ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 7 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE
Www.bankinhausanovels.com.ng
ya janyo wannan tashin gwauron zabin (go-slow) da ake. Ban da Karar (horn) babu abin da kake ji, ita bata yi gaba ba shi kuma wanda ya yi laifin yaki fitowa daga cikin tashi-motar don yaje ya bata haKuri. Motar Kirar Peogoat ce C350 ash colour, sabuwa fil da ita sai daukar ido take. Cikin mutanen da suka matsu suna gaggawa nan take suka shiga Korafi ganin babu – mai motsi cikin su, kai tsaye wasu suka nufi bakin motar tata, nan suka fara mata ihu da hayaniyar ta kauce ta basu guri idan bata da abin yi susuna da shi. Kashe motar tayi daga (slow) din da take, ta bude Kofar motar ta fito.
Kyakkyawar matashiyar budurwa ce ajin farko, jajir da ita kamar ta hada jini da jinsin
Larabawa. Doguwa sosai, tsayin ta bai yi yawa ba kuma bai yi kadan ba.
Sanye take cikin English wears doguwar riga ce jikinta har Kasa, sannan ta dora top mai dogon hannu akan rigar. Kayan sun yi matuKar karbar jikinta, kanta dauke da daurin da ake yi na wannan zamanin, don haka daurin yake shim. Fuskarta dauke take da makeken (glass) da ya yi matukar Kawata fuskarta, kai daga ganinta kasan ‘yar dan boko ce, hutu da jin dadi da wayewa sun gama haduwa guri guda. Kallo daya zaka yi mata ka tabbatar mada , kanka cewa ‘yar hutu ce ta gasken gaske.
Tana fitowa ta daga (glass) din dake fuskarta ta dora shi a goshinta, nan take annurin da kyawunta suka Kara bayyana don duk wanda ya ganta yasan ya ga ‘yar gayu da aji.
Sam bata bi ta kan masu yi mata Korafi ba, kai tsaye ta nufi bayan motarta don ta ga irin barnar da ya yi mata, domin bata da abin da zata oya cewa da su.
Taku daya, biyu, uku ya kaita ga bakin motar ta wanda shima ganin ta fito yasa ya samu damar fitowa. Kallon sa tayi sosai shi da motar tasa, tace.
“Malam kayi min barna amma jin kai da gadara irin naka yasa ka kasa fitowa ka zo ka duba barnar da kayi min, ko kai makaho ne baka ga abin da kayi min ba?” Ya yi niyyar bata amsa wani daga cikin barin daliban da suka matsu ta basu hanya su wuce cikin fushi yace “Malama dalla ki bamu hanya mu wuce,
idan baki da abin yi to mu muna da shi, kin wani bi kin kashe mana hanya sai kace titin na . gidanku ne”
Cikin fusata ta juyo ta daga masa hannu na alamar dakata, sannan ta ce.
“Ban yi magana da kai ba, idan kana saun ka yiwa motar ka (wings). fuffuke ka tashi sama, wannan ba damuwa na bane”. Ta mai da kallon ta ga mutumin, ta ce, “Malam ka bani amsar tambayar da nayi maka, ka wani tsaya kana kallo na, ko kai kurma ne? Kana bata min lokaci”.
Cikin sanyin jiki ya ce, “Na nemi alfarmar da ki shiga motarki ki matsar da ita domin ki bani damar nima na wuce don mun shiga hakKin mutane, idan sun wuce ma yi maganar’””Ka ma raina min hankali, ba zan matsa nan da can ba sai ka amsa min tambayar da nayi maka, ko nima kasan ka bata min lokacin? Yadda suka matsu nima haka na matsu, kasan irin sauri da nake don kada na rasa (lecture) din nan? Domin (lecturer) din bashi da mutunci, kai kuma ka zo ka bata min lokaci, kayi min asarar (class) din fa kenan”
Jin dariya suka yi, take taji sowa da sauri ta juya cikin hasala sai ta ga daya daga cikin daliban ne da ya yi mata na dazu. Yace, “Allah na gode Maka tunda kema kina da taki matsalar, kinga kenan ba mu kadai ne muka cutu ba har da ke”Cikin tsiwa da masifa ta ce, “Wai kai wane irin wawa ne? Ba a yi magana da kai ba kana sawa mutane baki, wannan ai dabbanci ne” Cikin zafin rai da zafin nama ya daga hannu da niyayr zai zo ya mare ta, domin kalaman da tayi masa sun harzuka shi, yayi kuma muguwar kufula. : Caraf mutumin ya yi saurin sanya hannu ya rike shi, yace“Haba ‘yan samari, meya kai ka ga son nuna Kwanji akan diya mace? Wannan ai keta dokar Allah ne da ta makaranta, ko ka manta a inda ku ke ne?”
“Yallabai da ka barni na koya mata hankali gaba ba zata kuma jifan wani da irin wadannan kalaman ba, dama ire-iren masu kudin nan basu da wata tarbiyya, don ta ga tana hawa wannan motar shi ne zata tsaya tana raina mutane, a girme kayi Kanwa da ita ta wajen nawa shi ne za ta tsaya tana fada maka wannan maganar don bata samu tarbiyya a gida ba”.
Cikin masifa ta ce, “Kada Allah Yasa ya hakura din, ya zo ya dora hannunsa a kaina ya gani, ta nan ne zai gane cewa mu din bamu da tarbiyya, don wallahi sai na sa Ya Abba ya batar da kai, an neme ka an rasa, ta nan ne zaka gane cewa bamu samu tarbiyya ba. Dan rainin hankali kawai, nima bari na bude maka ido ka san bana shakkar nan”. Nan ta saki wani uban tsaki. (Security) na Karasowa gurin yana nufar gurin motar tata, kai tsaye shiga yayi ya yiwa
motar (key) ya matsar da ita, nan take mutane suka shiga wucewa abin su. Bin mutumin tayi da kallon mamaki, don ta ga wani irin isa da yake yi akan ta yadda har ya samu damar shigar mata mota ba tare da ta bashi izini ba. Haka ya dawo gabanta ya tsaya jama’a na wucewa suna ta mita, ta bude baki da niyyar yi masa magana kenan taji an Kwalla mata kira.
“Haana, lafiya dai na ganki a tsaye anan? Ko dama ku ne ku ka haddasa mana wannan (go-_ slow) din?”
Juyowa tayi ta yi dan murmushin Karfin hali, ta ce. . . Bintu barni kawai, wallahi nice kinga mutumin da ya janyo min bacin ran nan, takaici na ma wannan mugun (lecturer) din, don naji irin yadda aka ce yana da ra’ayi, ga shegen jin kai da (rules). (Please) parker ina zuwa mu wuce tare”. .
Ta juyo ta kalli mutumin taje ta ciro (key) din motar ta kama hannunsa ta dora masa akai, ta ce.
“Malam ga (key) din nan ka san yadda zaka yi ka gyara min kafin na fito daga (lecture) don ba zan yarda ba, gaba ba zaka sake yiwa wata haka ba, don babu abin da nafi jin haushi . kamar na rasa (class) din nan, don idan na rasa sai nayi maka Allah Ya isa”. Tana gama fada masa haka tayi gaba abinta, taje ta shiga motar Bintu suka yi ciki. Tun da suk*ma shigo cikin (Faculty) dinsu na (Law) duk inda .haana ta gifta sai kaji an ambaci sunanta, cikin fara’a ta shiga daga musu hannu, . wasu ta sansu wasu kuma ba ta sansu ba, amma haka zata nuna kamar ta sanka, domin bata da jinkai ko nuna ita’yar wanice. Haana tayi suna a cikin (school) din, -.. musamman cikin (Faculty) dinsu don tayi suna sosai don tsabar kwanyar da take da shi, hakan sai yasa malaman su babu wanda bai santa ba. Farin jini gurin jama’a sai dai godiya gurin Allah, domin kuwa Ya hore mata shi, babu wanda take Kyamata kowa nata ne duk wanda ya nuna yana sonta.Kallo daya zaka yi mata kasan ‘yar gidan ° manya ce, don idan ka ga yadda take da irin motocin da take hawa zaka yi tunanin zata yi tsananin -girman kai da nuna ita ‘yar wani ce, amma sam tsarinta ba haka yake ba, sauki ne da – ita, Sai dai idan mutum ya shiga gonarta nan ne zai gane irin kalarta, don bata daukan wargi da raini.
Sai dai tambarin da aka yiwa ‘yan (Departruint) dinsu cewa suna da jin kai da dagawa, don gani suke kaf makarantar idan ba law kake ba ba karatu ka shiga yi ba, sai daukar su masu jin kai. Banda wannan tambari nasu babu wani matsala da Haana take da jama’a da matuKar mutunta jama’a da nuna Kauna gare su, don da hakan ne yasa tayi farin jini gurin jama’ar da suke tare da ita, tana da yawan tausayi da taimakon wanda taga bashi da abu.
Tana shiga cikin (class) dinsu nan ta hango ‘yan (class) dinsu da sauri ta Karasa ta saki murmushi, tana zuwa ta soma sauke numfashi kamar wadda aka biyo da gudu. Sallama tayi musu suka amsa, bayan ta bawa kowa hannu sun gaisa, ta ce.
“Kai Allah na gode Maka, duk irin bata lokacin da nayi hakan bai sa wannan (lecturer) din ya zo ba, Allab Ne Ya duba zuciya ta”.
Zahra wadda ita ce shakikiyarta a cikin su, ta ce, Hmm! Allah Ya taimake ki kuwa, don wallahi yadda kika makara din nan da babu abin da zaki yi masa ya barki ki shigo masa aji, don baki ga mutumin ba, dan zafin kai ne ga jan aji”.
Tabe baki tayi ta ce, “Matsalar sace, amma dai zan yi KoKari na bashi hakuri ko zai barni nayi (test) din da ya baku jiya tunda ina da dalilin rashin zuwan nawa”.
Eh to, bana ce ba, sai dai ki jarraba”. Salma ta ce, “Zahra kin manta dai me ya ce jiyan? Babu (makeup) fah, ni dai wallahi har na fara tsorata da (lecture) dinsa don kada yaje ya jefar damu a (course) din nan mai dan banzan wuya”.
“Allah dai Ya taimake ni ya saurare ni. Hmmm! Ba ku tambaye ni ya akai na makara ba, _ kamar yadda muka rabu da ku sai na riga ku zuwa”
Saudat ta ce, “Nima nayi mamakin hakan da ya faru, to ya aka yi?” Zahra ta ce, “haana kece fa, idan ki ka fadi abu wata rana sai dai anga kin yi sannan.
Nan take ta kwashe ta fada musu duk abinda ya hada su da mutumin nan ta fada komai, a take suka zaro idanu waje suka ce. Haana, kina da hankali kuwa? Baki san mutum ba ki dauki (key_ din motarki ki damKa masa a Hannu? Lallai kin cika wawiya, shi kuwa Wanga mutum idan ba na Allah bane to shi kuwa zai yi murna da hakn, don Kila tsohuwar motar sa zai bari a wajen ya dauke taki”.
Nan take Haana ta ji gabanta ya fadi, don da bata yi tunanin zai gudu da motar ba ko dai wani zaton, tayi ganganci. Take ta gane ba Karamin shirme ta aikata ba. A ranta ta tuna cewa sabuwar motar Ya Abban ta ce da aka siyo masa ko ganinta bai yi ba ta saka sai ta hau ta dana kafin ya zo, to gashi kuma babu wanda yasan ta hau daga shi Ya Abban sai Granny da ta fadawa, don ta san idan ta fadawa Amminta ba lallai ne ta bari ta hau masa motar ba.
Babu wanda ya janyo mata haka sai wannan sabon (lecturer) din da aka tsorata ta da
baudadden ra’ayinsa, ta ayyana hekan cikin ranta.
A bayyare kuma tace da su, “Gaskiya nayi kuskure, amma bana jin kamar zai gudu da motar, kai ko ma dai me ya faru wannan mugun (lecturer) din ne ya janyo min, don ni har naji na tsane shi ma, kuma da wuya idan za muyi shiri da shi”. Zahra ta ce, “Tashi muje mu duba gurin ko yana nan”, Girgiza kai tayita ce, “A’a ki bari ya zo idan ya shigo sai mu nemi izini muje mu dawo, _ don kada mu tafi mu dawo ya hana mu shiga”. Salma ta ce, “Haana, ba irin mutanen da kika sani bane, Ka’idar sa idan ka shigo ba wani (excuse) har sai ya gama sannan za ka fita. Idan kuma ya shigo da (five minute) to ba zaka shigo ba. Idan ka fito to sai (next class). Tsaurin sa ya yi yawa, baki ga yadda aka cika (class) din ba yau? “Barshi kawai zan fada masa idan ya barni
to idan bai barai ba shi ne ya jiyo”.
Zahra ta ce, “Kema kin jiyo don kin fishi yin asara, tashi kawai ku zo muje komai ta fanjama fanjam”.
Hirar su suke sosai basu yi aune ba suka ji ajin duk anyi shiru, da sauri suka fara duve-dube, ashe shi ne ya shigo cikin sauri kowa ya shiga komawa gurin zaman sa. Haana dama ita ta dan juya baya bata san ma hakan yake faruwa ba, don basu saba yin haka ba. Zahra ce ta zungure ta, ta ce. Ke, mutumin ne fa ya shigo”Buda baki tayi tac me”Wa?”
Don har ta manta da cewar shi ne zai shiga, tana juyawa shi kuma yana mai da hankalinsa kan allon da ke manne jikin garu don soma rubuta (headline) abinda za su tattauna akai. Tsaki tayi ta ce, “Shi ya jiyo”. Da sauri Zahra take mata magana KasaKasa.
“Ke Haana ki yi a hankali, don baya son ana masa surutu, baki ji dokokin da muka fada miki ba, kada ki janyo ya kada mu waje” Juyowa ya yi yana dan dube-dube kamar ya dan jiyo alamun murya na tashi Kasa-Kasa, ganin ya juyo Zahra tayi sauri ta basar, tayi kamar ba ita ce ke magnar ba.
Haana kuwa dauke kai tayi bata ma dube shi ba, can dai sai ta juyo ta kalli inda yake jin ya yi shiru bai ce komai ba.
Mamaki ne Karara ya bayyana a fuskarta lokacin da suka yi ido hudu da (lecturer) din, nan take ta ji gabanta ya yanke ya fadi. Ba komai ne ya janyo haka ba sai gane shi da tayi,
ba kowa bane illa abokin fadanta a bakin (gate), mutumin da ya buga mata motar ta ne. Bude baki tayi domin nuna tsananin ~ mamakinta da ganinsa, ashe dama shi ne malamin nasu da ake fada ne? Yau ta shiga uku, ya zata yi da tarin tsaurin idanun da tsiwar da tayi masa dazu?” Shima kallon nata ya yi mai cike da mamaki, to amma sai ya Boye ya nuna kamar bai ganeta ba. Shiru (lecture hall) din ya yi sannan ya yi gyaran murya, ya shiga ya yi dan dube-duben sa cikin I-pad dinsa, sannan ya ce.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG