HASKE CHAPTER 6

HASKE

CHAPTER 6

Alhaji Zailani yana cikin barci sai gabansa ya fadi ya farka na rashin dalili. Hakanan yaji bazai iya barci ba face ya zaga yaga kowa na gidan. Hadiza da Baraka suna kwance gefensa suna razgan barci da sauti na barci yana tashi a hankali. 

Dakin Haske yaje wanda take kwana tareda Fijr, ita tana sama sai Annoba tana kasan gadon. Abin al’ajabi sai gashi babu Haske babu dalilinta. Kara haska tocila yayi amma bata wajen. Asalima gefen kayanta babu komai. “Ke ina yar uwarki?” yace da karfin tsiya. Fijr ta farka tana mistike ido. Sake daka mata tsawa yayi mai rikatar wa “Ke nace Shamsiyya ina take?” yadda taga fuskansa babu wasa sai ta soma inda inda. “Dama… Dama… Dama” “Daman mene? Tana ina ko saina saba maki” ya zare mata kyawawan idanuwan sa. 
“Ammi ne tace bazata kwana cikin gida ba saboda tayi mata rashin kunya, kila tana wajen …….. ‘ ‘ bata karasa ba ya arce a sittin ya soma bude kofar falo zai fita. Ita kuma Hadiza taji hayaniya saita fito sanye da rigar barci. 
“yaya dai! Lafiya Naji hayaniya ba’a so muyi barci?“ Baiko tanka taba sai ya fita abinsa, Fijr na bakin dakinsu tana raba ido, ita ma Hadiza haka. Koda yaje varanda yaga Haske ta kankame jikinta duk sanyi yayi mata yawa tana numfashi da kyar. “Innalillahi” “innalillahi” yayita maimaitawa bila adadin. Haka ya dauke ta kamar yar tsana ya shiga da ita, kan 3 seater ya ajiyeta duk ta fita hayacin ta. Gaban Ammi ya dan fadi amma saita kanne fuska. Daki ya wuce ya dauko bargo ya lullube ta. Daga nan ya wuce ya duba flask, cikin sa’a akwai ruwa a ciki saiya saka a kwano tareda dauko tawul. A hankali ya rinka shafa mata a fuska dajikinta. 
Dakin tsit bakajin karar komai saina Fridge dake chan kurya yana aikinsa. Ammi tanata dai kallo daga tsaye, tsab batayi nadaman abinda tayi ba. Fatan ta baifi yace zai mayar da Haske Zaria da zama ba. Wajen minti talatin ana abu daya sai Haske tayi ajiyar zuciya a hankali. ’ 
“Shamsiyya, kina jina kuwa?” yace da sauri. 
“Idan kinaji dan Allah ki bude ido” ya sake fadi. A lokacin muryansa yayi kauri. Kanaji kasan dab yake da yin kuka. Babu abinda yake tunawa sai Hafsa, ya san cewa bai kyauta mata ba. Ta bar masa amanar yarta gashi ya kasa rike wa. Sam ya kasa gane me Haske ta tsone ma Hadiza take gallaza mata haka. Da tun farko yasan zatayi mata haka da wallahi bai aureta ba saboda shifa baya sonta ko dis. Amma kuma yanzu sunada yara, daya sani yaje ya aure wanda yakeso idan zata gallaza mata sai yasan dama bare tayi. Sai dai cikin ikon Allah komai ya kare. Dama talauci ne ya kawo masa wannan abu, amma yanzu komai yazo 
karshe. A hankali Haske ta soma hawaye tun kafin ta bude ido, dogon suma tayi wanda sai yanzu ta farfado. Shafa mata kai da hannun sa yayi na wasu dakikai kana yace, “Na zuba maki abinci?” 
Yunwa na bala’in dawainiya da ita amma batajin zata iya ci, bala‘in sanyi takeji har cikin bargonta. Girgiza masa kai tayi alamun a’a. “Na hada maki shayi?” wannan Karon saita yarda. Ragowar ruwan Flask ya samu kofi ya zuba, saiya saka lipton da siga yakai mata. Taimaka mata yayi ta zauna sannan ta soma sha. 
Hadiza cikin borin kunya ta kama hanyar daki, har ta kusan shiga saita waigo ta kalle Fijr,” Kije ki kwanta gobe akwai makaranta karki makara“ haka itama ta tafi suka bar wajen. Da 
kansa ya wuce kitchen ya kunna kettle, sannan daya tausa ya zuba mata cikin bokati yakai mata bayi. . Haka taje cikin 3 na dare tayi wanka. Abin ya bala’in mata dadi saboda taji 
dama dama bayan yanda ta jibgu. Baka ganin komai ajikinta sai shedan duka, ga gefen bakinta yayi bala’in kumbura. Sannan idanuwan ta sunyi kanana kamarzasu shide. 
Barci kadan tayi asuba yayi, haka ta tashi tayi sallah wanda kayan Fijr ne Daddy ya ara mata dukda yayi mata girma. Haka ta koma barci saboda ya gargadeta akan karta fito balle tayi wani aiki. Abin yayi ma Hadiza ciwo sosai, su sukayi ma kansu breakfast suka fita abinsu. Shima Daddy ya fita wajen bakwai da rabi amma yace ma Haske zai dawo kafin azahar. 
Dayake barci barawo ne gashi kuma tanadan masassara saita rizga barci mai rai da lafiya. Wajen Sha biyu Daddy ya dawo da manyan ledoji a hannun sa da Buhun hunan abinci. Dama yaje yayi reporting a aikinsa ne kamar yadda ya dace, sannan ya gama wasu documentation nasu bank da komai. Anan ne aka bashi wani kudi wanda ake ma lakani da ‘wanke talauci’. Ana bada kudin ne saboda kayita shirin aiki sosai. 
Kasuwa yaje ya siyan mata uniform din boko dana islamiya, sai dogon riguna guda biyu. Sannan atampha yan madaidaita guda 3,jens skin da riga. Sai takalmin makaranta dana silifas. Under wear, pant, sannan breziya kuma kawai ya dauko wanda yayi tunanin zai dace da ita. Duk abinda take bukata idan ya fado mashi a rai zai siyan mata. Sannan saiya siyan masu Fijr, Imran da Baraka kala biyu suma yar kanti. Sai su Buhun Shinkafa, semovita, garwan man gyada da sauran kayan amfani. Yanzu tunda ya samu yan kudi, abubuwan da Hadiza takeyi Allah ya amfana amma an dena daga yau. Zai rinka lura da gidansa yadda ya dace a matsayin sa na mai gidan. Mamaki Fal a fuskar Haske sanda taga kayan. Kallon sa da ido tayi tana so ya fada mata inda ya samu kudi. Mika mata appointment letter dinsa yayi yana murmushi. Haka ta karanta Taji dadi sosai kuma ranta yadan sauka saboda tana tunanin abinda zatayi kila kawai ko ta fara fita aiki. Akwai wata Iya Sunday a bakin bus stop tana siyar da abinci. Tana tunanin ko zata rinka zuwa tana tayata da aiki sai a biyata sannan a bata abinci. 
Gashi ofis din Daddy sun bashi motar hawa wanda ga sunar Hajj Commission dankare akai. Peugeot ne 504 wanda babu laifi babu fallasa a lokacin. Yana ajiye kayan saiya koma aiki ita kuma ta kaima Maman Jawahir na bayan Layin su dinkin uniform wanda zata karba nanda kwana 5 duka. Dama ba zuwa makaranta zatayi ba saboda tana bala’in ciwon jiki wanda Daddy yayi mata alkawari zasuje chemist anjima idan ya dawo. 
Koda Ammi Hadiza ta dawo taga kaya birjik, abin yayi bala’in bata mamaki inda Daddy Zailani ya samo. Gashi kuma Haske dukda ciwon jiki bai hanata aiki ba ta gyara gidan fes. ldan akwai alheri daga cikin abinda Ammi Hadiza take mata bai wuce rashin san jikin datake dashi ba ga uban tsabta. Saboda keta abu bai taka kara ya karya ba Ammi zatace a wanke, tun tana gajiya harta saba. 
Kusan duk wata saita wanke su labulayen gidan da rug. Komai na gidan Kal Kal kamar na amare. Haka Haske ta dafa masu shinkafa da wake Wanda Daddy ya siya. Saita yi miyan dagedage na kayan cefanen data siya jiya wanda daga alama ledojin indomie dataga ya nuna shi sukacijiya.
Nan taci tayi nat ta koma daki, koda Ammi ta dawo basu hadu ba tana barci. Ammi tana 
cikin tunane tunanen ta saiga Haske ta shiga dakin domin tayi mata barka. “Assalamu alaikum” 
“Assalamu Alaikum Ammi, sannu da dawowa?” ta sake cewa. Mamaki da ban tsoro Ammi tayi dataga Haske da yan kanti mai kyau a jikinta. Gashi fitted yayi mata bala’in kyau kamar ba ita ba. Tanada kyau mai natsuwa kamar sallar asuba, gashi ta kara Haske kamarwata ranar 12. Tsab batada bambanci da Hafsa sanda take shekarun ta saidai hasken fata, amma yawan fara’a da dimples dinta duk sunyi kama. “Me kika dafa?” “Shinkafa da wake“ Ammi Hadiza saida tayi barazana tukun kafin tace a zuba mata. Haka ta saka mata a cikin plate ta kai mata saita sake komawa kitchen ta dauko mata ruwa kana ta tafi lta Ammi jira take Zailani ya dawo idan ba shi ya kawo kayan ba ta sake daka Haske.Kamar yadda yayi mata alkawari zai kaita Chemist haka kam akayi. Bayan Magrib ya dawo ko abinci bai ci ba sai suka tafi asibitin Al-Mansur. Ya siyan mata magani da kuma fruits saboda karin jini. A hanya yayita binta da baki yana bata hakuri, ta riga ta san cewa Ammi bata kaunarta amma tana mamakin laifin me tayi mata. Wai ace tunda take kullum daga zagi kamar su, mayya, shegiya, azzaluma k0 Tsinana shi take binta dashi. Babu albarka balle magana mai dadi ko hira. ldan bata aiki wanda ba kasafai ake samun haka ba.To tana daki abinta tana duba takardun makaranta saboda idan tace zata zauna a falo rashin kunyar Fijr ya isheta. Gaida Ammi tayi sai ta wuce daki. A dikilce Ammi ta amsa duk ta kagu taji bayani inda ya samu kudin facala. 
Fijr tace kawo mashi abinci wanda dama bai ci ba. Jan kafarta tayi tanata tura baki. Koda taje wajen cooler banda bugawa da karfi tanata karab karab da cokula. Bata saka mashi nama ba saboda dama ba kullum ake saka mashi ba saidai yaci lami. Duk da akwai wajen yanka 7 raguwa a tukunya kowa yaci nashi. lta ce ma ta tsinto daya ta soka bakinta tana ci. Saida yaci yayi nat saiya soma magana, nan ya gayama Ammi Hadiza batun aikinsa da duk abinda ya siya masu sanadiyar kudin da aka soma bashi ne. Sannan kuma ya gode mata akan yadda ta rike gidan sanda bashi dashi kuma yanzu karta damu. Komai take nema karta yi shayin tambayarsa. Nan ta soma washe baki tana murna, koba komai kudinta ya huta. Balle tana bala’in san ta siya mota. Yadda take murna abin ya bashi mamaki ainun baiyi tsammani tana san cigaban sa ba. Faram faram tayi masa kamar sanda suna sabon aure, sai wani murmushi takeyi tana shige da fice. Nan ta nace bari ta kara masa abinci. Dataje kitchen taga nama a tukunya saida tasa masa yanka hudu tareda watsa ma Fijr Harara sanda suka hada ido. 
Duk yaran an basu kayan su kuma sunyi godiya, sam bata damu da yadda bai siyan mata komai ba. Tana bala’in san yaranta kuma tunda ya faranta masu rai abin ya biya. Koda yake tayi kishi kadan da Haske tunda nata yafi yawa. Amma kuma ko a haka batada kayan dazatai takara da yaranta. 
A kwana a tashi gidan Alhaji Zailani ya canza fasali, akwai dan walwala kuma an rage 
tashin hankali. Hajia Hadiza an sauke farali ta dankara hakora biyu na zinare a bakinta. Daddy ya biya mata tunda shine Chairman kuma dole Shima yaje saboda aikin sa. Haske ke 
komai a gidan har suka dawo abin yama Ammi dadi saboda harda tsaraba tayi mata daidai da na Fijr. Kuma ba’a dukan ta saboda ya hana. Bama ita kadai ba yanzu an soke zancen duka a gidan. Koda yan Zaria sukaga Haske yanzu sunji dadin yadda babu damuwa sosai a tare da ita. Balle dama Hadiza ta shirga masu karya akan cewa rashin aikin Zailani ne ‘tasa a rai duk ta qwarzaba kanta da damuwa. 
Yanzu haka zasu zana JSCE amma haryau bata fara al’adanta a matsayin na ‘ya mace ba. Su Laila kam tun JSl second term ta soma. Sam abin baya damun Haske saboda akwai wanda suna kaiwa 17 kafin su fara. lta kam Fijr iyayen rashin kunya tuni an tsufa a boarding. Jumping tayi daga primary 5 saboda girman jiki, kamar uwarsu take a ajin tayita bugu, iyaye sai complain sukeyi. Headmaster da kansa ya siyan mata form din common entrance ta zana. Da karma karma ta ci point din daidai babu kari inda tayi gaba. Koda ta dawo ta sake budewa da girma saidai tayi baki. a 
Rashin kunyarta ya sake karuwa ta fara al’ada Haske bata fara ba. Gatada da uban kazanta kamar mutum yayi amai. Ko dan wanka da gyara jiki batayi haka zakaji tana doyi. Sai Ammi ne zatayi mata fada akan tayi wanka tun safe tana zaune. Gashi bakinta baya rasa tauna cingam zatayi ta kararas tana hura hanci da balan balan. Ta bala’in cika ta batse jira take ta fashe. Sannan kuma tayi saurayi wanda ta bashi number din Ammi. Anan zai kirata suyita hira, kuma cikin dare a kwana ana free call. Haka zata ishe Haske tana hira tana dariya kuma duk maganar mara kan gado. Abin mamaki wai ace sunar mutum ‘Lalos’ waika amsa shi. Kawai tana bala’in jin dadin yadda take boarding soba kasafai suke haduwa ba sai hutu kuma babu yawa. 
Ranar da zasu zana Intro Tech da Hausa Haske ta tashi cikinta yana mata ciwo amma saita danne. Hausa ne paper na farko wanda yayi bala’in mata dadi. Sai kuma Intro Tech da Yamma. Suna cikin jaraba zata juya ta tambayi yan bayanta amsar number 2 wanda yayi mata wuya. 
Me zata gani??? Jini ne ya bata mata Wando harda farin rigan gaba daya, gashi da uban yawa. Mamaki take yadda bata jiba balle ta lura gashi abin yanzu yaci karfin ta. Dadin abin bata zauna kan hijab dinta ba data raina kanta. Gashi ba wajen zaman su daya da Laila ba tunda ita Mohammad ne ita kuma Zailani. Hawaye ya ciko mata bata san yadda zatayi ba. Haka ta mike tayi submitting paper dinta tinda dama an soma fita. 
Ashe Laila harta fita, bata ce mata komai ba saitajuya mata baya ta gani sannan ta cigaba da hawaye. Hannu Laila ta rike mata sai suka tafi masallaci inda ta dan dauraye wajen. Sannan Laila da kanta ta fita chan shago ta siyan mata Always ta kai mata tayi managing kafin takai gida. Toh fah tun daga ranar soyayyar Laila ya kara samun waje a wurin Haske. Komai zata mata idan ta tuna ranar saita mance kawai saboda tayi mata halarci.

Bayan wasu shekaru…

Haske ta gama Kaduna State university inda ta karanta Accounting ita da Laila yanzu suna 

jiran a turasu bautar kasa. ltama Fijr an gama secondary amma admission yakita. Jamb 
ba’a samun abin arziki daga 90 na farko sai 110 na biyu. Babu Poly dazai dauketa balle 
jami’a. Haka taketa zaman banza zaman gantali. Baka rasata da biki ko suna Sai tace tama fasa makaranta ita aure takeso. Yanzu saurayin ta sunar sa lsiya amma da Isi ake kiransa. Kullum a dakinsa take yini daka safe haryamma babu abinda ya shalle ta. Dadin abin Unguwar Sarki yake ba’a santa a wajenba. ” 
Yanzu aiki yayima Alhaji Zailani yawa arziki ya bunkasa harma sun canza gidansu 
dunguzugum. Suna Malali din amma ta wajen FGC yayi gini inda yayi ma yaransa biyar kowa da dakin sa, dukda auta Anisa bata kwana a dakinta tana tareda Ammi kasancewa shekararta hudu. 
Wani asabar kowa yana gida, Ammi Hadiza tana gyara ma Daddy kayansa dasu takardun aikin sa. Tanayi kuma tana karanta wanda suka dauki idonta. Taga an rubuta ‘Next of Kin’ sai taga ya rubuta SHAMSIYYA ZAILANI ABUBAKAR. 
Nan tayita nanatawa watau bama itace next of kin dinsa ba ko yaranta saidai Shamsiyya. Yanzu idan ya fadi ya mutu ta hanasu gadon su ta gudu dashi banan gabanta ya sake faduwa ba saida taga takardun banki na Bank of Industry na neman hannun jari wanda ya soma cikawa da sunar Haske. ” “Idan kun san wani baku san wata ba” ta fada a fili. Ranar kwana tayi tana tunani yadda zatabi. Abinda tasani shine saita rabashi da ita. Dukda tasan ba’a raba da da mahaifi. Bahaushe yace ko mutuwa ma na tsoron idon iyaye. Amma dole sai Haske ta bar rayuwar su. Gashi yan kwanaki nan gizo take mata da Hafsat. Sai gabanta yayita fadi na rashin dalali gwara ta tattara ta tafi kafin ta haukatata Sosai abin ya soma damunta harwata sa’in tayita sumbatu “Hafsat kin mutu dan Allah ki kyale ni na huta” 
Ana haka ne Ammi ta yanke shawara gwara tabi malamai ko zasu taimaka mata. Gurin wata mata taje mai duba. Nan ta buga kasa tayi surkulle tareda fada mata karya da gaskiya. 
Daga nan ta shaida mata idan tanaso a raba Zailani da yarsa zai yiwu yadda zai koreta 
kuma ya sallameta daga dangin yaransa. 
Kawai dai abinda zatayi shine ta kulla ma Haske wani makirci da duniya zasu dauka kuma baza’a san da saka hannun ta a ciki ba. 
Komai ya fado mata saita sake tunanin saboda bai mata ba, abu daya yazo mata kawai Haske ta samu ciki yayi fatali da ita. Yanzu dai waye zata samu yayi mata fyade? Wannan kenan! 

Hmm Labari yana tafiya yanzu Haske ta kusan barin gidansu. Sannu a hankali zamuga yadda zai faru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *