WANI QANGI COMPLETE

 WANI QANGI COMPLETE 

 Hadari ne sosai ya gangamo yanata cida da walqiya alamun ruwa yana gaf da sauka masu halin gudu sunata gudu domin tsira daga dukan ruwan saman me sanya zaazabi a wasu lokutan da matsananciyar mura. 

skace ta taso me hade da qura wacce ta haddasawa garin canza launin yanayi, cikin iskar wata matashiyar budurwa wa tana tafe tana kakkare fuskarta saboda iskar tayi Mata yawa, tsayawa tayi cak a guri daya sabida tunanin idan taci gaba da tafiyar zata iya faduwa, ta jima a tsaye kafin lafawar iskar ruwa ya kece me qarfin gaske daidai Ikcn da wata mota ta shararo a guje tazo ta giftata, takawa ta farayi a nutse tana rungume da hannunta a qirjinta | hannuta dayan riqe da bokitin awararta. 

Ji tayi an taka wani uban birki a bayanta ta juya da sauri cikin tsoro ga mamakinta sai taga an tsaya tare da zuge glass din motar daya kasance baqi an leqo. 

Wani matashin magidanci ne da bazai wucce talatin da takwas zuwa arba’in ba, qasa tayi da kanta ta raba zata wucce taji yayi horn alamun da suke nuna saboda itane ya tsaya, sake gyara tsaiwarta tayi ya leqo sosai yace “ina Zaki haka da bazaki iya neman guri ki fakewa dukan ruwa ba” sake sunkuyar da kanta tayi abinda yabawa young Alhajin damar qare Mata kallo ya sauke ajiyar zuciya yace “kizo na rage miki hanya ruwan nan zai iya sanyaki zazzabi” 

Saurin dago kanta tayi ta bude bakinta cikin siririyar muryarta tace “na gode” kawai abinda ta iya furtawa kenan ta juya da sassarfa har tana hadawa da gudu ta wucceshi abinda ya sanyashi fitowa da sauri batare daya shirya ba, duk da ruwan da ake makawa bana wasa bane amma bai dakatar da Alh Hafeez dagabin bayan Hannah ba. 

Harda sassarfarsa yake hadawa saboda kada ta qurewa ganinsa cikin saa yana karya kwana 

yaga ta fada wani gidan bulo wanda baayiwa plaster ba, yaja ya tsaya tare da sauke ajiyar zuciya ya juya ya koma inda ya aje motarsa ya shiga ya figeta yanajin wani nishadi, duk da bayason dukan ruwa sosai zazzabinsa jigata gabbansa yakeyi kawai yau saiya tsinci zuciyarsa dayin haske tayi fari tas daya rintse idonsa hoton yarinyar yake gani tsaye gabansa cikin ruwan. 

Da wannan tunanin ya isa gdansa yayi parking ya jima zaune cikin motar har saida ruwan ya tsagaita sannan ya fito ya shiga cikin gdan ya bude qofar parlourn ya shiga, wata matace zaune a parlourn ta miqe da sauri ta tareshi ya daga mata hannu yace “na gde a jiqe nake kada ki qaraso” kallonsa tayi tace “meye yasa ka jiqe haka?” Murmushi yayi a ransa yana tuna dalilin jiqewarsa amma a fili sai yace “tayar mota tace tayi faci shine na fita na cireta nasa wata so kafin na gama ruwan ya sauko” 

Bata wani yarda ba saboda tasan halin mijin nata sarai wannan bai !sa dalilin da zai sanyashi ya fito har ruwa ya dakeshi ba amma bazata tambayeshi ba, komawa tayi ta zauna ya bude qofar dakinsa ya shiga Kai tsaye bathroom ya shiga yayi wanka ya fito daure da towel yana tsane jikinsa yana gamawa ya shafa mai ya dauki doguwar riga ya saka yaja blanket ya rufe jikinsa tare da kiran likitansa kasancewar har zazzabi ya fara saukar masa. 

Yana kwance yanata juyi zuciyarsa ta tafi wata duniya ta daban matashiyar budurwar ta tsaya masa a ransa ganinsa da itana uku kenan duk a hanyarsa ta dawowa daga masallacin juma’a murmushi yayi daidai Ikcn da likitan ya buga qofar yabashi izinin shigowa ya shigo yayi treating dinsa sukayi sallama ya tafi. 

kkekkkkk 

Shigarta gda keda wuya ta rabe a tsakar gidan tanata sharar hawayenta daidai Ikcn da Mama ta fito taganta a tsaye taja da baya da sauri tace “ubanki kikeyi anan salon kijamin kisan kudi ko to waima ubanme ya tsayar dake anan din?” Cikin in’ina tace “kuk…kudin ne….” “Kudin me suka zube kome?” Durqushewa tayi ta fashe da kuka tace “wih bansan sun zube ba sai yanzu dana shigo Zaure kawai naga babus….”. Wata fuzga tayi Mata ta shaqeta ta wawuro maburgi ta fara jibgarta tana ihu tana komai amma babu me qwatarta_ saida ta daka iyakar dukanta sannan ta saketa tace “shegiya makira wadda ta tsotsi makirci a nonon uwarta wato kinje kin boye kudin kince sun Zube to wlh bazan yarda ba dole uwarki ta biyani kina Ina Ladi fito wlh fito wannan tsinannannu asararrun yayan naki na gaji da asarar da sukeyimin dole yau a biyani, awarar dubu daya da dari biyar na zubawa Hannatuh taje ta cinye ta rabawa kwaratanta ta dawomin empty to wlh dole a biyani idan ba hakaba yau ran Salisu ya baci” 

Fitowa Ummah tayi daga daki ta matso inda Hannah take ta dagota Ummah Ladi mace me haquri halin matan aljanna da kawaici ta duba jikin yar tata da taketa rawar sanyi tace “Yi hqr Uwata garin yaya kika zubar Mata da kudinta?” Cikin rawar murya tace “wl…wlh Ummah bansani ba wani mutum ne ya biyoni shine Ina gudu bansani ba kudin ya fadi wata gwabza Mama Adama takaiwa bakin Hannah tace. 

“Shegiya makira ga iya tsara zance da meye na gudun mazan baqinki ne ko yau kika saba basu sunaci suna baki kina kawowa to wlh yau ko Zaki kwana da ubanki Salisu sai kin dawomin da kudina” Jibrin ne ya fito daga dakinsa yace “haba Mama wannan wacce irin magana ce naga dai kullum tana kawo miki kudin nan yau daya don asara ta gilma sai kizo kina wadannan maganganun na rashin da’a” hayayyaqo masa tayi tace “Eh Jibrin in kaga dama ma kace nice banida da‘ar mana tunda Salisu da Ladi sunada ita ai shikenan nidai Kudine sai an bani” 

Ya bude baki zaiyi magana Ummah Ladi ta daga masa hannu tace. 

DOWNLOAD HERE 👈

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *