ZUMA CHAPTER 1 BY SHATUUU
Sunana Fadima amma a gidan mu ana kirana Nanah, nakan manta cewar suna na Fadima saboda hatta a school Nanah ake kirana dashi. Gidan mu na kanyi murmushi duk lokacin da zan bawa wani labarin gidan. Kuma kuma a hankali zaku fahimci daga gidan dana fito. Mahaifina dan asalin hadejia ne ta jihar jigawa, mahaifiyata mutuniyar bidda ce dake jahar niger so you can imagine yadda aure yake kaika ko ina. Mamata banufiya ce wadda idan ka kalle ni zaka ga traces na nufawa a jikina most especially idanuna, inada ido shiyasa mutane suke ganin inada kyau to amma nasan ba komai ke rudar su ba illa maganai da nake dasu. Ni baka ce kamar yadda aka sani idan ka fiya baki a jigawa akan ce ko kai din dan hadejia ne? To nima haka nake ban bar wannan gidan ba nayi musu kara sosae, saboda mahaifina baki ne kuma a gidan mu ina daya daga ciki top 3 blacks. Yayan Daddy mu goma sha uku ne amma ina tabbatar muku tara daga cikin mu kowa da mahaifiyar shi, sauran hudun kuma su biyu Maman su daya sauran ma haka, to sune wanda tasu uwar tayi karko mu kuwan tamu bata ma ci litinin ba balle talata. Ni karewa tawa mahaifiyar ma a gidan iyayenta ta haife ni se daga baya sannan aka dawo dani gidan mu.+
Mahaifina alkali ne ya fara tun daga matakin barrister har seda yakai matsayin chief judge na jigawa kafin yayi retire bayan kuma yayi retire aka masa appointment a matsayin commissioner of justice. Dukkan rayuwar mu munyi ta a garin dutse ne cikin famous unguwar Gida dubu kuma koda dutse ta fara cika ma bamu tashi ba sede gyaran gida da Daddy ya dinga mana. Bansan menene matsalar da take faruwa tsakanin Daddy da matan da yake aura ba amma dai Nasan mahaifina yana da auri saki, saboda idan ance dukkansu suna da matsala to shi kuma Daddy fa? Babu yadda zaayi ace mata goma sha daya baka samu kwata daya tak daidai da taste dinka ba. Wannan ba magana bace, nasha jin labarin inda akai haka to amma a ciki akan samu daya ta jure ta zauna, to banda gidan mu duk masifarki Daddy yasha kanki, gashi dai judge ne amma haka yayi fatali da family law, shariah da mu’amalat daya koya a makaranta, ya maida Aure tamkar canja rigar jikin shi. One funny thing about life dukkan mu mu sha ukun to mata ne ziryan babu namiji ko daya, se Daddy ya zama very careful akan aurar damu, amma baka yiwa rayuwa wayo.1
Matar shi ta farko cousin dinsa ce da akai musu auren gida, Habiba sunan ta, tunda sukai aurennan bana tunanin a labarin da aka bamu ance sunyi zaman lafiya na wata hudu. Shi mutum ne me fada, idan nace fada ina nufin mafadaci sosae, ga mita in fact abu a gurin Daddy baya wucewa, itama kuma fada ne da ita. Ita ce ta haifa babbar yayarmu Anty Hauwa a yanzun tana nan hadejia tana aure, matar shi ta biyu ita kuma yar kazaure ce sunan su daya itada Anty Hauwa bansan abinda ya kashe auren ba amma itama yarta daya Anty Sumayya, matar shi ta uku yar katsina ce so kunsan fadan Yan katsina ga kuma ya hadu dana Daddy to se gidan ya zama kamar irin gidan tashin hankali, kullum balain yau daban na Gobe daban at last ita dinma a gida ta haifi Yaya Nasiba. Zuwa lokacin kowa ya farga da halin Daddy yaya uku babu wanda uwar shi ke gidan se ya zamana ya maida su hadejia gurin mahaifiyar shi. Bayan kusan shekaru biyu ya samo wani auren anan hadejan. Ya tattaro yayan ya kawo mata, ita abinda ya raba su akan su Anty Hauwa ne dan su karba wahala hannunta, shi kuma abinda bai yarda dashi ba kenan, yayan shi basu san komai ba su yara ne dan haka dole duk wadda tazo gidan se ta zauna da yaran shi. Bansan me tayiwa Daddy ba amma shi kanshi ya karbi wahala a gurin ta kuma ita kadai ce ya sake ta taki tafiya ta zauna karshe seda yayi mata saki uku sannan ta hakura, shi a auren shi babu kome idan ya sakeki an gama kenan. Yayanta biyu Yaya Rahama da Yaya Mariya. A wannan lokacin kuma yaje saudiyya yin aikin hajji anan ya hadu da tawa uwar, sunan mamana A’isha, mahaifin ta shi ke rukon sarautar bidda, dukda kasancewar yan sarauta ne amma ya yadda sosae da karatu. Mummy tayi karatu a wajen uncle dinta dake kano anan BUK tayi degree dinta akan law same field din da Daddy yayi. Farin cikin tayi passing law school exams dinta yasa mahaifinta ya biya mata aikin hajji, ita ce mace ta farko da Daddy ya fara aura tayi karatu me zurfi haka kuma daga kanta bai kara ba saboda ya alakanta abinda ya faru da cewar mummy ta waye da yawa shiyasa. Lokacin da mummy ta kai zancen Daddy gidan su mahaifinta bai wani ji dadi ba haka itama mahaifiyar ta balle da akai bincike aka fahimci halayen Daddy se ya zamana kawai dai anyi auren ne babu yadda zaayi dan shi bai san abinda mummy zata ga basu kyauta mata ba. Mummy sunyi zaman lafiya itada Daddy saboda dukda bai wani daure ba, bata fi watanni uku ba ta samu ciki. Kamar samun cikin nawa ake jira shi kenan zaman ya lalace kuma yawancin matsalar akan yara shi ne, idan yayi tafiya zaiyi waya yafi sau uku a rana akan ta hada shi da yaran shi, haka zata bisu tabasu waya amma yana gama magana dasu to xai kashe kuma ko ta kira bazai dauka ba, wannan abin ya dinga bata mata rai kuma itama batada hakuri ko kadan, fadan ta yafi na Daddy ma. Ya bata yaran shi basu ganin girman kowa ko itama da take zaune dasu, so se ya zamana da sunyi abu zata dake su tun suna yin shiru har ranar Anty Hauwa ta fada masa, ranar Ko mummy ta sha duka ba kadan ba a hannunshi, ya manta ma ciki ne da ita ya nada mata duka wanda seda yasa jikinta ya fashe sannan kuma ya dankara mata saki biyu. Mummy ba zata taba mantawa da gidan mu ba har abada. A ranar mummy ta tafi da cikina wata bakwai ta tafi gidan uncle dinta a kano. Koda ta koma gida can bidda Babanta yace se ya kai Daddy kotu aka taushe shi amma fa ranshi ya baci, aka barta har cikina yakai haihuwa aka kaita asibiti ta haihu and aka haifeni safe and sound. Mummy ta kalleni idonta kawai na dakko amma komai na uba na ne hatta dogayen gabban danake dashi ya ke nuna cewar zanyi tsawo irin na baba nane. Ance min sau daya ta bani nono mahaifinta ya karbe ni dan yayi min addua, bai zame ko ina ba se Dutse bai ma fadawa kowa ba balle a taushe shi, cikin hukuncin Allah ya samu Daddy a gida shi da yaran shi suna cin abinci, aka fada masa ana sallama dashi seda ya gama cin abincin tas sannan ya fita hannun shi rike dana yaya Rahama, suna zuwa ya fara kame kame ganin mutumin dake tsaye a gaban shi. Ya tsugunna ya fara gaida baban mummy, amma ko amsawa baiyi ba ya mika masa ni tareda fadin1
“A’isha kadai na aura maka, bata zo da kowa ba, dan haka ga yar ia nan se kayi yadda zakayi da ita”
Daga haka ya juya yayi tafiyar shi, gaba daya hankalin Daddy ya tashi, ya jima tsaye yana kallona lullube cikin shawl kamar yayi kaki ya tofar, haka ya juya ya shiga dani ciki su Anty Hauwa suna ta murma sunyi kanwa.
Akan kujerar dake gefen shi ya ajeni, dukkansu suka zagaye ni suna kallona inata bacci saboda nayi j na gaji tun a hanya ban kuma samu abinda nake so ba. Anty Sumayya ta dubi Daddy tace
“Daddy a siyo mata milk idan ta tashi kuka zatayi.”+
Se lokacin Daddy ya sauke ajiyar zuciya dan dama kallon da yake min tunanin yadda zaiyi dani yake idan na tashi, Anty hauwa ta daura ruwa kan stove lokacin shekarar ta duka goma sha daya, Anty Sumayya kuma goma se Yaya nasiba
takwas, yaya Rahama biyar ita kuma Yaya Mariya shekarar ta biyu a gurin Anty Hauwa take so ni se yaya Sumayya ta karbeni. Dukda cewar dukkanmu iyayenmu daban amma saboda yadda muka tashi yasa kanmu yake a hade, saboda tashi kawai mukai muka san kanmu bamu san wata uwa ba balle wani. Bayan yaje shi da Anty Sumayya sun yimin siyayya ya dawo ya tattara kanmu muka tafi hadejia, a hanya na farka na dinga tsalla ihu a motar, gaba daya Daddy ya gigice wannan ya jijjiga wannan ya karba, a haka Anty Sumayya ta hada min Nan aka bani and crap na karba na fara sha.
Daddy bashi da uwa bashi da uba dukkansu sun rasu, dama mahaifin shi basu girma dashi ba, mahaifiyar shi kuma bayan haihuwar yaya Rahama ta rasu. Bashi da wani mafadi dan ko cikin yan uwansa shi ne wanda yake da kudi kamar shi ne breadwinner cikinsu, so kusan maganar shi kawai suke ji basu jin ta kowa se tashi kuma kunsan idan kana da kudi ko kai ne auta to ka koma babba, your words are gold. Tunda muka isa ya tafi wajen kanwar baban shi dan samo masa me rainon da zata kula dani na lokaci kafin ya maida ni bidda, aka dace aka samo wata Baba Asabe daga kafin hausa. A lokacin ma ta manyanta dan tafi arbain muka taho da ita dutse, komai nawa ya koma gunta ita da Anty Sumayya. Seda nayi kwana bakwai Daddy yayi yanka yasa min Fadima sunan mahaifiyar shi Anty Sumayya ta saka min Nanah dan Baba Asabe tace musu su boye min suna. Washegari da assusuba ya daukeni ya nufi bidda da adduar Allah yasa mahaifin mummy ya yadda su karbe ni saboda kwana bakwan da nayi na azabtar dasu, bana bacci se kuka da daddare, da safe se na kusan yini ina bacci ina ramawa, idan na fara kuka kowa se ya tashi a gidannan, shi yasa Daddy yaga bazai iya ba gwara ayi wadda zaayi. Anty Sumayya tayi ta kuka da zai tafi dani ita ta yarda a barni zata rikeni.
Yana isa tun a kofar gidan me wanki ya bashi shawarar ya koma saboda indai Alhaji ne to abin bazai masa dadi ba, amma Daddy yayi shigewar shi, mummy tayi kukan tayi rokon amma babanta yace ta manta dani se ya hukunta ubana, haka ta rame saboda tunanin halin da nake ciki. Kafin Daddy ya samu ganin Alhaji suka hadu da babban yayan mummy, ya kalleshi sannan ya kalleni ina bacci na so peacefully kamar bani bace me kuka, ya jashi gefe yace
“Kaga zan baka shawara kada ka bari Alhaji yasan da zuwanka , saboda abinda ya shirya maka, ka dauki yar ka ka koma idan ba haka ba…”
Se yayi kwafa kawai, Daddy ya bata fuska yace
“Meye laifin yarinyar nan? Ita bata yi laifi ba tunda kuwa haifarta akai, kada ku hukunta ta da laifina mana”
Shidai Kawu Ahmad bai kara cewa komai ba ya bar Daddy zaune yana ta mita, yana fadin ko nawa ne zai biya mummy dan ta shayar dani, yana nan a zaune har fin mintina talatin yaji kuka daga kofar shigowa parlon, muryar mummy ce tana fadin
“Dan Allah Alhaji kada ka hukunta yarinyar da bata ji ba bata gani ba da laifin babanta, dan Allah ka barni na ganta!”
“Kina taka kafarki ciki ki sani babu ni babu ke, shashasha marar tunani kawai”
Tana kuka sosae ta kasa daga koda kafarta jin abinda yake fada, jikinta na kyarma ta kalla mahaifiyar ta dake tsaye idanunta sunyi ja itama, kamar na san abinda ke faruwa na fara tsalla kuka, Daddy ya mike tareda fitowa yana jijjiga ni ya nufi mummy da ta kafe ni da idonta, gabanta yaje ya mika mata ni, hannunta tasa da niyyar karba Alhaji yace
“Kina karbar ta , to kuwa ni dake har abada! Na cireki a yayana”
Ta tsugunna a gurin tana kuka nima a cikin shawl inayi, scene din is heartbreaking. Daddy ya nufi gurin Alhaji ya fara bashi hakuri, har ya gama magana Alhaji bai tanka shi ba, seda ya gama sannan yace
“Darajar yarinyar nan kaci amma niyyata idan kazo gidannan se nasa an maka duka yadda kayiwa yata, ka fita ka barmin gida!”
Haka ya fita with a heavy heart ya dawo dani dutse gurin yan uwana. Bayan nan rayuwa ta cigaba da tafiya Daddy bai kara aure ba seda nayi shekara uku sannan ya auro Anty Maryam, yar kano ce tazo gidan mu ta haihu yar ta Amina, itama akan mu Daddy yayi waje da ita, amma ita da Amina ta tafi saboda yadda taga muna shan wahala tasan yadda ta wahalar damu dole haka zaayiwa tata yar. Seda Amina ta shekara biyar sannan ta dawo da ita a lokacin har yayi wani auren Anty Rukayya. Matar nan nada hakuri ban taba koda jin labarin hakuri irin nata ba, tayi juriya ba kadan ba, ta kuma yi shekara shida a gidan mu. Ta rike mu tamkar ita ta haife mu, babu wani a cikin mu da zai bude baki ya fadi sharrin Anty Rukayya. A zamanta seda Daddy yayi aure uku tana nan, babu cin kashin da baayi mata ba, a kanta na fahimci hakuri babbar riba ce a rayuwa, nasha naji yan uwanta suna zugata ta bar auren amma se tayi murmushi tace Zaman mu take, kunji fa itada a lokacin ko haifa ba tayi ba amma tausayin mu takeji.Ita ta haifi Lubna da Nawwara, bayan ta haifi Lubna Daddy ya auri wata yar yola, hmmmm mukam munga mata iri daban daban. Wannan matar ita kuma tsiya a kanta ta kare, duk ranar da take da girki abinci baya isa, kuma Daddy bai isa ya ganmu ba, haka take ga duka a gurin ta, ga kissa munsha wuya hannunta, gashi kamar hadin baki duk wadda tazo gidan mu se ta haihu kuma tana haihuwa zaa sake ta amma se tayi, Anty Hauwa daga baya dukkan mu muka koma ce mata Mom saboda a gurin mu ita ce uwar mu, ita muka bude ido muka sani. Anan aurenta ya mutu ta bar Amal, daga nan se ya auro Anty hamida ita kuma da shirinta tazo asiri ta dinga banka masa ya kasa gane kanshi, ya amshi azaba a hannunta, ya kamata tana binne laya cikin dare shi ne ya mata duka ya saketa, da ciki wata uku daga baya aka kawo mana A’isha. Ta biyun karshe ita ce Maman Ummu, ita ta kori Anty Rukayya kuma itama ta gagara zama dan halin Daddy yafi karfin ta. Daga wannan auren se kuma Daddy ya dauki break na kusan shekara biyar sannan ya kara auren matar shi ta karshe wadda tasa masa abinda ya daina marmarin mata, ya kance ko a kafa aka kulla masa mace to zai kunce ya yar. Anty nazifa. Ita din yar sokoto ce kuma ita kadai ce bazawara ya aureta inada shekara tara, na kusan gama primary dina, tayi abinda take so ita maza take kawowa idan baya nan, ta maida gidan tamkar gidan karuwai kawayenta suyi ta zuwa suna lodging da abokan tsiyar su, gashi lokacin su Mom duk sun girma suna peak level din yan matan cinsu. Allah ya taimaka makocin mu yayi masa magana ya dawo yazo ya tarar da gidan shi, ya kaita police station da takardar ta, se yanzun na tuna bata haihu ba, mun tashi mu sha biyu ne yaran daddy, Daddy ya aura mata sha daya. Wannan kenan!Na fara karatuna a karamar shekara, primary dina anan famous Dutse model nayi na gama haka ma secondary school dina tas anan na gama. Idan ka kalle mu zaka dinga jin tausayin mu saboda mu bamuda uwa, bamu rayu da uwa ba, ko abu mukeyi zaka san namiji ya raine mu. Bamu zuwa ko ina kamar yadda baa fiya zuwa gurin mu ba, Daddy kadai muka sani shi ne uwar mu shi ne uban mu, bamu ganin mutuncin kowa se nashi, haka ya nuna mana shi ne komai namu, kada mu nemi komai a gurin kowa se a gurin shi, kuma a haka muka taso saboda tarbiyyar mu kenan. Nasan to you guys mahaifina is a monster, believe me a gurina mahaifina is more of an angel.+
Most hadejawa tamkar kiranye ake musu Idan sallah tazo zasuje gida suyi sallah, to banda mu, muna gida dubu muna gidan mu. Iyayenmu mata dama da kin kawo yar ki to kin rabu da ita so wajen mu takwas bamu san wacece uwar mu ba balle dangin mu, Anty Rukayya ce ma take dan zuwa tana ganin mu lokaci zuwa lokaci kuma bai hana ba, saboda ita rabuwar arziki sukai,amma ranar da Maman Amal tazo seda muka kulle daki saboda fadan da korar karan da yayi mata, balle kuma ni ban taba ganin mummy ba, bansan ya take ba se Anty Sumayya ce ta fada min garin su da kuma sunanta da kuma yadda ta bar gidan mu, shi ne kadai abinda na sani, mummy bata taba nemana ba haka koda yan uwanta, na dai san uwata yar bidda ce, a kullum ina adduar Allah ya hada fuskokin mu especially idan naga wani daga dangin maman shi yazo ranar se na kusan yini ina kuka.
Na yadda rayuwa ZUMA ce tana
da zaki sannan da dafi, wani lokacin idan ka dandana wannan zakin se kaji tamkar nan duniya babu wani abu me dadi se ita, idan kuncin ya juyo se kaji tamkar kai kadai duniya ta juyawa baya, to haka rayuwar take, it’s a cyclical thing! Daddy bai yarda da boarding ba saboda a cewar shi idan muka je wani zai iya juya mana tunani hakan yasa dukka day mukeyi a secondary se daga baya ya yadda muka fara zama a campus.
A kowacce safiya Mom ke fara tashi daga bacci, daki uku muke dashi, kowanne mutum hudu, Mom itada Yaya Mariya, Ummu, da Amal. Dakin mu Anty Sumayya, dani da Lubna da yaya Rahama, dakin karshe yaya nasiba, nawwara, Amina da A’isha. Tana tashi zata tashi dukkan mu muyi sallah, kilan kuyi mamaki bamuda uwa amma muna da tarbiyya daidai gwargwado anyi mana ballantana kuma akan sallah, sannan Baba Asabe na tare da mu duk wannan badakalar da akeyi. Da mun tashi kowa yasan aikin shi bayan mun yi sallah. Bamu a da me aiki mu muke yin komai namu da kanmu, lokacin school nayi driver zai zo ya kaimu sannan time nayi zai dawo damu. Da mun dawo se shirin islamiyya wani lokacin ko abinci bamu ci sede yawanci munada dambun nama ko cincin da juice. Daga islamiyya se assignment muyi kallo da baban mu sannan bacci. Wannan shi ne daily routine.
Ni da kuke ji da gani banida hakuri, in fact ban masan wani abu wai shi hakuri ba, inada fada, ko makwabta dukda ba shiga muke yi ba sunsan ni mafadaciya ce, a gida idan kaji ana fada kada ka raba dayan biyu to dani akeyi, wani abun mamaki kuma idan kika bi diddigi to ni ce me gaskiya, that implies bana bari kawai wanda yayi min se nayi masa. Mom ta fara aure, kamar yadda Daddy ya aura Maman ta a matsayin cousin dinsa, itama Mom cousin din mu ta aura a hadejia. I was thirteen lokacin da akai auren amma i still remember irin yadda akai biki, lokacin da zata tafi babu wanda ya iya rakata a cikin mu, saboda yadda mike kuka, kowa seda ya tausaya mana, anyi taro tabbas dukda bamuyi tunanin mutane zasu zo ba, mussamman dangin Maman ta dukda dai mu din dangi daya ne.
Aure na biyu, shi ne na Anty Sumayya da Yaya nasiba. Bungun se yayi mana yawa dan tsakanin auren su bai fi six months ba, lokacin ina ss3. Anyi taro sosae aka kai amare dakin su. Daga nan se muka koma daga mu se halin mu har lokacin Daddy bai kara aure ba, a lokacin yana matsayin Chief judge.
Ina gama secondary na samu admission a FUD, i was so super excited nima na Zama babbar yarinya zan tafi jami’a, kuma a gidan mu ni ce na fara samun admission a university duk wannan abin na Daddy to a polytechnic suka kare shi a dole baza mu bar dutse ba. Anty Sumayya na fara kira na sanar mata admission din dana samu tayi ta min murna sannan tace idan Daddy ya dawo naje na fada masa. Ko da ya dawo da daddare na same shi a dakin shi bayan na kai masa abinci saboda ranar ni ke da girki, yes! Kowa da ranar girkin shi, idan ranar ka ce kai zaka contrlling gidan gaba daya, kai zakai breakfast zuwa dinner. Yana bude flask din ya fara murmushi yana fadin
“Nanah! Abincin yayi dadi sosae”
Murmushi nayi nace
“Nagode Daddy amma labarin da zan baka yafi girkin dadi”
Da murmushi saman fuskarshi yace min
“This is cheating! Ki bari na gama cin abincin se ki fada min kada kisa na kasa ci”
Na danyi dariya tareda gyada kaina, ya cigaba da cin abincin shi ni kuma na maida hankali na wajen kallon tv. Muna nan zaune sega yaya Mariya ta shigo, zama tayi tana gaishe shi ya amsa da fara’ar shi. Haka yake to us he’s the best dad ever! A shekarun mu ya kamata mu nemi iyayen mu mata amma saboda yadda Daddy ya cike mana kowanne gurbi, nakan manta uwa ce take haifar mutane, amma akwai lokuta da wani abin idan ya faru se nace how i wish i have a Mom! Especially da ina school idan na hadu da mutane suna fadar Mamaa tayi kaza, ummeiy ta bani kaza, munje kaza da Ammi se naji I’m missing the person I’ve never met. Wani lokacin naji to meye ma zan damu kaina bayan ita uwar tawa bata neme ni ba, nayi shekaru da yawa ni daya Ba tareda support dinta ba, to yanzun ma bazan mutu ba dan ban ganta ba. Thought dai kalakala haka.
Seda Daddy ya gama cin abinci tasa sannan ya dubeni yace
“Nanah what’s the good news we have?”
Bakina kamar zai yage saboda murmushi nace
“Daddy na samu admission a FUD!”
Se naga yayi shiru maimakon yayi murna kamar yadda yayi ranar dana fada masa cewar naci waec da neco yau se naga akasin haka.
“Daddy kayi shiru, kayi murna mana”
Na fada ina jan hannun shi tareda bata fuska, kallona yayi sannan yace
“I’m proud of you of course amma ki manta da wannan FUD din , zan sama miki makaranta!”
Kafin nayi magana yaya Rahama da tun shigowa ta anan na sameta tace
“Kai Daddy but this is unfair! Ta yaya ta samu admission zakace ta barshi”
“I will compensate her Rahama, Nanah look, akwai abinda na tanadar miki kinji”
Raina dama already ya baci, na girgiza kai tareda mikewa na buga kafata nace
“Nidai Allah se naje!”
Kar kuga laifin mu, haka muke kuma baa kwabe mu ba, so dan haka wannan shi ne least abinda yaya irin mu zasu iya yi. Bansan ya sukai da yaya Rahama ba nidai na wuce daki ina kuka, ina tuna effort din da nasa dan ganin nayi making jamb da post utme amma ace ya tafi in vain. Da matsala. Aminatu ta biyo ni saboda ita na fara haduwa da ita a parlo tana karatu.
“Ya Nanah menene? Wani abu aka miki?”
Da nayi mata shiru inata shehseka se ta fita, cikin mintuna se gashi ta dawo da dukkan sisters dina, kun manta cewar nace daku hadin kai ne damu? Seda suka lallasheni na daina kuka kafin na fada musu me ya faru, kowa was against abinda Daddy yace.
Washegari girkin yaya Mariya ne, muna parlo muna kallo naga ta fito da couscous rike a hannunta, dariya nayi tareda gyada mata kai ta wuce. Can se muka ji muryar Baba Asabe tana fadin
“Yanzun Mariya kinsan babanku baya son couscous me yasa zaki dafa?”
Ta dago ta kalleta ta bata rai tace
“Muma bai mana abinda muke so ba, so far zamu nuna mishi ran mu ya baci”
Tasan halin mu hakan yasa ta rabu da ita ta koma dakin ta, dan tunda muka zama determinant akan abin to ba zamu fasa ba. Daddy bai dawo ba se dare, kowa yasan dama Amal ke bude mishi gate idan ya dawo, tana ji yana honk amma tayi burus ta cigaba da abinda take, cikin mu babu wanda yayi mata magana, se ya bude da kanshi yayi packing ya nufi parlon shi, already abincin shi anyi serving hakan ya tabbatar masa munyi fushi. Murmushi yayi ya bude abincin amma take ranshi ya baci saboda ganin couscous ma bata masa rai yakeyi. Bai ce komai ba yayi wanka thinking daya a cikin mu zata shigo masa oyoyo but har yayi wanka yayi shirin bacci muna parlo muna ihun wani movie da muke kalla. Da sallama ya shigo hannunshi rike da ledar kazar daya kawo mana. Tunda muka amsa sallamar se kowa ya gimtsa fuska, munsan shi ne abinda yafi tsana mu hade masa kai. Nasani kaddarar Daddy haihuwar muce, mu yaran kirki ne amma muna bashi tough time, shi yasa ko bai san abu to saboda halin mu zai hakura yayi mana. Dukkan mu kasa kasa muka gaishe shi sannan na mike nace
“Girls I’m sleepy, se gobe in Allah ya kaimu!”
Daga haka na wuce ciki ina jin idanun Daddy sukai min rakiya, to ko mintina uku banyi ba naga kowa ya shigo dan kwanciya and we left him all alone, nasan zuwa washegari zai amince naje university.