RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 2 BY HALIMA K/MASHI
Yace Hajiya, Ki saurare ni zan yi mikI bayani
yanda za ki fahimta’
Ta mike tana fadin,
“Kana bata min lokaci, ga WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
shi can ana kiran magariba. Ni kawai cewa na yi ka
saki waccan abin”, Ta nuna Salma wadda ke durkushe
a kan Kafafunta, tun gurin da aka titsiye ta Kafatunta
sun yi sanyi sun sage, har ba ta san ta yi motsi mai
karti don azabar da suke yi mata.
Shatima ya ce, “Hajiya.
Ta sake katse shi,
“Bana son jin komai daga
gare ka, sakinta kawai na ce ka yi. Ba zan fahimci komai ba”
Alhaji ya fado Takin babu sallama, ya amshi zancen Hajiya da cewa,
“Wa za a saki?”
Shatima ya mike da sauri tare
* da fadin,
*Alhamdu lillahil.
Alhaji Musa ya ce,Zauna Babana, zauna kar
ka sake faduwa
Alhaji ya isa gaban danshi da sauri ya kama
shi, ya zaunar tareda fadin, “Zauna abinka
Shatima ya zauna cikin farin ciki, tare da ci
gaba da yi wa Allah godiya.
Hajiya ta yi matukar girgiza, mamaki ya cika ta
da gain Alhaji. A zuciyarta ta ce,
“To wa ya fada ma
Alhaji?”
Alhaji ya dube ta rai bace, fuska daure, “Yanzu
Hajiya Amina kin yi daidai kenan? Ki taso tun daga
Zaria da sunan gaida mara lafiya don ki samu lada,
amma ki buge da tada husuma cikin gidan danki?
Ina hankali da tunaninki suka shige? To wa kike fadin
fadin a saki ma?”
Ya kalli Alhaji Musa,
“Dubi wani abin kunya
don Allah
Alhaji Musa ya ce
“Ga wadda za a ce ta yi abin
kunya nan. Kin z0 gidan
“yarki gaban kishiyoyi, gidan
suruki kin tada hankali? Wannan abin fadin da me yayi kama? To da kin yi sanadin rayuwarshi, me za ki
Ce?”WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
Hajiya cikin borin kunya ta ce, “Ni ban tada
wata husuma ba.
Wane munafuki ne ma ya kira
Alhajin?”
Ta kai Karshen maganar tare da kure Mustapha da ido.
Shatima ya ce, “Alhaji, don Allah ku zauna, ni
dai na gode wa Allah da ya turo mini ku a daidai
wannan lokacin. Don Allah ku taimaka min ku zauna
don a warware wanna matsalar. Domin duk wata
matsala a duniya ana warware ta ne ta hanyar zama a
tattauna ba ta „anyar tashin hankali ba. Ba kuma ta
hayaniya ba
Alhaji yace “‘Mu yi sallar magariba tukunna
ko?”
Hajiya ta ce, “Ni fa kawai a yita ta kare, ya
saki *yar can mu kama gabanmu”. Ta fada tare da nuna
Salma.
Duk suka dubi gurin da Salman ta ke a
tsugunne, sai lokacin Alhaji ya ga Salma din.
Hajiya ta ci gaba da fadin, “Ni fa duk wannan
abin lafiyarsa ni ke yi ma wa, ku ba za ku fahimta bane an fada min cewa uwar yarinyar nan ta je ta kai
sunan Shatima an tsaface shi don ya dinga kashe musu
kudi. An hada asirin da yawun bakinta, an yi surkulle
an ba shi ya ci. Kuma asirin ya ci shi domin ga shi
yanzu duka yaushe aka yi auren ma ya sa ta a
makaranta mai tsadar gaske, kullum sai ya ba ta dubu WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
da dari biyar. Ita na haifar ma shi kenan?” Salma ta fashe da sabon kuka tana fadin. “Na
rantse da Allah Hajiya, Innarmu ba ta zuwa gurin masu
asiri. Ko Babanmu da yake da ciwon Barin jiki cewa tayi
yi kar a kai shi grin masu maganin gargajiya ciwonshi
na asibiti ne kar su bata masa jinya su ce wani ne ya yi
masa asiri. Allah na rantse ba mu taba yi wa Yaya asiri
ba. Allah ma ba zai barmu ba, domin shi taimakonmu
ya yi. Na sani ban kai Yaya Shatima ya aure ni ba, mu tsoro ma muka ji da ya ce shi zai aure ni. Ga ma Yaya
din a tambaye shi, ko ruwan gidanmu bai taba sha ba
bare har ma mu ba shi nama ya ci”
Ta saki ajiyar zuciya, sannan ta karasa maganar
a hankali,
“‘Ko yanzun da nike matarshi bai ci abincina
ya kai sau goma ba. Cewa yake ni ban iya girki ba”
Ta jero shesshekar kuka a tare, sannan ta ci
gaba da gunjin kuka.
Alhaji ya kalli Hajiya,
“To ke da ki ka ce an
fada miki, wane ne ya fada miki din?”
“Hajiya Azumi ta yo min tambaya a gurin
malamai, kuma ta ce guri biyu ta je duk bakinsu daya
Alhaji ya kalli Alhaji Musa ya ce, “Ka ji ko?
Imaninta ta saida a gurin makaryatan bokaye. To da WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
izinin wa ki ka je?” Ta zaro ido cikin firgici, ta ce,
“A’a Alhaji, Niba zuwa nayi ba. Ina fada maka Hajiya Azumi na aika
Shatima ya amshe zancen da cewa,
*Alhaji,
kamar yanda Salma ta fada ne, ko ruwan gidansu ban
taba sha ba. Hajiya ma da ta yarda da wanna karyar ta
so ta yarda ne. domin ta fi kowa sanin yanayina domin ba
kowane abu ni ke iya ci ba,
Kuma kudi da Hajiya take magana ina ba
Salma, ita ce ma ba ta samu gatansu ba, komai na
sauran matana ya fi na Salma. Gida da Hajiya ke
magana haya ce na kama musu, ba siya na yi ba don ko alakar aure ba ta hada ni da ‘yarsu
ba ina yi musu. Taimako irin wannan ban san adadin
da na yi ba, Munnir ya san haka ba sai na zo na ce
Hajiya, ko Alhaji na taimaki wasu ba. Haka ko a hanya
na sha kashe rigimar kudi da aljihuna in wucce Ba ina
fada ba ne don alfahari ko gori ba, ina son a fahimce
ni.
Maganar kudì wane magulmaci ne ya fada?”
Aliya ta ce, “Ai na sani kudin nama ne ka ke ba
ta, mu kuma kana saka mana nama a fridge. Na fada
ma Hajiya” WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
Shatima ya kalli Alhaji,
“Ga su nan rago na
dubu talatin-talatin nike siya musu su uku, kowacce a
gyara a saka mata a fridge ga kaji guda goma-goma na
wata daidai kenan, amma cikinsu na Amna ne kawai
ya kai watan. Su kafin haka nasu ya fare, ita ko Salma
dubu daya a wata, dubu talatin, sannan bana sai mata
kaza. In na siyo gasasshiya har da su nike saye. Haka
kuma akwai kudin kati da nike saka musu duk sati, ita
ko ko wayar ma ba ta mallaka ba bare kudin kati ya je
mata
Shatima ya dubi Hajiya,
“Zancen makaranta
kuwa,
alkawari na dauka tsakanina da mahaliccina
cewa, zan taimake ta tuñ kafin in yanke shawarar zan
aure ta
Ya numfasa sannan ya kalli Mama,
“Akwai
abin da ba ku sani ba. Babu son Salma ko digo a cikin
zuciyata, so na soyayya dai sam babu wannan. Na auri
Salma ne don in taimaki rayuwarta ta yi karatu. Ta so
in aura mata wani ne, in mata kayan daki don ta cika
burin Babanta. Ni kuma na aure ta don ta cika duk
burikan guda biyu ne. Zan iya zama da Salma har karshen
rayuwarmu, in kuma da zuri’a a tsakaninmu har mu
samu rabo, ba zanyi Ki ba. Amma ba don so ba. In kuma WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
tana bukatar rabuwa da ni yayin da burinta ya cika, zan
iya sahale mata ta je ta auri wanda ta ke so, yake sonta.
Ban fadi haka don cin fuska ga Salma ba, sai
don hakan shine gaskiya, kuma Hajiya ta gane cewa,
Salma ba su yi min asiri ba
Salma kanta a sunkuye wasu zafafan hawaye ke
zuba a idanunta masu radadi. Tun da aka soma rigimar
bata tsinci kanta cikin bakin cikin da ya kai na yanzun
nan ba. Kalaman Shatima sun yi tsauri, kuma sun yi
ma zuciyarta daci, sannan sun yi ma kwakwalwarta
nauyi. Har ma ta ji da ma ya bi umarnin mahaifiyarsa
ya sake ta din zai fiye mata jin wadannan munanan
kalaman da suka fito daga bakinsa. Ta soma rainon
zuciyarta, har ta soma koyon sonshi, da tantance son
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.DAILYNOVELS.COM.NG