TSANGAYAR MATI
CHAPTER 8
Kamar wasa cikin Fadime ya tabbata, Inna har Asibitin Kauyen ta mika ta tare da Abule da Nene wadanda suka tike akan sai sun bisu sun ji da kunnuwansu. Itama Innar ba tayi gigin hanasu ba don tafi so suji abinda zai hana su bacci.
Ranar kam sun riga suyin gaba, zagi da tsinuwa ba irin wanda Fadime da Inna basu sha ba.
Tun daga wannan lokacin kuma sai sabon tashin hankali da makirci ya kara ballewa a gidan. Akwai ranar da Nene ta shigo da Kuliya cikin gidan, sanin cewa Fadime ba taso. Hakanan ta lallaba ta dora mata ita bisa gadonta tana cikin barci. Allah ne ya tsare da kwallayenta na jere basu zubo bisanta ba, saboda yadda ta dinga razana tana bige»bige a dakin. Karshe dai Inna ta cece ta da fitsari ya fiddo ta, ta juyo motsi barin Fadimen. Shi kuwa Mati yana can ya saki ganɗa dakin Abule. Sai washegari ne Inna ta sanar masa, karshe dai tayi maganin abin da cewa duk wacce ta kara kawo wani Abu gidan ko da ‘Bera ne, k0 tajewa Fadime ko Mati da bak’ar magana to a bakin aurenta. Da wannan aka samu bakinsu ya rufu suka koma rara gefe, karshe dai Nene ta tattara ta tafi wani kauye bikin kanwar kishiyar matar babanta.
Inna zaune gefen Fadime tana lallabata ta samu taci kwadon Zogalen data hadamata, ita kuwa Abule tana tankade Garin Tuwo tana wake-waken habaici. Fitowar Nene daga bayan gida ya sanya suka bita da kallo. Tayi daurin kirji da tsohon zanin da taci ‘yanmatancinta da shi duk a huje, kasan duk ya rarake har idan ka zura hannu a buli guda zai tabo mazaunanta. Fatarnan kallo daya zaka yi mishi kasan akwai nakiyayyar dauda da bai kammala fita ba,jikinta kuwa babu alamarya wanka. Sai kyalli takeyi da nason datti da hamami dake tashi.
“Ke jikar Maduga, wai wankan da ruwan Tabo kika yi shi ne?” Cewar Inna.
Juyowa tayi ta mata murmushi, sai kuma tayi gaba tana murzo wata nadaddiyar dauda a wuyanta.
“Ah’ah Nene magana fa nake miki.” Fasa daga labulen kabar ta tayi tajuyo tana kallon Innar, sai kuma ta hade mata hannuwa biyu tana roko alamun ta kyale ta.
“Uhm! Sabon salo, wai gemu a kafada, halan da kika je bikin rashin magana kika koyo? To ai gaba ta kai mu, tuntuben me carbi” Inna ta fada tana rike haba.
Ganin haka yasa Abule ture tankaden gefe, ta mike zuwa dakin Nene. Da shigarta ta same ta tsaye tanajan Jagira a girarta me kama data Tunku. Ai sai tayi turus da mamaki tana kare mata kallo daga kasa zuwa sama. Ta sha Atamfa koriya fatau, da dinkin rigarta irin na Lema, wani abin mamakin har kallabin irin na atamfar ne, ba wai wari da wari ba. Kwalliya dai irin wacce ko da tana Amarya bata taba yinta ba. Sai kamshin man kadanya ke tashi data mulkawa jikinta. “Wannan kallon fa? Banfa san irin kakannin kiba?” Ta fada tana kadawa Abule hannu ganin yarda ta kame. “A’a mamaki kawai nake, tunanina k0 dai kanwar Nene aka musaya mana. “Uhm! Kibar mamaki, kawai nasihar da Innata tamin kan zaman duniya da kiyama nake ta tunanowa yau.” “Anya kuwa Nene? Ke din ce kike tuna wanda ya mutu? Abokin kuka ai ba a boyemasa mutuwa. Ki fadamin abinda ya faru dake kika saki makaman haka? Ko duk tsoron kar Innar Mati ta kora ki gida ne?”
Ai sai ta gundumo ashar tana me ture daurin kallabin data dade tana murdashi En yayi kyau nene. “Ni wallahi har kin batamin rai, tsohuwar banzar can zan ji tsoro? To Talle Bodara ce ta bani maganin Bari, sharuddan cikar maganin shi ne ko daka Ni Uwar Miji za tayi kar na sake na tanka ta. Kin ganshi a bakin Masai ake barbadashi.”
Ta karashe gami da bankada kasan katifarta, wani kulli ta fiddo a bakar leda ta nunamata. Abule ta washe baki don tsabar farinciki. Ganin babu damar ihu ya sanya ta kaiwa Nene runguma sai dai tun kan ta kara sa hada jikinta da nata tayi baya da sauri tsabar tashin da Nene keyi kamar mai warin kashi.
“Dagaske ki keyi?” Nene ta tabe bakinta. “Ni idan na fadi abu nafi son ki yarda, zan miki karya ne? Nan da kike ganina bata wasa bace ba. Bari ki gani, wuyarta dai Fadime ta tsugunna saman Masai, ko kwado ne a cikinta sai ya fado.
Jin haka suka saki shewa gami da cafkewa, sai kuma da sauri suka rufe baki. “Um kinga bari naje kafin wannan Tsohowar karuwar birnin ta ankara.“ Dariya Nene tayi. “Ai mukam Allah Ya hadamu da suruka.”
Suka dara sannan Abule ta fice.
Shiru-shiru ciki zai zube anjima, gobe, bai zube ba. Ko ciwon kai Fadime ba tayi ba ballantana a kai ga ciki.
Ganin haka Abule ta yanke gwada tata sa’ar ko za’a dace. Nene ta bata goyon baya dari bisa d’ari, da wannan ta shirya tafiyar kwana daya da sunan ziyarar jikar abokiyar kakarta.
Dawowarta akayi sa’a babu kowa sai Nene a gidan dake faman zazzaga bala’i ta katanga tare da Delu wai Akuyar Delun ta shigo ta cinyemata shanyar da tayi ta kanzo.
Ganin Abule ba karamin dadi taji ba, itace har da rungumarta tana tsalle, da ace akwai mutane a gidan da sun sha mamaki.
Bayan sun kule a d’akin Abule ne ta hau bata labarin abinda ta samo.
“Ba karamar wuya na sha ba in fadamaki. Ban taba rawar ‘yan bori ba amma shege la’antaccen bokannan sai daya sanyani yi. Amma tunda kwalliya zata biya kudin sabulu da sauki. Bari ki gani.”
Ta balle barin zaninta ta fiddo kullin magani har biyu ta nunawa Nene.
“Yace na kwaba lalle da garin na daurawa Inna a kafa don rufe bakinta. Shi kuma
wannan.” Ta nuna dayan, “A hada Lemon Zobarodo a sanyawa Fadime a ciki ta shanye.”
Shiru ya biyo baya kafin Nene ta jinjina kai.
“Tabdijam! Aikija! Yanzu banda abinki ina mu ina iya haka? Ni kinga banda kwada zobo da kuli ba abinda na sani kansa, sai yau da naji ana lemonsa, kema kuma na san duk sammakal. Inna kuwa bata yanda zata amince waninmu ya dauramata lalle. lna maflta?”
Hmm