RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 17 BY HALIMA K/MASHI
Ta ce, -Atamfa ishirin da biyar, leshi kuma
talatin da biyar
Ya Ce,
“Ta Gauki leshi guda daya, atamta biyu.
Nawa kenan?’ Tace,
“Tamanin da biyar
Shatima yace
“To a bata haka. Sai kuma ita
Aliya a bata leshi guda daya”
Ta ce, “To ‘yar gidanka fa?”
Ya ce, “Barta wannan, ba lallai ta zo sunan ba
ma. Kuma ga biyan kudin makarantarta. Gaba daya kudinki zai zama dari da goma ko?”
Ta ce, Haka Yace
“To za a dai daga min Kafa
Ta ce, Babu komai”
Bayan sun yi bankwana ya dubi Hajiya,
“Cikin
dari da hamsin an cire tamanin da biyar, saura nawa?”Hajiya ta ce, “Sittin da biyar”
Ya ce, “Shine abin da zan ba su su yi girki.
Domin Amna ma dari da hamsin na ba ta
Ta ce, “Na ji kana a ba Aliya leshi, ita gudar
fa?”Shatima ya ce, “Kyale ta ba dole ma ta je sunan ba fa”
Hajiya ta yatsina fuska, “Ni dai bana son a ja
– sunana a ce ni ce na hana a yi wa wani
– Shatima ya ce,Ga kudin makarantarta, sannan ta shiga islamiyya da hadda kwanan nan’ Hajiya ta tabe baki tare da fadin,
Umm, ku dai ku ka sani
Ya mike, “Bari in leka gidan Munnir in wuce”
Ana gobe suna Salma ta koma gurin Aliya, don
ranar dakin Aliyar ya kwana, tace
“Don Allah Anty
kin ko tambayar min zuwa gidan sunan din?”
Aliya ta tabe baki, “Na manta sam. Amma bari
dai ya dawo”
Duk da haka Salma ta tura mishi sakon cewa.
za ta je kitso da Talle a makota. Ok kawai ya turo mata.
Aliya don ta nuna ma Salma gadara, bari ta yi
sai da Shatima ya dawo ya shiga dakin Salma, sannan tabiyo shi za ta tambaya mata unguwa a gabanta. Kai
tsaye ta shiga dakin Shatima yana zaune a tsakiyar
katifa yana aiki a laptop. Ta zauna a bakin katifar tare da fadin,
“Sannu da dawowa
Ya amsa da,
“‘Sannunki. Kafin ki ji dadin zama hado min shayi”Ta ce,
“To mijina, ko kwanciya nayi ai
dole in tashi in hado maka shayi”.
Ya ce, “Yau dare zan raba ina aiki, don ina da
aiki. Ga shi za mu yi sammakon tafiya Zaria, saboda taron suna
Ta ce,
“Yauwa, da ma na zo in maka magana ne
a kan ya kamata Salma ta je sunan nan. Fisabilillahi
yarinyar nan bana jin dadin yanda ka ke mata. Ka ga
ko zanin nan da ka sai min ita ba ka sai mata ba, banso ba na yi shiru ne kawai
Ya ce,Ki bar wannan zancen”.
Ta ce,Na bari, yanzu dai ina son don Allah ka
barta goben sai mu tafi tare”
‘Zai yi magana ta ce, “Don Allah ni za ka yi ma
wannan
Yace Shi ke nan ta ci albarkacinki”
Tace,Na gode”.
Ta jima sannan ta fito ta samu Salma zaune a
‘falo, a hankali ta ce, “Ki shirya za ki je”
Salma ta ce,Na gode Anty.
Washegari suka nufi suna, Salma ba ta ji komai
ba da ta ga Aliya ta saka sabon leshi irin na maijegon,
sun yi armashi duk da bai kai na Amna ba, amma taro
ya yi kyau tunda an tashi lafiya. Kwanansu daya suka dawo.
Kwanci tashi masu jego suka yi arba”in. sai da
Nafisa ta gama zaga dangi sannan ta dawo. Jaji gurin Antynta sai da ta kwana biyu, Anty Maimuna ta
sa aka hada mata *yan gara masu kyau. Da ma da suna cewa tayi ba za ta ba ta komai na gudunmawa ba,
ta ce za su hadu in ta yi arba”in. tun a lokacin ma ta hada mata wani tsumi wanda ta ke sha a cikin jego.
Don haka Nafisa a shiryenta ta dawo, Amna kuwa sai
da tayi wata biyu da kwanaki sannan ta dawo. Lokacin
ne aka gama zuba zama. Aliya ta soma shige ma Nafisa
kafin dawowar Amna, ta dauko Ashraf shi ne
sunan da suke kiran yaron Nafisa. A goya shi, ta yi ta wannan fi’ili bare ma in ta ga Shatima yana nan, ko in ya shigo da shi, a amshe shi a goye a baya ram!
Da Amna ta dawo sai kuma aka koma gurinta,
sam Amna ta hana danta in ta zo sai tace yana bacci, ko za a yi masa wanka da dai sauran uzuri, har
dai ta gane ba a son ba ta shine ta hakura.
Sai ma wani sabon haushi da ta tsinci kanta,
wanda kuma ba ta da damar magana. In Shatima yana dakin Nafisa ko Amna ba ya fitowa da wuri, ta san
yana can yana wasa da yaranshi. Haka dai ya kan zo da
Ashraf don Amna ba ta bada yaronta. Ya kan ba da duk
hankalinshi a kan yaron, yana yi masa wasa. Wani
‘lokacin ma ko tana magana ba ya ji, sai in ta yi dabara
ta amshi yaron ta goya, sannan za su yi hira. Hakan yana matukar kona mata rai.
• Salma kuwa karatunta ta sa a gaba. Sannu-
sannu su Salma sun zana jarrabawar fita daga J.S sun shige SS 1, har lokacin Salma ba ta kara Kiba ba sai
‘ tsawo. Amma cudanya da yaran masu kudì irin su Salma Dankasa da sauransu ya sa ta waye sosai. Babu
yanda za a yi ka ga Salma ba ka yi tunanin cewa “yar masu kudi ba ce Zuwa yanzu ta manta yanda Shatima
yake fara”a, ta fi sabawa da yanayinsa na yanzun. Tana
Kallonshi matsayin wanta mai kula da ita, kuma wanda
take shakkarsa. Sai dai ta kasa manta kalaman nan
masu muni da ya yi mata, hakan ya taimaka kwarai gurin Kara nesanta zuciyarta da son Shatima.
Har zuwa yau za ta yarda cewa, ba ta san so ba,kuma ba ta damu da ta sanshi ba. Haka lokuta da dama ta kalli kanta a madubi ta san cewa, ita ba mai kyau
ba ce, amma kuma ba ta da munin da Shatima zai ki ko da sake nuna sha’awarsa a gare ta matsayinta na
matarsa. Ta yarda rashin so ne kawai dalili. Domin don
ya neme ta sau daya ba ta yarda ba bai isa ya zama dalilin da zai sake kasa gwada sa’arsa ba. Zuwa yanzu
ta fi daukar kanta a ba matar aure ba. Hakan ya fi saka ta kwanciyar hankali. Haka kuma ba ta tambayarshi
komai sai in fita unguwa za ta yi. Game da kudi ko wani abu ba ta ce masa tana son kaza, sai abin da ya
kawo ya ba ta. In ko kudin makaranta ne, sai dai ta
kawo masa takardar banki na islamiyya kuma da ma na
shekara yake biya mata. Daga cikin kudin motanta *yar
dari biyar din nan take makalewa shine take siyan dan kayan bukata irin na mata.
Aliya dai tun tana boye damuwarta na rashin
samun ciki, har ta dawo tana nunawa. Sai dai ta kan jl
sauqi kadan in ta tuna cewa ba fa ita kadai ba ce ba ta
yi cikin ba, ga Salma nan. Shatima kullum yana
lallashinta a kan haka, sai yake ganin kamar tana
zargin shi ya kasa. Don haka da ta zo masa da batun
son neman aiki a asibiti baiqi ba, don yana son ta rage kewa. Ganin in har tana fita aiki za ta dan samu kwanciyar hankali. Ta hanyar abokin aikinsa ya sama mata aiki a
asibitin Kawo, Amna kuwa wata plaza yayanta ya siya
a kan titin Ahmadu Bello da ke Kaduna, don haka
Momi ta ce a ba ta shago daya don ta zuba kaya. Shago
biyu aka ba ta tunda suna tausaya mata, suna ganin
tana auren mara karfi. Daya aka sa mata kayan kicin,
daya aka saka mata na yara. Aka nemi masu saida mata
aka zuba, kullum take zuwa don da office dinta a ciki.
Shatima bai so- ba, amma dole ya yi shiru don
ya san ma ba za ta yarda ba ko ya hana ta. Lokacin
Jafar wanda suke kira da Junior Mamansa kuma tana ce masa Honey. An yaye shi don shekararsu daya,
Nafisa dai ba ta yi niyyar yaye Ashraf ba, sai ya shekara da rabi cif? Sai dai ita ma ta tada balli a kan
cewa za ta shiga makaranta, don ko ba za ta yarda ba
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE