RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 16 BY HALIMA K/MASHI
sunan Amna, Aliya da ke zaune kusa da maijego a bakin gado tana sauraron hirar da su Nafisa suke yi ita da yan uwanta. Nafisa ta ce,wai da sunan Mus’ab wa ta yi muku cake na ji ana ta labarin dadinsa
Ta ce, Gidan Alhaji Sani ne
Nafisa tace
“Don ni ma duk abin da ya yi ma
wacca matar a sunanta ni ma fa haka zai min
Aliya ta ce,
“Kar fa ki ce komai, kin dai san su
suna da halinsu, wani abin da kansu za su yi Nafisa ta ce,
“Ina ruwana, dole dai ya yi min duk abin da ya yi mata”Aliya ta ce,
“Ni ban ce kar ya yi miki ba, amma
kar ki ce komai
Safina tace
“Dole ya yi mata mana, don su masu kudi ne?”
Nan dai suka shiga surutu. Aliya ta ji dadin
haka, domin ita ba taqi su kwabe ita da Shatima ba. Nafisa tace
“Ni ya zo mu yi maganar kayan
fitar suma, don su ma irin nata nike so’
Aliya ta ce, “Sun ko yi kyau kayan sosai”
– Nafisa tace
“Ai irinsu sak zai min”.
Haka dai suka yi
ta mata famfo tana hawa kamar farashi.
Salma tana son zuwa suna, amma ta san ba za a
barta ba. Hanya daya ce kawai ta saka Aliya ta nemar mata izini, Ta san Aliyar za ta yi tunda tana son irin haka.
Ta riski Aliya a dakinta, tace
“Anty ina son
don Allah ki rokar min Yäya, ina son zuwa suna ko zai bar ni”
Ta balla mata harara, “Ke ba ki da baki ne?”
Salma ta ce, “Ai ba zai saurare ni ba ne Anty,
ke kadai yake jin maganarki ba ya miki gardama
Salma ta fada cikin son tula mata kasa.
Aliya ta saki murmushin jin dadi, ashe har
mukaminta ya kai haka? Kishiyoyinta har sun gane ita
din babba ce, gaskiya abin ya yi mata dadi. Wannan
sokuwar ma ta gane bare sauran, lallai ita ce a sama.
Cikin isa ta ce, “Shi kenan, je ki zan tambayar
miki”
Salma ta ce, “Na gode”
Shatima ya zauna a bakin gadon fuskarsa dauke
da murmushi, ya amshi jaririnsa daga hannun Hamida.
Ya kalli Nafisa wadda ke cin gasasshen nama a cikin
faranti, ga yaji tana dangwala.
“Sannunki mai jego”
Ta ce,Sannu mijin maijego”
Suka yi
“yar dariya. Ya kalli yaron Babana din
nan fa yana kama sosai da Jafar”
Ta kalle shi, “Wane ne Jafar?”
Shatima ya ce, “Yayanshi mana
Ta dan tabe baki, “Ni dai wannan ya fi min
kama da kai”
Ya yi murmushi a ransa ya ce, Nafisa sarkin
son kai. A sarari ya ce,
“‘Duk su biyun suna kama da ni
ne. Wannan ya nuna karfin jinina ne”
Ta yin murmushi, “Menene kuma na yin
al fahari?” ›murmushi yayi Yace
“Dole in yi don duk wanda ya dube su
ya san yayana ne babu bata lokacin kwatance”TaceKa, Ni lokaci yana ta tafiya
amma ban ji kayi maganar kayan suna ba Yace,Kayan suna kuma?” Ta sake kallonshi,na fitar suna mana Ya ce, *Shi nazo mu yi magana. Anty Momiy ba tazo ba?” Ta ce, “eh bata zo ba Yace,zatazo takawo miki kayan ki zaba.Kala uku za ki dauka, Aliya ma a bata guda daya”Nafisa ta Ce,
“Irin kayan Amna kawai za a
kawo min, ko.ba ita cè ta kawo mata ba?
Ya ce, a,a bansan inda suka sai kayansu ba, Nafisa ta dube shi cike da zargi. Tace Kawai dai ka ce ita ka yi mata irin nasu na
masu hali, ni kuma ka yi min na daidai ni
Ya. tausasa murya da nufin. kwantar mata da
hankali, ya ce, “Nafisa in na fada miki cewa.banyi,. wa
Amna kayan fitar suna ba za ki yarda?”
Ta sake hade rai, “Ba zan yarda ba gaskiya?
Ya ce, “To ban yi mata ba, kuma ita da kanta tace in barshi”
Ta tura baki, “Ni dai a yi min adalci ah to!”
Ya dan daga murya don nuna jin zafinsa, *Kina
sa ran zan cuce ki kenan?”Ta yi shiru.
Yace
“To na gode”
Ya mike ya kwantar da yaron a kan gadon ya yi ficewarsa. Suka yi kici6is da Mama ta fito kicin da
Fulas na ruwan zafi za ta dakin mai jego.
Ta ce,
“Ba dai har ka fito ba? Ga abinci can
Hamida za ta kawo maka’
Ya ce, “Na koshi Mama. Nafisa ce ta bata min
tai?
Ta ce,
“Nafisa ko?” Ta aje kayan tare da fadin,
Zo nan”
Ta shiga dakin su Hamida. Ya fada mata duk
yanda suka yi, ya ce,
“Mama Amna ban sai mata kaya
ba, saboda ta ce kudin abincin da zan ba ta ya yi kadan
kuma ba ta son a ce na kasa”
. Ya fada mata duk yanda
suka yi da Amna. Mama ta Ce,
-Kai Nafisa kishi yana son ya
maida ta mai hassad
Ta dubi Shatima,
“Kana ji ko Baba, ka kwantar
da hankalinka, shirme ne ma in tace za ta hada kanta
da Amna. Abin da za a yi idan Momiyo tazo kawo Kayan, to ka zabi wanda ranka ya yi maka kuma daidai
Karfinka ka siya. Batun abinci kuwa babu takura, duk
abin da Allah ya hore shi za a yi. Duka yaushe aka
gama waccan sabgar? Mu ne fa iyayenka, mune masu
yi. Don Allah ka kwantar da hankalinka ka ji ko?”
Ya Ce,
“Balle ma ita ma zan mata komai da
yardar Allah. Na fi son ta kwantar da hankalinta Mama ta ce,
“Babu komai ka kwantar da naka,
ita ma za ta kwantar da nata hankalin”
Ta so ya ci abincin, yace ya koshi.
Gidan Hajiyanshi ya wuce: Tana zaune a falo,
Ya gaishe ta, ta ce,
“Zuwan kenan?”
Ya ce,
“A’a tuni na zo, daga gurin su Nafisa nake
Ta ce,
“To ka sallame su ko?”
Ya ce,
‘”‘Abin da na je kenan. Anty Momiyo ba
ta kai mata kayan ba ma”
Ta ce,
“Ni dai ka yi mata komai kamar yanda
da yi wa Amna, bana son ka yi rashin adalci tsakani,
bare wasu zantuka ma su shigo. Allah ma ba zai bar kaba
Yace
“Insha Allah ba
zan canza daga
tarbiyyarku ba Hajiya, kuma Amna kudi na bata shi ne
Da na so da Anty Momiyo ta zo ta kawo kayan da na san
ko na nawa ta dauka, sai in ba ta sauran kudin kamar
daidai adadin kudin da na ba Amna
Hajiya cikin gamsuwa ta
ce, To ka kira
Momiyo din kawai mana’ Ya ce,
“To, bari in kira ta”.
Bayan sun gaisa ya ce,
“‘Anty ashe ba ki kawo
mata kayan ba?”
Ta ce,
“Kai dai bari Shatima. Autana ne ba shi
da lafiya, ka ganshi nan yanzun nan na gama ba shi magani ya kwakkwara amai”
Shatima ya ce,
“Allah sarki. To Allah ya ba shi
“lafiya. Ya za a yi kenan?”
Tace
“Gobe insha Allahu zan zo in kawo
mata” Ya ce,
“Uku za ta dauka.
“Yan nawa-nawa ne?”
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe