TAGWAYE CHAPTER 12

TAGWAYE 
CHAPTER 12
Kofar dakin Maisha yake bibbigewa yana ambaton sunanta ahankali. Kwance take kan gado tana kunbura haushi da damuwa sunyi mata yawa, jujjuyi take tin dazun ko zata samo mafita Amma dabarunta duk sun ‘kare “babu wata mafita face ta sayar da gidanta, ta sai madeideicin gida sannan tayi anfani da sauran kudaden. 
Ma’isha kibude, kudi nakawo miki naira Million Uku kamaryadda kike bukata”. Muryar Kawu Saminu data riski kunnuwarta ne yamatukar tsoratata, inda nan take tamike koro’koro ta zaro idanuwarta a tsorace tabude masa kofa “Hey me kake anan? Kuma Wasu kudade kake magana, Ta fada ahankali. 
Jakar dake hannunsa yamiko mata yanacewa: na saurari duk maganganun dakukayi da Mahaifiyarki cewa kina bu’katar kudi kuma baki samo kudaden awajen saba shine naciro nawa kudaden dana tara nakawo Miki domin kiyi anfani dasu. 
Magana take muryarta ciki ciki domin kada wani yaji tattaunawar dasuke “Ba’nida bu’katar kudadenka sabida Kai ba kowa bane awajena kuma ni Maisha ba matsiyaciya bace irinka kawai katafi kabani wuri. 
“Ma’isha inaga har yanzu baki fahimci Mahaifinki bane, Yai saurin katseta: kwata kwata yanzu Sambo baya yi dake , kin rigada kin watsa masa ‘kasa a ido babu inda kudinsa suke ‘karewa se gun Yar lelensa Ma‘inah kuma gashi yakaita chan gidan daula da arziki tana more rayuwarta keko kina shan Bakar azaba anan. 
Me kake nufi? Ma’isha ta tambayesa cikin rudani. Bazaki taba ga’ne abinda nake nufi ba har se kin ansa wannan kudaden danayi niyar baki. Yafada ayayinda yake Miko mata jakar ‘Idan kin ansa wa’innan kud’aden toh ko zakiji komai gamida Ma’inah kuma zan sanar dake inda take ayanzu. 
Tabe Baki Maisha tai cikin mamaki tace’ Bazan karbi ko sisi daga wajenkaba sabida Nafi ‘karfin kaimin kyauta koda ta naira biyarce wallahi matsayinka bata kai hakaba tukunna, the only solution shine ka sai gidana Million Goma babu kari ba ragi sannan ne zan anshi kudadenka. Murmushi Saminu yai ‘Babu komai na yarda zan sai gidanki amma abisa sharadi guda ko kadan kada kisake kifadawa Mahaifiyarki ko Mahaifinki hartse kin mallakamin takardun gidan. 
Jinjina Kai tai “Deal na amince Kuma nima inada tawa sharadin ‘kada ka sake ka sanar da Daddy Shirin mu kuma Koda kanunamin gidan daya boye Ma’inah kada ka sanar dashi Until I destroy her life bit by bit. 
“Zaid why did you stop the car? Ma’inah ta tambayesa cikin mamaki. Babu musu ya amsa ‘I want to make a call. 
Ganin bai taba bata ansa kai tseye hakaba se yau yasa tai farin ciki har cikin zuciyarta, tana murmushi yayinda tace ‘babu komai just make it fast kada mu makara. 
Jinjina kai yai shima yana murmushi. 
“Kodei budurwarsa yake ‘kira? Ma’inah ta tambayi ‘kanta ahankali tace’ Anyway koma wacece batayi dacen mijiba he,s such an arrogant. 
“Helo Asad I’m sorry na dan makara amma ina hanyan zuwa, yanzu Zan ‘karaso ka tabbata ka’tara late comers, musamman sabbin ma’aikatan nan wanda zasu fara aiki yau 
because today is there first day in office bai ‘kamata suyi latti ba. 
Shiru yai nadan wasu mintuna sannan yace Good sunyi kokari and who among them is absent? kace Ma’inah Sambo Maidugu? 
What? Kallonsa Ma’inah tai cikin rudani “Come on Zaid ba office din muke zuwa yanzu ba? Kafad’a masa Mana Asad is a good man he will definitely understand. 
Manna mata hauka yai “Alright Asad idan tashigo kawai kasa aturomin ita sama. Da wannan ya katse wayar sannan yafara tuki. Shiru Ma’inah tai tana binsa da kallo tareda mamakin halinsa babu wanda ya’kara cewa komai harseda suka ‘karaso. Motartana tsayawa bo’sawansa suka bude, inda suka rufa masa baya ana binsa tamkar ya’fi kowa masayi a duniya. 
Fitowa tai ahankali take tafiya har seda ta ‘karaso ciki, seketeriya ce tai mata magana “Ma’inah Sambo Maidugu why are you late? ‘Daga ido tai takalleta sannan ta tasau’kar ahankali ‘am Sorry ma,am ba’nida lafiya shiyasa Amma… Just shut up you are not responsible at all, kitanadi bayananki zata anfaneki idan CEO ya tambayeki dalilin dayasa kikayi latti amatsayinki na Masinjarsa. 
Gani nayi CEO da kansa yanzu ya’karaso. Ma’inah ta amsa kai tseye. 
Are you trying to be stubborn, nafiki matsayi anan confanin Kuma yazama dole ki girmamani Ma’inah Sambo Maidugu. 
Babu abinda ta’kara fadi tafiyarta tai kurun tayi banza da ita, inda tahauro sama bangaren CEO Villa. Kad’an yarege suyi jiki da jiki da Asad yayinda yakawo kafa yana kokarin gangarowa “Miss Ma’inah Alhmdulillah daman wajenki nanufa, Why are you late, ran CEO yabaci sosai fa. Yafada cikin nunfashi daya. 
Tare mukazo, Ma’inah ta amsa masa Kai tseye cikin sanyin murya tace ‘ni kwata kwata bana gane masa meyesa yake wulakantani haka ba? Kodei mantawa yakeyi nima dan Adam ce irinsa meyasa baya darajani. Shiru Asad yayi yatsaya yana binta da kallo har saida takammala yace “Ma’inah ba’nasan ganinki cikin bacin rai, Zaid Mutumin kirki ne you should just be hard working kuma kibishi a hankali Zaki ganemasa lnsha Allah. 
Gyada kai tayi bata kara cewa komai ba, Murmushin ‘karfin hali tayimasa sannan tafara tafiya, babu inda ta tsaya se Ofishin sa, inda tai sallama tashigo kai tseye. Yana zaune kan kujera yana daddanna computer dake gabansa. Tana shiga yamike “Why are you late? 
I‘m sorry, ta amsa cikin sanyin murya. 
Guntun tsaki yaja sannan ya‘kara kure mata ido ‘Laifi nane sabida tun afarko ban baki ainihin lokacinda ya’kamata ki ringa zuwaba Amma daga gobe as my messenger you will be here exactly 6:00am I’m I clear. 
“Yes sir’ ta amsa batareda ta daga Ido ta kalleshiba. 
“Alright make me some coffee’ Babu musu tajuye “Excuse me” ya ‘kara tse da ita ‘ga wannan aiyukanda zaki ringa yine amasayinki na ma’sinja; Yamiko mata wata takarda. Hannu biyu tasaka da ban girma ta’karbi takardan sannan tafara tambaya “Excuse me, dan karamin AC nan duka sannan ki ‘kara gudun fankokin suma. 
Mamaki Ma’inah tai ganin sanyin d’akin yayi yawa, yanzu ma dakyar take daurewa tsaban sanyin ofishin, Bata musa masaba remote tadauka duk takakkaro gudunsu harda fankokin dika. “Good job. Yafada cikin sanyin murya sannan yacire Jacket dinsa ya ijiye. 
‘kas Kas kas hakoranta suke haduwa jikinta na rawa tsaban sanyin dake wajen shiko Zaid kamar ma haryanzu sanyin bata ishesaba domin se cire riguna yake yana nannade hannun rigar datarage ajikinsa. 
Hadamasa coffee tai, shima ta ijiye masa akan table “Bakiga aiki nakeyi ba, feed me please. Yafada kai tseye. What? Ma’inah ta dakatar dashi cikin mamaki. What do you mean? Ni matar kace. Girgiza kansa yayi sannan ya’kara da murmushi ‘Mata kuma? Me kike nufi ? Ina nufin taya zan baka abinci abaki ni matar kace? Mikewa yai yanacewa ” Alright fine idan bazaki iyaba, zan iya Kiran wata tabani sabida wasu zasu iya sadaukar da dukkan Dukiyar dasuka mallaka don samun wannan damar kai wasuma inaga they will definitely sacrifice their life’s just to get this chance even though it will be once in there life time. 
Dariyan Mamaki Ma’inah tai “You are so full of your self Sir yanzu Daman haka kake gani, oh my God CEO you are mistaken. Ta ‘kara fashewa da dariya. Kallon mamaki Zaid yake mata “Zaki iya k0 kuwa? Ya ‘kara tambayarta. 
Alright baby boy. Chokali tadauko daganan Bata ‘kara maganaba ahankali take basa abaki kaman yedda ya umarceta, shi ko yacigaba da aikinsa yanakuma sha tamkar jariri. Sallamar Asad suka amsa a lokaci daya “A gafarceni na shige muku wuri kai tseye haka” Asad yafada cikin zolaya “Miss Ma’inah A gafarceni Koh. 
Wata dan guntun tsaki Zaid yaja ‘me kake bu’kata? 
A-l-D_Manaja is absent sir ta ‘kira tunda safe tai reporting cewa Mahaifinta bashida lafiya hakan yasa bazata samu zuwan aiki ba se bayan mako guda. Asad yafada cikin nunfashi d’aya. 
Innalillahi wa Inna ileihi rajiun Maisha ce Manajar A-I-D kenan mahaifinmu take nufi Asad me yafaru da Daddy, meya tsameshi?‘ Chokalin dake hannunta ta saki yayinda tai saurin ajje cofin sha’in datake rike dashi. Aguje tafice, Asad da Zaid duka mikewa sukayi alokaci daya suka biyota abaya. 
Toh yakaga gida? Tabar ‘Kallah Masha Allah gida ‘yaayi babu laifi kuma zan saya gida na amince. Murmusawa Maisha tai “Toh yaushe zaka bani kudaden? 
Tabe Baki Saminu yai yanacewa ” Zamuyi biya Uku, yanzu zan Baki million Uku, bayan kwana Uku Zan baki million Biyar sannan bayan kwana shida inbaki million biyu, yakika gani? Alright na amince. Ma’isha tafada cikin farin ciki yayinda suka shige motar Saminu yana tuki suna shawarwari. 
“Hey Saminu motar waye wannan? Babu irin wannan motar aduk garin nan, Mota ce mai tsananin tsadan tsiya. Ma’isha tafad’a cikin mamaki “kana ganinta kuwa gaskiya kasan kudi ya had’u. Adedai garrage Saminu yai parking cikin mamaki yace ‘Kai mota ce mai kyau wallahi ko dei abokanan Mahaifinki ne yazo dubajikinsa. 
Babu wanda ya’kara magana cikinsu har tseda suka ‘karaso ciki. 
Zaid da Asad sunbiyo Ma’inah har gida, Adedeita tsahu tahau inda Zaid da Asad suka 
biyota da motarsu, tana isowa ta hauro sama tabarsu a parlour’n ‘kasa. 
Aguje Maisha tashigo tana isowa Parlour tahangosu “Innalillahi wa Inna ileihi rajiun’ Mutuwar tseye tai tana kallonsu dawata irin mamaki afuskarta, take farin ciki ya mamayi zuciyarta “Ohh my God, Today is my lucky day, burina yacika Zaid yazo har gida neman aurena
Hannu ta daga musu “Hello, Ina yininku, tai musu sannu cikin wata tsiririyar murya” toh yanaga kun tseya anan, ku ‘karaso sama man anan falon Daddy yake? K0 dei ba‘kin Momcy ne. 
Asad ne ya amsa mata cikeda fara‘a yace”Tare mukazo da ‘kanwarmu Ma’inah. jikin Alhaji Sambo mukazo dubawa. 
Wani dammm!!! Taji azuciyarta, daman ashe wannan ne Saminu yake kokarin tsanarda ita, toh ashe shiyasa yace Daddy ya ‘kai Ma’ina gidan daula ita kuwa k0 oho ya barota anan tana shan ‘bakar wahala da azaba. Cikin matukar kad’uwa da mamaki tace’ Taya alakarku tahadu da Ma’inah? Kuma a ina kuka santa wanda har kanawani zagewa wai ita ‘kanwarku ce, Anyway banama yi dakai Zaid dakai nake magana meye yahadaka da Ma’inah? Manna mata hauka yai tamkar ba dashi akeyiba, ko motsi baiyi ba bare yadaga Ido yakalleta, iPhone X_plus dake hannunsa yacigaba da daddannawa. 
Ma‘isha bata ‘kara tan’ka musuba haka tahauro aguje tana kwala ihu, sunan Ma’inah take ambata har takai Falon Daddy, Momcy ce take wajen tareda Daddy suna tattaunawa se 
dariya suke suna nishadi Ma’inah tana nan third floor hauro ki tsameta’ Momy tafad’a cikeda fara’a ta’kara dacewa Ni kaina nayi farin cikin ganinta sosai jeki sameta Yata I’m sure you miss her… Da’kata momcy  Daddy kunsan wa nagani a parlour kuwa. Girgiza kansa yai alaman a‘a. Toh Zaid Muhammad Zabir, ZMZ Bulders CEO dakansa tareda Assistant dinsa Asad Abdallah su nagani a parlour’n mu yau. Zaid Muhammad Zabir kuma. Daddy yamike cikeda mamaki yaushi suka zo kodei tare suka taho da yarinyan nan Ma’inah. Bai tseya Maisha ta‘kara wata maganaba nan take yatafi se wani rawanjiki yake yana zumudi tamkar yau aka farayin baki agidan. 
Sake baki Maisha tai tana kallonsa “Iyee su Daddy manyan ‘kasa ashe dei anrigada anyiwa Yar gata future planning ankaita chan gidan masu arzikin duniya tana shan sha’ani, Ni ko anbaroni a nan gidan ‘kasa. Shiru tai tana jiran amsa daga wajen Momcy. Mikewa tai itama tamkar bata saurari mitar da Maisha take ba, cikin fara’a da tsannanin Farinciki tabi sahun mijinta “Yau munyi babban Baki a gida ZMZ Builders CEO dakansa ba aika ba maraba marabanku. “Mumcy ki tseya ki saurareni man Daddy yaci amanata, yaci zarafina Kuma ya fiflta Ma’inah sama dani Momcy please kidawo gareni ke kadei ce mai gaskanta damuwata mummy kada kibarni. Zubewa a ‘kasa tai inda tafara rusa kuka tana da’nasanin rayuwarta, Ma’inah you destroy my life wallahi se naga bayanki and you will never be happy I promise. 
Share hawayenta tai “I need to be strong and I need to earn Momcy’s trust again‘ jiki a sanyaye tahaura falon sama nan tahango Ma’inah achan tana tseye adedei window tana lekowa kuma da dukkan alamu Zaid take gani sabida ko kiftowa idanuwarta ba ‘suyi. Idanuwarta suna hawaye yayinda takura mata ido tana bakin ciki, zuciyarta na tafasa tse huci take tamkar kare ‘Mainah why did you have to take everything from me, wani laifi na aikata kike sa’kamin da wannan Bakar sakamakon. 
Ma’inah batasan hawaba bare sau’ka, Jin Maisha kurun tai abayanta kamardaga sama inda tafara bubbugeta da sandar dake hannunta tanajanyo gashin ‘kanta tamkar igiya daganan suka tada fada.a Falo duk sun wargaza glasses duk Maisha ta parpasasu kan Yar uwarta kujera duk sun tangale up side down, har TV tayi kokarin cirowa amma ta ‘kasa se ihu suke suna fad’a kamar gidan dambe. Daddy Ma‘inah take ihun ‘kira amma babu amsa 
ganin sunyi sama sosai babu mai sauraransu “Mommy, Daddy harma da Zaid tafara ‘kira a 
yanzu. Ma’isha Ko ranta se ‘kara baci take tana ‘kara jibganta. 
Gudu Ma’inah tafara, ganin Maisha zata iya hallakata sabida kome ta’samo take jefowa. Ahaka har suka sauko bene ta biyu. Ma’inah ‘ana gaba, Ma’isha na baya tana binta da Sanda hartasauko ‘kasa. Daddy, Mommy, Asad da Zaid duk mikewa sukayi cikin tsananin mamaki Kuma alokaci daya. Jinin dakejikin Ma’inah ne yamatukar tsorata Daddy inda k0 minti daya bai ‘karaba ya sume awajen. ‘karshen Sandan data sauko akan Ma’inah ne yafitar da ita daga cikin hankalinta Wanda Maisha tasa duk ‘karfinta tasaukeshi adedei ‘kan ta. 
Bibbiyu tafara ganin duniyar, Idanuwanta suna duhu duhu daga nan tafita hankalinta, Nan take Zaid ya’karaso wajen, da hannayensa yarike’ta just like a protective charm bai bari ta ‘karaso kasa ba, chak!!! ya daukota tamkar jinjira. Ma’isha najiran jin abunda zai fada amma babu infact hankalinsama gaba daya suna kan Ma’inah dake hannunsa. Aguje yakaita Mota inda ahankali yakwantar da ita abaya, yafara tuki. Dakyar yarike sterin yana tuki tamkar mai farfadiya hannayensa suna karkarwa, yana nunfashi sama sama, ya ‘kasa rike hawayensa zubowa suke tamkar fanfo se yau yaga’ ne matsayin Ma‘inah awajensa wanda ako yaushe idan yasata a idanuwarsa yakanji wani iri wanda shi kansa baisan dalilin hakanba. San Ma‘inah yake har cikin jijiyoyin jikinsa, Soyyayyarta tarigada Tashige zuciyarsa tun Rana ta farko dasuka fara ganinjuna Kuma har cikin ransa ba’zai jure rashintaba. 
Asad ne yadauko Daddy amotarsa tareda momy suka tafi dashi asibiti, inda aka baro Maisha agida ita kadei tana jujjuya idanuwa ko kadan batayi da’nasanin abunda ta aikataba hasarima aganinta daga wannan dukan, Ma’inah zatasan inda zata  Daddy ko suman dayayi dedei ne alhakkin tane yafara bibiyarsa tun ayanzu, baimaga komai ba tukunna. Da wannan tunanin tawuce d’aki inda kai tseye tafara tattara ‘kayanta dama sauran abubuwanda ta mallaka wandake gidan. Hoton Zaid da Ma’inah take gani a idanuwarta ta ‘kasa ganin komai se fiskokinsu musamman lokacinda yadaukota suna barin falon, yedda yakure mata Ido dakuma irin tashin hankalinda yabayyana a fuskarsa tamkar Romantic Moment a series film na India. 
Akwatin kayyakin data tattaro ta fito dashi cikin masifar bacin rai ta watso su ‘kasa, d’aya bayan d’aya tafara wargaza su tana rangada ihu tamkar sabuwar mahaukaciya. “Banda Zaid, Ma’inah Banda Zaid zaki iya tsace kowaye aduk fad’in duniyar nan amma banda Zaid shi narigada nai planning future’n mu tare. Doguwar nunfashi ta saukar ‘You really made the wrong decision this time Ma’inah Sambo Maidugu zakiyi da’nasanin shiga rayuwata. 
®NEXT CHAPTER SPOILER ®
Jakarsa yake turowa yana ja sejujjuyi yake yana gannin bayansa tamkar gudun wani yakeyi. Mutanen Airport kowa kallonsa suke kaman mara gaskiya. 
Karo sukayi da ‘Yarsa Miemah yayinda yabude lifta yana kokarin shigewa ita kuwa tana fitowa. Kallonta yai sama da ‘kasa tana Jan ‘jakarta alamun yanzu tasauko daga jirgi all the way from Maiduguri. “Me kike anan? Tambayarda yafara mata kenan. Cikeda Farin ciki tarungumeshi “Abba tun shekaran jiya mukayi magana da Kawu Sambo he is so worried about me na fad’a masa lafiyata ‘kalau amma ya ‘karyatani yace ba’zai yarda da maganataba hartse nazo gida Abuja sannan ne za‘muje wajen likita yatabbatar masa da maganata har kudin jirgi shi ya aikomin ….. 
Zufa Saminu yafara sharewa daga fuskarsa “Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun y’ar nan kin tona’min asiri na shiga uku. 
Na sayar masa da gidana Million Goma, na mallaka masa takardun gidan da komai harda makullai amma mutumin nan baisan ko wacece ake ‘kira Maisha ba, yayi min wasa da 
hankali million Uku kachal yahadani da ita yai tafiyarsa yanzu ba’nida wani gida ka san 
cewa na bar gidan iyayena gashi nadawo kuma Nayi masa Miss Calls 
kusan arba’in bai dagaba, me yake nufi, 7 million naira kudadena dake wajensa yanzu. “ 
Gyada Kai Auwal Wiski yai yana hura sigarin dake bakinsa yayinda yace “Na fahimceki Maisha cool down yanzu me kikeso ayi masa???? 
Wannan CHAPTER din sai a slow kuyi haquri ban zauna bane

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *