RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 14
Nafisa ta tashi zaune, ta ce Hamida ta saka
mata pillow zata jingina. Ta ce “Hamida yanzun
Karfe nawa?” Ta ce,
“Tara na dare.
Nafisa ta CE
“Tabdi! Kin san wai me nike son ci?”
Hamida ta yatsina baki ta ce, “A’a
Ta ce
“Zogala! Ji wata fitina, ni da bai dame ni ba
Hamida ta ce
“Ni yanzun ina za a samu wani
zogala?” Nafisa ta ce,
“Kira min Ya Shatima.”
Yana dakin Aliya daidai lokacin da wayar tayi
ringing, ya zo daidai da lokacin da Salma tayi
sallama a dakin na Aliya, hannunta dauke da
littafin ta wanda za”a koya mata,
Aliya ta amsa, sannan Shatima ya kalleta bayan
ya dauki wayar yana duba suman. Zumbur! Ya
mike tare da daga wayar ya ce, “Nafisa!”
Hamida ta ce,
“Ni ce, ta ce kazo* Ya ce,
“To
gani nan zuwa.Ya kalli Salma
“Ya aka yi?”
Tace,
“Yaya dama assignment ne za a nuna mini.”
Ya kalli Aliya,
“Duba mata don Allah, bari in je
gurin Nafisa in ji
Aliya tayi
‘yar dariyar yake tace WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
“Sai ka
dawo, don Allah ka ce ina yi mata sannu.
Yana fita Aliya ta kalli Salma kallon sama da
kasa irin kallon wulakanci da raini, ta ce “Aka yi sati da Lahadi duk ba ki tuna da assignment ba sai
yanzun da ki ka ganshi a nan dakin? To bari in ja
miki kunne, duk ranar da yake dakina na haramta
miki zuwa.
Salma ta ce, “Anty don Allah kiyi hakuri, ina ta
tunanin yanda zan ma Yaya magana ne,
” Aliya ta
fizgi takardar tana dubawa. Salma ta cE
” Anty
bari ki ga yanda aka ce….
Aliya ta katseta da cewa,
“Da Allah ni yi min
shiru, ke ce za ki nuna min, tun kafin a haifi uwar
me alli Balbela take da farinta.”
Salma ta ce,
“Me ki ka ce?” Aliya ta ce,
“Tun
kina^yar mitsitsiyarki ni ke zuwa boko, kuma
muke rubuta maths.
Salma ta ce, “Yi hakuri.”
.” Don ta lura Aliyar
tayi maganar cikin fushi ne. bata koya mata ba, sai
dai ta rubuta ta bata tare da cewa gashi nan ni bani
da lokacin yi miki wani nune-nune.
Salma taje daki tana dubawa cikin kokwanto,
tana tunanin gaskiya da kyar in haka ne, amma
zata je da shi Makaranta ta nuna ma Salma
Dankasa
Shatima ya shigo,
“Ina Salman?” Ta ce,
“Nayi
mata ta wuce, yarinyar nan Allah Yasa dai tayi
karatu, naga dan abin da ta kasa ganewa,
ga takardarta duk ziro
Ya ce,
“To don Allah ki ke taimaka mata, sai a
hankali.
Aliya ta ce,
“Har Lesson na ce zan ke yi
mata.” Ya ce, “To ai ko na gode. Yanzu ina zan
samu zogala?” Ta ce, “Wake so?” Yace”Nafisa.Ce. WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
Tace
“Gashi dare ya yi. Amma ka tambayi
Maigadi, in za’a samu danye sai a
dafa mata
yanzun ayi mata kwado.
Ya ce,
“Haka ne.
Maigadi ya ce, “Can makotan suna da shi
Sai gashi an samu, nan da nan Aliya ta zage ta
dafa, ta cE
“Sai kuma in da za a samu kuli-kuli
Nan ma Maigadin aka sake tuntuba. Shi ya bazu
cikin unguwa sai kusan sha daya saura ya dawo.
Kura-Kura aka samo. Aliya dai aka zage aka
daka, ta kwadanta mata. Nan ya
dauka ya kai
mata. Tasa a gaba kuwa tayi ta ci, cikin ikon Allah
kuma sai gashi bata yi amai ba,
Salma tana zuwa Makaranta, ta nuna ma Salma
Dankasa, Salma ta ce
“Wa ya yi miki?”
Tace
*Matar Yayana
Salma ta ce,
“To ba daidai bane.
Ta dauko littafinta ta nuna mata.
*Kin ga nIfa.
* Salma mamaki ya cikata, amma ta share tace
‘”Bari ta sake kwalewa sai tayi kafin Malaminsu ya
ISO.
Amna cikin bacci taji karar wayar Shatima. Ta
kalle shi yana ta bacci, da alamu yau ya gaji sosai,
don sun je Abuja ne sai ma goma ya shigo gidan.
Ta kai hannu ta shafa fuskarshi,
“Honey ana WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
kiran wayarka tun dazu.” Ya bude ido da kyar, taCe
“Ka gaji ko?” Ya ce,
“Na gaji sosai.”
Yana
daukar wayar daidai lokacin kiran ya tsinke.
Yana dubawa yaga sau tara ana kira. “Nafisa!”
ya furta da karfi tare da mikewa tamkar bai taba
bacci ba. Amna ta dube shi, “Wai ina za ka?” Yace,
“Nafisa, ina zaton jikin ne.”
Amna ta sakko itama bata yi mishi magana ba,
illa dai taje ta murda makullin kofa ta cire key din
tare da fadin, “Ba za ka fita ba. Na gaji da irin
wannan abun, don ciki bai fi ciki ba.
Saboda salo bata tashi kiranka sai ranar da ka
ke dakina? Sau biyu tana yi min haka, ba zan bari
tayi na uku ba, tunda naga abin nata yana neman
ya zarme.
Shatima ya ce, “Haba Honey, kin san fa cikinta
ba irin naki ba ne.
Ta ce, cikin mamaki,
“Au!
Dama akwai wani ciki na musamman ne wanda
kayi mata shi ni baka yi min ba?” Ya ce “Ba haka
nake nufi ba, nata cikin me yawan laulayi ne. Don Shatima ya kira. Hamida ta ce,
“Tun dazun
yake kira.” Aliya ta ce “Bar shi kar ki daga har sai
ya fito, in yana dakin wannan ‘yar gwal din ba ya
iya fitowa, yanzu dubi jikin baiwar Allahn nan
amma ya wofintar da ita. WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
Hamida ta ce
“Allah nima abin ya bani haushi,
na kira shi ya fi sau ishirin amma bai ko daga ba
Da ya daga ya ce min yana zuwa shine fa shiru
Aliya ta ce,
“Sai ga shi ya kira ni wai inzo
Hamida ta cE
“Ai mun gode, Allah ya saka da
alkairi. Ai har Mamanmu na fada mata irin
taimakon da ki ke mana.
Aliya ta ce,
“Ai yi wa kai ne.
.” Sai da aka kira
sallar Asubahi sannan ta koma dakinta.
Shi ko Shatima zama ya yi a kan durowar gefen
gado, yana ta kiran layin Aliya, ita kuma ta baro ta
can dakinta domin da ta Nafisa ya yi ta kira yana
tambayar Hamida ko Aliya tazo? Tana fada masa
cewa bata z0 ba.
Bayan yayì sallah ya ce “To yanzun sai ki bude
ni in dubo ta ko?”
Ta Ce
‘”Ai ba yanzun ka ke zuwa ba.
Ya cE
“To yanzun kuma zamu iya
samun matsala tunda gari ya waye
Ta ce,
“Mu
samu mana, dama nasan ba zaka kula dani ba kaje ka rabo ni da gidanmu ina can cikin tattali
kaje ka dauko ni.” WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
Ya ce, “Kin raina kulawar da nake ba ki? To ki
fada min abin da ki ke son in ke miki don ki
tabbatar da ina kula da ke
” Ya fada ranshi a bace.
Ta ce
“Ga shi ka kwana zaune kana dakina
zuciyarka na gurin wata.”
Ta ce, “Yiwa kai ne dai,
kuma bana fata kema wata rana in haka ta faru za
ki ji dadì in ta hana ni fitowa in wofintar da ke?”
Ta ce”Ni dai ba zan bude ba, dama ka shiga
wanka in ba haka ba zaka yi lattin zuwa office.”
Ganin da gaske ba za ta bude ba, ya bi shawarar ta
ya shiga wanka. Kan ya fito ta bude sai ya fita
zuwa dakinsa ya hau shiri.
Bai ko kalli karin da Ladi Mai aiki ta hada
mishi ba, ya nufi fita. Kofar a damke take, ya
waigo ta fito tana tsaye a falon. Ta ce,
“Ga abin
karinka.
” Ya girgiza kai, “Bana jin yunwa.
Ta ce,
‘”Ai ko ba za ka dakin wata ka karya ba.
Ta soma hada mishi shayi, Har gurin Kofar ta
Zota bashi. Ya amsa tare da fadin “In da ace za ki
ke hada min ko shayin ne a duk ranar da nike
dakin ki da na yi tasa miki albarka WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
Ya kai
Karshen maganar tare da kurbar shayin
Da sauri ya watso shi domin suga ya ji har
cikin kwakwalwar kanshi. Ya mika mata shayin
“Ga abin ki, bude ni.” Ta kalli agogo, duk abinka
sai shida ta cika,
Ya ce,
“Amna har yanzun ina mamakin ki
sosai, ashe kin iya mugunta har haka?”
‘ Ta ce,
Na daina bari ana raina min wayo.”
Ya jingina da
bango,
“Shidar dai saura minti hudu.
Ta ce,Inma minti daya ne sai ya cika.”
Ya samu Nafisa a yan da take, ya kira Likita
ya ce zai kawo ta asibiti don fa jikinta ya yi laushi
Likitan yace
“Ko ka kawo ta babu abin da zamu
¡ya mata da ya wuce wannan ruwan. Amma zan
fita zuwa asibiti, ka fito bakin titi in same ka sai
muje in ga.jikin.
Haka kuwa Shatima ya fita ya yi jiran kusan
minti biyar kafin Likitan ya iso. Shi kanshi Likitan
ya tausaya ma Nafisa, ya ba da wata allura ta
tsaida amai, ya ce ayi mata a gani. Amma ciki irin
wannan Kila sai ta kai wata biyar zata samu dan
Salma tana ta jiran Shatima har takwas ta gota
Ta fito taje dakin Aliya nemanshi. Aliya ta ce an fada miki nan yake?”
Salma ta ce,
“Ni wallahi
yanzun bana tuna in da yake.”
Ta ce, WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
“Yana dakin Amna.
” Har zata wuce sai
taga sun fito da Likita. Ta rusuna ta gaida su,
sannan ta ce.
“Yaya mun yi latti.
Ya kalli agogon
hannunsa. “Haka ne, ya ba ki tafi ba? Nafisa ce ba
lafiya ban san lokaci ya tafi haka ba.
Ta ce,
“Anty ba lafiya, bari in dubata.
Sun
gaisa da Hamida, sannan tayi wa Nafisar sannu.
Ranar latti taje Makaranta, sai da ya roka aka bude
mata don har sun ce ta koma.
**
Wata ranar Litinin misalin Rarfe biyu da minti
bakwai. Salma ta sauka daga kan Mashin a bakin
Gate din gidansu. Ta ba mai mashin kudin sai taga
bakuwar mota zata shiga gidan.
Maigadi yazo yana tambayar Direban gurin wa
suka z0? Salma ta kalli Direban, kamar ta taba
ganinshi a wani guri. Sun yi kama da Shatima
kadan.
Taji lokacin daga bayan motar an ce,
“Uwar
Maigidan ce
Gaban Salma ya fadi, domin ko a
ina taji muryar Hajiyar Shatima ba za ta manta ba.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE
WWW.DAILYNOVELS.COM.NG