TAGWAYE CHAPTER 23

TAGWAYE




CHAPTER 23





Asad yana idar da Sallah yai Gangaren Aunty Rahila daman cikin damuwa yake sosai, dakyar yai Sallah yana idarwa kuwa ko Addu’a baiyiba haka ya ninke Sallaya yafito masallaci aguje babu inda ya tseya sai bangaren Mamy da sallama yashigo falo sedei Babu kowa anan, mikewa yai kai tseye zuwa d’akin Mainah a ransa yake Allah Allah yatatar ta tashi sabida idan wani Abu ya tsameta k0 kad’an ba’zai taba yafewa kansa ba. Cikin wannan tunanin yashige d’akin ko sallama babu, kace wurgoshi akayi daga waje. Shigewarsa ke da wuya yai Kacibis da Zaid, mutanen gidan duk suna nan ajere sekace wa’inda suke karban sadaqa, ya kallesu d’aya bayan d’aya, Yana maida ldanunsa kan gado kuwa yaga Ma’inah zaune agefen Yarinyar daya kade, ‘Kara bud’e ldanunsa yai sosai ya gogeta ko mafarki yake, Aiko yana ‘kara duba kan gadon ba abunda ta chanza Ma’inah ce 
take zaune tareda mara lafiyan. 
Cikin rud’ani yajuye yana tambayar Zaid” CEO Maisha ce tazo dubajikin Ma’inah? Ya’kara bude Idanunsa sosai yace” Amma ai Ma’isha bata irin wannan shigar kuma ako yaushe takansa Jan baki a lebban ba’kinta dahakan kowa ke banbantasu. To sedei kuma abunda ya’kara rude Masa kwakwalwa itace” Yarinyar da ya kade she looks exactly thesame as Mainah babu abunda ya banbantasu daga shigarsu harma da nitsuwar fuskarsu iri daya ce. “Kodei Ma’isha ce na kade? Asad ya’kara tambayar kansa. 
Mu ‘kanmu cikin rud’anin muke: Aunty Nasibah takatse masa tunanin tanacewa; Ba 
Ma’isha bace ka kad’e Asad Miemah ce. “Wacece kuma Miemah?. Tabe baki Zaid yai 
yanacewa; Amsarda muke bu’kata gun Mainah kenan, amma ta’kasa cewa komai sa’ta 
agaba tai tun tuni tana wannan kukan wanda baya ‘karewa. “ 
‘Kamata yai mukyaleta har zuwa lokacinda hankalinta zai kwanta. Aunty Rahila tafad’a inda kai tseye tamike tareda Aunty Nasibah, Anisa ma mikewar tai jiki a sanyaye ta shafa kan Ma’inah sannan suka fita, Zaid ma mikewar yai tareda Asad dikkansu sunyi Jugumm suna tafiya Yana bin Mainah da kallo shiko Asad yanabin Miemah da kallo ahaka har suka fito. 
Suna fita Mainah ta rungume Miemah, ta’kara fashewa da wata sabuwar kuka. Ahankali Miemah tabud’e idanuwarta nan da nan hawaye sukafara zubowa a idanuwarta “Teddy, Umma da Abba suna gidan yari” abunda tafara fad’a kenan, muryarta na karkaruwa tace'” Mominku ta koroni daga gidanta ayanzu ba’nida inda zanje. Share hawayenta tai tareda ajiyar zuciya” teddy kiyi hakuri ki rokarmin mutanen gidan nan su kyaleni incigaba da zama anan ko wanke wanke nayimuku ….. Bata ‘karasa furucintaba Ma’inah tasa hannu tarufe mata baki, Da mamaki a fiskarta yayinda ta’kara tambayarta” Umma da Abba suna gidan yari kamarya? 
Kai tseye Miemah ta gyad’a kai. Anan ta kwaso dikkanin labarin ta tsanar mata. A wannan lokacin kuka suke sosai abun tausayi suka rungumejuna sunata kuka. Sun dade cikin wannan yanayin Ma’inah ce tafara magana” Karki samu damuwa na tabbata Zaid zai barki mucigaba da dazama anan, ke dei ki kyalesu kada ki sanya damuwa aranki, da Momin da Maisha’n duk mutane ne Suma kuma wataran hakan zata iya faruwa dasu, ki mance da maganar su, ki kaddara su ba komai bane a rayuwarki batun Umma da Abba kuwa zan sanarwa Zaid da Asad na tabbata zasu taimaka mana, kada kisa damuwa aranki after all we can do it. Hannu suka hada Kai tseye sukayi tapi dashike sun saba dawannan tun suna tare. “Don‘t you worry we can do it fabs” hada ba’ki sukayi alokaci d’aya suka ‘kara fad’an “Teddies smile for whole peace. Wa’kar dasuka ‘kara yi kenan sannan suka Kara wata tapi, kai tseye suka rungume juna suna murmushi dashike sun dade basu samu damaryin wannan wakokin nasuba tun rabuwarsu alokacinda suke ‘kanana. 
Aisha tana Gidan yari Amma ta’kasa samun sukuni, tunanin halinda Miemah takeciki ne ya addabe zuciyarta, tunda tashige gidan yarin ba’taci ba‘ta sha, barci ma ba’ta samu isheshshe sai aikin kaiwa da kawowar da taketayi tana kuka da tinani sabida aganinta idan har bata bayyana wannan sirrin da Saminu yafad’a mataba ko kad’an ba zata samu sukuni arayuwarta ba, kuma ba zata taba yafewa ‘kanta ba, sabida Miemah ce aka zalunta ba kowa ba, ta taso cikin rayuwar talauci Wanda ko kad’an bata dace da matsayin taba amasayinta na Yar attajiri Sambo Maidugu. Ya zama dole Miemah tasan Iyayenta na ainihi kamar yedda kuma yazama tilas Maisha itama tasan Iyayenta wa‘inda suka haifeta takuma dawo ‘kauyen Mai Riga gidan Mahaifinta tacigaba da zama achan sabida ita tafi dacewa da wajen anan Mahaifanta suke rayuwa. 
Kwana uku kenan Aisha takebin layin Waya na gidan yari amma bata samu. 
Daman ta rike lambar Safeenah ‘kiranta zatayi kai tseye ta bayyana Mata sirrinda mijinta ya dade yana Goyewa. Amma ba’a barinsu suyi waya ako wace rana mutane biyar ko shida suke waya itako tunda tazo take rokansa amma babu wanda ya kula da damuwarta kowa sha’anin gabansa yakeyi. 
Haka ta rungume kaddara tacigaba dazama tana kuma addu’oi, Akan Allah ya bayyana wannan sirrin ko tawace hanya. 
Maisha ta Sha barci isasshe babu takura babu matsi, ta shafa kusan awanni goma zuwa Sha biyu tana barci babu wanda yatasheta, wayartama kashewa tai sabida ba’tason hayaniya. Karfe shida da minti talatin da yammaci ‘ta tashi jikinta babu karfi, ahaka tamike tanaja dakyar tai bathroom inda tawasa ruwa ajikinta tareda alwala, Kai tseye tadawo d’aki nan tahad’o duk sallolinda batayiba alokacinda take barci, sallar azahar, la’asar harma da magribar ta’yi. 
Tsusayen cikinta sai kuka suke tana Jin yunwa sosai amma ahaka ‘tadaure tana zaman jiran Momy tazo wajenta sabida ta rarrasheta sukoma kamaryedda suke a da, tunda tatashi take mamaki, atunaninta tun dasafen Momi zatadawo ta rarrasheta amma ta’ji shiru, Sanda tajira har nawasu awanni sannan barci ya d’auketa. 
Ta’yi barci mai zurfi har izuwa wayewar gari tana Sallah tayi ajiyar zuciya tafito falo ahaka tai zaman jira har zuwa Iokacin ‘Kari nan ma Momy bata fitoba ita kadei ta ‘karya, ayanzu dei babu abinda zuciyarta bata saka mata “Ko dei fushi momcy tai da ita? To Amma Abun mamakin kuma, kwata kwata wannan ba halin momcy bace tunda ta taso momcy bata 
tabayin fushi da itaba ko sau daya…. 
Tana cikin wannan tunanin yayinda Momy tafito daga d’akinta, uffan momy bata 
tankamata ba Kai tseye dining table tawuce nan ta zauna tana ci k0 ajikinta, duk dacewa ita ‘kanta wannan abubunda takeyi karfin zuciya ce ba‘wai har cikin ranta takeson yin hakan ba, so take Ma’isha taga’ne kuskurenta shiyasa kwana biyu ba ta shiga sabgarta. Duk dashike tunjiyan take zamanjiran lokacinda Ma’isha zataga’ne wannan hanyarda ta d’aura ba hanyar bullowa bacejira take Ma’isha tazo ta ba’ta hakuri sabida sukoma yedda suke Ada. 
Shiru Maisha tazauna tanabin Momy da kallo Yayinda take tuna irin soyayya dakuma bin bayanta da Momy keyi ako da yaushe idan tayi laifi Momy ce take goyon bayanta dazaran kuma Daddy Yana fushi da ita Mommy ce zata nemo hanyarda zatabi ta deideita tsakaninsu. Wa’innan dalilan yasa Maisha take matukarji da Momy Kuma Ko da zasu bata da duk mutanen duniyan nan dazaran suna tare da Mommy batada wata matsala a rayuwalta. 
Momy tana kammala breakfast tamike babu abunda tafad’a, Maisha ‘kanta tana kokarin yin magana amma dagin kanta ya hanata, haka tazuba Mata ldo yayinda Momy tawuce daki, ta dade bata fitoba, sai chan dajimawa taflto a shirye sap! Tareda key motarta, Anan Maisha tamike Kai tseye tai ajiyar zuciya tace’ Momcy fushi kikayi dani? 
Ta’so tai magana amma kawai danna zuciyarta tai she is really burning inside haka ta batsar babu abinda tafada bude kofar tai kai tseye tafice, Maisha ma bata tseye anan ba fitcewan tai aguje tashige gabanta “Momcy I’m sorry bazan ‘karaba …… 
Bata ‘karasa furucintaba Momy tasha‘reta agun, inda tawuce gun motarta Kai tseye tashige, aganinta yin hakan ne zaiyi tsanadiyar shiriyar Maisha. Jan motar tai zuciyarta na konawa ta ciki yayinda tafara tuki, inda tabar Maisha tseye awajen. 
Tabe baki Ma‘isha tai tazuba Mata ldo cikin sananin mamaki tanabin Motar da kallo har tseda tabacemata “Gaskiya akwai matsala” abunda tafad’a kenan sannan takoma d’aki jikinta na ‘karkarwa yayinda ta tattaro kayanta kamar kullum duk ta sa’su cikin akwati. Tana fita Babu inda ta tseya sai garraj nan tabude butt ta jefe akwatinta tashige motar kai tseye tafara tuki. “Zaid Kaine gata na, ayanzu ba ‘nida wata gata aduniya bayanka, Gani gareka my prince Charming Zaid Muhammad Zabir, Ma ‘inah lokacin barinkigidan Zaid tazo 
Tsit! Zaid yazauna Yana bin Mainah da kallo har Sanda ta gama bayyana masa ko Wacece Miemah, dashike musamman yau ya’kirata har zuwa falonsa kuma babu kowa anan daga shi sai ita sai kuma securities d’insa, Ma’inah ta sakejiki dashi ayau sosai sabida Babu abunda tarage masa a labarinsu kap! Ta kwaso d’aya bayan d’aya ta tsanar masa. Zaid ya matukar tausaya masu sosai wannan labarin nata yasa soyayyar Ma’inah ta’kara shiga zuciyarsa sosai. Itama Ma’inah ayau ji tai babu wani mahalukinda zata iya soyayya dashi a duniya bayan Zaid tunda tazauna idanuwansa take gani tareda mamaki sabida bata taba ganin kyawawan idanu ko a mafarki makamancin idanun Zaid ba, Ga’shin jikinta har tashi suke ayayinda tadan sauke idanuwarta zuwa dan ‘karamin lebban bakinsa shima dei ‘kasa 
kau da idanuwarta akansu tai, tana ‘kara mamakin kyaun sa. 
Gyara muryarsa yake tun tuni, Sabida ya lura Ma’inah ta dad’e tana kallonsa, ya ‘kara gyara murya Amma har yanzu bata kauda idanunta daga kansaba, Murmusawa yai shima yakure mata Ido. 
Tana ganin wannan murmushin nasa wanda suka dad’a bayyana dimples din fuskarsa, batama san lokacinda murmushin ta bayyana a fiskarta ba itama “Masha Allah” tafada yayinda ta’kara kurewa dimples d’in nasa ido. 
“Miss Ma’inah how do I look? Zaid yafada kai tseye. 
Cute, Mainah ta amsa masa babu tsoro ko fargaba. Mikewa yai kai tseye yazauna kusa da ita, inda ya d’aura hannunsa kan kafadarta, nan Mainah ta sheki wata irin kanshinda tunda take rayuwa a duniya bata tabajin irintaba. Yana wannan murmushin nasa yace” Thank you so much Mainah. Ya’kara kuremata ido sosai yayinda yad’aura hannayensa kan tattausar fiskarta Wanda take sheki da haske tamkar auduga ya kashe muryarsa kamar kullun cikin nitsuwa yace: Mainah you are the most beautiful creature in the whole universe. Sanda yaja wata doguwar nunfashi sannan ya’kara cewa” Zaid Muhammad Zabir is the most luckiest man alive, na gode Ma’inah kece tsanadiyar farin ciki na I love you so much. 
Bai karasa kalamansa ba Mainah ta rungu’meshi tana farin ciki sosai ji tai tamkar a mafarki, shima Kai tseye ya doura hannayensa abayanta yanakuma rad’amata a kunne “Yea Nine Zaid Muhammad Zabir ba Mafarki kikeyi ba Mainah Sambo Maidugu. Itama akunnensa 
tace Masinjarka Koh? Shiru yai nad’an wasu mintuna sannan yayi dariya akunnuwarta ya rad’a “Kinsan meyasa nadauraki a masayin masinjata sabida inaso akoda yaushe 
mukasance muna tare dani dake no third partner.
Murmusawa tai inda ta’kara sauke ‘kanta kan shoulders dinsa tana feeling over protective. 
“Kai dan talakawa, banza shashasha wallahi na’fika iskanci zaka budemin kofa ko kuwa?” Tabe baki securitin gidan Zaid yai ya’kara dubata sosai “Hajiya kince sunanki Ma‘isha. Bai karasa kalmarsaba ta katseshi; kwarai kuwa da gaske sunana Maisha Sambo Maidugu, kada kuma kasa’ke kirata da Mainah sabida babu abinda yahada mu da ita ka fihimta sosai, idan majahilcin ce tai maka yawa you can repeat after me “Ma’isha Sambo Maidugu. 
Dakata Hajiya gaskiya indei Maisha ce ke da gaske, toh Oganmu Alh Zaid yace kada abarki kishigo, we are sorry madam kawai kikoma inda kika fito. 
Fitowa Ma’isha tai daga motarta, cikeda masifa tarike rigarwannan security babu tsoro a 
fiskarta tace‘ wallahi Malam ka kiyayeni ninan dakake gani Matar Ogan naku ne dakansa wallahi idan kana kokarin rainamin hankali. 
Matarsa kuma? Yayi aure neh? 
Ba’a saniba “Maisha takatse shi; so kake kasamu damar magana dani k0. toh wallahi nafi karfin ka kaje chan gidajen getto kanemi matsiyaciya irinka kuyi magana, kawai Malam idan zaka bud’emin kofa kabud’e Dan rainin hankali kawai. 
Haka Maisha da wannan securitin suka fara hayaniya har Sanda mutumin yakusan dukanta tana turesa shima haka yake tureta sunata masifa. Nan da nan Sauran securities na ciki duk suka fiffito, Sanda suka nuna mata bindiga sannan ta gane hankalinta inda yake. Ogansu ne ya fito “What the heck is happening here?
“Wannan yarinyar da Oga yace kada abari tashigo ne tazo nan tana rashin kunya. A nitse ya matso har kusa da ita “Malama Idanfa kinason zaman lafIya kawai kija motarki kitafi sabida kamar yedda kika ganmu anan gate one (1) idan munbarki kin wuce Kuma thesame thing zaki tarar a gate two (2) akwai kuma gate (3) har zuwa gate (9) inda nan ne asalin sojoji suke militaries masu tsananin dokoki Kinga idan ma kinshigo nan da kafafunki Zaki ‘kara dawowa ba’tareda karasowa cikin gidan ba. 
Ja da baya Maisha tai yayinda taja masa wata doguwar tsaki tanacewa” Wallahi zakuyi da’nasanin wannan wulakancinda kukayi min idan Zaid ya auroni duk sai an koreku daga aiki mayunwatan banza mayunwatan wofi …… ‘Daga hannu securitin yai zai kai mata mari taf to “Kudakata”. Aguje Maisha tai bayanta “Momcy kasheni zasuyi ki taimakamin” ta kashe murya cikin salon Kisisina. 
“Sun isa su kasheki. Momy ta ‘karaso har gun ogan nasu tafara magana cikin matsifar bacin Rai “Uban wa yabaku damar wulakanta Yata? Maisha tafi karfinku wallahi taya zakusamin yarinya agaba kuringa jibgarta babu gaira ba dalili, wallahi duk sai an daure ku matsiyata, babu wani mahaluki a duniya wanda zai wulakanta jini na ya kwana lafiya wallahi sai nasa Zaid ya koroku dika daga aiki because you are not responsible at all. 
Tunda tafara magana baba fashi sai zuba take tamkar lalatacciyar fanfo nan da nan tafarajin ciwon kai “Wai yau jininta ake wulakanta how dare them” Kalmar da take kara nanatawa tun tuni kenan “Se nasa an daureku, Yata tafi karfinku wallahi. 
Hajiya diyar takice sai a hankali, yarinya ba tarbiya, kwata kwata batada manners, mu nan 
datake gani aikinmu mukazo yi ba wai matsifa ce takawomu Nan ba kuma idan ta’kara laifi makamancin wannan wallahi doka tabamu damar mu kasheta. ‘Daya daga cikin securities din ne yasoma ba‘kin sa” Kuma mun kashe banza aradu. 
Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun’ rungume Maisha Momy tai Kai tseye tafara zubar da hawaye “Lailaha illahu Muhammadu Rasoulul Allah (SAW) Yattawa zaku kashe lallai kun cika yan iska, yanzu zan ‘kira Zaid, nai masa magana wallahi zamanku ana gidan ta‘kare. Hannayenta na ‘karakarwa yayinda ta’kai layin Zaid Kai tseye tafara ‘kiransa…. 
“Allahu Akbar” Aunty Nasibah da Aunty Rahila suka hado baki alokaci daya sukace “Lallai ko wannan Matan tacika mara mutunci, Safeenah nan anyako tana tsoron Allah? 
Asad kuwa share hawayensa yai bayan jin wannan labarin Miemah “Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun’ Mikewa yai kai tseye ya matso har kusa da ita yana share mata hawaye “Miemah just trust me zan taimaka miki, Insha Allahu lyayenki zasu fito daga gidan yari nan badajimawa ba. 
Miemah ta’so kizo nan. Cikin sanyin jiki ta‘karaso inda take, Kai tseye Aunty Rahila ta rungu’meta “ki share hawayenki Miemah, zan rike ki Amana tamakar Yata, har zuwa ranarda Allah zai fito da Ummanki daga gidan yari kada kisamo damuwa kinji kisake jikinki, Kuma daga yau Zaki iya kirana da Mamy nazama maharfiyarki, Zaid shine babban Yayanki, dake da Mainah kuwa daga yau kunkoma yan biyu kamar yedda kuke alokacinda kuke ‘kanana. Murmusawa Miemah tai cikin farin ciki tace”Na gode Mamy sedei kuma Banga yayan nawaba.
Asad ne yai sauri ya amsa mata yana murmushi yace” Ai Yayanki da twin sisternki suna nan cikin lambu suna more rayuwarsu. Lambu kuma mesukeyi achan? Aunty Rahila takatseshi ” Aunty bazaki gane bane Miss Miemah na’san ke kin gane abunda nake nufi Koh? 
Murmushi Miemah taimasa tareda gyad’a kai ; Na gane. Tafad’a cikin zazzakar muryarta. Asad baiyi maganaba, daga nan shiru yazauna yana binta da kallo “Masha Allah” ahankali yace” Finally Asad yasamo Mata alhamdulillah, Miemah da Asad hashtag MieSad Wow! agaskiya mun dace sosai Miesad. Ya’kara lumshe ldanunsa yashiga duniyar tinani. 
Aunty minah save me, save me. Munah tai wajen Ma’inah aguje tana kelkelewa da dariya yayinda Ma’inah tadaukota sama suka fara gudu Zaid Yana binsu abaya. Cikin ruwa suke, irin madaidaicin ruwa hakan nan, swimming pool ce wacce aka tsarata 
musamman tawasa, akwai balloons dama sauran ababe na wasa a cikin ruwan. 
Dashike Zaid yanason ruwa sosai, ko ina cikin gidansa akwai swimming pools, wannan itace swimming din dake bayan gidansa ya yi’ta ne kuma musamman sabida yaringa shiga Yana wasa aciki shi da Munah, ba’a barin kowa yashigo Gangaren sai bodyguards d’insu dakuma y’an Sanda bayansu babu wanda yakeda damarshigewa Gangaren sai kuma abokinsa Asad shima wataran yana zuwa suyi wasa. 
Zaid ya’kai Ma’inah bangaren ayau, dashi da ita dakuma d’iyarsa Munah. Kana shigowa bangaren wani irin sany’i zakaji ajikanka, wurin na kanshi sosai gakuma kyaun ta “Soo romantic. wajen yayi mata sosai babu laifl, haka suka shige cikin ruwan sukayita ta wasa, itama Mainah akwai ta dasan ruwa, sunyi wasa sosai acikin ruwan, sunkumayi hotuna da dama, Munah ta saki jiki da Mainah nan da nan ayanzu ita ‘kanta cewa take “Aunty Minah is the best Aunt ever”. 
Assalamu Aleikum sir. Wani Soja ne mai bakin Kaya yataho inda suke ” Sorry for the interruption sir, wayarka ce take ringing tun dazun nace ko ‘kila important call ce daga wajen aiki. Fitowa cikin ruwan Zaid yai kai tseye, daman jikinsa akwai kaya (Swimming suit) “waye ne? Sojan yana share masa jiki da towel yayinda yace M2 aka rubuta. 
Miko hannunsa yai ya ‘karbo wayan “ko meyasa Mahaiflyar Mainah take kirana awannan lokacin? Bai rufe bakinsaba wayarta’kara ringing, d’agawa yai da sallama kamar yedda ya sa’ba. “Zaid muna kofar gidanka Yan Sanda sun hanamu shigowa don Allah kafito ka samemu zasu kashemu. 
Bata jira amsarda zai bataba ta katse wayan kai tseye. 
Tabe baki Zaid yai cikin mamaki yace’ Taya za’a hana Mahaifiyar Mainah shigowa, wato securities din gate one sam basa’jin maganata ayanzu ko wa yabasu damar yin hakan oho? Yana magana shi kad’ei har tseida ya’karaso swimming pool dashike bai iya ihu ba Yana
magana da karfi ba, Sojan nasa ne yai ihu ya’kira Ma’inah “Madam kufito”. 
Mainah taji dad’in wajen sosai ba’tason fltowan amma kawai yazamo mata dole, d’auke Munah tai suka fito. Da ‘kanta tasharejikinta da towel, duk dacewa Zaid ba’yason hakan ita ko bata sa’ba da wannan irin ga’tan ba she feels awkward sometimes. Shiyasa kwata 
kwata Ba’ta barin suyi mata abu komai da kanta takeyi cikin kwanciyar hankali. 
Munah ko daman cikin ga’tan tataso tana fita akazo da towel d’inta, nan da nan suka share jikinta tsap!!! sannan Naninta tazo tad’auketa suka shiga ciki domin achanza mata kaya. 
Ma’inah ta’gama sharejikinta cikin Kwanciyar hankali sannan taje wajen Zaid Kai tseye inda yacire Jacket dinda aka sakamishi yasanya mata ajiki sun fara tafiya yayinda yace; Mahaifiyarki tazo, tana waje yanzu tabugomin, Wai an hanata shiga sabida haka kawai ki chanza kifito muje tare. 
Wata Mata ce mai sanyeda Uniform tazo gunsu “Madam kayanki yana d’aki a second floor ki biyoni. Saida tajuye ta kalli Zaid ya gyad’a kai”Go ahead. Sannan ne tabiyo matar a baya suka shige lifter, suna flta matar tanuno mata d’akin. Babu tsoro Ma’inah tashigo “Wow! Doguwar nunfashi ta saukar tsaban had’uwan d’akin, ta sake ba’ki tamkar bakauyiya tai ta kallace kallace da tabe taee, Ta sany’a rigar tafito Shar! a jikinta, a yau ji take babu wata macenda tai sa’a a duniya irinta. 
Zaid ya nunamata soyayya da kulawa wacce ko a mafarki bata ta6a tunanin zata samo irin wannan masayin a duniya ba shiyasama soyayyar Zaid take dad’a karuwa aranata every second ….. 
“Madam oga yana jiranki awaje” kwankwasa kofar d’akin dataji akeyi ne yadawor mata hankalinta, inda a guje tafito, tana sau’ka ta tsameshi a falo, duk da irin had’uwar da tai Zaid bai ganta sau biyu ba sabida kada shaidan yashigo ciki, rike hannayenta yai suka fita. 
Suna shiga mota wayar’tasa takara ringing, “Assalamu Aleikum Mamy, yai sallama cikin sanyin murya kamar yedda yasa’ba. Subhanallahi, abunda ya’kara fad’i kenan. Toh shikenan muna nan zuwa. 
Mainah batayi maganaba har sanda tajira yagama wayar tukunna tace’ laflya? 
Twin Sister’n ki tadawo nan gidan dazama. Dasauri takatseshi”Miemah kenan kake nufi? Girgiza kansa yai “Ma’isha. 
Hadiye miyau Ma’inah tai “Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun yaushe hakan tafaru? Kuma tayaya. Babu abunda Zaid yafad’a tabe baki yai “Haka dei mamy tafad’a. 
Shiru Ma’inah tazauna sai zura idanuwa take dashike tafi kowa sanin halin Ma’isha Kuma 
idan har dawowar tai da gaske daga yau farin cikinta ta gushe kenan da ita da Miemah 
sabida ta’san Maisha ba‘zata taba barinsu suji dad’i acikin gidan ba dazaran tana nan kuwa Zata iya yin tsanadiyar rabuwarta da Yayanta (Zaid) …..

IYA ABUNDA YA SAWWAKA A YAU KENAN
®©NEXT CHAPTER SPOILER ®© 

“Yau lafiya kuwa nakejin banguna da ta’shin kida haka ta Bangaren nawa. Bata ,,, yai yace: ba’yan kuma kowa yasan babu abunda nafl tsana a duniya irin hayaniya. Haka ya’kara tambayar kansa “Cikin gidan Zaid Muhammad Zabir din ne yau ake irin wannan sautukan? 
Mamaki duk ya ishi Zaid so yake kawai ya’karaso cikin gidan yaga wainar da ake tauyawa. Dasauri yasa drebansa yafara tuki, suna shiga yafito cikin sananin mamaki yaduba gidan sama da kasa duk an sa decorations se walkiya take anata buga ganga masu waka sunata waka harma da yan rawa. Kai tseye ya tambayi wani d’an sandansa lafiya meke faruwa cikin gidan? 
Mahaifinka ne yasa aka shirya komai, duk wannan mutanen gayyatarsu yasa akayi da kansa. Mahaifina? ‘kara d’aure masa kai mutumin yai, amma bai ‘kara tambayarsa komai ba, aguje yanufo Sha’shin Mahaifin nasa, yana shigowa falon, wasu yan kauye ya tarar sunata ci tamkar basu taba ganin abinci a rayuwarsu ba. 
Zaid Yana shiga suka mike, Zuuuu! suka kewaye shi tamkar masifa “Ga ango, Ga ango, su ango ansha kanshi, Mintuna ‘kalilan yarage a daura aurenku. Toshe bakinsa yai harma da hanci, Yanaja da baya ahankali ahankali baiso ya amsa musuba amma irin maganganun dasukeyin yasa shi dole yace” ‘Wai mekuke nufl ne? Aure kuma? Dani dawa? 
Mutanen had’ Baki sukayi alokaci d’aya sunata dariya “Laaaa jimun Ango tamkar bai saniba, ‘Daurin aurenka mana da Malama Maisha yar gidan dattijon arziki Sambo Maidugu. 
Yace watttttttttt

Hmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *