SIRADIN RAYUWA CHAPTER 2 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

 SIRADIN RAYUWA CHAPTER 2 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA


tunanin idan sukaga rauni a nata idanun yaya nasu zuciyoyin zasu kasance?,saboda haka ta juya kawai tafice a dakin,saidai tana isa tsakar gida ta kasa riqesu suka soma bin kuncinta,tasanya tafin hannunta a hankali tana sharewa gamida dosar gofar fita gida qafafunta kamar ba zasu dauketa ba,duk da bata da yaqinin samun abinda zataje nema,amma tana fatan a dace kodon 


yaran. 


Karo suka kusayi da wanda ke ke shigowa,dukkaninsu sukaja baya yana fadi cikin 


fada fada “Kai,waye wannan?!” “Nice” ta fada a tausashe tana daga kai don ganin waye,sulaiman neyaya 


a wajenta wanda suka hada uba daya,kusan rabi da rabi yake rayuwarshi a gidan,saboda kaf nauyinsa baikai mahaifinsa,d’a ne ga matar malam bilya ta farko wadda suka jima da rabuwa,tafiye tafiye yake qwadagonshi da neman kudinsa,kuma ba laifi yana samun na rufawa kanshi asiri,duk da bai tsinanawa uban komai sai abinda yaga dama,saboda haushi da takaicin yadda ya watsar da 


rayuwarsu dake cike a zuciyarsa. dg *SIRAD’IN RAYUWATA® 2 


*_Wannan littafin na kudine,amana ne a hannun duk wanda yasiya,idan kina da buqatar a dama dake,nemi wadan nan lambobin ki saya ki karanta ta hanyar data 


dace cikin nutsuwa da kwanciyar hankali,babu cigiya,babu a dauko mana_* 


“Maigado?,ina zaki haka?” Ya fada bayan ya sassauta muryarsa daga fada zuwa sanyi,maimakon tabashi amsa saita sadda kai tana wasa da yatsunta,hawayen da take qoqarin riqewa tun dazun suka balle mata,daidai lokacin da nepa suka kawo 


wuta,hakan ya taimakawa sulaiman wajen ganin hawayen nata “Lafiya?,cewa nayi ina zaki,idan babu amsa kuma matsamin nawuce” “Zanje na samowa yara mai da yajin da zasuci abinci ne” shuru ya ratsa tsakani 


sulaiman najin takaici na sake ratsashi,mai hali dai bai fasa halinsa?,saiya sanya hannunsa a aljihun wandonshi yaciro dari biyar da yayi niyyar baiwa baban nashi 


ayau yamiqa mata “Ungo wannan,ki saya muku wani abun” hannunta har rawa yake saboda murna 


da dadin dataji,wani abu da yaketa quile mata numfashi tun dazun taji ya 


saketa,farinciki yacikata har murmushi ya subuce mata “An gode yaya sule,Allah ya qara budi” 

“Maigado?, ina zaki haka?” Ya fada bayan ya sassauta muryarsa daga fada zuwa sanyi,maimakon tabashi amsa saita sadda kai tana wasa da yatsunta,hawayen da take qogarin riqewa tun dazun suka balle mata,daidai lokacin da nepa suka kawo 

wuta,hakan ya taimakawa sulaiman wajen ganin hawayen nata “Lafiya?,cewa nayi ina zaki,idan babu amsa kuma matsamin nawuce” “Zanje na samowa yara mai da yajin da zasuci abinci ne” shuru ya ratsa tsakani 

sulaiman najin takaici na sake ratsashi,mai hali dai bai fasa halinsa?,saiya sanya hannunsa a aljihun wandonshi yaciro dari biyar da yayi niyyar baiwa baban nashi 

a yau yamiqa mata “Ungo wannan,ki saya muku wani abun” hannunta har rawa yake saboda murna 

da dadin dataji,wani abu da yaketa qulle mata numfashi tun dazun taji ya 

saketa,farinciki yacikata har murmushi ya subuce mata “An gode yaya sule,Allah ya gara budi” “Amin” ya fada yana binta da kallo sanda take ficewa cikin hanzari,sosai yarinyar 

take bashi tausayi,yana lura da kuma ankara da yadda take dawainiya da rayuwar yaran bakin qarfinta,tamkar ita ake haifawa su,ko kuma daga cikinta suka fito,ita kanta abar tausayice,saboda baya manta sanda mahaifiyarta take raye gatan data samu,baya kuma manta sanda anty zuhra take nan,duk da baisan meye dalilin bacewar anty zuhran da daina ganin gilmawarta cikin rayuwarta ba,da 

wannan tunanin yacusa kanshi cikin gidan. 

Abu kala kala ta dinga ayyanawa a ranta,tayi tunanin siya musu suci su more 

a daren da kudin,har tayi hanyar sai kuma taja ta tsaya turus tana juya kudin a hannunta,idan har tace zata siya musu abu me dadi suci to kuma gobe fa waye zai basu?,hakan ya sanya ta sauya tunani,ta nufi kanti ta siya musu garin kwaki da suger,sannan tashiga gidan gwaggo rabi maqociyarsu ta siyi mai da yaji maidan dama,takuma siya gasarar koko da yake suna saida ita,ta ayyana a ranta gobe bazasuyi tashin yunwa wunin yunwa ba,mai da yajin yanzu zata zuba musu a qanzon suci,ta rage wani gobe ta kwada musu da garin,da safe kuma ta dama musu kunu susha,tuna hakan kawai ya jefa murmushi kan fuskarta,harya bata qwarin gwiwa da karsashin nufar gida bayan ta siyawa hauwa’u paracetamol satches daya,tana fata ko zazzabin ne kawai ya saukar mata,duk da tasani ba 

shine ainihin maganin daya kamata tasha ba,amma ragi ragi ne. 

A hanzarce tashiga soron gidan nasu wanda jan qwai na wuta ya haske,saita hangeshi rakube daga bayan qofa riqe da takardar tsire yana kaiwa baka da sauri da sauri,da alamu baison wani ya ganshi,gabansa kuma robar fanta ce qaramar 35cl. 

Motsin da yaji ya sanyashi saurin cilla ledar tsiran da gara robar saqon gofar yana boye hannunsa dake cike da maiqo da quli qulin tsire,saita sadda kai kamar bata ganshi ba zata wuceyayin da jikinsa yabashi cewa tariga data ganshi,saboda 

haka yahau nade tabarmar kunya da hauka “Ke maigado daga ina kike a daren nan?” Kafin ta bashi amsa yadora da bambami “Banason iskanci da diban albarka fa,wato yawon dare kikeson koya ko?, ina cewa 

baki jima da dawowa daga wajen aiki ba shine yanzu zaki sake zargawa qafarki 

igiya ki fice?” “Kayi haquri baba,maqot….” “Rufen baki ki wuce ki bani waje,sakarya kawai” bata sake yunqurin cewa komai 

ka kare kanta ba tawuce ciki,don dama ta qagu ya sallameta dinjunda tasan fadan gwaggo a kofa yakeyi,idan da sabo ta saba da ganin dabi’unsa kala kala,ita abinda yafi damunta yabarta takaiwa ‘yan uwanta abinci,idan yaso idan tadawo 

ko gutsi gutsi da namanta zaiyi yayi. 

A zagaye ta samesu da farantin qanzon kai kace tururuwa ta samu hasken candle guda daya,tasauke ajiyar zuciya tana godewa Allah daya sanya tasamu mahadin 

da zata kawo musun,da batasan ya zataji ba a yadda ta samesu. 

Cikin hanzari ta hada kwadon tsafjtasa kowanne ya wanke hannu suka soma ci a tare,bayan sun gama ta baiwa hauwa’u paracetamol din tasha sannan sukayi 

shimfida da zannuwan da sukan lullube sumuntin dakin su kwanta. 

Sai data tabbatar da kowanne ya sanya haqarqarinsa ya kwanta sannan ta zare yalolon hijabinta ta fita zuwa tsakar gidansu dontayi alwalar da zatayi shafa’i da wuturi,abu na qarshe da takan gabatar duk dare kafin ta kwanta,saboda bakoda 

yaushe take samun damar tashi sallar tsakar dare ba. 

Tana bakin famfo a duge tana daura alwalar amma tana iya jiyo cecekucen baban nasu da baba katti,cin mutuncine dai data saba masa duk sadda ta hadosu,tana 

iya jiyoshi yana cewa “Abincine dai ki jiqa kayanki ki sha,da baki bani ba ai Allah yabani wanda yafi 

naki,bakin da Allah tsaga baya hanashi abinci,kuma wallahi nasan maganinki,na gane take takenki,saboda kwana biyu kina ganinki ke kadaice cikin gida kike tunanin kinfi qarfina kinsha kaina,to zanyi maganinki ne,mu zuba dani dake,shege 

ka fasa” qaramar guda umma kattin tasaki kana ta dora da cewa “Ahayyeyoni Allah na tuba wane darene jemage bai gani ba?, aisai na ranar 

mutuwarsa,kare kuma da kudinsa sai yasha lahaula,kai kaga zaka iya,ga fili nan 

ga mai doki saura sukuwa….” Itadai daga haka tasamu ta gama alwalarta tashige daki tana mai qyamatar rayuwa irin ta gidansu,ta tuna mahaifiyarta,duk da 

cewa sanda tarasu bata da wayo amma tana iya tuna wasu abubuwa dangane da ita,jhawaye ya sake cika mata idanu sanda taga nan da nan bacci ya kwashe yaran,ta kabbara salla tana maida dukka damuwarta baya don ganawa da 

ubangijinta. 

Ta jima saman abun sallar tana addu’a kamar yadda tasaba sannan ta shafa,ta nufi can bangon dakin inda akwatinta take,wadda asanda take sabuwa ta zuba kyau da d’aukan hankali,anty zuhra ce ta taba siyo mata ita dab da sanda zasu tafi,budeta tayi ta ciro unifoarm dinta tana dagawa,tun daga tsarin dinkin da kalarsu zakasan cewa na private school ce mai tsada,duk da yadda suka tsufa amma tsarinsu bai bace ba,a wanke suke fes kamar yadda bata taba barinsu babu wanki duk da yadda suke neman agajin hutu saboda tsufa,saita zauna anutse tasoma musu ninkin guga,ta shinfidasu qasan wajen kwanciyarta,tana fatan su mige kafin safiyar gobe,saboda batasamu gogesu ba yau,duk da cewaa kwance suke saboda laushi da sukayi dakuma sabo da guga,sai data gama jerasu 

sannan ta shinfida zaninta a sama ta kwanta kamar sauran ‘yan uwanta. 

Ta kafin bacci ya ziyarci idanunta saboda tarin tunane tunane na rayuwa da abubuwan da suke cikinta na qalubale iri daban daban,daga qarshe dai sarkin barayin yayi nasarar saceta,baccin da yake cike da mafarkai na burikanta na 

rayuwa da takeso ta cimma,ciki kuwa harda inganta rayuwar qannenta. 

HR HKKKRK KRKKKKRK KKKKE 

Sanye da daurin qirji da kuma lullubin hijabinta tashigo dakin nasu wanda yake share fes kamar ko yaushe,kai bakace ana kwana a dakin ba saboda tsananin 

tsafta,duk da cewa babu komai qasan dakin sai sumunti da kuma tabarmar da kusan rabi da rabinta a cinye yake da suke kwana akai amma saika zuba abinci 

akai kaci. 

Fitowarta kenan daga wanka bayan tagama tsaftace gidan,takumayi wanke wanke kamar yadda tasaba kullum kwanan duniya,sai data tsugunna ta rarrabawa duka qannen nata kunu a cikin kofin sannan ta miqe tasoma 

shiryawa,idanunta akan ratattaken agogon da iya awanni kawai yake iya nuna 

mata,ta maqalashi saboda tashinsu sallar asuba dakuma lokacin tafiyarta makaranta,tana giyasta mintinan da zasu kaita makaranta daga nan gida,tana 

saka ran ta isa kafin lokacin da za’a soma assembly yacika. 

Mai kawai ta shafa,sannan ta goga alimun a hammatarta,kafin ta dangwali turarenta dan duri da take siya duk qarshen wata,unifoarm dinta dake saman 

akwati ta dauko tahau sanyawa,cikin mintina galilan tagama shiryawa tsaf. 

Wani irin sassanyan kyau unifoarm din sukayi mata,kai kace wasu kaya ta saka na azo a ganiya fidda sigarta sosai fiye da kayanta na gida,abu dayane tak ya musu 

cikas tsufan da sukayi,saidai tsaftarsu tadan boye wani daga cikin aibunsu. 

“Takwas tanayi hannatu karki bar kowa kuwuce kamarantar allo,kar nadawo acemin yau wani baije ba, hauwa’u kawai na yarda abari tasake jin qwarin jikinta 

tukunna” “To yaaya” hannatu ta fada sannan suka fara mata rige rige na adawo lafiya tana 

amsa musu harta fice daga dakin,ta ratsa tsakar gidan nasu tana wuce custumers din baba katti dake siyen qosai harta fice daga gidan gaba daya ta dauki hanya 

cikin nutsuwa kamar yadda tasaba. 

Ajiyar zuciya tasauke sanda tashiga harabar makarantar taga ba’a fara fita 

assembly ba,hakan ya alamta mata ba qaramin sauri tayi ba. 

Kamar ko yaushe ajin yasoma cika,saboda makarantace dake da tsari da doka,ba kasafai dalibanta ke makara ba,duk da cewa makaranta ce ta ‘ya’yan masu hannu 

da shuni. 

Babu wanda zaiji sallamarta ma idan tayi saboda kowa sabgar gabanshi yake, hayaniya ce ke tashi,saboda haka saita wuce direct sit dinta,wanda kowa dama yasan wajen zamanshi kuma anan yake zama koda yaushe,kujerarka da 

table dinka kai kadai harda ‘yar locker daga qasa. 

Ganin kamar akwai sauran lokaci yasa tazauna tazuge jakarta tana sake gyara zaman litattafanta,gamida sake dubasu daya bayan daya taga kota dauko kowanne,lokaci lokaci masu shigowa takan daga kai ta amsa sallamarsu,wasu 

idan sun kirayi sunanta ta amsa tare da qogarin dora murmushi kan fuskarta. 

Kusan ita daya take rayuwa cikin ajin tsahon shekaru,bata yarda ta rabi kowa ba,kamar yadda babu wanda ta bawa fuskar ya rabeta,ta sani ko ba’a gaya mata ba dukkaninsu kaf ajin matakin rayuwarsu da nata ba iri daya bane,kallo daya zakayi ka tantance hakan,akwai mutane da dama da sukaso qulla qawance da ita amma ta toshe wannan kafar,;wanda hakan yasa wasunsu suka qullaceta suke ganin tsabar girman kaine,ko don taga tana da kyau?,ko kuwa ubanta qila wani 

shegen ne wanda wala‘alla yafi dukka nasu iyayen hawa tudun muntsira. 

A hankali daga bisani kuma sai abubuwa da yawa da suke gani tattare da ita suka sauya tunaninsu suka sakasu acikin duhu,na farko dai ita ba‘’a mota mai kyau da tsada ake kawota kamar su ba,koda motar haya bata hawa bare akai ga ta gida,a qafa kulli yaumin take zuwa,abu na biyu,bata zuwa da abinci mai tsada irin nasu hakanan idan lokacin break yayi bata kashe ko ficika da sunan siyan wani abu da zata saka a bakinta,hasalima saidai ta dauki litattafanta a sannan ta sake sabon xaman karatu,ko kuma tafice daga ajin tatafi can baya inda babu mai ganinta bare ya dameta ta zauna,harsai an gama sannan tadawo cikin aji,na uku tunda suka soma karatu basuga wani sauyi daga sutturar unifoarm jaka ko takalmi ba daga gareta,kamar yadda yawancinsu ba unifoarm guda daya garesu ba,duk da haka kuma lokaci zuwa lokaci sukan sauya da sabo koda ace bai tsufa ba,wannan sune abubuwan da suka sauya tunanin wasu da dama a kanta amma banda mutum guda AFNAN ABDALLAH KAISA. 

Yarinyar da jinin sarauta ke zagayawa a jikinta,hafaffiyar diya ga sarki Abdallah mu’az kaisa,babbar masarauta wadda keda qarfi iko da kuma izza,masarauta ce mai matugqar girma da fadi da iko cikin dukka masarautu dake nahiyar,masarautar da a tarihinta dama can gwarzuwar masarauta ce wadda tayi shuhura takuma yi 

suna. 

Baya ga jinin sarauta dake yawo a jikin afnan ‘yar gata ce wajen mahaifiyarta,sannan uwa uba Allah ya hore mata baiwar kyau hakanan tana da qwaquwalwa da basira da saurin gane karatu,saidai dukka wadan nan abubuwan sai taga tamkar bilkisu bilyamin nason zartata kyau dakuma kaifin basira,sannan yanayin da take kallon bilkisun tana mata kallon mai zallar girman kai,bayan bataga wani abu da zata nuna mata ba game da gata ko sarauta,kusan kowa na ajin neman fada yake a wajenta dason samun shiga,amma sai taga hakan sam bai 

damu bilkisu ba bare ya dadata da qasa,hasalima rayuwarta take ita daya abunta 

ba tare data damu da shiga sha’ani ko shirgin kowa ba,sai Allah ya jarrabi afnan da dora dukka idanunta da damuwarta kan bilkisu,tana fata dai dai da rana daya bilkisun ta rabi kota shigo gonarta,amma hakan bata taba gittawa ba,dalili kenan daya sanya haushin bilkisu yasake cikata,tasake amannawa ranta cewa zallar 

girman kaine kawai ke damun bilkisun ba komai ba. 

Hakan saiya haifar da takura ga bilkisu,afnan ta sanya mata idanu duk wani motsinta,koda hanyace ta hadasu sai tayi wani abu na nuna wulaganci takura ko muxanci a gareta,babu abinda bilkisu ta tsana a rayuwa irin wulaqanci muzanci ko toxarci,tana da haquri dauke kai da kawaici,to ammafa bata jurar wulaganci,duk inda tasan zata wulaganta idan tashiga takanyi namijin qoqarin janye jikinta daga wajen,ta san afnan din ko wacece,don tanajin yadda sautari ‘yan ajin ke hirarta gamida yadda kowa keson ace itace babbar qawa a gareta,duk da kuwa har yau bata da wata gwana guda daya a cikinsu,ta auna takuma 

sani cewa ita din ba kowan kowa bace akanta,dalili kenan daya sanya tasake qauracewa hada koda hanya da ita,babu abinda take bari ya gitta tsakaninsu saidai tsautsayi wanda baya wuce ranarshi,tsakaninta da afnan ko kallo bata bari ya hadasu saboda gudun bacin rana,tana gudun ranar da zata kaita bango ta tabbatar abun bazai musu dadi ba,wanda bata fatan hakan saboda gudun fadawa bigiren da ba nata ba,tunda tasani koma meye yafaru ita zafa zamo a 

qasa,bata da wanda ya tsaya mata,bata da wani gata bare galihu irin nasu. 

kararrawar data buga ita ta alamtawa kowanne dalibi lokacin fita assembly yayi,hakan ya sanya kowanne dalibi tattara komatsansa zuwa filin assembly, ciki harda bilkisu. 

Kamar kullum haka tabi layi da kowanne dalibi kebi saboda gudanar da abun a tsare,a darare take kamar kowanne lokaci,gani take kamar kowa kallonta yake,kamar kowa ya lura da tsufan unifoarm dinta,kamar kowa yana iya ganin 

aibun dake tattare da ita. 

Cikin sahun daliban daya dake baya ta tabo ta gabanta tana shuna mata bilkisu wadda rashin tazara dake tsakaninsu yasanya karaf idanuwan bilkisun ya nuna mata su,amma saita dauke kanta ta maida idanunta ga abinda ake gabatarwa a wajen,duk da haka kunnuwanta suna iya jiyo mata maganganunsu,duk da cewa 

dafarko bata jin me suke fada 

“Gafa mutuniyarki” saita tabe baki “Sai shegen kyau amma da alama babu abun” dariya suka saki Kasa Kasa sannan 

ta sake cewa “Anya ko ba ‘yar aikin wani gidan bane suka taimaketa suka sata a school din 

nan?,don ko kusa ko alama batayi kama da wadanda iyayenta zasu iya sata a nan 

ba” dariya dayar tasake kunshewa sannan tace “Da alama dai kam…” Maganar da principal yasoma ita taja hankalinsu ya 

hanasu ci gaba da tattaunawa akan bilkisun,wadda tuni tashiga dogon nazari da tunani,abinda ta fuskanta shine,duk sanda talaka yayi gangancin shiga tsarar masu hannu da shuni ya banu?,ba gasu iyayen ba baga yayansu ba,ta lura kamar gado ko kuma halayyace a jininsu,mafi yawa yaran suma sukan taso da irin wannan dabi’a da halayya irin ta iyayensu,saboda za’a iya cewa sun taso sunga 

sunayi. (5/29, 11:32 AM] MAMAN ASLAM: ¢# = *SIRAD’IN RAYUWA* J 

*_Wannan littafin na kudine kuma amanace a hannun duk wanda yasiya,idan kina da buqatar a dama dake,nemi wadan nan lambobin ki saya ki karanta ta hanyar 

data dace cikin nutsuwa da kwanciyar hankali,babu cigiya,babu a dauko mana_* 

09032345899 

Ko 

09033181070 

*_KI/KA/KU DUBI GIRMAN ALLAH KU SIYA DA KUDIN KU, DON GUDUN SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA, DAMA WADANDA KE SIYARWAR MUNA MARABA 

DA KASANCEWA DA MASOYAN MU.._* 

Har aka kammala assembly din ba zata iya tuna abu Kwaya daya data dauka ba,bata dawo hayyacinta ba sai data tsinto sunanta ana kiranta amatsayin wadda zata rufe taron da karatun Kur’ani,kamar yadda tasaba yawancin lokuta ita ake 

kira. 

Wata baiwa ta musamman Allah yayi mata na dadin murya da iya rero 

Kur’ani,saidai zata iya cewa ta tsani wannan kiran,kiran yakan sanyata taji gaba 

Har aka kammala assembly din ba zata iya tuna abu kwaya daya data dauka ba,bata dawo hayyacinta ba sai data tsinto sunanta ana kiranta amatsayin wadda zata rufe taron da karatun kur’ani,kamar yadda tasaba yawancin lokuta ita ake 

kira. 

Wata baiwa ta musamman Allah yayi mata na dadin murya da iya rero Kkur’ani,saidai zata iya cewa ta tsani wannan kiran,kiran yakan sanyata taji gaba daya ta muzanta,kana ta tsargi kanta,amma babu yadda ta iya haka ta taka zuwa gaban taron assembly din dake cike da dalibai da malamai,cikin daddadar muryarta dake cike da tsoro har tana dan rawa rawa tayi basmala sannan tasoma 

karanto ayoyi daga cikin suratul anbiya’i shafi na qarshe. 

Kamar koyaushe dukka idanu sukayi mata caa,kowanne akwai abinda ke kawo 

cikin ranshi dangane da ita,;wanda mai tunani na karshe ke ayyana “Kyakkyawar sura mai dauke daddadar murya,cikin tsaffin tufafin 

makaranta”,abu mafi ban mamaki a idanuwansu,don kaf fadin makarantar babu wanda yake da suturar unifoarm maqasqanciya irin tata,banda Allah yayi mata baiwar tsafta da iya kula dasu da ba’asan yanayin da zasu kaya ba, ita kanta tasan 

da cewa zasu tashi tamkar na almajirin dake karatu a tsangayar da babu kulawa. 

Gamawarta yayi dai dai da shigowar motar dake kawo afnan makaranta,wanda hakan ke nuna yau ta makara kenan,wanda ba kasafai hakan ke faruwa ba,bata daga cikin sahun daliban dake makara,gajeran jawabi aka dauraye dashi kana aka 

sallami kowanne dalibi kamar yadda aka saba. 

Dai dai kofar aji sukayi kacibus da afnan wadda ke KoKkarin amsar jakarta daga hannun wata matashiya da suke kusan sa’annin juna;wadda kusan koda yaushe itake riko mata jaka da sauran abinda tazo dashi makarantar har zuwa kofar aji,;wani lokaci kuma har mazauninta,duk da cewa itama daliba ce amma da alama an sanyata makarantar ne musamman saboda afnan din,don kusan itace take mata dukkan wata hidima data shafi makarantar,kamar dauko mata jaka yayin zuwa da komawa,da kuma kuma kawo mata abincin break,siyo mata wani abu 

idan tana da bukata dadai sauransu. 

Wani kallo ta jefawa bilkisu,wanda sarai ta ganta amma ta dauke kanta kamar 

bata ganta,don ita ko daya bata a cikin lissafinta,jhakanan bataga na meye zata 

damu kanta da rayuwar wani ba. 

Kamar kullum kuma kamar ko yaushe,ta bada dukkanin hankalinta ga karatunta,don tanaji a zuciyarta shine abu guda daya tak da zai iya kaita ga tudun muntsira nan gaba,duk da bata da yakinin yadda rayuwa zata kasance anan gaba,akwai yiwuwar ci gaba ko kuwa guguwar data afko tsakiyar rayuwarta zata sanya dukkan Karfinta ta sake aza mata nauyin da dole zai sanyata takai kasa 

saman gwiwoyinta?. 

Daidai okacin da aka saba fita don dalibai su huta na tsakiyar lokacin karatu aka kada Kararrawa,babu bata lokaci kowanne yasoma tashi daga mazauninsa don yasamu ya sarara yakuma huta,ga bilkisu ma haka take,saidai yau ta danyi nawa sakamakon note da bata gama kwafa ba saman allo,gwanar sauri ce ta fannin rubutu,amma saboda wanki data mai yawa jiya a gidan umma luba na kayan sawarta yatsunta ke mata zugu har zuwa yanzu,tayi wankinne tana fatan idan an lissafa zata hada mata da albashinta wani abu ya dadu akai wanda zata rike a hannunta bayan ta gama biyan bashin umma katti saboda Kannenta da 

bata kaunar ko miskala zarratin tagansu cikin yunwar da bata da abun basu. 

Mintina goma kyawawa ta dada kafin ta kammala,zuwa sannan ajin nasu yasoma dumamewa da Kamshin abinciccika da kuma snacks kala kala,ta zuge jakarta a nutse ta maida littafinta,kana ta zari wani da zata duba zuwa lokacin da za‘a 

koma daukan darasi. 

Dai dai lokacin afnan da kawayenta suna saman babbar darduma mai kyau da laushi da sukan shimfida suci abinci anan,wanda duka cikin kayan afnan ne da take zuwa dasu,gab da zata qaraso inda suke ta jiyo jan tsakin afnan din,cikin 

murya dake cike da izza tace “Bansan nayi kuskuren zabar school din nan ba sai daga baya,nayi tunanin zata 

zama best makaranta cikin list na makarantun da magajiya tabani na zaba,sai 

kuma naga kaman ba haka ba” “Me yafaru?” Halima Kawarta dake buga game a tablet dina ta fada bayan ta 

dakata da game din da take,kaman ba zata amsa ba sai kuma tace “Ina ganin mutanen da ba ajin rayuwarmu daya ba a cikinta,hakan ai zubewar 

girma ne,qasqanta ce a wajenmu” karshen maganar tata yazo daidai da sanda bilkisu tazo dab dasu,dukka sai suka daga kai suna kallonta kana suka sheke da 

dariya,saboda sun fuskanci inda maganar tata ta saka gaba 

“Don’t mind mana……kinsan da yadda aka shigone?,may be ‘yan alfarma ne kamar yadda basira take tare dake anan,ki gane mana” farha daya daga cikin 

aminan afnan ta fada. 

Wani abu ta hadiye tanajin maganar na mata suya har cikin ranta,daya daga cikin dalilan kenan daya sanya bata bari koda hanya ta hadata da afnan din,saita kara sauri tafice daga ajin gaba daya,tana Kokarin sharewa da manta abinda 

kunnuwanta suka jiye mata. 

karfe biyu na rana aka tashi kamar yadda Ka’idar makarantar take,kamar yadda ta sabawa kanta tana daga cikin sahun farko farko na daliban da suke riga kowa fita daga makarantar,saidai yauma tayi nauyi kamar dazun,sakamakon kwantan note da malamin daya shigo musu a period din Karshe ya musu da bata kammala ba,da sauri sauri ta kammala ta hade kan litattafanta ta baro ajin,gaba daya hankalinta kuma yakoma kan Kannenta da gidan aikinta,tana fatan yau idan taje 

ta dace umma luba ta sallameta da kudin aikinta. 

Kamar kowanne lokaci dai harabar makarantar zuwa wajenta akwai ababen hawa sosai,wadanda dukkaninsu sunzo daukan dalibai,haka ta dinga ratsawa harta samu hanya tafice gaba daya tadauki hanya zuwa gida,cikin tafiyarta dake cike da nutsuwa da kamun kai,saidai tun batayi nisa ba taji kugin mota daga bayanta,wanda kafin a ankara tazo ta wuce da mugun gudun daya haddasa tashin kura har saman fuskarta,da hanzari ta daga kai tabi motar da kallo,daya daga cikin motocin masarautar kaisa ne,gakuma tabbacin fuskar afnan ta 

glass,wanda suna hada idanu taja glass din xama ta zuge. 

Kai kawai bilkisun ta kada,wai na meye?,meta tsare mata?,da wannan tunanin da bacin ran tadinga takawa zuwa gida,zafin rana qura da yunwa irin ta kowanne 

dalibi dake kwasota daga makaranta tana sakadarta. 

Dukkaninsu babu wanda bai haddace lokacin dawowarta daga makaranta ba,saboda haka batayi mamaki ba data samesu zaune dukkaninsu suna dakon dawowar tata,yar rige rigen taryarta suke,tana kallonsu fuskarta cike da murmushi,zuciyarta cike da farinciki idan ta tuna a ranar yau tana da abinda zata basu suci,babu abu mafi daga hankali da sanyata cikin kunci irin ranar da 

zatazo,suyi mata irin wannan tarbar amma bata da abun basu. 

Sai data dora hannunta saman kan kowa ta amsa oyoyo dinsa,hauwa ce ta 

karshe,ta dubeta cikin kulawa “Fillo(da yake wani lokaci da sunan da take kiranta kenan),kice yau da celebration 

jiki yayi kyau kenan ko?” Kaita daga tana murmushi “Na warke yaaya,naji sauki ai,/harma na debowa umma katti ruwa” duban yarinyar 

take sosai,ba zata hanasu yi mata aiki ba saboda ko babu komai a matsayin babarsu take,saidai wani lokaci tana mamakin rashin imani da tausayin umma katti,a yanzu tana da yakinin idan ta karasa cikin gidan akwai abinci cikin abincin da take saidawa,amma babu wanda zata iya sanma cikinsu,idan kaga ta bayar 

ta ranar ba Karamar sa’a suka taka ba,ko ranar babansu ya kawo cefane,ko wani 

cikin custumers dinta yaji tausayinsu ya siya musu “Ya akai hannatu?” Bilkisu ta tatambayeta sanda take kada kansu zuwa cikin 

gidan ganin yadda tazuba mata idanu,saita saki murmushi tace “Babu komai” daga haka ta hada kansu dukka suka shige ciki. 

llai kuwa tana tsakiyar kulolin abincinta tana ciniki tana hada kan kudinta,tanayi tana ‘yan wake wakenta duniya tayi mata dadi,donko kula da sannu da gida da bilkisu tayi mata batayi ba,itama bata damu ba ta jasu suka shige daki,domin 

idan da sabo ya zame mata jiki,ba baqon lamari bane a wajenta. 

Tasan yunwa suke ji,saboda haka tasoma dauko garin ta wanke tabarshi ya jika kafin ta sauya kayanta,wanda da zarar ta dawo take fiddasu daga jikinta,bata 

sake tabarsu,don idan tabarsun suka sake jin jiki bata da wata madafar. 

Tana canza kayan tasake lura da hannatun dai tana kallonta kamar dazun,sai data gama sanya atamfar tata riga da fallen zani wadda tadan soma jin jiki tayi haske daga ainihin kalarta ta daura dankwali sannan ta isa gaban hannunta ta 

duka “Anya kuwa lafiya kike hannatu?irin wannan kallo?,kamar yau yaaya maigadon 

ta zama baquwarki ne?” Sai ta saki murmushi wanda idan kalura dakyau akwai 

abinda ke damunta a zuciya,saita sake kallon nata sannan tace “Ba abinda yake damuna yaaya,kawai ina sha’awar yadda kike zuwa makaranta 

abinki,sai nakeji a raina dama nice ke,inason naga na iya karatu da rubutu irin naki,inason na zama likita nadinga saka fararen kayan nan,ina yiwa mutane allura” daga yadda take maganar zai gaya maka har cikin zuciyarta da 

gaskene,hakan saiya kashe jikin bilkisu,ta kakaro murmushi tace “Hannatu,wannan karatun saboda ku nake,saboda kuma ku samu kuyi karatun 

nake nawa karatun,karatuna nakune,na muku alkawarin in sha Allahu nan gaba 

dukkaninku sai kunyi karatu yadda ranku yakeso,kowa zai zama abinda yakeso da izinin Allah, kudai kuyimin addu’a ko yaya nasamu aikinyi kunji” dukkaninsu babu wadda fuskarta bata fadada da fara’a ba,wanda hakan ya nuna mata yadda sukeson karatun sosai,saidan kawai babu yadda zasuyi ne,da wannan murnar tabarsu tajawo garin kwakin tasoma kwada musu,kafin daga bisani ta rarrabawa kowa itama tazauna cikinsu sunaci tare tana sake jansu da hira,tare da basu labarin abubuwan da take da burin yi musu nan gaba idan Allah ya hore mata,hakan kuwa yasake faranta musu da basu qwarin gwiwa,kowa yadinga jefa mata tambayoyi tare da sake karanto mata abinda yakeso,bata gaza ba bata kuma qosa ba tadinga bin kowa tana bashi amsa daidai da yadda yakeson ji,tana 

kuma cike da fata a cikin zuciyarta ta cika musu mafarkansu. 

Cikin raha da annashuwa suke ci kai kace sun samu naman kaza ne,haka kowa yacinye yasha ruwa,cikin ikon Allah dayake ba wani ci ne dasu ba duka sun Koshi alhmdlh,sannan tasake gyarawa ta dauki hijabinta tamusu sallama tawuce wajen aikinta,bayan ta jadda musu banda yawo,ana kuma idar da sallar magariba dukkaninsu suwuce makarantar magariba,itama sai an taso daga makarantar 

dare sannan zata dawo gida. 

Tunda tafito daga gidan nasu ta fuskanci layin nasu cike yake da jama‘a,a rayuwarta bata kaunar irin wannan ranar da samarin layin nasu kan zauna su kafa dandalin hirawanda yawanci duka bai wuce zancen wane da wance,meyake 

faruwa a wannan gidan,wancan gidan me ake ciki?. 

Hakance kuwa ta kasance,don tunda ta doso majalissar aka sauya topic din 

yakoma kanta,matashi nafarko da ake kira auwali shiya soma tankawa “Tubarkalla ma sha Allah,kaf unguwar nan….kai bama unguwar nan ba,nidai a 

rayuwata ban taba katarin ganin yarinya mai kuruciya da kyau irin yarinyar nan 

ba” wani daga can sashen ya cafe zancan “Sai rashin dace da uba da tsantsar rashin gata da talauci ba….kaini wallahi ban 

taba ganin asararren mutum irin ubanta ba,Allah yabaka kadarar yara mata amma kayi watsi da ita?ita kadai wannan yarinyar kadarace,ba qaramin jari bace 

a wajensa amma bai sani ba’sai wani shima ya kama “Ai yarinyar nan wallahi inda ace ni wani shege ne da tuni na saka kai nayi wuf da 

ita,kai wannan idan tasamu wani hutun dajin dadin aiba Karamar mace za’ayi ba” 

sai sauran sauka sanya dariya,wani daga ciki yayi hanzarin katsesu “Kai gatanan fa takusa isowa,kada kusata ta tsargu da Allah,waske kawai”. 

Dai dai lokacin da abubakar saddik ke tsaye daura dasu,jikin wani shago daya siya kati ya tsaya yana lodawa,dukkanin maganganun cikin kunnuwansa sukayisu,baiko dago ya dubesu ba saboda hirar tasu sam batayi masa ba,hakanan yasamu kanshi da sha’awar daga kai yaga wacce halitta suka sanyawa idanu haka,daidai sanda yagama sanya digits na katin ya dannan request kana ya daga 

kai yana kallon sashen da yake tsammanin tanan ta taho. 

Baisan ya akayi ba,baisan me yasa yasamu kanshi da binta da kallo ba kamar sauran,duk da cewa baya cikin dabi’arsa sam,saiya lumshe idanunsa kana yabude sanda ta tserewa ganinsa,kunnuwansa sukaci gaba da jiyo masa hirar samarin suna ci gaba da dorawa daga inda suka tsaya,hakanan yaji bazai iya jurar ci gaba dajin abinda suke fada a kanta din ba,saboda haka ya taka zuwa inda ya aje motarsa Kirar kia Karama mai kofa hudu yabude yashiga yazauna yana kiran 

wanda yasanya kudin saboda shi. 

Sun dan dauki tsahon wasu mintuna suna magana dashi kafin su kammalaya datse kiran yana sauke numfashi,hakanan saiya samu kanshi da gaza tafiya yana sake nazari kan wasu abubuwa,daga bisani uzurin dake gabanshi yasanya tilas yakunna motar yana barin layin,saidai yanaji ajikinsa tabbas lallai akwai yiwuwar 

dawowarshi unguwar nan gaba. 

Kamar kullum aiki tasamu sosai gidan umma luba,tunda ba kasafai take iya tsaiwa ta kauda komai ba agidan,don wani lokaci sammakon fita take wajen aikin nata,smusamman idan akwai wani abu da za’a gudanar ko wani aiki na 

musamman. 

Bata damu ba don ya zame mata jinin jiki,ta zage tayi dukkan abinda ya kamata,kafin wani lokaci gidan yakoma hayyacinsa sannan ta dora mata girki kamar yadda tabar mata sallahun ta girka din amma kuma kadan,don ba kasafai ma ake mata girkin ba,saboda yawancin lokaci zuwa lokaci takan taho da lafiyayyen abinci daga can gidan aikin nata,har itama wataran idan rabo ya rantse 

takan samu. 

Tana tsakar gida bayan ta idar da sallar magariba tana addu’ar Allah yashigo da umma luba yau da wuri don tasamu zuwa makarantar dare,saboda yau zata bada 

haddar akhdari da sukeyi,addu’arta taci,don kuwa ana gab da soma kiran sallar 

isha’i sai ga sallamarta. 

Cikin girmamawa bilkisu tamike tana mata sannu dazuwa,ta amsa fuskarta a 

sake da fara’a tana cewa 

“Sannu mai gado da aiki” murmushinta mai sanyi tayi ta amsa 

“Yauwa sannunmu” 

“Wayyo Allah makashin kakata” tafada tana sauke uban faggon kayan dake daure 

a kanta bayan tasamu gefan abun sallar bilkisu ta baje,da alamu a gajiye take 

sosai “Bani ruwa in soma sha don Allah bilkisu,ki zubomin abinci yau a tsaye muka 

wuni,hidimar tafi ta kullum yawa” saita miqe a nutse takawo mata ruwan da 

abincin,sannan tasamu waje tazauna,tana jira ta sallameta tawuce. 

Tana cin abincin tana sakowa bilkisun hira,duka kusan na gidan aikinta ne da irin ayyukan yau da sukayi,umma luba badai surutu ba,sai kuma akayi katari ita bilkisun bamai yawan son magana bace,amma duk da haka ita bai dameta ba,duk sanda taso hira takan zauna tayita zuba mata labarine koda da murmushi zata amsata bata damu ba,a haka harta gama cin abincin ta wanke hannu sannan 

bilkisu tamige tana jawo takalmanta “Umma zan wuce gida” “A gurguje haka,ki tsaya yau Allah yayi albashinmu ya iso kema na 

sallameki,nasan kina da bukatu da yawa…kai wannan rayuwa Allah ya iya mana”ta qarashe fada tana tabe baki,bata amsa ba sai komawa da tayi tazauna tanajin 

ranta yana mata fari,don ba karamin jin dadin samuwar kudin tayi ba. 

Jakarta ta rataye data shigo da ita ta janyo,ta zuge zif din tana fidda sabbin 

kudi kar daga ciki bakinta har kunne tana cewa “Ai in gaya miki yau shar damu,albashi harda kari,wai amma karin da muka samu 

mu samu mabukata dake cikin anguwrmu muyi musu sadaka….kinji fa,saikace mu ba mabukatan bane,ai babbar bukata kawai najisu a lalitata,atoh”dan murmushi bilkisun kawai tayi,don ita zancan bai burgeta ba,don wannan tana ganin yashiga nau’in ha‘inci,ttunda tamkar an amince maka ne an baka wani aiki amma ka gaza cikashi,banda hakama ita kanta shaida ne su umma luban suna Karuwa sosai da gidan da suke aikin,saboda ana yawan musu kyautar abinci danye akai akai,harshi kansa kudinma koda ba lokacin albashinsu bane,hakanan suturu babu laifi 

masu tsada tana dasu duka silar gidan aikinamma dayake dan adam dan adam 

ne,batasan mesuke da bukata ba kuma. 

Kudin aikinta cas ta irgo ta bata “Ungo rike nan,ga kudin watanki saura na wanki”hannu biyu tasa ta karba kamar 

kyauta ta bata tana godiya,sannan ta sake irgo wasu ta bata “gashi wankin ki na dubu ne da dari biyu” sosai taji dadin karin,don bata 

tsammaci zata samu har haka ba “Na gode” “Nice da godiya ai mai gado,saboda yadda kikemin din nan sai kalilan masu 

amana,tsahon lokaci ko cokali ban taba nema na rasa ba ai kuwa kinga ba duk mutum ba….ungo cikin kudin sadakar dai na bada wani abu, aidai nayi tunda 

na fitar komai ganqantarsu” dubu daya tasake mika mata,data hada kudaden hannayenta sai taga ta kusa tasamma dubu biyar,abinda ba zata iya tuna yaushe 

ne hakan tafaru ba,riqe kudi masu yawa har haka ba. 

Harta mike ta sake dakatar da ita “Sake zama yarnan ki dangwali alfanun rikon amana”tayi magana tana janyo 

Kullin uban kayan data shigo dasu tana sake cewa “yau muma mun dangwala mun dangwala harmun godewa Allah,kayan diya 

kuma jinin sarauta yauni luba a hannuna,muma zamu rabawa jikinmu irin suturarsu,muji abinda suke ji,;wannan karamci nasu ya isa”. Tana maganar tana 

kokawar bude qullin kayan. 

Tana kwance kayan wani daddadan kamshi na musamman ya bule wajen,kayane faggo guda kamar za’a sunce dila,namijin daurin da aka masa yasa 

baka ganin yawansu sai an bude. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *