MISBAH BOOK 3 CHAPTER 3B BY SA’ADATU WAZIRI

MISBAH BOOK 3 CHAPTER 3B  BY SA’ADATU WAZIRI

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 


Mama ta yi dariya ta ce, “amma kuwa na ji dadin wannan shawara da kika yanke, tabbas kina bukatar canjin wuri da yanayi, ai can Lagos ma gida ne, sai inda kika zaba, in can gidanmu ne sai a yi wa masu aiki waya su gyara, in kuma gidan su Deeni ne duk daya ne.
Nan taji an sosa mata inda yake mata kaikayi ta ce, “Ina ga gara wurin su Bahijja, can ai ba za mu ji dadin zama mu kadai ba.
“Haka ne, in ji mama, ta fada sannan ta ci gaba da cewa “to sai ku sa rana, ku shirya ku tafi, zan yi magana da baban naku zan fada masa.

“To mama, na gode, Allah ya kara girma da lafiya.” “Babu komai Farida, mu ai farin ciki da walwalarki muke so.”
Wani yammaci Deeni ya taso daga gidan gonarsa, zuciyarsa cike da walwala da nisahdi yadda kajinsa sun kara habaka, duk injinan da ya yi order daga (Italy) an kafa masa su, ya samu sauki sosai, haka nan kajinsa sun samu walwala da karin lafiya, wanda hakan ya ba su damar saka kwayaye fiye da na da, haka nan yana samun nasara sosai ta fanin nomansa, da shuke-shukensa da sauran dabbobinsa, wannan ya sanya nishadi da farin ciki a ransa, ba wanda yake bukatar gani a irin wanan lokacin sai Bahijja. Haka nan ya dinga jin dokin ya ganta ya fada mata irin nasara da ya samu saboda ta taka muhimmiyar rawa sosai tare da ba shi goyan baya don ganin ya cimma burinsa.
Haka kuma burinsu ne duka su ga an kammala saka machines din successfully. Kai tsaye ya wuce asibitinta inda yake da tabbacin zai same ta, hakan kuwa aka yi, ya same ta a cikin marasa lafiya tana ta fama da su kamar yadda ta saba, tana cikin farin ciki. Tabbas, aikinta na sanya ta nishadi a duk lokacin da Bahijja ke cikin patient dinta, wani

annuri na musamman yake gani a tare da ita, sai kuma in ta fada duniyar rubutu wani lokaci ya kan yi kishi da hakan. Sai dai, ya san matsayinsa da muhimmancinsa a rayuwar Bahijja ya wuce haka.
Harde hannayensa ya yi ya tsaya yana kallon ta yana murmushi tare da jin son ta na ratsa
Www.bankinhausanovels.com.ng
jijiyoyinsa, ina alfahari da ke Bahijja, duk namiji da ya ajiye mace irin ki to, tabbas ya san ya ajiye mace, na gode wa Allah da ya ba ni ke, ya mallaka min ke a rayuwata, mace mai hikima da tarin ilmi, ga kyau ga tsari ga addini, macen da ta san kanta, mace mai manufa.
Kamar da wasa, ta dago kai suka hada ido, ta sakar masa wani sassanyan murmushi mai ratsa zuciya, ta ji sonshi na sukar ta, ya yi matukar haskata, ta ga ya mata wani irin kyau na musamman, yanayinsa ya nuna yana cikin farin ciki da nishadi. A duk lokacin da Deeni yake guri ba ta ji da ganin kowa sai shi, hakan nan ba ta iya yin komai sai , da tsananin son kasancewa tare da shi, hakan yana sa ta tsananin farin ciki tare da ba ta wani iria jin dadi.
Ai kuwa, ba ta bata lokacin ba, ta nufe shi da wani nishadi da farin ciki tare da rungume shi, ya kuwa bude hannu ya yi mata kyakkyawar tarba, don kuwa shi ma yana bukatar hakan, sun dau tsawon mintuna a hakan, suna jin saukin juna sannan suka saki juna, su dai jama’ar asibiti sun saba ganin haka sai dai tabbas na yau ya bambanta da na kullum.
Nan ya ja hanunta suka bar wurin suka nufi motar Bahijja, ta kasa hakuri sai da ta tambaye shi, “wai Deeni mene ne haka ya saka tsananin farin ciki, yau na lura nishadinka na daban ne.” Nan ya nemi wuri mai kyau ya yi parking ya kalle ta tare da rungumarta sosai ya ce, “albishirin ki!” cikin
Www.bankinhausanovels.com.ng
doki ta amsa da cewar, “goro fari tas, sai wanda ka zaba min.” “Yau dai burina ya cika, an gama min aikina na
poultry farm dina duk machine da na yi order an yi installing dinsu, yau din nan suka fara aiki, na gwada su, da hannu na nai operating, komai ya min yadda nake so, wannan shi ne burina na zahiri a yanzu, ban da wata sauran matsala a rayuwar nan, ina tare da iyalina ina farin ciki business dina halal ne da nake taimakon dunbin al’umma da shi, ina jin dadin zama da iyayena, suna sanya min albarka, ina tare da macen da nake matukar so, macen da ta fi kowa kima da daraja a rayuwata, Bahijja me ya fi wannan farin ciki a zayuwa sai fatan gamawa da duniya lafiya da fatan samun zuriya dayyiba,”
Tsananin Feria iki da annuri ya sauka a fuskarta, tana dariya ta ce, “tabbas abin farin ciki da murna ya same mu, wannan ba burinka ba ne kai kadai, har da ni ma, sabida cikar burinka da ci gabanka shi ne nawa, Allah ya kara wa kasuwancinka albarka, Allah ya dauka ka, Allah ya raba ka da sharrin makiya.”
Ya rungmeta da fadin, “na gode my love da goyon baya da hadin kai da kika ba ni tare da shawara da kuma fahimta, Allah ya bar mu da juna HAR  ABADA.” “Ameen my Deeni” ta amsa tana murmushi.
Ya ce “Yau dai ranar hutu da shakatawa ce, ba aiki sai soyyaya, da gani sai Misbha na za mu yi refreshing soyayyarmu da memories dinmu, yau
Www.bankinhausanovels.com.ng
zan nuna maki tsananin kauna da na jima ban nuna maki ba, zan ba ki dukannin lokacina da attention dina wanda sanadiyar aiki da rashin zama ya sa ban baki ba”
“Wow,” ta fada tana murmushin jin dadi ta ce, “Amma na ji dadi Deeni, wannan muhimmacin da ka ba ni, ya fi min komai a rayuwa, tabbas ina da bukatar kebewa in kasance tare dakai saboda na yi tsananin kewarka a ‘yan kwanakin nan, hankalinka da tunaninka gaba daya, ba sa tare da ni saboda aikinka wanda sai na dinga ganin kamar kana overworking din kanka ne saboda ka manta wani ko dai ka guje wa wata damuwa da tunani. “Sai dai kamar kullum na yi maka kyakkyawan
zato da fahimta, saboda a zauna lafiya,” tana magana tana kallon kwaya idonsa. Ras! ya ji gabansa ya fadi kamar wanda Allah yabata tunanin da ilimin sanin halin dan-Adam, irin
wannan tunani na Bahijja yana bashi tsoro.
Nan da nan cikin gaggawa ya kawar da idonsa daga nata, ya tada mota yana dariya yana cewa, “ku fa likitocin nan wata ran kuna da kokarin wuce gona da iri, don kun karanta a takarda ba zai sa ku fahimei tunanin mutum ba, don haka kar ki yi kokarin samun tunanin da ba nawa ba.”
Murmushi ta yi da girgiza kai tare da fadin “yes boss, dariya su kai duka. Shopping mall suka wuce domin siyayyar kayan da za su sa na wannan yammacin, har zuwa dare tare da kayan da za su bukata a poultry farm dinsu don ya nuna mata
Www.bankinhausanovels.com.ng
yadda aka sa machines din da yadda ake aiki da su. Nan suka wuce control room din inda ake ganin komai na farm din, da yadda ake sarrafa komai.
A nan dai Bahijja ta bude baki tana kallo ta zama yar kauye, ta kalli Deeni cikin tsananin farin ciki ta ce, “Tabbas ka ci gaba, ina murna da wannan ci gaban naka sai kace ba a Nigeria ba, zan so a ce ka bude irin wannan a Arewa saboda wahala da jama’ar Arewa suke sha, in suna bukata ba sai sun zo har nan kudu ba.
Ya ce, “Insha Allah zan bude Arewa farm,” ta yi
murmushi ta ce, “Allah ya yarda.”
Bayan sun gama zagayawa sai suka nufi farm house din, nan da nasu ta ji zociyarta ta cika da fa
rin ciki da nishadi.
A wannan yammacin Deeni ya nuna wa Misbah kauna sosai irin wacce ya dade bai nuna mata ba, sun yi soyyaya sosai ta yadda kowanne daga cikinsu ya kasance cikin farin ciki da nishadi da kewar dan’uwansa, musamman yadda aiki ya sa kowa gaba, sun dade ba su ba wa juna lokacin juna ba sai a wannan daren.
Deeni kwance jikin Misbah ya yi mata alkwarin ba mai shiga tsakaninsu, ba kuma abin da zai raba su, sabani ko rashin fahimta ba za su taba shiga tsakanin su ba, saboda iya zaman da suka yi da juna na isawon shekaru suna son juna. Sun yi alkawarin ba boye-boye kuma ba rashin fahimta a tsakaninsu.
Ya kara manna ta da jikinsa ya ce, “Misbah, ina son ki yarda da ni, ba zan taba cutar da ke ko cin
Www.bankinhausanovels.com.ng
amanarki ba, haka kuma bani da sirri da zan boye maki, ki yadda da so da kauna da nake maki. Amanace na rike ki, idan na ci amanarki, Allah ya saka maki.”
Misbah ta ja dogon numfashi ta ce, “Na yarda da kai Deeni, kuma na yarda da nagartarka da duk wani abu da ya fito daga bakinka, kai mutum ne mai gaskiya da rikon amana, kuma mun riga mun zama daya, ba sirri ba boye-boye a tsakaninmu, kuma na yarda da soyayyar da kake mani, kai amintacce ne a wurina, duk da dan-Adam ajizi ne, ni na san Deenina cikakken mutum ne mai adalci da gaskiya tare da rikon alkawari, duk wasu alkawuran da ka mun ina sane da su kuma ina da tabbacin za ka cika su
“Haka ne, ni ma duk alkawuran da na yi maka zan cika su, daga ni har kai mun san mahimcin cika alkawari, karya alkawari yana daya daga cikin alamun munafukai, wanda na tabbatar daga ni har kai ba ma ciki, na yi alkawarin juriya da hakuri da kai, da daukar nauyin sa ka farin ciki kamar yadda ka dauki nawa nauyin na sa ni farin ciki.
“Ka san ba abu mafi dadi da kwanciyar hankali a rayuwar ma’aurata irin su kasance masu faranta wa juna rai, kar su bar juna cikin kunci da damuwa, wannan shi ne babban nasara da muka fara samu a rayuwar aurenmu. Ina alfahari da kai Deeni, ba ka taba bari na na yi kwanan bakin ciki ko yini cikin bakin ciki, ko bari na cikin bacin rai ba, kana
Www.bankinhausanovels.com.ng
kokari har sai ka gannni cikin walwala, wannan ya kara min ganin kima da darajarka.
“Hakan ya sa na kudiri aniyar zama da kai a rayuwa, duk wuya duk dadi, ka san duk yadda mutm ya kai da kokari da hikima da ilimi, idan yana cikin kunci ba ya iya aikata komai, da shi da wanda bai sani ba duk daya suke, yadda ka ba ni mutunci da muhimmaci da daraja da daukaka shi ya sa nake yi ma komai kuma yana tafiya min daidai yadda nake ji, ko matar shugaban kasa ba za ta nuna min jin dadi da alfahari da miji ba, ina godiya matuka Deeni, tsakanina da kai sai addu’a, Allah ya biya ka da gidan Aljanna, ya ba mu ikon zama ma’aurata har a gidan aljanna.”
“Ameen Misbahna ” ya fada yana sumbatar goshinta tare da furta cewa, “Gaskiya, yau na ji dadi kasancewa tare da Misbah, wacce har yake tunanin cewar ba za a samu mace irinta ba, halayyarta da kyakkyawar zuciyarta ya sa ba a iya lura da kurakuran ta.
A yau, yana so ya fada mata maganar Farida, amma ta ina zai fara, saboda ya san Misbah takan iya fahimtar komai, amma ban da maganar Farida, saboda Allah ya jarabce ta da kishin Farida, da duk iya kokarinta amma ba ta iya boye shi tsakanin son da take ma Deeni yasa kishin Farida ya zama tamkar wata masifa a zuciyarta, saboda tana ganin cewa ita kadai ce macen da Deeni yake so fiye da kowa wanda a zahiri ba haka ba ne.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Tabbas, Deeni ya so Farida, so mai tsanani amma zuwan Misbah sai rayuwarsa ta sha gaban Farida, babu macen da zai hada son ta da na Misbah, amma Misbah ta kasa fahimtar hakan. Ita mace ce mai ilimin sanin halayyar dan-Adam, abin da ya shafi tunaninsa da zuciyarsa, bayan karantawa da ta yi, wannan wata baiwa ce da Allah ya yi mata ta musamman, sai dai duk da haka zai jure ya fada mata, saboda yadda suka taso babu boye-boye ba karya tsakaninsu.
Haka nan suke, abokan shawarar juna. Nan ya dagota tare da kifata bisa faffadan kirjinsa, wanda har sai da dukiyar Fulanin ta shiga kogon kirjinsa, ya ji ta tana tadar mashi da wani irin tsananin sha’awa, lallausar fatarta da mamanta masu laushi suka taba shi, ya ji tsananin son ta tare da kaunarta suna ratsa shi, tuni ya ji ya fara fita daga hayyacinsa, take ya soma sumbatar ta da tsotsar duk illahirin jikinta. Ba ta yi kasa a gwiwa ba ko nuna gajiyawa ta ba shi hadin kai tare da yi masa abin da yafi so, tana faranta masa rai. Nan take suka biya bukatun junansu cikin so da tsananin shaukin juna. Abu guda da ya fi burge shi da Misbah ke nan, ba ta taba gundurar sa ko yau ta fita a ransa ba, abin sha’awarta ko da yaushe ya kalleta sai ya ji tana attracting dinsa.
Bayan sun kintsa, sai ya kalle ta ya ce, “Thank you my Misbah, Allah ya yi maki albarka, ina jin dadin kasancewa tare da ke, kina faranta min rai,

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *