UMM ADIYYAH CHAPTER 56 BY AZIZA IDRIS GOMBE
Mun tsaya
Da gaske ne kenan?” Kai ta gyada masa, amma ta Kara da cewa. “Hakan ne amma dai nan din da ta zo kamar yadda ka ce ne, hutu ta zo yi.” Ta fada zancenta cike da harshen damo. “Yau kuma. To na gode, ayi hutu lafiya.” Ya fada yana murmushi.
Haka nan ya kau da maganar bai sake dagowa ba, suka shiga wasu hirarrakin, Www.bankinhausanovels.com.ng
sannan ya yi masu sallama, bayan ya shigowa yaran da wata Katuwar leda cike da tsaraba.
Lokacin da ta fito da gyarraren cakes din ta samu suna sallama, don haka ta kai su
mota ta leKo ta ce, “Sai anjima.”
Idanunsa ne suka sauka a kanta, ya gyacla mata kai ba tare da ya ce komai ba, tana
fita Adda Zubaida ta ce, “Ni ban ce kar kayi mata magana ba fa, na ga kun koma
zancen kurame ne.”
“Shi ya sa ba ki ga na yi ba ai, yanzu ina yi za ki fasssara. Ni na gaishe ku sai cikin
weekdays kuma, idan Allah ya kai mu.” “Allah Ya kai mu.” Www.bankinhausanovels.com.ng
3 29s 2k 2s 2 2 2 2k 2 os OK OK OK
Washegari ya sake dawowa, bai ce komai ba, nan ma ya gaishesu ya tafi, a daren
Umm Adiyya ta samu wayarsa daga bakuwar Lamba, kasancewar tun aurenta ta yi
deleting lambobin su duka. “Sunana Ahmad Tijjani Muhammad.”
“Ban san ka na amfani da dayan ba ai, ina wuni.”
“Lafiya Kalau, duk wanda ya kama ana amfani da shi. Yaya ‘yan Kiriniyarki?”
“Lafiyarsu Kalau, suna nan sun yi barci.”
Shiru ne mai tsawo ya ratsa tsakaninsu. Umm Adiyya dai tana jira ne ta ji me zai ce,
tunda dai ita ba ta ‘yar waya da shi, rabon da ta sa shi a idanu ma ta mance, banda
haduwarsu na barin ket, sai jifa-jifa take samun labarinsa wurin Adda Zubaida. Nan
ma idan hirar ya kawo ne, ko Kannensa mata idan sun zo gidan Addartata.
“Maman Walid ke facla min abinda ya faru.”
Wani tsinkewar gaba taji, rabon da ta ji ana mata jajen mutuwar aurenta har ta fara
mantawa, ko dai a kalleta ayi shiru ko a nuna ba ma san auren ya mutu ba, ko kuma
Www.bankinhausanovels.com.ng
ayi ta bin ta da kallon tausayi.
“Uhm, eh haka ne.”
“To Allah ya yi maku canji da abinda ya fi alkhairi, idan kuma akwai rabon samun
sulhu. Allah ya daidaita tsakaninku.” “Ameen Ya Rabbi, na gode sosai.” “Ta ce min hutu ki ka zo yi.”
Dariya ta yi ta ce, “Masters dina na ke yi anan.”
“To fa Karamar Injiniya ba za ta bar mana sudiin bokon ba. Allah ya bada sa’a ya
taimaka.”
“Ameen na gode.”
“Sai da safe na gaisheki. A shafa kan yaran.” “Ka na fadia, sai a zaci zuga guda ne.”
“Eh to kadfan ne ai ake fatan su yi albarka.”
Kashe wayar ta yi, ta ga yana neman ya shagala da zarcewa da hirar. Amma
wannan ba ta sani ba, yana Claya daga cikin hirarraki da yawa da za su yi a kan
waya, ba na komai ba, sai na gaisuwa haka nan a ganinta. Har ya koma Abujansa.
Lokaci-lokaci yana kira su gaisa.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Of oi 9 oe ok oe ok 2 oe a
Ta fito daga Lectures ranar da yamma ne kawai ta yi turus! Ta tsaya. Idanunta suka
bude kacfan. Sannan ta lalubo murmushi ta dorawa fuskarta, ta isa inda yake tsaye.
Sanye yake cikin shadda ruwan Kasa jamfar riga da wando da hular da ta zauna a
kansa cif-cif! “Ina wuni.” “Lafiya Kalau, yaya karatu?”
“Alhamdulillah! Kai ma ka jona makarantar tamu ne ko aiki ka fara a nan?”
“A‘a na zo wurin abokina ne, na hango ki na fitowa, shi ya sa na tsaya jiranki. Kin
gama ne?”
“Eh, mun gama dai na yau kam.”
“Kin zo da motarki?” Kai ta girgiza masa. “Mu je to na ajiyeki.”
“Da ka bar shi ma kawai, akwai wata Kawata yanzu Za ta fito za ta ajiye ni a gida.”
“T insist.”
Murmushi ta yi, tana Gaga kanta ta hango Malam Yusuf. “Uhmm! Amma za ka iya
jirana minti biyar? Ga can supervisor nan na hango shi, dama na shiga wurinsa na
Www.bankinhausanovels.com.ng
samu baya nan. Bari na je na gan shi.”
“Ba damuwa ki dauki lokacinki, zan jiraki.” Da sauri ta juya ta Karawa ‘yan Kafafunta sauri
har ta same shi daf, da shiga Kofa, ta san za ta iya juyawa ta neme shi, ta rasa
kuma ba ta son shiga ofis dinsa, wannan ya sa ta ce, “Assalamualaikum! Ina wuni
Malam?”
“Umm Adiyya, ki na lafiya?” Ya fada lokacin da ya can tsaya. “Wani abu ne?” Ya facia tamkar bai ji dadiin ganinta ba.
“Malam na kawo maka gyaran da kayi min ne ka Kara dubawa, na shiga ban
sameka ba dfazu.”” “Okay, shigo na gani.”
Kamar ta fasa ihu take ji, yana tafiya tana bayansa, ta shiga neman lambar Maman
Abul, don ta shigo ta kawo mata Clauki.
Haka ya Karaci surutansa, ya mika mata. “Na kiraki shekaran jiya.”
Eh ya kira sau biyar, duka ta kife fuskar wayar ma har ta gaji da kira. Ta san ba abin
makaranta bane zai sa ya kirata Karfe sha clayan dare. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ba na kusa ne.”
“! believe, wayarki tana karanta (Missed calls) ai?”
“Eh ta kan yi wani lokaci, ka san gida da yara, sai su taba maka waya ma ba ka sani
ba.”
“To shi kenan, tunda ga ki a nan, zan ma iya fada miki dalilin yin wayar. A ina
maganarmu ta kwana?”
Umm Adiyya ta bude baki da idanu da hanci tana ganin ikon Allah.
“Malam ana jira na.” Ta facfla, ta sa kai za ta juya.
“Kin manta abin naki.” Ya fada hade da mika mata hard copy na gyaran da ta kai
masa. Ta sa hannu za ta karba ne, ta ji ya riKe takardar gam! “Ki rinKa daukar
waya.”
Ta gaza yarda da batun mutumin nan, yana nufin zai yi mata abinda yake so ne, don
tana kwas dinsa kuma yana kula da ayyukanta?
“Malam, na riga na fito, ban boye maka ba, babu alaKar da za ta yiwu tsakaninmu,
da ta wuce ta Caliba da Malami, koda kuwa za ka kada ni a courses Clin da na ke yi
ne, ko kuwa ka hanani gama makarantar nan.
Hakan bai dameni ba, amsata daya ce har gobe. A‘a ba na sonka. Ba zan kuma iya
ba ka dama ba. Allah ya hada kowa da rabonsa. Amma zan fi so maganar so ko
Www.bankinhausanovels.com.ng
aure ko waya ko ma meye da bai shafi aikinka ba, ka ajiye shi a gefe, mu yi abinda
ya hada mu a nan, da fatan mun samu fahimta a kan hakan?” Ta Karasa idanunta
kar! A kansa.
36 OK 26 28 2k 2K OK KK OK KK
BABI NA TALATIN DA BAKWAI
Sake mata takardar ya yi, sannan ta gyada kanta ta fice a ofishin. Da ta fito, sai da
ta girgiza, ta gaza yarda ita ta fadi duk abubuwan da ta fadla yanzu, amma sai ta ji
kamar tana shawagi a iska, don samun sassauci da ‘yanci.
Yana jingine da jikin Kofar motar, fuskarsa makale da murmushi har ta iso inda yake
tsaye, yana jiranta.
“Ban yi tsammanin maganar ta tafi da dadi ba.” Ya fada yana kallon yadda fuskarta
ta dagule.
“Yi hakuri na Hata maka lokaci, kawai dai ban san me ya Sa…”
Shiga motar suka yi, ya tayar sannan ya ce, “Ba sai kin yi bayani ba na fahimta,
sha’ani na makaranta. So, yaya su Maami?”
“Lafiyarsu Kalau, ta ce ta daina ganinka kwatakwata.”
Www.bankinhausanovels.com.ng
Murmushi ya yi ya maida hankalinsa kan titi. “Na ji kin koma karatu, hakan yana da
kyau ai.”
“Ka yi aure.” Ta facla tana kallon titin da ke gabansu.
Murmushi ya yi, ya kawar da kansa kacfan, sannan ya juyo ya kalleta, “Yes, I am
married.”
“Har ma da ‘yarku, tana kama da kai, kyakkyawa da ita ‘yar dagwas. Na ga hotonta
a wayar Maman Walid.” Ta fada murmushi a
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG