WALIJAAM CHAPTER 4 BY MAMAN TEDDY

WALIJAAM CHAPTER 4 BY MAMAN TEDDY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

*🐄WALIJAAM🐄*

*_Ga masu bukatar wannan littafi xasuna iya mgn dani ta wannan link din 👇_*

https://wa.me/qr/7UGIAODZY3LON1

_Ki tausaya ma yar mutan mallawa kar ki fitarmun da littafi idan kin siya ,kema kar ki karantamun idan ba biya kikayi ba don Allah._

*_SADAUKARWA GA DUK KANIN FULANI🐄_*

*Alheri writers asso.📚*

_________________________

“Shikam Anwar ne da yake zuba idon yaga Irin cin mutumcin da Abbas zai mawa Shatun , a zuciyar shi yana godiya ga Allah don bai ta6a farin ciki da iskancin da Abbas yake mawa mata ba sai a yau ,da ya tare Shattu …wannan yasa shi ma juya masu baya ,yana jirar ji da ganin Abbas ya daga shattu ya wurga a moto sai dai kuma yaji abun da yazo masa unexpected da bai zato ko tsammani ba jin saukar marin da shattu ta wanke Abbas dashi . Ta6 Babban magana abun da nima kaina nace kenan ,Marin soja ai ba wasa ba. Wani irin huci Shatu keyi ranta na tafasa ,nan take ta juyo ga Sadeeq da shima ita yake kallo yayi mutuwar tsaye…

Shikam Anwar ji yayi kaaman ya shako Shatu ya kashe da duka don takaici  nan take tsanan ta ya dada lunkuwa a zuciyar shi…ware_ware yayi da lulun idon shi yana bin Sauran yaran Sojojin da kowa ke aikin shi babu wanda yaga komai dake faruwa.

Nisawa yayi yana mai yin Hamdala a zuciyar shi .

Shikam Abbas mamaki ne ya hanaasa ce mawa shatun komai idon shi lokaci daya ya kada ,dama shi mutum ne mai bakar zuciya ,a fusace ya daga hannu yana kaiwa saaman kuncin Shatu ,amma sai Sadeeq da yagama tsorata da Al’amarin Wannan bafullatana yayi saurin rike hannun nasa ,kamin ya girgixa masa kai…wani irin fixgar hannun sa Abbas yayi daaga garesa kamin ya kuma damko Shatu a

karo na biyu yana hadata da jiikin moton da take gyefen su …wani irin kallo yake mata yyn da hadata dam wannan moton da yayi nan jaririyar ta hau ihu tana karawa ,hankalin shatu ya tashi matuka don a wannan lokacin ganin yanda Abbas yakoma kaman wani mayunwacin zaki yasata tsorata matukar gaske. Sadeeq ne yace dashi ” Abbas ka cika ta matar Aure ce kada kayi mata komai da goyo a bayan ta…A fusace Abbs yayi mgnan ba tare da ya juya ya kalli Sadeeq ba da ce masa ” allah yasa tsohon ciki ne a tare da ita wlh sai na yi abun da nagadama da wannan yarinyar yau…ai nayi burinn ace ma A gaban mijin ta nake da a agaaban shi xanyi mata fyade “.

Wani irin abune Anwar yaji ya daki kirjin sa lokaci daya da baisan dalilin hakan ba”. Ihun da wannan jaririyar takeyi ne yake masa kai kawo a kwakwalwa…sam bai san lokacin da yayi saurin fincike Abbas daga jikinn Shatu ba da takasa motsa kanta sakamakon wani irin damka da tasha ,don har ya yarda mata da mayafi goyon jaririyar yarinyar na dab da faduwa kasa … Kai Abbas rabu da ita Daddy ne ke kirana yanxu “. Jin yanda Anwar din yayi mgnan ba da wasa ba yasa Shi cika ta ,yana wani irin jan numfashi na zuciya tare da dafe kirjin shi dake halbawa kamar zai fito .

Komawa yy yana rintse idon tare da yi mawa zuciyar sa Alkawarin kota halin kaka sai ya keta mawa wannan bafullatanan hadin ta .

Itakam Shatu ganin ta samu ya cika ta da kyar ne tayi saurin gyara goyon bayan ta  tana daukar mayafin ta tuni ta silale ta gudu ba tare da dukkan su sun lura ba . Sai Sadeeeq kadai ne yaga ta juya takoma ta hanyar da ta fito… Shiru Sadeeq yayi yana tunanin abubuwa kamin lokaci daya kwakwalwar shi ta bashi cewan Wannan Bafullatanan ba mutum bace ba ,aljana ce…

Sai a sannan Abbas ya bude idon shi da yakoma kaman an watsa mashi borkono don jah ,bin Sadeeq yake da wani irin kallo kamin yace ” Allah kasa ifritu ce wlh sai na kyeta mutumcin ta .

Bin su da Kallo Anwar yayi kamin yace ” Daddy na kirana har ya katse ban dauka ba akan wannan wahalalliyar bagidajiyar bafullatanan dajin . Mtswww tom me ma zakayi da itane Abbas ,mu wuce kawai yakamata a yau na koma gida saboda ina tunanin  Dad ya dawo “. Huuuuummmm A tare shida Abbas suka sauke numfashi kamin su shige moton nasu suna bata wuta don ko wannen su ransa a bace yake . Shikam Sadeeq ran sa ya baci don kwartancin Abbas ya fara damun shi a cewan sa yanxu yafara kokarin jawo masu balai ,tun da yafara kokarin yin iskancin shi da mutanen 6oye .

*******

Shiru_shiru Mama tana xaman jirar fitowan Asma’u a dakin nata amma shiru bata fito ba. Mikewa Mama tayi tana nufar dakin nasu wanda ya kasance nasu ne itada Teemah . Mamaki ne sosai ya kamata ganin Asma’u na salla da tsakar rana wuraren 11am. Sakin labulen dakin tayi tana komawa inda take zaune hadi da daukar tray din shinkafan da take tsinta hadi da fidda shefin dake ciki .

Tsawon lokaci sai ga Asma’u ta fito sanye cikin wata doguwar riga roba da yake kama jikin ta  ta yana karamin mayafi …Abun ka ga mamaki da Mama tayine yasata cewa” Asma’u yau kece da Sallah bama na farillah ba Nafila??. Keko me kike nema haka har kika dawo kikasan Allah daya ne??. Cewar Mama tana kallon Asma’u da itama Maman take kallo .

Murmushi tayi kamin tace ” Ohh mama kenan ,tom Teeema nake tayawa addu’a don samub miji kaman leutanant Anwar abune mai wuyar gaske . Yau zata sanar mawa Mahaifiyar sa da Abun dake zuciyarta game da d’an ta kinga kuwa sai da rokon Allah muyita jamata sura.

Wani dariya Mama tasa wanda ya 6ata ran Asma’u ,buden bakin Asma’u cewa tayi ” kai Anya Mama kece kika haifemu kuwa ? Sam baki son ganin cigaban mu ,mudai gsky idan bakece kika aifo mu ba ki fadi mana kawai munema Uwar mu mu huta . Cewan Asma’u tana wani irin gallare gallare.

Wani irin murmushin takaici Mama tayi kamin tace” hmm banyi mamakin mgnan ki ba Asma’u don dama kunsaba fadimun abun da yafi hakan ,kuma koda nayi dariya naga shashancin kune da har kuke tunanin wai auren Wannan matashin sojan ,a irin wannan dabi’ar takuce kuke wannan tunanin tabdijam….hmmm Allah sarki na tausaya maku ,bakwa ganin mahaifinku ,mahaifiyar ku da kima har daa akwai wani mutumin arxiki da kirki da xaiso hada zuria daku kunyi gwari kam yara !! Mama tayi maganan tana ca6e baki ,kamin tace nice mahaifiyar ku Asma kije Allah ya shuryaku abun da nake maku fata kenan a kullum kuma akoda yaushe .

Uhmm Asma’u tace tana barin mawa Mama filin tsakargidan hadi da ficewa daga gidan tana wani irin tafiya da motsare botsaren jiki da duwawu ,kunsan dai Cat Walk irin tafiyan da takeyi kenan tun tana na iskanci yanxu ya zama mata jiki .

Da kallon shiriya mama tabita dashi har ta bar gidan kamin ta girgixa kai tana cigaba da tsintar shinkafan nata.

*******

A 6anagaren gidan Dr Haulat kuwa fada ne ya kacca6e tsakanin Teemah da Zabeena ,don tun isan ta ta tadda Dr Haula bata nan tana daya daga cikin Asibitocin ta .hakan yasa Teema ta zauna a falon nata ,nan itama Zabeena ta zauna ,a nanne suka hau yadawa juna da habaici da maganganu tsawon lokaci don dukan su sun san manufan su a cikin wannan gida .

Hmmm lallai wannan shine hausawa kece mawa iska na wahalar da mai kayan kara ,ina mutum ina gwarzona Anwar ? Hmm abun ma baa hadi sam….Waye ne mutum waye kum
a ubanshi….uhmmm bari na baimawa kaina amsa na daya dai mutum dinnnan ba kowane ba face dan gidan talakawan likis…na biyu kuma uban shi ba kowane ba face cikakken misakin talaka wanda babu sana’a cikakke sai buba buga….hmmm uhmmm tom ina ke don allah ina Anwar ,Anwr nawa neni Zabeena… Kutumar ubannan Abun da Teemah tace kenan kamin ta daga ruwar dake glasscup din gavan ta tana wanke wa hadi da sheka shi saman fuskan Zabeena da tayi gigif ta mike daga tsaye ,don batasan da zuwan ruwan ba .

Itama Teeman mikewa tayi a fusace tana kallon Zabeena da take bun ta da kallon mamaki . Nine kika watsa mawa ruwa a saman fuska….cewan Zabeena cike da mamaki.

Wanii irin kallon sama da kasa Temmah tayi mata kamin ta ta6e baki gyefe tana mai cewa” kwarai kuwa kena watsa mawa ,kinsan duk sabo dameye nayi maki hakan ?? Saboda ambaton sunan Anwar da kikayi da mijin ki ,tom kisani wannan ruwan ruwa na watsa maki na gaba ruwar petir ne ko kalanzir zakiji a saaman fuskar ki na kyetta ashana na babbakaki ,wannan duknasaboda son da nake mawa Mijina Anwar ne??? .

Mijinki?? A yaushe ne Anwar din ya xama mijinki sauna? Cewan Zabeena tana fiddo da ido waje cike da bakin ciki . Kamin ta cigaba da cewa” wlh nikuma duk ranan da kika kara kirar sunan Anwar da mijinki sai na Kashe kin bar duniyar baki daya ….

Allah ko tom ko zaki kwatantan ta eiye? Cewan Teemah tana fito da ido hadi da matsawa kusa da Teemah na ki kwatanta mana .

Meye haka kuma? Meye kukeyi ne?? Shigowar Dr Haula tana mgnan murya sama_sama kaman numfashin ta zai dauke yabar gangar jikin ta .

A matukar fusace Zabeena ta juyo ga Hajiya Haula kamin tace ” kiji mun wannan shashashan yarinyar don Allah Mom “. Wai Anwar ne takeso…!!

Yau ni naga takaina Haula ,har nine Alhaji Jalingo zai yaudara ya cuceni nida da na?? Wlh bai isaba sam vazai yuwuba…Cike da mmki Zabeena take bin Dr Haula da kallo kamin tace” Momy me yafaru ne?? … Dago da idanunta Dr tayi tana watsasu akan na Zabeena kamin ta kuma kaiwa ga na Teema da take cika hannun ta stiill da glss cup din. Hmmm kuna ta hauka a cikin jaji kuna ta lalube cikin duhu ,kun jirarr jirara tom duk wanda kuka fada akansa a yanxunnan mahaifin sa ya kirani a waya yana shaidamun cewar Y aura masa wata yarinyar dani bansan taba ,shima kanshi Anwar din bai san taba …..wani irin jiiri ne ya kwashi Zabeena batasan lokacin da ta zube a saman kujera ba tana dafe kanta dake sarawa ba kakkautawa .

Itakam Teema sakin glsscup din tayi lokaci daya kwallah yafara zubo mata ta cikin kwarmin idon ta masu zafi da tafasa zuciyarta.

Itakam Mom Haula wani irin gumi ne ke karyo mata na takaici da tsananin bakin.ciki ,idon ta ya sauya ya rine buden bakin ta cewa take wacece wannan yarinyar da tayi mun shigar sauri a rayuwata da na Anwar? Wacece ke shirin mun yankar kauna tsakanina da d’ana?? Wlh ko an daura auren sai an warware indai ina raye kuma ni nake da iko ga Anwar!!!

_*Littafin WALIJAAM na kudi ne kaman yanda kuka sani*_

_*Ga masu bukatar wannan littafi xasu na iya mgn dani ta wannan whatsap link din👇*_

https://wa.me/qr/7UGIAODZY3LON1

_Normal grp 200_

_Vip grp  500_

_Spc group 1k👌_

_Idan kati xaki turo MTN ne ._

_Idan kuma ta account ne ta nanan👇_

_0028799846_

_Farida Hashim stanbic bank_

_Yan niger kuma zaku tura katin 500f ne na Airtel ta wannan number na kasa👇_

_+22797780373_

_Idan kuma Spc grp kk bukata 800f ._

_________________________

_FREE  page na dab da karewa masu bukata zasuna iya magana dani ta link din dake saman page ,Don Allah kar kimun mgn kiga ban baki amsa ba , kwana biyu ina busy sosai ,idan biyan littafin zakiyi ga hanyoyin biya nan nasa a kasan wannan page din ,idan kin biya kimun screen short na evidence dinki ,idan kati ne kk turo zan gani kuma xan saki a paid grp 2 inshaallh… Masu tambayar grp link na comment wlh ya cika ,idan biyan littafin xakiyi sai ki biya kaawai a saki a paid grp 2 ngd…_

*_Taku mai kaunar ku tare da nuna mawa masoyan ta soyayya da kauna ,kulawa duka wato_*

*MAMAN TEDDY🧸*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *