HASKE
CHAPTER 3
Haske tana kwance kan gado hawaye yana malalan mata, ita tunda take bata taba samun karbuwa wajen mutane ba musamman ma wanda take so. Daga Mahaifmta har mahaifiyarta sun mata tsana na rashin dalili wanda shine makasubin zamanta gidansu Laila.
Sanda ta hadu da Bilal tana tunanin kakarta ta yanke saka saboda shi ne zai bata gata da nuna mata son data rasa a kuruciya. Amma kuma sai aka samu akasin haka. Shi ma bai wuce labarin gizo da koki ba. A duniya tana muradin taga ana mata so na hakika, k0 kasuwa taje kokuma asibiti idan taga iyaye suna tattalin yaransu abin yana tafiya da imanin ta tayita dariya.
“Tunanin me kike yi?” Laila ta tsinke ta. Murmushi ta kakalo saita share hawayenta, daga nan sai ta zauna zaman allo. A hankali ta soma magana wanda yanzu ya zame mata yanayi, da chan tanada bala’in surutu kamar ta hadiye radio amma saboda wahalar rayuwa yanzu dakyar kaji bakinta. Bakin ciki yayi mata cinkoso magana ma gagaranta yakeyi.
“kina ganin kamar na nuna ma Bilal so dayawa koh?” ta tambaya Laila sannan kuma tabi fuskanta da kallo saboda ta karanci yanda zata amsa. Ajiyar zuciya Laila tayi, tabbas Haske ta nuna ma Bilal so fiye da yadda ya dace. Amma kuma gaba take kallo ba baya ba, idan ta aminta da batun nan zata dauke mashi wuta haryayi sanadin rabuwar su. lta kam bazata dauka wannan abu ba, Bilal yana kashe masu kudi fiye da samari goma idan aka tara.
Kama hannun Haske tayi tana murzawa saita sakar mata murmushi, “Haba Haske wani irin nuna so kuma? Ni a ganina kin fiye basarwa ma wallahi” ta fada tareda ajiyar zuciya mai karfl. Kirjinta yanata bugu da karfl wanda idan ka kai dodon kunne ka wajen zaka tabbatar.
Itama Haske Murmushi tayi, “Wallahi ina sha saboda na nuna ina sanshi ne yasa yake wulakanta ni” Anan dai Laila ta rinka bata shawarwari akan yadda zata bi dashi. Dayake Laila tun suna J52 takeda samari ta kware sosai a wannan fannin. lta kam Haske ‘tashin hankali a gidansu bazai barta ta samu wannan yanci ba.
Badman Bilal in dai addini ne toh fah yanada shi, yanada bala’in sani a Alqurani mai girma da fassara. Idan yaso gulma yana magana yana fassara . Sai dai Musa a baki ne Firauna a zuci tunda baya aiki da sanin sa. Dan kam babu ranar da zai rabu da girman kansa na bala’i.
Rabon daya yi fashin sallar asuba a jim’i shekara goma sha biyar kenan. Kullum yana kan sahu amma mugun halinsa yaci tura, idan ka bibiya sabida sallan ne yake haka, da ba haka ba daya buwaye al’umma. Tsabaragen girman kansa yasa damun kowa musamman iyayen sa, sau da dama abin yana jan masu tsegumi a cikin jama’a. Baya amsa gaisuwar ko uban waye balle ya gaida ka. Kana mashi magana zaiyi shan kunu ya tamke fuska tamau, balle yanada dambun gashi dole ka tsorata dashi.
Ko masallaci yaje wanda ke kofar gidansu sai dai ya wuce abinsa ciki, kuma yana idarwa zai zura silifas dinsa yayi gaba. Balle ma ayi tunanin zaiyi ma yan anguwa horn din mota idan ya gansu zaune kofar daki. A takaice baya ta’ammali da mutane sai tsiraru.
Bashi ya kira Haske ba saida ya biya Falon Abbansa domin yayi masa bayanin yadda ake a business dinsu. Daga nan suka ci Dinner tare. Wani abin burgewa gamida Bilal bai wuce tsabta ba wanda yanada degree dinsa.
Koda ya koma dakinsa ya cire kayan jikinsa, a tsanake ya ninke kafin yasa a kwandon shargi. Komai nasa tsab tsab kamar dakin amarya. Bandaki ya shiga ya watsa ruwa mai
dumi daga nan ya fito yana goge dogon gashin sa. ‘10:25′ agogon bango ya nuna masa wanda yasan Haske ta dade dajiransa wata kila ta soma barci. Wando mara nauyi Three quater yasa da singlet, sai ya bude fridge dinsa domin ya tsiyaya fresh yoghurt. Wannan dabi’ansa ne saiya sha yake iya barci. Ya kishingida yana nishadi saiya dauko waya domin ya kirata, saida ya kusan kaiwa karshe kafon ta dauko. Siririn muryanta zai tabbatar maka da cewa har ta soma barci. A hankali ta gaida sa cikin barcin da bai gama sakinta ba. Yana wanijin kansa namijin dawa ya amsa yana girgiza kafa. Muryanta yayi sanyi wanda duk girman kansa saida ya sakashi shiga wani yanayi mara misaltuwa.
“Sweet kin soma barci ne” ya fada chan cikin makoshin sa.
“Eh inata jiran ka amma barci barawo yayi hali” ta fada a shagwabe wanda halinta ne kuma yana cikin abin da ke burge shi gameda ita. Yana bala’in san mata masu shagwaba, sannan kuma da saurin kuka.
Sautin dariyar sa taji, saita cigaba da magana. “Ka isa gida lafiya, yasu Mommy?” “Lafiya lau, mommy kuma gobe zata dawo daga UK ancejikinta yayi sauki”
“Allah ya kaimu”
Shiru sukayi na wasu daki kai, zukatan su na aikawa wa juna sako wanda su kadai suka san ma’anar sa. Shi yayi gyaran murya ya soma magana,jaraban shi ya ciwo shi. Wata sa’in mamaki yakeyi wai ace har yau ta kasa gane inda ya dosa. Sam bata yarda suyi soyayyar zamani wanda abin yana bala’in bashi haushi.
“Sweet har kinsa kayan barci ne, wani iri ne?”
Nan gabanta yayi mummunan faduwa saboda bata san irin haka ba, bata ce komai ba kuma shima tabbas yasan bazata amsa ba. “Sweet kyaleni kikayi? Wai menene dan nasan irin kayan dakejikin ? Ban kai ba kenan?” “Ba abinda nace ba kenan” ta amsa da sauri “Ai abinda kike nufi kenan, bankai nasan me kika sanyawa ba, kin mance ke tawa ce kuma ni naki ne. Ke sirri nane, komai naki kuma mallaki nane, auren ki fa zanyi. Idan baki yarda dani ba wazaki yarda dashi…” bata tsinke Shiba haka yayita magana dayaga batada niyyar magana saiya kashe wayan. Da sauri ta kirashi tanaso ta bashi hakuri amma yaki dauka. Haka tayita masa miss call guda 15 amma ko gezau. Yanda tasa shi shiga wani yanayi haka shima yau saiya bata mata rai. Tabbas yasan yau bazata iya barci ba, ya lura ita mace ce wanda bata san gaba k0 aki mata magana. Abin yana takura mata ta kasa sukuni ainun.
Laila ta tashi cikin dare taga tana kuka, cikin haushi ta soma balbale ta. “wai ke meyasa bakya daukan darasi ne, sai kinyi mugun abinki kizo ki ishemu da kuka”
“Bafa kisan meya nema wajena ba, yanzu an daina soyayya tsakani da Allah kenan” tace cikin shesheka. Wani makoko a wuya ya makale ma Laila kamar tayi ta dukan Haske. Yadda take ma Bilal kuka zaka sha ita ta fara soyayya, kullum saiya sakata kuka. Abin da takaici sosai wai Ace batada sana’a saina kuka.
“Toh koma menene yace maki ki rufawa kanki asiri ki yardan mashi, kowa fa yana soyayyar nan bake kika fara ba. Mai daki shiya san inda yake mashi ciwo. Duk abinda yake zai iya samu a wani wajen bafa ke kadai kike da ita ba” daga nan ta buga uban tsaki ta kwanta barci abinta.
Bayan nan barci ya samu ya sace Haske, bata farka ba sai asuba wanda ma Laila ce ta tadata 5:30am. Dakin bashida wani girma tunda a zaure yake, katifa 6 inches ne aka shimfida sai zanin gado lanyayye tareda bargo ‘kafl amarya laushi’. Sannan an masu durowa daga gefe inda suke saka kayan su tareda akwatuna a saman wajen. Kana akwai shoe rack da bag hanger. Sai labule da ledar kasa.
Nan ta tashi tayi sallah tanata lazimi mai uban yawa. Koda yake duk matsalar datake ciki wani zaiso ya tsaya a matsayin ta. Wajen shida ta tashi taje cikin gida ta janyo ruwa a rijiya, tunda solardin dake Layin ba’a kunna ba. Wani mutum ana kiransa Baban Hiya shike in charge. Dattijo ne mai shegen jaraba yayi babakere a wajen kuma abin gwamnati ne. Ruwan wanka ta daura a heater kafin a dauke wuta.
Sannan ta kama aikace aikace wanda tace su bar mata watau Sharan tsakar gida, nan tabi ta share fes kafin nan ruwanta yayi saita juye sannan ta daura ma Laila nata. Dama Laila bata komai a ganinta tanada kannai birjik.
Da gari ya waye Sadiya yarinyar Saifullahi ta murmure sosai kamar ba ita ba. Abin ko yayi masa dadi saboda takwaran mahaifiyar sa ne. Sunci biredi da tea da kwai wanda Sameera ta siya da kudin ta sunyi Nat. saiya Kai su Abul Khair da Mubina makarantan su dake cikin Unguwan. Uniform dinsu green ne mai layi layi dinkin pinafore tareda hijab na mata, maza kuma necktie da Barrett. A lunchbox dinsu kuma ta soya masu indomie da kwai wanda duk ita ta siya.
Bayan sun tafl ta tashi ta kwashe kwanonin. Nan ta soma aikinta tanayi tana tunanin mijinta. Tabbas akwai abinda ke damunsa amma babu halin ta tambaya. Koma menene fatan sauki take Allah ya bashi.
Wajen 9:303 ya shiga wanka a lokacin ta gama gyara kitchen, nan tayi maza ta share falo da dakinsa kam ya fito, dayake shi mutum ne mai dadewa a ban daki saiya shafe awa kamaryana birne mutum. Koda ya fito blue shadda da hula dasu boxers dinsa yana kan gado yana jiransa, baisan sanda murmushi na jin dadi ya kufce masa. Ya dauki wayar sa yana duba WhatsApp sai yaga msg din Laila. Harya soma murmushi saiya kanne fuska. A duniya baya san mutum mai kawa zucci, kullum kana cikin roko.
Haka yayi mata transfer din 10k wanda tun wancan satin tayi masa maganar abin. Sameera kam bayan ya fito itama ta shiga bandakin, anan ta tsala wanka tayi kwalliya simple. Kyakkyawar mace baka ajin farko bugun billboard. Duk yanda ka kalle ta saika sake. Bakin ta mai kyau ne ga sheki, sannan tanada bala’in fara,a.
Yazo zai fita kenan sai ta tambayeshi ya bada kudin mai gyaran kofa da kuma kayan abincin yara na break saboda sun kare. Cikin masifa ya soma magana, “Bazan bada ba, koko ni kadai nake zaune cikin gidan?” saiya zura takalmin sa yayi gaba.
Abin ya mata ciwo saboda a bakin dakinsu yayi haka kuma ga makota sun fito kofar dakinsu, koda yake indai da sabo sun saba ganin abinda yafi wannan.
lta kam Laila taga alert na banki saita daka tsalle a ofis, amma kuma sai fuskanta ya canza dataga rabin kudin. Tashi tayi daga teburin aikinta taje chan waje domin ta balbale shi. Yana tuka motarsa zashi wajen aikinsa na ruwa(pure water)
Da azama ya dauka yana jiran ta watso masa kalaman soyayya, ita kam dayake yar musawa ce ba abinda tayi ba kenan. “Haba rabin raina ai ba haka mukayi dakai ba” mamaki yayi ko godiya babu ta soma korafi amma saiya kanne.
“Ki bari idan munyi ciniki yau zan tura maki sauran yau” daga nan ta sakijiki ta soma masa kalaman dayakejira harda tambayarsa ina Yayarsa (Sameera)
Bushewa da dariya yayi saiya ce, “Wato harda ke a cikin zolaya ta koh?” “Dole na zolaye ka tunda ka gwammace kayita zama da ita”
“Wallahi ba haka bane kawai al’mura ce, duka dangina suna santa shiyasa, amma ko munyi aure babu ruwanki da ita dole tasan kece yar lele na” sosai taji dadin zancen harda dariya mai sauti tana layi da jiki. Sannan ya soma bata labarin yanda yau yayi mugun breakfast da shayi da biredi. Shine ya cigaba da cewa yasan da tana nan zata bashi karin kumallo mai rai da lafiya.
lta kam Haske maganar Laila ya soma tasiri a jikinta, kodai dama haka ake soyayya? Dole ka sallama ma saurayi jikinka kafin ka samu kanshi? Wani karamin murya a ranta ya raya mata toh idan ta gama sallama masa jikinta ya gudu fah. Nan kuma dai ta ayyana a ranta. lta dai tanaso ta kare mutuncin ta, bataso wani abu ya shiga tsakanin ta da wani namiji idan ba mijinta. Sau da dama takanji korafe korafe akan samari dake gudu bayan sun samu abinda suke so. Tabbas soyayyar zamani yanzu saika kai zuciya nesa idan ba haka saika halaka.
Sunyi waya da Bilal da safe wanda itace ta kirashi, anan tayi masa korafl akan rashin daukar wayanta. Ce mata yayi bayan ya kashe ya kifar kan katifa kuma dama silent yake. Shima yana da niyyar kiranta sai wayanta ya shiga.
“Wallahi mamaki kake bani idan na ganka da Haske, dama kana soyayya da farar mace?” Abokin Bilal ya fada.
“Ai mace iya mace ita ce baka, kawai dai Allah ya hadamu da wannan ne”
“Maza baka bani labari ba, an wuce wajen koh?” ya tambaya yana dariya. Kwafa Bad yayi saiya juya kai, daga bisani yace, ” A duniya ban taba ganin yar rainin wayo irin Haske bah, haryau babu labari sai wani kwana kwana take mun”
“Kai ya akayi hakan ta faru? Hotel zaka kama maku kaje kuyi eh ya ne”
“Mts, bazaka gane ba, kullum tana nuna innocent bazan iya fito mata baro baro ba. Amma a ina ka taba ganin za’a baka appointment bakayi interview ba? Alquran bazan aureta ba sai nayi tasting” Nan Khamis ya bushe da dariya harda tafi tabbas yasan Bilal kuma yasan ba zaiyi ganganci ya aure yarinya ba tareda yayi tasting dinta ba, dole suyi mata audition.
Bilal ya gyara zaman sa saiya cigaba, “Banda rainin wayo kasan ba gidansu take zama ba, an koreta saboda tayi abin kunya! Cikin shege tayi fah! Amma wai she’s a virgin dan iskanci, wai bama cikin gareta ba sharri akayi mata mts. Sannu Virgin Mary maman Jesus” saiya doka uban tsaki Khamis yayi shiru na wasu daki kai sai yace, “toh kai ya akayi ka sani? lta ta gaya maka?”
“Ba ita bace fah, kawarta Laila wanda suka tashi tare na tirke akan rashin zaman Haske a gidan su, amma shine ta rokan karna tunkari Haske da maganar saboda denying zatayi” “Kila sharrin ne” khamis yace saboda sam Haske bata yi kallar yar hannu ba. Sai dai kuma mutum mugun icce ne, kuma mugu baida kama. Wannan kenan! a
~~~~~~~~~~~-~~~~~
Hmm Shin Haske zata bama Bilal kanta kuwa?
Dama Haske ta taba cikin shege ko sharri akayi mata? Waye yayi mata wannan mugun sharrin?
lyayenta suna ina?
Ya auren Laila zai kasance da Saifullahi?
Duk kubiyoni domin jin amsar tambayoyin nan.