande tayi murmushi tace Nema haka mameeta karkuma kidamu dani Ne mutuniyar kirki ce kums yar asali mai tarin dangi….

     ” Wallahi naji ajikina ‘yata kuma nasan ke alkhairi ce kafin ta karasa maganar suka shigo su abdul…

    ” su meenal ne suka rangada sallama aguje suka rungume mamee…

     ” Ashe zakuzo din, ‘yata gashi ancika miki alkawarin ki…

    ” Abdul ne ya zauna akusa da kujerar gadon ta tare da cewa yanzu kin daina fushi dani ko!…

    ” dariya tayi nina isa dama nayi fushi da kai…

    ” meenat tace sannu anty Allah yakara sauki….

      ” meenal tace aimu bamusani ba datuni munzo…

      ” kande da hankalin ta yafi karkata zuwa Nasiba dake dallah mata harara, ina yini?

     ” lpya, kaikuma kazo kawane matsa kusa da’ita aikin…

     ” jikin kande ne yayi sanyi sai tayi saurin dauke kanta tana kallon su meenat sunata yimata hira..ajikin ku nawa?

    ” muna primary 4 akuma islamiyya muna aji biyar…

     ” wonderful Amma dai kuna kokari ko?

     ” eh munayi zaki dinga koyamana karatu ne?

    ” murmushi tayi tace ga mum dinku nan ta dinga koya muku mana!

    ” Nasiba tayi cahhh kanta ni banason shishige aikin banza kawai…

    ” Mamee dai abu mamaki ya bata..

    ” kande tayi murmushi tace Kafin kayi ma wani mutum hukunci ka fara sanya kan ka a Matsayin shi sannan kayi rayuwa irin nashi daga nan sai ka fadi abinda kake so….

     ” meenal ce tace hakane Anty…

    ” meenat tace mufa jira mukeyi muje ilimin da zaki bamu?

    ” hahaha kunjeku sai kace wata mai ilimi…

      ” meenal tace yauwa gayamana akan sallah please akwai wani assignment da’aka bamu….

     ” Kande tayi shiru tace toh bari na tuna nagani can kuma tace yauwa a cikin bukari da muslim a kawai hadisi mai numba 615,981 Wanda yake magana akan sammako zuwa ga yin sallah An karbo daga Abi Huraira Allah ya qara yarda a gareshi yace: Manzon Allah SAW yace: ((…Da ace sun san -ladan da ke cikin- sammakon -zuwa yin sallah da sai sunyi- tsere game da hakan…Alhadith )) Bukhary da Muslim….

    ” meenat tace anty dan karayi mana Dan takaitaccen Karin bayani…

   ” kande tace Wato wannan cikin wani dogon hadisi ne, da ke magana akan saurin zuwa masallaci da jiran sallah, da mutane sun san ladan da ake samu ga wanda ke zuwa masallaci da wuri yayi nafila ya zauna; da ba wanda zai yarda a wuce shi bisa ga hakan, ko kuma da sai yakai ga mutane na yin quri’a don samun sawun farko a masallaci…..

     ” mungode sosai kinje kullum zamu dinga zuwa…

    ” Ni ke da godiya mamee basu alawowin nan…

  ” Nasiba ce tayi wane dogon tsaki tace wannan aure ai saina hakura ina dalili? Taja kofa zata fita sai kande tace ….

    ” yaya abdul?

         ” har cikin kansa yaji kiran cikin murmushi yace my humairat?

     ” Tace Wasu daga cikin mata sukan rudu har su dauka zama da namiji da suke yi cutar da kansu suke yi, don haka sai zuciyarsu ta rinka zuga su akan su kashe aurensu,Daga bisani kuma su kasa samun wanda ya kai mijin da suka rasa ko ma su zauna babu aure,Babu mutunci da rufin asiri ga diya mace kamar a ce: mutuwa ta riske ta a dakin mijinta cikin biyayya ga Allah….

   ” Mamee ce tace hakane wallahi ‘yata…

    ” Abdul ya miki yace we have to go dare yayi ya matso daf da kande yace pray before sleep kinje…

    ” kashe masa ido daya tayi tace don’t worry ya abdul…

    ” su meenat sukace bye bye…

  Birni

     Dady ke faman sintiri a palour haba haba wannan batan kanden yasani a masafi yar uwata bamu taba bata da’ita ba amma wannan karan tace har kotu zata kaine wallahi kullum addua nakeyi….

    ” mumy tace haka tace kaika dauketa ne? +

    ” tace kuka batar da kande takuma bani wata daya in baa ganta ba sai takaini kara…

    ” mumyce gabanta ya buga tace karka damu duk rikecin tsofa ne!

    ” haruna ne ya fito yace tabbas gidan nan abun zargi ne domin na tabbatar ranar ta dawo gida, fitar tace ba’agani ba…

    ” mumy tace ohoo mukuke zargi kenan?

   ” ohoo wayasani aishi zargi shi yake zargin kansa da kansa kuma indai ina duniya zan nemo kande Auren da ba’aso ayi sai anyi…

   ” dady ne ya zauna yana tuna wasu maganganu….

   Jigawa

   Yau aka sallemi su kande kafar ta danyi kwari amma still sai an ruketa soyayyarta da mamee kullum daduwa takeyi…

  ” mamee tanata tsokanar ta sai kuwa kande cewa tayi…

    ” mamee wayannan mutane wai ne sukazo dubawa har mota goma?

    ” mamee tace ai kadan daga cikin dangina ma dan ma bansanar dana kano ba suma suna tafi…

   ” kai amma nagode ina karas idin dakko na yanka miki…

    ” ‘yata kinaso kiyi aikin nan dai gashi jikinki babu kwari bari na hau sama nayi wanka na dawo..

   ” tohm sai kin fito, tafiyar mamee somun kukan kande yan uwanta taketa tunawa Nan haruna ya wado mata last maganar sa akan aure ce (nagaji kande ina bukatar mata yanzu please ki amince ), kuka takara sakawa sannan tace nabarwa firdausi kai….

    ” abdul ne yayi sallama yana shigowa yaga kande ta sunkuyar da kanta zama yayi akujerar kusa da’ita sannan yace nasan kuka kikeyi akan kuma danginki karki damu komai zai huce kuma suma zasu nemiki…

    ” wane yaki tayi tace ina kwana?

    ” idunsa kar akan nata yace lafiya lou kinci abinci?

    ” aa banciba hanuna ne ke yi mun zuge…

     ” mikewa yayi ya zubo mata sannan yace bude bakin to…

     ” budewa tayi yafara bata ina tare dake my….Tohm sai kin fito, tafiyar mamee somun kukan kande yan uwanta taketa tunawa Nan haruna ya wado mata last maganar sa akan aure ce (nagaji kande ina bukatar mata yanzu please ki amince ), kuka takara sakawa sannan tace nabarwa firdausi kai…. +

    ” abdul ne yayi sallama yana shigowa yaga kande ta sunkuyar da kanta zama yayi akujerar kusa da’ita sannan yace nasan kuka kikeyi akan kuma danginki karki damu komai zai huce kuma suma zasu nemiki…

    ” wane yaki tayi tace ina kwana? iya lou kinci abinci?

    ” aa banciba hanuna ne ke yi mun zuge…

     ” mikewa yayi ya zubo mata sannan yace bude bakin to…

     ” budewa tayi yafara bata ina tare dake my Humairat ki daina jin komai, kuma banason Naga kina yawan yin tunani….

     ” a hankali ta sunkuyar da kanta tace Na koshi ya abdul…

     ” kadan fa kikace my dear?

      ” Allah Na koshi mamee tabani kunu dazu kuma am okay fa!

    ” mamee ce ta sakko daga bene tana fadin lahh abdul yanzu dan Allah ko kunya bakaji ba ace kai kake bata abinci a baki anya abdul?

    ” haba mamee yakikeso to nayi tak’i cin abincin kuma zama da yunwar ta zai iya dawo da baya gaba, da spoon na bata ba tabata Nayi ba…

    ” Amma ai da sai kajira Nafito ko ame takeso sai nabata!…

    ” mamee kafin kifito yunwa tafara cinta..but Am sorry mameeta bazan saki ba…

     ” yauwa haka nakeso naji katashi mudanyi dan taka ta rike hannun kande …

     ” mamee nifa kafafuwa sun gaje please basaimun fita ba!…

    ” aa ‘yata tashi muje a haka kafar zatayi kwari sosai…

      ” okay my mamee i love u….

   ” har cikin ran mamee taje dadi bama aci abdul da yayi wane murmushi…

    Haka suka fita sunata hira abdul sai dariya yakeyi wa kande haka yayi musu sallama ya huce zuwa gidansa…

Lokacin da abdul yatafi office ya huce yana zuwa suka gaisa da manager nan suka dan tattauna sannan ya huce gidansa….

    ” oyoyo abba oyoyo abba rungume su yayi yace yakuke dotas?

    ” lpymu lou abba yanzu baka zama gida sosai kokana gurin anty?

    ” minal ina zuwa office yanzu!..

     ” meenat tace anty fa kaddai baka zuwa?

     ” ina zuwa mana dazuma naji tace ingaida ku kuma tana jiran zuwanku….

    ” gobe babu makaranta saimuje ko? Nifa ina sonta dama ta dawo gidan mu abba!

     ”  Nasiba ce tace see this mummus kuzaku kara masa auren kenan? Ku tashi kuje kuyi wasa…

    ” abdul ne yayi dariya ina abinci na?

      ” Abinci kuma ita humairan bata dafa maki ba? Nifa karka dameni…

     ” Nasiba Karfa kimanta Ne mijinki ne kuma ita humaira kanwa na dauketa kamar yadda kema nakeso ki dauke ta kanwarki…
    ” mikewa tayi ta huce zuwa dak’inta kayan jikinta ta chanja sannan ta kwanta akan gado…

     ” sallama abdul yayimin sannan ya zauna akusa da’ita hannunta ya kamo sannan yace My dear wife me yafaru kika zo zaki kwanta?

    ” hutawa zanyi bacci zanyi kaga nifa nagaya maki kadaina damuna kaje can gurin humairan taka!

    ” murmushi yayi yace ai banida wacce tafi ki ke fa uwar ‘ya’yana ce kuma farin cikina kinsan adadin son da nakeyi miki kuwa?

     ” murmushi tayi ta rungumesa tare da fadin i love u too my husband, ahankali ya fara kissing dinta Nan salo ya chanja…

Birni

   Uncle isyaku ne ya samu dady bayan sunyi sallar isha’i ah isyaku yau kaine a gurin nan?

    ” eh alhaji ina yini?

        ” lpylou ya kokari naku?

     ” kokari lafiya lou har yanzu babu labarin kande ko?

    ” eh wallahi abu ya faskara gashi muna tafi har wata biyu da kwanaki…

     ” To dai Allah ya kyauta wannan dai abune acikin duhu Allah kadai yasan gaskiyar lamari Dan haka nakawo maka katin dauren aure na jibe ne!…

    ” Aurenka kuma? Eh aure na jibe Allah ya bayyana kande.. +

   ” cikin mamaki dady ya tafi gida tarar wa yayi mumy da mama farida sunata fada cikin masifa yace ko wai wasu irin matane?

      ” mama farida ce tafashi da kuka alhaji sai bata kande takeyi sai kazafi takeyi yimata….

     ” Dady ne cikin masifa yace wai ke mumy bazakiija girmanki bani ba?

     ” wane irin girma kuma kande ce dai ta bata muga mai dawo da’ita gidan nan inbanda kunyi wa su haruna asiri tayaya zasuci suna santa har yaushe tagama secondary ga ‘ya’yana masu class….

     ”  kuyi mun shiru komai na kande yazo karshe domin kuwa zan dauki mataki tsattsaura….

     ” hamza yafito kowa tuhumar gidan nan yakeyi akan mumaka sace kande Dan haka yakama akwai alamar tambaya acikin gidan nan?

    ” mama farida tace nidai bana gidan ma abun yafaru zuwa nayi na tarar dan haka sai a tuhumi na gidan…

     ” Mumy tace to in ma sace ta akayi na sace ta sai uban me muma a batar damu idan an isa mana…

     ” kowa yayimun shiru bana son shashanci koma ya abun yake zan tumtuba…

      ” Dak’in mumy farida da firdausi suka shige mumy akwai fa matsala sosai karfa asirinmu ya tonu…

    ” banda abunki farida ai munjawa wancan mai gadi kunne shi kadai yasani ai…

    ” karku damu tunda kunyi masa kashe di  bazai fada ba…

      Haruna ki faman juya kujerar dake office dinsa yanzu ya zanyi da soyayyar kande? Ya zanyi ta yaya zancire ta?

    ” mukhtar ne yayi dariya mutumina kawai ka hakura ga yan mata agidanku gasu kuma aduniya so feel free kazabi wacce kakeso kuma naji hamza ma yana sonta yanzu yaya zakayi?

      ” abokina nasan inason kande wallahi soyayyarta ta dadi azuciyata nidai nasan matar mutum kabarinsa indai matata ce zan aureta…

     ” hakane abokina kayi shawara mai kyau Allah ya dubi lamarin!…

   ” Ameen zanje kauye gobe please in ankawo kayan nan help me sign it…

   ” okay

Jigawa
    Mamee fito kiga Ni kadai nafito daga daki mameeta?

    ” Dan Allah fa? Kai Alhamdulilah sauki ya samu Allah yakara sauki to karaso kikarbe wayar Abdul yanata kiranki….

     ” hello yaya abdul what wrong?

    ” wane size na shoes kike sawa?

     ” i think 38 ne…

           ” okay am coming right know kice mamee ta dafamin indomie…

    ” bari na dafamaka toh, kitchen ta shiga amma tanayi tana hutawa tana karasawa ta fito palour…

     ” mamee ce tace da Alama agidanku kin kasance kina aiki sosai…

     ” mamee kenan kusan hakani domin tun ina karama aka hureni da aiki har nagirma ninakeyin komai nagidan mu!…

    ” ai hakan yana da kyau ‘yata Allah ya kara miki lafiya aduk lokacin da na tuna zan rabu daki alokacin bakin ciki ke ziyarta ta…

     ” mamee karki damu Nema banason rabuwa dake in ba bisa dole ba…

    ” Assalamu alaikum sannunku da hutawa…

    ” kande ce ta mik’i sannan ta huce zuwa karbar ledar hannunsa!…

    ” murmushi yayi yace this is serious my humairat kice kike tafiya batare da an rike ki ba?

     ” yes yaya nice Allah yabani lafiya!..

    ” kai Alhamdulilah wallahi naji dadi kuma nayi farinciki yau gashi Allah yabaki lafiya baki zama gurguwa ba!

     ” Lokacin da nafadi haka duk ina cikin rudune shiyasa…

     ” mamee kinsan menene kuwa?

     ” me yafaru abdul?

” Nakasance a kamfanin mu komai nawa dabanne sai nake ganin mutane basa shiga har kar abunda nake rubutawa ashe ne bansan komai kwafata sukeyi ba yanzu fatihu dayake nuna kamar baya kula abunda nakeyi, zanin tabarmar danayi har yaji ya kwafa ya rubuta a anasa littafin…..

    ” kande ce tayi murmushi yaya kenan ai dama su mutane haka suke mafi sharrin mutane sune wayanda sunsan kana rubuta abu mai kyau amma bazasu nuna maka ba sai dai su kwafa, mafi sauki cikin mutane sune masu yabonka suna kwafarka, Kai dai kakasance mafi amfanu wa daga mutane….

     ” mamee ce ta kalli kande tace lallai ke ta dabbance….

    ” Nayi rayuwa acikin kauye kamar yadda nayi acikin birni nakasance mai iya zama da mutane Amma daga karshi su suka yaudare ne suka sakani cikin wannan halin…. +

     ” abdul ne yace karkiyi kuka my humairat kansu suka cuta kuma Allah yana tare daki….

    ” kande takara fashiwa da kuka bansan halin da mahaifana suke ciki ba? Bansan ahalin dasuke ba? Bansan halin da masoyana suke ciki ba? Na kasance ina laluban duhu kullum dasu nake kwana Sun rabani da dangina sun kuma rabani da karatu na daga karshe suka rabani da masoyi na Kuka ya subuce mata Amma ni bamai fushi baci ba duk Abunda sukayi min Allah yayimusu….

     ” abdul cikin tausayin ta yace su wanene wayannan kisanar dani domin da daukar miki fansa my humairat?

     ” dangina ne kuma iyaye na ne kuma uwa take agurina sukuma yayye suke agurina….

   ” mamee tace subhnllahi amma basu kyauta ba ita Nasara ta tare da kaddara kala kala kidai kullum kiyi adduar cin kaddarar nan kuma karki manta kansu sukayi wa kuma zai koma musu shi Allah baya zalunci kamar yadda yahana zalunci….
     ” cikin shashekar kuka tace Nasan da haka kuma inayi, Kunnu namin karamci da kulawa jinku nakeyi kamar ‘yan uwana! Ada nakasance fitsararre ya nayi abunda bai kamata ba gashi yanzu rashin kunyar danayi tana bibiyata ya ubangiji ka yafemun….

    ” toh kidaina kukan mana haba my humairat Allah yana tare da me neman yafiya da me hakuri…

    ” Na daina to…

Kauye..

  Yanzu sabida Allah haruna yau kwana 10 da aikawa akirawo ka sai yanzu kaga damar zuwa? Kokaima sun hure maka kunnen ne? kuda kande ba yar uwarka baciba darajar hidimar da tayiwa mahaifiyar ka ai baka zauna baka nemeta ba?

    ” Kiyi hakuri iya habu nasan nayi kuskure Amma wallahi sai jiya alhaji ya tunamin….

    ” hassan ai yazama sauna wazai bi tatashi? Mata sun maidashi huhulawo bashida karfi sai nasu….

    ” haba iya baba hassan bai cancanci zagi agurinki ba, akan matsalar da bazai iya rufeta ba akan matsalar da bazai iya dakatar da’ita ba?

    ” To tayaya haruna yana ganin kande ta bata?

   ” shi abunda Allah ya rubuta babu abunda yaisa ya tsayar da ita ballanta na aci kaddara ma, koda kande tana hannunki sai fa tabata, baba hassan ya kula da d’anki ya biya masa makaranta yakuma yi masa abubuwa da dama ai in baki gode masa ba ai kya kare masu zagin shi domin uwa daya uba daya kuke….

     ” kuka iya habu tasaka tace wallahi hakane Allah yarufamin Asiri ban yanki zumunci ba, haihuwa Nada rana yau ga dana ya tunasar dani, Alhamdulilah da kazama nutsatse Allah yayi maka Albarka yakuma baka mace tagare ita kuma kande Allah ya bayyanata….

    ” Ameen iya habu, Nima kiyimin afuwa abisa maganganu na idan sunyi miki tsauri?

      ” babu abunda kayimin sai gyarane dakayi da kuma chanja bakin zaren zuwa dama…

    ” yauwa nagode kuma kullum binciken ‘yarki akeyi inshaa Allahu za’a ganta…

     ” Allah yasa sai ka lika kagaida goggo…

    ” sallama ya ranka’da musu Nan suka amsa ciki da murna inayini goggo?

     ” lafiya lou haruna ya mutanen birnin?

     ” lafiyarsu kalou, goggo kikwantar da hankalin ki duk inda kande take tana cikin koshin lafiya…

     ” To Allah yasa shima Aliyu yasamu aiki ajigawa wane shagon kaya duk ran jumma’a yake zuwa…

    ” Aliyu yace inata son nasanar dakai ma mantawa nayi anjima ma zan koma…

    ” mashaa Allah fatan nasara da saa danuwa ni bari natafi agaida sadiya naji ance makaranta takeyi…

    ” goggo tace eh ta yamma take zuwa..

    ” Allah ya bada saa ga dubu goma nan babu yawa adanyi cefani…

     ” laah haruna baka gajiya ai mai yawan kenan Allah ya taimaka yasa Albarka kagaida su kawun….

     ” zasuje…


Birni..

    Hamza da baba me gadi da haruna ke faman hira haruna yace yanzu mutane dan suna tsoron wasu mutanen sai su tauye gaskiya?

    ” dady ne yazo ya samesu yace baba gurin ka nazo domin kai kadaine wanda zai bada shaida Akan kande inason kaje tsoron Allah katuna in kayi mana karya alahira baka isa kayi ba?

    ” haruna daya fuskance baba ya k’edemi yace yakamata kacire tsoro domin kai dattijon arzukine….

    ” kuyimin kuyimin afuwa karkuce nasanar daku domin firdausi da farida sunce nema sai sun kasheni idan nafada!…. +

      ” dady ne zufa ta fito mai cikin saurin baki yace oya kafada munajinka….

    ” baba me gadi yace tabbas kande ta dawo gidan nan daga makaranta shigarta palour kida wuya mumy tafara dukanta tare da yayanta sai da sukayi mata raunuka sosai ta kasa tafiya sannan suka cillata can gefen titi….

    ” haruna ne ya tashi afusace kaji ko kaji ko basa tsoron Allah ka dubi cin zarafin da sukayi mata yanzu ina take….

    ” dady ne ya shiga gida baisan lokacin daya fara duk’an su firdausi ba halin uwarku ko halin uwarku ko gwara na kasheku na huta tunda baku da imani…..

   Jigawa..

  Tunda takalmin baiyi muku ba ku tashi mutafi shagon sai ku chanja!

    ” mamee ce ta dakko hijjabin su kande tasaka nata sannan suka fita zuwa boutique din…

    ” tunda suka shiga kirjen kande ke faman bugawa…

    ” my humairat ba na hanaki tunani ba?

    ” Murmushi tayi tace to Allah ya hanine ni ma…

   ” Nan mamee ta zabar mata sun tafi zuwa biyan kudin kenan kande tace malam bani sweet din gefanka…

      ” dago kansa Aliyu yayi cikin mamaki yace kande???

    ” Tana daga kanta tace ya Aliyu…sai ta sume 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *