Makaranta. Duniya
Chapter23
Har ta dawo ko kwanon bai bude ba. yana rabe da kunci. Ta yi tsaye, “Haba lmamu! Meye haka ne kamar an yi mutuwa? Ya yi dan gajeran tsaki, ya tashi. “Bari in wuce Inna! Bai jira komai ba, ya suri ‘yar karamar jakar takardunsa da ‘yan kayayya kin da ya zoda su, ya yi waje, da sauri ta biyo shi tana fadin “Kai tsaya mana ka ji! Yau ‘ na ga shegantaka.’
Ya ja ya tsaya suna duban juna, “Ko ba za ka ci abincin ba, ai ka tsaya na ba ka na mOta k0? Ya ce, “Yi hakuri Inna.” Ta juya ta koma daki, ta fito da kudi a hannunta, ta mika masa dari biyar ta ce ka yi ta addu’a. Allah ya sa yayanka ya huce, tunda ba ka so ya yi mata fada. Ba wai ka zauna ka na tagumi ba.”
Ya ce “Shi kenan Inna, sai an kwana biyu.” Ta ce “Allah ya kai mu.” Ta raka shi har zure, sannan ta dawo gida ta yi sallah tare da mamakin wannan soyayya da ke tsakanin Imam da Jamila ko ba’a tambaya ba, an san ta yi tsanani, baran mashi Imam din.
Yinin nan zungur! Bai yi sukuni ba, ko dama shi ba mai hayaniya bane ko abokan zamansa a dakinsu sun rasan shi bai fiye harka ba, shi ya sa ba shi da wani tsayayyen aboki, duk wanda ka gan su tare, idén ka bincika za ka sami karatu ne ya hada su. ,
Dare ya yi, ya kasa barci saboda bai san halin da Jamilarsa _ke ciki ba. Ba wannan tunanin kadai ke damunsa ba, wai me ya sa Yaya Sulaiman ke ta yawan fushi da fada,.tunda suka zo? Me ya sa da za su wuce ko kallonsa bai yi ‘ba? Sannan me ya Sa ko da wasa bai tanbayi masa maganarJamila ba, alhali ya san yana son ta?
Wadannan tambayoyi su suka taru suka hana zuciyarsa sukuni,.maras misultuwa. Kafin gari ya waye, shi kan sa ya san ya rame, don bai ci abinci ba ya kwanta, dole ta sa da sassafe ya hada shayi ya shanye, don da ya fito wanka harjiri ya rinka gani, cikin ajin ma
zaune kawai yake amma zuciyarsa na Bauchi, tana mesa laluben halin da abar son sa take ciki.
Kusan haka ne ga Jamila. tunda suka dawo bata da walwala, ‘ko yanzu din ma kunshe take cikin daki, tana tunanin masifar da Dadinta ya rinka balbala mata tun jiya har zuwa wayewar garin yau, kafin ‘ ya fita ofis “Ke shashashar wofi, in ce k0 ke mahaukaciya ce ko kuwa sakarci ke damunki, ki na nufin soyayya za ki sa a gaba ba karatu ba?
To Wallahi tallahi za mu sa wando kafa daya da ke, idan har ba za ki tsaya ki fuskanci abinda na ke’ gaya miki ba! Kuma ki sake cewa za ki je‘ Kaduna, sai nai mugun bata maki rai! Ai wannan iskanci ne, “yar karama da ke har kin san ki kebe da saurayi, yana koya ‘ miki rashin kunya. Wallahi ahir din ki, daga ke har Imam din sai na ci mutuncin ku
Ta kara kankame filo kukanta ya karu k0 sallamar Murja ba ta ji ba, ta zauna bakin gadon ta ce, ‘Watau kukan nan ba za ki daina shi ba, sai ya’ zame’ miki ciwo k0? Murya na rawa ta’ ce, ‘Dadi yana ta faman fada, yana ta faman fada, ba dole in yi kuka ba! Ai yakamata ya yi hakuri, tunda na ce ya yi hakuri, hazan sake ba.‘
Ta ce, ‘Ai maganin ki kenan, domin kin fi kowa sanin halinsa, idan Mutum na son zama lafiya da shi, to ya bi umarninsa, saboda haka ki natsu ki kama karatunki k0 kya zauna lafiya da Dadinku, kin ji na gaya mki. Ta shi ki wanko fuska, ki koma cikin ‘yan—uwanki ‘ yi walwala-‘
Ta kamota, ta taso ta raka ta bayi tana rarrashinta. Tana bada baya wayarta ke ta ruri, ta katse sake dauka,~ta katse ta sake dauka. Karo na biyar nan ta fito ta same ta tana rerawa. Ta sa hannu ta dauka lambar, babu suna, ta latsa O.k, ta zauna bakin
gado tana fadin, “Hello! Ya numfasa ya ce, “Haba Bebina! Ba za ki dauki wayar bane?
Gabanta ya fadi, ta dan yi shiru kafin ta ce, “Yaya Imam! Ka yi hakuri ba na kusa da wayar ne, ya karatu? Ya ce, “Mun gode Allah ya ku ka je gida? “Lafiya lau, kamar ba ki da lafiya Bebina, ki na ta kuka tun jiya k0?
Take nan wani hawayen ya tsirgo mata, ta kasa daurewa, nan ta sake su sharr! Suka_ zubo. Hakan ya hana mata magana. “Look, Jamila ki yi hakuri mana, ai mun yi laifi tunda muka bar Yaya tsaye yana jiran mu, kin ga dole ya yi fada.” ‘
Ta gage kwalla ta ce; “Na ji Yaya Imam, amma ka san abin da na ke rokonka, don Allah mu sassauta wa juna akan maganar soyayyar nan zuwa lokacin da zan gama karatu, don Allah.” ‘
Nan da nan’ya daburce “Me ki ka ce me Jamila? Me ya kawo wannan maganar’? Ta ce “Caji zai yi maka yawa, idan muka tsaya dogon surutu. Yaya Imam tunda’ ka fahimce ni kawai, shi kenan mu bar wa zukatan mu abinda ke cikin su, zuwa nan gaba kadan.” Ya ce. ”
“Lallai ki na so na mutu ne Jamila, muddin ba na jin motsinki da kalaman bakin ki, kOmai zai iya faruwa da ni, idan kuma Yaya ne baya so na, kawai ki fito fili ki gaya min in sani ……
‘Ji yayi shuuu… Ta kashe wayar, da sauri ya kara nemo ta, kUka take tana karawa da ta ga zai dame ta, sai ta kashe wayar gaba daya.“lnna-Lillahi~wa-lnna- Ilaihir—Raji’un!
Tun daga’ranar gaba dayan’
su suka shiga wani hali na rashin jin dadi, wanda maikaratu baya bukatar ya sani, don kwakwalkwarsa ta jima da . yi masa hasashe. Duka bangaren biyu suna samun rarrashi, sai’ dai ba iri daya ba. Shi Imam hakuri iyayensa ke ba shi,
suna nuna masa mahakurci mawadaci ne. kuma matar Mutum kabarinsa, kawai abinda suka lura Sulaiman baya farin-ciki da soyayyar yaran, wanda ba za su ce ga hujjarsa ba. ‘
Duk da cewa’al’amarin yana ba su mamaki tare da daure masu kai, sam sun kasa ganin bakin SUlaiman saboda kaunar dasuke masatsakani da Allah kuma ba sa son maganar ta shiga zumuncinsu. Ita kuwa JamiIa rarrashin gata ta ke samu da tarairaya’ sulaiman, yana nuna mata muddin ta bi umarninsa,duk abinda take so zai yi mata. “
.’ Jamila na son kyale-kyale kwarai shi ya ‘sa rantsatstsiyar wayar da ya canza. mata ya bala’in daukar hankalinta. Banda saturan da yake yawan kawo mata. Tabbas ta ci—gaba da bin ra’ayin Dadin shiyasa take yadda take so. Take nan ta yarda da shawarar canza lambarta, dalilin da ya sa kenan Imam ya daina Samun wayarta har tsawon lokacin da‘hutun su ya kare,
ta koma makaranta.
, Kai Imam yana wahala kuma ya na fama da kayan son JamiIa da Allah ya dora masa cikin’ zuciyarsa. Hakuri kawai yake yi kamar yadda kowa ke gaya masa. Kamar wasa ya rasa kan gadon Jamila, idan ma har ya samu damar ganin na ta kenan, wanda ba zai wuce sau biyu a shekara ba. Duk da cewar ya sake samun lambar wayarta, ba dole”bane in ya. kira ya same’ ta, walau a kashe ko ta ki dauka kiri-kiri. . A hakikanin gaskiya Imam ya kasa gane irin son ‘da take masa, wani lokaCin ta yi masa lafazi mai dadi, wani lokacin ya ji maganar kamar ba daga bakin.ta take fitowa ba, sai dai shi abinda ya sani ba zai iya rabuwa da ita ba, muddin gaba‘dayansu suna numfashi. Ita kan ta Inna tana kokarin tunasar da Sulaiman cewa
lallai Imam yana son Jamila kuma shi take so ya ba
auran ta idan har ta kare karatun, kamar yadda yake cewa.
Amma sai ya yi biris da maganar ya share ta, tamkar bai taba ji ba. Dalilin da ya sa kenan tsakanin Alhaji Abdul-Rasheed da Hajiya Suwaiba, babu wanda ya taba zaunar da shi ya yi masa maganar balle su rake shi. Koda yake ba su ji ya ce zai ba Imam auranta ba, Illa iyaka ya ce karatu za ta yi. Amma menene manufar yin biris din? Ai da yana maraba da abin da ya fi ko‘wa zumudi.
~~.~‘~s~s sssssss
haka Imam ya kammala digiri din sa cikin zafin rashin abubuwa biyu muhimmai a wajensa, kudi
da Jamilarsa, yayin da ita. ma take zaman jiran (Adimission) a jami’ar Gombe. Can ya za‘bar mata, saboda baya so ta zo kusa da Imam,- ya tabbata muddin tana Zariya ko Kano. Imam zai sami damar kusantarta ya ci-gaba da cusa mata ra’ayin sa.
Shi kansa ya san Imam namiji ne mai nagarta da cikar dukkan abin. bukata, illar sa daya, talauci da ke damunsa, wanda ba shi ne kalar mijin da yake so ‘ya‘yansa su aura ba, dalilin da ya sa kenan yake masu tanadi tare da nuna masu muhimmancin jin dadi cikin daula.
Wata biyu da‘fara karatun Jamila a fanni akanta. Sunayen masu tafiya bautar kasa suka fito. Allah da ikonsa sunan Imam ya fito a Gombe, shi kan sa bai amince ba, sai ‘da ya yi ta maimaitawa. Sannan ya tabbatar wa zuciyarsa lallai Gombe zai tafi kai! Bai san inda zai sa farin-ciki ba, ko da ganin yadda yake da doki, ‘su Alhaji su ka gane inda farin—cikin‘Imam ya fuskanta.
Bai wani fuskanci matsalar kudi ba, domin Alhaji ya tanadar masa tun lokacin da ya yi wa Muddasir fijiSta
a’ (Poly), sauran kudin ya aje saboda tafiyar ta Imam-
abinda ya kara wa Imam farin-ciki tare da kaunar , . shi ne ‘yar wayar da Alhajin ya siya masa ta
(Multi—link) suke yi, ya yi kundunbala ya siyo masa da ‘ ragowar kudin hannunsa, saboda in ya tafi su rinkajin motsinsa. –
‘ Lambar Jamila ita ce lamba ta farko da ta fara shiga wayar kuma ita ya fara kira‘ a wannan rana ta taji labarin tafiyarsa, amma kash Bai same ta ba, wayar tana kashe tsawon wannan rana har zuwa washe gari, kafin ya tafi, sai da ya karbi lambar Hamisu makwafcin su, saboda ya rinka isar masa da sako a gida.
_ Yana zaune cikin mota, ba a k0. fita garin Kaduna ba, kamar an ce dauko waya ka sake neman Jamila’, ya zaro ta gaban aljihu ya nemo lambar, jimawa kadan ya yi ta shige, ta hau bugawa, murna ta kamashi. Sai da ya numtasa.‘ Ba ta dade ba kuwa ya jiyo :muryarta, cikin salo ta ce “Hello! .Ya ce ‘Haba‘ ‘yan’ mata kuma sai ki rufe wayar ki? Ta yi ‘yar dariya “Yaya kenan, to ya ku ke? Ya ce ‘Kalau! ‘Amma kin san me? Ina mamakin yadda ki ke saurin gane ni.” Ta ce “Ka ji yaya dai, ya ba zan gane ka .ba? Ni da jinina.” Ya yi murmushi “Haka ne, tun jiya na ke neman’ki in yi miki albishir cewar a Gombe zan yi sabis –
, Hannunta a kirji ido waje ta ce “Don Allah da ‘gaske? Ya ce “Yanzu haka ma na kamo hanya, idan na sauka, zan neme ki.” Ta ce “Wai Kace yau Gombe suna :da ‘manyan baki, tome zan shirya ma? “Baki je School bane? ‘
“Ka manta yau lahadi! “0h! Na; manta fa, na rude ne, ai kin gane k0? Ta ce, “Me za ka ci Yaya Imam? Ya ce, “Abinda ya fi dadi a Gombe.” Cike da‘ murna ta ce “An gama. Allah ya kawo ka lafiy.” Ya amsa da amin. Ya kashe waya, dadi kamar’ya kashe shi.
Lafiyayyen gida Sulaiman ya kama wa Jamila, suna zama tare da kawarta kowacce da dakinta’ ma’ana gidan mai dakin kwana biyu ne, nan Imam ya fara sauka, ya ci ya sha har da wanka, sai dai zuciyarsa na cike da tunanin kokarin wasu iyayen da ke tura‘ya‘yansu mata karatu wani gari har su kama masu gida su kadai su zauna. Shi kan sa ya ga Jamila ta canza,ta waye, idanuwanta sun kara badewa, tun daga shigarta Imam ya tabbatar Jamila ta shiga jami’a.
. Yana kishingide bisa sallaya, ita tana zaune gefen katifa, ta dube shi ta ce, “Ka san me? Why not ka yi zaman ka anan, sai mu dawo nan. Bilkisu mu bar maka dakinta.’ Ya zuba mata ido baki sake, kafin ya ce, “Nan? Haba dai kamar an ce je ka ka gani!
Ta ce, don me? Kowa ya dube ka ya’san kai Dan-uwana ne.” Ya kada kai ““Ah’ah kyale ni a cikin ‘yan-uwana maza, tunda ba biyan haya za mu yi ba ai da sauki.” Ta tabe baki, “Shi kenan, wai na ganka da sabuwar waya ne, siye ka yi? Ya ce, “Ba kin min alkawarin za ki siyan min’ ba ……
Ta katse shi, “To an gaya maka na manta ne? K0 na: fasa ne? Ya ce “Oho, ina zan sani, amma shekara nawa, ni kaina ma ki na min walle—walle, yau ki na so na gobe sai ki sauya.’ Ta turo daurin dan kwalin ta‘goshi, ta ce “Au, haka ka ke gani’? Dama da fuska ka ke kallo na? _
Ya tashi ya zauna sosai ya ce, “Na rantse da Allah Jamila yadda ki ka damu da ni da, yanzu babu kashicasa’in .bisa dari, ni kuwa a’ yadda na ke tunani karatu ba zai hana soyayyar mu bunkasa ba, kamar yadda soyayyar ba za ta hana karatun ba, na so ace ra’ayin mu ya ci-gaba-da tafiya kamar yadda ‘ya faro asali, amma sai ki ka barni akan hanya, ina ta bandan’ bandan me ya sa?
Ta aje kai kasa ta numfasa. Ka na ta dago ta dube shi, “Ba za ka gane bane Yaya. ni na san har yanzu muna tare, shi kuma aure nufi ne na Allah. Kullum ina gaya maka ba na so ka rinka damuwa.‘ Bai amsa ba suka ji ana kwankwasa kofa, ta ce “Yes! Shigo!
Wani dogon saurayi ya shigo wankan tarwada. ta mike tsaye “Ah Najeeb! Ya zuba wa ‘Imam ido tamkar yadda yake kallonsa, ganin haka ya sa ta yi wuf! Ta’ ce, “Dan-uwa na ne. Yaya Imam, sabis ya zodaga Kaduna. Yaya Imam ga Najeeb, (Course Mate) dina ne. ‘
Ya hadiye miyau da kyar, ya mika masa hannu tare da sallama Najeeb ya ,amsa,‘yana fadin. “Amma kun yi kama sosai, da gani ba tambaya, ka zo lafiya? Ya cé, “Lafiya lau, ya karatu? Ya ce, “Muna ta tabawa, to ya ka ga Gomben ta mu? Ya yi murmushi ya Ce, “Gwanin kyau.” Ya mike. “Jamila bari in isa masauki na.”
Jiki babu kwari ta ce, “Tun yanzu? “Ina ganin ya kamata ai.” Ta kalli Najeeb da ke ta kada makullén hannunsa, “Bari in raka ‘shi Camp! Ya ce “To ku zona kai ku mana.” imam ya ce, “Ah’ah kar ka .damu, na gode.” “Haba Yayan mu, taho mu je kawai, ba matsala.”
Ta dora a baya ta yafa dan gyalen‘ta, ta Sum jakarsa, “Mu je Yaya Imam.” Suka fito~ta yi wa Bilkisu sallamasuka fice, (Camry) ce motar Najeeb, k0 kunya Jamila ta shige gidan gaba, shi ya sa imam ya dawo maraya a gidan baya.
Bakin-ciki kamar ya kashe shi, duk da cewar
’Jamila ba ta share shi ba, har ma ta fi son ta yi magana
da shi akan’ Najeeb, sam zuciyarsa ba ta yi sukuni ba, don ya tabbata akwai yaudara tsakanin sa da Jamila.‘
‘ -Ko wane daki mutun biyu ~ke cikinsa, domin kananan gidaje biyu ke cikin kowanne daki. jamila ta gyara masa gefen sa, sai dai babu zanin gado, take nan ta ce zata kawo masa ba sai ya siya ba don tana da su._ ‘ da yawa. Sun dan taba hira su ukun kafin najeeb ya ce
ya kamata su tafi. suka yi sallama. Najeeb ya yi gaba. Jamila ta biyo bayansa. ‘Jamila
Imam ya kira ta. ta dawo tana amsawa, ta tsaya , gabansa, ido cikin ido yake mata magana. ‘Ko zaki- yaudare ni, don girman Allah da son Manzonsa karki bari ke samarin zamani su yaudare ki da kyale—kyalen’ abin hannunsu. Please Jamila, ba mutuncin ‘ya mace“ bane saurayi ya rinka yawo da ita cikin motarsa, ki sani zuri ar mu masu kima ne da daraja.”
Ta gyara tsayuwa ta yi dan murmushi. ‘Yaya Imam kenan, ka na zaton ban san me na ke yi ba k0? Ai shi ma Najeeb dan mutunci ne, kuma babu komai tsakanin mu sai mutuncin. Dadi ma ya san shi. sau uku yana kai ni (Weekend) Bauchi. Saboda haka ka sa ranka a inuwa, kai daban Najeeb daban, kusan ma ka fi Najeeb a guna, domin kai mataki biyu ka haye. Najee kuwa yanzu na san shi.” .
Ya numfasa ido taf Da kwalla ya ce, ‘Shi kena ki dai kula, gobe in na taso aiki zan biyo wajen ki.‘ Tace ‘Ah’ah ba zan wahalar da bako ba, ni ma zan zo nan daga nan in kawo maka zanin gadon.‘ Ya kada ka “Ban yarda ba.”
“Saboda me? Ya ce, “Maza sun yi yawa a nan ba na so ki na zuwa. Ni zan je wajen ki.‘ Ta yi ‘yan dariya, ta sa fos din hannunta, ta dan bubbuga‘kuncinsa. ‘Kishi ko Yaya Imam …… ? To shi kenan ina jiranka, bye! Ta wuce tana ci-gaba da dariya, ba tare da ‘ya sake cewa komai ba.
Ya tashi a hankali ya biyo ta, fitarsu harabar‘. wurin kawai ya gani, ya yi tsaye kamar ya yi kururuwa jama’a su kawo masa gudunmuwa, su kwato masa abar son sa. Da kyar ya dawo daki ya yi kwance bisa gadon ‘ sa. tunani ya lullube shi.
‘Da na san abinda zan zo gani kenan a Gombe, .
da ban kwana doki ba, da ban azalzalawa zuciyata
kwadayin zuwa Gombe ba. Allah gani gare ka, ka fi ‘kowa sanin yadda na ke son Jamila. son kai ka sanya min. Allah na roke ka ka tsare min ita daga sharrin da ‘namiji! ‘ , Ko cikin sallolinsa ma addu‘ar daya rinka yi kenan. Allah Sarki Imam, so hana ganin laifi. duk irin firgitar‘da ya yi sakamakon ganin Jamila da Najeeb da irin bayanin da ta yi masa cewar har Bauchi yana kai ta, sam zuciyarsa ba ta aibanta masa Jamila ba, illa kishinta da ya‘hana shi sukuni.
Tun bayan lssha yake neman layin ta, amma bai samu ba. da ya kira, sai a sa masa (User Busy). watau ana amfani da wayar. Haka ya raba’ dare, sai ‘a ajiyar zuciya yake shi kadai a daki, domin bai sami abokin zama ba tukuna ba, bai san lokacin da barawo barci ya sace shi ba. ‘
Washe gari da yamma likis! Ya isa wajenta ya iske ta dawo har tayo cefane, tana masa miyar kaji dakwale guda biyu, ya yi mamaki da ya ji ta ce miyarsa ce take yi masa, bai yi mata maganar Najeeb ba. ita ma ba ta yi masa ba, ga zannuwan gado nan kala hudu ta ware masa gefen filo ta ajiye su.
Ya dauka yana gani, da ganin su za su yi kudi.
don suna da kyan kallo. nan’ya yi sallar magariba sun ci abinci, ta kwashe masa miyar a wata matsakaiciym samira, ta ce idan ya je gida ya dan bude murfin ta sha iska. Suna tsaye kofar gida yana jiran mai mashin, sai ga Najeeb na fakin a gaban su. nan da nan bakin~ciki ya ‘ rufe shi, kishi ya rufe masa ido. “Ah. Yayanmu. har _ka fito ne? Salamu-alaikum! Ya mika masa hannu, ‘Yanzu ,na ke shirin tafiya.” To ai sai mu je a sauke ka. Bari mujeko? Kamar ya buga masa guduma a kirji», da kyar _ ya iya cira kafarsa ya shiga motar. shi ya sa ma suka riga shi shiga.
Wannan wane irin abu ne? Wane irin bakinciki na ke fuskanta? Haka zan sa ido ina kallo Wani na neman ya wargaza rayuwar abar so na? Fita da daddare? Kai! Ba zan yarda ba
Ya yunkura ya tashi ya dauko waya ya kira ta ,ya -kuwa yi sa’a ta dauka. “Hello Yayana.” Murya raunane Ya ce, “Jamila ki tabbata kin koma gida, ki kuma Kama kanki, ki sani babu abin burgewa a“ haramtacciyar mu’amala tsakanin namiji, da mace,” rike mutuncin ki Jamila.
Shine’ _kawai rokona gare ki,‘ kin san’ina tsananin son ki Jamila, zuciyata ba ta sukuni, muddin kina tare da Najeeb. Ya kamataki gaya masa ni ne wanda za ki aura, don ya daina kallona a matsayin dan-uwanki kawai”.
Ta tsuke fuska cikin fushi ta ce, “Wai me kake nufine?’Me ka dauke ni ne? Karamar yarinya? ‘ Kuma wa ya gaya maka Najeeb bai saukeni gida ba? Ba kai za ka gaya min abinda ya kamata ta ba, saboda- ni ma Big girl ce.yanzu, na san ciwon kaina! Ta kashe waya tare da jan dogon tsaki. ;